Chapter 1
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
LABARIN ALJANI YA TAKA WUTA Part 1.
Duk wannan kadan ne daga cikin cikin kaunar da
yarinyar take nuna masa yau kusan shekaru shida
kenan tun suna firamire, kullum aikin t kenan
taso shi ta kuma yi masa wahala, kuma duk
sanda zai koma makaranta ita ke zuwa da motar
gidansu ta mayar dashi, bayan yan kananan siye-
siye da take yi masa har kudi take bashi. Amma
kuma abinda bata saniba shine mafi yawa daga
cikin kudin da take bashi a shaye shaye da
yawace-yawacen banza suke tafiya,domin in har
kana neman shaidani a duk fadin makarantarsu,
idan ka sami Nuraddin ka kare."Badawiyya
kenan". Nuraddin yace gami da dan tattausan
murmushi."Nuri 'darling' kenan". Badawiyya
tace.Ga mamakinsa sai ya ga ta dauko tsohuwar
jakar da take cewa bazata dauka ba, ta rataya
kafada."Zo mu tafi dan Allah Nuri so kake muyi
rana?Nuraddin na gaba dauke da jakankunan
ledar biyu, ita kuma na biye dashi a baya dauke
da mushenzakaran jakar Nuraddin. Duk inda ta
wuce, sai tabar iskar gurin da madaukakin
kamshin turaren dake jikinta, tana tafiya iska na
kada siraran gashin kanta wadanda ke kokarin
fitowa ta ciki farin gyalenta mai raga-raga dake
lullube da kanta.Hajara ta fito daga daki a dai-
dai lokacin da yaran biyun suka ratso tsakar
gidan. Badawiyya tayi sauri ta durkusa."mama
ina kwana?""Lafiya lau Badawiyya", Mahaifiyar
Nuraddin ta amsa, sannan kuma ta dubi
Badawiyya. "oh 'yar nan bakya rabuwa da
wahala, ko yaushe dai sai kinyi masa wahala,
'Badawiyya ta sunkuyar da kai cikin
girmamawada alkunya tace a hankali."ba.... Babu
komai mama"."An gode to, Allah ya saka miki
Badawiyya." mahaifiyar Nuraddin tace da ita
sannan ta juyo ga Nuraddin."Ga wannan ka tafi
da ita, malam ne yace a baka, maganin tsautsayi
ce, yace duk inda zaka, ka rinka tafiya da ita," Ta
mika masa wata 'yar kankanuwar laya wacce aka
rufeta da jara fata.Nuraddin ya karba, ya dubi
Badawiyya suka yiwa juna murmushi, sannan sai
yara biyun suka juya suka tafi."Allah ya kiyaye
Nura." mahaifiyarsatace dasu."To mama saina
dawo.Koda yaran suka fice daga gidan saibabar
Nuraddin ta dubesu sannan ta Dubi Badawiyya ta
girgiza kai sannan tace cikin zuciyarta "kai
wannan soyayya ta yaran nan da ban mamaki
take, yanzu ace yarinyakamar wannan ta
makalewa wannan yaro wanda shi ba komai ba,
to, meyiyuwa dai shima farin jinin malam zai
biyo." sai kuma abinda bata sani ba shine farin
jini ma yanzu ya fara, domin kuwa bada dadewa
ba farin jinin zai sake hada shi da wata sabuwar
budurwar mai ban mamaki.*** *** ***Nuraddin ya
mika, sannan yayi wanikwakwaran fito ya dirgo
daga kan gado, ya dubi sauran gadajen dake
dakin babu kowa akansu sai gado daya wanda
Auwalu surajo ke kwance a kai yana karatu. Karfe
tarada rabi na dare, duk sauran daliban dake
daikin sun tafi ajujuwan karatunsu domin bitar
abinda aka koya musu.Nuraddin ya durkusa karka
shin gadonsa ya janyo akwatinsa, sannan ya
bude ciki. A lafe a kasan akwatin, kudin kusan
Naira dubu biyar duk Badawiyya ce ta bashi
kudin. Nuraddin ya zaro dari daga cikin kudin ya
tura ciki aljihun gaban rigarsa. Sannan ne yaji
motsia bayansa, yayi firgigit cikin sauri yarufe
jakarsa don gudun kada wanda ke shigowa yaga
kudin da yake ciki. Duk yake dai Nuraddin yasan
babu wani shege a cewarsa, daya isa ya taba
kayansa koda wasa ballanta nada sunan sata,
amma yasan in an tambaye shi dole shima ya
bayar, tunda ana bashi, wannan shiyasa baya son
asan yanada kudi da yawa."Mene ne na boyewa
ai mu dama ganin falleliyar babynnan ta
kawokacikin arniyar motar nan munsan da
karfinka ka dira.Nuraddin ya juyo domin ganin
mai maganar, duk da dai kafin ya juya ma yasan
duk daniyar ba mai muryar nan sai wazirinsa
Nafi'u {BOSS}."shegen duniya daga ina haka,
dakin karatu ko makaranta?" Nuraddin yace
sannan ya mika masa hannu suka tafa tas!
Kamar an mari jaki da faranti."wace irin
makaranta kuma banda wannan da muke ciki?"
Nafi'u boss ya tambaya lokaci guda kuma ya
zauna bakin gadon Nuraddin."Ku dubu allonku
daya nake nufi".Oh shet! Men, ai abin da ya kawo
ni kenan, ance kuwa fim din yau wani arnen
Indiya ne, ana fadamin labarin sai ka fado min a
rai, to ni sam-sam ban dauka ka bayyana ba to
shine hamza siyasiya ya ce min ai dazu yaga
bayyanarka kuma wai wata ba kyau din beby ce
ta kawoka,nan da nan na garzayo, domin yau duk
aljihun ka zamu shiga sinimar nan dan bai yiyuwa
fim din nan ya wuce mu". Nafi'u boss yace ya
dan tsagaita yana mayar da numfashi."to uban
shegen surutu ka gama tsarani din?""Ah! Haba
Nuri namu, kai kasan ai mu da kai haka muke".
Ya hada tafikan hannunsa biyu guri guda."wai ina
su Basiru logarizim ne?" Nuraddin ya tamba.Duk
suna can bayan 'central hall' kai muke jira kawai
yau duk aljihunka zamu shiga sinima kai harsigari
ma yau ba mai siya da kudinsa......
Aljani Ya Taka Wuta!..2
;
;
sunyi sanadiyar faduwar dalibai da dama
jarabawa, haka nan tun da suka shigo
makarantar basu da aiki sai shiririta, yau kusan
shekaransu shida kenan, wannan itace
shekaransu ta karshe a sakandiren. Da yawa
daga cikin su suna zuwa makarantar ne kawai
don ace sun gama, amma badan su sami sa
kamako mai kyauba. Ba kowanne mutum bane,
ba kuma ko wanne mai karfin zuciya bane zai
baƙin kungurumin dajin dake tsakanin makarantar
zuwa cikin gari ba, domin tafiyar kusan kilo mita
biyar ne zuwa cikin garin, an kuma ce zai hanyar
cike take da aljanu da kwumakwumai, amma
hakan bai tsorata su ba musamman Nuruddin,
domin shi ko babu mai zuwa zai gwab kama
hanya abinsa shi kaɗai, dole ne sai yaje. Anyi
musu nasiha sunkiji an horesu da bulala duk
banza kai har wa'azi na anyi musu. Malam
mahmud bashir malamin arabiyyane a
makarantarsu Nuruddin ya taɓa cewa dasu
watarana suna ɗaukar darasi " kuyi a hankali
yara, mun sami labarin akwai wasu takadarai
acikin ku waɗanda kullum kwanan duniya sai sun
shiga gari sunyi kallo a sinima, to ina
shawartarku ku da ku bari, ba don komai ba
kuma sai don lafiyar ku, kunsha da jin haɗarin
dake tattare da wannan dajin na irin kwankwamai
dake ciki, amma don taurin kai ku nace sai kun
fita cikin dare. To wallahi kuyi a hankali inba so
kuke watarana wani ya farka a cikinku da siririn
hannu shanyayye kamar lagwanin risho ba "
yaran suka fashe da dariya to amma nasihar
malam mahmud bashir tamkar zuga ce ga
takadaran yaran biyar. "kai rabu dashi ajawo,
muzai yiwa wa'azi da wani dogon gemunsa
kamar buroshin wanke kwalabe ". Nuruddin yace
da yaran su kuma suka bushe da dariya. Watanni
biyar kenan da faruwan hakan.
****
Cikin sinimar ya dauki hayaniya lokacin da
bangwaleliyar kalmar *{ THE END }* ta yiwa
kanta gurin zama a kan farin allon sinimar. Ba a
dade ba su Nuraddin suka fito, suka kamo hanyar
dawowa makarantar karfe daya da rabi na dare,
domin ranar fim biyu akayi a sinimar.Yaran biyar
suka keto cikin bakin daji, bakajin komai sai
hayaniyar yaran wadanda ke tafiya sunata
hayaniya gami da tada kura kamar shanu. Babu
alamar farin wata a cikin dajin, babu kuma wani
kwakkwaran sauti sai jefi-jefin kukan gyare dana
tsuntsaye nan da can."Kai ku tsayani na taka
kaya." basiru logarizim yace dasu."Gafara can
malam waye zai tsayaka, ka kwana ma a nan
mana waya damu da kai". Nuraddin yace
dashi."To kada ku tsaya din mana wata tsiyar
ce". Sauran yaran suka busheda dariya sannan
sukayi gaba suka barshi gurin tsugunne yana ko
ƙarincire kayar.Basu dade da barinsa ba, sai
basiru yaji motsi a bayansa yana juyawa sai
sukayi ido biyu da wata katuwar kyanwa baƙa ƙirin
da ita kamar kwanta. Idanunta jajaye suna sheki
kamar kwalba a cikin rana. Basiru ya dubi magen
itama ta dubeshi , iska taci gaba da karkada
ganyayyakin bishiyoyin dake zagaye sannan ya
rarumi wani bushashen itacen bishiya dake kusa
da shi ya nufo magen, amma sai taki
guduwa."Ah! Kaga marar kunya! Basiru ya fada
cikin karaji sannan sai ya ɗaga itacen yakai mata
duka. Tun kafin itacen yakai ga kan magen yaji
hannunsa ya yi sakh yayi lararraf dashi kamar
tsumma, babu nauyi, ga mamakinsa sai yaga
hannun yana motsewa a hankali a hankali har ya
koma kamar kaurin kyandir, sannan sai yaji
hannun nasa ya fado jikinsa tamkar dama ba a
jikinsa yake ba."wayyo Allah na shiga uku! Ah!
Ah! Ah! Nura! Dan Allah kuzo na shiga uku.....Na
lalace".Sannan sai wata kakkausar murya ta kece
da dariya, muryar babu dadin ji kamar muryar
jaki.Ihun da suka ji a bayansu, shiyasa su juyowa
lokaci guda tamkar sojoji yayin faretin ban girma
a gaban shugaban kasa."Kunji wannan shegen
kamar sunana yake kira, ihun menen...Sauran
maganar ta makale a fatar bakin nuraddin lokacin
da sukaji an sake ihun, a wannan karon har da
kuka. Yara hudun suka dubi juna sannan suka
dubi ciki duhun dajin inda suka baro Basiru. Kuzo
mu ko mu gano shi. Nuraddin yace da sauran ko
wannensu tsumayake, sun gama tsorata don haka
sai sukayi sororo kamar gumaka suna kallon
Nuraddin."ko bakwaji nane?
¤¤¤¤
A dai dai lokacin ne suka hangi basiru ya ratso
cikin duhun dajin yana tafiya yana hada hanya
kamar dan giya hannunsa na hagu a dafe
ahannunsa na dama yana kuka, sannan sai
kakkausar muryar mai kama data jaki ta sake
kecewa da dariya. Yaran suka fara waige
waigecikin firgici a tsorace sai dai kuma basu ga
mai dariyar ba, duk abin nan da akeyi, shi
Nuraddin ko ajikinsa, domin idan akwai wani
abuda ake kira tsoro a duniya shi baima sanshi
ba."yau ga shegantakar banza inba tsoro ba a fito
fili mana!" Nuraddin yace cikin karaji. Dajin ya
amsa kuwwar abin da yace.Cikin firgici, Nafi'u
Boss ya matso kusa daf da Nura ya dakeshi a
baya."Me...Menene kuma haka nura, so kake a
halaka mu a banza?" Yace bakinsa na
rawa.Nuraddin ya buge hannunsa gefe guda
sannan yayi sauri ya tari Basiru wanda ke tafe
yana tangadi kamar dan giya. Nuraddin na taba
shi sai basiru ya zube kasa yana kuka.
Aljani ya Taka Wuta!.....3
-
-
-
yana tangadi kamar dan giya. Nuraddin na taba
shi sai basiru ya zube kasa yana kuka, yamu
sashshen shanyayyen hannunsa ya fadi gefe guda
sharaf kamar mushen maciji.Wata sassanyar iska
ta fara busawatsakanin yara biyar gashi dai ba
lokacin sanyi bane amma iskar tafi iskar sanyi
sanyaya kashi da bargo. Nuraddin yaji gashin
jikinsa duk sun mimmike. Ko kusa ko alama,
dafarko Nuraddin bai tsorata da ihun da yaji ba,
to amma ba karamar girgiza yayi ba lokacin
dayaga hannun basiru ya tsotse ya yamushe
tamkar lawashin albasa a cikin rana. Ba karamin
bala'i bane ace 'yan mintoci kadan kuna tare
damutum kowa da hannayensa biyu, amma kuma
tsakanin wani dan lokaci ace hannunsa dayan ya
shanye ya zamama daya da rabi.Nuraddin ya
tallafi Basiru ya tashe shi tsaye sannan yace da
sauran kuzo mu tafi.Samarin suka bishi a baya
sumu-sumu ba magana. Fara tafiyar ke da wuya
sai karfin iskar yafara karuwa, saida takai ta
kawo samarin na tafiya da kyar sbd karfin iska.
Wannan al'amari shi yasa samari biyar din suka
dada rikicewa, tuni sun fara tunanin anya kuwa
zasu koma da hannunsu bibiyu? Kamar hadin
baki lokaci guda sai kowanne daga cikin yaran
banda Nuraddin goggoya hannayensu a bayansu
wai a tunaninsu yin hakan na iya kare
hannayensu daga shanyewa irin na Basiru. Abinda
yafi basu tsoro shineduk irin mahaukaciyar iskar
dake karkadasu tana wasa dasu kamar shanya
hakan baisa koda ganye daya daga cikin
ganyayen bishiyoyin dake wajen motsi ba. Hakan
shaya tabbatar musu cewa iskar sukadai take
kadawa a cikin dajin domin inhar basu kadai take
karkadawa ba yaya to ganyen bishiya baya
motsi?Adai dai lokacin samarin dake ratsawa ta
cikin iskar domin tsira daransu, sai kwatsam wani
abu ya bayyana a gabansu. Babu zato
babutsammani wani mai kamar bakin labule ya
ziraro gabansu. Saboda tsananin duhun dake
gurin idan suka juya baya basa hango bayansu.
Adai-dai lokacin ne kakkausar muryar ta sake
kecewa da dariya mai hargitsa hanjin cikin
mutum, awannan karon dariyar harda
kyakyatawa. Su Nuraddin sukayi tsumu suna
dube-dube ga iskar na kadawa amma gumi kamar
ruwa ake zuba musu a jiki, da zaka tsaga wani
acikinsu dazaiyi wuya ka sami jini ajikinsu
saboda firgici."kudaina waige-waige! Domin
kuwaduk wani waige-waigenku bazai iya hango
muku ni gaba dayana, sai daikuna iya ganin
tsakiyar kaina duhunda kuke gani a gabanku ba
duhu bane nice na tsare hanyar tsakiyar kaina
kuke gani haka bakin kirin".Kaukausar muryar tayi
shiru ga barin magana mummuna sannan sai taci
gaba da cewa. "daga yau saiyau, kada na kara
ganinku akan hanyar nan cikin dare, domin nan
hanyar mahaifina ce ba taku bace, in banda
rashin kunyarku ta bil'adama ina ku ina bin
hanyar sarkin sarakunan aljanun duniya. Zan
baku hanya ku wuce' sai dai kuma duk wanda ya
sake tunanin karan banin b tanan gurin to na
tabbatar masa cewa saina nannadeshi kamar
alkaki.Kamar budin ido kakkausar muryar nayin
shir duhu ya yaye iskar ta tsaya cak, sannan sai
dajin ya dawokamar yadda yake. Yaran suka dubi
juna jikinsu na diga kamar an narkasu sbd gumi.
In banda shanyayyen hannun Basiru da sai ka
rantse da Allah babu abinda ya faru.Yara ukun
suka dubi Nuraddin wanda ke rungume da basiru,
sannan kamar daman sun shawarcijuna sai suka
ruga da gudu suka nufi hanyar makaranta.Basiru
ya dubi yace yanzu kaima guduwa zakayi ka
barni?"Haba Basiru ah ko nawa hannun zata
shanye bazan gudu na barka ba. Bakomai Basiru
ka barni da ita zamu sake haduwane"."Tayaya
zaku hadu? Basiru ya tambaya har yanzu a
jingine yake ajikin Nuraddin."Bata ce kada
musake biyo hanyar nan ba, to wallahi ni banga
uban da ya isa ya hanani bita hanyar nan ba
tunda ba hanyar ubanta bace......Kafinya rufe
bakinsa, sai yaji muryar nan na cewa kayi a
hankali marar kunya idan baso kake na nanna
deka ba! Dajin.........Nuraddin ya dubi basiru
wanda tuni ya sume a jikinsa saboda tsoro. Don
haka sai ya sungumeshi kamardamin itace ya
dorashi a kafada ya kama hanyar makaranta
dashi. Yana tafiya shanyayyen hannun basiru na
dukan gadon bayansa. Fara tafiyar keda wuya sai
yaji mummunar muryar ta sake kecewa da dariya.
Daga nan kuma ba'a sakecewa dashi komai
ba."zaki yi dariya"! Nuraddin yace a fusace.
-
**** **** ****
Tun acikin daren da al'amarin ya faru labarin ya
iske duk kusan rabin makarantar, sannan kafin
tara na safiya ranar, labarin ya gama mamaye
cikin gari kamar wutar daji.Mutane sukai ta bada
labari iri-iri nagaskiya dana karya. A cewar wani
mai gadin makarantar wanda ke bada labari a
cikin gari, yace duk kusan yara biyar din
shanyayyen hannu suka shigo makarantar, kuma
wai kowannensu da ido daya yadawo, sannan
kuma ya dada da cewar wai duk agabansa aka
wuce da yara biyar din duk kuwa da
cewarrabonsa da gadin dare tun wancan satin da
ya wuce.A safiyar ranar aka tara daliban
makarantar gaba dayansu a gurin taron dalibai,
sannan malam mahmud malamin arabiya ya sake
yin nasiha gami da dada jan kunnen dalibai.
ALJANI YA TAKA WUTA 4.
Nuraddin ya yi mika, sanna ya yi wani
kwakkwaran fito ya dirgo daga kan gado, ya
dubi sauran gadajen da ke dakin babu kowa
akansu sai gado daya wanda Auwalu Surajo
ke kwance a kai yana karatu. Karfe tara da
rabi na dare, duk sauran daliban da ke
dakin sun tafi ajujuwan karatunsu domin
bitar abinda aka koya musu.
Nuraddin ya durkusa karkashin gadonsa ya
janyo akwatinsa, sannan ya bude ciki. A lafe
a kasan akwatin, kudi ne kusan naira dubu
biyar duk Badawiyya ce ta bashi kudin.
Nuraddin ya zaro naira dari daga cikin kudin
ya tura cikin aljihun gaban rigarsa. Sannan
ne to ya ji motsi a bayansa, ya yi firgigit
cikin sauri ya rufe jakarsa don gudun kada
wanda ke shigowa dakin ya ga kudin da ke
ciki. Duk da yake dai Nuraddin ya san babu
wani shege a cewarsa, da ya isa ya ta6a
kayansa ko da wasa ballantana da sunan
sata, amma ya san in an tambayeshi dole
ne shima ya bayar, tunda ana bashi,
wannan shi ya sa ba ya son a san yana a
kudi da yawa.
"Mene ne na 6oyewa, ai mu dama ganin
wannan falleliyar Bebinnan ta kawo ka cikin
arniyar motar nan mun san da karfinka ka
dira.
Nuraddin ya juyo domin ganin mai maganar,
duk da dai kafin ya juya ma ya san duk
duniya babu mai muryar nan sai wazirinsa
Nafiu (Boss).
"Shegen duniya daga ina haka, dakin karatu
ko makaranta?" Nuraddin ya ce, sannan ya
mika masa hannu suka tafa tas! Kamar an
mari jaki da faranti.
"Wacce irin makaranta kuma ban da wannan
da muke ciki?" Nafiu Boss ya tambaya
lokaci guda kuma ya zauna bakin gadon
Nuraddin.
"Ku dubu allonku daya nake nufi".
"Oh Shet! Men, ai abin da ya kawo ni ke
nan, an ce kuwa Fim din yau wani arnen
Indiya ne, ana fadamin labarin sai ka fado
min a rai, to ni sam-sam ban dauka ka
bayyana ba, to shi ne Hamza Siyasiya ya ce
min ai dazu ya ga bayyanarka kuma wai
wata ba kyau din Bebe ce ta kawoka, nan da
nan na garzayo, domin duk a aljihunka
zamu shiga sinimar nan, dan bai yiwuwa
Fim din nan ya wuce mu". Nafiu Boss ya
dan tsagaita yana mayar da numfashi.
"To uban shegen surutu ka gama tsarani
din?"
"Ah! Haba Nuri namu, kai ka san ai mu da
kai haka muke." Ya hada tafikan hannunsa
biyu guri guda.
"Wai ina su Basiru Logarizim ne?" Nuraddin
ya tambaya.
"Duk suna can bayan 'Central Hall' kai kawai
muke jira, yau kowa a aljihunka zai shiga
kallon fim, kai har sigari ma yau babu me
saya da kudinsa."
Cikin murmushi sai Nuraddin ya kama
hannun Nafiu Boss suka yi waje. Ko da suka
nufi kofar Hostel din, sai Nuraddin ya dubi
Nafiu ya ce. "Ah, yau zaka shigo da
mutuniyar taka ne?q
"Wa kenan?" Nafiu ya tambaya yana
kallonsa.
"Ladi dala-dala mana."
"Oh shege Nuri, ashe baka manta ba, kai ma
kasan ai dole ne na shigo da ita tunda ka
shigo gari."
Mintina biyar da yin hakan, sai samarin
biyar suka dunguma suka fice daga
makarantar zuwa cikin gari.
Wadannan samari biyar shedanun mutane
ne, domin Allah ne kawai Ya san iya yawan
daliban da suka dora akan hanyar banza.
Sunyi sanadiyar faduwar dalibai da dama
jarabawa, haka nan tun da suka shigo
makarantar ba su da aiki sai shiririta, yau
kusan shekararsu ta karshe a sakandiren. Da
yawa daga cikinsu suna zuwa makarantar ne
don kawaia ce sun gama, amma ba dan su
sami sakamako mai kyau ba.
Ba kowanne mutum ba ne, ba kuma
kowanne mai karfin zuciya bane zai iya
ratsa bakin kungurmin dajin da ke tsakanin
makarantar zuwa cikin gari ba, domin tafiyar
kusan kilomita biyar ne zuwa cikin gari, an
kuma ce wai hanyar cike take da aljanu da
kwankwamai, amma hakan bai ta6a tsorata
yaran ba, musamman Nuraddin, domin shi
ko da babu mai zuwa zai iya kama hanya
abinsa shi kadai, dole ne sai ya je. An yi
musu nasiha sun ki ji, an horesu da bulala
duk a banza, kai har wa'azai ma an yi musu.
