Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

PART 29

Adon Dawa Book 1 Complete Hausa Novel 15,271 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

.
kamar bola, yanzu kaltum kika kasa daukar shatar mota kitaho bur sudan inyaso inkinzo nabiya ko nawane?

kaltum ta dago da sauri ta dubi fatsuma yayinda fatsuma tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa gami da haduwa da matsananciyar faduwar gaba kada kaltum ta fadawa mambela cewar ita tasace mata kudin tafiyar,

kaltum tamayar da kanta kasa batare datace
komaiba ya juya ya dubi fatsuma yace akwai wani chemist ne anan kusa dazasu dinke mata wannan ciwon?

fatsuma tace akwai sai dai da dan nisa.
mambela ya dubi kaltum duba na tausayi hade da kulawa da tsansar so da kauna ya fada cikin laulausar murya zaki iya takawa ko muje mu taho da masu chemist din?

ta langwabe cukuikuyeyyen kan nan nata tace zan iya tafiya, tayunkura zata mike tsaye mambela yacewa fatsuma yimaza ki riketa karta fadi.
fasuma ta cafketa ta taimaka mata ta mike tsaye yayinda ta shiga tsakanin hannun ta suka dinga takawa a hankali mambela na binsu abaya ransa yana matukar baci idan ya dubi jikin kaltum da kayan jikin ta,
saiyaji tamkar ya kurma ihu, taya akayi yana
raye aduniya kaltum tazama haka?
menene anfanin dimbin dukiyarsa tunda kaltum na nan abincin da zataci ma ya gagareta?

sunyi tafiya mai yawa sannan suka shigo gari suka isa wani chemist karami da sukaga girman ciwon sai suka ce bazasu iya dinkewaba gara sukaita asibiti,
mambela ya tambayesu a inane asibitin?

aka kwatanta masa asibitoci guda biyu,
daya na yaku bayi daya kuma na masu hannu da shuni ne amma kowanne sai anshiga mota,
suna fito daga chemist mambela yatare musu taxi yashiga gaba su biyu suka shiga baya babban abunda yabashi mamaki shine yadda ya hasko fuskokinsu ta madubi suna murna suna dariya sai rade sukeyi suna kashewa da hannu,
Ya rasa dalilin yin hakan bayan dazunnan suke hawaye ko bayan fitowarsu daga chemist kafin su shiga mota, yakasa daurewa dai sai ya juya ya dubi fatsuma yayi murmushi yace fatsuma murnan me kukeyi?
Ki fada mini gaskiya don nima na taya ku murna,

kaltum tayi sauri ta kiftawa fatsuma ido alamar kada tafada, sai fatsuma ta tunsire da daria tace ba komai,
mambela yace kaltum ce ta hana ki ki fada ko?
Ai naganta tana kifta miki ido ki fada min gaskiya babbar suna ne garekifa masu sunanki basa karya,
fatsuma tace to bari na fadi gaskiya murna mukeyi saboda yau munshiga moto don rabonmu da mu shiga munfi shekara uku tun sanda muka taho daga nigeria, saidai muga ana hawa bamu taba hawa ba, duk inda zamuje saidai muje da kafa....
kaltum ta ririketa saida ta tona musu asiri,
mambela da direba suka kwashe da dariyar da basu shirya ba, direban ya juya yadubesu dan lekensu ta madubi bai isheshiba gara yasake duban kyauyawan nan ya juya ya dubi mambela yace yan Nigeria ne ko?
masu shigowa sudan da niyar tsallaka ruwa su shiga jidda suke zube wa akasarnan suna wahalar tsince-tsince da bara daman ina sukaga kudin shiga mota wani aiki zasu makane ka dauko su?

Nan da nan mambela ya tsuke fuska yace wadannan ba irin almajiranda kake fada bane daya matata ne dakuma kanwata,

sai direba yayi shiru bai sake cewa komai ba yayinda kwakwalwarsa ta rude yace aransa yaya za ayi yace wadannan yammatan jininsane alhali yanayinsu ya bambamta kana ganinsa kasan dan sudan kana ganinsu kasan yan nigeria ne daga ganin jikinsu kasan almajiraine to amma meyasa zai boye masa wadannan?
tambayoyi fal a zuciyar direba saidai kash baiga fuskar tambayaba ya isa asibitin masu mulki da masu arzikin kasar ne ke iya biya saboda tsadarsa da kwararrun likitocinsu,
suka firfito yayinda mambela ya biya kudin mota sannan suka nufi cikin asibitin, haryanzu fatsuma da kaltum basu daina hada ido suna dariya ba, wannan karon dariyar shiga hadadden gini suke mai benaye kamar london,
hadaddun matayene suke shiga asibitin da yayansu da mazajensu ajere-ajere cikin sutura na alfarma da kamshin turare, fatar jikinsu jawur a simulce ko kurji daya babu balle kasamu kirci irin nasu kaltum don haka mambela ya tsayardasu ajikin wata mota ya hana su shiga yacesu jirashi anan yana zuwa,
cike da mamaki suka saya suna kallonsa ya fice da sauri wajen get ya dan jima bai dawoba sannan ya dawo rike da ledoji guda biyu ahannunshi sannan ya mika wa kowaccesu leda daya cikin sauri ku bude saiga lafaya (pink colour) mai kyan gaske da
takalmi masu kyau (flat shoe)suka zura masa ido lokaci daya, sai yayi murmushi yace kusa wannan akan kayan jikinku ku nada sunfi kyau yayinda ya masu dagun don su kimsa akan kayan da suka maka amma duk dahaka sunfito fes bakamar da ba,

yadawo sukabi bayansa har cikin asibitin,
kudi mai yawa aka karanto masa nayankan file da kudin ganin likita kawai ba ama zancen aikin da za'a mata dana magun-guna, mambela yabiya sannan aka nuna masa dakin da zasu shiga suga likita,
sanyin A.C ne da kamshi kawai yake tashi yana ratsa kasusuwan jikin su, farin ciki ya bakunci zuciyoyinsu kasancewar sun gansu a cikin yan kasa suna wadakarsu kamar kowa wanda a da basuda damar yin hakan,

kaltua ta manta da katon ciwonda ke kafanta ta biyewa fatsuma sai yake hakora sukeyi suna murna bayaga kalle kalle da tabe-taben da sukeyi saidai idan mambela zai gansu saisuyi sauri su daina su sunkuyarda kai kasa,
likita ya duba kafar kaltum sannan ya shaidawa mambela cewar zasu shiga da ita dakin tiyata za awanke ciwon a yanyanke fatocinda suka babbako sannan a dinke wajen sannan zai rubuta musu magunguna, dan haka ga takarda yaje kan kanta ya biya,
kudi mai yawa amma bashi yadami mambela ba illa wahalarda kaltum zatasha ji yake dama ace ciwon yadawo kafarsa yaji zafin kaltum tahuta, kallo daya zaka masa kasan ya shiga damuwa, jikinsa yayi sanyi kalau ya isa wajen biyan kudin da sayin magunguna sai ya saka mai sayar da magunguna agaba da tambayoyi kala-kala yaci sa'a yasamu mace mai fara'a domin tana bashi amsar tambayoyinshi harma takara masa bayani ta tabbatar masa wadannan allurai da likita ya rubuta masu kashe zafin ciwone, ko ana dinkewa bazataji zafin komaiba, sannan mambela yaji sanyi aransa ya biya kudin ya karba yakawowa likita yayinda likita da ma'aikatan jinya mata suka shiga da kaltum dauke da almakashi da tasoshi abaya ga iodine da shashshabalin, abunka da nauyin aljihunkane darajanka a yanzu sai lallashi da wasa da daria sukewa kaltum babu kyara balle zagi irin na asibitin yaku bayi ba irin wanda kalah ta kwanta ba.
aka umurci mambela da fatsuma su zauna akan wasu kujera na alfarma mambela ne zaune ya rike kai da alamar damuwa atattare dashi,
fatsuma ta lura da hakan ta nisa tace kayi hakuri zataji sauki in shaa Allahu,
mambela yaji sanyi da kalaman fatsuma sai
ya gyara zama yace bakomai fatsuma mu tayata da addu 'a Allah Ya sausauta mata,

sukayi shiru na wani dan lokaci ba wanda yasake magana sai dai bakinsu yana motsawa da alaman addu'a suke yi,
mambela ya dubi fatsuma yayi murmushi yace fatsuma naga alamar kina son kaltum, kun shaku, kin san tane dama tuntuni ko anan kuka hadu?

fatsuma tayi dariya tace anan nasan ta gidanmu daya dakinmu yana kusa da nasu tun zuwanta su kalah suka wulakantata suka hana ta abinci shine nace tazo mu dinga zuwa wajen sana'ata don itama tasamu abunda zataci,

mambela ya yatsune fuska yace menene sana arki?

Fatsuma tace kasuwan markadi muke zuwa da sassafe a lokacin da ake sauke kayan miya kwando-kwando ana ciccire masu kyau ana zubar da rubabbu, idan an zubar mukuma sai mu dinga tsintar masu saukin rubar mu wanke muje kasuwar adare mu sayar mu saya abinci.

mambela ya dafe kai yayi shiru don tausayawa takaici ya isheshi can ya dago ya dubi fatsuma fuskarshi cike da damuwa yace kinyi maganan wata kalah da ta wulakanta
kaltum ta hanata abinci wacece kalah?
kibani labarin kaltum kakaf a Khartoum tun daga ranarda tazo Khartoum har rana irin ta yau dana ganku abayan gari naje gidanku na iske yansanda suna kame wai meya farune ?

Fatsuma ta gyara zama ta fayyacewa mambela rayuwar kaltum kakaf a Khartoum bata boye masa komaiba tunda bata boye masa sace kudin kaltum datayiba ai bazata boye masa wani abuba,
hawayene ya dinga digowa daga idanuwan mambela saboda tausayin abar kaunansa kaltum,
tambaya daya yasake yiwa kaltum da alama ita tafi tsaya masa arai itace game da ABBAS,
yace kin tabbatar kaltum batason Abbas ko kadan aranta?

fatsuma tayi mamakin wannar tambaya nasa tabashi amsa cike da tabbatarwa kaltum batason Abbas kokadan duk da irin nacin da yayi da irin lallabata danayi ta yarda amma taki yarda don hakane ma yafara takura mana, har yasa aka hanamu tsintar kayan miya shinema ya dinga turen ya sanda gidanmu don akoremu, yaji haushi kaltum bata sonshi,

mambela yayi murmushi ya juya ya dubi fatsuma yace kinci sa'a da kaltum bata yarda taso Abbas ba duk lallabata dakikayi saboda nasha alwashin takurawa duk wanda yayi kokarin raba ni da kaltum.

fatsuma taja da baya atsorace tana rawan jiki mambela yayi dariya yace kada kiji tsoro babu abun da zan miki yanzu amma da ace da kika lallabata tayarda taso Abbas da ina mai tabbatar miki da gaske har Abbas bazan raga muku ba,
don saina nemoshi koshi wayene kuma kodawa yake takama.

su dukka sukayi shiru nadan lokaci sai mambela yasake dagowa ya dubi fatsuma yace kaltum bata taba baki labarin wata mata Madina a bur sudan ba?

fatsuma ta gyada kai ta fada cikin fargaba tace tabani labarin Madina.
Yace AlhamduLillah tunda kinsan shakuwa da soyayyarda ke tsakaninsu da taimakonda Madina tayi wa kaltum a irin zamansu dakowa takanshi yakeyi ina girmamata kuma ina matukar kaunar duk wanda yake kaunar kaltum kamar Madina amma yanzu bana raga mata ko kadan saboda sanadin da tayi na rabani da kaltum.

fatsuma tayi caraf tace kayi hakuri bansaniba da farko amma daga ranarda kaltum tafadawa Abbas cewar yarabu da ita, ita da mijinta a bur sudan mai suna mambela tundaga ranar bansake takurata ta kula shi ba, shima daga ranar ya tabbatar akwai wanda take so bazai sami soyayyarta ba don haka yatakura mata,

daga dukkan alamu mambela yaji dadin bayanan fatsuma saiya tuntsure da dariya yace dagaske kike kaltum ce ta furta haka da bakinta takirani da sunan mijinta?

fatsuma ma dadi ya kamata ta gyara zama ta
bararraje akan kujera don ada a takure a karshen kujera tana gudun kar yakaimata bugu tace duk abunda nafada maka agame da kaltum ba karya bane tayi niyyar komawa wajenka Allah baiyi ba,
mambela yace tunda kika bani wannan labari mai dadi har nayi dariya tokema zansaki dariya a rayuwar ki in shaa Allahu daga yau kindaina kuka fatsuma.

farin ciki ya rufe fatsuma tafara godia tunkafin ya fadi abunda zai yi mata,
mambela ya nisa yace menene matsalarki yanzu ?
Me kike so arayuwarki?
kinaso kikoma kasarku Nigeria inbiya miki kudin mota kokuwa a Khartoum kike son zama nabaki jari?

