Chapter 17
BOOK 3
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 16
Fuskar wayar yake kallo tare da raya abubuwa da dama acikin zuciyarsa ,wani irin abu yake ji yana tsarga masa a gbdy sansar jikinsa, sai wayar ta kusan shiga sai ya katse ,yayi haka ya kai sau uku yana katsewa cike da fargaba ya rike wayar a hannunsa yana tafiya acikin d'akin yana tunani ." maganar mahaifiyarsa ta shiga dawo masa "zuciyarta na tattare da damuwa mai tsanani ,da ciwo a zuciya ba kowa bane zai iya dauriyar abinda ya faru daita .
“Dan hk ka dinga mata hakuri kana tausaya mata mutuwar miji fa baqaramin ciwo bane ," runtse idanuwanshi yayi sosai yana kiran sunan Allah a lokacin da ya tuna yadda hawayenta ya dinga zuba akan wani matacce .”wani dogon tsaki yaja ya sake cilla wayar akan gado yana sake jan tsaki tare da kai hannu ya dafe goshinsa ahankali ya bud'e idanunshi wad'an da suka kad'a sukayi jajur saboda tuno abinda ya faru jiya. kukanta da damuwarta akan wani namiji wanda bashi ba ."wannan abu yayi matuqar masa ciwo ,qirjinsa na wani quna ya juya wa wayar baya kamar itace tayi masa laifi ."
Ya kamo lip's dinsa na qasa gabad'aya ya dinga taunewa da karfi gashi dai zafi yake ji amman zafin kishin maryama ya zarta zafin da yake ji acikin zuciyarsa ,byn kmr second goma ya sake juyowa da sauri yana kallon wayar kmr zaiyi kuka ,"bazan ta'ba bayyana miki soyayyata a yanzu ba dan nasan ko na bayyana miki a acikin wannan halin bazaki ta'ba sona ba amman zan san abunyi ," ya furta a fili yana sauke wani naunayen ajiyar zuciya ya sake d'aukar wayar stil numberta ya shiga kira yana tunanin mgnr da zai fad'a mata da zai sa tazo aiki dan yayi imani tunda bata zo jiya ba tabbas yau din ma bazata zo ba "to idan ina kirata ta d’aga me zance mata ?” ya sake tambayar kanshi yana sake danne lip's dinsa da hakori "idan ta d'auka kace mata tazo aiki amman karta zo maka da past dinta , ta bar komai a gida baka buqata that's all ."
sai dai wayar na daf da shiga ya sake ya katse wa yana sauke zazzafan numfashi ."maryama ta tsaya shiru acikin haraban ma'aikatan tana tunanin hawa sama ,kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin fargaba, ita ba wai tsoronsa take ji haka nan ba kamar yadda sauran ma'aikatan suke rawar jiki idan sun gashi disgi da tozarcinsa ne bata so kuma shi babu ruwansa ko gaban uban waye shuka rashin mutuncinsa yake kuma kamar bai d'auki hakan a wani abu ba ."da kyar ta tattare jarumta ta sanya ajikinta ta nufi kofar shiga lift byn ta shiga ta shiga, mutane da dama sun shiga a natse ta danna number inda zata sauka sannan ta ra'be jikinta waje d'aya tana jin mummunar fad’uwar gaba ,kofar na gama rufewa wani sabon fargaba yayi mata diran makiya gabanta ya dinga luguden bugu har sanda kofar ta bud'e , sai da kowa ya fita ya barta kamar ta koma kasa amman wata zuciyar ta dinga karfafa mata gwiwa.”
Ahankali ta fito zuciyarta na bata kwarin gwiwa "haba maryam kowa tsoronsa yake ,ya kamata ki zama zaka acikinsu ba wai ki masa taurin kai ba aa ki zama jaruma ."kai tsaye ki shiga office dinsa ko kuma ki kirasa “ta zaro wayarta ta rike tana tunanin abinda zata ce masa idan ta kirasa "sir kayi hakuri nayi realize din mistakes dina bazan sake aikata wannan kuskure ba shikenan kina yin hk zai yafe miki ."tana cikin tunanin kawai taji wayarta ta d'auki qara a matukar tsorace ta duba sunanshi ta gani yana yawo a scren din wayar nan take bugawar da zuciyarta take ta qaru yayinda sansar jikinta ya kama kyarma ,amman tayi karfin halin ta daidaita natsuwarta ta d'aga kiran cikin sanyayyar muryarta mai sanyi da bugar da zuciya duk wanda ya saurara "assalamu alaikum " !.
