Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

BOOK 3

Maradams Book 3 Complete Hausa Novel 3,335 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 20

  A matukar rikice ta juya tana mai   had'e hannu wanta waje d'aya tana jin wani irin mummunar fad'uwar gaba  mai tsanani "gabad'aya yanayinsa yayi matuqar tsoratata. a bangaren mr ata kuwa wani sanyi dadi ne ya mamaye sansar jikinsa sakamakon d'aura kwayar idanunshi da yayi  akan sanyi idaniyansa da sanyi safiyar nan , wani tunani maryama tayi wanda yasa ta juyo da sauri tayi taku biyu ta tsaya kusa dashi muryarta na rawa tace "good morning sir"! bai amsa mata ba ya qarasa shigowa cikin office din sosai yayi kmr yadda yake
yi a duk sanda ya shigo  hannunsa d'aya cikin aljihun wondonsa  yayinda d'ayan hannun kuma ya d'aura   akan table . shiru tayi tana ciza harshenta kamar tayi dariya dan wannan salon nasa yana matukar burgeta kuma yana sakata jin nishad'i acikin ranta sai dai ganin yadda yayi mugun had'e rai fiyye da kullum dan fuskar nan tashi sam babu annuri kirki yasa tayi maza  ta sanyawa jikinta natsuwa tare da lumshe idanunta na second biyar sannan ta bud'esu fess akan kyakkyawar fuskarsa ta sake gaishesa a karo na biyu ". “good morning sir ?!

“still shiru ne ya sake biyowa  baya batare daya kalli inda take tsaye ba "maganar me kike yi ?taji saukar muryarsa ta doke dodon kunnenta,a natse ta kallesa qirjinta na dokawa da qarfin gaske tace"ba maganar komai  nake yi ba "!tsumammun idanunshi ya waigo ya kalli inda take tsaye har lokacin tana wasa da yatsun hannunta ,kana kallonta kasan tayi kama da mai laifi domin ko a iya haka ma rashin gaskiyarta ta nuna ,ya motsa lip's dinsa ahankali yace "ya zakice ba maganar komai kikeyi ba byn da na shigo naji kina cewa wani abu me kikeyi cewa ?"nan take hantar cikinta ya kad'a ilahirin jikinta ya kama rawa.
sosai ta firgita "kar dai yaji abinda ta fad’a?"inna lillahi!" ta furta acikin ranta ,zuciyarta cike da matsanancin tsoro take kallonsa."ya gyara tsayuwarsa sannan ya fuskanceta tare da zura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ya tsura mata tsumammun idanunshi masu firgitarwa  “maryama kince wani abu, abinda kikace nake son na sani ".

muryarta cike da in ina tace "ina..ina.. dai magana da zuciyata ne yayi shiru still kwayar idanunshi na yawo a sansar jikinta wanda ke qara saka zuciyarta shiga rud’ani bayan kamar second goma ya sake motsa lip’s dinsa " amman kamar kina raact kmr ni ?da sauri ta fito da shanyayyun idanunta  waje tana cewa "no no sir me yasa zanyi haka?" ni sam ban yi haka ba kawai dai ..."sauran design's din dana baki aikinsu last week  sunyi ready "?ya katseta ta hanyar fad'ar haka  yana cigaba da kallonta kamar zai cinyeta,  shiru tayi ta kasa  cewa komai dan tuni ta ajiyesu a gefe tana  kan new desing's din da zasu gabatar  ne ,wani kyakkwan shu'umin kallo ya d'auketa dashi wanda yasa take tsigar jikinta d'aya bayan d'aya  suka fara mikewa tayi saurin cewa "no basu yi ready ba  sir "ko zan iya sani dalili ?."tayi shiru qirjinta na lugud'en bugu da qarfi .”

