Chapter 3
PART 35
TARE DA SADIN MAA.
DAGA Al-Hada Hada Hausa Book stories
.
misalin karfe biyar na yammacin litinin kaltum yar makaranta sanye take da uniform na makaranta harda jakar littatafanta agoye a bayanta tana tafe a bayan babur na adai-daita sahu Keke napep, bata tsaya ako inaba sai a kofar gidan su shahida ta zaro kudi ta biya mai napep yatafi,
ta kalli kofar gidan tsaf tana tunanin yanda zataga shahida, garin waige-waigenta ta hango wannan zukeken saurayin zaune akan motar sa yana dubanta daga kofar gidansu wato dan gidan general tukur daga yanda yake kallonta kasan akwai magana, bayan duban mamaki da ganinta akwai duban dama ke nake nema babu mai kubutar dake daga wajena yau saikin fadi abunda kike zuwanan kike nema,
bata tsorata ba saima ta harareshi ta kawar da kai gefe ta cigaba da tsayuwa akofarsu shahida, ya tsaya kawai yana duban ikon Allah yayinda kansa yayi masa gingiringim yayi sauri ya cire bakin gilashin da ya ragemasa ganinta sosai yayi sauri yayi kamar ya kwallawa sojojin dasuke yi musu gadi kira su kamo masa yarinyan nan sai ya fasa ya zura mata ido don yaga gudun ruwanta amma tabbas ya kudiri niyyan a yau dai bazai bari yarinyannan ta subuce masa ba sai ya damketa yaji wacece ko waye ya aikota kuma me take nema a wajen shahida.
tsawon mintina ashirin tana tsaye shi kuma bai daina kallon ta ba sai ga shahida da kannenta sun taso daga islamiyya suna isowa wajensa suka duka suka gaishe da makwabcinsu cikin ladabi ya amsa gami da cewa shahida ga bakuwarki can tana ta jiranki tun dazu,
shahida ta dubi kofar gidansu domin can ya nuna nan da nan shahida ta isa inda kaltum ke tsaye suka rike juna cike da murna,
kaltum ta rike hannun shahida tayi mata magana cikin sirri sai shahida ta waiwayo ta kalli gidan general tukur gami da nunawa da hannu abun mamaki sai gani yayi sun dunguma gidansu yana kallon kaltum duba na mamaki yayinda take masa duba na gani kashe ni bana tsoro,
suka wuceshi kai tsaye suka tura katafaren get din gidan suka cusa kai basu dauki dogon lokaci ba wajen amsa tambayoyin sojoji masu gadi kasancewar sunga kaltum da yar gidan wato shahida shahida ce ke gaba yayinda kaltum ke biye da ita tana tafe tana duban gidan yayi mata kyau kuma ya tsaru tunda farfajiyar daga farfagiyar gidan har zuwa babban falon gidan, abunka da gidan yan boko komai an jere shi inda a inda ya cancanta kasancewar babu kananan yara dazasu bata waje dan haka ko ina tsaf-tsaf kamar an tande da harshe, babu kura ko datti ko da yake ba abun mamaki bane kasancewar hadiman gidan suna da yawa mata da maza kowa da bangarenda yake kulawa dashi.
a babban falo kaltum ta zauna yayinda shahida ta kutsa kai can ciki tana rada sallama domin basu sami kowa a falonba kalle-kalle kawai kaltum keyi yayinda idanuwanta suka dira wani rusheshen hoto enlargement amanne a jikin bango da alama dai hoton yan gidan ne kakaf uwa da uba da ya yansu,
nan da nan kwakwalwarta ta fara tuno mata lbr da madina ta bata don bata manta da sunayensu ba tace aranta ga general tukur da mummy hafsat ga babbar yarsu Surayya ga yan autansu tagwaye hassan da hussaini daga nan kuma takasa tantance Abba da mabiyinsa Anas saboda girmansu daya kamarsu daya kayan jikin su ma iri daya a hoton, kuma irin wannan fuskar ta wuce a kofar gida don haka ba tantama kanin Abba ne, taci gaba da jimamin mutuwar Abba a ranta yayinda hawaye ya cika mata ido a yayinda ta ayyanowa Abba da Madina rayuwar aure domin sundace da juna kowannensu kyakkyawane, Abba Allah Ya jikanka ka yafewa Madina itama bata kinka,
kaltum ta fada azuciyarta yayinda taci gaba da duban fuskar Abba da kaninsa kasancewar ta rasa waye Abba a cikin su, shahida ne ta katse mata tunanin da ta keyi tace wai ki shigo inji mummy hafsat tana falonta, kaltum taji zuciyarta ta harba sai yanzu tafara fargaba, ta fara tunanin abunda zai je ya zo, kada fa haryanzu suna kufule da Madina kuma ace suna nemanta su kama ta fushin da sukeyi da Madina ya shafeta gashi ta shigo lungu ko duka ne kafin ta samu ta fito angama dirkarta, ga uwa uba sojoji masu jajayen ido a bakin get sai yanda Allah Ya yi da ita yau kenan, ta fara jero salati a zuciyarta na neman agaji daga rabbis samawati Ya taimaketa ta isar da sakon da ta kudira a ranta ba don ta sami wani abu ba kuma badon ta burge kowa ba sai don ta taimaki Madina ta wanketa daga zarginda akemata domin tunda ta dawo ta kasa samun sukuni da kwanciyar hankali har saita fitar da abunnan aranta zata huta koda fadarshi shine hanyar ajalinta,
shahida na gaba kaltum na biye da ita a baya har suka isa katafaren falo na alfarma a inda idanuwanta ya hasko mata wata lafiyayyiyar mata mai kamala, yanda mummy hafsat ke duban kaltum haka itama kaltum ke dubanta, dukansu mamaki ne fal a idanuwan su,
kaltum bata zauna a kujerunda suke farko-farko ba har saida ta karasa gaban mummy hafsat ta zube kasa ta kwashi gaisuwa cikin fara'a ta amsa tayi mata izinin ta tashi daga kasa ta hau kan kujera saboda sanyin tiles,
kultum ta gyara zama ta girgiza kai tace nan ma ya isa mummy hafsat,
kiran sunan ta datayi shine ya kara mata mamaki kasancewar ko amafarki bata taba ganin mai kama da kaltum ba balle tace yar gidan wane ne ba, ta gyara zama ta dubi kaltum tayi murmushi cike da zumudi ta tambayeta yar makaranta yaya sunanki ?
Daga ina ?
Kaltum tayi murmushi ta amsa sunana kaltum daga nassarawa G R A nake ina makaranta a crensent collage ajina shida, haryanzu dai bata amsa mata tambayanta ba saima hargitsa mata tunani datayi mummy hafsat ta yatsuna fuska kadan tayi shiru can tace ke yar gidan waye kenan?
kaltum tace yar gidan malam sale a gidan alh Adnan muke....
a fusace kyakkyawan saurayin nan ya turo kofa ya shigo damin dama labe yake ajikin kofa yanaso yaji abunda kaltum ke tafe dashi sai yaji ta shiga shirme kuma daman bai yarda da ita ba, ya daka mata tsawa mai firgitarwa har saida kaltum ta zabura ta dafe kirji,
yace mummy kirabu da yarinyannan bata da gaskiya tunba yau ba take zuwa gidan nan tana leke-leke ba, munafuka ce, ki barni da ita kawai in sa su Ashiru masu gadi suyita gana mata azaba harsai ta fadi wanda ya turo ta a mota da take zuwa wani direba yake kawota shine take amfani da shahida tana tambayanta sirrin gidan nan, yau kuma ta shigo da kanta gashi nan tana kame-kame yau sai kin gwammace baki shigo gidan nan ba.
yayinda yake kwanto belt din jikinsa mummy hafsat ta jawo kaltum jikinta ta daga hannu wa dan nata ta dakatar dashi gami dayi masa gargadi kada ya sake yakaraso gabanta balle yataba yarinyan nan da sunan duka, a tsaye yake rike da belt din sai tsuma yakeyi don bacin rai yayinda kaltum ta rushe da kuka hakama shahida kukan takeyi sai kakkarwa jikinsu yakeyi mummy hafsat tana rike da hannun kaltum tana durkushe agabanta, tasa hannu ta share mata hawaye tace daina kuka fadamin meke tafe dake?
waye ya aikoki?
me kike nema?
kaltum ta share hawaye tace babu wanda ya turoni nina nemo gidan dakaina nazo..
ya sake kufula ya cije lebe yaji tamkar ya damko wuyan ta ya shake, mummy hafsat harararsa takeyi alamar karya kariso, ta dago da kan kaltum sama tace yarinya kimin bayani yanda zan fahimceki ban san ki ba amma kekin sanni har kina kiran sunana dasai agida ake fada min balle ince a wajen aikina kika sanni ke yar sakandarine ko jami'a bakije ba balle ince ke dalibatace, meke faruwa ne kaltum ?
Kaltum tayi ajiyar zuciya ta matse hawaye game da gyara zama ta sunkuyar dakanta kasa ta fada cike da fargaba mai yawa don bata san abunda furucinnan nata zai haifarba, farin ciki ko bakin ciki,
awajen Madina naji sunanki ita tabani lbrinki da kwatancen gidanki.
su dukka ukun suka maimaita a lokaci guda MADINA!!!
Zuciyoyinsu cike da mamaki shahida ta mike zunbur ta dafe kirji a inda aka hau kallon kallon a tsakaninsu su hudun ba tare da wani ya kara iya cewa komai ba,
kaltum ta dubi kowannensu daya baya daya ta ce eh Madina mamar Abdul Malik Abdul hakim da shahida tsohuwar matar Tasi'u itace ta bani labarin rayuwarta kakaf harma ta sako zancen nan gidan general tukur da mummy hafsat tayimin dalla-dalla akan rasuwar Abba, Madina ba itace silar hatsarin Abba ba, ba mayya bace bata taba sanin yadda ake maita ba, Madina musulma ce mumina mai rikon addini wacce bata dauki rayuwar duniya da zafi ba, ta fada ta maimaita irin tsananin son da takeyiwa Abba musamman bayan ya mutu hawayenda,
kaltum ke fitarwa saida na mummy hafsat ya linka nata yayinda na shahida ya linka nasu dukka, saurayin ya jefar da belt kasa ya dafe kai yayi wuf ya fice itama shahida sai ta zankada da gudu waje akabar kaltum da mummy hafsat sunata kallon kallo,
zuciyar kaltum ta cika da fargaba kasancewar bata fuskanci matsayin labarinta a wajensu ba, bata san matakinda zasu dauka ba ita dai daman ta kudiri niyyar saita isar da sakon nan dayan biyu ko ta mutu kotayi rai, Shahida ce ta shigo tare da samari guda 2 ko ba a fada ba yayun tane fuskarsu iri daya su dukka sak Madina da alama daya daga barci aka tasoshi daya kuwa shirin filin ball yayi zaije kwallo hankalinsu a tashe tun kafin su shigo cikin falon idanuwansu sun leko suna ta kokarin hasko kaltum zasuyi magana mummy hafsat ta dakatar dasu ta nuna musu alamar suyi shiru sannan ta yi musu nuni da kujeru alamar su zauna, haka kuwa akayi kowa ya zauna yayi carko-carko ga tagumi iri-iri yayinda zuciyoyi suka hau bubbuge-bubbuge wajen tsaro labari daban-daban,
sautin ajiyar zuciyarsu ne kadai yake tashi a falon hakika sun kagu a fara bayani, wayar mummy hafsat ne ta dau ruri yayinda ta mika hannu kan teburin dake gefenta ta dauka ta duba sai ta ambaci kalmar AlhamduLillahi sannan ta danna, Sumayyah tukur ce ta fada cikin farin ciki da tsantsar Kauna,
mummy kina gida?
Gani nafito zanzo na ganki tunjiya nake missing dinki har mafarkinki nayi nace meyayi zafi in hakura da aikin mana yau nazo na yini guda naga uwa ta?
tayi murmushi ta lumshe ido donjin dadin kalaman yar tace kizo ina gida babyna ki karaso da sauri kiga ikon Allah, da baki neme niba daman yanzu zan nemoki,
sumayyah tayi daria tace Allah mummy. Allah Ya sa alkhairi ne,
mummy hafsat tace alkhairi ne ma saikin karaso dai kiyi tuki a hankali ba gaggawa bane,
wata muryace tayi sallama sai dukkansu suka daga kai suna kallon mai shigowan sai ga wani saurayi sanye da bakar riga da wando suit farar riga ce aciki wuyan sa daure neck tied, kafarsa ba takalmi sai dai akwai bakar safa da alama daga bakin kofa ya cire takalmin sai dai yana dan dingisawa da alamar bacin rai a fuskarsa domin dakyar yake magana, abun mamaki sai sukayi kama sak da saurayin da ya fice yafice inji kaltum tafada aranta ko shine yaje ya canzo kaya?
amma kamar wancan ya dan fi wannan kiba kuma wannan yafi wancan tsayi yama fishi kyau sbd yafi wancan dogon hanci da haske, kuma fuskarsa a zagaye da kasumba, yazo ya durgusa ya gaishe da mahaifiyarsa yace Anas yace inzo kina kirana?
ta gyada kai tace eh sami kujera kazauna yamike tsaye yana muzurai da alama bayason zaman nan yayinda ya fara duban al'ummar da ke zaune a falon daya bayan daya sai yanzu ya lura da wanda ke zazzaune,
matukar mamaki bayananne a fuskarsa duba yake musu na kurilla sai su dukka suka zamo daga kan kujera suka gaisheshi ya amsa da kyar kasancewar harshensa ya masa nauyi ya dubi kaltum ya sake dubanta sai ta sunkuyar da kanta kasa ya juya ya dubi mahaifiyarsa ya fada cike da gargadar murya mummy lfy?
ta kawar dakai gefe tace lafiya ka nema waje ka zauna kawai.
yace fadamin abunda ke faruwa nabar mutane a mota?
wannan karon tsawa ta daka masa tace ka nemi waje ka zauna nace ko?
Ko sekon bai kara ba ya zauna....
.
To yau an samu post biyu, ya kamata kuma a samu kwana biyu kapin a yi, saboda na san kowa ya sha karatu ya gaji, idan aka huta sai aci gaba,
Lol.
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 36
.
TRUE LIFE STORY
.
Ya xauna yacigaba da dubansu daya bayan daya,
daka shigo falon duban farko da zaka yiwa
kowannensu dauka zakayi a kotu suke suna jiran hukuncin kisa, a zabure suke haka a kage suke su dukka tamkar su rusa ihu, cikin wannan hali sumayyah Tukur ta shigo ta iskesu sai ta cika da mamaki bata ma gama amsa gaishe gaishen da yaran sukeyi mata ba saita yada jakar hanun ta akasa ta runtuma wajen mahaifiyarta da sauri ta rike ta tambaya take lafiya mutuwa akayi?
nemi waje ki zauna inji mummy hafsat.
kafin sumayyah ta kara cewa komai samari biyu ne suka shigo na dazu da abokinsa yayinda kaltum ta dinga kallon masu kama dayan nan tana tantance inda suka banbanta, suma suka sami waje suka zauna yayinda suka kurawa mummy ido kowa yana so yaji abunda zata fada,
ta dubi kaltum wanda tuni cikinta ya duri ruwa ta fara nadamar zuwanta, ta zata suda mummy hafsat zasu labarinsu ta tashi ta tafi sai gashi anyi gaiya an cika falo,
fito daga lungu yarinya ki dawo tsakiyar falo ki zauna yayinda ta daga kai tadubi idanu ca akan ta saita sunkuyar dakai kasa,
daya daga cikin samarin nan wato mai riga suit ya dubi agogo ya girgiza kai yace afuwan mummy kibani minti 2 zanyi magana inaneman izini zan tafi saboda inada uzuri labarin wanan yarinya ba wani abu zai karamin ba tunda banida wani alaka da ita da labarinta...
ka rufamin baki ai kai dama ba a komai da kai ko kasanta ma ba sauraronta zakayiba tunda bakason shiga mutane ko wani uzurine gareka saika tsaya ka saurara kobazai kare ka da komai ba, inji mummy hafsat.
atakure yake jinsa kamar a daure shi yaci gaba da hararar kaltum yakagu ta gama yatashi yatafi yace aransa banda abu irin na mata tayaya zaiyi su dauko yarinya yar secondari da uniform da jakar ta a goye a bayanta ta tara kartai ace ta basu labari, me ta sani a duniya mezata fahimtar da su ilimi ma aikatanda suka goge da ilimin digiri da masters abu na biyu da ya ayyana a ransa shine ko kawota akayi sunganta ko daya daga cikinsu ace ya aureta jira yakeyi yaga gudun ruwansu yaji karshen labarin sannan yaja musu burki duk da yarinyan tanada kyau amma batayi masa ba bazata taba yimasa ba, koda tafara labari saiya tsinci kansa ya fara nutsuwa yana sauraron ta takai takawo ya gyara zama ya mika tunaninsa da hankalinsa kacokan a gare ta, kwakwalwarsa takasa tantance masa karshen labarin kome take shirin baiyanawa?
yaji wata kalma wacce keyimasa gizau don haka sai ya katse ta zai yi mata tambaya yayinda mahaifiyarsa ta katse tambayarsa ta mayar masa da amsar yayi shiru ya saurara kawai kada wani a cikinsu ya sake magana har sai kaltum ta gama,
yaja numfashi ya rike kai yana jujjuyawa domin ya tabbatar shin gaske ne ko kuwa barci yakeyi ga abubuwan tambayanan kowa yanaji amma babu daman yinta saboda hani daga mummy hafsat.
kaltum ta fuskanci hankalin kowa nakanta da alama labarinta yanada tsarkakiya da rikitarwa don haka sai ta dinga bin salo irin na marubuta masu batar da tunanin mai karatu wajen kasa gano abun da zaifaru anan gaba har sai anzo karshen labari, aketantance ta fara basu labari daga ranarda
suka hadu a daura da kayansu suka shiga motoci zuwa maiduguri suka tsaya suka yi sallah suka ci guzurinsu sukaci gaba da tafiya har suka isa bur sudan da yadda suka kwanta akan kabarurruka sukayi barci tabasu labarin ranarda aka zo aka tantance masu tafiya wadanda takardunsu suka cika akabar wadanda suke da takardar bogi sannan ta fara basu labarin yadda rayuwar su takasance su da aka barsu abur sudan sannan tafito da sunan MADINA baro-baro saiyanzu suka fara fahimtar inda labarinta ya dosa sai yanzu su kasan dalilin tarasu daka akayi a cikin labarin da Madina ta bata tundaga onisha har ranar da ta rabu da Abba a asibiti har dalilin ta na barin kasar ta kuma basu labarin rabuwarta da Madina da kuma ra ayinda ta barota na cewa bazata kara dawowa nigeria ba har abadah ko gawarta bazasu gani ba...
kafin kaltum ta rufe bakinta tayi sharkaf da hawaye yayinda duk wanda yake falon hawaye yake yi,
mummy hafsat ta share hawaye tace kaltum wayace da Madina Abba ya mutu a gabanta ya mutu?
abokinsa mukaddam ne yayi mata waya duk da cajin wayarta yakare bataji karshen maganar ba taji koke-koken mata kuma ya ambaci Abba ya ...Sai wayarta ta katse,
mummy hafsat ta nuna daya daga cikin samarin nan tace ga mukaddam din nan,
kaltum ta juya da sauri ta dubeshi ya gyara zama ya murza jajayen idanuwansa yace hakika nayiwa Madina waya alokacin da ta tafi Abba ya farfado yake cewa akira masa Madina zai fada mata wata magana kasancewar ranga-ranga yake rai ahannun Allah, watakila wata wasiyyah zai bari wacce yaki fadawa kowa sai ita dana kirawo ina
tambayan ta ina take yanzu sai hayaniya tayi yawa naga kuma tana kidime tana tambayana ko lafiya?
inaso nace Abba yatashi yace akiraki sai wayan ta dauke to banmasan ta zaci nace abba ya mutu ba,
kaltum ta dubeshi ta gefen ido alamar rashin fahimta ta tambaya cike da fargaba Mukaddam kana nufin Abba bai mutu ba?
Mukaddam ya nuna saurayin nan mai bakin Kaya suit yace ga Abba, yayinda aka hau kallo kallon tsakanin kaltum da Abba,
ya dafe kai sai yajujjuyawa kalma daya yake fita daga bakinsa shine InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un yayinda hawaye suke tarwatse a idanuwansa,
shahida ta daura hannu akai tana kuka tana cewa wayyo mamana, Abdul Malik da Abdulmajid ma ba asan wanda yafi wani karfin haliba kuka suke suna fadan a ina zamu nemo mama?
Dr sumayyah tukur ta mike tsaye ta kifa kai ajikin bango tana kuka tana cewa Madina kiyafe mana abunda muka miki kiyi hakuri kidawo muna sonki aminiyata...
general tukurne ya fado cikin falon yasake juyawa ya dubi ya yan Madina daya bayan daya saiya girgiza kai yace Allah Ya kyauta Allah Ya sauwake ya suri bindigansa ya fice, wani dogon numfashi kaltum taja don samun kwanciyar hankali da aka fitar da bindigarnan, dr sumayyah tukur ta sharce hawaye ta dubi kaltum cikin siririyar murya tace kaltum ya akayi kika rabu da Madina kika dawo gida?
kaltum ta langwabe kai tabasu labarin sanda hauwa tazo ta dauketa da yadda sukayi sallamar karshe a fili jirgin kasa taci gaba da cewa watannina bakwai a Khartoum daga
nan iyayena suka turo aka taho dani sai dai mambela ya tabbatar min cewar Madina tana bur sudan koda yake yanzu na shekara daya da rabi da dawowa duk da haka ina kyautata zaton tana bur sudan ammafa mambela ya ce babu yadda baiyi da ita ba akan ta rakoshi Nigeria wajena taki tace ita da Nigeria har abada,
Abdul hakim ya zabura ya mike yace nizanje bur sudan nemanta kibani kwatancen wajen.
mummy hafsat ce tace dukkanku ku dakata kada wani ya yanke hukunci harsai abunda muka shawarta da daddy, kada inji wani ya tarki hanyar sudan kwanan nan.
abba ya nisa ya dubi kaltum da idanuwansa
dasuka canja launinja saboda kuka yace yaya
Madina ta zama?
kaltum ta ciro jakarta daga bayanta saita ciro wasu hotuna guda uku ta mika mishi yakarba da sauri ya duba yayinda hannuwansa yahau karkarwa yasa hannu ya toshe bakin sa saboda kada ya rushe da ihu yaji dadin ganin
madina araye kuma Allah Ya amsa addu arsa da Ya bayyana inda take amma ya gigita daganin yadda ta lalace ta fige kamar kaza tayi duhu tamkar mutanen da aka tono su daga cikin kasa haka ya gansu yaro-yaro almajirai ne sak ba wai kama da almajirai sukayiba donma hoton bikine a ranar duk sunyi kwalliya, da basuyi kwaliya ba ashe daba a san yanda za a gansu ba, dagasu har gidansu abun tausayi, ya dubi hoto na farko Madina ce da kaltum sun saka tsohon nan mai sayar da ruwa akan jakinsa atsakiyarsu hoto na biyu kuwa Madina ce tsaye tsakar gidansu sanye da hijabinta tana dariya, hoto na uku kuwa abakin tekune su dayawa ranar bikin Amina.
sumayyah tukur tasa hannu ta karba ta duba saita mikawa mamarta ta kallah itama ta girgiza kai saita mikawa 'yayan Madina, tsananin kukanda sukeyi shi ya sake tayarwa Abba da hankali, sai mukaddam ya lura ciwon kirjinsa da ciwon kansa sun fara tashi yayi marmaza ya tashi yafita dashi yakaisa dakinsa don ya basa magani,
Anas kanin Abba sai yanzu yayi magana ya dubi kaltum yace kiyi hakuri kaltum bansan labarin Madina kikeson bayarwa ba harnaso na dake ki.
ta girgiza kai tace bakomai nagode.
sumayyah Tukur tace kaltum koda Allah Ya sa kin riga mu ganin Madina ki gayamata bada niyyah mukamata abunda mukayi ba rashin sanine amma daga baya Abba da bakinsa yabamu labarin abunda ya faru a tsakaninsu kakaf, sai mukaji kunya mukayi dana sani, muka nemi Madina sama ko kasa bamu sameta ba mukaji ina mamu ganta munemi gafararta mu aura mata Abba Allah bai sa munganta ba sai muka nemi gafarar Abba da na 'yayanta mukaci gaba da addu ar Allah Ya baiyana mana ita Allah Ya sa tana hannu nagari idan kuma ta mutu Allah Ya jikan ta, saigashi Allah Ya amsa addu ar mu ya bayyana mana inda take, zamu shawarta
yanda za ayi mu dauko Madina dole zata dawo wajenmu ko bazata auri Abba ba don muna so Madina tazama tamkar jinin mu, Anas tashi kamayar da kaltum gida kaga inda take saboda watarana ku tafi da shahida kada agidansu aganta dana miji,
kaltum tayi godiya suka dunguma suka fice sai ayanzu hankalin kaltum ya kwanta data isar da sakon Madina sai dai kash ta kasa gano hanya guda daya cal da zata aikawa madina sakon cewa Abba bai mutu ba, tayi tunanin duniyannan babu ta hanyarda zata iya turawa Madina wasika ko a waya suyi magana,
kaltum tayi gum da bakinta bata taba bawa wani dan gidansu labarin madina ba babu wanda yasan tana zuwa unguwarsu shahida.
haka ta taso tun tana karama rayuwarta ita kadai takeyi bata shawara ko doguwar hira ita da iyayenta daman batada wasu kawayen kirki tuntuni su hadu a makarantane surabu abakin get, gara yanzuma datake makaranta wayayyu tana da kawaye masu nitsuwa su biyu Hamida da Aisha suma kawancennasu iyakaci a makarantane kawai basu taba zuwa gidansu kaltum ba itama haka garama da alh Adnan ya sayo mata waya daga America kwanannan suna yawan hira a waya suta zazzaga labari, da turawa juna sakonni amma ko kadan kaltum bata tattauna abunda ya shafi rayuwarta ko gidansu, ajinsu shida don haka suna tsakiyar karatu kamar yadda alh Adnan yake yawan gargadinta kada tasake ta fadi jarabawar su ta karshe akallah ta sami credit bakwai a waec da neco ta dage taci jamb kuma don ta wuce jami a kai tsaye,
a dai dai lokacinda take tsakiyar karatu haikam dai dai lokacinne jikin goggo fattu ya tsananta har aka gaji da zamanta a asibiti aka dawo da ita gida.
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 37
.
TRUE LIFE STORY
.
kuma a dakin kaltum aka ajiyeta duk da akwai iya uwani awajenta wato kanwarta kenan amma ta fara kosawa da zaman don haka kullum tana karairayi saita kirkiro tafiya zangon daura, yau gaisuwar mutuwa gobe suna, bata cika zama ba kaltum ne mai kulawa da ita tunda asuba take tashi ta fara fama da wanke-wanken zannuwan goggo fattu na fitsari da bayan gida ko kaki da amai, ta goge mata jikinta sannan ta bata abinci da magani,
daga kwance goggo fattu saitayita kurawa kaltum ido tana kallonta tana tuna bakar muguntarda tayi mata a baya tana nadama a lokacinda take tunanin rayuwa tajuya mata baya yayin da yanzu yan kankanuwar yarinyarda take azabtarwa itace mai karfi kuma mai taimakonta sai gashi ta maye muguntar da tayi mata da alkhairi sai kaga hawaye yana surnanowa da alama tana nadama sai kaltum tasa gefen zaninta ta share mata hawaye ta kara da cewa goggo kidaina kuka komai ya wuce.
rayuwa kenan har sai kaltum tagama hidimar goggo fattu sannan ta fara shirya kannen ta da ita kanta sannan su tafi makaranta, tana makaranta ma tana tunanin halinda goggo Fattu take ciki shin batayi fitsari ko bayan gida a kwance ba kodai tanajin yunwa ko kishi ruwa babu mai jiyo kiranta idan ba sofi bace ta leko dakin taganta ba, babu wanda zaisan halinda take ciki ita kuwa tana kicin kullum hidimar girkin ta ma ya ishe ta,
kaltum tana da tausayi duk da duk sanda takalli goggo fattu saita tuna abunda tayi mata a baya amma zuciyarta bata taba ayyanamata ta wulakantata ba ko tarama abunda tayi mata abaya ba don tana da ikon da zata rama din ko duka zata iya mata babu wanda zai sani don a kwance take bata iya ko daga hannunta bakinta a jirkice gefe don haka ko magana take ba a ganewa idan ma ba duka ba zata iya hanata abinci kotaki cire mata kayan data bata duk hanyoyine na musgunawa amma kaltum ko kusa bata tunaninyi mata haka ba.
tana tuna nasihohi da hadisanda ake musu a
issalamiyyah akan mutum ya zama mai yafiya da kyatatawa.
duk rayuwa mai dadi da kaltum ta tsinci kanta baisa ta manta da Madina da Mambela ba sai kuma tatuno ta fatsuma aminiyarta takan yi kuka saboda tasan wahalan rayuwar da ta dandana abaya tanaso ta zauna dasu amma bata sha'awar ta koma wajensu inama za akwaso minsu akawominsu kano muyi rayuwarmu anan?
tunaninta da addu'ar ta kenan a koda yaushe,
zuwan kaltum gidansu Abba ya kawo cece kuce iri-iri a cikin gidan domin Abba ya tubure saiya tafi sudan ya nemo Madina iyayensa kuwa sunce bazasu barshi ba saboda basusan halinda zaije ya fada ba akasarda baitaba zuwa ba,
Tasi'u kuwa ya kullaci Abba domin shima ahalin yanzu Madina yake nema ido rufe domin yagane Madina ce mace tagari mai sonsa ita ta dace dashi inhar Ya tabbatar zai samu Madina tabbas saiya sallami sauran matansa dukka domin Madina mace dayane tamkar da dubu sai bayan tafiyar ta Ya tabbatar ya rasa mace, duk wadannan matansa har guda uku sunansu mata ammadai ba mata bane basu san ma yadda ake daraja mijiba babu tsafta babu komai don haka kowaccensu yayi mata saki bibbiyu ahalin yanzu igiyoyi daya daya ya rage musu, kuskure kadan zasu tafka yakarasa tsittsinkawa, gidansa ya zama sansanin yaki saboda kishi rige rigen haihuwa akeyi masa don haka 'ya'ya kanana ne burjik agidansa, nauyi ya karu yayinda kasuwa tajabaya jari yaragu don haka Tasi'u yarasa kwanciyan hankali a rayuwar sa, ya tsufa ya rame ya lalace ya kazance kasancewar ya rasa matarda takeyi masa wanki da guga da girki mai kyau koda kudinsa ko babu kudinsa zaici,
saigashi yanzu da kudinsa ma ba a dafa mai mai dadi sai yanzu ya dau son duniya ya dorawa ya yan madina musamman shahida idan ya kalleta sai yaga tamkar yaga Madina, saboda kamarsu daya sak, shiga goma fita goma saiyace ina shahida ina Abdul hakim da Abdul Malik?
saiyagansu yakejin dadi, yana tarasu a falonsa yahau yimusu bayanai marasa tushe tamkar tababbe sunayimasa kallon ya fara zautuwa tsabar nadamarda yakeyi yana danasanin abunda yayiwa Madina, bai damu da kishin da matan sa sukeyiba akan yawan ambaton Madina,
sunan madina dayakeyi fiye da sau goma arana burinsa kawai ya ambaci sunanta yaji sanyi aransa saida ya tabbatar madina tayi masa nisa kuma ta haramta agareshi sannan ya nutsuwa yashiga hankalinsa yayinda duk abubuwan alkhairi da tayi masa yake dawowa kwakwalwarsa, Tasi'u ya matse hawaye ya dubi shahida ya juya yadubi yayanta Abdul hakim da Abdul Malik ya girgiza kai yace kuyi kokari ku gaji halin mahaifiyarku idan kuka yii irin halayenta zaku ci ribar zaman duniya da lahira, ku kwaikwayi Madina domin mace ce mai hakuri da tawakkali, ni Tasi'u na yi kuskuren rabuwa da mace ta gari irin Madina na tafka asarar da har abada bazan sami macen da zata yi kwatankwacin rabinta ba ma balle ace irinta sak, na cuci Madina matana ne suka cuceni meya kaini kara aure ma?
dan da ban auro Sa'ada ba daba ta dinga kulla mata tuggu ba nikuma na hau na zauna nabiyeta na wulakanta,
Madina mace mai kaunata tsakani da Allah, madina kiyafe mini kuma yayan ta kuyafe min danayi muku sanadiyyar rabaku da mahaifiyarku,
kutayani addu'a Allah Ya bayyana Madina Allah ma Ya fara amsar adduar da Ya bayyana aka sami labarin kasar da take don a da ba amasan ko araye take koma ta mace. yadda Allah ya bayyana inda take to in shaa Allahu Zai kawota gida ta zo dakanta idan tazo kutayani rokarta ta yafe mini sannan tazo muzauna tare in sallami sauran matan gidan tunda basu da amfani agareni, sannan inaso ku bujire ku nuna baku yarda ba bakwaso ta auri wancan dan banzan yaron wato Abba don na fuskanci nemo ta yakeso yayi ya aureta har nacinsa yasa iyayensa sunyarda zasu aura masa ita, ku aganinku ya dace ace mahaifiyarku tana auran yaro karami?
ai zubar da mutuncine maku a wajenku abun gori ne idan kukaje gidan ma zai iya korarku kasancewar yaga yanada kudi iyayen sa ma masu kudine gara ace mahaifiyarku ta dawo hannun mahaifinku gaku ya yanmu muzauna tare ai yafi kwanciyar hankali ko ba haka bane?
