Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

BOOK 3

Maradams Book 3 Complete Hausa Novel 2,220 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 6

     sai da gabansa yayi wani mummunar fad'uwa, zuciyarsa ke qoqarin motsawa amman ya dinga kwantar daita dan idan ya bari maganganunta sukai tasiri zai yi daya sani dan haka yayi shiru kawai ya cigaba da kallonta ba dan ya rasa abun yi  ba she's the most beautiful  girl I have ever seen in my life ya fad'a acikin zuciyarsa yayinda fuskar maryama ke cikin wani yanayi na fushi sai dai kuma kwayar idanunta na kanshi ta tsura masa idanunta kamar yadda yayi mata muryarta a sanyaye ta cigaba da motsa lip's dinta "kana tunanin dan zanyi aiki daku zan d'auki  wannan wulakanci ne ?no I can't take it any more ta  fad'a tare da zaro masa  fararen idanunta ,da wani irin sauri ya tashi daga kan kujerarsa yana cewa" yana da matukar mahimanci kisan wani abu , yana da kyau  kisan cewa kinyi mistake arayuwarki ba wai wulakanci bane kmr yadda kika d'auka, har sau biyu  kina samu aiki damu kina rejecting wacece ke da zakiyi rejecting din  aiki alokacin da kika só sannan ki so aiki alokacin da
kika so "yayi mgnr yana kallon cikin kwayar idanunta ."

Ahankali ta kawar da  kanta zuwa gefe tana hura  hanci tace  "to kuma saboda banyi joining aiki daku ba alokacin da kuka so sai ya zama matsala ? wani irin kallo yayi mata mai tattare da gargadi sannna yasa hannusa d'aya cikin aljihunsa yana kallonta yana jin wani azababben qaunarta na bin jinin jikinsa ahankali ya dinga sauke numfashi  kamar wanda  yayi  gudun tsare sannan yaja tsaki ya kai hannu sumar kanshi ya shiga ya mutsawa yana ciza gefen lips dinsa da d'an karfi "ya Allah karka sa yarinyar nan ta bani matsala "yayi mgnr a kasan ransa still yana cigaba da kallonta ." kusan mintuna goma ya d'auka yana  kallonta sannna ya koma ya zauna yana sauke numfashi ya sake d'aukar wani  file ya cigaba  dubawa sakamakon rashin abunyi "kawai kuce kun nemi na dawo ne saboda kunsan ina da baiwar fikira da zaku amfana dashi well shikenan kawai sai ku rubuta ku ajiye ya zama tarihi ga AGC  compaing ,sun ga maryam hussein na da baiwar fikira sun dawo daita aiki  byn sun koreta a ranar farko ."yana jinta  amman yayi mata banza yayi tamkar bai ji abinda ta fad'a ba haka kuma  bai d'ago ya kalleta ba ya cigaba da abinda yake yana satar kallonta  ta kasan ido yana danne bugun zuciyarsa dan wani irin sabon yanayi ya dinga jin yana shigarsa."

yayinda maryama tayita fad'ar maganganu  son ranta wannan karon kam a matukar zuciye ya  ajiye file din da yake rike dashi ya sake tashi  ya tsaya cak a gabanta yana sauke numfashi har suna iya shakar numfashi juna  da jin bugun zuciyoyinsu "Keep your mouth shut  ki kama kanki kisan irin maganar da zakiyi anan dan ba'a kawo min raini , ba'a sakani kuma ba'a hanani and no body question me okay ."ya fad'a a matukar tsawace yana  sanya kwayar idanunshi cikin nata, shi aiki da mahimanci ake d'aukarsa kamar yadda  shi mai kasuwanci yake d'aukar kasuwancinsa ,ban dawo dake dan kizo kina min haukan banza anan ba, na koreki ne saboda na nuna miki kuskurenki, sannna na dawo dake  ne saboda tausayawa domin na fahimci kin shiga tashin hankali mai tsanani a wancan ranar dana koreki idan zaki iya aiki damu kiyi  idan kuma bazaki ba "leave!ya nuna mata hanyar waje da d'an yatsansa yana fesar da huci mai zafi daga bakinsa yayinda zuciyarsa ke cike da matsanancin fargaba dan yasan kad'an da aikinta zata iya  juyawa  ta kama gabanta ."

