Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

BOOK 3

Maradams Book 3 Complete Hausa Novel 5,820 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 1

Wani irin abu ya dinga jin yana bin jijiyoyin jikinsa ,zuciyarsa kuwa banda bugawa da matsanancin karfin babu abinda take tmkr zata fasa qirjinsa ta fito waje haka ya dinga ji ,"tabbas wannan fuskar fuskar yarinyar mafarkinsa ce tsaye a gabansa ."suna cikin wannan halin some ta turo kofar office din ta shigo cikin tsananin tashin hankali, muryarta na rawa ta soma magana cike da tsoro "me yasa kike da matsala? "maryama hussein mai ya shigo dake cikin  office din nan bayan na fad'a miki mai gida baya da bukatar ganinki?"  "sir please kayi hakuri ban san lokacin data shigo ba "ya d'ago idanunshi wad'an da suka rikid'e zuwa ja ya saukesu akan some dake rawar murya da jiki "kayi hakuri sir yarinyar ce tana da taurin kai na fad'a mata baka da bukatar ganinta am very sorry sir." "malama ki gyara kalamanki dan suna sani jin wani iri acikin kwakwaluwata ,na shigo ko aka shigo dani ?" Idanunshi dake kan some ya dauke ya maidasu kan maryama  caraf sukayi 4 eyes da ata ido cikin ido suke kallon juna wani irin zirrrr ya soma ji a gbdy sansar jikinsa ,wani irin kallo mai tafiyar da ruhi ya dinga mata , a zuciyarta tace" ko me yasa yake min irin wannan kallon kamar zai cinyeni ?saurin cire kwayar idanunta cikin nashi sakamakon bugawar da zuciyarta ta fara yi ."

Sosai ya sakankace a kallonta har sai da some ta soma zargin wani abu akan mai gidan nata dan bata ta'ba ganin macen da yayiwa irin kallon da yake mata ba hasalima shi mutun ne da bai fiyye son kallon mata ba , ta juya ta kalli salim dake tsaye shima ata yake kallo fuskarsa d'auke da tarin damuwa,sautin muryarta ce ta dawo dasu natsuwarsu ," kisani ko nace kusani gabd'aynku maryama tafi karfin wulakanci sannan tafi karfin tayi aiki akarkashin mutane irinku marasa mutunci da tausayi ."gaban ATA yayi wani irin  mummunar fad'uwar da bai ta'ba jin irinsa ba sai a yau din nan ."yay mugun  tsura mata kwayar idanunshi yana kallonta nan take yaji maganarta tayi balain d'aga masa hankali 'yayi taku biyu zuwa inda take tsaye jikinta na kyarma sai dai ya kasa cewa komai dan koma yace zai yi magana a halin da yake ciki bakinsa bazai iya furta komai ba "an fi karfina ne yasa kuka sake ganin qafafuwana acikin kamfaniku dan wlh a karon kaina bazan ta'ba turo maku sakon neman aiki ba tunda nasan halinku bare har na tako domin yin aiki ".tana gama fad'ar haka kan ATA yayi wani irin  tsarawa tare da sauke wani zazzafan numfashi ya kai tattausan tafin hannunsa daidai saitin zuciyarsa da  ke mugun bugawa da sauri sauri dan tun data soma magana qirjinsa yake bugawa fiyye da kaida "kisani ko nace  kusani  maryama tafi karfin wulakanci sannan tafi karfin tayi aiki akarkashin mutane irinku marasa mutunci da tausayi shine maganar da yake ta yiwa ata yawo acikin kwakwaluwarsa ."

maryama ta sauke idanunta da suke a rine tsabar tashin hankalin da take ciki akan ATA dake tsaye wanda ya tsareta da tsumammun idanunshi masu firgitarwa hakan yasa ta kawar da fuskarta gefe sannan ta fara fad'ar abinda take son fad'a "karo na  biyu kenan kana ci min mutunci laifin me nayi maka ?" ta tambayesa tare da d'ago fuskarta ta zuba masa tana mai danne kwalla dake qoqarin zubo mata "baka son ganina arayuwarka ko  "?ta fad'a tana sheshekar kuka " wallahi ban san me yasa na yarda na kawo kaina inda zaa tozartani ba ."subhallah !ata ya furta a kasan ransa yana jin kamar ya qara taku biyu din da yayi saura a tsakaninsu ya fixgota yayi mata kyakkyawan riko tare da mata masauki a faffad'an qirjinsa "what the hell is going on?me yasa kike fad'awa mai gida haka instead ki bada hakuri ko zai taimaka ya d'aukeki aiki sannan ki gyara kuskurenki shine zaki zauna kina fad'awa mutane magana I can't tolerate that "saboda me zan bada hakuri ?"laifin me nayi da zan bada hakuri ?Ko kuma kuskuren me zan gyara idan kina wasa ne to ki daina dan babu hakurin da zan bayar dan kawai nayi aiki daku  "cike da tashin hankali ata ya fixgar da   numfashi sannan ya motsa labbansa  a hankali ya soma magana "some !"