Babu wanda acikinsu ya bashi amsa saima murtuke fuska da suka sake yi sai Tasi'u yafara tsorata da alama basa goyon bayan sa, har ya sallamesu suka bar falon babu wanda ya furta masa kalma daya shi yayi kukansa ya lallashi kansa.
suna fita suka dunguma kofar gida don su sami lungu da zasu fake suyi shawara kasancewar cikin gidan ko ina mutane ne, can wani kofar gida suka sami wani dakali suka zauna Abdul hakim ya dubi yan uwansa yace Allah sarki mamanmu Allah Ya yi mata jagora Ya taimake ta aduk inda take, mun saba mata mun zargeta alokacinda kowa ke zarginta maimakon mukasance mu kadaine masu bin bayanta aduk duniya, na tabbata dabadon abunda mukayi mata a asibiti ba da bata shiga duniya ta barmu ba, dako saboda mu zata zauna a kasar koda kuwa za a dinga jefinta ne don tsana...
saiya fara kuka yayinda dukka suka rushe da kuka.
Abba Tukur ne ya bayyana agabansu basuga tahowarsa ba saida suka daga ido suka ganshi a tsaye akan su, ya dubesu daya bayan daya sai yaji tausayin su, ya sunkuyar dakai kasa sai hawaye ya surnano daga idanuwansa yayi karfin hali ya fara magana amma kuka ya hanashi cigaba, ya dade a tsaye yana hawaye marar kakkautawa sai can ya tsagaita yarasa wanda zai fara lallashi
acikinsu saboda tsananin halin kuka da yaran suke ciki, ya ce 'yayan Madina nasan damuwarku wanda take dai-dai da damuwata nasan irin zafinda kuke ciki na rashin mahaifiyarku wanda yayi dai-dai da yanda nakeji idan ma bai dara naku ba, kubar kuka
ku tayani da addu'a iyayena sumin lamunin tafiya,
zanje na karbo adireshi a wajen yarinyan nan
kaltum inje in taho muku da ita kusani ina so na auri madina saboda ina sonta saboda Allah idan na auri Madina nagama samun farin ciki a rayuwata, nayi muku alkawari zan rike muku mahaifiyarku tsakani da Allah daku 'yayanta gaba daya, kada ku biyewa mahaifinku da yake fada cewar rashin kunya ce ni dan yaro inason in auri Madina, ku tuna auren Nana Khadija da Manzon Allah S.A.W
Ya aureta tana bazawara kuma ta girmeshi bai haramta ba kuma bai hanata yi masa biyayyh ba....
Abba bai rufe bakinsa ba yaji wata murya mai
firgitarwa daga bayan sa sai suka waiga da sauri a gigice,
Tasi'u ne ya fita a fusace daga cikin motarsa ya tunkaro Abba Tukur yana magana cikin fushi yana nunasa da yatsa kai Abba kafita daga harkan gidana tunkafin ta kaimu ga kotu, daman nasan kai kake tara yarannan kana yi musu hudubar banza to bari kaji na fadamaka baka isa ka auri Madina ba indai ina raye ko kai ko ni.
Abba yayi murmushi yayinda ya zura dukka hannayensa acikin aljifan wandonsa ya sunkuyar dakai kasa kamar mai tunani can ya dago yadubeshi yayi murmushin karfin hali yace kada ka manta ka saki Madina saki uku, aurenta dakai ya haramta sai in har ta auri wani ta fito sannan zaka iya mayar da ita, kaga ko bani zata aura ba sai ta auri wani sannan takoma gidanka inhar zata koma kenan,
malam Tasi'u banzata akwai ranarda zaka dawo kana son Madina ba bayan musgunawa dakayi mata ka wukantata ka koreta, banaji akwai wani nauyi ko kararta zanyi maka akan aurena da Madina ba saboda bazan kira rabuwarku da kaddara ba kana sane ka saketa iyayena sun lura inasonta sun kuma yarda in auri abunda nakeso don haka babu mai hanani auren Madina...
a fusace Tasi'u zaikaiwa Abba mari sai yarike hanun nan da nan alh Isa da malam muhammadu makwabtan su suka garzayo da gudu suka shiga tsakaninsu, akaja Tasi'u
zuwa motarsa Abba kuma aka kaishi gida.
hankalin 'yayan Madina yakara tashi ya sake tashi amma gaba dayansu sunfi amanna da aurenta da Abba akan ta koma gidansu, gidan wahala da tashin hankali, fatarsu ma aga Madina tukunna sannan afara zancen aure, yaran madina sunfison Abba sunsan shi mahaifinsu dayake wannan fada ina yaga kudin jirgin da zai je ya daukota a sudan?
idan yadaukota ma ai bazai iya auranta ba saboda babu wani sauran igiyar aure a tsakanin su, rabuwa uku ce Abba kuma in har an amince masa agidansu yanada kudinda zai iya hawa jirgi ya taho da ita kuma sun yarda da sonda yake mata idan ya aureta zai riketa amana ba ita kawaiba harsu kansu tun bayan da yashekara akwance a asibitin london ya warke ya dawo yake basu duk wani abu da sukeso aboye naci kona makaranta basu taba tambayansa wani abu sun rasa ba ko basu tambaye shi ba shi dakansa sai ya kirawosu ya basu kudi mai yawa duk da ma yana tsoron basu kudi mai yawa kar mahaifinsu yagane to inaga ya auri mahaifiyarsu kuma?
Abdul Malik yanzu jami'ar ABU zaria yake yana level 3 yayinda Abdul hakim yake level 1 a BUK, Shahida kuwa a sakandari take aji biyu duk wannan fadace fadace da ake yi har ana ambaton kotu duk fa akan Madina ne to bata nan, ba amasan inda za a same taba,
gata batada niyyar dawowa kuma .
lalle Tasi'u dagaske yake kuma yadau abun dazafi saboda da daddare yashiga har cikin gidansu Abba ya iske mahaifinsa da mahaifiyarsa a falo ya lankwashe kafa yakawo karar Abba akan ya rabu da matar sa Madina,
abun yabasu mamaki domin su basu zata akwai ranarda Tasi'u zai sake waiwayan Madina ba bayan juya mata baya dayayi yanunawa duniya yagaji da ita baya kaunarta, irin tsawon lokacin da mummy hafsat take batawa wajen gargadinsa kada yasake ya rabu da Madina amma baijiba sai gashi yau agabanta yana kuka yana maimaita nasiharda tayi masa abaya yana nadama,
takaici yahana genaral tukur furta koda kalma daya tak har Tasi'u yagama yatashi ya tafi,
mummy hafsat ce mai bashi hakuri amma ta shaidamasa basuda ikon hana Abba son abunda yaji yanaso kasancewar Madina batada igiyar wani akan ta,
da alama baiji dadin abunda sukayi masa ba ba haka yaso jiba so yayi suce zasu tsinewa dansu idan bai rabu da zancen Madina ba.
barister Abba Tukur ne da kaninsa engr Anas suka dira akofar gidansu kaltum da misalin karpe biyar na yammacin laraba, suka ajiye motarsu a wurin get yayinda suka tura kai cikin gidan, mai gadi ya taresu don jin wanda suke nema dasuka shaidawa malam saleh kaltum suke nema saiya yi matukar mamaki gami da fargaba ya tambaya cike da firgici lafiya kuwa kuke neman kaltum?
lafiya mana maigadi inji Anas yayinda yake murtuke fuska saboda rashin jin dadin tambayanda yayi musu kasancewar yasan basu san shi ne mahaifinta ba, sai bai tamuba ya shaida musu cewa batanan ta tafi makarantar islamiyyah sai karfe shida zata dawo,
sai suka koma wajen get suka shiga mota suka zauna zaman jiranta suka ci gaba da shawarta abunda yake tafe dasu,
tajikin madubi Anas ya hango kaltum ita da kannenta suna kokarin tura get zasu shiga gidansu ya fito ya kwala mata kira ta tsaya cak tana dubansa cike da mamaki ta rasa inda ta taba ganin fuskarnan, ya karaso gareta yayi murmushi yace kada fa ace baki gane ni ba kin manta gidan sojojin nan da kike zuwa a yankaba inda aka kusa zaneki da belt kwanakin baya?
idan kin manta ai bazaki manta gidansu shahida ba yar Madina,
sannan kaltum ta tuna da fuskar ta kwace da dariya tace Anas ashe kaine?
malam saleh ya fito wuf ya dubi kaltum ya juya ya dubi Anas ya tambaya cike da bacin rai waye wannan ?
Matsalan kaltum bata tautauna halinda take ciki da mahaifanta don haka basu taba sanin labarin Madina ba balle ta shaida musu taje ta nemo danginta,
idan takama nan saita saki ta zargo can, zancen dai a cukurkude bai fahimceta ba don
haka yayi mata umurni ta shiga gida ba zata gansu ba,
Anas baiji haushiba saidai ma mamaki daya hanashi magana saboda baizaci mai gadi yana da ikon hana yar maigidan abunda takeso ba, ya tsaya yana duban malam saleh kawai har ya rufo get ya shige yabarshi tamkar gunki,
hankalin Abba ya tashi saboda yanaso ya shaidawa mai gadin cewar suba samarinta bane kawai maganar Madina zasuyi, Anas yace su tafi kawai har yaushe zasu tsaya suna rokar maigadi da wata tsummar rigar sa?
suje saisu dawo wata rana,
Abba yakasa sukuni kwana biyu da tafiyarsu yaji bazai iya jurewa ba har saiya dawo yaji labarin madinarsa don haka bai gayyaci Anas ba saiya figi motar sa yayi gidansu kaltum tunda yaga hanya, yazo da yamma tunda yasan jummaa ne babu issalamiyyah tsayuwar sa abakin get din kenan yayi dai dai da lokacin da alhaji Adnan ya iso daga Abuja don bazai ya shiga da motarsa ciki ba saboda Abba yatare kofa, kallon-kallon aka hau yi a tsakaninsu alhaji Adnan, ya fuskanci tabbas Abba bai sanshi ba ne maigidan ba, kuma so yake yashiga da motar ciki don haka sai ya fito ya dubi Abba yayi murmushi yace ranka yadade kozaka matsa gaba inaso inshiga da mota ciki.
Abba yayi sauri ya shiga mota yace kayi hakuri na tareka don Allah idan ka shiga ciki Kamin sallama da kanwarka kaltum,
mamaki ya dabaibaye zuciyan alh Adnan ...
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 38
.
TRUE LIFE STORY
.
mamaki ya dabaibaye zuciyan alh Adnan ya ratso har fuskarsa ya dubi Abba ya dubi tsalaleyar motar da yake ciki,
bayan ya matsar da motarsa sai alhaji Adnan ya danna horn malam saleh ya bude masa get ya kutsa ya shiga cikin gida, bayan yan sannu da dawowa sun iso suka kwashi tsaraba zuwa cikin gida wato kaltum da kannenta kenan daga yanda alhaji Adnan ya amsa mata da yadda ya kalleta ya watsar tasan ba haka ya saba yi mata ba, tabbas akwai dalili daga yanda malam saleh yaga yau alh Adnan baya fara'a yasan ba lafiya, don haka sai hankalin kowa ya tashi,
alh adnan yafito kofar gida batare dayayi bayani ba,
tabbas malam saleh ya zargi ko yan gulma ne suka fada masa cewar samari sunzo neman kaltum shekaran jiya.
alh Adnan yakarasa har jikin motar abba a inda ya iske shi a tsaye yayi masa sallama ya mika masa hannu suka gaisa,
alh Adnan ya dubi Abba yayi murmushin karfin hali yace kaltum kake nema ko?
daga ina yayi?
murmushi yace sunana barista Abba Tukur a unguwar yankaba nake .
alh Adnan ya kura masa ido yana dubansa can yayi ajiyar zuciya yace naji sunanka yaro sai kuma inji dalilin nemanta da kake yi, daman ka santane kokuma tasan da zuwanka?
abba yayi dariya domin yaji tambayoyin sunyi masa kama da tambayoyin da lauyoyi sukeyi wa mai laifi a kotu, ya ce kaltum tasanni amma batasan yau zanzoba nazo shekaranjiya mai gadinku ya hanata zo wajen mu dalilin zuwana bawani abu bane illa dai ina so tazama ido na ko ince itace fitilar da zata haskaka min hanya wajen neman allura cikin duhu.
alh Adnan ya dago da sauri ya dubi Abba yayinda ya caka masa mashin harara ya fada cike da gadara yaro ban fahimceka ba?
Abba ya girgizakai yakara yin wani siririn murmushi yace ranka dade karkadamu nazo neman alfarmane a wajen ku kanwarka kaltum ne tazo min da labarin ta baro matata a sudan tana can tana bara shine nake so tamin kwatance ko ta taimakamin ta rakani inda Madina take mu dauko ta don mu mun rasa inda take har mun zata ma ta mutu...
alh Adnan yakatseshi tunkafin yarufe bakinsa
cikin sakin fuska da dariya yake magana don ya fahinci abba ba zance yazo ba yace yi shiru yaro na fahince kana so kace min kaima matarka tana cikin yan gudun hijira ko ince masu tarar aradu da ka masu tafiya makka da kafa ko?
to sai dai mu musan abunyi domin kaltum bazata sake leka wa sudan ba da sunan takawaba ba balle rakiya, kai da kasan wahalarda nasha kafin akawo min ita ai da bazakace zaka nemi izinin rakiyarta ba, kaltum karatun jarabawane a gabanta banaso a dinga maganar sudan da ita saboda ina ganin alamun damuwa a tattare da ita idan aka ambaci sunan sudan don haka banaso ka sake sakata ma acikin maganan duk abunda kakeso ko kake nema ka nemeni nayi maka alkawari zan taimaka maka iya taimako saboda nasan yadda kake ji.
ba karamin tashin hankali bane ace an gano matarka ko yarka ko kanwarka awata kasa tana bara ba, sai sunyi bara sannan suci abinci mace musamman budurwa ai bala'in yayi bala i sai fatan Allah ya kiyaye gaba, yanzu dai ka rubuta numban wayata ka kirani gobe da safe muyi magana daga abuja nake yanzu nagaji,
sai godiya abba yakeyi ba iyaka yayinda farin ciki ya mamaye zuciyanshi yaji tamkar ance masa ga Madina nan adaki za a fito masa da ita, ya dauko waya alh Adnan yana karanto
masa yana rubutawa ya fada cike da ladabi wani suna zan saka?
alh adnan yayi murmushi yace ka rubuta kaltum Adnan.
Abba ya maimaita sunan kaltum Adnan...
alh Adnan yace karka damu ka rubuta haka sai kafi ganewa,
ya juya ya bar Abba a tsaye cike da mamaki yayinda yabishi da kallo har saida ya shige cikin gida zuciyarshi cike da tambayoyi shin wannan mutumin yaya yake da kaltum?
Gashi dai sunso suyi kama amma yace shi ba yayanta bane kuma baici ace babanta bane don shekarunsa baici ace ya haifeta ba ita ba matar aure bace bare kuma ace mijinta ne to ko kawunta ne ?
Amma da gatanta to meyasa suka bari ta tafi sudan ?
Gara ace Madina ace rashin gatane kodayake a labarin ta ta ambaci wata tsohuwace ta tafi da ita ta ambaci wani masoyinta abar kaunanta mambela don haka wannan ba mijinta bane koma dai wanene wannan yana sonta kuma yana kula da ita sosai tabbas yana tattalinta..
tunanin da abban Madina yake yi kenan a zuciyar sa har ya iso gida bai iya barci ba daga ya rufe ido sai yaga kamar Madina sai yayi sauri ya jawo hotonta yaga Madina ta lalace ta susuce ta fita hayyacinta idan yayi kuka saiyayi adduar Allah ya bayyana masa ita amma jikinsa yakanyi sanyi idan ya tuna Madina zata iya zuwa taci gaba da bujirewa aurensa.
bayan gari ya waye Abba waya yasa agaba yana kirga awannin yana jiran goma na safe yayi sannan yakira kaltum bayaso yadoka masa sanmako.
alokacinda agogon alh Adnan ya buga karfe goma da wayar Abba tare suka isa kunnuwansa alokacin da yake tautaunawa da mai gadinsa malam sale a katafaren falonsa ya dubi agogo ya juya ya dubi wayarsa baisan lambar ba dan haka bai damu da sai ya amsa ba yaci gaba da bayanansa amma wayan bata daina ruri ba da zarar ta gama saita kara daukar kururuwa dole tasa ya saka hannu ya amsa ko dai wanene tabbas bakone don duk wanda yasanshi yasan dokarsa ba ayi masa waya kafin karfe 12 rana, alh Adnan ya amsa
sallamar mai yi masa waya sai ya kasa kunne yana sauraronsa Abba ya fara da gabatar da kansa dakuma inda yake da alama har yanzu alh Adnan bai gane ko wanene ba daga yanda yake amsa masa Abba ya fahimci haka don haka sai ya bashi labarin yadda suka hadu jiya cewar mijin Madina da take sudan tareda kaltum sai yanxu ya fahimce shi don haka sai ya saki ransa suka gaisa cike da faraa,
cikin fargaba Abba ya tambaye shi yace alh kace yau inkira zaka bani shawara ka taimake ni alh in samo madina kamar yanda Allah Ya taimakeka ka tsinto kaltum.
alh Adnan yayi murmushi yace samari ka kwantar da hankalin ka zan taimakeka abu daya ne nace bazan iya yi maka ba shine daka roki alfarmar kaltum ta raka ka sudan wajen Madina, bazan barta ba saidai zan hadaka da wanda na sani acan su taimakeka.
Abba ya yi godiya sannan ya gyara zama yana sauraronsa yayinda farin ciki ya lullubeshi...
malam saleh yakara tura hula keya yaci gaba da durgushewa yana sauraron abunda bai taba sani ba arayuwarshi wato maganan kaltum da Madina, koda wasa kaltum bata taba basu labarin rayuwarta a sudan ba saigashi alh Adnan ya sani harma suna tattauna da wani akan haka.
alh Adnan yabawa Abba labarin yadda akayi aka kawo kaltum gida yayi masa alkawari zai tuntube alh saadu yaji yan da za ayi ya nemo musu Madina a bur sudan ayi ciniki ya fadi yanda za a biya shi, ya umurci Abba yakirashi da yamma don yaji yanda suka tattauna.
Abba yayi farin ciki matuka yanata godiya har suka kashe wayan malam saleh ya jinjina kai
yayi murmushi yace wata yar gudun hijira ce ake nema ?
Alh Adnan ya kyalkyale da dariya yace yar gudun hijira ne kawar kaltum,
malam saleh yayi dariya ya sake lankwashe kafa yace daddy amintar nan taka da kaltum sai Allah kaga harta fada maka labarin kawarta a sudan mukuwa agida bata taba bada labarin tasan wata asudan ba ko da wasa bata taba zancen sudan da wani acikin mu ba, ka santa da miskilanci dakai kadai take hira shine kwanaki muke tattaunawa da sofi muke cewa ga kaltum ta kusa gama sakandari a cikin watan nan zasu gama, samari har sun fara biyota ranan ma saida na fita na fatattaki wasu a kofar gida bana so taci gaba da karatu a gida gara tayi jami'a agidan mijinta idan mijin ya yarda, saboda dandazo gidan nan zai zama dan ma bata kulasu shine mukayi shawara da zaiyu kuma idan kanada ra'ayi da sai na damka maka kaltum duniya da lahira hankali na zaifi kwanciya babu wanda zata aura yafi kulawa da ita fiye da kai duk da dai madam saliha ta kufula yanzu in taji zatace cin amana ne amma ai bai haramta ba, Alh sunan mun haifi kaltum ne kawai amma kai ka rainata da wahalhalunta dukka da taimakon Allah da taimakonka ne kaltum ta zama mutum,
badan haka ba ai da tuni ko a kwabo ba wanda zai dauke ta, saboda a kauye ko a sudan ta dauwama tana bara tunda bamuda kudin da zamu dauko ta, banida abunda zan iya saka maka taimako da rufin asiri da kayi min nida zuriata aduniya bazai misaltu ba, don haka na dauki yarinyan nan sukutum na baka nasan duk da haka ban biyaka ba kuma har abada bazan iya biyanka ba, ranka ya dade a duba maganata sosai agani idan da yuwuwar yin hakan ayi idan kuma nayi kuskure a cikin maganata na bata maka rai ayi hakuri kasan zuciya da sake-sake ni da sofi ne muka shawarta haka.
alh Adnan dai yayi shiru kansa akasa baya murmushi haka bai bata fuska ba da alama dai yana sauraro kuma yana nazari.
malam saleh ya mike cike da tsoro yace alh na barka lafiya zan koma bakin get naji motsi,
alh Adnan ya bashi amsa da to madallah sai anjima,
daga dukkan alamu dukkansu biyun sun shiga halin tunani da sake-sake kala-kala acikin yinin wannan rana, don tun wannan lokacin alh Adnan bai tashi daga kan kujera dayake zaune ba har karfe daya da rabi na rana, motsin shigowar danladi direba ne dajin muryan kaltum ita ta katse masa tunaninda ya dulmuya aciki,
kaltum ta gaishe da mahaifinta sai ta juya ta dubi motar alh Adnan ta tambaye shi Abba daddy bai fita ba yana nan ?
Malam saleh ya amsa cike da farin ciki, yau bai fitoba yana falonsa ta juya da sauri ta nufi falon alh Adnan fuskarta cike da faraa bakinta cike da magana da alama wani labari ta kunso masa,
malam saleh yayi tsaye ya hada hannu yana mamaki mai hade da fargaba yana tsoron kada maganar da yayi wa alh Adnan dazu ta bata masa rai ya juya musu baya, taimako da fara ar da yake musu ya daina, kada kuma ya dauka turo kaltum sukayi da tsigar yaudara..
ta shiga falo shiga falon.
yanzu kada fa ya dauka kwadayin dukiyar sa suke yi shine suka kakaba masa 'ya?
zuciya da sake sake haka ya dinga sakawo malam saleh wadannan tambayoyi InnaLillahi wa inna i ailaihi raji'un kalmar da malam saleh ya fada kenan a bayyane yayinda ya dora hannu aka ya shiga dakin gadi ya kasa zama sai leke-leke yake ta jikin labule yana so ya gada wanne irin yanayi kaltum zata fito, da farin ciki koda bacin rai idan ya Koro ta, ya shiga zargin kansa da kansa me yasa ma ya furta wannan kalmar?
gashi zai raba zumunci musamman idan
saliha taji.
kaltum ta isa cikin falon da sauri gami da rada sallama yayinda suka yi kayi ido hudu sai kowannensu yayi murmushi ta karasa gabansa ta durgusa ta gaisheshi ya amsa cike da fara a gami da mamaki hade da zumudin jin abunda zata fada,
ta bude jakarta ta zaro wata doguwar takarda ta mika masa ta ce daddy yau math mukayi na fada maka daman nafi iya maths in shaa Allahu ''A'' zanci don na amsa dukka.
Yayi ajiyar zuciya ya lumshe ido gami da wani
laulausan murmushi ya amsa mata cikin tattausan murya, yayi kyau kaltum Allah Ya yi miki jagora nikuma nayi miki alkawari idan kinci jarrabawar ki sosai zankaiki duk inda kikeso kiyi karatu a fadin duniyar nan inhar kina so, zan saya miki duk abunda kikeso.
dadi ya lullube zuciyar kaltum ta rufe ido da tafukan hannayenta tayi godiya ta mike cike da murna, zata tafi kamar daga sama taji ya kira sunanta ta dawo da sauri ta tsuguna a gaban sa tana sauraron abunda zai fada,
ya dube ta yace kaltum wacece Madina?
waye kuma Abba?
saitaji kirjinta ya buga don fargaba sai hankalinta ya tashi, tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa yayinda aka fara daukar dauki ba dadi tsakanin harshenta da labban bakinta, magana daya sak ta kasa fitowa daga bakinta ya sake maimaita mata tambayarsa
haryanzu ba ta sauya zani ba, amsa ta gagara sai kame-kame takeyi.
ya tsuke fuska yayi magana cikin kakkausar murya Yace zauna kaltum ki nitsu ki fahimce tambaya na kibani amsar gaskiya, inaso ki bani labarin, saboda in sani kafin inshiga maganar, bansan kida karya ba ada ban san ki da munafunci ba bakya boye min komai koda kin boyewa malam saleh da sofi, kada kiyimin karya don bana tare da mai karya bana shiri da mutum mai kame-kame nafi shiri da mai gaskiya.
saita durgushe ta zauna a sanyaye yayinda idanuwanta suka cika taf da hawaye ta tabbatar alh Adnan yaci karo da su Abba a jikin get, fargabarta kada ya zargi ko saurayinta ne,
muryanta na kakkarwa ta bashi labarin Madina kakaf sannan ta gangaro ta fada masa dalilin da yasa ta nemo Abba,
daga yadda ta fahimci alh Adnan ya tausayawa Madina kamar yadda ta san shi da makurar jin tausayi, saita fara sakin jikinta tana koro bayanai, yayi shiru tsawon yan mintina yana tunani,
yayi ajiyar zuciya ya dubi kaltum yace lallai Madina tanada mutunci kuma ta taimake ki ya kamata itama ataimaketa yanzu idan taji Abba bai mutu ba ai zata yarda ta dawo ko?
ma'ana idan na aika alh sa'adu ya daukota.
.
kaltum tace baxa ta yarda ta dawo ba dan ta kamu da matukar son Dan Aunty kamar yadda nima nake matukar kaunar sa. Lol.
.
AlhamduLillah, yau dai duk masu kokonto ina patan kun daina daga yau, tunda kunji yarinya da bakin ta tace ni take matukar Kauna, kuma haka ma uwar dakin ta,
Yanxu tunani nake yaya auren nasu dani xai kasance?
Ku bani shawara en uwa, za'a para na Madina ne daga baya ayi na kaltum ko kuma ayi duka rana daya?
LOL..
.
Sai Allah Ya kai mu gobe muci gaba,
Naku, a kullun masu kaunar nishadantar daku a ko da yaushe Sadin Maa da dan aiken ta Dan aunty angon MK ma'ana Madina and kaltum.ADON DAWA 39
.
TRUE LIFE STORY
.