Malam Mahmus Bashir malamin Arabiyya ne
a makarantar su Nuraddin ya ta6a cewa da
su wata rana suna daukar darasi.
"Ku yi a hankali,mun samu labarin akwai
wasu takadirai a cikinku wadanda kullum
kwanan diuniya sai sun shiga gari sun yi
kallo a sinima, to ina shawartarku da ku bari,
ba don komai ba kuma sai don lafiyarku,
kun sha fa jin labarin hadarin da ke tattare
da wannan dajin da irin kwankwamai da ke
ciki, amma don taurin kai ku nace sai kun
fita cikin dare. To wallahi ku yi a hankali in
ba so ku ke wata raba wani ya farka a
cikinku ya tsinci kansa da siririn hannu
shanyayye kamar lagwanin risho ba" Yaran
suka fashe da dariya.
To amma nasihar malam Mahmud Bashir
tamkar zuga ce ga takadiran yaran nan
biyar.
"Kai rabu da shi ajawo, mu zai yiwa wa'azi
da wani dogon gemunsa kamar burushin
wanke kwalabe"
Nuraddin ya ce da yaran, su kuma suka
bushe da dariya. Watanni biyar ke nan da
faruwar hakan.
BY NAZIR ADAM SALIH.
.............ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN
LABARI {5}.......
Nuraddin ya dubi basiru wanda tuni ya sume a
jikinsa saboda tsoro. Don haka sai ya sungumeshi
kamar damin itace ya dorashi a kafada ya kama
hanyar makaranta dashi. Yana tafiya shanyayyen
hannun basiru na dukan gadon bayansa. Fara
tafiyar keda wuya sai yaji mummunar muryar ta
sake kecewa da dariya. Daga nan kuma ba'a sake
cewa dashi komai ba.
"zaki yi dariya"! Nuraddin yace a fusace.
* * *
Tun acikin daren da al'amarin ya faru labarin ya
iske duk kusan rabin makarantar, sannan kafin
tara na safiya ranar, labarin ya gama mamaye
cikin gari kamar wutar daji.
Mutane sukai ta bada labari iri-iri na gaskiya
dana karya. A cewar wani mai gadin makarantar
wanda ke bada labari a cikin gari, yace duk kusan
yara biyar din shanyayyen hannu suka shigo
makarantar, kuma wai kowannensu da ido daya
yadawo, sannan kuma ya dada da cewar wai duk
agabansa aka wuce da yara biyar din duk kuwa
da cewar rabonsa da gadin dare tun wancan
satin da ya wuce.
A safiyar ranar aka tara daliban makarantar gaba
dayansu a gurin taron dalibai, sannan malam
mahmud malamin arabiya ya sake yin nasiha
gami da dada jan kunnen dalibai akan fita daga
cikin makarantar.
"ku guji fita yawace-yawacen banza marasa
amfani cikin dare, kuyi zamanku a makaranta ku
karanta littattafan ku yafi muku. Na tabbata indai
dalibi ba fita yayi ba to Allah subhanahu wata'ala
bazai baiwa kowanne aljani ikon cutar daku ba,
"wasu daga cikin dalibai sukayi kabbara. Lokacin
da malam mahamud yazo karshen jawabinsa.
Daga karshe aka yiwa su Nuraddin horo mai
tsanani, sannan aka basu gargadi na karshe
wanda daga shi idan suka sake laifi to korarsu
za'ayi.
"kai! Rabu dasu, wa zasu yiwa wa'azi"! Nuraddin
yace da Nafi'u (BOSS) lokacin da suke kan
hanyar ajujuwan karatunsu bayan an sallamesu
daga gurin asambili.
"Ni dai nasan wannan mai muryar jakin bata isa
ta hanani fita kallon film din yau ba don wallahi
canis za,a yi da 'American film' ballen kuma
wa'azin wani mai dogon gemu, 'yar bulalarshi
ashirin! Sufa sun dauka wai duka zai hanamu
abinda mukeyi ko? Nuraddin ya tambaya yana
duban abokinsa Nafi'u.
Nafi'u yayi masa irin kallon dazaka yiwa
kyankyason daya fada a cikin furaraka yace.
"kanka daya kuwa Nura"?
"to in ba daya bane ina na baro dayan ko kai da
kai biyu kake ganina? Nuradadin yace yana jijjiga
littafin dake hannunsa a dai-dai lokacin da suka
karaso kusa da ofishin shugaban makarantar.
"To inba haka ba mezai sa da hankalinka da
komai ka kai kanka ga halaka, aini wallahi ko
karatu dare na daina fita, haka kawai naje nima
hannuna ya yamushe tab! Ai idan ka ganni a
lahira to kaini akai bada kafata naje ba.
Nuraddin ya dubeshi ya fashe da dariya. "wallahi
bansan kai mugun matsoraci bane sai yau, yanzu
kai da haka kake da tsoro har ake kiranka da
Boss, to in dai hakane daga yau bani ba kai
domin bana abota da matsoraci".
"Wallahi tafi nono fari". Nafi'u yace. "Domin idan
mutum ya biye ta kai sai ya tsinci kansa a
kushewa kwanansa bai kareba.
"Ai me rabon ganin badi sai ya gani ko ana ruwan
kibiya daga sama da kasa.
Nafi'u ya girgiza kai kana ya dubi nuraddin dai
dai lokacin da suka kawo kofar ajin. "Kana nufin
yauma fita zakayi kenan"?
"Ai idan kaji fita daya kenan ma, kai dai tsaya
nan kana shirme, haka kawai ka bari wasu
kananan kwankwamai da muryar jaki su mayar
dakai laushi, ka jirani na dawo na baka labari".
Nuraddin ya juya abinsa zai yi gaba.
Nafi'u ya sa hannu ya rike rigarsa ta baya.
"Nura kaga fa wallahi........"
Bai karasa ba Nuraddin ya tankwabe hannunsa
yana zazzare idanu. "Kada ka bata bakinka Nafi'u
domin banga dalilin dazaisa ta shanyewa dan
uwanmu hannu ba mu kyaleta tunda tace kada
mu sake bi ta hanyar, to ni yau saina bi na
tambayeta dalilin shanewa dan uwanmu hannu."
yayi shiru sannan batare da ya dubi Nafi'u ba wai
kai Nafi'u (BOSS), to in gaskiya ne yau ka biyoni
muga iyakacin taurin kanka". Nuraddin ya wuce
cikin ajinsu ya bar Nafi'u nan tsaye yana kirga
takun sawunsa.
"Mahaukaci ne, tabbas mahauka cine. Babu
mamaki abinda ya faru jiya ya tabashi". Nafi'u
yace da kansa.
Nuraddain ya shiga ajin Nafi'u na biye dashi a
baya. Shigarsu keada wuya sai dalibai suka dauki
ihu baki daya 'boss! Boss! Suka daga Nafi'u
sama suna yawo da shi acikin ajin da kyar suka
ajje shi.
Nafi'u ya dubesu sannan yace "Ga Boss nan a
gabanku". Ya nuna Nuraddin da dan yatsansa
hannunsa na rawa. Har yanzu ganin mahaukaci
yakewa Nuraddin Nafi'u ya zagaya ya nufi gurin
zamansa, a ganinsa kowanne lokaci zai iya
hawansa da duka.
"A'a yau kuma guduna kake yi?" Nuraddin yace,
sannan ya fashe da dariya. "karyar banza ashe
dai gabama da gabanta wai Aljani ya taka wuta,
ka kake cewa wai ko shedan ne mutum baka
tsoronsa."
anya kuwa nima xan iya bin Nuraddin domin jiyo
muku abinda zai faru?
Sai kuma mun sake haduwa daga
Aljani Ya Taka Wuta!....6
-
-
-
-
Dajin yayi shiru bakajin komai sai motsin
ganyayyaki bishiyoyi dake gogayya da juna
sakamakon iskar dake busawa cikin wasu lokuta
kuma akwai jefi-jefin kukan tsuntsaye da sautin
ruwan dake gudana cikin koramun dake zagaye
da gurin.
-
Nuraddin yaci gaba da tafiya, amma har yanzu
jikinsa rawa yake, domin daya daga cikin
kawunannan masu gemu daya gani, yaso yayi
kama da kan malam mahmud, malamin
arabiyarsu, ni kuma wanda na gani yaso yayi
kama da kan mai karanta labarin nan hehehe.
-
Bai dade da fara tafiya ba sai yazo daf da inda
hanyar ta rabu gida biyu, hanyar datayi gabas,
itace zata kaishi har zuwa makaranta. A daf da
gurin tsakanin wasu bishiyoyi guda biyu, wata
katuwar tsamiyace mai duhun ganye. Anan ne to
Nuraddin yaga abin mamaki.Yana zuwa inda
hanyoyin suka rabu, sai ya mike cikin sauri yabi
wacce ta nufi gabas din ba zato ba tsammani sai
bishiyar tsamiyar dake tsakanin bishiyoyi biyun ta
girgiza sannan saita tunbuko daga cikin kasa,
jijiyoyinta a waje tsirara, sannan saita nufi
tsakiyar hanyar da Nuraddin kebi ta dasa kanta a
hanyar. Nuraddin yayi turus ya tsaya cikin
kaduwa, yayi kamar ya koma da baya, to amma
idan ya koma da baya din ina za shi? Jikinsa na
rawa sai ya karkata yabi daya hanyar data nufi
kudu lokaci guda sai bishiyar ta sake tunbukewa
ta tashi sama sannan ta sauka a tsakiyar hanyar
daya fara bi ta sake dasa kanta. Nuraddin ya
sake yin turus ya tsaya akaro na biyu, sai dai
wannan karon lokaci guda ya juya a razane zai
gudu, sai yaga bakin labulen duhun nan ya sauko
a gabansa da sama bakinkirin babu hanyar gudu.
Ga yamma tayi bakinkirin babu hanyar wucewa
ga gabas bishiya ta tare hanya. Nuraddin ya juya
nan, ya juya can yana neman hanyar gudu lokaci
guda kuma kwakwalwarsa nakokarin tuno addu'a
kowacce irice ma, sai dai rabonsa da rike addu'a
ma, tun yana karatun dare a waje babansa.
A dai-dai lokacinne wata katuwar mage ta keto
da gudu daga cikin bakin duhun daya rufe
bayansa, ta nufi kan katuwar bishiyar. Hawan
magen keda wuya sai bishiyar tayi girgiza nan da
nan ta rikide ta koma wata irin halitta mai zako-
zakon hakora kamar kibiya, gashin kan halittar
tamkar kayoyin aduwa. Halittar tana da kofato,
sannan abin mamaki kuma shine dukkan jikinta a
lullube yake da gashi kamar tunkiya.Nuraddin ya
dubi jibgegiyar halittar ya rufe idanunsa yana mai
fatan dama mafarki yakeyi, sai dai kuma arufe
idanun nasa ma bai hana shi ganinta ba. Ya sake
bude idanun nasa ma bai hana shi ganinta ba.
Yasake bude idanun har yanzu dai tana nan
shirim! A gurin tana dubansa da jajayen idanunta
masu kamar garwashin wuta."Bance kada na kara
ganinku a hanyar nan cikin dare ba"? Ta bugawa
Nuraddin tsawa hayaki na fita daga bakinta
kamar salansar mota."kai kafi kowa taurin kai
ko"?Nuraddin yayi tsaye yana kallonta, yana
kuma sauraronta. Tun abin na bashi tsoro harma
ya soma bashi haushi."shin baka ji kashedin da
nayi maka bane"?"Banji ba"! Nuraddin ya samu
kansa yana mai cewa. Bai san lokacin da kalmar
ta subuce masa ba, amma ya gama yanke kauna
cewa wannanitace kalmar karshe da zai furta a
duniya, jira kawai yake yaji tayi sama da shi ta
jefa a cikin wangamemen bakinta mai kama da
kofar gari.Shiru-shiru baiji komai ya faru ba, babu
kuma alamar motsin komai a dajin sai sautin
zubar yayyafar ruwan da har yanzu bai daina
zuba ba. Nuraddin ya bude idanunsa a hankali, ga
mamakinsa sai ya hanyar wayam babu matar
nan ta bace haka nan bishiyar tsamiyarnanma ta
koma inda take ta zauna. To amma lokacin da
Nuraddin ya waiwaya bayansa, saiya ga har
yanyu duhun dake bayansa bai yayeba. Wannan
shiya dada tabbatar masa da cewa har yanzu
yana cikin hadari, domin ya san mai zako-zakon
hakoran batayi nisa da inda yake ba.Daga inda
Nuraddin ke tsaye yana jiyo rugugin aradu jefi-jefi
a can wani bangare na cikin dajin. Ba'a dade ba
sai aka sake kwatsama wata aradun mai karfin
gaske wannan karon ma har tafi wadanda akayi a
can baya tsoratarwa. Walkiya mai hasken gaske
ta biyo bayan aradun. A cikin'yan dakikun ne to
Nuraddin ya fara ido biyu da wata kyakyawar
sura. Walkiya ta haskaka wajen, Nuraddin yakai
idanunsa ga ruwan dake gudu a gefen hanyar, a
cikin ruwanne to yaga kyakyawar fuskar ta tana
masamurmushi."Yau na gamu da gamona".
Nuraddin yace cikin zuciyarsa. A daidai wannan
lokacinne sai yaji wani irin ni'imtaccen kamshin
turare ya mamaye gurin, sannan ne to ta
bayyana a gabansa a zahiri kamar an jehota daga
sama, fuskarta na sheki da annurh, hasken
kyakykyawar fatar jikin budurwar shiya haskaka
dajin. Kyawun budurwar bashi misaltuwa ga dan
adam. Doguwa ce ba can ba'yar shafalfal mai
tsukakken jiki da kyawun girar idanu, fatar
bakinta narai narai dasu jajaye suna kyalli kamar
ka taba jini ya fito, gashinta abin kallo da daukan
hankalin duk wani da namijin duniya....
Aljani Ya Taka wuta!.....7
-
-
-
"Jarumi Nuraddin". Tace dashi tana haskaka
fuskarsa da tattausan murmushin Allah kashe ni
dan dadi.Nuraddin ya dubeta duban nutsuwa tun
daga sama har zuwa kan kafafunta. Hakika duk
halittar dake jikin budurwar babu makusa, tunda
yake bai taba ganin halitta mai kyawunta ba, ko
shakka baya yi, yasan ta ninka Badawiyya kyau
nesa ba kusa ba. Ga mamakin Nuraddin sai yaji
duk tsoro da fargaba sun sake shi lokaci guda
kamar cirar kaya.To amma fa duk wannan kafin
idanun Nuraddin ya kawo ga kasan kafarta ne.
Ko da idanunsa suka kawo ga kafarta, sai
kamannin sha'awar dake fuskarsa suka
sauya,suka rikide zuwa tsoro da fargaba. Ba wani
abune yasa jikinsa sanyi ba, sai ganin
kyakykyawar buduwar dake gabansa bata da tafin
kafafu irin na bil'adama, maimakon hakan, sai
kafta kaftan kofato irin na giwa.Kai Allah wadan
naka ya lalace. Nuraddin yace cikin zuciyarsa
lokacin da yaga kofaton. Ga doki hardoki amma
kofaton na sakainane. Ya sake cewa da
kansa.Buduwar ta dubeshi yayin data tabbatar ya
kare mata kallo, sannan ta fara matsawa kusa
dashi.Nuraddin ya yi tsalle gefe guda don gudun
kada ta taka shi da kofato."kada kaji tsorona
Nuraddin, domin yanzu tsakanina dakai babu cuta
ko cin amana, sai so da kauna da amincewa, duk
duniyar nan a yanzu babu wanda nake kauna sai
kai, ba dan komaiba kuwa sai dan ganin kaine
mutum na farko daya fara ganina a mummunar
kamata bai sume ba".Ta danyi shiru ga barin
daddar magana cikin murya mai kama da sarewar
mutanen hindu, sannan taci gaba da ce.Dubeni da
kyau Nuraddin, kyakykyawa ce kana sona?
Nuraddin ya dubeta tun daga kan kyakykyawar
fuskarta har zuwa kan kofatonta jikinsa na rawa
ya sake dubanta yace."Tabbas babu wani dam
adam dazai ganki yace baya sonki, amma idan
yana da hankali babu abin dazai sa ya kusanceki
ballantanamaharya soki da wadannan kaba-
kaban kofato a kafarki. Ya nuna kofaton dake
kafarta, sannan ya dada ja da baya kamar wanda
ake bi da wuta.Budurwar mai kofato, ta dubeshi
sannan ta hade fuska tace"da wani ne ya fadi
haka bakai ba saina tsotse jininsa na shanye
bargonsa, sannan na karairaya kashinsa na
watsar a bayan duniya.Tsohon lokaci buduwar
tana kallonsa kawai batace dashi komai ba. Jikin
Nuraddin ya fara tsuma domin tunaninsa rikidewa
zatayi zuwa jibgegiyar halittar nan ta dazu,to
amma ga mamakinsa sai budurwa ta haskake shi
da wani tattausan murmushi.Ka daina jin tsorona
Nuraddin, ai na riga nayi maka alkawarin bazan
taba cutar dakai ba, kuma ni mai kokari ce gurin
cika alkawari, ba kamar ku bane bil'adama.Budur
war mai kofato ta ja baya, sannan saita durkusa
kasa, kyakykyawar doguwar rigar dake jikinta mai
sheki da kamshin gaske ta sauko ta lullube
kofaton. Kusan tsahon dakiku ashirin, sannan ta
sake mikewa tsaye. Tun kafin doguwar rigar ta
gama dagewa sama Nuraddin ya hango santala-
santalan kafar kyawawan gaske, baitaba ganin
tafif kafar mace mai kyawunsu ba.Daman ku'yan
Adam gajen hakurine daku da tun farko ma kayi
hakuri, sannu a hankali zaka ga surar da baka
taba ganin irinta a jikin wata'ya mace ba a
duniyar nan. Ta danyi shiru tana karkada
awarwaron dake hannunta kan taci gaba da
cewa."sunana AMAL'yar sarkin Aljanu. Mahaifina
shike sarautar duk aljanun dake wannan nahiyar,
muba kananan Aljanu bane. Dan haka inaso ka
kwantar dahankalinka da sannu zan kaika ku
gana da mahaifina, mutumin kirki ne, kuma nasan
dole ne ma ya kaunaceka in dai na bashi
labarinkadomin yana son jarumi irinka.Budurwa
Amal ta daga hannunta sama, sai farantan abinci
da kayan marmari iri-iri na sauka a gabansu.
Ba'a dade ba sai wata katuwar rumfa ta alfarma
ta sauko daga sama ta kare musu ruwan saman
da har yanzu yake zuba kadan-kadan.Amal ta
zauna, amma Nuraddin yakimotsawa daga inda
yake, har yanzu gani yake kamar zata sake
rikidewa zuwa wata halittar mai ban tsoro.Zauna
mana Nuraddin, ko har yanzutsorona kake ji?
Haba nuraddin ka yarda mana da alkawarina, ai
ni dakai yanzu mun zama daya.Jin haka, shiyasa
nuraddin ya koma can gefe guda a cikin rumfar
ya zauna akan lallausan kilishin daya mamaye
duk cikin rumfar. Nuraddinya dan lallatsa kilishin
da hannusa, laushi tubus kamar katifa. "Matso
kusa dani mana Nuraddin". Tace dashi a
tausashe.Nuraddin yayi karfin hali ya matso kusa
da ita ya zauna jikinsa na rawa, har yanzu tunani
yake zata rikide.Amal ta dubi Nuraddin sannan
tayi masa murmushi, ta dada matsawa daf da
shi, har yana iya jin hucin numfashinta mai
kamshin turare a fuskarsa.Ashe suma aljanu suna
numfashi irin na dan adam. Nuraddi ya fadi cikin
ransa."Kayi min murmushi mana Nuraddin ko
baka sona ne"?A karo na farko da Nuraddin yayi
koka ri, ya jefeta da wani dan saurayin fatalwan
murmushi.Amal ta dafa kafadarsa tace."Nuraddin
kana sona kuwa"?
Aljani Ya Taka Wuta!......8
-
-
-
Wanene zai iya dubanki a haka yace baya son
kyakykyawa kamarki? Ai kowa yana son mai kyau
indai kafa babu kofato". Nuraddin yace da ita
yana duban fuskarta mai sheki.Amal tayi shiru
tana sauraronsa, sannan sai ta rankwafa ta dora
kyakykyawan kanta akan kafadarsa tace."Naji
dadi Nuraddin, wallahi nima ina sonka matukar
so, naji dadin cewar kaima kana sona". Ta danyi
shiru, tana wasa da gashin kanta akan
kafadarsa.Nuraddin ya dimauce, saboda ni'ima da
kamshin turare dake tashi daga cikin
gashinta."Ina so ka sani cewa daga yau kayi
sallama da talauci har abada, muddin kana tare
dani, ni'imar duniya kam ka hadu da ita, duk
abimda kake so ka ambace kawai ka samu
masoyina, sannan kuma nayi maka alkawarin
idan jarabawarku ta karshe tazo, kada ka dami
kanka da wani karatu, domin nida kai zamu yi
jarabawar zan bude maka tafin hannuna duk
abinda kake bukatar sani yana nan a rubuce, sai
dai kuma ina so ka sani cewa kai kadai kake da
ikon ganina."Amal ta danyi shiru sannan taci
gaba da cewa."To, Nuraddin nidai kaji alkawarina
saura naka Nuraddin, ina so kayimin alkawarin
idan duk nayi maka wadannan abubuwan dana yi
maka alkawari zaka aureni"?Amsa kuwar
tambayar ta daki dodon kunnensa a bazata,
hakika al'amarin ban mamaki na faruwa gareshi
cikin daren nan. Nurdaddin yasa hannunsa a karo
na farko ya dafa kyakykyawan hannunta yana
tunani. Ni Nuraddin yau da auren aljana? Ya fadi
cikin ransa. Koda yake ba aibu bane na aureta,
indai har zata mayar dani mai arziki, to daman
duk duniya ma me ake nemainba kudin ba? To
kuma gashi sun zomin a bulus, in kuwa hakane
mezai hanani aurenta. A lokacin ne to Badawiyya
ta fado masa a rai. Hakika yana son Badawiyya
matukar so, domin ta dade tana wahala akansa
iri-iri dan me yanzu dare daya zai mata haka, don
kawai ya hadu da aljana mai siffa biyu,
mummuna da kyakykyawar siffa, waya sani ma
ko nan gaba in ya sake ya aureta ta sake
rikidewa. Amma dai bari na fara cin bulus din
kafin na yanke shawara. Tabbas bazan taba barin
Badawiyya ba mai sona tsantsa, ba dan jarumta
ta ba, ko rashin tsorona. Yace da kansa a zuciya,
sannan sai yace a fili."Zan aureki Amal".Amal ta
dago kanta dake kan kafadarsa ta dubeshi
tace"da gaskeNuraddin? Don Allah da gaske zaka
Aureni"?Dagaskenake Amal, ai na fada miki babu
wani mutum dazai ce baya kaunarki a duniyar
nan Nuraddin yace yana duban fuskarta."Alkawari
fa Nuraddin, nasan halinku na'yan Adam baku da
alkawari.""To, shikenan Nuraddin, tunda ka
amince gobe saika shirya mutafi na kaika gurin
mahaifina ku gana, sannan kuma shima kayi
masa alkawarin zaka aureni". Gaban Nuraddin ya
fadi, jin cewa za'a tafi dashi gurin sarkin Aljanu,
ya dubeta a tsorace zaiyi magana sai ta daga
masa hannu."Nasan abinda kake tunani, indai
idan wannan ne, kada ka damu kanka, domin
babu wani aljani daya isa ya tabamin bakona
ballantana kuma masoyina". Ta danyi shiru
sannan tace."kayi kokarin rike alkawari Nuraddin,
domin bana son mai karya alkawari, kuma daga
yau bazaka sake ganinaba cikin mummunar
siffata ba ta farko. Nayi maka alkawarin hakan".