jikin some  na kyamar ta amsa da "yes sir! leave.."!
"Okay sir am sorry  !ta juya da sauri ta nufi kofar fita hakan da maryama taji yasa ta biyo ta bayansa  ta  ra'ba ta gefensa zata fita har tana zozon jikinsa wani abu yaji mai kama da wutar lantarji ya ziyarci gabad'aya ilahirin jikinsa  ,fuskarsa dake a murtuke ya tsaida akanta yayinda da sauri salim ya biyota ya  sha gabanta yana cewa "dan Allah maryama ki tsaya ki natsu ki kwantar da hankali duk abinda kike bukata acikin kamfanin nan a shirye muke zaa miki shi amman ki dan bamu  dama zamuyi magana mai mahimanci dake ."nan da nan 'bacin ran maryama ya sake nunnukuwa zuciyarta ta dinga tafarfasa bata ce masa komai ba sai dai ta balain had'e fuskarta sannan a  natse  ta ra'ba gefensa ya sake shan gabanta "a gaskiya raina ya fara 'baci da abinda kake min sannan zuciyata ta fara tafarfasa ,ni mace ce mai tsnanin hakuri  karka bari nayi maka abinda ban ta'ba yi wa wani mahaluki a duniyar nan ba ".
"me zaka fad'a min ko kuma nace me zaku me bayan wulakanci da tozarcin da kuka min ?nasani shima ATA daya aikata haka bai san ko ke.."enough please bana son jin komai matsa kawai ka bani hanya na wuce bana bukatar taimakonku."ta fad'a tana mai sake ra'bawa gefensa ya sake shan gabanta ai kuwa zuciya ta rufeta bata san sanda ta d'aga hannunta ba ji kake tas ..! ta sauke masa wani lafiyayyen mari   akan Kuncinsa a gigice ya dafe kuncinsa yana kallonta cike da tsananin tashin hankali. ta juya a matukar fusace tana kallon ATA dake tsaye tamkar wanda aka dasashi a wajen tsabar tashin hankali "ka fad'a masa ya fita rayuwata ya bani hanya na kama gabana". yadda ta tsura masa ido tana kallonsa cikin 'bacin rai haka shima ATA kallonta yake baya ko kifta idanunshi ga wani kalar tashin hankali dake shigarsa yana bin ilahirin jinin jikinsa ."bai ta'ba jin yayi laifi yayi nadama ba sai a yau ."

"Ka fad'a masa ya bani hanya na wuce na kama gabana."tayi maganar muryarta cike da rauni a hankali ya furzar da wani iskan mai zafi daga bakinsa cikin wani irin salon magana tmkr bashi da laka  yace "salim barta ta wuce !"yana gama fad'ar haka ya juya masu baya jin haka yasa salim ya matsa gefe ya bata hanya batare da ya sake cewa komai ba ,batare da 'bata lokaci ba maryama ta gyara zaman jakarta ta fice daga office din tana jan tsaki ,jiki a sanyaye maryama take taku tamkar bata son taka qasa."tasa hannu ta goge hawayen dake tsiyaya daga cikin kwarnin idanunta ta fita daga haraban ma'aikatan inda zuciyarta ke wani irin bugawa da karfin gaske ."tana tsaye a gefen  get din ma'aikatan jiran abun hawa sai ga motar ammar kallo d'aya yayi mata ya fahimci tana cikin damuwa nan take shima yaji damuwa ta shigesa umarni tsayuwa ya bawa direbansa tun kafin ya shigar da  kan motar ciki ." direba bai gama daidaita tsayuwarsa ba amar  ya fito ya tako ya sameta har inda take tsaye tana goge hawayen dake tsiyaya "maryama !ya kira sunanta ta d'ago da sauri ta tsura masa ido "lafiya kike tsaye a bakin titi kina kuka ?yayi mata tambayar cikin tsananin damuwa "ba wannan mara mutuncin mai kamfanin ATA creation din bane .."sai hawaye sharr suka zubo mata dan haka  ta kasa cigaba da magana "zo mu shiga daga ciki Kiyi min bayani abinda ya faru ".ta girgiza masa kai "har abada oga amar qafafuwana bazasu sake shiga cikin wannan ma'aikatar ba "tana gama fadar haka ta juya ta soma tafiya tana bin gefen titi da sauri ya biyota ya sha gabanta "fad'a min wanda ya 'bata miki rai ? yayi mata tmbyr ne domin ya tabbatar da abinda yake son sani "mai kamfanin da kanshi sai wani da bansan ko waye ba sun taru sun wulakantani sun tozartani "mai kamfanin ATA creation da kanshi ?ya sake tmbyrta cike da mamaki ta gyda masa kai alamun "eh! yana kallonta ta ra'ba gefensa ta wuce ta cigaba da tafiya da kallo ya bita dashi kafin ya juya da sauri ya nufi cikin ma'aikatan."