Kaltum Tace bazata yarda ta dawo ba har sai dai idan anje da Abba, idan ta ganshi kila ta yarda ta dawo saboda zuciyar ta tariga ta daskare ta sawa ranta har abada tabar kasar nan bazata dawo ba.
alh Adnan ya gyada kai yace gaskiyane ke kika santa kika san ra ayinta, da shawarwarinki za'a yi ampani, jeki ngd za a dawo da madinarki,
tayi murmushin jin dadi tayi godiya ta mike cike da farin ciki zata fice harta kai bakin kofa zata fita taji yakara kiran sunanta sai taji hankalinta ya tashi mamaki ya rufeta ta dawo cikin sanyin jiki ta durgusa agabansa tana sauraron sa,
yayi murmushi yace kin bani labarin rayuwarki a bur sudan kakaf keda Madina da irin taimakonda Madina tayi miki amma koda wasa baki ambaci mambela ba?
daga inda yake yana juyo ajiyar zuciyar da tayi, saitayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa tayi shiru,
yaci gaba da cewa ni tuntuni nake jira ki maimaitamin abunda kika fadamin a waya kin samu miji dan ADON DAWA zaki bishi garinsu bur sudan, mutuminda ya taimakeki tun zuwanki bur sudan ya biki har Khartoum yana shirin mayar dake bur sudan ya aureki ai bai kamata ba har ki gama bada labari baki ambace shi ba,
Sai yaga tana kuka share-share da hawaye batada shirin magana don haka ya kyaleta ya hakura dajin amsarta ya umurce ta data tashi ta tafi gida,
ta mike jiki a sanyaye ta fice, a bakin baranda ta tsuguna ta sharbi kukanta ta goge hawaye sannan ta gangara ta shiga gidansu,
haryanzu mahaifinta yana labe a jikin labulen
dakinsa yana kallonta hankalinsa yayi matukar tashi daga yanda yaga tafito tana kuka, abunda yake zargi ya tabbata cewar ya tafka kuskure daya furtawa alh Adnan zancen ya auri yar sa kaltum gashi nan ya jawo mata tsana tunda daga lokacin yasawa ransa zamansu ya kare a gidan nan sai ya shiga tunanin ta yanda zamansu yakare agidannan sai ya fara tunani inda zasu fara babu gida babu gona babu sana a.
fitar kaltum keda wuya alh Adnan ya jawo wayar sa ya kira lambar alh sa'adu ta Nigeria yajita a kashe saiya kira layinsa na sudan sai kuwa ya same shi bayan sun gaisa yake shaida masa akwai wata mata da akeso anemo musu ita mai suna Madina a bur sudan amma ana tunanin matar bazata yarda
tazo ba har sai an tafi da mijinta,
alh saadu ya zabura yace kai haba kamar bani?
aiko a daure zan daukota kamar bakasan dauki ba dadin da mukayi da wannan bararojin ba mambela?
ai koshi kace in kawo maka duk da kasarsu ce sai na kawo shi da karfin tsiya balle yar ci rani wacce ba kasarsu ba kuma mace ai karamin aikine wannan, alh ka bani wuka da nama ka turo kudin jirgi kawai shine aikinka idan nakawota sai kabiyani yadda aka biyani waccan karon, nikuma sauran aiki ya rage nawa nasan bur sudan nasan gidajenda mutanenmu suke zama na tabbatar idan naje na tambayi sunanta za'a nuna min ba boyayyiya bane tunda kowa yasan kowa a tsakaninsu.
alh Adnan yayi dariya yace karka damu da wannan zan fita anjima zanje banki zan turo maka kudin komai ammafa kayi mata a hankali, ban saka dukan matar mutane ba koka daureta da igiyaba, cikin lumana zaka tahoda ita idan taki kabata waya zanyi mata magana in sha Allahu zata yarda ta biyoka, alh sa idu ya rusuna yayi godiya gamida yarda dabin umurnin alh Adnan, suka yi sallama suka ajiye,
missed calls biyar ya gani da sunan Abba yanata kokarin nemansa a lokacin da yake waya da alh Sa'adu ya amsa kafin Abba yayi magana ya bashi tabbacin cewar ya kwantar da hankalinsa za'a kawo masa madinarsa har gida ba sai yasha wahalar zuwa ba, Abba yaji labarin alh Adnan kamar tatsuniya bai fahimce shiba ma kwata-kwata sai ya shiga jero wa alh Adnan tambayoyi cikeda magiya
yana neman alfarma ya taimake shi yadda Allah Ya taimakeshi,
alh Adnan ya fahimci Abba bai gane abunda yake nufiba baya da haka baisan waye alh Adnan ba, shiyasa yake kokonton abunda ya fada masa, maganar karshe da alh Adnan yayi itace Abba kabani sati daya za a kawo maka Madina insha Allah.
Abba yayi godiya suka ajiye waya batare da Abba ya yarda da abunda alh Adnan ke fada ba kai har yanzu bai fahimci komai ba don haka sai hankalinsa yatashi, kamshin zuwan madina da ya fara ji ada ya gushe, ya kwanta yaji kwanciyar ba dadi ya tashi zaune yaji zaman ya gagareshi saiyayi zumbur ya mike yayi waje, a falo ya hadu da mahaifinsa ya zauna agabansa ya fara koro masa bayanan da alh Adnan yayi masa,
sai mahaifinsa yace to ai shikenan mu jira zuwa sati dayan,
ba haka Abba yake son ji ba, yafiso mahaifinsa yace ya shirya yaje sudan din,
su kuwa mahaifansa da en uwansa bazasu taba barinsa yaje sudan yadda sukaji labarin cewar Madina tace har abada ba zata dawo Nigeria ba to tabbas idan Abba yaje taki biyoshi waje zai samu ya zauna da ita shima bazasu kara ganinsa ba.
Abba ya mike jikinsa a sanyaye ya shiga dakinsa ya dade a tsaye ba tare da yasan abunda zaiyiba can ya dauki makullin motarsa ya fita da sauri ya kuwa ci sa'a babu kowa a falon ya fizgi moto sai kofar gidan alh Adnan,
a wajen get ya ajiye motarsa ya fito ya nufi cikin gidan shigarsa keda wuya sukayi kicibus da maigadi, malam saleh ya dubi Abba shima ya dubeshi sai hankalin malam sale yayi matukar tashi saboda ya gane wannar fuskar, saurayin nanne dayazo wajen kaltum ranan su biyu, malam sale ya tsuke fuska ya tambaye shi a fusace waka zo nema ?
Kamar yadda saleh ya gane Abba haka Abba ya gane mai gadinda yakoresu rannan ne don haka shima afusace ya amsa masa wajen masu gidan nazo,
sale ya hasala yace kai yaro ba inda zaka wuce in har baka fada wajen wacce kazo ba.
Abba yace mai ya hadani da mace ai wajen mai gidan nazo alh Adnan yanzun nan muka
gama waya dashi kashiga kace masa barister Abba Tukur ne daga yankaba,
sai sale yayi sauri ya rabe ajikin get,
Abba ya wuce batareda wani ya sake magana acikinsu ba.
baisan kofarda zaibi yashiga wajen alh Adnan ba shikuma bayaso ya tambayi wannan mara mutuncin mai gadin nan sai gashi Allah Ya
jeho masa kaltum ta fito daga cikin gida dauke da bokiti zata yi shanya a igiyar dake daure a farfajiyar gidan kamar kullum daga ta dawo daga makaranta zata fara aikin wanke kayan kazantan goggo fattu tana ganin Abba saitayi turus tana dubansa cike da mamaki yayinda shi kuma farin ciki ya lullube zuciyarshi yayi dariya yace yauwa kaltum ashe kinanan, yayanki kuwa yana ciki?
ya fadi hakane don yanaso yasan dangantakarta da alh Adnan,
saita dubeshi duba na rashin fahimta shima ya fahimci haka saiyace alh Adnan nake nufi, sai tayi ajiyar zuciya ta nuna masa kofarda zai shiga jikinta a sanyaye maimakon yatafi sai ya tsaya yana dubanta yana duban kayan shanyarda yake hannunta yana duban kannenta da suka baibayeta yana duban mahaifiyarta datake daka agefe ga goyo don ko ba a fada masa ba yana duban sofi yasan itata haifi kaltum da alama nan boys quaters
shine gidansu amma kuma babban gidan ta nuna tace nan ne inda alh Adnan yake ciki, tambayoyi fal acikin zuciyarsa babu damar tambaya saiya wuce zuwa bangaren da ta nuna masa ya tura kofa yayi sallama sai suka
ci karo a tsakiyar falo har alh Adnan yayi wanka ya shirya da makullin moto a hannunsa zai fice, yayi mamaki da ganin Abba don haka suka dunguma suka koma wajen kujeru suka zazzauna,
alh Adnan dakansa ya dauko masa lemo da ruwa acikin firij sannan suka fara tattaunawa.
malam sale tsaye a bakin get har yanzu yana zullumi, zuciyarsa tana ta tsaro masa karya da gaskiya yace aransa wato dai alh Adnan yasan wannan saurayin kaltum ne don haka ya aika akirawosa zai ba shi ita tunda shi bazai iya auranta ba amma tayaya zandauki yata inbawa wannan fitsararren yaronda yake yi min magana cikin gatsali ba mutuntawa?
saidai kuma bazan iya yiwa alh Adnan musu ba akan duk hukuncinda zai yanke akan yar nan don shi yayi wahalarta, ni wani tsausayine ma yasa na furta masa wannan kalmar taya auri kaltum?
malam sale ya nufi gida da sauri ya iske kaltum na shanyan har yanzu sofi na daka ya dafe kirji ya fada cike da damuwa kaiku tsaya da aikin nan,
gaba daya suka sankare a tsaye suna sauraronsa cikeda fargaba yace wata katobara nayi wacce ta dameni ga ta zata zame mana matsala, game da zancen yarinyan nan kaltum da alh Adnan,
kaltum ta dafe kirji tace Abba lafiya?
mena yi?
ya juya ya dubi kaltum yace ina kika samo wancan yaronda ya shiga cikin gida?
kaltum agigice tace Abba ne ai wanda zai auri Madina.
wacece Madina zaki fara boye-boyen nan naki ko?
don ba a taba jin cikinki ba, basu bane kwanakin baya na koresuba?
saita fashe da kuka tana rantse-rantse,
sofi tajashi cikin daki don taji kan labarin saboda kar su alh Adnan din suji yanda yake magana da karfi a fusace yayinda kaltum tazo ta labe a bayan wundo tana jiyo duk abunda mahaifinta yake fada ya zayyanewa sofi duk yanda sukayi da alh Adnan da kuma hukuncinda yake zargi alh Adnan zai zartar yana zargin Abba saurayin kaltum ne wajenta yake zuwa kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita...
.
To jama'a wannan episode din yana nuna mana kuskure na mal saleh da matar sa Sofi da aka daura su na rashin jituwa da er su da pahimtar juna,
Da akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin su da er su da ba'a kawo nan ba, da tun wuri sun sake da ita da ta basu labarin komai, kuma da sun san komai da ya shape ta maimakon ta sanar da wani,
Wasu yaran tsabagen babu puska a wajen iyayen su abokai suke baiwa labarin kukan su da daria, idan akayi rashin sa'a abokin bana gari bane sai ya basu shawara marar kyau,
Ana so iyaye lokacin da dan su yake taso wa xuwa shekara 7 su nuna masa soyayya, daga 7 xuwa wani 7 su nuna masa abu mai kyau da marar kyau (ma'ana su tarbiyyar tar dashi,) daga wani 7 din kuma su mai dashi abokin su, ta haka ne baxai na boye musu komai ba, xasu san irin halayen sa da irin abokan sa kuma xai koyi irin halin su.
Amma wasu iyayen sunan sun aihu ne kawai, sai su barwa dunia ta raina musu 'yaya.
Sai kaga uba bai san halayen yayan sa ba, bai san abokan yayan sa ba, banda gaisuwa babu abun da yake hada sa da su balle a samu lokacin hira ya pahimci damuwar su ba.
Ina mai Jan hankalin iyayen mu mata da maza ake shiga lamarin yaya, a jasu a jiki, ba sai abu ya kwabe ba azo ana dana sani, wani kapin a ankara yaro ya lalace.
Allah Ya tsare mu baki daya.
Aamiin
.
Sadiq Halima.
Abbas Abdulkadir Hada HadaADON DAWA 40
.
TRUE LIFE STORY
.
kila alh Adnan ya kirawoshi yabashi ita donshi ya zame ya fita daga nauyin da akeso a daura masa.
sofi tayi tagumi tayi shiru can tace malam kayi kuskure daka amayarda wannan magana abunda muke tunani muke addu'a dama yakasance shine zaka je ka fada?
yanzu ga irinta nan,
malam sale yayi ajiyar zuciya yace tsausayi ne wallahi nima ina dana sanin, don kaltum bazata fadi abunda ya fada mata bane dazu da ta shiga ta dade aciki saita fito tana kuka kila zaginta yayi ma.
kaltum dake labe a bayan wundo saitaji kamar zata kurma ihu don haka ta damke bakinta kuka ma mai tsanani ya kece mata, hankalinta ya tashi matuka yayinda ta fuskanci gaba daya zancen mahaifinta zargi ne baisan gaskiyar al amari ba,
na daya baisan abunda ya sata kuka ba dazu ba, haka baisan tsakaninta da Abba ba, baisan dalilin zuwan Abba wajen alh Adnan ba, wannan kalmar duk bai dameta ba tunda zargi yake, babbar matsalarta yadda yaje ya furtawa alh Adnan wannan kalmar ta aure alhali ga mijinta can a bur sudan wanda a koda yaushe yana ranta, tana muradin ganinsa babu wani da namiji a duniya dayakai mambela a cikin zuciyanta bata da wani uba ko uwa dayakai alh Adnan a ranta, don haka kowa da matsayinsa, ta koma dakinta ta zauna ta kifa kai da gwuiwarta tana kuka,
Goggo fattu na kwance akan gado tamkar gunki amma sai yunkuri take tanaso ta tambayi kaltum me aka yi mata take kuka amma maganar bata fita,
kaltum ta fahimci abun da goggo futtu keson ji cikin kuka ta fara magana batareda ta dubeta ba tace Goggo abur sudan kika tafi kikabarni ba uwa babu uba babu mataimaki sai Allah, iya mairo kawarki da jikarta rakiya dakika hadani dasu suka dinga tsangwamata sai na hadu da wata mata a cikin mu mai suna Madina, itake taimakona bayan ita sai na hadu da wani saurayi a garin ADON DAWA mai suna mambela shima yana sona kuma ya taimake ni, munyi alkawarin aure dashi, shi nake so na aura amma sai gashi Abba yaje yatari alh Adnan yace ya bashini ya aureni alhali ni a matsayin uba na dauke shi, babu mai kula dani babu mai yimin wahala babu mai bani abunda nake bukata a duniya sai alh Adnan, kiduba kiga irin tashin hankalinda matarsa mummy salaha ta jefamu, ki tuna kiga irin rigimar da za a tafka idan ta samu labarin maganar da mahaifina ya furta a yanzu tun kafin ma azo ga auren,
ta tsaneni bazata bari inzauna lafiya ba gashi inason mambela har yanzu shine na shaidawa kawayena zan aura har an yi mana baiko.....
ki auri Adnan kalmarda goggo fattu ta furta kenan radau ta dira a kunnuwan kaltum,
kaltum ta zabura ta dago kai ta dubi goggo Fattu wacce ke kwance luf kamar ba ita tayi magana ba, matar da a shekaru biyu maba a taba gane abunda tafada ba sai yau,
kaltum ta share hawaye tace goggo me kika ce?
shiru bata sake magana ba amma hawaye yana ta kwaranya daga idanuwanta,
kaltum ta rushe da kuka ta saka gefen zaninta tana gogewa goggo fattu hawayen da yake kwaranya daga idanuwanta,
kafin lokacin makarantar islamiyyah yayi kaltum ta saka kayan makaranta ta dauki Qur'an nta tanufi makaranta saboda kawai kada Abba da alh Adnan su fito su kirawo ta.
Abba yayi shiru yana nazarin akan bayananda alh Adnan yayi masa, saiyaji tunaninsa ya hargitse ya kasa magana har lokaci mai tsawo?
Abba yayi ajiyar zuciya ya dubi alh Adnan yace alhaji meye abunyi yanzu kace kaltum ta bada shawarar lallai a tafi dani sannan Madina zata yarda ta dawo, kace alh saadu yace shizai iya kawo mana ita yaya ka gani ?
Alh adnan yace kabar alh Sa'adu mugani din idan zai iya idan yagagara sai kaje din ta ganka kuma nace idan ya ganta yabata waya zanyi magana da ita nasan abunda zanfada mata.
Abba yace to shikenan amma inhar ta yarda zata taho to kada maka fada mata ina nan ka boye mata bayan ta dawo kun hadu ka roketa ta aureni saboda kai zata iya yarda da maganarka ina fargaba ta bijire ta ki aure na.
alh Adnan yayi murmushi yace yarinta ke nan kana so aki fada mata baka mutuba kana tunanin zata yarda tazo din in baka nan?
Abba yace ina kyautata zaton zata iya yarda da maganarka idan ta dawo zata iya bijirewa taki aurena,
Alh Adnan yace ka bari ta dawo din nayi maka alkawari zanyi iya kokarina ka auri Madina,
Abba yayi murmushi yace Allah Ya taimaka, alhaji nasan Madina tanada alkunya kayita magiya zata yarda, yanzu nawa zaikama dukka harkawota kano da dan rakiyar kuma nawa za a biya mai kawowar?
alh adnan yace karka damu nizan dau nauyin komai saboda Madina ta taimaki kaltum tanada matukar mutunci, naji inaso na taimaka mata nima.
Abba ya langwabe kai yayinda kwallah ta cika
masa ido yace Wallahi alh ba wanda zai zauna da Madina koyaji labarinta baiji ta kwanta masa a rai ba, macece mai matukar kirki da sanin ya kamata, madina ta banbanta da sauran mata don haka duk wanda na tinkara nakeja da baya domin basuda halin Madina, alh ka taimakeni nasamu Madina a rayuwata, inason matar nan idan ban aureta ba nahakura da aure kwata kwata...
kayi addu a Abba, Allah Ya zaba maka abunda yafi maka alkhairi a rayuwar ka, alh Adnan ya fada yayinda ya mike tsaye yana daura agogo,
Abba ma ya mike tsaye yana godiya yace bari natafi naga kana shirin fita ina ta bata maka lokaci ko?
ai idan na sami wajenda za ayi min zancen madina banaso intashi daga wajen na gode
alh Allah Ya kara zumunci Allah Ya taimake ka yadda ka taimakeni.
alh Adnan Ya amsa da amin. suka dunguma suka fito,
saleh ya tako da gudu ya zo ya duka ya gaishe da alh Adnan yana jira yaji hukuncinda aka yanke masa na mummunan laifinda ya tafka dazu, saiyaga alh Adnan cike da fara a ya dube shi yace saleh ga Abba ku gaisa, kaltum na cikine ka kirata su gaisa?
sai malam sale yaji fargabar da yakeji ada ta dadu ya dago ido ya dubi Abba shima ya dubeshi sai Abba ya gaishe shi, malam saleh ya amsa a sanyaye gami da kirkiro busasshen murmushi yace ai kaltum ta tafi islamiyyah dazu,
alh Adnan yace to ai shi kenan dama gaisawa zasuyi da bako yayinda, Abba yake kokarin furta tambayanda ya addabeshi aransa haka ma malam sale yake furta tasa a wannan lokaci sai su dukka suka tsaya suna kallon juna,
alh Adnan kamewa yayi atsaye yana sauraronsu malam saleh yace da Abba yaro fadi maganarka tukunna sai nima inyi tawa.
Abba yace daman tambaya zan yi ince yaya kake da kaltum?
sai malam saleh ya dubi alh Adnan ma'ana yabashi amsa,
alh Adnan yayi dariya yace mahaifin kaltum ne,
Abba yasake duban malam sale da alaman mamaki ya gallabi zuciyarsa amma bai sake cewa komaiba saidai kallo daya zakayimasa kasan ba iyakar tambayarsa kenan ba,
malam saleh kuma yace nikuwa tambayanda zanyi shine waye wannan?
don ko a danginku bantaba ganinsa ba saboda asan juna idan an hadu a wani waje a dinga gaisawa kada ayi abun kunya,
Abba ma alh adnan ya kalla ma'ana yanzuma shizai bada amsa,
alh adnan yayi dariya yace wannan Abba kenan angon Madina ne wacce suka zauna da kaltum a bur sudan.
malam sale yaja dogon numfashi sai a yanzu ya samu nitsuwa.
Abba yayi musu sallama ya fice yayinda alh Adnan ya shiga motarsa malam sale kuwa yahau aikinsa na bude get harsaida alh Adnan ya fice sannan ya rufe get ya koma ya zauna akan benci yayi zugum yana sake-sake da alama ya yarda da zancen kaltum cewar Abba ba saurayinta bane.
labbaika rasulillah sautin dake fita daga wayar alh Adnan kenan wayarsa tayi ta ruri misalin karfe takwas na safiyyar asabar yayinda yake tsakiyar barci akan luntsumemen gadonsa da yake katafaren gidansa na hadaddiyar unguwar nan mai suna asokoro a babban birnin tarayyah Abuja, da kyar ya daga hannunsa ya lalubo wayar a karkashin filon da yake kwance ba tareda ya iya bude ido yakaranta sunan mai kiranba saboda tsananin barcinda yakeji saiya danna yamaka a kunne daga kwance batare da ya iya magana ba haka yakasa amsa sallamar da mutumin yake radawa sauraronsa kawai yake yi hello alh kana jina?
gani abur sudan tareda Madina,
kalmarda tashiga kunnen alh Adnan kenan a take yanemi naunauyan barci nan yarasa sai yaji idonsa ya wartsake garau ya tashi ya zauna daram akan gado yayinda matar sa salaha ta fasa ficewa daga dakin ta dawo ta tsaya akansa tanaso taji waye mai wannan wayar da har ta wartsakar dashi daga barcin da yake,
yace alh sa adu da gaske kake katabbatar itace Madinan Abba?
alh sa adu yace kwarai kuwa itace kadai Madina ma agidan tasan kaltum kaima tace tasanka Allah cikin ikonSa ma ankawo service din waya garin, itama da waya ahannunta don haka gatanan zakuyi magana don naga a tsorace take bata yarda dani ba, alh sa adu ya mikawa Madina waya ta karba atsorace hannunta na kakkarwa gami da yimasa sallama cikin ladabi da girmamawa, ya amsa cike dakulawa yakara da cewa Madina kamar yanda kikeda labarina nima inada labarin ki kakaf banason tone-tone banason maimaita magana banason jin ra layinki na da, magana zamuyi ta yanzu maganar da ya wuce, kaltum tafadamana irin kokari da kikayi ko ince jihadi da kika yi kika ceto rayuwarta a wajenda kowa takansa yakeyi, ta fadamana dalilinki na barin ya'yanki
kikayi gudun hijira da zummar har abada baza ki dawoba a yanzu dai atakaice ni alh Adnan na aiko alh saadu abokinane shine wanda na aika ya dauko kaltum inaso ki biyoshi ku dawo m
ta rushe da kuka mai firgitarwa ta girgiza kai tace alh naji dadin kulawarka agareni Allah Ya saka da alkhairi ammakayi hakuri bazan iya biyo shi ba har abada bazan dawo Nigeria ba.
alh Adnan yaji hankalinsa yatashi yatambaya agigice Madina meyasa?
amatsayinki na musulma kike fadin haka?
bakisan kaddara ba?
kobakya yafiya?
ta girgiza kai ta share hawaye da gefen gyalenta tace bahaka bane alh nafi jin dadin rayuwa anan fiye da can, na yafewa duk wanda ya zalunceni irinsu Tasi'u da matansa nayafewa duk wanda sukayimin Kazafi irin mummy hafsat general Tukur da kawata sumayyah, na yafewa 'yayana dasuka ki min biyayyah amma na hakura da kara cigaba da rayuwa dasu babu mai wankeni a duniya sai Allah, Abba ne yafi kowa sanin gaskiya lamarin shi zai fitarda ni, shikuma baya raye to mezanzo nayi?
sai ta rushe da wani kuka mai daga hakalin mai sauraro,
alh Adnan yayi ajiyar zuciya yace kinaso kigayamin da Abba na raye zaki yarda ki dawo saboda zai wankeki daga zarginda ake miki?
Madina ta gyada kai tace eh da Abba naraye zan dawo saboda nayarda da son da yake min koda ace bazan aure shi ba, Saboda na hadu da wanda nake matukar so shine Dan AUNTY... LOL.
To ya kamata dai yanzu kam kowa ya yarda da wannan alamari, gashi dai Madina ta shaidawa dunia cewa ni take so,haka ma kaltum, tun daga yanxu xan para celebration na auren su.
DMK (Dan Aunty, Madina and kaltum).
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 41
.
TRUE LIFE STORY.
.
Ko da ace baxan aure shi ba inason Abba har raina.
kinaso kice min da Abba naraye yace har yanzu yanakan bakansa na auranki da yake son yi zaki aure shi?
Madina tace tabbas da matacce na dawowa da zan auri Abba, nayi nadamar abunda nayi masa gashi duk da gudun rigimarda nakeyi naki amincewa saida ta afku har fiye ma da ace na yarda,
alh Adnan yace bakya tunanin 'yayanki musamman karamar mace?
ta sharce hawaye tace alh na rayu ba uwa ba uba babu yayye amma daga baya na hadu da mutanen da suka fiye min iyayena da dangina alkhairi duniya da lahira don haka rashina bazai zama shine karshen gatansu ba Allah shine gatan bawanSa Allah Ya hadasu da abokan zama na gari, ina daganan ina jifansu da kyawawan addu'o'i bazasu tagayyara ba insha Allahu, babbar damuwana daman kaltum ne na matsu ta koma gida ta rayu da iyayenta tayi aure cikin mutunci Allah Ya amsa addu'a ta yanzu hankalina ya kwanta zanji da kaina,
alh Adnan ya shiga yi mata magiya yana hadata da ta duba girman Allah da darajar Manzon Allah (s.a.w)ta dubi matsayin musulmi awajen dan uwan ta musulmi yayi mata alkawarin bazai fadawa su mummy hafsat ta dawo ba bakuma kano zataje ta zauna ba, a Abuja zatazo ta zauna tare kaltum,
tun Madina tana bashi hakuri akan ya daina ma rokarta bazata dawo ba har tayi shiru ta rasa abunda zata fada masa daga karshe ya fada mata wata magana da tayar mata da hankali yace da ita Madina dalilin da yasa nace a nemoki shine Abba bai mutu ba, duk tsawon shekarun nan yana kwance yana jinya a asibiti anan Abuja, bai daina Kiran sunanki ba ki tausaya masa kizo ki ganshi ko Allah zaisa ya warke...
alh Adnan ya katse waya ya barta a zaune kikam rike da waya ahannu tamkar gunki,
Hajia salaha ta dubi maigidan nata ta tsuke fuska yayinda ta rike kugu ta girgiza ko ba a fada masa ba yasan yau akwai rigima ta tambayeshi tamkar danta, dawa kake waya wacece Madina?
daman kai ai komai inda Madina aciki kafi bashi muhimmanci, wato bayan kaltum dinda aka aika aka dauko har kawarta xaka dauko?
kaine bawansu kai zaka dauko ta to bari kaji babu matarda zata dakomin gida don naji kana lallashinta idan batason kano taxo Abuja.
Alh Sa'adu kuwa sai magiya yake mata da nasihohi iri iri yake jero mata akan ta taho su tafi, haka mata da mazan gidan suke shawartarta ta shirya ta tafi tun kafin damar nan ta subuce mata suna masu yi mata albishiri da sune suka sami wannan dama da karshen matsalarsu tazo a dunia, daga karshn Madina ta shirya tayi sallama da yan gidansu aka yi ta kukan rabuwa saboda an saba, sabo turken wawa, bata fito daga bur sudan ba saida ta garzaya jim arab kasuwar yan ADON DAWA ta iske mambela a rumfarshi da abokansa suna shan jubna yana ganin jajayen idanuwan Madina sai ya wurgar da kofin jabna ya zabura ya mike tun bata karaso rumfar ba ya tareta yana tambayar ko lafiya?
agigice ta rushe da kuka cikin yaren ADON DAWA tace mambela nima anzo daukana zan koma Nigeria gidansu kaltum.
ya dade yana dubanta bai iya magana ba cikin sanyin murya yace da ita ki daina kuka ki share hawayenki abun murna ne ki gaishe min da kaltum kice har yanzu ina son ta,
sai hawaye ya kwaranyo daga idanuwansu su dukka ya juya ya koma cikin rumfa ya zauna jikinsa ya mutu ya zurawa Madina ido har ta kure, yaki amsawa abokansa tambayoyinda suke ta jera masa,
daga bur sudan Madina da alh sa adu jirgin kasa suka hau na zuwa Khartoum ya kai ta gidan wasu mata yan Nigeria acan ta zauna har tsawon kwanaki hudu ana cuku-cukun tafiya visa da ticket sannan suka sami tahowa bayan komai ya kamkama,
ranar talata da yamma Madina da alh sa'adu suka dira a birnin tarayyah Abuja, daga filin jirgi suka bugawa alh Adnan waya yace su ba wa mai taxi waya yayi masa kwatancen gidan, tunda dan gari ne nan da nan yagane anguwar gwarumpa gidan alh Mansir babban amininsa na Abuja kenan,
kafin sukaraso har alh Adnan ya bayyana a gidan daman ya shaidawa mai gidan zai kawo musu bakuwa su rike masa har zuwa wani dan lokaci saboda yasan halin matansa bazata bari ta sauka agidansa ba,
hankalin alh Adnan ya tashi dayaga Madina daga ita har jikinta da buhun kayanta da take rike dashi, ya fada aransa daman wannan itace madinar da Abba yake muradin so kamar zai rasa ransa adalilin rashin ta?
to koba haka take ba ada yanzune tazama haka?
