*MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *Alhamdulillah na gode Allah da ya bani ikon rubuta wannan labarin da na daɗe ina son rubuta shi. Allah ya bani ikon rubuta abun da zai amfani al'umma.* *Ni ce ta ku dai marubuciyar nan da na saba faɗakar da ku da misaɗantar da ku, to yanzu ma na zo ma ku da sabon labari mai cike da sarƙakiya tuggu da makirci, wanda zai bar ku cikin shauƙi da zumuɗi. Ku dai ku biyo ni kun san dai ba taɓa ba ku kunya ba, wannan na daban ne mu je zuwa* Ɗanɗano Page0️⃣1️⃣ Tafiya yake yi cikin takunsa na natsuwa da kamala, Sandar dake da hannunsa yana dogarawa ne zai tabbatar ma ka da cewa makaho ne shi, kuma sandar ce jagoransa. Sai baƙin glass dake sanye a idanunsa wanda ya zauna a karan dogon hancinsa da ya dace da kyakkyawar fuskarsa. Fari ne dogo mai matsakaicin jiki, sai dai kallo ɗaya za ka yi wa kyakkyawar fuskarsa ka fahimci cewa shi ba mai yawan fara'a ba ne da sakin fuska. Yana da ƙirar jiki da cikar zati irin na cikakken ɗa namiji. Sanye yake da wani royal blue yadi mai sauƙin kuɗi wanda ake kira da yi shirunka maraya, daga ganin kayan jikinsa za ka san sun sha jiki sai dai da dukkan alamu saurayin mai tsafta ne don kayan fes suke babu datti duk da kasancewarsa makaho ne. Tafiya yake yi a cikin layin unguwar da ta kasance unguwa ce ta ma su hannu da shuni, tun daga ganin shimfiɗaɗiyar kwaltar da ta shiga cikin unguwar ta ko ina har zuwa ƙerarrun gidajen dake cikin unguwar. Unguwar ta kasance shiru ne ba hayaniya. Har ya iso daidai katafaren wani gida ya tsaya, shiru ya yi na tsawon mintuna biyu kafin ya yi knocking ɗin danƙareren gate ɗin dake gidan. Daga ciki ya ji muryar Musa mai gadi yana cewa. "Waye nan?" Don tun da ya ji ba'ayi horn ba ya san ko ma waye ba da mota ya zo ba talaka ne. Ƙarasawa ya yi don dama daga toilet ya fito yana surutu shi kaɗai. "Ko ma waye dole za ku haƙura ku koma, don ita matar kirkir dake da tausayin talakawa kuke zuwa rana ba ku yanzu Allah ya karɓi rayuwarta ba ta raye, wacce ta rage a gidan ko mutuwa za ku yi ba za ta lalle ku da gashi ba ballantana ta taimaka ma ku." Yana buɗe ƙofar ya ga wanda ke tsaye ya ce ya ce. "Mallam makaho ne?" Shiru ya ma sa bai yanka ma sa ba, sai ya sake cewa. "To daga yau sai dai ka daina zuwa don wacce kake zuwa domin ta take ba ka Allah ya larɓi rayuwarta, tsawon kwanaki hamsin kenan yau, kuma na san ka zo ta'aziyya , kuma ka zo bayan wata ɗaya da rasuwar . Ina mai ba ka shawara ka bar nan kafin waccen marar mutuncin ta fito ta ganka uwar ɗakinka ta rasu ka sani ko?" Gundura ya fara yi da maganar ta Mallam Musa sakamakon ba ya son magana ko hayaniya , ga shi Mallam Musa bai iya magana a hankali ba, cike da mishkilanci ya yamutse fuskarsa yana ƙokarin shiga cikin gidan. Da kallo Mallam Musa ya bishi yana cewa. "Sai shegen girman kai da mishkilanci, ga shi nakasashshe yanzu an koro ka ka fito." Mamy ce ta fito tana kallon Makaho tana washe baki tana cewa. "Ango ya iso daukar Amaryarsa kenan Alhamdulillah." Bai ce komai ba sai sake tsuke fuska da ya yi, yayin da Mallam Musa ya cika da mamaki to waye angon ba dai makahon nan ba. Tsuke bakinsa ya yi ya koma bakin aikinsa yayin da Mamy ke yi wa Makaho iso tana cewa. "Shigo sirikina." "Alhaji dake zaune a falo ya ɗago kai yana kallon Makaho dake shigowa tare da sallama. Yana mai amsa sallamar ta sa yana bashi izinin zama. Zama ya yi a kan lallaudan centre carpet dake tsakiyar falon "Ina wuni Daddy." "Lafiya lau Khalifa." Kallo ɗaya ya yi wa Mamy ya kau da kai kamar an masa dole ya ce . "Ina wuni Mamy?" "Lafiya lau angon Ma'eesaha." Ta amsa tana wani dariya na mugunta. Shiru falon ya yi tana jiran Dady ya yi magana sai ta ji shiru, gabadaya baya cikin tunanisa. "Alhaji" Shiru bai amsa ba sai da ta sake kiransa a karo na uku Sannan ya dawo tunanisa yana cewa. "Na'am." "Ga shi ya zo ɗaukar Amaryarsa da aka ce ya zo ya ɗauka, ka bar shi zaune." "To ai na kira ita Ma'eesha tana hanyar dawowa." "Okay, ka jira amaryar ta karasa sai ku tafi ta je lalle da kitso ne." Bai ce komai ba illa ya sunkuyar da kai ƙasa. _Ma'eesha_ Fitowarta kenan daga cikin shagon saloon tana sanye da rigar Abaya green colour, tana gyara mayafin abyarta hannunta rike da handbag ɗin ta da wayarta I phone 16 pro max. Wayarta ce ta fara ruri tana dubawa ta ga Inno ce me masu aiki. Ɗaga wa ta yi ta maƙala wayar a kunne tana maƙe kafaɗarta yadda wayar za ta zauna, ta zuge zip ɗin handbag ɗin ta ta ciro makullin motarta tana cewa. "Hello Inno ya aka yi ne?" Shiru Inno ta kasa magana don har ya nufi motarta ta bude Inno ba ta yi magana ba. Zama ta yi a driving seat sannan ta ce. "Inno lafiya kuwa." Cikin kuka ta ji muryar Inno na cewa. "Ma'eesha kada ku dawo gidan nan ki je wani wuri." Cikin faɗuwar gaba ta ce. "Me ya faru ne Inno?" Ta ji ta sake cewa. "Aure aka ɗaura ma ki yau da wannan makahon da ya taɓa ceton ran mahaifiyar ki har ta ke kyautata ma sa." Wani dariya Ma'eesha ta yi tare da cewa "No ba zai yiwu ba, kada ki dake Mani wannan wasar." Ta katse kiran wayar tana cewa. "Haba wane irin aure ba tare da an nemi amincewa ta ba, ko auren ne ma ai sai a ce na fito da wanda nake so amma ba za'a yi ma ni dole ba, ballantana s ce wani makaho wanda ko a mafarki bai isa ya zo mijina ba ballantana a zahiri?" Tsuke ta ja tare da yi wa motarta key ta bar harabar Saloon ɗin. Horn take dannawa har maigadi ya wangala ma ta gate ta shigar da motar tana mai yin yin parking a parking space. A hankali ta sako da fararen ƙafafuwanta da suka sha zanen kalli ja ba baƙi. Fitowarta yi hannunta rike da handbag ɗin ta da makullin motarta. Da sallama ta shiga falon gabanta na faɗuwa. Gabadaya suka amsa ma ya sallamar ta shiga ciki. Ganin makaho ya haifar ma ta da wata faɗuwar gabar da ba ta san dalili ba. Bayan ta gaida Dady da Mamy ta miƙe za ta nufi ciki ta ji Mamy na cewa. "Alhaji ka sanar da ita ta fito ta bi mijinta tun da ga shi nan zaune yana jira tun ɗazu. Mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, wanda har sai da ta saki handbag ɗin ta a ƙasa. "Ke Ma'eesha zo nan." A hankali ta take taku kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta zo gaban Dady ta zube. "An ɗaura auren ki da Khalifa makaho yau, ku tashi ki bi mijinki Allah ya ba ku zaman lafiya." Kallon Dady take yi kamar wata sokuwa ta ma rasa me za ta ce ma sa, don ganin abin take yi kamar wani alamara. "Da...Da...Da..." Ta ma rasa me za ta ce wani kalma za ta kama da za ta yi amfani da shi wajen yi wa Dady magana. Kafin ta samu ƙarfin zuciyar furta. "Dady wane laifi na aikata da ka hukunta ni ta wannan han?" Tsawar da ya daka mata ne ya saka ta firgita. "Tashi ki kwaso kayan sakawarki ki bi mijinki, idan kika sake yi Mani wata magana a nan sai na ba ki mamakin da ya fi wanda kike ciki?" "Ba da ke mahaifinki ke magana ba kina zaune?" Jiki ba ƙwari ta miƙe ta ɗauki handbag ɗin ta da makullin motarta ta nufi ɗakinta. Nan ta samu Inno mai masu aiki, tana ganin Inno ta fada jikinta ta rungume ta tana fashewa da matsanancin kuka." Ita ma Inno kuka take yi tana cewa. "Allah ya yana tare da ke Ma'eesha, shi ya sa na kira ki a waya na ce kada ki dawo gidan nan. Wannan kishiya mahaifiyarki ba ta tsoron Allah, so take kawai ta ga rayuwarli ta tagayyara shi ya sa ta saka mahaifinki ya aura maki makaho musaki wanda ba ya da cin yau balle na gobe, ta ya ya mace irinki da kika taso cikin gata da jin ɗadin more rayuwa za ki auri fakiri nakasashshe? Ita me ya saka ba ta saka ya auri ƴarta Agola ba, sai ke da gidan uban ki ne za'a yi ma ki wannan cin kashin?" Cikin kuka Ma'eesha ta ce. "Mamy ba ta so na ta tsane ta saka mahaifina dake son farin cikina yanzu ya juya mani baya ya tsane ni, duk da haka bai ishe ta ba sai da ta saka ya aurar da ni a inda ta san zan wahala me na yi ma ta ne, Da zuciya daya mahaifiyata ta kawo su gidan nan ita da yaranta suna cin arziki, karshe ta ci amana ta auri mijin aminiyarta suka ci gaba da zama duk da haka Mahaifiyata ba ta nuna ta ji zafin abinda ta yi ma ta na aure ma ta miji ba, ta zauna da ita da zuciya ɗaya, sai bayan ran mahaifiyata ne za ta ma ni haka sakayyarta ga Mahaifiyata kenan?" Kuka suke yi dukkansu, kamar daga sama suka ji an daka ma su tsawa. A firgice suke kallon ƙofar. Mamy ce tare da Autarta Laila. "Sannu muna munafuka kina hure ma ta kunne ko?" Cikin rawar jiki Inno take ba Mamy hakuri ta fita daga ɗakin. Ma'eesha ta kalle su da idanunta da suka yi ja ta kawar da kai ta cigaba da haɗa kayanta a cikin babban trolly tana kuka. "Hi Amaryar makaho ya kike?" Cewar Laila tana dariya. "Mamy idan ta tafi ɗakin nan zan dawo da zama don ya fi nawa girma, ko funiture ɗin ya fi nawa kyau." Mamy ta kalli ƴarta ta ce . "Kar ki damu Shalele sai yadda kike so za'ayi." Kallon Ma'eesha dake hada kaya ta yi ta ce. "Ba ke mai gidan uba ba? Har kina yi wa yarana gorin cewa su agololi ne ko? To yanzu ke da gidan uban ki ne na saka uban naki ya yi waje dake, su agolan da kike yi wa taƙama da gidan uba su ne za su yi iko da gidan, ke kuka sai ki je ki fara cin garin kwaki, don ko kayan Gara da kayan ɗaki na hana ayi ma ki su ki je can ku ƙarata. Kina hutawa anan sai dai masu aiki su gyara Maki ɗaki su wanke Maki toilet ayi maki wankin da guga, ki sa a girka Maki abinda ranki ke so yanzu duk ba wannan a gidan makaho." Laila da Mamy suka sake saka wata dariyar har suna tafawa kamar wasu kewaye. Wannan karon Ma'eesha kukanta ne ya ƙaru sosai kamar ranta zai fita, ita kadai ta san halin da