Cike da matsanancin tashin hankali ata ya zagaya ya koma mazauninsa yana sauke wani zazzafan numafshi sai dai ya kasa zama  ya d'auki wani  file da kwayar idanunshi ya kai garesa ya soma dubawa  cikin tsananin tashin hankali yake amman dake shi din nmjin  duniya  ne bazaka ta'ba iya gane hakan attare dashi ba sai dai acikin zuciyarsa kuka yake yi irin kukan da bashi da mafuta "me yasa rayuwarsa take shiga rud'ani?"me yasa abubuwa suke faruwa dashi ne ?"wannan wani irin tashin hankali ne mai sarkakkiya?yarinyar nan itace yarinyar da kasa aka kora  a sakonni da suka gabata  "I know? ATA ya fad'a atakaice ya na mai ajiye file din hannunsa ya sake zagayowa ya tsaya cak  a tsakiyar office din ya zira hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa yana jin wani irin tashin hankali mara misaltuwa na kusanto rayuwarsa ga ciwon da kansa yake yaki dainawa sai ma cigaba da sarawa yake  ." salim ya tsaya sororo yana kallonsa  tamkar mai shirin yin kuka "kace ka sani ?"yes of course na sani amman  a yanzu  kenan bayan nasa an koreta naga kana magana hankalinka kwance yarinyar mafarkinka ce fa ?"I know! salim ya girgiza kai yana kallonsa ."

ata ya kallesa a d'age yace  "sannu da shan mari na qoqarin tsaidaita ai da kasani ka barta ta wuce  ."ya fad'a tare da samu guri ya zauna akan  kujerar sofa dake office din ya daura qafarsa d'aya akan d'aya yana girgizawa tmkr baya tare da wata damuwa salim  ya shafa kuncinsa  daidai inda yasha mari yace" gasky na maru ,mari biyu kenan na sha a hannunta".  ata ya kallesa da tsumammun idanunshi dake cike da tashin hankali "tayi min d'aya a waje kafin na shigo daita yanzu kuma tayi min d'aya a gabanka "wani irin kuncin ya sake mamaye zuciyar ata dan shi kad'ai yasan halin da yake ciki "dan allah ka tashi  muje ka tsaidaita idan ta tafi bakasan inda zaka sake ganinta ba ."wa kenan zai tashi ?ya tsare salim da kwayar  idanunshi masu firgitarwa "wai ni !?ya sake tambayesa  yana nuna qirjinsa da yatsan hannunsa "ka sanni kasan halina hakazalika duk wanda yake tare dani yasan ina mutuwar son yarinyar nan , nayi hauka a bayanta amman  bazan yi haukan soyayya a gabanta ba ."matsalata da kai kenan girman kai wallahi tun wuri ka dawo cikin hankalinka shekara da shekaru kana neman yarinya amman ka ganta har ka wani tsaya jin kai? " ka sani  salim wannan ajinina yake" yana gama fad'ar haka ya mike tsaye "kasan wani abu na had'u daita kwanaki baya acikin ma'aikatan nan sai dai sanye da nikaf na ganta amamn naji ajikinta cewar itace sai dai wannan mugun abun da take amfani dashi ya karyar min da gwiwa  har na tsaida zuciyata akan ba ita bace ina ganin wannan mugun abun da take rufe fuskarta dashi ne yasa nayita shan wahalar nemanta wata kila da bata sakawa da iwar haka munyi aure har ma ....."shiru yayi ya kasa qarasa maganarsa yana jan tsaki "

"har ma me ? salim ya tamabyesa a d'age ata yayi shiru ya kasa cewa komai yana mai  cizan lip's dinsa da karfi "da  har kayi mata ciki ba ?ata ya kallesa kawai batare da yace kala ba "nasan abinda kake qoqarin kace kenan "wannan kuma fad'arka ce ba tawa ba ." ya zarce da cewa "wancan zanen hotona  da kake ta magana akansa itace ta zana shi ya nuna masa zanen da yatsan hannunsa "woooo gsky yarinyar ta had'u sosai yanzu ya zaayi musan gidan su ?bai bashi amsar tambayarsa ba ya shiga wata magana " kasan yarinyar nan muguwar yar rainin sense ce itace fa yarinyar da muka bukaci tayi aiki  akarshin Z&A daman ni tun tuni jikina ya bani itace "congratulations! na me kenan ?na ganinta da kayi ga kyau ga ilimi ga baiwa wacce ba kowa yake daita ba ina tayaka murna domin kuwa lokacin farin cikinka ne yazo "ka daina murna salim dan kuwa  matar aure ce  .."yana gama fad'ar haka ya juya masa baya ."what?ya furta da karfi shi kuwa ata kasa juyowa yayi sai ma  numfashi da yake janyowa da kyar tmkr mai cutar asthma duk abinda yake dauriya ce kawai irin tashi amman da zaa bud'e qirjinsa da an hadu da gimgima gimman tashin hankali."

