Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

BOOK 3

Maradams Book 3 Complete Hausa Novel 4,292 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 18

Bayan maryama ta gama aikinta taje ta kulle koina ta dawo d'akin mahaifiyarta ta shiga bayi ta kama ruwa tare da d'auro alwala ta fito ta hawo har kan gadon aunty ta zauna a bayan aunty ta soma karanto adduaoi tsari ta shafe ilahirin jikinta dashi haka ma ta shafe jikin mahaifiyarta a qarshe ta karanta suratul muluk sannan ta ja pillow ta kwanta ."sai dai tana kwanciya komai ya tsaya mata ,bacci ya kauracewa kwayar idanunta, ta d'auko tunanin wannan ta ajiye ta dauko tunanin wannan ta ajiye. sosai ta tsunduma cikin tunani wanda kusan duk tunanin mr ata yafi na kowa yawa ganin data masa a yau din yana shan sigari kuma a gabanta wannan abu ya hana zuciyarta sukuni ta qarshe ta tsaida tunaninta a inda take masa magana akan new desing's din da take son su gabatar a boye batare da sani kowa ba "yes I can't do it coz this is your plan ,kuma cutar wa ne bugu da qari bama kasuwan cinmu haka ,ba haka mahaifina ya d’aura mu akai ba idan zaa yi kasuwanci kowa na kawo ayyukansa ne a zube sai clet ya zabi wanda yayi masa dan haka bana ciki ,am not supporting ta sauke wani wahalallen numfashi tana kallonsa acikin kwayar idanunta "rigimamme kawai ".ta fad'a a fili tana qoqarin gyara kwanciyarta ."ta jiyo sautin muryar aunty cike da mayen bacci tana cewa "waye rigimamme kuma ?"tsam maryama tayi da ranta kafin ahankali tace "babu kowa aunty kiyi baccinki kawai ."daga haka aunty bata sake cewa komai ba."

Yadda maryama bata runtsa ba haka bangaren mr ata shima bai samu damar runtsawa ba juyi kawai yake akan makeken katifarsa yana tsara yadda zai yi rayuwar aure da princess dinsa, a naked yake ganinta acikin kwayar idanunshi tana kwance faffad’an qirjinsa , koshi yana kwnace ajikinta yana sarrafa sansar jikinta most especially brest dinta haka ya dinga imagenation dinta batare da ‘bata lokaci ba jijiyarsa ce ta mike sambal ta cika qaramin wondon da yake sanye dashi sakamakon neman abincinta ya had’e hannuwansa duka ya sanya abayan kanshi yayinda jijiyarsa ke cigaba da harbawa wani juyi yayi ya janyo pillow ya rungume gam a qirjinsa yana jin tamkr itace rungume ajikinsa sai daf da asuba wani bacci mai dadi ya kashesa ana raka’a ta biyu a masallacin dake cikin estate dinsu ya farka da kyar ya mike zaune ya kunna wutar d’akin yana kallon jikinsa inda gabad’aya wondonsa ya jike da ruwan shaawa.”

“Ya rabbi ka taimakeni yarinyar nan tana matukar bani wahala . ya fad’a a fili yana dafe goshinsa can ya janyo wayarsa ya duba time 5:30 har ta wuce ya yunkura da kyar ya nufi bayi bai wani jima ba ya fito ya janyo jallabiya ya saka yayi sallarsa a daki dan ya rigada yasan ya rasa jimai yana idar da sallah a daddafe yayi azkar ya mike ya koma ya haye katifa batare daya cire jallabiyar jikinsa ba .ko cikakken mintuna shabiyar bai yi ba bacci ya kwashesa bashi ya tashi ba zai karfe goma saura yayi wanka yayi shirin zuwa office .hankali motocin mr ata suka tsaya acikin ma'aikatar AGC bayan an bud'e masa ya fito cikin isa da takamar shi wani ne, ya fara taku a natse sanye cikin riga fari long sleeve da wondo baki sai dai ya nad'e hannun rigar kad'an wanda hakan ya qara masa kyau matuka ,yayinda tsintsiyar hannunsa ke d'aure da agogon fata baki ya zuba duka hannunwansa cikin aljihunsa.”