Amal tace sannan saita mika dan karamin dan
yatsanta na dama tace tana murmushi."mukul
la".Nuraddin ya mika dan yatsansa suka kulla
alkawari sannan sai Amal ta cire daya daga cikin
zoben zinariya ukun dake hannunta, ta kama dan
yatsansa ta sa masa zoben ta ce."Daga yau in
kana son ganina, sai ka murza wannan
zoben,zaka ganni nazo, sai dai kuma inason ka
sani cewa bana zuwa da goshin magariba,
bakuma na zuwa da asuba, dan haka kada ka
murza zoben a wadannan lokutan dan bazaka
ganni ba, sannan kuma babu wani aljani daya isa
ya tabaka inhar kana tare da wannan zoben koni
dana baka shh kafi karfina, nima daga wajen
mahaifina na gajesu. Guda ukune daman gashi
nan na baka daya ka kula dashi da kyau kada ka
sake ka baiwa kowa, domin yanada matukar
amfani da daraja. Mahaifina ya taba rantsewa
yace duk dan adam din da aljanu suka taba ya
haukace koya nannade, ma'ana sassan jikinsa
suka shanye, to dazarar anjika masa zoben nan a
ruwa yasha zai warke kamar wani abu bai taba
samunsa ba, sannan kuma in har kana tare da
zoben nan babu wani aljani daya isa ya tabaka,
koda kuwanice kamar yadda na fada ma tun
farko.Tayi shiru tana jujjuya kanta akan
kafadarsa, tana mayar da numfashi."Gobe sai mu
hadu dakai anan kamar wannan lokaci, sai mu
tafi nakaika wajen mahaifina, domin ya dade yana
damuna akan na samo miji, to gashi na
samu".Amal ta miki tsaye ta dubi Nuraddin zaune
tace". Rufe idonka".Cikin mamaki sai Nuraddin
yabi umarninta. Alokacinne yaji tace."To nuraddin
sai goben kenan, Allahbamu alheri kana iya bude
idanunka".Bude idonsa keda wuya ya ganshi
zaune akan gadonsa.
...ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI part
{11}...
Cikin mamaki, sai yayi sauri ya dirgo daga kan
gadon yana waige waige, domin a tunaninsa Amal
ce keson cigca da wasa da hankalinsa. Nuraddin
ya dubi sauran gadajen dake daki, sai yaga duk
abokan kwanansa ne wadanda ya sani kwance
suna bacci abinsu. Ya leka tagar dakin, sai ya
hango farfajiyar makarantar kamar dai yadda ya
santa, ciki mamaki sai ya dawo ya zauna a bakin
gadon, sannan ya rufe idanunsa da tafukan
hannayensa. Nuraddim ji yake kamar ya farka
daga wannan mummunan mafarki. Adai dai
lokacinne ya tuna da zoben data bashi, cikin
gaggawa ya dubi dan yatsansa. Tabbar zoben
nan yana sheki. Nuraddin ya murza zoben.
"Menene kuma"? Amal ta sake bayyana acikin
daren, sanye da doguwar rigar bacci tana
murmushi. Dakin ya game da tattausa kamshin
turare. "Ko baka jin baccine nazo na tayaka
hira"? Tace dashi tana murmushi.
Nuraddin ya juya ya dubi sauran yaran dake
kwance a dakin suna ta sharar bacci, gabansa na
faduwa yana ta addu'ar Allah yasa kada wani ya
farka ya ganta a dakin.
"kada ka damu dasu, ai baza su iya ganina ba,
bakuma zasuji hirarmu ba, koda wani ma a
cikinsu ya farka to a kwance zai ganka kana
bacci".
Tana gama fadin haka sai ta jefeshi da tattausan
murmushi ta bace.
Awashegarin ranar, acan kofar makarantar
misalin goma sha biyu na rana musa mai gadi ne
keta jayayya da wata kyakykyawar yarinya dake
tsaye a gabansa.
"Kacd dashi Badawiyya ce keson ganinsa". Ta ce
dashi cikin kaguwa.
Ai ba fadar sunan ne wahala ba, abin da nakeso
ki gane shine neman mutum daya ciki duban
dalibai cikin wannan uwar ranar mai kamar ta
tashi Alkiyama ba karamin aiki bane". Mai gadi
yace.
Badawiyya ta kule, sannan sai wani tunani yazo
mata nan da nan sai ta juya ta dubi direbanta
tace dashi. "Dauko min jakata".
Cikin sauri direban ya tura hannunsa ta cikin
budadden gilashin motar, ya laluba kujerar ta
baya ya daukowa Badawiyya jakarta.
Badawiyya ta bude jakar, sannan ta dauko "yan
wasu adadin takardun naira hamsin-hamsin tace
da maigadin. Ga wannan kasha ruwan sanyi,
amma don Allah taimaka ka nemomin shi".
"Ai dole ne tunda kin bada maganin rana!
Maigadin yace yana rawar jiki. "yaya kika ce
sunansa"?
"Nuraddin Abubakar". Badawiyya tace.
Maigadin ya ruga da gudu, ya nufi cikin
makarantar, zuciyarsa tana mai mamakin abinda
ya hada wannan kyakyawar yarinyar mai kwarjini
ga karfin mayen karfen kudi a tattare da ita da
wannan watsattsen shaidanin yaron Nuraddin.
Abin da ya faru a daren shekaran jiya ya tambara
Nuraddin a duk fadin makarantar kai harma cikin
gari, dalibai kuwa har kanana "yan aji daya babu
wanda baisan shiba, domin ko yau aka kawoka
dalibi makarantar sai an baka labarin Nuraddin.
Ba'a dade ba sai ga mai gadin sun dawo tare da
Nuraddin, sanye da kayan makaranta farare, da
koriya Hula.
Nuraddin ya dubi Badawiyya cikin Mamakin
abinda ya kawota bayan kwanansa uku kacal da
rabuwa, tabbas ba lafiya ba. Amma ga
mamakinsa sai yaga tundaga nesa Badawiyyi ta
fara masa murmushi.
"Wallahi Nuri tunda ka taho bana iya barci,
tunaninka ne ke damun zuciyata, shiyasa nace
bazan iya ba gara na lallabi direbanmu ya kawo
ni na ganka, yanzun ma kaga ko sani ba'ayi a
gida ba".
Nuraddin ya dubi abar kaunarsa cikin mamaki, so
da kaunarta suka dada kwarara a cikin zuciyarsa.
"kina nufin abinda ya kawoki kenan kawai ki
ganni"?
Badawiyya tayi murmushi, sannan ta gyada kai
tace. "Ai ya wuce kawai Nuri, domin tunda ka tafi
nake Mafarkinka, wallahi 'darling' duk inda zani
dakai nake yawo a zuciyata, gaskiya ni dai ina
ganin daka gama sakandire zamuyi aure, ko kana
sami damar ganinka kullum a kusa dani, inka
shiga jami'a ma take tafiya da matarka.
Nuraddin ya fashe da dariya. "Lallai kam kinyi
dabara, kinga naji dadin zaben kala-kala acan
jami'ar naji ance canne gidan mata".
Badawiyya ta harareshi tace. "kama fara mana"!
Ta danyi shiru, kana ta dubi dan yatsansa ta
girgiza kai tace". Koda yake ma dai nasan Maza
baku da tabbar. A ina kuma ka sami
kyakykyawan zoben nan, watace ta baka"?
Badawiyya tace tana murmushi. To sai dai kuma
lokaci guda murmushin dake fuskar Nuraddin ya
subuce daga fuskarsa, gabansa ya fadi.
"Au! Menene na wani bata rai, don kada nace a
bani, to duk abinka saina karbi zoben nan a kalla
dai inna dube shi yake tunamin dakai, ya dauke
min kewarka".
Nuraddin yayi shiru yana dubanta cikin taraddadi
da fargabar abinda zai biyo baya, lokaci guda
kuma maganar Amal ta fado masa
*kada ka rabu da zoben nan domin yana da
matukar daraja da amfani ga bil'ada".
To, amma ai Badawiyya ma masoyiyarsa ce,
kuma tayi masa wahalhalu da dama a rayuwarsa,
duk dayake dai haduwa daya kawai sukayi da
Amal amma ta mayar da shi mai arziki. Tun safe
yake kashewa abokansa kudi, dayasa Hannu a
aljihu sai kawai ya yita zaro kudi, kai duk abinda
yayi niya idan yasa hannunsa a aljihu saiya
dauko. To koma dai menene Badawiyya ita ta
fara wahala akansa kafin kowa.
saida yamma.
Aljani Ya Taka Wuta!......12
'
'
-
Hakika zoben kyakykyawane kamar Nurinta.
Tambayar kawai da har yanzu takasa ramun
amsarta itace. A ina Nuri ya sami wannan
kyakykyawan zobe? Ita dai ta san kudin da ta
bashi bai isa ya saya masa irin wannan kerarren
zoben ba. Amma bari ya dawo zan tambaye shi.
'
Badawiyya ta fadawa kanta kana ta kuma duban
zoben, sannan sai ta kama zoben ta murzashi
tana murmushi, a ganinta zoben kamar Nurinta
ne. Da ba goshin bane, da Badawiyya tayi
kaduwar da bata taba yin irinta a duniya ba,
domin tana murza zoben mai shi zata bayyana a
gabanta. Badawiyya tayi sa'a domin'yar sarkin
aljanu Amal bata bayyana da goshin magriba,
amma da zarar magriba ta wuce zata iya
bayyana a sa'ar da aka murza zoben, ta koma
kan daya daga cikin dogayen kujerun alfarmar
dake dakinta ta fara cire kayan dake jikinta tana
jefawa akan kujerarta.
'
Al'adar da ta samawar kanta a duk magaribar
duniya take son farawa.Al'adar a kullum kwanan
duniya shine wankan magariba. Koda yake wasu
lokutan in har bada wuri zata kwanta ba, ta kan
bari har sai lokacin barcinta yayi saita shiga
wankanta. Amma idan har Nuraddinyana nan Nuri
Darling a yadda takankira shi, wankan magariba
wajibi ne a gareta ba mustahabi ba. A duk sa'ar
da Nuraddin ya dawo hutun makaranta, takan
shiga wanka tun karfe bakwai na yamma.
Wankan da shafe-shafe da kuma kyale-kyalenta,
takan shafe akalla sa'a guda tanayi. Da zarar ta
gama saita nemi guri ta zauna cikin annashuwa,
annuri na fita daga fuskarta, yayin da daddadan
kamshi madaukaki ke hurowa daga jikin
kyakykyawar halittarta, taci gaba da jiran abin
kaunarta Nuraddin wanda idan yazo suka fara
hira basa rabuwa sai karfe goma shabiyu na
dare. Aikin kenan kullum kamar karatu, har kuma
sai Nuraddin ya koma makaranta sannan sai duk
soyayyar ta koma kan hotonsa.
-
Badawiyya ta fito a hankalin tana rangwada, ta
daura farin zani iya kirji, gashin kanta ya
warwatsu akansantalelen wuyanta mai kamar na
barewa. A duk sa'ar data motsa sai ruwa ya
fantsamo daga cikin gashinta. Fitowarta kenan
daga al'adarta ta wankan magariba.Ta zauna a
hankali akan daya da cinwasu kujeru takwas
masu numfashida suka zagaye dan madaidaicin
dakinta, kana ta janyo wan dan karamin teburi
fari mai tafiya akan kananan tayoyi. Wannan
teburin shine dan dakon kayan kwalliyar
Badawiyya. Sannu a hankali tana tafe tana
rausaya har takai ga wani tangamemdo madubin
kwalliya ta fuskanceshi. Daga cikin madubin tana
iya hango kofar dakin da zata kaika har falon
cikin gidan.Badawiyyata dauki wata 'yar doguwar
kwalbar rob, wacce ke dauke da lallausan man
shafawa mawadacin kamshi, ta matso man akan
tafin hannunta na hagun. Sannan tasa na dama
ta fara shafawa. Agogon dake jin bangon dakin
ya fara rera sarewa, karfe takwas na dare,
Badawiyya tayi murmushi data tuna da abin
kaunarta Nuraddin. Ta daga hannanayenta izuwa
fuskarta ta farashafa lallausan man, sannan ta
lumshe idanuwanta cikin annushuwa tace.NURI
DARLING!!! Bata dauke hannayenta daga fuskarta
ba, ba ta kuma bude idanunta ba, domin ji take
kamar hannayen Nuraddin ne ke lullube da
fuskarta. A haka taci gaba da tunaninta. Sabanin
al'adarta ta yauda kullum a ka'ida Badawiyya
bata wanka karfe takwas na dar har sai idan abin
begenta Nuri yana gari, amma yau sai gashi tayi
saboda dalilai biyu. Na farko mafarkin da tayi a
daren jiya na matar nan mai mummunar halitta
wacce ke kokarin kwace mata Nuri. Hakan shiya
sata wanka yau tun kafin karfe takwas na dare.
Domin a tunanin Badawiyya koda Nura baya nan,
kamata yayi ace tana raya lokacin hirarsu.
Wannan shine dalilin wankanta domin tayi
alkawarin zatayi kwalliya ta zauna tasa hoton
Nuraddin a gaba tayi ta hira koda kuwa bazai
amsa mata ba,ba kuwa zata daina kallonsa ba
har sai sha biyun dare wanda shine ka'idar
lokacin rabuwarsu da Nuri darling.Dalili na biyu
kuma shine tana tunanin idan takai sha biyu
batayi barci ba, da wahala ta sake mafarki da
mummunar matar nan mai kokarin kwace mata
Nuraddin. Hakika mafarkin ya tayar mata da
hankali. Domin Badawiyya bata da wani abokin
gaba a duniya da ya wuce wanda zai rabasu da
*NURI DARLING*.Da farko da tayi mafarkin mata
mummuna ce amma sa'ar data farka ta sake
komawa barcinta, sai matar tazo mata a siffar
kyakykyawa. Abin bakin cikin kuma ga Badawiyya,
surar matar a wannan lokacin tafi tata kyau nesa
ba kusa ba. Mafarkine kawai amma duk da haka
ya tayar mata da hankali.Tunaninta ya katse
sakamakon sauyin yanayi dataji a jikinta. Haka
kawai ba zato ba tsammani, sai taji jikinta ya
fara rawar sanyi sannan taji wani abu mai kamar
iska ya na kada gashin kanta, sannan abu
mafitashin hankali da figitarwa shine lallausan
man datake shafawa a fuskarta sai taji yayi sanyi
kalau tamkar tana shafa kankar adai dai lokacin
ne taji karar budewar kofa kuu!Ina vaxan iya
ganin wannan tashin hankalin ba. Wani abu yayi
ta kururuwa cikin kwakwalwarta yana cewa kada
ta bude idanunta, saidai kuma mai gargadi ya
makara.......
-
"""ALJANI YA TAKA WUTA CI GABAN LABARI
{Part 13}"""
Nuraddin yaci gaba da tunani, sai gashi kuma
lokaci guda Amal na barazanar zata mayar da
burin wani shudadden mafarki. Bazai yiwu ba,
yace a ransa. Nakoma matsiyaci, tabbas ba zata
sabu ba bindiga a ruwa.
Nuraddin ya dubi amal ya sunkuyar da kansa
kasa yace da ita a tausashe. "kin kasa fahimtata
Amal, abinda nake son ki gane shine, so nake mu
rabu da Badawiyya cikin salama, ke yanzu kina
ganin bayan abinda tayi min ya dace na watsar
da ita gefe guda"? Nuraddin ya girgiza kai sannan
yaci gaba da cewa. "Daga yanzu Amal zan rike
dukkan alkawarin danayi miki, kece baki san
zuciyata ba amma wallah tunda na doraki a
idanuna naji begenki ya lullube tsokar zuciyata,
dan haka ina son ki kwantar da hankali nayi miki
alkawari idan na koma gida, da zarar mungama
jarabawarmu ta karshe, zanyi kokarin mu rabu da
Badawiyya.
Ni kaina nasan ba dai dai bane ace "yar talakan
mutane tana takara da 'yar gidan sarkin aljanun
duniya mai kyawun sura kamarki".
jin hakan keda wuya, sai wani tattausan
murmushi na farin ciki ya subuce daga bakin
Amal. Ta sunkuyo da kai a hankali zata sumbace
shi, sai ta tuna she bai riga ya aureta din ba.
Cikin sauri sai ta dauke kanta ciki jin kunya, kana
tace dashi. "Alkawari fa Nuraddin"?
"eh alkawari, kada kiji komai ai sanin kanki ne ba
daya kuke da Badawiyya ba ai ko ba'a gwada ba
linzami yafi karfin bakin kaza, duk da yake dai
itama kyakykyawa ce acikin mutane, amma ai
gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta".
"tsokana fa kenan"? Amal tace tana dariya
wallahi wannan karin maganar taku ta mutane ta
fita daga bakinka".
Nuraddin ya fashe da dariya, sannan ya juya
firgigit yana leken taga don kada wani yaji sautin
dariyarsu ya shigo ya ganshi shida yar sarkin
Aljanu.
"kada ka damu da wadanda suke waje, domin ko
sun shigo ma baza su iya ganin mu ba, kai dai
kawai shirya mutafi mahaifina na can yana
jiranka.
Nuraddin yayi ajiyar zuciya hakika yana tsoron
zuwa garin da babu kowa sai aljanu, amma
yanzu ya tabbata Amal bazata bari a cuceshi ba.
Nuraddin ya mike tsaye a tsorace yace "mutafi".
Nuraddin yabi umarninta. Rufe idonsa keda wuya
yaji tace bude. Yana budewa sai ya ganmu a
cikin wata katuwar alkarya mai dauke da gine
ginen alfarma iri-iri. Adai dai lokacin ne muka
kawo ga wata katuwar kofa tsayinta ya kusan
tokare. Sararin samaniya.
Amal ta dubeshi tace. "kada kaji tsoro, nan
gidanku ne babu abinda za'ayi maka".
Kofar garin tayi kara mai kamar rugugin aradu,
sannan sai ta bude a hankali wata shintimemiyar
halitta ta fito harshen halittar guda biyu ne
manya manyan kamar tabarma. Fitowarsa keda
wuya sai aljanin ya zuro harsunansa waje ya
shimfidasu gaban Nuraddin da Amal.
Nuraddin yayi baya cikin razana.
"kada kaji tsoro Nuraddin, hau daya harshen nima
na hau daya, akansa za'a kaimu zuwa fadar
mahaifina".
A dai dai lokacin ne to wata katuwar murya tayi
ihu mai tsanani sannan tace.
"Allah ya kiyaye wani dan Adam ya aureki bani
ba"!!
Kafin kiftawa da bisimillah sai wani farin hayaki
ya fara mamaye ko wanne sashe dake katuwar
kofar.
"Amal!!" Nuraddin ya kwala mata kira a gigice
domin baya iya ganinta saboda hayakin.
A dai-dai lokacin da duk wannan ke faruwa,
Badawiyya na can kwance male-male akan
gadonta tana barcin. Acikin barcin nata ne tayi
mafarkin wai suna cikin tafiya ita da Nuraddin
aciki wani kungurmin bakin daji, sai suka hango
wata mage ta nufosu da gudu tana zuwa
gabansu saita rikida da ta zama wata jibgegiyar
mata, mai zako-zakon hakora kamar kibiya,
jikinta duk gashi kamar na tunkiya. A lokacin ta
zaro tafka-tafkan hannayenta ta kama wuyan
Nuraddin zata yi sama dashi.
Badawiyya ta kwala ihu a rude sa'ar da taga abin
dake shirin faruwa.
A hakan hajiya habiba mahaifiyarta ta sameta ta
kankame matashin kai tana ihu.
"ke menene"?
Badawiyya ta yi firgigit ta tashi zaune, sukayi ido
biyu da mahaifiyar ta.
"momi, wallahi wani mummunan mafarki nake".
"kuma dan kina mafarki sai kiyi ta ihu, bazaki
ambaci sunan Allah ba? Duk abinda ya sameki na
masifa sai kice innalillahi wa inna'ilaihirraji'un".
Badawiyya ta sunkuyar da kanta tana tunanin
mummunar matar dake kokarin dauke mata
Nuraddin.
"kada na sake ganin kina ihu a mafarki, addu'a
akeyi ba ihu ba". Mahaifiyarta ta kuma fadi
sannan ta fice daga dakin ta koma dakinta. Karfe
uku na dare abin ya faru, to amma har gari ya
waye Badawiyya bata sake komawa baccin ba.
Washe gari da yamma misalin karfe shida
Badawiyya na zaune a dakinta. Sai tunani Nuri
'DARLING' dinta ya fado mata. Ta mike tsaye a
hankali ta fara suntiri a cikin. Oh! Nuri 'DARLING'
yanzu yana can makaranta ko me yake yi yanzu?
Ta tambayi kanta. Sannan ne to idanunta ya
kawo ga ZOBEN da Nuraddin ya bata.
Asannan nima lokaci yayi. Sai gobe da safe..
ALJANI YA TAKA WUTA!_14
'
'
Ko da Amal ta dubi idanunta saitaga kamanninta
sun fara sauyawa daga na firgita zuwa na wani
yanayi da ban.
"Badawiyya". Amal ta kira sunanta. "inaso ki
fahimci cewa koda ada can Nuraddin masoyinki
ne, to ki yarda cewa yanzu ya miki nisa, domin
na fiki sonsa, na kuma fiki daukaka, iko da karfin
mulki ballanta kuma uwa uba kyawu. Wannan
itace maganar data raboni da Nuraddin nazo
gareki na sanar dake cewa daga yau babu ke
babu shi"!
-
Badawiyya taji kamar Amal ta watsa mata wuta a
fuska. *NA RABU DA NURADDIN? Tab! Ai kuwa
sai dai mutuwa, kai ba 'yar gidan aljanu ba, ko
'yar gidan balbalin bala'i ce bata isa ba.
"kada ki bata bakinki"! Badawiyya tace cikin fushi
tana dubanta acikin madubin. "Bazan rabu da
Nuri ba, babu kuma wanda ya isa ya rabani dashi
sai Allah".
Ta danyi shiru tana duban Amal, wacce ke tsaye
acikin madubin cikin kaduwar ganin wacce keyi
mata magiya tana rokonta kuma yanzu ta birkice
take fada mata bakaken maganganu.
"kuma naji abin da kika fada 'yar gidan sarkin
aljanu, kince kin fini mulki, da iko da dukiya, da
kuma kyawu to duk naji na yarda, domin duk
Allah ne ke bada su ba mutum ba ko aljani.
Amma kin san dai cewa duk halittar ubangiji babu
wacce tafi mutum daraja, kuma kyawun da kike
takama dashi ai na karyane domin a siffarmu ta
'yan adam kika fito min, in gaskiyane ki koma
kirarku mana ta aljanu sai muyi takarar
kyawun...."
"Ke! Marar kunya kisan abinda yake fita daga
bakinki in kuma ba hakaba wallahi zakiyi
nadama". Amal tace a fusace.
"Rashin kunya ba gadonta akeyi ba Amal agurinki
na koya, wahala kuma ko nadama indai akan Nuri
Darling ne to hutuce agareni. Bazan barshi ba
kuma barin na maimaita miki babu abin da ya isa
rabani da Nuri sai ko mutuwa. Haba Amal tunfa
ina 'yar kankanuwa Allah ya dasa harsashin
kaunarsa a raina, ina girma itama kaunar na
girma cikin zuciyata, tare muka girma shine jini,
tsoka, kashi, bargo, ke shine rabin ruhin raina.
Shi bakiji sunansa ba ne Nuri? Ma'ana hasken
raina. Koma garinku Amal ki auri dan uwanki
aljani mai kan karfe, NURI kam nawane".