Fatsuma tayi caraf tace nafiso nazauna a Khartoum inyi aure ni da mijina mutara kudi mu tsallaka saudiya saboda abun kunyane yanzu in koma garinmu babu hakorin Makkah, ace banje saudia ba dadinta ma nakoyi larabci a sudan, idan suka ji ina larabci wasu zasu yarda amma kuma nayi baki na rame bazasu yarda saudiya naje ba.

mambela yayi dariya ya girgiza kai yace yaranta mai dadi, nikuwa aganina babu gatanda za amiki kamar asaki a mota kikoma wajen iyayenki sune gatanki sai kiyi aurenki a mutunce.

fatsuma tace ai saurayina da nake bala'in so musa anan garin yake yace bazai koma nigeria ba saiya koma makka don da niyyar haka yataho.
mambela yace shima dan garinku ne?

fatsuma tace shi dan maigatarine nikuma yar
malam madorine duk acikin jahar jigawa muke bamuda nisa.

mambela yayi shiru kamar mai tunani can ya
nisa yace tunda haka kikafiso bari nafara ganin sa tukunna sai inji a ra'ayinsa game da shawarar da kikayanke idan naga yanada hankali kuma yanason auren sai kuyi ku zauna inbashi jari ya rike ki in Allah yasa kuntara kudi saiku shiga makka.

fatsuma ta kwashe da dariya tace bari inkirashi awaya ma yazo yasamemu anan asibitin, nasan yanzu yataso daga gun aiki.

mambela yace har aiki yakeyi kenan aibakuda matsala ma sosai.

fatsuma tace eh dako yakeyi akasuwan markadi anan muka hadu bari na kirashi ka ganshi ta zaro wannan gwabjejiyar wayanan ta ta wanda sai andaki bayanta take kawo wuta takira abun kaunarta musa ta fara koro masa bayani kenan yahango ma'aikatar jinya sun riko hannun kaltum suna fitowa da ita daga dakinda akayi mata aiki dan haka yataso da sauri ya iso garesu cike da kulawa kalma daya ne ya fito daga bakin shi shine sannu ,sannu kaltum da ciwon har yanzu ko ya daina?
da sauki tafada a kunyace

fatsuma ta taso da sauri ta rike hannun kaltum suna hada ido sai suka tuntsure da dariya wannan dariya tasu tabawa mambela mamaki dominshi ya rasa abun dariya anan.
magunguna cike da leda ya saya mata suka dunguma suka fito daga asibiti,
tafiya sukeyi ahankali saboda dingishinda kaltum keyi, fatsuma na rike da ita mambela kuwa a gabansu yake yana tafiya a hankali suna isa bakin titi sai mambela ya nufi wani katafaren kanti a tsallaken titi, su dai suna biye dashi suna jiran suji abunda zai fada musu suka shiga ciki sai suka iske kata faren waje ne a lailaye da tiles fari mai dauke da teburi kashi-kashi masu kujera hurhudu a
kowani teburi fulawowiyi ne a kowace kusurwa ga A.C mai sanyi da fankoki kana tura kofar gilashi sanyi da kamshi ne zai bugi fuskarka, da alama kamshin abinci ne na alfarma ke tashi,

ma aikata suka taresu da fara'a yayinda aka
nuna musu wajen zama suka zauna doguwar
takarda aka mikamusu mai dauke da hotunan abinci kala-kala da sunayensu da farashin ajiki ma'ana su zabi wanda sukeso sai akawo musu,
mambela ya zaba ya nuwawa ma'aikaciar, sannan ya mikawa su kaltum,
fatsuma ta zaba, kaltum kunya ya hanata ta zaba don haka mambela ya zabar mata, shinkafa da taliya mai tiriri aka fara kawowa farati uku sai ga farantin miya kala-kala, kifi ne a bankare game da wasu dakwalen kaji sun yi rashe-rashe akan faranti , salad ne hadadde gami da kayan marmari a yanyanke wato fruit salad . lemuna (freshe juice )a kofuna aka kawata shi da tsinken tsotsa.

kamar a mafarki haka sukejin kansu yayinda
farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu,
mambela da fatsuma basu jira komai ba suka fara ba cikinsu hakkinsa yayinda nauyi da kunya ya hana kaltum ci ya juya ya dubi fatsuma yace me ya hana kawar ki cin abinci ?

Fatsuma tayi dariya tace tun dazu take taka min kafa tana mintsinina wai intashi mu
chanza tebur ba zata iya ci a gaban ka ba,

mambela yayi dariya ya dauki farantin abincinshi ya canja tebur ya juya musu baya
sannan kaltum tazage ta dinga tura abincin nan, kasancewar da dad'addiyar yunwa ce atattare da ita rabonsu da cin abinci tun na jiya da rana basuci ba suka kwanta da safe suka farka da gagarumar rigima a gidansu, don haka da kyar suka tsira babu zancen nemo na karin kumallo,
suka ci suka yi nak duk cikinsu babu wanda bai yi cinda da kyar yake juyiba.
mambela ya biya kudi mai dunbim yawa saboda restaurant ne mai tsadar gaske yana daya daga cikin wajen cin abinda yake tashe a babban birnin Khartoum,
kai saye bakin titi suka nufa a inda suka tsayar da taxi suka shiga suka zauna kamar dazu,
mambela ke zaune a gidan gaba ya juyo ya
dubi fatsuma fada masa sunan anguwanku da mu saukeki, nida kaltum zamu wuce tashan jirgin kasa zuwa bur sudan,

cikin fargaba ta dafe kirji tace '' yanzu da kaltum zaka tafi yaya zanyi ni kadai?

sai hawaye ya surnano daga idanun ta, kaltum kuwa farin cikine mara misaltuwa ya kamata sai itace tafadi sunan anguwan domin fatsuma ya hanata magana, kaltum ta dafata tana lallashinta game dayimata tayi idan tanaso ta biyosu ta kaura bur sudan suje cen suyi zamansu,
fatsuma ta girgiza kai cikin harshen hausa tace aure zamuyi da musa bari ma insake kiransa awaya kafin ku wuce yazo kofar gidanmu su hadu da mambela, yace yanason
ganinsa zaiyimasa zancen auren mu idan da gaske yana son aurena mambela yace zai bamu jari mu zauna,

farin ciki ya rufe kaltum ta mika mata hannu suka tafa ta ce ai shikenan tunda duk muna tare anan, kizo nima inzo,
fatsuma tayi murmushi dadi ya lullubeta tazaro wayanta ta bugawa musa kafin tayi magana yace na shirya ganinan zuwa wanne asibiti zanzo yanzu?

fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,...
.
Allah sarki, har mambela ya bani tausayi, yadda naga yana ta rawar jiki akan kaltum bai sai ina dap da kwace ta ba..
Yayi abu mai kyau tunda yana kiwata min mata 😊 😊.
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 30.
.
TRUE LIFE STORY.
.
fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,
suka isa kofar gida yayinda mambela da direba suka tsaya a mota, fatsuma da kaltum suka nufi cikin gida harsun kusa shiga gida mambela yayi kiran sunansu suka waiwayo atare sai suka ga mambela ya tunkaro inda suke,
suka tsaya suna dubansa suna mamakin Kiran, yakaraso inda suke yace kaltum ki shiga kiyiwa mutanen gida sallama kifito mu tafi kada mu rasa jirgi, duk tarkacen kayan nan na tsummakarai kibarsu zan saya miki wasu a can,
kaltum da fatsuma suka hada ido suka tuntsure da daria,
kaltum ta ce wanka zanyi da sallah kawai na fito,
mambela yace nidai bazan sallami direba ba bari inje nima inyi sallar azahar kafin ki fito...
kafin mambela ya rufe baki fatsuma tace lah ga musa yazo kuzo mu gaisa, musa ya karaso inda suke gami da mika wa mambela hannu suka gaisa, musan sun kuwa dace da fatsuma dai-dai gajere bakikirin shan koko daukan rai shine wanda takeso duk duniya bata ganin ko wanne namiji da gashi sai shi, shine gwaninta, musa babu kamarsa musa ya mikawa mambela hannu suka gaisa duk da fatsuma ta fara masa bayani amma bai gama fahimta dukka ba don haka sai ta fara kara masa bayanin tunda gashi ga mambela, wata murya ne abayansu akace yauwa ga kaltum din don haka dukkansu suka waiwoyo atare cike da mamaki,
mariya sukagani daya daga cikin yan dakin su kaltum tare take da wasu dattijai guda biyu mai kiba da siriri senye suke da manyan rigunan malum-malum da alama dai hausawa ne, tafiya suke suna sabe riga suna sauri kamar zasu kifa da kasa, da alama awahale suke mariya tace kaltum ina kika shiga wadan nan mutanen tun tsafe suke neman ki?

kaltum ta dubesu cike da mamaki amma bata san su ba don haka sai ta zura musu ido tana sauraro taji meke tafe dasu haka mambela ya sankare a tsaye yana sauraronsu kafin su yi wata magana sai wayan mai kibar ta fara ruri yayi sauri ya duba sai ya latsa gami da cewa AlhamduLillah ga kaltum din muna tare da ita sai yanzu aka nemo mana ita, rike wayan ya mikawa kaltum waya ta mika hannu ta karba a sanyaye kafin ta daura a kunne sai ta kalli mambela ya gyada mata kai alamar ta amsa sannan ta daura waya a kunne tana sauraro batare da tayi magana ba, kaltum ta zazzaro ido ta dafe kirji da alama zuciyarta ce ta buga saboda mummunan firgitan da tayi, kan kace kwabo ta fara karkarwa idanunta ya kawo nan take su zatonsu mutuwa aka fada mata, mambela ya fada cike da damuwa cikin larabci kaltum lafiya dawa kike waya?
meyake faruwa?

Ta katse wayar da sauri dan gigicewa ta fashe da kuka.
yaya kika kashe wayan bayan baku gama magana ba?
inji katon mutumin ya karbi wayan ya sake latso lambar ya mikawa kaltum a fusace ya fada cikin fushi ki amsa waya malama ana nemanki tun tsafe meyasa zaki kashe wayan?

ta karba ta sake karawa akunne haryanzu batayi magana ba sauraro kawai take mutuminda yake mata magana awaya ya sake magana yace hello kaltum kina ji kuwa?
ni ne alhaji Adnan daga kano kitattaro kayanki ki biyo wadannan mutanen yau din nan ku taho Nigeria, nabasu kudi zasuje office din immigration ayi miki passport ku hawo jirgi ku taho gida kinji na fada miki kada ki yarda ki sake subucewa a rasaki arasa yan aike.

kaltum ta juyo ta dubi mambela ta cigaba da sauraron abunda alhaji Adnan yake fada yayinda tashiga rudani mai yawa takasa tantance yanda zuciyarta ta karkata, saboda tana matukar son mambela tanaso ta zauna dashi don tana da kyakkyawar zato akansa zai riketa amana, ta yarda da tsantsan sonda yake mata saboda Allah haka bataso ta sabawa alhaji Adnan a matsayinshi na mutum da yake kulawa da ita wanda bayaso yaga ta tozarta, mutuminda yake ta salwantar da dukiyansa wajen kokarin nemota ta dawo gida, ya damu da ita kamar yar da ya haifa ta cikinsa shine cinta da shanta iliminta da lafiyarta, magana yake mata cikin damuwa da fargaba don kada ta subuce..

kwakwalwar kaltum ta dinga jujjuyawa a kokarinta na tantance da tattace abunda zaifi alkhairi a rayuwarta don gudun fadawa dana sani nan gaba, sai ta tuno kyakkyawan kulawa da alhaji Adnan ke bata tasan tabbas idan ta koma Nigeria makaranta zata koma ta karasa sakandari harzuwa jami'a, babban burinta kuwa a rayuwa shine ta ganta a jami'a ta hada digiri amma data tuno halin ko inkula da iyayenta ke mata da irin gallazawa irin na goggo fattu da take mata don kadan daga cikin halin goggo fattu ta dawo daga makka tace zata dauketa sukoma makkah iyayenta kuwa ko musu bazasuyi mata ba yarda zasuyi,
sai ta dubi dayan bangaren kuma wato mambela mutum ne mai kyauta da kyautatawa yana sonta yana bata duk abunda takeso basai ta roka ba sannan ta tuno rayuwarta da madina a bur sudan rayuwar yanci dajin dadi wasa da dariya da tsalle-tsalle, abinci ya wadata babu yunwa ko kishir ruwa tace aranta bazan koma Nigeria ba gara ingama rayuwata a bur sudan...

alhaji Adnan ya katse tunaninta data tsunduma tanayi yace kaltum magana fa nake miki bakice dani komai ba?

cikin kuka da sanyin murya tace na'am dady,
jin muryan kaltum ne yasa alhaji Adnan doguwar ajiyar zuciya game dayin hamdala a cikin zuciyarsa domin sai yanzu dayaji muryanta ya tabbatar da cewa da kaltum dinsa yake magana saboda yana kokonto ko ba ita bace, ya yi farat ya mike daga luntsimemiyar kujerar daye juyi a babbar offishinsa dake Abuja babban birnin tarayyah yafada cikin zumudi da farin ciki kaltum kece ?
To naji dadi yanzu abunda nakeso dake shine ki biyo alhaji sa'adu da alhaji jabiru ku taho nigeria sauran bayanai in anzo za ayishi wahala da gallazawa da su Fattu suke nuna miki a da ya wuce rayuwa ce mai kyau da kyanciyan hankali zaki samu a Nigeria, me zakiyi da rayuwar wahala har bara akace kinayi ni, alhaji Adnan ina raye a duniya kaltum kiyi bara?
InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un..
sai kaltum ta fashe da kuka ta girgiza kai tace daddy ka yafe mini banyi niyyar saba maka ba, nasan kokarin da da kayi akaina amma bazan iya dawowa Nigeria ba, yanzu zanbar Khartoum inkoma bur sudan inda nafi sabawa dasu zan auri mambela domin shine mai taimakona..
acan alhaji Adnan ya dafe kirji yafada cikin gigita kaltum waye kuma mambela ?