tunda ya shigo kananan ma'akata da manya suka shiga gaishesa yana d'aga masu hannu wasu kam ma basu samu wannna damar ba sai dai ya wuce har ya qaraso sama ."kai tsaye ya tsaita kwayar idanunshi zuwa office dinsu maryama qirjinsa na bugawa da matsanamcin karfi adduarsa ya fara sanyata acikin kwayar idanunshi sai dai duk ma'aikatan da suke aiki tare daita suna zaune a wajen ban da ita .
wani iri abu yaji a gabad'aya ajikinsa yana masa yawo ,ya sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ya cigaba da taku yana zance zuci ."me yarinyar nan take nufi dashi ?sai lokacin da yayi mata dadi take zuwa office ko dai ta fahimci wani abu ne atattare dashi ?"ya kai hannu ya tsotsa bayan keyarsa yana sake zance zuci "babu wata alama dana nuna mata da zai sa ta fahimta kawai tsabar rainin hankali ne irin nata da takamar ta iya aiki "to amman kai haka zakuyita tafiya bazaka fahimtar daita matsayin da take dashi a wajenka ba?zuciyarsa ta aikawa kwakwa luwarsa wannan tamvayar ?".

daf da zai shiga office dinsa suka had'u da madam some cike da girmamawa ta gaishesa "good morning sir ?"morning !"ya fad'a atakaice tare da wuceta ya shige office dinsa . "bayan kamar mintuna shabiyar da zuwansa maryama ta shigo da hanzarinta dan taso ta makara sakamakon hodop din data had'u dashi a hanya .wani zazzafan numfashi ya sauke sakamakon ganinta yana jin wani irin sanyin dadi na ratsa sansar jikinsa rayuwarsa ce maryama ."bai d'auka zai iya wannan dauriyar ba idan ya ganta .ya d'auka gigicewa zai yi ya haukace mata sai gashi bai yi ko d'aya ba amman shi kad'ai yasan me yake ji a game daita,acikin irin abinda yake ji zai iya sadaukar da duk abinda ya mallaka akanta ."
ahankali ya danna wani farin bell dake ajiye akan table dinsa cikin kankanin lokaci madam some ta bayyana a gabansa "ki tattara duk wasu kwararrun masu zanen da muke dasu a meeting room akwai bayanin da nake nayi masu "okay sir !" ta fad'a tare da juya da sauri ta fice . “

kai tsaye ta isar da sakon mr ata garesu nan take kowannensu ya sha jinin jikinsa sannan kowanne ya nemi natsuwa ya sanya ajikinsa dan sun san baya son wasa bayan mintuna ashirin duk suka hallara zaman jiransa ."some ta shigo office dinsa tana sheida masa "kowa ya hallara shi kad'ai ake jira ya yunkura ya mike a natse yana ciza gefen lips dinsa na qasa sannan ya fita inda madam some ta biyo bayansa da sauri atare suka qaraso meeting room din duk suna zaune har maryama ya tsaida kwayar idanunshi kyam akanta dan itama shi take kallo da kyakkyawan idanunta, had’ad’den bakinsa tabi da kallo aranta tace “ga baki har baki mai kyau amman ana sha masa sigari .” bai dauke idanunshi akanta ba wanda hakan yasa tayi saurin d'auke kanta ta maida kan file din dake gabanta har ya qarasa jikin writing board amman still kwayar idanunshi na kan kyakkya war fuskarta. yayinda yake hango yadda take sauke numfashi ahankali ahankali hannunta d'aya na rike da pen ta d'aura akan file din gabanta da alamun shi take jira ya fara bayani ita kuma ta soma aikinta ."

kusan 20 minutes yana tsaye yana kallonta ta d'ago ahankali idanunsu ya tsarke cikin juna tayi saurin d'auke idanunta tana runtsesu gam dan wani iri take ji ajikinta a duk sanda idanunta ya hade da nashi wanda ta rasa dalilin jin haka shi kuwa yaki d'auke tsumammun idanunshi akanta so yake ta dago ta sake kallesa domin akwai abinda yake son ya d'an fahimta atattare daita sai dai maryama taki d'agowa dan tayi imani kwayar idanunshi suna yawo ne a sansar jikinta sakamakon bugawar da taji zuciyarta take yi da qarfin gaske ."a natse ya soma masu bayani aikin da yake so yana zagaye makeken table din da suke zaune yana cigaba da kallonta zuciyarsa na sake narkewa akan soyayyarta." ita din daban ce acikin zuciyarsa kuma yayi imani tunda Allah ya hallata zuciyarsa ya sanyata aciki ,kamata yayi ya mallaketa cikin sauki batare da saninta ba, ahankali sai ya dinga shigar da soyayyarsa dan a yanzu soayyar wannan mataccen mutumin bazai bar zuciyarta ta amshesa ba ."

" taya zaka sameta cikin sauki "?ya tambayi kanshi samunta shi yafi komai sauki da yuwuwa agaresa tunda kawunta gali yana raye yasan bazai ta'ba bashi matsala ba "ya bawa zuciyarsa amsa da haka sama da awa daya yana bayani kuma duk hankalinsa da natsuwarsa suna kanta duk sanda ta d'ago kanta dole zata kallesa dan idanunshi na kanta bayan ya gama bayani ya basu lokacin da zasu yi submitting aikin sannna ya sallami kowa har ta mike kasance war itace last person din da zata fita yace "tsaya .”
tana kallonsa ta koma ta zauna tana jin wata irin mummunar fad'uwar gaba mai tsanani sam bata son wannna mayataccen kallon da yake mata yana saka zuciyarta jin wani irin firgici." mr ata ya samu waje ya jigina jikinsa da bangon d'akin tare da rungume duka hannuwansa a qirjinsa yana cigaba da dubanta cike da tsananin qaunarta.”

wani abu ya gani kamar hawaye yana diga a saman hannunta .bai san lokacin da yayi taku ya qarasa inda take zaune ba, ya zauna a gefen table din da hannunta ke kai ya duko da kanshi daidai fuskarta qirjinta ne yayi wani irin tsalle sakamakon sanyayyen kamshin turarensa daya ziyarci hancinta tayi saurin runtse idanunta tana sake jin fad'a uwar gaba ."hannunsa ya kai ya d'ago ha'barta agigice ta bud'e idanunta dake runtse ta zuba masa nan yaga hawaye cike da idanunta suna siyayya bai ce mata komai ba ya sanya kwayar idanusnhi cikin naya sannan ya ciro handkerchief a gaban aljihun rigarsa mai azababben kamshin turaren red ya soma goge mata hawaye . inda maryama take binsa da wani irin firgitaccen kallo kafin ahankali ta kawar da idanunta gefe tana mai danne hawayenta Itafa gaskiya ya fara takura mata da kallon nan shi na babu gaira babu dalili ,dan idan akwai abinda ta tsana arayuwarta daga nmj to bai wuce yawon kallo ba sam bata són shi kuma ta rasa dalili da koda yaushe idanunshi na kanta ."