Amal 'yar sarkin aljanu tayi sororo cikin tsananin
takaici da kaduwa tana duban Badawiyya. Dakiku
ashirin suka shude Amal na tsaye ta kasa cewa
komai. Can sata nisa tace. "Nagode Badawiyya,
daman kunce jiki magayi to jikinki zai gaya miki,
kada ki tsorata domin bake zan taba ba, Nuri naki
zan nannade na mayar dashi kamar abinciku
alkaki, fitsari da kashi sai a kwance inyaso ki
aureshi haka ki nuna min kin fini kaunarsa ko"?
"Na daina tsoronki Amal kuma kada ki sake cewa
ina tsoronki, abinda ya dazuma nake baki hakuri
na dauka wani abune dabam ya kawoki, amma
indai zancen ki rabani da Nuri ne to bani ba
tsoronki har abada, nasan dai bai wuce kice zaki
nakasa shiba, ko ki kasheni, to bari kiji Amal indai
in rabu da Nurine, saidai kiyi duk abinda kikayi
niyya, domin rabuwa dashi sunfi mutuwa ko
nakasa zafi a gareni".
Badawiyya ta mike tsaye tana duban Amal, tawul
din wankan dake daure a jikinta rike a hannunta
na hagun.
"shikenan Badawiyya ma jiyi ma gani, a ga wanda
zai gaza". Amal tace. Sannan tayi shiru tana
duban zobenta da ta bawa Nuraddin a hannun
Badawiyya cikin takaici. Amal taji zuciyarta kamar
ta fashe da kuka. Mahaifinta yasha bata tarihin
zobunan guda uku, biyun da suke hannunta da
kuma wanda ke hannun Badawiyya a yanzu.
Mahaifinta yasha cewa da ita.
"Wannan zoben yafi shekara dubu biyar a gurina
tun zamani annabi sulaiman {A.S} yake, zoben
alkawarine, dan haka ki rikeshi da kyau kuma
kada ki sake ki cutar da duk bil'adaman dake
sanye da daya daga cikin zobunan guda uku, idan
kuwa kika aitata sabanin haka, to ki kuka da
kanki domin nannadewa zakiyi ki zama gurguwa
baiwa wulakantacciya a cikin jinsin aljanu, kiyi ta
yawo a kwararo da lungu-lungun duniya cikin
kazanta".
Tunanin wannan dogon jawabi na mahaifinta, da
kuma fargabar abinda zai biyo baya, shiya hana
Amal ta nannadewa Badawiyya kafafu da hannu.
Kai in ba don zoben dake hannunta ba, da saita
kakkaryata ta shanye bargonta.
"sai gani na biyu Badawiyya huduwar da ina
tabbatar miki da cewa bazata zamo alkhairi
agareki ba, kuma aure ni da Nuraddin kamar anyi
ne, kinga yanzu haka ma muna tare dashi a kofar
gidanmu zamu shiga su gaisa da mahaifina sai
kawai naji kinyi kirana".
Badawiyya ta dubi Amal cikin rashin fahimta tace.
"kamar yaya nayi kiranki, kufa Aljanu bakwa
rabuwa da karya da yawan son wasa, yanzu ke
ko kunyar fada bakya yi wai kuna tare dashi? To
Allah yasaa ma baya garinnan, yana makaranta.
Kuma da zaki ce nayi kiranki yaushe na kiraki"?
Amal ta dubi zoben dake hannun Badawiyya ta
girgiza kai. Zakisan yadda akayi kikayi kirana,
amma sai nan gaba, kuma sai kinyi nadama
marar kunya.
ALJANI YA TAKA WUTA!__15
-
-
-
...Wani bakin hayaki ya turnuke dakin sannan
lokaci guda sai ya washe.
Badawiyya taja da baya cikin kaduwa, sa'ar da
bakin hayakin ya washe, sai ta sake duban
madubin. Babu alamar kyakykyawar surar Amal
sama ko kasa ta bace.
Adaidai lokacinne kofar dakin ta bude, "keda wa
naji kina magana yanzunnan"?
Badawiyya ta nufi mahaifiyarta da gudu ta
rungumeta sannan ta fashe da kuka wiwi.
****
"Amal! Nuraddin ya sake kwalawa Amal kira karo
na biyu daidai lokacin da farin hayakin yaci gaba
da tunuke gurin.
Tuni Nuraddin ya fara zargin kansa da wautar da
yayi, wai soyayya da aljana, kuma dan karin
sabon haukama wai har ya amince ya biyota
garinsu, togashi nan yanzu ta kawo shi gaban
mai dogo harshe mai muryar jaki suna kokarin
hallaka shi.
Nuraddin yaji kamar akan iska yake ninkaya
domin kafafunsa basa taba kasa, amma duk ba
wannan bace tafi bashi tsoroba, sai muryar nan
da yaji mai amon kukan jaki tana cewa dashi
wai ya rabu da Amal ba mai aurenta sai ni.
Yanzu inba dan rigima ma irin tawa ba ina ni ina
takarar budurwar aljanu, kuma aljanun ma masu
muryar jaki? Nuraddin ya tambayi fuskars.
Adai dai lokacinne ba zato ba tsammani sai farin
hayakin ya washe tamkar ma ba'ayi shiba
Nuraddin ya dubi inda yake fuskanta cikin
mamaki domin har yanzu dai yana nan tsaye
gindin katangar nan, hakannan kuma dankareren
aljanin nan mai dogon harshe na tsaye yana zalo-
zalo da harshensa kamar tabarma.
"Kada kaji tsoro". Wata muryar tace da Nuraddin
wacce daga baya ya fihimci ashe muryar aljanin
nance mai dogon harshe. "kai bakonmu ne,
bazamu cutar dakaiba. Muryar daka ji tana yi
maka tsawa ta wani shaidanin
dan sarkin ce daga cikin kananan sarakunan
aljanu. Ya dade yana son ya auri Amal amma taki
amince masa, bata kaunarsa koda kwayar zarra.
Ya cika nacin tsiya, munsha yi masa kashedin ya
rabu da ita kuma kada ya sake
zuwa gidan nan amma yaki, to yau munyi
maganinsa, domin a yanzu haka yana can cikin
karkashin kasa mun daure shi, saboda tsawar
da yayi maka a matsayinka na babban bakon
sarkinmu. Don haka a madadin sauran aljanu
ni babban maigadin gidan sarkin aljanu inayi
maka barka da zuwa mijin gimbiya".
Koda aljanin ya gama dogon jawabinsa, sai
Nuraddin ya bude baki da niyyar ya tambayeshi
inda Amal ta tafi ta barshi. Kafin ya tambayane
to Amal ta sake bayyana a gabansa cikin sauri
kamar an jehota daga sama.
"kayi hakuri Nuraddin," Amal tace "Wallahi
kiran gaggawa akayi min shine na tafi, amma
daman nasan babu abinda zai sameka, shiyasa
na bar maigadinmu ya kula da kai kada
nacaccen nan ya tabamin kai".
"Ina kika je"?
Amal ta dubi Nuraddin sannan ta sunkuyar
dakai Bazata iya fada masa cewa daga wurin
Badawiyya take ba ballantaoa kuma azo ga
zancen alkawarin da tayiwa Badawiyya na
nannade shi. Don haka ba tare da ta iya hada
idanu dashi ba tace.
"Al'adar gidanmu ce duk lokacin dakazo da
bako mai mahimmanci kamarka, sai anyi
kiranka kayi bayanin cewa kun karaso, sannan
sai a shigo da bakon.
Nuraddin ya dubeta cikin rashin gamsuwa, ko
shakka babu yasan karya take.
Amal ta sake matsowa kusa dashi taci gaba da
cewa ina fatan ka gamsu"?
Nuraddin ya gyada kai baiyi magana ba.
"To ai sai mu tafi ko"? Tace dashi.
Kafin kiftawa da bismillah, katon aljanin nan
maigadi ya shimfida dogon harshensa mai
kamar tabarma. Suka hau sannan yayi sama
dasu ya tsallake katangar gidan. Har sa'ar da
aka ajiye Nuraddi agaban sarkin aljanu bai
daina zargin kansa da wauta ba, haka nan yayi
wa kansa alkawarin inhar ta mayar dashi
makaranta bazai sake binta ko ina ba. A wani
bangaren na zuciyarsa ma saida ya fara tunanin
anya kuwa zai iya ci gaba da soyayya da ita?
Nuraddin ya dago kansa a hankali cikin
fargaba, yana kallon aljanun da sukayi sahu-
sahu a fadar sarkin aljanu. Tun da yake, bai
taba ganin halitta mai ban tsoro da muni irin
tasu ba. Fadar cike take makil da jinsin aljanu
iri-iri, kuma tun daga kan bakake da fararen
aljanu zuwa kan masu faka fakan kunnuwa
kamar faranti, kai wasu babu kunnuwan gaba
daya, haka wasu zako-zakon hakora da manyan
kunnuwa, wasu kuma manyan kawuna kamar
goran kamun kifi, wasu kuwa 'yan kawunansu
gwanin ban dariya, domin 'yan kananane kamar
dunkulen fura, sai katon uban jiki kamar
giwaye. Nuraddin ya dubi surukinsa sarkin
sarakuna
mai mulkin Aljanu wato mahaifin Amal, sai
yaga kansa kamar an taka gwanda da tayar
mota, kunnensa daya ido daya haka nan
hancinsa dogone kamar karas.
"ka rike alkawari Nuraddin," sarkin Aljanu ya
fara jawabi, yayin da sauran aljanu sukayi tsit
suna da faman fifita da faka-fakan
kunnuwansu. "Muna farin ciki dakai, kuma in
dai zaka rike alkawari, to zan baka 'yata Amal
ka aura domin tace duk duniya babu wanda
take kauna sai kai, bisa wannan dalili dole ne
nin na kaunace ka, domin duk abin da take
kauna nima ina kaunarsa. Yaya kake gani, zaka
iya rike alkawari zaka kuma aureta??
Aljani YaTaka Wuta!....16
-
-
...abin da take kauna nima ina kaunarsa. Yaya
kake gani, zaka
iya rike alkawari zaka kuma aureta??
"Kuyi hakuri ansamu typin errors a wannan page
na littafin "
-
Tun fara hangenta daga nesa Nuraddin ya fadawa
kansa cewa lallai ba lafiya ba, domin fuskarta
murtuk! Take a hade, kuma abinda ya kara sashi
kaduwa ma shine harya kusa isa gurinta
Badawiyya bata saki fuskarta ba ballantama tayi
masa murmushin nan na alkawari data saba yi
masa maimakon haka ma sai harara.
Nuraddin ya matsa kusa da Badawiyya a hankali
wacce hannunta ke dafe da saman motar kirar
Toyota da aka kawota a ciki, fuskarta na duban
kasa, akwai wani yanayi dake kan fuskarta wanda
yasa 'yar autar hantar cikin Nuri kadawa.
"sannu da zuwa". Nuraddin yace da ita sa'ar da
ya dada matsawa kusa da ita.
"sannunka dai". Badawiyya ta fada a yatsine. Tayi
shiru bata sake cewa kala ba.
"Badawiyya meke faruwane ina fatan dai lafiya"?
Nuri ya tambayeta cikin damuwa.
"Lafiyar kenan". Badawiyya tace sannan tayi
ajiyar zuciya ta sunkuyar da kanta kasa tana
duban inuwarta ajin mota.
Nuraddin ya sake dubanta cikin tsananin damuwa
sannan ya dan dauke kansa gefe guda ya dubi
can cikin farfajiyar makarantar inda dalibai ke ta
harkokin gabansu.
"Badawiyya kada ki boyemin komai in wani abune
ki sanar dani mana kin barni cikin zulumi da
damuwa, ni kuma nasan ba wani abu na miki ba
tunda shekaran jiya-jiyan nan fa kika zo da farin
ciki da sanyi rai muka rabu dake amma gashi
yanzu kinzo ranki a hade ni...ni dai na kasa gane
wannan abu"?
"nace dakai babu komai, in kuma zuwa gurin
naka danayi baka so to sai nayi tafiya".
Badawiyya tace fuskarta a murtuke.
Cikin damuwa, Nuraddin ya lalubi aljihunsa ya
zaro kyalle daga goshinsa.
"kada kiyi min haka Badawiyya, alkawarin dake
tsakanina dake baice haka ba, ki tuna fa tun
muna yara muke son juna, wani sabani
makamancin wannan bai taba shiga tsakaninmu
ba, in kuwa hakane mezai sa yanzu ki rufe idonki
a kaina"? Ya danyi shiru yana mayar da numfashi.
"idan kuma laifi nayi miki batare dana sani ba ki
fada mana saina baki hakuri tunda dai Allah ya
halicci kaunarki cikin zuciyata".
Jin haka shiya sa Badawiyya ajiyar zuciya sannan
ta dago kai ta dubeshi da dara-daran idanunta
tace. "Nuri meye hadinka da aljana"? Numfashin
Nuraddin ya dauke. Daman ni nasa a rina wai an
saci zanin mahaukaciya. Ya fada cikin ransa.
"Ban fahimce ki ba". Ya fada a fili. Lokaci guda
kuma ya fara kokarin sa alamun rashin
fahimtarta akan fuskarsa duk kuwa da cewa
zuciyarsa ta dade da zargin abinda ya faru.
"Nace inda alkawarin kamar yadda ka gama fada
meye hadinka da aljana? Badawiyya ta sake
maimaitawa.
Wani sassanyan gumi ya fara sartu wuyansa ya
gangaro har zuwa ramin tsakar bayansa.
"Badawiyya waye inba mahaukaci ba zaiyi
soyayya da aljana," Nuraddin yace cikin karfin hali
yana girgiza kai. "Gaskiya nin Badawiyya duk kin
rudani...ni yau na kasa fahimtar inda kika sa
gaba".
Badawiyya ta dube shi tana kokarin karantar
fuskarsa sannan tace. Mu shiga daga cikin motar
in fahimtar dakai, labarin nada yawa". Tana fadin
haka sai ta bude gidan baya na motar ta zauna.
Nuraddi jiki ba kwari, ya shiga ya zauna a kusa
da ita yanata sakar zuci.
Badawiyya tadanyi shiru na lokaci tana hangen
direban daya kawota wanda ke can gefe guda
kusa da wata tsohuwar rijiya da dalibai kan dauki
ruwa idan ana wahalar ruwa a makarantar.
"Nuri" ta kira sunan a sanyaye, sannan taci gaba
da cewa. "wata aljana ce ta bayyana kanta
agareni tace duk duniyar nan ba wanda take so
ta aura sai kai".
Kusan tsawon mintuna arba'in kenan Nuraddin na
zaune yana sauraron abin al'ajabi daga bakin
masoyiyarsa Badawiyya. Ko shakka baya yi duk
abinda tace sunyi da Amal 'yar sarkin aljanu
gaskiya ne, domin ganau ne ba jiyau ba.
A daidai lokacin da Nuraddin ya fara jin kamar
kansa zai rabe gida biyu saboda firgicin labarin,
sai Badawiyya tayi ajiyar zuciya, ta kare zancenta
da cewa.
" shin to kai Nuri, a ina kuka hadu da ita?
Nuraddin yayi murmushin yake yace. "Nima
tambayar dana kewa kaina".
Badawiyya ta dubeshi cikin rashin fahimta "kamar
yaya kenan kake nufi"? Ta sake tambayarsa karo
na biyu.
"saboda ni ban san wata aljana wai ita Amal ba
ballantana ma harna iya soyayya da ita".
Nuraddin yace batareda ya iya hada idanu da
itaba.
Badawiyya ta dubeshi a rude amma babu alamar
zargi a fuskarta, hakan ya karwa Nuraddin karfin
gwiwar lallai zai iya jirkitar da zanceta, ya mayar
mata da duk abinda sukayi jiya itada Amal ya
zam kamar mafarki.
"To.... Kana nufin kace duk surutun da mukayi da
ita a daren jiya ba gaskiya bane"?
Nuraddin yayi ajiyar zuciya, sannan ya dubeta da
murmushi yace. "wallahi yau kin sani cikin
damuwa a banza, ni da na dauka ma wani laifi
nayi miki? Yanzu keda wannan dan abin duk
shiya rikitaki haka"? Nuraddin ya danyi shiru gami
da dubanta ido da ido.
"Bari na fada miki wani abu da baki sani ba,
aljanu ne kawai suke son wasa da hankalinki
saboda ganin irin tsabar kaunar da muke wa
junanmu.
-
Nuraddin ya kara cewa, kinga nima kaina a 'yan
kwanakinnan haka nake ta fama da 'yan
mafarke mafarken ban tsoro, fada mikine kawai
bana yi dan kada hankalinki ya tashi, amma ni
basu taba zuwa min a zahiri ba, kema dan
macece, shiyasa amma kada ki damu, ki
kwantar da hankalinki in kinje gida kisa a miki
rokon Allah kada suci gaba da zuwa miki a
zahiri".
Badawiyya ta dube shi gami da ajiyar zuciya
tace "Nuri darlin wallahi ni har na gama tsora
na dauka da gaske soyayya ka fara da aljana.
Nuraddin ya girgiza kai da dan murmushi.
"karya ce kawai da iya shegen aljanu kin sansu
da son wasa kamar daren sallah. Allah ne kawai
zai iya rabani da ke Badawiyyata".
Acan gefe guda, kimanin taku ashirin Daga inda
suke zaune, Amal ce 'yar sarkin aljanu ita da
fadawanta tana kallon duk abin dake faruwa
tsakanin masoyan biyu.
"shegiya nacacciya kya yi kya barshi saina
munana fuskarki"! Amal ta ce ciki zuciyarta a
fusace.
Saura kwanaki uku kacal su Nuraddin su fara
jarabawarsu ta karshe, wato ta kammala
karatun su a makarantar.
Karfe hudu da 'yan mintuna na yammacin
ranar ne Nuraddin ya shiga makarantar dauke
da farar leda ahamnunsa. Daga cikin gari yake
jakar dake hannusa kayan marmari ne da ire-
iren nau'in abincin gwangwani wanda a yanzu
sun abin shansa da cinsa. Wannan ba abin
mamaki bane domin duk sa'ar da yaso ya kashe
kudi hannunsa kawai zai tura cikin aljihunsa sai
yaji dumus, ya zaro iya adadin da yake bukata
ya kashe abinsa.
Yau kusan kwana arbain kenan rabonsa da
Badawiyya Amal kuwa tun sa'ar da ta dawo da
shi daga garinsu bai kara ganinta ba ido biyu
ba, amma takan zo masa a mafarki cikin dare
suyi hira abinsu. A ire- iren hirarrakin da suke
yine ma a daren jiya tace dashi yayi jiranta yau
zata zo gurinsa da yamma domin su tattauna
akan maganar fara jarabawar sannan kuma tace
da shi da zarar ya kammala karatu zata kawo
masa kudin da zai sai motar hawa shima ya
samin abin yawo a gari.
Wannan ita tasa Nuraddin shigowa makarantar
cikin sauri har yana sassarfa. Amma fa duk
wannan hira da ake sha tsakaninsa da Amal
'yar sarkin aljanu, har yanzu hankalin Nuraddin
a tashe yake zuciyarsa ta kasa tsayawa guri
guda.
A gaskia so kam ya fi kaunar gimbiyarsa ta
ainihi wato Badawiyya. Tasha wahala akansa
kuma a kullum idan ya kwanta barci yakan ce
da kansa da Badawiyya ce keda arzikin Amal, to
da ko raine tana iya saya masa idan tana da
iko, Amma Amal fa? Cewa tayi tana kaunarsa
saboda shi jarumi ne. Gaskiya ba kwanta min
ba soyayyarta bata da inganci. Yace da kansa.
Aljanun nan basu da tabbas, yanzu idan wata
rana ya aureta ta kuskure ta sauya kamanni irin
na mahaifinta mummuna mai dogon hanci
kamar karas yaya zaiyi? Tab!! Falcao! Kenan
yace a ransa sa'ar da ya tuna wani aljani da ya
gani mai manyan kunnuwa kamar takalmi.
Tambaya daya da Nuraddi yake wa kansa ita ce.
Idan Amal bata kwanta masa a rai ba meyasa
ya dau alkawarin aurenta? Arzikin da tace zata
baka. Wata zuciyar ta bashi amsar tambayarra.
Tabbas yana bukatar kudi. Wani babban sirri
dake boye a zuciyar Nuraddin shine, tun
farkon fara haduwarsu da Amal Nuraddin ya
amince mata ne duk saboda Badawiyya. Ya sha
fada ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba
cewa, wahalar da Badawiyya keyi masa ta isa
haka, domin abin yayi yawa, tun suna firamare
take wahala dashi, sau da yawa ma ita ke zuwa
musu da abincin ma da suke ci idan sun fito
tara, hakanan kuma ita ke bashi kudin kashewa.
A lokacin Nuraddin ma kazami ne bai fiye son
wanka ba, ansha fito dashi filin taron dalibai
ayi masa bulala a matsayin dalibin da yafi
kowa rashin tsafta. Amma duk wannan bata sa
daidai da kwayar zarra Badawiyya ta kyamace
shi ba. Wasu lokutan ma idan aka dake shi ya
fara kuka, ita takan zo tayi ta lallashinsa har
sai ya huce. A haka har suka zo sakandire, nan
ma taci gaba da wahala akansa, kudin
makaranta, na kashewarsa, littafansa da kayan
amfaninsa na yau da kullum. To irin wannan
dawainiya ita tasa tun nuraddin baya damuwa
har abin ya fara damunsa, ya fara tunanin a
duniya fa babu zaman wacce yake inba
Badawiyya ba, kullum burinsa a duniya shine
Allah ya azurta shi ya nunawa Badawiyya cewa
tofa shima dane. Don haka haduwarsu da Amal
keda wuya sai yaga cewa damarsa tazo na ya
saka mata na sama da abinda ta masa. Abinka
da takadiri irin Nuraddi, ko kusa ko alama
zuciyarsa bata taba tsoratar dashi irin hadarin
da yake kokarin jefa kansa aciki ba. Tunaninsa
kawai Badawiyya, tuni ya fara tunanin idan
Amal tazo bashi kudin sayan motar da tayi
masa alkawari zaiyi kokarin ya karbin kudin
mota biyu datasa da ta Badawiyya.
Wadannan tunane-tunane suke ta kai kawo
cikin zuciyar Nuraddin har sa'ar da ya kawo
cikin makarantar.
Lokacin da ya karasa bangarensu na Seniors
{manyan dalibai} gurin babu ko dalibi daya duk
sun tafi daukar karatu, saboda kusantowar
jarabawar da zazu fara nan da kwana uku, da
yawa daga cikinsu basa dawowa dakin sai waje
asuba Nuraddin ya nufi dakinsu cikin sauri sai
yayi
turus da....-
Aljani Ya taka wuta!....18
-
-
-
Nuraddin ya fara tafiya a
hankali baki bude cikin
mamaki. A iya sanin Nuraddin daliban da
suke cikin dakin basu
taba tafiya sun barshi a
bude ba, haka basa
barin wutar lantarki a
kunne tun bayan wata gobara da aka yi suna
aji daya, amma yanzu da
Nuraddin yaci gaba da
nufo dakin sai yaga
dakin a bude, haske ko
ina duk kuwa da cewa har yanzu da sauraran
hasken ran, kuma abin
mamaki hasken har
waje kamar kwaya-
kwayan wutar lantarki
dake dakin sunkai dari. Gaban Nuraddin na
faduwa amma ba wai
don tsoro ba sai don
mamakin da kuma
dokin ya shiga yaga
abin dake faruwa. A haka Nuraddin ya shiga
dakin.
Shigarsa keda wuya sai
sukayi ido biyu da ita
zaune akan gadonsa
tana haskake masa idanu da fararen
idaninta.
"Sannu da zuwa". Amal
tace dashi cikin
annushuwa.
"Haba ni fa nasan wani aikin sai ke". Nuraddin
yace shima cikin
murmushi, lokaci guda
kuma yana kallon
sauran zobunan guda
biyu da suka rage a 'yan yatsunta.
Nuraddin ya karasa
cikin dakin yana fara'a
ya zauna kusa da ita.
Duk kamshinki ya
mamaye mana daki" Nuraddi yace yana
dubanta.