Kaltum ta sharce hawaye tace mambela dan ADON DAWA.
ne alhaji Adnan ya sulale yayi zaman dirshan a kafet yayinda yasa hannu ya fisgo hulan kansa don tayimasa nauyi a halin yanzu wayar ya ajjiye a gabansa yana duba batare dayasan abunda zai yi ba, ji yake tamkar ya huda wayar ya ganshi a Khartoum kusada kaltum ya damkota ya dawo da ita gida, zufa yaketa hadawa duk da babbar rigace a jikin sa ai akwai sanyin split A.C a offishin,

tsabar tashin hankaline kawai kaltum ta mikawa mai kibar wato alhaji sa'adu wayansa ta koma bayan mambela ta labe har yanzu mambela acikin rudani yake don bai tsinci kalma daya ba a cikin duk wannan bayani da akeyi ba, ya juya ya dubi kaltum cikin harshen larabci yake tambayanta wai meyake faruwa ne?

saita rushe da kuka yayinda kukanta yake sake daga masa hankali.

alhaji sa'adune ya duba wayarsa har yanzu sekonni na tafiya ma'ana alhaji Adnan yana kan layi saiya kara wayar a kunnensa ya dinga magana sautin maganan ne ya ankarar da alhaji Adnan cewar su kaltum nakan layi basu kashe ba, saiya rarumo wayar ya kara ta akunnensa muryan alhaji sa'idu yaji yana magana, alhaji sa'adu yace yanzu ranka ya dade haka za a kyale yarinyar nan tayi abunda ta ga dama ?
Mufa da muke zaune a sudan mu mukasan wahala da wulakanci da mutanen mu suke gani,
alhaji Adnan yayi tambaya cikin fushi wai wani irin yare takeminne naji tace mambela zata aura kuma wai daga ADON DAWA anya kuwa ba aljanine ya auri yarinyannan ba domin a bil'adama babu mai suna mambela kuma aduniyan nan kakaf ban taba jin wata kasa ADON DAWA ba saidai in a garin aljanu, don haka kuriketa kada tashiga daji bada mutum take zama ba.

alhaji sa'adu yayi dariya ya subuce masa yace ranka ya dade mutum ne mambela, ADON DAWA kuwa kabilarsu ce, a bur sudan suke.
alhaji Adnan yace kai ya akayi ka sani ?
kana ganin mambela da idonka ko itace take fadamaka ?

Alhaji sa'adu yace ina ganinsa alhaji.
"alhaji adnan yace ka tabbata shi mambela datake fada kana ganinsa?

Alhaji sa'adu yace tabbas mutum ne saidai idan kuka kuskura kuka bar yarku ta auri wannan dan ADON DAWAn to mu'amalanku da ita har abadah, a cikin dawa suke rayuwa gidan katako da 'kaya, abincin su dabino da madarar shanu ce kawai.
hankalin alhaji Adnan yakara tashi baisan sanda ya yaye babbar rigar sa ya wurgarba ya mike saye yana magana cikin daga murya da dukan bango har ma' aikatansa suka dinga rugowa a guje zuwa offishinsa don suga abunda yake faruwa sunsan ba lafiya ba, basu tabajin yana irin wannan hayaniya ba da daga murya kasancewar mutum ne mai sanyin magana cikin kamilalliyar murya, mutum mai hakuri da fara'a yau bacin ran kaltum yana sashi ruri tamkar zakin da yaga nama,
alhaji Adnan yace alhaji sa'adu da kai da alhaji jabiru nabaku amana kuma kun karba nace ku yanke da kanku yawan kudin da kukeso da kanku kunyi kokari kunnemomin kaltum kamar yanda kukace inyi zamana basai nazo ba zukuyimin komai gaku ga kaltum ga kuma aljanin saurayin ta mambela kuna tare ni ina Nigeria sannan zaku dinga tambayana abunda zakuyi?
alhalin kunsan ra'ayina shine ku kawo mini kaltum gida ko tana dariya ko tana kuka duk yanda zukuyi kuma duk yanda za ayi karkubar kaltum ta subuce muna bukatarta anan, idan kwatarta zai muku wuya to ku kira yan sanda su kaiku kotu a fara shari ' ah nikuma kan a gama zanshigo sudan din ayi dani kungama aikinku.

alhaji sa'adu ya tuna makudan kudinda alhaji Adnan yayimusu alkawari mai dumbin yawa sai jikinsa ya hau makyarketa kaikace dan taure ne.
yace alhaji Adnan kwantar da hankalin ka daman ra ayinka nakesonji ko ka canja kuma ina neman izini kar rigima ta kwabe kace baka sani ba ace mana mu masu satar mutane ne hukumar sudan kuwa tanada zafafan hukunci akan masu aikata irin wannan kazaman laifi, kabani nanda minti goma zan sake kiranka kaji halinda ake ciki sannan suka kashe waya.

mambela ne ya fusata ya damko gashin kaltum ya wujijjiga yana magana cikin gigita dazubo da hawaye mai yawa yace kifamin abunda yake faruwa anan kunzamar dani mushe a tsaye bansan meyake faruwa ba kuma gashi sai anbaton sunana akeyi wai shin laifi nayi dana baro garinmu nafito nemanki a Khartoum don in ceto rayuwarki da kuma nuna miki kaunar da nakeyi?

kaltum ta rusa kuka harda kurma ihu kaikace rai ake fitar mata,
fatsuma ta karaso da gudu ta kwaci kaltum a hannun mambela abun mamaki saiyaga fatsuma kukan takeyi sannan ta fara yi masa bayani abunda yake faruwa,
data kira sunan alhaji Adnan sai ya tuno da sunan wato kishiyarsa don haka sai yayi shirin gagarumin rigima a zuciyarsa yasan yau za ayi dayan biyu koya kashe ko akasheshi wajen kwatar kaltum,
sai yayi wani irin dariya mai ban mamaki ya juya yadubi kaltum wanda har yanzu tana rungume ajikin fatsuma yace kaltum kije kishiga cikin motar can taxi ki zauna gani zuwa..

jikin kaltum na karkarwa ta juya aguje ta nufi inda motar take yayinda alhaji sa'adu ya cire babbar rigarsa ya hada da hular dake kansa ya wurgar akasa ya damkara da gudu ya damko kaltum ta baya saiya fisgota tamkar kaza saboda rashin nauyi..
da mambela yaga haka sai ya fusata ai ko sekon daya ba karaba ya kaiwa alhaji sa'adu wani dankareren naushi a hanci yayinda jini ya wanke masa fuska nan da nan ya saki kaltum ya rike hanci ya durgushe.
da abokinsa alhaji jabiru yaga haka sai shima ya ya fisgo hannun kaltum ya tura keyarta cikin gidan su,
mambela ya yunkura zai hana sai alhaji Sa'adu ya mike a fusace ya cafki mambela da dambe...
.
Yayin da ni kuma Dan Aunty na tsaya kallon mafadata akan abar kaunata,
Wannan shi ake cewa '' kura da shan bugu... ''
A gama komai nazo na aure ta, shi kenan.
.
Sai kuma wani satin xaku jimu dauke da ci gaban .
.
Saady Dan Aunty 👫.ADON DAWA 31
.
TRUE LIFE STORY
.
jama'a suka farga kan kace kwabo an shiga tsakaninsu,
mata da maza sun firfito, masu wuce a kafa, babura ,keke da masu motoci duk sun tsaya kallo da neman ba'asi don a sulhuntasu,

zage zage ake tsakanin mambela da alhaji sa'adu yayinda dukkansu jikinsu na tsuma sunaso a sake su su kaure, zuciyoyinsu sun hargitsa karfine yazo musu yayinda hannayensu ya hau kaikayi, naushi kawai sukeso sukaiwa junan su,
larabcine ke tashi inda mambela yake dukan kirji yana cewa kaltum tasa ce babu mai dauke masa ita,
shima alhaji sa'du yana ikirarin baban yarinya ne mahaifi yasa a dauko masa ita don haka duk kotun da za aje sai dai aje amma bazai bar kaltum ta subuce masa ba, bayan watanni shida da suka kwashe suna nemanta a Khartoum gida-gida,

malam Abdulkadir aka kira ya fito daga gidansa da sauri hankalin sa atashe ance yazo ana wani fada a kofar gidansa,
dazu mata ne yanzu kuwa maza ne ke casuwa ransa abace sai karanto InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un yake, yana ta jan dogon carbinsa, yana karasowa ya dubi mambela ya juya ya dubi alh.sa'adu yaga babu wanda ya sani a cikinsu, sai bacin ransa ya fadada cikin harshen larabci yace kukuma su waye daga ina ku kazo kofar gidana kuna dambe?
Dazu yan sanda sun zo ana can ana shari'ar fadan dazu ba a gama ba yanzu ma an ce antafi kira suzo su iske a kofar gidan ne kuma ?
Yanzu daman abun alkhairi zai zama sharri?
don nace duk mutanenmu wadanda ba su da gida suzo su zauna kyauta sai in zama abun tozartawa a garin nan?
sunan gidana ya shiga tsinuwa a bakin jama'a ?

Alhaji sa'adu ya fara jawabi cikin harshen hausa ya yiwa malam dalla-dalla akan abunda ake ciki

Kowa ya gamsu don haka kobin ta bakin mambela ba ayiba malam ya yanke hukunci nan take kaltum baza tabi mambela ba, kasarsu za a mayar da ita domin shima babban burinsa kenan, duka manyan matan nan da yammata da kananan yaran dake zube a gidansa su wa kansu fada su koma kasarsu cikin gata da yancin kai.

kaltum tanajin haka saita kurma ihu ta fadi tana kuka, fatsuma na riketa itama kukan take taya ta, sauran matan gidan kuwa hayaniya sukeyiwa kaltum suna dungure mata kai suna cewa keba dadinki bane da har kika sami iyayenda suka damu dake su aiko a daukeki ko ba kece mai kuka da ihuba a sanda kalah ta karbi kudin iyayenki ta arce ta bar kiba?
Me ya yi miki zafi da zaki koma bur sudan da rayuwa kauyen da babu wuta babu ruwa babu wayar sadarwa, kakaf garin babu gidan siminti sai na katako, amma ki koma Nigeria kasarki a najeriyan ma a babbar birnin kano ai kin caba don haka ki tashi kibi mutanen nan kawai.

cikin kuka kaltum tace saceni zasuyi malam bazan bisuba.

sai jikin malam yayi sanyi ya dubi Alh.sa'adu yace da kamshin gaskiya idan anbi ta barawo sai abi ta mabi sawu, ku su waye ?
Kuma daga ina kuke ?