"maryama !"
Taji ya kira sunanta muryarsa a raunane kamar mai shirin yin kuka ta waigo ta kallesa a natse idonsa cikin nata , ya matsota sosai tare da riko laulausan tafin hannunta cikin nashi yana murzawa wani irin yanayi suka tsinci kansu ciki mai wuyar misaltuwa nan take jikinta ya kama rawa alamun rashin sabo "ina son zan miki tambaya biyu .yayi maganar fuskarsa a had'e kamar ko yaushe bai tsaya jin amsarta ba ya soma magana ."me yasa kike yawon kallona ?"ta d'an ware idanunta sosai cikin nashi tana mamakinsa "ita ya kamata ta tmbyesa amman dan rainin wayo da karfin hali irin nasa shine zai ambayeta ?tayi mgnr a qasan ranta tana lumshe masa shayayyun idanunta tare da sauke naunayen ajiyar zuciya "ki bani amsa kafin na shigo da tambayata ta biyu ."

still shiru tayi dan idan tace zatayi magana to bakar magana zata fad'a masa wanda hakan zai iya dagula komai ."okay tunda baza kiyi magana ba bari naje tamvayata ta biyu ta natsu sosai tana jiran taji tambayar rainin hankalin da zai sake mata "me ya sakaki kuka yanzu ?"shiru tayi kawai tana kallonsa dan bata da abinda zata fad'a masa a zahiri , amman zuciyarta cewa tayi kwayar idanunka ne suka sakani kuka bana son yawon kallonka ."ya tsuke bakinsa yana duban cikin kwayar idanunta batare da yace mata uffan ba ."tayi qoqarin ta cire tafin hannunta cikin nashi sakamakon wani salon da yake mata mai fitar da mutun haiyacinsa amman taji ya rike yatsun hannunta gam ji tayi wani sanyin dadi na ratsa sansar jikinta har tsigar jikinta na mikewa abinda bata ta’ba ji ba kenan a iya tsawon rayuwarta akan wani d'a namiji sai akanshi ."

Allah ya taimaketa rigar dake sanye a jikinta mai dogon hannu ce tasan data shiga uku idan ya gani dan tayi imani sai ya tamvayeta dalilin mikewar gashin dake kwance ajikinta ."ya sake had'e fuska sosai tamkar zaki kana yace "ko kina kukan tsohon mijinki ne ?"shiru tayi kafin ahankali ta tsinci kanta da ce masa" eh ! rashinsa yasa bana jin dadin rayuwata .tayi maganar idanunta na cikin nashi "zafi nake ji sosai a qirjina "ta sake mgn cike da dakiya ai gama fad'ar haka da tayi keda wuya taji ya sakar mata hannun tare da mikewa tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ya juya ya fita daga d'akin zuwa office dinsa zuciyarsa nã qauna da tafasa zariya ya soma acikin office din yana zance zuci ".shikenan rayuwarsa tana cikin uku bala'i yana mutuwar sonta ita kuma tana mutuwar son matacce ya zai yi kenan ?" shirin mallakarta da yake son yi bashi da wani amfani kenan ?"ya fad'a a fili tare da dungule hannunsa ya d'aura akan table "shikenan wahalarsa ta tsawon shekaru ta tashi a banza ?"no no!! it can be possible "dole ne nayi duk abinda zanyi na cire shaukin soyayyar acikin tunaninta ."

Ahankali ya samu waje ya zauna yana sauke numfashi tare da dafe goshinsa yana jan tsaki inda zuciyar maryama ta cika da tsananin mamakinsa wannan shine karo na biyu da yake nuna damuwarsa akan mijinta to me haka yake nufi ?”ta tambayi kanta ganin ta kasa gano dalilinsa kuma kamar matsawa kanta da son gano dalili tamkar bawa kanta wahala ta tarkata komai ta watsar ta mike ta fito ta koma office dinsu .mr ata ya jima zaune ahaka yana saka da warwara ahmed yaronsa na Z&A ya shigo cike da girmamawa ya gaishesa sannan yaja kujerar dake fuskantarsa ya zauna ya ajiye masa file a gabansa "sir ana bukatar saka hannunka anan da anan ya fad'a tare da zaro biro a gaban rigarsa ya mika masa ya karbi biron yayi sign sannan suka fara tautaunawa akan kasuwanci sun d'auki sama da awa d'aya sannan yayi masa sallama ya wuce yana fita James ya shigo ya ajiye masa cup din coffee wanda ya za me masa jiki sannan ya ya juya fice .”

