A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel
Read A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel, an emotional Hausa story filled with suspense, wealth, betrayal, hidden plans, family tension, and unexpected twists.
Shiru na yi ina kallon wani gefe tamkar ba dani take magana ba, ganin bani da niyyar amsa mata yasa ta koma mazauninta ta zauna sosai ta yi tagumi. Babu abinda take tunani illa miliyoyin da aka alqawarta mata, amma qiri-qiri ina neman yi mata buqulu.
“Ya zama dole in bullo mata bayan gida, wallahi bata isa ta jamin asarar wadannan makudan kudaden ba.” Abinda ta fada kenan a zuciyarta, sannan ta fara qoqarin sakin fuskarta don kar inyi tunanin tana niyyar cutar dani.
“Hajiya zan koma, tunda naga an gama bikin birthday din, Allah ya qaro miki shekaru masu albarka.”
Ina gama fadin haka na mika mata kyautar da na riko mata, wanda na nade shi a cikin leda. Ban saurari godiyar da take shirin min ba na nufi hanyar ficewa daga gurin taron.
Karar tsinin takalminta da yake bada qara qas qas akan tiles din daya malale qasan gurin taron ya tabbatar min da tana biye dani a baya.
Ban waiga ba sai da na isa jikin motata, abinda ya bani mamaki shine ganin wasu mata har su shida bayan Hajiya Danasha sun iso gurin motar tawa.
Unexpected Encounter
“Baby har zaki wuce?”
Wata Hajiya wacce taji kayan kudi hannu da qafa ta jefo min wannan tambayar, sai da na kalleta sama da qasa sannan nace:
“Eh.”
“Hajiya Danasha ce ta kara cewa:
‘Kunsan wannan zuwan da ta yi mana tsananin sa’a ne. Don haka karku damu, da sannu zumunci zai dore a tsakaninmu Insha Allah.’”
Read Also:
A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel
Ta fada tana kallon cikin idona, amma ban kalleta ba. Na bude motata na fada ciki ina qoqarin tayar da motar.
Da sauri Hajiyar ta bude qofar mai zaman banza ta sakamin wata babbar jaka tana fadin:
“Aysha ki gaida gida, nagode qwarai.”
Dan murmushi kawai nayi sannan nace:
“Nima haka.”
Ina gama fadin haka na ja motata na bar gurin, a zuciyata ina tir da halin Hajiya Danasha da qawayenta.
Tun a hanya na tsaya na yar da jakar da Hajiyar ta bani ba tare da na duba ko me aka zuba a ciki ba.
Return Home
Na isa gida qarfe goma sha daya da kwata na dare. Shigata cikin falon naga duk sun saki ajiyar zuciya sannan sun sauke tagumin da sukayi.
Dariya na tuntsire da ita daga bisani na ce:
“Waye ya mutu a gidan namu?”
Murmushin yaqe Baba Jummala ta yi sannan ta ce:
“Alhamdulillah tunda kin dawo gida lafiya, da fatan babu abinda ya sameki?”
Sai da na isa kusa da ita na dafa kafafunta cikin murmushi na ce:
“Babu abinda ya sameni Baba, kuma duk cikinsu babu wacce ta yi qoqarin cutar da ni. Na je lafiya na dawo lafiya da taimakon addu’ar da kukemin a ko da yaushe, saboda haka dukanku ku kwantar da hankalinku.”
Da haka na samu suka saki ransu muka ci gaba da wata hira daban.
Hidden Intentions(A Dalilin Da Namiji Book 2)
“Danasha wai ya kukai da ita?”
“Hmmm! Kedai bari Fulani, wallahi yarinyar nan tana da taurin kai fiye da yanda kike zato.”
“Amma kin kwadaita mata irin miliyoyin kudin da zata samu?”
“Qwarai kuwa, matsalar shine ita kanta yarinyar ba talaka ba ce. Idan kikaga irin motocin da take hawa da yanda take kashe daloli zaki tabbatar da haka.”
1 thought on “A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel”