Launin Fata Book 2 Complete Hausa Novel

Launin Fata Book 2 Complete Hausa Novel

Kan Rabi’a na ƙasa, gabanta na faɗuwa kamar zai tsage ya fito. Tana jin dariyar da Muhammad ke kyalkyalawa yana faɗin, “Ko dai ki ba ni haɗin kai, ko in ƙulla miki sharrin da ba za ki iya fita ba.”

Muryarta na rawa ta ce, “Ka ji tsoron Allah, ka tuna ranar da za ka haɗu da shi. Ni matar ɗan uwanka ce, bai dace ka nemi yin alfasha da ni ba…”

Ya ce, “Ke kin san kuwa kyakkyawar surar da kike da ita? Ko mutum bai niyyar kallanki ba sai ya kalla. Sha’awarki ta daɗe tana wahalar da ni, ba zan iya haƙuri da ke ba.”

“Na ba ki minti biyu, ina zuwa. Ki yi tunani. Ban ce dole sai kin yarda ba, amma abin da zai biyo bayan rashin yardar taki ba zai miki daɗi ba.”

A hankali ya sulale ya fice daga ɗakin, yayin da Rabi’a ta sulale ita ma ta zauna. Ta kama kai da hannu biyu tana faɗin, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Wace irin rayuwa na faɗo haka?”

Tunanin abin da ya faru ranar, ita yau makamancin na jiya, ya faɗo mata.

Fitowa ta yi daga ɗaki, ta tsuguna gaban Tahir ta ce, “Me zan faɗa maka, mai gida?”

Kafin ya yi magana, sai ga Dije ta ɗaga labulan, ko sallama babu, ta tsaya a kansu ta ce, “To munafuka uwar kinibibi, me bin miji da rana? Ko ki zo hura wutar tuwo.”

Tahir ya manna mata harara ya ce, “Ba ta zuwa.”

Da jin haka, Ali ɗan Dije ya ruga ɗaki gaya wa Kawu, “Ga Tahir can yana zagin innarsa don ta ce Rabi’a ta zo ta hura wuta.”

Haka shi ma Kawun ya faɗo ɗakin yana huci kamar wani kumurci. Dije na ganinsa ta fashe da kuka ta ce, “Yawwa, gara da ka shigo Malam. Ni na gaji da wulakancin da Tahir yake wa kowa a gidan nan a kan matarsa.”

Kawu ya ce, “Dama ba ka da mutunci ko Tahir? Akan matarka kake zagar mini mata haka?”

Tahir ya ce, “Ni fa ba zaginta na yi ba, Kawu. Yarinyar nan ba lafiya gare ta ba. Ya dace a dinga saka ta aikin da ya fi ƙarfinta? Amana ce a guna, dole ne in kare mutuncinta daga dukkan abin da zai cutar da rayuwarta.”

Kawu Tanimu ya ce, “Af, ni ma zagin nawa za ka yi? To zage ni ko ka dake ni, karewar zagi sannan ne na san ka isa, marar mutunci.”

Tahir ya zauna kan kujera, bai kuma magana ba. Dije da Kawu suka kare masa cin mutunci tas a gaban yayansu, yara da manya.

Kawu ya ce kuma tilas ne ya bar matarsa ta ci gaba da ayyukan gida kamar kowace mace, don ba fin matar kowa ta yi a gidan ba.

Har suka gama bala’insu suka fice, Tahir bai motsa ba sai hawaye ke zubo masa.

Rabi’a na ɗaki tana nata kukan. Tabbas zaman gidan ya yi fitina. Ta miƙe ta fito falo, ta zauna kusa da Tahir, ta kamo hannunsa ta ce, “Ka yi haƙuri. Komai na Allah yana da iyaka. Wata rana duk wannan labari zai zama.”

Ya miƙe ya bar ta zaune, don bai son ta ci gaba da ganin hawayansa.

Ɗakin Hajiya Yaya ya shiga. Tana kwance kan gadonta na ƙarfe tana fama da zazzaɓi. Ya zauna kan kujera ya yi tagumi.

Ta miƙe zaune da ƙyar ta ce, “Don an yi maka faɗa kan abin da kake yi kake yin kuka? Shi kenan dai kai ba za a faɗi gaskiya a kan matarka ba?”

Ya marairaice fuska ya ce, “Don Allah Hajiya, kada ki goyi bayan wannan rashin gaskiya. A hannunki na tashi a cikin gidan nan. Mutanen nan babu ƙiyayyar da ba su nuna mini ba. Har Allah ya raya ni, ke ma kin san ba ƙaunata suke ba.”

“Za su ci gaba da yin duk abin da za su yi ne don ganin sun ga bayan zaman lafiyata da kwanciyar hankalina. Shi yasa tun farko ban yi tunanin zama a gidan nan ba, saboda na san abin da zai faru kenan.”

“Ba na tuna kin gaya mini wata magana ya kasance ban yi aiki da ita ba. Shi yasa na zo na zauna. Duk wanda zai samu sassauci a gunsa a gidan nan, bayanki zan bi. Idan ban samu sa’ida ta ɓangarenki ba, a gun wa zan samu?”

“In har kin goyi bayan wulakancin da Kawu da matarsa suka yi mini, na san kin yi haka ne don ke ce kika haife shi, ni kuwa maraya ne. Ba ni da uwa, ba ni da uba, ba ni da mai goya mini baya kan gaskiyata.”

Hankalin Hajiya Yaya ya tashi da jin kalaman bakin Tahir. Ta kama kuka ta ce, “Tahir, yau bakinka ke faɗar waɗannan kalaman marasa daɗi gare ni, abin da ba ka taɓa yi ba.”

Ya ce, “Hajiya, gaskiya dama haka take, ba ta taɓa yi wa wanda ake faɗa wa ita daɗi ba. Ki yi haƙuri. Ko da ba ke kika haife ni ba, ke kika haifi mahaifina.”

Shi ma ya kifa kai a kujera ya shiga kuka.

Hajiya ta ce, “Ka yi haƙuri Tahir. Ni ma na san ba a kyauta maka a gidan nan. Babu yadda zan yi da Tanimu ne, nuna ya fi ƙarfina. Shi da matarsa Dije su ne kan jagorancin duk wani rashin gaskiya da son zuciya da ake yi a gidan nan.”

Ya miƙe ya fice. A ranar baƙin ciki bai bar shi ya ci abinci ba. Rabi’a ta yi lallashin har ta gaji, ta sa masa ido.

Haka aka ci gaba da zaman ba daɗi, kullum cikin ɓacin rai.

Leave a Comment