shiru taji bai amsa ba ,dan a can bangarensa bai san kiran ya shiga har ta d'aga ba yana can yana tunaninsa sai jin sautin muryarta yaji "assalamu alaikum .""hello ta sake maimaitawa duk da yana jinta amman yayi mata shiru yaki yin magan yana shan kamshi kamar tana gabansa . ji tayi kamar ta saki fitsari ajikinta tsabar yadda gabanta yake dukan tara tara ."jin shirun yana son yayi yawa ta sake motsa labbanta cike da girmamawa tace "good morning sir" morning !ya fad'a atakaice yana ciccin magani sannan ya juya ya cigaba da tafiya acikin d'akin batare da ya sake cewa komai ba." itama shiru tayi .”har kusan second talatin bai ce komai ba ga mutane sai faman wuceta suke suna kallonta dan Allah yayi mata baiwar kyau mai d’aukar hankali da tafiyar da ruhi ,dole ne idan ka kalleta ka sake kallonta sannan ka yaba da irin zallar kyawun da Allah tabaraka wata ala yayi mata .”
ta sauke naunayen ajiyar tana sake duba screen din wayar ta gani ko kiran ya katse ne yasa taji shiru gani tayi still yana kan layi can dai tace "sir ko akwai abinda zakace ne ?"no...sai kuma yace "yes !"what !?
“what do you want to say sir ?ta furta a dan kid'ime shiru yayi yana sauke mata numfashinsa a kunne wanda hakan ke sake haddasawa zuciyarta mummu nar kidima da shiga tashin hankali muryata a matuqar raunane ta sake tambayarsa ” me kake son kace sir ? "abinda zance kizo office akan lokaci "okay sir ..!kafin tace wani abu ya katse kiran murna da farinciki suka taru suka lullu’beta ,kafin ahankali tayi shiru tsaye tana nazarinsa " ko me yake son fad'a mata? kamar ba wannan maganar yaso fad'a mata ba" kai koma dai menene matsalarsa ce wannan tunda har ya furta tazo tana da hujja kare kanta idan zai tozartata .""wayyo allah dadi "ta furta a fili cikin tsananin farinciki bai ma san na kusan shiga office ba, allah na gode maka da kasa ya furta nazo da bakinsa .”
Cike da kuzari ta soma tafiya cike ta shiga office dinsu lokacin kowa ya hallarar "sautin muryarta suka jiyo daga sama "good morning !good morning!!ta furta gbdy suka mike sakamakon ganinta sectary tace "me yasa shekaranjiya da jiya baki zo aiki ba ?”gsky baki kyautawa mr ATA ba kin kunyata shi tunda nake aiki dashi ban ta'ba ganin abokan kasuwamcinsa sun masa haka ba yusura da surayya duk suka matsota suma dai tmbyarta dalilin rashin zuwa kwana biyu suke "nima ba haka naso ba na .."
“ba haka kika só din wa ba ?”daman dayawa ya'yan talakawa basu iya samun guri ba sannan basu iya d'aukar aikinsu da mahimmanci ba "inji cewar sultana dake zaune tana watsawa maryama wani mugun kallo ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan tace "haba sultana gsky banji dadin kalmarki ba rayuwar nan fa da mai arziki da talaka duk daya né a wurin allah babu bambamci sai wanda yafi wani jin tsoron allah ."
Maryama tana cikin wannan bayanin mr ata ya taho a hankali hannunsa daya cikin aljihun wondonsa tun kafin ya qaraso kamshin daddaren turarensa ya kawo masu ziyara, bai tsaya a koina ba sai a bayan maryama yana kallonta” tayi kmr zata juyo ya bar gurin kad'an still dai yana bayanta kuma idanunshi na kanta numfashinta kawai take janyowa da kyar tana fesarwa dan gbdy acikinsu babu wanda bai firgita da ganinsa ba kafin a hankali suka shiga gaishesa daya byn daya da girmamawa ."itama maryama ta bude baki da kyar ta gaishesa dan zuwa alokacin ya dawo gabanta ya tsaya kyam yana kallonta sai dai bai amsa gaisuwarta ba illa tsura mata tsumammun idanunshi da yayi ta cikin medical glas dinsa yana kallonta itama shi din take kallo sai dai ita a dan rikice take ."