Madina ta durgushe agabansu ta gaishesu ba tare da ta matso tsakiyar kafet din da yake tsakiyar falonba balle ma ta hau kan kujera ta zauna,
hajiya zainab matar alh Mansir ta taso da fara'arta ta karbi buhun kayan Madina tana mai yimata sannu da zuwa da bata izinin ta iso cikin daki, Madina ta na biye da ita a baya zuwa cikin daki, katafaren daki mai dauke da
tafkeken gado da madubi da durowar saka Kaya, bandakin acikin daki bayan ta saka buhun kayanta a durowa sai ta nunawa Madina bandakin ta umurceta ta shiga ta yi wanka za a kawo mata abinci yanzu, sai mamaki da farin ciki ya lullube zuciyar Madina yaushe rabon duniya da ayyaraye wai yau ita ake cewa ta shiga kayataccen bandaki tayi wanka ta fito taci abinci?
da irin wadannan tunane tunane ta shiga wankan kafinta fito ta iske mai aiki ta jera mata abinci kala-kala agaban gado, kamshi da tururi ne suka daki hancin ta,
haj zainab ta shigo da fara-arta ta dubi Madina tace ga wata atamfa nan tawace sabuwa ce na dinka ko sakawa banyi ba jiya aka kawomin daga wajen dinki ki saka alh Adnan yace kada abari kisake mayarda kayan
jikinki yace kikawo buhun kayan a zubar zai dinka miki wasu, kin san shi dan gayune ga tsafta baya son tsohon abu, sannan kici abinci mutafi asibiti yanason a duba lafiyanki gaba daya agani ko akwai rashin jini ko wata cutar a baki magani,
madina tayi kasake tana duban hajiya zainab kamar a mafarki take jinta, tayi murmushi yayinda hawayen farin ciki ya cika mata ido tace to ta jawo sabuwar atamfa super holland ta saka kayan kuma daidai jikinta kasancewar itama hajiya zainab din bamai kiba bace saidai kash bazata iya yafa tsalelen gyalenda aka hado mata da atamfarba, hijab kawai take iya sakawa tafita waje saita yiwa hajiya zainab bayani cewa inda hijabi ta bata bata yafa gyale aka kuwa yi sa'a akwaita da hijabai kala kala saita dauko mata ruwan daurawa wanda ya dace da atamfar kalar koriya ce da ruwan daurawa,
Madina ta zauna ta fara bubbude manyan fulasan abinci taga soye soyene na doya da dankali da wainar kwai ga flask din shayi ga biredi da cake duk wanda takeso zataci, tsohuwar yunwa dake jikinta ta taso sai citakeyi batasan inda abincin ke tafiya ba ma, har taci rabin abincin batayi rabin koshiba rabonta da tasami abinci mai dadin wannan harta manta.
alh Adnan alh Mansir dakuma alh sa'adu haryanzu suna zaune a falo suna tattaunawa akan irin wannan matsananciyar rayuwa da mata da yara kanana suke jefa kansu ta tafiya kasashen wasu da zummar neman kudi, daga karshe naira na dukan naira har naira dubu dari biyu da hamsin aka bawa alh sa'adu bayan tikitinsa na komawa sudan kamardai yanda ka bashi dayakawo kaltum sukayi sallama,
alh Sa'adu yana sake nanawa alh Adnan cewar yana nan dai idan aka sake samun irin haka a tuntubeshi a shirye yake daya taimaka sannan ya tafi,
bayan ya sallami alh sa'adu sai Adnan ya caske kudi yabawa haj zainab ya umurce data kai Madina asibiti a kwantar da ita a asibiti ko lafiyarta kalau akwantar da ita ta huta sannan a dinga Saya mata duk wani abinci mai gina jiki domin daga ganin Madina ko ba a fada maka ba kasan babu blance died a jikinta, yasa aka kira masa Madina ya dade yana yimata nasiha akan ta kwantar da hankali a sami lafiyarta kafin ayi maganan Abba...
Sai tayi caraf tace alh zanso nafara ganin Abba tukunna kafin inje asibiti tunda dai ahaka lafiyata Kalau.
ya girgiza kai yace ta Abba mai saukine bani nace Zaki gashi ba?
zankawo mikishi ki ganshi.
ta sunkuyar dakai kasa sai hawaye sharaf sharaf sharaf sharaf tasan wayo yayi mata don ta dawo amma babu Abba, ya mutu
alh Adnan ya lura kuka takeyi sai ya shiga lallashinta yana dada jaddada mata zataga Abba ta kwantar da hankalin ta ita dai ta fito daga asibitin tukunna.
tayi ajiyar zuciya tace Allah Ya kaimu Allah Ya sa muga alkhairi, ina kaltum kuma?
alh Adnan yace kaltum tana nan lafiya itama zaki ganta tare da Abba,
saita kura masa ido tana masa duban rashin
yarda yayinda tashiga kokonton ko ta fada hannun yan damfarane?
saitace aranta Allah na tare da ita Shizai fitar da ita ko a wanne hali ta tsinci kanta,
alh Adnan yayi musu sallama ya tafi,
Haj zainab da mai gidanta suka umurci Madina ta biyo su za'a kaita asibiti tana zaune a bayan moto tana duban gari yayinda hawaye bai daina zuba ba, wata zuciyar nace mata meyasa ta yarda ta dawo gashi ita ta zo ita bada ganin kaltum ba balle Abba, wai shin ina hankalinta da tunaninta yatafine da har akayi mata wayo aka dawo da ita Nigeria?
Sai ta tuna da komai yasami bawa mukaddarine ne daga rabbul samawati abunka da mai ilimi saita share hawayenta taci gaba da kallon gari tana duban manyan gine gine da titina kayatattu a birnin tarayyah Abuja daman bata taba zuwa Abuja ba a rayuwarta tace aranta ashe muma munada kudi a kasarmu. tome sudan zata nuna mana dahar muka je muka makale musu.?
ta gangaro tunanin 'yayan ta taji a ranta babu abunda tafison gani ahalin yanzu irin ta ga ' ya yanta tayi kamar tace musu sukaita tasha su sakata a motar kano ta fasa zuwa asibitin
saita daure tayi shiru tana mai biyayyah da umurnin wanda ya taimaketa alh Adnan,
suka isa kelina hospital dake cikin unguwar gwarumpa, lafiyayyen asibiti mai kunshe da kwararrun likitoci.
.
Saady Dan AuntyADON DAWA 42
.
TRUE LIFE STORY
.
haj Zainab ne da Madina suka shiga ciki da yake suna da file a asibitin lambar file din ta fada, aka tambaye ta likitan da zata gani sai kuwa ta jero likitoci daya bayan daya har guda shida kowanne kuma kudin ganinsa daban, ta biya,
kamar yadda aka yiwa kaltum binciken nan da gwaje gwaje irin sa alh Adnan yace ayiwa Madina ma, yana ta koro bayanai a waya har saida likitoci sukayi masa abunda yakeso daga karshe sakamakon gwaje gwajen suka firfito, Madina batada wata matsala ajikinta sai hawan jini da ciwon zuciya tanada rashin isheshen jini da ruwa a jikin ta, sai ya umurcesu dasu kwantar da ita su bata kulawa ta musamman har sai komai ya daidaita zasu sallameta, kada su damu da yawan kudinda zai kashe, daki mai tsada na kwanciar mutum daya yace a bata, sannan asibiti su shirya mata time table din abincin da zai kara mata jini da kuzari su dinga bata basai haj zainab ta dinga zirga zirgar kawo mata abinci ba saida komai ya daidaita sannan akabawa Madina gado ta kwanta haj
zainab ta dawo gida alh Adnan bai daina waya ba yana fadar yanda za ayi da Madina ba, yace gobe haj zainab taje kasuwa ta siyowa Madina kayan sawa sannan ya sake umurtarta haj zainab taje da almakashi asibiti ta askewa Madina gashinta,
Haj zainab ta tuntsire da dariya tace haba dadyn Mashkur yaya za ayi ka sani in dauki almakashi Inje in hau gwaguyewa mace kai haka kawai baruwana kanta ras yake da kitsonta gata da gashi mai tsawo da tsananin baki,
alh Adnan yace ai na zaci irin gashin kaltum ne uwarta ta rasa ma yadda zata taje kan sai askewa tayi sbd cukuikuiyewa, kura da amosanin fari tas,
haj zainab tace a'a wannan da kitsonta kuma mai tsafta ce dayake babbace basai anceta gyara jikinta ba, kaltum kuwa ai yarinyace,
tunda alh Adnan ya fara waya da haj zainab Abba ne akan layi yanata nemansa a waya yana gama waya da haj zainab sai wayar Abba ya shigo bayan sun gaisa alh Adnan yabashi hakuri cewar yaga missed call dinsa
tun dazu yana ta amfani da wayar bai samu ya kira ba,
Abba yace babu komai yau sati daya yacika kamar yadda alh saadu ya dauka ko akwai wani labari daga gare shi?
alh Adnan yace kwarai kuwa akwai alamar nasara ka kwantar da hankalin ka zan kawo maka Madina har kano.
Abba yayi shiru na tsawon mintina daya yakasa magana yayinda zuciyarsa ta sakamasa lalle alh Adnan ya daukeshi karamin yaro don bayaso kaltum tarakashi sudan shine ma yake kokarin hanashi zuwa har ma yake masa wayo wai ya kwantar da hankalinsa zai kawo masa Madina har gida?
tayaya zai kawo masa ita gida?
saiyaji haushin alh Adnan ya lullube zuciyarsa
yayinda alh Adnan yayi ta magana shi kadai batareda Abba yana sauraron ma abinda yake cewa ba yana can yana tunani, can ya dawo da hankalinsa kan alh Adnan kalmar dazu dai yake maimaitawa har yanzu basai kaje sudan ba har gida zan kawo maka Madina da izinin Ubangiji,
Abba yaja dogon numfashi yayi murmushin takaici yace alh ina ganin zaifi kyau in shirya in tafi sudan din nan sai ka hadani da alh saadu muje nemanta tare,
alh Adnan yace Abba kasanni ne ada ko nayi
maka kama da karamin mutum wanda zai yi maka karya?
Abba ya girgiza kai yace a a ranka ya dade,
alh Adnan yace to tunda nace maka ka kwantar da hankalinka zan kawo maka Madina har gida da izinin ubangiji zan kawo ta.
abba ya sankare a zaune har sai da alh Adnan ya kashe waya bai cire wayar sa daga kunnensa ba, kwakwalwarsa ta hautsine tamkar hayaki ake turnuka masa, ya shiga kokonto ya kasa gane gaskiyar al amarin alh Adnan baiyi kama da wanda zaiyi masa karyaba to yayi masa karya a wanne dalilin?
idan yayi masa karyar mezai samu?
kodai iyayensa suka hada baki dashi don a hanashi zuwa sudan?
irin wadannan tunane tunane ya yini ya kwana yanayi sharkif cikin tunani da damuwa ya kasance sai da duk yan gidan suka lura da haka aka tambayeshi yaki fada sai shi sai zuciyarsa ne suka san gaskiya.
saida Madina ta cika sati daya cur a asibiti kafin aka sallamota hartayi kuzari tayi kyawun gani ba kamar yadda tazo ba, washe garin ranar da sassafe misalin karfe bakwai alh Adnan da direbansa simon suka dira agidan alh Mansir batare da Madina tasan ita suka zo dauka ba, tayi sallar asuba tunda assalatu tana zaune akan abun sallarta tana ta tasbihi tana kwararo addu o i kala-kala akan Allah Ya sa alh Adnan da dagaske yake
Abba bai mutuba kuma Allah Ya sa jikinsa da sauki bai nakasaba yadda bazai sake moruwa ba, ta kara da addu a Allah Ya sa 'yayanta suna raye suna cikin koshin lafiya da nutsuwa,
haj zainab ta shigo dakin yayinda ta zauna a gefen gadon har saida Madina ta shafa addu'a a fuskarta suka shafa a tare,
Madina ta waiwayo ta dubi haj zainab saitayi murmushi ta gaishe ta,
haj zainab ta amsa cikin fara'a tace alh Adnan da direbansa sunzo daukarki zaku tafi kano ashe tun giya ya fadawa mai gidana shikuma ya manta bai fadamin ba, balle na fada miki, ki shirya gasu can a falo ke suke jira amma ki shirya a nitse suma sai sunyi karin kumallo zaku wuce.
sai Madina taji wani abu ya harba a cikin zuciyarta fargaba mai tsanani ta far mata saita fara karanta InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta, ta amsa da to sannan ta mike a sanyaye ta shiga bandaki ta dade a tsugunne a bandaki tana kuka tana fargabar abunda zata je ta iske a kano, taji kamar tace bazata je kanon ba gara a bata kudin mota ko jirgi ta koma sudan ko ta bazama cikin Abuja a neme ta arasa,
kafin ta fito daga wanka an jera mata abinci kala kala a tsakiyar dakin bata yi wata wata ba ta bude akwatinta trolly wacce aka shake mata da kaya har kala biyar gaba dayansu a
dinke aka sayesu, dinkin yan senegal, ta zabo wata shadda kalar jan duhu maroon ta saka a jikin ta yayinda ta zabi bakin hijabi ta saka da ta zauna cin abinci sai ta kasa ci saboda fargaba ta tura loma biyu ta mike ta harhada sauran komatsanta ta cusa a cikin akwatinta ta kinkimo ta fito falo jikinta a sanyaye, ta durgusa ta gaida alh Adnan da abokinsa suka amsa mata cike da kulawa sannan suka dunguma zuwa wajen mota.
haj zainab na rike da akwatin Madina har cikin mota, Madina ta shiga gidan baya alh Adnan na gaba da direba yana tukawa,
alh mansir da matarsa sunayiwa Madina fatan Allah Ya kiyaye hanya ita ma tana musu godiya hadi da fatan Allah Ya saka musu da alkhairi bisa abun arzikinda suka mata,
suna daga mata hannu suma suna daga musu hannu har suka hau titi suka fara tafiya, madina taja dogon numfashi tayi ajiyar zuciya yayinda tayi tagumi tana sauraron inda Allah zaiyi da ita nan gaba, ta kurawa wundo ido tana kallon gari tabbas akwai attajiran da sukejin dadin rayuwarsu a kasarnan ashe ba duk en Nigeria bane rayuwa tayi musu zafi ba, akwai masu jin dadi saboda sunsha wuce tsala-tsalan motoci dauke da zankada-zankadan en mata a kame a baya direba yana tuka su, kota gansu tareda mazajensu da 'yayan su, kallo daya zaka musu ka tabbatar suna cikin ni ima
basuda damuwa,
dasuka bar cikin gari sai suka fara keta daji babu abun kallo kuma saita bude yar karamar jakarta da yake rataye a kafadanta ta zaro Qur'ani tahau karantawa yayinda taketa jero addu o i a zuciyarta tana fatan Allah Ya nuna mata alkhairi a kano kada ta hadu da abun ki shine ta iske Abba a raye ta samu 'yayanta
lafiya, tana matukar fargabar haduwa da general Tukur da iyalansa da kuma Tasi'u da matansa, tana gudun kada Allah Ya sa a maimaita mata waccar kalmar datayi sanadiyar rabata da kasarta wato maita sai hawaye ya balle mata yana gudana daga idanuwanta yayinda alh Adnan ya tsura wata ido ta madubin dake gefensa da yake a saitin bayan sa take zaune, ya zare farin gilashin da yake fuskarsa ya ajiye jaridar da yake karantawa ya waiwayi baya ya dubeta yace haj Madina meye matsalarki ne a yanzu?
tayi sauri ta dago da jajayen idanuwanta ta dubeshi saita girgiza kai tace bakomai alh,
yace ki cire damuwa ki fauwalawa Allah komai nayi miki alkawari zan taimakeki zan tsaya miki a duk al amuranki har sai kinji dai dai kamar yadda kowacce mace takejin dadin rayuwarta a gidan ta, kuma a kasarta kada ki manta shi alkhairi baya fadawa a kasa duk abunda ka shuka shizaka girba, kaltum ta fada min irin abun arziki da kulawar da kika yi mata a waccan duniyar taku a inda ake takai-takai hatta kakarta wacce ta rabota da iyayenta ta tsallake ta barta amma kika kula da ita saboda me yasa ni bazan taimaka mikiba?
ta fashe da kuka tana matukar godiya dashi albarka,
ya juxa ya saka gilashinsa yaci gaba da karatun jaridarsa kamar daga sama yaji muryan Madina ta furta masa wata kalma wacce tayi matukar bashi mamaki sai ya juyo a hankali ya dubeta batareda ya iya sake tambayarta abunda ta fada ba ko kunnensa ne baijiye masa daidai ba,
madina ta maimaita maganar tace alh mezai hana ka auri kaltum?
ina ganin zatafi samun nutsuwa a rayuwarta tunda kun shaku, kaltum na son ka kuma ta shaku da kai don kusan kullum tana bani labarin ka,
ya juya ahankali yacigaba da karatun jaridarsa batare da yagane abunda yake karantawa ba, kwakwalwarsa ta shiga rudani yakasa tantance dalilinda yasa mutane sukeyi masa sha'awar auren yarinyar nan karama, wai shin ko akwai wata alama da yake nunawa yanason kaltum afili bai sani ba?
har suka isa birnin kano ta dabo tumbin giwa babu wanda yasake magana acikinsu sai wa'azinda yake tashi daga rediyon jikin motar, dama Simon (direba) ko hausa bayaji balle yaji abunda ake fada ya bude wuta sai gudunsa kawai yakeyi yayinda sanyin a.c ya dinga ratsa jijiyoyin jikinsu,
Madina ta zubawa garin kano ido tana ganin irin ci gabanda akasamu fiye da da bakamar yanda ta bar garin ba ta rufe Qur'ani da ke a hannunta ta mayar cikin jaka ta ci gaba da dararradin abunda zata gani ko kadan bataga sun nufi gidan general Tukur ba can wata unguwa suka kutsa saitaji dan sanyi a ranta, a gaban wata get suka tsaya aka matsa horn batareda bata lkc ba sai wani bakin mutum ya wangame get da alama dai mai gadi ne saboda yanayinsa a kukkuje yake akwai alamar rashi a tare dashi suka kutsa da motar cikin gida sai gasu a farfajiyar wani kayataccen gida mai kamada aljannar dunia, alh Adnan ya juya ya dubi Madina yace BismiLlah fito munzo gida,
cikin sanyin jiki Madina ta sa hannu ta bude kofar mota ta sako kafarta daya waje kafin ta
sauko da dayar sai ga kaltum ta manno da gudu ta yi tsalle ta danneta tana ihu don murna,
suka rungume juna suna murna fuskokinsu cike da annashuwa yayinda mamakin ganin Madina ya hana kaltum sakat, kalmar farko da kaltum ta fara furtawa Madina itace ina mambela?
sai karaf a kunnen alh Adnan wanda ke tsaye a gefe yana dubansu.
Madina ta dago da sauri ta dubeshi sai a lokacin kaltum ta lura da cewar ashe yana tsaye a wajen, kunya ta kamata sai taje da sauri ta durgusa ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a yakara dacewa nafara cika miki burinki na kawo miki Madina?
kaltum ta tsunkuyar takai kasa tana murmushi tace ngd.
kaltum dauke da akwatin Madina suka nufi cikin gidansu basu tsaya a ko ina basai a gaban gadon goggo fattu ,
Madina ta dade a tsaye tana duban tsohuwarnan itama tsohuwar tana dubanta
kowaccensu ta kasa tuno inda tasan fuskar nan,
kaltum ta lura da hakan saita katse tunaninsu tace aunty Madina goggo fattune fa batada lafiya shekara da shekaru, goggo Madina ce wannan wacce muka tafi sudan da ita a mota daya, sai Madina ta dauki dogon salati ta karasa da sauri wajenta ta zauna a gefen gadon ta rike hanun ta tana maiyi mata addu'ar Allah Ya bata lafiya, hawaye ya fara surnanowa daga idanuwansu su dukka ukun goggo fattu ta bude baki dakyar tayi magana
duk da maganar bata fita gaba daya amma ana gane wata daga ciki tace Madina kinga kaltum ita ke kula dani tabani abinci a baki tayimin wanka, tayimin wankan tsarki,
madina ta girgiza kai tace Allah sarki rayuwa goggo ki nemi gafarar kaltum domin kin zalunce ta a baya kice ta yafe miki, don Allah ba ya yafe wa wani laifi wani, sai goggo ta gyada kai har sau uku sannan ta fashe da kuka, Madina ta jawo hannun kaltum ta hada danata goggo fattu ta ce kaltum ki yafe mata duk abunda tayi miki a baya.
cikin hawaye mai tsanani kaltum ta gyada kai ta ce goggo nayafe miki duniya da lahira, ana cikin wannan hali sofi da saleh suka shigo cikin dakin suna masu marhaba da zuwan Madina bayan sun gaisa kaltum ta gabatar da Madina ga iyayenta sannan ta gabatar dasu ga Madina sai a lokacin kaltum tabasu tarihin rayuwarta da Madina a bur sudan da irin taimakon datayi mata da yadda akayi ta nemo ta, yayinda iyayen kaltum suketayi mata godiya ita kuwa Madinar hankalinta ba ya jikinta ta nutsa kogin tunani da rudani mai yawa a sanadiyyar sunan Abba da kaltum ta dinga ambato a cikin labarinta, bata iya katse kaltum ba a lokacin sai da iyayenta suka fita kaltum ta yunkura zataje ta dauko mata ruwa sai Madina ta rike hannunta ta dawo da ita ta zaunar da ita ta dubeta cike da kidimewa tace kaltum naji kina ambaton Abba a zancenki wanne Abba kike nufi?
kodai anas kanin sa kinsan fa kamar su daya Abba ai ya mutu kin manta?
kaltum ta dafe kirji tace ahaf ashe na manta
ban fada miki ba na dauka kinsani Abba bai mutuba naganshi da idona yazo gidan nan har sau biyu,
sai Madina takame azaune tana duban kaltum kamar gunki harta fice daga dakin ta kasa magana tace aranta daman alh Adnan da gaske yake yi dayace Abba bai mutuba yana raye?
amma ai yace min a kwance yake har yau bashida lafiya kuma kaltum tace yazo gidan nan har sau biyu lafiyarsa lau kenan wai shine menene gaskiyar al amarin nan ko dai don su kwantarmin da hankaline suke kiran Abba na raye?
kaltum ta shigo da babbar kofi dauke da lemo da kananan kofuna tazo ta ajiye agaban Madina zata juya ta fice saitaji Madina ta damko hannunta, kultum ta firgita da ganin jajayen idanuwan Madina mai zubar da hawaye mai yawa, cikin rawar murya take magana tace kaltum ki fadamin gaskiya game da Abba na riga nazo Nigeria ba komawa zanyi ba idan na iske ba Abba na yarda da kaddara haka alh Adnan ya fadamin Abba na raye kema gashi kina fada min.
.
AlhamduLillah, yau baki na har kunne, mata na biyu sun hadu, saura shirin biki, dan haka ba magana,
Ina so nayi ampani da wannar damar wajen gaishe da duk wata mai sunan AUNTY na Maryam.
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 43
.
TRUE LIFE STORY
.
kaltum ki fadamin gaskiya game da Abba na riga nazo Nigeria ba komawa zanyi ba idan na iske ba Abba, na yarda da kaddara haka alh Adnan ya fadamin Abba na raye kema gashi kina fada min Kinga Abba, kinsan ina da matsalar ciwon zuciya ban cika son samun faduwar gaba ba, idan shi babbane yayimin irin wannan wasa ke karama ce bana irin wannan wasan dake.
hankalin kaltum ya tashi ta sulale ta zauna agaban Madina tace Wallahi Abba na raye yana nan lafiyarsa kalau ai da dashi ma za aje daukoki daddy yace zai sa alh sa adu ya
kawo ki donni ma shiya nemoni,
Madina ta sulale tayi sujjada ga Ubangijin talikai don farin ciki da godiya ta daga kanta sama da hannayenta biyu tana fadin AlhamduLillah Allah kaine abun godiya tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya halicce ni ya raya Abba Allah na gode maKa daKa amsa addu'ata Ka wanke ni a idon duniya kafin inbar duniya, naji dadi daKa fitar da 'yayana daga bakin dunia cewar uwarsu tabar musu abun gori,
kaltum ta toshe bakin Madina gamida zaunar da ita tace aunty Madina kiyi shiru mana da karfi kike magana fa kada mutane su shigo su dauka wani abu ne.
madina ta rushe da kuka tace kaltum dole ne in godewa Ubangijina domin Ya amsa addu'ata dana dade inayi, farin cikin da nake yi ba dan in auri Abba ba sai don Allah Ya taimakeni Abba bai mutu asanadiyyata ba ya
warke ya tashi daram na tabbata zai yi musu bayanin duk abunda ya faru na gaskiya, Allah Ya wankeni 'yayana zasu huta da gori shine kadai fatana daman,
kaltum tace kwarai Abba yayi musu bayani sun gamsu sunyi nadama sun bazama nemanki don sunemi gafararki basu sameki ba dole tasa suka hakura,
Madina ta mike da sauri ta ce tashi ki rakani gidan su Abba,
kaltum tace ki bari gobe ko anjima kici abinci tukunna har a gama,
Madina ta girgiza kai tace bazan iya kara awa guda ba banje naga Abba da 'yayana ba, kafin kaltum tace wani abu Madina ta suri akwatin kayanta ta fice tsakar gida don haka kaltum ta dubi goggo Fattu wacce har yanzuke kwaADON DAWA 43
.
TRUE LIFE STORY
.
Jama'a patar za ku mana uzuri, wannan coplete ne.
.
kaltum ki fadamin gaskiya game da Abba na riga nazo Nigeria ba komawa zanyi ba idan na iske ba Abba, na yarda da kaddara haka alh Adnan ya fadamin Abba na raye kema gashi kina fada min Kinga Abba, kinsan ina da matsalar ciwon zuciya ban cika son samun faduwar gaba ba, idan shi babbane yayimin irin wannan wasa ke karama ce bana irin wannan wasan dake.
hankalin kaltum ya tashi ta sulale ta zauna agaban Madina tace Wallahi Abba na raye yana nan lafiyarsa kalau ai da dashi ma za aje daukoki daddy yace zai sa alh sa adu ya
kawo ki donni ma shiya nemoni,
Madina ta sulale tayi sujjada ga Ubangijin talikai don farin ciki da godiya ta daga kanta sama da hannayenta biyu tana fadin AlhamduLillah Allah kaine abun godiya tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya halicce ni ya raya Abba Allah na gode maKa daKa amsa addu'ata Ka wanke ni a idon duniya kafin inbar duniya, naji dadi daKa fitar da 'yayana daga bakin dunia cewar uwarsu tabar musu abun gori,
kaltum ta toshe bakin Madina gamida zaunar da ita tace aunty Madina kiyi shiru mana da karfi kike magana fa kada mutane su shigo su dauka wani abu ne.
madina ta rushe da kuka tace kaltum dole ne in godewa Ubangijina domin Ya amsa addu'ata dana dade inayi, farin cikin da nake yi ba dan in auri Abba ba sai don Allah Ya taimakeni Abba bai mutu asanadiyyata ba ya
warke ya tashi daram na tabbata zai yi musu bayanin duk abunda ya faru na gaskiya, Allah Ya wankeni 'yayana zasu huta da gori shine kadai fatana daman,
kaltum tace kwarai Abba yayi musu bayani sun gamsu sunyi nadama sun bazama nemanki don sunemi gafararki basu sameki ba dole tasa suka hakura,
Madina ta mike da sauri ta ce tashi ki rakani gidan su Abba,
kaltum tace ki bari gobe ko anjima kici abinci tukunna har a gama,
Madina ta girgiza kai tace bazan iya kara awa guda ba banje naga Abba da 'yayana ba, kafin kaltum tace wani abu Madina ta suri akwatin kayanta ta fice tsakar gida don haka kaltum ta dubi goggo Fattu wacce har yanzuke kwance tana kallonsu taji tausayinta ya kamata sai ta dawo ta tsiyayi lemo a kofi ta daga kanta ta bata sannan ta juya mata kwanciyar kamar yadda ta saba yi mata kullum idan ta juyata dama in aka jima sai ajuya ta hagu kota zaunarda ita ta jingineta ajikin filo don dai taji dadi a jikin ta, cikin sanyin murya kaltum tayi mata magana tace goggo zan raka Madina sauri take yi nasan kina jin yunwa ba yadda zanyi dana baki abincin kafin mutafi amma zan fadawa mama ta baki saidai tace bakya ci dayawa idan bani na bakiba ki daure kici dayawa anjima zan dawo,
goggo fattu ta gyada kai tayi murmushi sannan itama kaltum taji dadi tayi dariya ta fice kuka kawai Goggo Fattu keyi tana nadamar abunda tayiwa yarinyannan sai gashi duk duniya babu mai kula da ita irin kaltum yanzu ko ancewa sofi tazo ta bata abinci saita ga dama zatazo, hidimar mijinta dana 'yayanta ne kawai agabanta,
hankalin sofi a tashe take tambayan kaltum yaya bakuwarki tace tafiya zatayi ko abinci bataci ba?
kaltum tace hankalinta yayi wajen' yayanta bazata iya zama taci abinci ba ki barta kawai zan rakata idan daddy ya barni ga Goggo can a daki tana jin yunwa kibata abinci saina dawo zanci,
sofi ta amsa da to saikun dawo, kaltum ta fita tana waige waige tana neman Madina can a jikin get ta hangota tana amsa tambayoyi malam saleh mai gadi,
kaltum ta wuce kai tsaye cikin gidan alh Adnan a babban falo ta tsaya tana rada sallah ma can yaji ya amsa bayan yan mintina ya fito daga daki a alama a kwance yake yana hutawa, dubanta yakeyi cike da
mamaki domin ya ganta da gyale harda jaka
arataye ya tambaya lafiya ina zakije da tsakar rana?
ta durkusa agabanshi ta sunkuyar dakai kasa tana magana cikin ladabi daddy Madina zan raka wajen 'yayanta da Abba tace ko minti daya bazata kara ba don hankalinta yayi gaba.
alh Adnan yayi daria yace daman tana son Abba da yaranta ta tsallake su tabarsu dakyar ta yarda ta dawo?
ke ma daman kina son Adnan kika ki biyo sa'adu a dadin rai kikace dan ADON DAWA zaki bi?
sai kaltum tayi sauri dukar dakai kasa har ya gama bayanansa bata kara hada ido dashi ba daga karshe yace kije ki duba danladi yakaiku a motarki ya jira ki ku dawo tare kafin la'asar, kaltum ta amsa da to mungode ta mike ta fice tabar alh Adnan da tunani iri iri,
kaltum da Madina a cikin mota gidan baya babu wacce take magana a cikinsu kowaccensu na tunani yadda za a yi arangama da juna har sun kama hanyar yankaba Madina tace kada muje gidan general tukur gara ku kaini gidan sumayyah tukur a koroa road saitace danladi koroa road zamuje ba yankaba dan haka saiya juya kan mota ya doshi can.
Madina tana nunamishi hanya har bakin get din gidan dr sumayyah anci sa a kuwa bata manta gidanba duk a akwai yan canje canje a unguwar ba ta manta lambar gidan ba da alama dai tana ciki saboda motoci har guda ukune a tsaye a farfagiyar gidan har kaltum ta fito daga mota madina na zaune cikin mota bata da niyyar fito wa, lafiya kika ki fitowa?
kaltum ta tambayi Madina.
madina ta girgiza kai tace saida nazo kofar gidannaji bazan iya shiga ba saina tuna marin da sumayyah tayimin da bakaken maganganun da ta fada min gara mu tafi basai mun shiga ba,
Kaltum sai kawai ta tura get ta shiga cikin farfajiyar gidan da sauri bata kula da kwalla kira da Madina take mata ba haka bata saurari dogayen horn dinda danladi ke matsa mata ba burinta kawai ta ganta a cikin gida, dai dai falon shiga taci karo da sumayyah da kaninta Abba suna fitowa da alama tafiya zaiyi don yana rike da makullin motarsa a hannunsa sukayi kicibus suka tsaya suna kallon juna aka rasa wanda zaiyi magana wakike nema yammata?
sumayyah ta tambayi kaltum, Abba ya
dubi sumayyah yace baki ganeta bane?
kaltum ce wacce ta kawo mana labarin inda Madina take,
sumayyah ta rike baki tace na tuna kaltum lafiya?
kaltum tayi murmushi tace lfy klau,
sumayyah tace ya ake ciki da zancen nemo Madina?
babanki yayi masa alkawari zai kawo masa Madina Abba ya damu yanzu haka zance ya zo muka yi ina tabashi hakuri kalli idanuwansa kiga yadda sukayi ja kwana yake bai yi bacci ba ku taimakemu...