take ciki a wannan yanayin. Bayan ta cika babban trolly ne ta ɗauki madaidaici ta zuba underwears ɗinta a ciki. Sannan ta dauki karamin cikinsu ta zuba kayan kwalliyarta da turarruka, sannan ta dauko set sarƙar zinarenta za ta saka Mamy ta ce ke dakata ba in da za ki je da wannan." Wani kallo Ma'eesha ta yi ma ta ta ce . "Na mahaifiyata ce ita ta bani kyautatarsa dole ne tafi da shi." Daidai lokacin Dady ya shigo yana cewa. "Me kike yi ne har yanzu?" Mamy ta yi saurin cewa. "Alhaji ka karbi sarƙar set ɗin Gold ɗin nan kafa ta tafi da shi a sace ka san dai darajarsa." "Ke Ma'eesha kawo ɗan akwatin nan." Ta mika masa kawai ta zuge zip ɗin, sannan ta bude wata drawer ta ɗauko 🏧 card ɗin ta na cire kuɗi. "Alhaji ka karbi ATM ɗin nan, su ma, ta tafi haka nan daga ita sai kayanta." Tana rufe baki ya karɓa Atm card ɗin kamar me jiran umarni.key ɗin motar dake saman handbag ɗin ta Mamy ta kalla ta ce. "Har da makullin motarta ma ka karba, don gidan da za ta zauna ba ƙofa ballantana a samu gate na shigar da motar, idan aka ajiye waje za'a sace." "Eh haka ne." Ya fada yana mika hannu. Ba musu Ma'eesha ta miƙa ma sa ya karɓa ya fice daga ɗakin. "Ai duk wani abu da na san zai Maki amfani ba zan bar ki da shi ba." Ta fada tana jan hannun Laila suka fice. Ɗayan trolly ɗin ta fara fitowa da shi ta ajiye falon ta koma ciki. "Kai makaho tashi ka dauki babbar akwatin kayanta ku tafi za ta fito da kananan." Tashi ya yi yana lalube har ya ji ya ci karo da akwati ya ja yana yi wa Dady godiya da sallama ya fita. Tana fitowa rike da dayan madaidaicin akwatin sai karami dake da kayan turarrukannta ta nufi hanyar fita ba tare da ta kallon Dady ba ballantana Mamy." Sakin baki Mamy ta yi tare da cewa. "Amarya ba sallama?" Ba ta yanka ma ta ba ta fice daga cikin falon. "Ikon Allah, ko irin sallama da iyaye a nemi tafiyarsu ba za ki yi ba kin fice ko, za ki zo gidan za ki ga wulakanci. Kasancewar tana bakin ƙofa ta ji komai ya saka ta ce. "Idan kin ga na zo gidan nan Mamy duk wulaƙancin da kika dama ki yi ma ni." Ta saka kai ta fice Mamy ta saki baki yayin da Dady ya sunkuyar da kai ya kasa kallon Ma'eesaha. "Ungo Laila ga kudin sadakinta nan dubu uku ki ɗauka ki kai ma ta hakkinta ne." Da sauri Laila ta ɗauki kudin ta fice tana dariyar mugunta. A harabar gidan ta gan su Yana gaba da babban trolly tana bin sa da kananan a baya. Daidai lokacin motar Jamil babban yaron Mamy Yayan Laila ya danno hancin motarsa cikin gidan. Ko parking ɗin kirki bai yi ba sakamakon ganin Ma'eesha na kuka, ga makaho na gaba da wata babban trolly wanda ya fi na hannun Ma'eesha girma, ga Laila na miƙa wa Ma'eesha kuɗi. "Subhanah Ma'eesha me ya same ki kuma ina zuwa da kaya?" Ba ta tanka ma sa ba ta yi gaba. kallon ƙanwarsa ya yi yana cewa. "Munafuka me kuka yi ma ta kuma yanzu?" "Aure Mamy ta saka aka yi ma ta da wancan makahon, shi ne ya zo ɗaukarta za su wuce, ga kudin sadakinta dubu uku ta ki amsa." "What?" Ya yi tambayar a firgice. Yana ƙarewa makaho kallo ganin yadin jikinsa ba ta wuce dubu ɗaya ba, kuka daga gani kayan ma sun ji jiki, ko takaman ƙafarsa ma na soso ne sai wata hular taɓa ni ka ji hadisi da ya saka. "Aure da wannan nakasashen?" Girgiza kai ya yi tare da cewa "Da sake!." Ya bi bayansu a guje yana kiran sunan Ma'eesha, har ya karasa inda suke tafiya ba ta kalle shi ba. Haka ya dinga bin su yana rokon Ma'eesha amma ba ta saurare shi ba, haka ya hakura ya bar ta ya dawo. Kamar zai tashi sama haka yake tafiya har ya isa gidan. Don yau ya kara jinjina makirci da rashin imani irin na mahaifiyarsa. *KADUNA* Da sanyin asuba ta fito daga cikin bathroom dake cikin ɗakinsu. Harara ta watsawa ƙanwarta dake zaune saman sallaya tana karatun Alkur'ani mai girma. Cije laɓɓanta ta yi cike da takaici ta yi tsuki. Bayan ta kai karshen surar da take karantawa ta kalli yayat tata ta ce. "Aunty Sidra lafiya kuwa?" Harara ta watsa ma ta tare da cewa. "Ban sani ba." "Allah ya huci zuciyarki." Ta faɗa tana mai ci gaba da karatunta, don in da sabo ta saba da halin yayar tata. Komawa toilet ta yi sakamakon jin wayar dake hannunta tana vibration Ɗagawa ta ji bayan ta rufe kofar toilet ɗin, sannan ta amsa kiran daga cikin wayar ta ji an ce. "Haba Sidra ki yi ki fito ma na kin ce na zo na ɗauke ki karfe biyar da rabi ga shi ba ki fito ba, ko na wuce za ki zo da motarki ce?" Cikin yin ƙasa da murya ta ce. "Ba haka ba ne Sadiya kin san ƙanwata Nasara tana zaune idan ta ga na fito da trolly za ta gane zan tafi wani waje ne, kin san kuma za ta iya sauro ta faɗa a gidan namu idan aka kama ni fa? Yanzu ki bani mintuna kaɗan zan tura ta wani wajen idan ta fita zan fito ba tare da motata ba don asirina zai iya tonuwa." Tana fadar haka ba ta jira jin me ƙawar za ta ce ma ta ba ta katse kiran wayar . Fitowa ta yi tana kallon Nadra dake karatun Alkur'ani ta kira sunanta. "Ke Nadra!" Nadra ba ta dakata da karatun Alkur'anin ba sai da ta kai aya ta ce. "Na'am Aunty Sidra." "Ki tashi ku je garden ki duba mani zobe na ya faɗi ina ganin lokacin da muke fira da Fahad jiya daddare." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Aunty Sidra why not ki bari sai da safe, yanzu akwai sauran duhu gari bai gama wayewa ba, idan gari ya waye sai na fita na duba ma ki. Za'a fi gani ma idan ba duhu ai, amma yanzu ba lallai a gan..." Idan ba za ki je ba ne ki fada ma ni, ai ga wayarki nan ki kunna torchlight ku je ki duba ma ni." Ba tare da ta sake yin magana ba ta miƙe tsaye tana cewa. "Bari na je na duba ma ki." Fita ta yi daga ɗakin ba tare da ta cire dogon Hijabin dake jikinta ba, wmhannunta rike da wayarta tana cewa. "Allah ya huci zuciyar Amarya a gidan Yaa Fahad, ai bai kamata a ce yau za'a ɗaura ma ki aure kina faɗa ba." "Ke dai kika sani munafuka." Sai da ta tabbatar ta nufi Garden ɗin sannan ta janyo trolly ɗin ta daga cikin wardrobe, kasancewar dogon Hijabi har ƙasa ta saka ba's ganin ko me take ɗauke da shi. A hankali ta bude ƙofar ɗakin bayan ta rataya handbag ta saka wayarta ciki. Akwai mutane a falon wasu na kwance wasu na zaune, kasancewar bikin auren Sidra ake yi ƴan uwa da abokan arziki na nesa duk sun zo garin, ɗakin ɓakin ya yi ma su kadan wasu suka kwana a falon. Cikin sanɗa take tafiya wata ma ta dake zaune ta ce. "Ke wace ce nan ke sanɗa?" Sai da gaban Nadra ya faɗi sannan ta juyo ta ce. "Ina kwanaku?" "Oh Amaryar ce ashe, lafiya lau ya kike?" Suka hada baki wajen amsa gaisuwar, wata dattijuwa ta ce ni fa ba na banbance wace ce Sidra wace ce Nadra." Wata buduwar ta ce . "Wacce ta fara fitowa ta karasa ta durƙusa ta gaishe ku ita ce Nadra, wannan ta yanzu kuma ita ce Sidra wacce za'a ɗaura wa auren yau, ai suna da banbanci ita Amaryar Sidra ai fara ce, ita kuma Nadra baƙa ce." Ita dai ba ta bi ta kansu ba ta wucewarta waje. Sai wata buduwar ta ce "Ai wannan Amaryar ba ta da kirki wallahi, jiya da Nadra ta ce mu zo mu kwana a ɗakinsu tun da su biyu ne amma fir wanan Amaryar ta ce wai ga falo nan ai, Sidra ba ta da kirki." Suna ta firarsu har Nadra ta dawo ta yi ma su sannu ta shiga ɗaki. Sai dai ba ta ga Sidra ba a tunaninta tana toilet ne don haka ta koma ta zauna a saman sallayarta tana cewa. "Aunty Sidra ban ga komai ba wallahi." Ta cigaba da karatunta don hadda take yi ba da Alkur'ani take karatun ba. _Sidra_ Tana zuwa harabar gidan ba kowa maigadi dawowarsa daga masallaci kenan ya ga tana kokarin fita ya ce. "Amarya lafiya kuwa." Kamar ba za ta yi magana ba ta ce. "Zan ba kawata saƙo ne tana waje." "A dawo lafiya." Ya fada yana zama kan kujerarsa hannunsa rike da carbi. Tana ƙarasawa ta buɗe bayan motar ta saka jakar kayanta sannan ta zagaya ta zaune wajen me zaman banza. Ba tare da ɓata lokaci ba Sadiya ta yi wa motarta key suka bar layin. "Na daɗe ina jiran ki fa." "Wallahi Nadra ce nake ta so na ɗauke hankalinta kar ta ga fita ta da akwatin kaya ta tona ma ni asiri shirina ya lalace." Shiru Sady baby ta yi tana rage gudun motar tana rage gudun motar bayan sun bar layin. Kiran waya ne ya shigo wayar Sidra, ta ɗaga tana cewa. "Hellow Khadijah ya aka yi ne?" "Kina ina ne?" "Ya kike tambaya ta kamar ba ki san komai ba, amma ai na fada ma ki komai kasancewar ki ƙawata." "Sidra abun da kike ƙoƙarin aikatawa kuskure ne, za ki wulaƙanta iyayenki ne, bayan kin san sun tara jama'a ana shagalin biki yau za'a ɗaura auren ki a ce kin gudu ya kike so su yi da jama'ar da suka tara? Sannan ga shi Fahad ɗin da iyayesa su ma sun tara na su jama'ar sai su ji labarin matar da Ɗan su zai aura ta gudu zai ji shi Fahad ɗin." "Ke ba gudawa fa zan yi ba, da zaran na samu abinda na je nema zan dawo ne sai a sake saka ma na ranar ɗaurin auren zuwa gaba, don na san Fahad na masifar so na dole ya jira sai na dawo, iyayena kuma za su hakura ne kawai ba yadda za su yi da ni bayan na dawo, kin ga idan na ba su haƙuri ai za su karbe ni ko da sun yi fushi kuwa. kuma ba wani daɗewa zan yi ba me yiwuwa nan da watanni uku na dawo." Tana fadar haka ta katse wayar tare da kashe wayar gabɗaya. "Khadijah ƙawata ce tun da na fada ma ta plan ɗina ta saka ni gaba wai kar na aikata." "Da ma me zai kai ki faɗa wa wata idan b ke ba." Daga nan ba wanda ya sake magana a cikinsu. _Nadra_ Tana idar da karatun Alqur'ani ta yi knocking ƙofar toilet ta tabbatar ba kowa kafin ta tura ƙofar. Ganin ba Sidra ya sa ta dauka ko ta fita zuwa wajen su Umma ne, don haka ta fita zuwa falon mutanen ɗazu ne a ciki, tana sanye har lokacin da hijabi ta nufi part ɗakin Umma. Da sallama a bakinta ta tarar da Umma tare da ƙanwar Abba wacce suke kira da Goggo Laraba da suka kwana ɗakin Umma." Ta durƙusa ta gaishe su cikin girmamawa, suka amsa ma ta cike da kulawa. Gwaggo Laraba ta ce. "Ina Amaryar take ne ko tana can tare da ƙawayenta?" "Ai ƙawayenta tun jiya ta Kore su wai ta sallame su ba ta son kowa ta kwana a gidan." Da mamaki Umma ke kallon Nadra, Gwaggo Laraba ta ce. "Sidra ba ta da mutunci wallahi." "Kira ma ni ita." Cewar Umma tana budar drawar da take zuba magungunanta a ciki. "To Umma bari na je na duba duk da ba ta cikin ɗakin." Tana fita ta nufi part ɗin Abba ta gaishe she shi shi da wani wan Umma suna zaune . Gaishe su ta yi cikin girmamawa sannan ta fita ta koma ɗakinsu. Ta nemi Sidra ba ta ciki. Don haka sai ta yi tunanin bari ta zagaya duka gidan ko tana wanni wajen a cikin gidan. Umma kuwa ta buɗe drawar da take saka magungunanta a ciki dan ta ɗauko man maganinta na sha'awa a ƙafa. Sai ta ga wata farar takarda, tana fitowa ta warware ta fara karantawa kamar haka. *Assalamu alaikum* *Iyayena ku gafarce ni zan yi wata tafiya domin cikar burina. Na san za ku shiga tashin hankali a yayin da kuka ga wannan wannan ya wasiƙar ta wa. Ku ba wa Fahad da iyayensa haƙiri na san yana so na zai jira har lokacin da na dawo mu yi aure.