Jikin salim na wani irin kyarma yace "matar aure kace fa ? shiru ata yayi masa yana kokuwa da numfashinsa dake qoqarin barin ganganr jikinsa "wani irin matar aure adam ?still shiru ata yayi "dan girman allah ka juyo kayi min bayani ta yadda zan fahimceka still shiru yayi tamkar ba magana yake masa ba  "da gaske matar aure ce maryama ?"tabbas matar aure ce  salim !suka jiyo murya daga bayansu wanda yasa suka juyo atare amar suka gani tsaye  fuskarsa dauke da damuwa sanye cikin brown t shirt da blook trouser hannunwansa rike da wasu takardu da alamun saka hannun ata ne ya kawoshi  ."
Ahankali ata ya kai hannunsa yana shafa goshinsa yana ciza lip's dinsa da karfi,da sauri  salim ya qarasa ga ammar  tare da dafa kafad'ansa yana dubansa "yaakayi kasan matar aure ce ?ammar ya zame kafadansa ya soma taku acikin office din ya isa kusa da ata "nasan komai akan maryama ,yadda kasan ata na bulayin nemanta haka nima nake tayasa nemanta batare da saninsa ba kwatsam na ganta Z&A amatsayin mai bautar kasa na yita qoqarin su had'u  dashi saboda ina son nayi surprised dinsa  amman taurin kai irin nasa  ya hana "me yasa kayi masa  haka ammar ?me yasa bazan masa haka ba?" shi me yasa bai bukaci ganinta ko sau d'aya bane ."ai shi kullum acikin  matsla zai qare rayuwarsa ." ata ya kallesa idanunshi cike da tashin hankali gashi sun jazur tmkr garwashin wuta "yes kana min wani irin kallo bancin  kana da matsla da tuni ka sameta arayuwarka ".

"me yasa ka kasa gaya min cewar yarinyar mafarkina ce ?"you could have told me ammar da yanzu bata zama mallakin wani ba ata ya fad'a jikinsa a sanyaye "kasan karin maganar nan daake cewa jifan tsuntsu biyu da dotse daya shi nayita maka naso ka had'u daita tun kafin ta zama mallakin wani amman taurin kai da nuna isa da girman kai yasa kaki yarda dani saboda taurin kanka yasa ka rasata a rayuwarka."
"wallahi nayi imani a lokacin da zaka furta kana son maryama  zata kar'beka da hannu biyu amman  a yanzu maryama tafi  karfinka kai tafi kowa tsanarka yanzu wa gari ya waya ?shiru ata yayi yana zurfafa tunaninsa "tabbas ammar yayi iyakar qoqarinsa na ganin sun had'u daita amman yaki sai gashi a had'uwarsu akaron farko ya fad'i warwas "me yasa kayi min haka ammar ?me yasa baka kasheni kafin zuwan wannan ranar ba ,you could have kill me ammar ." ya qarasa maganar kamar zai yi kuka nunfashi ammar ya sauke you know I can't fause you,abinda kasani ne baa takuraka baayi maka dole akan komai sai abinda kaga dama ."

kallonsa yayi cikin tsananin bacin rai "okay babu damuwa na hakura daita a fusace ammar ya kallesa sannan ya cigaba da magana cikin zafin rai kamar shine mai son maryama din "karya kake kace ka hakura daita domin wannan yarinyar itace rayuwarka itace nasararka."itace natsuwarka idan babu ita acikin rayuwarka komai zai iya faruwa da kai " ta yaya zaka fad'a min haka bayan tun daaka haifeni nake tare da nasarata "da farko zuciyarka na tsananin sonta ,abu na biyu zuciyarka na bukatar tayi aiki daita ,abu na uku ka rasata kasancewar matar aure ce , abu na hud'u gashi ta tsaneka" wadan nan abubuwan zasu shafi lafiyarka da komai naka kaga ka rasa nasararka ,to yanzu sai ya kenan? "sai na mutu me kake nufi  ?ammar yayi shiru yana masa duban tsanake kafin ahankali yace kana sonta ko kuwa jin matar wani ce ka hakura daita "yes I love her so much " to muddin kana sonta  sai ka shirya yadda zaka dawo daita cikin rayuwarka ko karkashinka amatsayin maaikayarka idan ba haka ba zaka cigaba da azabtar da zuciyarka da rayuwarka ne kawai a banza da wofi ."karka damu da wannan  karka damu da irin son da nake mata dan babu abinda zan iya yi kasancewarta matar wani ya ruguje komai da nake ji akanta kana nufin ka hakura daita  kenan ?tabbas ina sonta sosai amman na hakura   domin bazan yi muamula da matar wani ba ,yadda bazan yarda wani ya keta min haddin aurena  ba haka zalika bazan yiwa wani ba "ka bata aiki akarkashinka "shima bazanyi ba ."to kuwa zaka shiga matsla dan kimar data rage maka a idanun mutane zata rushe domin kuwa yanzu ne zakayi haukan so dan ka dinga ganin damuwa kenan akan damuwa sai ma idan ka gano irin son da takewa mijinta " me kake son yayi ammar byn kasan matar wani ce ? salim ya tambayesa cikin tsananin tashin hankali "ina son ya nuna shi din cikakken nmj ne ya fuskanci mijinta gaba da gaba ya kwace soyayyarsa daga hannun sa". salim ya girgiza masa kai yana masa kallon mara hankali da lissafi "taya zai yi haka ammar ? kaima fa da bakinka kace matar aure ce amman kake son ya shiga hurumin ubangiji ?