"Naji dadin hakan".
Amal tace cikin fara'a da
jin dadi, duk mai hankali
idan ya dubi irin kallon da take yi masa zai san
cewa lallai tarko nan mai
magani daya ya mamayi
zuciyarta ya cafketa
wato S0!.
"Na bata miki lokaci ko? Cikin gari wallahi naje
siyan 'yan kayayyaki,
dan ma nayi sauri da
bazan karaso yanzu ba".
"Haba Nuraddin ba
komai wallahi, nima dai azarbabina ne ya kowo
tun wuri, kuma gashi
DUNDUMA baya kusa na
aike shi karas SIN
ballantana ma ya sanar
dani inda ka tafi, naso ma na biyo ta cikin gari
na daukoka muzo tare".
Nuraddin ya dubeta
cikin rashin fahimta yace
"wanene kuma
DUNDUMA"? "Bawa na mai kula
dakai".
Nuraddin ya dubeta
kirjinsa na bugawa cikin
fargaba. Ashe 'yar masu
dogon hancin nan han dan leken asiri ta
makalkalamin. Nuraddin
ya fada a ransa. Wani
sansanyan gumi ya fara
kwararowa a tsajiyar
gadon bayansa. Yanzu da magulmacin ya dauki
duk maganganun da
sukayi da Badawiyya ya
fada mata yaya kenan?
Maganar Amal ta katse
tunaninsa. "Tunanin me kake yine? Dan kaji nace
DUNDUMA? Ai tsaron
lafiyarka yakeyi, yaushe
zan bari tsautsayi ya
samar min kai Nuraddin?
Ai bazai yiyu ba, kai dai na san abin da kake
tunani, to ba leken
asirinka yake yiba".
Nuraddim yai ajiyar
zuciya gami da
murmushin yake kana ya dubeta yace "ke
kuwa kin cika zargi, to
ni tunanin da nake ma
bai shafi wannan ba".
"to Me kake tunani?
Nuraddin ya jefeta da tattausan murmushin
yaudara. "Ranar
aurenmu nake tunani".
Amal ta washe baki
cikin farin ciki, sannan ta
dan matso kusa dashi. "wallahi nima kullum
tunanina kenan.
Nuraddin yaushe zaku
fara jarabawar ne nina
matsu ku fara ko kwa
gama a fara zancen aurenmu".
"Ai ranar litinin dinnan
mai zuwa zamu fara. Yau
saura kwana uku".
Amal ta dubeshi tace
"kada ka damu kanka, saurara da kyau, idan
ranar litinin tazo zan
shigo cikin ajin daza
kuyi jarabawar, zan
buda maka tafin
hannua, zakaga duk amsoshin a jiki".
Nuraddi bai gaskata,
kunnuwansa ba ya
dubeta cikin kaduwa.
"kada ka damu, duk ajin
babu wanda ya isa ya ganni sai masoyina".
Ranar litinin, rana ta
faduwar gaba ga kusan
dukkan daliban da zasu
fara zan jarabawarsu ta
karshe a makarantar. Wasu daga cikinsu suna
fargabar ranar ne
saboda basu yarda da
kansu ba, domin sun
tabbata dan abinda suka
karanta bai isa sukai labari ba. Yayin da wasu
kuma suke fargaba
kawai saboda basu taba
zaman jarabawa ma
mahimmanci wannan ba
a rayuwarsu. Haka kuma basu san
wadanne irin tambayoyi
za'a kawo ba a wannan
shekarar.
Koma dai menene shi
Nuraddin ko a jikinsa wai an mintsini
kakkausa. Tun karfe
tara saura na safiyar
ranar suka fara
jarabawar. Basu dade da
shiga ba malaman suka shi rarraba musu
takardun jarabawa tare
da bakaken 'yan sanda
guda hudu dake binsu a
baya suna muzurai
kamar zasu hidiye mutum danye da ransa.
"kai gyara zamanka"!
Wani daga cikinsu ya
bugawa Nuraddin tsawa
sa'ar kafar Nuraddin ta
hagu ke kan teburin rubutunsa.
Sai da akayi kusan
mintuna arba'in da fara
jarabawar Nuraddi bai
zana alif ba. Yana zaune
yana tsammanin warabbuka wai malam
yaki yin Noma don
zakka. Adai dai lokacin
Nuraddin ya fara
zazzare idanu yana
tunanin ko bazata zoba, sai kawai ya kamar
daga sama yaji ance.
"Kada ka damu
masoyina, ina nan kusa
da kai. Da yardar Allah
yanzu zaka gama". Sannan sai Amal ta
bayyana kusa dashi
tana murmushi.
Nuraddin ya daga kansa
ya dubi sauran daliban
da kuma malaman dake tsaronsu, ko kusa ko
alama babu wanda
hankalinsa ya kawo
gareshi, ballantana ma
su nuna alamar sunji
abinda tace. "Dubi tafin hannuna,"
Amal tace dashi a
tausashe, lokaci guda ta
daga tafin hannunta
sama, kamar wasa sai ga
rubutu a jiki "fara kwafa wannan ce amsar
tambayarka ta farko".
Nuraddin jiki na rawa ya
fara kallon tafin
hannunta yana rubuta
abinda ya gani ba magana don gudun
kada a jishi a cikin aji.
"Idan kaso muna iya yin
hirar mu ma kana
aikinka. Domin babu mai
jinmu ballanta ganina.
Aljani Ya Taka Wuta!...19
'
'
Ranar d su Nuraddin suka gama jarabawa ta
karshe ranar wata juma'a ce da aka wuni ana
tafka uban ruwan sama.
Dama tun tashin Nuraddin da asuba ya
fuskanci garin ya bata rai murtuk baya fara'a
sai tartsatsin walkiya gami da rugugin aradun
tsohuwar daminar dake barazanar barka
sararin samaniya gida biyu.
Ba'a ko idar da sallar asubahi ba, aka barke da
ruwa. Haka shiyasa mafi yawa daga cikin
dalibai sai da lema suka tafi dakunan
jarabawarsu, wasu kuwa da rigar leda. Har
suka gama ba'a daina tafka ruwan ba sai dab
da sallar juma'a sannan ruwan ya tsagaita.
Tun a ranar wasu dalibai suka fara tafiya
gidajensu, makarantar ta kaure da hayaniyar
dalibai sunata yaga fararen kayan makarantar
su cikin murna domin a cewarsu wai yau Allah
ya rabasu da likkafani, yayin da wasu kuma ke
ta bakin cikin rabuwa da juna.
Nuraddin tare da 'yan tawagarsa kowanne
dauke da jakankuna suka fito daga makaranta
sunata hira cikin jimamin rabuwa, gami da
musayar adireshi. Nuraddin bai tafi ba sai da
yayi sallama da kowa sannan sai ya juya a
hankali domin yiwa makarantar kallon karshe.
A wannan lokacine yaji wata murya tayi kiran
sunansa. Nuraddin ya juya domin yaga mai
kiran.
Musa maigadi ne.
"Nura dama zuwa nayi muyi sallama gashi yau
zamu rabu".
Nuraddin yayi murmushi yace. "To ai rayuwa
kenan baba maigadi, yanzu da masu zagina
suna cemin gagararre, damasu sona duk ba
gashi yanzu zamu rabu ba."
"kwarai kuwa Nuraddin" ya fada ba tare da
nuna alamar tayiya daga wurin ba, ga dukkan
alamu akwai abinda yake son fada. "Nuraddin".
Maigadin ya kuma kiran sunansa.
Na'am baba maigadi. Ya amsa.
Daman shawarace nake son baka. Yace kana ya
danyi shiru.
"yarinyar nan mai zuwa ziyartarka a mota, ka
riketa da kyau masoyiyarka ce kaji". Maigadin
yace.
Nuraddin yaji dadin maganar. "Nagode baba, in
Allah yaso zanyi duk abinda kace". Sannan ya
juya ya nufi hanyar da zata kaishi tashar mota.
Ya fara tafiya kenan dauke da jakunkunansa
biyu, acikin harda wacce Badawiyya ta bashi
sa'ar da zaizo, sai yaji wani ni'imtaccen
tattausan hannu ya dafa masa kafada.
"haba Nuraddin, bazaka tsaya ko sallama
muyiba kafin ka tafi"?
Nuraddin ya juyo tun kafin ya juyo yasan duk
duniya babu mai wannan murya sai 'yar sarkin
Aljanu AMAL. Nuraddin yayi mata murmushin
karfin hali.
"Nadauka bazaki zoba". Yace a bayyane, acikin
zuciyarsa kuma yana cewa lallai na daukowa
kaina jaraba.
"Haba dai, kaima kasan babu abinda zai hanani
zuwa, kadai fadane kawai dan kaji dadin
bakinka". Amal nagama fadin haka sai ta daga
hannunta sama, mamakin Nuraddin saiga
fararen kujeru na azurfa sun fado daga sama
Amal a ajje kujerun sannan ta dubeshi cikin
girmamawa ta so da kauna tace.
"Zauna sonake muyi hirar karshe kafin ka
tafi".
Nuraddin ya dubi gefen hanya a tsorace. Daga
inda yake tsaye, yana iya hangen kofar
makarantarsu, inda dalibai keta bulbulowa
suna shirin tafiya gida, nuraddin yasan takan
wannan hanya da ta ajje kujeru dalibai zasu
wuce, amma yanzu ya fara imani da cewa babu
mai iya ganinsu. Nuraddin ya ajje jakankunan
dake hannunsa ya zauna.
Amal ta dubeshi cikin kunya tace. "Nuraddin
ina son ka sani cewa zuciyata ta gama mutuwa
da kaunarka, hakan cema tasa na kaika har
gaban iyayena, inda ka dauki alkawarin aurena
a gabansu. To gashi dai yau Allah ya kawomu
ka gama makaranta. Don haka nake rokonka da
cewa dan Allah da zarar kaje ka sami iyayenka
ka musu bayani kamar yadda na yiwa nawa
iyayen". Amal ta dan numfasa tana dubansa
kana taci gaba da cewa. "Daga yau Nuraddin
bazaka sake ganina ba sai bayan wata uku zan
zo har gidanku naji yadda kuka yi da iyayenka".
Nuraddin ya dubeta cikin zargi. "mezai hanamu
haduwa da juna har tsahon wata uku? Ya
tambaya lokaci guda kuma yana tunanin
alkawarin da tayi masa na bashi kudin sayen
mota.
"Saboda nasan sai kasha gwagwarmaya wajen
shawo kan mahaifanka akan su barka ka auri
aljana. Bana son kayi musu karya ka sanar dasu
koni wacece. Na baka tsahon wata ukune
domin kayi duk yadda zakayi ka shawo kansu".
Amal ta sake yin shiru akaro na biyu tana
dubansa. "Duk abinda kake so masoyina, ka
lalubi aljihunka da niyar daukar zaka same shi
aciki. Tayi kamar zata mike tsaye sai kuma ta
koma ta zauna. "Ni zan tafi sai na dawo jin
yadda kuka kare dasu, kada kuma ka damu za
muke hirarmu kamar yadda muka saba acikin
mafarki. Rufe idanunka na kaika gida". Amal
tace dashi batare da ta mike daga kujerar data
ke zaune ba.
Adaidai lokacin da wannan ke faruwa, wata
katuwar marsandi taja ta tsaya a kofar
makarantar. Daga inda suke zaune Nuraddin
yana iya hango motar haka ma Amal.
Kofar motar ta bude, Badawiyya ta fito cikin
fara'a ta nufi inda masu gadi suke zaune.
Nuraddin yaji zuciyarsa ta harba, tabbas
Badawiyya shi tazo dauka.
"Badawiyya ce ko"? Amal ta fada a fusace.
"Itace". Nuraddin ya fada Bakinsa a bushe
kamar mai azumi.
"Wannan maiyar yarinyar mai nacin tsiya saina
gurguntata idan bata kyalemin kaiba". Ta kuma
fadi a fusace"
Aljani ya taka Wuta!...20
'
'
Nuraddin yaji kaman ta watsa masa ruwan wuta
a fuska saboda zagin Badawiyya datayi.
"Rupe idonka mutafi". Amal ta sake cewa
dashi.
Nuraddin yaso yaki, amma babu yadda ya iya
don haka sai kawai ya rufe idanunsa, yana ji,
yana kuma ganin Badawiyya.
Juyin farko da Nuraddin yayi, sai kafarsa ta
zunguri tsohuwar akwatinsa ta da, wacce suka
sha jayayya shida Badawiyya akanta sa'ar da zai
tafi makaranta.
Nuraddin yayi mika gami da salati, sannan ya
dubi tsohon dakin kwanan nasa rufin azara,
wanda ke kokarin rubzowa a kowanne lokaci. A
saman dakin yanar gizo-gizo ce ko'ina kai har
jikin bangon dakin, haka nan duk indaka taba a
dakin sai kura tayi sama buu!!
Nuraddin yayi tsaki sannan ya zuro kafarsa
kasa. Kura ta sake yin sama sakamakon motsin
da tsohon gadon yayi. Wani katon gizo-gizo ya
kawowa Nuraddi cafka, cikin sauri ya dauke
hannunsa gami da murmushi, kana ya mike
tsaye yana kallon gizo-gizon a zuciyarsa yana
cewa, idan ba tsoroba ka kama Amal mana,
sannan ya dada cewa, kai Allah dai ya kowomin
karshen wannan jaraba.
Tunanin abubuwan da suka faru a yammacin
jiya suka fara dawowa zuciyarsa. Abu na farko
daya fara dawo masa shine tunanin Badawiyya.
Har sa'ar da Amal ta kawo shi gidansu cikin
'yan dakiku jikinsa bai daina rawa ba, haka nan
kuma a karo na farko tun sa'ar da suka fara
haduwa da ita sai Nuraddin yaji gaba daya ya
tsani Amal 'yar sarkin Aljanu, badan komai ba
kuwa sai dan irin mummunan furucin da tayi
wai zata nakasa abar kaunarsa Badawiyya. Nifa
wannan jaraba ta fara isata. Yace da kansa sa'ar
da ya mike tsaye yana duban tarin tarkacen
kaya masu tarin kura dake dakin. Sannan sai ya
lalubi aljihunsa. Kudi dumus! Suka gaishe da
tafukan hannunsa. Ga mamakin Nuraddin sai
yaji a karo na farko, ya ta6a kudin bai burge
shiba.
"salamu alaikum, har yanzu baka tashi ba".
Nuraddin ya juya a firgice ya dubi mahaifiyarsa
tsaye a kofar dakin tana dubansa, akwai wani
irin yanayi dake fuskata dayasa Nuraddin ya
fara tunanin lallai akwai labari a bakinta.
"wallahi.... Baba gajiya ce ta hanani tashi. Ina
kwana". Mahaifiyarsa tace, sannan ta dubeshi
ido da ido tace. "kayi bakuwa".
Nuraddin yaji zuciyarsa ta harba ras!
"wakenan"? Ya tambaya baki na rawa.
"wakake tsammanin zata zo gidan nan namu da
sassafe nemanka inba Badawiyya ba"?
Nuraddin yayi ajiyar zuciya. Tunda ya dawo
gida baiji maganar data faranta masa rai ba
irin wannan.
"Baba ya fitane"?
Mahaifiyarsa tayi dariya.
"kai dan Allah in zaka fito ka fito ni banason
gulma, Baban naka da yake fita tun asussuba
kuma....
Maganar ta katse sakamakon sautin tafiyar da
sukaji an Nufo dakin.
"salamu alaikum". Badawiyya tace. Sannan taci
gaba da cewa. "Ummi idan barci yake rabu
dashi in anjima na dawo".
"idonsa biyu, gashi zaune yana jinki".
Karfe tara saura kwata Nuraddin ya fito
dagaNuraddin yaji kaman ta watsa masa ruwan
wuta
a fuska saboda zagin Badawiyya datayi.
"Rupe idonka mutafi". Amal ta sake cewa
dashi.
Nuraddin yaso yaki, amma babu yadda ya iya
don haka sai kawai ya rufe idanunsa, yana ji,
yana kuma ganin Badawiyya.
Juyin farko da Nuraddin yayi, sai kafarsa ta
zunguri tsohuwar akwatinsa ta da, wacce suka
sha jayayya shida Badawiyya akanta sa'ar da zai
tafi makaranta.
Nuraddin yayi mika gami da salati, sannan ya
dubi tsohon dakin kwanan nasa rufin azara,
wanda ke kokarin rubzowa a kowanne lokaci. A
saman dakin yanar gizo-gizo ce ko'ina kai har
jikin bangon dakin, haka nan duk indaka taba a
dakin sai kura tayi sama buu!!
Nuraddin yayi tsaki sannan ya zuro kafarsa
kasa. Kura ta sake yin sama sakamakon motsin
da tsohon gadon yayi. Wani katon gizo-gizo ya
kawowa Nuraddi cafka, cikin sauri ya dauke
hannunsa gami da murmushi, kana ya mike
tsaye yana kallon gizo-gizon a zuciyarsa yana
cewa, idan ba tsoroba ka kama Amal mana,
sannan ya dada cewa, kai Allah dai ya kowomin
karshen wannan jaraba.
Tunanin abubuwan da suka faru a yammacin
jiya suka fara dawowa zuciyarsa. Abu na farko
daya fara dawo masa shine tunanin Badawiyya.
Har sa'ar da Amal ta kawo shi gidansu cikin
'yan dakiku jikinsa bai daina rawa ba, haka nan
kuma a karo na farko tun sa'ar da suka fara
haduwa da ita sai Nuraddin yaji gaba daya ya
tsani Amal 'yar sarkin Aljanu, badan komai ba
kuwa sai dan irin mummunan furucin da tayi
wai zata nakasa abar kaunarsa Badawiyya. Nifa
wannan jaraba ta fara isata. Yace da kansa sa'ar
da ya mike tsaye yana duban tarin tarkacen
kaya masu tarin kura dake dakin. Sannan sai ya
lalubi aljihunsa. Kudi dumus! Suka gaishe da
tafukan hannunsa. Ga mamakin Nuraddin sai
yaji a karo na farko, ya ta6a kudin bai burge
shiba.
"salamu alaikum, har yanzu baka tashi ba".
Nuraddin ya juya a firgice ya dubi mahaifiyarsa
tsaye a kofar dakin tana dubansa, akwai wani
irin yanayi dake fuskata dayasa Nuraddin ya
fara tunanin lallai akwai labari a bakinta.
"wallahi.... Baba gajiya ce ta hanani tashi. Ina
kwana". Mahaifiyarsa tace, sannan ta dubeshi
ido da ido tace. "kayi bakuwa".
Nuraddin yaji zuciyarsa ta harba ras!
"wakenan"? Ya tambaya baki na rawa.
"wakake tsammanin zata zo gidan nan namu da
sassafe nemanka inba Badawiyya ba"?
Nuraddin yayi ajiyar zuciya. Tunda ya dawo
gida baiji maganar data faranta masa rai ba
irin wannan.
"Baba ya fitane"?
Mahaifiyarsa tayi dariya.
"kai dan Allah in zaka fito ka fito ni banason
gulma, Baban naka da yake fita tun asussuba
kuma....
Maganar ta katse sakamakon sautin tafiyar da
sukaji an Nufo dakin.
"salamu alaikum". Badawiyya tace. Sannan taci
gaba da cewa. "Ummi idan barci yake rabu
dashi in anjima na dawo".
"idonsa biyu, gashi zaune yana jinki".
Karfe tara saura kwata Nuraddin ya fito daga
wanka ya shigo dakin inda har yanzu Badawiyya
ke zaune tana jiransa. Bai damu da shafa mai
ba ballantana taje gashi, sai kawai Nuraddin ya
zauna kusa da ita.
"Badawiyya haka da sassafe? Ai dama kin
hakura nima da yamma nake son zuwa
gidanku.
Badawiyya ta jefeshi da murmushin ruwan
bege, ta dauke kai gefe guda.
"Kai kenan NURI DARLING, amma ni bazan iya
kaiwa har yamma banga fuskarka ba, bayan
kuma nasan ka dawo kana gida. Jiyafa har
makarantarku mukaje daukoka bamu sameka
ba".
Nuraddin yaji kirjinsa yayi kunci sa'ar daya
tuna da abin da ya faru yammacin jiya. Lokaci
guda saiyayi kokari yasa alamar mamaki a
fuskarsa yace. "Gurina fa kika ce? Kina nufin
kice jiya kina cikin makarantarmu"?
"kwarai kuwa". Badawiyya tace gami da tafa
cinya tana yi masa murmushi. "Ni da direban
gidanmu muka je zamu daukoka, tun da safe
ma muka yi niyyar zuwa, to ruwan saman da
akayi ta tafkawa, shiya hanamu tafiya shine
mama tace mu bari sai an dauke ashe da rabon
sai mun makarane, muna zuwa maigadi nan na
makarantarku yace yanzun nan kuka rabu
dashi, har tasha muka biyoka bamu ganka ba".
Tayi shiru tana dubansa, tana wasa da tsohon
mayafin dake shimfide akan gadonsa, wanda ko
shi Nuraddin daya saba zama cikin dakin yasan
mayafin Wari yake yi.
Nuraddin ya girgiza kansa yana nuna takaicinsa
a fuska.
"Ayyah na wahalar dake, wallahi abinda ya faru
ina fitowa saiga motar gidansu wani dan
ajinmu to su suka daukoni suka kawoni har
gida".
Badawiyya ta bude baki cikin mamaki tace
Amma ummi kuma danazo cewa tayi dani a
motar haya kazo".
Gaban Nuraddin ya fadi saboda jin karyarsa
zata tashi, domin lokacin daya dawo jiya cewa
yayi da mahaifiyarsa a motar haya yazo tuda
dai babu yadda za'ayi yace da ita aljana ce ta
kawoshi.
Abinda nace da ita kenan Nuraddin yace yana
kokarin tuno da wata sabuwar karyar.
"kinsan Ummi ce bata fiye son shige shige ba,
kullum takanyi min fada akan wai na iya
talaucina, to kinga gadai jiya hanyace kawai aka
ragemin amma idan na fadawa ummi hakan zai
iya zama laifi shiya sa na 6oye mata"
wanka ya shigo dakin inda har yanzu Badawiyya
ke zaune tana jiransa. Bai damu da shafa mai
ba ballantana taje gashi, sai kawai Nuraddin ya
zauna kusa da ita.
"Badawiyya haka da sassafe? Ai dama kin
hakura nima da yamma nake son zuwa
gidanku.
Badawiyya ta jefeshi da murmushin ruwan
bege, ta dauke kai gefe guda.
"Kai kenan NURI DARLING, amma ni bazan iya
kaiwa har yamma banga fuskarka ba, bayan
kuma nasan ka dawo kana gida. Jiyafa har
makarantarku mukaje daukoka bamu sameka
ba".
Nuraddin yaji kirjinsa yayi kunci sa'ar daya
tuna da abin da ya faru yammacin jiya. Lokaci
guda saiyayi kokari yasa alamar mamaki a
fuskarsa yace. "Gurina fa kika ce? Kina nufin
kice jiya kina cikin makarantarmu"?
"kwarai kuwa". Badawiyya tace gami da tafa
cinya tana yi masa murmushi. "Ni da direban
gidanmu muka je zamu daukoka, tun da safe
ma muka yi niyyar zuwa, to ruwan saman da
akayi ta tafkawa, shiya hanamu tafiya shine
mama tace mu bari sai an dauke ashe da rabon
sai mun makarane, muna zuwa maigadi nan na
makarantarku yace yanzun nan kuka rabu
dashi, har tasha muka biyoka bamu ganka ba".
Tayi shiru tana dubansa, tana wasa da tsohon
mayafin dake shimfide akan gadonsa, wanda ko
shi Nuraddin daya saba zama cikin dakin yasan
mayafin Wari yake yi.
Nuraddin ya girgiza kansa yana nuna takaicinsa
a fuska.