adduar ya shiga yi domin neman taimakon Allah" ya Allah kada kasa zantuttukana suyi tasiri a zuciyarta Allah kasani ina matukar son yarinyar nan da d'aukacin rayuwata  ta shiga zuciyata dayawa ta sace zuciyata,ya  Allah kasa na shiga cikin rayuwarta kamar yadda ka shigo daita cikin rayuwata domin ta zamo abokiyar rayuwata ta har abada ina matukar qaunar wannan halitta taka ya Allah ka jarabeta da soyayyata tun kafin na kai ga furta mata soyayyarta dake raina domin na azabtu akanta ,na sha wahala akanta ,ya Allah ka tausaya min ."Ita kuwa maryama shiru tayi na second goma tana dubansa batare da tace masa komai ba har ya gama maganarsa sai dai maganarsa tasa zuciyarta tayi sanyi daga zafin datayi tare da tunani ,duk da ya jefeta da kalmar hauka amman kuma ta wani bangaren sai taji  kamar ya fita  gsky domin kuwa a wannan zamani aiki wahala yake, idan ba kana  da hanyar samunsa ba  ko wata baiwa ba sai dai ka mutu haka babu aiki amman da kwalinka da karatunka sai su zama banza bazasu maka amfani ba ."dan haka Ke maryama kiyi maza maza ki  shiga taitayinki ki dawo cikin hankalinki karki yarda Kiyi kuskuren da zaki sake rasa aikin nan dan haka muryarta a sanyaye tace "shikenan zanyi aiki da amana da gasky kuma in sha allahu kamfaninku  zatai alfahari da ... "da kyau go back to work ." yayi sauri katseta ta hanyar  fad'ar hk  batare daya kalleta ba duk da kallon nata yake da bukata dan baya gajiya da kallonta amman ya kasa sai ma boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke dan maganrta ba qaramin dadi sukai masa ba ."

"Yanzu ko zan iya sanin da me zan  fara ?meet sectary "ya fad'a a dake ,ta juya jikin a sanyaye  har ta kama handle   zata bud'e kofa ya tsaidaita ta hanyar cewa "ke .." ta tsaya cak batare data juyo ba  sai dai qirjinta na wani irin bugawa  da sauri sauri "idan zaki zo  aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package  din,  kizo cikin tsari shigar aiki Kmr  kowani ma'aikaci ."da sauri ta juyo tana masa kallon tsana zuciyarta cike da mamaki to mai ya samu kayanta ?ta jefawa kanta tambaya tana dubansa bai  kalleta ba sai dai ta  kasan idanunshi yake d'aukar kallonta tana kallonsa ya janyo system gabansa ya cigaba da aiki ta bud'e kofa ta mayar  da karfi  ji kake kiiiiii  har sai daya d'ago yana duban kofar kai kawai ya girgiza tare da furta cray girl kawai ."maryama ta fice tana jan tsaki ranta duk babu dadi  "a hankali ta dinga  tunanin maganga nunsa gabadaya maganarsa babu dadi sai bugar da zuciya  da saka mutun cikin tashin hankali ta sake jan tsaki tana maimaita kalmarsa ta karshe "idan zaki zo aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package  din, kizo cikin tsari Kmr  kowani ma'aikaci har ta shiga babban  office din daaka tanada masu a ranar farko maganarsa bata bar zuciyarta da gangar jikknta sun huta ba ."