a matukar fusace ammar yace "ni kasan iyakar abinda nayi akansa?"kasan laifin dana aikata duk akan ya sameta?"enough ammar ka takaita mgnrka dan bazan iya komai ba kuma karka sake zuwa min da maganar makamanciyar haka idan ba haka ba  zan dagargazaka idan ka sake zuwa min da irin wannan maganar acikin alamarina tabbas ina sonta fiyye da komai  kuma itace rayuwata amman bazan yi wasa da hakin allah ba ,bazan shiga hurumin aure ba dan haka ka kula idan ba haka ba zamu samu matsala yana gama fad'ar hk ya juya ya soma daga kafafuwansa cikin zafin rai yana cewa "me yasa rayuwarta take shiga rudani ne ?me yasa abubuwa suke faruwa dani ne wannan wani irin tashin hankali ne?me yasa tazo a matsayin matar wani ?"ya Allah! ya furta yana buga table din gabansa da karfi nan take tarin takardun dake ajiye akai suka tarwatse ya runtse idanunshi gam tare da dunkule hannunsa daya ya dauke numfashinsa dan so yake numfashinsa ya bar gangar jikinsa ko ya huta da wannan tashin hankali ,"maganar duniya salim yayi masa amman yaki motsawa haka ma ammar  "both of you should leave my office !"sukaji sautin muryarsa cike da karsashi babu wanda yayi yunkurin barin office din illa salim daketa qoqarin kwantar masa da hankali shi kuwa ammar ko a jikinsa dan daman yayi masa haka ne dan yaji wani ciwo akanta "what are you stil doing here ?ya fad'a atakaice batare daya kallesu ba jiki a sanyaye suka soma ja da baya kafin ahankali daya byn daya suka bar office din ."

fitarsu ke da wuya  ya sauke wani wahalallen numfashi ."ahankali ya zauna jagwab akan kujera kwakwaluwarsa ce ta shiga caji na neman mafuta dan dole yasan abun yi anya kuwa bazai d'auki shawarar ammar ba ?ya furta hakan a fili zufa na tsatsafo masa a saman goshinsa da karan hancinsa ahankali ya soma magana shi kadai"adam dan dole ka nemawa kanka mafuta dan zuciyarka na tsananin son yarinyar nan akanta kai ba kowa bane ka tuna tun lokacin daka dauka kana dakon soyayyarta  tana da tasiri acikin rayuwarka kamar yadda ammar ya fad'a "to mai zanyi ?mai zanyi ?!!yayiwa kanshi tambayar da bashi da mai bashi amsa shiru yayi yayinda ya maida idanunshi ya runtse gam yana jin wani irin zafi mai tarwatsa  sansar jiki."yayinda bangaren salim da ammar kuwa tautaunawa suke akan abinda ya faru salim ya dubi ammar dake gefensa  hankalinsa a matukar tashe ya cigaba da magana "a zahirin gaskiya ammar baka kyauta ba sam sam bakayi wa adam adalci ba kafa san komai akanshi tun daga tahirin mafarkinsa irin tashin hankalin daya shiga alokacin da zaa aura masa maryam kuma kasan duk akanta ya kasa bawa matan dake mutuwar sonshi dama amman sai kayi masa haka kai da kamata yayi ka d'aukota ka kai masa ita ba sai kayi masa surprise ba   "kai dan allah naga ka damu dayawa yarinyar fa bata da aure yanzu amman ta ta'ba yin aure ."yana gama fad'ar haka ya cigaba da tafiya da sauri salim ya biyosa ya sha gabansa yana cewa "da gaske ammar ?murmushi ammar yayi yace "wallahi babu aure yanzu akanta nan dai ya zayyana masa komai daya faru daita bari naje na fad'a masa salim ya juya zai koma ammar ya rikosa "ka barshi tukun  zan fad'a masa da kaina amman sai naga karfin soyayyarsa gareta, ba dai yace ya hakura ba ?zan gani da gaske zai iya hakura daita kamar yadda ya saba hakura da komai ." da kallo salim ya bishi dashi fuskarsa dauke da murmushi yana mai qara godiya ga allah daya sa maryama ba matar aure bace ."

a qalla ata ya kusan minti talatin zaune yana nazarin maganar ammar wanda zuciyarsa take son ya dauka ahankali ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa tare da jan qaramin tsaki bai san me zaiyi ba idan yace zai dauki shawarar ammar "me kenan zaiyi ?"me ma yasa zai aikata haka ?duk runtsi duk wuya zai danne abinda yake ji akanta bazai ta'ba shiga gonar wani ba dakace babu auren kowa akanta ne to yana da tabbacin duk wanda yayi yunkurin aurenta to sai dai a bayan ransa amman yanzu bai ga abinda zai yi da wuce hakuri ba, yayi hakurin rashin ganinta abaya a yanzu kuma ya zame masa dole yayi hakuri da sabuwar qaddarar data samesa ,bama zai bari wani mahaluki yasan da zaman wannan labarin ba ". mikewa yayi cikin sanyi jiki zuciyarsa cike da rauni yana jin kamar ya zubar da kwalla ya shiga zagaye office din yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsare kafin ahankali ya shiga yamutsa gashin kanshi sannan ya koma kan kujera ya fara aiki akan system
zaune ata yake yana aiki amman sam tunaninta yaki barinsa ji yayi  kwata kwata  gara kawai ya cireta gbdy aransa ya huta ."

