Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1



Rudin Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel 50,651 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:                  RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

Free pages are not much, subscribe for ₦300 only.
Contact 07063065680 for more information

                             Page 1

Harabar makaranta ce babba sosai, ɗauke da manyan ajujuwa, da dogayen ƙawatattun benaye, wanda suka sha tiles, a kowane aji yana ɗauke da na'urar sanyaya guri, ko ina ƙal ƙal babu datti ko ƙazanta, kallo ɗaya zaka yiwa ɗaliban dake zirga zirga, da ita kanta makarantar kasan cewa tabbas duk ɗan dake wannan makaranta, ɗan masu ido da kwalline, ko wanda ya tsaya masa ya tara masu gidan rana.

Ɗalibai mata sanye suke da shuɗin skirt me cizawa ga mata, maza kuma wando, se farar riga 'yar ciki me dogon hannu, se kuma 'yar saman kalar skirt ɗin, se ƙaramin farin hijabi ga musulmai mata, saka ƙaramin hijjabin ma ra'ayi ne, babu tilas saka shi ga ɗaliban, da yawa ɗalibai matan skirt ɗin nasu iya gwiwa ne, wasu kuma da kaɗan yafi gwiwar su, da yawansu Uniform ɗin nasu sun matsesu matuƙa, kuma galibin ɗalibai mata suna cire rigar saman kayan su bar ta cikin suna yawansu.

Da yawa masu wannan shigar, za kaga matasan 'yan matane, da suke kan tashen balaga, gasu 'yayan gata, dan haka suna ɗauke da ƙirane me matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haka ɓangaren ƙananan yaran ma da suke firamare, wasunsu kansu ko ɗan kwali babu, kai kace makarantar ƙasashen ƙetare ne, saboda yanayin tsarin makarantar da ɗaliban da ke ciki.

Ɗaliban sunata hada hadarsu, sun fito break, wasu na ciye ciye, wasu wasanni wasu kuma suna hira, ƙararar sautin jiniyane ya karaɗe ilahirin makarantar, wanda hakan ke nuna lokacin komawa aji yayi, domin cigaba da ɗaukar darasi.

Nan ɗaliban suka shiga komawa cikin azuzuwansu, dan cigaba da ɗaukar darasi.

Gaba ɗaya makarantar tayi tsit, an koma aji, dan tuni wasu sun fara ɗaukar darasi ma.

wata tawagar ɗalibai maza da mata ce ta ɓullo harabar makarantar, a ƙalla sun kai su goma, suma sanye da Uniform suna tafe suna hirarsu suna ƙoƙarin bin wata baranda dan komawa ajin su.

Wani malami ne yai musu tsawa da harshen turanci "hey, from where are you? "

Wata zaƙaƙura a cikinsu ta kalli malamin cikin iyayi tace. "we went out for breakfast"

'who gives you the permission to go out? Don't you know that you supposed to be in your classes by now?"

Malamin ya sake maganar cikin tsawa.

Wani ɗan kyakkyawan saurayi ne a cikinsu ya ɓata rai sosai, ya kalli malamin Yace "No need to seek permission from anyone, we have the right to go where ever we want at any time to have our break, we are semifinalist, and the teachers have to wait for us to come back, because our parents pay for it, hope I made myself clear?"

Cikin zafin rai malamin Yace "Are You stupid?, is this the way you supposed to talk to me? Semi finalist ɗin banza, me ka taka a harkar karatu da kake gayamin wai You Are semi finalist"

Matashin ya ɗage kafaɗa alamar oho maka, sannan Yace "it seems that you are New here, anyway this is our policy you have to go and know more about it"

Shewa sauran ɗaliban suka dinga yi suna.  "Weldone The Lion prince, munga yazo da zafinsa yana ji da izza, zamu sauke masa duk wannan zafin kan nasa"

Suka tafi suka bar malamin baki buɗe yana binsu da kallo, a ransa yace 'in dai dagaske haka yaran nan suke, to basu da tarbiyya sam"

Ya juya ya nufi ofishin Director.

Sukuwa ɗaliban ajinsu suka nufa, suna sake koɗa wannan matashin,ya kallesu Yace 'kuje class, ni zan tsaya inga sanyin idaniyata"

Yai maganar cikin sanyin murya, wanda ke tabbatar da abunda yake faɗa har ransa.

Ɗaya daga tawagar ɗaliban ya daki kafaɗarsa yace. "shegen kaya, kai dai ka dage akan yarinyar Nan'

Murmushi yayi, bece komai ba suka wuce aji, shikuma ya nufi wata hanyar.

Window wani aji yaje ya tsaya ta waje, ba malami a Ajin, ɗaliban ajin kowa na abunda yaga ze fishseshi, wasu na hira, wasu na waƙe waƙen su, suna rawa.  can ya hango ta a gefe ɗaya ita kaɗai, ta duƙufa tana ta rubuce rubuce, ta nutsu sosai ta maida hankali akan abunda take yi, fito ya yayi da ƙarfi wanda seda ya janyo hankalin da yawa daga cikin ɗaliban, suka waiwayo.

Da sauri ita ma ta juyo dan ganin wanda yake fiton,  ta ganshi a jikin window yana kallon ta.

Yai mata alama da hannunsa da tazo, mmurmushi tayi, sannan ta miƙe tana nufar hanyar fita daga ajin, cikin takunta na ƙasaita me cike da nutsuwa da kamala, me tafiya da zuciyarsa.

Gaba ɗaya ya ƙura mata ido, gani take duk takun da take tamkar tana girgiza jikinta ne, ta fito tazo inda yake tsaye tace 'good morning'

Seda ya gama ƙare mata kallo sama da ƙasa, sannan ya murmusa ya shafi sumar kansa da ke ta ƙyallin mai yace "Morning my love, baki zo class ɗinmu ba yau, lafiya dai ko?"

Tai murmushi, wanda ya sanya fararen haƙoranta bayyana, ta ɗan rausayar da kanta  tace "lafiya ƙalau classwork nakeyi, shiyasa"

Yai murmushi Yace "kinci Abinci kuwa?'

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ɗan gyara tsayuwarsa yace "Ƙarya kike, naji a jikina bakici komai ba, ga Abinci nan nazo miki da shi, kije ki ci, sannan ki bani classwork ɗin, zanje aji in Miki"

Cikin shagwaɓa tace "what if I was asked, to explain how I did it?"

Yace "You should tell them, that am the one who did it, bana son gaddama, karɓi takeaway ɗin nan, ki ɗakkomin littafin, zanje class ɗinmu in miki ki zauna ki huta"

Tasan halinsa, idan ta cigaba da jayayya ransa ze iya ɓaci, dan haka ta koma class ɗin nasu ta ɗakko masa littafin da take classwork ɗin, ta dawo ina da ta barshi a tsaye ta miƙa masa, ya karɓa ya bata ledar hannunsa, ta karɓa cikin jin kunya tace "Thank you very much"

"Meye wani Thank you kuma? Is my responsibility to take care of you baby, idan na gama zan kawo miki, koma class Ina kallonki, kar wani abu ya taɓa min ke"

Tai murmushi ta juya, yabi bayanta da kallo, seda taje ta zauna yana kallonta ta window, sannan ya juya, ya koma nasu ajin.

"Yallaɓai yaran nan basu da tarbiyya sam, baka ga yadda suke min magana ba ɗazu, duk premises ɗin makarantar nan be isa suyi break ba se sun fita? Kuma su dawo lokacin da suka ga dama, ana kallonsu na musu magana suna nema su zageni"

Director ya gyara zaman Glass ɗin fuskarsa sannan Yace "Naji abunda duk ka faɗa corper Nazir, Amma abunda baka sani ba shine, wannan yaran na ss2 lallaɓasu muke mu rabu lafiya, dan ko na samansu ss3 basa bamu ciwon kan da suke bamu, duk yaran makarantar nan da yawansu yaran manyane, sedai kusan na Ss2 iyayensu manyane sosai masu faɗa aji, taɓa yaran nan tamkar barazana ne ga makarantar nan, shiyasa muke binsu sannu a hankali, hadda 'ya'yan ministoci da kwamishinoni a cikinsu"

"amma Yallaɓai, bafa karatu kawai suke buƙatar a koya musu ba, harda tarbiyya fa, wannan zasu iya baka kunya wataran a gaban wanda bekamata ba, makaranta ba gurin koyon karatu bane kawai, yarane matasa da ake sa ran sune Manyan gibe, yakamata su tashi da tarbiyya"

"Nazir, yaran nan jarine a gareni da makaranta ta, daga 'ya'yan manyan sojoji sena 'yan siyasa, kuma duk competition da aka fita da su se an ciyo shi, ga iyayensu suna sakin kuɗi sosai, mezesa in bari a ɓata musu rai? Kuma duk wata tarbiyya ai ana musu a gidajen su, su sun san yadda suke tarbiyyar yaransu, amma taɓa yaran nan matsala ne babba, kawai ka dinga kau da kanka, kana haɗawa da haƙuri dan ba kowane ubane yake yadda da a horar masa da yaro ba"

Corper Nazir yabi director da kallon mamaki, be sake cewa komai ba ya tashi ya tafi, dan ze shiga Jss2 yanzu.

Shikuwa matashin yaron nan ajinsu ya koma yaje ya duƙufa, yana solving classwork ɗin daya karɓo.

"Prince, waime kake yi ne haka?"

Cewar wani daga ɗaliban, ya ɗago idanunsa ya ɗan kalleshi Yace "Farhan na kewa classwork"

"amma meyasa kake mata? Naga yarinyar dai itama ƙwaruwace a ajinsu fa"

"eh nasani Amin, na kai mata Abinci ne, idan ban karɓa na mata ba, ba zata maida hankali taci Abinci ba"

Al'amin da sukewa laƙabi da Amin yace "gaskiya kana yin yarinyar nan over prince"

"Ƙwarai kuwa, Farhan is my wife to be inshallah"

Kwashewa da dariya Amin yai yace

"How? Yaushe ka gama karatu, kayi jam'ia ka aureta? Jiranka zata tsaya yi, just enjoy your life with her, beauty one's are yet to born, zaka samu wata zazzafar da fita ne ka Aureta"

Prince ya girgiza kai Yace "I have a plan for our feature, dan haka bana wannan lissafin da kake yi, Farhan kawai"

Amin Yace "gaskiya ne mutumina, Allah ya kaimu lokacin, amma dai wannan kamar tayi ƙanƙanta kasamu mace me suna mace mana"

Prince yace "Amin, ka kalli Farhan da kyau, za'ayi babbar mace nan gaba, nidai a haka nake sonta, size ɗinta da komai yai min yadda nake so"

"To Allah ya barku Tare"

"Ameen ya Allah"

Ya duƙufa seda ya kammala mata class work ɗin, kasancewar yana da yawa , yana kammalawa ya miƙe ya tafi ajinsu Farhan, kamar kullum tana zaune a gefe ɗaya, 'yan ajinsu basa wani shiga harkarta kasancewarta ba 'yar masu kuɗi kamarsu ba, saboda ita scholarship ne ta samu, saboda wani competition da taci, aka bata scholarship ɗin, gata suna ganin bata waye ba kamar su, dan haka basa involving ɗinta a sabgarsu, itama bata musu shishshigi kullum tana gefe, ba ruwanta da kowa se karatunta, sekuma Yanzu da Prince ya shigo rayuwarta.

Duk hayaniyar da ake a ajin, Prince na shiga sukayi tsit, dan juniors suna tsoronsa, saboda akwai dealing, baya son raini sam.

Ya ƙarasa seat ɗinta ya zauna a kusa da ita Yace  "Baby gashi na gama miki" yai maganar yana ajiye mata littafin.

Ta sa hannu ta ɗauka tana dubawa, ta ɗago tai murmushi tace "Nagode sosai Prince"

Maimakon ya mata magana, seya kashe mata ido ɗaya.
Sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya.

Yace  "ya kika wani sunkuyar da kai? Ina fatan babu wata matsala dai ko?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Yace "Ai idan ma akwai matsalr bazaki iya faɗa ba, ke naga maganar ma wahala take baki Farhan, nasan maybe yanzu malami ze shigo muku, bari in koma ajinmu, amma kisani zanzo musamman kimin hira, ina son dinga jin muryarki sosai, saboda tana sani nutsuwa"

Ji take kamar ƙasa ta tsage ta nutse dan kunya, gashi ya tsareta da idanunsa, gaba ɗaya nauyinsa take ji.

Corper Nazir ne ya shigo ajin, ɗaliban suka miƙe suna gaisheshi, banda Prince dake zaune, Nazir yabishi da kallo, yana tunanin meya kawo wannan fitsarraren yaron kuma Jss2.

Prince ya miƙe ya kalli Farhan yace
"Mu haɗu in an tashi'
Daga nan ya juya ya fice abunsa.

Corper Nazir Yace  "Ke Farhan, meye haɗinki da wannan yaron mara ɗa'a?"

Farhan ji tayi kamar Nazir ya soketa, Sadik ɗinta ne wai mara ɗa'a.

Shiru tayi ba tace komai ba, "Am talking to you Malama" yai maganar cikin tsawa.

Sunkuyar da kai ta sake yi, jikinta na rawa amma ta kasa furta koda kalma ɗaya.

Daga can gefe wani ɗalibi yace  "sir saurayinta ne"

"Saurayi kamar yaya?"

"Ai duk makarantar nan, babu wanda be san budurwar prince bace, saurayinta ne" cewar ɗalibin.

Aikuwa Cikin faɗa Nazir Yace  "baki da hankali ne? Kina Jss2 harkinsan wani saurayi? Shi iyayenki suka turo ki yi? Kuma ma wannan shegen yaron mara ɗa'a kike kulawa, zakiga saurayi sena zauna da babanki na gaya masa, come out here and kneel down, stupid girl kawai, zaki ɓata rayuwarki kina jss2 amma kin san wani saurayi"

Gaba ɗaya ido ya dawo kan Farhan, ta fito jikinta na rawa, kamar ta nutse tazo gaban class tayi kneel down.

Nazir ya ƙaremata cin mutunci tsaf a gaban 'yan ajinsu, taji zafin abinda malam Nazir ya mata, dan haka nan da nan se ta fara hawaye, wani na bin wani kuka sosai, kamar ƙaramar yarinya.

"Will you shut up your mouth, stupid girl kawai, a haka kamar mutuniyar kirki, kin biyewa wannan sakaran yaron"

Sadik daya koma ajinsu kuwa, ya tarar classmates ɗinsa maza sun haɗa kai suna kallo a waya, matan kuma suma sun ja nasu gurin, suna Magana ƙasaƙasa suna shewa.

Ya ƙarasa ya leƙa abunda su Amin suke kallo, sedai ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, yaja uban tsakiya ja da baya.

Amin ya ɗago ya kalleshi Yace  'babban yaro ya dai, ku matsa masa yazo ayi dashi mana"

Cikin damuwa ya girgiza Kai Yace  "Ni bazan iya kallon wannan shirmen da kuke kallo ba"

Nasir ya kalleshi yace  'ji banza sekace ba namiji ba, wannan ba shirme bane alaji, just come an enjoy"

Sadik ya girgiza Kai Yace  "I can't, kuma Allah ya shiryeku, dan ubanku zaku makance da wuri ne, kawai ku kewaye waya kuna kallon blue Film, shegu zakuyi bayani idan Allah ya tona muku asiri"

Amin Yace  'dan Allah malam ƙara gaba, tunda bazaka kalla ba ai shikenan"

Sadik ya samu kujera yai zamansa ya ɗakko wayarsa, yana Game.

Seniors ne suka shigo class ɗin Ss2, kansu ɗauke da colored ties, mazan kuma huluna alamun prefects ne, wata zaƙaƙura a cikinsu cikin harshen turanci kamar baturiya tace  "who ever knows he spoke vanacular, should come out and pay his 500, before I call names"

Banza sukayi musu, basu ko ɗago kaiba balle su tanka musu.

Nan ta ƙame ta fara kiran sunayen wanda sukayi Hausa, Sadik yana ji aka faɗi sunansa, amma ƙafafunsa na kan benci yana cigaba da game ɗinsa.

Babu sunan kowa a ciki sena Sadik, dama shi duk wata doka a makarantar nan, shine ke fara karyata a makarantar nan.

Ɗaya daga cikin prefects ɗin yace "Sadik, magana fa ake maka"

"Bazan biya ba" ya basu amsa

"You Are still speaking vanacular , you know you must pay' cewar wadda ta kira sunayen.

"Ke wallahi bazan bayar ba, baza'ayi turancin ba, yaren uwatane kona ubana? Ko meye haɗina da wasu turawa da senayi yarensu, har a wani dinga cewa wanda yayi hausa seya biya, baza ai turancin ba, kuma bazan biya ba tunda ba ubankine yake bani kuɗin ba"

Dukan benci tayi ta nuna Sadik tace "don't insult me Sadik"

'idan na zagekin me zakiyi? Jeki gayawa duk uban da zaki gayawa, yarene a makarantar nan se wanda naga dama zanyi, bazan turancin ba, uban turancin, ke uban mungo park da sarauniyar England, ƙaryar banza kawai ba za'ai turancin ba"

Fitina sosai Sadik yaso tayarwa, dan da an ƙyaleshi ze iya dukan yarinyar nan.

Wata ɗalibace ta shigo ajin tana faɗin  "Prince, ga Farhan can an sata kneeldown a rana, tayi wa wannan corper ɗin laifi, kuma wai tayi vanacular ance ta biya kuɗin vanacular tace "bata da kuɗi".

Ashar Sadik yayi Yace  "what! Farhan ɗin?"

Beyi wata wata ba yai waje, hakan yai daidai da shigowar wani malami, da aka sanar masa ana rigima da Prince a ajinsu, ya taho yai maganin abun, sukayi karo da Sadik a hanya, yana masa magana amma yayi masa shiru, ya ture malamin yai hanyar ajinsu Farhan da hanzari.

Baiwar Allah, Farhan tana ƙofar ajinsu tayi kneeldown tana ta zubar da hawaye, ga zafin rana.

Sadik yaji tamkar ya ɗora hannu a kai yai ihu, ya ƙarasa inda take da sauri Yace "waye ya saki wannan abun?"

Kasa magana tayi, se kuka da takeyi beyi wata wata ba, ya jata office ɗin director.

Sadik se huci yake, director ya kalleshi Yace "Prince Sadik, what's wrong? Why is she crying?"

"Sir, ka shiga tsakanin mu da wannan new corper ɗin, why Will he gave her such kind of punishment, and that stupid Tina humilate her because of 500 naira, is she not a human being?"

Director ya kalli Farhan dake ta faman kuka, idonta yayi jawur, shidai yasan Sadik bashi da alaƙa da Farhan,  amma yana gudun ɓacin ran wannan yaron, Yaron fitainanne ne, akwai taurin kai da rashin ji, sedai uwarsa zata iya ɗaure malami akan sa, ana ji da shi a gidansu kamar ɗan gwal, sama baya taɓuwa yarin nan, dan haka Yace "is ok my Boy, zan ɗau matakin daya dace, kayi haƙuri , Farhan kiyi haƙuri kinji"

Farhan dai ba tace komai ba, se kuka da take yi, Sadik yai waje a zuciye tabi bayansa, ya rakata har bakin toilet,yace ta shiga ta wanke fuskarta, ya jirata ta shiga ta fito, ya kalleta Yace
"duk wanda ya kuma saki wani purnishment a makarantar nan, koya miki ba daidai ba kizo ki gayamin kinji ko? Ko "

Ta jinjina masa kai, Yace  "Akwai inda yake miki ciwo ne?"

Cikin muryarta me narkar da zuciya tace  "kaina yana ciwo, da ƙafata"

"shikenan, muje class ɗinmu ki huta in Baki paracetamol"

Ba musu ta bishi, dan bata iya kaucewa umarnin Prince Sadik, ko da wasa bata zaton zata iya kaucewa umarninsa.

Tabbas nickname ɗin nasa na Prince ya dace da shi, saboda gashi Young adult be gaza shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai ba, amma yana jida kansa, giyar arzikin iyayensa da tashen balaga na matuƙar ɗawainiya da shi.

Suka je ajinsu, ya bata paracetamol, ta karɓa ta sha, ta kifa kanta akan benci ta lumshe idanunta.

Babu daɗewa, aka kunna jiniya, alamar lokacin tashi yayi.

Farhan ta tashi, Sadik yaje class ɗinsu Farhan ya ɗakko mata jakarta, suka fito harabar makarantar, inda dandazon motoci suke taruwa, domin ɗaukar yaran gata.

Farhan tace "bani Jakar, zanje in hau napep in tafi gida"

"No ga motar gidanmu nan, muje semu saukeki a gida, kinga baki da lafiya"

A ɗan tsorace tace  "za'ayi min faɗa fa a gida, idan aka ganni a motar ku"

"Karki damu, ba wanda ze miki komai"

Haka yasa ta shiga motar, shima ya shiga, ta gayawa direban inda gidansu yake, suna tafe Sadik yana jera mata sannu, Tare Da yin ƙwafa lokaci zuwa lokaci.

Aka zo bakin layin gidansu Farhan, ta kalli Sadik tace  "Nagode sosai Prince"

"Ki kirani da suna irin na masoya mana, haba my Farhan" yai maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai tata.

Rufe fuskarta tayi cike da jin kunya, yace  "idan baki faɗa ba, zamu yi ta zama a motar nan ne fa" yai maganar yana sake kafeta da idanunsa kamar wani babban saurayi.

"Toni me zance?"  Tai maganar a shagwaɓe.

Kasa magana yay, se ido da yake binta dashi, a hankali yace "koma meye kice kawai my wife"

"Thank you my Love" ta faɗa cike da jin kunya, kamar wadda tai saɓo, kasancewar shine mutum na farko data furtawa kalma me girma haka.

Ya lumshe idanunsa Yace  "ina sonki my Farhan, jeki gida kar ayi miki faɗa, idan aka yi miki faɗa bazanji daɗi ba"

Tai murmushi ta buɗe motar, ta fita har direban zeja motar, Sadik Yace  "tsaya inga ta shiga gida mana"

Direban ya tsaya yana mamakin, wannan taɓara da ƙarfin hali  gami da tsaurin ido na wannan Yaro, ko secondary school be kammala ba, amma yasan ya tsara yarinya ta soshi, itama kuma ta biye masa maimakon ta maida hankali akan karatunta, Koda yake duk RUƊIN ƘURICIYA ke damunsu.

Sadik kuwa bin bayan Farhan yayi da kallo, duk da ta ɗora ƙaton hijjabi akan uniform ɗin nata, seda ya dena hangota sannan Yace  "mu tafi gida"

Direba yaja mota suka nufi gida.

Suna zuwa tangamemen gidan, direban ya kutsa da motar yai parking, Sadik ya buɗe motar ya fito, kai tsaye cikin gidan ya shiga, sakamakon shriye shiryen bikin Yayansu da ake, mutane suna ta shige da fice a gidan nasu.

Yana kallon mutane a falo, amma ya hau bene, ba tare da ya kula kowa ba.

Yayar mahaifiyarsa ce ta hangoshi ta shiga kiran sunansa  "Sadik, kana kallon mutane amma ka wuce baka kula kowa ba?"

"Zan kulaku anjima idan kuka ragu, duk kun cika mana gida"

Be jira me zata ce ba ya ƙara gaba, ɗakin mahaifiyarsa ya shiga, ya tarar da ita tana ɗakko kaya a wardrobe ɗinta, ta dubeshi tace  "sweetheart, ka dawo ya school ɗin?"

Cikin shagwaɓa Yace "Am so much tired , gashi duk an wani zo an cika mana gida da hayaniya"

"Sorry, kasan shirye-shiryen bikin yayanka ake yi, dole mutane suzo amma ko zaka ɗakinka na BQ ka kwanta ka huta?"

Girgiza kai yayi Yace  "No, a ɗakin Daddy zan wanka in kwanta, a kawomin Abincina nan"

Ta shafa sumar kansa tace  "considered it done my auta"

Yace  "Mother dan Allah a miƙomin jallabiyata, idan kin sauka ƙasa"

Ta jinjina masa kai, Sukayi murmushi tare, ta fita daga ɗakin.

Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, ya fito daga shi se gajeren wando ya tsaya a gaban mudubi, yana ƙarewa kansa kallo, Farhan ce ta faɗo masa rai, a hankali ya lumshe idonsa, yana saƙawa da warware abubuwa da dama a ransa.

Buɗe ƙofar ɗakin akayi tare da yin sallama, ya amsa ba tare da waiga ba, saboda yaga me shigowar ta mudubi.

"Sadik manya, ashe ka shigo amma ba labari, ko neman mutane baka yi"

Murmushi yayi Yace "ai ban san kina gidan nan ba, na dawo kawai na tarar an wani cika falon, babu ma hanyar da zanbi in wuce ɗakina, shiyasa kawai na taho nan"

Ta ƙarasa inda yake tsaye, ta ajiye kayan Abincin, sannan ta ɗora masa ash ɗin Jallabiyarsa a kafaɗarsa tace "gashi nan, Mother ce tace in kawo maka, sarkin rashin son Mutane"

Yai murmushi, yana ƙoƙarin zira jallabiyarsa, ta ƙura masa ido sannan tace  "Semi finalist, next year by now insha Allah an kusa grad, kaima ka wuce Dubai"

"Waye yace miki zanyi SS3, this year zan gama makaranta ni"

Tace  "meyasa zaka gama this year? Jumping zakayi kenan?"

Ya juyo ya fuskanceta sosai sannan Yace  'Khairat, jumping zanyi in kammala secondary School this year insha Allah, saboda Aure nakeso, Aure zanyi nan kusa"

Kwashewa Khairat tayi da dariya tace  'look at you, dan kaga kana da girman jiki? Secondary school fa zaka gama, Yaya Usman ma daza'ayi Aurensa Yanzu, seda yayi PHD, wakake tunanin ze maka wani aure yanzu?"

Ƙurawa khairat ido yayi sannan Yace "kina ganin nayi ƙanƙanta inyi auren ne?"

'ƙwarai kuwa, guda nawa kake zakayi zancen wani aure? Better build your future my friend, and stop talking this rubbish"

Tai maganar tana dariya, ta bar ɗakin.

Sadik ya daɗe a tsaye a gurin yana tunani, sannan ya ɗakko sallaya ya tada salla, bayan ya idar yaci Abincinsa ya kwanta.

Farhan ma harta koma gida, ta shirya ta tafi islamiyya, tunanin Sadik ɗinta ne a zuciyarta, tana tuna yadda yake yawan kyautata mata, amma abun tambayar anan shine, zasu iyayin aure kuwa ita da Sadik? Ita dai tana jin ƙaunarsa sosai a cikin ranta.

Se yamma sosai Sadik ya tashi, yai sallar la'asar sannan ya sakko ƙasa, har yanzu gidan da mutane sedai sun ragu ba kamar ɗazu ba, Yayyansa ne maza zaune tare da Yayar mahaifiyarsu, suna shirya atamfofi a cikin akwati, wanda za'a kaiwa Usman na lefe.

Sadik ya nemi guri ya zauna, yana bin kayan da kallo.

Mamansu Khairat ta kalli Sadik tace "dan ƙaniyarka ina maka magana ɗazu, amma kamin banza ko?"

Yai murmushi Yace 'na gajine, kaina na ciwo, gashi kuma an cika falon, shiyasa ban tsaya ba, wai wannan kayan duk na lefen ne?"

Maman Khairat tace  'eh gasu nan, jibi zamuje mu kai masa insha Allah"

Usman Yace "Autan mother Babu ko kara, ko 'yar sarƙa baka siya ka bani ba, a matsayin gudunmuwa"

Sadik Yace  "gaba ɗaya fa siyayyar nan kaɗan ce akayi maka a Nigeria, duk a waje aka yota, kowa yazo baka kuɗi kawai yake kaida Mummy, kuma kace Sena saimaka abu na  baka duk kuɗinka Bross"

Faruk Yace  'ji ɗan rainin hankali yaron nan dan Allah, duk gidan nan babu wanda ake sakarwa kuɗaɗe kamar ka fa"

Usman yace  "wallahi kuwa, yaron nan kuɗine dashi kamar banza a account bema san me zeyi dashi ba"

Sadik ya karkace ya gyara zamansa akan kujera yace  "aini na dena cin kuɗina, nima lefe zan fara tarawa, next year by now za'a kamin nawa lefen"

Maman khairat tace "Usman, dan Allah makemin mara Kunyan yaron nan"

Sadik yace "Nifa Mummy dagaske nake, aure zanyi nima, zamu yi magana da Daddy idan ya dawo gari, nifa banƙi a haɗa bikina dana Yaya Usman ba"

Umar ne ya kai masa duka Yace "yi mana shiru dan ubanka, mara kunya kawai, ubanwa ze maka auren? Ko dan kana ganinka ƙato haka? Better concentrate on your study, shikansa Bross Usy seda ya haɗa PHD ze aure balle Kai, da yanzu Balagar ta zo maka "

Harar Usman Sadik yayi Yace  "meye wani PHD?  Aure ze hanani karatune? Ai da sauƙi tunda balagara ta zo, Zan baku mamaki kwanan nan.

Ya miƙe yana zumɓura baki ya bar falon.

Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

                            Page2

Sadik na fita harabar gida, ya tarar abokansa sunzo wai zasu snuka, ya bisu suka fice dan yaje ya sarara.

Corper Nazir kuwa ya sha faɗa a gurin director, saboda ƙararsa da Sadik ya kai, ya dinga mamakin wannan lamari, shikenan dan yaran masu kuɗine baza'a basu tarbiyya ba? Yara duk ba ɗa'a? Ai makaranta ba iya gurin koyon karatu bane, hadda tarbiyya shikenan se a zuba musu ido su lalace, baza'a tsawatar musu ba dan kar iyayensu suji haushi?

Abun ya dameshi sosai, Tare da ganin rashin ma'anar wannan lamari akwai buƙatar a duba, idan bahaka ba rayuwar yaran zata ɓaci a banza.

Da wannan damuwar ya koma gidan daya kama, da yake ba'a camp yake a zaune ba, gida ya kama yake zaune a ciki.

Washegari ya shirya Domin zuwa makaranta, kamar kullum anyi assembly an gama, Farhan nata rarraba ido taga ta ina zata hango Sadik, sedai bata samu ganin nasa ba, ta duba inda yake tsayawa amma baya nan, duk setaji ta damu, haka aka sallamesu suka tafi azuzuwansu.

Sadik kam yau makara yayi sosai, corper Nazir yana harabar makarantar a tsaye yana zazzagawa, dan tabbatar da komai ya tafi daidai.

Motar gidansu Sadik ce ta kunno kai cikin makarantar, har Corper Nazir ze shiga cikin makaranta, yaga zuwan Sadik, dan haka ya tsaya.

Sadik ya fito daga mota, ya rufe motar ya saɓa jakarsa, ze shiga cikin makarantar.

Cikin shouting corper Nazir yace "hey come here'

Sadik ya juyo ya kalleshi, sama da ƙasa kamar kar yaje, sukuma yaje kiran, yana wani bossy walking yaje inda Nazir yake tsaye, Nazir ya kalleshi yace  "why are you just coming?"

Sadik ya kalleshi ya ɗauke kai.

"Check your watch, what's the time now?"

Sadik ya ɗauke kai kamar ba dashi ake magana ba, principal ne ya taho inda suke tsaye, yana faɗin"what's going on here?"

Nazir Yace  'Sir, wai Babu wani penalty na makara kowani laifi, idan yaran nan sun karya doka? Kalli lokacin da yazo makaranta, kuma na yiwa director magana akan haka amma ya nuna min is like you don't punish them"

Principal ya kalli Sadik yace  Yace  "Sadik, why are you late? Baka san lokacin da Yakamata kazo school bane?"

Tura baki Sadik ya shiga yi, yana hararar Nazir.

PC yace  "idan ka sake makara, sena baka punishment me wahala, ɗau jakarka ka bar gurin nan kafin in ci mutuncin ka"

Sadik ya ɗau jakarsa fuuu yai cikin makarantar, yana tunanin yadda ze koyawa Nazir hankali.

Principal ya kalli Nazir yace  "ka manta da director, duk abunda yakama na hukunci a hukuntasu, shi yana la'akari da yadda ze samu kuɗine kawai, shiyasa baya goyon bayan hukuntasu, kuma wasu daga yaran iyayensu nada kuɗi yanzun nan se su ɗaureka, amma dan dai punishment wanda zasu iya, in sunyi laifi kar a saurara musu"

Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin yaran.

Koda Sadik yaje ajinsu da malami a ciki Yana lesson, amma babu neman izinin shiga ko makamancin haka, ya kunna kai cikin ajin nasu, yaje gurin zamansa ya zauna, Tare da ajiye jakarsa, fuskar nan tasa a ɗaure yana ta jan tsaki.
Duk ajin suka waigo suna kallonsa, daga bisani malamin ya cigaba da Koyarwarsa.

Sadik be saurari me Malamin ke koyarwa ba, ya kifa kansa akan benci, zuciyarsa cike da jin haushn irin yadda Nazir ke zaƙewa da son cusawa hukumar makaranta wani ra'ayi na daban akansu, dole yayi maganin Nazir.

Malamin na fita su Amin suka zo inda Sadik yake, Nasir Yace"babban yaro ya dai? Meyafaru ne mun ganka Wani iri"

Sadik yayi tsaki Yace  "dan Allah ku rabu dani"

Amin yace "haba Sadik, Ya hakane? Mun tambayeka meyafaru kana wani cin magani"

Banza Sadik yayi musu, suka gama surutunsu 'yan matan class ɗin ma sukazo kan Sadik suna nasu surutun

"Babban yaro waye ya taɓo mana kaine?"

Kamar da Dutse suke Magana, yai musu shiru ƙarshe se haƙura suka yi suka ƙyaleshi.

Farhan kuwa gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, ta kasa samun kwanciyar hankali saboda rashin ganin Sadik, ɗalibai kowa yana harkokinsa amma banda Farhan.

Ganin da tayi zaman baze fishsheta ba, yasa ta miƙe ta nufi hanyar ajinsu Sadik.

Tana zuwa gaba ɗaya ta kasa shiga, ta tsaya a waje tana leƙa ajin, ba zata iya shiga ajin ba, saboda na Seniors ɗintane, gashi bata san kowa a ajinba se Sadik, dan haka tana jin nauyi sosai.

Ta window ta tsaya, tana leƙawa dan taga ko zata hango Sadik ɗinta.

"What are you doing here?" Da sauri ta waiga dan ganin me Maganar, Nasir ne abokin Sadik, ya kalleta yace "ko kina Neman Sadik ne?"

Farhan ta ɗan sunkuyar da kai, cike da jin kunya.

Nasir ya ɗan tsaya yana ƙare mata kallo, da jinjinawa mugun jin kunya na Farhan, se dai babu mamaki irin wannan halayyar ga 'ya'yan talakawa, sam basu da wayewa.

Yace "to ki shiga mana, yana ciki ai"

Kamar wadda aka yiwa dole, ta shiga ajin can ta hango Sadik, zaune ya kifa kansa, gabanta ne ya faɗi tai tunanin ko bashi da lafiya ne?

Da ɗan hanzari ta ƙarasa bencin da yake zaune.
Jin mutum a kusa da shi ne yasa ya ɗago da sauri dan yiwa wanda yazo kusa da shi ɗin masifa, sedai kuma yayi tozali da fuskar Farhan.
Ajiyar zuciya ya sauke, bece komai ba.

A hankali tace "baka da lafiya ne?"

"No Farhan, lafiyata ƙalau"

"Amma ban ganka a gurin assembly ba?"

"Nazo a makare ne, kuma wancan corper ɗin ya ɓatamin rai, sena gyara masa zama tukuna"

Farhan tace "me yayi maka?"

"Yana min shishshigine, dan yana saka wannan koɗaɗɗun uniform ɗin na NYSC, idan be kiyayeni ba zan koya masa hankali"

Farhan tace  "kasan meyasa ya sani punishment jiya?"

Sadik ys girgiza mata kai, tace  "wai saboda kaje gurina, ya tambayeni meke tsakanina da kai, shine 'yan ajinmu suka faɗa masa, shine yaita min faɗa ya sani kneeldown"

Sadik ya daki benci yace "har akwai wani sakaran daze sawa soyayya ta ido a makarantar Nan? Wallahi idan mutumin nan be kiyayeni ba sena sa an karairayamin shi"  yai maganar a harzuƙe wanda seda hankalin 'yan ajin ya dawo kansu.

Aminu Yace  "wai kai Sadik meke damunka ne?"

"Wannan Nazirun ne, da gemu kamar soson wanka wallahi ya cigaba da shiga sabgata kota Farhan wallahi sena masa illa"

Farhan ta kwantar da murya tace  "dan Allah kayi haƙuri, dana sani ban gaya maka ba"

Wata cikin 'yan class ɗinsu Sadik me suna Amina amma suna cemata meenal ta taɓo ƙawarta tace  "Taslim, kina ganin wani abu kuwa, wannan budurwar Sadik ɗin akwai iya barikanci, kalleta saliha kuma yarinya amma ta dabaibaye zuciyar ɗan mutane ji yadda take masa magana"

Taslim tace "ke dai Bari, kina gani Tun ɗazu muke tambayarsa meya dameshi, yai banza damu amma tana zuwa ya ɗago kansa, na rasa meya ja ra'ayin Sadik akan yarinyar nan, kaf class ɗin nan Sadik bashi da budurwa,  ya rasa a inda zeyi budurwa se a Jss2, duk wannan iyayin nasa.

Meenal tace  "lallai ma ke ɗin nan, Sadik wayone da shi ya samo yarinya fresh, wadda bata san komai ba ya koya mata sonsa, zeyi tattalin kayarsa kuma ki ƙare mata kallo, yarinya ce amma me ƙirar manya, tana da zubin halitta me jan hankali sosai"

Suka cigaba da gulmarsu a gefe, Sadik kam se banbami yake akan Corper Nazir, Farhan tace  "ni ka dena wannan faɗan ko in tafi"

"Farhan ya bazanyi faɗa ba, yana nema ya kassaramin soyayya, ina ruwansa damu?"

Nasir Yace "Sorry Prince, ai komu ba zamu bari a kassara wannan soyayyar ba, wadda muke saka rana ta shiga kundin tarihi kamar ta su Laila majnun"

Kamar Farhan za tayi kuka tace"dana sani ban gaya maka ba, nace fa kayi haƙuri"

Sadik yai shiru yana cigaba da huci, Farhan tace  "kayi haƙuri mana, dan Allah ka dena fushi Kaji, ka ga malamnmu ne, koba komai ya koyar damu, ka dena zaginsa"

Sadik Yace "ke dalla ƙyaleni, na tsani mutumin nan wallahi"

Miƙewa Farhan tayi zata tafi, jin yadda yayi mata magana a tsawace, ya riƙo hannunta da sauri, wanda hakan ya haddasawa Farhan mummunar faɗuwar gaba, taga kamar kowa suyake kallo.

Tace "ka dena taɓani, meye haka?.

Sadik yace "am sorry, na dena amma dan Allah kiyi haƙuri, zauna"

Farhan ta nemi Guri ta zauna, yace "kiyi haƙuri bazan sake ba insha Allah"

Ta zauna tana ɗan tura baki, taƙi kulashi, ya sake kashe murya yace "haba na face kiyi haƙuri"

Tai murmushi tace  "Na haƙura ai"

Suka cigaba da hira ita da Sadik, yama  manta da maganar wani Nazir.

Har aka koma class Farhan bata sani ba, tana zaune tana hira da Sadik cike da nishaɗi, duk da mafi yawan hirar shi yake mata, ita murmushinta yafi yawa akan magana.

"Ke Farhan!" Sukaji muryar Sir Nazir.

A rikice Farhan ta waiga, dan ji tai an kira sunan nata tamakar saukar Aradu, Kamar yadda ta zata sir Nazir ne ba wani ba.

"What are you doing here? Is this your class?" Ya tambayeta yana zazzaro ido.

Cikin tsoro Farhan ta girgiza kai, alamar a'a  yayinda attention ɗin class gaba ɗaya ya dawo kansu, kowa ya zubo ido.

"Me kikeyi a kusa da namiji a zaune? Ajin ku ne nan? Tashi ki bar ajin nan ki koma ajinku"

Sadik ya fusata ze yi magana, Farhan ta girgiza masa kai, ta tashi da sauri ta fita, Sadik ya tsaya yana kallon kallo da Nazir.

Naziru yai ƙwafa ya fice, yana fita Sadik ya daki benci yana muzurai, Nasir Yace  "easy Prince, kayi haƙuri"

"Mutumin nan yana wuce gona da iri fa, zanyi masa kaca kaca a makarantar nan wallahi"

"Kayi haƙuri, zamu san matakin da zamu ɗauka a kai"

Farhan kam da Kusan gudu ta ƙarasa ajinsu, ai kuwa Nazir ya rufa mata baya, a gaban 'yan ajin ya shiga zazzaga mata bala'i.

"Ke wace irin yarinya ce ne? Abunda kike kin kyautawa kanki ko iyayenki? Gurin wannan ɗan iskan yaron aka turoki? Me kike zuwa gurinsa yi?" Yai maganar yana tsatstsareta da ido.

Farhan ta girgiza masa kai, alamar ba komai.

"Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba sena haɗa miki assembly, kuma in kira mahaifinki in gaya masa abunda kike aikatawa, gara tun wuri ki fita harkar wannan ɗan iskan yaron, tun be lalata Rayuwar ki ba"

Farhan tana jin zafin cin mutuncin da Nazir yake mata, sedai jinsa kawai take dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik,sum sum taje ta zauna a gurin zamanta tana sunkuyar da kai, Nazir na cigaba da zazzaga Mata cin mutunci.