* _Sidra Abdallah Maitama_ Wani jiri ne ya ɗebi Umma ta yi luu za ta faɗi, cikin zafin nama Gwaggo Laraba ta tare ta tare da zaunar da ita bakin gadon. Takardar Gwaggo Laraba ta ɗauka tana karantawa. "Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un." Shine kalmar da Gwaggo Laraba take furtawa. Kafin ta ɗauki wayarta ta kira lambar wayar Yayanta wato Mahaifin Sidra. Bugu ɗaya ya ɗaga, ta sanar da shi ya zo ɗakin Umma yanzu. Sannan ta fita zuwa ɗakin da Mahaifiyarsu ta sauka, ta tarar da ita ita kaɗai, don ba wanda ya je wajenta saboda masifarta. Ita ma Gwaggo Laraba ba ta sanar da ita abun da ya faru ba, ta dai ce ta zo ana neman ta a ɗakin Umma. Carko-carko suka yi a ɗakin Umma, Daga Abba har mahaifiyar su da suke kira Ammi da Gwaggo Laraba. Umma na kuka kamar ranta zai fita yayin da kowa ya kasa magana. Abba ransa ya kai matukar tashi, idanunsa sun yi jajir, Ammi sai alawadai da Sidra take yi yayin da Gwaggo Laraba ta kasa magana. Nadra ce ta shigo da sallama, ganin mahaifinsu kwance tana hawaye ya saka ta ruga gabanta ta rike hannunta tana hawaye ta ce. "Umma me ya same ki ?" Ta ji tambayar tana hawaye. Ganin haka ya saka Gwaggo Laraba janyo Nadra tana cewa. "Ba abinda ya same ta tana kukan rabuwa da Sidra ce, kin san daga Anjima za'a ɗaura aurenta shi ke nan fa ta zama yar wani Family." Haka kawai Nadra ta ji ba ta gamsu ba tana son yin magana ta ki Umma na cewa. "Kada ki damu Nadra kewa ne kawai da zan yi na Yayarki." Ya karasa maganar tana murmushin karfin hali. "Umma na duba ko ina ban ga Sidra ba." "Eh ta tafi wajen gyaran jiki ne Anjima za ta dawo. Ta shi ki tafi." Haka kawai jikinta ya yi sanyi ta tashi ta tafi . Cikin damuwa Ammi ta ce. "Amma yarinyar nan ta gama tozarta mu, sai da ta bari mun tara jama'a gida ya cika da mutane sannan za ta ma na haka? Ga wasu mutane suna kan hanyar zuwa daga wasu garuruwa na nesa don halartar wannan ɗaurin auren ne za ta kunyata mu." Sai da ta goge hawaye kafin ta ce. "Abdullahi ka kira wadanda ke hanyar zuwa garin nan wajen daurin aure ka dakatar da su su juya su koma ba zancen auren kuma. Wadanda ke nan garin na dan dole su zo don Allah kaɗai ya san yawan su idan sun zo a basu hakuri su koma. Suma dangin angon a kira a ba su haƙuri su sallami baƙin da suka gayyata na nesa su koma garinsu na kusa kada su zo, wallahi Sidra ta gama kunyata mu ta tozarta mu." "Ba za'a kira kowa ba ba wanda za mu dakatar daga zuwa kowa ya zo, kanta ta yi wa ba mu ba, wallahi ba ta isa ta tozarta mu ba. " Da mamakin kowa ke kallonsa kafin ya ce. "Za'a daura auren yau sai dai ba da Sidra ba tun da ta gudu, za'a ɗaura auren da ƙanwarta Nadra." Da mamaki Gwaggo Laraba ke kallonsa kafin ta ce. "Kar ka aikata abun da zai zo ya saka mu yi nadama, ka san irin soyayya da shaƙuwar da Fahad ya yi da Sidra, suna masifar son juna, ba wanda ya haɗa su sune suka ga juna suka hada kansu suke soyayya. Shin idan aka yi haka kana ganin Fahad zai yarda ya karbi ƙanwar Sidra a matsayin matarsa, ita ma Nadra za ta yarda ta zauna da saurayin Yayanta a matsayin mijin aurenta? Kuma shi Fahad irin mazan nan ne ƴan boko ma su son rayuwar wayewa, Shi ya sa ya nemi Sidra don ita ma haka rayuwarta take ba, amma ita Nadra da take da kunya da ustazanci ba ta damu da rayuwa ba shin ta ya ya zaman su zai yi daidaita tun da ra'ayinsu ba ɗaya ba?" *To masoyana ga ni ɗauke da sabon labari, tafiya ne tsakanin duhu da haske, wata kila ya zo daidai da ra'ayinku🥰 watakila kuma akasin haka😒 Ni dai fatana a duk lokacin da kuka ci karo da abinda bai ma ku ba a cikin labrina to ku kasance ma su fahimtata da kuma yi ma ni uzuri. A cikin wannan labarin za mu fuskanci rayuwar waɗan nan jaruman guda biyar* Khalifa (makaho) Ma'eesha Ibrahim Khalil Fahad Umar Majidaɗi Sidra Abdullahi Maitama Nadra Abdullahi Maitama *Waɗan da suke da labari mabanbanta, ku dai ku kasance da ni a cikin wanan labarin don ganin wani dararasi ya zo da shi.* *Maman Ihsan ce*✍️ Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣2️⃣ "Kar ka aikata wani abin da zai zo ya saka mu yi nadama, ka san irin soyayya da shaƙuwar da Fahad ya yi da Sidra, suna masifar son juna, ba wanda ya haɗa su sune suka haɗa kansu suke soyayya. Shin idan aka haka kana ganin Fahad zai zai yarda ya karɓi kanwar Sidra a matsayin matarsa, ita ma Nadra za ta yarda ta zauna da saurayin Yar ta a matsayin mijin aurenta? Kuma shi Fahad ɗin irin mazan nan ne ƴan boko ma su son rayuwar wayewa, shi ya sa ya nemi Sidra don ita ma haka rayuwarta take . Amma ita Nadra da take da kunya da ustazanci ba ta damu da rayuwa ba shin ta ya ya zaman su zai daidaita tun da ra'ayinsu ba ɗaya ba?" "Ka da ki damu Laraba in sha Allah babu nadamar da zai biyo baya in dai Nadra ya aura. Ni na haife su na san halin kowacce a cikinsu, sai ya fi jin daɗin zama da Nadra akan Sidra. Domin ita ce nake da yaƙinin zai iya sarrafa ta ta sarrafu ma sa yadda yake so, kuma ita ce zai iya daka ma ta tsawa ta saurare shi saɓanin Sidra. Da a ce tun farko Nadra ya gani yake kuma ta gudu, to ba zan taɓa cewa zan musanya ma sa ita da Sidra ba, don kada ya yi kuka da ni daga baya, amma Alhamdulillah tun da har Sidra ce ta gudu zan musanya ma sa madadinta da Nadra na tabbatar wata rana sai ya yi alfahari da wannan madadin, domin kuwa Nadra mace ɗaya ce har da ƙari." Shiru dakin ya ɗauka ba wanda ya sake yin wata magana, domin kuwa sun san cewa Nadra ba ta da matsala. "To yanzu ya kamata ka sanar da Fahad ɗin idan ya amince da Nadra." Cewar Ammi tana kallonsa. Wayarsa ya lalubo a cikin aljihun rigarsa yana dannawa lambar Fahad kira. _Fahad_ Kwance yake a gadonsa ya lulluɓe da bargo yana barci. Wayarsa dake saman side ta fara ruri. Cikin barci ya ji kiran wayar, a tunaninsa Sidra ce, don da ita ya kwanta a ransa, bai same ta a waya ba. Kuma ya san ita ba ma'abiciyar kashe waya ba ne, kuma kullun asuba yakan kira wayarta ko ya turaa ta saƙon barka da safiya. Amma yau sai ya kira switch off. A hankali ya bude idanunsa yana tashi zaune ya miƙa hannunsa ya ɗauki wayar. Ganin sunan Mahaifin Sidra ne sai da gabansa ya faɗi. Ya ɗauki wayar tana gab da tsinkewa. "Assalamu alaikum." Daga cikin wayar ya ji muryar Abba ya ce. "Wa'alaika salam Fahad?" "Na'am Abba." "Idan ba damuwa ina son ganinka yanzu a gidana." "To Abba." Ya amsa sannan Abba ya kashe kiran wayar. Bargon da ya lulluɓe ya yaye ya sauko daga kan gadon. Farin wando ne Three-quarter ya sanya, babu riga a jikinsa ga wani zanen Tattoo a ƙirjinsa zuwa hannunsa. Bathroom ya faɗa don yin wanka. Tsawon mintuna talatin ya ɗauka yana wanka kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani ƙarami yana goge dogon gashinsa. Jikinsa sai kamshin shower gel da turaren wanka yake yi. Tsadadden man shafawarsa ya shafa a jikisa, sannan ya fesa body spray. Closet ɗin sa ya shiga ya cikin tsadadden ɗanyar shaddar sky blue, sannan ya fesa turarensa mai suna Creed Aventus turare mai ƙarfi da jan hankali. Sannan ya ɗauki agogonsa Rolex date just ya ɗaura a tsitsiyar hannunsa. Ya duba bangaren takalmominsa ya ɗauki takalminsa Jimmy choo ya saka a ƙafarsa tsakanin nevy blue don haka ya saka hularsa nevy blue. Ya fito ina da ya dauki wayoyinsa tare da key ɗin motarsa ya fara takunsa cikin izza wanda kallo ɗaya za ka yi ma sa ka san yana kan cin ganiyar samartakansa, kyau da cikar haibarsa suka sake bayyana. Ƙamshin turarensa ya tabbatar wa da jama'ar dake falon yana gab da saukowa. Idanu suka zuba wa upstairs ɗin yayin idanunsu ya sauka akansa. A ƙalla mutanen da suke falon za su kai su goma kuma duk baƙi ne da suka zo bikin. Gaishe su ya yi suka amsa suna ma sa ƴar tsokanar da ake yi wa ango. Bai saurare su ba ya nuf part ɗin Mama. A falo ya same ta ita da ƙanwarta ya gaishe su. "Ina za ka je na gan ka da makullin motar ko breakfast ba ka yi ba." "Ina sauri zan je na dawo kafin abokaina su iso don suna hanya." "Ina za ka je ne wai?" Cewar Aunty Nana ƙanwar mahaifiyarsa. "Gidan surukaina ne suke nema na." "Okay a dawo lafiya." Daga nan ya fice, zuwa part ɗin Baba. Shi ma ya gaishe shi sannan ya sanar da shi fitar da zai yi. Ta ƙofar falon Baba ya fita ba tare da ya koma main falon ba. Wajen motar da zai fita da ita ya nufa, ya shiga motarsa ƙirar Mercedes Benz G63 AMG ya yi ma ta key, kafin ya horn har maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fice da motarsa. Wanda kallo ɗaya za ka yi wa motar ka san cewa an narka dukiya wajen siyen motar. Kai tsaye ya dauki hanyar da za ta sada shi da unguwar su Sidra. _Maeesha_ Tafiya kawai take yi tana hawaye hannunta rike da akwatina biyu, yayin da Makaho ke jan babbar akwatin da ɗaya hannunsa. Ɗayan hannu kuma yana rike da sandarsa yana dogarawa. Bin bayansa kawai take yi ba tare da ta san in da za su tafi ba. Tsawon lokaci suka ɗauka suna tafiya, kasancewar ba ta saba yin tafiyar kafa ba ga kaya duk ta bi ta gaji. Don haka ta tsaya ba tare da ta yi magana ba, shi ma sai ya tsaya kamar ya san ta tsaya. Sai dai bai yi magana ba ya yi shiru. Ganin ba ta da niyyar cigaba da tafiya ya saka ya ce. "Ki yi hakuri mu tafi akwai sauran tafiya a gaban mu ga magrib ta kusa." "Ba zan iya sake wani tafiya ba na gaji." Kafin ya yi magana ta hangi mai keke nape ya fito layinsu tsaida shi ta yi ya tsaya a gabanta . "Hajiya ina zuwa." Kallon Makaho ta yi tare da cewa. "Ka zo ka faɗa ma sa sunan unguwar." Ya karasa yana lalube da sanda ya faɗa wa mai napep ɗin . Mai nape ya saka akwatunan a baya ya ajiye daya a gefe, sannan ya ce su shiga . Sai da ta shiga sannan ta ce wa makaho. "Mallama ka shigo." Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya shiga baya bayan ya laluba ya zauna. Shi ya sanar wa mai napep ɗin unguwar da zai kai su tare da ma sa kwatance. Tun da suka shiga layin jikin Ma'eesha ya yi sanyi . Don kallo ɗaya za ka yi wa yankin ka san cewa unguwa ce ta talakawa. Don ba gini mai kyau a layin da zai tabbatar ma ka da akwai masu rufin asiri a layin. Kamar yadda ya yi ma sa kwatance da masallacin kuwa haka aka yi, sai da ya kawo daidai masallacin da ya sanar da shi ya tsaya ya ce. "Mun iso wajen." "Mallam don Allah ka taya mu sauke kayan kasa." "To Hajiya." Ya fada yana saukowa bayan ya kashe keke nape ɗin nasa. Sai dai ya sauke ma su kayan sannan ta tambaye shi kudinsa. "Nawa ne mallam." "Ki bada yadda kuke zuwa ." "Mallam ka yi magana ban san ya ake biya ba, don ban taɓa hawa keke nape ba sai yau." Wani kallo ya ma ta har zai yi wata magana sai ya lura da haƙorin Gold ɗin dake bakinta, hakan ya tabbatar ma sa da cewa Hajiya ce ita, kuma yanayin ta ma ya nuna ƴar hutu ce. "Ki bayar da dubu ɗaya." Ya fada yana shiga cikin napep ɗin nasa. Handbag ɗin ta ta zuge ta ciro 1k ta bashi. Bayan ta sallame shi ne Makaho ya ja akwatin kayanta babba ya yi gaba, ita dai bisa ta yi a baya har suka ƙarasa ƙofar wani gida. Gidan ƙofarsa ta ɓalle tun daga waje ma ana hangen wa su matan dake tsakar gidan. 'Na shiga uku ni Ma'eesha wane irin gida ne nan na faɗo.' Sallama Makaho ya fara yi sai da aka ba shi izinin shiga sannan ya shiga tana bin sa a baya. Ɗakunan gidan za su kai Ashirin. Don tsakar gidan ma cike yake da mata ga yara barkatai ta ko ina. A tsakar gidan. Wasu yaran suna wasa, yayin da wasu na faɗa sai wasu yaran zaune sun jeru suna kashi a ta ko ina suke zaune ba tsari . Wata dattijuwa ta kalli Makaho ta ce. "Mallam Khalifa ka dawo ?" "Eh Baba na dawo." "To ma sha Allah, wannan ita ce Amaryar taka?" "Eh ita ce." Wata uwar ashar suka ji an danna, wanda ya saka hatta Makaho da Ma'eesha sai da suka tsaya cak daga tafiyar da suke yi. Larai Dillaliya ce ta yi zargin tana kallon takalmar dake ƙafar Ma'eesha wanda a ƙalla kuɗinsa za su kai dubu ɗari 100k haka handbag ɗinda ke hannunta ma zai kai dubu ɗari. Kafin a gama mamakin ashariyar da ta ɗura aka ci muryar Larai ta sake cewa. "Wannan ita ce matar Khalifa makaho kenan?" "Makaho ya cigaba da tafiya Ma'eesha kamar za ta faɗi sakamakon idanun da ta ji suna yawo a jikinta, sai dai kanta a ƙasa ba ta ba da damar ganin fuskarta sakamakon mayafin abyarta da ta rufe rabin fuskarta da shi hawaye ne kawai ke bin fuskarsta ba tare da kowa ya sani ba. Hakan ya saka kanta a sunkuye tana kallon ƙasa yake tafiya ba ta yarda ta gaishe da mutanen gidan ba saboda kuka zai iya ƙwace ma ta matukar ta ce za ta buɗe baki ta yi magana. Ɗakin karshen gidan wanda ke da ƙofar langa-langa ya tura ya shiga da sallama. Ita ma shiga ta yi idanunsa na sauka kan buhun siminti da aka shimfiɗa a ɗakin Ƙafarta ya harɗe cikin buhun da ake shimfiɗa madadin carpet. Nan ta lura ashe ɗakin ko flour babu, ba'ayi simintin ƙasar ɗakin ba ƙasa ne kawai sai aka shimfiɗa buhu a ƙasan ɗakin wanda ya rufe ƙasar ɗake ƙasan ɗakin. Hatta bangon ɗakin ana iya ƙirga bulo ɗin don shi na bangon ba'a shafa ma sa siminti ba. Ga bangon duk ya yi gantsa kuka alamar ya sha ruwa kafin aka yi rufin ɗakin. Kanta ta ɗaga sama tana kallon rufin ɗakin, nan take hangen haske daga sama, wato zink ɗin ɗakin ya hude a wasu wuraren aka hangen hasken waje, langa-langa ba sabo ba ne aka saka. Kuma idan ana ruwan sama da alama ba ƙaranin yoyon ruwa zai yi ba, don ba makawa dai ruwa ya cika ɗakin idan har mai ƙarfi ne. Toshe bakinta ta yi tana kuka don kada sautin kukan ya fita, kafin ta ji tsayuwar ya gagare ta ta zube akan ƙafarta tana kuka mai tsuma zuciya. Kamar ya san kuka take yi sai ta ji ya kira sunanta cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da nutsuwa. "Ma'eesha." Ba ta amsa masa ba sai hawaye dake bin fuskarta. "Ki yi haƙuri na san wannan gidan bai dace da macen da ta taso cikin gata da hutu ba, kin taso cikin farin ciki na sani kina kwana a cikin A.c da katifa mai laushi ba'a dauke wuta ko an dauke ba iya sani saboda na'ura za ta fara aiki ki nan kuma ko fanka babu ballantana A.C ba na da halin da zan iya ciyar dake irin abincin da kike ci da ruwan da kike sha..." Shiru ya yi sakamakon jin fitar ta daga ɗakin, tana fita ta yi tozali da fo da yarinya ta yi kashi ta tashi ba tare da an yi ma ya tsarki ba tana wasar ta. Wani na zaune kusa da fo ɗin yarinyar shi ma yana Kashin, Ma'eesha ta yamutse fuska, ta ji wata mata na cewa. "Amarya hakuri za ki yi ɗakinki shi ne kuka da banɗaki dole ki dinga ganin haka. "Ina ne banɗaki." Ta tambaya tana kallon matar da idanunta da suka kumbura. "Ga banɗaki nan jikin ɗakinki. Bari a kawo ma ki buta." Kafin matar ta yi magana sai wata budurwa ta kawo wa Ma'eesha buta da ruwa a ciki. Karɓa ta yi tana shiga ban dakin ta toshe hanci tare da fitowa a guje ta duƙa ƙofar ɗakinta tana kakarin amai, sakamakon wari da zaurin fitsari dake tashi a toilet ɗin. Da kallo suka bi ta wasu na yi ma ta sannu. Bayan ta gama ne ta ga wannan buduwar da ta ba ta buta tana cewa . "Tashi bari na gyara wajen." Tana magana tana mika ma ta kasar pure water na ruwa, karba ta yi ta wanke baki sannan cikin kasalliyar murya ta ce. "Thank you." Cikin ɗakin ta koma ta ga makaho tsaye kamar yadda ta bar shi. "Wallahi ba zan iya rayuwa a cikin wannan gidan ba." Tana fadar haka ta janyo akwatin kayanta ta fito, shi ma ya janyo babban ya biyo ta suka fito suna tafiya." Baba ta lalle su ta ce. "Lafiya kuwa Khalifa?" "Baba ina zuwa " Abun da ya iya fada kenan saura. Matan kowa sai bin su yake da kallo. Suka ji muryar Larai Dillaliya tana cewa. "Ni Ko da na kalli yarinyar nan na san ba kamar unguwar nan ba ne ballantana gidan nan, ko dai asiri Khalifa ya yi wa iyayen yarinyar nan ne da suka ɗauki ƴa suka ba shi aure?" Ita dai Ma'eesaha ko kallo ba ta yi ma ta ba ballantana ta gane wa ke magana . Tana zuwa ƙofar gidan ta ajiye akwatin hannunta, shi ma ya tsaya in da ya ji ta tsaya, ya ajiye akwatin amma sandarsa ta Manafi na hannunsa. Handbag ɗin ta ta buɗe ta duba daga wayoyinta sai kuɗi 9k dama dubi goma ne ta ba mai napep dubu ɗaya ya rage dubu tara. Ga shi matar Babanta ta amshe ATM card ɗin ta wanda a ƙalla tana da Naira sama da miliyan biyar a ciki. Pink lips din ta ta cije tana goge hawaye. Kafin ta ce. "Ina zan samu gidan haya kamar na zaman mutum ɗaya?" "Gaskiya ban sani ba, amma dai idan aka tambaye Iro mijin Larai Dillaliya zai samo ma na, saboda dillancin gidajen haya yake yi a unguwar nan." "Ina za'a same shi yanzu ?" Kafin ya yi magana ne suka ji muryar wani mutum dake ƙoƙarin shiga cikin gidan yana cewa. "Mallam Khalifa Amaryar ce nan?" Yana tambayar amma idanunsa akan Ma'eesha wacce ta tsuke fuska, sakamakon kallon ƙurillar da yake yi ma ta. "Yauwa Mallam Iro ka dawo?" "Eh Allah ya yi." "Dama yanzu muke maganar ka dai ga shi ka zo." "Ikon Allah, ka san an ce ɗan halal ya ƙi ambato." Kallon Ma'eesha ya yi yana cewa. "Amarya ya garin ." Ba ta amsa ma sa ba ta ce. "Gidan haya za ka nema ma ni a yanzu nake buƙata iya na zaman mutum ɗaya." Shiru ya yi yana tunani kafin ya ce. "Eh akwai guda ɗaya a unguwar nan, shi kadai ne iya na zaman mutum ɗaya, sauran dole sai kin samu makota." "Ina so sannan ina son ya kasance gidan mai tsafta ne." "Ba matsala in dai tsafta ce, sai dai ƙarami ne sosai gidan. In taƙaice ma ki iya ɗaki ɗaya ne tal a ciki wato single room ne, ba falo ɗaki ɗayan nan ne sai banɗaki da kitchen madaidaita." Ba haka ta so ba ta so ko da mai falo ɗaya da ɗakin barci a samu, amma tun da ya ce wannan kadai ne za ta amshe shi, ya fi ma ta wanann gidan da ta fito yanzu na ƙazamai." "Ina ne gidan?" "Farkon layin nan ne?" "Okay nawa ne kuɗin?" "Ba tsada dubu hamsin ne a shekara ɗaya." Tunanin ta ina za ta samu dubu hamsin ne, ga shi dama ba ta iya yin transfer money from account ɗin ta har tana tunanin zuwa bank sa saboda matsalar ga shi dubu tara take da shi yanzu haka, ga shi ana maganar gidan dubu hamsin. *KADUNA* _Fahad_ A ƙofar gate ɗin gidan su Sidra ya yi horn. Maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga da motarsa ciki . Bayan ya yi parking bai fito daga cikin motar ba ya ɗauki wayarsa ya kira Abba. Ya sanar da shi ya iso, nan Abba ya ce ya shigo yana part ɗin sa. Da sallama ya shiga ƙofar part ɗin Abba. Suka amsa ma sa gabaɗaya suna zaune a falon. Abba, Umma, sai mahaifiyar Abba wato Ammi, da ƙanwar Abba Gwaggo Laraba sai Aminin Abba Alhaji Abubakar Kallo ɗaya Gwaggon Laraba ta yi wa Fahad a zuciyarta ta ce. "Sidra kin yi wa kanki, domin wannan yaron miji ne na kece raini ne da da gudun wuce sa'a. Allah ya sa ya amince da zaɓin Nadra kada ya ki amince." Ƙamshinsa ya cika falon ya karasa ya durƙusa ya gaishe su. Suka amsa ma sa gabaɗaya. Shiru ne ya biyo baya, kafin Abba ya ce. "Fahad." "Na'am Abba." "Ka yi waya da Sidra ce?" "A'a Abba ba mu yi waya da ita ba." "Tun yaushe kenan kuma wani magana kuka yi?" "Wannan karon sai da gabansa ya faɗi sakamakon tambayar da aka yi ma sa." "Lokacin ta ce mani za'ayi ma ta zanen lalle zuwa dare za mu yi waya, to a daren na yi ta kira ba ta ɗauka ba har yau na ji wayar a kashe ." Cikin fargaba ya ce. "Ina fatan dai tana lafiya ba wani abun ne ya same ta ba ko?" "Tana lafiya." Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana jiran dalilin kiransa. Abba ya mika ma sa wasikar da ta bari ya karba ya fara karantawa. Sai da ya mike tsaye tsabar dirgici da tashin hankali. Kafin ya kalli gabɗaya jama'ar dake falon ɗaya bayan daya, sai a lokacin ya lura da dukkansu a kwai rashin hankali a tattare da su. "Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un." Kalmar da ya furta kenan idanunsa sun rikiɗe zuwa ja. Cikin sanyin jiki ya zauna yana cewa . "Sidra why why do this to me me ya sa kika amince tun farko? Ina kika je kika bar ahalinki cikin tashin hankali ba tare da yin tunanin halin da za su shiga ba." Tashi ya yi yana kallon su idanunsa sun yi ja hatta farar fuskarsa sai da ta ji ja. "Ku sanar da mutane kawai an fasa daurin auren , zan je ni ma na sanar da nawa dangin da abokan. Da ma su niyyar zuwa su dakata, ni ma zan dakatar da ma su niyyar zuwa. Duk da dai dama akwai wadan da za su zo daga ƙasar waje or ready suna hanya ba zancen juyawa tun da fly ne ba mota ba." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Abba ya sauke kafin ya ce. "Ka bar su kawai su zo kar ka dakatar da kowa." Da mamaki Fahad ke kallon Abba kafin ya yi magana Abba ya ce. "Sidra ta gudu a ranar aurenka da ita, don haka zan maye ma ka gurbin ta da ƙanwarta Nadra idan har ka amince " A matuƙar ruɗe Fahad ya kalli Abba ya na girgiza kai alamar a'a. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣3️⃣ "Sidra ta gudu a ranar aurenka da ita, don haka zan maye ma ka gurbin ta da ƙanwarta Nadra idan ka amince." A matuƙar ruɗe Fahad ya kalli Abba ya na girgiza kai alamar a'a . Sai a lokacin Ammi ta yi magana ta ce. "Kai yaro Fahad kake ko, to bari na faɗa ma ka gaskiya auren Nadra da za mu aura ma ka gata muka yi ma ka, ka rubuta ka ajiye wata rana sai ka zo ka durƙusa kana yi ma na godiya, sannan za ka ce gara ma da waccen fitananniyar ta gudu ta bar ka ta gudu. Ka ga waccan da ta gudu masifar, girman kai, isa da gadara, sannan ga shegen taurin kai, ko ka aure ta da ƙyar za ta yi ma ka biyayya saboda ko anan gidan ba ta ganin kowa da gashi sam ba ta san darajar mutane ba. Amma yanzu Allah ya raba ka da ita za ka auri mai hakuri juriya da hangen nesa, uwa uba ilimin addini da tarbiyya." Shi kam gabaɗaya Fahad ba ya ma gane me suke faɗa, don hankalinsa da tunaninsa na can wata duniyar ne daban. Ya kasa gane dalilin da zai saka Sidra ta aikata haka. Muryar Abba ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula. "Fahad ban yi ma ka tayin auren Nadra ba sai da na tabbatar da cewa na ma ka sakayya ne akan abin da Sidra ta yi ma ka, in dai har za ka iya zama da Sidra zaman aure to ina mai tabbatar ma ka sai ka fi jin daɗin zama da Nadra akan Sidra. Amma ba zan takura ma ka ba idan har ba ka son ka aure ta shi kenan mu bar maganar kawai Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi." Shiru ya yi yana nazari shi dai gaskiya ba ya jin son Nadra a Zuciyarsa. Kuma rayuwarta da ra'ayinsa ya sha banban da nata, shi ya fi son wayayyun mata masu aji kamar Sidra, ita kuma Nadra ga ta nan kamar wacce ba ta waye ba, shi tun da yake ma bai taba ganinta babu hijabi ba. Kullum cikin hijabi ko a cikin gida ma saka hijabi take yi kamar wata mai takaba, wani namiji ma zai ga surar jikinta har ta ja hankalinsa ya ce yana son ta, sannan ita baƙa ce shi kuma baƙar mace ba ta burge shi. "Ba ka ce komai ba." Sai a lokacin ya daga ya kalli Abba da Umma wacew ta kasa cewa komai, don tun da ya shigo bai ji muryar ta ba, ya san tashin hankali ya yi ma ta yawa. Sannan suna da karamci da mutunci, yanzu indai bai amince ba kamar ya kunyata su ne , domin tabbas da kunya sun tara jama'a a ce an watse ƴar su ta gudu ranar aurenta. Wanann ciwon zai dade bai bar zuciyarsu ba domin sun kunyata a idanun mutane, shi bai damu da kansa ba don an fasa aurensa iyayen ta ne abin dubawa . Cikin sanyin murya ya ce. "Na amince." Gabɗaya suka saki ajiyar zuciya tare da saka ma sa albarka. Tashi ya yi ya ma su sallama ya yi ficewarsa. Abba ya kalli Ƙanwarsa ya ce. "Kada a sanar da Nadra wannan zancen sai bayan ɗaura aure." "Me ya saka haka to Yaya, tun da an ji ra'ayinta shi ma ya kamata a ki nata ra'ayin." "Ba sai an ji ba, domin na san yarinya ce ita mai biyayya, ba ta taɓa tsallake magana ta ba, idan na ajiye kara na ce kada ta tsallaka ba za ta tsallaka shi ba. Ba ta da ra'ayi in da iyayenta muna so, don haka na hana a fada ma ta ne saboda tana da raunin zuciya, za ta shiga tashin hankali da damuwa wanda zai tona asirin abun da muka binne. A bar zancen akan cewa dama Nadra ce Amaryar ba Sidra ba, an yi mistake wajen saka sunan ne. Ko ita Nadra kada ta san cewa ba Sidra ta gudu ballantana hakan ya shafi walwalarta." Jinjina kai Goggo Laraba ta yi ta fice daga part ɗin. Kai tsaye ɗakin su Sidra da Nadra ta nufa, bakinta ɗauke da sallama. Nadra tana waya da Ya Sayyadin ta, wato Mallamin su na islamiyya ke son ta suna son juna duk da cewar shi talaka ne, amma hakan bai dame ta ba. Ganin Goggo Laraba ta ta ce. "Zan kira ka Ya Sayyadi." Daga haka ta katse kiran wayar tana kallon Goggon tasu. _Ma'eesha_ Kallon Mallam Iro mijin Larai Dillaliya ta yi tana cewa. "Mallam ina bukatar gidan hayan nan a yanzu ba sai Anjima ba. Amma gaskiya ina son na zaman mutum ɗaya ne kuma ya kasance akwai toilet da kitchen a ciki ." "Hajiya idan na fahimce ki ginin zamani kike so ko? To gaskiya babu a unguwar nan. Gidan haya mai zaman mutum ɗaya da na sani akwai a ƙasa yaba can farkon layin kamar yadda na fada ma ki, sai dai ƙarami ne gidan, kuma ɗaki ɗaya ne tal ba barci bai da falo, sai kitchen a tsakar gida, toilet ma a tsakar gidan ba cikin ɗaki yake ba, kuma tsohon gida ne ba na zamani yadda kike so ba, idan dole sai ba zamani sai dai ki je ki nemi manyan dillalan gidan haya." Cikin gajiya ta ce. "Yanzu shi wanann da kake magana akwai a ƙasa nake so yanzu nan, amma ba na da kudin yanzu a ƙasa." Kallon ta ya yi ya tabbata ba ta yi kama da wacce za'a ce miliyan ma ya fi karfin ta ba ballantana dubu hamsin. "Hajiya ai wanan ba matsala ba ne za ki iya transfer." "Account ɗina ya samu matsala sai dai na cire kuɗi da ATM card amma ba na iya transfer, sai na je banki akan matsalar." "Yanzu yanzu ya kike so ayi dubu hamsin ne za ki iya zama ?" "Idan ba za ka damu ba, ina son ka ka bani gidan yanzu, in sha Allah zuwa gobe da rana ka zo ka karbi kuɗin hayar gidan. Don ba kuɗi ba kuɗi hannuna 4k ne kawai." "Ba damuwa mu je na kai ku gidan ga shi can farkon layin ba nisa gida uku ne ya shiga tsakanin da wanann gidan da aka ba makaho ɗaki kyauta kin ce ba kya iya zama." Yana gaba suna bin sa a baya har suka wuce gidan uku, a na huɗun ne ta ga ya tsaya a ƙofar wani karamin gida dake da kofar fale-fale. Sakata kawai ya cire ya tura kofar suna bin sa a baya . Ƙaranin gida ne sosai ba wani wadancan tsakar gida. Kuka tsakar gidan ma ƙasa ne ba'a shafa siminti ba, hatta ƙofar ɗakin ma na fale-fale ne sai karamin window shi na ƙofar fale-fale ne. Barandar ƙofar ɗakin dai siminti ne sai cikin ɗakin siminti ne sai dai an shafa siminti a bango. Daga tsakar gidan ga toilet nan karami shi ma siminti ne a ƙasa, sai kitchen wanda ba wai gina shi aka yi ba, fale-fale aka buga aka killace wurin ya zama kitchen, aka masa ƙofa. Godiya ta yi ma sa ya fice yana ma su sallama. Akwatunan kayanta ta kalla ta kalli ko ina na gidan, kasancewar lokacin sanyi muke ciki gidan duk ya yi ƙura. Ga shi ita ba wani aikin kirki yake yi ba a gidansu . Masu aiki ke gyara ma ta daki da gado su wanke ma ta toilet, ayi ma ta wanki da guga, girki kawai take yi shi ka Mahaifiyar ta ce ta ce sai ta koya, gidan mijinta wata rana za ta tafi ba kowane namiji ke cin abincin masu aiki ba. Ta ina za ta iya rayuwa ba wanda zai yi ma ta waɗan nan ayyukan? "Dole na je banki gobe na samu na yi transfer ɗin kuɗaɗen dake cikin account ɗin na, za su iya kai miliyan goma. Zan nemi gida kamar na miliyan uku na siya mai kyau da zan iya rayuwa a cikinsa. Sannan zan ja jari na fara sana'a ko da Naira miliyan biyar ne, saura miliyan biyu da zai rage ma sai na siya kayan daki da kayan kitchen da abinci ma su sauƙin kuɗi." Tana cikin wannan maganar ta ji karar shigowar sako a wayarta, sai da gabanta ya faɗi. Tana dubawa ta