*****

A matukar jigace maryama ta karaso unguwarsu  da kyar qafafuwanta suka qaraso daita  cikin haraban gidansu  kai tsaye bangaren umma ta nufa tana layi inda ta iske su tare da hajiya grany suna ganinta a yanayin da take suka zabura suka mike cikin tsananin tashin hankali nan kuma suka shiga kallon kallo umma ta kalli hjy itama hjy ta kalleta a karshe suka maida hankalinsu ga maryama da kyar umma ta bud'e baki ta kira sunanta maryama !"da sauri ta qaraso gareta dan sam maryama babu kuzari ajikinta ai kuwa zubewa tayi ajikin umma ta fashe mata  da kuka tana kiran sunanta  umma .."
"Me..."me kuma ya   faru dake maryama "?cike da muryar kuka tace " sun wulakantani umma sun tozartani a qarshe kuma sun koreni a gurin aiki ta qarasa mgnr tana sake rushewa da wani sabon kuka Shikenan na sake rasa aikina ban san meke faruwa dani ba kamar ni kadai ce acikin  duniya ,laifin me nayi ?umma ki fad'a min meye laifina "kai kai karki sake cewa haka babu wani laifi da kikayi jarabawa ce ,itama hjy ta qaraso suka sakata a tsakiyarsu gbdy suka rud'e, umma na shafa mata kai hjy na shafa mata bayanta alamun rarrashi "akan wani dalili kenan suka koreki byn sun d'aukeki aiki ?" wai kawai dan nayi rejecting din ayyukansu wannan  kawai shine dalilin da yasa suka koreni byn ban yi hakan dan bana so yin aiki dasu  bane , nima ina son aikin nan amman alokacin suba'a  tafini bukatar shi allah ka gani nayi komai saboda kai ne."

" kun gani ba !shikenan allah ya amsa adduata ba ke uwar yan kankaba yau ga abinda gwaninta ya jawo miki sarkin iya taimako cewar Aunty hasana data fito daga kitchen ".haba hasana haba Hasana !dame kike son yarinyar nan taji ?idan bazaki mata addua ba ai  bai dace Ki fad'a mata haka ba."  ta kwabe fuska koma dai menene tunda ta rasa aikin ai shikenan bukatata  ta biya .ni a gurina wannan jarabawar daga allah ne kuma yana sane da komai bari zanje ma'aikatan da kaina naga mai kamfanin inji cewar umma "a'a umma karkije ,karki wani wahalar da kanki akan zuwa wajensu kawai suje su wulakanki a banza kamar yadda suka wulakantani "a'a bazasu wulakantani ba hakuri zan basu maryama "a'a ban yarda ba kuma wallahi ko kinje bazan qara komawa wannan kamfanin ba da sunan aiki bayan sun gama wulakantani sun tozartani har fa na fara aiki umma suka koreni basu ma tsaya sun fahimceni ba wai da gangan naki aikin dasu , wallahi banason aikin nan kuma kema bazan barki kije koina ba kuma ko zan mutu babu aiki bazan qara zuwa wannan kamfanin ba duk wannan maganar tanayi ne tana kuka har da shesheka "

umma ta rungumeta sosai ajikinta tana rarrashinta "kiyi hakuri maryama in sha allahu zaki samu sausauci ki cigaba da addau lokacin wahalarki  ta kusan zuwa karshe da izinin allah Aunty Hasana ta kallesu tana turo  masu baki alamun zund'e aranta tace "kwayi kwa gama idan wannan tsinanniyar yarinyar ce mai kashin tsiya ai duk inda arziki yake sai an korota ,sosai umma da hjy suka dinga rarrashinta har hankalinta ya d'an kwanta "yanzu umma kina ganin wata rana zan fita cikin wannan wahalar ?"sosai kuwa maryama  zaki fita mana wannan ai duk matakin d'aukaka ne amman fa idan kika d'aure kika d'aina fadar duk abinda yazo bakinki duk maseefar data samu bawa baa son yana yawo fad'ar abinda bai dace ba,abinda ake so mutun ya  yawaita furtawa inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ko lallaha illa anta subuhanaka inni kuntun minal zalim, ya hayyu ya qayyum ya zaljalalu wal ikram da sannu allah zai wanke miki zuciyarki da farinciki
."maryama ta share hawayenta ta zauna sosai a tsakiyarsu tana jin damuwarta ta yaye, ta kamo hannu umma cikin nata "wallahi umma  bakiga kamfanin ba komai a tsare kuma na dade  ina neman aiki a gurin tun alokacin da yaya sadam yaki amincewa da yin aikina  dole ce tasa na barwa subai'a wancan aikin "karki damu  nayi imani zaki samu aiki wanda yafi wanda kika rasa  Ke dai ki rike allah da adduar allah zai bi bayanmu .maryama tayi cikin jikin umma tace "Allah yasa ummah ina sonki mamana murmushi umma tayi tace "nima ina sonki maryama in sha allahu zaki ga haske arayuwarki "ummanki kawai kike so maryama nifa ?hjy ta fad'a tana dungure mata kai lumshe idanunta tayi tana dariya suma dai dariyar sukayi ."