anan taga yusura tana ganinta  ta qaraso da sauri ta rungume maryama  tana cewa  "kai naji dadi kawata da kika sake dawowa amman fa Kiyi hattara da mr ATA  da mr sultan dan ba kai  garesu ba kowa anan tsoronsu yake ji ,suna cikin mgn  sultana ta shigo tana cewa "maryam hussein  sannu da dawowa compaing mu " wani kallo mryma  tayi mata na mamaki  fuskarta da alamun tmby "yes ! Ok fa a she bakisani ba ko, to bari na fadi miki wannan kamfanin had'in gwiwar iyayenmu ne ni cousing sister din Mr ATA ce nan maryama ta fahimceta sai dai bata ce mata uhmm bare uhmm uhm  .""Kinyi  sa'a da kika   dawo wannan kamfanin  amman kuma Kisani  nice nan  sanadin dawowarki domin nice na nunawa ya Adam zanenki da kikayi wanda tashin hankali an koreki yasa kika tafi kika barshi "shiru  maryama  tayi kafin a hankali tace "na gode excuse"ta fad'a sannan ta ra'ba ta gefenta ta wuce ."
Gabdaya suka samu guri suka zauna akan makeken table din dake  zagaye da office din ."maryama ta bud'e jakar kayan aikinta  ta d'auko abun aikinta hanakalinta kwance ta fara gudanar da aikinta "wannna duk wahalar banza kikeyi domin duk kwarewarki bashi zai sa ki burge ya adam  ba tana gama fadar haka fita daga office din maryama tabi bayanta da kallon mamaki  ."

Aunty hasana ta qaraso ta mikawa hjy granny kofin shayi ta amsa tare da cewa "na gode ta kai cup bakinta  sai dai da sauri ta kirata tana cewa " hasana bai kamata ina shan sugar haka ba amman kalli yadda kika zabga min sugar cikin tea ai ko baa fad'a miki  ba Kinsan bai dace mai shekaruna haka ta sha sugar ba duk maganar da hjy granny take Aunty hasana bata jinta saboda hankalinta na  kan kallon tv "ke hasana bada ke nake magana bane ta juyo a dan firgice tana cewa  "na'am hjy kina magana ne  ?ya zaki saka min sugar haka acikn shayi ?abun kunya kawai ace kamarki ace shayi ma sai anci  gyaranki  ba kya ganin yadda maryama  take komai nata tana kokarin kula dani fiyye dake  sam bata kuskure wajen abinda take min  amman ke babu abinda kika iya sai aikin zagin ya'yan mutane da saka ido bazaki tsaya Kiyi koyi  da mutanen kirki ba." zaginta tayi sosai ai kuwa haushi ya kamata "hjy ai daman ni na dade dasanin kin tsaneni  bakya qaunata komai zaki fad'a ki fad'a ba damuwata bace" idan dai zaki canza ki canza umma ta shigo tana tmbyr lafiya hjy nake jin fad'anki "ina fa Lfy wannan yarinya ce anyi mgn zata fadawa mutane babu dadi me kike son nayi miki hjy ?" bansan me nayi mata ba komai nayi mata  sai ta  kushe to ki daina sakani aikin ki dinga saka wadan da kike so aranki ta fad'a hawaye na cika idanunta."

umma ta dafata  tana cewa "haba hassana ki daina fadawa mahaifiyata magana haka sam bazan ji dadi  ba  bugu da qari Ke ma uwa ce idan yaranki suka miki bazaki ji dadi ba "to ni yanzu me nayi dag suga yayi yawa a tea sai  ta hau min fad'a karbi tea ki sha kiji wallahi ba  wani suga na saka ba "ki barta kawai  itama ai ta haifa yaya idan ma bata haifa ba akwai na kasa daita zasu mata  duk abinda tai min sam bata son gsky tunda take min rashin tarbiya kinji na ta'ba magana akai idan ba yau ba ?dan allah kiyi hakuri hajiya bazata sake ba suna cikin haka maryama ta shigo cike da murna ta tsaya  kusa da umma tana cewa "umma  ki tayani murna na fara aiki ." umma
tai murmushi cike da farinciki Allah yasa kin fara kenan "Ameen ya allah na gode sosai  babu wata matsala dai ko ?babu matsalar komai umma duk da dai mr ata ya dan so yayi min hauka amman nayi hakuri .zanyi aiki dashi ne kawai saboda  bazan iya bari wani abu ya samu komai naki ba faduwar ki faduwar gabadayanmu ne ."shiru umma tayi kafin tasa hannunta ta  kamo maryama karki ce komai umma duk abinda nasan zakiyi farinciki zanyi shi koda kuwa raina ne zan iya mallaka miki shi umma ta lumshe mata ido tana cewa " na gode sosai maryam allah yasa albarka hatta hjy ma taji dadi  suka saka a tsakiyarsu suna saka mata albarka ."