“sosai ya tsareta da idanunshi duk tayi masa laifi mai girma amman kallonta a yanzu ya d’an rage masa kashi hamsin na cikin damuwar data haifar masa sakamakon wani zazzafan kyau datai masa domin sosai kayan dake sanye a jikinta suka mata masifar kyau gashi dai bata bayyanar da surarta afili, amman kowani kaya ta saka sai ya zauna ajikinta kuma suyi mata kyau “princess kinyi masifar kyau yau..."ya furta a can qasan ranshi yayinda ita kuwa tashiga tsananin damuwa dan a zahiri yake iya kallon yadda take hadiyar zuciya
irin kallon da yake mata yasa numfashinta ya soma qoqari d'aukewa "sir ..!tana furta hakan ya juya ya wuceta da sauri ya shige office dinsa .”aiko nan take wani sabon fargaba da tsorone sukayima maryama dirar mikiya, jitake kamar tasaki fitsari mai wasali a wando tsabar yanda gabanta yake bugawa .”
Yayinda duka wata gaba da Allah subhanahu wata'ala ya halitta ajikinta rawa takeyi,kallo daya zaka mata kagane hankalinta amatukar tashe yaje . qafafuwanta dake karkarwa ta shiga motsawa ta juya da zumar zata bi bayansa gbdy sukayo kanta har sectary "karki kuskura ki shiga office dinsa yanzu “ki barshi zuwa wani lokacin sai ki gansa "cikin tsananin tashin hankali tace "karku damu ku barni na gansa yanzu domin a yanzu ya kamata naje na nemi yafiyarsa ba sai an dauki lokaci ba , idan naki zuwa yanzu zai dauka cewar da gangan nayi , ko ya d'auka girman kai zan masa ,ku dai kuyi min addaur da fatan nasara tana gama fad’ar haka ta wuce su "uhmm ba dai ya Adam ba sai kin gwamace baki je ba sultana ta fad'a a kasan ranta tana murmushin mugunta sannan ta gyara zamanta zuwa kallon office din mr ata tana jiran taga irin korar wulakancin da zai mata."
Ahankali maryama tayi knowking tare da cewa" ko zan iya shigowa sir "abun mamaki sai ji tayi yace "comming "! zazzafan numfashi da ajiyar zuciya ta sauke tana mai tura kofar glass din ta shiga idanunta kyam akanshi tare da maida kofar ta rufe ahankali batare data juya ba, yana tsaye yana waya ahankali cikin yin kasa da murya "okay kuna bukatar qarafe kimanin adadi nawa ?okay okay !!
"shikenan zan hadaka da ahmed zan tura masa komai yanzu zai nemeka amman fa bazan qarfi wannan farashin ba zaa sauke komai akan tsare no gsky bazan bada a wannan farshin ba gbdy mun qara farashin komai namu saboda ingancin abubuwan da muke amfani dasu dan haka ka tura kudi sai tura maka kaya."
Cike da sanyi muryar maryama ta bude baki "sir ! ya dakatar daita da yatsan hannunsa yana cigaba da magana "ka tsaya ka fahimceni wannan matsalar ba daga gareni bane ,Okay idan yayi maka shin kenan sai najika idan kuma bai maka ba babu matsala ma hadu zuwa gaba".shayayyun idanunta ta tsura masa tana kallon yadda yake magana a natse cikin harshen tsadadden turancinsa bakinsa ma da kyar yake motsawa har sanda ya ajiya wayar office yana kallonta tare da qara girman idanunshi akanta tunda daga kasanta ya dauki kallonta har zuwa samanta yadda bai ce mata komai ba haka itama bata ce masa ba saboda gudun wulakancinsa.”
ta lumshe idanunta ta sake rungume littafin dake hannunta "dan kawai ki tsareni da wadan nan idanuwan naki kika shigo min office? "no sir ammm actually actually ..!!sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da magana "actually what ?"ya tambyeta yana sake tsareta da tsumammun idanunshi ."idan baki da abun cewa kina iya wucewa ki bar min office dina "no sir ina dashi daman nazo maka design din shejaranjiya ne na qarasa shi ajiya gashi nazo dashi ta ajiye agabansa ."tana mai sunkuyar da kanta kasa tare da jin wani sabon fad'uwar gaba mai tsanani ."
"this is totally nonsense maryama “me zanyi dashi?ya tamvayeta cikin zafin zuciya yana tsareta da kwayar idanunshi .”
ahankali ta dago kanta ta zuba masa idanunta " ki dauke min wannan shirmen daga gabana dan basu da wani amfani a wajena yanzu dan takalmin kafarki ma ya fishi daraja a wajena dan hk ki daukeshi banason ganinsa .”tana kallonsa jikinta na rawa dan azahiri ake iya ganin yadda jikinta yake rawa Matsowa tayi kusa dashi kad'an still tana kallonsa tana jin kamar ta kamo hannuwansa gabadaya cikin nata ta rike ta rarrashesa dan tabbas ta aikata masa ba daidai ba.” manzon Allah sallallahu alaihi wasalam yace “idan aka ‘bata maka ka nuna fushinka dan kai ba jaki bane ." haka zalika idan aka baka hakuri ka hakura dan kai ba sheidan bane sai dai tasan duk abinda zatayi a yanzu bazai sauko ya karbi aikin ba sakamakon mugun taurin kan dake garesa uwa uba zuciya " kin wani tsaya kina kallona ?”
ta marairaice masa fuska kamar zatai kuka .”