Abba cikin gigita yace kaltum kada fa kice anje nemanta ba asameta ba?
kaltum ta girgiza kai tace kafin ince muku wani abu kuzo bakin get kuga wani abu ta juya da sauri ta fara tafiya yayinda cike da fargaba suke biye da ita a baya babu wanda a cikinsu yakawo abunda take shirin nuna musu ko a mafarki koda wasa basu taba zaton zasuga abunda ta nuna musu ba, kwatsam saiga Madina a zaune acikin moto tamkar a maparki bakin kowannensu ya kasa rufuwa,
sumayyah tukur ta kwalla kara ta fada cikin daga murya lah Madina kece?
AlhamduLillah Allah nagode maKa, suka rugo da sauri suka rungume juna yayinda hawayen farin cike yake zubowa daga idanuwanta su dukka hudu sai aka hau kallon kallo tsakanin
Abba da Madina saboda kallonta Abba har karkace kai yakeyi batareda ya iya mata magana ba,
(Sadin maa nace, "Allah Sarki So, Boss se yaya? ")
ta fashe da kuka tace Abba Abba kaine wannan ashe zansake ganinka a rayuwata?
saiya share hawaye yace Madina mai yasa kika tafi kika barmu?
meyasa baki zauna ba kikaje kika jefa rayuwarki cikin wahala?
sumayyah taja hannun Madina ciki da sauri
yayinda Abba da kaltum ke biye dasu a baya har babban falo suka zazzauna sumayyah ta jawo wayarta ta bugawa mummy hafsat tana dauka sumayyah ta fashe da kuka tace mummy ki taya mu murna ga Madina a gida na.
mummy hafsat ta dau dogon salati ta karasa da hamdala sannan tace abawa Madina kan wayan cikin farin ciki da fara a madina take gaishe da mummy hafsat sai data ji muryarta sannan ta yarda Madina ce,
ke kuwa madina me yayi zafi haka dazaki tafi kibarmu haba?
madina idan baki zauna danmuba ai saiki zauna don Abba mai sonki da kananan 'yayanki.
Sai hawaye ya surnano daga idanuwan madina tayi shiru kanta a sunkuye akasa batasan amsar da zata bata ba.
Abba ne ya taso da sauri ya mika mata hankici fari mai kamshi ya fada cikin lallausar murya madina goge hawayenki ki daina kuka
(WAI INA BOSS NE?)
Ta dago ido ta dubeshi saita yimasa lallausan murmushi ta gyada kai alamar naji sannan ta karba a nutse take sharce hawayen,
ya koma kujerar da yake zaune a saitinta ya kura mata ido ko kiftawa bayayi fuskarsa cikeda annuri kamar wanda aka yiwa albishir da gidan aljannah,
kaltum kuwa Abba kadai take kallo
tana mamakin irin wannan so dayakeyi wa madina duk da lalacewarda tayi,
SADIN MAA NA CE, AI SO BB WASA, YADDA NA KAMU DA SON JAMA'AR GIDANNAN
tayi baki ta rame ba kamar yadda take da kyau kamar da ba saita dinga ayyanawa a ranta dama itama a nemo mata mambelanta
😉 (yess bosss)
kamar yadda aka nemowa Abba madinarsa,
madina ta mikawa sumayyah waya tace mummy tace yanzu zatazo nan gidan aida ta bari naje na gaishesu ita da daddy,
dr sumayyah tace ai daddy baya kasar kinsan mummy bazata iya hakuri ba ta zo ta ganki ba yanzu saboda ta damu da rashinki kullum tazo cin abinci sai tace Allah sarki Madina ce mai dafa min abinci kala kala musamman idan ta tuna sakwararki wani lokaci sai dai kaga tana hawaye.
Madina ta girgiza kai tace rayuwa kenan yaya za ayi da kaddara idan Allah Ya kaddarawa bawanSa bai isa ya tsalleke ba cikin ikon Sa da yardarSa Ya dawo dani gida na ganku lafiya Shine abun godia.
daddadar muryarta da lafazanta masu ma'ana sai suka ratsa jijiyoyin jikinsa ya lumshe ido don dadi ya bude ido ya dubeta yaji kamar ya hadiyeta ya fada aransa inason madina Allah Ka yarje min in aureta Ka bani ikon riketa amana, (SADIN MAA NA CE, AMEEN ABBA)
sumayyah Tukur ta harareshi tace tashi ka tafi wancan falo ka zauna kabamu waje mu tattauna da aminiyata kazo ka tsura mana ido,
Abba yayi dariya yace sister sumayyah keya kamata kitashi ki bamu waje mu tattauna, sumayyah tace indai Madina ce sai ka gaji da ganinta karewa ma gidanka za a kaita kuje can ku karata, sai Abba yaji gabansa ya fadi kar Madina ta fada abunda zai daga masa hankali sai yaga ko kusa bata bijireba saima murmushi datayi kawai tace Allah ne mai yadda Ya so da bayinSa Allah Ya zaba mana mafi alkhairi.
sai hira sumayyah takewaya Madina tana fada mata irin mummunan hali da suka shiga a sana diyyar rashinta sannan sunyi nadama
da sukaji gaskiyar al amari cewar ba laifinta bane, ta kara da cewa hudubar shaidan ne ta shigesu suka manta da kaddara har suka zargeta kuma harda zugar makiya wadanda daman basa so su gansu tare, suka zuga su kuma suka tunzura suka yi mata abunda sukayi mata, hawaye ne kawai ke zubowa daga idanuwan Madina shi kuwa Abba babu abunda yafi daga masa hankali shi ne idan yaga tana kuka yace da 'yayarsa 6star sumayyah don Allah ki bar zancen nan kina sata kukafa... shigowar mummy hafsat da ' yayan madina shi ya katse hirar da suke yi murna da hayaniya ta gauraye falon, Madina ta tashi da sauri ta rumgumi mummy hafsat sannan ta rungumi 'ya yanta su dukka ukun suka kankame ta suna kuka don farin ciki da kyar sumayyah ta bambare su daga jikin uwarsu suka zauna,
mummy hafsat ta shiga lallashinsu domin har yanzu basu tsagaita da kukanba saiga Tasi'u ya shigo wur janjan yana fadin ina matata Madinar take?
fuskar Abba zaka kalla kaga yadda ya bata rai yana hararar Tasi'u yayinda kishi ya tashi,
(ta yadda nima tawa kishin ya tashi sabida jama'ar gidannan me albarka) Sady.
kayi mata sannu da zuwa ka tafi mana saboda nan gidan surakai ne ba gidanmu bane bai kamata ma aringa irin wadannan maganganuba,
Madina ta dago ta dubi Tasi'u sai taji ranta ya baci yana tsaye akanta yana ta surutai barkatai kamar tababbe itadai tunda ta gaisheshi bata kara bashi amsa ba,
yace Madina ke kuwa meyasa zaki zauna a can?
kuskurene mukayi kuma kowa ya gane Madina ki rike amana ki tuna nine mutum na farko da kika fara sani a arewa, nine mijinki uban 'yayanki na girmeki nafiki hankali nafiki sanin dunia haka kuwa ya kamata miji ya kasance tsakanin sa da matar sa,
Abba yasan habaici Tasi'u yake masa don haka saiya fusata yayi magana cikin fushi yace ina ganin bai kamata a fara yiwa madina irin wadannan zantuttukaba barkatai don yanzu ta zo ko hutawa batayi ba ita ya dace ta zabi wanda zata zauna dashi basai anzabar mata ba, saboda tafi kowa sanin abunda yafi dacewa da ita a rayuwarta, tasan halin wahala da takaicin data dandana a baya, zata yi hasashe wacce irin rayuwa za tayi nan gaba.
Tasi'u ya fusata ya juya ya dubi mummy hafsat yace mummy kinajin yaron nan ko idan manya suna magana saiya dinga tsoma baki alhali niban ambaci sunansa ba.
mummy hafsat tace tashi ka koma wancan falon karka sake magana, Abba ya mike ya fice daga gidan ma gaba daya,
Tasi'u dai ya lankwashe kafa yana ta magiya Madina ta dawo gidansa,
takaici yafi damun 'yayansu ma basu madinarba ma,
Abdul Malik ya fusata yace haba baba ka bari ta huta mana kafin ka sako wata magana a ina aka taba yin saki uku kuma a koma a zauna?
Tasi'u yace ai nasan tayi aure a sudan ko batayi ba ma zata iyadawowa ta tausayamin ina son ta da ba tanan a gidana sai duk ya mutu,
Madina ta girgiza kai tace Allah Ya saukake ni banyi aure acan ba,
sumayyah tace kinga babu zancen kome tunda saki ukune kuma batayi wani aurenba,
kema bayan kanin naki zakibi?
sumayyah haka zakimim?
Tasi'u ya pada ransa a bace,
mummy hafsat tace Tasi'u don Allah kabar
maganan a nan saikun hadu daga kai sai ita,
Madina duk hukuncinda ta yanke shikenan ai wannan ba maganar da za ayita bane agaban yara ba, sannan matar nan yanzu tazo ko wartsake gajiya batayi ba.
Tasi'u ya gyada kai yace hakane gaskiyane ai
shiyasa ake neman shawarar manya toni zan tafi Abdul Malik kuzo mutafi,
Abdul Malik ya girgiza kai yace ba yanzu zamu tafi ba, tare da mummy hafsat mu kazo daman,
Tasi'u yayi kasake don shima bayason tafiyan bai gaji da kallon abar kaunar sa madina ba duk da hautsinewar datayi batada
kyauwun nan nata irin na da amma duk da haka tafi sauran matansa tsari da kyan gani, yayi ajiyar zuciya yace to banyarda wani acikinku ya kwana ba ina gida ina jiranku kafin magruba mekukeci na baka na zuba kuda uwarku zata dawo gidanku kacokan ma ku kwana a dakin ta,
kowa ya zuba masa ido yana dubansa kamar wanda yake kallon tababbe a talabijan babu wanda ya iya magana har ya fice a farfajiyar gidan suka sake jiyo muryarsa yanayiwa Abba hayaniya duk dai akan Madina Allah cikin ikonSa sai Abba yaki kulashi ko kallo ma bai isheshiba yayi surutunsa ya gaji ya tafi.
Madina ta juya ta dubi 'yayanta tace me yake damun mahaifinku ne?
ya gamu da matsalar kwakwalwa ne bayan
tafiya ta?
Abdul Malik yayi dariya yace lafiyarsa Kalau mama,
madina ta dubi sumayya tace anya alamaran
Tasi'u akwai hankali a ciki kuwa?
sumayyah ta kwashe da dariya tace zafin so ne da tsananin kishi yake damunsa.
mummy hafsat ta tabe baki tace nadama ce hakkin zalunci suke tambayarsa ni wallahi har alamarin nan ya fara bani tsoro tun kafin ki dawo yake neman tashin hankalin balle yanzu da kika dawo bamu san wahalar da zai ballo mana ba.
Madina tayi tagumi tace Allah ma zai yayyafa wa abun ruwan sanyi Allah Ya sa ya gane gaskiya daga nan suka bar hirar Tasi'u,
Abba ya shigo aka dinga hira wasa da dariya yayinda sumayyah da masu aikinta suke can akicin suna ta hidimar dafa abinci iri iri suna fitowa da shi, ana jerawa a gabansu madina..
Jama'a gaskiya kishi na nima ya motsa PA, har yana neman sanya min hawan ruwa, kowa kullum se Dan Anty kawai ake ta ambato domin an pi son sa an pipita sa a kaina bayan nima ina yin ku kuma kun sani..
To yau nima ina son a so mu tare ko kuma a kawo karshen typing when!!!
Post na yau sadaukar wa ne gare ku masoyan Al-Hada Hada, daga taku har kullum me son nishadantar da ku SADIN MAA tare da Boss ina me muku posting DAN ANTY.
Allah Ya bar mu tare. 🙏🏽🙏🏽🙏🏽
.ADON DAWA 44
.
TRUE LIFE STORY
.
sumayyah ta kwashe da dariya tace zafin so ne da tsananin kishi yake damunsa.
mummy hafsat ta tabe baki tace nadama ce hakkin zalunci suke tambayarsa ni wallahi har alamarin nan ya fara bani tsoro tun kafin ki dawo yake neman tashin hankalin balle yanzu da kika dawo bamu san wahalar da zai ballo mana ba.
Madina tayi tagumi tace Allah ma zai yayyafa wa abun ruwan sanyi Allah Ya sa ya gane gaskiya daga nan suka bar hirar Tasi'u,
Abba ya shigo aka dinga hira wasa da dariya yayinda sumayyah da masu aikinta suke can akicin suna ta hidimar dafa abinci iri iri suna fitowa dashi ana jerawa a gabansu Madina
kaltum ta sami hira da ciye ciye saita manta da direba a waje ta kuma manta da gargadinda alh adnan yayi mata kada ta dade ta dawo da wuri,
bayan sunyi sallar magruba ne kaltum ta zaro
wayarta acikin jakarta saita ga 10 missed calls din danladi 5 missed din alh Adnan nan da nan sai hankalinta ya tashi sukaga tahau rawar jiki har ta kasa yafa gyalenta dai dai, kaltum lafiya saurin mekikeyi haka?
madina ta tambayeta.
na manta a gida ance kar in dade wayata a jaka bansan suna ta kirana ba shine nakeso naje gida da wuri, a tsaitsaye tayi masu sallama ta suri takalminta ta tafi bata ma tsaya ta saurari rakiyar madina keyi mata da rokon da takemata ta dawo gobe ba burinta
kawai ta ganta a cikin mota ta ganta acikin gida gaban alh adnan sannan tayi shirin amsa dogayen tambayoyinsa,
danladi ya dubeta da alama ransa ya baci ya fisge mota batareda wani daga cikinsu yayi
magana ba saida suka yi nisa kaltum tace danladi kayi hakuri na barka kanta jira bansan lokaci ya ja ba anata hira wayata a jaka ban ji kiranku ba.
dan ladi yace ai bani ne abun ji ba daddy ne kinga irin fadan da yake yimin a waya wai me yasa za mu dade haka nace kina cikin gidan yace in aika a kira ki narasa dan aike kuma nayi kiran wayar ki ba amsa niyanzu nasan duk fadan akaina zai kare,
sai kaltum ta dafe kirji tayi shiru tana karanto duk addu ar data gifto bakinta suna isa bakin get taji wata jijiya ta harba acikin kirjinta tamkar zuciyarta ce ta tsinke don fargaba daga yadda saleh ya bude get a fusace tasan yau ba lafiya saita fara kuka, suna tsayawa da mota saita fito a hankali tana mai tafiya a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa mata a ciki,
alh adnan ta tsinkayo a tsaye akan baranda ko zama ya gagare shi da alama fuskar nan ba annuri daga ita har danladi sai sunkuye sunkuye suke yi da kai kasa aka rasa wanda zai fara wucewa gaba yaje yayi bayani.
tsawa ya daka musu saisu dukka suka hargitse fargabar ta karu yace bazaku karaso
bane ina tsaye ina jiranku sai wata sanda kuke yi kamar wasu hawainiya?
nan da nan suka karaso gabansa suka durkusa suna jiran hukuncin za a yanke musu,
hakika danladi yayi gaskiya fadan dukka akansa ya kare an gargadeshi da kada yasake kaita anguwa da zasu kai magruba, kalma daya ya jefawa kaltum ita ya sallameta ta fada da sauri yace daga yau kada ki sake cemin zakije wajen Madina tunda nan ba a sudan kukeba dazaku kwana kuna hira,
ta shiga gida ta iske fadan sofi da saleh sunatayi mata fada ba kakkautawa sun nuna mata cewar da ta bata wa alh adnan rai gara ta bata musu rai, ta shiga daki a sanyaye ta iske an bawa goggo abinci da magani hartayi bacci sai dai tulin zannuwan kayantar da aka cire wa goggon yana gefe yana jiranta ta dawo ta wanke, saboda rashin kuzari a jikinta da tsoron fita tsakar gida don kada taci karo da mahaifinta ko alh adnan suyi mata wani fadan saita shige lungu ta kishingide tayi lamo tana tunani taji duk kasar ya isheta tamkar ta koma bur sudan wajen yan ADON DAWA ta zauna tareda mambela kamar yadda Madina ta dawo wajen abbanta,
saida ta tabbatar dare ya tsala sha biyu harda rabi kowa yayi barci sannan ta fito ta hau wanki ta gama tsaf ta shanya sannan ta dauro alwala tazo tayi sallar isha i ta dinga jero nafilfili tana ta addu ar Allah Ya zaba mata abun da yafi alkhairi a rayuwarta,.
Madina ta kasance agidan aminiyarta sumayyah tukur dakinta da bandakinta a ciki aka mallaka mata ita kadai cike da kayan more rayuwa babu abunda ta nema ta rasa ga 'ya yanta kusan kullum sai sun zo sun ganta ita ma ta gansu tayi hira dasu taji dadi,
sumayyah tukur a matsayinta na wayayyayi cikekkiyar yar boko tana matukar kokari wajen wayarwa da Madina kai domin duhun kai ne ya same ta a sudan bata san abubuwan da ake yayi ba yanzu da yadda ake tsara kwalliya, tafi gane ta saka atamfa ta kunshe kai da hijabi ko acikin dakine.
.
.
.
Post yau babu yawa ,patar zaku ci gaba da hakuri da mu.
Muna kuma dada niman addu'ar ku ga yayan mu Abdul Aziz Allah Ya tashi kapadar sa da ma sauran en uwa musulmai baki daya.
Ko wannen mu nan yana da bukatar sa, Allah Ya biyawa dukkanin mu bukatunsa da dukkan khairi, Ya karo lapiya da zaman lapiya masu albarka.
Ameen.
.
.
Saady Dan Anty.ADON DAWA 45
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina ta kasance agidan aminiyarta sumayyah tukur dakinta da bandakinta a ciki aka mallaka mata ita kadai cike da kayan more rayuwa babu abunda ta nema ta rasa ga 'ya yanta kusan kullum sai sun zo sun ganta ita ma ta gansu tayi hira dasu taji dadi,
sumayyah tukur a matsayinta na wayayyayi cikekkiyar yar boko tana matukar kokari wajen wayarwa da Madina kai domin duhun kai ne ya same ta a sudan bata san abubuwan da ake yayi ba yanzu da yadda ake tsara kwalliya, tafi gane ta saka atamfa ta kunshe kai da hijabi ko acikin dakine.
sumayyah kuwa tace bata isa ba dole saita zama yar gayu kamar yadda yammata suke gayu saboda saurayi zata aura, tun Madina na cijewa tana kin saka matsattsun dinkunan leshina da material har ta fara yadda tana sakawa,
sumayyah ta hana kitso saidai ta kai ta saloon a gyara gashin kafin watanni biyu sun cika Madina ta waye tamkar ba itaba, haka Abba yafi kowa jin dadi da ganin wannan sauyi yana kuma godiya wa yayarsa sumayyah da irin wannan taimako da tayi masa duk da yawanci kudi yake bawa sumayyah tayi mata duk hidimamomin nan ko madinar ma bata sani ba, kankace kwabo rayuwa ta dawo mata sabuwa tar ta fara mance himilin bakin cikin da ta shaka a baya, babu ranar da Abba baya zuwa wa Madina sai dai har yanzu Madina bata bari hiran soyayyah ya shiga tsakanin su ba duk hirarda za a yi a gaban sumayyah akeyi sai dai a tsakanin waya wato text masseges yana turo mata dadad'an kalamai masu shiga zuci sai tayi murmushi ta lumshe ido, amsar da take bashi bata wuce na gode,
godiyarda take mishi ta ishe shi farin ciki ko bata biyashi daddad'an kalamai ba ya lura Madina ta fara sakin jiki dashi, ta nuna a fili karara tana son shi,
koda yaushe Madina tana damun Abba ya kira alh Adnan a tambaye shi kaltum kuwa lafiya bata zuwa gashi ba tada lambarta?
sai Abba yace sunyi waya dashi yace kaltum tananan lafiya.
hankalin Madina bai kwantaba harsai data sa sumayyah takaita gidansu kaltum ranar alhamis da yammah ranar da suka tabbatar ba islamiyyah a karkashin wata katuwar bishiya a kwance a tabarma suka hangota a farfajiyar gidan, kai tsaye suka tunkaro ta tana daga kwance tana dubansu a zatonta bakin mummy salaha ne sukazo ne manta don bata dade da komawa Abuja ba, kaltum tace aranta ko su waye wadannan masu kudine da ilimi saboda kamshin turarenda ya daki hancinta tun basu karaso inda take ba, sallama suka mata cikin wata lallausar murya saita amsa sannan tayi firgigit ta tashi zaune ta dube su ta daka tsalle ta mike da sauri sannan ta rugumesu tana murna,
kaltum ta rike baki tana duban Madina tana mamakin irin wannan canjin data gani cikin dan kankanin lokaci, tace aunty Madina haka kika wani canjawa?
Madina da sumayyah suka kwashe da dariya, sumayyah tace kema kya pada,
Madina tace ke kaltum kya yi zancen canzawa kinga inda kika zama wata katuwa fara tas wa zaice kece yar yarinyar nan ta ADON DAWA.
kaltum tace aini na shekara uku da zuwa kefa bakifi watannin biyu ba, su dukka sukayi
dariya suka zazzauna suna hira sunajin dadin inuwar, zata kawo musu ruwan sha ma suka ce yanzu suka sha swan water da juice a mota don haka kaltum ta koma ta zauna,
sumayyah ta dubi kaltum tace gaskiya kin canza saboda jiya madina ta nunamin hotunanku a bur sudan tamkar an tono ku daga kabari wasu dakwal-dakwal daku yar 'kankanuwa dake amma yanzu dubi yadda kika girma kin zama cikekkeyar budurwa yar gayu maganar ma kamar turawa,
suka sake kwashewa da dariya su dukka , Madina tace ai kuwa da kyawun p
hoton nan muke gani kaltum dashi take kwana a karkashin pilo a jima ta zaro ta duba ta mayar,
sumayyah tace naga hotonta da wani zankadeden saurayinta mambela duk da a dawa yake yanada kyau da ace a birni ne wayayye dan boko da matan kasarnan sun dinga tuntube suna waiwayensa,
kaltum tayi murmushi yayinda idanuwanta suka cika da hawaye ta dubi Madina tace aunty mun kasa samun damar da zamu zauna muyi labari tun ranar nake tambayar ki ina mambela bakiban amsa ba .
Madina tace baki damu kiji labarinsa ba tuda baki sake dawowa ba tun ranar da nazo, haba kaltum nice fa madinarki?
inzo kasarnan saboda ku amma ki shareni?
kaltum ta girgiza kai tace ba haka bane, nayiwa daddy laifine a ranar saboda nakai dare shiyasa ya hanani fita ko ina kuma bani da numbarku shiyasa vankira va amma kullum ina tunaninki, bani labarin mambela bayan tafiyana koya manta da nine?
madina tayi murmushi tace yaya za ayi mambela ya manta dake a rayuwar sa?
kema baki manta dashi ba balleshi dayafi son ki?
kaltum ta gyara zama tace kinsan ya biyoni har Khartoum zamu tafi bur sudan kenan aka aiko aka tafi dani.
Madina tace kwarai ya gayamin amma na dauka karya yakeyi kokuma ince ya zautu ne kawai yakeyimin shirme,
Madina ta dinga bawa kaltum labarin halinda mambela ya shiga na damuwa a sanadiyar rashinta, da yadda ya daga musu hankali ya ce, duk sai sun bar kasarsu tunda kaltum ta tafi, sai dai daga baya ya hakura, ya yadda da kaddara. Daga karshe ta bata sakon da ya fada mata cewar ta fadawa kaltum har yanzu yana son ta ba zai dena ba har abada.
Kaltum ta rushe da kuka ta rungume madina, sai ita ma ta dinga hawaye. Sumayya ma ta tausaya sai ta girgiza kai ta dafa kafadar kaltum.
Ta ce, "yarinyar Mai zai hana ki kwantar da hankalinki, ki cire zuciyar ki daga kansa, ki zo ki gina sabuwar rayuwa da 'yan kasarku? Dube ki mai kyau ba mu da irinku da yawa a kasar nan masu suffar larabawa, fulanin asali ki zabi saurayi ki darje, ke ko gwamna ya ganki sai ya so ya aure ki. Ina ke ina dan ADON DAWA? "
Kaltum ta sharce hawaye ta ce, "zuwa na kasar nan na yi samari masu dimbin yawa, kuma attajiran gaske, manya da samari, amma bana kula kowa, mambela nake so, sai dai kash!!! Maganar nan da muke yi sati guda ke nan da a ka bayar da ni. "
Suka dafe kirji su dukka suka ce, "waye mijin? "
Kaltum ta yi murmushin karfin hali ta ce, "Alh. Adnan ne.".
Madina ta gyada kai ta ce, "yayi daidai, kin yi dace da miji na gari, mai tausayi wanda yasan darajar mutum. Kin yi dace da mijin da yake matukar son ki ba don komai ba, sai don Allah, kamar ni da Abba, tabbas mutum ne mai kirki, kun dace, Allah Ya barku tare ".
Madina ta dafa kafadar kaltum ta ce, "me yasa kike kuka alhali kin dade da sanin yana son ki, ke ma kuma kina son sani? Mambela yana son ki, amma kin san auren ku, abu ne mai wuya, saboda kun yi hannun riga wajen dabi'unku, yarenku da kasar ku, ba a san asalinsa ba, ba a san inda ya fito ba, zai yi wuya a yarje masa ya aure ki".
Kaltum tace, "nasan da haka, amma ni ina son mambela, ina tsoron matar Alh. Adnan mummy salaha, takura min zata yi ni da iyaye na".
Madina tace alh Adnan bazai bari ta cuce ki ba itama auranta yayi kamar yanda ya auroki, babu abunda zata iya yi miki, yaya akayima ya furta zai aure ki?
kaltum tace bai fada ba, babane yace ya bashi ni, da farko bai amsa ba sai acikin wannan satin yan uwan baba suka sameshi a zangon Daura suka sake mishi magana sannan ya yarda , yanzu jira ake jarabawar jamb dinda nayi ya pito inga inda suka bani domin nacika U.B.K Da gwagwalada Abuja, idan kano suka bani sai ya gina min gida a kano ayi bikin idan kuma Abuja ne sai akai ni Abuja.
madina tace babu komai kada ki damu Allah Ya sa haka shine mafi alkhairi, kaltum na lura duk hankalinki atashe yake har kin rame ba kamar sanda na ganki ba kwanaki, alh Adnan din naki kike ki?
haba kaltum idan kikayi masa haka baki kyauta masa ba, suma iyayanki sunga babu irin godiyar da zasu mishi ne illa subashi ke domin yayi dawainiya dake kowa yasan yana son ki.
kaltum ta matse hawaye tace ba kiyayyarsa bace ta sani damuwa ba, nauyin sa da kunyarsa nakeji tamkar babana na dauke shi, ramewa da kiga nayi bai wuce Zafin mutuwar goggo fattu ba da har yanzu take damuna.
madina ta zabura ta dafe kirji tace InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu goggo fattu ta rasu?
kaltum ta matse hawaye tace yau sati biyu kenan a zangon daura akayi jana izarta bamu dade da dawowa ba, ai acan yan uwan baba suka hadu sukayiwa alh Adnan maganar auren mu dayaje gaisuwa daga baya ma matarsa taje dana gaishe ta bata amsa ba, shine yasa nashiga damuwa nasan halin kishinta zata iya babbakawa kishiya wuta.
madina da sumayya suka cigaba da bata shawara da nasihohi masu kwantar da hankali sannan sukace ta rakasu wajen iyayanta don su musu gaisuwa,
Madina ta karbi numbar wayar alh Adnan tace idan taje gida zata kirashi tamishi gaisuwa sannan su tattauna don taji ra'ayinsa akan maganar auren.
a haka suka rabu kaltum ta raka su har wajen get inda suka ajiye motarsu suka shiga suka tafi ita kuma ta dawo gida.
tafiyarsu Madina da kwana uku alh Adnan ya kirawo kaltum a waya, cikin rawar murya da fargaba ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a yace gobe ki shirya danladi yakaiki gidansu Madina ki yini, da yamma ya koma ya dauko ki,
ta amsa da to na gode, bayan yakashe wayar sai mamaki ya rufe ta nan da nan takira Madina tana tambayarta yadda sukayi da alh Adnan don yanzu ya kirata yace gobe taje su yini,
madina tayi dariya tace dadin baki na masa na nuna ina goyon bayan aurenku dari bisa dari shiyasa yaji dadi,
kaltum tayi dariya kawai ta kashe waya.
washe gari da wuri kaltum ta shirya ta caba ado da wata hadaddiyar shadda gezna kalan jan duhu wato maroon colour wacce akama surfani da brown din zare, riga da siket da dankwali, ta saka takalmi da gyale kalan brown, tayiwa iyayenta bayananin abunda alh Adnan ya umurceta tayi sai sukaji farin ciki ya kamasu tunda har akasamu ya fara yi mata waya a yanzu,
ta kame a bayan motar danladi yaja bai tsaya a ko inaba sai kofar gidan Doc sumayyah Tukur,
kamar yanda ta umurceshi ta sake umurtarshi daya tafi ya dawo da la'asar, ta shiga ciki kai tsaye ta iskesu a falo su uku ne kadai Madina , sumayyah da maigidanta Doc bashir, sunata hira babu abunda yake damunsu arayuwa sai dariya suke kyalkyalawa, suna ganin kaltum sai suka hau murna ta durgusa cikin fara'a ta gaishesu sannan ta sami kujera ta zauna.