"Irinku ne masu komawa iyayensu da ciki ,ku lalace tunda ƙuruciyarku, saboda RUƊIN ƘURUCIYA na ɗibarku, sun turo ki kiyi karatu amma kina biyewa 'yan iska, a haka gaki kamar saliha amma baki da hankali, in sake ganin kinje inda yake, sena zaneki a makarantar nan"

Farhan tai shiru, ta sunkuyar da Kai tana jin yadda maganganun nasa ke mata dirar mikiya a ƙirjinta, taji zafin yadda yake cin mutuncin ta a gaban 'yan ajinsu, dan seda tayi kuka, sedai sam maganganun nasa basuyi tasiri a zuciyarta ba, dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik, tun da ita dai bata ga aibun Sadik ba, a barshii da zafin rai dai wasu lokutan da rashin son raini, amma yana da sauƙin kai sosai, sedai ta yanke shawarar zata yi duk me yuwuwa ta nesanta kanta da Sadik ko dan kaucewa cin mutuncin Sir Nazir da dizginsa da kuma gudun kar ya haɗa ta da mahaifinta, dan a duniya tana tsoron Allah, tana tsoron mahaifinta sosai.

Nazir ya gama faɗansa san ransa sannan ya shiga gabatar da lesson ɗinsa.

Har ya gama karatunsa Farhan kuka take yi, dan sam na ta fahimci komai ba har yai ya gama.

Bayan ya fita wata daga cikin'yan ajinsu wadda ake cewa Lilly tazo ta dafa kafaɗar Farhan, Farhan ta ɗago kanta ta kalli Lilly.

"Ki dena kuka ki rabu da wannan ɗan rainin hankalin kinji, ki dena kuka"

Farhan ta jinjina mata kai alamar to.

Koda aka tashi daga school, Farhan bata jira kowa ba ta silale ta tafi gida, Sadik yaita nemanta be ganta ba, haka ya haƙura ya tafi gida, yana mamakin yadda aka yi ta tafi basu haɗuba.

**********

Gudu gudu sauri-sauri haka ta faɗo makeken tsakar gidan, hannunta ɗauke da jakar makaranta, tana zuwa ba tayi wata wata ba, tai jifa da jakar a tsakar gida, ta faɗa banɗaki.
Dattijiwar dake zaune tana mulmula fura, ta kalli jakar makarantar da yarinyar ta jefar a tsakar gida, ta girgiza kai ta cigaba da aikinta, kusan mintuna biyar sannan ta fito daga banɗakin, ta tsaya a tsakar gida ta shafa cikinta tace  "wayyo Allah, fitsari idan ya matseka ba arziki, ina tafe a hanya kamar zanyi hauka, saboda yadda ya matseni"

Dattijuwar ta kalleta tace "zaki zo ki ɗauke wannan jakar da kikayi jifa da ita a tsakar gida, ko kuwa se nayi yaƙi da bakina"

Ɗan tura baki tayi, taje ta ɗauke jakar Tata, ta kai cikin  ɗaki ta ajiye, ta cire duk kayan jikinata, ya rage daga ita se dogon wandon makarantar ta, ta fito tsakar gida tana faɗin "Innarmu, wai yau me aka dafa ne?"

Inna ta ɗago zata yi magana, amma taci karo da yadda yarinyar ta fito tsakar gida.

"Nana waike wace irin sha3 ce ne haka? Kalli fa a yadda kika fito, kowane lokaci za'a iyayin sallama a shigo gidan nan, amma kika fito tsakar gida a haka"

Ummi ta ya mutsa fuska ta kalli kanta tace "to ni innarmu me nayi?"

"Dan ubanki baki san kin fara girma bane? Dubi ƙirjinki kin fara ƙigar dangi, amma kin fito a haka bako Kunya, ko 'yar shimi ba ki saka ba"

"Meye kuma ƙirgar dangi?" Ummi ta tambaya cike da wauta.

Inna tace "kin wuce kin nemi riga kin saka, ko sena taso na iskoki a gurin nan, gaɓuwa kawai ba kya ganin yadda ƙirjinki ya tasa? Amma kike yawo a haka? Karki adana su ki bari su fito a wulaƙance, naga alamar idan banyi dagaske ba, haka zakiyi budurci ba kintsi, 'yar butar uwa da kai kamar gwai gwai"

Ummi ta faɗa ɗaki, tana kumbura baki, dan bata son wannan faɗace faɗacen na Inna, Gashi idan ta tashi yi bata rufe komai, haka za tai ta sakin bayani, ko a gaban waye kuwa haka za tai ta sakin zance da sunan faɗa.

"Sarkin faɗa, ke da waye kuma da tsakar ranar nan kike faɗa haka?"

Cewar dattijon da yake shigowa, jikinsa sanye da Alkyabba.

"Dawa zanyi faɗa banda wannan yarinyar, duk gidan nan wake sani magana banda Nana, yarinya kamar ba'ace mata bari, taɓara da iya shege sinƙi sinƙi a cikinta"

Dattijon yai murmushi Yace "haba ke kuwa, takwarar taki guda, Ki dinga haƙuri da ita, yarinyace har yanzu ke kike ganin girmanta, amma yarinya ce ƙarama"

'ko da yarinta, harda iskancinta wani lokacin, bata taɓa jin daɗi idan bata sani magana ba"

Yai murmushi Yace  "to yanzu dai ba wannan ba, zuwa wani satin insha Allah, gidan Abdullahi  zasu kawo lefen Usman ɗin, ina fatan kina nan kina shiri?"

Inna tace "eh ina shiri, naji yace bikin bada tsawo za'a saka ba, ina ga idan suka kawo Kayan, zan bisu se kuma anyi biki, dan bana son yawan tafiyar motar nan"

But Nana dta fito daga ɗaki da ɗaurin ƙirji tace "Alhaji wai waye zeyi aure ne? Wai su wannan ɗin nan na birni?, wanda basa dariya sosai masu tara gashin nan kamar ƙabilu? 'ya'yan kawun nan?".

Dattijon Ya buɗe baki Yace "yayyen naki ne baki san sunansu ba? Se masu tara gashi?"

"Ni a ina zan san sunansu, bayan ba kula mutane suke ba, kuma ma ba zuwa gidan nan suke ba"

Alhaji ya jinjina kai Yace  "ikon Allah, lallai wannan abu bemin daɗi ba, Dole a tafi da Nana, kuyi kwanakin Tare, dan ta ga 'yan uwanta sosai"

Ummi tai tsalle tana faɗin "yee, zani birni inje asha bikin 'yan gayu dani"

Inna tai tsaki tace "mara hankali, ai idan kikaje ma kallon kwantacciya zasu yi miki, musamman matar Abdullahi, me wa mutane kallon banza"

Alhaji Yace "ai haka nan za'aje da Ita, rashin zumuncin yayi yawa, ace ba tama san sunayen su ba, shikenan ace yaran nan ko garin nan basa zuwa, balle su shaƙu da 'yar uwassu?"

Inna tace  "to ya zamuyi tunda uwarsu bata so? Nace a kai maka furar turakarka ne idan an dama?".

"Eh, a kawomin turaka, ina so idan na sha na ɗan huta, zanyi baƙi da yamma"

Inna tace "to shikenan, Allah ya baka yawan rai, zan kawo insha Allah"

Ya nufi hanyar ɗakinsa, Inna ta tashi, ta wanke hannunta, ta shiga ɗaki, ta tarar da Nana da ɗaurin ƙirji tana shirin Dutse"

"Nana kinyi salla kuwa?"

"Inna ai da sauran lokaci fa"

"To kuma kafin kiyi wanka, ba lokaci yayi ba?"

Nana ta zumɓura baki tace  "wai Inna ba nayi wankan nan da safe ba? Shikenan ni kullum cikin wanka kamar wata tarwaɗa?".

Inna tace "kyaci ubanki, lokaci na nan zuwa da za kiyi medalili, wanka ba wataran da asubar fari, koman sanyi haka zakiyi shi"

"Wankan?" Nana ta tambaya cike da mamaki.

Inna tace  "ƙwarai kuwa wankan da ki ke gudu, kuma dole ki koyi wanka da tsafta tun Yanzu kina gida, gaba nake jiye miki, kuma Yanzu ki ke girma kina kan tashen balaga, warin jikinki daban ze dinga fita, kuma duk wanda ki ka bari yaji wari a jikinki kin faɗo, ze dena ganin mutuncin ki, kuma dan ubanki na sake ganinki da ɗaurin ƙirji Sena makeki, idan baki alkinta abubuwan nan ba haka zasu fito ba tsari, kiyi 'yan matanci amma nono a zube, kizo kiyi aure ba zasu dinga birge miji ba"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, waike Innarmu kiyi ta faɗan magana ba kyajin kunya"

Inna tace  "Naƙi inji kunyar, idan ban gayamiki ba wani a waje zan jira ya gaya miki?, kin tashi kin tafi wankan ko sena zo inda kike? Na watsar da ke"

Nana ta tashi tana bubbuga ƙafa, da takaicin yadda Inna ke sata wanka ba gaura ba Dalili, ta ɗebi ruwa ta tafi banɗaki.

Bayan shigar Nana banɗaki, Inna tace "A kula idan za'ayi wanka, a wanke hammata da kyau, wuya da duk wani lingu....

'innalillahi Inna na haddace wallahi, na haddace ko karatune wannan na iya ke kullum sekin nanata min yadda ake wanka wai?"

'rufemin baki, gara in nanata miki ai, dan banƙi in zuba ruwa in wankeki da kaina ba,wani warin jikin yana faruwa ne daga rashin iya wanka tun a ƙuruciya, in kin gama wankan ga ruwan alumun nan da miski ki shafe jikinki dashi"

Nana ta yiwa Inna banza, dan wannan karatuttukan na Inna basa ƙarewa.

Inna ta damawa Hakimi furarsa, ta shiga kai masa, ta tarar dashi yana dariya, ta kalleshi tace  "lafiya naga kana dariya?"

Yai murmushi yace  "dariya nake miki keda jikar taki, kina takura yarinyar nan da yawa fa"

Inna tace  "a'a ba takura bace, gara in gaya mata ai, duk da Allah be taɓa bani 'ya mace ba, amma ni ban yadda se an sawa yarinya rana, sannan a dinga gaya mata ƙabali da ba'adi ba, tun tasowar yarinya ya kamata a dinga koya mata yadda zata kula da kanta, da yanayin Rayuwar Aure"

Hakimi yai murmushi yace "eh to hakane, amma ai Nana tayi ƙarama da yawa, da wannan karatuttukan naki"

"Taɓɗijan, kai kake ganin tayi ƙanƙanta, ba tayi ƙanƙanta ba, ba dan karatun boko ba, ai da yanzu idan ba'ayi aurenta ba, ana nan ana shirin hakan, kuma karkayi mamaki suna tattaunawa a junansu, yaran zamani ka kallesu kawai, gara in horata da nawa karatun, da wanda za'a karanta mata a waje ta ɗauka"

Hakimi ya jinjina kai yace "hakane kam, naga zasu yi hutun makaranta, shiyasa nace ki tafi da Ita bikin nan, wallahi ina jin banƙin cikin rashin raɓata da jikokina basa yi"

"Ka dena damun kanka fa, ita uwar yaran nata halin kenan, yaranta baza suzo ƙauye ba, dan haka ka haƙura ka bar mata yaranta, shi shine ɗanmu kuma yans zuwa inda muke, meye na damuwa dan yaransa basa zuwa?, Baga Ummi nan Allah ya baka ba"

Ya ɗanyi shiru Yace  "na tabatta da baban Ummi na raye ba yadda ze hana yaransa zuwa inda muke, kin sanni da ƙawa zucin yara, Allah be bani su da yawa ba, duk ya karɓe abunsa, ina ƙaunar yaran nan, irin son da nakewa mahaifinsu, haka nake sansu"

Inna tace "ni dai nace kayi haƙuri, ka maida komai ba komai ba, Ummin nan kawai in Allah ya bamu yawan rai, seka ga ta haysyyafa, ta cika mana gida da jikoki"

Hakimi ya jinjina kai Yace "wai, idan ba wani ikon Allah ba, ina ni ina ganin 'ya'yan Ummi, 'ya'yan jika fa?"

"Eh mana 'ya'yan jikan, ai abun na Allah ne, kai dai Allah ya baka tsawon kwana me amfani Saraki"

Yai murnushi, yana jin daɗin yadda matar tasa take masa addu'a, ko kuma yi masa kirari.

Inna na nan zaune tare da megari, seda ya kammala shan furarsa, ya kwanta sannan ta fito daga turakarsa, tana zuwa ɗaki ta tarar da mutuniyar tata, tana cin Abincin rana.

"Yawwa ta Nana, gaki nan fes dake se ƙamshi kike, haka ake son mace a ganki kullum cikin gyara, ga kayanki can na islamiyya an goge miki, idan kin gama seki shirya ki tafi Makaranta"

Nana tace 'to Hajiya Inna"

Shirye shirye suna ta nisa, na bikin Usman, Sadik ma yana ta nasa shirin, dan yana son ya gwangwaje da bikin nan, zasu yi shagali sosai shida friend's ɗinsa.
Yauma yaje school sedai har ya shiga aji be samu ganin abar ƙaunarsa ba, ana fitowa break ya tafi ajinsu Farhan, sedai ya tarar bata nan.

Cikin takunsa na isa ya shiga cikin ajin, ya kallesu Yace "ina Farhan?"

Lilly tace  "Ana fita break ta fita, bamu san inda ta tafi ba"

Be kuma cewa komai ba ya fita, yana tunanin ina ta shiga haka? Tun jiya be sake ganinta ba.

Ita kuwa bayan wani aji taje tai zamanta, dan karma su haɗu Sir Nazir yai mata faɗa, koya kira babanta, sedai sam itama zuciyarta a takure take, tana son ganin Sadik ɗin nata.

Sadik yana zaune yayi shiru, Meenal ce ta zauna a kusa da shi, Tare da ɗan dukan cinyarsa tace  "Babban yaro, what's wrong ne? Ka wani yi shiru"

Cikin damuwa ya ɗan lumshe idonsa ya buɗesu, sannan Yace  "Farhan na nema na rasa, naje har ajinsu bata nan, kuma ita bata zo nan ba"

"Shine ka zauna kai wannan shirun haka? Lallai yarinyar nan ta kama zuciyarka fiye da yadda kake tunani"

Yai murmushi Yace  "ke dai bari kawai, yarinyar ta musamman ce, komai nata abun burgewa ne, I can't do without her"

Meenal tace  "Ranar daka bar makarantar fa?"

"Zan bita har gida mana"

"Hmm Sadik manya, banda abun so dai, banga me ka gani a jikin wannan Farhan ɗin ba, ita gata bata wani cika mace ba"

Sadik yai murnushi sannan Yace  "Ni idona sun gane min abunda naku idon baya iya gani, ku kuke ganinta ƙarama, amma ni nasan me nake gani"

Yai maganar yana lumshe idanunsa.

Meenal ta kalleshi tace   "Allah me iko, kaga ni dai dan Allah yi mana ordern Abinci, yunwa nake ji wallahi"

Sadik ya zaro wayarsa yana faɗin "bari inyi, kuma fa nima yunwar nan nakeji, amma banga zuciyata ba, ban sani ba itama taci ko bata ciba, ba zan iya ci ba"

"Can ta nannaɗe muku kai da ita, ni dai dan Allah yi mana"

Seda aka kunna jiniya, kowa ya koma aji, Sannan Farhan ta fito daga inda ta ɓuya zata koma aji, zuciyarta nata raya mata taje ajinsu Sadik ta ganshi, amma ta danne zuciyarta ta tafi ajinsu.

A bayan wani aji ta hango wani malami, yana kissing ɗin Tasleem ta ajinsu Sadik, nan da nan mamaki ya cikata jikinta ya ɗau rawa, abun ya bata mamaki sosai, Malami da kansa yake haka shi da ɗalibarsa, ta shiga ajinsu cike da tunanin abunda ta gani.

Ta zauna a gurin zamanta tana tunani, Lilly tace  'Farhan, ina kika shiga ne? Prince Sadik yazo nemanki fa'

Maimakon ta bata amsa se dai murmushi kawai da tayi Mata.

Koda aka tashi, cikin gaggawa Farhan ta ɗauki jakarta, dan ta gudu gida kafin Su haɗu da Sadik, sedai tana fita harabar makarantar tai karo dashi.
Mazewa tayi niyyar yi ta fece, aikuwa ya riƙo hannunta cikin hanzari ya kalleta Yace
"meye hakane Farhan? Kamar kina guduna ne 'yan kwanakin nan lafiya kuwa?"

Farhan ta ɗan haɗe rai cikin shagwaɓa tace  "Nika cikani meye haka?"

Sakin hannuta yayi, tare da shan gabanta  Yace  "tun jiya fa nake nemanki ban ganki ba, ko laifi nayi miki ne?"

"Ni ba abunda kayi min, kawai ka dena bina".

"Wace irin magana ce wannan haka?"

"Ka dena bina ko zuwa inda nake kawai, Sir Nazir yace ya kuma ganinmu tare ze kira babana"

Nan da nan annurin Fuskar Sadik ya ɗauke, ya canza fuska jikinsa har rawa yake ya kalli Farhan Yace  "dama shine dalilin da yasa kike guduna? Waye Nazir? Me akai akayi shi? Farhan wai so ƙaryane? Zaki fara wahal dani dan ina sonki? Ina ruwansa damu, meye nasa a cikin soyayyar mu, idan sonki yake ya fito Ya faɗa mana in bar masa ke, kuje kuyi dashi, nafi ƙarfin Wulaƙanci Farhan, karki sa zuciyata ta yanke hukuncin da zesa mu cikin dana sani nida ke".
Nan da nan ido ya dawo kansu, babban abinda bata so kenan, wannan saurin zuciyar da zafin rai na Sadik, gashi ta kasa Magana, ga idon mutane da yai yawa a kansu.

"Shikenan, tunda kin fifita decision ɗinsa aka abinda zukatanmu ke so, kije Nagode sosai da kika bari zuciyata tai zurfi a sonki, na sakankance kema kina sona, ashe nayi kuskure"

Tasleem dake gefe tace  "shege Prince, akwai kalamai dole ya sace zuciyar yarinya ƙarama"

Ganin yadda ransa ya ɓaci sosai, yasa Farhan sake dirircewa,  cikin muryarta me sanyi tace  "Ss..Sadik. wallahi"

"Karki gayamin komai malama, kije na bar masa ke, ya kwaɗaki ya cinye"

Fuuuu yai gaba, bebi ta kan jakarsa daya baro a aji ba, ya nufi inda motarsu take ya haye.

Farhan kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu, dan a duniya bata son ɓatawa Sadik rai, dukda bata ta taɓa ɓata masa rai ba, amma taji ba daɗi yadda ransa ya ɓaci haka.

"That's good, na gaya miki muddin na kuma ganinki da yaron nan, sena gayawa mahaifinki, wannan yaron dai ba aurenki zeba, ze ɓata miki lokacine kawai da rayuwa".......

Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                            Page 3&4

Waiga wa Farhan tayi ta kalli Sir Nazir, dake tsaye yana mata Magana, ji tayi tamkar ta shaƙeshi, saboda shine silar da yasa ta janye wa Sadik, kuma ga abunda tai yasa ran Sadik ɗin ya ɓaci.

Abunda be taɓa zato ba, yaga Farhan ta galla masa harara, irin up anda down ɗin nan, tai gaba abunta, tsayawa yayi cak ya zuba mata ido harta ƙulewa ganinsa.

Sadik kam a ɗakinsa na BQ ya tsaya, yana zuwa ya cire belt ɗinsa yai jifa dashi, ya cire neck tie ɗin wuyansa na makaranta ya jefar, ya cire rigar itama yai jifa da ita, ya faɗa kan gadonsa yai ruf da ciki, zuciyarsa na wani irin zugi, dan gaba ɗaya idonsa ya rufe, wata irin muguwar tsanar Nazir yaji tana ratsa shi, gefe guda yana ganin laifin Farhan da ta biyewa Nazir ɗin.

Befi mintuna sha biyar da kwanciyar tasa ba, Yayansa Faruk ya shigo ɗakin Sadik, ya kalli Sadik yace  "Kai, Lafiya kuwa? Meke damunka kalli yadda kayi watsi da kayan makarantar taka fa, koba lafiya ne?"

"Lafiya ta ƙalau" ya bawa Faruk amsa a taƙaice.

'ban yarda lafiyar ka ƙalau ba, kaga yadda idonka yayi ja kuwa?"

"Budurwata ce ta ɓatamin rai"

Zaro ido Faruk yayi Yace "What? Budurwa fa kace Sadik"

Sadik ya tashi zaune Yace "eh, ko ban kai inyi ba?"

"Ni na isa ince baka kai ba? Ka kai harka wuce ma Autan Mother, dama mates ɗinka ne suka zo, suna son ganin ka naga da alama ko gida basu je ba, dan jikinsu da uniform"

Sadik Yace "kace musu su shigo"

Faruk ya juya ze fita yana kallon Sadik, kamar yayi dariya wai ɗan wannan jaririn yaron ne yake da budurwa, harta kai ga ɓata rai, ko uwar me yake gaya mata oho?"

Nasir ne da Aminu Manyan abokan nasa suka shigo bedroom ɗin.

Nasir Yace "mazaaaaa, Yanzu ɓacin ran ne yasa ka tafi ka bar school bag ɗinka a school?"

Sadik ya ɗanyi tsaki Yace "ƙyale ni kawai, ni bata jaka nake ba, raina ya ɓaci sosai, na rasa me nayi wa wannan banzan coper ya sani a Gaba, se kace ni kaɗaine ɗalibi, ko kuma nika ɗaine nake soyayya a makarantar nan?, duk ya samana ido, har yana wa Farhan barazanar ze kira mahaifinta, ita kuma ta fara guduna, to idan ya kira babanta ma me zece masa? Meye laifin zuciyata dan ta kamu da son Farhan? Ni nafi zargin anya ba sonta yake ba shima?"

Aminu ne yai wata irin shewa Yace  "Oh my God, gayen nan kana burgeni Wallahi, dole ka tafi da zuciyar that innocent beb, ka iya kalamai, manyan yara a school suna crushing akan ka, amma ka dage kace kai se Farhan, that little baby, gashi ka koya mata son ka"

"Bana tunanin Farhan na sona fa, bata taɓa gayamin tana sona ba fa"

Nasir Yace "ka gane, yarinyar tana son ka, sedai kasan 'yar talakawa ce, and yaran talakawan nan some of them are not well civilised, shiyasa ita komai Kunya that's why ba zata iya gaya maka tana sonka ba"

Sadik Yace "Karfa ka zageta, kuma ni kunyarta tana burgeni sosai, You don't know how much I love that girl"

Nasir Yace  "Wai tsaya, dan Allah meyasa kake son yarinyar nan ne? Ba dai mummuna bace na sani, amma bata wani cika mace ba, she's still a Baby, you have to look for a hot and sexy Baby, but this one is too small for you, ƙwaya nawa wannan 'yar take?"

Sadik ya kashingiɗa, ya shafa afro hair ɗinsa, sannan ya murmusa yace  "ina son Farhan sosai, ina son ta tashi da soyayyata ni kaɗai a ranta, ta fara so a kaina ta gama a kaina, kuma wallahi ni so nake na aure ta, dan banƙi a Auramin ita a Yanzu haka ba, saboda yadda nake ji akan ta"

Wata shewa Aminu da Nasir sukayi, suka tafa, Aminu ya kalleshi Yace "Prince, kana wuta mutumina wato kai ko yanzu ka aure ta?"

Sadik yace "Ku dena ɗauka da wasa nake fa, ina son yarinyar nan sosai"

Aminu Yace "jika, kamar zaka iya wani abun arziki ne in kai Auren a yanzu, kana cika wa mutane baki"

Sadik ya kalleshi yace "Nayi kama da nakashashshene? Nima cikakken namiji ne me lafiya, tsaf Zan iya zama da Mace nima a yanzu haka"

Nasir Yace "we thought you don't have feelings na, even those movies you can't watch, I don't even thinks ka taɓa ko kissing Mace, shiyasa fa kallon soyayyar taka muke kawai shirirrita, babu wani armashi, You Are not romantic at all, your love is so bored, ɗan hugging ɗin nan ma kai bayi kake ba, a haka kake kiran kanka namiji, wai aka maka aure zaka zauna da mace? Malam if you can't do anything to a girl that will make her ehh... Ka gane ai You Are still a boy, ka jira lokacin da zaka zama cikakken namiji ba yanzu ba"

Sadik ya jinjina kai, yana murmushin takaici dan yaji haushin abunda Nasir ɗin ya faɗa, Amma Yace "naji am still a boy, all I know is that, I love Farhan ina sonta sosai zan raini kayata harta zama yadda nake so in Aureta"

Aminu yace 'Prince, that girl is not your type, taya zaka aureta? Kafin ka gama karatu ka tsaya da ƙafarka, ka aureta lokaci ya ƙure mata, dan haka shawarata a gareka koda ma Shi wancan wawan Nazir ɗin sonta yake, kawai ka bar masa empty, ka share hanyar kawai ka tsallak boda"

Sadik Yace "ban gane me kake nufi ba?".

Suka kwashe da Dariya, Nasir Yace "shiya sa muke ce maka You Are still a boy my friend, kawai ka more ƙuriciyarka da yarinyar nan, tana sonka sosai,  kawai ka huta, in yaso ka bar masa sauranka, kai da kana kallon B films ɗin nan da muke kallo da base ance maka ga yadda zaka yi ba, amma kai se Kaita abu kamar wani kidahumi"

Aminu Yace "ka kawo System ɗinka, muna dasu kala kala, a tura maka kayi caji Yau, when you try it yarinyar nan ba zata sake jin maganar wani ba se Kai, saboda a yadda kake ɗin nan, You look so energetic, ba zata sake gangancin gudunka saboda wannan sakaran ba"

Sadik ya girgiza kai yace  "Ina son Farhan ne ba dan in ɓata mata rayuwa ba, hasalima ni kamun kanta, sanyin halinta da kunyarta ne yasa na fara sonta, kuma ni sam bani da interest akan aikata abunda be dace ba, ni bazan kalli filma na batsa ba, bashi da wani amfani Sam, bayan ya toshewa me kallonsa ƙwaƙwalwa ga kuma zunubi, sannan nafi ƙarfin ku kirani yaro wallahi, cox i always have dreams, ina jin feelings kamar kowane lafiyayyen namiji, sedai ni ina son Farhan ne dan Allah ba dan wani abu ba"

"Taɓɗijan, aikuwa in dai dagaske kana jin feelings, and you even have dreams ma, to tabbas a hankali watarana seka so kasancewa da mace,  kuma ga Farhan a kusa da kai, tunda ba aure za'a maka yanzu ba, Yawan kasancewarku tare komai na iya faruwa"

Nasir yace "dalla bar ɗan rainin hankali, wai shi na Allah, se iskanci a baki amma baze gani ba koya aikata, my friend you better enjoy your life, that girl can do anything you ask her to do, gara ka gwada kanka kaji capacity ɗinka, ko ka ƙare a kame Kame, ƙishirwa ta addabeka, ga ruwa a kusa da Kai amma kaƙi maganin ƙishirwar"

Aminu yace "rabu dashi, taso mu tafi Baba, duk ƙaryar banza ce ba namiji bane, har yanzu yarone".

Suka kwashe da dariya, suka tafi suka bar Sadik cikin tunani.

Nzarin maganganun sa ya dinga yi, gaba ɗaya yaji kansa yai dumm, yama rasa wane tunani zeyi? Su Nasir sun caza masa kai, suna ƙoƙarin cusa masa wani tunani, ga ɓacin ran Fargan kuma.

Farhan kam harta je gida gaba ɗaya bata hayyacin ta, bata san ma daya taje gida ba, saboda tunanin ta ɓatawa Sadik rai, mussaman yadda ya dinga faɗan nan, ta san tabbas ransa ya ɓaci sosai, nan ta fara tuhumar kanta meyasa ma ta biye maganganun Sir Nazir, ta fara gujewa Sadik, ƙila ma barazana kawai yake Mata, ba wani Babanta daze kira ya gaya masa, dan gara ma a gayawa Babanta, ta san baze wuce ayi mata faɗa ba shikenan, amma idan Sadik ya dena kulata bata san ya zata yi ba.

Jiki a sanyaye take yin komai, har seda mahaifiyarta ta lura da hakan, tace "Farhan meke damunki ne? Ko a makarantar ne akai miki wani abu?"

Farhan ta girgiza kanta tace "A'a Umma, ba abunda akayimin"

"To idan ma wani abun akayi miki, kiyi haƙuri, ki iya talaucin ki nasan duk makarantar babu ɗan talaka kamar ke, kema Allah ne yayi zakiyi wannan makarantar, saboda scholarship ɗin nan, dan haka sedai kiyi ta haƙuri"

Har Umman Farhan tayi maganarta ta gama, sam Hankalin Farhan baya kanta, tunanin ta kawai yadda zata shawo kan Sadik, dan ta lura yana da kafiya wasu lokutan da zafin zuciya.

Salla kawai tayi ta nemi Guri ta kwanta, Ummanta ta shiga ɗakinsu ta ganta a kwance "Islamiyyar ce ba zaki ba, ko kuma wani sabon salon wulaƙancin ne haka?"

"A'a Umma, kaina ne yake ciwo"

Daga nan Umma bata sake cewa komai ba, ta fita daga ɗakin, bin bayan Ummanta tayi da kallo taji ina ma Ummanta tana sauraren ta, kasancewar ta 'yarta ta fari sam bata wani shiga sabgarta, ko hirar kirki ba ta yi da ita, lokuta da yawa abu na damunta, amma ba zata taɓa iya tunakarar mahaifiyarta da maganar ba, duk da ƙanƙantar shekaru na Farhan, tana son hira da mahaifiyarta, amma sam mahaifiyarta bata bata lokaci,ba ta raɓar duk wani abu da ya shafi Farhan saboda kunyar ɗan fari.

Ajiye wannan tunanin tayi, ta shiga neman mafita akan yadda zata shawo kan Sadik, shiru tayi ta shiga tuna haɗuwarta da Sadik, da yadda suka fara soyayya.

Bayan an sanar da iyayen Farhan ta samu scholarship, a makarantar su Sadik saboda ƙwazonta, sunyi murna sosai dan makaranta ce ta 'ya'yan manya, kuna akwai karatu sosai a makarantar.

Sedai Ranar farko da Farhan ta fara zuwa, ta tsorata da ganin yaran dake makarantar, saboda duk yadda ake zuzuta makarantar ta yaran masu kuɗi ce, bata zaci zata ganta haka ba, Yarane na alfarma a makarantar, 'ya'yan hutu rainon AC, gaba ɗaya tsarin rayuwarsu ya sha bamban da wanda ta taso taga anayi, kalar fatarsu kawai idan ka kalla ka ga yaran hutu, dan kaso mafi yawa na yaran farare ne ƙal.

Suna da cikakken 'yancin aikata abinda suke so a makarantar, da ƙalubalantar duka' wani malami da yayi musu ba daidai ba, saɓanin makarantar data baro, Wadda ta kasance ta gwamnati, baka da wani kataɓus se Abinda malami yaga dama.

A makarantar data baro ta saba da idan an fita tara, suje su kashe kuɗin makarantar su da idan yayi wuta naira hamsin, amma a wannan Makarantar idan aka fita tara masu zuwa da abinci zakaga Abinci ne na alfarma, kaji ko nama yanka zuƙu zuƙu akan abinci, ko kuma tarkacen kayan cake da chocolate da sauran kayan kwaɗayi, se kaga ɗalibi da sama da naira dubu guda.

Ta saba a makarantar data baro, in an fita break, wasansu baya wuce 'yanta, 'yar gala gala da sauran wasannin yara, amma a wannan makarantar daga basket ball, football, volleyball irin wannan wasannin suke, sannan suna bawa birthday mahimmanci da sauran bidi'oi wanda bata saba dasu ba, suna da manyan gangaunan kiɗa da manyan speaku na disco, har clubs clubs ne na koyarda rawa ta zamani, da waƙe waƙe a makarantar.

Ga uwa uba dressing, ita makarantar da ta baro dukda a Jss1 ta baro makarantar, amma hijjabinta ya wuce gwiwarta, manyan hijjabai suke sawa, amma a wannan makarantar, skirt ne gajere daidai jikin ka, ka rufe ƙwaurinka da safa idan kana buƙata, ga ɗan ƙaramin hijjabi, sam bata iya Ratsa unguwarsu da wannan ɗan guntun Hijjabin, seta saka babba a kai.

Wannan banbance bambancen ne yasa Farhan ta sake takure kanta a makarantar, komai nasu ganinsa take daban takasa sabawa da abubuwan makarantar, saboda sun sha banban dana wadda ta baro, ta 'ya'yan talakawa.

Sam bata da wasu ƙawaye a nan, dama dai bame kwashe kwashen ƙawayen bace.

Gaba ɗaya yanayin makarantar da Al'adun makarantar se sukayi mata wani iri daban, babban abinda yake ƙara ɗaure mata kai be wuce yadda ɗaliban da wasu daga malaman ke mu'amalantar juna tamkar jinsinsu ɗaya ba, ta hanyar yin wasanni tare, kamar na ƙwallon ƙafa da sauransu, cin Abinci tare, gaisawa da juna ta hanyar musabiha tsakanin maza da mata, rungumar juna da dai sauransu, wanda a normal al'adar malam bahaushe hakan ya saɓawa tarbiyya da addininmi, dan haka gaba ɗaya Farhan take baya baya da lamuran makarantar nan dama ɗaliban, ta kama karatunta tunda shi tazo yi, suma ɗaliban ba kowa ke shiga harkarta ba saboda suna mata kallona wadda bata waye ba sam.

Wataranar juma'a, lokacin kusan satinta uku a makarantar, Sadik ya dawo aka ce yaje Umra shida 'yan gidansu, anyi rabon kayan dabino bagaruwa, zam zam carbi agoguna, haka aka dinga rarrabawa, abunda Farhan ta lura shine, Ana matuƙar son Sadik, baga malamai ba baga ɗalibai ba, saboda barkwancinsa da yawan kyautarsa, dukda duk yaran masu kuɗine abokan nasa, amma yana musu ɓarnar kuɗi sosai.
Gashi yana da ƙoƙari sosai, sedai ta lura bayan sonsa da akeyi kamar abun harda tsoronsa akeji, seniors ɗinsa na shakkarsa, haka juniors ɗinsa, ko gaban assembly ne ake surutu kafin a fara assembly malamai suzo, daya hau kan stage kowa yake yin shiru, Sadik akwai tsafta da gayu sosai da sosai, gashi baya son raini ko kaɗan, ko tahowa yayi Junior ya taho se an bashi hanya ba'a haɗa hanya dashi, koda kuwa 'yan SS1 ne, sedai Wasu lokutan yakan shiga cikinsu yayi Wasanni kamar ball da sauransu, sabida bayan kasancewar sa gwarzo a aji, ƙwararren ɗan wasa ne, dan ba dan mahaifinsa yaƙi bashi goyon baya ba, da ƙasar waje ze tafi makarantun koyan tamaula.

Wata ranar juma'a, duk 'yan makarantar na gurin wasanni, wasu na wasa, wasu na gurin kaɗe kaɗe, Sadik ya shiga cikin makarantar ɗakko ATM card ɗinsa, ze fita cin Abinci, yazo wucewa ta ƙofar ajinsu Farhan, ya hango ta a zaune ita kaɗai a ajin, tunda ya dawo daga Umra ya ganta a makarantar, baƙuwar fusaka ce dan be santa ba kan ya tafi, sedai yana lura da yadda sam ba ruwanta da kowa, abinda ya dameta shi kawai take yi.

Tura ƙofar ajin yayi, wanda hakan yasa ta ɗago da sauri, ya ɗan ƙura mata ido sannan Yace "ke bazaki gurin wasan bane?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To saboda me?"

"Bakomai" ta faɗa a sanyaye.

"Amma You Are new in this school ko?"

Ta ɗaga kai alamar eh.

Sadik yace "Yayi kyau, amma Yakamata ke ma ki fita gurin wasanni, ki dinga motsa jiki"

Farhan ba tace masa komai ba se binsa da kallo da tayi, Sadik dogo ne chocolate color, kana ganinsa ka san ɗan hutu ne, yana tara suma a kansa, Afro style ko yaushe sumar tana ƙyallin mai, da wuya ka ga kansa a bushe babu mai, gashi da dogon hanci sosai, masha Allah ɗan kyakykyawan matashi ne Prince Sadik.

Tun daga ranar da yai mata magana, duk in da suka haɗu se yai mata murmushi yace mata "Sannu"

Wasu lokutan ta kan mayar masa da murmushin tace "Yawwa"

Haka nan take burge Sadik, saboda shiru shirunta, kusan kullum se sun haɗu ko a hanya ko kuma a gurin assembly.

Watarana ana birthday party na headgirl ɗin makarantar, gaba ɗaya an tare a gurin da ake raye rayen, Sadik ya duba duk gurin partyn amma be ga Farhan ba, ko a gurin assembly be ganta ba, haka nan yaji yana son ya ganta, dan haka ya tafi ajinsu.

Ita kaɗaice a ajin, ta kifa kanta a kan benci, Sadik ya ƙwanƙwasa ƙofar clss ɗin, hakan ya sa tai saurin ɗagowa, kamar kullum yau ma musayar murmushi suka yi.

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, zaman da Sadik yai a kusa da ita se taji tamkar wani babban zunubi ne, take fargaba ta shige ta da tunanin idan aka zo aka gansu a haka fa?

Prince yace "meyasa baki je gurin birthday ɗin ba, Why do you always like to isolate yourself from the people?"

A hankali tace "bakomai"

"Ke kin fi son zama ke ka ɗai?"

Ta jinjina masa kai.

"Wai ni meye sunanki ne ma?"

"Farhan" ta bashi amsa.

"Wow, what a very nice Name, Farhan gaskiya baban ku ya iya zaɓen suna, kin dace da sunan naki, Farhan"

Ɗan sunkuyar da kai Farhan tayi, taji daɗin yadda ya yabi sunanta, amma wannan zaman da yai a kusa da ita duk ya takurata.

"Zo muje gurin party tare, kowa yana can yana walwala ke kuma kullum a takure, wai ke baki da ƙawaye ne?"

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"To shikenan, daga yau ni ne ƙawarki, kuma nine abokinki, ta so muje"

"Ba se naje ba, ina hadda ne an jima idan naje islamiyya zan bada hadda"

Sadik yace "wow, masha Allah yau kinyi doguwar magana, kina da murya me daɗi sosai, amma kullum nai miki Magana se ki amsamin a taƙaice, anyway ayi karatu lafiya se anjima"

Yai maganar tare da miƙewa ya fice,haka kurum ta shiga yin murmushi, mussaman da ta tuna yadda yace muryarta na da daɗi.

Har aka tashi  daga makaranra, da tayi mosti, se ta tuna Sadik, da ya faɗo mata rai kuma se ta kasa riƙe murmushin ta.

Washegari an cika a gaban assembly, Sadik ne ke leading assembly ɗin, duk da kasancewar sa a Ss2, amma ƙwazonsa yasa ake sakar masa yin abubuwa da dama, ya kira wata kirista ta fito ta gabatar da addu'a a gaban assembly, ta koma yana ƙoƙarin kiran wanda ze Addu'a a cikin ɗalibai musulmai, kawai idonsa ya sauka akan Farhan yace "Farhan from Jss2, should come over and recite qur'an for us"

Gaban Farhan ya faɗi jikinta ya shiga kyarma, tana zuwa competitions daban daban, amma ita gaba ɗaya wannan makarantar da mutan cikinta tsoro suke bata da kwarjini, seda ya maimaita abun da ya faɗa Sannan ta fito jiki a sanyaye.

Aikuwa kowa ya bita da ido, cikin takunta da ta saba yi, kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ta hau kan stape, takun da ke matuƙar burge Prince idan tana yinsa, ta kalli uban ɗaliban da suka zubo mata ido, ta waiga ta kalli inda Sadik shima ya kafe ta da nasa idanun.

Ta daidaita nutsuwarta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta fara rero karatun Alqur'ani cikin muryarta me daɗin sauraro, take gurin yai tsit kamar babu wata halitta a gurin, se muryar Farhan da ke tashi a gurin.

Ayoyi goma ta karanta na farkon suratul Yusuf, sannan ta rufe da addu'a, tana idarwa akai mata kabbara, seda Sadik ya dinga wasata kafin ya miƙa ragamar assembly ga malamin da ke duty a ranar.

Ta sha yabo ma daga gurin malamai, saboda yadda tai karatun cikin nutsuwa, bayan an watse daga Address, maimakon ya tafi ajinsu, se ya tafi ajinsu Farhan.

Ya sameta a gurin zamanta yace "Weldon dear, gaskiya kin iya karatun Alqur'ani sosai Masha Allah, you have a nice voice"

Se taji kalmar dear ɗin nan ta ɗan mata girma (😂😂 kun sanmu hausawa wasu lokutan)

"Ya naji kinyi shiru, ba zaki ce komai bane?"

Sunkuyar da kai ta kuma yi, kamar wata amarya, Sadik yace "shikenan, tunda ba zaki Magana ba, I love Your voice, in am fito break zan zo"

Ai take gabanta ya faɗi, he loves her voice kuma? Allah yasa wani be ji me yace ba, love kuma? Wannan ya fiye rigimar tsiya.

Sadik yana zuwa aji, Nasir yace "wai ina ka tafi ne?"

"Na je Jss2 ne"

Amin yace "wai uwar me kke a ajin nan da kake yawan zuwa,, kamar me zuwa neman wani abu?"

yace "Wallahi gamo  nai a ajin"

"Wane irin gamo kuma?"

Prince yai wani ƙasaitaccen murmushi yace "a very beautiful Young beb, ban san meke damuna ba, se dai ina son kasancewa kusa da ita ko yaushe, in dinga kallon kyakykyawar fuskarta ɗauke da ƙasaitaccen murmushin ta"

Nasir yai tsaki yace "ji banza, meye haka se kace wani a hausa film, malam ba fa acting ka ke ba, real life ne, kai ka fiye shirme wasu lokutan"

"Ba shirme nake ba Nas, i think am in love with that beautiful creature"

Amin ya kwashe da dariya yace "kaga wata asara, kuma da 'yar Jss2? Yaran da duk ƙwailaye ne,  maimakon ka samo wata zazzafa duk matan school ɗin nan ka rasa ina zaka samo budurwa se Jss2 dan ci baya, duk matan Senior classes ɗin nan, wanda suka amsa sunan su mata, dan tsuya se  a Jss2?"