"wai mai yasa kika rainani har haka ?"sake fito da idanuwanta tayi sosai  tana kallonsa zuciyarta na sake shiga tashin hankali "na shiga uku ta fad'a acikin ranta “wallahi ta d'auka bazai nemesu da wuri ba yasa ta tattara ta ajiyesu "yaushe zaki fara bin umarnina?" yayi mata tmbyr yana qara taku d'aya zuwa gareta "yaushe ne idan na baki aiki zakiyi min shi cikin dad'in rai batare da 'bata lokaci ko jayayya ba "?ya qarasa maganar yana sake yin taku d'aya ya matso daf da inda take sosai yana mata wani wahalallen kallo." tayi saurin ja da baya tana furta kalmar "inna lillahi !”yau na bani me ya kai ni shiga wani aikin bayan ban qarasa masa nashi ba "?lallai maryama kin tarp match dan kin fara wuce limit dinki ,amman duk abinda nake ai ina yi ne domin shi ,ina yi dan na wanke masa zuciyarsa akan kuskuren da nayi masa, ya sake matsota sosai "ina jinki ki bani amsar tmbyoyina "saboda kin rainani yasa kike aikata min haka ko?

takure jikinta tayi waje d'aya tana wata irin kyarma tace "wayyo allah tsigar jikina " gbdy ta kasa motsi duk ta rikice sakamakon kusancinsu da yayi yawa dan har suna iya jiyo bugun zukatansu da saukar numfashinsu "wannan shirun ma kanshi cikin rainin da kika min ne ko ba haka ba ?"da sauri ta girgiza masa kai "alamun a’a!”idan ba haka bane taya ina magana kina jina amman kiyi min shiru?" kayi hakuri sir sabon aikin dana nemi izininka na fara "wa ya sakaki ?"wa ya baki izini ?yayi mata tambayar ajere yana sauke mata zazzafan numfashinsa a fuskarta da wuyanta ,ta firxgo numfashi da kyar sannan ta d’ago ta kallesa zuciyarta na karkarwa “banace bana supporting ba ?"kayi hakuri kace but .."but what ?wannan karon a matukar tsorace yayi maganar wanda yasa tasa hannunwanta duka ta toshe kunnenta tana durkushewa qasa a gabansa.”

wani dogon numfashi ya sauke yana binta da kallo ganin yadda ta gigice ta rikice ta mugun bashi dariya kasa rike dariyar yayi har sai data bayyana akan fuskarsa ,inda ya kamo gefen lip’s dinsa na kasa ya fara cizawa ahankali ahankali,suna cikin wannan halin sai ga oga amar tun daga nesa ya hango bayan mr ata kuma nan take jikinsa ya bashi maryama ce durkushe a gabansa domin dai yayi imani babu wannan macen a duniya da ata zai tasata gaba irin haka ."Jin shiru yasa maryama d'ago  idanunta sha'be sha'be da ruwan hawaye ta zuba masa tana “kayi hakuri nayi kuskure sir,amman zan ‘bata komai na aikin ,haka zalika zan dakatar da kowa kuma in sha allahu gobe zanzo maka da desing’s dinka .”ta qarasa maganar wasu hawaye masu zafi suna gangarowa akan kuncinta adaidai lokacin  oga amar ya samu qarasowa wajen. ya tsaya yana kallonsu da bayyana nen mamaki akan fuskarsa kafin daga bisa yace "ya haka ata ?".

Mr ata ya juyo ya kallesa alokacin da oga amar ya bud’e baki zai sake cewa wani abu nan take mr ata yaja hannunsa suka fita daga office din dan yasan zai iya masa ' baran 'barama  a gaban maryama shi kuma bai shiryawa hakan ba tukun, yana da plan akanta  suna shiga office dinsa oga amar yace "ata ka dinga jin tsoron Allah fa “me nayi?!” dan  ubanka ya kake  tsoratar da  yar mutane kaga yadda yarinyar nan ta fita haiyacinta tana zubar da hawaye wallahi zaka ballowa kanka ruwa ,kai yanzu soyayyar ma sai ka nuna mata seniority?"mr ata yayi bayyana nen murmushi mai d’an sauti kad'an abinda bai ta'ba yi ba kenan a tsawon rayuwarsa sannan yace "yarinyar nan wallahi bazaka ta'ba  gane rashin kirkinta ba bugani take kamar ta samu kwallon kafa  ga rashin bin umarnina ka shigo min da kaidodin na babu gaira babu dalili ." karya kakeyi ata " kai dai wallahi mugu ne sam maryama bata haka kawai dai kayi niyyar kasa yarinyar mutane kuka ne da sassafe "ai daman nasan haka zakace tunda kai ma sonta kake yi ."