*******

Baba qarami yana zaune a cikin wani qaramin office dake cikin falon hjy zulai  an tanadi office din ne saboda marigayi alhaji tariq alokacin da yake raye nan ne wurin zamansa ATA ya sauko daga samansa sanye cikin  wasu hadaddun kananan kaya marasa nauyi kallo daya yayi masa ya d'auke kansa zai nufi kofar fita yaji sautin muryarsa "Adam zo nan ya tsaya Jim da kamar bazai je din ba sai kuma ya yi wani tunani ya juyo a hankali ya shiga har inda yake zaune fuskarsa a hade kamar ko yaushe "ka zauna saboda me kenan zan zauna? ya tamvayesa atakaice yana hura hanci baba qarami yayi shiru yana dubansa "kana da magana ne ?zan kiraka ne  idan  bani da abinda zance ? ya fad'a a zafafe shiru ata yayi ."Ka natsu ka shiga hankalinka ba wai ana jin tsoronka bane me ake ciki akan maganar danayi maka akan sultana idan kaki auren hindu ka turata magarkama sultana fa uwarta na bukatar jin raayinka?babu wani abinda ake ciki dan bazan yi abinda Zanzo daga baya ina danasani ba sultuna is not my test ina da raayina haka ma hindu "da alamun  zaka dawo da zabin mahaifiyarka ya zama shine  raayinka .? a fusace yace "yes !"yana kallonsa
"ka koyi respect Adam sam baka da respect bakasan yadda ake magana da babba ba zaka iya fad'awa mahaifinka haka ? Ko da yake wannan uwar..."
"enough baba qarami ."! ya fada a tsawace karka sako sweetheart cikin maganarka aure ne  ni nake da ikon aure and sultana   she's not my tast abawa wani kawai "bari na fad'a  maka wani abu komai zakayi wannan karon sai dai kayi amman sai  ka auri wata daga cikin family's din nan bare kuma tunda  sultana tace tana sonka an gama maga.." kafin ya qarasa mgnrsa tunin  ata  ya juya ya barshi "kai dawo nan !"ata  ya sake dawowa hannuwansa duka cikin aljihu" "wai meye haka ne baba ?nifa nasan abinda zai yi daidai da rayuwata dan allah ka barni na huta bana bukatar wani auren zumunci arayuwata a yanzu shin  lallai ne sai ni zaku bawa ya'yanku ."?

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Table of Contents

Chapters

50 chapters
  1. 1 BOOK 3
  2. 2 BOOK 3
  3. 3 BOOK 3
  4. 4 BOOK 3
  5. 5 BOOK 3
  6. 6 BOOK 3
  7. 7 BOOK 3
  8. 8 BOOK 3
  9. 9 BOOK 3
  10. 10 BOOK 3
  11. 11 BOOK 3
  12. 12 BOOK 3
  13. 13 BOOK 3
  14. 14 BOOK 3
  15. 15 BOOK 3
  16. 16 BOOK 3
  17. 17 BOOK 3
  18. 18 BOOK 3
  19. 19 BOOK 3
  20. 20 BOOK 3
  21. 21 BOOK 3
  22. 22 BOOK 3
  23. 23 BOOK 3
  24. 24 BOOK 3
  25. 25 BOOK 3
  26. 26 BOOK 3
  27. 27 BOOK 3
  28. 28 BOOK 3
  29. 29 BOOK 3
  30. 30 BOOK 3
  31. 31 BOOK 3
  32. 32 BOOK 3
  33. 33 BOOK 3
  34. 34 BOOK 3
  35. 35 BOOK 3
  36. 36 BOOK 3
  37. 37 BOOK 3
  38. 38 BOOK 3
  39. 39 BOOK 3
  40. 40 BOOK 3
  41. 41 BOOK 3
  42. 42 BOOK 3
  43. 43 BOOK 3
  44. 44 BOOK 3
  45. 45 BOOK 3
  46. 46 BOOK 3
  47. 47 BOOK 3
  48. 48 BOOK 3
  49. 49 BOOK 3
  50. 50 BOOK 3
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});