Prince yace "ba zaku gane ba ne"

Nas yace "wait, wacece a cikin Jss2 ɗin?"

"Farhan, Yarinyar da tai karatun Alqur'ani a assembly ground"

A tare Amin da Nas suka ja tsaki.

Amin yace "dan Allah meye abun so a wannan Yarinyar? Wannan kwata kwata yaushe aka yayeta daga shan Nono aka kawo ta makarantar?"

Nasir yace "taɓɗijan, a part from sexy eyes banga meye abun burgewa a wannan Yarinyar ba, gata wata kidahuma, kullum tana aji da littafi kamar al huda huda, kullum kanta a ƙasa kamar munafuka, tana kallon Mutane ta ƙasan ido, da an tashi ta zumbula wani uban hijjabi kamar wata me da'awa ta ɗau jaka dunkum dunkum kamar 'yar 419, she don't even look romantic at all"

A fusace Sadik yace "zanci ubanka Nasir, bana son wulaƙanci a haka nake sonta, ka sake faɗan wani rashin hankalin a kanta, zan fasa maka baki"

"Allah ya baka haƙuri, Allah ya bar wannan ƙauna, ta shiga sahun tarihi fiye da Romeo and Juliet, ashe zaka iya yin budurwa Prince?"

Tsaki Prince yai ya tashi ya bar ajin gaba ɗaya, saboda yadda suka sashi gaba da iya shege.

Sadik ya sa Farhan a gaba, duk inda ya san ze ganta se yaje, shi babban abunda yake damunsa da Farhan rashin magana, gashi taƙi sakin jiki da shi sosai, ko abu ya bata ba zata karɓa ba.

Wataran ya ritsata an tashi, ta  ɗau jakarta zata tafi gida, ta jiyo muryarsa yace "sweet heart"

Da sauri ta waigo, dan tantance  da wa yake, kasancewar ba ita kaɗaice a gurin ba.

"Da ke nake Farhan, yau ban ganki ba, Ina kika shiga ne?"

Waige waige ta shiga yi taga ko su ake kallo, amma taga ba wanda ya damu da su, wannan kalma haka me nauyi da ba'a jinta se a bakin mayan samari da 'yan mata kuma masoya, amma ya kirata da ita a cikin jama'a.

Ya ƙaraso inda take tsaye yace "Akwai abunda ki ke nema ne?"

Ta girgiza masa kai, yai ajiyar zuciya yace "yau Friday shikenan ba zan sake ganin ki ba se Allah ya kaimu Monday?"

Sunkuyar da kai tayi, tana wasa da yatsunta.

"Farhan kalleni"

Ta ɗago ta kalleshi ta mayar da kanta da sauri ta sunkuyar, saboda yadda yai mata kwarjini.

"Farhan, ban taɓa budurwa ba, amma am feeling something different on you, ina sonki Farhan!"

Se da ta de na ji na wasu ɗan lokuta, wannan gingimemiyar kalmar, wai yana sonta, taji kamar ƙasa ta tsage ta shige saboda yadda kalmar tai mata dirar mikiya.

"Ya naga kamar kina tsoron wani abu ne? Ko dai ba kya sona ne"?

Tai shiru ba tace Komai ba "shikenan, muje se mu sauke ki a gida"

Da sauri ta girgiza kai tace "Za'amin faɗa a gida"

"Ok, to mu fita gate ɗin tare"

Ba zata iya yi masa musu ba, amma Jerowar da sukayi da Sadik ji take tamkar ta zura da gudu, wannan ai rashin kunya ne, yadda suka jero tare, amma shi ko a jikinsa.

Har ta koma gida juya maganar Prince take, wai yana sonta, shi ko nauyin kalmar be ji ba, ta shiga fargabar kar a gida a gane, wani yace yana son ta dan ta san za ta sha faɗa, dan haka sai tai ta ƙoƙari ta manta da Sadik, amma bata cikakken mintuna ashirin kalmar Sadik na yana sonta be faɗo mata a rai ba.

Tun da Sadik yace yana son Farhan, suke 'yar ɓuya, ba ta yadda su haɗu saboda nauyinsa da take ji, idan kuwa suka haɗu har ya gama surutunsa ba zata tanka ba.

A hankali tun tana jin nauyinsa, saboda yawan haɗuwa da suke da zuwa gurinta da yake, yasa ta fara rage jin nauyinsa, take ɗan sakin jiki da shi.

Gefe guda tana fuskantar tsangwama daga wasu ɗaliban, saboda yadda Prince ke ji da ita, ga kyawawan yara da suka fita komai suna crushing a kansa, amma ya je ya liƙewa Farhan.

A hankali ɗalibai suka dinga gane alaƙar da ke tsakanin Prince da Farhan, kasancewar he is very popular a makarantar.

Shaƙuwa ta fara shiga tsakani ta da Prince, ya zamana idan ma be zo inda take ba, da kanta za ta je ajinsu Sadik dan ta ganshi,

Dawowa tai daga dogon tunanin da ta tafi, tana tunanin meye mafita akan yadda zata shawo kansa ya haƙura.

Dan gaskiya she's ready to do anything dan taga Sadik ya dena fushi da ita, yanzu idan ya dena kula ta fa? Ko ya canza budurwa ya za tayi?!

Ji tai gabanta ya faɗi, da tai tunanin Prince ya canza budurwa.

YANZU AKA FARA, SALON NA DABANNE.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
AYSHERCOOL
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                               5_6

Da sauri Farhan ta miƙe, ta kwaso Uniform ɗinta, taje ta wanke ta shanya.

Ta na cigaba da tunanin, ya zata shawo kan Prince ɗin ta.

Prince kam shima abun duniya ya ishe shi, ya rasa abunda yake masa daɗi, ya dinga jujjuya maganganun su Nasir, ɓangare guda yana jin yadda zuciyarsa ke ƙara jin son Farhan.

Maganganun su Nas na kiransa Yaro, tabbas sun ɓata masa rai amma hanyar da suke ɗora shi a kai, ba me ɓullewa bace.

Miƙewa yai zaune ya kalli agogo, har huɗu da rabi, tunda ya dawo be fita daga ɗakin ba.

A hankali ya tashi ya shiga toilet yai wanka, ya fito yai sallar la'sar, sannan ya shiga cikin gida.

Abun dai da baya so, mutane na ta shiga suna fita a gidan, saboda shriye shiryen bikin Yayansa.

Yatsuna fusaka yai ya shiga falon, ya nufi ɗakin Mother.

Yana shiga ta ɗago ta kalle shi tace "Autan, i have been looking for you since, where have you been ne?"

"Mother ta ya zan shigo, duk an bi an cika mana gida, kamar an fara bikin, mutum da gidan su a hanashi sakewa"

Tai murmushi tace "Ai Arziki ne abun farinciki ya samu brother ɗin ka, an zo taya mu murna, sedai kayi haƙuri, da anyi bikin an gama shikenan"

Prince yace "Da anyi nasa se nawa kuma"

Mother ta kalli Sadik ta ɗan buɗe baki tace "sannu, kai fa baka da kunya wasu lokutan, a beg go carry your food and eat"

"Mother dagaske fa nake"

"Zan make ka, tashi ka bani guri, ka ci Abinci ka ɗau litattafnka ka karanta, bana son shirme"

Bin mahaifiyarsa yai da kallo, yana mamakin yadda suka ɗaukaki boko, ashe akwai daru a gaba, dan gaskiya baze iya zaman jiran wai se ya gama wata jami'a ba.

Ya ɗau Abincinsa ya zauna yana ci a bedroom ɗin, amma tunanin sa na kan wani abu daban.

"Auta, ya naga baka cin Abincin? Meke damunka ne?"

"Bakomai" ya faɗa a taƙice, da ya kammala cin Abincin a nan ya bar kwanukan, da gurin yai gaba abunsa.

BQ ya koma ya sake kwanciya, abun duniya duk ya dame shi, a gaskiya shi baze yadda da wanan aƙidar bokon ba, haka kurum wannan ai cutar mutum ne, ace wani seka yi master's tukuna.

"Nana! Nana!"

"Na'am Innar mu"

"Au da kina jina nake ta faman kiranki  kika min banza?"

"A'a, na amsa fa"

"Ai kin san ni ɗin kurma ce da ban ji ba ko?"

Ta girgiza kai alamr a'a.

Inna ta ɗan ƙureta da ido sannan tace "Ni kin ma yi wanka tukuna yau?"

Tura baki Nana tayi, jin Inna zata fara halin tace "nayi mana"

"Amma kayan jikin ki masu datti ne ko?"

"A'a jiya fa na sasu daf da magariba, kuma na cire na sa na bacci"

'wai ke wace irin yarinya ce me azababben taurin ka ne? Nace miki idan ki kai wanka ki ka sa kaya masu datti, da kinyi wanka da baki ba duk ɗaya jikin ki baze fasa wari ba, haka idan ki baki wanka ba ki ka sa kaya masu kyau shima ba zaki dena wari ba, amma kin kasa ganewa kinfi so kullum in ta yaƙi da ke ina maimaita miki abu ɗaya"

"Haba Innarmu, wallahi bana wari, kayan fa ba datti su kai ba, kuma ko gumi ban ba"

"Zaki wuce kije ki canza kayan ne, ko sena sa miki abun duka? Kije ki cire wannan kayan, ki ɗebi ruwa kije ki sake wanke hammatarki, ki kama ruwa ki wanke fusakarki, ki shafa mai ki canza wannan kayan bera ƙazama"

Nana kamar ta ɗora hannu a kai ta ihu, Inna a duniya idan ba ta takura mata ba bata samun nutsuwa.

Taje ta ɗebi ruwa tana kumbure kumbure, taje ta wanke jikinta, ta fito zata zira kaya, amma Inna ta kuma cewa "ba zaki bar ruwan jikin ki ya tsane ba, ki shafa ruwan alumun ba a haka zaki maka kaya a jikinki? Shiyasa nan da nan kike gumi, ki fara ƙari"

Haka Nana ta shirya a gaban Inna, tace shafa kaza a nan, goga wancan a nan, su nayi Nana na zumɓura baki.

Seda ta canza kaya ta shirya tsaf tai kyau, Inna tace  "yawwa ko ke fa, yanzu kije gidan Rabin kuka, ki ce ina gaisheta, ta baki saƙon nan ki kawomin, kuma ki sauri ina nan ina jiranki"

Nana tace to, ta saka takaliminta ta fita, har taje ƙofar soro na farko, Inna ta ƙwala mata kira Nana ta dawo.

Inna tace "na kira ki ne in sake jadad da miki, bake  ba Zuwa inda ban aike ki ba, kije ki karɓomin saƙo kawai ki dawo, ban da faɗi ba'a tambayeki ba, ko tsoma baki a abunda ba ruwanki, kinji na gaya miki ko?"

"Eh naji"

"Yawwa maza jeki"

Nana ta juya, Inna tace "banda kula mazan da baki sani ba, wanda ki ka sanin ma tsakanin ki da su gaisuwa, kinji ba?"

"To" Nana ta faɗa cikin ƙosawa.

"To Allah ya kiyaye, ban da bi ta Majalisar maza, a tafi ana saka hannu a hijjabi, in ba haka ba, 'yan abubuwan nan da suka fara fitowa, wani ze taɓa ya gudu, kuma idan kika bari wani ya taɓa ba Aurarki yai ba, a haka zasu zauna, harki mutu ba zasu kuma fitowa ba, tun da ba kya alkinta su"

Nana a ranta tace 'Allah ya kiyaye suƙi fitowa har in girma, shikenan ba zan zama 'yan mata ba taɓ"

Inna na shirin kuma ɓaro wani abun, Nana tai waje abunta, dan ta gaji da wannan takarar ta Inna da bata ƙarewa se kace karatu.

Ko da taje gidan da aka aiketa, ta shiga da sallama.

Cikin wata siriryar murya wata ta amsa tace "waye?"

Nana tace "Nice innarmu ce ta aiko ni"

"To shigo mana"

Nana ta shiga ɗakin da sallama, suka gaisa da wannan budurwar, ta girmewa Nana sosai, Nana tace "ina maman take?"

"Ta shiga dubiya, nan maƙota yanzu zata shigo ki ɗan jira"

Nan Nana ta zauna tana jiran dawowar wadda aka aiko ta gurinta. budurwar ta tashi ta ɗebi ruwa a bokiti ta tafi wanka.

Tana shiga banɗaki Nana ta miƙe, taje gaban gadon dake ɗakin, ta ɗau wata brezia dake kan gadon, taje gaban mudubi, ta saƙala ta a haka ta kalli kanta a mudubi tace

"Ohh ni Allah, Allah ka nuna min lokacin da zan fara saka wannan abar nima, wai da anga iyayi, ai ko a makaranta da ba kowa zan kula ba,taku ɗai ɗai zan dinga yi, in dinga yiwa kowa gani gani, Allah dai yasa nima nawa suyi girma, Innar mu ta saimin"

Seda ta gama sakarcinta ita kaɗai, sannan ta ajiye ta nemi guri ta zauna.

Tana zama babu daɗewa sega matar gidan ta dawo, tana shigowa taga Nana ta faɗaɗa murmushin ta, Nana ta durƙusa ra gaisheta, sannan ta faɗa mata saƙon Inna.

Rabi ta ɗakko wata leda, ta bawa Nana tace "gashi nan ki riƙe da kyau, ko hanzarta ki koma, kar ta ga kin daɗe"

Nana tace to, ta karɓi leda tai waje, tana daf da barin layin gidan, ta ga wata Budurwa tana ta zance a ƙofar gida, saurayin yana kan babur, ita kuma tana tsaye, yana mata magana tana murmushi haɗe da Rufe fuskarta.

Cak Nana ta tsaya tana kallonsu, so take ta fahimci meyake gayamata haka da yake sata wannan nishaɗin, take murmushi haka.

Nana ji take kamar ta janyo girma, abubuwa da yawa suna burgeta, a hakan nan ma a 'yan ajinsu akwai masu saurayi, amma tasan idan Hajiya Inna ta san tana da saurayi, se ta dafata ta sha romonta saboda terere da faɗa, gaba ɗaya se jama'ar ciki da wajen gidan sun san meyafaru, amma ita har ga Allah tana son jin me ake ji a tsakanin saurayi da budurwa.

Haka ta tafi tana tunanin ko yaushe itama za tai saurayin nan taji me ake ji haka oho?.

"Hajiya Nana 'yan mata!"
Jin abunda aka faɗa yasa ta waiga da sauri, wani Jamilu ne ɗan me unguwa, ita ko magana bata haɗa ta dashi, saboda yawan kashedin Inna ba kowa take kulawa ba a maza, saboda gani take da taje gida Inna zata gane.

Tsayawa tai sororo tana kallon Jamilu, ya ƙarasa inda Nana take yace "ba gaisuwa?"

Nana tace "ina wuni?"

"Lafiya ƙalau 'yar gidan Hakimi, daga ina haka?"

"Inna ce ta aikeni"

"Masha Allah,ya Innar da kowa da kowa?"

"Lafiya ƙalau"

Jamilu yace "muje, dama nima gurin unguwar taku zani"

Cikin Zare ido tace "A'a, haka kurum aje a gaywa Hakimi ko Inna an ganmu a tare,amin faɗa gaskiya a'a"

Jamilu yai murmushi yace "ba wanda ze gaya musu, ai gaisawa kawai muke"

"A'a to ai na gaisheka ba shikenan ba?"

"Nana manya, wai yanzu ajinki nawa ne?"

"Ina ruwanka da ajina?"

"Bakomai, kawai tambayarki nai"

Ta ɗan murguɗa baki tace "ni gaskiya ka ƙyaleni, kar Inna ta gane na kula maza a waje"

Yai murmushi yace"Shikenan na ƙyaleki, yadda ki ke so haka za'ai, kyakywar jikar Hakimi da duk garin nan babu Tamkar ta a gata ko kyau"

Nana ji tai Jamilu ya wani Mugun fasa Mata kai, tace "dan Allah dagaske kake?"

"Sosai, dagaske nake, ke me kyau ce Nana"

"Amma Inna take cemin bani da kyau"

"Wasa take miki, amma kyawunki ya wuce a misalta ma"

"Kai amma naji daɗi, bari in sauri in tafi kar tace na daɗe"

Ta rungume ledar ta, ta zumbuɗa da gudu, dan kar Inna tace ta daɗe.

An fara kiraye kirayen sallar magariba, sannan Nana ta faɗo a guje, Inna ta kalleta tace "lafiya, kike wannan gudun haka?"

Numfashi ta dinga saukewa sannan tace "Gudu nai dan karki ce na daɗe"

"Au gudu Nana, haka kika ratso cikin mazan gidan nan da wannan uban gudun haka? Ke komai naki cikin hauka da hauma hauma ba nustuwa ba komai kamar rainon maza"

"Allah ya baki haƙuri, ga kayanki nan"

Ta ajiyewa Inna saƙon ta tai ɗaki abunta.

Bayan sallar magariba, Nana tana cin tsiren da Hakimi kan sa a kawo mussaman saboda ita, tace "Innar mu, dan Allah dagaske na fi matan ƙauyen nan kyau?"

Yatsina baki Inna tai tace "Wane maƙaryacin ne ya gaya miki haka?"

"Ba fa maƙaryaci bane, Jamilun gidan me unguwa ne"

"Me ya haɗa ki da Jamilun gidan me unguwar har ya gaya miki haka?"

Gaban Nana ya faɗi tace "wallahi ba abun da ya haɗa mu, kawai gaisheshi nayi"

"Daga gaishe shi ya fara ce miki kinfi kowa kyau? Dama idan na aike ki gurinsa ki ke tafiya ko?"

"Na shiga uku, wallahi ni bana zuwa gurinsa kawai a hanya muka haɗu, yace ban gaisheshi ba, wallahi bana zuwa gurinsa, kuma wallahi ban tsaya  ma a kusa da shi, yace ze rako ni gida naƙi"

Nan da nan hawaye ya wanke fuskar Nana.

Inna tace "Naji ya isa haka, kin san me nake so dake?"

Nana ta girgiza kai, "ban hana ki hulɗa da mutane ba, ko ki gaida mutane ba, ba haka bane, ina jiye miki sharrin mutanen zamanin nan, mussaman ke da RUƊIN ƘURUCIYA, Yake ɗibar ki.

Komai lokaci ne da shi Nana, idan lokaci yayi dole ko ina so ko bana so in barki ki kula samari, a lokacin da nake sa ran ki mallaki hankalin kan ki, kin sai daidai kin san ba daidai ba.

A wannan shekarun naki, za'a iya amfani da ƙanƙantar shekarunki, da rashin wayo gami da RUƊIN ƘURUCIYA a cutar da ke, su maza ba tabbas ne dasu ba, wataƙila ma abunda yasa ya tsaida ke wannan 'yan abubuwan na ƙirjinki yake kallo"

A razane Nana ta kalli ƙirjinta, tai maza tasa hannu ta rufe ƙirjin ta, tare da gwalalo idanuwan ta waje.

Inna tace "eh mana, kuma idan baki wasa ba wataran taɓawa zeyi, kuma ki ka bari ya taɓa ba ke ba Aure, ba haihuwa kuma ba zasu cigaba da fitowa ba"

"Wayyo Allah na shiga uku, amma dai yanzu zasu cigaba da fitowa ko, ai be taɓa ba"

"Eh to ba tabbas, amma dai ki kula, kuma kita istigfari ko zasu fito, maza ki ɗau carbi, ki shiga saƙo kiyi ta Astagfirullah".

Jiki a saɓule, Nana ta cire hannunta daga ledar tsire ta koma gefe, ta ɗau carbi.

Inna ji tai kamar ta tuntsure da dariya, Nana ta nutsu tana istigfari, Allah ya karɓi tuban ta.

Farhan kuwa, ana kawo wuta ta tashi ta goge Uniform ɗinta, gaba ɗaya zuciyarta da tunaninta suna kan yadda za tai da Prince.

Washegari da sassafe, Farhan ta shirya, ta shashafa turare, ta kints da wuri tai sallama da Ummanta, ta tafi makaranta.

Ana buga jiniyar Assembly, Farhan tana cikin 'yan gaba gaba na fitowa gurin Assembly.

Suka tsatstsaya a filin assembly, ta dinga rarraba ido amma ba ta hango Prince ɗin ta ba, ji tai kamar ta je ta tambayi abokansa ko ya zo?.

Gaba ɗaya ta kasa samun nutsuwa, ba taga Prince ɗinta ba, Nazir ne yazo wucewa ta kusa da Farhan, se waige waige take, ya kalli Farhan yace "what are you looking for?"

Kallon sir Nazir tai ta ɗauke kai, dan haushin Sir Nazir take ji.

Yace "ba Magana nake miki ba?"

Ɗan sunkuyar da kai tayi amma taƙi magana, tsaki Nazir yai ya wuce ta.

Har aka kusa gama Assembly, ba Prince ba dalilinsa, hankalin ta duk yaƙi kwanciya, babban burinta shine tai tozali da Sadik.

Har aka kammala assembly, aka fara tafiya classes, Sadik be shigo ba, jiki a sanyaye take ƙoƙarin barin assembly ground ɗin.

Ba tsammani ta hango shi ya shigo, cikin bossy walk ɗin sa yake tahowa, hannunsa ɗaya goye da ƙatuwar jakarsa, ya cake comb a kansa, su Nasir ne suka je inda yake, suka fara gaisuwar su irin ta samari.

Farhan kuwa tsayawa tayi ta zuba musu ido, karaf idon Prince ya sauka a na Farhan, amma cike da jarumta ya kauda idonsa kamar be ganta ba.

Suka zo suka wuce ta gaban Farhan suna hira, Nas yace "Prince beb ɗin can fa saboda kai ta tsaya, kuma ka wani basar"

"Na sani, amma dole in nuna mata mahimmancin soyayyata a tare da ita, zanga wa zata fifita tsakanina da wancan a jawon"

Dariya suka kwashe gaba ɗaya su kai class.

Farhan gaba ɗaya jikinta tai sanyi, shikenan Prince ya dena sonta, tun da har ze iya ganinta ya share ta haka? Kenan ya dena sonta?.

Jiki a sanyaye ta tafi ajinsu, jinta take tamkar mara lafiya, wai yau ita Sadik ya gani amma ya share, ko meyasa ta biyewa maganganun Sir Nazir oho?

Haka ta nufi ajin nasu, sedai tsayuwar da tai a hanya, tana zuwa ta tarar da Sir Nazir har ya shiga.

Gabanta ya faɗi, amma ta dake ta shiga ajin, aikuwa ya ƙureta da ido.

Hakan yasa ta ɗan dirirce, "from where are you?"

"Assembly ground" ta bashi amsa.

"Ni zaki wa ƙarya? Tun yaushe aka baro Assembly ground ɗin? Kin dai tafi gurin wancan banzan yaron mara tarbiyya ko?"

Da sauri ta ɗago ta kalli Nazir, ta msida kanta ƙasa tana sake haɗe rai.

"Wuce kije ki zauna, mara jin Magana kawai, ki cigaba da biye masa zan gauraya dake ne"

Yana ɗauke kai ta murguɗa baki, taje ta nemi guri ta zauna.

Ya ɗau marker, yaje kan White board ɗin, ya rubuta date da sunan subject ɗin, sannan ya zo ƙasa ya rubuta Adoloscent period, ya ja layi sannan ya juyo ya kalli 'yan ajin.

"Today's lecture we are going to talk about adolescent period, but let me warn you guy's, if any body among you misbehave, i will mercilessly deal with that person, hope i made myself clear?"

Suka amsa da yes sir.

"Can anyone among you tells me a little he understand about this topic?"

Gaba ɗaya ajin sukayi shiru, ba wanda yace komai.

"So non of you ever heard this word before?"

Nan ma shiru suka yi, Farhan ya kalla da ta ƙurawa guri ɗaya ido ko ƙyaftawa ba tayi.

"Hey!" Ya daka mata tsawa.

A razane ta dawo hayyacinta tana kallonsa.

"Meke damun ki ne?"

Ta girgiza masa kai tace "Nothing sir"

"Oya stand up"

Ba musu Farhan ta tashi tsaye, Nazir yace "what do you understand by Adoloscent period?"

Sunkuyar da kai tayi, tai masa shiru.

Yai maganar juyin duniya amma taƙi, magana.

"Farhan, I don't know what you are turning to, you are gentle and so obedient before, amma yanzu gaba ɗaya kin canza, kin zama me taurin kai da rashin ji, a haka zaki lalata rayuwarki da tunanin iska da shirme, sit down senseless child"

Farhan tana zama se hawaye, ta rasa me ta tsarewa sir Nazir da take damunta haka ya tsaneta, bayan yasa Sadik yana fushi da ita, amma ya gza dena binta da miyagun kalamai.

"Kamar yadda ku ka gani a allo na rubuta, Adolescence is the period of transition between childhood and adulthood. Children who are entering adolescence are going through many changes (physical, intellectual, personality and social developmental). Adolescence begins at puberty, which now occurs earlier,than in the past, due to environmen and the kind of food we eat.

Shi Adolescent period, lokaci ne na tashen balaga, lokacin da mutum ke canzawa da ga yarinta shiga mataki na girma.

Yaran  da suka shiga matakin balaga, suna fuskantar sauye sauye a halittar jikinsu, yanayin mu'amalar su, tunaninsu da kuma hange.

A baya a kan samu jinkiri, kan yara su shiga matakin tashen balaga, sedai a wannan zamanin yara na shiga matakin balaga ne a ƙananan shekaru, saboda yanayin Muhallinmu, Abincin da muke ci, kallace kallace da sauransu.

Lokacin tashen balaga lokaci ne mafi hatsari a rayuwar ɗan Adam, idan mutum ya samu kyakyawar kulawa ya bar wannan stage ɗin lafiya, ans  sa masa ran yai kyakykyawar rayuwa, idan mutum ya bari ya lalace a wannan lokacin, to girman sa sedai wani ikon Allah, as how some of you are doing now, trying to be spoiled at their adolescent age, hanging around with stupid and spoiled guys.

Sarai Farhan tasan da ita yake, amma ta basar.

Ya cigaba da karatunsa.

"Akwai sauye sauye da dama, da Yara maza da mata ke fuskanta a lokacin tashen balaga, da suke nuni da sun shiga wannan mataki na girma.

A ɓangaren maza, akwai buɗewar murya, daga ƙaramar muryar su ta yarinta zuwa babbar murya, akwai fitowar gemu ko saje, akwai fitowar gashi a hammatar su da mararsu, manhood ɗin su ze ƙara girma, ba kamar da da suke yara ba, za su fara mafarki..

"Sir ai dama kullum ana mafarki" cewar wani yaro.

"No is not a usual dream, mafarkin suna having sexual intercourse, wanda idan suka farka ta kan kai ga sun fidda maniyyi, akwai developing sexual feelings da opposite sex ɗinsu, saboda aiki da homones ɗin su sukeyi toward that, shiyasa in this period ba'a son yawan cakuɗeɗeniya da mu'amala a tsakanin opposite sex, saboda a  wannan lokacin ƙwaƙwalwa na negative thinking towards satisfaction of sexual feelings among the Adolescents.

A ɓangaren mata kuwa, suma muryarsu na ƙara daɗi, daga muryar yarinta zuwa ta 'yan matanci, ta yadda muryar ta su kan iya atrackting opposite sex ɗinsu.

Akwai development of breast, ƙirjinsu ze fara girma Yana tasawa, saɓanin da da yake a shafe Bakomai.

Gashi ze fito a hamattar su, da kuma al'aurarsu.

Zasu fara developing feelings towards opposite sex.

Akwai fara jinin al'ada, zasu fara zubar da jinin al'ada duk wata.

Any one of this signs is a sign of puberty, ba dole se mutum ya haɗa su gaba ɗaya ba lokaci ɗaya, wani na iya farawa da gashin hammata, wata za tai developing breasts amma ba ta da gashi a hammata, ko ta fara jin feelings amma ba ta fara al'da ba.

Alamomin ba suna zuwa lokaci ɗaya bane, they are coming one after the order.

The must dengerous part of it, is when a lady start seeing her menstrual period, and she's not able to maintain her sexual feelings, anything can happen at that time, she can easily get belle God Forbid.

In our next class insha Allah, we will continue from where we stop, and we will discuss the other signs, and personal hygiene during puberty insha Allah, if anyone of you has a question he can ask, before i ask my own when ever I decide to do so, my question will be as assignment or test.

Ya kammala ya tattare takaddunsa, ya fita, dan ba wanda yai tambaya.
yana fita 'yan ajin suka sa shewa.

Lilly tace "wai, yau zamu gane wanda suka reaching adolescent period, a mata zamu ga wadda ƙirjinta ya fara tasawa da wadda har Yanzu take Small Baby".

Kwashewa su kai da dariya, wata yarinya tace "aikuwa maza kuma zamuji masu husky voice, da wanda suke da Baby voice har yanzu"

Lilly tace "ke Hasina masu babbar murya wannan ai se daga ajin su Prince zuwa sama za ki ji wannan, sedai in layi za suyi a leƙa hanmatar mu gani"

Hasina ta kwashe da dariya tace "ko muji in da wanda ya fara dreaming ba"

"Hmm yau zamu tantance adults da Babies, ɗaya bayan ɗaya zamuyi screening, muji wadda ta fara saka brezia, da wadda har yanzu take sahun yara, maza kuma azo a bamu labari wanda suka fara dreams"

Dariya suka kuma yi, Lilly tace "Yasmin ke fa 'yar iska ce wallahi, se su hau layi ki fara dubawa ai"

Suka cigaba da taɗin su, Farhan kuwa tai shiru tana tunani, wasu daga singns ɗin nan na adolescent period, already ta fara Experiencing ɗin su, amma ita banda yau ba ta taɓa sanin wannan alamomin balga bane, babu wanda ya taɓa gaya mata.
(Ƙalubale gareku iyaye)

Tunani ta fara yi meye wannan sexual feelings ɗin, tasan shi ake nufi da sha'awa tun da sunyi a islamiyya, amma meye shi ɗin? Ya mutum ze gane that he has sexual feelings towards his opposite sex?

Yanzu tarayyarta da Prince ze iya sa taji feelings akan sa kenan? Kuma hakan na nufin matsala ne kamar yadda Sir Nazir ya faɗa?.

Kai koma me ze faru, ta san ba wani abu da za taji ko ya faru, dan tana tare da Prince, kuma ma ai shika ɗai ne namijin da take kulawa, ai ita ba shiga sabgar maza take ba.

Da sauri ta tashi ta fita waje, ta nufi ajin su Prince.

Tana zuwa ta tarar 'yan aji suna fitowa, da alama wani gurin za su.

Mazan sun saka kayan sport wears, prince ya fito hannunsa ɗauke da ball, yana buga ta yana cafewa.

Farhan ta zuba masa ido, ya ɗaga kai suka haɗa ido, ɗauke kai yai kamar be ganta ba ze wuce.

"Sadik" ta faɗa a sanyaye.

Ɗaga kai yai ya kalleta, be ce komai ba.

Ganin ba za tai Magana ba, yasa shi yin gaba ze wuce, ba tare da shirya ba ta riƙe rigarsa.

Ya waigo ya kalleta, yaga idonta ya cika da hawaye.

Jiki a sanyaye tace "Am sorry please"

"Sorry for what? You don't need to apologise, ki je ki biyewa wancan ajawon kiyi watsi da soyaya ta"

"Dan Allah kayi haƙuri"

Prince yai wani irin murmushi da ke sanya Farhan farinciki, yace "ok shikenan my Farhan, ai ba zan iyayin fushi da ke ba, na ma fasa zuwa gurin ball ɗin, hira zamuyi"

A'a kar ka fasa zuwa, tun da kayi niyya"

"No kin fiye min ball mahimmanci"

Amin ne ya dawo yana mita yace "wai dalla me kake a gurin nan, tun ɗazu muna fili muna jiranka?"

Prince ya jefa masa ball ɗin yace "ga shi nan kuje kuyi, ni na fasa zuwa"

"Kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya maka mana"

"Amma wallahi ka cika mara mutunci, wannan ai wulaƙanci ne, ya za'ai an shirya abu kuma kace ba za kai ba?"

Prince ya kalli Farhan yace "let's go inside my dear"

Suka shiga ajinsu Prince, suka bar Amin a gurin.

Amin ya juya ya tafi yana masifa, yana zuwa filin ƙwallon ya saki ball ɗin a ƙasa yana mita.

Nas yace "ahh ya haka? Ina Prince ɗin?"

"Waccan mayyar yarinyar ce taje gurinsa, Shine ya jefomin ball ɗin wai baze ba, ya tsaya a gurinta"

Taslim tace "wai dan Allah meya sa Prince yake wa mutane hakane?"

Meenat tace "ai shegiyar yarinyar ce mayya"

Amin yace "maganin ta zamuyi, idan har zata cigaba da rayuwa da Prince to dole za ta shigo clique ɗin mu"

Nas yace  "ƙwarai kuwa, rabu da shi za muyi maganinsu daga shi har ita"

Daga nan suka fara ball ɗinsu a tsakanin maza da mata (😲🙄🤔).

"Farhan, ko kina doubting akan son da nake miki ne?"

Farhan ta girgiza masa kai.

"To meyasa kike guduna Farhan? Wallahi i really love you"

Shiru tai ta sunkuyar da kai, tana hawaye, Prince yace "ok I got you, is ok ki dena kukan"

Yai maganar yana ƙoƙarin kai hannu ya share mata hawaye, amma ta jabda baya da sauri"

Yace "ok sorry, karɓi hancky ki goge hawayen, ki dena zubarmin da su a banza"

Ta karɓa ta goge hawayenta, tana cikin gogen hawayen aka kawowa Prince Abincin da yai order.

Yaje ya karɓo ya dawo yace "My dear, me za'a kawo miki ne?"

"Nothing" ta faɗa a taƙaice.

"Why?"

Tace "Na ƙoshi"

"No baki ƙoshi ba, muci wannan tare"

Farhan tace ba zata ci ba, Sadik yai ƙasa da murya ya ɗebo a spoon ya kai bakinta, yana mata wani irin kallo Yace "dan Allah kici ko nima in ƙi ci"

Ji su kai an buɗe ƙofar ajin da ƙarfi, suka waiga gaba ɗaya.....

Free pages are not much, hurry up and subscribe yours.

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                               7_8

Jikin Farhan har ya fara tsuma zaton ta Sir Nazir ne.

Shi kansa Prince ya ɗauka Nazir ne, dan ya shirya tsaf dan maida martani ga duk wanda ya kuma kawowa soyayyarsa barazana koma waye.

Se dai ba ba yadda suka zata bane, wani ɗan ss3 ne wanda ake cewa Babba.

Ya shigo ya kalli Prince yace "wai kai Prince wane irin banza ne? Ya za'ai an shirya abu da kai kace ba za kai ba meye hakan?"

Gyara zama Prince yai ya kalleshi Yace "an shirya yin abu dani, yanzu kuma nace ba zan ba, ba shikenan ba"

"Dalla kar ka gayawa mutane Maganar banza mana, wannan ai wulaƙanci da rashin mutunci, wai kai meyasa kake haka a rayuwar ka ne?"

Banza Prince yai masa, yaƙi ko kallonsa.

Babba ya dinga zazzagawa Prince jaraba, amma ya mirsisi yaƙi sake tanka masa, seda Farhan ta fara jin haushin abun da Babban yake wa Sadik.

Babba dai takaici ya isheshi, yai waje yana mita.

Yana fita Sadik ya girgiza kai kawai yai murmushi.

Farhan tace "Naga sun ji haushin abunda kayi, bari in tafi kawai kaje kai Ball ɗin"

Sadik yace "No, ni kin fiye min ball ɗin nan, maza muci Abincin nan kar ya huce"

Fafur Farhan taƙi cin Abincin nan, yai yai da ita amma ta ƙi yadda ta ci, se ƙyaleta yayi.

Yana cin Abincin suna ɗan taɓa hira, duk da Mafi yawa daga hirar shi yake mata, can tace "wai meyasa ake ce maka Prince ne?"

Wani kyakyawan murmushi Prince yai, da yai matuƙar birge Farhan, yace "Kinga ni ba sarki ba, ba ɗan sarki ba amma ana cemin Prince ko?"

"A'a kawai tamabaya nayi?"

"Kakana Hakimi ne, Kakata ma 'yar Hakimi ce, sannan babana yana da sarautu daban daban har a kudancin ƙasar nan, kwanan nan ma an masa wata Sarautar a Ghana, kuma ana ɗan cewa ina da jin kai, wanda ba hakan bane, kuma ni ne auta a gidanmu suna ji dani sosai wannan dalilin ne yasa ake cemin lil Prince"

Murmushi Farhan tayi tace "Sannu Prince"

"Yawwa matar Prince" ya faɗa yana kashe mata ido.

Haka suka cigaba da hira ita da Prince, tana jin wani farinciki maara misaltuwa kasancewar ya dena fushi da ita.

Da yake Friday ce, har aka tashi suna tare, ya raka ta har ajinsu ta ɗakko jakarta, suka fito harabar makarantar.

Suna fitowa kuwa su kai arangama da Nazir, ya zubo musu ido yana musu kallon tuhuma, dan ba kowa a cikin makarantar se su, dan duk ana waje gurin wasa.

Gaban Farhan yai mummunar faɗuwa, amma ta dake ta ƙi kallonsa.

"Hey daga ina kuke!?"

Ya faɗa cikin shouting, wani Mugun kallo Sadik yaiwa Nazir, yaja hannun Farhan da sauri, wanda se da hakan yasa ta firgita, be tsaya ko ina ba se bakin motarsu, ya buɗe mata yace "shiga"

Ta waiga ta kalli Nazir ta kalli Prince, a hasale yace "shiga nace"

Da sauri ta shiga, shima ya shiga motar ya cewa direba ya ja su tafi.

Ta kalli Prince ta na so tayi magana amma taga ya wani haɗe rai, tilas ta ja bakinta ta tsuke, dan ko cikin kuskure ba tavsin sake aikata abunda zesa yai fushi.

Har suka sauke Farhan be kuma ce mata uffan ba suka nufi gida.

Shikuwa direban Sadik addu'a yake Allah yasa kar Sadik ya ɓata Yarinyar nan ganin yadda take masa biyayya kamar ubanta.

Sadik suna zuwa gida, ya tarar da mahaifinsa a harabar gidan, shi da wasu baƙi, watanni biyu kenan mahaifin nasa baya gari, se Yau ya dawo.

Da gudu Sadik ya sakko daga mota, ya nufi mahaifinsa da gudu, ga abokan mahaifinsa a gurin amma be bi takansu ba, ya rungume mahaifinsa yana faɗin "I miss You Daddy"

"Miss you too Auta na, how are you and how was your studies?"

"Fine Daddy, amma meyasa ba ka gayamin yau zaka dawo ba? Kawai se in dawo in ganka?"

"Eh mana, i warn Your Mum kar ta gaya maka zan dawo yau"

Murmushi Sadik yai, ya kuma kallon mahaifinsa yace "I really miss you"

Mahaifinsa yai murmushi ya shafa sumar kan Sadik yace "maza kaje ka canza kaya ka huta, in zo muyi hira"

Ɗaya daga abokan mahaifun nasa yace "Wai Sadik ne ya zama haka? Ya girma sosai, ko dan na daɗe ban ganshi ba?"

Daddy yace "Shine gashi ya zama big boy ba"

"Gaskiya girman ɗan mutum ba wuya, kwata kwata yaushe muka je da kai a kai masa kaciya, ai nasan ba ze manta dani ko dan wannan ba"

Sadik a ransa yace "kutmar, ji ɗan rainin hankali wai suka kaini kaciya, abu ya wuce shekara goma sha, amma dan wulaƙanci wai an kaini kaciya dan cin zarafi, Allah yasa ma ba a gaban wanda zeji kunya ya faɗa ba, ya rasa dame ze tunani se sun kaini kaciya"

Saidk ji yai kamar ya yi tsaki, amma ya maze ya wuce, ba tare da ko sannun ku ya cewa abokan mahaifinsa ba.

Kuma hakan be damu mahaifinsa ba, dan yasan halin ɗan nasa na rashin son mutane, da kula jama'a.

Da daddare bayan sallar isha'i, Sadik ya shiga cikin gida, dan gaba ɗaya ya bar ɗakinsa na cikin gida, saboda yawan mutane da suke zuwa gidan.

Ya tarar da Daddynsa da Mother, da su Usman a falonsa, suna tattauna maganar bikin Usman.

Prince yana zuwa ya haye kujerar da mahaifinsa yake zaun yace "bari in zauna ta nan inji ɗuminka sosai"

Faruk yace "wai kaji ɗuminsa, kamar wani wanda za'a shayar"

Daddy yai murmushi yace "kar ka damu ɗan auta mana, ƙyaleshi ya zauna kusa dani, nima ɗumin nasa zanji ai, nayi kewarsa sosai"

Ango Usman kuwa ɗan taɓe baki yai, saboda taɓarar da Sadik yake yi tana yin yawa, yaiwa Daddy yaiwa Mother, kuma lailaya shi suke kamar wani ɗanyen ƙwai.

"Auta na ga saƙonka kan in dawo, kuma shirye shirye sunyi nisa sosai, na tura kuɗin Neco da Waec ɗin ka, kamar yadda ka buƙata zaka kammala secondary this year ina sha Allah"

Cike da farinciki yace "Wow, thank you so much Daddy, Nagode sosai Allah ya ƙara Arziki me Amfani"

"Ameen My Son"

Mother tace "wai dagaske jumping za kai masa kenan? A ss2 yake fa"

"Ai ba laifi kin san yaron nawa ƙwaro ne, he can do it yace yana so, kinga ban san me yake hange da yace yana son ya kammala secondary School a wannan shekarar ba, may be he's planning something better for his future"

Mother tace "to ai shikenan, Allah ya bada sa'a, shine ni ko a gayamin"

Daddy yai murmushi yace "to ai gashi yanzu kin sani, kai kuma seka hanzarta gayamin jami'ar da kake so a waje, a fara processing tun da wuri"

Nan da nan jikin Sadik yai sanyi, dan yasan tabbas da zarar ya kammala makarantar nan, ƙasar waje za'a ce ya tafi karatu, Farhan ɗinsa fa zata iya jiran sa? Ƙaddara ma zata jira shi, shi baze iya jiran tsayin wannan lokaci, yana bautar biro da takadda ba, bayan shi abunda zuciyar sa take so daban ba, gaskiya Aure yake so, dan yafi damuwa da Yayi Aure akan wannan bokon.