ahankali ya d'auki cup din ya kai bakinsa kamar ance ya kalli office dinsu maryama wani maaikaci mai suna ema ya hango duke a gabanta suna magana fuskarsu d'auke da annashuwa duk da bai san maganar me suke yi ba amman fuskokinsu ya nuna alamar maganar tana masu dadi sosai .”anatse ya ajiye cup din hannunsa ya zagayo hannuwansa duka cikin aljihunsa yana taku zuciyarsa na tsinkewa yana shiga office din bai ce masu uffan ba sai ji ema yayi mr ata ya zagaye wuyansa da hannunsa yayi hanyar waje dashi a gigice yake kallonsa yana biye dashi ,haka ma maryama a gigice tabi bayansu da kallo ahankali ta maida kanta ga aikin da take kafin ya gama dashi ya dawo kanta "kai tsaye office dinsa ya nufa dashi tare da hankad'a keyarsa ."fuskarsa a hade tamkar kumurci macijin dake neman abinci yace " zance me kuke yi ?"yayi masa tambayar yana juya masa baya ".

“kayi hakuri sir muna magana ne akan wannan sabon aikin dakayi mana bayani akanshi d'azu na banjana company shi muke sake tautaunawa akai domin yana bukatar nazari sosai "bayan shi kuma?”
”amm sai kuma dan naga sabuwar zuwa ce ita shine nake son na koya mata wasu abubuwa "mr ata ya juyo a natse fuskashi babu annuri yace "waye yace maka bata iya abubuwa ba ?ema yayi shiru sai dai à matukar firgice yake da irin kallon da mr ata yake jifansa dashi ".wannan da kake gani tafika fikira sannan tafika kwarewa akan komai zai fi kyau ka tsaya iya inda aka ajiyeka aiki ba yawon shiga cikin rayuwar wasu ba "wannan gsky ne sir dan yadda take magana ma kawai ya isa yasa mutun ya manta tarin ayyukan dake gabansa dan tana magana ne cike da shauki "what .?"mr ata ya furta acikin ransa qirjinsa na wani irin luguden bugawa sannan yana aikawa da ema da kallo mai hargitsa tunanin mutun da saka mutun shiga uku ."

Ya tsaita kallonsa sosai ga ema sannan ya cigaba da magana "yadda take magana da kai haka take magana da karnuka da kuma aladu da jakuna dan kasan ba wai matsayinka ne yasa take magana da kai haka ba ,ka tattara ka koma office din qasa kwata kwata "ema ya zaro idanu waje da sauri yana dubansa a marairaice "kana ‘ batawa kanka lokaci maza kaje ka tattara ka koma inda nace "ayi hakuri sir ban san cewar matsayinta ya .."leave my office kafin nasa a dakatar da kai gabad'aya ai da wani mugun sauri ya juya har ya kusan kai bakin kofa ya jiyo sautin mr ata cak yaja ya tsaya da girmamawa “bance ka fad'awa kowa dalili ba muddin kuma naji wani to kasan ka kori kanka da kanka aiki da sauri ya qarasa ficewa ya shiga office na tsakiya wanda ya kasance anan yake aiki ya dauki bakar jakarsa ya saba a kafad'ansa sannan ya d'auki laptop dinsa ya rungume yana kallon sauran abokan aikinsa yusura tace "ema ina zuwa haka "?an maidani office na qasa gabad'aya "what ?"ta mike tsaye hankalinta a matukar tashe alokacin da shi tuni ya fito.”

