A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel
Read A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel, an emotional Hausa story filled with suspense, hidden secrets, dangerous plans, betrayal, mystery, and unexpected twists.
“Arne na Kan Tudu.”
Ta zagaya guraren bokaye har biyar duk amsarsu iri daya take kasancewa da bokan da qawarta Mariya ta kai ta gurin shi.
Tana da tabbacin buqatarta za ta biya, tazo inda za a share mata hawaye. Amma bokan yana da sharudda kafin a isa gurinsa. Shi yasa ba ta zuwa gare shi sai ta ga buqatarta ta sha gaban kowane boka da take harka da shi.
Ta san da zarar ta kawo mishi matsalarta yake magance mata. Babu wata buqata tata da ya gaza biya mata.
Strange Conditions
Daya daga cikin sharuddanshi shi ne:
“Za ki daina bin duk addinin da kike kai har na tsawon kwanaki uku kafin ki je gare shi.”
Na biyu kuma tun daga gurin da kika ajiye abin hawanki za ki fara hawa kan tudun da bokan yake zaune.
Tafiya ce ta tsawon awa biyu kafin isa gurin.
Daf da isa gurinshi za ki ga wani dan kamfai rataye a ganyayyaki sai ki dauka ki sanya sannan ki qarasa gurinshi.
The Meeting(A Dalilin Da Namiji Book 3 Complete Hausa Novel)
Kallon ta yake da manyan idanunshi jajaye masu firgita qaramin yaro. Qaton kanshi da yake dore a d’an siririyar wuyarshi yasa ake jin tsoro tun daga kallon farko.
Ihu mai qarfi ya qwalla bayan ya gama kallon qwayar idonta. Busashhen hannunshi mai nuna alamun rashin jini ya buga a qasa yana babbaka dariya.
Nan take hoton kyakkyawar fuskar Aisha ya bayyana.
“Kin zo a kan wannan, kuma kin je gurin mugaye har biyar sannan kika zaiyarce ni, ko ba haka ba?”
Ya tambaye ta cikin tsawa da daga murya yana watsa manyan idanunshi a kanta.
“Haka yake mugu dan muguwa, jikan mugu, tattaba kunnen mugwaye. Wadancan sun kasa saboda rashin qwarewarsu a kan mugunta shi ya sa na zo gare ka shugaban mugwaye.”
Ta amsa cikin daga murya kamar yadda ya yi mata tambayar tare da yi mishi kirarinshi.
A Dangerous Mission
Idanuwanta tsaye suke kyam a kan fuskar Aisha tana murmushin mugunta, domin tana ganin lokaci kadan ya rage mabudi da mukullin rayuwar Aisha ya dawo hannunta.
Ta sha alwashin maida Aishan hanyar samun makudan kudade sannan daga qarshe ta lalata rayuwarta saboda wahalar da ta sha kafin ta samu biyan buqatarta.
Dariya ya qyalqyale da ita cikin wata siririyar murya mara dadi.
“Tabbas za ki samu biyan buqata idan ba ki manta da qa’idojina ba.”
“Ban manta ba mugu dan muguwa, jikan mugu, tattaba kunnen mugwaye.”
“Kamar yadda wadancan suka sanar da ke, yarinyar tana da kariya a jikinta. Idan ba mu samu damar shiga rayuwarta ba, mugu zai dauki ladan aikinsa a jikinki.”
Sai dai ba ta ji tsoro ko kadan ba saboda tana da tabbacin babu abinda zai gagari wannan mutumin a kan al’amarin Aisha.
Hope for Success
Da qwarin gwiwa ta baro gurin bayan ta gama dukkan abubuwan da ake bukata.
Also Read:
A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel
Ba ta damu da mutanen da suke kallonta ba yayin da take komawa cikin motarta.
Tana gama shiga mota ta ja da gudu tana dariya da farin cikin cewa nan da kwanaki biyu buqatarta za ta biya. Saboda haka wannan shi ne abinda wannan littafin ya kunsa ga duk wanda ya ji dadin labarin nan ya aje muna raayinsa a comment section na wannan posting din sannan kuma ya muna sharing domin karfafa muna gwiwa sosai.