Oga amar  ya kyalkyace da wata dariya yana kaiwa kafad'ansa duka "gsky ata ka gama dani amman kasani da son maryama nake da tuni an wuce gurin da sai dai ka bud'e idanunka ka ganta a gidana a matsayin matata "da kuwa anyi burouba!"ya fad'a yana zabga masa wata qatuwsr harara "sorry friend maryama taka ce kai kad’ai daman kace babu macen da zaka bi sai ita kuma naga hk sauran ka zama bita zai zai ko da yake shima ka fara zama " anji cewar oga amar "ai soyayyar yarinyar nan tana wujijjjiga rayuwata ,ni yanzu kiran da nai  maka nace mu hadu anan  shawara zamuyi  ina son naje nema aurenta "
“waya fada maka barno gabas take ,suka kwashe da dariya "suka samu waje suka zauna alokacin da karfe takwas ta buga wanda zuwa wannan lokacin wasu daga cikin maaikata sun fara zuwa "ina jinka abokina wannan labari yafi kowani irin labari dadi domin ina matukar son na g maryama a qarqashinka ."

Mr ata ya numfasa kana ya cigaba da magana a natse "ina son naje neman aurenta koma nace ina son tazama mallakina acikin tsukukun lokacin nan dan sai nafi samun kwanciyar hankali idan na aureta ahankali kuma sai na shigar da soyayyata sai dai  kasan wani abu bana son sweetheart da kowa nawa su san da wannna auren zai tsaya ne a tsakaninmu dagani sai kai ita kanta yarinyar bana son tasani yanzu “ya qarasa maganar tare da yin shiru ya zuba ma oga amar idanu yana son yaki me zai ce "Ko me yasa ka zabi kayi haka ?bayyana maryama a halin yanzu zai iya janyo min abubuwa da yawa. abu na farko idan sweetheart da sauran yan’uwana suka san mafarkina ce zata fuskanci mummunar tsana daga garesu kasamcewar naki zama da zabinsu abinda ka rigada kasani ne bazan d'auki raini ga matar danafi so ba haka zalika bazan wulakanta yanuwana da Mahaifiyata akanta ba,shiyasa nake son na aureta a boye ,muyi rayuwarmu dagani sai ita da yaran da zata haifa min ".

numfashi oga amar ya sauke "amman kace itama maryama din baka son tasani ?"a yanzu ba amman daga baya ai dole zata sani idan lokacin da ya kamata tasani yayi, zan aureta a  yanzu na dinga janta ajikina ina d’an rage zafi "tunda ita shasha ce da zata yarda ka dinga ta'bata batare data san meye matsayinta ba "wannan kuma matsalarta ce tunda ni nasan matsayinta ai shikenan."kai dai wallahi mugun jarababbabe ne “sosai kuwa number one ma ni kad'ai nasan irin dauriyar da nake akanta wallahi amar ina da mugun karfin shaawa akanta idan shaawarta ta taso mun kwana nake gabana a mike duk na rasa yadda zanyi ,inga ya maka jijiya ta bata kwanciya har sai asuba tayi wata rana ma haka zan yini kaga gara nasan abunyi.” naunayen ajiyar zuciya oga amar ya sauke yana cewa "ni dai gsky kayi tunani sosai akan wannan raayi naka gara ka fahimtar daita idan yaso sai abar maganar daga kai sai ita sai kuma ni da zan zamo sheida saboda halin rayuwa ".