ta biyosa tana tambayarsa dalili amman bakinciki ya hanashi yi mata bayani haka ta juyo jikinta a sanyaye ta koma office cike da kewarsa dan gskiya ema yasan kan aikinsa gashi da sauki kai ,dan duk lokacin da ya gama aikinsa zai kar’bi nasu yayi.."
Yau Kamar abun had'in baki kusan hankalin mazan dake aiki tare da maryama duk yayi kanta bini bini zasuje inda take ita kuma cike da sakin fuska take sauransu suyi abinda zasu yi su koma mazauninsa wanda hakan keta faman baqanta ran mr ata hatta masu shiga da fite dan duk wanda ya shigo sai dai idan bai daura kwayar idanunshi akanta ba amman sai hankalinsa ya tsayu akanta wannan alamari fa ya daga hankalin mr ata matuqa sosai yasanya ido akanta ".Mr ata na zaune tare da wasu abokon business dinsa mutun uku alhj deeni ,alhj farooq alhj bb ya tsinkayo muryar maryama tana neman izinin shigowa.”

muryarsa a tsarke ya bata izini a natse ta shigo tunda ta shigo wad’an nan mutun nan suka tattara hankalinsu gareta,cike da girmamawa ta gaisheku
Sannan ahankali ta qaraso gaban mr ata ta ajiye masa file din da zanen datai ." ya tsurawa zanen ido na second goma kafin ahankali ya motsa labbansa yace "you can go back to your work ."har tayi taku biyu yace "ke.."ta juya a natse idanunshi na kanta kamar yadda idanun bakinsa ke kallonta kamar zai cinyeta wanda hakan ya haddasa mata jin wani mummunar faduwar gaba "shiru yayi kafin yace d'auki cup din can ki samu some ta nuna miki yadda ake had'a min coffe "okay sir “. ta furta cikin sanyayyar muryarta yayinda jikinta ke rawa rawa
ya d’auke kanshi ya maida kan bakinsa daya lura sunata kallonta amman sai ya share .”

Ta qarasa inda cup din yake ta dauka ta soma tafiya kamar wace aka hankada aiko qafafunta suka hard'e tayo kansu mr ata bai san sanda ya mike tsaye ya shiga tsakaninsu ba ta fad'a saman faffad'an qirjinsa tayi masauki atare suka dinga sauke ajiyar zuciya "ki dinga bi ahankali kada ki jima kanki ciwo kija ma kanki asara.” ya furta cikin wani salo da sautin murya mai sanyi yayinda hucin bakinsa dana numfashinsa na dukan wuyanta da fuskarta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa yrrrrr".
"Kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta dinga furtawa ahankali ahankali sakamakon yanayin data tsinci kanta .”ya riko tafin hannunta ya zaunar daita akan kujera qirjinta na bugawa fat fat kamar zata fasa qirjinta tayo waje . ta had’e yatsun hannunta waje daya tana murzawa shi kuma ya janyo wata kujera ya ajiye adaidai saitin bayanta ya zauna yana kallon inda su alhj deeni ,alhj farooq ,alhj suke zaune sun zubawa ma iyalinsa idanunsu kowa da abinda yake sakawa a ransa,a hankali mr ata ya lumshe idanunsa tare da sanya hannunsa a saitin kirjinsa yana murza dai-dai indai zucyarsa take beating vry fast,su kuwa cigaba da kallonsa suke
suna kallon sarautar Allah "dan babu tan tama mai kamfanin AGC ya kamu da mummunar qaunar yarinyar nan qauna kuma mai girma qauna ce da ma basu ta'ba ganin irinsa ba ".