"maryama leave my office right now I don’t want to see your face ." ya fad'a yana nuna mata kofar fita ."
"Dan girman Allah sir ka sake bani wata dama .”
"babu wata dama da zaa baki domin ke kullum cikin matsala kike sannan rayuwarki kullum acikin second chance take ko wace dama zaa baki sai wannan mataccen yasa kinyi loose "ya fad'a yana jan tsaki tai shiru tana nazarinsa da mamakinsa ta rasa dalilinsa na daukar zafi har haka akan mijinta "bata gama tunaninta ba ta sake jiyo muryarsa "there's no second chance maryama go back to your work ."
"am so sorry sir ..."I said go back to your work ya fad'a a tsawace "go! ya sake furtawa yana nuna mata kofa da bakinsa jikinta a sanyaye ta kallesa sai dai hankalinta a tashe yake, ta juya da sauri tun kafin ya rufeta da duka dan taga alamun zai iya aikatawa yabi bayanta da kallo kafin a hankali ya zauna akan kujera ya sauke numfashi ya dauki wayarsa dake ringing "yes sweetheart daga can bangaren tace "fatan ka isa office lafiya ?lafiya sweetheart “yarinyar tazo office ne ."?
"yes sweetheart !" fatan kayi abinda nace kayi "? ya juya ya kalli kofar da maryama ta fita yanzu "ai nasan bazakayi ba ,wacece ni da zance kayi abu kayi min alokacin da nace ? tana gama fadar hk ta katse yayi shiru kawai yana tuna maganar daya gama fada mata tanzu "I said go back to your work yana cikin wannan halin ya sake jiyo muryarta tana neman izinin , itama kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali tayi koda ta koma office dinsu bata iya aikata komai ba ,zuciyarta ce ta dinga azalzatar ta dawo garesa ko zai kasheta gara ya kasheta ta huta."
ya tsura mata ido kawai ganin irin kallon da yake mata ya sake kidima ta tana qoqarin sake juyawa ta fice idanunta suka sauka akan takardar zanen data ajiye masa da hannu ta nuna masa saman table dinsa "sir na manta file dina .”
ya nuna mata da hannunsa alamun ta d’auka tasa hannu ta d’auka "madadin ta wuce sai tayi tunanin ta sake bashi hakuri "kayiwa girman allah da girman iyayenka kayi hakuri akan laifina bazan sake aikata wannan Kuskuren ba idan nayi ka d’auki kowani irin hukunci akaina “ ta qarasa maganar cike da raunin zuciya wanda adaidai lokacin ya juyar da kanshi gefe ganin hk yasa itama ta juya cikin sanyin jiki ."
Har tayi taku biyu taji sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta "am sorry too for yesterday ."da wani irin mugun sauri ta juyo ta tsura masa ido.”
Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Table of Contents
Chapters
- 1 BOOK 3
- 2 BOOK 3
- 3 BOOK 3
- 4 BOOK 3
- 5 BOOK 3
- 6 BOOK 3
- 7 BOOK 3
- 8 BOOK 3
- 9 BOOK 3
- 10 BOOK 3
- 11 BOOK 3
- 12 BOOK 3
- 13 BOOK 3
- 14 BOOK 3
- 15 BOOK 3
- 16 BOOK 3
- 17 BOOK 3
- 18 BOOK 3
- 19 BOOK 3
- 20 BOOK 3
- 21 BOOK 3
- 22 BOOK 3
- 23 BOOK 3
- 24 BOOK 3
- 25 BOOK 3
- 26 BOOK 3
- 27 BOOK 3
- 28 BOOK 3
- 29 BOOK 3
- 30 BOOK 3
- 31 BOOK 3
- 32 BOOK 3
- 33 BOOK 3
- 34 BOOK 3
- 35 BOOK 3
- 36 BOOK 3
- 37 BOOK 3
- 38 BOOK 3
- 39 BOOK 3
- 40 BOOK 3
- 41 BOOK 3
- 42 BOOK 3
- 43 BOOK 3
- 44 BOOK 3
- 45 BOOK 3
- 46 BOOK 3
- 47 BOOK 3
- 48 BOOK 3
- 49 BOOK 3
- 50 BOOK 3