Dr bashir yace af dama wannan ce kaltum matar mambela dan ADON DAWA?
su dukka suka tuntsire da dariya.
sumayyah ta harareshi kaji har sunan ADON DAWA ya rike, kamar dashi akaje bur sudan?
shigowar Abba da kaninsa Anas ita ta katse hirarsu aka hau gaggaisawa,
kai tsaye Abba ya wuce gaban Madina ya ajiye himilin ledoji a gaban ta,
ta dubeshi tayi murmushi ta fada cikin sanyanyar murya mai cike da sakon so da kauna tace Abba bazaka yarda da maganarda nake gayamaka bako?
so kake muyi pada kenan?
nace saye sayen nan naka yayi yawa ka dinga hutawa kaki jiko?
sumayyah Tukur tace a'a mu munaso inke bakya so, da bakya nan ai bai sayo mana ba, kudi ne dashi, me anfanin kudin in ba aci ba?
Madina ta bude ledojin daya kayan itatuwa ne lemo ayaba da abarba daya ledar kuma tuffa ce da inibi, daya ledar kuma mayukan shafawane da turarurruka sai wani dan karamin kati (greeting cart)mai dauke da sakon so da kauna, katin kadai madina ta dauka ta karanta ta kalli Abba tayi murmushi ta ajiye a gefenta shima irin murmushin ya mayar mata.
sumayyah Tukur ta dubi Anas tace kaga ka fita daga idona na rufe zan tona maka asiri idan baka daina turamin sako cikin wayata ba,
sai kowa ya dubesu,
yace yi hakuri 6star ki rufamin asiri, Abba yace sako wani iri kuma?
dr bashir yace eh gaskiya a tona wannan sirrin kowa yaji, ya duk muna zazzaune ka dinga tura mata sako don gulma?
sumayyah tace ya dade yanason kaltum wai ce min yayi in kira masa ita wancan falon su gaisa wai in fada mata yana sonta.
su dukka suka kwashe da dariya.
kaltum taji kunya saita sunkuyarda kanta kasa bata sake dagowa ta dubi Anas ba, madina tace wallahi kuwa kun dace saidai karigada ka makara anbayar da ita da sai na tsaya maka kanina.
Anas yaji hankalinsa ya tashi yace ai tunda ba ariga an daura ba zan iya shiga filin dagar adama dani mai rabo ya dauka.
sumayyah tace kadama ka fara shiga filin dagarnan don dakai zata kife wanda za aje neman aurenta wajenshi shine zai aure ta.
ban fahimce kiba?
Abba ya tambayi yayar sa.
madina tace alh Adnan zata aura nan da yan watan ni,
Abba ya gyada kai yace lallekam babu mai jadashi yaro karma ka shiga bakin rijiya don ba wajen wasan yara bane, nifa na dauka yayantane da farko sai nace ko babanta ne ashe shi ya riketa yanzu zai aureta ko sun dace yana da matukar kirki.
Anas ya fice daga gidan, kallo daya zakayi masa ka tabbatar baiji dadin maganarnan ba,
madina taja kaltum dakinta a inda ta dinga nuna mata abubuwan alkhairin da ta samu dawowarta nan, dinkuna kala kala wadanda Abba yayi mata ta nuna mata wasu akwatuna masu kyau har guda hudu saiti tace kayan lefenta ne Abba ya fara hadawa, auren nan da watanni uku, a Abuja zasu zauna sbd acan yasami sabon aiki shine lauyan babban bankin nan CBN, Madina ta dubi kaltum ta fada cikeda fara a tace kaltum ki duba kiga yadda Allah Ya canza mana rayuwa cikin dan kankanin lokaci, shi yasa duk halin da musulmi ya tsinci kansa ya godewa Allah, jarabawa ne idan Allah Ya tashi sakayyah sai ya juye maka dadin da baka taba zatonsa ba, banda Allah wazai yi mana irin wannan kyautar?
kiduba kiga yadda ni dake muka canza kada kiyi bakin ciki da duk yadda kika tsinci rayuwarki, alh Adnan alkhairine da rayuwarki, ko ba a fada miki ba nasan mambela ma mai kaunarki ne Allah cikin ikonSa da hikimarSa Ya raba ku, ki godewa Allah a duk halinda kika tsinci kanki.
kaltum ta gyada kai tace hakane aunty Madina nasan da haka ina addu'a kuma zanci gaba da addu'a har karshen rayuwa ta.
.
.
Muna masu godiya da addu'ar ku, Allah Ya saka da alkhairi.
.
.
Saady Dan Anty 👫ADON DAWA P 46
LITTAFI NA HUDU
TRUE LIFE STORY
.
nasan mambela ma mai kaunar kine, Allah cikin ikonSa da hikimarSa Ya raba ku, ki godewa Allah a duk halinda kika tsinci kanki.
kaltum ta gyada kai tace hakane aunty Madina na san haka ina addu'a kuma zancigaba da addu a har karshen rayuwata, na godewa Allah kuma bazan taba raina abunda Ya bani ba.
Madina tace Allah Ya yi miki albarka idan kika rike wannan bazaki taba danasani ba a rayuwar ki, kiyi addu a kibarwa Allah zabi Shine abunda na rike tuntuni kuma bana nadama, ta bude wata katuwar leda ta zazzabo mayuka, janbaki da hoda turarurruka da atamfa ta zuba ta mikawa kaltuma tace gashinan na baki kije kitayin kwalliya naga kina son ado.
kaltum ta rike baki tace haba aunty kin juyemin kusan dukka ai yayi yawa ki rage nima duk karshen wata alh Adnan yana bani kudi inje well care super market in sayo kayan kwalliya.
Madina tace ai ina da su dayawa keda Shahida na rabawa wannan, bakiji ina yiwa Abba kashedi ba?
cewar ya isheni haka, shiga gowa fita goma sai yayi min sayayyah bansan irin kyawun da yakeso inyi ba koso yake in koma indiya don kyau oho.
kaltum tayi murmushi tace Abba yana son ki ko minti daya kayi dashi zaka gane hakan,
Madina tace kwarai kuwa nasan dahaka tuntuni daddy Tukur ma yasha kirana har falonsa ya yita bani hakuri a bisa wulakancinda sukayi min a rashin sani sannan ya rokeni in saki jiki in kwantar da hankalina inyarda in auri Abba tunda ya tubure duk duniya babu wacce yakeso saini, kuma ba haramun bane raya sunnah ne saboda Manzon Allah (s a w)Ya auri nana Khadija (R.A)a bazawara kuma ta girmeshi ya
nuna min kuskuren da nayi a baya dana hana Abba ya bayyana musu halinda yake ciki, ai ba zasu hana ba saboda sun yarda da tarbiyyata sunsan bazan cuci dansu ba, daga karshe ya roke ni da rike dan su amana fiye da yadda na rike Tasi'u, inso Abba kamar yanda duniya ta shaida Abba yana so na, irin wadan nan nasihohi mahaifinsa yake min aduk lokacin da muka hadu.
kuma duk bayan kwana biyu ina zuwa gidansu Abba inyiwa mummy hafsat duk abunda takeso kamar share-share da girke-girke,
nida Tasi'u kuwa general tukur yayi mana katangar karfe haka tsakaninsa da Abba, saboda ya fara takurawa rayuwarsa koda yaushe saiya tari Abba a hanyah yanayi masa hayania harda cewa sai yaga bayansa sannan nima ya dinga bina kenan har tsakar falon mummy hafsat wai ni matarsa ce, shine ran daddy tukur ya baci allurar soja ta tashi yasa sojojin nan suka wurgo shi waje sannan muka sami lafiya.
kaltum tayi ajiyar zuciya tace har ya bani tausayi ma daman haka dunia take hakkin wani masifa ne idan ka cuce mutum tun a duniya Allah Ya ke fara nuna sakayyah dubi ni
da goggo fattu fa saida Allah ya kaskantar da ita kafin ta bar dunia, tayi nadama hade da danasani ai ina tsoron daukar hakkin wani.
madina tace haka alkhairi yake idan ka gina alkhairi zaka girbe shi sbd bayan tafiyata sanda gaskiya ya bayyana sai yan anguwa suka para tausayin 'yayana su kayi ta kyautata musu musamman ma shahida ko abinci aka hana ta agidansu sai makwabta su kirata su bata suce Madina muma ta taimakemu alokacinda bamuda shi, su bata sutura suce madina ta cire kayan jikinta ta bamu idan mukayi sha'awar kayan, kin gani da abun tsiya na shuka alocinda makwabta dana tsallake na tafi na bar 'yayana sai an zageni a gabansu kuma baza ataimakesu va.
kaltum bata dawo daga wajen Madina ba harsaida ta sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda nasihohi da ta dinga yi mata, data isa gida da farin ciki kaltum ta nunawa mahaifiyarta abubuwan alkhairan da Madina ta bata sannan ta kira alh Adnan a waya ta shaida masa ta dawo.
sai yayi mamaki da yaji muryarta radau tana walwala harma da kirkiro masa hira take sai ya tabbatar da Madina tayi masa gini mai karko a zuciyar kaltum, don haka ya sake tabbatarwa Madina macece mai nutsuwa da sanin ya kamata.
akai akai kaltum na ziyartar madina haka itama madina tanasa sumayyah ko abba su kawo wajen kaltum su dade suna tautaunawa da neman shawarwari akan abunda ya shafi aurensu daci gaban rayuwarsu gaba daya har wata rana madina tazo da daddare ita da abba koba a fada maka kaga ango da amarya masu matukar kaunar juna sun burge kaltum matuka yanda taga suna tafiya suna hira wasa da dariya saisu ka mika mata katinan bikin su,
daya na walima daya daya kuwa sunan alh Adnan dana malam saleh ne shine na daurin aure,
farin ciki ya lullube kaltum bata san lokacinda tafashe da kuka ba ta rungume Madina sai ita ma ta fara kuka irin wannan hawayen farin
cikin ne ya surnanowa abba daman ance kuka iri irine na bakin ciki shine mai radadin fita na farin ciki kuwa sanyi kalau zai fito babu zafi idan ya fito shar sai a goge a yi dariya a tafa.
.
RANAR DAURIN AURE
asabar ce ranar daurin auren barister Abba Tukur da Madina a farfajiyar gidan general tukur shine uban amarya kuma daman Uban angone don haka tuwona maina kenan.
kamar yanda kowa yasani babban goro sai magogin karfe ba kasafai zakaga jifgin talakawa ba a al'amuran attajirai kamar yadda ganeral tukur da iyalansa suke da matsayi abokansu ma masu matsayine, danginsu masu kudi ne, abokan aikinsu daga ma aikatan daban-daban sun hallara ma'ana manyan sojoji sunzo don general tukur haka manya furofesoshi sunzo saboda da barista hafsat tukur jami'a daban-daban, sannan manyan likitoci daga manyan asibitoci daban daban sun hallara saboda Doc sumayyah da maigidanta Doc Bashir,
injiniyoyi ba abarsu abaya ba saboda engr Anas, sai dimbun dalibai daga jami'ar unguwar sun hallara,
saboda Madina don kirkinta alh Adnan da malam saleh suma suna daga gaba gaba, kusada ango maroka da makada suna nasu aikin yan jarida da hotuna da bidiyo suma sai dauka suke kowa yana fadar albarcin bakinsa na alkhairi saboda farin ciki.
masu iya magana na cewa da dai dan wani tarkataccen wani, a lokacinda dubbannen jama a suke cikin shagalin cin alewa da goro bayaga lemuka da abinci iri iri a wajen daurin auren Abba da Madina.
shikuwa agidan Tasi'u a cikin tashin hankali suke saboda Tasi'u nacikin gidansa hankalinsa inyayi miliyan ya tashi haka ya tashi hankalin iyalansa saboda rike kai yayi yana ihu yayinda ya dinga faduwa kasa fuk sai an yayyafa masa ruwa sannan ya farfado, 'ya yan madina su dukka uku basu iya halattar wajen daurin auren ba suna ceto ran mahaifinsu haka ma matansa tun suna ganin shirme yake don suji haushi yakeyi har suka fara tsorata suka tabbatar ba wasa yakeyi ba da gaskene, suka rugo suka kamasa, suka dauka a surutunsa baya fasa tsinewa sa'ada wacce itace tayi sanadiyyar rabuwarsa da Madina, ya dau alwashin Madina na tarewa agidan Abba itakuma zata tare a gidansu ma'ana zai saketa, rirrikeshi sukeyi hakuri ake bashi shikuma tamkar dalmar wuta ake dana
masa a kahon zuci musamman dayaji an mika sadaki lakadan dubu hamsin aka shafa fatiha, jama'a sun shaida Abba ya zama mijin Madina saiyaji tamkar ya cire kayansa ya danna waje da gudu aka rirrike shi.
Madina dai batasan abunda yake faruwa va tana can agidan sumayyah itada mata yan uwanta suna ta shagalinsu don kaltum da jakar kayanta tazo sai ta shafe kwanaki uku cur rakiyar amarya har Abuja za aje da ita,
alh Adnan ya yarje mata, yinin biki tayi kyau walima tayi kyau an ragargaza wa azi da karatun alkur ani haka ango da abokansa sunyi reception hadadde amarya da ango sun caba ado sunyi kyau matuka ko makiyansu vaza su kushesu ba, komai ya wadata babu yunwa babu kishir ruwa an bubbuga abubuwa daban daban aka rarrabawa wadanda suka halacci bikin da hotunan amarya da ango a kalandu da memo, t shirt hankacib, barguna, atamfofi , bokitin roba agogo da dai sauran su.
amarya da manyan aminanta a jirgi suka tafi
Abuja sauran jama'arne suka tapi a motoci,
kaltum na makale a kugun amarya itada shahida don haka sun sami tafiya a jirgi
koma dai ame sukaje kowa dai ya isa lafiya kuma kowa ya dire akatafaren gidan amarya da yake unguwar maitama, gida ne matsanancin girma dauke da falo biyu kicin daya dining area, dakuna uku kowanne da bandakinsa aciki ga farfajiya mai fadi inda zai ci motoci uku sai boys quaters daga bayan gidan,
ba girman gidan bane keruwar gidan, tsara shi shine keruwar gida saboda gidan nan ya
tsaru da ga ginin har kayan ciki anzuba kayan
kalarda ya dace komai nagidan ruwan zuma ne brown, yadda kowa yaga gidan nan haka ita ma Madina saida aka kaita tagani koda wasa Abba bai shawarce taba ko a labari bata san sanda ya gina ba balle lokacinda zai zuba kayan ciki babu sisinta ya zuba mata komai sabo,
hawaye kawai take zubarwa na farin ciki saitayita godewa Allah a zuciyarta.
farin cikinda kaltum da shahida suke yi har yafi na kowa saikace su aka mallakawa gidan,
kowa yana san barka musamman sumayyah tayiwa Madina murna tayi mata fadan zama lafiya,
kwanaki biyu akayi cur a gidan amarya aka kalkalewa amarya da ango gidansu tas tas sannan aka tapi aka barsu su kadai,
Abba yace saboda zaman kadaici da kuma girman gidan zai samo mata masu aiki biyu babbar mace daya da yarinya karama donsu tayata aiki,
Madina tace Allah Ya sauwake ita bata bukatar yan aiki zatayi aikin ta dakanta haka bazai hanata ta kula da mijinta ba kuma,
dole tasa Abba ya hakura da zancen yan aiki saidai koda yaushe suna rigima idan yazo tayata aiki, shi yana tausayinta wai aikin gida yayi mata yawa ita tana tausayinsa bataso yasha wahala tafi so ya koma ya zauna ta dafa ta kawo masa yaci, daga karshe suka tsayarda shawara guda daya cewar duk sanda zata shiga kicin Abba zai jawo kujerarsa ya zauna yana tayata hira amma bazai tayata aiki ba, saboda bayaso tayi nisa dashi dole ce take fita dashi wajen aiki daga ya taso daga aiki baya zarcewa ko ina sai gida wajen Madina, haka ita ma batajin dadin zuciyarta idan Abba ya fita bata samun nitsuwa har saiya dawo gareta don haka Abba ya dawo dan lele ko jariri sai haka, tabbas hasashensa yazama gaskiya ba dukka mace vane zata iya biyayyar da Madina takeyi ba musamman ma yanzu data kara wayewa a wajen sumayyah ta kara, kozuwa da wahalar rayuwa ta sake tabbatar wa Abba mai kaunarta ne duk duniya babu mai kaunarta fiye dashi, ta sake tuna amanarsa da mahaifansa suka bata ta dinga tuna irin hatsari da tuggun da Tasi'u ya dinga jeho masa don ya tsoratar dashi yafasa aurenta amma baiyi ko gezauba, uwa uba irin dukiyarsa daya kashe don ya dadadawa rayuwarta yana kan kashe mata ma don duk abunda ya mallaka baya kyashin bata har sai tace ya isa haka,
bayan aurensu da watanni biyu ranar litinin da misalin karfe goma sha daya na safe Madina na kishingide akan doguwar kujerar dake tsakiyar falonta tana rike da tsadaddiyar wayar ta wacce aka yi mata lakabi da Black Berry tana turawa abun kaunarta Abba sakon soyayya da tsantsar bege sai taga wata lamba ta shigo, ma'ana ana kiranta saidai tana matukar mamakin ganin sunan mai kiran dai dai wannan lokaci tayi firgigit ta tashi zaune ta amsa cike da fargaba ta fada cikin girmamawa, alh Adnan ina kwana?
ya amsa cike da fara a, yace ina mai gidan ki tun dazu ina kiransa vai dauka ba.?
Madina tace yana wajen aiki ko baya tare da wayar akusa dashi nima dai munyi awa rabonda muyi magana.
alh Adnan yace ba mamaki to, don Allah idan yakira kice masa yayi kokari ya kawo ki ofis dina ina neman ki.
ta dafe kirji tace alh lafiya?
badai matsala dai aka samu da kaltum ba?
alh Adnan yace karki damu va matsala vane sai alkhairi.
cikin sanyi jiki tace to shikenan zan fada masa zamu zo insha Allah.
yace to daga nan zuwa karfe uku na yamma ina ofis idan ya wuce uku to saidai kusameni a gida.
suna ajiye wayar sai Abba ya kira tayi caraf ta dauka cikin laulausar murya tace my heart inaka shigane alh adnan yayita kira va ka amsa ba?
Abba yayi murmushi yace my life Wallahi aikine yayi yawa yanzu na dauko wayar naga missed calls dayawa hardana alh Adnan din nace sai na kira gimbiya ta tukunna zankirawo su daya vayan daya, lafiya yake nemana?
Madina ta lumshe ido tace to dai da baisameka ba niyakira yace infada maka ka kai ni ofishinsa yana nemanmu kaga nan kiran mahimmanci ne kuma da gaggawa.
Abba yace to Allah Ya sa alkhairine bari inkirawo shi inji, ki shirya zanzo yanzu na daukeki muje.
ba ayi awa ba saiga Abba a gida ya tarar da Madina ta shirya tsaf a zaune a falo tana jiransa, ya dube ta yayi murmushi yace my love kinyi kyau,
ta lumshe ido tace na gode ai kai daman konayi wanka ko ban yi kwalliya ba sai kace nayi kyau,
yace tashi mu tafi na kira shi yace mu kwantar da hankalinmu ba matsala bace bazai wuce dai zancensa da kaltum bane, ya kama hanun ta ya jata suka pita, ya bude mata murpin mota ta shiga sannan ya xaga Shima ya shiga suka pice.
basu sha wahala ba wajen hawa suna shiga suka iskeshi a luntsumemiyar kujera yana juyi yayin da yake ta rubuce rubuce akan wasu file yana ganinsu sai yayi dariya yana nuna musu kujeru,
suka zauna bayan sun gaisa sai ya jawo wayarsa ya kira wata lamba cikin harshen turanci yake magana yace kazo ofishina gasu sun zo.
Madina ta kalli Abba shima ya dube ta cike da mamaki gaba daya suka kalli alh adnan sai yayi murmushi yace kada ku damu so nake mutumin yashigo Ya tabbatar min kuyake nufi sai inyi muku bayani, idan kuma baku bane shi kenan.
Madina ta gyara zama tadafe kirji tace alh lafiya dai ko waye mutumin yasan mune me muka yi masa?
Abba ya dafa kafadarta ya fada cikin laulausar murya my love ki kwantar da hankalinki kinsan fa kina da hawan jini banaso ki dinga yawan damuwa meyasa kike firgita alhali kinsan babu wanda kika yiwa laifi kuma ke kike yiwa jama'a nasiha su yarda da kaddara....
kafin ya rufe bakinsa aka turo kofa aka shigo, gaba dayansu su dukka suka dago ido suna duban mai shigowa,
idonsa ya dira akan Madina itama ta dubeshi saitayi wuf ta mike tsaye kamar an zabureta ta fada cikin yare wanda yayi kama da inyamuranci sai shi ma ya mayar mata da amsa sai suka ruga da sauri suka rungumi juna suna rusa kuka.
hankalin Abba ya tashi ya fada cike da damuwa Madina lafiya kikaje kika rungumi kato?
Kin san shi ne?
kuka ya hanata bayani shi kuwa daman mutumin ko hausa bayaji balle ya fahince abunda Abba ke fada,
alh Adnan ne ya hauyiwa Abba bayani yace wannan mutumin da kake gani mun dade muna harkar karuwar arziki tare daga enugu yake, muna safarar man fetur ne shekara da shekaru muna abota, mutum ne mai amana har Allah Ya sa ya auri musulma muka masa nasiha ya musulunta, sunan sa ada innamani yanzu kuwa Abdullahi, dazu yazo ofishina sai kawai yayi ido hudu da kalandarku ta bikin aurenku gata can sai naga yatafi da sauri ya fisgo yana kallo har hannayensa yana rawa na tambayeshi lafiya dai ko?
saiyace tayi masa kama da kanwarsa data bata shekara da shekaru yana neman ta daman ance masa tana kasar hausa ta auri musulmi .to shine na kira wayarku alokacin babu tantama nasan Madina ce yar uwarsa, tunda na sami labarin tarihin rayuwarta ashe kuwa itace din, shi ne yasa kagasun rungumi juna suna kukan murna .
Allahu akbar Allah abun godiya kalmar da Abba yake ambato kenan alokacin da alh Adnan yake bawa Abba labarin abunda yake faruwa ita ma Madina cikin yarensu ta bawa yayanta tarihin rayuwar ta sannan ta gabatarda mai gidanta Abba,
yayanta ya rumgume Abba yana farin ciki sai godiya yake yi masa nandai suka dunguma suka tafi gidan Madina don yaga muhallinta shima kuma ashe matansa biyu daya ba musulma ba ce tana enugu amaryar ce musulma beyarabiyace tana nan cikin Abuja a maitama, basu da nisa ma,
rayuwa ta dawowa Madina sabo fil mai tafe da tsagwaron farin ciki tana kuka tana bawa yayanta tarihin yadda Abba ya tarki tafiya enugu nemansa saiya yi hatsari a hanya saigashi cikin ruwan sanyi Allah Ya hadasu.
Kun ga yadda na yiwa Abba Mutumci na tausayawa rayuwar sa, gaskiya ya matukar bani tausayi, shi yasa na roki madina ta da ta yarda ta aure shi kawai, ni na rike kaltum. Lol
.
.
Saady Dan Anty.ADON DAWA 47
.
TRUE LIFE STORY
.
rayuwa ta dawowa Madina sabo fil mai tafe da tsagwaron farin ciki tana kuka tana bawa yayanta tarihin yadda Abba ya tarki tafiya enugu nemansa saiya yi hatsari a hanya saigashi cikin ruwan sanyi Allah Ya hadasu,
tun sanda Madina tahadu da dan uwan ta bata ta taba kwana ta yini ba batare data kira shi awaya taji muryarsa ba, haka shima bai taba kwana 2 baizo ya ganta ba indai yana gari haka yake ta ambulo mata dukiya domin mutum ne mai dinbun dukiya da kyaututtuka da ya kamata yayiwa iyayensa da danginsa sai yake jifgewa Madina domin ita kadai ta rege masa, ita yake gani yaji dadi, yafita shiga damuwa daya rasa ta, ya fita wahalar neman inda take yafita dauriyar addu ar Allah Ya sa ya ganta.
ta dinga buga waya kano tana shaidawa masoyanta cewar taga yayanta innamani kuma babban farin cikinta ya musulunta shima,
farin ciki ya rufe kaltum, sumayya, mummy Hafsat, general tukur da 'yayana,
har kano tazo dashi yaga 'yayanta da iyayen Abba,
yayi musu godiya Madina ta nunawa su sumayyah sabuwar motar da ya bata, lalle Allah mai kyauta duniya da lahira mai yanta bawa Ya azurta talaka a dare daya babu abun da madina take yi sai sallah da gode wa Allah babu abunda tanema ta rasa a duniya yanzu sai dai ta nemi lahirarta, ta sami dan uwa da miji masu sonta haka ta sami arziki marar iyaka, tanaci tana wadata 'yayanta tana kyautatawa masu kudi badan basu dashi ba sannan tana taimakon mabukata saboda tasan illar talauci da yunwa.
Madina ce ke zaune cikin falonta na kano bangarensu a cikin gidan surukanta aka fitar musu tana karatun kur ani Abba na gefe yana
sauraronta har lumshe ido yake saboda daddadar kira'arta sai wayarsa ta hau ruri Madina ta tsaya da karatun ta dube shi ta lumshe ido tace amsa wayar sai inci gaba.
yace alh Adnan ne harta katse ma kafin in amsa,
Madina tace kirashi saboda Kiran wayar alh Adnan alkhairine mutum ne mai hada khairan baya sharri,
Abba ya kira lambar nan da nan ya sameshi bayan sun gaisa saiyace ina Madina?
inason ganinku.
Abba ya gyara zama yace ga madinar a kusa dani sai Abba ya mikawa Madina kan wayar cikin fara a da ladabi ta gaishe shi yace da ita kuna gidane anan gida a Abuja?
madina tace a'a muna kano shekaranjiya muka zo sai mun yi sati biyu zamu koma Abba mai gidanane yake hutu sai.
alh Adnan yace yauwa daman nafiso mu hadu a Kano nima zan shigo kano in anjima dan haka bayan magruba kuzo ku sameni agidana zamuyi wata magana.
sai madina ta tambaya cike da fargaba alh badai wata matsala bace dai ko?
ka fara fadamin don hankalina ya kwanta.
alh adnan yayi dariya yace alkhairi ne Madina wannan karon dai maganata ce da kaltum.
madina tayi dariya tace AlhamduLillahi haka nakeso inji saboda har na fara damuwa ina tambayar zuciyata ko lafiya har yanzu bakayi magana ba gashi harta sami admission ta fara zuwa makarantar BUK.
yace ai maganar ta taso gadan-gadan yau dai komai zai bayyana.
Madina tace Allah Ya tabbatar sai munzo na gode, farin ciki ya rufe madina suka dade suna tautaunawa da Abba har saida ta daidaici yamma tayi lokacin dora abinci dare yayi sannan ta tashi ta shiga bangaren mummy hafsat ta durgusa ta gaishe ta ta tambaya cike da ladabi mezan dafa miki yau mummy?
mummy hafsat tayi dariya tace 'yata Madina ki dafa manan duk abunda da kika ga yadace da tsofaffi,
su dukka suka tunsure da daria, madina tace to shikenan abinci kala goma zanyi muku keda daddy duk sai kun cinye.
karfe takwas nadare afalon alh Adnan tayiwa su Madina, ga alh Adnan ga kaltum azaune akan kafet ga Abba da madinarsa akusa dashi akan kujera daya gefe kuma sofi ce da abun kaunarta saleh su ma suna sauraron abunda alh Adnan zaice, kowa zuciyarsa cike da fargabar abunda yasa alh Adnan ya tara su.
can alh Adnan ya daga kai ya dubi kowannen su yayi murmushi yace AlhamduLillah da Allah Ya bamu ikon haduwa anan kafin muce wani abu Madina ki bude mana taro da addu'a,
Madina tace suka karanta salati goma ga Annabi (s.a.w) sannan ta dinga koraro addu o i kala kala daga karshe ta shafa.
alh Adnan yace nakasance ina kaunar yar yarinyarnan kaltum tun tana yar yarinya karama naga ya dace ta sami mai tattalin ta da nuna mata kauna kamar kowanne yaro domin ta rasa shakuwa da shagwabarda zata yiwa iyayenta naji inason kaltum tamkar nina haifeta mun shaku tamkar kawata haka muke labari duk yanda zanyi na gyara tarbiyarta nayi haka, nayi kokarin turata makaranta don ta samo ilimi kamar kowacce 'ya, duk inda kakai ga iko da dan wani bakayi kamar iyayenda suka haife sa ba, sun fini iko
da ita saboda bana gari suka cireta daga makaranta suka turata makka wai neman kudi taje ta wahala aka bautar da ita tamkar baiwa, nayi takaici nayi kuka don takaici na hakura har saida Allah Ya yanke mata akadawo da ita tazo takoma makaranta sannan wasu shekaru aka sake daukarta bada shawaraba akasake tafiya da ita sudan, shekaru biyu da tafiyarta muna tunanin tana
makkah sai ga marigayiya goggo fattu an kamo ta sai a lokacin ma take fada ai basa tare da kaltum ta barota a sudan, dana bincika sai aka ce ai bara sukeyi a sudan na aika kudi a daukota aka daukota tabbas kamar yadda saleh da sofi suka fada cewar ni nafi can-canta in auri yarsu saboda ni nafi kowo sanin darajarta zanfi riketa amana fiye da kowane da na miji hakane gaskiyane saidai kash!
kaltum ta hadu da wanda takeso fiye dani wanda take ganin zatafi samun nutsuwa dashi, wannan kuwa shine mambela.
sai kowa ya zazzare ido yana kallon alh Adnan daga nan suka hau kallon kallon a junansu hawaye ya surnano daga idanuwan kaltum ta girgiza kai tace basai mambela zan aura ba,
sofi ma ta fashe da kuka tace alh yarinyarnan batada zabi mu bata taba ce mana tana da wani mambela ba niban ma taba jin sunan ba.
alh Adnan ya girgiza kai yayi murmushi yace sofi ke baza ki san mambela ba kuma na yarda vaki sanshi ba din saboda bata hira daku yanada nasaba da babban kuskurenda kuka tafka arayuwa na rashin janta a jiki, tun farko ta tashi tana dar-dar daku bata sakin jiki daku tamkar dodonni wannan ba daidai bane amma nida take hira dani take fadamin matsalolinta ta shaida min tana son Mambela, Madina tayi rayuwa dasu acan ta tabbatar min akwai mambela daga dukkan alamu shima yana kaunarta sosai tsakani da Allah.