"Ya naga kayi shiru? Ko baka son karatun ne?"

Ji yayi kamar yace baya so, Aure yake so ai masa Kafin karatu, amma yace "A'a ina so, ina nazarin wace jami'a zan tafi ne, don't mind me zanje inyi tunanin wace jami'a ta dace da ni"

Yai maganar yana miƙewa tsaye, Daddy yace "in wani abu ya shige maka duhu, ga yayyenka nan ko kazo ni ka sameni mu tattauna"

"To Daddy, Good night"

Yai maganar yana ficewa daga ɗakin.

Da yaje nasa ɗakin ma kasa baccin yayi, ga ƙoshi ga kwanan yunwa.

Da ƙyar bacci ɓarawo ya sace Prince Sadik, saboda damuwar da yake ciki.

Washegari ya kama Asabar ranar da za'a kai kayan Auren Dr. Usman gidan Hakimi, wanda se an kai can sun kwana sannan za'a kai gidan su Yarinyar da ze Aura ɗin.

Kaya sun kai kaya, akwatuna goma sha biyu ne na alfarma shaƙe da haɗaɗɗun kaya, masu tsadar gaske.

Lefen ya haɗu ƙarshen haɗuwa, haka aka zuba kayan a mota, za'a tafi.

Sadik yana saman bene, yana kallon yadda ake zuba kayan a Mota, ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "Allah ka nunamin lokacin da zan haɗa kaya fiye dana Dr. a kaiwa Farhan ɗina, a ce yau gani zan Aure nima.

Yana nan a tsaye aka ja motocin aka tafi dasu.

Shima komawa yai ɗakinsa, ya shirya cikin ƙananan kaya ya fice nasa guri, dan a 'yan kwananin nan zaman Gidan nasu sam baya masa daɗi.

Nana na tafe a hanya tana zura hannu a hijjabinta, tana rarraba ido kar taje wani ya kalleta a banza, Ta koma gida Inna ta gane, tana tafe tana ta sauri kamar wadda take da wani uzuri a gabanta.

Tana zuwa ƙofar gida ta tarar da cincirindon motoci a ƙofar gidan, dama tun safe ta ga ana dafe dafe a gidan, ta tambayi Inna me ake haka amma ta gaya mata baƙar magana, taƙi gayamata meke faruwa.

Fararan fararan ta shiga ratsa mutanen dake harabar gidan, ta shiga cikin gida.

Ta tarar da mata a zazzaune ana ta rangaɗa guɗa, banda masu bushe bushe da ta baro a waje.

Neman Inna ta shiga yi cikin lungu da saƙo na gidan, cikin sa'a ta hango Innan, ta sha Kwalliya.

"Innarmu wai me akeyi ne haka?"

"To tambaya, daga daowarki ko cire kayan makaranta baki ba, kin zo kin cikani da tambaya"

"To Inna ni duk an zo a cika gidan a ina zanje in canza kayan ko ina mutane"

"In kin gama fitsarar kya tafi kije ki canza kayan" Inna tai maganar tana cigaba da hada hadarta.

Ɗakin Inna ta shiga ba kowa a ciki, ta cire kayan makarantar ta, ta zunduma uban hijjabi sannan ta shiga tai wanka, ta fito ta canza kaya.

Inna ta shigo ɗakin zata ɗau abu, ta ga Nana na binta da kallo, Inna tace "kayan lefen Usman aka kawo mu gani, sati me zuwa za'a kai shikenan?"

"Waye kuma Usman?"

Nana ta tambayi Inna, tana ɗan tura baki.

"Au Usaman ɗinma baki san shi ba? Iko se Allah to bari in miki yadda zaki gane, yaran nan masu tara gashi, na gidan Abdullahi"

Murmushi Nana tayi tace "Au se yanzu na gane, to ina kayan lefen suke?"

"Suna turakar Hakimi"

Nana ta zabura tace "bari inje ina gani"

"Ke bana son hauka, da baƙin a gurin zaki je? Kefa wani lokacin kwantacciya ce"

Nana ta ɗan haɗe rai, dan taji haushin ce mata kwantacciya da Inna tayi.

Se la'sar sannan masu kawo kayan suka tafi, Hakimi yace a bar kayan a nan, Ranar da za'a kai lefen, za'a tafi dasu daga nan.

Haka kuwa akayi, aka tafi aka bar kayan a nan, akan se ranar da za'a kai sannan za'a tafi dasu.

Ko da labari ya ishi Mother an baro kayan lefen nan a ƙauye Gidan Hakimi, abun ya baƙanta mata rai, ta dimga sababi akan me za'a baro mata kaya a can, salon a sace musu wani abun, haka tai ta sababin ta ta haƙura.

Ranar Monday a school prince yai shirin ko ta kwana ko da Nazir ze gaya masa wata maganar banzan akan abunda ya faru Ranar Friday, amma yaga be kulashi ba.

Ita kuwa Farhan faragaba ta dinga yi, dan kar ya cimata mutunci, dan ta fuskanci ya tsane ta sosai, ba ita kaɗai ke soyayya a makarantar nan ba amma yabi ya sa mata ido.

Cikin ikon Allah kuwa be tanka mata ba daga ita har Prince ɗin.

Ana fita break kamar jira take, ta tafi ajinsu Prince, sun barbaje suna ta hira ana kwasar dariya, suna tsara irin yadda zasu raƙashe a bikin Yayan Prince da za'ai nan da wata ɗaya, wanda ze kama a cikin hutun kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Sallama tayi tana duba inda za ta ga Prince, yana kashingiɗe yana game a wayarsa, sedai in sunyi abun dariya shima yayi.

Duk d rashin son kallo da Farhan ba tayi, da kwarjini da 'yan ajin nasu Prince ke mata, hakan baya hanata shiga ajin in dai za ta ganshi, kamar yasan ta shigo ya ɗago aikuwa su kai ido huɗu da Farhan.

A tare sukayi murmushi yace "welcome my cwt"

A hankali ta tako cikin tafiyarta me ɗaukar hankali.

Taslim ta kalleta ta ɗan yatsuna fuska, dan yanzu haushi Farhan take bata tace "wai ke kam ba kya gajiya ne? Kullum cikin sintirin zuwa ajin nan ki ke?"

Take jikin Farhan yai sanyi, ta ɗanyi sororo tana kallon Taslim, kuma Maganar Taslim tana kan gaskiya.

Prince yace "Taslim wallahi zan tatala miki rashin mutunci da baki taɓa tsammani ba, ina ruwan ki da ita? Me tai miki ko ajin daga gidanku ki ka zo da shi? Bana son haka ban sawa kowa ido ba, dan haka nima kar a samin"

Taslim tace "Allah ya baka haƙjri sarkin fushi, wasa nake mata"

"To ba'a san wasan" ya faɗa yana harar  Taslim.

Ya kalli Farhan yace "ƙaraso mana"

A hankali ta ƙaraso tana ɗan wasa da yatsunta.

Kan ta zauna ya ɗan tsaya yana kuma ƙare mata kallo, girma Farhan take ƙara yi, ƙara buɗwa take ga wani kyau da take ƙarawa.

Ɗan lumshe ido yai yana murmushi, ta zauna a ɗan nesa da shi kaɗan.

"To ya, kina lafiya my love?"

Sunkuyar da kai tayi cike da jin kunya, tace "lafiya ƙalau"

"Ai tun ɗazu naso in zo ajin ku, sedai nace bari in jira inga zaki zo?"

Murmushi kawai tayi ba tace komai ba.

"Nifa bana son wannan shirun, hira zaki min inji muryarki, kullum sedai ki zo ki kalleni kina murmushi, duk da murmushin naki burgeni yake, but say something"

"I have nothing to say" ta faɗa a ɗan shagwaɓe.

Dariya yai yace "muryarki da turancin kamar baturiyar England"

Seda ta ɗan zare ido jin abunda Prince ɗin nata yace.

"Farhan, an kusa bikin Yayana, zaki zo ko?"

"Yaushe ne?"

"Nan da 1month insha Allah, ai zaki zo ko?"

"Ina tunanin ko za'a barni inje a gida"

"Meyasa ba za'a barki ba?"

"Baban mu yana da tsaro sosai, ba'a barina fita sedai in a 'yan ajinmu wasu zasu je, su zo mu tafi tare, kuma ka bani kati in kai gida"

"Karki damu dan wannan ba Matsala, yama za'ai ai bikin bro tawa matar va taje ba, kin san daga bikinsu se namu fa"

Zare ido tayi sosai kamar ya faɗi wani abun tsoro.

"Meye naga kina zare ido haka?"

"Ya za'ai amana Aure yanzu, mufa yara ne"

Ƙasa ƙasa suke hirara ba wanda yake jina bunda suke faɗa, amma jin abunda Farhan ɗin tace yasa Prince cikin ɗaga murya cewa  "What!".

Seda aka jiyo aka kallesu, Prince ya basar yai ƙasa da murya tare da ɗan haɗe rai yace "suwaye yaran?"

Ɗan tura baki tayi tace "to ai naga ko makaranta ba mu gama ba, kuma base mutum ya girma yake Aure ba, waye ze mana Aure a haka?"

Seda Prince yai murmushi, ya jinjina wauta da ƙuriciya irin ta Farhan, sannan yace "waye yace miki shi girma a fili yake, waye yace miki sharaɗin Aure ne se mutum ya girma sosai za'a masa Aure?"

"Ai haka naga anayi"

"Hmm Farhan kenan, yanzu idan Dad ɗina yazo nema min Aurenki baza'a bni ba?"

Ya faɗa in a very serious tone.

Kamar za tai kuka tace "wallahi ina ga se ya kusa ɓallani, cewa ze ya akai nai saurayi har na fara Maganar Aure?"

"Hakane You Are still Baby, but looking so....

Se kuma yai shiru yana cigaba da ƙuara mata ido, har seda ta ɗan tsargu.

"Amma ai kina sona ko?"

Ɗaga ido tai ta kalleshi, ta mayar ta sunkuyar.

"Hmm i understand"

Babba ne na ss3 ya shigo ajin, yana shigowa Taslim ta miƙe da gudu ta rungumeshi, ya ɗagata yana juyi da ita a tsakiyar class ɗin.

Mamaki ya cika Farhan, wannan wane irin rashin hankali ne da rashin ta ido.
A shagwaɓe Taslim tace "I miss You Honey"

"Miss you too dear, ai tunda na dawo tun lats week ba kya Zuwa bamu haɗu ba"

"Bama gari, munje Abuja that's why, you are well dear, amma dai ka warke ko?"

Babba yace "Alhamdilillah jiki yayi sauƙi sosai"

Farhan kama gaba ɗaya seta tsargu, wata kunya ta mamayeta, ganin haryanzu sunƙi sakin juna Taslim da Mubarak wato Babba.

Sadik yace "gaskiya Mubarak ku fita can waje kuyi, kun san Babyna jaririya ce kuna iskanci a gabanta karku ɓatamin mata ku sa mata wani tunanin daban"

Taslim tace "ba wani jaririya, ta san komai, don't mind them my sugar"

Tai maganar tana kissing Mubarak a kumatunsa.

Nasir yace "kaga in da ake abu, ba irin soyayyarku ba, soyayya irin ta zamanin iyaye da kakanni"

Farhan ta miƙe tace "Na tafi aji"

Sadik yace "sun kore ki ko? Banzaye kawai muje in kaiki class"

Ya miƙe suka jera suka fita, sedai Nas yabi bayan Farhan da kallo.

Amin ya daki cinyarsa yace "kai lafiyarka kuwa?"

"Lafiya ƙalau, ina kallon Yarinyar nan ne kawai, gaskiya ina ni zan sharewa Prince hanyar nan, kan uba ka ga abunda na gani kuwa?"

"Aikuwa da yaci ubanka la'ada waje"

"Kai dall ƙyaleshi, se wani abu yake waishi na Allah, this girl is looking so hot ka gane ai"

"Karka kuskure ya gano ka wallahi, dan karonku baze maka daɗi ba, nasan akan yarinyar nan ba abunda baze iya ba"

Nas yace "za'a cigaba da ɗora shi a layi, idan yaƙi ɗaukar haske zega aika aika"
Suka cigaba da hiararsu ta rashin ɗa'a.

Kwanci tashi asarar rai, satin kayan lefe guda cif, duk 'yan uwa dangin Alhaji Abdullahi duk suka zo suka ga kaya, sannan Inna ta shirya ita da Jikarta aka kawo motoci aka kwashe su su da kayan.

Can gidan Alhaji Abdullahi suka tafi da kayan, Nana ta ware ido ta finga kallon gidaje kamar biscuit, kamar a ɗauka a ci dan kyau da tsaruwa.

A ƙauye ana cewa ba gidan da ya kai na Hakimi ƙaruwa, amma yanzu idonta ya gane mata in da ake gidaje.

Da ana zuwa da ita tsohon gidan, amma Inna ta daɗe bata taka ƙafarta gidan nan ba se yau.

Hajiya Hauwa kuwa wato Mother, taji haushin yadda aka taho da 'yan ƙauye, wai za'a kai kayan lefe, abun nan ya baƙanta mata rai a nata faɗar zasu ɓata mata lamari dan ba hankali suka cika ba.

Ba yadda ta iya tunda ga uwar mijinta, kuma shikansa maigidan yana gari balle tai rashin mutunci, tun asalin kai kayan ƙauye ma abun be mata ba, balle kai kayan lefen tare da su, ga ƙawayenta da 'yan uwanta 'yan gayu amma za'a haɗasu da tarkace.

Aka kuma shishshsigo da Akwatuna, Inna tasa aka sassauke kaya aka sake buɗewa, Hakimi ya sa an ƙara atamfofi dozen a ciki, Inna kuma ta saka zobuna da sarƙoƙin azurfa.

Nan aka dinga guɗa ana Allah ya sanya Alkhairi.

Wata ƙawar Mother tace "kai Hauwa, dangin mijin nan naki duk da 'yan karkara ne, amma sun san abunda yakamata, wallahi da nawa dangin mijin ne, sedai a kaisu a haka inma basu saci abunda zasu sata ba, amma kalli aabun arziki kuma atamfofi masu tsadar gaske, su kansu azurfofin nan masu tsada ne sosai"

Tsaki Mother tayi tace "nifa duk abunda za'a saka da mutanen nan ba sonake ba, inma bayarwar ne a aiko dasu mana, kawai an kwashi kaya an kai musu, an kuma kwasowa an dawo, za'a kuma kwasa a kai kaya dasu, ni Allah yasa ba wani abun sukai wa kayan ba, dan ni ba wani yarda nai dasu ba"

"Ke Hauwa, meye aibun hakan? Taɓɗijan, a zaminin nan ki samu dangin miji suna son 'ya'yanka, ai wallahi banga aibun hakan ba"

Tsaki Mother tai, ta cigaba da cika tana batsewa, tana wani basar da su kamar taga bola.

Daddy ne ya shigo tare da Ango, wato Usman.

Take 'yan ƙauyen nan suka kaure da guɗa ana shewa, Alhaji Abdullahi ya dinga murmushi, haka shima Usman ya dinga murmushi.

Alhaji Abdullahi ne ya fara zubewa a gaban mahaifiyarsa wato Hajiya Inna, ya dinga mata kirari sannan ya gaisheta abun gwanin burgewa.

Ya cire hular kansa ya durƙusa a gabanta yace 'barka da zuwa farar uwa me farar aniya, 'ya ga Hakimi mata ga Hakimi, katangar sukari kowa ya jingina dake se ya lasa, farar uwa abun alfahri 'ya'yanta, shalelen Hakimi barka da zuwa uwata ta kaina"

Seda mutanen da ke falon suka saka shewa, saboda abun gwanin burgewa.

Murmushi Inna  tayi, wanda se fararen haƙoranta suka bayyana sannan ta amsa masa "Sannunka ɗan gidan Innarsa, mun sameku lafiya"

"Lafiya ƙalau Inna"

"An shab turai, Usaman Allah ya kawo mu lokacin Aure, Ubangiji Allah ya Sanya Alkhairi"

"Ameen Inna"

Usaman yace "Inna ina wuni"

"Ba zan amsa ba, bayan ba kwa zuwa inda nake"

Usman yace "ba haka bane Inna, kin san ba zaman ƙasar muke sosai ba"

"Eh kuna can kuna yiwa nasara bauta ba, ai shikenan ni gani nazo ai, ina nan har a yi biki ai, ga kaya nan Hakimi ya ƙara maka, yace yana maka murna, se kuma Allah ya kaimu Lokacin ɗauren Aure ze zo"

Alhaji Abdullahi yace "Masha Allah, muna godiya ranki ya daɗe, Allah ya ƙara arziki yasa afi haka"

Nana ce tace "Kawu ina wuni?"

Ɗagowa Alhaji Abdullahi yai ya kalli Nana yai murmushi yace "ai ban kula dake ba, ni yakamata in gaisheki Uwata ta kaina, ina wuni Ummana"

Rufe fuska Nana tayi cike da jin kunya ba tare da ta amsa ba.

Inna ta nuna mata Usman tace "to kin san wannan? Ko kuma baki sanshi ba se me tara gashi?"

Nana tace "Nasan shi mana"

"To ya sunansa?"

Shiru Nana tayi tana tunani, amma ta kasa tunawa.

"Kaga abunda nake faɗa ko ko Abdullahi, bata san sunan 'yan uwanta ba, sedai tace 'ya'yan kawunmu masu tara gashi"

Alhaji Abdullahi yace "Ayi haƙuri Inna, insha Allah za'a san abunyi"

Nana gajiya tayi da zaman, ana ta hira ta tashi dan fitowa harabar gidan ta sake ganin abubuwa.

Ta fito tana ƙarewa motocin dake harabar gidan kallo, bin motocin ta dingayi ɗaya bayan ɗaya tana shafawa, tana sake lelleƙawa.

Ta gaji da wannan ta nufi wani ɓangaren daban.

Leƙe leƙnta ta cigaba dayi, tana zazzagawa.

Motar Prince na shiga gidan, ya fuskanci da yauma da mutane a gidan, tun daga cikin motar yake jan uban tsaki yana cewa aikin banza anzo an cikawa mutane gida, an hanasu sakewa.

Ya saɓo jakarsa ya nufi BQ yana ƙwafa yana masifa, sedai yana shiga falo ya tarar da ita tana tattaɓa ƙatuwar plasma dake jikin bango.

"Ke wace wannan? Uban me kike a nan?!"

A razane ta waigo ta kalleshi tace "yi haƙuri ban san ba'a shigowa nan ba"

Gani yai kamar ya santa amma ya manta inda a santa.

'ke wace irin banza ce, daga zuwa gidan mutane kawai kije inda ba'a aikeki ba, dama kinga mutane na zuwa nan ne?"

Haɗe rai tayi tace "kar ka sake zagina ba nace kayi haƙuri ba" tai maganar tana tura baki.

'dalla zoki fita ki barmin ɗaki, mahaukaciya kawai"

Nana tace "Kut, wallahi kaine mahaukaci bani ba"

"Ni kike cewa Mahaukaci?"

"To uban waye yace ka fara gayamin mahaukaciya?"

"Ubanki ne" ya bata amsa.

"Sedai ubanka bani ba"

Aikuwa ya nufi inda take gadan gadan....

Free pages are not much, hurry up and subscribe yours.

Ayshercool
07063065680.

[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

9_10

Kafin ya cinma ta tuni ta arta a na kare, kamar walƙiyya ta bar falon da gudu, ya bi bayanta sedai yana fitowa ya neme ta ya rasa kamar aljana, se kace iska ta kwashi takadda, ba ita ba alamarta.

Ya ja tsaki ya koma ɗakin, yana ƙoƙarin tuna in da ya taɓa ganin fuskarta.

Ganin hakan ba ze fushsheshi ba yasa ya shige bedroom ɗinsa yana tsaki, gami da jin haushin bikin nan na Yayansa, dalilin wannan bikin da yayime yayimen mutane ake a gidan, masu hankali, sekace akansa aka fara Aure.

Haka yana ƙunƙuni yana mita, ya cire kayan makarantar sa ya shiga yai wanka, ya fito yai sallar azahar, yana son shiga cikin gidan cin Abinci, amma ganin taron jama'a da ke gidan ya hanashi shiga, dan baya son taro sam.

Ya ɗakko tsaleliyar wayarsa ya nemo lambar Khairat ya kirata.

Tana fara ringing ta ɗaga tace "ya akayi?"

Seda ya ɗan yatsuna fuska sannan yace "kina gidanmu ne?"

"Eh ina nan"

"Suwaye a cikin falon nan?"

Khairat tace "ji wata Magana, ta yaya zan iya lissafo maka wanda suke falon, mutane ne da yawa gasu nan a gidan"

"Wani taimako nake son kiyi min"

"Ok am all ears"

"Abinci na zaki kawomin BQ"

Kamar Sadik na gabanta ta ɗan murguɗa baki tace "meya hana kazo ka ɗauka da kanka?"

"Nifa kin san taron mutanen nan ne bana so, in ba zaki kawomin ba shikenan"

"Zan kawo maka ba dan halinka ba"

"In dan halin nawane karki kawomin, bana son wulaƙanci fa"

"Meye wani abun wulaƙanci kuma? Ina zaman zamana ka sani aiki"

Tsaki yayi ya kashe wayar ya ajiye yace "Aikin banza ayi a gama wannan bikin ya tafi ya bawa mutane guri, ko ma huta da wannan jarabar, kullum gida a cike mutum baze huta ba, Aikin banza kawai"

Se mita yake shikaɗai, haka nan ya tuno Nana da ta zage shi ɗazu a falo.

Wani dogon tsakin ya kumayi, ya ji ina ma ya kama Nana, da se ya kusa karyata, seya tataka ta ya koya nata hankali, daƙiƙiyar yarinya fusaka kamar ta yaron aljani.

Shikaɗai ya cigaba da soki burutsunsa, yana zage zage.

Khairat tai sallama ta shigo bedroom ɗin, ta kalleshi tace "lafiya kake tsaki kai kaɗai, tun daga falo ana jiyoka kana masifa ciki ciki"

"Bakomai" ya bata amsa.

"Kai faɗan naka ya kai ka dinga yi kai ka ɗai ma a ɗaki, sekace me aljanu?"

"Ke kika sani miƙomin Abinci na ni"

"Au in maka abun arziki amma ba godiya, se gadara da isa ko, wallahi ka canza hali Sadik, wannan ba halin shiga jama'a bane"

"Ina ruwana da wata jama'a, kawai an takurawa mutane, mutum da gidansu anzo an hanaka sakewa, wai ma dan Allah suwaye yau kuma a gidan nan, dan ni wata mahaukaciya ce ta shigo min ɗaki yau"

Dariya Khairat tayi tace "wace irin mahaukaciya kuma? Gaskiya duk baƙin Gidan nan banga Mahaukaciya ba"

"Ni na ganta ai"

"Gaskiya ba wata mahaukaciya, Kakar ka ce fa tazo da 'yan ƙauyen ku za'akai lefen Dr."

"What!" Sadik ya faɗa yana yatsuna fuska.

" 'yan ƙauye kuma Farhan?"

Cikin mamaki Khairat tace "Farhan kuma? Ka manta sunan nawa ne?"

"Ohh sorry, Khairat nake so ince, meye haɗin 'yan ƙauye da kuma kai lefe? Kai Allah ya sa dai yau wannan tsohuwar zata tafi"

Khairat tace "kakar taku?"

"Ita ɗin mana, tsohuwar nan jarababbiya ce ta ƙarshe wallahi, faɗan tsiya ne da ita ga takurar masifa da sa ido, ni shiyasa ko ƙauyen nan bana zuwa, dama am allergic to the water of the village, ke nifa Even iskar garin nan is irritating me, Abincinsu ma ƙyama yake bani, sam bana zuwa garin nan"

"Taɓ aikuwa tace tana gidan nan har ayi bikin dr."

"Kut, wallahi Farhan barin gidan nan zanyi, ina zan iya da tashin hankali da takura?"

"Farhan again?"

"Ohh sorry, ke nifa Farhan ce a zuciyata da kuma harshena, shiyasa nake kiranki da sunanta"

Ɗan haɗe fuska Khairat tayi tace "wace kuma Farhan?"

"Sirikar mother ce, ana auren dr. Se nawa da Farhan Yarinya"

"Aure kuma Sadik, waze maka Aure Yanzu?"

"Ke dalla ban isa auren bane, ke tashi ki ban guri ma kin sani a gaba, zanci Abinci"

"To ni meye haɗina da cin Abincin ka?"

"Zaki tashi ki barmin ɗaki ko sena ji miki ciwo"

Ta miƙe tace "kana cewa kakarka masifaffaiya, ai kaima masifaffaen ne da be san abun arziki ba, kuma gobe ma rana ce"

Share Khairat yai ya zuba Abincinsa ya fara ci.

Yaci ya ƙoshi ya miƙe tsam, ya haye gadonsa ya fara chatting, tunani yake ina ma Farhan ta na da waya, da ya kirata ya ji muryarta yaji daɗi.

Faruku na shiga falo, ya tarar da Inna ga Daddy da Usman duk a zaune a falon, dam be san da zuwansu ba, ya ƙarasa gaban Inna yace "Sannu da zuwa"

Ta ɗaga kai ta kalleshi tace "Sannunka, ba'a ganinku se anzo inda kuke ko Faruku?"

Ya ɗan shafi sumarsa yace "ba haka bane Inna, ya Hakimi yana lafiya?"

"Yana lafiya, sedai yana mitar baya ganinku"

"Abubuwa ne suka ɗanyi yawa amma insha Allah muna nan tafe"

Inna tace "yadda ka tara wannan gemun ai kyawunta ace kaima da naka auren za'a haɗa"

Daddy yace "haba Inna, guda nawa Faruk ɗin yake? Dan ya tara gemu yarone ƙarami kawai abunsu ne na yaran zamani ya tara wannan uban gemun, amma haryanzu be kammala karatu ba"

"Haka dai, boko boko boko, to boko yana hana Aure ne, in dai yaro yana da yadda zeyi, ku dena yiwa 'ya'yanku kallon yara fa, zamanin nan se addu'a kawai"

Ran Mother ya fara ɓaci ds Inna, a ranta tace "da yake kowa irinku ne, Aure, Aure, da yaro ya fara tasawa besan komai ba se a hau Aure, se tara 'ya'ya nan da nan mutum yabi ya lalace ya tsofe da wuri, saboda ku dai Jima'i shikaɗai mutumin ƙauye ya sani" ta ja gajeren tsaki ta bar falon.

Inna tace "Ni haryanzu banga ɗaya yaron naka ba Abdullahi"

Daddy yace "ina ga be dawo daga makaranta bane"

"Aikuwa dai ina son in ganshi dan rabona da shi na manta"

Daddy yace "a daiyi haƙuri ranki ya daɗe"

"Sadik! Sadik!"

Ya jiyo muryar Faruk na kiransa tun daga falo, tsaki Sadik yayi yace "sekace be san in da nake ba yake min wannan kiran daga waje"

Yai banza ya cigaba da danna wayarsa.

Faruk ya shigo bedroom ɗin yace "kana ji ina kiranka amma kai min banza?"

Sadik yace "na amsa ba ka ji bane kawai"

"Kaje Inna tazo, tana neman ka kaje ka gaisheta"

Yatsuna fuska yayi yace "tana nemana kuma? Me nayi?"

"Se kayi wani abun tukuna? Kajeka gaisheta"

"Nifa yanzu na dawo daga school gaskiya na gaji, Yanzu ina zuwa zata fara ƙaƙalen abunda za tai faɗa a kai, dama ni ba ta sona wannan tsohuwar, kawai ka ƙyaleni"

"In baka je ba, kaga ta ji daɗin hucewa akan Mother, tace ita ke sangarta ka"

Tura baki Sadik yayi ya juya baya, dan karma ya cigaba da jin abunda Faruk ze faɗa.

Se bayan la'asar sannan aka kai kayan lefen nan gidansu Yarinyar da Usman ze aura, iyayenta duk da kasancewa suma masu abun hannu ne, amma sunyi murna sosai sunyi appreciating kayan da aka kawowa 'yar ta su na lefe.

Daga nan gurin kai kayan 'yan uwan su Daddy na ƙauye aka maida su, aka dawo da Inna da sauran ƙawayen Mother gida.

Sadik kuwa be fito ba se bayan la'asar, ya fita ya silale ya bar gidan, ya tafi nasa yawon.

Ɗaki aka bawa Inna ita da Nana a falon ƙasa, ɗakin ba laifi babba ne, da banɗakin sa a ciki, ga gado da katifa a ɗakin, se ƙaramar sif ta kaya.
Nana nata faman taka tsantsan akan abunda za tayi, dan kar tayi abunda Inna zata mata tijara a cikin mutane, dan ita Inna ba ruwanta koba gaban waye idan tai ba dai dai ba faɗa za tai mata.

Sadik kuwa Be dawo ba se dare, lokacin kowa ya kwanta, sannan ya shiga falo ya wuce Kitchen, ya ɗakko Abincin sa ya koma BQ.

Ita kanta Mother ba ta ji daɗin zaman Inna a gidan nan wai se biki ba, dan sam bata son sa ido irin na Inna.

Mother na ta zuba ido taga ɗan auta, amma sam auta be shigo Gidan nan ba, tasan dama ba lallai ya shigo ba saboda mutane da ke gidan.

Dan haka da safe tai niyyar zuwa ta ganshi kafin ya tafi Makaranta.

Nana kuwa ba ta gajiya da ƙarewa gidan nan kallo, saboda tsaruwar gidan ba ƙaramin burgeta yake ba, tana sha'awar cigaba da zagawa da ganin in da ba ta shiga ba ta gani, sedai tana tuno arangamar da su kai da Sadik tai tsaki tace "Aikin banza kawai, Allah yasa kar in kuma haɗuwa da wannan sakaran, idan na kuma ganinsa kuwa nima sena masa rashin mutunci"

Gari ya fara haske, Inna tana can tana laziminta, Nana ta lallaɓa ta fito, masu aiki se kaiwa suke suna komowa, suna ƙoƙarin tsaftace gidan, Suna ta ƙoƙarin gyara komai, Mother na fitowa suka fara ƙoƙarin gaisheta, amma se wani shan ƙamshi take tana amsawa da ƙyar tana cigaba da basu umarni.

Ɓangaren Daddy ta nufa, tarara ya tashi, ya kalleta yace "good morning sweetie"

"Morning dear, ka tashi lafiya?"

Kamar ƙaramin yaro ya ɗan ɓata fuska yace "not that fine, kin gujeni mun dena kwana tare"

"Mutane na kaiwa na komowa, kawai a ganni a ɗakinka ga mahaifiyar ka a gidan nan"

"Ina ruwan Inna damu, ai ita ba ruwanta damu, yakamata kije ku gaisa, ni naje na gaisheta kuma tana mitar Sadik be zo ya gaida ita ba"

Mother tace "ai kasan halin ɗan naka, shifa mutane ne ba ya so, ni kaina ban ganshi ba tun jiya, yanzu nake sa ran zuwa in dubi shi ma, zan sa yazo ya gaisheta"

"Ai gara yazo su gaisa, kar ranta ya ɓaci"

A ranta tace "jarababbiyar tsohuwa ba, yanzu se ta samu a gaba da ɗana da surutu" amma a zahiri tace "insha Allah zan tura shi, me zan dafa maka ne?"

"Komai ma kika dafa ni ci zanyi, am missing Your food, komai kika bani zanci"

Tai murmushi tace "shikenan ina zuwa"

Ta jiya ta fito, Nana cikin masu aikin nan su talatu ta shiga, tana tai musu surutu da tambayoyi, tace su bata ta taya su mopping, amma suka hanata.

Sedai surtun nata dariya yake basu, Nana Akwai baki, amma duk da dariyar da suke Mother na fitowa, suka nutsu suka cigaba da abunda suke.

Nana ta kalli Mother tace "Ina kwana"

"Lafiya" Mother ta amsa da ƙyar.

Ba ƙaramin haushi Nana taji ba da yadda Mother ta amsa nata gaisuwa, Nana a ranta tace "aikuwa za'a daɗe ban kuma gaisheki ba"

Ta jiya ta fita harabar gidan, abun sake burgeta yayi, duk yadda yake da hadimai a gidan Hakimi, amma wannan sun sha banban.

Saboda an fito da wasu daga cikin motoci ana wankewa, ga masu gyara flowers, suna basu ruwa komai gwanin ban sha'awa.

Nana ta ƙarasa gurin me wanke mota tace "Dan Allah ka bani abun zuba ruwan nan in wanke motar nima"

Dariya yayi ya kalleta yace "kina mace zaki wanke Mota, ai wannan aikin maza ne"

"To ai iya zuba maka ruwan kawai zanyi"

"A'a ba ruwana, ai ba aikin mace bane"

Nana tace "to me bawa bishiyoyin nan ruwa idan nace ya ban ze bani, ai naga mata ma zasu iya yi"

'je ki tanbaye shi kiji"

Ba musu ta nufi inda dattijon kewa Flowers ban ruwa, tace "dan Allah nima zanyi"

Waigowa yai ya kalli Nana yace "ke jikar Inna, wannan aikin ai ba naki bane"

"Kai ya akai kasan ni jikar Inna ce?"

Yai dariya yace "kai ai tun kina zanin goyo nasanki, kuma gaki nan kamar ki ɗaya da ita sak"

Nan ta cigaba da zuba masa surutu kamar wadda aka ƙona a ka.

Faruk ne ya fito da gajeren wando da vest, da gani motsa jiki yayi yace "Baba Ilu sannu da aiki"

Baba yace "yawwa Faruku"

Nana a ranta tace "ikon Allah, ji wanan ƙato ba kunya ƙwauri duk a waje yana yawo a cikin gida, duk tsiraicin sa a waje"

Ya kalli Nana da ta ƙura masa ido yai murmushi yace "kin tashi lafiya?"

Ɗaga masa kai tayi alamar eh, yace "Yama sunan naki?"

Tace "Nana"

Yace "Ohh yeah, Naana exactly, weldone Naana"

Yai maganar yana tafiya, ita kuwa binsa tai da ido tace "iyayi, Nanan ma baza'a faɗa yadda kowa ke faɗa ba se anyi wani iyayi, maganar ma da wani iyayi ake yinta, waisu lallai turawa'

Daga ƙarshe ta koma ƙirga motocin dake harabar gidan.

Mother ta shiga ɗakin Sadik, ta tarar yana saka belt ɗin sa na Uniform.

Yana ganin Mother yai murmushi yace "good morning mother"

"Ba zan amsa ba, yaushe rabon da kaje inda nake?"

"Hmm mother kenan, kema kin san bana son taron mutanen nan, kowa sekabi kana gaishehi ana wani kallon mutum, ana surutu that's why kawai naƙi shigowa, but am really missing you"

Yai maganar tare da kissing ɗin hannun Mother.

Ta kalleshi tace "naji, but kasan Granny ɗinku ta zo ko?"

Yatsuna fuska yayi yace "na sani"

"Amma ba kaje ka gaisheta ba? So kake tazo ta sani a gaba da masifa tace ni na hanaka zuwa ka gaisheta"

Cikin shagwaɓa da sangarta yace "Mother kin san fa ni matar nan ta tsaneni wallahi"

"Haka nan dai zakai haƙuri kaje"

"To yanzu na saka Uniform, kar in makara zanje school, idan na dawo zanje"

"Yawwa Son, safe journey ka kula da kanka"

Ya jinjina kai ya cigaba da shirinsa, ita kuma Mother ta fice daga ɗakin.

Seda ya kammala shirinsa tsaf, ya fito Falo ya tarar Mother ta ajiye masa Abincin sa, ya zauna yai breakfast sannan ya fito dan tafiya makaranta.

An fito da motar da ake kai Sadik makaranta, motar tayi fes se ƙyalli take kamar sabuwa.

Tun daga nesa ya hango Nana a jikin motar, tana leƙawa tana zagaye motar tana shashshafa motar.

Prince na hangota ya tunkaro inda take a fusace, "Ke meye haka! Ƙazama a wanke motar kizo kina taɓawa, wallahi kika sa min datti sekin wanke ta"

Wata uwar harara tai masa tace "motar banza motar wofi, an shafa dattin, sedai ka mutu"

"Ke ni kike gayawa haka? Wallahi zan tattka ki banza Mahaukaciya kawai"

"Seka takanin in gani ai, kuma an shafa dattin, ta tofa miyau  a jikin motar ta zura da gudu tai cikin gidan.

Sadik ya tsaya soror yana kallon motar, ba abun yabi Nana ba ya sake makara, yai ƙwafa ya buɗe motar ya shiga, ranasa a ɓace yana tunanin kalar rashin mutuncin da ze mata.

Shikam Musa direban Sadik, kamar ya tuntsure da dariya, saboda abunda Nana tai masa, amma ya gimtse dariyar sa, kar yayi Sadik ya masa rashin Kunya.

Sadik na zuwa makaranta ya samu guri ya tsaya a gurin Assembly, yana jin yadda su Nas suke masa Magana, amma yai shiru yaƙi kulasu.

Farhan na ta leƙe ta hango abun ƙaunarta, sedai yadda ta ga fuskarsa tasan yana cikin damuwa, ransa a haɗa babu alamar fara'a sam a tare da shi.

Jikinta se yai sanyi ta shiga tunanin meya sami Prince haka yai wannan mugun haɗe ran haka?

Aka sallame su daga Assembly ground, suka tafi aji.

Suna zuwa aji, malamin da suke da shi ya shiga ajin, dan haka abokan Sadik basu samu damar tambayar sa abunda ke damunsa ba.

Har malamin ya koyar da abunda ze koyar ya fita, Prince yana tsaki lokaci zuwa lokaci, gaba ɗaya ransa a jagule yake.

Taslim ce ta fara magana tace "Allah ya temaki Yarima, what's wrong with you know? You look somehow disturbed"

Tsaki ya kuma yi tare da ɗan hura hanci, ya gyara zamansa.

Amin yace "yeah, that's what I want ask since, kika rigani meke going ne?"

Prince ya ɗan nisa sannan yace "wallahi mutane ne suka zo suka cika mana gida, harda wata mahaukaciyar yarinya, kidahuma 'yar ƙauye"

Nas ya kwashe da dariya yace "kai Prince, wannan cin mutuncin fa? Ba relative ɗinka bace?"

"Ni nama san wacece? Ni na manta in da nasan ta ma gaba ɗaya, kawai ganinta nai a gidan nan, wata fitsararriya 'yar ƙauye"

Amin yace "kai harka kira wata 'yar ƙauye, ai budurwarka ce 'yar ƙauye"

Sadik yaiwa Amin wani warning glance, ba shiri yace "Ohh am sorry i dont mean to hurt you"

Sadik yace "Ai se nayi maganin yarinyar nan dan na tsane ta gaba ɗaya bana son ganinta"

Taslim tace "to aini har Yanzu banji abunda tai maka ba"

Nan Sadik ya basu labarin abunda Nana tai masa, daga jiya zuwa yau, sosai suka dinga dariya, hakan ya ƙara bawa Prince haushi, dan haka ya tashi ya bar ajin.

Ajin su Farhan ya tafi, sedai suka haɗu a hanya, ya zuba mata idanunsa seda ta ƙaraso in da yake sannan ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta.

"Lovely meyasa ba ki zo ajinmu ba yau?"

"Na ganka ɗazu a gurin assembly kamar ranka a ɓace, shiyasa ban zo ba"

"Amma Farhan ki ganni a cikin damuwa amma ki ƙi zuwa in da nake, baki damu da halin da nake ciki ba kenan ko?"

"A'a ba haka bane, naga idan kana fushi baka son aje in da kake ne"

"Kuma se akace miki hadda ke? Da kinzo da tuni na manta da abunda ya faru, kin barni wancan Nasir ɗin sun sani a gaba suna sake bani haushi, dan dai ban biye musu bane"

Farhan tace "am sorry, kayi haƙuri dan Allah"

Yai murmushi yace "bakomai, ai matata bata laifi"

Jin maganar tasa tayi wata uwar gundumemiya, wai matarsa ba ko kunya, shi baya jin kunyar wani yaji yana faɗar irin wannan maganganun sam.

Suka jera suka tafi har ajinsu Farhan, a can ya zauna suka dinga hira, yana bata labarin kayan da aka kaiwa yayansa na lefe yace "ji nai kamar in ƙwace kayan nan a kai gidanku, ace na aurenmu ne Ni da ke Farhan"

Shiruu tai ba tace Komai ba, kuma ba ta ɗago idonta ba.

"Farhan, wai meyasa a duk lokacin da nai miki irin wannan zancen kike yin shiru ne, ko dai ba kya sona ne?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To meyasa ba kya son in miki Wannan zancen?

Tai shiru ba tace komai ba, ya gyara zama yace "Look Farhan, ina da kuɗin da zan iya yin Aure, kuma wallahi ni dagaske nake sonki Farhan, dan Allah ki dena doubting a kaina Please"

Ta sake jinjina masa kai yace "Yawwa,  zaki ci wani abun ne?"

Tace "A'a"

Ya zira hannu a aljihunsa ya ɗakko dubu biyu ya ajiye mata.

Zare ido tayi za tai Magana amma ya haɗe rai yace "shhhh" ya juya ya fita ta bi bayansa da kallo.

A varrender ajinsu Farhan, ya haɗu da Sir Nazir, Nazir ya tsaya ya bishi da ido, Sadik ya haɗe rai sosai, ko kallon inda Nazir yake be ba ya wuce.

Tunani Farhan ta shiga yi akan ya za tai da wannan kuɗin da ya bata?

Ba tai aune ba taji mutum a kanta, tana ɗaga ido ta ga Sir Nazir, yace "wato ba ki rabu da wannan yarn ba ko?"

Ɗan tura baki tai, ta sunkuyar da kai.

"Wai ke dan Allah da ma haka kike da taurin kai ne? Waima meyake gaya miki da ya sa kika liƙe masa haka? Ko kuma me kuke yi da yasa kullum se yazo in da kike?"