"Ayyah na wahalar dake, wallahi abinda ya faru
ina fitowa saiga motar gidansu wani dan
ajinmu to su suka daukoni suka kawoni har
gida".
Badawiyya ta bude baki cikin mamaki tace
Amma ummi kuma danazo cewa tayi dani a
motar haya kazo".
Gaban Nuraddin ya fadi saboda jin karyarsa
zata tashi, domin lokacin daya dawo jiya cewa
yayi da mahaifiyarsa a motar haya yazo tuda
dai babu yadda za'ayi yace da ita aljana ce ta
kawoshi.
Abinda nace da ita kenan Nuraddin yace yana
kokarin tuno da wata sabuwar karyar.
"kinsan Ummi ce bata fiye son shige shige ba,
kullum takanyi min fada akan wai na iya
talaucina, to kinga gadai jiya hanyace kawai aka
ragemin amma idan na fadawa ummi hakan zai
iya zama laifi shiya sa na 6oye mata"'
Aljani ya Taka wuta!____21
'
'
Badawiyya ta gyada kai cikin fahimta. Sannan
ta zura masa idan kawai tana kallonsa mar zata
hadiye shi, idan shima ya kalleta sai tayi masa
murmushi kawai ta sunkuyar da kanta kasa.
Hakan ita tasa Nuraddin ya gane cewa lallai
akwai abinda take son fadh dan haka sai yace.
"Meke damunkh ne darling"? Naga dazun nan
kike magana, gashi kuma lokaci guda kinyi
shiru. Badawiyya tayi masa murmushi har
fararen hakoranta suka bayyana baki daya.
"Ba...babu komai". Tace tana tafa hannayenta
biyu, sannan ta kalle shi ta sake sunkuyar
dakai.
"Haba Badawiyya duk wanda ya kalleki yasan
akwai wani abu dakike son fada amma kin kasa.
"Ya danyi shiru yana mayarda numfashi kana
yaci gaba. "Ko wanine yayi min juyin mulki"?
Badawiyya ta harareshi gami da dafe kirji tace.
"Na shiga uku! Kada Allah ya nuna min ranar
rabuwata dakai Nuri, haba dai wacce irin
magana ce wannan kake yi marar dadin ji, in
banda abinka duk duniyar nan waye ya isa yayi
maka juyin mulki a gurina"?
Nuraddin ya fashe da dariya yace "ke da wasa
fa nakeyi ai kece kin yimin shiru idan wani
abune fadi mana mu biyu nefa kawai adakin,
ko kunyar dakin kike ji kada yaji abinda zaki
fada"?
Badawiyya ta girgiza kai, sannan ta muskuta
cikin jin kunya tace. "Babana ne yake son
ganinka akan maganar aurenmu".
Nuraddin yaji jikinsa ya dauki rawa sa'ar da yaji
kalamanta. Bawai don baya son auren bane
yasa cikinsa kaduwa, sai dan tunanin alkawarin
daya dauka na auren Amal agaban sarkin aljanu
mai hancin karas, sai gashi kuma yanzu
Badawiyya tazo masa da zance wai mahaifinta
na son ganinsa".
"Yaushe yake son ganin nawa"? Nuraddin ya
tambaya ya murmushin karfin hali.
Badawiyya ta mike tsaye ta kashe masa idanu
da tattausan murmushi, sannan ta sunkuyo
kansa har saida ya fara jin hucin daddadan
numfashinta a fuskarsa tace dashi cikin murya
tattausa. "yanzu zaka shirya mu tafi, yana gida
yana jiranka kuda da amincewarsa nazo
gurinka ya umarcen mu tafi tare".
Wannan shine karo na farko da Nuraddin ya
fara shiga cikin gidansu Badawiyya tun sa'ar da
suka gama makarantar firamare. Duk kusan
danginsu Badawiyya babu wanda baisan
soyayyar dake tsakaninta da Nurinta ba, wasu
da dama su nuna kyamarsu akan lamari tunma
farkon soyayyar, domin a tunaninsu bama
karamar faduwa bace ga kyakyawar yarinya
kamar Badawiyya 'yar mai hali ta rasa wanda
zata makalewa sai wani jikakken tsumma a
randa waishi Nuraddin. Amma sa'ar da suka
fahimci irin tsananin soyayyar da Badawiyya
keyi masa, sai duk suka ja bakinsu alaikum
sukayi shiru, musamman ma kuma da suka
fahimci cewa, Alhaji Danbaba, da matarsa
Hajiya Falmata suna matukar kaunar Nuraddin
din.
Lokacin da aka shigar da Nuraddin cikin gidan
sai ya zama sauna saboda kalle-kalle da waige-
waige. Ada can ma da suna yara idan sun shigo
gidan ba'a barinsu su shiga falon shakatawar
Alhaji Danbaba. Tunanin farko da ya fara zuwa
zuciyar Nuraddin shin in Allah ya yarda saina
gina mana gidan da yafi wannan sau ashirin
nida Badawiyya, sannan saiya shafi aljihunsa
yaji kudi dumus aciki, Nuraddin yayiwa kansa
wani dan marayan murmushi sannan yace
acikin zuciyarsa, uhm su Amal manyan gari ga
kudi ga munanan iyaye.
Alhaji Danbaba ya muskuta a hankali akan daya
daga ciki kujerun alfarma da suka yiwa dakin
kawanya sannan ya dubi Nuraddin wanda ke
zaune ya sunkuyar dakai kasa yana wasa da
'yan yatsun hannunsa.
Kofar ta bude sannan Hajiya Falmata ta shigo
dakin Badawiyya na binta a baya. Duk kusan
jikin mahaifiyar Badawiyya lullube yake da
farin mayafi. Suna shigowa dakin sai Badawiyya
ta zauna kasa kusa da Nurinta, ita kuma Hajiya
Falmata ta wuce kai tsaye ta zauna da mai
gidanta Alhaji Danbaba.
"Muhammadu Nura". Alhaji Danbaba ya kira
sunansa.
"Na'am Baba" Nuraddin ya amsa.
"Daman ba wani abune yasa na kiraka ba sai
don ina ganin lokaci yayi da ya kamata
soyayyar nan taka da Badawiyya ta zam mai
ma'ana, ko ba haka ba Falmata"?
"Gaskia fa Alhaji". Hajiya ta amsa sannan Alhaji
Danbaba yaci gaba da dogon Bayani.
"To, Nuraddin kaga dai tun kuna makarantar
firamare kake tare da ita, tun kuna abotarku ta
yarinta har abin ya zama da gaske kuma har
abin ya kawo da ita yanzu Badawiyya ta isa
Munzalin aure. Kaga manemanta suna damuna
da sunturi ana zuwa neman aurenta, zaiyi wuya
ace kwana ukun duniya suzo su wuce ba'a zo
mana da zancenta ba, duk da yake ita
Badawiyya din bata zuwa gurin kowa, to amma
gaskiya yawan suntirin da jama'a suke kullum a
kofar gidan nan ya ishemu". Alhaji Danbaba ya
sake yin shiru karo na biyu sannan ya daga kai
ya dubi matarsa yaci gaba. "shin to nake ganin
gara ka turo iyayenka mu kare magana, ko
kuma kace da mahaifin naka ni zanzo na
sameshi mu tattauna. Ah.. Kuma inaso ka
kwantar da hankalinka kada ka bari tunanin
rashin karfi na mahaifanka ya dameka, duk da
kai yarone karami wanda yanzune ma ka
kammala karatunka na sakandire amma wannan
bazaisa na hanaka komai ba saboda wallahi ina
kaunarka matuka
HASKE ko DUHU?
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {P.22}
Ranar d su Nuraddin suka gama jarabawa ta
karshe ranar wata juma'a ce da aka wuni ana
tafka uban ruwan sama.
Dama tun tashin Nuraddin da asuba ya
fuskanci garin ya bata rai murtuk baya fara'a
sai tartsatsin walkiya gami da rugugin aradun
tsohuwar daminar dake barazanar barka
sararin samaniya gida biyu.
Ba'a ko idar da sallar asubahi ba, aka barke da
ruwa. Haka shiyasa mafi yawa daga cikin
dalibai sai da lema suka tafi dakunan
jarabawarsu, wasu kuwa da rigar leda. Har
suka gama ba'a daina tafka ruwan ba sai dab
da sallar juma'a sannan ruwan ya tsagaita.
Tun a ranar wasu dalibai suka fara tafiya
gidajensu, makarantar ta kaure da hayaniyar
dalibai sunata yaga fararen kayan makarantar
su cikin murna domin a cewarsu wai yau Allah
ya rabasu da likkafani, yayin da wasu kuma ke
ta bakin cikin rabuwa da juna.
Nuraddin tare da 'yan tawagarsa kowanne
dauke da jakankuna suka fito daga makaranta
sunata hira cikin jimamin rabuwa, gami da
musayar adireshi. Nuraddin bai tafi ba sai da
yayi sallama da kowa sannan sai ya juya a
hankali domin yiwa makarantar kallon karshe.
A wannan lokacine yaji wata murya tayi kiran
sunansa. Nuraddin ya juya domin yaga mai
kiran.
Musa maigadi ne.
"Nura dama zuwa nayi muyi sallama gashi yau
zamu rabu".
Nuraddin yayi murmushi yace. "To ai rayuwa
kenan baba maigadi, yanzu da masu zagina
suna cemin gagararre, damasu sona duk ba
gashi yanzu zamu rabu ba."
"kwarai kuwa Nuraddin" ya fada ba tare da
nuna alamar tayiya daga wurin ba, ga dukkan
alamu akwai abinda yake son fada. "Nuraddin".
Maigadin ya kuma kiran sunansa.
Na'am baba maigadi. Ya amsa.
Daman shawarace nake son baka. Yace kana ya
danyi shiru.
"yarinyar nan mai zuwa ziyartarka a mota, ka
riketa da kyau masoyiyarka ce kaji". Maigadin
yace.
Nuraddin yaji dadin maganar. "Nagode baba, in
Allah yaso zanyi duk abinda kace". Sannan ya
juya ya nufi hanyar da zata kaishi tashar mota.
Ya fara tafiya kenan dauke da jakunkunansa
biyu, acikin harda wacce Badawiyya ta bashi
sa'ar da zaizo, sai yaji wani ni'imtaccen
tattausan hannu ya dafa masa kafada.
"haba Nuraddin, bazaka tsaya ko sallama
muyiba kafin ka tafi"?
Nuraddin ya juyo tun kafin ya juyo yasan duk
duniya babu mai wannan murya sai 'yar sarkin
Aljanu AMAL. Nuraddin yayi mata murmushin
karfin hali.
"Nadauka bazaki zoba". Yace a bayyane, acikin
zuciyarsa kuma yana cewa lallai na daukowa
kaina jaraba.
"Haba dai, kaima kasan babu abinda zai hanani
zuwa, kadai fadane kawai dan kaji dadin
bakinka". Amal nagama fadin haka sai ta daga
hannunta sama, mamakin Nuraddin saiga
fararen kujeru na azurfa sun fado daga sama
Amal a ajje kujerun sannan ta dubeshi cikin
girmamawa ta so da kauna tace.
"Zauna sonake muyi hirar karshe kafin ka
tafi".
Nuraddin ya dubi gefen hanya a tsorace. Daga
inda yake tsaye, yana iya hangen kofar
makarantarsu, inda dalibai keta bulbulowa
suna shirin tafiya gida, nuraddin yasan takan
wannan hanya da ta ajje kujeru dalibai zasu
wuce, amma yanzu ya fara imani da cewa babu
mai iya ganinsu. Nuraddin ya ajje jakankunan
dake hannunsa ya zauna.
Amal ta dubeshi cikin kunya tace. "Nuraddin
ina son ka sani cewa zuciyata ta gama mutuwa
da kaunarka, hakan cema tasa na kaika har
gaban iyayena, inda ka dauki alkawarin aurena
a gabansu. To gashi dai yau Allah ya kawomu
ka gama makaranta. Don haka nake rokonka da
cewa dan Allah da zarar kaje ka sami iyayenka
ka musu bayani kamar yadda na yiwa nawa
iyayen". Amal ta dan numfasa tana dubansa
kana taci gaba da cewa. "Daga yau Nuraddin
bazaka sake ganina ba sai bayan wata uku zan
zo har gidanku naji yadda kuka yi da iyayenka".
Nuraddin ya dubeta cikin zargi. "mezai hanamu
haduwa da juna har tsahon wata uku? Ya
tambaya lokaci guda kuma yana tunanin
alkawarin da tayi masa na bashi kudin sayen
mota.
"Saboda nasan sai kasha gwagwarmaya wajen
shawo kan mahaifanka akan su barka ka auri
aljana. Bana son kayi musu karya ka sanar dasu
koni wacece. Na baka tsahon wata ukune
domin kayi duk yadda zakayi ka shawo kansu".
Amal ta sake yin shiru akaro na biyu tana
dubansa. "Duk abinda kake so masoyina, ka
lalubi aljihunka da niyar daukar zaka same shi
aciki. Tayi kamar zata mike tsaye sai kuma ta
koma ta zauna. "Ni zan tafi sai na dawo jin
yadda kuka kare dasu, kada kuma ka damu za
muke hirarmu kamar yadda muka saba acikin
mafarki. Rufe idanunka na kaika gida". Amal
tace dashi batare da ta mike daga kujerar data
ke zaune ba.
Adaidai lokacin da wannan ke faruwa, wata
katuwar marsandi taja ta tsaya a kofar
makarantar. Daga inda suke zaune Nuraddin
yana iya hango motar haka ma Amal.
Kofar motar ta bude, Badawiyya ta fito cikin
fara'a ta nufi inda masu gadi suke zaune.
Nuraddin yaji zuciyarsa ta harba, tabbas
Badawiyya shi tazo dauka.
"Badawiyya ce ko"? Amal ta fada a fusace.
"Itace". Nuraddin ya fada Bakinsa a bushe
kamar mai azumi.
"Wannan maiyar yarinyar mai nacin tsiya saina
gurguntata idan bata kyalemin kaiba". Ta kuma
fadi a fusace.
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {P.28}
Ya kama kofar kenan zai bude sai yaji an
kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya mai
kama da sautin muryar jaki.
"Karyar ka tasha karya mayaudari"! Muryar ta
fada "hahahahahaha"!!!
Nuraddin ya waigo a firgice. Nan da nan sai
yaga kyakykyawar fuskar Amal ta fara lotsewa
tana damewa ta koma kamar mulmulallen
dutse, a hankali kuma sai zoko-zakon faratanta
suka fara zazzagowa daga cikin kyawawan
yatsun budurwa Amal. Cikin minti guda ta
rikide ta koma masa tamkar ranar da suka fara
haduwa da ita.
"karya kake mayaudari"! Muryar ta sake
fashewa da mummunar dariya, sannan sai wani
farin hayaki ya turnuke dakin.
Nuraddin na tsaye cikin kaduwa sai kawai yaji
kafafunsa sun kasa daukarsa, lokaci guda yaji
duk sunyi yaushi sun koma kamar tsumma, nan
take ya fadi kasa sakayau ba nauyi. Ba'a dade
ba sai hannuwansa suka fara shanyewa a
hankali-ahankali har suka koma 'yan siri-siri
babu kwari sunyi yaushi kamar lawashin
albasa, wata kumfa-kumfa sai fita take daga
bakinsa sannan kuma sai ya fara fitsari da kashi
a kwance a take gurin. Farin hayakin nan ya
yaye dakin ya zama wayam, babu duriyar Amal
haka nan kuma babu hayakin sai dan sauran
kututturen dan abinda ya rage a jikin Nuraddin
dake nannade.
Adaidai lokacin da duk wannan ke faruwa sai
aka kwankwasa kofar dakin, Badawiyya amarya
ce ta gaji da jira, domin tuni sun karaso, aka
ce da ita mijinta suna ganawa da wata mace
shine to ta biyo sawunsa.
Koda Badawiyya ta leka sa tace "NURI DARLING
a ina kake ne, duk nan kaifa muke jira ya
mamallakina".
Nuraddin ya jita, amma bazai taba iya amsa
mata ba.
Da farko har ga Allah hankalin Badawiyya bai
kai ga inda Nuraddin yake ba, domin abinda
take tsammanin gani shine. Nuraddin tsaye
sanye da kyawawan kayansa na angwanci tare
da budurwar da aka ce suna ganawa.
Dan haka koda Badawiyya ta sake matsawa
cikin dakin sai ta dada cewa.
"Nuri darling fito mana nawa". Akwai alamun
murmushi akan fuskarta.
Shiru ta sake gaishe da kunnuwanta bai amsa
mata ba. Mamaki ya rufeta domin tabbas ance
Nuri na cikin dakin tare da wata budurwa, haka
nan tayi imani da cewa in har Nuri yana cikin
dakin babu yadda za'ayi ta kira shi har sau
biyu bai amsa mata ba. Lallai kam baya dakin
Badawiyya ta dada nanatawa zuciyarta.
Ta tuna wata rana da NURI DARLING dinta ke
cewa da ita.
Badawiyya duk duniya ban taba ganin macen
da nake fahimta kamarki ba.
"me kake nufi"? Ta tambayeshi cikin shagwaba.
"Nuri yace "Abinda nake nufi shine, ko
inuwarki na gani Badawiyya zan iya ganeki, ko
motsin sautin tafiyarki naji a bayana zan iya
gane cewa kece ba tare dana juya ba. Ke
barima ta wannan hatta numfashi idan akayi a
bayana, indai kece sai na gane domin ba
idanuna bane kawai suke ganinki ba Badawiyya,
hakika duk wani shashe na jikina ganinki yakeyi
musamman ma zuciyata".
Wannan tunani shiya dada sa Badawiyya ta
sakankance cewa Nuraddin baya dakin.
Wata zuciya tace da ita fita ki nemi mijinki a
waje. Badawiyya, domin dakin da take tsaye shi
kadai ne bashi da kwan wuta. Dama ba wata
tsiya bace a cikin dakin, kilishine kawai
shimfide da kujeru kanana guda biyu, tuni
daman Badawiya ta sanar da mahaifinta cewa
gidan fa ya musu girma ita da mijinta Nuri,
domin dakuna sunyi yawa aciki.
Badawiyya na nan dai tsaye tana son ta juya,
amma tsigar jikinta sai wani yar-yar take yi.
"NURADDIN". Ta sake kiran sunan cikin wata
rarraunar murya, shi ta dada gaishe da
kunnenta. Wani sassanyan gumi ya fara sartu a
gefen fuskarta. Badawiyya tayi sauri tasa bayan
hannunta ta share, babu abinda ta tsana irin
ace tayi kwalliya, amma gumi ya fara kokarin
bata mata kwalliyar musamman ma wannan
rana data shafe sama da sa'o'i biyu gaban
madubi tana shafe-shafe da goge goge, duk dan
mijinta Nuri.
Idanun Badawiyya sun fara sun fara sabawa da
duhun dakin, hakan ita tasa ta fara hangen
duhu-duhun wani abu kamar kullin kayan
wanki acan kuryar dakin.
Abu na farko data fara tunani shine inda
makunnin lantarkin dakin yake, duk da dai a
iya saninta, har lokacin da suka zo duba gidn
ita da Nuraddin yana daya daga cikin dakunan
da basu da kwan lantarki, amma tasan tun
shekaranjiya mahaifinta ya turo ma'aikata
domin susa duk wani abu da babu shi a gidan.
Wannan shiyasa Badawiyya ta dada matsawa
kadan jikin bango ta fara laluben makunnar
lantarkin dakin.
Adaidai lokacin da hannunta ya tabo makunnar
wutar lantarkin ne to taji kafarta ta zunguri
wani abu. Gabanta ya fadi ras! Abinda ta
zungura yaso yayi mata kama da jikin mutuma.
Badawiyya tayi tsaye nan sororo hannunta akan
makunnin wutar. Tsahon dakiku tana nan tsaye
zuciyarta na harbawa, daga inda take tsaye
tana jiyo haniyar samari da 'yan mata dake
shagali da sowa a farfajiya gidan. Ba zato ba
tsammani sai taji abinda ta shura da kafarta ya
dan motsa. Badawiyya taji kamar ta saki fitsar
a wando saboda kaduwa, kwatsam kuma sai taji
an fara wani gurnani marar dadin ji, gurnanin
yaso yayi kama dana namun daji, hantar
cikinta ta kada.
maryam Ellelah
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {P.29}
"Na shiga uku" Badawiyya tace gami da rike
numfashi. Cikin gaggawa tayi niyyar ja da baya
domin ficewa daga dakin, rabon sai tayi
mummunar gani, sai dan yatsanta ya janyo
makunnar kwan lantarki batare da ta sani ba
nan dan dakin ya gauraye da haske.
Da farko Badawiyya bataga komai ba har sai
bayan dakiku uku lokacin da idanunta suka
saba da hasken sannan ta lura da dan sauran
abin da ya rage daga jikin masoyinta Nuri.
Dan tsurut acikin babbar rigar kafar a shanye
hannu a shanye kyakykyawar fuskar da ganinta
kan jefa Badawiyya cikin nishadi da farin ciki
duk ta yakune kamar matsatstsen lemon tsami,
hakoransa sun fito sarari gayau! Dasu babu
kyan gani sunyi reras dasu acikin bakinsa dasu
babu kyan gani sunyi reras dasu acikin bakinsa
kamar gonar kasusuwa, kan yayi kato tim
kamar dan tulu, idanun sun zazzaro waje
gwara-gwara kamar idon kwado. In banda
agogon dake daure a shanyayyen hannunsa
wanda ya nuna mata a daren jiya yace dashi
zaije wajen shagalin bikinsu, da har abada
Badawiyya bazata taba imani wannan
shanyayyiyar halitta mai kamar aljani a
matsayin Nuri dinta ba.
Da farko tsabar kaduwa da girgiza tasa
Badawiyya ta kasa motsi da zurawa mutum
mutumin Nuraddin idanu tayi can kuma sai ta
dora hannu aka ta kwala ihu.
"Wayyo Allah! Nuraddin na shiga uku"! Ta dada
kwala ihu.
Dakunan gidan da basu sami isassun kaya ba
suka amsa kuwar ihun kukan Badawiyya. Tun
kafin amsa kuwwar ta dusashe Badawiyya ta
fadi gefen Nuraddin sumammiya.
A can kuryar gidan daga bangaren gabas, wasu
motoci ne a jere marsandi fara, honda shudiya
da kuma dankwaleliyar jeep launin rawaya.
Wadannan motoci guda uku kyautace ta
musamman daga mahaifin Badawiyya. Tun ana
sauran kwana uku a daura auren yasa aka kawo
musu. Da yawa daga cikin bakin da aka gayyata
babu wanda zai iya kallon motocin ba tare da
ya sake kallonta ba, domin sababbine fii-fil
hakan ce tasa wasu daga ciki masu karancin
wayewa har hannu suke sawa su dan shafi jikin
motocin suji yadda suke kome suke ji a jikin
motar? Allah masa. Dayake tsakanin inda
motocin suke zuwa inda ake shagalin bikin da
'yar tazara, sa'ar da aka sami damar gyara
wutar sai duk baki suka bar inda motacin suke
suka nufi can cikin gidan. To amma fa banda
wasu samari biyu wadanda ke boye a bayan
motar suna shawagi, lokaci guda kuma suna
mahawara.
"kaga Yusuf, tunda dai kanada Aysha a hannu
kamata yayi ka barmin bakuwar nan". Saurayin
dake magana sunansa Abbati, dan gajerene baki
kakkaura, fuskarsa tana da kyawun gani, sai dai
kuma kansa yafi uban jikinsa girma, wannan
shiyasa da yawa daga cikin abokanansa suke
kiransa da Abba kwandal.
"zance banza kenan", yusuf yace dashi yana
harararsa. "Me kake nufi da inada Aysha a
hannu? Aysha da kullum saita gasamin aya a
hannu ita ce har kake kokari kafamin hujja da
ita? Kaga Abba kwandal nifa *bebe* din nan
babu mai rabani da ita sai Allah".