Madina tayi ajiyar zuciya tace zancen mambela ai ya wuce alh duk inda aka kai da yabon kyawawan halayensa baikai kamar ka ba, duk yanda mambela ya kaiga sonta da kula dakai bai kaiga yadda ka kula da rayuwar kaltum ba itama ta sani kowa anan ya sani ba kaltum kadaiba koni danazo a baya bayan nan kayimin halacci da ko dangina ba aminba nida mijina Abba babu irin addu ar da bama maka, saita fashe da kuka.
malam saleh yace alh mudai kai muka sani, kai muka bawa babu kyau mayarda hannun kyauta baya, yanzu mudai ba mu san da wannan saurayin nata ba, ko baxa ka aureta ba bazan bashi ba tunda ban san asalinsa ba, ba yarenmu daya ba kuma ba kasarmu daya ba....
alh Adnan yayi caraf yace amma addininku daya ko?
mambela mutum ne mai nitsuwa wanda yasan ya kamata, mai amana da tsoron Allah na yaba da halayyarsa kuma na yarda yana son kaltum zai riketa amana ko bayan ranmu.
sai kowa ya zubawa alh Adnan ido suna duban sa duba na rashin fahimta ko basu furta ba tambayarda suke jerowa azuciyoyinsu bai wuce kai ina kasan mambela da har ka shaida shi da irin wadannan kyawawan halaye?
alh adnan yayi murmushi ya dubesu daya baya daya yace zaku tambaya ina nasan mambela da har na shaideshi?
to ba almara bace kuma bana duba amma zan iya rantse muku da Allah duk halayyan nan dana zayyano muku mambela ya hadasu dukka.
kaltum tayi ajiyar zuci yayinda kwakwalwarta ta kasa tantance abunda alh Adnan yake nupi ta tambayi zuciyarta shin ko Madina ce ta bashi tarihin mambela?
sai Madina tace alh abunda kake fada akwai daure kai don kaltum ta baka labarin abun alkhairinda yayi mata shine ka gama tantancewa har ka shaideshi?
ko kuwa alh Sa'adu ne ya fada maka haka?
alh Adnan ya girgizai ya kwashe da dariya yace ga kaltum nan zaune ki tambayeta nida ita mun taba zama munyi labarin mambela?
tun a waya da ta ambaci sunansa bata sake ambatonsa ba a gaba na ba, haka Sa'adu babu wanda yaki jini irin mambela sbd har hanci ya fasa masa a garin kwato kaltum suka yi dambe har yau zaginsa yakeyi yace sanda yaje dauko Madina ma sun hadu ko kallon juna basu ba don haka zancen ko wani ne yabani labarin ma ki cire.
ni na san mambela kuma na zauna dashi har tsawon shekara uku ina ta gwada shi a bangarori daban daban kuma yaci jarabawata kuma ya cancanci ya auri kaltum .
Sai sofi da malam saleh suka daura hannu akai suna ambaton InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un.
yayinda kaltum taji maganar alh Adnan tamkar almara ko kuma mafarki ta rasa dalilin dayasa taji zuciyarta ta kamu da farin ciki Mai tsanani ta tsunkuyar da kanta kasa tana jinjina hikimar ubangiji tana mai gaskata
addu ah bata faduwa kasa komin daren dadewa Allah Ya na amsa addu ar bayin Sa duk abunda suka rokeShi, ta kagu taji karshen labarin.
madina ta tambaya cike da mamaki alhaji ina ka hadu da mambela?
kaje bur sudan ne?
alh Adnan yayi murmushi yace ko sudan air port din nan ban taba hawa ba balle in yada zango a airport din Khartoum tunda nake a rayuwata amma saiga Allah Ya hada ni da mambela tun bayan dawowar kaltum da wata
guda,
membela ya kirani a waya kasancewar bayajin turanci balle hausa sai malam Abdulkadir yayimin magana da hausa.
kaltum tasan malam Abdulkadir din, malaminda ya basu masauki a Khartoum wajensa mambela yaje ya karbi lambata saboda a ranarda nakira sa'adu ya bani malam shima munyi magana daga baya malam din ya kira ni da lambarsa nima nakirashi to bai goge lambar ba yana da ita, mambela yayi masa bayani shima kuma yayin min bayanin komai game da soyayyarsa da kaltum ban dauki abunda muhimmanci ba a nan na bar zancen, saida aka kwana biyu mambela ya sake kirana wannan karon kuma abokinsa ya bawa waya mukayi magana donshi yanajin turanci, sake rokona sukayi wai in ba shi izini yazo ya auri kaltum, amsar da na basu shine ai kaltum ba yar tsana bace, na kashe wayata na sharesu mambela dai bai daina kira ba wani lokaci in fahimci larabcin da yakeyi nima in gwamutsa
masa nawa ya fahimce abunda ya tsinta bayani dai dayane kaltum ta dawo gida bata koma garin ADON DAWA ba, yar makarantane bazata auri wanda bashida ilimba, kunsan saboda maganarnan dana fada masa ya bazama burni neman lesson teacher da zai koya masa turanci, anyi watanni da dama banji mambela ba sai gashi ranar ya kirani yana magana da turanci duk da bai kwareba amma zaka fahimce shi yace min ya shiga makaranta saboda kaltum don na yarje mishi ya aureta, saina fara gaskata soyayyarnan dayake ikirarin yana yiwa kaltum, don haka saina tambayeshi meyakeso yanzu?
Yace min so yake abashi izini yazo da iyayensa Nigeria su nemi auren kaltum.
sai nace masa a a kada yazo da iyayen sa yazo shi kadai tukunna, nayi masa hakane don na kure shi naga ko bazai zo ba sai kwasam najishi a waya yana tambayana adireshina na Abuja, bayan kwanaki biyu da yin wayarsu saiga mambela dan ADON DAWA a ofishina an rakoshi.
Madina tayi kabbara gami da cewa Allah mai iko Allah mai hada soyayya, yanzu mambela sai daya zo Nigeria saboda kaltum?
ashe bai hakura ba?
malam saleh ya gyara zama yana sauraron irin wannan abun al ajabi yayinda sofi ma ta buga tagumi tana sauraro, Abba ma yakura wa alh Adnan idanu yana kallon hikima da dabaru irin na mai ilimin da yake amfani da iliminsa,
kaltum ta dade da bude duk wata hudarda dake jikinta tana sauraron labarin, ta kasa tantance karshen abun da zai faru taji ta sake son mambela ta sake girmama alh Adnan tabbas ko baban ta daya tsuguna ya haifeta ba zaiyimata irin wannan kiwon da tattalin ba irin yadda a alh Adnan ya damu da rayuwar ta ba.
saiyaci gaba da cewa sai gani ga membela mun hadu muna kallon kallo ko kadan bantaba zaton haka membela yake ba, wayayyen mutum natsattse mai ilimin addini shine babban abunda yasa na fara sauraronsa nan bayan nabashi abinci da ruwa ya huta saina shiga yi masa tambayoyi game da tarihin rayuwarsa banajin ya boye mini komai, ya bayyana min koshi wanene da turanci duk muke magana saidai idan turancin ya kakare ya mako larabci duk ina fahimtarsa, yayi labarinsa ya gama sannan nace meyasa ya tsallake duk yammatan sudan kyawawa ya makalewa kaltum?
saiyace ba ruwansa da kyau ko kudi shi dai yana son kaltum don Allah sai kuma halayyarta ta gari da nutsuwa yasa yaji baya son kowa sai ita, zai kuma dauwama cikin damuwa idan bai auri kaltum ba yayi kokarin rabuwa da ita
tunda ta tafi zuciyarsa ta kasa daurewa ya
shaidamin a shirye yake wajen yin duk abunda aka umurce shi don ya sami kaltum, na zayyano masa dokoki masu yawa kuma masu tsauri da wahala sai ya amsa da cewa zaiyi duk abunda na umurce shi, sharadi dayane baiji dadinsa ba danace bazaiga kaltum ba har sai an shekara uku cur saiya gama cika duk rukunnan dana gindaya masa kuma sai kaltum ta gama makaranta sannan zasu hadu.
ya rokeni da nabarshi ya ganta ko sau dayane, nace mai ai kaltum bata garin nan tana kano garin kano kuwa da nisa daga Abuja, don sai an hau jirgi kafin aje.
Abba ya gyara zama yayi murmushi yace alh wanne irin sharuda ka gindaya masa haka?
alh adnan yayi dari ya yace ce masa nayi idan ya auri kaltum a ina zai ajiye ta?
saiyace a Khartoum zai ajeyeta bazai kaita kauyen su ba saboda suna da gidaje a burni,
sainace a'a bazan bar kaltum ta zauna a Khartoum ba saidai idanshi zai dawo Nigeria ya zauna,
Sai yace min iyayen sa bazasu yarda ba amma in bashi dama yaje ya gina rayuwarsa a dubai saboda yanzu abunda yan kasarsu suke yi kenan, kawunsa ma yana dubai ya ginu yayi kudi yana kasuwanci ta jirgin ruwa yake tura kaya sudan dama yanada sha'awar yin hakan, don haka yakeso ya sayar da gidanjensu guda biyu a Khartoum ya ja Jari, iyayensa bazasu hana shi ba.
nace yaje dai ya shawarci iyayensa idan sun amince yazo zan hada shi da abokan ciniki na na gari wadanda zasu saka shi a harkar kasuwancinsu a can dubai din, na shaida masa nima ina kasuwanci a dubai harma na mallaki gida a dubai a jamaira so nake d'ana Mashkur ya kammala karatunsa a London ya dawo dubai ya kula da harkokina na can, sai mambela yayi murna ya kwana bakwai tare dani a Abuja, hotel na kama masa duk yamma ina daukarsa in zagaya dashi gari har yake sha awar kasarmu yana cewa ashe Nigeria kasace mai kyau haka mai dimbin arziki amma mutanen kasarnan suke zuwa sudan suna bara ana korarsu suna kin tafiya tamkar karnuka?
nace masa mutuwar zuciyane kawai da rashin hakuri da kaddara, munada arziki akasarmu rashin shugabanni na garine babbar matsalarmu a kasar.
membela ya koma kasarsu bayan watanni naga ya kira ni da lambar dubai ya shaidamin ya dawo dubai harya fara kokarin gina sabuwar rayuwar sa, na sake shawartarsa daya nemi ilimin boko don bashida ilimin boko, ya shiga wata makaranta mai kama da diploma kuma yaki da jahilci ce amma zaka fita da satifiket dinda za a iya baka aiki, abur Dubai makarantar take ana koyarda turanci da larabci, lissafi dakuma kompita tamkar yanda ake koyawa yara yan aji daya kuma da karfe shida na yammah zuwa karfe takwas na dare ake zuwa aji, don haka tundaga safe har yammah mambela yana kasuwancinsa, karatun na wata shida ne kacal saidai in dai kanaso kaci gaba akwai makarantar da zaka shekara kanayi ita ma satifiket da za a baka, ya kirani a waya ya shawarceni cewar ya gama wannan makarantar yanaso yaci gaba da karatu nace yaje ya shiga ya shiga yaci gaba da karatu na shawarceshi ya shiga makarantar koyar tuki dake quasis don y huta da zirga zirgan hawan bus daga ajman garinda yake zaune zuwa bur dubai inda makarantar take idan yaje ya tafi makarantar koyan boko, saida ya shekara cur a dubai sannan naje dubai na yi masa shigar ba zata awajen container inda ake lodi na iskeshi ya tube yana loda kaya har abin tausayi, muka gaisa naje har gidan da yake zaune shi da yan kasarsu nayi masa kyautar bata taka kara ta karya ba na taho abuna.
mambela yake fadamin a hira cewar yasha yi min zargin ni mugu ne banida tausayi na rabashi da iyayensa na kawoshi yana wahala kuma dakyar in zan yarda ya auri kaltum yaudararsa kawai nake yi sai daga baya ya fara ganin alfanun abun, daman masu iya magana na cewa bayan wuya sai dadi, dai dai
sanda ya gama makarantar koyan tukin moto ya sami driving liences abune mai matukar wahalar samu a dubai daga nan sai ya sayi moto wacce ba abune mai tsada ba a kasar sannan ya sami sakamakon babbar diploma,
da sakamako mai kyawun gaske yadda zai iya samun aiki a dubai sannan ya kware wajen magana da turanci da iya rubutu da turanci, ya iya amfani da computer.
sannu ahankali saiga mambela ya goge a dubai yasan komai ya sami alkhairai masu yawa harta kai ta kawo shima yana da yaranda suke yi masa aiki suke samun alkhairi a wajensa.
ya shekara yana aiki a wata ma'aikata da take garin NASIR KAIMA daga baya ya daina da yaga kasuwancin yafi ci, sunata tura kaya daga Dubai zuwa sudan nan danan ake juyewa a hada masa kudinsa, koda yaushe mambela yana tuntuba ta awaya yana shaidamin duk irin cigabanda ya samu nikuma sainayi masa addu ar fatan alkhairi. naje dubai naga canjin da ya samu a rayuwarsa yayi min hidima tamkar yanda ake karrama gwamna ko shugaban kasa haka shida abokansa da kawunsa sukayi min, bayan abubuwan arziki da suka hadamin nida kaltum nace suyi hkr bazan iya daukar abunda suka bani ba nagode na taho na bar musu kayansu duk da basuji dadi ba dole ce tasa don babu inda zankai himilin kayan nan tunda ni kadai nake abuna kaltum bata sani ba, a wani bangaren kuma nasa malam Abdulkadir na Khartoum yaje ya binciko min asalin mambela, su waye iyayen sa, yaya rikon addininsu yake.
ya kira ni bayan ya gama binciko min asalin mambela dan asaline karewama su suke rikeda sarautar garin su ba boyayyu bane kowa ya sansu kuma gidansu gidan malamai ne masu riken addini ne.
da lokaci ya cika na gama tabbatarwa da abunda nake so in tabbatar gameda mambela sai na umurce shi yazo Abuja yasameni muyi magana.
abangaren kaltum na binciketa kuma nasa kaninta ya taya ni bincike muka tabbatar har yanzu tanason mambela idan ta kebe ita kadai tana koke koke tana yawan saka hoton mambela a gaba tana kallonsa, Abdul ya shaida min ni ma kuma na lura da haka na dai amsa muku ne kawai zan auri kaltum amma ni a zuciyata nasan wanda ya dace da ita, aikina shine in tabbatar mun aura mata miji na gari wanda zai riketa amana ko babu idanun mu.
.
Duk abun nan da ya paru ni na tsarawa alh Adnan saboda mambela har gida ya same ni yana kuka kamar xai mutu, shi yasa na daga masa kapa kamar yadda na dagawa Abba, kuma duka ai jahadi nayi tunda ceton rai nayi, rayuka ma xa'a ce.
Saura wani yace ba haka bane kasa ni akayi, ehe.
A haka ma na hango wata..... 😊.
Saady Dan AuntyADON DAWA 48
.
TRUE LIFE STORY
.
na dai amsa muku ne kawai zan auri kaltum amma ni a zuciyata nasan wanda ya dace da ita, aikina shine in tabbatar mun aura mata miji na gari wanda zai riketa amana ko babu idanun mu.
AlhamduLillah na cika alkawari dana dauka, na cika amanarda na kudira a raina zancika shine na aurar kaltum ga mutumin da ya dace wanda zai riketa amana ta dauwama a cikin farin ciki, mambela ya dace da ita da kyakkyawan zato zai rike ta amana in shaa Allah,
Allah sarki alh mungode Allah Ya biyaka, kanuna mana kauna, sofi ce ke fada yayinda take zubarda hawayen farin ciki kaltum ma kukan takeyi ta rasa kalmar da zata yi amfani da ita wajen godewa wannan bawan Allah.
madina ta dubi Abba tace kaji wata hikima ta ubangiji ko?
Allah sarki rayuwa ashe akwai mutane masu koyi da hali irin na sahabbai irinka alh ?
Alh Adnan yayi murmushi yace bancika son kuna godemin ba nayi ne don Allah ina neman sakayyah awajenSa duniya da lahira, ku saurareni zan shiga daki na fito, saiya miki ya tashi ya shiga dakin sa.
kaltum ta rugo tazo ta rungume Madina tasa kuka, Madina ta shafa kanta tana ta bata baki sai kuwa sukaji motsin fitowar alh Adnan suka daga ido su dukka suka dube shi sai suka ga su biyu shida mambela, idanuwan mambela akan sofi yanata kallonta domin yaga sunyi kamada kaltum sosai kamar daga sama yaji kaltum ta kwalla kiran sunansa yah mambela!!
ya waigo da sauri sai yaga abar kaunarsa kaltum saiyaji ya gigice gaba daya saboda ta goge tayi kyau kamar ba kaltum dinda ya sani ada ba yaji tamkar ya sureta ya cafe saiya daure ya koma gefenta ya zauna cike da farin ciki, cikin harshen larabci yace kaltum daman ina da rabon in ganki a rayuwa ta?
AlhamduLillahi ko bazan aureki ba na godewa Allah da Ya nuna min ke a rayuwata kafin in mutu, sai hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansu dukka biyun.
madina ta ambaci sunansa cikeda farin ciki sai ya juya da sauri ya dubeta sai yanzu ya shaida Madina ce, itama ta canja ta goge kamar ba ita ba sai mamaki mai dimbin yawa ya rufeshi ya fada cikin yarensa na ADON DAWA a ah yaya naganku kunzama tamkar larabawa dama kunfi jin dadin a kasarku kukaje kasarmu kuke wahala?
dubi yanda kuka zama fa?
kaltum da Madina sai dariya sukeyi kawai donsu kadai sukeji abunda yake fada.
Madina cikin harshen turanci ta gabatar masa da Abba, mambela ya mika masa hannu suka gaisa cikin harshen turanci yace Abba na dade inajin labarinka ashe baka rasu ba?
Madina ta gabatar masa da saleh da sofi cewar ga iyayen kaltum, da taga mambela na kokarin mika masa hannu sai tayi masa larabci tace ya durgusa ya gaishesu al'adarmu ba a hannu da surukai don haka mambela yaje gabansu ya durgusa ya gaishesu da larabci suka amsa da hausa ya dawo ya zauna a kasan kafet kusa da abar kaunarsa kaltum,
alh Adnan yayiwa mambela bayani cewar ya fada musu komai kuma in shaa Allahu babu matsala komai zai dai daita yanzu abunda ya rage shine idan ya koma kasarsu ya taho da iyayensa mata da maza da duk kayanda akeyi na al adarmu ta hausa wajen nemar aure,
mambela ya tambayeshi me ake bukata a auren hausawa?
alh ya nuna kaltum yace ga amarya ka tambayeta ta yadda akeyin komai amma kafin atashi daga wannan zaman inaso inbawa iyayen kaltum dama ko suna da abun fada ko korafi ko suka gameda hukuncinda na yanke saboda kunada hakki akan yarku, wlh duk abunda baiyi muku ba ku fada zan cenza ra ayina kuma bazan damu ba.
saleh ya girgiza kai yace ko da wasa baka taba zartar da hukunci akan kaltum wanda zai zama ba dai dai ba ko wanda zata yi nadama daga baya ba, ka fimu ilmi kafimu tunani kafi mu kula da rayuwar yar nan sunan mun haifeta ne kawai babu wata matsala wallahi fatanmu Allah Ya bada zaman lafiya kaikuma Allah Ya saka maka da alkhairi,
sofi ma irin wannan addu ar ta dinga zazzago masa,
Abba da Madina ma sunyi masa addu'a da godiya a bisa kyakyawar niyyarsa.
kaltum ta durgusa a gabansa tayi masa godiya haka ma mambela sannan ya umurci kowa ya tafi sai da safe kuma,
suka duguma su dukka suka fita daga falon,
alh Adnan kadai aka bari a zaune fuskarsa cike da fara a da alama yafi kowa farin ciki da Allah Ya nuna masa ranar daya cikawa kaltum burinta.
Madina da Abba suka raka har motarsu suka shiga suka tafi sannan sofi da saleh ma suka shiga gida,
mambela da kaltum ne a zaune akan kujera a farfajiyar gidan suna rera hirar yaushe gamo hirar so da kauna suna masu godewa Allah daya sake hadasu badon sunaso ba sai don dare yayi sukayi sallama kaltum ta shiga gida mambela ma ya shiga gida, alh adnan dama ya nuna masa dakinda zai kwana anan ya ajiye akwatinsa tun sanda sukazo yadda bacci ya gagari idanuwan mambela haka ya gagari kaltum juyi kawai sukeyi suna tunanin juna yayinda farin ciki yayi musu katutu a zukatansu kamar wadanda suka hada baki a alokaci guda suka ayyana aransu tunda bacci ya gagara gara su tashi suyi alwala suyi sallah su godewa Allah dayayi musu wannan
babbar kyauta.
Madina ma da Abba suna can a gidansu sun raba dare suna hirar wannan abun al'ajabi ashe sofi ma da saleh farin ciki ne ya hanasu
barci suma suna daga daki suna tattaunawa sai dai duk rabin hirar tasu addu a ce suke jerowa alh Adnan suna yi masa fatan Allah Ya biya shi da gidan aljannah.
daya bangaren kuwa alh Adnan ne kwance kan gadonsa ya takure yayinda kuka ya kece masa yana addu ar Allah Ya kara masa dangana da juriya rabuwa da kaltum domin yana sonta har cikin ransa kuma yayi niyyar auranta saidai ya fuskanci zai tauye mata rayuwa saboda akwai wanda takeso bashi ba don haka ya sadaukar da son da yake mata ya bata wanda takeso donta sami nutsuwa arayuwarta shiya yarda da duk wani tsanani da zai shiga na sanadiyar rabuwa da ita,
juyi kawai yakeyi yayinda zuciyarshi ke tafarfasa don tsananin tashin hankali da yake addabarsa, yana kiran InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah Ka yayemin abunda nakeji kada in dauwama dason kaltum a raina har gara in mutu da in dauwama cikin wannan hali ,
ahankali yaji zuciyarsa na sanyi saiyayi wuf ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala yazo ya kwana yana sallah yana neman hakurin dangana da neman sauyi mafi alkhairi,
washe gari da safe sofi da kaltum suka dinga hidimar dafe dafen abinci kala kala don su bawa bakonsu, sun san halin alh Adnan ba cin abincin safe yakeyi ba kofin shayi dayane zaisha saikuma da rana ko sun kai sunsan bazai ci ba saidai mambela.
kannen kaltum ne suke jerawa kan daning table dinda ke falon alh Adnan yayinda alh Adnan da mambela suke zazzaune a falon suna tattaunawa da alama alh Adnan shiryo tafiya zaiyi harda yar jakar kayansa a gefensa, ya umurci mambela daya cigaba da zama a gidan kamar na sati biyu ko uku Madina ta zayyano masa komai sai ya tafi ya shirya suyi waya su fadi ranar da zasu zo sai a buga katin gayyata anan a rarraba suna zuwa sai a daura aure ayi biki gaba daya.
farin ciki ya rufe mambela ya rumgume alh Adnan yayi godiya suka dungumo suka fito zuwa bangaren su kaltum.
sofi da saleh suka fito da sauri suka durgusa suka gaishe shi, alh har zaka koma Abuja da sassafe haka ko karyawa bakayi ba?
sofi ta tambaya cike da kulawa,
alh adnan yayi dariya yace ai yau akwai aiki saboda mambela nazo amma zan barshi anan ya zauna har sawon sati biyu ku saba sosai kuma ya gana da amaryarsa sannan sai ya tafi daga nan basai yaje Abuja ba idan ya shiryo sai yazo da iyayensa a daura aure ayi biki akai ta dubai shi kenan, yasaka hannu a aljihu ya damko kudi ya ambulowa saleh a hannunsa yace ka rike wannan saboda cefene ya karu adinga dafawa mambela abinci mai kyau kuma kala kala ina kaltum din ne?
kaltum tayi wuf tafito daga daki sanye da hijabi tazo ta durgusa ta gaishe shi yayi dariya yace kin iya abincin zamani kuwa kosai tuwo irin na sofi?
donshi shi tafi kwarewa kullum kaga sofi to muciya ce ahannunta tana tuki ba a yin soye soye mijin kuma dan gayu ne ya saba da snacks da shawarma, kazar kfc, mr biggs, mcbanas, pizza a dubai ba ya cin tuwo idan baki iya ba kije Madina ta koya miki tun wuri nasan ita ta iya.
kaltum da iyayenta suka tunzure da dariya yayinda mambela yake tsaye yana kallon bakinsu ba tare da yasan abunda suke fada ba cikin harshen hausa, yaji yanaso ya koyi yaren hausa domin yanajin dadin sauraronsa tun ba yanzu ba.
daga yadda alh Adnan ya fuskanci mambela yana yawan kallon kaltum ya tabbatar yana sonta matuka har kamar zai hadiyeta, zuciyar sa na ayyane ayyane sai alh Adnan yaji kishi ya turnuke shi babu yadda zai yine kawai yaga kaltum ta kara kyau dariyarta ta zame masa lu'u lu'u a idanunwansa sai ya dinga karanta a'uzubiLlah minal shaidanir rajim kuma ya gaggauta barin wajen, da mambela ya rakashi mota sai alh adnan ya damko kudi ya bashi yace ya sayi duk abunda yake sha'awa, da farko mambela yaki karba yace yana da kudin Nigeria daya canza kuma yana da dalar.
alh Adnan yace saiya karba dole don haka mambela ya karba yayi godiya,
alh adnan yaja mota ya tafi yayinda hawaye mai radadi ya dinga fita daya bayan daya har saida ya ji turnukukin da yake damunsa ya ragu saboda karatun kur'ani daya kure a rediyon motarsa, addu'ace maganin masifa
haka hakuri maganin zaman duniya ya isa gida kuma ya iske matarsa na jiransa domin sai yanzu yan gulma suka kawo mata labarin aurensa da kaltum ta ayyana a ranta tafiyarda ya tarka da tsakar rana zancen auren yaje don haka tace ya zaba ko ita ko kaltum don bazata zauna da kaltum a matsayin kishiyarta ba.
saiyaji ya kasa magana kallonta kawai ya zauna yanayi saboda babu ciwon da yafi aibu irin jahilci ya yarda jahilcine ke damun salaha
kamata yayi ta tambayeshi gaskiyar magana tunda bayayi mata karya ai zai fada mata gaskiya saita yarda da gulmarda yan gari suka fada mata ta zartar da hukunci yasan hankalin mata tunanin su ragagge ne a matsayinsa na namiji sai bai kula ta ba tayi ta fadanta harta gaji ta daina.
kaltum da mambela sun kasance koda yaushe suna zama tare a kan wasu fararen kujeru a farfajiyar gidan sallah da cin abinci ne kadai yake tashinsu hira kawai suke yi cike da farin ciki marar misaltuwa idan dare
yayi kowa ya shiga barci sai su dinga magana a waya har assalatu sannan su tashi suyi wanka suci ado su fito su kafa kujera su zauna hira.
sofi da saleh suna ganin ikon Allah yarinya ta iya hira rairairai duk da larabci suke yi basa fahimtar abunda suke fada amma suna ganin murmushi da kashe ido da muryar da takeyiwa masoyinta ko ba a fada musu ba sun san sai yanzu kaltum ta sami wanda takeso wanda take ganin ya dace da rayuwar ta.
dan ladi direba ya zagaya da kaltum da mambela gidajen yan uwa da kawayenta, sunsha zuwa gidan madina da abba su gaisheta, madina ta taya su murna tayi musu nasihohi masu yawa ta rubutawa mambela duk abubuwanda ake bukata a auren hausawa ta kuwa zabga kudi fiye da yadda aka saba , sadaki ne kawai ta rubuta kadan don neman albarkar auren, dalilinta guda biyu na farko dan tasan suna da kudin sannan tanaso ya kashe kudi yaji ajikinsa zaifi rike aurensa da daraja duk da tasan ya gama shan wahala kafin ya sami kaltum, inda kudin yafi yawa shine wajen kayan lefe akwatuna shida tace ya ciko da tsadaddun Kaya baya ga lifgin gwala gwalai data ce ya zuba, abun mamaki sai taga bai damu ba harma yana ce mata yanzu haka saiya koma dubai don ya kai kudin gwala gwalan kamfani suyi masa disign mai kyau wanda za a rubuta sunan a jiki da sunansa.
satin mambela uku a kano acikin kwanakin daya yi saida sukayi kwana uku a zangon daura kwanaki uku a garinsu sofi saleh da danladi direba suka raka shi yaje ya gaishe da dangi su suka ganshi tabbas sunyi farin ciki da zuwan mambela don dollar ya dinga raba musu nan da nan suka ji kaunarsa a ransu sunyi amannah ya aure yarsu.
ranar dayazo tafiya madina da abba da kaltum ne suka kai shi filin jirgi sai ga kaltum da mambela suna kukan rabuwa, madina tana musu tsiya,
mambela ya tafi yabar kaltum zuciyoyunsu va
dadi amma bayan ya isa dubai sai suka bude shafin yin waya ba dare ba rana bai damu da daruruwan dirham din da yake kashewa ba wajen kiranta ba shi dai shidai burinsa yaji muryarta haka da ya isa sudan tun a Khartoum ya saka layinsa ya fara Kiran ta har saida ya isa bur sudan yanzu service har garin yan ADON DAWA don haka ba dare ba rana waya sukeyi saidai idan sallah zasuyi ko cin abinci da sauran uzururruka suna gamawa kuwa to sai su hau waya ko dayake mambela ne mai kudin kira ita nata sakon wasika ne tafi iya turawo da turanci koda larabci ko da wanne yare ne ma dai yana bata
amsa, kalaman dai naso da kauna ne da tsantsar bege duk wanda yasan kaltum saiya san labarin mambela haka shima sarki ya rasa kansa ba ya zuwa fada ko kadan yana daki a nade yana waya ko yaushe.
iyayensa sun yarda da bayanansa sun amince zasu shirya zuwa Nigeria.
saboda farin cikin an bashi kaltum mambela ya sami yan gidan su kaltum na bur sudan yayi musu albishiri da cewa duk wanda a cikinsu yake so ya koma kasarsu ya dauki nauyin biyan kudin motarsu da guzurinsu har zuwa Nigeria duk ya sadaukar saboda kaltum,
su iya mairo da jikarta su akawa wannan saboda sun matsu su koma Nigeria amma babu kudin mota, kadan daga cikinsu ne sukeson zama a bur sudan da yawansu sun amince zasu tafi ya umurce su suzama cikin shiri sai daf da bikinsa da kaltum a kano bayan biki zai bawa kowa kudin mota ya tafi garinsa, suka hau murna da tsalle suna masu yi masa addu ar fatan alkhairi sai suka hau hada tsummokarai suna wankewa.
kaltum ma bata zauna ba ta amince da shawaran alh Adnan tana zuwa gidan madina akai akai tana koyar abinci kala kala, i dan madina ta koma abuja sai mummy hafsat ta koya mata ko ta tafi gidan dr sumayyah ranarda bata zuwa aiki ta koya ba abinci kawai suke koya mata ba suna koya mata duk yadda ake zama da miji da yadda ake masa biyayyah yadda za arike zuciyar mai gida yaji babu wata a gabansa sai ita.