*****

ATA na zaune  yana aikin  tura sako wayarsa ta dauki ringing ya dauki wayar ya manna a kunnesa yana lumshe ido  "yes kuna magana dashi ,okay kuna bukatar kaya new design ok just a second cewar ATA nan take ya kira sunan sectary ,sannan ya cigaba da abinda yake da sauri ta shigo  ta tsaya tana cewa "sir ! ya katse kiran byn ta shigo still ya cigaba da daddana system "mutumin dana gama waya dashi sabon  customer ne  yana bukatar kaya sabbin design dan haka Kiyi kokari ki hada Kan masu fresh design da muke dasu su bamu design masu kyau ayi abinda sabon customer zai ji dadi fatan kin fahimta "yes sir ."ko mu gwada sabbin dauka mugani ? " Eh hakan ma yayi domin muga kwarewarsu " okay sir "ta fita da sauri "maryama hussein ?!ya furta sunan a natse yana danna keyboard din system dinsa da karfi sannan ya cire hannunsa ya jingina jikinsa da kujerar da yake zaune yana jujuya jikinsa "waye mijinta a wani unguwa  take ?da gaske dai idan bai dauki shawarar ammar ba ya rasa natsuwa kenan kuma har abada dan ya tabbatar wa kanshi bazai iya rayuwa babu ita ba"waye mijinta a wani unguwa take duk yana bukatar yasani amman dole yabi komai ahankali darajan auren da take  dashi  ." amman dai zai nemi ammar din dan yana son yasan wani abu a game daita kafin yasan abun yi ."

Cikin kankani lokaci sababbin ma'aikatan suka hallarar a cikin officer dinsa kowannensu rike da takardar zane ya yunkura ya mike da kyar ya zagayo daya bayan daya ya dinga amsa yana dubawa sai dai gabadaya babu wanda yayi masa acikin zanensu . yaja qaramin tsaki ya tsaya ya rike kugunsa yana aika masu da wani mugun kallo mai tattare da abu biyu ,abu na farko damuwar da yake ciki abu na biyu kuma takaicin basu yi masa abinda yake so ba "wannan shine iya kwarewarku?shiru sukai gaba dayansu zuciyarsu cike da matsanancin tsoro kallonsa kawai yana firgita da mutun bare kuma maganarsa cikin zafin rai ko waye kai sai kaji fargaba "ban d'aukeku aiki dan biyaku batare da kun iya komai ba ,na daukeku né saboda kunce kun iya wannan shine karshen iyawarku ?ya sake jefa masu tamabyar data sake gigitasu suka ji kamar su falla da gudu amman babu hali ."wallahi duk na daukeku né saboda best design not nonsense ya fad'a a matukar tsawace  ." sannan ya maida idanunshi Kan sactry" some can you see your self ina gwajin da kikace kinyi masu ?"sir duk angwadasu  "most of the...."

"Culmdown ata ! aka fada tare da turo kofar office din ,shiru yayi yana dago tsumammun idanunshi zuwa kofar shigowa ganin sultana yasa ransa ya qara baci ,ya lumshe idanunshi yana furzar d iska mai zafi  daga bakinsa fuskan natashi babu annuri ko daya sultana ta qaraso har gabansa hannuta rike da farar takarda "nazo da abinda kowa ya kasa kalli nan kaga" ta fada tana jujjuya masa jiki tare da kai takardar gabansa "kalli irin kwarewata nasan wannan ne exactly abinda kake bukata? shiru yayi zuciyarsa na wani irin tuttukin bakinciki "Listing !this is my last warnin karki kara shigo min office batare da kinyi knowking ba  sannan idan zaki kirani kisa girmamawa call me with sir ..."yana gama fad'ar hk ya juya  da sauri zai barta tai saurin cewa " okay sir !ta fad'a tana masa fari da idanu wanda ko kadan bai girgiza zuciyar ATA  ba sai ma qara tsanarta da yayi "my design ! ta furta cikin salon jan hankali tana duban farar takardar dake rike a hannunta a kaikaice ya juyo ya fixge takarda daga hannunta ya tsurawa zanen tsumammun idanunshi dake cike da tashin hankali yana karewa zanen kallo yayinda ta cigaba da juya  masa jikinta tana murmushi tana kallonsa sai dai gabanta banda dukan uku uku babu abind yake ."

Wani irin dariya ne yaso kufce masa saboda ganin abinda take takamar ta zana awajensa shi da  jagwal gwalo bashi da wani bambamci amman ya danne  dan dariya bata kamace masa ba a halin da yake ciki sai dai  kana kallon fuskarsa zaka fahimci abun yaso bashi dariya wani irin sanyin  dadi ne ya mamaye gabadaya ilahirin jikinta ta sake gyara tsayuwa tana kallonsa tana jiran taji me zaice ."a natse taga ya shiga matsé takardar har ya matseta  gabadaya yana  mata wani irin mugun kallo sannan ya kalli inda abun zuba shara yake ya cilla takardar aciki ."
sake fuskantata yayi cikin fushi yace "wa kike da suna sultana ko me ,wannan shine sakamakon abinda kike zana yana gama fadar haka ya juya ya soma tafiya zuwa mazauninsa wani irin numfashi ta sauke da karfin gaske tana kiran sunansa "ya Adam !a matukar tsawace yace "me zanyi miki ?wato burinka ka wulakantani a bayyanar  nasi ba ?ta sauke numfashi tana furta why ?Kina san kisan ina da ikon wulakantanki ko bani da ?tayi shiru tana dubansa "to ki daina shiga tsabgata ki kama kanki akan komai nawa ki tsaya iya inda aka ajiyeki stay a way from me sultana oya leave ..."ya fad'a yana nuna mata kofa  tare da zabga mata harara cike da in ina ta kira sunansa "ya..ya Adam"i saida leave ya sake nuna mata hanyar fita ."