Alh sa adu yace nima mutumin kano ne amma bazan ce muku komai ba bari na hadaku da mahaifinta awaya kuyi magana, ya latsa number alhaji Adnan nan da nan ya amsa alhaji sa'adu ya ce alhaji rigima fa aketa tafkawa yanzu haka an fasamin hanci yana jini saidai yarinyan tace bata san mu ba saceta zamuyi shine nakeso kayiwa wani dattijo bayani wanda kusan kaltum a hannunsa take don ya gamsu, a gabansa abawa kaltum waya kayi mata magana don idan ita bata san mu ba mu barayin mutane ne kai ai baza ta kiraka barawo zaka saceta ba, alhaji sa'adu ya mikawa malam Abdulkadir waya suka dade suna magana daga karshe malam Abdulkadir ya fahimci ashe kaltum jikar fattu ce, fattu kuwa tare sukayi wasa a zangon Daura .
don haka ya yarda kaltum tabi wadannan mutane,
da yan sanda sukazo malam ya kora musu bayani cewar ba rigima bace don haka basai an tafi police station ba,

mambela yanaji yana gani aka tafi da kaltum cikin gidan malam tana waiwayensa yayinda shi kuma mambela a tsaye, musa da fatsuma da mai taxi suna lallashinsa hawaye yana zuba daga idanunwansa zuciyarsa kamar zata fashe dan tsananin tafarfasar da takeyi,

fatsuma ta sharce hawaye tace da mambela yayana mambela zantaimake ka ka sami kaltum, kamar yadda baka san mu ba ba nida musa ka kudiri aniyar zaka taimake mu.

mambela ya koma ya zauna a cikin taxi gidan gaba yayinda ya jingina da kujera, ya daga kansa sama ya cije lebe wannan shine ake kira ga samu ga rashi ya samo kaltum da kyar amma ta subuce masa yana ji yana gani,

mambela ya yunkura zai tashi a fusace musa ya mayardashi,
yace da musa kabarni inshiga cikin gidan malamin nan muyi duk abunda za ayi kosu kasheni ko in kashe su saboda alkawari nayi saina lahanta duk wanda zai rabani da kaltum...

musa da direba su kayi kukan kura suka danneshi ya koma ya zauna,
sunfi minti talatin suna bashi baki sannan ya yarda zaitafi,
Su fatsuma suka shiga motar suma aka tafi dasu zuwa tashar jirgin kasa ta zuwa bur sudan,
cikin hawaye mambela ya zaro kudi mai yawa ya bawa mai taxi, farin ciki ya rufe direba ya dinga yi masa addu'ar Allah Ya bashi kaltum Ya kwato masa ita daga hannun wadancan. mambela ya amsa da Ameen ya juya ya dubi musa da fatsuma yace ina yi muku fatan alkhairi a shirin aure da kuke yi, kuma ina baku goyon baya dari bisa dari nayi alkawari zan taimake ku ba ku kadai ba ma duk wasu masoya da suke son junansu zan taimaka masu duk rintsi su auri junansu duk na sadaukar wa kaltum.....
sai hawaye ya kara kwaranya harya kasa ci gaba da magana.

saisuma suka fara kuka don tausayinsa, can ya juya ya dubi musa yace a halin da nake ciki yanzu bazai bari muyi wata magana ba
saidai kawai duk sanda ka shiryo kazo wannan tashar kahau jirgi kazo Khartoum Tutti ka gangaro bur sudan kusa da ruwa zakaga garin yan kasarku hausa, sai kace sununa maka garin yan ADON DAWA gidan sarki kokace musu mambela kake nema, ko karamin yaro ka tambaya mai shan nono indai ya iya magana to yasan sunan mambela, idan bana gida to za a rakoka bakin kasuwarmu Jim Arab nanne kadai wajen zuwa na, kazo mu zauna muyi magana game da auren ku, nayi alkawarin zancanja muku rayuwarku da izinin Allah amma da sharadi guda daya, idan har kasan bada gaske kakeson fatsuma ba yaudaranta kake kada kazo inda nake, kaga fatsuma amanace a wajanka inhar ka yarda ka aureta kaine uwa Kaine uba a gare ta, don batada kowa a kasar nan, tunda wuri ka fadamin gaskia sai inbiya mata kudin jirgi tabi kaltum su koma Nigeria.

nan take suka zaburo don tashin hankali saboda suna kaunar junansu baza su iya rabuwa ba sai su duka suka durgusa a gaban mambela suna rantse-rantse cewar zasu zauna amana,
sai mambela ya sake shiga damuwa yasake tausayawa kansa da kaltum, ku mike tsaye kada ku damu zaku zauna tare, Allah Ya baku zaman lfy da zuri a ta gari, sukace kaima Allah Ya baka kaltum ya kwatota ta dawo wajenka ka aureta da yardar Allah.

mambela ya girgiza kansa yace ada dana rabu da kaltum zuciyata ta kasa fitar da ran zanganta kuma nazo naganta a halin yanzu banji ajikina zan sake haduwa da kaltum ba har abada, nasan na rasa ta kenan ko bayan mutuwata kuka hadu da ita ku shaida mata ina sonta bazan daina sonta ba kowa na aura kuma kome na zama a wannan dunia,
kuka da hawaye yabe-yabe mambela , musa da fatsuma keyi harsuka rabu.
ya yanko tikiti yaje yahau jirgi ya zauna yayinda suke tsaye agefe suna daga masa hannu basu baro tashar jirgin kasa ba sai da jirgi ya tashi sannan suka juyo gida Jiki a sanyaye.

al amarin malam Abdulkadir dasu alhaji sa'adu kuwa suna shiga gida a falon malam Abdulkadir aka zauna aka sake mayar da magana da alhaji Adnan a waya aka tsayar da shawarar kaltum bazata sake fitowa kofar gida ba, a dakin matar malam zata zauna har tsawon kwana biyu har a gama cuku-cukun tafiya,
malam yace da kansa zai rakasu har filin jirgi yaga tashinsu.

kaltum ce zaune a falon Manal amaryan malam Abdulkadir kenan, budurwa ya aura yar kasar sudan ce,
kaltum tayi kuka ta gaji don haka ta hada kafafuwanta ta kifa kanta ta kanannade don takaici, abinci mai lfy ne a gabanta miya ce nashe-nashe da kaji masu maiko amma ko kallo basu isheta ba balle ta dandana.
Manal tayi larabcin duniyan nan wajen lallashin kaltum don ta daina damuwa taci abincin nan abu bai yiyuba, saita shiga yi mata nasiha akan to ta tashi tayi sallolin da ake binta sannan tayi addu'ar abunda yafi alkhairi.

kaltum batada mafita ita kanta tasan addu'a ce kadai mafitarta don haka ta tashi tayi sallah tana kuka tana fadawa mai duka, amma idan tayi addu'ar Allah Ya zaba mata abinda yafi mata alkhairi sau daya sai ta roki Allah Ya mayar da ita wajen mambela sau goma dan shi zuciyarta tafi so.
kaltum tana son mambela a halin yanzu tafi sota zauna dashi data koma cikin yan uwanta data zauna da alhaji Adnan abun kaunar ta.

tsowon kwana uku kaltum na cikin gidan malam daga daki sai bandaki duk inda tayi ana biye da ita ana zuba mata ido, a cikin gida ma kenan balle a kofar gida inda yake dankare da malamai da almajirai ta ina zata fice ai bazai yiwu ba, kamar yadda ba a bari ta fita ba haka aka hana kowa ya shiga ya ganta, duk irin nacin da fatsuma tayi don a barta taga kaltum ba a barta ba.

ranarda kwanaki uku suka cika a lokacin komai na tafiya ya kammala alhaji sa'adu ya iso gidan malam dauke da tikitin tafiyarsu a hannu, yazo ya nuna wa malam yace karfe takwas na dare ne buking din su,
don haka karfe shida na yamma kaltum dasu malam suka dunguma suka fito yayinda fatsuma da yan gidansu suka yo waje a guje, waje ya dauka da hayaniya cewa ake ku fito na cikin gida kaltum zata tafi...

lah kaltum tafiya zakiyi?
da dai sauran surutai irin na mata.
malam ya umurci kaltum da ta shiga gidansu ta dauko buhun kayanta tazo su tafi, sai ta girgiza kai ta sharce hawaye tace nabarwa fatsuma dukka tayi amfani dasu.

fatsuma ta kamkame kaltum tana kuka tana cewa yanzu kaltum tafiya zakiyi kibarni?

Sai da malam Abdulkadir ya hada da shauda mata carbin hannunsa sannan ta saki kaltum, dan anyi mata maganar duniyar nan ta saketa taki, malam ya dubi fatsuma cikin fushi yace wannan yarinya rawar kanki tayi yawa ke kike sake tunzura kaltum kike kara sata kuka idan bakiyi wasa ba sai na koreki daga gidana yau din nan,

fatsuma najin maganar kora saita nitsu don idan aka koreta yanzu ina zata nufa?
musan nata da take takama dashi su shidane a shago daya suke haya.
a ina za a cashe idan bikinta ya tashi inba a
makeken tsakar gidan nan na malam ba?

saita koma gefe tayi tsuru da ido, da niyyarta dama ta tubure tace saita shiga motar tabisu airport, kaltum ce ta shiga gaban taxi malam da alhaji sa'adu suka shiga gidan baya,
yan gidan suna dagama kaltum hannu itama tana daga musu yayinda direban mota ya fizgi mota,
kaltum kuwa jiniyar kukanta ta barke, malam da alhaji sa'adu kuwa sukace dawa Allah Ya hadamu inbada kaltum ba sukatayi mata surutu har suka kai filin jirgi suna cewa inbanda yarinya da rashin hankali ina za a hada zaman sudan da Nigeria?
ke a najeriyan ma yar gata ce yar gidan masu hali zakiyi iliminki asirinki a rufe ki zauna kina wulakanta kanki a nan?
daga bara sai tsince-tsince a bola.

kaltum dai tayi mukus tana sauraron su kukanne bazata daina ba.
kaltum taga yanda mata suke cin ado a filin jirgin nan na Khartoum ai sai ta raina kanta ta ganta tamkar daddawa a cikinsu duk da wannan pink lafayan nan da mambela ya siya
musu ita da fatsuma ce ta wanke ta saka takalmin ma sabo ne wanda mambela ya saya mata ga matar malam ta bata sabon siket da farar t shirt daga ciki ta saka ta cire yagaggu na da, ashe da bata carallee ba abar gudu da kyama zata zama a cikin jirgi, nan sabon brush matar malam ta siya mata ta wanke bakinta tas turare kawai bata samu ta shafaba saboda yanzu Abbas baya bata, matar malam kuma bata bata ba amma duk da haka kayanta na kamshin koren sabulu na wanki ,
ina laifinta abunda kaltum ta dinga zaiyanowa a zuciyarta kenan don haka ta saki jikinta a cikinsu bayan anyi musu screening sai aka yi bording suka shiga cikin jirgi suka zauna duk da ta taba shiga jirgi tana karama amma sai taga kamar bata taba shiga ba.
Domin ganin jirgin tayi tamkar aljannar dunia do kyau saita tsinci kanta tana mai farin ciki harda murmushi, Alh sa'adu ya juyo ya dubeta ya tabbatar murmushin takeyi ba gizau ba yayi dariya yace ja'ira waya fada miki borno gabas take?
ana so a ceto ki kina ki har kika ja wannan aljanin saurayin naki yake kokarin ya cire min hanci,

sai kaltum ta sha kunu ta tura baki don taji ya fara cewa abun kaunarta mambela mutunci.

kujeru masu zaman mutum uku ne, alh sa'adu ne a jikin wundo kaltum a kusa dashi sai wata matashiyar mata mai suna Hajir a karshe, tunda suka zauna Hajir ta dinga surnanowa kaltum larabci tana jero mata tambayoyi.

kaltum bata bata amsa ba saboda a tunanin Hajir kaltum yar sudan ne hutu zai kaita Nigeria,
Hajir ta shaidawa kaltum cewa ita yar Khartoum ce ta auri wani hamshakin dan kasuwa a kano yanzu haka kakarta ce ta rasu tazo tayi gaisuwa zata koma.

kaltum tayi murmushi tace ni kuwa yar kano ce aure ya kawo ni bur sudan mijin ADON DAWA ne mai suna mambela.

Hajir ta damke baki don mamaki tace keko meya miki zafi da zaki baro kano birnin garin
arziki ki taho sudan a sudan dinma a bur sudan?

alhaji sa'adu ya zabura yace karya fa takeyi bata da wani miji abur sudan.
sai aka hau kalon kalo tsakanin Hajir da kaltum da kuma alhaji sa'adu batare da wani yasake magana ba a cikinsu.
mamaki mara misaltuwa zaka iya gani a cikin idanuwan Hajir, ta shiga tunanin meyasa kaltum zata mata karya irin wannan alhali karyan ma bata dadi bace ?
ko kuwa wannan mutumin ne ya ke karya ?
To ko babanta ne yaje ya raba auren ya dauko ta zai mayar da ita garinsu ita kuma tana son mijin ta?
kwarai haka ne ma don daga gani kaltum anga wanda ta kwaso da talauci. abun da Hajir ta dinga sakawa kenan a cikin ranta kenan,
jirgi ya tashi ya bar Khartoum ya lula cikin gajimare da izinin Ubangiji yayinda fasinjoji suka hau tofa addu ar nan ta matafiya wacce shugaban halitta ya koya mana, '' Allahu Akbar, Allahu akbar , Subahanaanal laziii sakkhara lana hazaa wama kunnaa lahu mukrinina wa innaa ilaa Rabbina lamunkalibuuna, Allahumma innaa nas'aluka fii safarinaa hazaa birra wat tak'waa wa minal amali maa tardha ,Allahumma antas saahibu fis safari wal khaliifati fil ahlil ,Allahumma innii a uzu bika min wa,asa'a'is safari ,wa ka aabatil manzari wa suu il munkalabi fil maali wal ahali.''

yayinda kaltum ta runtse ido hawaye mai zafi ya dinga zubowa daga idanuwanta tana fadin wayyo mambela a zuciyarta.