ga messages ne daga banki, jikinta na ruwa ta duba in da ta ga miliyan goma da ke account ɗin ta an kwashe su duka. Salati ta saka tare da sakin wayar ta faɗi ƙasa, dubawa ta yi akan guiwar ya tana riskar kuka. Tabbas ta san cewa mahaifinta kawai ya san Pin ɗin ta na cire kuɗi, kuma Mamy ce ta karbi ATM card ɗin lokacin da ta shigo ta ga tana tattara kaya. Kenan Mamy ta tambayi Mahaifinta Pin ɗin ya fada ma ta kenan, sun kwashe kudin don sun san za ta iya transfer suka riga ta. Cikin kuka ta ce . "Innalillahi wa 'inna ilahir raji'un, Allah humma ajirni fi musibati wa'a khalifni khalifan min ha." "Shi ke nan Mamy kin ruguza Mani rayuwa Allah ba zai bar ki ba. Allah ga ni gare ka ka da kai na dogara ya zuljalalu wal ikhram." Kuka take yi sosai ana kiran sallar magrib ta ga ya fita da sandarsa yana dogarawa ya fice daga gidan ba tare da ya ce ma ta koma ba. Ta dade tana kuka kafin ta mike tsaye tana goge hawayenta ta ce. "Daina kuka Ma'eesha ki daina ɓata hawayenki anan zaluncin da aka yi ma ki, ki rungume ƙaddarar da ta zo ma ki Allah yana tare da ke. Kuka ba bali ba ne ki shirya fuskantar sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki a ciki." Ita kadai take magana kamar wata zararriya. Fitilar wayarta ta kunna kasancewar akwai duhu kuma ba wutar nepa. Waige-waige take yi nan ta lura ashe akwai rijiya a gidan can karshen gidan Handbag ɗin ta ta duba ta ciro karamin bottle of water wanda ta shiga shagon saloon da shi ba ta sha ba. Alwala ta yi sannan ta duba cikin akwatin kayanta ta dauki Ɗankwali ta shimfida ta gabatar da sallar magrib. Tana cikin addu'a aka kira isha'i ta tashi ta gabatar. Tashi ta yi bayan ta yi addu'a ta nufi kofar fita gidan hannun ta rike da handbag. Wani shago dake kusa da gidan ta tambaye shi in da ake fitar da tsintsiya da faka ya ce wata bayarabiya ce kuma tun karfe shida take rufe shago ta wuce gidan. "Cikin damuwa ta ce . "Ba wani wajen kuma?" "Gaskiya sai dai ki bari da safe ." "Yanzu nake bukata wallahi." " Daren nan kuma?" Ya tambaya yana mamakin yadda ta dage. "Eh yau muka tare a wancan gidan, ya yi ƙura dole sai na share kafin mu kwana a ciki." "Allah Sarki, bari na ara Maki na shagona zuwa da safe sai ki dawo Mani da shi ko?" "To na gode." Ya mika ma ta tsitsiyar da faka ta amsa ta tafi. Har ta fara tafiya ta dawo ta fiye ruwar roba gida biyu ta wuce. Ko da ta koma ta samu makaho tsaye a tsakar gidan hannunsa rike da sandarsa. Ba ta kalli in da yake ba ta shiga cikin ɗakin. Yanar gizo-gizo ta fara cire wa a silin da bango, sai da ta kakkaɓe sannan ta share ɗakin ta kwashe dattin cikin faka tana kai wa waje can karshen bangon gidan. Sannan ta fito ta share simintin barandar ƙofar. Tsakar gidan ta fara share wa, sai dai kasancewar kasa ce ba siminti ba ƙura ya addababe ta ta fara atishawa da tari sakamakon kuran. Gefen mayafin abayar dake jikinta ta sa tana toshe hanci da daya hannun daya hannunta tana shafa har ta gama. Fita ta sake yi tana tari da atishawa ta koma wajen me shagon. Ganin akwai mutane ta tsaya gefe tana jiran a rage, bayan an rage ta samu ta karasa bakin kofar shagon. "Hajiya kin dawo?" "Eh dama ina son ne ka bar mun tsintsiyar nan da zuwa gobe sai na siya maka wata, saboda zan wanke toilet da shi ne kuma bai dace na dawo maka da ita ba bayan na wanke toilet." "Ba damuwa ki rike duka na bar ma ki." "To na gode sosai." "Ina son ka ba ni detergent da hypo ne." Daidai lokacin da wani mai siyar da robobi yake dawowa daga talla. "Dakata mallam." Sai ya tsaya ta karasa wajensa ta siya madaidaicin bokintin roba na 1k ta detergent da hypo dama ta siye ruwa Roba biyu ta kashe 1k ta zuba su a roba ta koma cikin gidan. Handbag ɗin ta ta duba tana tafiya ta ga 2k ya rage ma ta cikin 5k da ga bar gidan da shi Cire kayan ta yi daga cikin bokitin sannan sai ta karasa wajan rijiyar duk da ba ta da tabbacin cewa akwai guga. Ta haska torchlight na karamar wayarta ya ga an daure guga jikin karfe dake jikin murfin rijiyar. Abinda ba ta taɓa yi ba a rayuwar ta jan ruwa daga rijiya . Kamilalliyar muryarsa mai cike da kamala ta s ji ya ce. "Me kike ta yi a daren nan ne?" Kamar ba za ta amsa ma sa sai ta ce . "Ruwan zan ka a rijiya zan wanke ɗakin ne da kuma toilet, don ba zan iya amfani da su a haka ba." "Bari na taya ki jar ruwan, ki je dakin sai na kawo ma ka." Kallon mamaki ta masa ta ce. "Da wake idanun za ka gani ruwan kuka har ka kawo mani?" Ganin bai yanka ta ba kuma kamar ransa ya ɓaci ta wuce ta ba shi wuri." Laluben rijiyar ya yi har hannunsa ya sauka akan gugar ya janyo ta ya ji nauyi, don dama igiyar na ɗaure a jikin karfe guga na cikin ruwa . Sau uku ya janyo ya cika bokitin. Ya kai tana mamaki ya karba ta wanke dakin bayan ta zuba hypo da detergent. Sau biyar yana ciki bokitin yana kawo wa tana wanke wa tana sharo ruwan a waje, tana kashewada faka har ta gama ta wanke barandar. Daga nan kuma ta nufi toilet ɗin, nan ma siminti ne irin toilet na tsuguno na gargajiya. Sai dai ya kawo ma ta ruwa bokati uku ta ɗauraye toilet ɗin bayan ta wanke. Tana kallon ikon Allah makaho da ɗibar ruwa a rijiya, yana rike da bokitin a daya hannu yayin da daya hannun kuma yake dogara sandarsa ta makafi. *KADUNA* Bayan Nadra ta katse kiran wayar da take yi da Ya Sayyadinta. Cikin ƴar damuwa ta ce . "Goggo har yanzu ban san in da Aunty Sidra ta shiga ba, tun dazu nake zagaye gidan nan, ko dai ta fita ne?" "Eh kada ki damu ta je gyaran jiki ne kuma a'ba za ta dawo da wuri ba." "Allah ya dawo ma na da ita lafiya." "Amin ya Allah. Yauwa ki tashi yanzu nan direba zai kai mu wajen gyaran jiki da kitso." "Waye za'a yi wa?" "Da ni da ke." "Goggo ke ma kin san ba na son kitso, saboda gashin kaina yana da yawa sosai, tsayin kitson ma yana damuna." "Sai da an yi shi don haka ba baƙi mintuna Talatin ki yi breakfast ki fito." "Toh." Ta fada duk da ba ta son kitso sai dai ta dunƙule kanta kanta ta cusa cikin hula ko Ɗankwali. Amma kasancewar ta ba mai musu ko gardama ba ne ya saka ta tashi ta nufi bathroom don yin wanka. Bayan ta fito ne ta shafa man ta mai sanyin ƙamshi ta shafa, wanda yake karɓar baƙaar fatarta mai sheƙi. Ta shirya cikin kayan doguwar rigar material ta saka. Sannan ta sanya dogon Hijabinta ta dauki handbag da wayarta ta fice bayan ta saka flat shoe. Wayar Sidra take sake kira har lokacin switch off. Part ɗin mahaifiyar ta ta nufa saboda tana son sake duba jikinta. Sai dai an fada mata Umma na part ɗin Abba. Kamar sa ta bi ta can sai ta fasa Tana fitowa ta ga jama'a kowa na kallonta jama'ar dake falon dangin Abban ta ne. Wata ma daga cikin su ta ce. "Allah Sarki Nadra rabon dai ke za ki riga yar taki aure.?" "Ni kuma ?" Ta tambaya cikin mamaki. Matar za ta sake magana kenan sai Goggo Laraba ta dakatar da ita ta hanyar girgiza ma ta kai." Hakan ya saka matar ta fahimci Nadra ba ta san da ita za'ayi auren ba. Shagwaɓe fuska ta yi ta ce "Goggo lalle kawai nake so jiya fa na je saloon aka gyara mun kai na " Murmushi Gwaggo Halima ta yi ta ja hannun ta suka nufi ƙofar fita suka fice . Direba ne ya kai su har shagon da Gwaggo Laraba ta sanar da shi Bayan sun fita ya tsaya jiran su yayin da suka shiga. Nadra ta zauna yayin da Goggo Laraba ta yi wa mai saloon maganar uzuri suna sauri kuma amarya ce za su je reception ne, take ta kira ɗaya daga cikin yaran aiki ta ta karasa yi wa wata lalle, ita kuma ta fara tsantsara wa Nadra lafiyyarnb zanen lalle mai dauker hankali. *Maman Ihsan ce.*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣4️⃣ Nadra ta zauna yayin da Goggo Laraba ta yi wa mai saloon maganar uzuri suna sauri kuma amarya ce za su je reception ne. Take ta kira ɗaya daga cikin yaran aikinta ta karasa yi wa wata lalle, ita kuma ta fara yi wa Nadra lafiyyarn zanen lalle mai ɗaukar hankali. Kamar yadda ta nuna ba ta son kitson haka aka yi ba'ayi ma ta ba, sai sai gashin na ta ya sha gyara sai sheƙi da wani ni'imtacen ƙamshi take yi. Abun da ya sake ba ta mamaki bayan na gama ma ta sai ta ga Mama Laraba ta ce su je ta shiga ciki za'ayi ma ta gyaran jiki. "Mama wani gyaran jiki kamar wata Amarya?" "Ai ke ƙanwar Amarya ce ya kamata duk abin za'a yi ma ta a yi ma ki?" "Amma Mama ban taɓa jin in da aka yi haka ba." Ganin za ta ba ta ma su lokacin kuma tana son su koma gida akan lokaci ya sa ka ta ce. "Nadra ki shiga don Allah ana jiran mu." "To Goggo Dinner da za'a yi ai sai bayan an ɗaura aure ne, karfe biyar aka..." Ganin yadda Goggon nata ta tsuki fuska ya saka ta ja bakinta ta yi shiru, kasancewar tana da gudun ɓacin ran mutum. Shiga ciki ta yi aka ce ta cire kayan jikinta. Aka ba ta wasu ƙananun kaya ta saka aka shigar da ita wani ruwa mai kumafa da ƙamshi. Matar sai lallaɓa ta take yi tana cewa ban san har da gyaran jikin nan za'a yi ma ki ba da shi muka fara yi kafin muka yi lalle. Ita dai ba ta ce komai ba sai faɗuwar gaba da take tsintar kanta a ciki. _Makaho_ Sai da ya gama dibar ruwar yana daukar hannu daya da bokitin ruwa hannu daya da sandar dogarawa har ya gama. Don sai da Nasara ta wanke banɗakin nan tas da detergent da hypo. Duk da cewar ba tile ba ne a toilet ba ne siminti ne. Bayan ta gama ne ruwan karshe da ya kawo ta ajiye a banɗakin ta fito. Duk abinda take yi hawaye bai tsaya daga tsiyayar da take a idanunta ba. Kiran sallar isha'i ake yi don haka ya ce ma ta . "Zan je masallaci." Ba ta ce ma sa komai ba, shi ma bai jira cewar ta ba ya fice. Tsayawa ta yi tana kallon ɗakin da take haskawa da wayarta, tana tunanin dakin zai dauki lokaci