Abbati kwandal ya fashe da dariya. "yaufa ake
zukin mazallako wai da daga ciki yana rokon
uba kwabo. Yusuf meye kuma na wani fusata?
Babe din da ko sunanta ma bamu sani ba".
Yusuf ya girgiza kai yace. "kaine dai ba san
sunanta ba, amma ni na sani".
Abbatai kwandal ya dafa motar da suke boye a
bayanta da hunnunsa na hagun. "To menene
sunanta idan ka sani"?
Yusuf da wasa yake yiwa Abbati, domin shima
kamar sauran duk mazajen dake gurin yau ya
fara ganin kyakykyawar budurwar ballantanama
har yasan sunanta, dan haka sa'ar da Abbati ya
tambayeshi sunan sai ya daga kai sama kamar
wanda yake kokarin tuno sunan.
"sunana Amal". Wata sassanyar murya
busasshiya mai tayar da tsigar jiki, maral
alkibla tace dasu daga baya.
Samarin biyu suka juyo firgigit cikin mamaki-
mamaki tsoro-tsoro, domin basu taba jin irin
sautin muryar ba. Koda suka juya sai sukaga
wayam ba kowa abayansu.
Yusuf ya dubi Abbati, sannan Abbati ya dubi
yusuf a rude.
"ma...magana naji anyi a bayanmu ne? Yusuf ya
tambaya bakinsa na rawa.
Abbati ya gyada kai a tsorace. "Magana ce...
Magana ce akayi wallahi".
Samarin biyu sukayi mutuwar tsohuwa a gurin
jikinsu na bari kamar mazari, gashi dai inda
suke tsaye suna iya hangen samari da 'yan
matan a can wani bangare na gidan ta ciki
gilashi motar da suke tsaye a bayanta, amma
tsoro ya hana su motsawa daga gurin, ko
shakka basayi maganar mace sukaji gashi
basuga mai maganar ba.
Abba kwandal ya mirgina katon kansa mai
kamar masaki gefe guda kana ya karkata
kunnuwa yayi fakare kamar zakara yana
kokarin ya sake jin daga inda muryar ta fito.
Yusuf na nan tsaye kusa dashi bayan rigarsa ya
jike sharkaf da gumi, a zuciyarsa yanata zargin
kansa da wautar rabo kansu daga cikin jama'a.
Shi daman tun farkon shigowarsu gidan sai
daya ayyana a ransa cewa yanzu haka acike
yake da kwankwamai domin girmansa yayi
yawa.
"mu bar gurin nan". Abbati yace da yusuf cikin
rada yana magana da gefen baki. A daidai
wannan lokacinne fa suka ji daga can cikin
gidan an kwalla ihu da karfin gaske.
Time up.
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {PART
31}
Dakta sulaiman yayi fakin da motarsa kirar honda
a farfajiyar asibitin, sai ya bude kofar motar cikin
gaggawa ya nufi cikin asibitin. Akwai alamun
farin ciki da nishadi karara a fuskarsa, wannan ce
matasa aranar da duk leburan da yayi masa
barka da zuwa sai ya juya ya jefe shi da
murmushi. Wani sa'in ma har tsayawa yakan
danyi ya danyi musu wasa da barkwanci kana
yaci gaba da tafiya.
Wannan sabuwar dabi'a da Dakta sulaiman ya
shigo da ita asibitin aranar ta baiwa kowa
mamaki, musamman ma kananan leburori
wadanda su dama Dakta sulaiman bai daukesu
komai ba, baya da dillalan kashi.
Dakta sulaiman Bafillatanine dan kimanin shekaru
talatin a duniya, dogo fari sosai, yanada fashin
goshi, amma bai fito sosai ba. Yana da farin jini
mai tarin yawa a gurin mata duk kuwa da cewa
sun tsani tsabar girman kansa. Dakta sulaiman
ma'abocin sa farin tabarau ne, tunda ya fara aiki
a asibitin, ba'a taba ganinsa ba tabarau ba. Wani
makaryacin ma ya rawaito cewa wai Dakta
sulaima da gilashin yake bacci. Da yawa yawan
mata abinda ke burgesu ga surar daktan shine
fararen kwayar idananunsa da kan fito
rangadadau ta cikin farin tabaran. Abinda basu
sani ba shine, duk kyawun idanun farinsu da
girmansu gululun banza ne domin baya gani sosai
sai da taimakon farin gilashin nan.
Wannan ya samo asali ne saboda tsabar karatu
da hana idanu barci gami da kallon farar takarda
acikin hasken rana zamanin da yake karatun aikin
likitansa a jami'a.
"Barka da zuwa wani yankunannan tsOho dake
faman goge tayil da tsumma yace dashi.
"yauwa baba tanimu, har yanzu baka tafi gidaba?
Karfe tara saura na dare fa".
Tsananin mamaki da kaduwa ya hana tsohon
kara cewa uffan, sai kawai ya bi dakta sulaiman
da kallo. Tunda tsohon yake aiki a asibitin sama
da shekaru ashirin da doriya baitaba ganin likita
mai tsabar girman kai kamar iblis irin sulaiman.
Ai a tunaninsa ya gaishe da Daktan sama da dari
uku amma bai taba amsa masa ba.
Duk wannan bata hana tsohon cigaba da gaishe
da litkitan ba, domin ko banza lokaci lokaci idan
Dakta Sulaiman ya bushi iska, yakan mika masa
naira dari zuwa dari biyu ba tare da yayi masa
magana ba.
Dakta sulaiman yaci gaba da tafiya cikin sauri
yana duban agogo tara saura kwata. Ai nayi sauri
ma. Yace cikin zuciyarsa kana ya yiwa kansa
murmushi.
Duk da yake dai ba dadin rai ne ya kawo shi
asibitin ba, amma cike yake da farin ciki. A cikin
shekaru uku da yayi yana kula da al'amuran lafiya
na iyalan Alhaji Danbaba kullum addu'arsa itace
Allah ya kawo dalilin dazai sa ya sami damar da
zai duba wannan kyakykyawar budurwa. Amma
bata taba ko ciwon kai ba ballantana ya sami
damar ganawa da ita, sai gashi yau a banza
sa'arsa ta haska, mahaifinta da kansa yayi masa
waya yace wai yayi sauri yaje asibitin ya duba
Badawiyya.
Sulaiman ya yi tsaye jikin farar kofar na 'yan
dakiku yana nazarinta, kana daga karshe sai ya
tura kofar a hankali ya shiga dakin zuciyarsa na
harbawa das! Das!
Dakin da dakta sulaiman ya shiga yana daya
daga cikin dakuna na musamman da aka tanada
a asibitin don kwantar da masu hannu da shuni.
Dakin bashi da girma sosai, gado daya ne jal a
cikinsa sai wata kujerar roca guda daya.
Lokacin da Dakta Sulaiman ya shiga cikin dakin
bai damu da yayi sallama ba, haka nan kuma bai
damu da ya kalli matan dake ciki dakin ba, domin
gaba dayan hankalinsa yana kan gadon da
Badawiyya take kwance. Dakta sulaiman ya
mayar da kofar ya rufe. Ya matso da a hankali
kusa da Badawiyya ya rankwafa hannayensa akan
bakin gadon ya kurawa Badawiyya idanu baya ko
kiftawa.
Kai wannan yarinya da kyawun sa dauke
numfashi take. Sulaiman yace a cikin zuciyarsa.
Tsahon lokaci yana rankwafe yana ta nazarin duk
wani bangare na jikin Badawiyya sai hadiyar
yawu yake kamar tsohon maye.
"Ta farka kuwa"? Sulaiman ya tambayi jerin
matan dake cikin dakin a karo na farko. Inda a
lokacin za'a tambayeshi bai san mata nawa ne a
cikin dakin ba.
A gaskiyar Al'amari mata biyar ne cikin dakin
akwai mahaifiyar Badawiyya, sai kakarta ta wajen
uba hakan nan kuma akwai kanwar babanta.
Sauran matan biyu dangin uwartane, wannan iya
wadanda ke ciki kenan amma farfajiyar asibitin
akwai 'yan uwa da abokan Arziki sama da guda
ashirin.
Sa'ar da Dakta sulaiman yayi tambayar bai sami
amsa da gaggawa ba domin matan babu abinda
suke yi sai sharbar kuka. Tsohuwar nan kakar
Badawiyya ita tayi karfin hali ta dago kai tace
dashi.
"Ta farka harma ta bude idanunta... Sai dai kuma
shi... Tsohuwar ta sake fashe wa da kuka sauran
matan suka rufe mata Baya...............................
Dafatan kunajin dadin labarin matasa maza da
mata???????
ALJANI YA TAKA WUTA CIGABBN LABARI {PART
33}
"Kaine likita sulaiman"?
Yawun bakinsa ya kafe, dan haka sai kawai ya
gyada mata kai kamar kadangare.
'yar budurwar ta dada bude kofar sosai, sannan
ta matsa gefe guda. "zo muje na rakaka, yana
ciki yana jiranka".
"To nagode". Dakta sulaiman ya fadi a karo na
farko.
Budurwar ta wuce gaba tana rausaya kamar
dawisu, shiko dakta na binta a baya, a zuciyarsa
yana tasbihi ga sarki mai komai mahaliccin
kyawawa.
Budurwar ta tsaya dab da wata kofa launi kasa-
kasa mai sheki kana ta juyo ta dubeshi da
murmushi tace. "kana iya shiga.. Yana ciki kai
yake jira".
Dakta sulaiman yaji dadin murmushin dan haka
shima ya haskaketa da fararen hakoransa. "kefa
baza ki shiga ba"?
Budurwar ta girgiza kai. "maganarku ce kai
dashi".
Suka danyi shiru na 'yan dakiku suna tsaye suna
duban juna. Daktanne ya fara magana.
"kinso ki yimin kama da wata kawata A'isha da
mukayi jami'a tare.
Budurwar ta gyara tsayuwa tana murmushi tace.
"Allah ko"?
Sulaiman ya gyada kai.
"To, ni dai ba Aisha nake ba".
Sulaiman yaji zuciyarsa ta harba shin wannan
dama ce agare shi ta ya tambayi sunanta"?
"Me kike to"?
Budurwa tayi dariya har da tafa haNnu. "Au!
Kaima wato irin maganata kake kwaiKwayo ko?
To sunana Badawiyya". Ta danyi shiru kana sai
ta dada da cewa. "Ko kuma kana iya kirana ma
da Badawiyya Nuri".
Dakta sulaiman yaji kamar ta watsa masa wuta a
doron zuciya. Yayi sauri ya boye kishin dake
ruruwa a zuciyarsa ya dubeta cikin mamaki yace.
"Badawiyya Nuri"?
Ta gyada kai. "Kwarai kuwa shine mijin da zan
aura insha Allahu".
Tun daga wannan lokaci har zuwa yanzun nan da
Dakta sulaiman ke tsaye akan Badawiyya bai
daina Addu'ar Allah yasa wata dama ta sake
hadasu ba, saboda tun bayan wannan al'amarin
bai sake samun damar tsayawa da ita daidai na
minti guda ba, sai dai gaisu a tsaitsaye.
Dakta sulaiman yayi firgigit, tunaninsa ya katse a
daidai lokacin da yaji tsohuwar nan kakar
Badawiyya tana cewa.
"Badawiyya... Badawiyya bude idanunki".
Dakta sulaiman ya lura da cewa ashe Badawiyya
ta farka. "ku kyaleta sannu a hankali zata
wartsake". Yace dasu a sanyaye lokaci guda
kuma ya mike tsaye yana duban matan guda
biyar wadanda motsin Badawiyya du yasa sun
mike.
"kuyi hakuri ku dan jirani a waje zan dubata".
Cikin biyayya ba musu, matan suka nufi kofar
fita, kakar Badawiyya ce agaba sauran matan
biye da ita. Mahaifiyar Badawiyya itace ta
karshen fita sa'ar datazo fita saita dubi sulaiman
tace bakinta na rawa.
"Don Allah likita.... Ka dubamin ita da kyau...
Bana son ta mutu..." zuciyarta ta karye sai ta
fashe da kuka.
Dakta sulaiman ya matsa dab da ita, ya tausasa
murya gareta, wani abu da bai taba yiwa wani ba
yace. "kada ki damu kaduwace kawai ta sata
sumewa". A haka ya lallabata ta fice daga dakin.
Fitarta ke da wuya sai idanun Badawiyya suka
bude. Sulaiman ya kurawa kyakykyawar fuskar
idanu baya ko kiftawa. Tsawon lokaci suna nan a
haka. Ga shi dai idanunta wayam a bude, amma
basa kiftawa. Sulaiman ya fara tunanin tabbas
har yanzu tana cikin tsabar kaduwa ne. Ya matsa
kusa da gadon sannan ya daga dan yatsansa na
dama da niyyar taba gashin idanunta.
"Kada ka tabani ina ganinka". Rarraunar muryar
Badawiyya ta katse masa hanzari.
Hannunsa makale a sararin subhanahu, a wannan
karon shine cikin kaduwa.
"Badawiyya... Sannu yaya jikin naki"? Ya sami
kansa yana mai fadi.
Shiru bata amsa masa ba. Can kuma ba zato ba
tsammani sai ta mike zaune zumbur ta dafe kirji
tace ciki karaji.
"Na shiga uku! Ina Nuri... Nuri... Nuri"! Ta sake
kwalla kara.
Cikin gaggawa sulaiman yayi waje ya dagawa
wasu daga cikin matan da suka fita hannu, suka
shigo cikin gaggawa.
"ku rikemin ita". Likitan ya basu umarni.
"wayyo Nuraddin! Dan Allah ku kyaleni na nemo
shi wallahi kashe shizata yi bata da imani. Dan
Allah ku kyaleni wallahi bata isa ta rabani dashi
ba, wayyo"! Ihunta ya kashe sa'ar da taji tsinin
allura ya soketa. Ba'a kara minti guda ba barci
ya saceta.
Dakta sulaiman yaja baya ya tsaya yana haki
cikin kaduwa. Bawai ihu, ko abubuwan da
Badawiyya keyi bane ya sashi kaduwa ba,
wannan yasha jinsu a baya amma maganganun
datake yi su suka jefashi cikin tunani. Nuri? Mijin
da zata aura kenan, shin wacece ke son rabasu?
Dakta sulaiman ya tambayi kansa.
*** *** ***
wani katon zakara mai jar cera yabi wata 'yar
karamar kaza aguje suka fara tsere a tsakar
gidan. Kai! Amma dai anyi girman banza.
Nuraddin yace cikin zuciyarsa sa'ar da yabi kajin
da kallo sun nufi zauren gidan aguje.
Kallo, numfashi da cin abinci mai ruwa-ruwa
sune kadai abinda Nuraddin zai iyayi tun bayanda
masifar ta sameshi.
Sannu a hankali kusan watanni shida kenan da
faruwar al,amarin. Acikin watanni shidan nan
abubuwa da yawa sun faru wadanda mafi yawa
daga cikinsu na bakin ciki ne. Alal misali tun
sa'ar da aka kawo Nuraddin gida mahaifiyarsa
bata kara samun lafiya ba, yau cuta gobe cuta,
kullum ta dubi Nuraddin a kwance akan katifa a
tsakar gida nannade kamar igiya sai ta sashi
gaba tayi ta kuka.
ALJANI YA TAKA WUTA
CIGABAN LABARI {part34}
Dakyar da ban baki da
rokon Allah 'yan uwa
suka shawo kanta ta
fara cin abinci kadan- kadan. Abangaren abin
da ya shafi magani
kuwa ya zuwa yanzu an
sami bokaye kusan
talatin, malaman tsibbu
arba'in da sauran 'yan bani na iya sama da
goma sha uku amma
duk a banza. Duk wanda
yazo ya dubi Nuraddin
sai ya girgiza kai yace.
Wannan sai dai abinda Allah yayi. Duk wannan
dawainiyar kashe-
kashen kudi da ake ta
faman yi ba wani ke
yinta ba sai mahaifin
Badawiyya. Ganin kullum sai kashe kudi
akeyi a banza babu
alamun sauki shiyasa
mahaifin Nuraddin wata
rana yaje har gida ya
sami mahaifin Badawiyya yace dashi.
"ya kamata ka daina
kashe kudinka haka
nan, abinda kayi Allah
saka maka da alherinsa,
Allah yaga niyyarka kayi kayi iya yinka Allah
ne dai baiyi zai samu
sauki ba".
Alhaji Danbaba ya dubi
Dattijon mahaifin
Nuraddin ya girgiza kai cikin tausayi kana yace.
"A'a malama ina fa zai
yiyu a kyale yaro acikin
irin wannan hali babu
magani ai bashi yiyuwa".
Mahaifin Nuraddin ya danyi shiru na wani
lokaci kana sai ya dago
kai yace. "Abinda nake
son ka fahimta shine
wadannan bokaye babu
abinda zasu iya yiwa yaron nan, shiyasa nake
ganin kawai mu mika
komai ga Allah a sami
malamai suci gaba da yi
masa addu'a kullum".
Tun daga ranar sai suka ajje zancen bokaye a
gefe, Alhaji Danbaba ya
sami wasu amintattun
malamai wadanda duk
kwana ukun duniya sai
sun karantawa Nuraddin Al-qur'ani mai
girma su kuma yi masa
addu'ar Allah ya bashi
sauki.
Tunda Badawiyya ta
sami sauki sai ta tare a gidansu Nuraddin, anan
take kwana sai dai
akawo mata suturunta
da abincinta nan. Ita ke
taimakawa mahaifiyarsa
suyiwa Nuraddin dinta wanka, ita ke bashi
ruwan zuma ko madara,
da sauran dangin abinci
masu ruwa-ruwa. Haka
Badawiyya ta kasance
acikin wannan hali na tsawon lokaci, kullum
haka zatasa masoyinta
agaba tana cewa cikin
kuka.
Nuri darling nida kai
alkawari ne babu mai rabani da kai sai
mutuwa. Wani sa'in da
zarar ta fadi haka, saita
tallabo kwandalelen kan
Nuraddin ta dora akan
cinyarta tana kuka kuma tana cewa...
"sannu Nuri kaji... Kayi
hakuri Allah ne ya dora
mana, idan yaso yau ma
saiya yaye mana". Aikin
kenan ba dare ba rana. Wani sa'in idan
Mahaifiyar Nuraddin ta
jiyo Badawiyya tana
fadin irin maganganun
sai tayi sauri tabar guri
saboda tausayi, ta koma can cikin dakinta tayi ta
kuka a boye.
Wata rana a cikin
ranakun da suka biyo
baya, Badawiyya na
zaune tana durawa Nurin ta ruwan madara,
sai mahaifiyarsa tace da
ita cikin sanyin murya.
"Badawiyya ina ganin da
komawa kika yi gida da
kwana, kinga kwana anan bana irin naki
bane.. Makwancin bashi
da kyau kuma muddin
kina ganinsa a kullum
hankalinki bazai taba
kwanciya ba". Badawiyya ta sunkuyar
da kai gami da
murmushin yake lokaci
guda kuma ta fara yiwa
Nuri fifita. "Baba... Idan
na daina kwana ma anan ba daina tunaninsa
zanyi ba, gara dai ina
kusa dashi idan mutuwa
ma zaiyi gara mu mutu
tare".
"mema ya kawo zancen mutuwa, abinda nake so
dake shine ki koma
kwana a gidanku inya
so in ma zuwan zakiyi
kya ke zuwa da safe,
amma yanzu kullum kina nan, gashi babu
ranar warkewa ki
barwa Allah Badawiya
nasan yadda kike ji a
zuciyarki to amma sai
hakuri". Tun daga wannan rana
ne Badawiyya ta koma
gida da kwana, yau
wata hudu kenan daidai
amma duk da haka
kullum karfe takwas na safe take baro gida tazo
gurin Nurin ta bazata
koma gida ba sai goma
na dare.
Adaidai lokacin da
katon zakaran mai cara yabi kazar da gudu ne
Badawiyya ta shigo
zauren gidan
hannayenta dauke da
jakankunan leda guda
biyu wadanda ke cike da kayan shaye-shaye
iri-iri.
"salamu alaikum".
Badawiyya tai sallama.
Mahaifiyar Nuraddin
wacce ke shara a tsakar gida ta amsa sallamar
gami da mikewa tsaye.
"Badawiya har kin iso"?
Badawiyya ta gyada kai.
Sannan idanunta suka
nufi inda kuturturan Nuraddin yake.
"ina su Hajiya da Alhaji
ina fatan dai suna
lafiya"?
"Lafiyarsu kalau".
Badawiyya ta amsa, kana ta nufi inda Nuri
yake ahankali tana
nazarin yanayin jikinsa.
Akwai tsammanin dake
damun zuciyarta,
akullum idan tabar Nuri tunani take yi kamar
gobe idan ta dawo zata
same shi ya warware.
Amma sabanin
tunaninta duk sa'ar data
zo saita tarar dashi jiya ya yau.
Suturar dake jikin
Badawiyya ba wata ta
kuzo ku gani bace
doguwar riga ce baka
kafarta kuwa takallamine silifa, tun
ranar da Nuri ya
nannade ta daina
kwalliya.
Badawiyya ta matsa
dafda katitafar da yake kwance ta ajje
jakankunan ledar a gefe
guda, sannan ta fara yin
abubuwan data saba yi
masa na al'ada tun
tsawon watannin shida da suka shude.
"Nuraddin ina kwana".
Tace a tausashe tana
duban fuskarsa, tasan
bazai amsa mata ba
domin babu bakinsa an rufe, amma duk da haka
akwai alamun da take
ganin a fuskarsa ta
gamsu da cewa lallai ya
amsa gaisuwarta.
"ya jikin naka"? Idanuwansa suka motsa
wannan shi ya tabbatar
mata da cewa ya amsa.
Tun a mako na farko da
faruwar al'amarin
Badawiyya ta fahimci cewa duk abinda aka ce
da Nuraddin yana
fahimta mayarwa ne dai
bazai iya ba.
======ALJANI YA TAKA WUTA CI GABAN LABARI
{P.35}=======
Wannan tunani na Badawiyya gaskiya ne, domin
tun ranar da aljana Amal ta shanye shi, duk
abinda ake cewa yana ji, sai dai bashi da ikon
magana. Bakin cikin dake kunshe a zuciyar
Nuraddin yafi bakin cikin bayan tukunyar dahuwar
shayin bakin kasuwa. Yaya za'a ce kullum sai
Badawiyyarsa tayi masa magana amma shi baida
ikon maganar. In banda tunanin da sa ran
akullum zai iya warkewa, su sake ganawa sosai
da masoyiyarsa Badawiyya da tuni ya hadiyi
zuciya ya mutu.
Akwai lokuta da dama da Amal kan bayyana
gabansa tayi ta kyakyata masa dariyar mugunta.
Zuciyar Nuraddin takan tafasa ta kone saboda
bakin ciki. Badawiyya ta dada matsowa kusa da
Nuri ta tallafi kansa ta dorashi bisa cinyarta,
kana ta bude daya daga cikin jakankunan ledar da
tazo dasu ta dauko wata doguwar kwalba mai
dauke da tacacciyar madara sannan a hankali ta
bude ta fara baiwa Nuraddin a baki.
*Bani da kamarki Badawiyya, Allah ya bani sauki
na rama miki abinda kike yimin*. Nuraddin ne ke
fadin haka cikin zuciyarsa. Duk abinda Badawiyya
ke masa yana gani kuma yana ji.
Tsahon lokaci suna nan a wannan hali, Badawiyya
na bashi madarar shiko yana shan rabi, rabin na
kwararewa ta gefen Bakinsa.
"Bari inzo in gogge masa jikin". Mahaifiyarsa ce
ke cewa da Badawiyya hakan.
Badawiyxa ta girgiza kai cikin ladabi. "ki bari zan
goge masa".
