Chapter 25
Chapter 25
hosana ba hatta hafsat tayi mamakin jin abunda Momyn nata tace lokaci guda ta canza tamkar ba ita ba, tsayawa sukayi suna kallonta baki asake, Ganin hakan yasa aunty babba ƙarasawa ta ruƙo hannun kowannan su , sannan cikin sanyin murya ta wanda yayi nadama tace "Haƙiƙa nasan na cutar daku sosai, Allah ma ba zai yafe mun ba, tabbas jiki na yayi sanyi, nayi danasanin abun da na aikata muku dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun........' Hawaye ne suka soma saukowa daga idon aunty babba fuskarta duk a yamutse tana kallonsu, cikin mamaki hafsat tace "Shin mafarki nake ko gaske!? Mom are u serious about what are u sanying? Ko dai kin sha wani abu ne bayan na fita? kece dakan ki kike danasani hada neman gafara a wurinsa? ɗago ido aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace "Shin ni ba mutun bace kamar kowa daba zanyi laifi na nemi gafara ba"? na zauna nayi wani tunani menene riba ta idan na cuci waɗannan bayin Allan? Allah fa dakansa ya haramta ma kansa zalunci kuma ya haramta shi atsakanin mu, kuma yace kada muyi zalunci, amma ni na kansance mai son zuciya..........' Sam ta kasa ƙarasa maganar saboda shessheƙar kukan da tafara, juyawa hafsat tayi ta kalli jahad yayin da ita kuma jahad idonta na akan Hosana wadda ke kallonta, gaba ɗayansu mamaki ne ke ɗawainiya dasu, shin taya zasu gasgata tuban da Mommyn hafsat tayi? Anya ba wata ƙullalliya bace? "Naji kunyi shiru baza ku yafe mun bane? In har baku yafe mun ba bana ji zan iya bacci adaren nan," Cikin sauri Jahad da hosana suka haɗa baki wurin cewa "Aunty mun yafe miki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya," Murmushi Aunty babba ta saki tare da sa hannu ta haɗa su duka ta rungumesu ajikinta, tana faman ci gaba da basu haƙuri akan kuskuren da tayi masu na jibgarsu da tayi, Jikinsu duk yayi mugun sanyi, gaba ɗaya kwalwarsu ta rikice sun rasa gane dawa zasu YARDA? SHIN HAFSAT ko MOMMYNSU? Taya hakan zaiyiyu ace lokaci guda sun canza musu izuwa mutanen kirki masu tausayin su? Bayan aunty babba ta janye su daga jikinta ta mayar da idonta kan na hafsat tace "daughter daga yau inaso ki ɗauke su tamkar ƙannen ki, ni kuma insha Allah zan ɗauke su tamkar nice na haife su, zan basu duk wata kula daya dace uwa tabawa ya'yanta, " Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Insha Allah mommy as from now hosana da jahad sun zama ƴan gida, zasuyi rayuwar ƴanci acikin gidan nan, babu wanda zai sake cutar dasu acikin mu," Jinjina kai aunty babba tayi sannan tace "ina so daga yanzu su koma ɗakin Ladi mai aikin mu da kwana," Hafsat tace "a'a Mommy, mattress ce kawai acikin ɗakin, gaskiya ni nafison su dawo bedroom ɗina da kwana yadda zanfi basu kulawa," Aunty babba tace "hakan ma yayi, yanzu yakamata ku shiga ciki ku huta, sannan hafsat ki taimaka ma hosana tayi wanka da ruwa mai ɗumi ko taji daɗin jikinta, Hafsat tace "insha Allah mommy," sannan ta mayar da idonta kansu hosana tace "mu shiga ciki," hannun su cikin na juna suka bi bayan hafsat har izuwa cikin bedroom ɗinta, Da taimakon hafsat hosana tayi wanka ta canza kayan jikinta izuwa doguwar riga mara nauyi, bayan ta kammala hayewa kawai tayi saman gadon hafsat, tana jiran zuwan jahad wadda ta shiga toilet yin wanka itama, Ajiyar zuciya kawai hosana ke saki amma tana jin fargabar canjin da su ka gani wurin hafsat da Mommynta, sam bata amince dasu ba, kuma taci Alwashin muddin YA OMAR yazo ƙafarta ƙafarshi