“kai ma kazo da magana mai kyau amman kasan wani abu ?oga amar ya girgiza masa kai "bazan iya fahimtar daita da bakina ba "akan wani dalili ?i don’t know,kai dai kace tsoronta kake ji “wani irin tsoro kuma amar yarinyar da loma d'aya zanyi daita na gama daita ni kawai damuwar sweetheart ne data yanuwana ce banaso, sun dade suna tautaunawa a qarshe suka ajiye ranar da zasuje su samu baba gali ."qarfe goma daidai oga amar yayi masa sallama ya wuce  yayinda maryama ke ta faman kuka surayya wacce ta shigo ta isketa tana kuka ta fara  rallashi tana tambayarta dalilin kuka sai dai bata ce mata kalallahu ba dan haka taje ta kira yusura itama dai tmbyrta dalilin kukanta tayi a qarshe tace "ko dai mr ata ne ?"maryama ta gyada mata kai alamun eh me ya had’aki dashi ?tayi shiru dan bazata iya fad'a ba ,da kyar  yusura ta rarrasheta ta tsaida sheshekar kukanta tana cigaba da tmbyeta  "aikin banza kawai kuna damun kanku akan wannan  figaggar yarinyar kuma tunda kukaga   tayi shiru har yanzu taki cewa da ku komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki irin nata ai sai ku rabu daita haka ".sultana dake tsaye a bakin kofa ta fadi haka tana mazurai yusura kam ta yarda maryama tana da zurfin ciki sosai "ban wani d'auki lokaci mai tsawo daita ba amman na karanci maryama  din nan tana kafiya da zurfin ciki maryama ta kalleta da idanunta da suka canza kala "kina kallona kamar karya na fad'a akanki “tana gama fadar haka maryama ta d'auki jakar aikinta ta rataya a kafad’anta ta fita ta bar office din da idanu suka bita da kallo ."

Har qarfe biyu da wasu mintuna maryama bata dawo office ba, yayinda mr ata ya shiga office din yafi sau babu adadi amman bai ganta ba ya yi mamakin inda ta shige har zuwa wannna lokacin dan ya lura tun shabiyu bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba kuma shi bai ga fitarta ba dan hk ya kira layinta bai shiga ba ,hankalinsa ya dan tashi ya kira madam some zuwa office dinsa  bayan ta shigo ya kalleta atsanake yace "ko maryama tana ina ne ?na ganta dazu da safe ,”yanzu nake magana "eh gsky bansan inda taje ba amman yau din dai kamar bata da lafiya dan naga yanayinta wani iri kamar ma tayi kuka amman naga su surayya suna ta rarrashinta nafi tunanin ko akwai matsala daga gidansu ne sir "numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare yana cewa "you can go "!ta juya a natse ta fita .”

Ya mike ahankali ya nufi d’akin da camerar cctv suke masu kula da bangaren wajen suna ganinsa suka mike cike da girmamawa domin dai duk lokacin da zasu ganshi da kansa abu ne mai mahimanci ya kawosa ,mr ata ya zauna a mazauninsa na musam man wanda an tanadi wajen ne dan shi kad’ai camera mai kula da bangaren office dinsu maryama zuwa first flow ya bukaci gani tukun, da sauri suka fara tariyo masa wanda zuwa wannnan lokacin ya hade hannunwansa duka waje d’aya ya tokare habarsa yana duban screen din tv ahankali ya fara kallon d’aukar yau inda mutane da suke shiga da fita har yazo kan shi da maryama yayi shiru yana kallon shi daita sosai yaga yanayinta cikin tsananin damuwa d’aukar tayi gaba zuwa inda su surayya da yusura ke tsaye akanta da sanda sultana tayi mgnrta ta juya ta bar office din kuma at the same time alokaci maryama ta mike tana goge hawaye ta fice daga ma’aikatar gabad’aya .