Ƙin ɗago kanta tayi da ga sunkuyar war da tayi.

"Kije ki cigaba da biye masa karki fasa, nan gaba idan ya gama morar ki, ze watsar da ke ne, a lokacin ne zaki nadama mara amfani, wannan yaron sam ba tarbiyya ce da shi ba, ɓata miki lokaci ze a banza"

Babban abunda yake ɓatawa Farhan rai be wuce duk wanda suke soyayya a makarantar nan ita kadai ya sawa  ido ba, kuma abun takaicin be wuce yadda yake dizgata a gaban kowa ba, saboda Prince.

Nazir na fita Yasmeen ta ja tsaki tace "nifa wannan mutumin ya fara ɓata min rai akan abunda yake wa Farhan, ya fiye sa ido da takura wallahi"

Lilly tace "ke bake kaɗai ba nima haka wallahi, ni yana burgeni yadda ya iya dressing ga shi kyakykyawa, sedai ya fiye shishshsigi, ni da ni yakewa haka wallahi da tuni nayi maganinsa dan ba zan ɗauka ba sam"

Ita dai Farhan ba tace musu komai ba, can Yasmeen tace "ku akwai labari fa"

Lilly tace "labarta mana muna jinki"

"Wallahi Sister na naji suna hirar Wani book, so romantic ina son in samo Book ɗin nan"

Hasina tace "haba dan Allah ki ɗakko mana mu karanta mana"

Yasmeen tace "dalla a wayarta ne fa, kuma ni ban san sunan littafin ba, amma yadda naji suna hirar littafin na manyan kai ne"

Lilly tace "ke dalla muma manyan kan ne, ki samo mana kawai"

"Ku bari zan ɗau wayar tata in duba mana"

Haseena tace "saura ki shanya mu, kiƙi nemo mana"

"Dalla ni na gaya muku fa, zan nemo mana shi"

Suka cigaba da taɗin su.

Kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki, haka Farhan ta koma gida, zuciyarta fal tunanin Prince, dan lokacin da aka tashi daga school, akwai Malami a ajinsu Prince, dan haka ta samu ta tafi gida.

A gidan ma kasa sukuni tayi, tana son samun wanda zata tatauna Maganar Prince da shi, amma babu ita ba me son yawan Magana bace, ba ta damu da yawan surutu ba, dan haka ko ƙawaye ba ta da su sedai 'yan makarantar su, suma ɗin ba kula su take ba, Ga mahaifiyarta ba ta sakar mata fuska sam, dan haka ba yadda za'ai ta tunkare ta da Maganar Sadik.

Tana son tabattar da waye me gaskiya tsakanin Prince da Nazir, dagaske RUƊIN ƘURUCIYA ce soyayyar da suke? Ko kuma soyayyar da Prince ke nuna mata gaskiya ce?

Gaba ɗaya ta rasa wane tunani ma Yakamata tayi, ta buɗe tsakiyar litattafan ta, ta saka 2k ɗin da Sadik ya bata, tana sake jin wani irin shauƙi yana fizgarta akan Sadik ɗin.

Yauma a gajiye Sadik ɗin ya koma gida, ya kwaso gajiya matuƙa idonsa har lunshewa yake saboda gajiya, gashi yau ne ranar da ustaz ɗin dake masa lesson ze zo.

Ya canza kaya kenan, sega kiran Mother a wayarsa, yana ɗaga wayar tace "Sadik wato seka janyo min zagi agurin wannan tsohuwar ko? Ba zaka zo ka gaisheta ba se raina ya ɓaci kenan?"

Seda ya tura baki Sannan yace "Yi haƙuri gani nan"

Ya ajiye wayar yana cigaba da kumbura baki.

Ya fito ya nufi cikin gidan yana tura baki, ya haɗu da Khairat.

Ya kalleta yace "ke wai kullum sekin zo mana gida ne?"

"Lallai daɗinta ma muma muna da gidan ai"

Murmushi yai ya janyota jikinsa yace "Sorry Sisto na, wasa nake miki fa"

Nana dake hango su ta window ta buɗe baki tace "taɓ ga 'yan iska, Allah yasa Inna ta gani, kut ya taɓa ta taɓɗijan, dama wannan yai kalar 'yan iska"

Inna na zaune a falon Sadik ya shigo, tun da ya shigo Inna ta ƙurawa Sadik ido, cikin majestic walk ɗinsa ya ƙaraso, ya ɗan durƙusa yace "Sannu ina wuni"

Inna ko ƙyafta idonta ba tayi ta kafe shi da ido, dan seda ya fara tsarguwa tace "Sannu Abubakar"

Ya shafi sumar kansa yace "yawaa an zo Lafiya?"

"Ban sani ba, tun jiya ina gidan duk 'yan uwanka sun zo sun gaida ni amma banda kai, kuma ance min kana nan"

"I was little bit busy that's why"

"Ni ba gane wannan Yaren nasaran nake ba ai, wannan wane irin aski ne haka a kanka?"

Ya shafi kan yace "suma ce kawai"

"Wannan uban gashin kamar ɗan daudu? Kai ko damunka baya yi, ni yaushe ka girma har ka tara wannan gashin haka ma? Rabona da kai yafi shekaru uku, uwarku ba zata zo ba kuma ba zaku zo in damuke ba ko?"

Mother tace "A'a ni bana hanansu zuwa, ya za'ai in hanasu Zuwa inda kuke?"

"Idan ba ki hana su zuwa ba ai baki koya musu zuwa ba ko?"

Sadik yace "wannan garin me uban sauro ga ruwan garin ɓata ciki yake ya za'ai mutum yazo"

Inna tace "ba shakka ba yadda za'ai a zo kam, be kamata azo ba kar ruwan garin ya kashe mutum"

Inna tai maganar cikin gatse.

Sadik ya sake cusa baki, Mother tana ta masa signing akan ya kintsa bakinsa.

Inna tace "kafin in bar garin nan ina son a rate wannan sumar ta kanka tunda kai ba mace bane, kuma ba kitso za kai ba"

"Inna wanan sunar na asketa ai ba kanta, wallahi kuɗin da nake kashe mata yafi kuɗin dokunan gidan Hakimi"

"Lallai kam naga alama, tashi kaje Allah ya shirya"

Ya miƙe ya juya abunsa ze fita, sedai sukai karo da Nana tana ƙoƙarin shigowa falon, ta zuba masa miya a riga.

Ya kalleta a Mugun fusace yace "ke! Wace irin dabba ce ke? Baki da hankali ne mahaukaciyar ina ce ke?"

"Kar ka sake cemin Mahaukaciya, kai baka gani ne, kana tafe kana kallon sama"

"Wai dan Allah wannan banzar 'yar waye, daga ina take? Waya kawo mana Mahaukaciya gida, wallahi na tsani ganin Yarinyar nan"

"To kasheni ka huta, fitsararre"

Inna na ƙoƙarin tashi ta ƙarasa inda suke, ya shaƙo hijjabin Nana!

Don't Miss this book wooo, akwai damalamalin cakwakiya 😂😂😂

Domin Sharhi gyara Ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:     🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                            11_12

Tuni Sadik ya shaƙe Nana da hijjabinta, dan da ƙyar take iya numfashi ma, ta ware maƙogwaro ta dinga rafsa uban ihu.

Da hanzari Inna ta yo kansu, Mother ma ta taho da Sauri tana faɗin "Sadik meye haka? Baka da hankali ne?"

Inna tace "saketa kar ka kashe ta"

Zuciyar Sadik se tafasa take saboda takaici, ji yake kamar ya cigaba da shaƙeta seta suma tukuna.

Da ƙyar Sadik ya saki Nana, Inna tace "ba shakka ka kyauta, 'yar uwakka ka shaƙe haka kake cewa ka tsaneta, jinin ka ce fa kuma dan rashin kunya da rashin ta ido, a gaban nawa kake iƙrarin ka tsani 'yar uwaka, lallai ga illar rashin zumunci ai"

Saroro Sadik yai, se yanzu ya tuna in da yasan Nana ma, shi tun asali Nana ba tai masa ba, lokacin da ya santa tana yarinya sosai, tun tasowarta idan suka je ƙauye idan ya ganta haushi take bashi, mussaman yadda take shagwaɓaɓɓiya, ga tsiwar tsiya ga shegen ci, kuma ba'a isa a taɓata ba saboda son da Hakimi yake mata, amma yayi mamakin ganin girman da tai, tayi tsawo sedai halinta yana nan.

Mother tace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi Halin Sadik se a hankali, in kika bibiya be ganeta bane shiyasa"

"Eh ai dama baze ganeta ba, tunda tana ƙauye shikuma ba zuwa ƙauye yake ba, amma tabbas da dangin ki ce ba yadda za'ai yace be santa ba, yayi kyau"

Mother taja hannun Sadik suka fice daga falon.

Inna tace "ke kuma dan ubanki in rashin kunya abun yi ce gobe ma ki sake, se da nace ba zan taho da ke ba amma ya dage in taho da ke, kije ki cigaba da neman Magana da rashin nutsuwa ya illata ki a banza a wofi kan mu bar gidan nan"

Gefe Nana ta koma ta zauna ta na kuka, dan taji shaƙar da Sadik yai mata ba kaɗan ba.

Mother kuwa suna fitowa da Sadik tace  "Sadik meyasa ba ka gudun magana ne? Allah kaɗai yasan iya ɓacin ran da zaka jamin saboda abun da ka aikata, meyasa kake da baƙar zuciya ne kamar haka?"

Cikin takaici Sadik yace "Mother, kalli jikina fa kalli yadda ta ɓatani da miya, tun jiya na ga Yarinyar nan, take zagina ni na manta ma in da na taɓa ganinta se yanzu, gaba ɗayan ta Mahaukaciya ce"

Mother tace "Koma mece ce Ni dai ka lallaɓa mu rabu lafiya, karka jamin magana"

Sadik be kuma cewa Komai ba, ya wuce ya nufi ɓangaren su kamar ya fashe da kuka dan takaici.

Inna kuwa sosai ta cigaba da yiwa Nana faɗa, akan rashin nutsuwa da rashin zama guri ɗaya da ba tayi.

Inna tai faɗanta son ranta, Nana kuma ta ƙule Sosai ta ƙuduri aniyar se ta yiwa Sadik rashin mutunci ta rama abun da yai mata.

Khairat kuwa da akan idonta komai ya faru, ta fi jin haushin Nana, dan ta fuskanci Nanan ba dai rawar kai ba, ga iyayin tsiya.

Nana tana nan a gefen ƙafafuwan Inna, tai zuru tana kallon tv amma ba tv take kallo ba, tana son ta fita ta sha iska, amma tasan tana fita Inna zata zageta tsaf, koma tace zata daketa.

Har la'asar suna nan a Falo, Alhaji Abdullahi ya fito daga sashen sa, ya fito falon, yazo ya samun Inna cikin girmamawa yace "sannu da hutawa Inna"

"Yawwa sannunka"

Ya kalli Nana da tai tsuruu a bayan Inna yace "Mamana, ya na ganki a haka? Na ganki wani iri"

Inna tace "eh nina hanata fita"

'amma Inna meyasa, ko bari tai walwala mana gidansu ne fa nan"

"A'a ba dai gidan su ba, a gabana ba kunya ɗan autanka ya shaƙeta, wai shi be ma santa ba, Wannan rashin zumunci har ina Abdullahi, ace  'ya'yanka basu san ƙanwarsu ba, ko bayan ran mu wa take da su ban da kai da iyalinka?"

Mother kuwa wani takaici ne ya ƙuleta, anyi abun nan ta bawa Inna haƙuri amma ta zaunar da Daddy tana maida yadda akayi.

Daddy yace "subhanallah, Sadik ɗin ne yace be santa ba?"

"Zan masa ƙarya ne? Haka yace be santa ba, amma na tabbatar da a dangin mahaifiyar sa take baze ce be santa ba, gaskiya Abdullahi yana da kyau ka sake sa ido sosai akan iyalinka, wannan halin na Sadik sam be min ba, kun sangarta shi da yawa ba shi da ɗa'a sam"

"Ayi haƙuri Inna, insha Allah za'a gyara"

Ya kalli Nana yace "Amma ayimin afuwa, an takura Mamana da yawa, bari mu ɗan fita tare da ita"

Inna tace "sekun dawo"

Yai murmushi yace "taso Mamana"

Da murna Nana ta tashi, Daddy ya riƙo hannunta, suka fito harabar gidan.

"Mamana ajinki nawa ne?"

Nana tace "Ajina shida, daga wannan hutun zan shiga Sakandire"

"Masha Allah, Yarinya ta girma, Allah ya temaka"

"Ameen" ta amsa tana kalle kallenta.

Alhaji Abdullahi ya ɗakko wayarsa ya nemo lambar Sadik.

Sadik na ɗagawa Daddy yace "kana ina ne?"

Sadik yace "Ina BQ"

"Fito waje ina son ganinka"

Mintuna kaɗan sega Sadik na tahowa, sedai yana hango Nana a kusa da Daddy ya haɗe rai hadda hura hanci.

Ya ƙaraso yace "Daddy gani"

"Sadik, wai baka san Nana ba?"

Sadik ya galla mata harara yace "Eh amma na tuno ta daga baya"

"A gaskiya banji daɗin abunda ya faru ba, Inna ta yi min complain da kai Sadik, gaskiya ban ji daɗi ba"

"Daddy nifa ba abunda nayi, kawai kasan dama ni ta tsane ni, ba ta sona kawai, tana son Dr. Da Faruk amma ni ta tsaneni kuma wannan 'yar ai itama ba ta da kunya"

Daddy yace "ba wannan na kiraka ka gayamin ba, na kiraka ne in ƙara jadadda maka, Nana ƙanwarka ce kamar Yadda Khairat take ƙanwar ka, bana son sake jin kunyi rigima ko ka gayamata wani abu mara daɗi ka ji ko?"

Sadik fuska a cunkushe ya jinjina kai, sedai yana ɗago kai Nana tai masa gwalo, sannan a ɗan sanyaye tace "kuma ma da ya shaƙemin wuyan hijjabi na, seda na dena numfashi, wuyana ma Ni yanzu ciwo yake min, da ƙyar nake haɗiye miyau"

Daddy yace "Ya Salam, kiyi haƙuri ze dena insha Allah, dan Allah ku dena faɗa 'yan uwa ne ku"

Sadik A ransa yace "Allah ya kiyaye wannan me kama da cartoon ɗin ta zama 'yar uwata, shegen bakinta kamar ramin tsutsa'

Daddy yace "bari mu fita shan icecream tare, ku ƙara sanin juna a dena faɗa"

Sadik yace "Please Daddy, i scheduled to be with my friends by 5:00pm, if you don't mind i wanna be with them"

"We must go together!" Shine amsar da Daddy ya bashi.

Sadik kamar yai bindiga, haka yasa direba ya fito da mota suka fita tare, Sadik da Nana a baya, Daddy a gaban mota.

Suna tafe a hanya da ya waigo ya kalli Farhan, se wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarsa, Nana kuma suna haɗa ido zata murguɗa masa baki hadda fari da ido.

Ji yake tamkar ya turata waje ta window kowa ma ya huta.

Daddy yace "Mamana, idan kin girma me kike son zama ne?"

Seda Nana tai wani ƙasaitaccen murmushi ta ɗanyi fari da ido sannan tace "Ina son in zama 'yar jarida, in din ga aiki a gidan Radio ina karanta labarai, ko in dinga hira da mutane, in dinga karanta labarai da turanci"

Daddy yace "wow masha Allah, Allah ya cika miki burin ki Mamana, da kin kammala sakandare insha Allah za'a samo tsadajjiyar jami'a kije kiyi karatun insha Allah"

Murmushi tayi tace "Kasan a wace gidan radion nake son in dinga karanta labaran?"

Yace "A'a"

"Ina wannan radion da Hakimi yake kaiwa yana ji da Asuba? Da kuma da rana rana haka"

"BBC ko America?" Abba ya tambayeta yana murmushi, dan ya san Hakimi da son jin BBC.

Tace "Yawwa BBC, kasan da Asuba suke hira da hausa, idan haka rana ta ɗanyi idan aka kunna sekaji suna turancin turawa, to irin wannan nake son nima in dingayi, in dinga labarai da turanci ina maƙale muryata"

Sadik ya ja wani uban tsaki, dan gaba ɗaya Nana ba ta gajiya da surutu, bakinta ko ciwo ba ya yi, tai ta zuba kamar wadda aka kunnawa ashana a ka.

A hankali Sadik yace "sedai aikin gidan radion jakai shi zaki, ba dai na masu hankali ba"

"Ai kai ne jakin" ta faɗa tana hararar Sadik.

Sadik yace "ke da wa kike?"

"Da kai nake, waye yace kace min Jaka?"

"Nike nace miki jakar?"

Daddy yace "A'a ya faɗa kuma a gabana? Ba yanzu na gama yi muku nasiha ba akan faɗan nan?"

Nana tace "cemin yai Jaka"

Sadik a buɗe baki yana kallon Nana, wato bayan hauka hadda makirci ma Nana ta iya, in ba haka ba yauhse yace mata Jaka.

Daddy yai ta musu faɗa, yayin da Nana ta cigaba da gallawa Prince harara hadda murguɗa baki.

Suka je wani babban store, Daddy ya saiwa Nana kayan ciye ciye, sannan suka nufi komawa gida, Sadik be kuma cewa komai ba, Nana ne da Daddy suke ta hirar su tana masa shirme kala kala yana biye mata.

Alhaji Abdullahi yana da son yara sosai, amma baya sha'awar ya tara su da yawa, sedai duk in da ya ga yaro ƙarami yana jansa a jiki ya kyautata masa.

Se daf da magariba sukaje gida, Nana ta rungumi kayan da aka siyo mata ta kasa da gudu.

Masaukin su ta nufa kasancewar ba ta ga Inna a falo ba, tun daga waje take ƙwalawa Innar kira, sedai tana shiga ɗakin kallon da Innar tai mata yasa ta nutsu.

"Gudun me kike yi haka?"

"Bakomai"

"Ban hanaki wannan guje gujen ba, a Wannan sakarcin naki kika zubawa wancan yaron miya a jiki, shine yanzu ma kike maimaitawa ko? Bari in sa a kira Hakimin ya turo a ɗauke ki a maida ke gida"

"Dan girman Allah kiyi haƙuri, na dena ba zan ƙara ba"

Inna tace "da dai halinki ne ban sani ba, kiran me kike min?"

Nana tace "kinga abunda aka saimin"

Inna tace "kince masa kin gode dai ko?"

"Eh na masa godiya"

"To amma dai ki dena wannan guje gujen"

"To na dena insha Allah"

Da magariba ma Daddy yasa Sadik a gaba sukaje masallaci su kai salla, suna tafe yana masa Nasiha akan haƙuri da son zumunci, yai masa faɗa sosai yace masa Inna ba tsanarsa tai ba, amma ya dinga zuwa yana gaida Inna.

Shi dai Sadik be ce komai ba, yai shiru yana sauraren Daddy, amma shi duk wani abu da ze haɗa shi da Inna ba so yake ba, saboda ta fiye ƙaƙalen abun da za tai faɗa.

Da safe ya shirya tsaf ze tafi Makaranta, ya tuna kashedin Daddy, ɗan gajeren tsaki yai ya ɗau jakarsa ya kai mota, sannan ya tafi cikin gida.

Ɗakin Mother ya fara zuwa, yaje ya gaisheta, ya zauna yai breakfast sannan ya fito, ya nufi ɗakin Inna.

Yana zuwa ba Sallama ya shiga ɗakin, ya tarar Inna tana lazimi, Nana kuma nata bacci akan gado.

"Ina kwana" shine abunda ya faɗa a taƙaice.

Inna ta ƙare masa kallo sannan tace "lafiya ƙalau"  tana amsawa ya  miƙe ya bar ɗakin ba tare da ya kuma cewa komai ba.

Yau ya makara sosai a makaranta, dan har an kammala assembly sannan yaje school ɗin, miƙewa yai da nufin ya tafi ajinsu, yaji an masa tsawa daga bayansa.

Tsayawa yai ya waiwaya yaga wane ke masa wannan ihun haka.

"Why are you always coming late ne?"

Sadik ya watsa masa harar ya gyara jakarsa, ya cigaba da bin Nazir da kallon banza.

"Am i talking to robot? Ba Magana nake maka ba?"

"To me kake so ince maka, nifa gaskiya kana takuramin, ina ruwanka dani ka bi ka samun ido ka addabeni, kamar nikaɗai ne ɗalibi a makarantar nan, gaskiya bana son haka ka fita a sabgata na gaya maka"

"Ni kake gayawa haka?"

"To waye kai da baza'a gaya maka ba?"

Yana gama maganar ya nufi ajinsu yana tsaki.

Nazir yabi Sadik da kallo yana jinjina rashin tarbiyya na ɗaliban makarantar.

Yana zuwa ajin nasu ya tarar ba malami a ajin, kowa se harkar gabansa yake, gaban aji kuwa Nas ne da wata 'yar SS3 suke wani dancing challenge ana musu video, se ihu ake ana musu tafi.

Sadik ya ajiye jakarsa ya zauna, yana kallon su Nas, Nas ya kalleshi yace "Prince, ranar bikin Brother ɗinka Akwai casu wallahi, gaskiya yakamata ka shirya mana special party iya na 'yan school ɗin nan"

Sadik yai murmushi yace "nayi wannan tunanin nima, dole ma ayi special party da za'a gyagije, kan kuzo Dinner bikin"

Amin yace "idan hakane kuwa, na ga tallan wasu wanduna, Yakamata muyi order ɗinsu latest crazy jeans masu kyan gaske"

Sadik yace "nunamin in gansu"

Nan suka zauna, Amin ya nuna musu wandunan, Sadik yace "gaskiya sunyi kyau, ni blue ɗin nan nake so ɗan 15k ɗin nan, ku kuma zan muku order na 10k ɗin nan kuyi ankon su"

Shewa suka ɗauka a gurin, Taslim tace "omo What do you mean? Mu ɗin kuma fa"

Sadik yace "in dai zaku sa se ayi order da ku"

Meena tace "mw ze hana? A siya damu"

"Shikenan duk wanda ze je partyn, a saka order da shi, zan sa a bugo riguna polo, amma kowa siyan riga ze dan ubanku"

Dariya su kai, Nas yace "nasan iya wuya ba tafi  5k ba, na saiwa mata goma riguna, amma fa se zafafa wanda suka cika mata, wadda idan ta saka kayan nan za'a ga kaya"

Taslim ta buga wani uban ihu tace "yeee ina cikin wanda za'a saiwa riga ko ba'a so, dan na kai mace wallahi"

Nas yace "ba ƙarya muma mun seda ai"

Shewarsu suka cigaba da yi, suna ihu, suna cigaba da tsara rashin jin da za suyi a gurin party.

Knocking ɗin ƙofar ajin akayi, Sannan aka shigo.

Director ne ya shigo, shida wasu 'yan bautar ƙasa, maza uku mata biyu, sedai matan kiristoci ne, dan kansu ya sha ƙarin gashi.

Tsit sukayi suka gayara zamansu, Director yace "my dearest And beloved student, can't you greet?"

Seda yai Maganar, sannan suka gaishe su gaba ɗaya.

Nan ya gabatar musu da 'yan bautar ƙasar nan, a matsayin sababbin malamai.

Nan suka gabatar da kansu ɗaya bayan ɗaya ga 'yan ajin, bayan sun gama gabatar da kan nasu ne, Director da kansa ya dinga gabatar musu da ɗaliban da kansa, kowanne ya gabatar da shi da matsayin mahaifinsa.

Seda suka kammala yai musu jawabin da ze musu, akan su bawa malaman haɗin kai, dan samun ilimin da ya dace.

Meena ce cikin harshen turanci da iyayi, ta wakilci 'yan ajin ta yi musu barka da zuwa, da tabattar musu da za su basu Dukkan haɗin kan da suke buƙata, dan gudanar da aikinsu.

Wani fari daga cikinsu wanda ya gabatar da kansa a matsayin Nura daga Kogi state, shima cikin harshen turanci ya wakilci 'yan uwansa, yai musu godiya da irin karɓar da a kai musu.

Daga nan kuma suka bi Director suka fita suka nufi wani ajin.

Suna fita Meena tai murmushi tace "Subhanallah"

Taslim tace "ke lafiyarki kuwa?"

Meena tai murmushi tace "Taslim kinga abunda na gani kuwa?"

"Me kika gani?"

"Wallahi I fall for that guy"

"Wane guy kuma?"

Taslim tai maganar tana kallon Meena.

"That fair and tall Man, Nura looking very beautiful and energetic, wallahi yai min"

"Ke bana son iskancin banza fa"

"Ke wallahi ba ƙarya nake ba, before nafi ganin kyan corper Nazir, Amma yanzu naga abunda zuciyata ke so wallahi"

Taslim tace "Nifa daɗina da ke 'yar bala'i ce ke, ki rage leƙe leƙe wallahi"

"Ba wani leƙe leƙe ƙyaleni kawai"

Nasir kuwa cigaba da batun bikin yayan Sadik sukayi.

Yau Farhan ba ta zo gurin sa ba, dan haka da kansa ya kuma tafiya nemanta, sedai ya tarar ta kifa kanta akan benci, kamar me bacci.

Ƙarasawa yai a hankali, ya ɗagota da ga kwanciyar da tayi.

Hakan ya firgita ta sosai, ta shiga rarraba ido amma ba tace komai ba, yace "Am sorry na miki laifi, na firgita ki gashi na taɓa ki ko?"

Ba ta masa ba, ya samu guri ya zauna daf da ita yace "Honey meke damunki ne? Naga idonki yai ja"

Ji tai kamar Sadik ya taɓo mata inda yake mata ƙaiƙayi, tana da damuwa But she has no one to discuss with, she's developing some changes in her breast, suna mata zafi wasu lokutan, sedai ta kasa ganewa, is it the normal stage of puberty, ko kuma wata matsala ce daban, dan tana jin ana wayar da kai akan breast cancer, dan recently anyi taro a makarantar, na wayarwa da mata kai, akan ciwon sanƙaran mama, amma ita ta kasa gane a wani hali take? Gashi ba yadda za'ai taiwa Ummanta zancen, gashi ba wanda za ta iya gayawa damuwarta, a yanzu haka duk da ta na kwana guri ɗaya da Ummanta ta tashi, amma Babu wanda take da kusanci da shi a yanzu kamar Sadik, sedai shima ɗin Maganar tayi matuƙar nauyin da ba zata iya tambayarsa ba.

"Lafiya naga kin yi shiru kina kallona? What's wrong ki gayamin please"

Ajiyar zuciya tayi, cikin sassanyar muryarta tace "bakomai fa"

Ya kwaikwayeta yace "ban yadda ba gaskiya"

Hakan ya bata dariya da seda tai murmushi, yace "oya gayamin ina jinki"

"Dagaske nake bakomai, bacci nake ji ne"

'ba kya bacci sosai ne a gida?"

"Eh ina yin karatu da daddare"

"Wow that's very good ai, amma ki dinga rangwantawa kanki kinji Hubby na, bikin yaya na ya kusa, za'ayi events da aka shirya a gidan mu, amma akwai party da zan organising, so akwai kalar outpit ɗin da za'a saka, ayi order dake zaki saka?"

"A'a baza'a barni ba a gidanmu"

"Ok ba damuwa, nasan dama ba lallai a barki b, but I just decided to tell you ne, amma dai ko sau ɗaya zaki zo ko?"

"Eh Insha Allah"

"Yawwa my wife"

Sunkuyar da kai tayi ƙasa, dama yasan hakan ne ze faru, dan wannan kalaman nasa nauyi suke mata.

"Farhan" ya kira sunan ta.

"Na'am" ta amsa.

"Next week zan karɓo exams card ɗina, na kusa Barin makarantar nan Insha Allah"

Ai da sauri ta ɗago ta kalli Sadik tace "dan Allah dagaske ka ke?"

"Am serious, zanyi Waec ne in kammala karatuna akan lokaci"

Take jikin Farhan yai wani irin sanyi, ta kasa cewa uffan se dai damuwa ta bayyana ƙarara ta mamaye fuskarta.

"Farhan" ya kira sunanta.

A sanyaye ta kalle shi, yace "kin san meyasa nai haka? Duk cikin planing ɗina ne na in mallake ki, dan Allah Farhan kar ki kalli hakan da wata fuska daban, i really love you wlh, duk saboda nake wannan fighting ɗin, kimin addu'a samun nasara, bari in tafi aji kar Wannan jarababben mutumin yazo yai min masifa"

Ya tashi ya kalleta yace "I love You baby" ya kashe mata ido ɗaya ya juya ya fita.

Ai yana fita ta bawa hawayen da take ta kokawa da su damar zubowa, ta kifa kanta kawai ta fara kuka ƙasa ƙasa.

"Yanzu idan Prince ya dena zuwa Makarantar nan ya za tayi, a duk ranar da ba ta ganshi ba, tana shiga mummunar damuwa, se gashi ze bar makarantar gaba ɗaya, nan hawaye suka cigaba da zarya a kuncinta, ta sa hanky tana gogewa, tun a lokacin taji ta fara kewar masoyin nata, take ta manta da damuwar ta ta farko dake damunta.

Shi kansa Sadik tunda ya gaya mata yaga damuwa a fuskarsa, ya shiga damuwa shima, take yaji wani irin tausayinta ya kamashi sosai, shikansa ya san zeyi missing ɗinta, sedai barinsa makarantar ba yana nufin ya bar Farhan ba, akwai yiwuwar ya fara neman Hanyar cinma burinsa, na aurar wadda yake so a Wannan shekarun.

"Idan ka aureta Yanzu tata rayuwar fa? Karatun ta fa?" Wata zuciyar ta tambayeshi.

'ta ƙarasa a gidana' ya bawa kansa amsa.

Da gudu ta sheƙo ta kan varrender, tana ƙoƙarin ƙarasawa ajinsu "Lilly! Lilly" tsayawa Lilly tayi tana kallon Sir Nazir dake ta ƙwala mata kira kamar mafarauci.

"Why are you running like this? Where is your jacket?"

Ta kalli jikinta daga ita se inner shirt, da skirt ɗin ta iya gwiwa, ta cire jacket ɗin ta ajiye a aji, ta kalleshi tace "tana aji"

"Meyasa kike yawo a haka? Baki san kin fara girma ba, kuma kina gudu a cikin yara haka? Ga hijjabin ki ƙarami, Why are you exhibiting childish behavior, don't you know you are at your Adolescents period, you have to maintain your body?"

A ranta tace "ji ɗan iska, seka gayamin a Adolescents period nake, ai nima na sani"

Ta tura baki cike da sangarta.

Yace "idan na kuma ganin kin kuma cire jacket ɗinki kina gudu haka, sena zane ki, wuce ki ban guri"

Tafiya tayi tana yatsuna fuska.

Tana zuwa Ajinsu tace "hmm ƙawayen amana kun san abunda ya faru kuwa?"

Haseena tace "ya za'ai mu sani se kin faɗa"

Lilly tace "mhmm wannan sir Nazir ɗin ne na taho da gudu ya wani tsaida ni, wai meyasa nake yawo ba jacket nake gudu, wai ban san na fara girma bane na shiga Adolescents period, kuji min ɗan air mutum"

Shewa suka yi Haseena tace "Ya ƙyasa ne yaseen, shine ya gaza shiruu seda ya tanka, ya tsaida ke ne kawai dan kawai ya sake kalla sosai"

Ihu suka saka gaba ɗaya, tai wani juya tai girgiza tace "gani ba taɓawa ba asarar ido, nan gani nam bari ɗumamen mayya, kuma wallahi yawo ba jacket yanzu na fara, ke ni fa na kusa dena saka wannan ɗan hijjabin ma, haka zan dinga yawo, mutum ya kalla ko kuma ya runtse idonsa"

Yasmin tace "to Allah ya temake ka abubuwa sun fara fitowa ace ba zakai gayu da abunka ba, wani abun ma se munje Final year lokacin sun gama fitowa, lokacin ne zega yadda ake abu, yadda zamu addabi makarantar nan, ai ya gani ya kasa shiru shine ya tanka miki, sun tsole masa ido"

Lilly tace "aikuwa in hakane ya shiga tara mutumin nan, dan sena ganshi ma zan dinga kasawa da gud"

Yasmin tace "ai base kinyi gudu ba, kya yiwa kan ki ɓarna ai, kina tafe kina ɗan bada style ma ya isa, ban gaya muku ba ma, na fa samo mana littafin nan, ku kunji abubuwa a ciki kuwa"

Haseena tace "dan Allah dagaske ko da wasa?"

"Wallahi dagaske nake, ke kunga yadda aka fayyace komai ban dai karanta ba, page ɗaya kawai na karanta, amma naji sena zo da wayata mu karanta tare, kai akwai tafasassun abubuwa a littafin nan"

Lilly tace "shegiyar kaya, ai a kawo mana littafin nan, muji abubuwa kawai"

Su kaita shewa, ita kam sam Farhan hankalinta baya kansu, hankalinta kacokan yana kan maganar da sukayi da Prince ɗinta.

Shikansa Prince har aka tashi jikinsa a sanyaye yake, yaje ƙofar makarantar ya tsaya yana jiran fitowar Farhan.

Aikuwa ya hangota ta fito daga cikin makarantar, idanunta sunyi jawur sosai, tana tafiya a hankali, daga inda yake tsaye yake kallonta, kullum ƙara girma take tana kyau abunta, sheɗan ne ya fara ƙawata masa ita, da ɗarsuwar wani abu daban a ransa, take yace "Subhanallah" ya dawo hayyacinsa.

Tana ɗaga ido sukai ido huɗu da shi, murmushin dole tai masa, yace "ke muke jira taho mu tafi gida"

"A'a zan tafi ai"

"Bana son gaddama fa"

Ba yadda ta iya haka ta bishi ta shiga motar, suna tafiya yace "Anya ba kuka ki kai ba, naga idonki ya ƙara ja"

"Ba kuka nai ba, dama ina ciwon ido wani lokacin"

"Ciwon ido, lallai ma ashe makauniya ce matar tawa, gaskiya sena rage sadakin da zan bayar" yai maganar yana murmushi.

Direba ko a ransa yace 'ikon Allah, ji wani kwaɗo da fitsara wai ita game saurayi ta shiga motarsa yana mata kalaman banza na RUƊIN ƘURUCIYA, banda haka ina Sadik ina wata budurwa dan kawai yana ganin ya na da tsawon ƙafa!?"

Seda suka kai Farhan gida sannan suka wuce gida, babban abunda yaiwa Sadii daɗi be wuce yadda yau gidansu ba mutane ba, hakan yai masa daɗi sosai.

A ƙofar shiga BQ ɗin su ya haɗu da Dr. Ya kalleshi yace "Sadii yau kamar ba ka dawo da wuri ba, ina ka tsaya ne?"

Sadik yace "mun sauke Farhan a gida ne, sannan muka taho?"

"Wace kuma Farhan?"

"My wife to be insha Allah" Sadik ya faɗa kansa tsaye.

Usman yace "kasan me kace kuwa?"

"Eh mana na sani, budurwata ce da nake burin Aure, kuma insha Allah daga bikinka se nawa"

Usman ya jinjina kai yace "ba laifin ka bane, tashen balaga ne da RUƊIN ƘURUCIYA, ke ɗibar ka"

Sadik yace "tashen balaga kuma? Oho koma dai menene, I mean what I say wallahi"

Yana gama maganar ya wuce Usman, ya shige.

Usman ya bishi da kallo, kawai ya girgiza kai, ya juya ya nufi in da motocin gidan suke.

Sadik yai wanka yai salla, ya tafi ganin Mummynsa, sedai yana zuwa ya tarar ba ta nan wai ta fita.

Haushi ne ya kama shi ya shiga Kitchen, ya tarar Khairat na dafa indomie, tana yi tana bin wata waƙa da ke tashi a wayarta.

"Ss ke 'yar bainu" yai maganar da sigar tsokana.

Waiwayowa tai ta kalli Sadik, tace "ka ga karka kuma cemin 'yar bainu"

Yai murmushin yace "ke dallacan uwar fushi, ina Mother ta tafi ne?"

"Nima ban sani ba, da Mummy ta ɗakkoni daga makaranta tazo ta ajiyeni suka fita tare"

"To dafa indomie da ni, tunda Mother ba ta nan"

"Baza'a dafa ɗin ba, 'yar bainu ta dafa maka"

Dariya yayi yace "ke akwai zazzafan party da bikin dr. Fa, zamu shirya na 'yan school ɗin mu, kema za'a baki Card in da wanda zaki gayyata"

Tsalle tai tace "wow, dole muje ai, kai za'a cashe fa Prince"

"Ke dalla can, har wata rawa kika iya?"

"Taɓ kaji ka, wace kalar rawa ce ban iya ba? Wallahi na iya rawa"

Sadik yace "To yi mu gani, kuma in baki iya ba ba inda zaki"

Yai maganar yana ciro wayar a aljihunsa, ya duba wayar ya saka mata waƙa, take Khairat ta fara rawa tana juyi, tana karairaya jikinta.

Tafi ya fara yi mata yace "ba ƙarya kin iya, zaki je gurin partyn nan, let me join you"

Nam suka shiga rawa shida Khairat a Kitchen, ya riƙe hannun Khairat yaana juaya ta suna rawa tare, kamar yaran turawa.

"Lalalala! Innalillahi taɓɗijan, dama abunda kuke yi kenan? To wallahi sena gayawa Inna kuna abunda be dace ba, kuna taɓa juna bayan tace ba kyau.

Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                              13-14

A tare Khairat da Sadik suka juyo suna kallon Nana, dake tsaye tana musu kallon banza.

Khairat tace "is this girl serious?"

Sadik yace "A beg forget about her, she's mentally abnormal"

"Nima na gani"

Cikin tsiwa Nana tace "Wallahi Inna ta hana, tace babu kyau, kwata kwata babu kyau irin wannan abun, amma kai kuma kazo kana taɓata, tace marasa tarbiyya ne suke haka, kuma Allah ze fushi da mutum, Allah ya hana amma ka ke aikatawa, wallahi se na gaya mata"

"Dan ubanki tsayuwar  me kike a gurin baki tafi gayamatan ba? Kifi ruwa gudu banza da baki kamar mazirari"

"Kaine banza bani ba wallahi"

Ta juya ta tafi ɗakinsu da sauri dan ta sanar da Inna.

"Innarmu, Inna" ta shiga ƙwalawa Innan kira.

Inna tace "Ya akayi meye kike kirana haka?"

Se kuma Nana tayi saroro ta kasa Magana, kawai ta basar tace "kawai nemanki nake"

"Dan kina nemana seki biyoni da wannan kiran Kamar wata sa'arki?"

"To yi haƙuri"

"Naƙi haƙurin"

Nana ta ɗan sosa kai, ta nemi guri ta zauna.

A yanzu Kusan duk lokacin da Sadik ze shiga gida ya haɗu da Inna, se tai masa faɗan wani abun, kodai na sumar kansa, ko rashin son mutane, ko kuma taɓara, saboda haka yana dawo wa daga makaranta, yake ficewa yawon sa baze dawo ba se dare, se ya tabbatar da Inna tai bacci, se ya shigo ya ɗau Abincin sa ya fice ya bar falon, in ma Mother ze gani ya ganta a lokacin.

Wasu lokutan da ya fara ɓuruntu ze ɗau Abinci Nana ke farkawa daga bacci, ta fuskanci baya shigowa se kowa yai bacci, dan haka ta sa ido sosai ta lura be zo ɗaukar abinci da wuri ba, dan haka ta gane se daren ze zo ya ɗauka.

Har sun kwanta bacci, Nana ta daidaici Inna tai bacci, ta miƙe cikin sanɗa ta fito falon, ta janyo ƙofar falon ta rufe, ta kulle da mukulli ta ciki, ta nemi guri ta kunna TV tai zamanta tana kallon cartoon.

Wajen sha ɗaya da rabi na dare, Sadik yazo yana murɗa ƙofa ze shigo dan ya ɗau Abinci, amma yaji a rufe gam.

Ya jinjina ƙofar yaji ta a kulle, nan ya shiga ƙwanƙwasawa, nan ma ba wani respond.

Yayi mamakin yadda aka rufe ƙofar falon haka, dan ba'a cika rufeta ba, ko da yaushe tana buɗe, saboda ita ce babbar ƙofar da zata sada ka da kowane sashi na cikin gidan, amma abun mamaki yau an rufeta.

Ya zaga ya ɗaga labulen window, yaga koda wani a falon, ya hango hijjabin ta akan 2 seater, yana ganin hijjabin yasan itace, saboda kullum haka take yawo cikin hijjabin nan kamar me takaba, be taɓa ganin ta cire shi ba, kullum da hijjabi take yawo.

"Ke malama zo ki buɗe min ƙofar nan"

Banza tai dashi taƙi ko waigo wa balle ta kalleshi.

"Wai ba magana nake miki bane?"

"Ka nemi ke ta zo ta buɗe maka" ta bashi amsa

"Dalla ki buɗe zan ɗau Abinci"

Tasowa Nana tai, ta nufi inda yake tsaye a window tace "ba za'a ɗakko ba ɗin, idan kana son cin Abincin ka dinga zuwa da wuri kana ɗauka, base ka gama gantalin ka ba sannan kazo kana ɓuruntu kamar ɓera ka tasheni daga bacci ba"

Buɗe baki yai yana mamaki yace "tunda gidan ubanki ne ai dole ki samun doka"

"Ai dama bance Gidan babana bane, gidan babana yana ƙuaye ya mutu, ya barni a gidan Hakimi"

"Ke bana son iskanci, dalla ki buɗemin"

"Wallahi ba zan buɗe ba taimako ɗaya zan iya yi maka"

Ta juya ta nufi dining, ta ɗakko ragowar bredin safe, taje kitchen ta buɗe fridge ta ɗakko ruwan sanyi, Sadik ya zuba mata ido yaga me za tayi.

Ba kunya taje ta zura masa bredi da satchet water tace "ga shi nan, amma kar ka sake zuwa ka damemu"

Galala yabi bredin da kallo da tsananin baƙin ciki da takaici, Nana kuma ta kashe fitilar falon tai tafiyarta.