tsumammun danunsa ya ware sosai akansu yana cewa "mintuna goma kacal sun isa ku tattara duk wasu kalamanku masu mahimanci." sarai sun fahimci inda ya dosa dan haka suka taikaita maganarsu kamar yadda ya bugata suka kama gabansa tun kafin yace ya fasa halqallar kasuwanci dasu ."bayan tafiyar bakinsa ya mike tsam ya janyo kujera zuwa gabanta ya zauna tare da ware qafafunsa ,sunyi mugun yin daf da juna ta dan ja kujerar baya kad’an amman hakan bazai hana idan ya sauke numfashinsa taji ba. ganin yadda idanunshi ke yawo ajikinta yasa tayi saurin sunkuyar da kanta qasa natse alokacin daya soma magana a tsanake amamn idan mutun ya natsu sosai zai fahimci cikin tsananin fushi yake "anya kuwa kwakwaluwarki tana da cikakkiyar lafiya kuwa ?" ta d'ago kanta a gigice tana kallonsa "yes !dole na tambayeki dan kin wani tsareni da idanu "ya qarasa maganar yana lumshe mata ido .”

“Ko me ya gani atattare daita yasa zai had’a da wannan mummunar ciwo ?” tabi jikinta da kallo na second goma sannan ta d’ago ta zuba masa idanunta “me yasa zaki fad'a kan mutane ?" Muryarta na rawa tace “wallahi ban sani bane ni ma haka kawai naji jikina ya kama rawa.” taso ta fad'a masa idanunsu ne yayi mata yawa amman sai ta tsinci kanta da kasa fad'ar haka dan batasan me hakan zai haifar ba tunda ta rigada tasan halinsa abu kad’an ke hassalashi "idanun maza yayi miki yawa kina gani bai kamata kiyi aure anan kusa ki huta ba "?tayi shiru tana cigaba da kallonsa yayinda qararrawar zuciyarta na kad'awa da sauri sauri sakamakon kusancin da suka samu na haifar mata da shiga cikin wani yanayi "ya dai kamata kiyi tunani ko sanin cewar ke matar aure ce zai saukaka miki wasu abubuwan ."numafshi ta janyo ta sauke da kyar tana sake sunkuyar da kanta gabdaya ta sake neman natsuwarta ta rasa rawar da jikinta keyi ta qaru ".

“Maryama ki tsaida miji kiyi aure zai fiye miki kina aure kina aikinki , dan bai dace ki dinga kula kowani kare alade da jaki ba "idan dai kema din ba irin hallitarsu gareki ba ."ya qarasa mgnr yana jan tsaki tabi shi da wani irin kallo zuciyarta na tsinkewa idan ta fahimcesa da kyau" idan halittartata ba irin ta jaki kare da alade bace ta daina kula kowa kallonsa take fuskarta da bayananen mamaki “to shi da yake kulata take kulasa fa ?”kenan shima ya kasance d’aya daga cikin abinda ya lissafa kare da alade da jaki ne ?”tayi maganar a can kasan makoshinta ta yadda ko shi da yake zaune a gabanta bazai iya fahimtar komai .ya juya ya d'auki kwalin sigari ya bud’e ya zari d’aya ya kai bakinsa ya kai hannu ya dauki abun kunnawa tana ganin haka ta zabura ta mike ranta a matukar bace ta nufi kofar fita tana jan tsaki da kallo yabi bayanta yana ta'be fuska  "abinda zaki qarasa tsawon rayuwarki daita itace abar gudu ai gara ki fara sabawa daita sannna ya lumshe idanunshi lokacin guda kuma ya budesu yana cewa "ke dawo ki zauna ."!

Maryama taki tsayawa bare ta dawo kamar yadda ya bukata "idan kika  kuskura  kika bar office din nan ki tabbatarwa kanki  kin tafi kenan har abada bazaki  sake da aiki a AGC ba  ".cak taja qafafuwanta ta  tsaya tana sauke wani wahalallen numfashi daga inda yake zaune yana kallon yadda kafad’unta suke d’agawa sama alamun tana  kokuwa da numfashinta Ahankali ta juyo tare da sunkuyar da kanta  kasa dan bazata iya cigaba da kallonsa a yanayin da yake ba saboda yayi mugun tsareta da ido  yana kallonta tana takowa ahankali har sanda ta qaraso ta tsaya "set "! ya fad'a yana kunna sigarinsa muryarta sanyaye tace  "sir kayi hakuri ka kashe wannan abar bana son warinta "daga yau ki koyi son warinta set !ya sake maimaitawa" inna ilaihi ita kam ta shiga ukunta da wannan mutumin ta sake yin kasa da muryarta sosai kmr zatayi kuka "sir kada kamin haka dan Allah "me nayi miki  ?"ya tambayeta yana dage mata girarsa d’aya “sigari ce fa kawai ?meye illarta?"  set and don't let me repeat my seif again ".