Mahaifiyar Nuraddin tayi tsaye tana dubansu ta
tuna da cewa kwana daya kawai da daura
aurensu, masifar ta sameshi amma dubi yadda
take fama dashi kamar daman sunyi shekaru
masu yawa amatsayin ma'aurata. Hawaye ya
kwace mata. Cikin gaggawa ta juya ta nufi dakin
girke-girke domin bata son ta tashi hankalin
Badawiyya.
Wani yaro ya shigo tsakar gidan a guje, kaji da
tattabaru suka yi tsalle gefe guda. Kwakwazon
kajin shiyasa mahaifiyar Nuraddin dake dakin
girke-girke fitowa cikin sauri tana share hawaye
ta tari yaron.
"lafiya ka shigo a guje? Kufa bakwa rabuwa da
kiriniyar banza".
Yaron yaci gaba da tsalle-tsalle agabanta.
"wallahi wai...wai ana kiran Badawiyya..
Badawiyya taji abinda yaron yace cikin mamaki ta
dago kai ta dubi mahaifiyar Nuraddin .
"wai ke ake kira". Mahaifiyar Nuraddin tace tana
duban Badawiyya. Akwai alamun mamaki karara
a muryarta.
Badawiyya ta ajiye tsumman data gama goge
jikin Nuraddin, kana ta dada gyara masa
kwanciya ta dubi yaron. "wanene ke kirana"?
Kwakwalwarta ta fara tunanin gaggawa, a iya
saninta ko a gidansu babu wani mutum in ba
kawayenta ba da yake zuwa nemanta, sai gashi
yanzu wani na kiranta a waje. "ko kuwa dai
macece"? Ta kuma tambayar yaron.
"Wani ne... Wani mutum ne a mota yazo".
Sukayi jim na dan lokaci, mahaifiyar Nuraddin ce
ta fara magana.
"Ai sai kije ki gano, Allah sa dai lafiya".
Badawiyya ta mike a hankali, ta dubi Nuraddin
tace. "Ina zuwa Nuri yanzu zan dawo minti daya
kawai". Ta daga danyatsa akan fuskarsa kana ta
jefe shi da murmushin karfin hali idanun Nuraddin
suka kifta alamun ya fahinta.
Cikin gaggawa ta nufi kofar gidan don kawai
biyayya ga mahaifiyar Nuraddin bawai don taso
ba.
Badawiyya na fita tayi turus kamar ta fada cikin
fasassun tukwane.
A tsaye a jikin wata shudiyar marsandi sanye da
jaket da wando shudaye, kafarsa sanye cikin
takalmi baki mai walwalin dauke idanu. Idanunsa
boye a bayan farin tabarau, wani dogon saurayi
ne fari mai dan siririn fashin goshi.
Saurayin yayi mata murmushi yace "ki gafarceni
Badawiyya ina fatan kin ganeni"?
Badawiyya ta zura masa idanu kamar biri da
kararrawa tana kallonsa ko kiftawa batayi tsawon
lokaci bata dauke idanunta ba ita ko bace dashi
kala ba.
"Badawiyya ko baki ganeni bane"? Saurayin ya
kuma tambaya.
Badawiyya tayi firgigit kamar wacce ta nutse a
kogin tunani sannan saita sunkuyar dakai tace.
"Na ganeka mana ba kaine Dakta Sulaiman"?
Dakta Sulaiman ya laltbi kwibin aljihun rigarsa na
dama ya zaro wani rawayan kyalle na siliki
sannan ya fara goge fuskarsa. Tabbas gumi yake
yi. Akwai wani yanayi na ko in kula da lumbu-
lumbu dake kan fuskar Badawiyya, wannan shiya
sashi rauni, kana yaji gumi ya fara sartu akan
goshinsa. "Yaya gidan lafiya"? Ya sami kansa
yana fadi.
"lafiya Badawiyya ta amsa a takaice kana sai ta
dan juya masa baya tace.
"Sai kayi sauri ka fadi abinda kake son ka fada
domin minti daya na nemo izni.
Dakta Sulaiman yaji duk gwiwowinsa sunyi sanyi.
Ya dada share gumi yace muryarsa na rawa.
"maganganuna da nazo dasu suna da yawa
Badawiyya, domin sama da shekaru uku kenan
ina fatan Allah ya kawo mu wannan rana dazan
Amayar miki abinda ke boye a zuciyata".
Badawiyya ta juya a yatsine sannan ta gyara
tsayuwa tace. "Ina jinka amayar".
Dakta sulaiman ya gyara Tsayuwa ya jingina
bayansa jikin motar kana ya fara.
"Tun sa'ar dana fara dora idanuna akanki nake
kaunarki Badawiyya kuma nauyin mahaifinki da
nake ji su suka hanani na furta miki manufata
tun farko". Yayi shiru kana ya gyara farin tabaran
dak idanunsa yaci gaba.
Abdullahi Yusuf Maitama.
====ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI
{P.36}====
"Badawiyya ayau ciwon dake cikin zuciyata ya
tsananta, tun ina boyewa gashi har ya fito fili.
Badawiyya ina sonki sani cewa ayau bana ganin
komai sai ke haka banajin komai sai muryarki, sai
abinda kika yi dani".
Dakta sulaiman yayi shiru akwai alamun
taraddadi ta karaya karara akan fuskarsa domin
bai san irin amsar da zata fito daga bakinta ba.
"kagama"? Badawiyya ta tambayeshi a yatsine.
Jikinsa na rawa sulaiman ya dubeta kamar ya
fashe da kuka ya daga hannayensa biyu ya dora
akan cinyarsa yace. "Babu zance gamawa
Badawiyya sai da ace wannan shine mafi
mahimmancin abinda ke tafe dani".
Tsahon lokaci matasan biyu na tsaye suna duban
juna, akwai alamun damuwa karara a fuskarsa,
meyiyuwa su basu lura da hakan ba domin
kawunansu a sunkuye suke.
"Biyo ni mu shiga ciki in nuna maka wani abu".
Dakta sulaiman ya dubeta cikin mamaki, daidai
lokacinne wani katon kuda kore ya yiyo hijira
daga kan bawon ayabar da yara suka jefar ya
nufo kunnen Dakta sulaiman yanayi masa Bu!
Bu!! Dakta sulaiman yakai duka ya mari fuskarsa
a banza.
"Banjiki sosai ba kina nufin mu shiga ciki"?
Dan abu zan nuna maka yanzun nan zamu fito ko
minti daya ba zamu yiba". Tana gama fadin haka
saita juya ta fara tafiya ta nufi zauren gidan.
Sulaiman yayi kamar kada ya shiga gidan domin
baisan abinda take nufi ba gashi kuma uwa uba
babu alamun dake karfafa masa gwiwa. To amma
sa'ar da yaga gadan-gadan shigewa zatayi, sai
sulaiman ya bita a baya cikin sauri har da
sassarfa, kadan ya rage ya taka wuyan wata
farar kaza. Badawiyya ta rage sauri sa'ar dataga
yana biye da ita. Tana tafiya tana tunani. Acan
wani bangare na zuciyarta gani take yi abinda
tayi daidai ne domin ahalin da ake ciki a yanzu
itace hanya mafi sauki da zata kirkira domin ta
rabu da wannan sabuwar masifar da ta kunno
mata kai. Ta sani cewa duk tsayin lokacin nan
zuru kawai akayi mata saboda tausayin halinda
take ciki, amma da tuni an fara tunanin araba
aurenta da Nuri tunda dai babu ranar
warkewarsa. A gareta duk wani abu da zai rabata
da Nuri dinta masifa ne.
Tauraron da sa'ar Badawiyya ya haskaka sa'ar
da suka shiga tsaka gidan domin mahaifiyar
Nuraddin ta zagaya bandaki. Dan haka cikin sauri
sai Badawiyya ta wuce da sulaiman kai tsaye
zuwa inda Nuraddin yake kwance. Badawiyya ta
dago ta dubi sulaiman da niyar nuna masa
Nuraddin, amma alamun kaduwar data gani
karara akan fuskarsa. Sun isa ta san yaga
Nuraddin.
Tsawon lokaci likitan na tsaye ya kurawa
Nuraddin idanu, can sai yayi ajiyar zuciya ya dubi
Badawiyya yace. "wannan shine abinda kike son
nuna min din"?
Badawiyya ta gyada kai sannan tace. "zo mu
koma waje".
Dakta sulaiman ya bita a baya zugum-zugum
kamar rakumi da akala, duk ilahirin jikinsa rawa
yake kamar mazari. Suna fita kofar gidan sai
dakta sulaiman yayi sauri ya jingina da jikin
motarsa, domin ji yake yi kamar kafarsa bazata
iya daukarsa ba. A tsahon lokacin da yayi yana
aikin likita ya sha ganin munanan abubuwa,
kamar irin su gawar hadarin mota da sauransu,
amma sa'ar da yaga Nuraddin, sai da hanjin
cikinsa ya yamutse, gashi a kanannade babu kyan
gani amma wai da rai.
Badawiyya ta dubi fuskar Dakta Sulaiman taga ta
hada gumin sharkaf. "Ina fatan ka kare masa
kallo"?
Dakta sulaiman ya gyada kai lokaci guda kuma
yayi ajiyar zuciya yace bakinsa na rawa. "Menene
dalilin nuna min shi"?
Badawiyya ta dubeshi ido da ido tace. "Wadanda
suka kwatanta maka kazo nan ka sameni basu
baka labarin abinda ya mayar dashi haka ba"?
Dakta sulaiman ya girgiza kai, yawun bakinsa ya
bushe. Tsawon lokaci suna duban juna, can sai
tace dashi.
"wannan mutumin da na nuna maka mijina ne,
kwana daya da daura mana aure aka mayar dashi
haka".
Dakta sulaiman ya dubeta a rude. "mijinki fa kika
ce"?
Badawiyya ta gyada kai. "Kwarai kuwa, da
lafiyarsa kalau, kamarka yake a dalilin wai saiya
rabu dani yaki wata aljana ta mayar dashi haka.
Me yiyuwa bazaka yarda da wannan labarin ba,
amma haka dai abin yake". Ta danyi shiru kana
saita dubeshi. "shiyasa na nuna maka shi domin
na sanar dakai cewa duk da haka din da yake, a
duniyar nan babu wanda nake kaunar gani
kamarsa. Akan sai ya rabu dani aljana ta mayar
dashi haka, don haka nake son ka fahimta aljana
ma tayi kokarin raba mu bata samu nasara ba,
ballantana kai mutum mai 'yar kankanuwar
soyayya, babu mai rabani da Nuri darling sai
mutuwa". Tana gama fadin haka sai ta juya da
sauri ta koma cikin gida. Wata sassanyar iska ta
fara busa fuskar Dakta Sulaima. Abin yayi
matukar kadashi bai taba jin labari kamar
wannan ba.
Da sassafe misalin karfe shida saura 'yan
mintuna, Badawiyya ta tashi zaune akan gadonta,
domin lokacin yin wankanta yayi, sai taji kanta
ya fara sarawa. Dama tunda asuba kan nata ya
fara alamun zaiyi ciwo. Badawiyya ta janyo
matashin kan dake kusa da ita ta tura shi a
bayanta kana ta jingina da bango, lokaci guda ta
zura hannunta da dauko hoton Nuraddin dake kan
wani teburi dafda gadonta ta dora hoton akan
kirjinta sannan ta zura masa idananu.
Abdullahi Yusuf Maitama.
ALJANI YA TAKA WUTA {p.37}
Ba'a fi ko dakiku ashirin ba da fara kallon hoton
sai hawaye ya fara sartu akan kyawawan
kumatunta shar-shar.
Wannan sabuwar al'ada da Badawiyya ta tarka ba
karamin konawa mahaifiyarta rai take ba. Tun
tsawon watanni shidan nan, haka Badawiyya
kanyi aduk safiyar duniya.
Ga al'adarta kullum karfe shida take tashi na
safe, ta dauki hoton Nuraddin ta kura masa idanu
tayita kuka. Haka nan zatayi ta fama har zuwa
bakwai, wani sa'in har sai idan mahaifiyarta ta
shigo ta lallasheta, sannan zata bar kukan ta
wuce zuwa bandaki tayi wanka.
Dan haka wannan safiyar sai taji hawayen da
yake zuba yafi na kowacce rana domin in har
ciwon kan yaci gaba da takura mata zaiyi wuya in
har zata iya zuwa gurin Nuraddin dinta, wannan
kuwa yafi komai kona rai a gareta.
Aka kwankwasa kofar a tausashe. Badawiyya ta
dubi kofar cikin gaggawa, haka nan lokaci guda
ta ajiye hoton dake kan kirjinta akan katifar
gadon. Kofar dakin ta bude ahankali mahaifiyarta
ta leko, sanye take da doguwar riga baka kanta
daure da dan kwali na zani. Koda Badawiyya ta
dubeta sai taga alamun damuwa karara akan
fuskarta wannan shine yasa ta mikewa zaunen
sosai ta dubi mahaifiyarta, har yanzu akwai
sauran hawaye akan fuskarta.
"kukan dai kike Badawiyya"? Mahaifiyarta ta
tambaya. Adaidai lokacin data zauna a bakin
gadon ta fuskanci 'yarta Badawiyya.
"Ina ganin lokaci yayi daya kamata ki sallamawa
ubangiji dukkan abinda ke damunki kada ki bata
rayuwarki a banza".
Badawiyya taji gabanta ya fadi, domin bata taba
tsammanin haka daga bakin mahaifiyarta ba.
"yanzu ace mutum Badawiyya bashi da aiki
kullum kwanan duniya sai koke-koke da kuncin
zuciya, wannan ai sai hawan jini ya kamaki. Ina
ganin ya kamata ki rage zuwa gun Nuraddin haka
nan domin ganinsa shike jefa ki cikin damuwa".
Badawiyya taji kamar an watsa mata wuta a
fuska, ta dafe kirji cikin razana, rashin ganin
Nuraddin yafi kowacce irin masifa azaba a
gurinta, sai gashi kuma yanzu mahaifiyarta da
kanta tana cewa wai ta rage zuwa gurin Nuraddin
dinta. Nan da nan taji hawaye ya fara yi mata
sartu akan kumatu sar sar kamar ruwa.
"Ba kuka zakiyi ba, hankalinki yaki bani nan na
fahimtar dake abinda nake nufi". Ta danyi shiru
na wani lokaci, kana taci gaba. "Ba wai ina nufin
ki daina zuwa gurinsa bane kwata-kwata, amma
ya kamata ki rage . Ina laifin kina zuwa gurinsa
sau daya a sati. Amma ki tafi can ki tare kullum
sai kinje, watanni shida kenan fa. Kuma banda
wannan ma kina nufin zaki yi ta zama da shi
ahaka kenan har abada bazaki sake aure ba"?
Numfashinta ya dauke akaro na farko ta dago kai
ta dubi mahaifiyarta tace cikin rarraunar muya
tana kuka. "shi kuma fa.. Yaya zanyi dashi? Shi
ba mijina bane"?
Ganin halin da Badawiyya ta shiga shiyasa
mahaifiyarta ta matso kusa da ita sannan ta
dafata tace. "Nasan mijinkine Badawiyya, kuma
har yanzu da aure a tsakaninku amma yayi
muguwar nakasa, nakasar da bashi da wani
amfani agareki. Yanzu ke kya iya zama da
mutum a kanannade haka har abda? Sai dai ki
bashi abinci kiyi masa wanka ki kwantar ki tayar,
haka zata yiyu kuwa Badawiyya".
Badawiyya taji zuciyarta na neman tsagewa, irin
wandannan maganganu na mahaifiyarta sun fara
isarta domin basu da wata ma'ana agareta.
"mama saboda nifa Nuraddin ya shiga halinda
yake ciki ayanzu, da yabi umarninta ya gujeni da
yanzu yana nan lafiya klau kamar mu. Nikam
bazan iya rabuwa da shiba domin koda na rabu
da shi din ma zuciya da duk wani bangare na
ruhina suna tare dashi". Ta sake fashewa da
kuka.
"ke har yanzu yarinya ce ana rabaki da kiwon
akuya kina kwalla ta haihu abin da baki gane ba
shine kada ki kasancd mai yawan son kanki ke
kadai ki tunafa ni mahaifiyarki be, kuma kina da
mahaifi, ki sani kuma babban burinmu a duniya
shine mu sami jikoki muyi alfahari dasu kamar
kowanne kaka aduniya, to yanzu Badawiyya ta
yaya wannan buri namu zai cika idan kuna tare
da wannan yaro wanda a yanzu mutuwarsa tafi
rayuwarsa"? Tadan saurara tana nazarin fuskarta.
"ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki kuma
fahimci abinda nake kokarin yi miki. Kinga yanzu
akwai yaro dake masifar kaunarki kyakykyawa
dashi, shi baima san kinada aureba sai daga baya
tunda kullum a gida yake ganinki, kamata yayi a
raba aurenku da Nuraddin sai a hadaki dashi".
Badawiyya ta zabura ta dago a tsorace ta dubi
mahaifiyarta cikin kuka. "Bana fatan Allah ya
nunamin wannan rana... Arabani da Nuri"?
Mahaifiyarta ta harareta. "shashar banza, kinsan
dawa nake nufin za'a hadaki? Wannan likitanne fa
daya dubaki alokacin da kika suma, dakta
sulaiman. Kuma in kin aureshin dinma wayace kin
rabu da Nuraddin har abada, sai insa mijin naki
duk sati yana kaiki kina dubo shi".
Badawiyya ta zuro kafafunta kasan gadon kana
ta sunkuyar da kai tana shasshekar kuka tace.
"Bani da wani mijin da ya wuce Nuri, bazan iya
rabuwa dashi ba, tunda ya shiga masifa saboda
ni nayi alkawarin babu mai rabani da shi sai
mutuwa.
"zakwa ki ci ubanki 'yar banza sokuwa inkayi
wasa wallahi saina hana ki fita koda nan da
tsakar gidane".
JANI YA TAKA WUTA {P.38}
Awannan ranar saboda abinda ya faru tsakaninta
da mahaifiyarta bata sami damar dawowa daga
gurin Nuri dinta ba sai baya karfe goma sha daya
da rabi na dare.
Lokacin data dawo gida maigadi ya gaisheta,
sannan ya janyo kofar gidan ya rufe. Tsahon
watanni shida kenan kullum itace karshe shigowa
gidan saita shigo za'a rufe. Maigadin yan
matukar tausaya mata domin laraba mai dafa
abinci a gidan ta taba yi masa gulmar duk
abubuwan dake faruwa akan Badawiyya.
Cikin sauri Badawiyya ta nufi dakinta. Ta riga
tasan kullum da anyi sallar isha'i mahaifiyarta
take yin barci koda yake dai koda tsakar darene
sai mahaifyarta ta leko dakin ta tabbatar ta dawo
sannan zata koma ta kwanta.
Badawiyya ta tura kofar dakin ahankali sai taji
gabanta ya fadi ras, domin tana budewa sai wani
haske ya kashe mata idanu. Kusan dakiku biyar
tana tsaye kafin idanunta su saba da hasken dake
dakin. A lokacinne to Badawiyya taji gabanta ya
fadi. Hasken daga kan gadonta yake bullowa. A
zaune a bakin gadonta tasha kwalliya da kayan
kawa na gaske, fuskarta na kyalkyali kamar
madubi acikim rana Amal ce 'yar sarkin Aljanu.
Tun wani lokaci daya shude Amal ta daina baiwa
Badawiyya tsoro, dan haka a wannan irin yanayi
da ita kanta Badawiyya ke neman abokin mutuwa
sai taji ko kankani Amal ta daina razanata.
"Me zaki yimin kike jirana? Ko zuwa kika yi nima
ki nannade ni? Idan wannan ce niyyarki to
bismillah domin wallahi bani da kaico don kin
nannadeni tunda dai kin mayar da Nuri na haka
macuciya"!
Amal ta dubeta tana murmushi. "Bakaken
maganganunki na iya sawa kiyi nadama".
"Babu wata nadama da zanyi, domin a yanzu
bana tsoron komai, tun daga ranar da kika
nakastamin abin begena, naji na daina tsoronki
bana tsoron kowa a duniya inba Allah ba. Na riga
na kuna bana tsoron kauri dan haka a yanzu ina
umartarki dan Allah ki mayar dani kamar
Nuraddin dan uban da ya haifeki makira"!
Amal ta dubi Badawiyya cikin mamaki dan bata
taba tsammanin irin wannan taurin kai daga
gareta ba.
"Abin bai kai da zagi ba Badawiyya sasin kanki
ne idan inaso yanzun nan ina iya marayar dake
KARAS ko kuma TUNKIYA, amma ni ba wannan
ce ta kawoni ba, abinda ya kawo ni shine zuwa
nayi na baki dama ta karshe, domin ina tausaya
miki a matsayinki na 'yar uwata mace".
Badawiyya ta dubeta cikin rashin aminci, dumbin
tsana karara akan fuskarta. "Wacce dama kuma
zaki iya bani, tunda kin nannade abin kaunata"?
Amal ta mike tsaye daga kan gadonta ta nufo
inda Badawiyya take tsaye, a tsakar dakin.
Badawiyya tayi tsaye kikam ko gezau bata yiba,
duk kuwa da cewa ta lura da farin takalmin dake
kafafun Amal na farar azurfa ne. Badawiyya tayi
mamakin abinda ke cikin takalmin shin tafin kafa
ne ko kuwa kofato".
"kin cika taurin kai Badawiyya kamar Nuraddin".
Amal tace da ita tana dubanta.
"Wannan shiya tabbatar da cewa irin jininmu daya
da mijina Nuri". Badawiyya ta bata amsa. Mijina
din data ce shi yafi komai konawa Amal 'yar
sarkin Aljanu zuciya fiye da komai.
"zabin da zan baki shine na karshe, in kin yarda
kin tserar da shi, idan kuwa kinki to haka
Nuraddin zaiyi ta zama har abada ni kuwa baza
ki kara gani na ba".
"Allah ya fiki makira, kuma ko yaushe naga
damar ganinki saina ganki shin ko kin manta ne
da zoben dake hannuna"? Badawiyya ta daga
danyatsanta sama.
Amal ta dubi zoben da ta baiwa Nuraddin cikin
takaici, tasan duk cika bakin da take na banza ne,
do muddin Badawiyya na tare da zoben nan, ko
babanta mai hancin karas bai isa ya tabata ba
ballantana Amal.
"kinga Badawiyya irin halinda Nuraddin dinki ke
ciki, kashi da fitsari duk a kwance, amma idan
naga dama yanzun nan saina mayar dashi kamar
yadda yake ada in har zaki yimin alkawarin abu
daya". Badawiyya ta dubeta cikin rashin yarda.
"wane alkawari"?
Amal ta dubeta tace "ina so kiyi min alkawarin
indai na warkar dashi zaki bar min shi na aura.
Ke kuma ki sai ki auri wannan sulaiman din da ke
son ki yaya kika gani"?
Badawiyya ta harari Amal tace. "Amal idan zaki
yarda da kaddarar mahalicci, to ki yarda kawai ki
warkar da Nuraddin amma zancen na bar miki shi
baima taso ba' domin babu mai rabani da Nuri
darling sai muuwa.
Amal 'yar sarkin aljanu ta fashe da dariya tace.
"kada ki cuceshi ki cuci kanki, na baki daga yau
zuwa gobe kiyi tunani, in dai har dagaske ne kina
kaunarsa, ki bari mana na warkar dashi na
aureshi domin zamansa lafiya baya tare dake yafi
zamansa a nannade tare dake, ko kuwa me kika
gani"? Ta danyi shiru sannan taci gaba. "Gobe
zan dawo da daddare kiyi tunani da kyau
Badawiyya kawata".
Kafin kiftawa da bismillah Amal ta bace. Dakin
yayi shiru dif! Kamar makabarta. Badawiyya jiki
na rawa ta jingina da bangon dakin sannan ta
lumshe idanunta tace a fili.
"ALLAH kayi min maganin wannan masifa".
ALJANI YA TAKA WUTA
Table of Contents