Ji yai tamkar ya karya ƙofar ya shaƙe Nana, yai mata dukan da seta kasa motsi.

Cike da ɓacin rai ya koma BQ, ya tarar dr. Na zaune yana waya, se wani kashe murya yake cike da tsantsar shauƙi da Soyayya.

Sadik ya kalleshi ya ɗanyi guntun tsaki, ya wuce ya duba fridge ya samo cake, da lemo ya koma ya zauna akan 3seater, yana tura cake ɗin nan kamar ze fashe da kuka.

Gefe guda kuma Usaman na sake ƙular da shi, yadda ya nannaɗe murya yana zuba taɓara a waya, duk haushi ya cika shi, se tsaki yake yana hararar Usman, wanda be san me Sadik ɗin yake ba.

"Jeddaty, kamar in janyo Ranar Auren nan haka nake ji, zuciya ta ta kasa nutsuwa da samun sukuni, am about to loose control fa"

"Na fika ƙaguwa Nurain, sedai kayi haƙuri mu jira lokaci, kamar yaune zaka ga yazo, duk abu in dai an sama sa lokaci yanzu zaka ga yazo"

"Hakane Baby na, are you not sleepy?"

"No am not, when am with you, i keep everything aside, kai kaɗai zuciyar take kallo"

"Hmm Beb, yakamata ki kwanta dare ya fara yi fa, But are you on bed?"

"Yeah"

"Are you sure?"

"Quite sure Dear"

"So how do you dressed up, for today's night"

"I just wear my night gound"

"Ok am going to my room now, let me have a 1picture of you with the night dress, so that I can sleep well"

"Ohhk my Baby, as you wish"

Duk wannan wayar da Usman yake a gaban Sadik yake yin ta ba kunya ba Komai, Sadik ya dinga binsa da kallo, harya ta shi ya bar falon gaba ɗaya.

Ji yai ya dena jin ɗanɗanon cake ɗin, dama cin da yake na dole ne, ya miƙe shima ya koma ɗakinsa, ya nemi guri ya kwanta, sedai ya shiga tunani me zurfi, da kwaɗaituwar son yaga hoton da za'a turawa Usman ɗin.

Ina ma Farhan na da waya, da ko ba komai idan yaji muryarta ze ji daɗi a ransa, amma dai yasan ko kusa Farhan ba zata turo masa hotonta a kayan bacci ba, duk da ba mace a gidansu, amma yasan kayan Bacci na mata ba wasu kayan Kirki bane suke sawa, dan mafi akasari kayan baccin yana bayyanar da wani sashi na jikin su ne.

Take zuciyarsa ta cigaba da azalzalar sa, da ƙawata masa abubuwa daban daban, mussaman Farhan ɗin sa, ina ma ko sau ɗaya shima yaga hoton ta a night gound, ko yaya yana son ganin wani sashi na jikinta, a cikin kyakykyawar fatarta me ɗaukar ido.

Rumtse idonsa yai sosai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya furta Farhan, yai ruf da ciki ya rirriƙe pillow ɗin da yake kai, a hankali ya dinga faɗin "Subhanallahi wabi hamdihi, subhanallahil azeem"

A haka bacci yai awon gaba da shi, sedai kasancewar ya saka abun a ransa, se ga Farhan a cikin baccin sa, a yanayi me wuyar fassara.

Yadda ya kwanta da wannan matsanancin tunanin, haka ya dinga mafarkai barkatai har Asuba, kiran farko ya buɗe idon sa, ya jiƙe sharkaf da gumi, duk da A.C da ke ɗakin nasa.

Tashi yai yayi shiru yana tunanin mafarkin da yai, jinsa yai somehow abnormal.

Tunani ya shiga yi yanzu se yayi wanka kenan? Amma ai mafarki ne kawai, shiru ya kuma yi yana tunani, ya ɗakko wayarsa ya shiga yai searching, tabbas wanka ya kama shi since he has a dreams.

Tsaki ya ɗanyi, ya sakko daga kan gadon, a gurguje ya shiga banɗaki yai wanka yai alawala, ya fito ya zura rigarsa, sedai yana gamawa sega Faruk ya shigo ɗakin nasa, ya kalli Sadik yace "Au ashe ka tashi? Sarkin nauyin bacci, yau anyi abun arziki, dama Daddy ne yayo waya, amma ya nake ganin kanka kamar a jiƙe?"

Tsaki Sadik yai yace "Alwala nayi fa"

"Alwalar ce ka ke a jiƙe haka, kalli jallabiyar taka fa duk ruwa"

Banza Sadik yai masa, ya ɗau turare ya fesa a jikinsa, ya saka hullar tashi ka fiye naci.

Faruk ya kwashe da dariya yace "inyee, Su Auta an girma, iyee sekace wani magidanci wanka da Asuba haka, Lallai ka girma ka isa Aure, na yarda da batunka na cewa da kake ka isa Aure"

Haɗe rai Sadik yai yaƙi cewa uffan, a falo suka haɗu da Usman shima ya fito, suka fito suka tafi masallaci, sedai suna tafe Faruk yana tsokanar Sadik, Sadik ya ƙulu matuƙar ƙulewa, amma yaƙi cewa komai dan kar Daddy ya fuskanci wani abu.

Da suka dawo daga sallar ma Sadik be koma bacci ba, ya nemi guri ya zauna yana ta tunani kala kala daban daban a zuciyar sa.

Haka ya zauna har gari yai haske, ya shirya ya fice dan tafiya makaranta, ba tare da ya shiga ko cikin gidan ba balle ya karya yai musu sallama, direbansa ya fara jan motar kenan ya hango Nana ta fito, se yanzu ya tuna abunda tai masa daren jiya, tabbas ba dan ya riga ya shiga mota ba da Allah kaɗai ze iya raba shi da ita yau, se kuma ya tuna yana taɓata ze sha tujara a gurin kakarsa, kuma Daddy ma ze masa faɗa, ƙwafa yayi dan ko me za'ai sedai ayi amma se yai maganin ta.

Haka ya tafi makaranta yana ƙananun sambatu.

Farhan ta shirya tsaf cikin Uniform ɗinta, sedai a jikinta tana jin tana ƙara ƙiba, dan skirt ɗin da ta sa tana jin yadda ya matse ta sosai, ta juya ta juya ta ƙarewa kanta kallo a madubi, ji take kamar ta cire shi ta canza wani, amma ɗaya skirt ɗin ba a goge yake va gashi ta makara sosai.

Ta ɗakko ƙaton hijjabin ta ta ɗora akan Uniform ɗin sannan ta fito tsakar gida, ta kalli Ummanta da ke kaiwa tana komowa a tsakar gida tace "Umma na tafi"

Ba ta kalli in da Farhan take ba tace "Allah ya kiyaye" cikin yanayin sanyin halin ta, ta wuce ɗakin mahaifinta, se da tai sallama akai mata izinin shiga sannan ta shiga.

Tace "Abba ina kwana"

"Lafiya ƙalau Farhan, za'a tafi makarantar ne?"

"Eh Abba zan tafi"

Ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko Naira ɗari ya bata yace "ga kuɗin makarantar ki, Allah ya tsare kin karya dai ko?"

"Eh Abba na karya"

"To shikenan, Allah ya kiyaye hanya, ki kula da kanki ki kula da addinin ki da mutuncinki kinji Farhan"

"To Abba insha Allah, nagode Sosai"

Ta miƙe ta fito, a soro ta tsaya ta buɗe jakarta ta ɗakko turaren da ta siya da kuɗin da Sadik ya bata, ta shashshafa a jikinta, dan tana matuƙar son ƙamshi a rayuwarta, sedai ummanta bata damu da ta ɗorata a hanya da yadda zatai amfani da kayan gyaran jiki ba, ko da yake yaushe ma ta kulata balle ta koya mata wani abu makamancin haka.

Ta gama shafawa ta maida shi jakarta, sannan ta fita ta nufi titi.

Gaba ɗaya Sadik yau kamar mara lafiya haka yake jinsa, yama rasa gaba ɗaya meke masa daɗi, duk yadda abokansa suka so jansa da surutu amma yaƙi magana, ƙyaleshi su kai, dan sun san haka yake yi wasu lokutan.

Ana ta shirye shiryen fara jarrabawa a makarantar, wasu malaman duk sun ƙarƙare darususskan su, wasu sunyi teses ɗin da duka zasu yiwa ɗalibai, zasu fara jarrabawa.

Farhan ta kasa fita daga ajinsu ma, gani take kamar ita za'a dinga kallo idan ta fita saboda yadda skirt ɗinta ya matse ta sosai, gashi bironta ya ƙare tana son siyan wani, haka ta daure ta fita siyan biron, sedai shop ɗin a kulle yake.

Kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Prince ta karɓi aron nasa.

Ta ɗau littafinta ta fita, taje ajin nasu sedai tana shiga ta duba gurin zamansa ta ga baya nan, ita ba iya sakewa take da 'yan ajinsu ba, dan haka ta nemi guri kawai ta zauna tana jiran dawowar Prince ɗin.

Gudu gudu sauru sauri take hawowa step ɗin benen, jacket ɗinta na riƙe a hannunta ɗaya, ɗaya hannun kuma na riƙe da jarkar youghurt, yana daga saman benen a cikin malamai yake hangota tana hawowa, ilahirin jikinta na rawa, kanta a ƙasa ba tsammani tai karo da shi a tsaye yana kallonta.

Ƙoƙarin kaucewa tayi amma yaƙi ba ta hanya, yace "What did I told you last day?"

Kallon hannunta tai da ta riƙe jacket ɗinta, ta kalli jikinta ta ɗan yatsuna fuska tace "sir zafi nake ji shine fa na cire ta"

"Shut up! Bance karki sake cire jacket ɗinki ki tafi haka ba?"

Ta yatsuna Fuska tace "kace"

"Shine kika cire rigar kike yawo da ita a hannu dan rashin kunya ko?"

Shiru tayi tana zumɓura baki taƙi Magana, yace "oya wear it back"

Tana harararsa ta gefe haka ta maida rigar, sannan ya batta ta tafi.

Tana barin gurin tace "ɗan rainin hankali kawai" ta sake cire rigar ta tafi aji.

Corper Nura yace "Nayi matuƙar mamakin ganin irin wannan dress code ɗin na student, a garin Kano"

Nazir yace "ai ba kai kaɗai ba, abun da mamaki kam kamar ba garin musulmi ba, kalli yadda suke yawo kamar ba musulmai ba, kuma babban abun takaicin an rasa me musu magana akan wannan shigar ta yaran, kuma su kansu iyayen suna kallo amma sun yi shiru"

Nura yace "amma hakan be dace ba, ze iya buɗe ƙofar ɓarna a tsakanin malami da kuma ɗaliban kansu"

Nazir yace "ai kai kaga haka, su ba wannan ne a gabansu ba, su makarantar burinsu yadda zasu samu kuɗi, su kuma iyayen burinsu ace yaransu na makaranta me tsada, amma ɓarna kam a makarantar nan sedai ai shiru kawai"

"Subhanallah, Allah ya kyauta"

Nazir ya amsa da "Ameen"

Farhan kuwa gajiya tai da zaman jiran Prince, ga shi 'yan ajin se fitsara suke kala kala a gabanta, dan haka ta tashi zata bar ajin, harta fito taji yace "See me here"

Ta waiga taga yana tahowa a hankali kamar mara lafiya, tai murmushi tace "ina ka tafi ne na daɗe ina jiranka fa"

"Naje cin Abinci ne ina jin yunwa, kuma nasan idan nazo ma nace ki rakani ba zaki bini ba"

Tai murmushi ta koma ajin nasu, tana gaba yana binta a baya, sedai shima ya lura da yadda take tafiya a kunyace saboda yadda skirt ɗin ya matseta sosai.

Seda ta tsaya ya zauna sannan itama ta zauna, tace "dama pen nazo ka aramin, naje in siyo shop a rufe"

Murmushi yai yace "in baki pen dai ba in baki aro ba"

Ya zura hannu a aljihunsa ya ɗakko sabon biro ya bata ta karɓa tace "Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"

Be magana ba se jinjina mata kai da yayi, ta zauna tana ta 'yan rubuce rubucen ta, da alama tana solving maths ne, shikuma ya ƙura mata idanun sa, ko ƙiftawar kirki ba ya yi, se wata irin ajiyar zuciya yake.

Ta kalleshi "baka da lafiya ne?"

Ya girgiza masa alamar a'a.

"Amma na ganka wani iri yau"

"Am sick" ya bata amsa a hankali.

"Meke damunka"

Be magana ba ya lumshe idanunsa, ya kuma buɗe su a kanta.

Cikin damuwa tace "dan Allah meke damunka?"

"Nothing, cigaba da aikin ki"

Jiki a sanyaye ta cigaba da rubuce rubucen ta, tana monitoring ɗin Sadik ɗin.

Can aka jima ya tashi ya bar seat ɗin, ya koma baya ya kwanta akan wani benci.

Gaba ɗaya Farhan ta damu, ta tashi ta bishi tace "Ko Clinic zan raka ka su dubaka?"

"No zan ware insha Allah"

"To kaƙi gayamin meke damunka"

"Idan na gayamiki zaki min wani kallo na daban, just forget about it, kije class ɗinku kar Malami ya shiga"

Taslim ta kalli in da suke tace "lallai yau ana jin soyaya, sedai naga fuskokin masoyan ɗauke da damuwa"

Kallonta kawai Farhan tayi, ta tashi ta bar ajin cike da damuwa tana tunanin meya sa Prince a wannan mood ɗin haka?.

A ƙofar ajinsu taga Dodon nata wato Sir Nazir, ya tsareta da ido ta maze tare da ƙi ɓoye tsoronta, "Allah ya shiryeki, ina tausayawa rayuwar ki a nan gaba"

Farhan ba tace Komai ba ta wuce cikin ajin nasu, dan ita bata damuwa da duk surutun da Nazir ze mata akan Sadik.

Seda duk aka koma aji sanna Meena ta kalli Taslim tace "Ke nifa na tafi in je inga ta ina zan fara kaiwa gayen nan hari"

Taslim tai murmushi tace "jarababbiya idan me taurin kai ne kamar Naziru wahala zaki sha a banza a wofi"

"Shi ya isa ma, shi ma Nazirun dan ban dage bane, amma da shi ɗin banza"

"Hmm to ai shikenan maji ma gani"

Meena ta miƙe ta gyagyara zaman Uniform ɗinta ta fice.

Sadik ya rasa abunda yake masa daɗi, ya taso da niyyar ya koma gurin zamansa ya zauna, sedai idonsa ya sauka akan Taslim, da ta ɓalle botir ɗin sama na rigarta, wanda hakan ya bayyana wani sashi na ƙirjinta, dan kana iya ganin jar kalar brezia dake jikinta, ta nutsu tana danna waya.

Wani uban tsaki Sadik yaja ya kauda kansa, wanda seda ya janyo hankalin wasu daga 'yan ajin kansa.

Cikin muryarta me cike da iyayi Taslim tace "Prince what's going on ne? Gaba ɗaya yau ajin nan ba daɗi saboda mood ɗinka, what happens ne?"

Be ce mata uffan ba ya ɗauke kansa daga kallonta, mafarkansa na jiya ne kawai suke dawo masa kansa, zuciyarsa na ta raya masa abubuwa daban daban, na arziki da na banza.

Ganin Sadik ba shi da niyyar yin magana yasa Taslim ta ƙyaleshi, s cigaba da danna wayarta.

Mubarak Babba ne ya shigo class ɗin, ya nufi inda Taslim take, yana zuwa ya kalleta yace "you look sexy today Beb, kinyi kyau sosai"

Wani killer smile tayi, ta ɗan kashe masa ido, ta cigaba da danna wayar, zama yai kusada ita yasa hannu ya karɓe wayar yace "kalleni mana, ina Magana kina danna waya"

Hararsa tai tace "dan bani wayata"

"Sekin kalleni zan baki"

Idonta cikin nasa ta kalleshi tace 'na kallka yanzu bani wayata"

Wani irin kallo yake mata sanna yai murmushi yace "kinga abunda na turamiki jiya?"

"Ban gani ba"ta bashi amsa.

"Why?"
"Z" ta faɗa tana hararsa.

"Naga dai alama haryanzu fushi kike dani, duk da na baki haƙuri, shikenan in kin huce ma daidaita, But before ya kamata a rufe nan"

Ya kai hannu ƙirjinta, ya rufe botir ɗin ta dake buɗe tare da kashe mata ido.

Zumɓura baki tai taƙi kallonsa, ya gama surutansa ya fita.

Meena kuwa safa da marwa ta dinga yi a sashen Office ɗin da Corper Nura yake, can cikin sa' se gashi ya fito da litattafai a hannunsa, da marker da alama aji ze shiga.

Tace "good afternoon sir" waigowa yai ya kalleta yace "Afternoon how are you"

"Fine sir"be jira abunda za tace ba yai gaba abunsa, haushi n ya kamata na tafiyar da yai b tare da ya sake kallonta ba.

"Hey fine girl, what are you doing over there?"

Ta juya ta a wake magana, ɗaya daga sababbin corpers ɗn da suka zo tare da Nura ne, me suna George.

Ta ɗan haɗe rai tace "Nothing"

"But you are suppose to be in your class now, Why are you here?" Yai maganar yana sake ƙare mata kallo kamar maye.

Tsaki taja ta bar gurin, shikuma yabi bayanta da kallo yadda take tafiya, ƙwaurinta duk a waje ga matsatsen skirt da ɗan ƙaramin veil.

Ya jinjina kai yace 'lallai makarantar nan akwai 'yanmata'

Tana tafe tana tunanin ya zata ɓullowa Nura kuma.

Ta koma ajinsu tana zancen zuci.

Farhan ana tashi ta tafi ƙofar ajinsu Prince ta tsaya, tana nan tsaye se gashi ya fito, ta kalleshi tace "Sannu"

Yace "yawwa"

"Kawo jakar in riƙe maka"

"No kar in ƙara miki nauyi mu tafi kawai"

"A'a ka kawo tunda ba ka da lafiya"

Ta karɓi jakarsa ta haɗa da tata, Nas yace "shege Prince, a ɓoye dai ka gama da zuciyar ƙwailar nan, ta gama faller maka wallahi"

Wata uwar harara Farhan taiwa Nas, Nas yace "ke ni kike harara? Dan kina zuwa ajinmu ki zauna na ƙara ganinki a ajin sena ɓallaki"

Prince yasa hannunsa ya kamo na Farhan, sedai yana yin hakan yaji zuciyarsa tana harbawa da sauri, ita ma nata ɓangaren hakan ne, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai.

Sadik ya dake yaja hannun ta, su kai gaba.

Nas yace "Lallai Prince Mugun ɗan rainin hankali ne, yanzu har wannan 'yar ta fara wayewa ni zata harara"

Mubarak babba ya shafa fuskarsa yace "Yarinyar nan ba ta taɓa burgeni ba sam, ni hasali ma haushinta nake ji, amma yau tunda na ɗora idona akan hips ɗinta raina ya biya, Uniform ɗinta na yau sunyi pitting ɗin ta sun mata kyau sosai"

Amin yace "kaifa Babba wani lokacin Akuya ne, Kamar ya ranka ya biya?"

"Kamar yadda na faɗa mana"

Nas yace "Allah yasa Taslim ta jika"

"To taji ɗin seme? Dole wannan yaron ya liƙe mata, shiyake ganin abunda ya gani, sedai na ga shi kamar soko ne"

Wani wanda suke aji ɗaya da Mubarak me suna Ahmad yace "kai me kake nufi ne Babba?"

"Zan kauda damuwata ne" ya faɗa yana murmushi.

Nas yace "kai kamarya, wai kana nufin kai a yanzu haka kasan mata?"

"Me za'a fasa? Kana tunanin kowane ke iya tsallake sweet sixteens ƙalau? Ga wannan mata muna shiga muna fita a cikinsu, suna dressing kamar a turai, mu zauna guri ɗaya da su, mu ci Abinci tare dasu, muyi raye raye da wasanni tare, kai this is not easy fa"

Amin yace "taɓ ashe mu bamu san komai ba, ai mu iyakar mu romance da 'yan kallece kallace"

Nas yace "baka san komai ba dai, dan nima kawai dai eh"

Nan suka saka shewa, Amin yace "ashe ni kuka bari a tasha?"

Nas yace "tunin ma, amma fa nima zuciyata na ƙawata min budurwar Prince ɗin nan sosai wallahi"

Babba yace "What so ever, kan in graduation a school ɗin nan, Wannan Yarinyar sena san abunyi a kanta, she looks sexy in her every movement"

AMIN AFUWA KWANA BIYU NAYI BUSY NE SOSAI, AMMA INSHA ALLAH ZAN ƘOƘARI IN CIGABA DA KAWO POSTING AKAI AKAI

You can start subscribing now @₦300 only, Free pages are not much.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:          🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                            15_16

Suka sake kwashewa da dariya gaba ɗaya.

Farhan kuwa har gaban mota ta raka Sadik, ya kalleta yace "shigo mu tafi mana"

Ta girgiza masa kai tace "A'a, na ga ba ka jin daɗi, gara ka tafi gida da wuri, Allah ya sawwake"

Ta miƙa masa jakarsa tai gaba, Sadik ya bita da kallo yana lumshe ido, a hankali ya koma ya jingina da seat ya rufe idanunsa, babban burin sa be wuce ace ya mallaki Farhan ba, abunda yake ji game da ita yana neman yafi ƙarfin sa gaba ɗaya.

Farhan ma harta tafi hanya tana tunanin Prince, ba ta san meya same shi haka wanda ya sa shi shiga wannan yanayin na damuwa sosai ba.

Ko yana cikin damuwa idan ya ganta ya kan saki ransa, yai ƙoƙarin ɓoye damuwar ta sa, amma yau kam ya gaza ɓoye damuwar tasa gaba ɗaya.

Da wannan tunanin taje gida, ta tarar da Umma suna cin Abinci tare da ƙannen ta, duk sun sanya Uniform ɗin islamiyya, suna hira Umma nata dariya, amma Farhan na sallama ta haɗe rai, ta dena dariyar da take.

Ta kalli Umman tace "Umma na dawo"

"Sannu" shine kawai abunda Umman tace.

Farhan ta shiga ɗakin su ta ajiye jakar ta, ta canza kaya ta fito ta shiga wanka, bayan ta kammala tai salla ta shirya cikin Uniform ɗinta na Islamiyya itama, ta fito da niyyar cin Abinci, sedai tasan za'a kwashe wa kowa Abinci idan baya nan a adana masa, amma ita kuwa nata sedai ta tarar da shi a tukunya ya sandare.

Haka ta zuba Abincin ta shiga ɗakin umman nata ta zauna tana cin abinci.

Tana son tai hira da Umman, amma babu fuska sam.

Umman Farhan cikakkiyar ba fulatana ce, gaba da baya, kuma Farhan ita ce 'yarta ta fari, bisa ga al'adar Hausa fulani kuwa, dama ɗan fari ba'a jansa a jiki saboda kunya, sedai idan uwa tana da wata yaya wannan 'yar fari ko ɗan fari ya riƙi 'yar uwar uwa a matsayin uwa.

Sedai Umman Farhan ba ta da Yaya mace ko ƙanwa, duk se maza gashi ba'a gari ɗaya suke ba, dan haka abubuwa suna bawa Farhan wahala.

Wasu lokutan ta kanji a ranta anya kuwa Umma ce ta haifeta? Saboda abun ya wuce alkunya, abunda take mata tamkar tsana ne, har gara kwanan nan ta kan yadda su zauna a guri ɗaya, amma a baya ko zama tai a guri Umma ba zata zauna ba.

Dan haka babu wata shaƙuwa ta mussaman tsakanin Farhan da Umma, tsakanin ta da ita sedai kallo da ido, duk da Mahaifin Farhan kan yiwa Umman nasiha akan ta rage wannan alkunyar da take akan Farhan, sedai shima a nasa ɓangaren, ba wani sakin jiki yake sosai da Farhan ba, kasancewar ta mace kuma 'yar fari, yafi sakewa da ƙanenta maza, hakan ya ƙara saka Farhan ɗin zama mara kuzari ko a cikin yara 'yan uwanta.

Dama a yanayin halittar ta ma ba Yarinya ce me hayaniya ba, ba ta iya sakin jiki da kowa, idan kaga walwalata to tare da ƙanenta ne, suma wasu lokutan Umma na musu faɗan be kamata ta girma ta dinga shiga  cikin ƙannenta maza ba.

Shiyasa haɗuwarta da Prince ba ƙaramar Ni'ima ce a gareta ba, yadda yake janta a jiki da nuna mata kulawa ta hanyar kyautatawa, shiyasa take matuƙar jinsa a ranta, take jinsa tamkar wani gurbi me girma a tare da ita.

Tana jin Sadik kamar ɗan uwanta duk da kasamcewar alaƙar dake tsakanin su ba ta 'yan uwanta ka bace, wasu lokutan har ƙaguwa take gari ya waye taje makaranta su haɗu, ko ba komai Sadik akwai iya tsara kalamai masu kwantar da hankali.

Duk da irin wannan zama da take a gidan su, Farhan na matuƙar shakkar iyayenta, dan basu da sauƙi aguri tarbiyya sam, wani laifin idan tayi, da ido kawai za'a kalleta ta san tayi ba daidai ba ta hau tsma, dan a dunyta tsani ɓacin ran iyayenta dan kar ai mata faɗa, bata son faɗa dama rayuwarta.

Cin Abincin kawai take ba dan tana jin daɗin sa ba, dan ya riga yayi sanyi sosai, gashi Umman ta tashi ta bar ɗakin gaba ɗaya, ga tarin Magana da zata so ta tattauna da Umman amma babu fuska, ga damuwar Sadik ta dameta.

Haka ta tashi ta kai sauran Abincin Kitchen ta ajiye, ta ɗau jakar Islamiyyarta ta tafi.

Shirye shiryen bikin dr. Nata nisa, ana ta faman shirin bikin su.

Gefe guda kuma kullum cikin rigima da tashin hankali yake da Nana idan suka haɗu, ita tsiwa shi rashin haƙuri.

A makaranta kuwa tuni sun fara jarrabawa, wasu suna maida hankali kan karatu, wasu kuma suna sharholiyar su kawai.

Wasu lokutan Farhan ajinsu Sadik take tafiya, dan suyi karatu yana kusa da ita, yana tamaka mata a wasu abubuwan, dan Sadik ba ƙaramin gifted bane.

Wasu lokutan kuma a Library suke zama, Farhan ba gifted ce kamar Sadik ba, she needs to read hard, amma 'yar dagiya ce sosai ga nacin karatu, ga son taga ta iya abunda ba ta iya ba.

Ko a aji idan akai abu bata gane ba, da ta tambaya gara ta bari in malamin ya fita, ta tafi gurin Prince ya koya mata.

Sedai a 'yan kwanakin nan, babban abunda yake ɓata mara rai be wuce yadda Mubarak Babba ke damun ta da kallo ba.

Kusan kullum idan ta zo ajin, se ta ganshi ya zo gurin Taslim, amma se ya dinga mata wani irin kallon ƙurilla wanda ko Sadik baya mata, gashi kallon yana damun ta sosai, sedai ta lura sam Sadik be san Mubarak na mata wannan kallon ba, ita kuma bata gaya masa ba saboda gudun buyagin sa.

Yanzu ma tana ajin, tana wani zane da Sadik ya koya mata, kasancewar za ta shiga jarrabawar basic technology bayan break, tafi gane karatun Sadik sosai akan wanda akai musu a aji.

Tana ɗaga kai tai ido huɗu da Mubarak, ya kashe mata ido tare da lashe lips ɗinsa kamar wani maye, hakan ya ƙular da ita ta ɗauke kanta da sauri ta cigaba da abunda take.

Sadik yace "Honey, waike a wani club zaki participating ne? Debate, quiz dancing competition ko kuma sport, kin san duk bayan exams Akwai wannan events ɗin da za'ayi, ga end of term party da za'ai, a me zaki participating ne?"

"Ba kowanne" ta bashi amsa.

"Ban gane ba kowanne ba, ko quiz ba zaki ba?"

"Ai an ɗau sunan wanda za suyi tuntuni"

"To meyasa ba'a saka da sunanki ba, naga You Are very brilliant"

"Ni nace kar a saka, ni bama son duk abunda za'ace inyi performing a gaban mutane"

"Ji ta dan Allah, kin fiye damuwa Farhan, I want you to be famous in this school, ya zaki dinga ɓoye baiwar da Allah yai miki? Yakamata ki dinga participating fa"

"Ni bana son a dinga kallona" tai maganar a shagwaɓe.

Be san lokacin da yace "wow" ba.

"Ina son shagwaɓar nan taki Farhan, tana ƙayatar dani fa"

Cikin wata shagwaɓa tace "Nifa ba shagwaɓa nai ba, kawai maganata ce a haka"

Yace "Awwn so cute, ɗan sake inji" yai maganar zuciyarsa na ƙawata masa ya rungume Farhan yai kissing ɗin lips ɗinta.

Ɗan rufe fuska tai tana murmushi.

Yayin da shi kuma ya cigaba da bin ta da kallo, me ma'anoni daban daban.

Bisa kuskure Farhan ta ɗaga kai, ta sauke akan su Mubarak da ke kissing ɗin juna, shi da Taslim.

Wata mummunar faɗuwar gaba taji, take jikinta ya hau rawa dan abun ya bata mamaki, a makarantar nan ta fara ganin wannan watsewar muraran a zahiri.

Bata manta ranar farko da ta gani ba, a wani aji ba kowa ta hangi wani malami da wata yarinya suna kissing, se kuma yau da ake zahiran a gabanta.

Jiki na rawa ta miƙe ta kwashi litattafan ta, tace "Ni tafiya zanyi"

Sadik yace "Lafiya kuwa? Lokacin shiga exam ɗin yayi ne?"

Shiru tai masa tana ƙoƙarin raɓashi ta wuce, waiwaya yai dan yaga abunda ya ɗaga mata hankali haka.

Take ya gano abunda ya jefata cikin wannan rawar jikin, se dai duk da ba yau su Taslim suka fara wannan ta'asar a gabansa ba, amma kawai yau se ya tsinci kansa a wani irin yanayi, mussaman da ga Farhan a daf da shi.

Ya tattara nutsuwarsa yace "Farhan calm down, forget about them ina jin daɗin hirar nan da muke, ki zauna Please"

Girgiza masa kai tayi tana son ficewa.

Yana ƙoƙarin comforting ɗinta ta zauna, amma ina jikinta har tsuma yake ta bar ajin.

Ganin Prince ba shi da niyyar bata hanya ta wuce, yasa kawai ta fita daga bencin, wanda garin fitar seda Jikinsu ya gogu da juna, wani shock suka ji a tare, wanda yasa Farhan saurin waigowa zaton ta ita kaɗai taji abunda taji.

Sedai ta lura kamar shima yaji abunda ta ji, da sauri ta fice tana sassarfa.

Mubarak kuwa a hankali ya cika Taslim yana murmushi, Sadik ya kallesu a fusace  yace "kai Babba, dan kutmar.... Kar ka sake zuwar mana aji kana mana Iskanci, ka tafi ajinku ku dinga yi a can"

Mubarak yace "da can da muke a nan ɗin meyasa ba kai magana ba se yanzu?"

"Saboda ba ze yuwu ku dinga takura nawa jin daɗin saboda iskancinku ba, Farhan Yarinya ce be kamata ta dinga kallon irin wannan abubuwan ba"

Babba yace "A'a ka manta, a cikin mahaifa take ƙarewar yarinta, shikenan dan kana wannan soyayyar 'yan ƙauyen kowa ma irinta zeyi, yarinya se kidahumancin tsiya, wataƙila ma duk ƙaryar banza ce, dan yaran nan suma sun san komai"

Sadik yace "what so ever dai, in ma zakuyi idan tana nan gaskiya ku dena, na gaya maka in ba haka ba za'aji kanmu da kai"

Nas yai dariya yace "Allah ya temaki Prince, Your royal highness"

Sadik yai tsaki yaƙi kulashi.

Taslim tace "kaifa Prince ka fiye abun haushi, kai kaƙi bari Yarinya ta waye, kuma ka hana wasu jin daɗinsu akan me?"

Wata uwar harara Prince yai mata, tai murmushi ta kalli Mubarak tace "one more time Dear"

Suka kuma rungume juna suna kissing, Amin yace "shegu ai baku burgemu ba, tun da ba kuyi wancan aikin a gabanmu ba"

Mubarak ya saki Taslim yace "ji shege, Allah ya shiryeka"  suka cigaba da dariya kamar ba suyi komai na damuwa ba.

Prince kuwa sake jefa masa wani tunanin su kai a zuciyar sa, yana sake kwaɗaituwa da Farhan, shi duk iskancin sa ba ruwansa da kowace 'ya, banda ma yanzu da ya fara soyaya iyakar sa da mata, ayi hira ai ciye ciye, ayi party amma ba dai ya taɓa 'yar wani da sunan aikata alfasha ba.

Da fari sam ba shi da feelings akan Farhan, yana dai sonta ne sosai, Amma zigar abokansa da RUƊIN ƘURUCIYA, sun fara ɗibarsa zuciyarsa na ƙawata masa ko sau ɗaya yai kissing ɗin mace.

Shi da fari kiss ƙyama yake ba shi idan su Nas  sunayi, yaita ce musu ƙazamai, amma akan Farhan yana matuƙar son ko sau ɗaya yayi, yaji me suke ji ne, zuciyarsa na fara kissa masa abubuwa marasa kyau akan ta.

Ita kam gaba ɗaya mamaki ya hanata sukuni da damuwa duk suka addabeta, ta godewa Allah da yasa masoyinta baya cikin irin wannan masu muguwar ɗabi'ar ta fitsara.

Ta shiga ajinsu tana zancen zuci, sedai abun mamakin suda suke daf da shiga jarrabawa, se ta tarar da 'yan ajin nasu sunyi group sunyi tsit.

Zaton ta karatu sukeyi, dan haka ta nemi guri ta zauna, sedai tana zama taji muryar Haseena, ba ta kai ga jin me take faɗa ba, taji sun kwashe da dariya suna shewa.

Ba ta damu ba, ta cigaba da abunda ke gaban ta, sedai suna gama shewar da sharhin, suka sake yin tsit, Haseena ta ɗora da abun da take.

Waya ce a hannun Haseenan, tana karanto musu wani abu, wanda da fari Farhan ba ta kai ga gane menene ba.

Sedai da ta ƙara natsawa, ajin yai tsit ta fara fuskantar me Haseenan ke karantowa, wata irin narkakkiyar batsa Hassenan ke karanto musu, ba kunya ba tsoron Allah ba saye komai, yadda yake a rubuce haka take karanto musu.

Lilly tai shewa tace "Kambu dama haka abubuwa ke wakana amma muna gefe? Dama akwai irin wannan zafafan Novels ɗin na hausa ban sani ba, ai ban taɓa zaton ana irin wannan abubuwa haka ba, kuma ban san ana karantawa a waya ba, na ɗauka se a bugaggen littafi ai"

Haseena tace "inji wa, bugaggen littafi da kenan, ai yanzu an samu marubutan yanar gizo, littafi se wanda ki ke son karantawa, irin wannan litattafan zaki same su kala-kala. A gurin ƙawar yayata naji suna hirar, ina nan na bazama ina ta tara mana su, wasu marubutan kiji nasu littafin zallar nishaɗi ne, wasu hikima da iya rubutu kamar a gabanka akeyi, wata kuwa litattafan na ta zakiga wa'azi ne kawai"

Yasmin tace "wayake ta wani littafin wa'azi, idan wa'azi ne ai kasan in da zakaji, amma ga irin wannan yadda ake fayyace komai, wanda idan tambaya za kai bame gaya maka, sedai ace maka kai yarone ba yanzu ba, amma ji yadda ake faɗar abubuwa, kai ni gaba ɗaya ma se naji kamar aimin Aure yanzu wallahi"

Lilly tace "to shegiya zalamammiya, kema kar dai ace sex addict ɗin ce?"

"To wa ya sani ma, tunda kai bawa ba gwadawa kai ba"

Lilly tace "Ai na samo logics a littafin nan, ashe abubuwan attraction ɗin ma ba wuya, ba wuya ka tayarwa da maza hankali, shiyasa da ka ɗanyi abu kaɗan, se Sir Nazir ya hau masifa ahse abun ke damunshi jarababbe, ashe abar ke mintsinin sa, amma gaskiya i must try this seduction method fa"

Haseena tace "try it on who? Ke ki rufa mana Asiri maza sukai mu ba mata ba"

Lilly tace "on this guy Nazir man, wai shi man of God, komai ya dinga wani iyayi, kamar baya jin komai, ashe ga abunda yake damunsa yake sashi masifa dan mun cire jacket munyi yawo a haka, to wallahi akansa zan gwada pairing, in ga response ɗin shi"

Yasmin tace "ki rufa mana asiri mana, idan ki ka zaƙe kika ɗaga masa hankali yayi yaya, shi ba aure ba"

"Can ta mulmule masa, sauran malaman ma ai suna ji, amma suke ɓoyewa se shi baba suda uban masifa"

Haseena tace "kuyi shiru mu ƙara ko page biyu ne kan a shigo exams"

Su kai shiru, Haseena ta gyara zama ta ɗora da karanto wannan watsasten littafi.

Tsam Farhan ta tashi, sumi sumi tai waje.

Haseena tai tsaki tace "nifa na tsani yarinyar nan haushi take bani, wai ita ta Allah shine ta fita"

"Bar 'yar ƙauye" cewar Yasmin.

Lilly tace "A'a gaskiya karki zagi ƙawata, ni wallahi burgeni take ina son salihancin ta, dan bata magana ne, ni kuma ban iya ƙawance da mara magana, yadda Allah ya horemin maƙogwaron murya da harshe ba yadda zan iya zama da mara magana, amma wallahi ni ina sonta tana burgeni"

Yasmin tace "ai seki tayi, wannan 'yar ƙauyen yarinyar, sam bata waye ba ta fiye abun haushi, amma ta iya wahsewa namiji baki tana masa dariya da surutu"

Lilly tace "ke akwai Yarinyar da Prince ze toasting har taƙi saurararsa ne? Ku dena zaginta dan Allah bana jin daɗin hakan yaseen"

Haseena tace "dalla ku manta da ita mu cigaba da karatun mu"

Suka sake tattara hankalinsu akan baɗala.

Farhan a ranta tace "wannan wace irin masifa ce? Shikenan kowa lalacewa a makarantar nan ba me cewa wani bari, banda fitsara ai gara abunda ta gani a ajin su Prince, akan wannan lukutayen bayanannun fitsara da ake karantowa suna saurara.

Meenal ce ta shigo ajin tana tangaɗi, idanun ta duk sun kumbura alamar tana jin bacci, ko kuma tana cikin damuwa, ta nemi guri ta zauna a kusa da Taslim.

Taslim tace "hey beb are you ok? Meke going ne?"

Shiru Meenal tai ta kifa kanta akan benci tana ajiyar zuciya.

Taslim tace "wai meye ne? Or do you need me?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Kinje gurin mummynki ne ta ss3?"

Meenal tace "malama, wata ƙwaya na sha tun jiya take wahal dani, na kasa baccin na kasa komai ga jikina duk a mace, taƙi sakina gaba ɗaya, kuma bana son in koma gida a gane"

Taslim tace "calm down dear, nima farkon farawa ta haka naita fama wallahi, amma ki kwantar da hankalinki, ki matsa lemon tsami da yawa, ki zuba manja a kai ki sha, zan saka Mubarak ya kawo miki wadda zata dai-dai ta miki jikin naki, amma ki ƙwarara jikinki kiyi exams ɗin lafiya, kar a fuskanci wani abun"

Ta jinjinawa Taslim kai alamar to.

Haka invigilators suka shigo, suka fara arranging ɗinsu domin fara jarrabawa.

Sadik kam kusan rabin jarrabawar nan be san meya rubuta baz tunaninsa da hankalinsa na can kan wani abu daban.

Meenat kuwa duk da ta na cikin maye, amma taji daɗin ganin corper Nura a cikin invigilators ɗin nan.

Da sun haɗa ido zata masa wani killer smile tana lumshe ido, tun yana basarwa har ya ɗan fara dirircewa.

Murmushi tayi tace gayen nan ai dole ka shigo koma ta ko baka so.

Da ya zaga ya zagayo se yaga tana kallonsa, ba ya son dizgata a gaban ɗalibai dan haka ya ƙarasa gaban seat ɗinta yace mata "gani me kike buƙata"

Cikin kashe murya da magana ƙasa ƙasa tace "ni ba kiranka nai ba"

"Amma ki ke kallona"

"To sir dan kawai na kalleka, ni bani da lafiya ne"

"Eyya sorry, can You write the exam?"

"Yes am trying"

"Ok sorry, in kin gama kije Clinic a dubaki"

"Ok thank you sir"

Har ze juya ya tafi tace "oushh"

Ya juyo da sauri yace "ya dai cikin ne?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, "eyya ko dai zaki je a fara baki magani?"

"No i will finish the exams first"

"Ok sorry dear"

Ta jinjina masa kai tana wani marairaice fuska.

Yana wucewa tabi bayansa da wani irin shegen murmushi, a ranta tace "da Wannan raunanniyar zuciyar ta ka zan damƙe ka ta wuya"

Ta sake sakin wani murmushi, tana cigaba da rubutu.

Da wuri Farhan ta gama exams ɗinta, saboda tayi mata sauƙi sosai da sosai, duk da zare ido da muzurai da sir Nazir ya dinga yi, sam hakan be damu Farhan ba dan nan da nan ta kammala, dan abunda sukai bita tare da Prince mostly su suka fito musu.

Tana gamawa ba ta jira Komai ba ta nufi hanyar fita, ta jiyo Sir Nazir yace "daga nan ki ɗau jakar ki ki tafi gida, idan kika kuskura na ganki a gurin yaron nan sena miki duka"

Seda gaban Farhan ya ɗan faɗi, dsn tabbas yanzu Sir Nazir yana hukunta mutum idan yayi laifi, har duka yake, makaranta kuma sun kasa dakatar da shi, saboda jaki work da yake musu, he is very hard-working teacher, yana da jajircewa sosai suyi ta jibga masa jaki work, kuma hakan baya damunsa.