KANO NIGERIA

misalin karfe shida na safiyyan alhamis jirginsu kaltum ya sauka a malam Aminu international airport dake birnin kano, kaltum ta shaki iskar kasarsu saita lumshe ido taji sanyi a ranta atake taji ta fara farin ciki zataga kannenta da alhaji Adnan, ta tuno mahaifiyarta sofi da mahaifinta saleh sai taji tanaso ta gansu ma, tafi kowa sauri wajen shigewa gaba don saukowa daga jirgi da fitowa daga wajen bincike akayi aka gama suka fito waje inda kaltum take duban kanawa sai hausa sukeyi yayinda suma suke dubanta a matsayin bakuwa ba yar kasarsu ba,
musamman da suka ji ita Hajir sun juye harshe suna larabci, Hajir ta rubutawa kaltum nonbar wayanta a takarda ta bata tunda kaltum ta shaida mata batada waya,
Suna tsaye mijin Hajir da ya yanta biyu sukazo daukar ta, tana murna suna murna ta shiga mota suka tafi, sha'awarsu ta rufe kaltum ta ayyana a ranta dama ita da mambela ne suka sami sukuni haka..

kinsan hanyar gidanku idan muka shiga taxi?
alhaji sa'adu ya tambaye ta,
tayi shiru kamar mai tunani, yace idan bazaki ganeba zansaka layina na MTN na shaidawa alhaji Adnan munzo aiport ya aiko a dauke mu,
kaltum da zabura tace zangane gidan, domin bataso alhaji yazo tsoron haduwarsu take yanzu, kunyan bijire masa datayi takeji domin
ita kanta tasan baikamata ya turo azo daukarta kiri-kiri tace bataso tazo wajensa ba tafiso tabi mambela ba, alhaji sa'adu ya tsayar da taxi ya shiga gaba kaltum na baya tayi tsuru da ido, fargaba ta hadu mata da farin ciki suka cakude da takaicin rabuwa da mambela, tace da direba nasarawa G.R.A zaka kaimu babu bata lokaci direba ya manna da gudu yayinda kaltum ta tsura ido a jikin glashin wundo tana duban kanawa matan su da mazansu yara da manya sai hidindimunsu sukeyi, akasarinsu fara'a garesu kuma duk sun fito neman na kansu ga kasuwa iri-iri, haka ma'aikatan gwamnati kala-kala.
babu inda yafi kasarku dadi da yanci kaltum tafada azuciyarta yayinda ta hango almajirai akan bola suna tsintar gwangwanaye, taga ba'a hana su ba kuma zuwa zasuyi susayar ba bu mai hana su saboda suma yan kasane, sunada yanci ba kamar yadda su aka saka musu takum-kumi aka tsorata su da hukuma ba,
kaltum tana nuna musu hanyan tiryan-tiryan har bakin gidan ashe bata manta ba, a tunaninta ba zata gane ba duk a akwai canje-canje a unguwar da gidan amma bata manta ba, suka firfito daga mota, kaltum ji take tamkar a mafarki data ganta a tsaye a kofar gidansu, alh sa'adu ya fito da naira dari biyar ya mikawa direba sai kaltum ta zurawa kudin ido tana kallo domin ganin kudin tayi bambarakwai ba irin na sudan ba.

Muhammad da makwabcinsu ne yafara ganinta tsohon saurayin tannan nata, da farko baiganeta ba yayi mata kallo daya ya watsar sai tayi masa dariya har ya kawar da kai gefe, saidai yasake waiwayowa ya dube ta domin fararen hakoran nan nata masu haskawa har yanzu basu dafe ba suna kyalli duk sanda tayi daria, yace kamar kaltum?

ta amsa nice, sai da yahau salati yana mamakin yadda kaltum ta zama haka kamar ba ita ba, ta rame tayi baki ta zama bakauyiya, tundaganan jikin kaltum yafara sanyi tasan tazama wata halitta ba irin ta mutane ba tunda har Muhammad bai gane ta ba kuma ya tsaya yana tausaya mata,
suka tura gate sukaji akulle daga ciki ko bude gida ba ayi ba, bugu daya sukayi saleh mai gadi ya fito daga dan dakinsa na gadi ya bude musu da sauri da yake daman sun san da zuwanta don haka yau babu wanda yayi barcin kirki a gidan yaransu da manya, daga sunji motsi sai kowa ya bude ido,
alwalar asuba kuwa sun yi fiye da sau uku sai su ga ashe assalatu batayi ba saboda matsuwarda sukayi gari ya waye suga kaltum.

kallon-kallo ne tsakanin kaltum da mahaifinta, hankalinsa yatashi yadda yaga yarsa ta fige ta zama kaza ita kuma sai taga ya tsufa.

alhaji sa'adu ya fusata yace da malam saleh
matsa mu wuce kazuba mana ido inni ba kasan ni ba ai ita kasanta idan kuma batanan aka kawoka to yar gidan ne, yar gidan alhaji Adnan ce, daga sudan muke yasan da zuwanmu,
sai yaga kaltum da mai gadi sun hada ido sunyi dariya kaltum tace kai alhaji sa'adun nan kaci ka fada, babana ne fa,
ta durkusa ta gaishe shi sai yau yataba ambaton sunanta yana rawar murya yace AlhamduLillahi, kaltum naji dadin dawowarki da kika dawo kafin in mutu, Allah mai amsa addu'ar bayinSa, ki yafe mana kaltum..

sai su dukka suka rushe da kuka malam sale yasa hannu ya tashi kaltum tsaye daga sunkuyon da tayi suka dunguma cikin gida kai tsaye boys quaters ya nufa yana kwalla kiran sunan sofi!!
cewa yake ku fito ga kaltum ta zo, sofi ta manno da gudu abunka da mara kiba tazo ta rungume kaltum kuka take ta sharba ita ma taga uwar bari ko ina kunyar fulanin nan?

yayinda kaltum taga dandazon kannenta manya da yara da wasu guda biyu bata san su ba matane amma ko ba fada mata ba tasan kannenta ne, su kadaine sukayi kama da ita sak ta rumgumesu yayinda suke rera mata wakarda suka dade suna shiryawa ta marhaba da zuwanta, dadi ya rufeta ta shiga cikinsu tana tafi itama tana amsawa babu shakka hayaniyan nan ta isa kunnen makwabtansu ma balle wanda suke cikin gida,
daga ganin luntsumemiyar motar da ke tsaye a farfajiyan gidan kasan mai gidan yana gari wato alhaji Adnan fari mai farar aniya matashin dattijo mai tumbin naira,
.
Nima Dan Aunty baxa a barni baya ba wajen waka da tapi cikin murna, tunda ga masoyiya ta ta iso babu abun da xa'ayi sai shirin bikin mu ☺ ☺...
Masu son ganin wannan gaggarumin bikin su gyara xama, marassa so su gyara idon su dan gani....
.
Saady Dan Aunty 👫.ADON DAWA 32
.
TRUE LIFE STORY
.

Alh Sa'adu ya kosa yaga Alh Adnan don yasan karshen talaucinshi yazo yakawo masa kaltum har gida shima kuma yau zai cika masa aljihunsa da makudan kudin da yayi masa alkawari zai basu bayan kudin jirgi
daya tura masa na zuwansu da komawarsu.

malam saleh yayiwa alhaji saadu iso zuwa katafaren falonsa yace ya zauna kafin alhaji ya fito daga daki.
idonsa biyu bajimawa saiga alhaji Adnan ya fito sanye da doguwar riga jallabiya fara sol fuskarsa cike da murmushi, tafiya ce irin ta kasaita da nutsuwa, yazo ya zauna a luntsumemiyar kujerar da take tsakiyar falon, malam saleh ya sake durgusawa yayi gaisuwa yayinda alhaji sa'adu ya sulmiyo daga kan kujera ya zube ya kwashi gaisuwa, alhaji Adnan yaji duk baiji dadi ba dasuka zube a kasa yayi-yayi su zauna akan kujera sunki daman malam saleh duk yadda za ayi dashi bazai zauna akan kujerar mai gidansa ba don haka yakeyi tuntuni babu yanda za ayi ya zauna akan kujer mai gidan sa ko agabansa ko a bayan idonsa saboda
girmamawa.

Shi kuwa alh sa'adu daman baisan alh Adnan ba sai a waya, wani ya hada su dan haka baisan matsayinsa ba sai yayi abunda yaga yan gari sunyi yashiga tunani anya alhaji adnan ba gwamnan kano bane?
saboda haduwarsa da haduwar gidansa.

ina kaltum?
tambayanda alhaji adnan yafara kenan kafin yace komai nan da nan mahaifinta ya mike da sauri ya leka ya kwala kiran sunan kaltum
saida alhaji adnan yaji kansa ya daure don iya
saninshi baitaba jin ya kira sunanta ba. kaltum tashigo cikin falon a nutse cikin sanyin jiki tazo ta durkusa a gabansa ta gaisheshi idanuwanta a sunkuye a kasa, alhaji adnan yadau dogon salati fadi yake kaltum haka kika zama ba kya cin abinci
ko wanka ne bakyayi kika zama koso-koso haka?
subhan Allah, alhaji sa'adu 'kaya take ci a acan ne ta bushe haka ko azumin wata uku takeyi?
ai wannan ba tada jini ajiki sai ankara mata, jeki gida kiyi wanka ki cire dabaibayin nan iska mai sanyi ya shigeki ki shirya keda sofi direba ya kaiku asibiti bakida lafiya,

kaltum ta mike cikin sanyin jiki ta fice sai yanzu ta sake tabbatar wa ta tashi daga aiki,
tabbas tazama abun kyama abar kallo da nunawa a cikin yan Nigeria, duk talaucin gidansu ta gansu bul-bul sunfita kyawun gani, wanda yasan kaltum ada idan ba a fada masa itace a yanzu ba babu yadda zaiyi ya gane ta, farar yarinya dirarriya ta zama baki
kirin zololo kamar anyaga summa.

alh sa'adu yayi murmushi yace ai tayi kyawun gani a kwanaki ukun nan saboda a ranar da muka fara ganin ta abun yafi haka lalacewa don malam ya killaceta agidansane yabata abinci tayi wanka da wanki kuma ahaka take kokarin komawa kauye taci gaba da rayuwa, tabbas yakamata akaita asibiti domin wani sharcecen gyambone a kafarta da bandeji a yanzu haka,
alhaji adnan ya girgiza kai don tausayawa yajuya ya dubi malam sale yace ka naji da kunnuwanka kokuma kana gani da idanunka abunda kuka jawo wa yarku ta cikinku ko?
yanzu kaga illar kin bin shawata ai?

Malam saleh yadukar dakai kasa fadi yakeyi hakane alhaji ayi hakuri anyi kuskure babba baza a sake ba in shaa Allahu .
alhaji sa'adu ya gyara zama yanaso yaji lbr domin kansa ya daure yanda alhaji Adnan ya damu haka ashe ma kaltum bayarsa ta cikinsa bane yar mai gadin sace?
Lallai samun mutane masu kirki irin na alh adnan azamaninan sai an tona, taimakon talakawa saboda Allah alhaji sa'adu bai sami nasara an ansa masa tambayoyinsa ba alh adnan yace abar zance kawai su koma zancen abunda ya shafi tsakaninsu daman komai a lissafe yake alh adnan ya tura musu kudin jirgi da kudin wahalhalunsu na can yanzu makudan kudin da yayi alkawari zai basu ne ya rage inhar suka kawo masa kaltum har gida ba sako ba shine zunzurutun kudi har naira dubu dari biyu da hamsin. chafdi jam in fulani haka malam saleh ya bude ido da baki yana kallon kudin da bai taba rikewa a rayuwarsa ba,
alhaji adnan ya mika wa alhaji saadu batare da neman ragi ko gibi ba lalle alhaji sa'adu yaji wani iri, sai washe baki yake yana godiya amma malam sale yafi yawan godiya tunda saboda yarsa yafitar da wadannan makudan kudi, hawayene ya dinga zuba daga idanuwan malam saleh saboda farin cikin kaunarda alhaji adnan yake nuna musu,
alh sa'adu ya bude makamakan aljihunsa yadura kudin saf suka shige aljifan ya mike tsaye yana mai shirin tafiya yayinda alhaji adnan da malam saleh suka mike suma suna taka masa zuwa bakin get din fita,
alhaji sa'adu ya dubi alhaji Adnan yace idan irin haka ya taso a neme ni a shirye nake wajen taimakawa,
alhaji adnan yayi dariya ya ce Allah ma Ya kiyaye ai bama fatan Allah ma Ya maimaita mana irin wannan,
malam sale yace ai shi irin haka gaba takaishi don haka addu'a suke haka ya faru mukuma neman tsari mukeyi..
meyayi zafi ne haka maigadi ?
Ai ba abun bakar magana bane inji alh sa'adu.

alh adnan yace ya isa haka mungode da kokarinda kayi mana mukuma muna neman tsari da sake faruwar irin wannan, alhaji saadu yayi godiya ya tari babur ya haye yayinda alh Adnan yana yimasa nasiha dasu cire duhun kannan nasu nada su rungumi yarsu su nuna mata soyayyah kamar yadda kowacce ya take samu daga iyayenta, jahilci ne wannan kunyar ba addini bane,
da alama malam saleh yana gamsuwa kuma yana daukar gyaran kuskuren da ya tafka a baya,

kaltum kuma tana cikin gida ta fesa wanka da ruwan Nigeria, sabuwar atamfa sofi ta dauko mata abun mamaki musamman dan ita aka dinka aka ajiye mata, kannenta suka dinga biyo layi suna jera mata abinci kala-kala a daki kamshi tururu, taci ta koshi.

yayinda malam saleh yake faman duke-duke
yana zubawa alh adnan gunduma gunduman
godiya da shi albarka a jejjere, shikuma alhaji Adnan hankalinsa nacan wajen sofi yayinda take rike da gashin kaltum tana yanyankewa da almakashi a tsakar gida, sofi tayi-tayi ta warware bukuikuyayye hargitsattsen gashin nan da yayi wata bakwai ba a taje ba abu yaci tura don haka tayanke shawarar gunguntuleshi kawai kowa yama huta saboda yakoma wata halitta kamar ba gashi ba,
Sai bayanda aka aske gashin ne ma sukaga wani sabon abun tashin hankali a kokon kan sai kaga wata farar kura, ta dago sofi ta rushe da kuka yayinda kaltum ma tafara kuka hankalin alh Adnan yayi matukar tashi yayi magana cikin gigicewa da daga murya yace sofi maza tashi maza ki dauko gyalenki kikaita asibiti dan ladi direba yana nan zuwa, ba kuka zaki sata agaba kinayi ba ashe kinason yartaki kika wulakanta ta tuntuni ?
Ga illar da neke nuna muku kenan, zanyi waya asibitin infadi abunda yakamata ayi mata, kamata yayi ma su kwantar da ita har tsawon sati biyu ma suna dubata kuma don ta huta (bed rest) bai rufe bakinsa ba sai dan ladi ya bayyana ajikin get a inda yamasa horn malam saleh ya zabura zai ruga ya bude masa get alh adnan ya dakatar dashi yace karka bude basai ya shigo ba ku dunguma ku tafi tare asibitin tunda Abdul zai iya kula da yara harku dawo nima zanje nayi wanka in same ku acan, idan ba sai da zaman jinya ba da sai sofi ta dawo,
tafiya kaltum keyi zalo-zalo kamar mara laka ajiki harta shiga moto kanta a sunkuye akasa inda take gaskatawa tabbas ta tashi daga aiki tunda tazama abun kai wa asibiti akwantar don a bincika lafiyarta alhalin lafiyarta kalau babu inda yakeyi mata ciwo, ta
tabbatar tashiga rayuwar kulawa ba kamar rayuwar rashin gata datayi a sudan ba, tasan
tazama abar tausayi a gidansu kuma mai karancin lfy abar bincike don kada ta yada masu cututtuka,

alhaji adnan bai gushe daga bakin kofar gidan nan ba har saida ya daina hangen motar da kaltum da iyayenta suke ciki ya shiga gida yasa hannu ya rufe get yayinda ya
kwala kiran Abdul ya zaro kudi mai dan yawa ya bashi yace su sayi duk abunda suke bukata har iyayensu su dawo, ya durgusa harkasa ya karba yana godia,
alh adnan ya juya ya shiga gida yayinda ya lalubi numbern doctor ya buga batare data dade tana ringinba yaji ta amsa cikin ladabi docta Anisa ta gaisheshi ya ansa cike da kasaita domin yau ita kanta tasan tukunyar gidan ta saita kara zaki tunda mai girma alhaji adnan ya kira ta,
'' farin mutum mai farar aniya amma banda farar kafa, mai yayyafin kyauta kamar yayyafin ruwa acikin shuka sai ya raba har sai kowa ya samu '' kirarin da jama'a ke masa kenan,
yayi gyaran murya yace kanwata idan kina asibiti ki jirani idan kina gida marmaza ki garzaya asibiti yanzu na turo wasu yan uwana gurinki inaso ki bincikemin kaltum ciki da waje,
na farko inaso kiyi mata gwaji na ciki ,dana kanjamau ,sannan ki bincike ta shin cikekkiyar budurwace ko an lalatata?
Sannan ki duba ta taba haihuwa kota zubarda ciki ?

Dr Anisa Yahya ta dafe kirji ta bude baki don fargaba da tsananin mamaki duk da batayi magana ba yajiyo hucinta har saida ya fuskanci tashiga dimuwa, yayi ajiyar zuciya sai yayi dan murmushi yace nasan zakiyi mamakin irin wadannan bayanai nawa to dolece tasa za ayiwa yarinya budurwa irin wannan tonon silili, bata tayi har tsawon shekara uku sannan aka nemota cikin almajirai masu bara a can kasar sudan kinga komai zai iya faruwa saboda talauci.

Dr Anisa tayi ajiyar zuciya tace ayyah nafahimta ranka ya dade za ayi duk abunda ya kamata,
yayi murmushi yace idan kika gama ta bangarenki inaso ki hadata da kwararren likita da zai binciki gaba daya lafiyarta kamar koda,hanta,zuciya,sugar,gishirin jikinta da sauransu agani ko akwai wani organ da yatabu sannan abincika nasan ba zata rasa irinsu Ulcer ba saboda yunwa ko hawan jini saboda damuwa, idan aka gama sai ahadata da likitan kwakwalwa a bincika ko hankalinta ya tabu saboda tashin hankali idan duk babu matsala sai ki kaita wajen likitan fata yabata magani da mayuka da sabulai masu kyau wanda zasu fitarda kuraje,kirci,makero ,amosanin dasuka yayyame jikinta ta kokon kanta, daga karshe ku bata daki ita kadai ta kwanta tahuta sannan ku tsara mata time table na abincin da zasu gina mata jiki su kara mata jini,
idan kuma jininta yayi kasa sosai har sai an kara mata jini to saikiyi magana anemo asaka mata,
don Allah doctor kikula da ita sosai duk abunda ya kamata ayimata kudi ba matsala bane akwai isassun kudi a file dina adauka, amsa daya dr Anisa ke bayarwa na'am ranka ya dade an gama,
daga karshe suka yi sallama har suka kashe waya sunawa juna godia,

wanka kawai alhaji adnan yayi ya shirya ya fito ya zari luntsumemiyar motarsa ya nufi international hospital wajensu kaltum abunka da harkar naira gaba daya likitoci da aka bukacesu su duba kaltum sun hallara wannan najiran wancan ya gama da ita ya miko masa,
alh Adnan yaji dadi har ya yaba musu,
da yaga dr Anisa zata iya kula da ita sai ya umurci sofi da malam sale su tafi gida inyaso kullum Dan ladi ya dinga kawosu suna dubata har a sallameta, sofi da sale suna godiya cike da farin ciki suka shiga mota suka koma gida.

sakamakon dr Anisa ya kammala ta shaidawa alh Adnan kaltum tanada cikakkiyar lfy duk abunda yake zargi babushi a tare da ita,
sai yaji wani sanyi aransa da alama yana cikin farin ciki kudi mai yawa yabawa dr Anisa yace ta sayawa kaltum kayan sakawa masu kyau ta dinga dafa mata abinci masu gina jiki har tsawon zamanda zatayi a asibiti, baima sami ganin kaltum ba saboda tana can a dakin gwaji, yayi sallama da likitoci bayan ya gwangwajesu da naira ya buga motarsa ya nufi babbar burnin tarayyah Abuja, saboda yabar aiki dayawa zuwan kaltum ne yakawoshi.

kaltum tana kwance luf asibiti cikin kayataccen daki da bandaki aciki ita kadai tana kallon talabijan (settelite)baya ga kayan sanyi fal a firiji dinta, lemo sai wanda takeso zata bude tasha baya ga zuka-zukan kayan sakawa da tsukewa (english wears)akwati guda dr Anisa tasayo takawo mata kamar yanda oga Adnan ya umurceta,

likitocine da ma aikatan jinya (nurses)suketa kai kawo adakin suna duba lfynta da tambayar ko akwai inda yake mata kaikayi su sosa mata bama ciwo ba, ko kaikayi taji sunce ta fada musu su kawo mata agaji dariya kawai kaltum keyi domin taga gatan yayi mata yawa idan ta tuno rayuwarta abur
sudan, ta tuno rayuwar Khartoum sai taga akwai bambaci,
hakika tazo gida domin masu iya magana suna cewa '' kowa yabar gida gida ya barsa '' kayan dadi harsunyi mata yawa ci takeyi ta yada filo ta kwanta, wanka ne kadai da sallah yake rabata da lumtsumemiyar katifa da aka dora mata akan luntsumemen gado,
idan tasha magunguna ta shafa na shafawa a kircin jikinta da kanta saita kora lemo (juice)tayi gyatsa ta jawo cinyar kaza ta koma kan gado ta kishin gida tana matsa remote tana ganin tashoshi kala-kala, turawa ,india ,
amma tafi duban tashoshin larabawa kamar
saudia da sudan sai tayita duba tana ayyanawa a ranta da man a nuna mata Madina da Mambelanta a gansu?
a saudia kuwa saita dinga ware ido ko zata ga goggo fattu da sauran wadanda suka haye
tare,
bata taba sa'a ta hango ire irensu ba.

farin cikin ya lullube alh adnan a sanda kowanne likita ya turo masa sakamakon gwaje gwajen da akeyiwa kaltum ta e-mail dinsa sun tabbatar masa komai na jikin kaltum lafiya kalau yake ko maleria bata dashi rashin kuzari ne kawai da rashin wadataccen jini a jikinta a sakamakon cin gabza babu blance died shi kuwa wannan lokaci ne idan ta cike gurbin yunwa ta koshi jini zai gudana,

satinsu biyu a sibiti ta shana dayawa tayi kiba tayi haske kirci ya fara neman hanyar garinsu kura da dankararriyar daudar da taki fita a sakamakon rashin sabulu mai kumfa ayanzu sabulu mai kamshi da kumfa ya kore su tuni fatarta ta fara garai-garai.
hasken jikinta ya fara dawowa, kamshin turare designer ya fara kama tufafinda ta cire, kaltum ta dawo gidansu sai ta sake cika da mamaki a lokacinda ta tarar an canja fasalin da tsarin gidansu bakamar yanda tabarshi ba kafin ta tafi asibiti.
da ta tambayi sofi ya akayi?

saita bata lbr cewar alh adnan ya umurcesu da su fitar da rubabbun gadajensu da katifansu da duk wani shirgi su kai bola su zubar, aka yi fenti aka sake kofofi da gilasan wunduna aka zuba musu sababbin kaya, dakuna uku cur suka bayyana a gidan kowanne da gado da labule, , ledar daki mai kyau aka malala, daya dakin na sofi ne da saleh daya na kaltum ne ita kadai yayinda dayan na tarkacen kannenta ne baya ga kicin da bandaki duk a barandar hatta da abincinsu ya canja a gidan, duk saboda kaltum ta murmure.
alh adnan ya dauki nauyin aiko musu da kudi da kayan abinci, aiki yayi masa yawa don haka sai da ya shafe watanni biyu cur baizo kano ba bayan tafiyar sa Abuja kuma har da gudun zarginda matar sa madam salaha ke yi a kan kaltum.

Labarin dawowar kaltum kakaf a kunnuwanta don haka tafara yimasa tsiwa akan bata yarda yayi ta yawan zuwa kano ba, maganarta bazata hana shi shigowa garinsu ba a duk sanda yaga dama, yafi danganta rashin shigowarsa kano da yawan aikinsa dakuma cuku-cukun tafiyar dansa Mashkur karatu london, har Mashkur yagama sakandari yasami admission a combrigde university zai karanci computer, yabar kaltum a baya tana fama da kokon bara.

Allahu akbar rayuwa kenan wani ya fi wani saboda yatsun hannayenmu ma ba kansu daya ba, Allah Ya na azurta wani akan wani duk a cikin kudirarSa da kudirarSa, fadin AlhamduLillahi ala kulli halin shine kawai ya kamace mu a duk halinda muka tsinci kanmu,

mahaifan kaltum su kayi tunani sukaga ya kamata duk bayan wani lokaci sukira oga Adnan a waya su gaisheshi suyi masa godiya
sannan su mikawa kaltum waya ta gaisheshi tayi masa godiya bisa abubuwan alkhairi dayake musu, alh Adnan bai cika son inyayi kyauta agode masa ba don haka yawanci dasun fara doguwar godia sai ya katse su da cewar don Allah yakeyi kuma Allah ne zai biyashi su daina damuwa dayi masa yawan godiya,
Allahu akbar. kaji bayin Allah salihan bayi masu bayar da kalilan ranar gobe kiyama Allah Ya basu kasiran, Allah Ya sa mudace Aamiin.

la'asar sakaliya babu zato babu tsammani alhaji adnan ya diro masu ba tare da sunsan zai zo ba, bayan saleh yaji horn din mota sai yayi zuruf ya mike daga kan dogon bencinda yake zaune ya leka wajen get sai yayi mamaki da ganin mai gidansa ya runtumo da
gudu ya wangale get yayinda alh adnan ya kutsa da kan mota cikin gidan sa,
a farfajiyar gidan ya iske kaltum da kannenta kakaf suna wasa da ball suna tsalle-tsalle da guje-guje cikin tankiya da daria, sanye take da wata tsaleliyar riga da siket kayan kanti duk acikin kayanda Doc Anisa ta jifgo mata harma dawasu kayan 'yayanta duk ta hada mata, kanta babu dankwali sai dai wani lallausan gashi mai kama dana larabawa ne ya fara tahowa saboda mayuka masu gyara gashi data samu tana murtsukawa, tana hada ido da alh Adnan sai ta sa hannu ta dafe kanta alamar kunya, ta runtuma da gudu cikin gidansu yayinda kannen ta suka runtuma da gudu gare shi suna fadin oyoyo..
yataresu da murna yana shafa kan kowannensu kamar yanda yasaba yi musu,
saboda mutum ne mai tsananin so da tausayin yara, ya bude boot ya umurcesu da su kwashe duk abunda suka gani a ciki sukai gidansu, doya ce himili guda kuma manya-manya da dankalin hausa dana turawa baya ga manja kayan miya harda nono kwarya biyu aka juye masa a manyan ledoji, duk tsarabane yayi musu daga hanyar Abuja.

kaltum ta fito sanye da hijabi ta karaso da farin ciki gabansa takwashi gaisuwa...
tashi tashi tsaye inji alhaji Adnan domin bai cika so a zube a gabansa ba, ya dubeta yayi murmushi da alama yaji dadin ganin kyawun da jikinta yayi bai kashe kudinsa a banza ba, rama da baki kirin din nan datayi sun gushe saiyace da ita kaltum babu wata matsala dai ko?