"me yarinyar nan take nufi dashi ?"yasan duk akan abinda ya faru ne da safe ta kama hanya ta wuce gida abunta ahlin lokacin tashi bai yi ba yayi kwafa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ."bayan ya gama ganin komai ya mike ya fito daga office din cike da jin kai ya koma office dinsa ransa a matukar bace dan ganinsa maryama tayi mugun mugun rainashi babu wani maaikaci ko maaikaciyar da zata masa haka ya d’auka itama dan matsayinta ne yake d’aga mata kafa yaja tsaki yana rike kugunsa da hannu d’aya,bangaren maryama kam kai tsaye gidansu ta wuce abunta, ta zarce zuwa bangaren aunty tayi kwanciyarta akan doguwar kujera tare da kashe wayarta nan da nan bacci ya dauketa sakamakon daman daren jiya bata runtsa ba ."

******

Qarfe takwas  na dare da mintuna ashirin mr ata ya tako cikin parlour'n Mami wanda babu motsin kowa sai na na'urori da kuma hasken qwayaye, samanshi ya nufa kai tsaye yana furzar da hucin iska daga bakinsa yana  tuno gamuwarsa da maryama d'azu da safe sannan zuciyarsa na tafasa akan barin office da tai batare da neman izininsa ba gamuwarsu a gobe kawai yake jira dan  lamarinta na matukar 'bata ranshi ya tabbatar da cewa ta tafi ne dan musguna masa ta nuna masa iyakar shi wanda hakan ya sake tabbatar masa da bai isa daita ba  kamar yadda ya isa da duk wanda ke qarqashinsa ,shima kuma  yana nan akan nashi qudurin da raayi bai ga abinda zai sanya shi daga mata qafa  ba koda kuwa suma zai dingayi akanta ko mutuwa zai yi sai ya juyata ya tankwasata ya laddatar daita, qarfin soyayyarta bazai sa ya juri iskanci ba haka zai aureta ya kasa zama tsayayyen nmj acikin gidansa "never maryama dolenki ki bini sannan ki zauna lfiya."

Tsab tsab ya iske dakinsa koina neat sai kamshi turare yake wannan kuma yasan aikin sweetheart dinsa ne ita ke tsayawa akan masu gyara masa daki
A natse   ya qarasa bakin gado ya soma fidda kayan jikinsa byn ya gama cirewa bandaki ya shige yana niyyar hada ruwan wanka,yaga an had'a masa tsayawa yayi cike da shakku yana tunani ta ina aka samu haka? , cikin kokwanto ya sanya hannunshi cikin ruwan, anya ba jinnu ke neman yi masa wasa da hankali ba,dan tun da yake sweetheart bata ta'ba sawa an masa haka ba ,share mamakinsa yayi  yayi  wankan ya fito ya saka kayan shan iska farare sol ya fito yana taka step da kyar turus yayi sakamakon ganin maryam da sweetheart tare da aunty shahida zaune suna magana ganinsa yasa duk sukai shiru ya qaraso ya gaishe da mami da aunty shahida duk suka amsa masa ".maryam tayi karfin halin gaishesa duk da tasan bazai amsa mata ba "ina yini yaya ?"shareta yayi kamar yadda ya saba “ adamcy maryam na gaisheka ".

“lafiya!” ya fad'a atakaice sannan ya zauna mr ya daura kafarsa daya akan daya ya dauki remut ya kunna tv ya Kure volum alokacin da aunty shahida da maryam suka mike "to mami mu mun wuce sai an kwana biyu kuma "Allah ya kaiku lafiya zan lekoku in sha allahu maryam ki kula da kanki ki dinga shan maganinki akan lokaci Allah ya sauke min ke lafiya bai ji abinda suke tautaunawa ba shi dai yaga sun fice ko cikakken minti goma basuyi ba sai ga baba qaramin ya shigo kamar wanda aka jehosa  kai tsaye kan mr ata yayi yana nunasa da dan yatsa yana cewa "duk tsarinka ne bana wacce sabuwar maaikaciyar bace maryama akace sunanta ko me ,to kasani   na samu labari komai kuma bamu yarda ba bamu amince ba ayi wani aiki a boye sai dai a bari lokacin da kowa ya hada nashi sai ayi atare" .