.
RANAR DAURIN AURE
rana bata karya saidai uwar ya taji kunya watanni shida mambela ya dauka sannan ya
dumgumo yazo da iyayensa tafe suke da kayan aurensa kakaf, abun nayine sarki da matarsa sun hallara haka baban mambela da mamarsa aka zo sai maza biyu tsofaffi da mata biyu tsofaffi suka taho a jirgi.
dandazon yan gudun hijira motoci biyu j5 ne suka iso kofar gidansu kaltum da kayan su mata da maza da 'yayansu kanana su suka fara isowa kafin ma su mambela su iso , da yake ya shaidawa kaltum tun a waya kuma ya turo kudin da za a sauke su don haka tayi tanadin zuwansu an nemi gidaje biyu haya daya mata daya maza, aka dinga dafa abinci
ana cika daruka ana aika musu aka daura auren mambela da kaltum, aranar wannan asabar din alh Adnan ne waliyin amarya manyan mutane daga wuri daban daban sun halacci daurin auren nan, kawun mambela daga dubai da manyan abokansa sunzo yan uwan sofi daga camoroun sunzo matansu da mazansu haka yan zangon daura da yan daura suma ba a barsu a baya ba.
alh adnan bai manta da malam Abdulkadir ba na Khartoum, ya aika masa da kudin jirgi shi da dan rakiyarsa mutum daya suka zo.
madina da yayanta gami da mijinta da surukanta da 'yayanta suma ba a barsu a bayaba dasu aka yi komai a wajen shagalin bikin,
sai salaha taji kunya jikin ta yayi sanyi data gano ba mijinta za a aura ba,
.
Sai ayi hakuri na rashin samun post jiya sakamakon hidima na xabe,
Allah Ya xaba mana shuwagabannin na gari.
Aamiin.
Saady Dan AuntyADON DAWA 49
.
TRUE LIFE STORY.
.
sai salaha taji kunya jikin ta yayi sanyi data gano ba mijinta za a aura ba,
tayi bajintar da babu wanda ya yi saboda dawainiyar data yi da yawa ta buga kalandu da memo da robobi da barguna bayaga abinciccika da ta dauki ma'aikata aka yita dafawa, itace mai yiwa amarya kwalliya da zabar mata kayan da ya dace ta saka, a bangarenta amarya da kawayenta suke hidiman su duniya kenan budurwar wawa wanda ya biye ta saita kaishi ta baro shi, alh Adnan ya tsaya kawai yana duban matarsa yana mamakinta domin a iya sanin da yayi mata ta tsani kaltum tun tana karama ashe a lokacin ma kishi ne sai yanzu ta saki ranta kenan, sai ta shiga kame kame tana bashi hakuri a bisa rashin mutuncinda tayi ta shuka masa a baya a rashin sani.
gaba daya liyafar bikin nan ita ta tsaya ta tsara ta yadda ya kamata, bini-bini ta dafa amarya a dauke su a hoto abu kadan saita kira sofi gefe ayi shawara kanka ce kwabo an kulla kawance ita da Madina da sumayya tukur har da musayan lambobin waya,
danta mashkur ma yazo daurin auren daga London sun sha hotuna da amarya haka alh Adnan da amarya da ango anyi hotuna ba adadi.
sati guda aka kashe ana shagalin biki daga nan sai jama a suka fara watsewa da yake kowa yasan ba anan za'a ajiye amarya ba don haka babu jere, fataken da suka yo kaura daga bur sudan suka kama hanyar garuruwansu bayan mambela ya damka musu kudin motar da zasu karasa garuruwansu, yan Niger suka kama hanya, sakkwatawa suma suka nufi Birnin Shehu, daurawa ma suka nufi Birnin Daurawa suna masu godiya da fatan zaman lafiya tsakanin ma aura ta, yan camaroun ma suka daure kayansu suka nufi gida kanwar sofi ce joda
kadai bata tafi ba saboda sunanta ya fito a yan rakiyar amarya dubai.
malam saleh kuwa shine yace zai raka yarsa da kansa babu wanda zai wakilceshi daga danginsa sai kuma salaha daga bangaren kaltum kenan duk mambela ya dau nauyinsu, yan ADON DAWA ma sun juya zuwa kasarsu sarki ne kawai zai raka jikansa Dubai,
sai kuma Madina da Abba da suka dau nauyin kudin jirginsu daman sunada niyyar zuwa su huta.
maimakon kayan daki sai alh adnan ya kunshe zunzurutun kudi har miliyan daya ya bawa kaltum yace taja jari, jirgin emirate suka hau a legos basu tsaya a ko ina ba sai filin jirgn nan mai tsananin kyauwu da tsari wato
emara airport, kaltum da mambela sunga abunda basu taba gani ba sai suka ware ido suna kallo tunda basu saba fita ba kamar su Abba da mummy salaha ba har gara kaltum ma ta taba ganin wasu abubuwa a makkah amma dai shekarun da yawa babu wanda yakai joda dashi kansa ransa ya dade sarkin ADON DAWA shima bai taba fita ba idan yayi tafiya mai nisa to Khartoum ne sai santi yake yana basu dariya suna kyakyatawa.
acikin dubai gida mambela ya kamawa kaltum haya a wani anguwa da ake kira bur Dubai, dogon gini mai hawa ashirin ne gidaje don haka a hawana ashirin gidan kaltum yake babu wahalar hawa bene saboda akwai wuta ba a daukewa, na'urane zata kai ka cikin lokaci kalilan wato lifta.
tsantsari gidan yayi kyau domin an kara kayata gidan da kaya masu kyau da tsada da kalar da ya dace, dakuna biyune gidan da falo daya dining area da kicin sai bandaki uku hardana baki a falo babu wani abu na jin dadin rayuwa na wannan zamani da mambela bai saka mata ba wannan shi ake kira aljannar duniya, abun dariya harda katon photo yayi enlargement shida kaltum a bur sudan ya kafa a falo duk da basu waye ba anma sunyi kyau.
sati guda sukayi agidan amarya, mata adaki daya maza adaki daya duk da mummy salaha bata cika kwana agidan ba a deira take kwana cikin kasuwa saboda sare sarenta daman yar kasuwa ce, haka Madina da abba ma sau daya suka kwana suka kaura hotel sukayita yawo wuraren shakawa kala kala suna ta sayayyar abunda ya basu sha'awa nasu dana yayansu da iyayensu, tsaraba duk daban daban kowannensu ya kama gaban sa, ba a tare suka tafi ba sarki ne ya fara tafiya kasarsu ya tafi yana santin kyawun dubai da
Nigeria ya kudira a ransa yana komawa gida zai umurci talakawansa su fito birni suyi rayuwar jindadi, su fito da wannan dumbin dukiyarda suka boye suci su gina gidaje na zamani sai yanzu yasan ashe ba karamar tauyewa kansu rayuwa suka yi ba, sai ya tuna idan duk garin suka watse suka koma birni wazai mulka?
don haka ya canja shawara gara ya ce duk su rushe gidanjen katako nan da kaya suyi na siminti gwamnati tayi musu kwalta fitilu, makarantu a garin haka kuwa akayi yana isa ya kira taron gaggawa da manyan gari aka fara shawarwari.
daga baya mummy salaha, joda, malam saleh suka dunguma suka kama hanyar kasar su, sai kaltum ta fara kuka ta sun yoye sun barta nan danan ta hakura dasuka lallasheta saboda tana ganin Madina da Abba.
kwanakin madina biyu a asibiti da yake a alnahdah mai suna ZULAIKHA HOSPITAL ana duba lafiyarta hawan jini da ciwon zuciya
AlhamduLillahi lafiya ta samu sosai ba kamar da ba yanzu batada wata matsala arayuwa ciwo ne dai inya shigeka sauki sai a hankali amma lafiyarta kalau anan ne aka hango mata dan karamin ciki da take dauke dashi dan wata biyu,
sai farin ciki ya lullube Abba kan kace kwabo ya buga waya Nigeria yana yadawa, suma satinsu biyu sannan suka yiwa amarya da ango sallama zasu tafi, a filin jirgi kaltum ta rugume Madina sukata kukan rabuwa.
Abba da mambela sukayita basu hakuri, kaltum tanaji tana gani suka tafi suka barta daga ita sai mambelanta ido yayi jajawur tana zaune agefen mambela shiyake tukawa a hanyar su ta komawa gida daga airport ya dubeta yayi murmushi yace kaltum sai nake ta mamaki da naga kina kuka dan bakinmu zasu tafi na dauka yau murna zamuyi kowa ya watse ya barmu don mu samu mu sha hirarmu mu biyu, saina fara tsorata nace a raina koba wannan kaltum din bace take sona nake matukar kaunarta ba.
sai suka kwashe da dariya su dukka tun daga lokacin ta ware suka dinga hira har suka isa gida suna shiga gida mambela yahau harhada musu kayayyakinsu a cikin akwatuna guda biyu sai mamaki yakama kaltum ta tambayeshi ina zamuje da kaya?
mambela yace aimu da dawo gidan nan sai
nanda sati biyu banaso kiyi shara banaso kiyi
wanke wanke balle girki hotel zamu kaura a dinga dafa mana ana bamu.
kaltum zata yi magana ya toshe mata baki yace kada kice komai kibiyo ni kawai suka rufe gidansu suka dura akwatinansu a cikin mota suka tafi.
dankareren hotel suka kama yana daya daga cikin hotel dinda akeji dashi a dubai gari na wayewa saisu yini, wuni suna yawo manyan mall irinsu EMERATE MALLS DUBAI, MALL CANIPOUR CITY CENTER, da sauransu duk abunda takeso mambela sae ya saya mata, dayammah kuma sae su tafi Beach har sha biyun dare suna shagalinsu su shiga suyi wanka su pito su saya gasheshen kipi da lemo mae sanyi su sha ko su shiga kfc suci kaza da icecream daga nan suka kada sukayi cikin Deira land mark hotel suka sauka nan ne ma dae kaltum ta dinga haduwa da hausawa yan uwanta mata da maza tayi ta jin dadi,
kaltum ta kashe kwarkwatan idanuwanta don babu abin da ba a sayarwa nan ce babbar kasuwar dubai babu kabilarda babu kusan duk park din da take dubae mambela da kaltum sun zagaya, acan suka yini suna shan iska daga karshe kuwa cikin jirgin ruwa suka kwana jirgine mae girmar gaske wanda ya hada da dakunan kwanciya ,dakin cin abinci (restaurant)ga dakin rayel-raye da kide kide nan ne kadae basu zagaya ba sbd su dukka malamae ne, idan suka so sae su hau can saman jirgi kololuwa nan kuwa katuwar farfajiya ce babu rufi sae kujeru na shakatawa anan ne zaga dinga hango ruwan da jirgin yake ciki yana tafiya ahankali anan zaka hango ruwanda jirgin yake ciki yana tafiya ahankali anan zaka hango jirage da kwale-kwale ga jama'ah suna loda kaya a manyan jiragen ruwa mae daukar kaya wanda ake turawa kasashen ketare.
bayan sun cika sati biyu sun dawo gidansu su cigaba da zaman cikin kwanciar hankali so da kaunar da juna sae abunda yayi gaba sun shaku tamkar wasu tagwaye su yini tare su kwana tare su fita kasuwa tare suyi aekin gida tare,
mambela yana godewa Allah da Ya yi masa kyauta da mace da tafi sauran mata iya biyayyar aure, itama tana godewa Allah da Ya bata miji na gari mae tattalin mace da kula da ita tamkar kwae, kaltum bata mantawa da ginshikin rayuwarta wato alh Adnan, bata kwana biyu ko uku bata kirashi a waya sun gaesa ba, yana jin dadin wannan abu yana gode mata sae yayita tambayarta ko akwae wata matsala ta fada karta boye masa.
tana shaeda masa bata da matsala ko kadan a rayuwarta da mambela.
Allah Ya saukowa alh Adnan dangana zuciyarsa ta yi sanyi ya cire son kaltum a ransa, da matarsa ta gyara halayyarta sae shi ma suka dawo da tsohuwar soyayyarsu. tafiyar kaltum ba dadewa ba ya shawarci matarsa zae bar wa malam saleh da sofi gidan nan kacokan su koma babban gidan su bar boy,s quarters sae ta amince ya mallaka musu har da kayan ciki harda motarda danladi yake tukawa ya hada musu da kudinda zasu yi jari su ma su kula da kansu su bar zaman bauta a karkashin wani, yayi wa kano sallama ya koma Abuja kacokan sbd rashin kaltum bayajin dadin shigowa garin sae dae in wani uzuri daban ne ya kawoshi, ya sake gina wani gdn a can wani anguwa acan suke sauka yanzu.
ranar da sofi ta shaidawa kaltum wannan abun farin ciki sae kaltum ta fashe da kukan farin ciki ta kira alh Adnan a waya tayi ta godia tana kuka yana lallashinta ya bayyana mata duk abunda ka bayar a duniya shine rabonka a lahira,
kaltum na can acikin kayataccen gdnta tana sha aninta daga kallo sae waya da en nigeria yayinda mambela na can yana shirya mata abunda zai amfani rayuwarta.
da farko makarantar koyan tukin mota ya biya mata ta shiga bayan taci jarabawar aka bata dariving liences sae ya saya mata mota tana tukawa ahankali tasan ko ina a cikin Dubai, sannan ya kawo mata littatafae na karatu manya manya har ya gama yi mata registration a tsadaddiyar jami ar nan dake cikin garin Dubai wato MIDDLE SEX UNIVERSITY reshe ce ta university a england kwasa kwasan computer ne don haka a shekaru uku zata kammala digirinta a bangaren computer.
batare da vata lokaci va ta para tuka hadaddiyar motarta zuwa makaranta tana jin dadin karatun saboda tana ganewa sosae tayi kawaye dayawa acikin en matan ajinsu saboda akwae en nigeria dayawa a makarantar kuma hausawa sai turawa da larabawa.
wanda yasan kaltum a shekaru hudu ko biyarda suka shude zaesha mamaki idan ya ganta yanzu kamar ba wannan almajiran nan
mae bara ba, kaya ayayyage takalmi atsinke a daure da leda ko tsumma yanzu kuwa sae kayi da gaske zaka tantance wannan bakar patace ko balarabiya sai kaga kamar inka mata hausa zata fita da gudu tsabar firgita idan ka kalleta sae ka sake kallonta tsabar kyauwun fatarta duk da akasarin shigarta na
dugowar rigace da dankwalin abaya wani
lokaci ma hijabine har kasa sbd mambela yana kishinta idan yaga kallon da ake yimata yayi yawa sae yace ta saka nikafi.
da sukayi hutun makaranta sae shirya zuwa nigeria ganin gd sukaci sa a kuwa aranarda suka iso kano ranar Madina ta haepi santalelen danta mae kama da babarsa abba, ranar suna aka radawa yaro sunan kakan sa da babansa wato Tukur, ake kiransa da Khalifa Abba Tukur.
kaltum da mai gidanta sunyiwa Madina Kaya iri iri da kudi masu yawa haka tayiwa iyayenta da kannen ta tsaraba kala kala da akwatuna baya ga kudi masu yawa data rarraba musu, sofi da 'yayanta mata kuwa harda sarkokin gwal da en kunnen su ta hado musu.
satinsu kaltum uku a kano suka tapi Abuja gdn alh Adnan, shida matarsa sun karbesu
hannu bibbiyu sunyi musu hidima sosae suma kuma sun kawo musu tsaraba mae yawa.
satin su daya suka tapi sudan a bur sudan ma satinsu uku agarin en ADON DAWA, garin ya gyaru anyi matukar sumun cigaba sarki yayi matukar wayerwa da talakawansa da kae suna cin kudinsu yanzu suna sayan kayan more rayuwa sun fara gina gidajen siminti suna dinka suturu masu kyau ankae musu ruwan famfo da wutan lantarki gami da titina da makarantu duk acikin shekara guda.
su kaltum sunyita rabon tsaraba babu adadi, kaltum takai ziyara gidansu na da taga dakunansu har yanzu kuwa akwae saura daga ire ire mutanen tawagarsu wadanda zama Ya Mike sukayi aure suka hayayyafa sun ganeta kuwa kamar yanda ta ganesu tayi musu kyautar girma sunyi farin ciki,
kaltum bata manta da abokinta ba Karim mae kamun kifi yana nan a inda tabarshi ya auri yar ADON DAWA har sun haefu yayi farin ciki da ganin kaltum musamman data yi masa kyautar kudi da kaya mae yawa,
kaltum ta zagaya bakin kogi enda suke zama sannan ta zagaya garin Jange daga can suka shiga Jim Arab kasuwar yan ADON DAWA kae tsaye ta tunkari rumfar tsohon nan da ya kwace ta ahannun mambela da abokansa ta
tarar bayanan sae dansa ya shaeda mata Allah Ya yi masa rasuwa, saeta bawa dansa kudi tace mahaefinka ya taemake ni bazan manta da shiba zan zamo mae yi masa addu'ah duk sanda na tuna shi, Allah Ya yi masa rahma amin.
suna tafiya acikin tsaleliyar motarsu mambela ke tukawa a hanyarsu ta tafiya Khartoum suma takae musu ziyara taga yan gidansu suna nan kamar yadda ta barsu taga malam Abdulkadir da matansa ta kuma gwangwajesu da kyauta daga nan aka rakasu
gidan Fatsuma da Musa a can wata unguwa suke nesa, sunyi aure suna zaune lafiya harda 'yayansu guda uku. fatsuma tasha tsalle da murna da taga kaltum da kyar ma ta ganeta sbd canjin da ta samu sae alokacin take ta bawa kaltum labarin mambelane ya musu komae na aure hatta gidan nan shi ya kama musu ya biya musu hayar shekaru biyu sanan ya ba su jari.
kaltum ta sha mamaki don ko kadan bai taba fada mata ba ya dai ce mata fatima da musa sun yi aure a Khartoum.
agidan fatima kaltum da mambela suka kwana dayake gidan dakuna 2 ne kuma basu da talauci suna rayuwa cikin rufin asiri, washegari suka koma bur sudan bayan sun ambulo musu makudan kudi.
duk inda kaltum taje saetayi kuka saboda tana tuna baya tana tausayawa wadanda har yanzu suke cikin wannan rayuwa Allah bae yanke musuba tukunna.
hutunsu ya kare sae suka koma Dubai sukaci gaba da rayuwarsu,
lokaci daya mambela ya kira kaltum ya danka mata kudinta dala dubu goma da alh Adnan ya bata tun lokaci aurensu ya kara mata da wasu yace ta kira iyayenta a waya tayi shawara dasu ta zabi kasuwancin da zata dinga yi tsakanin Dubai da zuwa Nigeria. kamar da wasa suka fara yi da Madina tana turo da kaya tana sayar mata a Abuja sae malam saleh ma ya ke karbar kayan yana rabawa yan kasuwar sabon gari da kasuwar kwari bayan sati biyu sae su hado masa kudi ya dauki ribar sa ya turo mata uwar kudinta da ribarta kafin kace kwabo kasuwanci ya Mike suna samun alkhaeri, gaba dayansu kannen kaltum sun warware sun goge sunyi kyauwun gani suna karatu a makaranta masu kyau sunyi sallama da talauci a rayuwarsu.
Madina kuwa haehuwace ta mike kafin ta yaye khalifa ta sami wani cikin ta kara haehuwar namiji sae suka saka masa sunan Adnan sbd alkhairan da alh Adnan yayi musu.
yaji dadi matuka alh Adnan da wannan karar da suka masa alokacin kuma matar mashkur ta haehu shima da namiji aka saka masa suna Adnan ake kiransa Amir, sae ga waya daga Dubai aka shaeda wa alh Adnan kaltum
ta haihu na miji ansa masa takwara ana Kiran sa Daddy.
sae alh Adnan yaji hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansa.
mace mae kamar maza madina ta kutsa garinsu onitsha tana yakar arnar da har yanzu basu san akwae ubangiji ba wanda ya halicce su, bada makami take yakarsu ba da siyasa take samun galabarsu daya bayan daya take
zakulowa tana tahowa dasu Abuja ta zauna dasu ta cusa musu ra ayinta har sae sun gamsu ta basu jari da wajen zama saesu musulunta gobe ma idan taje wata zata jawo ta taho da ita, da kadan kadan suketa musulumta har suma wadanda suka musuluntar suke jawo wasu zuwa musulunci.
yayanta Abdullahi shima da shawarwarin Madina yake aeki tasashi ya musuluntar da uwar gidansa uwar 'yayansa da 'yayansa kakaf sannan tasa ya kwaso su dukka suka kauro Abuja suka shiga islamiyya suka sami ilimin addini.
.
Yanxu kuma babu abunda kowa ya sa a gaba da tsurawa ido sai jiran lokacin auren Dan Aunty da Shahida,
Saura na samu en uba kuma,
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 50
.
TRUE LIFE STORY.
.
da wannan karar da suka masa alokacin kuma matar mashkur ta haehu shima da namiji aka saka masa suna adnan ake kiransa Amir sae ga waya daga Dubai aka shaeda wa alh Adnan kaltum ta haehu na miji ansa masa takwara ana Kiran sa Daddy, sae alh Adnan yaji hawayen farin ciki ya surnano daga idanuwansa.
mace mae kamar maza madina ta kutsa garinsu onitsha tana yakar arnar da har yanzu basu san akwae ubangiji ba wanda ya halicce su, bada makami take yakarsu ba da siyasa take samun galabarsu daya bayan daya take
zakulowa tana tahowa dasu Abuja ta zauna dasu ta cusa musu ra ayinta har sae sun gamsu ta basu jari da wajen zama saesu musulunta gobe ma idan taje wata zata jawo ta taho da ita, da kadan kadan suketa musulumta har suma wadanda suka musuluntar suke jawo wasu zuwa musulunci.
yayanta Abdullahi shima da shawarwarin Madina yake aeki tasashi ya musuluntar da uwar gidansa uwar 'yayansa da 'yayansa kakaf sannan tasa ya kwaso su dukka suka kauro Abuja suka shiga islamiyya suka sami ilimin addini.
haka ' yayanta Abdul Malik da Abdul hakim sun kammala karatun digiri dinsu Abba ya samar musu da aeki, anan Abuja suke rayuwarsu yayindaduk wanda yasan shahida abaya zaeyi wuya yaganeta yanzu, Abba ya dauketa yadawo da ita gidansa yace shi zae riketa ko bayan ran Madina zae dau nauyinta harsae ya aurar da ita,
tashiga jami'ar A.B.U zaria tana karanta medicine.
Allah mai kyauta a duniya mae azurta wanda Ya so a lokacin da Yaso, tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikae.
misalin karfe tara na dare mambela ya dawo
daga wajen aeki daman yanada nasa makullin don haka sae ya bude kofar gidan ta baya ya shigo kamar yanda ya saba ganin kaltum a falo tana zaman jiransa yau sae bai ganta ba sae yayi tunanin ko tana daki ya leka dakinta yaga babu kowa daddy ne kawae ke kwance a dan gadon sa yana barci saeya leka bandaki batanan sai yace aransa to tana dakinta abun mamaki anan ma batanan ya leka kicin babu kaltum babu dalilin ta sai yaji hankalinsa ya tashi nan da nan ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya fara kiranta sai ga wayarta akan kujerar falo ba ta tafi da wayar ba, kamar wanda akace masa ya leka barandar waje sae kuwa ga kaltum tsaye ta rike karfen baranda tana kallon kasa, ya sadada yaje ta bayanta ya rufe mata ido ta zabura ta waewayo a firgice kamshin turaren jikinsa ne ya tabbatar mata da cewa rabin ranta ne mambela sae su dukka sukayi dariya yayi mata rada a cikin kunnenta cikin wata tattausar murya cikin harshen hausa,
kaltum tunanin kike yi anan?
akwae abun da na rage miki a rayuwa wanda
yake damunki baki fada min ba?
ko akwae wani hali wanda ba kyaso in daina?
kada ki boye min komae my love.
Sai tayi murmushi ta lumshe ido ta dubeshi sannan ta nuna masa kasa tace duba kaga Dubai da daddare haske tar kamar da rana sbd fitilu duba kaga kololuwar benen mu hawa harna ashirin, duba kaga motoci suna yawo a kwalta tamkar tururuwarda suka biyo layi haka muke hango su daga sama, ga teku mae fitar da iska lafiyayyiya yana kusa da mu saena tuna da Bur Sudan a inda muke bara muke kwalfo ruwan gishiri muna wanka da wanki muna barar kifi, yau gamu a Bur Dubai wancen duhun ya zama haske takalmanmu da yake tsinkewa mu daure da leda saboda yashi yanzu anan sae dai motoci su zagaya damu tsakaninmu da ruwa sai dai mushiga jirgin ruwa ta tuka mu shakatawa, gasashen kifi a faranti turawa zasu kawo mana cikin ladabi su ajiye mana.
Shi ne nake mai godiya da Allah da Ya yi mana wadannan sauyi. Duk inda ka ji balarabe ya ce bur, to tsallake ruwa ne, don haka nake godewa Allah da Ya rubuto min rayuwa ta a kusa da ruwa inda na ke shakar sanyayyar iska wacce take fitowa kai tsaye daga cikin ruwa duk a cikin ni'imomin Ubangiji ne. Maganin yunwa da talauci ruwa ne duk sanda aka rasa ruwan sama an rasa amfanin gona, idan zuciya tayi zafi, masu iya magana cewa suke yi, "a yayyafa mata ruwan sanyi."
Mambela ya tuntsure da dariya ya ce, "duk me ya kawo wadannan maganganun? "
Kaltum ta yi fari da ido tace, "idan Allah Ya yi wa mutum wata ni'ima ya kamata ya gode ma Sa, gobe se Ya kara masa wacce ta fi ta da."
Mambela ya gyada kai, yace "gaskiya ne sai wace ni'imar Ubangiji Ya yi miki bayan wannan? "
Kaltum tayi dariya ta langwabar da kai ta kashe murya ta ce "daga cikin ni'imomin da Allah Ya min, Ya azurtani da miji na gari, mai son ya ga farin ciki na, sai nima Ya jarabe ni da tsananin son sa har na ke ji a jiki na, ba zan iya rayuwa ba idan ba ya nan.
Idan baka manta ba, a shekarar da ta gabata, tafiya ta kama ka zuwa Abu-dahabi har ta tsawon KWANA ASHIRIN DA HUDU, sai na ji na damu, tun ina daurewa har ya kasance ruhina ya tafi Abu-Dhabi ranar da ka yini baka kira ni ba, nima na rasa ka a waya, sai na fara tunanin me yasa mambela be damu da ni ba?
Sai na fara tunanin ko dai, GANGAR JIKIN SA NA AURA, na fashe da kuka na dauki gyale na zan fice daga gidan don banga amfanin zamana ba inason maso wani har naje kasa saina tuna YARENA ADDININA bazan iya fita bada izinin mijina ba idan wani abu ya sameni a titi INA RUWAN WANI babu wanda yasanni bubu mai taemakona don haka na dawo gd na zauna nayi tagumi ina tunani naga dai KAI KAFI CANCANTA ka ce to ni daga cikin wannan hali dana shiga kuma kai kadai nakeso a rayuwa tamkar na taabu na shiga daki na canja kaya na caba ado da wannan tsadaddan leshen daka siya min na saka gyale da takalmi mae tsinin gaske, baya ga jan baki da hoda dana rambada na dubi kaena a madubi naga nayi kyau matuka na juya zan fita falo a tunanina kana can in nuna maka kwalliyar sai na tuna ashe bakanan sai nayi turus nayi kwalliya a dawa kenan babu mai gani na, wannan shine ADON DAWA sai na sulale na fada akan gado na goge kwalliyar na rusa kuka mai tafe da hawaye sai na naji wayata tana ruri a falo na ruga da gudu na dauka sai na duba nace a raina mambelane ina amsawa sai na jika kace ke bude min kofa na shigo gani a bakin kofa,
ina bude kofa sai na ganka, dan farin ciki bansan sanda nayi ihu nayi tsalle ba ina maraba da dan ADON DAWA.
mambela yayi dariya yace lalle kin iya hausa bayanan naki sunyi min tsauri ashe har yanzu da saurana ban koyi hausa ba dole sai na nemi sabon littafin nan wanda zai fito kwanan nan acikin 2011 din nan duk KYAN TALKALMI a kafa ake takawa don in sake koyan hausa.
sai dukka suka tuntsire da dariya suka kama hannu suka shiga cikin gida asuba ta gari kaltumbela.
.
KARSHEN LITTAFIN ADON DAWA
ALHAMDULILLAHI,
Sannan ina mai kara godia ga mace mai kamar maza wacce tayi na mijin kokari wajen ganin wannan littapin ya tapi gaba a wannan gida, wato Sadin Mama,
Wannar baiwar Allah ita ta dauki nauyin mana typing, Allah Ya saka mata da alkhairi Ya biya mata bukatun ta na alkhairi.
Aamiin.
Sai kuma sakon gaisuwa na xuwa ga daya daga cikin admin namu Aishat Gada, wacce ita ta kara sa min son littapin nan kapin na karanta shi,
Akwai kuma members na gidan nan wanda suka bada gudumowa na comments da likes da share, duk ina ganin ku wanda lokaci baxai bani damar irgo sunan ku ba,
Ina mai kara mika godia ta a gare ku matuka wajen kokari da kuka yi dan ganin littapin yaci gaba a kullun da bakwa gajia da comments.
Sannan ina mana patan alkhairi baki dayan mu, Allah Ya sa mu dauki darasi masu kyau daga ciki, Ya tsare mu da marassa kyau,
Allah Ya tsare mu da kunci na rayuwa Ya kare mu da shiga hali marar kyau, wanda suke ciki Allah Ya pitar damu.
Aamiin.
Kada dai ku manta ha'ila yau.... Bayan xabe aure na da Shahida.
Sai kuma Allah Ya sake hada mu a wani littapin na gaba....
Sadiya Abbas
Abbas Sadiya. 👫
Table of Contents