Launin Fata Book 1 Complete Hausa Novel
Falon ya yi tsit gaba ɗaya. Iyalan gidan na ciki, kowanne kansa a ƙasa, suna sauraron abin da zai ci gaba da biyo bayan bambamin da dattijo Sir Abdulkareem Baba ke zazzagawa diyarsa Rabi’atul Badawiyya, wadda ke durƙushe a gabansa rungume da yarinyar goye da ba ta wuce watanni goma ba a duniya.
Ya ci gaba da faɗin, “Na taraku ne a nan don ku zama shaida, kamar yadda na taraku a baya kuka zama shaida a kan abin da na gaya wa Rabi, ko ba a yi haka ba?”
Sai da ya maimaita tambayar, babban cikinsu Rufa’i ya ce, “An yi haka, Abba. Duk da haka muna ba ka haƙuri…”
Ya daka masa tsawa, “Tunda ka tabbatar mini an yi haka, ba ni buƙatar a ba ni wani haƙuri. Dole a yi abin da na ce. Karɓi wannan baƙar ‘yar da ta zo mana da ita, ta raka ka har inda ta yi auran, ta mayar musu da ‘yarsu. In ba haka ba, wannan ba ta zama min gida.”
Ya juya, har ya kai bakin ƙofa ya dawo ya ce, “Kar in dawo in samu yar nan a gidan nan. Ran kowa zai iya ɓaci idan ba a yi abin da na ce ba. A kiyaye.”
Yana fita, Rabi ta ɗora hannu a ka ta fashe da kuka.
Ta ce, “Ni na shiga uku! Yaushe zan ji daɗi ne a duniya? Yarinya ‘yar watanni goma za a kai gidan da ba a ƙaunata, ni kaina ake ba? Gidan da wahalarsa ta sa na fito, ba don ba na son mijina ba. Wacce irin rayuwa za ta yi a gidan wannan ‘yar?”
“Ko shakka babu, ba zan ba da yata ba a kai ta. Gara in haƙura da zaman gidan nan.”
Mahaifiyarta ta taso cikin tausayawa ta ce, “Rabi, rayuwa fa Allah ce. Duk wanda Allah ya nufa zai rayu, babu wanda ya isa ya hana shi rayuwa. Ke ko duk duniyar nan za ta haɗu a kan ba ta son rayuwar wani, idan Allah ya nufa, rayayye ne zai rayu.”
“Ci gaba da kafiya ga mahaifinki abu ne da zai ci gaba da kawo illa ga rayuwarki. Ba zai bari ki samu nutsuwa da walwala ba. Idan kika yi haƙuri, Allah ya ji kanta ya kai ta hannu na gari.”
“Ki tuna, rayuwarki ba ita ce rayuwar wannan yarinya ba. Idan kin dage sai kin rayu da ita, sai Allah ya karɓi rayuwar taki, ita kuma tana raye. Tunda rayuwar ta Allah ce, rai da yake jikin mutum kayan aro ne. Duk wanda wa’adi ya cika, mai shi zai karɓi abinsa ne. Ki yi yaya.”
Rabi ta kalli diyarta, nono na bakinta. Baiwar Allah ba ta san abin da ake yi ba, tana barci.
Ta ɗaga ta, ta rungume ta ƙam-ƙam tana kukan da ya bai wa kowa tausayi.
Ta ce, “Nabila, zan ba da ke ba don raina ya so ba, sai don babu yadda zan yi. Ina fatan Allah ya kai ki hannu nagari wanda zai tausaya miki. Dangin babanki ba sa ƙaunata, na san ke ma ba za su ƙaunace ki ba. Amma na san rayuwa ta Allah ce.”
“Wannan jarrabawa ce. Wata rana labari za ta zama, domin babu wani abu da ya taɓa dawwama, daɗi ko wahala.”
A hankali ta mayar da ita cikin zanin goyonta, ta miƙa wa yayanta Rufa’i. Ya karɓa ya rungume ta a jikinsa a sanyaye.
Ya ce, “Ki yi haƙuri, Rabi. Dole ne komai girman da uwa ba ta son rabuwa, ballantana jaririya kamar wannan.”