Baba qarami ya kalli inda mami take zaune yana sauke numfashi  “ki gaya ma danki dan nasan yana da matukar taurin ka idan kuma yayi Kuskuren yin yadda nace zai hadu da mummunar bacin raina da bai ta'ba gani ba ."wai meke faruwa ne baba qarami kai da danka kullum sai a jiku "karki qara cewa dana dan ba dana bane nasan ya'yana shima yasan ubansa numfashi mami ta sauke kana tace "shikenan Allah ya kyauta karka damu baba qarami zai ji maganata in sha allahu company AGC din ma zan sa ya bar maku tunda shi allah ya rufa masa asiri yafi qarfinsa " okay haka ma zaki ce ?to me kake son nace wannan yaron danka né halak malak kace a'a  ."adamcy danka ne banga amfanin idan  zakayi mgn dashi ba ka dinga daukar zafi ,idan kabi shi a hankali zai yi abinda kake só ta juya inda mr ata yake zaune wanda yayi kamar tunda akayi duniya bai san da wani halitta baba qarami ba bare ma yasan me yake cewa .”

"adamcy  tashi kaje dakinka zan kawo maka abincinka "zazzafan numfashi  ya sauke sannan ya yunkura ya tashi ya wuce cikin zafin zuciya saka makon bai samu damar fadawa baba qarami mgn ba  kuma daman mami tayi haka ne saboda gudun abinda zai biyo baya ."da kyar mami ta sauko da baba qarami akan lallai adamcy zai janye akan komai suyi duk yadda suke so jin haka  ya hakura sai dai tafiya yayi yana bambame  yayinda mr ata ya shiga zariya a parlour'nsa goye da hannuwansa duka abayansa  tunanin wanda ya fad'a ma baba qarami shirin maryama yake." tabbas ko waye yasan bai wuce sultana ba saboda da ita aka shirya komai . tafiya ya fara yi acikin parlour'n lallai tayi haka ne dan ta janyowa maryama mummunar tsana daga garesa amman shi hakan ba damuwarsa bace dan zai iya karawa da kowa  most especially akace za'a ta'bo masa zuciyarsa , abarshi shi a karon kanshi yayi mata  duk abinda yaga dama amman wani yayi mata he can't take it sai inda qarfinsa ya qare,da fari bai yi suppoting din plan din maryama ba amman a yanzu zuciyarsa ta yarda kuma ta amince bazai karyar mata da gwiwa ba zai yi supporting dinta da dukkanin karfinsa da rayuwarsa.”

Mmn Sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 BOOK 3
  2. 2 BOOK 3
  3. 3 BOOK 3
  4. 4 BOOK 3
  5. 5 BOOK 3
  6. 6 BOOK 3
  7. 7 BOOK 3
  8. 8 BOOK 3
  9. 9 BOOK 3
  10. 10 BOOK 3
  11. 11 BOOK 3
  12. 12 BOOK 3
  13. 13 BOOK 3
  14. 14 BOOK 3
  15. 15 BOOK 3
  16. 16 BOOK 3
  17. 17 BOOK 3
  18. 18 BOOK 3
  19. 19 BOOK 3
  20. 20 BOOK 3
  21. 21 BOOK 3
  22. 22 BOOK 3
  23. 23 BOOK 3
  24. 24 BOOK 3
  25. 25 BOOK 3
  26. 26 BOOK 3
  27. 27 BOOK 3
  28. 28 BOOK 3
  29. 29 BOOK 3
  30. 30 BOOK 3
  31. 31 BOOK 3
  32. 32 BOOK 3
  33. 33 BOOK 3
  34. 34 BOOK 3
  35. 35 BOOK 3
  36. 36 BOOK 3
  37. 37 BOOK 3
  38. 38 BOOK 3
  39. 39 BOOK 3
  40. 40 BOOK 3
  41. 41 BOOK 3
  42. 42 BOOK 3
  43. 43 BOOK 3
  44. 44 BOOK 3
  45. 45 BOOK 3
  46. 46 BOOK 3
  47. 47 BOOK 3
  48. 48 BOOK 3
  49. 49 BOOK 3
  50. 50 BOOK 3
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});