Da akai masa Magana akan dukan da yake yace shi koyarwa ko duk Makarantar ne ze koyar, baze dameshi ba, amma baze dinga kashe energy ɗin sa yana koyar da yaran da basu san darajar Malami ba.

Rashin Nazir ze sama musu babban giɓi a makarantar, dan haka suka ja masa kunne kome zeyi ya dinga yi sama sama, banda punishment me wahala ko duka, idan ba haka ba uban wani ɗan ze iya kulle shi.

Ajiyar zuciya Farhan tayi da ta tuna da haka, tana fita wajen ajin taji maganar da yai ta shiga ta kunnen dama ta fita a na hagu, ajin su Prince taje ta tarar be fito ba, dan haka taje ta nemi guri ta zauna tana jiran fitowar tasa.

Gajiya tai da zaman ta miƙe tsaye tana ɗan leƙewa cikin ajin.

Ji tai an kama rigarta an janyota ta baya.

Da sauri ta waiga amma taga Mubarak Babba ne da Wannan aikin haka.

"Meye haka, me nai maka?" Ta faɗa a ɗan raunane.

"Sekin min wani abu zan taɓa ki, i just feel like to do so, naga jiya kin bar ajinsu Sadik saboda nai kissing Taslim, shiyasa kema nake so in kissing ɗinki, in gwada miki yadda ake soyaya ba kamar wadda kuke ke da wancan wawan Sadik ɗin ba"

Nema yake ya haɗata da jikinsa, kasancewar gurin ba kowa, kusan itace ɗaliba ta farko da fito daga ɗakin jarrabawa.

Ƙoƙarin ƙwacewa take, ta hana shi ya haɗa jikinsa da nata, ga wani warin hammata da yake, take zuciyarta ta fara tashi.

Abunda ko da wasa ba ta taɓa jin Prince ɗinta yana yi ba, abun mamaki ya bata ma, dama yaran masu kuɗi ma na warin jiki? Ga ƙamshin turare a jikinsa, amma warin daban ƙamshin daban.

Ganin da tai bata da mafita yasa ta ware murya ta shiga kiran sunan "Sadik"

Da sauri Babba ya ƙyaleta, dan yasan gamonsa da Sadik ba daɗi.

Ta arta da gudu ta bar harabar gurin, tai waje.

Sadik kuwa da Sauri yai submitting paper ɗin sa ya fito, dan tabbas yaji kururuwar Farhan.

Sedai yana fitowa yaga be ganta ba, ya dudduba amma bata nan, ya nufi ajinsu ya tarar da wanda suka fito ya tambaye su Farhan, suka ce masa ai ta fita tun ɗazu.

Haka yaita zaga makarantar ko ze ganta, amma be ganta ba nan ya dinga mamakin abunda ya sata wannan uban ihun haka, gashi ita ba waya ba balle ya kirata.

Haka ya wuce ya tafi gida yana tunani.

A gidanma abunda ba ya so, dan sati me kamawa za'a fara biki, masu rumfuna da kujeru duk sun kawo sun jibge a harabar gidan, wannan ya shiga wannan ya fita ita kanta Mother bata da lokaci, kusan kullum ba ta nan, ita ce nan ita ce can saboda hidima.

Yana kwance a part ɗinsa da yamma, Nasir ya kira shi yace kayan da akai order sunzo, sedai nasa wandon ne se cikin satin bikin ze iso.

Sadik yace "i hope dai za'a kawon kafin ranar partyn nan"

"Za'a kawo insha Allah, ga sauran nan naje na karɓo rigunan ma, naso in biyo in kawo maka ka gani, amma ba mota a gidanmu duk an fita da su, a babur naje"

"Ok shikenan, gobe in Allah ya kaimu seka zo dasu a bawa kowa nasa"

"To shikenan Allah ya kaimu goben"

"Ameen" ya katse wayar.

Yanzu Nana ba ta haɗuwa da Sadik, sedai kuma abun ya koma rigima tsakanin ta da Khairat, haka kurum da ta motsa se Khairat ɗin ta fara hantarar ta, tana zaginta ko da kuwa a gaban Inna ne, Inna ba ta cewa komai dan ba ta shiga faɗan yara, in ba gani tai za su cutar da junan su ba, ita kuma Nana na gudun faɗan Inna.

Amma Nana ta fara ƙuluwa da abunda Khairat ke mata, kuma babban abun takaicin ma shine, ba iya Khairat ke mata hakan ba, mahaifiyar Khairat ɗin itama haka take, matar gidan ma haka take mata mussaman idan ta ga babu idon Inna a gurin.

Hakan ya fara damun Nana sosai, taji ita gaba ɗaya ma zaman Gidan ya isheta, gara su koma ƙauye dan a can matsalarta ɗaya faɗan Inna, amma kuma ba tsangwama da hantara, dan bata jin daɗin yadda ake hantararta a gidan.

Duk gidan ba wanda take ɗasawa da shi sama da Daddy, se masu aikin gidan se kuma Faruk, yana da fara'a sosai yana da kirki, ba kamar dr. Ba, dan shima baya kula mutane ba ya Magana Sosai, shikuwa oga kwata kwata nasa yafi na kowa, ga rashin son mutane, ga wulaƙanci, ga zagi da hantara ga iya muzurai duk shi kaɗai, Faruk ne me halin Baban su ba ruwansa shi da wannan zafin kan.

Yanzu ma Nana tana cikin 'yan aikin, ana girkin rana, Nana akwai son aiki sosai, sedai ko a gida Inna ba ta fiye sata aiki ba, Se su bata ɓarar maggi, ko jajjage ko shara, dan su huta da hayyatarta na lallai se taya su aiki.

Aka kammala girki, aka zuzzubawa kowa nasa, Nana ta ɗauka ta dinga kaiwa kowa har inda yake.

Ta kaiwa Inna nata, Ta ɗau na Mother ta nufi ɗakinta, da sallama ta shiga ɗakin, ta tarar da Mother da Maman Khairat se Faruk da yake riƙe da kuɗi a hannunsa da alama aikensa za'ai.

Ta ajiye kulolin Abincin tace "wai ga Abinci"

Mother ta kalli Nana tace "waye yace ki shigo nan?"

"Ba kowa kawai kowa kai masa Abincin sa nake"

"To daga yau kar in sake ganinki a nan ɗakin, ki dinga tsayawa a can in da aka sauke ku, baki da hurumin zuwar min sashe, idan kika kuma zuwar min nan sena saɓa miki"

Turus Nana tai tana kallon Mother, tana tunanin meye a nan ɗin da dan ta shigo za'a dinga mata wannan kashedin haka, nan da nan ranta ya ɓaci.

Maman Khairat tace "ba Magana ake miki ba kina jin mutane? Maza ki wuce ki bar gurin nan, da haka yaro ke koyar munafurci, yaran ƙauye dama ba kan gado suka cika ba, yanzu zaki ji ta haɗa wani abun ta gayawa kakarta ta kunno miki wata wutar"

Jiki a sanyaye Faruk yace "haba Mother, meye a ciki dan ta shigo me aka ajiye a nan ɗin, naga Khairat ba ta da iyaka a shiga duk in da take so a gidan nan, hakan da kike mata ba zata ji daɗi ba, ba daɗi hantara"

Mummy tace "to uban mu gayamana abunda yakamata"

"Ba abunda yakamata zan gaya muku ba, amma idan bata zo ta ga abunda za ta je ta gayawa Inna ba, ai ta faɗa mata abunda a kai mata, na baƙaƙen maganganun da ku kai mata"

Ya juya ya fita yana takaicin abunda sukai, dan shikansa baya jin daɗin wasu daga halayen mahaifiyarsu, Akwai ta da wulaƙanta ɗan Adam mussaman talaka, kuma Mummy ce ke zigata, kuma ko zata ƙyamaci kowa be kamata ta ƙyamaci dangin mahaifinsu ba.

Yana fitowa harabar gidan ya hango Nana akan barands, tai shiru tana wasa da tsinke, da alama tana cikin damuwa akan abunda akai mata.

Ya ƙarasa in da take yace "Naana What are you doing here?"

Ɗaga kai tai ta kalleshi, ita ba ta fiye gane irin wannan turancin da suke ba, a dinga yin sa a wani harɗe, wata kalmar ma bata fita sosai, zuba mai ido kawai tai ba tace komai ba.

Yace "ok, jeki gurin su Binta, su baki namu Abincin ki kawo mana BQ"

"Ina ne BQ?"

"Wancan sashen me farar ƙofa"

Tura baki tayi tace "wannan ƙanin naka zagina yake, idan naje ze iya zagina"

"No ba ze zageki ba, aini na aike ki"

Ta tashi ta koma dan cika Umarnin sa.

Yabi bayata da kallo, kawai yaji ta bashi tausayi, tsangwama bata da daɗi sam.

Nana ta koma ciki, ta karɓo kwando ɗauke da kayan Abinci da plates, seda tai sallama sannan ta shiga, amma tana shiga taga Prince ya harɗe ƙafa yana video game.

Kallon ta yai, ya tashi zaune yace "me kika zo yi nan? Ban hanaki zuwa ɓangaren nan ba?"

"To ban hanu ba, se kai abunda za kai"

AIMIN AFUWA FOR THE VERY LATE POST, ABUBUWA SUN SHA KAINA SOSAI DA SOSAI, AIMIN AFUWA.

Gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:     🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

TAƘABALLALAHU MINNA WA MINKUM, ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN UBANGIJI ALLAH YA KARƁI IBADUNMU YA MAIMAITA MANA, INA 'YAN UWA MASOYA, MARUBUTA DA MAKARANTA MURNAR BARKA DA SALLA, UBANGIJI ALLAH YA MAIMAITA MANA.
BAYAN HUTUN AZUMI ALHAMDILILLAH, GANI NA DAWO MUKU DA CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA.
INA FATAN ZAKU BINI SANNU, DAN JIK ƊUMBIN SAƘONNIN DA LITTAFIN YA ƊAKKO, WANDA SUKE TAMKAR BULALIYA GA IYAYE.

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

                           17_18

A fusace Sadik yace "ke ni kike gayawa haka?"

Murguɗa masa baki tai tace "eh ɗin, na faɗa ɗin"

Faruk ne ya fito hannun sa riƙe da wayarsa yace "Sadik meyasa kake hakane? Hantarar mutum ba daɗi, nine mace ta kawo mana Abinci nan"

Sadik yace "Amma dai bani a Wannan Abincin da ta kawo?, dan ba zanci Abunda wannan ƙazamar ta taɓa ba"

Aikuwa Nana ranta ya ɓaci sosai tace "wallahi ni ba ƙazama bace, kaje ka nemi ƙazama a can amma bani ba"

Ta dire kwandon Abincin, zuciyarta na mata zafi, yace "in kinyi zuciya ki tattara ki bar mana gida yau, kun zo kun cika mana gida kun hana mutane sakewa"

"Sadik meyasa kake hakane? She's lyk sister to you, be kamata ka dinga hantarar ta haka ba babu daɗi, yanzu ma fa daga gurin Mother take suna ta kyarar ta, ba bu daɗi hakan, kyarar ɗan Adam ba shi da wani Amfani ko rana"

Yatsune baki Sadik yai ya koma ya kwanta yana cigaba da video game ɗin sa.

Washegari a school kuwa, bayan fitowa daga exams aka kawo kayan nan da sukai order, wasu irin tsadaddun crazy jeans da riguna.

Ana ta ɗaɗɗaga kayan ana bawa kowa nasa, ana shewa da lissafin in da ya kamata a kama na partyn, amma hankalin Prince yana kan rashin ganin Farhan da beyi a ajin nasu ba yau.

Miƙewa yai tsaye yace musu yana Zuwa, ya fita da sauri ya tafi ajinsu Farhan, amma bata ajin, Library ya tafi ya tarar da ita a can tana karatu.

Sadik ya ja kujera ya zauna yana kallonta, ta ɗaga ido ta kalleshi tace "good morning"

"Naƙi in amsa gaisuwar taki, ba an gama exams ba, me ki ke a library kuma?"

Cikin sanyin halinta tace "Ai clubs suna rehasals yau, dan haka ance ba me tafiya se lokacin tashi yayi, shiyasa na taho nan kawai"

"Amma meyasa baki zo ajinmu ba?"

"Bakomai" ta bashi amsa a taƙaice.

Yace "yawwa, jiya ina exams kamar ihun ki naji kina kiran sunana"

Ɗan kallonsa tai tana zare ido, ta dake tace "bani bace"

"Kamar ya ba ke bace? Muryarki fa naji"

"Am serious ba ni bace"

"Ok shikenan, ta so muje class ɗin mu kiga kayan da zamu sa ranar bikin Brother na"

Ɗan noƙe masa kafaɗa tayi alamar ba zata ba.

"Baby meyasa?"

"Bakomai"

Sadik yace "kefa kin fiye mulki wasu lokutan, yau kuma ajin namu ne ba zaki ba?"

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Nagane, saboda abunda su Taslim su kayi ne ranar ko? Na musu magana ba zasu sake ba"

"Ni dai kawai yau ba zani ba"

"Ko wani abun suke miki a ajin namu"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

Yace "shikenan ni na tafi"

Ya miƙe ze tafi, da sauri tace "nace ba"

Be juyo ba yace "ki ka ce me?"

"I want to talk to you please"

Juyowa yai ya kalleta, ya dawo ya zauna yace "am all ears"

Cikin jin nauyi tace "dan Allah ka zauna a nan"

Yace "Why?"

"Kawai mu zauna a nan"

Tai maganar kamar wadda take furta saɓo saboda jin nauyinsa.

Wani ƙasaitaccen murmushi yai mata me cike da ma'anoni da yawa, yace "kina so in zauna?"

Ta gyaɗa masa kai.

Yace "Da sharaɗi gaskiya"

"Sharaɗi kuma?"

"Eh mana" ya faɗa yana kwaikwayon ta.

Tai murmushi tace "meye sharaɗin"?

Yace "Look up" ta ɗago ta kalleshi tai saurin sauke idonta, dan ji tai ba zata iya tsawaita kallon nasa ba.

"Kice ki na sona dan Allah"

Ba tare da ta kalleshi ba ta ɗan zaro ido tace 'taɓ'

"Ba zaki iya ba kenan?"

Shiru tai ba tace komai ba.

Sadik yace "Farhan kenan, kedai wannan fulatancin naki yayi yawa, shikenan tun da kince in zauna yadda kika ce ai haka za'ayi gimbiyar mata"

Yana zama kuma wata kunyar ta sake baibaiyeta tana mamakin kanta, wai ita ce ke cewa namiji ya zauna kar ya tafi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, farin ciki na ratsata kasancewar ga Prince a kusa da ita"

Haka shiru ya wanzu a tsakanin su, Prince ya katse shirun ta hanyar ɗakko mata hirarraki, a haka ta saki jiki suka cigaba da hirar tare.

Seda aka kaɗa bell, sannan suka baro Library ɗin tare.

Aka kammala jarabbawa, aka shiga shagulgula daban daban a makarantar, kullum akwai abunda za'ayi na nishaɗi, ko dai Quiz, Debate, inter House competitions, da dai games kala kala.

Farhan ta so tai zamanta a gida ta dena zuwa tun da hutu za'ayi, amma idan ta zauna a gidan a takure take ga damuwa, dan haka take zuwa school ko ba komai tana ganin abun ƙaunarta tana jin daɗi.

************

"Meena, wai anya lafiyar ki ƙalau kuwa?"

"Mum why are you asking? Me kika gani?"

"Gaba ɗaya kin ɗashe, se wata uwar rama da kike yi, ga wani uban bacci wanda na kasa gane miki gaba ɗaya"

"Am ok fa, kawai weather nan ce is not compostable to me, yau zafi gobe sanyi, and I have no appetite bana iya cin Abinci, shiyasa nake rama But i will be ok insha Allah"

"To shikenan, idan kuma ba hali muje Asibiti a duba ki"

"No don't mind Mum, sena dawo"

"Ok safe journey"

Meena ta amsa da "Thank you" sannan tai waje.

An taru sosai a gurin hall ɗin makarantar, dan kallon fafatwar da za'ai na Debate, ɗalibai 'yan kallo suna cakuɗe maza da mata, ana kallon fafatawar.

Farhan na kusa da Prince, ya bata wayarsa tana kallon pictures ɗin 'yan gidansu, yanayin hotunan nasu ya tabbatar mata da Lallai Prince ɗinta ɗan hutu ne, sannan da alamun akwai kyakkyawar alaƙa da shaƙuwa a tsakanin su.

Farhan ta kalli hoton Mother tace "she's Your Mum ko?"

"Eh mana, in law ɗinki ce, ai zaku haɗu agurin bikin Brother na, i will introduce you to my Family"

Zare ido tai tace "ni dai a'a gaskiya, se ace munyi rashin kunya ai"

"Meye wani rashin kunya, gara su sani tunda wuri ai, ko kin manta ina processing yadda zamuyi Aure ne? Gara su san da Maganar tunda wuri"

Shiru tai jikinta yai sanyi, duk da maganar Auren da yai yasa jikinta yai sanyi, amma a wani ɓangaren tana fatan Allah ya amince, yasa ta Auri Prince, First love ɗinta kenan, ba ta jin daga kansa zata kuma son wani namiji haka.

Ta cigaba da kallon hotunan ta, Sadik ya jiya yana magana da su Nas, yaji suna zancen wani Film.

"Nas, kune sarakan kallon series Films, dan Allah in mun bar nan System ɗina na mota, zaku turamin fina finai masu kyau sosai"

Amin yace "Allah mutumina, ka shigo layin kenan?"

Sadik yace "wani layin kenan?"

Nas yace "layin eh mana"

Sadik yai tsaki yace "Malam ba wannan haukan nace ba, just normal films nake so na Soyayya, za'ai hutu bayan bikin nan ina so zan kalla, ina son wanda ake soyaya sosai a ciki"

Amin yace "ji shi wai wani na Soyayya, se kace soyayyar suka iya, banda ƙauyanci da soyayyar yara ba abunda suke"

Farhan ta ɗago ta kalli su Amin, ta ja ƙaramin tsaki wanda Sadik ne kawai yaji, yai murmushi yace "don't mind them Baby, kar su mayar min da ke mafaɗaciya, i love Your silent character"

Farhan tace "ai ni ba faɗa zan ba"

"Ai tunda kika fara tsaki, nasan faɗan ma zakiyi ne"

Tai shiru ta cigaba da abunda take.

Sadik yace "Nasir zaku turamin ko kuwa?"

Nasir ya kashe ido ɗaya yace "meze hana a turamaka ranka ya daɗe, akwai korean, indian, American Chinese and many hot Love series, depending on which you wish to watch"

Sadik yace "Kawai me kyau nake so"

"Shikenan, bari a tashi daga nan ɗin, za'a tura maka Insha Allah"

Suna cikin maganar sega Babba ya nufo su, yana tunkaro gurin Farhan ta haɗe rai, jikinta ya hau tsuma, saboda yanzu a Duniya ta tsani ko ganin Mubarak.

Ya faki idon Sadik ya kashe mata ido, ta galla masa harara ta ɗauke kanta.

Ya zauna kusa da su Sadik ya miƙa musu hannu, su kai musabiha, miƙewa Farhan tayi zata bar gurin, Sadik ya kalleta yace "ina zaki kuma?"

Ɗan yatsuna fuska tayi tace "can zan koma"

Sadik yace "ok as you wish my love"

Tai masa guntun murmushi, ta koma cikin 'yan ajinsu mata, da suke ta zuba hira, gefen su kuma 'yan ajinsu Sadik ne, su Taslim da Meenal.

Can kuma ana can ana ta faman Debate, amma hankalin su ba'a akan abunda ake yake ba.

Su Lilly kam banda hirar litattafan da suke karantawa a Online ba abunda suke yi.

Taslim ta dubi su Lilly tace "Lilly, me kuke Magana a kai ne?"

Lilly tace "bakomai fa"

"A'a naji kamar kuna hirar romantic book ne na hausa"

A ɗan tsiwace Lilly tace "eh"

"Dama akwai romantic books na Hausa?" Taslim ta tambaya

Lilly tace "eh, akwai masu zafi ma kuwa"

Nan Taslim ta dinga lallaɓa su Lilly, suna bata labarin litattafn da suke karantawa a Online.

Gaba ɗaya hirar tasu ta gunduri Farhan, su gaba ɗaya makarantar daga mazan har matan tunanin su iri ɗaya ne, duk wata harka ta watsewa su ita suke so.

Haushi ne ya kuma kama Farhan, ta Tashi ta bar hall ɗin gaba ɗaya ta fito, zagayen ta ta shiga yi a makarantar, tana 'yan leƙe leƙen ta, makarantar shiru kamar ba kowa duk suna hall ɗin da ake gabatar da Debate ɗin.

Katsam idonta ya sauka akan corper George a cikin wani aji, abunda idanuwan ta su kai katarin gani ne ya kiɗimata, wanda har ya kusa awon gaba da nutsuwar ta na wani ɗan lokaci, a very deep Romance with his ss3 student, she don't even know the name of the lady, ta san dai shine class mastern finalist student ɗin.

Jikinta ne ya hau wata irin tsuma, kuma ta kasa motsi daga gurin, se idanunta da take ta faman jujjuyawa kamar taiwa Sarki ƙarya.

Ba tsammani George ya waigo ya ga Farhan tai musu ƙuri da ido, da sauri ya cika Nasreen, ɗalibar da suke watsewa taren, yana ƙoƙarin tattaro nutsuwarsa ya daidai ta.

Ganin da Farhan tayi sun ganta Ya bata ƙwarin gwiwar, fizgo kuzarin da ta rasa na wani ɗan lokaci, cikin sassarfa ta ja da baya cikin hanzari ta nufi hanyar da ta sauka daga kan benen.

Kana ganin ta kasan a firgice take, kamar wadda ke shirin zarewa, ba zato ba tsammani tai karo da Sir Nazir yana ƙoƙarin hawowa kan benan.

Cak ta tsaya tana cigaba da rarraba ido, kamar mara gaskiya.

Kallon tuhuma ya bi ta da shi, yana ƙare mata kallo yana son gano me ya razanata haka, fuskarta take bayyanar da alamun rashin gaskiya?

Hanya ta bashi, dan ya wuce sannan ita ma ta wuce, amma ya tsyaa kyam yana cigaba da kallon ta.

Ba tsammani taji muryarsa yace "me kike yi a nan?"

Girgiza masa kai tayi tare da faɗin "Nothing sir"

"Nothing as how? Ke da waye a saman gurin nan, bayan ba kowa duk ana hall ɗin da ake Debate?"

Rasa amsar da zata ba shi tai, ta cigaba da tsatstasare shi da ido.

"Ke da wannan shashashan yaron ne a saman ko?"

A razane ta kalli Sir Nazir, tana son tabattar da abunda yake faɗa.

Ganin Farham taƙi magana ta cigaba da bin sa da idanu ya sa ya ji zargin sa na neman zama gaskiya.

"You Are Much more than stupid Farhan, ki cigaba da biyewa RUƊIN ƘURUCIYA, Kina rusa Rayuwar ki, nan gaba se kin yi kuka da idonki, a lokacin da kuskuren da ki kai ba ze gyaru ba, ki cigaba da ba shi damar keɓewa da ke, sheɗan na buga muku ganga, nan gaba zaki gane shayi ruwa ne stupid girl"

Maimakon ya hau saman benen, se ya fasa ya juya ya sauka, zuciyarsa na ƙuna, ganin yadda rayuwar yara mata masu ƙananun shekaru, ke lalacewa saboda RUƊIN ƘURUCIYA.

Farhan kuwa kasa matsawa ta yi daga in da take, maganganun sir Nazir suka cigaba da sukar zuciyarta, yana zarginta da wani abu, wanda ba shi da tabbas a kai, dan duk wannan masifar da yake a yanzu, bashi da wata hujja da ze kafa, akan ta, amma ya sa mata ido yana binta da miyagun maganganu, tabbas duk da ƙanƙantar shekarunta, tasan idan har aka zarge ka da keɓewa da wani namiji, to kuna aikata wani abune da be kamata ba, take ta tuno abunda ta gani yanzu a saman benen, kenan da irin abun Nazir yake zarginta kenan?.

Hawayena ya shiga bin fuskarta, fan take ta ji ranta yai ƙololuwar ɓaci, haka ta sakko jikinta a sanyaye ta tafi hanyar gate ɗin fita ta zauna, ana kaɗa jiniya, tai gaba ba tare da ta jira kowa ba.

Tun ranar da Nazir yai mata wannan zargin, gaba ɗaya se ta tsargu take ganin kamar kowama haka yake kallonta, dan haka kasancewar da ma sun kammala jarrabawa, ba ta sake zuwa makarantar ba har aka yi hutu.

Hakan ya damu Sadik sosai, ganin ba ta zuwa har a kai hutu, ranar da za'ai hutu ya zo da system ɗin sa, aka tura masa fina finai, wanda ze dinga kallo kan a koma school.

Satin da a kai hutu, a satin za'a fara bikin Ussy, ana ta shirye shirye, mussaman Sadik ya bugo nasa invitationsa ɗin, da ze rabawa abokan sa.

Gefe ga son ganin Farhan da yake yi, gashi yasan gidan su Farhan Akwai tsaro sosai, dan mahaifinta malami ne, idan ya je gidan su Farham be san me zece ba.

Shiryawa yai, ya tafi gidan su Khairat, a falo ya tarar da ita tana cin Abinci.

Sadik yace "Ina Mama?"

"Ba ta nan, lafiya na ganka kamar an jefo ka? Ka wani sha Manyan kaya kamar wani ango, ni na taɓa ganin ka a manyan kaya kuwa?"

Sadik yace "Khairat gidan su Farhan na ke so ki rakani dan Allah"

Yamutsa fuska Khairat ta yi tace "wace hakan?"

"So nake na bata invitation, tace idan ban kai mata gida ba baza'a barta taje ba, ni kuma i dont know how to explain myself idan naje, shiyasa nace bari in zo muje tare"

Khairat tace "to ai ita Farhan ɗin nake son jin wacece?"

" 'yar ajinmu ce" ya bata amsa.

"Gaskiya ban yadda ba, kana yawan kirana da Sunan ta, ko 'yar ajin ku ce akwai wani abu a tsakanin ku"

"Eh budurwa ta ce"

Yatsuna fuska Khairat tayi tace "kuma shine ni zan raka ka?"

"Kinga idan ba zaki ba ba se kin rainamin hankali ba" ya faɗa a kausashe.

"Naji zani" ta faɗa cike da ɓata rai.

Ta tashi taje ta canza kaya, ta fito ta tarar da shi in da ta barshi.

Yau Sadik da kan sa yake driving, suna tafe yana tsarawa Khairat abunda za su faɗa.

A bakin layin su Farhan yai parking, gabansa se faɗuwa yake, ya hango mahaifin Farhan zaune a kan dadduma, yana tilawar Alƙur'ani.

Khairat kuwa ganin gidan da Sadik ke dosa ya sa ta ɓata fuska, tun daga farkon unguwar kasan ta talakawa ce, ko ina kwata, se wari kwatocin ke yi, ga wasu gungu gungun awaki da tumaki da ke kaiwa suna komowa a tsakanin layukan.

Ga kaji da ke ta sake haƙe kwatar da aka kwashe aka zubar a gefen hanya, gaba ɗaya haushin Sadik Yakamata, gasky Prince ya faɗo ya rasa in da ze samo budurwa se a wannan unguwar talakawan, sedai ba ta da ikon Magana, yanzu ze hayayyaƙo mata, haka tai shiru ta cigaba da bin sa.

Suna zuwa in da Mahaifin Farhan yake, Sadik ya samu guri ya ɗan risuna.

Mahaifin Farhan ya rufe Alƙur'anin gabansa ya kalli Sadik da Khairat, yace "Sannun ku da zuwa"

Sadik ya ƙara nustuwa yace "Abba ina wuni"

Baban Farhan yace  "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya gida?"

Sadik ya ƙara nutsuwa yace "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, dama ni ɗan makarantar su Farhan ne, wannan ƙanwata ce ajinsu ɗaya da Farhan a Makaranta, Yayan mu ne ze Aure, shine muka kawo mata katin gayyata ko za'a barta taje"

Sadik yai maganar tare da ɗakko katuna a aljihunsa ya miƙawa Baban Farhan.

Ya sa hannu ya karɓa ya duba, ya kalli Sadik ya jinjina kai, dan sunan mahaifinsa d sananne ne, ya ƙara tabattar da Allah ne kawai ya yi Farhan za tai wannan Makaranta, ban da haka ina ita ina karatu da 'ya'yan Alhaji Abdullahi.

A fili yai murmushi yace "Masha Allah, ai komai da sanarwa yana da daɗi, Allah ya sanya Alkhairi, shiga ki kai mata katin"

Khairat ta karɓa, ta nufi gidan da mahaifin Farhan ya nuna mata, tana sake tsantsame jikinta, dan ita ƙyamar gurin take.

Baban Farhan yana da kirki sosai, ya din ga jan Sadik da hira, tun Sadik na jin nauyin sa, harya saki jiki suka cigaba da hira sosai.

Yadda Sadik ya zo cikin shiga ta mutunci da girmamawa, ba ƙaramin burge mahaifin Farhan yai ba.

Khairat kuwa sallama ta yi tana ƙarewa gidan kallo.

Gidan tsaf da shi, ko tsinke ba bu a tsakar gidan, se ƙamshin turaren wuta da ke tashi.

(Dama ita tsafta ai ba se me kuɗi ba)

Sallama Khairat ta yi, ta tsaya a tsakar gida, Umman Farhan ce ta amsa mata, sannan ta bata izinin shiga.

Ta shiga ta gaida maman Farhan, ta amsa mata cikin kulawa.

Khairat tace "dama gurin Farhan na zo, na kawo mata katin bikin yayan mu"

Umman Farhan tace "Allah sarki, Allah ya sanya Alkhairi.

Ta nunawa Khairat ɗakin da Farhan ke ciki.

Ta shiga ta tarar da Farhan, sanye da dogon hijjabi ta na karatun Alqur'ani.

Khairat ta samu guri ta zauna, Farhan ta dakata ta kalli Khairat, dan ba ta santa ba "Sannu da zuwa"

Khairat tace "Yawwa, Farhan ko?"

"Eh, sedai ban ganeki ba"

"Ƙanwar Sadik ce"

Kunya ce ta kama Farhan, tai murmushi tace "Allah sarki, sannu bari in kawo miki ruwa"

Khairat tace "No, ba se kin kawo ba, dama katin gayyata ne na bikin Yayan sa, yace mu zo mu kawo miki yana waje, idan da hali yana san ya ganki"

Shiru Farhan ta ɗanyi tace "ai ban san yadda zan fitan ba ne, ina jin tsoro Abba na yana nan"

Khairat ta ɗan ƙare mata kallo a ranta tace 'taɓ, rayuwar yaran talakawa ba tai ba sam, wace irin jaraba ce wannan dan baban ka yana nana ace ba zaka fita ba?'

A fili tace "ai ba daɗewa za ki ba, kice kawai zaki rakani ne, se muje ku gaisa kawai"

Har ga Allah, Farham na son ganin Sadik, cikin sanyin jiki ta miƙe ta tafi ɗakin Umman ta, ta nemi iznin raka Khairat, ga mamakin ta se Umma ta amince, har da bawa Khairat ɗin kyautar turare, zaton ta ƙawar Farhan ce.

Khairat kuwa a ranta mamakin irin wannan rayuwa take, saboda tsabar abu Yarinyar ko wayon yadda zata fita ba ta da shi, fita rakiyar ma seta tambaya, lallai 'ya'yan talakawa na rayuwar takura da rashin 'yanci.

Cike da faragaba ta bi Khairat suka fita, cikin sa'a da suka fito baban Farhan ba ya ƙofar Gidan.

Ta hangi Sadik zaune akan barandar da ke gefen gidan su, ya sha shadda dark blue, harda hula kai kace wani babban mutum ne, ba ta san lokacin da ta saki wani ƙasaitaccen murmushi ba, shima ɗagowa yayi ya kalleta yai mata murmushin, tare da sauke ajiyar zuciya a jejjere.

Suna zuwa in da Sadik ke zaune ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta.

Sadik yace "Madam kawai se nemanki nai na rasa a makaranta, ki ka dena zuwa why? Ki ka bari ina ta cigiyar ki"

Kasa Magana tayi, saboda fargabar kar wani ya ganta ko babanta ya dawo, ga Khairat a tsaye a gurin.

Ganin yadda ta kasa sakewa, ya sa Sadik yace "zo muje daga bayan layin ku naga You are not comfortable here"

Duk da Farhan na cikin fargaba, amma ba zata iya yiwa Sadik musu ba, ta bisu suka nufi in da sukai parking.

Suna zuwa Khairat ta buɗe gaban mota ta shige, ta bar Sadik da Farhan.

Ganin Khairat ta basu guri, yasa Farhan yin ajiyar zuciya tace "ina wuni?"

"Se Yanzu zaki gaishe ni, kin ƙi ko kallona se wani ƙasa kike da ido kina kallo na, ki ɗago ki kalleni sosai"

Murmushi tai, ta rufe fuskarta tace "kayan nan sun maka kyau"

Sadik yace "dagaske?"
Ta jinjina kai alamar eh.

Yai murmushi yace "Alhamdilillah, Tunda sun burgeki, na haɗu da Abba a waje, munyi hira da shi sosai, Your father is very kind, Allah yasa idan aka zo nema min Auren ki ya bani, kar yace nayi yaro da yawa"

Shiru tai ta sake sunkuyar da kanta tana murmushi.

Shima murmushin yai yace "Anyway, meyasa ki ka dena zuwa school?"

Gaban ta ne ya faɗi, da tuna abunda sir Nazir yake zarginta da shi, a zahiri ta basar tace "Nothing naga ba'a komai ne a school ɗin"

"Shine, kika dena zuwa duk tunanin ki ya dameni, ga shi ba ki da waya balle in dinga kiran ki a waya"

Tai shiru ba tace komai ba.

Sadik yace "yanzu dai zaki zo bikin yayan nawa?"

Farhan tace "Ai ka kawo katin gayyata, za'a barni insha Allah"

Murmushi Sadik yai, wani farinciki ya kama shi, yace "Alhamdilillah, naji daɗi sosai"

Farhan tace "meyasa kake murna dan zan zo?"

Ya so ya gaya mata dalilin sa, amma se ya fasa dan yasan tsaf zata fasa zuwa,  ya gyara tsayuwar sa yace "My dan Allah ya zan dinga samunki a waya ne? Kin ga hutu za'ai ina son in dinga jin muryar ki, ko in dinga zuwa gida in ganki?"

Zare ido Farhan tai, ta girgiza masa kai tace "A'a, Abba ze tambayi dalilin zuwanka"

"To meye a ciki? Se mu faɗa masa gaskiya"

"A'a dan Allah kar ka dinga zuwa"

Sadik yace "to naji, yanzu ki bani lambar da zan dinga kiran ki in same ki a waya"

Farhan ta ɗan yi shiru, dan tabbas ita ma tana son hanyar da zata dinga waya da shi, dan ko ba komai a yanzu bayan karatun ta ba wanda yake ɗebe mata kewa sama da Sadik.

A hankali tace "ka bani lamabar wayar ta ka, idan na samu waya ni se in kira ka"

Yace "ki min ko flashing ne, ni kuma zan kiraki insha Allah"

Ya ɗakko jotter ya rubuta mata ya bata.

Tace "Bari in koma gida, kar a fara nema na"

"Ok to shikenan, amma tsaya muyi hotuna, wand zan din ga kalla ina jin daɗi"

Ba tace komai ba se murmushin nan nata me ɗaukar hankali.

Ya ciro wayarsa yai mata hotuna, sannan ya kalle ta yace "se Allah ya kaimu Lokacin bikin, i love You, take a good care of yourself"

Juya tai tana murmushi ta na jin yadda kalaman nasa ke sake tasiri a zuciyar ta.

Shi kuma ya koma motar su.

Yana shiga Khairat tai tsaki.

Ya kalleta yace "ke kuma lafiya?"

Khairat ta yamutsa fuska tace "kai kam me ka gani a wannan bagidajiyar 'yar talakawa?"

A hargitse Sadik ya kalleta yace "wallahi ki ka kuma zaginta sena miki rashin mutunci, a haka nake sonta"

"Allah ya baka haƙuri, amma gaskiya ta fiye kidahumanci, ace dabarar da zatai ta fito ma se da na gaya mata, ta fiye tsoro gashi kamar ba wayayyiya ba, ga ta yarinya sosai"

Sadik be ce mata uffana ba ya fara jan motar, jin yai mata banza ya sa ta ja bakinta ta tsuke, dan ta san idan ta matsa kuma, faɗa za suyi.

Suna tafe lokaci lokaci, seya shafi sumar kansa yai murmushi, yana jin so da ƙaunar Farhan ɗin na ratsa shi.

Kai tsaye gidansu suka wuce, suna zuwa yai parking a waje ya kalli Khairat yace "sauka, ni zani wani guri ne yanzu, maybe za'a kawomin wandon jeans, ki karɓa ki bawa Mother ta ajiyemin"

Khairat ta ɗan taɓe baki tace "to" ta buɗe motar ta fice, shi kuma ya ja motar yai gaba.

Khairat kuma ta shiga cikin gidan, sosai gida ya fara ɗaukar harami, saboda shirin shiga hada hadar biki.

A falo Khairat tai karo da Nana, tana ta hira ita da talatu me aiki, ta kalli Nana tai tsaki.

Nana ta kalli Khairat tace "Sannu tsaka"

Ba ta kuma kula Nana ba, ta shiga Kitchen ta ɗakko madara a roba, ta dawo falo ta na sha.

Dawowarta babu daɗewa, Sadik ya kirata a waya.

Ta ɗaga tace "Yaya ina jin ka"

"Kije gate ki karɓo min saƙon nan ki ajiyemin"

Khairat tace "to"

Ta ajiye robar hannunta ta fita, ba daɗewa ta dawo hannunta ɗauke da wata leda me kyan gaske.

Ta zauna ta buɗe ledar ta fito da wani haɗaɗɗen wandon jeans, kai da gani kasan wandon me tsada ne sosai, sedai abun takaici duk an yayyaga wandon ta cinya zuwa gwiwa, kamar kare ya tattauna.

Nana ta kalli wandon a ranta tace 'wannan wane irin wando ne?'

Faruk da ke fitowa daga ɓangaren Mother yace "Khairiyya, wannan wandon fa?"

Khairat tace "Wandon Prince ne, yace in karɓa in bawa Mother ta ajiye masa, kuma ban ganta ba"

Faruk yace "wannan wandon na ganshi Online ana advertising ɗin sa, yafi dubu goma a kuɗin Nigeria"

Khairat tace "Ai Sadik akwai rigima in yaso abu, amma wandon yayi kyau sosai"

Faruk yace "hakane, ina ga dai Mother ba ta nan, amma ki ajiye masa shi a wani gurin"

"Ko kuma in baka ka ajiye masa?"

Faruk yace "No, ajiye masa, Mother yace ko bawa, akan wandon nan se ya ɗagamin hankali"

Khairat tace "ok bari in Ajiye masa kawai"

Nana kam jinjina lamarin ta cigaba da yi a zuciyar ta, yanzu wannan wandon me kama da tsumma ne wai yafi dubu goma, gaskiya mutan Gidan nan ba su san darajar kuɗi ba, wannan ai almubazzaranci ne"

Faruk kuwa tuni ya bar falon, Wayar Khairat ce ta fara ringing, dan haka ta miƙe ta fita waje dan ta amsa wayar.

Tana fita zuciyar Nana ta dinga raya mata abubuwa daban daban, dama a ƙule take da Sadik da Khairat ɗin gaba ɗaya, dan haka ta miƙe ta waiga falon taga babu wanda yake kallonta.

A hankali ta ɗau ledar da wandon yake, ta ciro wandon ta zura a hijjabin ta, ta zaga kan baranda ta samu wani ruwan mopping da aka gama mopping da shi yai baƙiƙirin saboda datti, ta zura wandon a ciki.

Seda ya naɗi ruwan dattin nan Sosai Sannan ta matse shi, ta yar a gurin ta ƙara gaba.

A ranta tace "gobe ma ka sake zagina da kai da wannan shashashar Khairat ɗin, zaku gane kuren ku"

Ita kam Khairat ko da ta koma, ta cigaba da sha'anin ta, ta manta da batun wandon Prince.

WANDA SUKA RIGA SUKAI PAYMENT, IDAN FREE PAGES SUKA ƘARE SU KAWAI ZAN TURAWA TA WHAT'S APP, WANDA BE PAYMENT BA ZE IYA SA A MANHAJAR AREWABOOKS, DAN YAFI SAUƘI.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

19_20

Nana kam zuba ido ta yi ta ga yadda za'a kaya da wannan rigima.

Wandon Prince kuwa tuni ya koma tsumman ƙarfi da yaji, saboda yadda aka dinga sauke tukwane da shi.

Wandon yai baƙi ƙirin ya fita daga hayyacin sa.

Sadik kuwa da ya tafi nasa yawo be dawo ba se wajen sha ɗaya na dare.

Da takeaway ɗin sa ya dawo, dan karma ya shiga cikin gidan su, ya haɗu da Yarinyar da yafi tsanar gani wato Nana.

Ya so ya shiga gidan ya ga wandonsa, amma ya fasa ganin dare yayi, ya wuce part ɗin su.

Usman na kallon sa Sadik ya zo ya wuce, ya shige bed room ɗin sa, ya zauna yaci Abincin sa, yai wanka sannan ya nemi guri ya kwanta, sedai kwanciyar ta sa ke da wuya, yaji yanayin da ya saba ji ya fara bijiro masa, take bacci ya ƙauracewa idonsa, se tunanin Farhan da ya dinga masa yawo a ka.

Duk yadda ya so ya rintsa amma abu ya gagara, se juyi kawai da yake akan gado, ya rintse idanun sa sosai amma ba abun da ya sauya daga yanayin da ya ke ji.