Ta amsa da babu wata matsala dady.

yayi dariya yace to AlhamduLillah haka akeso kici gaba da cin abinci sosai sai kiyi kiba kinji ko?

ta amsa da to daddy.

malam saleh me kake fadamin ne dazu a waya ina hanya banajinka sosai?
alh Adnan ya tambayi malam sale wanda yake tsaye agefe nan da nan malam saleh ya duka ya fara bayanai cikin ladabi bansan zaka taho kano a yau ba nake shaida maka cewar jikin goggo fattu fa ya tsananta a can zangon Daura suna tamin waya ko asibitin kano zan kawota?
shine nace musu a'a subari tukunnn na shawarceka..
sautin ajiyar zuciyar kaltum ce taja hankalin su suka juyo su dukka suna duban ta, ta dafe kirji don mummunar fargabar data riske ta alokaci guda domin koda wasa bata zata goggo fattu na Nigeria ba tsawon watanin nan biyu da dawowarta iyayenta ko kannenta basu taba fada mata ba, ko amboton sunan goggo Fattu ma ba ayi agidan.
.
Kai! Ni kam ku taya ni parin ciki jama'a, sai kara pito min da mata ake gari, ku shaidawa Alh Adnan Dan Aunty yana kara godia,
Lokacin auren mu sai kara matsowa yake, kowa ya xauna cikin shirin shan biki.... 😊
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 33
.
TRUE LIFE STORY
.

.....ganin su duka sun kalle ta sai ta dukar da kai kasa ta gaggauta barin wajen. Ta shiga gida ta iske sofi a gaban risho tana faman tuka tuwon shinkafa kamar kullum, kamar yadda ta saba da yamma. Kallo daya ta yi wa kaltum ta tabbatar tana tafe da damuwa don haka ta tsaya cak da tukin tuwon tana duban 'yar ta tana sauraron abunda zata fada. Cikin sanyayyar murya kaltum take tambayar sofi.

"mama, daman Goggo fattu ta dawo daga makka har ma tana kwance a zangon daura ba lafiya? "

Sofi ta nisa ta ce, "fiye da shekara guda Goggo fattu ta dawo sharkab babu lafiya, babu hannu ba kafa, ai sai a lokacin muka san ba kwa tare da ita, don mu a tunaninmu kuna tare. Sannan ta tabbatar mana da cewa ta baro ki a Sudan. "

Kaltum bata sake magana ba cikin sanyin jiki ta wuce zuwa dakinta ta shiga lungu ta takure, ta rasa abunda yake yi mata dadi. Sai ta ji kuka ya rufto mata wanda yake tafe da sakonnin zuciyarta kala-kala. Ta tuno azabar da Goggo fattu ta gana mata a baya, sai ta tuno da ranar da ta shige jirgi ta kyaleta, ta tuno rayuwarta a Sudan ta wahala, sai ta ji tausayin wadanda ta baro a can a cikin wahala, don haka kuka ya rikito mata ba kakkautawa. Abayyane take fadin, "wayyo madina, wayyo mambela na, wayyo fatsima ".

Daddy da baba Saleh ne ke zaune a falo suna ta shawarwari kala-kala bayan an gama shawarar yadda za a shirya tahowa da Goggo fattu sai aka shiga shawarar shigar kaltum makarantar boko don ta karasa karatunta. Shekaru sun nausa tun da yanzu shekarunta goma sha takwas kuma daga J.S.S 3 ta tsaya don haka shawarar da suke yi ta ina zata datsa.

Alhaji Adnan ya zaro waya ya fara bubbugawa mutane daban-daban yana tambayar tsare-tsaren makarantu daban daban don tantance makarantar da ta dace da kaltum. Ya nemi shawarwarin abokansa masana makarantu ya hada da shawarwarin shugabannin makarantu daban-daban, daga karshe ya yanke shawarar ya saka ta a wannan makarantar da take tashe, wato "crescent". Ajin da za a saka ta ne aka ce sai an yi mata jarrabawa za a tantance, aka tsayar da shawara jibi littinin a kawo kaltum makaranta don zana jarabawa.

Alhaji Adnan ya umurci malam Saleh da ya kira kaltum ya shaida mata halin da ake ciki. Fitarsa babu dadewa sai gashi ya shigo da 'yar sa. Kallo daya zaka yi mata zaka kula da jajayen idanuwanta alamar ta yi kuka. Ta durkushe a kasa kusa da mahaifin ta wanda shi ma a durkushen yake suka nutsu suna jiran abun da uban gidan su zai fadi.

Ya sake luntsumewa a cikin lallausar kujerar da yake zaune, yace.

"Kaltum, kukan me kike yi? Ashe har yanzu akwai abunda yake bata miki rai a duniya? A tunanina kukanki ya kare tunda kika dawo gida ga mahaifan ki, ga mahaifiyarki ga ni nima ina tare da ku. Me nene matsalarki, ko me kike nema kika rasa in yi miki? "

Sai mahaifin ta ya fara zubar da hawaye, yace
"Alhaji babu gata da kulawar da baka yi mana ba, ko mu muka haife ka ko kai ka haife mu iyakacin abunda zaka yi mana kenan. Kukan da take yi kuwa ba wani abu ba ne, maganar Goggo fattu ce da ta ji muna yi cewar, tana kwance babu lafiya, sai dai ta yi komai akwance a kwashe. Ka san kaltum da tausayi shine ta je daki ta fara kuka".

Alhaji Adnan ya girgiza kai, ya ce "Allahu Akbar, haka mutum ya kamata ya kasance. Ya zama mai yafiya da maye gurbin mugunta da alkhairi. Ba komai kaltum, ki daina kuka ki yiwa fattu addu'ar Allah Ya bata lafiya, kuma ki yafe mata domin ta zalunce ki, idan ba ki yafe mata ba Allah ba zai yafe mata ba. Don Allah ba ya yafe laifin wani, ko yafiyarki zata sa ta sami rangwame daga ukubar da take ciki yanzu."

Kaltum ta fada cikin kuka.
"na yafe mata duk abunda ta yi min".

Malam Saleh ya dora da, "Alhamdulillah, Allah Ya miki albarka ke ma, Allah Ya baki 'ya'yanda za su miki biyayya ".

Kaltum ta amsa da, "Ameen ". Yayinda Alhaji Adnan ya shaida mata dalilin kiran da yake yi mata shine, a kan karatu. Ya bayyana mata cewar ta je ta sami 'yar makwabtarsu Nana ta fara koya mata karatun da ta manta kamar "Maths da English" saboda ranar litinin zataje tazana jarabawa don asan ajinda za a sata.

farinci mai baiyani zaka dinga hangowa afuskar kaltum kankace kwabo hawayen kuka ya kafe, idanuwanta sun washe sai
fararen hakwaranta ne ke haskawa afili don
dariyarda take kyalkyalawa, na gode dady inason makaranta daman,
kalmar da kaltum ke maimaitawa kenan ta kaura gidansu nana tana koya mata aikin yan aji biyar domin aji biyar takeda niyar farawa
duk da a kureren lokacine, kwana biyu kawai
amma yin karatun ya tuttuno mata da abunda ta manta abaya dayawa saboda tunda taje sudan ko biro bata taba rikewa ba balle tayi wani abu waishi rubutu, ta kanta kawai takeyi.

ranar litinin duk da alh Adnan baya gari amma yabar musu komai harda Danladi direba don haka sassafe kaltum ta shirya ta shige bayan mota direba ya kaita makaranta ta hadu da yan mata kamarta a cikin makarantar tana yi musu kallon suna jin dadi daman itace su suma sunayi mata kallon yar gata dama zasu sami gatanta yarinya karama da mota da direba.

a offishin shugaban makarantar aka bata jarabawar ta zauna tayi tsaf ta gama ta mika, kwanaki biyu kacal suka bata ta fara zuwa bayan sun duba jarabawanta zasusan ajin da zasu sakata, awaya suka shaidawa alh adnan cewar kaltum tayi kokari ta amsa musu jarabawan su wasu kuma ta fadi don haka a aji hudu ta cancanta a ajiye ta, ya amince yace ba damuwa ya riga ya biya kudin komai don haka direba yaje yakarbo mata kudin uniform da littatafai da yawa,
akace ta fara zuwa duk da haka tayi farin ciki kuma ta kudiri niyyar dagewa wajen gyara kuskuren jarabobi data fadi,

Dan ladi dai a fakaice yazama direban kaltum aikinsa kawai yakai kaltum makaranta da sassafe ya dawo gida ya ajiye mota idan karfe biyu na rana yayi ya dauki mota ya daukota, umurni daga alh Adnan don haka kallo daya zakayi mata ka tabatar rayuwa takeyi mai dadi da kwanciyar hankali yayinda damuwa ta kau sai kwakwalwa ta washe karatu tayi ta shiga babu duka babu zagi babu bauta ga abinci a wadace,
kaltum babu sauran kuka goggo fattu kuwa
ankawota asibitin malam aminu kano ana kulawa da lafiyarta duk da akwai wata tsohuwa a wajen ta kullum sofi sai ta kai abinci, kaltum kuwa duk ranar asabar da lahadi a asibiti take yini tana taimakawa da dagata abata abinci, kwashe kashi da wankin
fitsarin da take yi a shimfida duk da goggo bata iya magana bakinta ya juye amma da hankalinta tana fahimtar komai,
saitayi ta kallon kaltum tana hawaye da alama tana nadamar abubuwanda tayi mata abaya.

BABI NA GOMA SHA HUDU

ranar wata talata da misalin karfe uku na yamma kaltum ta dira a kofar gidan alh Tasi'u tsohon mijin Madina,
kaltum sanye take da riga da wando sai dan hijabi shine kayan makarantarsu sai bakin kamvas da farar safa, katuwar jakar littatafanta ta baro a mota da direba a jikin wata inuwa yana jiran ta, tafiya take tana sanda kamar wacce take tsoro kada akamata
kokuma ince mara gaskiya sai taji tafiya ta bayan ta a lokacin da tashiga zauren gidan tayi firgigit ta waiga ta bayanta wata yar matashiyar yarinya tagani wacce shekarunta bazai wuce shekara sha biyu ba amma kallo daya tayi mata taga kamar Madina, babu tantama yarta ce kaltum taji zuciyarta ta harba don fargaba yadda take duban yarinyar haka haka itama yarinyan take duban kaltum cike da mamaki, kaltum ta fara magana cikin tuntuben harshe batare da tasan abun da zatace ba tace yarinya nanne gidan alh Tasi'u ?