"Some ai na rigada na fad'a miki ki dauki kwararrun masu zane ba muna zane ba gabadayan ni banga na dauka anan ba "ya fad'a yana jan dogon tsaki  "sir kayi hakuri kowannensu yana ta qoqarin yaga ya zana abinda zai burgeka "shiiii! "ya fad'a a tsawace "common design sun kasa abinda zai fi ki sallamesu kawai gabadayansu a nemo min wasu "kayi hakuri sir amman  me zai hana a nemi maryama hussein  nasan zata maka abinda kake ...,"stop ! ya tsadata  a tsawace just stop some karki qara kuskure ina wata magana dabam kina sako wannan yarinyar ko kin fahimceni ? tai saurin gyada masa kai "bana bukatar wannan yarinyar kuma bazata sake tako kafarta zuwa cikin wannan kamfanin ba ,bama wannan kafanin ba har kowani kafani da suna aiki ita da yin aiki har qarshen rayuwarta ."

Bayan ya gama mgn ya numfashi yana kallonsu daya bayan "ku saurarani da kyau zan sake baku lokaci "yarinyar ce zaune a lap cike da natsuwa idanunta na Kan farar takarda tana zana doguwar rigar amarya da riga da wondo na ango  sosai tayi concentration gaban doguwar rigar tana da shape daga gaba yayinda bayan rigar ta sauko wanda ya hade da dogon gashin mace yana bayani yana kallon maryama cikin kwayar idanunshi cike da matsanancin qaunarta ,lumshe lumtsatsun idanunsa yayi "wannan shine tsarin zanen da nake so ku dinga bin komai daki daki tare da tsare fatan kun fahimceni ?gabadaya suka hada baki "yes sir ."oya maza maza aje ayi daya daga cikinsu ya kallesa yace  " kayi hakuri sir inshaallahu zanyi maka abinda kake so "very good ya fad'a yana tare da komawa  mazauninsa ya zauna yana jujjuyawa akan kujera sannan ya dauko cup din glass cup dake cike da ruwa ya kai bakinsa ya kurba ya ajiye ya daura hannunsa akan hannun kujera yana cigaba da jujjuyawa."

Bangaren sultuna kuwa office dinsu ta koma ta cike da tsananin tashin hankali da takaicin abinda ATA yayi mata waya ne a kunnenta tana magana da Aunty abida "kinga wulakacin da yayi min kuwa aunty agaban ma'aikatansa bayan ya gama  wulakanta zanen dana sha wahala na zana a gaban kowa wallahi bazan dauka ba Aunty bazan jura wannan wulakanci ba" nasan halinsa shegen gaske ne  zai iya aikata abinda yafi wannan ki daina damuwa abinda ya kamata kiyi  kokarin shine ki fara daukar hankalinsa ...amman Aunty .."No ki tsaya kiji abinda nace Kiyi shi zakiyi karki min mutsu dan duk ina yin wannan abun ne saboda jin dadinki ...."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 BOOK 3
  2. 2 BOOK 3
  3. 3 BOOK 3
  4. 4 BOOK 3
  5. 5 BOOK 3
  6. 6 BOOK 3
  7. 7 BOOK 3
  8. 8 BOOK 3
  9. 9 BOOK 3
  10. 10 BOOK 3
  11. 11 BOOK 3
  12. 12 BOOK 3
  13. 13 BOOK 3
  14. 14 BOOK 3
  15. 15 BOOK 3
  16. 16 BOOK 3
  17. 17 BOOK 3
  18. 18 BOOK 3
  19. 19 BOOK 3
  20. 20 BOOK 3
  21. 21 BOOK 3
  22. 22 BOOK 3
  23. 23 BOOK 3
  24. 24 BOOK 3
  25. 25 BOOK 3
  26. 26 BOOK 3
  27. 27 BOOK 3
  28. 28 BOOK 3
  29. 29 BOOK 3
  30. 30 BOOK 3
  31. 31 BOOK 3
  32. 32 BOOK 3
  33. 33 BOOK 3
  34. 34 BOOK 3
  35. 35 BOOK 3
  36. 36 BOOK 3
  37. 37 BOOK 3
  38. 38 BOOK 3
  39. 39 BOOK 3
  40. 40 BOOK 3
  41. 41 BOOK 3
  42. 42 BOOK 3
  43. 43 BOOK 3
  44. 44 BOOK 3
  45. 45 BOOK 3
  46. 46 BOOK 3
  47. 47 BOOK 3
  48. 48 BOOK 3
  49. 49 BOOK 3
  50. 50 BOOK 3
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});