kafin ya bushe. Kawatin kayanta ta buɗe ta ɗauki wani rigar sanyinta da yake da kauri ta san zai kashe ruwa, ta dauka ta dinga goge ɗakin har ya tsane ba ruwa a kasan simintin dakin. Ɗankwalinta ta shimfida sannan ta fita ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar isha'i. Bayan ta idar ta tsaya ta yi addu'o'i tana kai kukanta ga Allah ya ba ta karfin zuciyar cinye wannan jarabawar. Tana zaune ta ji ya yi sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam." Ya dinga lalube har ya ji ɗakin sannan ya shiga bayan ya cire takalminsa a waje. Shiru ne ya biyo baya har tsawon mintuna biyar ba wanda ya yi magana a cikinsu. Maganar zuci da take yi ya fito fili ba tare da ta sani ba. "Mamy ba zan yafe ma ki ba, kin aurar da ni in da kike ganin zan tagayyara, kin san cewa rayuwata za ta iya inganta ta hanyar amfani da kuɗaɗena. Kin amshe ATM card kin je kin kwashe kudint. Makaho ya gyara tsayuwar sa tare da jingine sandarsa a jikin bango ya ce. "Ba lallai sai ta ATM card kawai ba, ta yi multiple withdrawal (cire kuɗin sau da yawa a ATM daban-daban. Ko ta yi transfer ta amfani da USSD (*737# *901# da sai sauran su saboda ta san Pin ta samu damar yin hakan. Ba zai yiwu ta fitar da miliyan goma a ATM lokaci guda ba amma a cikin awa biyu za ta iya gama komai . Don idan har lissafi na ya yi daidai lokacin da kika fahimci ba kudin a cikin asusun ki an yi awa biyu da barin mu gidanku. Ta kwashe kudin ne ta hanyoyi daban-daban (ATM + Transfer kasancewar ta san Pin da bayanan asusun. Saƙonnin bankin sun nuna cewa kuɗin sun fita ne ta hanyoyi daban-daban a cikin awa biyu duk da sahihin Pin?" Da mamaki take kallonsa kafin ta ce. "Saƙonnin bankin sun nuna mani cewa ba ciro kudin aka yi ba, an kwashe kudin ne ta USSD da canja wuri (transfer) a cikin awa biyu duka da sahihin Pin." Mamaki ya kama Ma'eesaha ta ce. "Ya aka yi ka san irin waɗan nan tsarukan na banki?" "Ba abin mamaki ba ne, don ni ma wasu na ji suna fira ina kwance a masallaci ina jin su." "Su waye?" " Da wani idanun zan gane su? Wata rana bayan an sallame sallah ɗaya yake faɗa wa wani an kwashe ma sa miliyan goma ta hanyar amfani da ATM card na shi to wannan da aka fada wa ya fadi bayanin nan da na maki." Shiru ta yi dai tana kau da idsnun ta daga kallonsa, ita babban damuwar ta yadda idan Mallam Iro ya zo karɓar kudin haya wani bayani za ta ma sa kan dubu hamsin, bayan ya ma ta taimako a daren nan ba ba su gida. Su zauna. Ganin ga lokacin na tafiya kuma tauna ya addababe ta ne ga karfe tara da ta yi ne ya saka ta mike tsaye ta ɗauki handbag ɗin ta sauran 2k ɗin da ya rage ta dauka ta rasa me za ta siyo da za su ci a daren. Ita kanta ta san 2k ya yi kadan ya siya ma ta irin abincin da za ta ci ballantana ga makahon mijinta. Kuma idan ta kashe kudin duka da me za su yi breakfast da safe? Don haka ta ɗauki ɗauki 1k ta fita da shi sannan ta bar 1k a cikin handbag ɗin ta. Wajen me shagon dake kusa da gidan ta nufa, yanzu ma yana da jama'a. Don haka sai ta jira daga gefe har aka rage. "Mallam nawa ne coke na roba?" "Hajiya ɗari huɗu da hamsin ne." Shiru ta yi idan ta siye guda biyu kudin ba zai isa ba, don haka sai ta ce. "Ka bani guda ɗaya nawa kake siyar da bread. Biredin nan akwai na dubi daya da ɗari biyar, akwai na dubu daya da ɗari uku akwai na dubu daya, akwai na ɗari biyar dai kuma karamin nan na ɗari uku." "Ka bani na ɗari biyar ɗin." Ta amsa bayan ya saka ma ya a leda ya ba ta canjin Naira hamsin. Tana tafiya tana hawaye, da a baya ne kafin yau canji ko nawa ne idan ta siye abu ba ta karɓar canji sai dai ta bar wa mai kayan. Amma yau ita ce da karbar canjin Naira hamsin. Murmushi ta yi tana goge hawayenta ta ce. "Alhamdulillah ala kulli halin." Ta shiga gidan, sannan ta mai da ƙofar langa-langan ta rufe tare da saka sakata. Shiga gidan ta yi kasancewar ta fita da hasken fitilar wayarta, sai ta bar shi cikin duhu shi kadai a ɗakin. Ita a tunaninta tun da ba gani yake yi ba ai ba amfanin bar ma sa haske da za ta yi. Ta shafa ta same shi tsaye tana mamakin yanda ba ya gajiya da tsayuwa. Tana kallon ɗakin yanzu ina za su kwanta ne, ba tabarma ba katifa. Zaninta ta ɗauko guda biyu ta shimfiɗa ɗaya a in da take zaune, sannan ta ciro daya ta shimfiɗa ma sa a inda yake tsaye ta ce. "Ka zauna a nan." Kamar bai ji ta kuma ya ji ta ya san me take cewa . Coke din ta ciro tare da bread ɗin, ta ɗebi Biredin kaɗan sannan ta ɗebi rabin cike ɗin cikin robar ruwa da ta yi alwala da shi. Ta ajiye wanda ta ɗiba a gabanta sannan ta ajiye sauran da kuma ladar bread ɗin. Coke dake cikin goran ta ajiye ma sa da robar coke din da ta ɗiba ta bar ma sa sauran. "Ga bread nan da abun sha na ajiye ma ka." Shiru bai ce da ita komai ba, sake kallonta ta yi tana maimaita abun da ta faɗa, nan ma shiru bai amsa ba, don haka ta yi shiru tana kallon da da mamaki, har shi zai dinga ji da kansa waye shi? Murmushin takaici ta yi ta zauna a saman zanen da ta shimfiɗa. Da kyar take cin bread ɗin don ba ta taɓa cin irinsa ba, daure wa kawai take yi ba wai don dadi ba sai don yunwa. Haka ta cinye wanda ta ɗeba tare da coke ɗin, sannan ta janyo bottle wataer da ta siya guda biyu ta buɗe daya ta sha, sannan ta rufe ta ajiye . "Za ki iya kwana a nan ɗakin kuwa?" Wani kallo ta ma sa kafin ta ce. "To ya zan yi kana da gidan da ya fi wannan ne da za ka kai ni na kwana?" "Babu ni ma a masallaci nake kwana." Ba ta ce komai ba ta daga kai tana kallon rufin ɗakin. "Na kwanta a nan ne ko kuma na tafi masallaci da na saba kwana a ciki ne na kwanta?" "Wannan kuma ra'ayin ka ne." Shiru ya yi kafin ya ce . "Bai dace na bar ki ki kwana a nan ke kaɗai a cikin wannan gidan." "To idan ka kwana akwai abun da za ka yi mani ne? Ko za ka iya kare ni ne daga cutarwar wani abun?" "Saboda ina makaho ba na gani ko?" Da alama maganar ta soke sa a zuciya, bisa la'akari da yanayin amsar da ya ba ta ransa a ɓaci ko bai fada ba. Sandarsa ya ɗauka ya fice daga cikin ɗakin ya nufi hanyar fita ba ta ce komai ba. Tana ji ya fice daga cikin gidan. Sai anan take ta ji babu dad'i, ga wani tsoro da ta ji ya dirar ma ta lokaci guda. Ko ba komai idan tana jin motsin mutum kusa da ita ai ya fi da ta zauna ita kaɗai. Tsoron gidan ya kama ta ta mike zumbur ta fita daga cikin gidan ita ma tana cewa. "Wallahi ba zan iya kwana ni kaɗai ba." _Sidra_ Suna zaune a katafaren falon gidan, wanda kallo ɗaya za ka yi ma su ka gane wayayyun ƴan mata ne ma su ji da kansu. Wata daga cikin su ta kalli Sidra ta ce . "Yanzu ba za ki haƙura da wanann burin naki ki koma gida tun lokaci bai ƙure ma ki ba?" "Khadijah kenan, ai ba zan koma gida ba har sai burina ya cika." "Matsalarki kenan ki ce ke ba wanda zai fi ki sai dai ki fi kowa? Idan Allah bai yi za ki samu wanan ɗaukakar ba fa?" Murmushi Sidra ta yi kafin ta ce "Khadija duk abinda nake nema zan same shi , ban taɓa neman abu na rasa ba, Hakazalika wanann abun da na saka a gaba zan same shi in sha Allah." "Eh watakila ki samu wancan abu amma za ki iya rasa Fahad da kika ƙwallafa rai sai shi, kodayake yanzu ba ki son sa tun da kuka gudu a ranar aurenku." "Fahad nawa ne ni kaɗai ba wata mace da ta isa ta raɓe shi ban ga bayanta ba. Kuma ba wai don ba na son sa ba ne, sanin cewa yana masifar so na kuma na san zai jira ni na dawo ya sa na tafi ba tare da tunanin wata matsala ba, kuma iyaye na na san da zaran na dawo za su yafe mani don farin cikin gani na za su yi. Ke dai kawai Allah ya kai mu gobe mu bar garin nan na samu burina ya cika na samu ɗaukaka na dawo gida cike a alfahari." Ta yi maganar tana Murmushi. "Sady baby kin san na kashe wayata, ki ara mun taki wayar na kalli hoton masoyina Fahad." Mika ma ta wayar ta yi tana karba ta kunna Data ta shiga Instagram, shafin Fahad ta shiga in da ta dinga kallon kyawawan photonsa a shafinsa nasa na Instagram. Hoton da ya dora ta zuba wa idanu taba kallonsa. Sanye yake cikin tsadadden Suit baƙi a jikinsa, ya daura kafa ɗaya kan ɗaya, bakin hannunsa ɗaure tsadadden agogo. Ya yi kyau sosai, ba ta san lokacin da ta sumbaci wayar ba tana furta furta kalmar "I love you Fahad." Kafin ta rufe datar ta miƙa wa Sady wayarta. "Dole ki haukace akan son Fahad domin ya hadu iya haɗuwa ga kyau ga kuɗi ga gayu ai kowace mace za ta so shi." Wata ce ta faɗa a cikinsu Nam dai suka cigaba da firar su akan Fahad, ita kuma tana jin dadi yadda ake cewa saurayin ta ya haɗu. _Fahad_ Bayan ya yi parking motarsa ya fito daga cikin motar fuskarsa ta yi jajir. Gabɗaya jama'ar dake falon kasancewar duka dangi ne bare ba su fara shigowa ba. Muryar mahaifiyarsa ya ji tana cewa. "Fahad." Sai da ya ɗan tsaya kafin ya juyo duk suka kalle shi. Cikin tashin hankali Mama ta mike tsaye ta karasa inda yake tsaye ta dafa kafaɗunsa da hannayen ta biyu ta ce. "Daga gidan surukan naka kake?" Kai kawai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba. "Me yake faruwa to?" "Sidra ta gudu yau ba wanda ya san in da ta je." "What! Ta gudu?" Gabadaya falon shiru ya ɗauka yayin Mama ke salati. Kalarsa ce ta ce "Dama ba ta son sa ne?" Ma ta ba ta amsa da cewa. "Wallahi tana masifar son sa, maybe ma son da take yi ma sa ya fi nasa yawa. Ban san dalilin haka ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya Farida ta sauke tana mai farin cikin jin amarya ta gudu. Ko ba komai yanzu dole ya aure ta. Mahaifiyar Faridan ce ta ce. "Ga irin ta nan ya je ya nemi aure gidan ƙananun mutane, ga dangi ana ta yi ma sa tallar ƴan uwansa ya nemi daya ya ce baya so. Ga Farida nan