Duk da yanayin da yake ciki, ba ya hana shi murmushi, lokaci lokaci idan ya tuna Wasu daga halayen Farhan, na tsoro da kuma tsananin Kunya.

Abu kamar wasa Bacci ya gagari Sadik, maimakon ya tashi ya ɗau carbi, ko yai salla kawai se ya janyo laptop ɗin sa, ya kunna.

Films ɗin da su Nasir suka tura masa, ya buɗe ya fara kallo da nufin ko ze manta da abunda ke damun sa.

Sosai ya nutsu ya fara kallon film ɗin, kamar wasa film ɗin ya burgeshi yaji yana son ganin yadda za ta kaya.

Da ya gama episode ɗaya idan yai niyyar kwanciya, se yaji lallai yana son ganin me ze faru a next episode.

A hankali Film ɗin ya cigaba da burge shi, Soyayya ce me tsayawa a zuciya tsakanin Jarumin film ɗin da jarumar film ɗin, kasancewar film ne na masarauta, shi ɗan sarki ita kuma baiwa ce a gidan.

A hankali kuma Film ɗin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, yadda aka fara bayyanar da abunda ya zarce ƙa'ida.

Da fari ya fara jure kallon cuddling da kisses da ake nunawa, ya dake ya cigaba da kallon, a hankali kuma aka fara zarce wannan matakin aka shiga nuna romance tsakanin jaruman, da yadda yake samar musu da meeting point, a cikin wani lambu, yaje suyi hirar su ta masoya ba tare da kowa ya sani ba, wanda a nan ne a hankali suka fara da kissing.

Series ɗin yai matuƙar burge Sadik, sedai fa kansa ya soma cigaba da wuta, dan baze iya jure abunda yake cigaba da kallo a system ɗin ta shi ba.

Kashe system ɗin yayi ya saketa ta faɗa ƙasan gado, ya dafe kansa tare da cije laɓɓansa na ƙasa, ya firzar da wata iska yace "Subhanallah, Nas why? Meyasa zaku turamin irin wannan Film ɗin?"

A hankali ya tashi, ya tafi toilet yai wanka da ruwa me sanyi, ya dawo da ga shi se boxers ya kwanta.

Wayar sa ya laluba, ya nemo hotunan Farhan da yai mata ɗazu.

He Just stat zooming her beautiful face, seda hoton fuskar tata ya cika screen ɗin wayar ta sa.

Ya ƙara zooming ɗin hoton, kyawawan leɓenta suka bayyana Sosai, da fararen haƙoranta kasancewar ta yi murmushi a hoton.

He just start imagine himself kissing that her beautiful lips.

Ya dinga sauke ajiyar zuciya a jejjere, a hankali ya ajiye wayar ta sa, yai ruf da ciki a kanta, tare da ƙanƙame pillow, yana jin yadda zuciyar sa ke harbawa da sauri, ga wani abu da ke masa yawo tun daga kan sa har ƙafafuwan sa.

A haka bacci yai awon gaba da shi.

Seda Sadik ya makara sallar Asuba, dan be kwanta da wuri ba, ga tarin mafarkai barkatai da yai tayi.

Ya tashi yaje yai wanka yai sallar Asuba, ya koma bacci.

Se wajen tara da rabi Sannan ya fito falon su dan yin break fast.

A falon ya tarar da Faruk shima yana karyawa, ya nemi guri ya zauna yana ta wani ciccin magani, kamar wanda aka tursasa yai wani abu da baya so.

Faruk ne yace "naga wani wando a gurin Khairat, tace min naka ne, wandon yai kyau sosai"

Se yanzu wandon ya faɗowa Sadik a rai yace "Eh jiya aka kawo shi, se na shiga gidan yanzu zan nemota ta bani"

Faruk yace "good" daga nan ba wanda ya kuma cewa komai, Sadik ya ɗebi Abincinsa ya koma gefe.

Farhan kuwa da ta koma gida, kyakykyawar ajiya ta yiwa lambar Prince, ta na yi ta na murmushi idan ta tuna yadda ta ganshi cikin manyan kaya, ba ƙaramin kyau yai mata ba.

Haka ta ƙarasa wunin ranar cikin annashuwa da farinciki, lokaci lokaci ta kan ɗakko takaddar da ya rubuta mata lambar sa, dan jin ƙamshin turarensa da ke jikin takaddar.

Da safe kasancewar ba makaranta, yasa Farhan ta kammala ayyukanta na gida gaba ɗaya, ta koma ɗakinta tana karyawa.

Umma ce da Abban ta zaune a tsakar gida suna karyawa, can Abban Farhan yace "jiya yaran nan da suka kawowa wannan Yarinyar katin gayyata, 'ya'yan Alhaji Abdullahi me turare ne fa"

Umma tace "Ikon Allah, ina ta samo yaran wannan mutumin?"

"Ahh makaranta mana, kin manta makarantar da take yi ne?"

Umma tace "ban manta ba, ni dai ina fatan ta kammala Makarantar nan Lafiya a aurar da ita, dan ina jin tsoron cuɗanyar su ita da yaran masu kuɗi"

"Haba ki zama me kyautata mata zato mana, mun san tarbiyyar da muka bata ai, kuma ni yaran na gansu a nutse, ba rawar kai shiyasa na bar yarinyar ma ta shigo, kuma ni da ki kai zancen ta gama Makaranta a aurar da ita se ki ka tunanin da batun Yaron nan Sunusi"

Umma tace "Wane Sunusin kenan?"

"Sirikin ki mana, Wannan ba barbaren yaron, babban Almajirin malam Abbas. Na yaba da hankalin Yaron sosai, Malam Abbas ɗin ne da kansa ya zo min da zancen ya na son in bawa Sunusin Auren ta, ni kuma na gamsu da nustuwar yaron, nace masa ba damuwa amma ya bari ta ɗan ƙara girma kan ayi Magana"

Umma tace "Alhamdilillah, Allah ya tabattar da Alkhairi, tana gama wannan Makarantar se ayi Magana, Allah ya tabattar da Alkhairi"

Ƙosan da Farhan ke taunawa a bakinta, tafi ƙarfin mintuna tana kokawa da shi amma yaƙi haɗiyuwa, ji tai gaba ɗaya test ɗin bakinta ya ɗauke.

Gaskiya Sunusi be mata adalci ba, gaisawa ce da girmamawa tsakaninta da shi, dan me za'ai mata haka?

Gaba ɗaya, ba ya cikin tsarin ra'ayinta, ba ta san me ake ji a so ba, se akan Prince ɗinta, gashi ɗan gaye me aji, gashi me kyau, ina zata kai Sunusi, ga baƙi kamar an rina shi, ga tsagu a fuskarsa kamar ƙwarya, seya shafe sati yana saka yadi ɗaya, dama batun gayu babu shi, sedai Sunusi akwai haddar Alqur'ani me girma, dan gwani ma ake cema sa, da ka yake Rubutun Alqur'ani.

Ya san Alqur'ani sosai da sosai, sedai bayan ilimin Alqur'anin nan babu na hadisi, babu na fiqihu, amma idan ya zauna ze iya gaya maka adadin ayoyi na kowacce sura a cikin Alqur'ani, sau nawa Allah ya ambaci kowane Annabi, sau nawa sunayen Allah suka zo a Alkur'ani, adadin sunan Allah nawa ne a Alqur'ani da in da aka ambace su, duk da ka yake irin wannan abubuwan.

Duk da fankar ɗakinta na ta uban gudu ta na bada iska, Amma ita wata irin zufa takeyi, sam ta kasa samun nutsuwa.

Ummanta kuwa cigaba su kayi da hirarsu, yayin da Farhan kuwa ta shiga cikin zullumi da damuwa, dan ita a duniya yadda take ji a zuciyar ta, idan har ba Sadik ba, ba zata iya auren kowa ba.
Duk da ana yawan faɗa mata Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai, kuma babu lallai ya Aureta, amma ita yadda Sadik ɗin ke nuna mata ba ta jin ze kasa Aurenta, Amma idan aka haɗa ta Aure da Sunusi an gama cutarta, yanzu ta san ciwon kanta, ta gane menene so meye daɗin sa, sam zuciyarta ba zata iya karɓar Sunusi a matsayin mijin Aure ba!.

Sadik kam cikin gida ya shiga, yana zuwa ya tarar da Inna a falo Nana na kusa da ita, da sauran ma'aikatan gidan da ke ta shige da fice, da fara shirin karɓar baƙi, dan saura kwana biyu a fara biki, gidan a cike yake da mutane.

Sadik na ganin Inna ya ɗan ɓata fuska dan baya son damuwar tsohuwar nan, amma ya basar ya ɗan risina yace "Ina kwana?"

Inna ta ɗaga kai ta kalli Sadik, ta ɗan yi murmushi me cike da ma'anoni tace "lafiya ƙalau ka tashi lafiya?"

"Lafy ƙalau" ya amsa tare da miƙewa ze tafi.

"Su sauran jama'ar ɗakin ba zaka gaishe su bane?"

Haushi ne ya kama Sadik, ita dai tsohuwar nan ba ta san zaman lafiya kwata kwata, tun da dai ya gaisheta meye na wani seya gaida sauran mutanen ɗakin?"

Juyowa yai ya tsurawa Innan ido amma yaƙi magana.
Nana kuwa zuciyarta se dukan bakwai bakwai take, tana fargabar kar ya gano waitar da tai masa.

Ana haka sega Mother ta fito, akan Sadik ta fara sauke idonta tace "Sadik har ka tashi da safen nan haka?"

Inna ta kalli Mother, kusan ƙarfe goma na safe, amma tana kiran har ya tashi da safen nan.

Sadik cikin shagwaɓa yace "Mother, ina wandona?"

"Wane wandon?" Ta tambayeshi cikin rashin fahimta.

"Wanda Khairat ta baki ko ajiyemin" ya bata amsa.

Mother tace "A'a ba ta bani komai in ajiye maka ba, ni yaushe rabon da in sa Khairat a idona ma?"

Sadik yace "jiya fa nace za'a kawomin saƙo ta karɓa ta baki ko ajiyemin"

"To ni ba ta bani ba, kuje can ku ƙarata"

Sadik ya ɗan fesar da iska daga bakinsa yace "yau a nan gidan ta kwana?"

"A'a a gidansu ta kwana, amma nasan anjima kaɗan zasu zo"

Be ce komai ba ya jinjina kai ya bar falon.

Inna ta ɗago ta kallesu kawai ta girgiza kai.

Nana kam cikinta ya fara ɗurar ruwa, dan idan Asirinta ya tonu ta shiga uku.

Nan ta ga sam ba ta kyauta abun da tayi ɗin, be kamata ace tayi haka ba, duk da a ƙule take da Sadik da Khairat tayi hakan ne dan huce takaicin wulaƙancin da suke mata, amma kuma se taji gaba ɗaya ba ta kyauta ba.

Wajen ƙarfe sha ɗaya Khairat suka zo gidan, ita da 'yan gidansu, se iyayin yawon karɓar ɗinki da zuwa gurin Saloon take yi, gaba ɗaya ta manta da batun ajiyar Sadik.

Kamar an jefo shi se ga shi ya kuma dawowa, ya tarar da Khairat ɗin a falo, ita da wasu 'yan uwansu zasu koma gurin tela, Mother na musu sautu.

"Malama ina kayana?" Shine abunda yace da Khairat ba tare da ya kula kowa ba.

Tana ganinsa gabanta ya faɗi, dan gaba ɗaya ta manta, se kuma ta ga kamar ta bawa Mother ai.

"Na bawa Mother tun jiya"

"Na tambayi Mother ai, tace baki ba ta ba, ina kika ajiyemin kayana?"

Mother tace "Ni baki bani komai ba"

Nan Khairat ta shiga wulƙita idanu, dan gaba ɗaya ta manta da batun wandon nan ta shiga sabgar ta.

Cikin zafin rai Sadik ya daka mata tsawa "ina wandona malama?, ina miki magana amma kin tsaya kallo na"

"Am..wallahi Sadik ni kamar Mother na.."

"Dalla rufemin baki, wallahi sekin nemo min abuna, daga cewa ki karɓi abun ki bawa Mother ta ajiyemin seki ɓatarmin, a haraba fa naga ledar kamfanin wandon tana yawo, duk in da yake ki nemo min abuna na gaya miki"

Duk Wannan bala'in a gaban babar Khairat ɗin Sadik ke zazzaga mata, ba ta ido ba Komai haka ya rintse ido yana masifa.

Mother tace "Kai dai ka cika rashin haƙuri, Khairat kiyi tunani ina kika ajiye masa?"

Khairat da idonta ya cika da ƙwalla tace "I can't remember, na zata na baki ne, kuma yan...

"Wallahi sekin nemo min, na gaya miki gobe in Allah ya kaimu zanyi amfani da shi, ki nemomin kayana kawai, careless girl"

Nana kam se hailala da salati take, kar a ɗago wannan ɓarnar da tayi.

Sadik kam yana uban huci, haka ya bar falon.

Mother tace "ohh ni Hauwa'u Allah ya shirya min Auta, Khairat kiyi ƙoƙarin tuna in da kika ajiye masa wandon nan dan Allah kar ya zo ya kuma ɗaga mana hankali.

Jiki a sanyaye Khairat tace "wallahi Mother na zaci na baki ne, wallahi na manta yadda nai da wandon"

Sadik na fita yaci karo da abu akan baranda, abunda ya ɗau hankalin sa shine tambarin kamfanin wandon fa yai siyayya.

Tsayawa yai, yasa hannu ya ɗago wandon, aikuwa Tabbas shine, ya yi duƙun duƙun, da alama anyi goge goge da shi ha baƙin tukunya a jiki.

Wani abune ya soki ƙirjin sa, nan da nan jikinsa ya ɗau rawa.

A fusace ya koma falon yana wani irin huci, yana shiga ya jefawa Khairat wandon a jikinta.

Da sauri ta kauce, kasancewar yadda wandon ya koma tsumma, ya fita da ga hayyacin sa.

"Wannan shine abun da na baki ajiya, aka mayar da shi haka ko?"

Mother tace "ba dai wannan ne wandon ba?"

Tabbas shine, amma ya akai haka ta faru ya koma haka.

Cikin kuka Khairat tace "wallahi ban san yadda akayi ya zama haka ba, nasan a cikin ledar sa yake.

Mother ta ɗaga wandon, ba shi da maraba da tsumma.

Inna da tun ɗazu ba ta tanka ba se yanzu tace "Wannan ai tsumma ne, shine wandon da ake ta rigima a kai?"

Talatu me aiki tace "Ai wandon sabone"

Inna tace "wannan ɗin, amma na ganshi duk a yayyage? Ya za'ai sabon Wando a yage haka kamar na mahaukaci"

Duk da halin da Nana ke ciki na regeretin, se da tai dariya jin abunda Inna tace, duk yadda ta so riƙe dariyar ta kasa, ta miƙe ta bar falon tana darawa.

Sadik kuwa ji yai tamkar zuciyarsa ta tsaga ƙirjinsa ta fito.

Mummy tace "Khairat baki kyauta ba gasky, careless ɗin ki yayi yawa, nawane wandon Ni se in biya kuɗin wandon?"

Wata uwar harara ya gallawa ƙanwar mahaifiyar tasa yai waje yana fidda numfashi.

Inna ta girgiza kai, ganin yadda suke ta wani lallaɓa shi yana fizgar kai, sam ba ɗa'a.
Ita kuwa Khairat fashewa ta sake yi da kuka.
Mother ta janyota tana rarrashin ta, suna mamakin yadda a lamarin ya faru.

Farhan kam abun duniya ya hanata sukuni.
Tunda taji zancen Sunusi ko Abincin kirki ba ta iya ci, bacci ma gagararta yake yi, saboda tsabar damuwa.
Ba ta san meyasa iyayenta haryanzu suke rayuwar mutanen da ba, meze sa kawai ai mata miji ba tare da neman yardatta ba, shikenan an mata shamaki da kawo kowa tace ta na so.

"Yaya tunanin me kike ne?"

Muryar cousin ɗinta Huzaifa taji, wanda ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi.

Murmushi ta yi tace "ba abunda nake tunani"

Ya kalleta yace "ba wani nan, kin san tun yaushe na shigo, ina ta magana kinyi shiru, na shigo Umma ma bata nan"

Farhan tace "Kaga ni ba wannan ba, dan Allah wayarka da kuɗi a ciki?"

"Eh da kuɗi, amma ba yawa me zaki da ita?"

"Waya zanyi yanzu zan baka"

Ya sa hannu a aljihunsa, ya ciro wayar duk screen ɗin wayar ya tsatsage, wayar ta sha jiki, ya miƙa mata yace "kuma ki ka cinyemin kuɗi sekin biyani, minti ɗaya da rabi na baki"

Murmushi tai tace "godiya nake gwani Huzaifa"

Abba na son a kirashi gwani, saboda a duniya ba shi da burin da ya wuce haddace Alqur'ani.

Yace "kai kin sa naji daɗi sosai, in Allah ya yadda se na wuce ki a hadda"

Farhan tace "bari fa, na riga na wuce ka"

Murmushi yai ya fita yana faɗin, 'aikuwa zan baki mamaki"

Bayan ya fita, ta fito tsakar gida ta duba, ta ga Umma bata nan ta fita.

A hankali take tafiya kamar mara gaskiya, ta je ta duba ɗakin Abba ta tarar yana bacci, ta koma ɗakinta ta kulle ta saka sakata.

Litattafanta ta zazzage, ta ɗakko lambar Sadik, jikinta na rawa saboda rashin sabo, gani take kamar ana kallonta.

Jiki na rawa ta kwafi lambar ta sa, ta danna kira.

Sadik na kwance ya yi ruf da ciki, zuciyarsa na ta tafasa akan asarar da Khairat tai masa, wayarsa ta hau ringing.

Wani dogon tsaki ya ja ya ɗauke kansa da ga kallon wayar.

Tai ringing harta katse be ɗauka ba, gaba ɗaya se taji ba daɗi, amma se tai masa uzurin ko yana wani abun ne.

Ta tattare litattafan, ta mayar cikin jakarta, ta maida jakar ma'ajiyarta.

Taita dakon ko Prince ze biyo wayara, amma shiru.

Ba ta gaza ba ta sake kiran layin nasa, a fusace ya fizgo wayar ya ɗaga cikin masifa yace "Wai waye ne?"

Cikin sanyin muryarta, me sigar shagwaɓa tace "nice fa"

Wata irin ajiyar zuciya ya ja, tare da lumshe idanunsa, ba tare da yace komai ba.

"Ka na ji na kuwa?"

"Ina jinki Princess, ina tattaro kalaman ban haƙuri ne, na rashin ɗaga wayarki da farko, sannan kuma nai miki shouting, bari in kira ki"

Ya katse kiran, sannan ya kirata, seda ta kuma leƙawa tsakar gida ta ga ba kowa, sannan ta koma ta zauna ta ɗaga wayar.

"Ina fatan an karɓi ban haƙurina" yai maganar cike da kasala.

Ɗan tura baki tai tace "naji muryarka wani iri, meke damunka?"

A shagwaɓe yace "Princess ɓatamin rai akayi zanyi kuka"

Dariya Sadik ya bata tace "Subhanallah, kuka kuma?"

"Eh mana"

"No, sorry kar kayi kuka, kaifa namiji ne kuka ai se mata"

"Khairat ce ta ɓatamin rai"

Tace "am sorry ni ban tambayeka ya kuka je gida ba?"

"Lafiya ƙalau, wandon nan da na siya, aka kawo nace ta ajiyemin ta bari akai mopping da shi, wai an zata tsumma ne"

Kwashewa da dariya Farhan tayi, dan sosai ya bata dariya.
Cikin dariya tace "to ai ba kowane yasan wannan wandon gayu bane, abu duk a yayyage"

"Au haka zakice ko? Shikenan"

"A'a kayi haƙuri kasa wani"

"Ai raina ya gama ɓaci, sena hukunta ta akan abunda tayi"

"A'a dan Allah kayi haƙuri, tsautsayi ne"

"A'a wannan ba tsautsayi bane, za ta gane kurenta"

"Dan Allah kayi haƙuri mana"

Sadik yace "ko zan haƙura se nayi tunani, duk da ita ma ina sonta, duk wadda Allah ya bani a cikin ku ina so, sedai na fi son ki, da ke ki kai laifin da tayi ba abunda zan iya"

Ɗif Farhan tayi taƙi magana, Sadik yace "ya dai Baby Princess, naji kinyi shiru"

"Ba ka cemin ƙanwarka ce ba?"

"Ai cousin ɗina ce, akwai Aure a tsakanin mu"

Take Farhan taji zuciyarta na tafasa, jiki a sanyaye tace "se anjima"

Sadik yace "Malama kar ki kashemin waya, ban gama Magana ba"

A ɗan hasale tace "to ai aiki zanyi"

Rungume pillow yayi yace "na so ace am with you right now, in ga kishi na a kyakykyawar fuskar nan taki Baby, da wasa nake miki wallahi, tsokanar ki kawai nake"

Tura baki tai kamar yana ganin ta tace "to ni ina ruwana in ma dagaske kake"

"Ke ko kike da ruwa Yarinya, ba zaki tabattar da hakan ba, se kin ganni da wata, amma bana fatan hakan, ke kaɗai kin ishi Prince, am sorry kinji Babyna wasa nake miki"

Motsi ta jiyo a tsakar gida, dan haka da sauri tace "se anjima"

Ta kashe wayar, kallon wayar yayi, tare da yin murmushi, ji yai duk damuwarsa ta gushe, ya ji daɗin yadda yanzu take sakin jiki harta faɗa masa abunda yake ranta, a hankali yana sake gane halayenta.

Sauka yai daga kan gadon yana murmushi, da jin daɗin yadda kishinta ya kasa ɓoyuwa.

Ita kam Farhan shiru tayi, tana sauraren wanda ke motsi a tsakar gida, Huzaifa ya leƙo ɗakinta yace "kin gama wayar?"

Tace "eh na gama, ga ta Nagode sosai"

Ya sa hannu ya karɓi wayar yace "ba batun godiya, kuɗin kati kawai zaki kawo"

Ba tace komai ba se murmushi da tai masa.

Shiru tai ta na nazarin maganganun Prince, yanzu idan dagaske yake mata fa, Khairat ma budurwarsa ce!.

Da ma ana ta masa gorin yana Soyayya da ita, tana abu kamar 'yar ƙauye, amma da gani dama Khairat wayayyiace kamar Prince, dan yakan yi mata hirar Khairat ɗin, amma ba ta taɓa kawo komai a ranta ba, saboda cewa yake ƙanwarsa ce.
Gefe guda kuma ga batun Sunusi, da ta tuno zancen Sunusin nan, se taji gabanta ya faɗi gaba ɗaya se ta rasa sukuni.
Ba ta san da wani idon zata fara kallon tsabar idon Abbanta, idan lokaci yayi tace masa ba ta son Sunusi ba ita da wanda take so.

A hankali ta zame jikinta ta kwanta, ta lumshe idanunta tana sauraron yadda bugun zuciyarta ya ƙaru saboda damuwa.

Shikam Prince zuwa yamma tuni ya manta da batun wandon sa da Khairat tai masa asara, sema nemanta da yake suje taga gurin da ya kama, za suyi party da abokan sa.

Sedai ya nemi Khairat ya rasa, Mother ta sanar masa, ko ɗinkin ba taje ta karɓo ba, tunda yai mata tijara da safen nan, ba ta kuma fitowa ba.

Ɗan girgiza kai yai yace "lallai ma yarinyar nan ba ta da kunya, tai min laifi kuma ta hau fushi, Allah ya temaketa Princess ta bani haƙuri, fa sena tattaka ta"

Mother tace "wacece kuma Princess"

Ba kunya Sadik yace "sirikar ki ce" yai maganar yana nufar part ɗin Mother.

Ɗan girgiza kai tayi ta cigaba da sabgoginta, dan bata ɗaukar maganganun Sadik ɗin da mahimmanci, tana barinsu ne a mazaunin ƙuruciya, Ina Sadik ina wata budurwa.

Duk wani shirye shirye Sadik ya kammala, daga kama guri kuɗin Abincin da zasu ci shi da abokansa duk ya kammala biya.

Ranar Laraba ya kama ranar da Sadik ɗin zeyi tasa walimar, shida abokansa saboda ranar Alhamis za'a fara bikin.

Ɗan maidaidacin hall ne ya kama, yayi kyau sosai gurin, ƙarfe biyar motoci suka fara parking a harabar gurin.

Kallo ɗaya za kaiwa matasan yaran, masu ji da tashen balaga kasan 'ya'yan gata ne.

'yan secondary, Mazansu da matan suna sanye cikin crazy jeans, da riguna me ɗauke da sunan Amarya da Ango a gaba, baya kuma sunan mamammalakin rigar.

'yan makarantar sun wa Sadik kara, dan harda 'yan primary a cikin wanda suka zo partyn.

Shikansa uban gayyar duk da Asarar da Khairat tai masa, amma ya saka wani wandon, yayi kyau ya fito a ainihin ajebon sa, sumar nan tasa afro style ta sha wanki da mayuka, se wani irin ƙyalli take.

'yan mata sangan sangan se yawo suke a cikin maza da matsastun riguna da wanduna, duk sun matse halittun Jikinsu.

Tamkar jinsi ɗaya suke, haka suke shiga suna fita a cikin mazan nan, ba ruwansu da wannan namiji ne waccan mace ce.

Ita kanta Khairat da taje gurin, seda ta sarawa rashin ji irin na 'yan makarantar su Sadik, duk itama ta su makarantar suna nasu rashin jin, amma su Sadik sun damesu sun shanye.

Nan aka fara raye-raye, da ɗaukar hotuna, su Nas suna ta zuba rashin mutunci, da tanka 'yan matan in anjima su rungumo waccan, ko su kamo waccan suna rawa.

Shikansa uban gayyar haka 'yan mata suka baibaye shi, da sunan ɗaukar hoto suna rungumarsa, dan duk taƙadirancin Sadik a school, ba ruwansa da rungume rumgumen mata.

Kan stage suka janyo shi, suka dinga juyashi da sunan rawa.

Mubarak ne yace "mutumin nifa banga Farhan ba"

Haɗe rai Sadik yai yace "in ka ganta me za tai maka?"

"A'a bakomai, ai gani nai Yakamata ace tana gurin nan dan tayaka murna"

A taƙaice Sadik yace "ba ta zo ba"

Ba'a tashi daga gurin nan ba se goma na dare, amma anci an sha yadda yakamata, wanda aka gayyata da wanda ba'a gayyata ba duk sunci sun ƙoshi.

Wasu sukaiwa Sadik keyholders da Manyan kofuna na cas, da sunan couple's ɗin a jiki, kowa da abunda ya bayar na gudunmawa saboda shima Sadik ɗin meyi ne.

Seda aka watse za su taho gida sannan hankalin Sadik ya dawo jikinsa, Mother tai masa missed calls ba adadi.

Haka ma Khairat, itama wayarta kira ne rututu a ciki.

Khairat tace "Sadik kaga kiran wayar Mother, ga na Mummy bari in kira su inji ko lafiya?"

"No ƙyalesu in muje Gidan ayi duk wadda za'ayi"

Haka ya cigaba da driving, suka tafi gida.

Sedai suna zuwa gidan, a harabar gidan suka tarar da su Mother a tsaitsaye suna kiran layinsu, dan babu wanda yasan in da suka tafi, Sadik be gaywa kowa party ya shirya ba, dan karma asa wasu su bisu suje su hana su rawar gaban hantsi.

Ganin su Mother harda shi kansa angon a harabar gidan be dameshi ba, dan ko a jikinsa, amma idonsa na sauka a na Inna yaji gabansa yai wata irin mummunar faɗuwa!

Domin sauke manhajar AREWA BOOKS, Danna wannan link ɗin.

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f

Domin gyara, Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f

21-22

Jikin Sadik yai sanyi da kallon da Inna take masa, wani irin kallo take ƙare musu tun daga sama har ƙasa.

Mother tace "Auta ina kuka tafi haka? Tun wajen goma na safe rabonku da gidan nan, ba irin kiran wayar da ba'ai muku ba amma ba kwa ɗauka, ina kuka shiga ne?"

Tsuke fuska Sadik yai yace "mun shirya party ne da abokaina, 'yan makarantar mu, shine muka je da Khairat"

Usman yace "Amm ai seka sanar, duk ka ɗaga mana hankali kun sa mutane a damuwa"

Khairat dai tai tsit tana rarraba ido.

Sadik kam ƙara haɗe rai ya fara takawa, ze nufi sashin su.

"Kai zo nan" Inna ta kira shi cikin bada umarni.

Ɗan tsayawa yai yayi jim, se kuma ya juyo ya tako in da suke ya tsaya.

Inna ta kalli Khairat ta kalli Sadik, sannan ta kalli in da Mother ke tsaye tace "yanzu ke Hauwa tsakanin ki da Allah, Laifin da yaran nan sukai ba su isa hukunci me tsauri ba? Kalli shigar jikinsu, kalli jikin wannan Yarinyar, ta bishi cikin maza, tun safe ba sa gida se ƙarfe goma na dare suka dawo, maimakon ku tsananta bincikar su, ku san matakin da zaku ɗauka, kawai iya abunda zaku ce musu kenan? Kalli wandon jikinsa kamar mahaukaci duk a yayyage kamar wanda ya zare, kalli uwar sumar kansa kamar ɗan daudu, ita wannan Yarinyar kalli suturar jikinta.
Wannan wane irin riƙo kuke wa yaran nan? 'ya'yayenku fa se Allah ya tambayeku akan rainon su, suna shekarun su ne na RUƊIN ƘURUCIYA, Komai ze iya faruwa, amma har suje su shirya abu isu isu babu sa idonku a kai, wannan wace irin rayuwa ce, a tunanin ku wannan wayewa ce? Babu sa ido akan yaranku kun bar su suyi abunda suke so? Wallahi idan baku kiyaye kun kula da tarbiyyar yaranku ba watarn za kuga abun da ba kwa so"

Cike da ƙosawa Mother tace "Allah ya kiyaye ya tsare, dan Allah kima dena wannan maganar, kar ki musu baki yara idan ba'a bar su sun huta ba ya za'ai, a kirshe su, shima  yawan takura yana lalata yara, kuma naga yaran nan sun saba da rayuwa da turawa ne, in Allah ya yadda ba abunda ze faru, yawan yi musu faɗa ma raini yake kawowa, kuma party a tsakanin su yara ba yanzu suka fara ba, kuma ba abunda ya taɓa faruwa, sunyi ne kawai dan taya ɗan uwan su murnar Auren da ze"

Inna ta jinjina kai tace "ba shakka, 'ya'yan turawa ko, shikenan Allah ya temaki turawa, Allah ya shirya"

Tana gama faɗin haka ta juya ta koma cikin gidan.

Shi kam Sadik kamar ya fashe, saboda yadda ya kumbura baki yana wani irin huci.

Mother tace "kaga abunda ka janyo min ko? Na gayamaka tunda Allah yasa tsohuwar nan ta tare a gidan nan kayi komai a hankali, in ba haka ba ido zata samana komai ta gani taita masifa"

Usman yace "Mother, dan Allah duk kuyi haƙuri dan Allah komai ya wuce, karki kuma yin wani lafin, kuma dan Allah idan ta ɗau zafi ki dena tanka mata, hakan yana tunzurata, Yanzu dai duk kuyi haƙuri"

Sadik bece komai ba ya wuce ɓangaren su, Khairat ma ta shiga cikin gidan tana sunkuyar da kai kamar munafuka.

Mother kuwa tana zuwa ɗakinta, cikin 'yan uwanta ta hau masifa tana mitar Wai Inna tana ja wa 'ya'yansu masifa tana musu baki, ita Alla alla takema ayi bikin nan tabar mata gida duk tabi ta isheta.

Suka haɗu suka dinga yi da Inna suna zagin ta.

Ita kam Inna tunda ta koma ɗakin da suke, tai shiru tana tunani al'amuran Sadik na bata tsoro da mamaki, tabbas idan aka cigaba da tafiya a haka da wannan sakacin ko sakarcin na uwarsa tabbas Yaron ze lalace.

Dan ta lura halayyar sa daban da ta sauran yayyen sa, tarbiyyar Sadik na buƙatar jajircewa da kuma sa ido, saboda kansa yana rawa fiye da shekarun sa.

Sadik kuwa gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Alla Alla yake a gama bikin nan wannan tsohuwar ta bar musu gida, ya rasa me ya tare mata take masa wannan abubuwan, ba damar ya motsa se ta haushi da masifa.

Haka yana kumbure kumburen baki, yai wanka ya kwanta, amma bacci yaƙi zuwa.

Can kuma se partyn da su kai suka dinga dawowa kansa, take surorin 'yan matan nan suka dinga dawo masa kansa.

Ƙoƙarin banzatar da tunanin yayi, amma abu ya faskara, zuciyarsa ta dinga raya masa cigaba da kallon series film ɗin nan, amma wata zuciyar ta shiga gargaɗin sa.

Series ɗin yana ƙayatar da shi, amma kusan kaso arba'in na film ɗin yana bayyanar da very hot Romance ne tsakanin masoya.

Runtse idanunsa yai, amma se ya dinga Ganin Farhan a idonsa, da wannan kyakykyawan murmushin nata.

A hankali ya furta "Oh God"

Ya ɗakko wayarsa, ya dinga kallon lambar da ta kirashi da ita, se kuma ya kalli agogo yaga kusan sha ɗaya na dare, jiki a sanyaye ya ajiye wayar, ya nemi guri ya kwanta.

Da tunani barkatai cikin ransa da haka bacci yai awon gaba da shi.

Washegari Alhaji Abdullahi ya dawo daga tafiyar da yayi, wanda ya kasance ranar fara bikin ɗansa Usman.

Da yamma ya shiga gaida Inna, lokacin kusan duk jama'ar gidan sun yo ye sun tafi gurin biki.

Cike da girmamawa suke hira shi da Mahaifiyar sa.

Can Inna ta nisa ta kalli ɗan nata tace "Abdullahi!"

Wani banbarakwai yaji, dan Inna ba ta sba kiransa kai tsaye da sunan sa haka ba, se idan ta na da wata mahimmiyar magana.

Hakan yasa shi tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan ta, yana sauraren me zata ce masa.

Cike da damuwa tace "Kamar yadda ka sani, ni mace ce me son haihuwa, Allah ya bani haihuwa, sedai duk sun koma, kaine ɗana na huɗu, bayanka na hayayyafa amma duk ba su rayu ba, ɗan uwanka Abubakar ya taso ina murna Allah ya barmin, se bayan yayi Aure ya haifi wannan Yarinyar ya karɓe shi ya karɓi mahaifiyarta"

Mamakin maimaita wannan tarihi da ta ɗakko yake yi, wanda duk wannan abun da take faɗa ya riga ya san da shi.

Ta cigaba da cewa "Ni macece me son iyali na, fiye da tunani, duk da irin son da nake maka, Allah ya ɗaga ka, kayi Aure ka dawo birni da zama, sedai ƙawa zucina akan 'ya'ya ya ragu, tun bayan da Kai Aure, nasan dama namiji wataran mijin wata ne, mace ce duk inda take hankalinta na kan mahaifiyarta.

Na ɗora rai akan jikokina, saboda ganin suma duk tsastona ne, na ƙallafa rai akan su, sedai shima sena fuskanci matarka ba ta buƙatar hakan, ba ta son 'ya'yanta su raɓi ƙauyawa jahilai.

Sena maida hankalina kan Abubakar, ba dan zuciya ta ta dena sonka da 'ya'yanka ba, sedan bana son shiga cikin lamarin iyalan ka, saboda gudun matsala da zubewar mutunci.

Ashe Habu ma bame tsawon kwana ba ne, bayan yayi aure, an haifi wannan 'yar, matar tazo sake wata haihuwar Allah ya karɓeta, bayan rasuwarta nai ta fama da shi yai aure, amma be ba, har shima yai hatsari a hanyar dawowa daga gidanka zuwa ƙauye shima Allah ya karɓe shi.

Nasan za kayi mamakin sake maimaita maka abunda ka riga kasan shi, kuma ya wuce ban yi haka dan Komai ba, sedan sake jaddada maka irin so da ƙaunar da nake maka da 'ya'yanka, saboda dukkanin ku tsatsona ne, ba zan so inga wani mummunan abu ya sami zuriyata ba.

Ja da baya da nayi na zura maka ido kai da iyalan ka, baya na nufin na sallamaku bane bana kishinku.

Ka sani na sani, ni mace ce me zafi kuma da haka nai tarbiyyar ku, ba dan na dage da addu'a da jajircewa ba, da baka taso a haka har wani yai sha'awar Aura maka 'yarsa ba.

Abdullahi, kai da yaranka ba turawa bane ba, 'ya'yanka da kai Hausa Fulani ne masu kamala da tarbiyya, dan kayi boko, ko kun zuwa ƙasashen turawa ba shi ke nufin kuma turawa bane ba.

Bari in fito maka a mutum, yaranka ba su da tarbiyya!"

Da sauri Alhaji Abdullahi ya ɗago ya kalli Inna yace "Inna ba su da tarbiyya kuma?"

Cikin ƙwarin gwiwa, da nuna isa Inna tace "Ƙwarai kuwa, 'ya'yanka ba su da tarbiyya, mussaman me sunan Ƙarami ɗan Autan ka.

Allah ya sani ina ƙaunar yaranka fiye da yadda nake sonka, ka san yadda nake son jikokina duk da ba sa zuwa in da nake, amma hakan ba ze hanani faɗin gaskiya akan su ba.

Abdullahi ka sanya idanu akan tarbiyyar yaranka, kuɗi ba hauka bane ba, kafin kai dubun ka sunyi arziki kuma sun shuɗe babu su a duniyar nan, yana daga cikin sadaka me gudana bayan ran bawa, ya haifi ɗa na gari da ze dinga aikata aikin Alkhairi.

Kana tunanin wannan? Ko kuma neman kuɗin kawai ka saka a gaba, yau kana Habuja, gobe kana gurin wancan gwamana, jibi ka na waccan ƙasar, ka bar mace da tarbiyyar gidanka matar da ita kanta tana buƙatar tarbiyya, wannan ganganci ne haihuwa da damuna.

Ba ina kushe maka iyali bane, ko ƙoƙarin haddasa maka husuma a cikin gida ba, bulaliya nake maka, naga shekaranjiya, naga jiya gashi ana damawa da mu a yau, ko kai da kai boko ka zaga duniya, ba zaka gayamin sanin duniya da zamantakewa ba, bar ganina bagidajiya bafullatanar ƙauye, shekarun da nayi a duniya naga abubuwa da dama, kuma ina iya fahimtar abubuwa da dama.

Dan haka ka kula da iyalinka, ka sa ido akansu sosai ka kula da tarbiyyar su, ka barsu da ingantacciyar tarbiyya da kyakykyawar rayuwa yafi wannan kuɗin da kake tara musu, da basu san ciwonsu ba, sedai su ɗiba suyi ta bushasha"

Tun da Inna ta fara faɗan nan, ya sunkuyar da kai, bece uffan ba seda ta kammala, ya ja nannauyar ajiyar zuciya yace "Insha Allah Inna za'a kiyaye, in Allah ya yadda zan kula kamar yadda ki ka ce"

Inna tace "to Allah ya wuce mana gaba, ya kare dukkan zuriyar Annabi daga taɓarɓarewa da sharrin ƙarshen zamani"

Yace "Ameen ya Allah, Inna nagode Sosai"

Har ya miƙe ze fita tace "fita za kayi ne?"

Yace "eh Inna"

Tace "to zo in fesa maka turare"

Yai murmushi yazo gabanta ya durƙusa, ta ɗakko turare ta feffesa masa tace "yawwa duk da naji kana ƙamshin turare ai gara ka ƙara, ai ƙamshi rahama ne"

Yai murmushi yace "hakane Inna nagode"

Tai murmushi ta cigaba da laziminta.

Maganganun Inna sun damu Alhaji Abdullahi Sosai, duk d aba ta fito ta gayamasa ƙarara meyafaru ba, amma maganganun nata sun tsaye masa a rai sosai.

Se dare sannan aka din ga dawowa daga gurin kamun da aka tafi, wanda zasu kwana a gidan duk suka taho nan gidan, dan a tare motocin suka dinga dawowa.

Wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, Mother tayi wanka ta canza kaya, ta nufi sashin Megidanta da coffee.

Tun da taje take zuba masa hira, tana nuna masa hotunan biki, sedai ta lura kamar yana tunanin wani abun ne.

"Yallaɓai ya na ganka wani iri ne? Kai da Yakamata ace kana farinciki zaka aurar da ɗanka na fari"

Kallonta yayi sannan yace "Akwai wani abu da Sadik yaiwa Inna ne na rashin kyautawa"

Haushi ne yakama Mother, wannan takurarraiyar tsohuwar ta isheta.

A fili tace "wani abun tace ya mata ne?"

"No, ba tace min yamata Komai ba, sedai tamin hannunka me sanda a cikin Magana, dan haka dan Allah idan ma da wani abu na rashin ɗa'a ko kyautawa da yake, ki ja masa kunne, nima zan masa magana bana son ranta ya dinga ɓaci akan wani abu"

Ajiyar zuciya Mother tai tace "ni dai iya sani na ba abunda yai mata, sedai kasan ba su fiye jituwa ba, amma zan masa magana insha Allah"

Yace "yayi"

Yana ɗauke kai ta dalla masa harara, gaba ɗaya haushin Inna take ji, ta fiye sa ido da son hanasu rawar gaban hantsi ita da 'ya'yanta.

Aka cigaba da gudanar da biki cikin bajinta, da kuma wadata.

Ranar Dinner Inna tace ba in da Nana za taje, wani irin bikine baza'a fara shi ba se dare dan watsewa, waye ze sa mata ido akanta.

Nana hadda kuka, tana son zuwa amma Inna ta hana.

Faruk ne ya shigo cikin shadda coffee colour, se sheƙi take kamar shine ango yayi kyau sosai.

Table of Contents

Chapters

2 chapters
  1. 1 
  2. 2 Part ɗin Mother ze nufa, amma yaga Nana a zaune kusa da Inna tana kuka.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});