babu yadda maryama ta iya da rayuwarta haka tayi shiru ta toshe hancinta da hannunta d'aya dayan hannun kuma taja kujerar baya kad'an  domin rage kusancinsu ta zauna sai dai duk a rud'e take .
tunda ta zauna bata d'ago kanta ba yayinda shi kuma kwayar idanunshi ke kanta yana zugar sigari yana zance zuci  "ta d'ara duk matan duniya a idanunsa ita kadai  zuciyarsa  take so ,kuma bazai ta'ba son wata bayanta  ba ,sai dai duk runtsi bazai d'auki raini daga gareta ba farar takadar ya janyo ya ajiye mata sannan ya janyo wata roba da kayan zane yake ciki shima ya ajiye mata "ki zanani ahaka .
"what ?" !
ta furta à matukar razane tare da d'ago fuskarta ta tsura masa yana rike da sigari yana zuga muryarta a raunane tace "sir kayi hakuri bazan iya zanaka kana shan sigari ba ka canza min da wani aikin na yarda "okay ! zana min mata da miji rungume da junansu suna kissing din juna a bakin kofa "oh my goodness god ya rabbi ka taimakeni akan wannan mutunin ta furta a can qasan makoshinta sannna ta sake tsura masa idanunta gbdy ta rasa natsuwarta ji take kamar zuciyarta zata buga haka ne ma yasa ta cigaba da kallonsa ko dai a buge yake ne ?sai dai tsaf yake abunsa idan ma baa a gabanka yake shan sigari ba bazaka ta'ba cewar shi din dan sigari bane dan babu abinda ya nuna ko ya sauya ajikinsa "Kina 'batawa kanki lokaci domin kuwa babu inda zaki har  sai kinyi abinda nake bukata."

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 BOOK 3
  2. 2 BOOK 3
  3. 3 BOOK 3
  4. 4 BOOK 3
  5. 5 BOOK 3
  6. 6 BOOK 3
  7. 7 BOOK 3
  8. 8 BOOK 3
  9. 9 BOOK 3
  10. 10 BOOK 3
  11. 11 BOOK 3
  12. 12 BOOK 3
  13. 13 BOOK 3
  14. 14 BOOK 3
  15. 15 BOOK 3
  16. 16 BOOK 3
  17. 17 BOOK 3
  18. 18 BOOK 3
  19. 19 BOOK 3
  20. 20 BOOK 3
  21. 21 BOOK 3
  22. 22 BOOK 3
  23. 23 BOOK 3
  24. 24 BOOK 3
  25. 25 BOOK 3
  26. 26 BOOK 3
  27. 27 BOOK 3
  28. 28 BOOK 3
  29. 29 BOOK 3
  30. 30 BOOK 3
  31. 31 BOOK 3
  32. 32 BOOK 3
  33. 33 BOOK 3
  34. 34 BOOK 3
  35. 35 BOOK 3
  36. 36 BOOK 3
  37. 37 BOOK 3
  38. 38 BOOK 3
  39. 39 BOOK 3
  40. 40 BOOK 3
  41. 41 BOOK 3
  42. 42 BOOK 3
  43. 43 BOOK 3
  44. 44 BOOK 3
  45. 45 BOOK 3
  46. 46 BOOK 3
  47. 47 BOOK 3
  48. 48 BOOK 3
  49. 49 BOOK 3
  50. 50 BOOK 3
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});