sai ta bishi, 😠 **********SEHRISH************** A gajiye ta shiga cikin bedroom ɗinta bayan sun kammala gyare-gyaren gidan, sai lokacin tasamu damar yin wanka tare da alwala tafito ɗaure da towel, agaban dressing mirror ta zauna saman kujera tana Shafa mai ajikinta, bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare, sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗin kayanta, ta ɗauko dogon skirt brown color ta zura sannan ta sanya t-shirt fara, daga nan ta zura hijab tare da shimfiɗa carpet tayi sallah anatse, tun kafin ta kammala azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo, wuri ta samu gefen gadonta ta xauna, bayan sehrish ta kammala sallar ta naɗe dardumar ta mayar da ita cikin wardrobe tare da hijabin, sannan ta juya da fara'a tana gaishe da azmee "Ina yini aunty azmee," Azmee tace "lafiya lou sehrish, zo ki zauna," Ƙarasawa tayi ta samu wuri kusa da ita ta zauna, azmeee tace "sehrish wai ina wayarki take ne? Na lura tun ranar dana baki ita, ban sake ganinta a hannunki ba, kodai baki so ne? zuru sehrish tayi don ita tuni ta manta da zancen wata waya, kuma ba kowa bane yaja mata hakan ba face haroon, shine silar damuwar da tashiga harta manta in da ta jefe wayar "Ina sauraron ki ina wayar"? Azmee ta ƙara nanata mata, cikin en ina sehrish tace "Aunty azmee tun....ranar...da...kika...ban...ita..na manta inda na ajiye...ta,' ta ƙarasa maganar tana ɗan kallonta azmee tace "Sehrish kenan kin cika shiririta yanzu wayar mai tsada ita kika 6atar? To ina so ki nemo ta yau ɗin nan duk inda take, in ma saman ceilling kika turata ki hau saman ki fiddo ta, Ki kawo min ɗaki na ina jiranki,!" tana faɗin hakan ta tashi ta fuce........ tafa hannu sehrish ta shiga yi tana tunanin ta ina zata fara neman wayar, ita kanta abuƙace take da wayar ko don ta rinƙa ɗebe kewar zama ita kaɗai aɗaki, Tashi tayi cikin ƙanƙanin lokaci ta hargitsa ɗakin wurin neman wayarta, duk ta zabure har ƙarƙashin gado ta leƙa, ta bincika cikin laundry basket ɗinta, gaba ɗaya ta zazzago kayan wankinta dake cikinsa babu komai, agajiye ta mayar da kayan, zarya tashiga yi tana tunanin ina ta wurgar da ita, ci gaba da neman wayar tayi, a ƙarshe tayi deciding zuwa ɗakin junaid ta roƙesa ya kira layin wayar ko tayi ringing, cikin hanzari ta ɗauki mayafinta dake ajiye saman bed ɗinta, ta yarfa shi a head ɗinsa, sannan ta fita cikin sauri babu kowa a babban falon direct upstairs ta wuce da ƙarfi take tattaka stairs ɗin ko kallon gabanta batayi burinta kawai ta isa bedroom ɗin junaid,. Kamar daga sama taji ta bugi wani abu da ƙarfi nan take wani irin jiri ya kwashe ta, agigice tasaki wata irin ƙara ganin yarda ta tafi gaba ɗaya zata faɗi amma ina tuni yayi mata wani irin kwakkwaran ruƙo da hannu guda ya tallabo waist ɗinta, Zazzare ido sehrish tayi cikin Jin tsananin tsoro yayin da take faman sauke ajiyar zuciya, gabanta ne ya soma faɗuwa saboda tuna hannun wa take a ruƙe, sam tagaza ɗago ido ta kalle sa, ae tun daga ƙamshin turaren nan nasa ta shaida kowane ne, ɗago da ita yayi ta tsaya da ƙafafunta sannan ya wuce abunshi, juyawa sehrish tayi cikin sauri tana kallonsa ba ƙaramin wanka ya ɗauka, har sai da ya fice daga babban falon sannan ta kawar da idonta sannan ta ƙarasa haye wa upstair ɗin, har time ɗin jikinta wata irin kerma yake yi hannunta na dafe da ƙirjinta, A hankali tayi knocing ƙopar ɗakin junaid tana buga ƙopar a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47