Ta gyada kai ahankali tana mai duban kaltum a tsorace nan ne.
yaya sunanki ?
Kaltum ta tambaya,
cike da murmushi sunana shahida ta amsa mata, sai kaltum ta daina kokonto ta gasgata wannan itace yar autan Madina.

daga makaranta kike ?
Inji kaltum, shahida ta gyada kai tace eh, kaltum ta lura shahida a tsorace take da ita domin idan ta matso kusa da ita saita ja da baya kokorin guduwama takeyi, kaltum tace da ita toki gaida yayyanki Abdul hakim da Abdul Malik, sai shahida tasake dubanta cike da mamaki ta amsa da cewa to zasuji yayinda ta wuf ta fada cikin gida da sauri,

kaltum ta gaggauta barin zauren don kada
taje ta kirawo yan gidan su fito a tutsiyeta da
tambaya ace meya kawota ?
Tana fito wa sai ta dubi katafaren gidan da yake jikin gidansu shahida tana ganin sojoji biyu suna gadi ta gasgata nan gidan General Tukur, gidan su marigayi Abba taci sa a aka wangale get din gidan yayinda wata dambasheshiyar mota kalar (blue black)ta fito daga cikin gidan wani zankadeden saurayi ta gani a cikin motar sanye yake da jeans da tshirt baka hade da wani bakin glass a idanuwan sa, kallonda kaltum take masa na kwakwap shiya jowo hankalinsa ga dubanta shima har ya rage gilashin wundo ya rage tafiya suna kallon juna, kallon mamaki har sunkuyowa tayi tana lekensa bayan ya wuce ta, yayinda shi ma ya saita gilashin mudubin motarsa yana hangenta don yaga me take nema, wacece ita, kuma can yaga ta je a hankali ta leka get din gidansu, sai yaga ta da ka tsalle ta labe da alama ta hango wani da ga cikin gidansu yana tahowa, tabi jikin katangar tana shafawa a hankali yayinda takara dawowa kofar gidansu shahida ta tsaya ta dade sannan ta tafi, yana kallonta ta nufi wata camry ruwan silver ta bude kofar baya ta shiga ta kame direba yaja suka tafi, mamaki ya kama saurayin nan sai yaji ya fasa zuwa unguwan ma gara ya dawo gida domin ya tsorata da yarinyan nan yar makaranta tunda yake ko a hanya bai taba ganin mai kama da ita ba, yayi kwana ya juyo kofar gidansu masu gadi sukayi sauri suka
bude masa get sai ya canja shawarar shiga gida sai yaji gara yabi bayan yarinyan nan yaga daga ina take kuma me tazo nema a gidansu,?
saidai kash da yabi inda sukabi sai yaga wayam ko gabas ko yamma baiga ta inda sukabi ba ya dawo gida cike da mamaki shi kadai da zuciyansa ba tare da yasan yanda zai baiyana wa wani ba,

kaltum ma ta dawo gida cike da tsansar damuwa da nadamar meyasa bata bi shahida ta shiga har gidan Tasi'u ba, ta bayyanawa 'yayyan shahida inda mahaifiyarsu take kuma meyasa bata tsayar da dan saurayin nan ba, da alama dan gidan ne kanin Abba ta sanar musu labarin da Madina ta bata akan hakikanin gaskiyar abunda ya faru cewar Madina ba mayyh bace, ba ita ta kashe shiba kamar yanda suke zarginta, ta kuma fada musu inda Madina take dakuma wahalarda take ciki sai ta tuna sojoji ne, daga sanda basu gamsu da bayanintaba zasu iya afka mata da duka,
yini guda kaltum tayi cikin damuwa ko abinci takasa ci da zarar kuka yazo mata saita shige bandaki tayi ta wanke fuska ta fito bataso kowa yagane abunda yake damunta saboda babu wanda yataba tambayarta labarin sudan a cikin iyayenta.
da yamma makarantar islamiyyah take zuwa ita da kannenta dayake acikin unguwar makarantar take da kafarsu suke tafiya yayinda direba ya ajiye mota ya tafi gidansa aikinsa na ranar yakare indai ba oga Adnan bane ya aikesa cikin gari wajen yan uwansa ba sai dai ko madam salaha ce ta aikeshi gidan kawayenta ko en uwanta itama.

tafiya tayi tafiya kaltum tayi shekara da dawowa daga sudan haka har ta gama aji hudu tashiga aji biyar, ta sake gogewa ta waye saboda wayayyun kawayenda tayi a ajinsu kusan duk abunda suke dashi tana dashi saidai inbata fadawa daddy ba zai saya babu musu, kama daga sutura zuwa jaka da
takalmin makaranta masu tsada kayan kwalliya irin su hoda jan baki da sauransu,
aranar wata asabarce yan aji shida masu fita suke bikin fita (send up)amma da kayan gida kowacce taje dan haka kaltum tasa dandashen leshinta ruwan zuma mai fulawa koriya, anyi mata dinkin matsattse na riga da siket yayinda tahau kan wani dogon takalmi (high hill) saita kara tsayi sosai, gyalenta kore ne ya shiga da adon leshin yayinda jaka da takalminta suka zama ruwan zuma, ta dandasa wani farin gilashi a fuskarta, yalo-yalon gashin kanta yazubo zuwa keyarta, tayi fari jawur da ita saikazata idan kayi mata hausa bazata amsa ba, sun sha party anyi bayanai sannan akayi ciye-ciye da tande-tande bayan an cashe sai aka watse.
direba najiranta a mota don haka tana fitowa tafada mota bayan ta gaisheshi cikin ladabi sai ta shaidamasa unguwan yankaba takeso suje , tana fadar haka yasan inda take nufi domin sun doshi shekara suna zuwa kofar Tasi'u su tsaya tayita leke-lekenta su tafi wani lokacin ne idan sunga yarinyan nan shahida ta kirata tabata alewa su juya su dawo,
abun ya dade yana cinsa arai idan yayi alamar zai tambayeta saiya fasa domin kusan kullum idan sukaje gidan a hanyar su ta dawowa kuka ta keyi shi yasa ma baya samun damar tambayar ta, a yau kuwa ya sami damar jero mata dogayen tambayo yi a jejjere saidai kash guntayen amsoshi take bashi ya dubeta ta madubi yayi murmushi yace kina nufin wannan gida damuke zuwa bakya shiga?

kaltum ta gyada kai tace eh nan ne.
yayi murmushi yace yau dai zaki shiga ciki ko?
wannan karon ma gyada kai tayi tace eh zan shiga, Danladi ya fahimci kaltum bata son tambayoyin nan don haka sai yayi shiru.
a inda ya saba ajiyeta anan suka tsaya wato karkashin wata katuwar bishiya dake kallon kofar gidan Tasi'u, kaltum ta bude kofar mota amma bata fita ba, idonta ne cak akan kofar gidan Tasi'u tana fatan kuma tana addu'ar Allah Ya fito mata da Shahida,
Allah mai karbar addu'a sai ga Shahida ta fito burum daga gida sanye da hijabi kuma rataye da wata jaka mai kama da buhun sikari da alama makarantar islamiyyah zata tafi, idon shahida akan motar su kaltum a inda idanuwansu ya kyallaro junansu sai su kayi wa juna murmushi a lokaci guda.
kaltum ta daga mata hannu alamar kira babu
kokonto a zuciyar shahida saita tunkaro inda kaltum take zaune wato a cikin mota tana isowa saita zube akasa ta kwashi gaisuwa, kaltum tayi caraf ta dagota tsaye yayinda take rike da hannunta tana mai ambaton sunanta, shahida kin ini lfy?
ina zakijene da rana fatso-fatso?

shahida tayi dariya, islamiyya zan tafi.
kaltum ta tambaya cike damamaki islamiyyah da rana bada safe ko yamma ba?

shahida tace ina zuwa da safe duk ranar asabar da lahadi a taso mu shabiyun rana mu koma tahfiz karfe biyu zuwa hudu na yamma sannan bayan magrib muje na dare.

kaltum ta gyada kai tace lallai ashe yanzu kinkusa saukewa ki zama malama kamar mamarki?

shahida ta dubi kaltum cike da mamaki domin a iya saninta matan babanta dukkansu biyu jahilaine, to wacce mamar ta take nufi?

ta rike hannun shahida tace kinci abincin rana ko?
shahida ta girgiza kai tace a'a ba a gama ba
shine na taho karna makara idan na dawo zanci.

kaltum tace haba dai ya za'a yi ki iya karatu cikinki da yunwa?
shigo mota kici cake da meat pie da lemo a wajen party aka bani, shahida tashiga bayan mota kusa da kaltum ta zauna,
kaltum ta jawo ledoji dake ajiye a gefenta ta mika mata guda biyu kowanne akwai dankwalan cake da meat pie ga lemon kwali da daurin cin-cin,
shahida ta tsinci kanta cikin farin ciki ta karba ta fara turawa daga yadda take cusawa kasan tana tsananin jin yunwa.
.
Allah sarki, dan halak baya manta alkhairi, ko sharri aka masa sai ya saka da alkhairi, ku dubi yadda kaltum ta sakawa Gg Ftt da alkhairi akan tsiyar da ta mata, haka ma kala,
Kuma ku duba yadda ta sakawa Madina da alkhairi akan erta da irin alkhairin da ta mata.
Da patan xamu ke lura da duk wata gaba na wannan littapin mai kyau domin mu dauka, kuskuren cikin sa kuma mu nemi tsari wajen Allah da kiyayewa. Kamar yadda yau kaltum tayi shigar ta bai dace ba, kamata yayi ko wace irin sutura ta sa ta dauko hijabi ta daura akai ba gyale ba, yadda xai suturta ta a ko ina kuma a ko wani irin biki.

Allah Ya sa mu dace.
Aamiin.

.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 34
.
TRUE LIFE STORY
.
shahida ta tsinci kanta cikin farin ciki ta karba ta fara turawa, daga yadda take cusawa kasan tana tsananin jin yunwa. dakuma marmarin abunda takeci don bata saba ci ba,
tausayinta ya kama kaltum saitaji kwalla ta cika mata ido tana tuna sanda Madina take ciyar da ita asanda takejin yunwa, Allahu akbar, haka duniya take duk abunda ka shuka shi zaka girba idan ka shuka alkhairi shi zaka girba idan ka shuka tsiya ita zaka girba ta bibiyeka 'yaya da jikokin ka,
Madina ta taimakawa miskiniyar yarinya alokacinda take da iko da halin taimako yanzu ga yarinyar tazo ta taimaki yar miskiniyar yarta ba tare da ta taba zaton ko amafarki kaltum zata hadu da ire-iren zuri' arta ba,
kaltum kallon shahida kawai takeyi tamkar Madina take gani a idanuwanta sbd kamarsu da sak hatta farcen yatsun hannunsu iri daya ne, maganarsu, kallonsu, dariyarsu duk iri daya, kaunarta ta sake harde zuciyar kaltum kamar yadda takejin Madina a ranta, shahida ta lura kallon yayi yawa saita fara takura tanajin kunya,
kaltum tayi sauri ta kawar da idanuwanta kasa, can ta dago ta dubi shahida tace ina Mamar kine?

shahida ta kora lemon kwali tace tana gida.

kaltum ta girgiza kai tace ba sa'ada ba ina nufin mamarki data haifeki Madina.

shahida ta dago da sauri ta dubi kaltum yayinda ta tsaya cak daga abunda takeyi tajima bata iya cewa komai ba sai ta fara magana cikin sanyin murya tace mamana Madina ta bata an rasata.

da kaltum ta fara hawaye sai shahida ma ta fara kuka,
kaltum ta dafa kafadarta tace shahida daina kuka mamarki bata mutu ba tana raye kuma bata bataba tana nan.
shahida ta zubawa kaltum ido tana mata duba irin na karyatawa,
kaltum ta sharce hawaye tace kinaso kiganta?
shahida ta girgiza kai tace nasan bazan taba ganinta ba don bazata sake zuwa ba har abada,
kaltum ta gyara zama tace meyasa kika ce haka Shahida?
shahida ta sunkuyar da kai kasa tace ance mamana mayya ce ita ta cinye yaya Abba.

kaltum tayi caraf ta toshe mata baki tace karki sake fadar wannan maganar, kada kisake fadawa kawayenki wannan maganar
sai ayi miki gori, sharri ce akeyiwa mamarki, Madina macece mai kirki ga hakuri Allah zai wanketa in sha Allahu daga sharrin da akayi mata, kada ki fitar da rai zaki sake ganin mahaifiyarki don haka kiyita addu'a Allah Ya dawo miki da mamarki kema ki zauna da uwa kamar sauran kawayenki.
hawayene kadai yake kwaranya daga idanuwan shahida sai gyada kai kawai takeyi, kukane yakecewa kaltum harsaida danladi yayi magana don tausayinsu don tun dazu yana zaune agabar mota yana sauraron su yaji hawaye ya cika masa ido yace kaltum yayakike kuka keda kike lallashinta ai saiki tayar mata da hankali idan taga kina kuka.

get din gidan general tukur aka bude wannan karon ma zukeken saurayin nan ne ta ranan idanuwansa kiri-kiri akan kaltum da shahida kamar yadda suma suke duban sa har ya wuce su, saiya dannan rivas ya dawo baya yazo dai dai inda suke ya zuge gilashin wundon kasa ya kwalawa shahida kira a fusace,
shahida tahau karkarwa ta fito da sauri ta nufi wajensa sai kaltum taji ta tsorita ganin yadda yake harararta saita rufo kofar mota da sauri tacewa danladi direba ya fizgi mota su kara gaba don haka yakara tabbatarwa basuda gaskiya kuma bada alkhairi suke tafe ba saiya tsorata musamman daya tambayin shahida tace bata santa ba, batasan sunanta ba kuma gashi kullum sai ta zo ta kirata tana bata alewa ko biskit kuma tana tambayarta ina mamarta Madina?

ANAN MUKA KAWO KARSHEN LITTAFI NA 3

Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu muci gaba.
In kuma naga da masu so da yawa , akwai bonanza daya a kasa sai mu ci gaba anjima.
.
Saady Dan AuntyADON DAWA

LITTAFI NA HUDU

TRUE LIFE STORY

NA JAMILA UMAR TANKO (JUT)

Table of Contents

Chapters

3 chapters
  1. 1 ADON DAWA
  2. 2 PART 29
  3. 3 PART 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});