sabida son da take ma sa ta bar kowa nata ta zo ta tare a gidan nan sabida shi amma yake wulaƙanta ta. "Kalarsa ta ce ai kuwa dole ya aure ta." Daidai lokacin Baba ya fito daga part ɗin sa yana tambayar me ke faruwa. Mama ta ma sa bayani shi ma salati ya yi yana cewa. "Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi." Sai a je a kwaso kayan lefen da aka kai ma su ya ke ya siye uban kaya kamar wanda zai bude shago ko bai san zafin kudi ba. "Aunty kar ku je Please." Ya fada yana kallon ƙanwar mahaifiyarsa. "Saboda me?" "Sun bani hakuri sun ce na amince a maye mani gurbin ta da ƙanwarta Nadra." Wani kuka Farida ta saka wanda kowa sai da ya kalle ta, ta haura sama tana kuka. Baba ya ce. "Kai kana son ƙanwarta ɗin ne?" "Wallahi ni ma ban sani ba." Ƙanwarsa ta yi caraf ta ce. "Wallahi in dai Nadra ce ba ta da matsala, wallahi wacce kake so ita ce mai matsalar. Sai girman kai da izza ni dama wallahi ba da ɗin raina za ka yi auren..." Mugun kallon da ya yi mata ya saka ta ja baki ta yi shiru, ita kanta Mama ta ji dadin hakan, don ta san su sau uku suna zuwa gidan kuma ta fi yabawa da hankali da nutsuwar Sidra." "Yanzu aka amsa masu cewa za ka auri ƙanwarta?" Jinjina kai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Baba ya ce "Allah ya sa hakan ya fi zama alkhairi, a cigaba da shirye-shiryen da ake yi. Daidai lokacin da kiranta shigo wayar Fahad, ganin abokinsa ne ya saka ya fita zuwa harabar gidan, motoci guda biyu ne suka shigo. Matasan samari ne ma su ji da kansu kimanin su takwas suka zo gidan. Jagora ya yi ma su zuwa part ɗin sa, ta kofar baya ba tare da sun shiga part falon ba aika shiga part ɗin nasa. Suna shiga ciki suka Zazzauna a falon yayin da shi ya shiga cikin bedroom ɗin sa. Ganin yanayinsa ya sa suka san cewa a kai matsala, ba wanda ya yi magana har ya fito fuska ba walwala yake yi ma su barka da zuwa. Musamman waɗanda ba a kasar nan suke ba daga wata ƙasar suka zo halartar bikin aurensa. "Man lafiya kuwa?" A jiyar zuciya ya sauke don ya san ba ɓoye ma su komai zai yi ba. "Sidra ta gudu yau da safe." Mamaki da kasuwa suka shiga, suna tambayar sa dalili. Nan ya ba su labarin komai da ya faru har ƙanwarta da iyayen suka ba shi a madadin ta. Nan aka shiga jajanta lamarin tare da kara ma sa ƙarfin guiwa akan auren Nadra, sannan suka bashi shawara ya cire damuwa ko saboda jama'a da za su zo daurin auren kada a fahimci wata matsala. Haka suka dinga ba shi kwarin gwiwa har ya ɗan saki ransa suka fara shirye-shiryen zuwa ɗaurin aure. _Nadra_ Lokacin da aka fito da ita daga ɗakin da aka shiga da ita sai da Gwaggo Laraba ta saki. baki tana kallonta. Ba karamin kyau ta yi ba baƙar fatarta ta kara sheƙi da ɗaukar idanu. Kudin aikinsu Goggo Laraba ta bayar suka wuce don har lokacin dire ba na jiran su. Suna bayan motar Nadra ta sake gwada kiran wayar Sidra. Har lokacin wayar a kashe. "Gwaggo har yanzu fa wayar Aunty Sidra ba ta shiga, wani irin wurin gyaran jiki ta tafi da za ta kashe waya?" Gwaggo Laraba dai ba ta ce ma ta komai ba, sai ta sake cewa. "Maybe ma tana gida ta dawo ko?" "Ba na tunanin ta dawo don wajan da nisa kuma ana dadewa kafin a gama. Yanzu mutane sun taru ba mu son a san cewa Amarya ba ta nan, don haka ke ce za ki saka kayanta a matsayin kece Amarya kafin ta dawo, kin ga ba kowa ke banbance sunan ku ba ko?" Cikin rashin fahimta ta ce . "Ni na kasa gane wannan al'amari ta ya zan shirya a matsayin ta bayan ba ni ba ce Amarya." "Eh saboda mutane za'a iya ayi ta tambayar amarya ba dadi a ce ba ta nan, kuma Ummanki da Abba su ne suka ce a yi haka ko ba za ki bi maganar su ba ne?" "Shi ke nan zan yi Allah ya dawo da ita lafiya." "Amin yarinyar kirki ." Daga haka suka ƙarasa gidan dake cike da jama'a, don rana ta yi gidan ya fara cika. Ta part ɗin Umma suka bi suka shiga bedroom ɗin ta. Duk da ta yi kwalliya amma akwai damuwa a tattare da ita. Nadra ta rike hanjun Umma ta ce "Umma ba ki da lafiya ko?" Shafar gefen fuskar Nadra ta yi tana Murmushi ta ce "Lafiya ta lau ki yi sauri ga mau kwalliya can tana jiran ki tun ɗazu ta zo." Za ta sake wata magana Umma ta rufe ma ta baki ta ce. "Sarkin magana je ki kar ki ɓata ma su lokaci." Haka ta fita cikin sanyin jiki Umma ta bi ta da kallo tana goge ƙwalla. _Makaho_ Yana zaune a barandar masallacin ya jingina da bangon masallacin ya daga kai sama. Kamar daga sama ya ji ƙamshin turarenta, lalubar sandarsa ya yi ya na cewa. "Ma'eesha ke ce?" "Eh ka taso mu tafi gida." Tausayinta ta kama shi amma duk da haka bai hana shi cewa ba. "To ni da nake Makaho ba na gani wani amfani zan yi ma ki, tun da ba zan iya kare ki daga cutarwar wani abun ba." Shiru ta yi don ita ma ta san dole ya ji ba dad'i. Tashi ya yi ya na rike da sandarsa ya yi gaba ba tare da ya ce komai ba, ita ma tana bisa a baya har suka shiga gidan ta mayar da kofar ta saka sakata ta rufe. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065357995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣5️⃣ Shiru ta yi don ita ma ta sa dole ya ji ba daɗi .Tashi ya yi yana rike da sandarsa ya yi gaba ba tare da ya ce komai ba, ita ma tana bin shi a baya har suka shiga gidan ta mayar da ƙofar ta saka sakata. Da lalube ya shiga cikin ɗakin, in da yake tsaye ɗazu can ya je ya kara tsaya wa. Ta shiga tana rike da ƙaramar wayarta ta kunna torchlight. Wanka take so ta yi sai dai ba ta iya wanka da ruwan sanyi, ga shi ba ruwan zafi. Kayan jikinta ta cire ba ta damu da yana wajen ba saboda ta san makaho ne, towel ta daura ta nufi ƙofar fita. "Ina kuma za ki ke dare ne yanzu fa." Ba ta iya amsa ma sa ba sakamakon kukan da take yi na rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Sai dai kuka mara sauti take yi, idan ba wanda ya kalli idanunta ba to ba zai je tana kuka ba. Banɗakin ta nufa kasancewar akwai ruwa da makaho ya cika bokitin na karshe ta ajiye. Sai da ta rintse idanunta tana sakin ajiyar zuciya sannan ta iya yin wankan. Tana fitowa ta same shi tsaya a kusa da ƙofar banɗakin, ba ta yi ma sa magana ba shi ma bai yi ma ta magama ya fito rike da bokitin ya nufi bakin Rijiya zai ɗebo ruwa. Man shafar ta ta dauka bayan ta goge jikinta sannan ya shafa mai. Bayan ya shafa mai ta fesa turare na jiki wato body spray. Kayan barci ta saka riga da wando da wata hula mara nauyi ta saka. Tana kallon ɗakin ta rasa ta ina za ta kwanta, ga ba gado ba katifa ballantana tabarma. Tana tsaka da wannan tunanin sai ya shigo cikin ɗakin da sallama a bakinsa. Ta amsa ma sa ba tare da ta lalle shi ba. Yana shigowa daidai yana kawowa wajen shimfidar ta ta yi ma sa ta ce. "Ga zanin da na shimfida ma ka nan ka zauna akai ." Ba musu kuwa ya zauna ya tanƙware ƙafarsa, shiru dakin ya ɗauka ba wanda ya yi magana. Bayan ta gama tunani sai ta koma ta rufe kofar dakin ta saka sakata. Daidai lokacin nepa suka kawo wuta haske ya gauraye ɗakin gabaɗaya. Kallon bread da coke ɗin da ta ajiye ma sa ta yi ta ga bai taɓa ba. Taɓe baki ta yi sannan ta dauki karamin akwatin ta yi pilow da shi bayan ta kwanta. Sai ta ji ya yi ma ta girma da yawa wuyanta zai iya ciwo. Cire shi ta yi sannan ta yi pilow da hannunta ta kwanta. Lokacin karfe goma sha daya na dare ne. Wayarta ta soma ruri ta ga lambar ba ta ƙasar nan ba ne, kuma ta san waye, katse kiran wayar ta yi tare da gyara kwanciyarta da sam ba ta ji fadinsa ba." Sake kira aka yi har ya katse ba ta ɗaga ba, a karo na uku ne ta ambaci sunansa. "Oh Allah Abdul ban san me zan ce ma ka ba." Ta yi maganar tana goge ƙwallar tausayin kanta da take ji, take wani sabon kuka ya zo ma ta sai ta toshe bakinta tana yin sa a hankali. Messages ne ya shigo wayarta ta duba still shi ne. *Ina fatan jina cikin aminci farin cikina, na ga kina katse ma ni kira fatan ba wani laifin na aikata ba, Please ki amsa wayata ko hankalina zai kwanta.* Tana gama karantawa ta katse kiran wayar, gabaɗaya ta kashe wayar ta koma ta kwanta tana hawaye. Kamar sauro na jiran ta kwanta suka fara kai ma ta hari. Abinda bai taɓa faruwa da ita ba kenan, sauro su addababe ta haka. Ga cizon sauro ga kuma kukan sauro da suke yi ma ta a kunne. Tashi zaune ta yi ta saka kuka tana kara sakin kuka kamar karamar yarinya. "Ma'eesha lafiya." "Wallahi sauro suke damuna ba zan iya barci a haka ba." "Ayyah sorry, ba ni ɗankwalin kayan ki." Ba musu ta zuge zip ta ɗako ta mika ma sa, ya matso kusa da ita ya karɓa. "Ki manta to." Kwanciya ta yi kamar yadda ya ce, ya dinga kore ma ta sauro da ɗankwalin. Tana jin kamar yana ma ta fifita har ɓaci ya ɗan fara daukarta kuma ya hadu ma ta da gajiya. Haka makaho ya dinga yi wa Ma'eesha fifita har ta yi barci . Tun karfe sha daya har biyu na dare yana zaune yake kore ma ta sauro. A lokacin ta farka ta ga yadda ta bar shi haka yake yi ma ta fifita. Awa uku kenan yana abu ɗaya. Tausayinsa ya kama shi cikin tashin murya ta ce . "Ka kwanta ka yi barci na gode." "Ba za ki iya barci ba idan na daina ku yi barci kawai, dama ni ban saba yin barcin dare ba." Barcin ta cigaba da yi har aka yi kira sallar asuba. Sai a lokacin ya ajiye ɗankwalin ya mike tsaye daidai tana buɗe idanunta. "Da ido ta bishi ya fice daga dakin bayan ta dauki Sandarsa." Bayan kamar mintuna goma ya shiga da alama alwala ya yi, sai ya ce . "Zan tafi masallaci sai an yi sallah zan shigo." Kai kawai ta jingina kamar yana ganin ta, ita ma tashi ta yi ta nufi banɗaki don ɗauro alwala. _Nadra_ Tana shiga cikin ɗakin ta samu mai kwalliya na jiranta. Da sallama dauke a bakinta ta shiga in da ta samu ɗaiyar Gwaggo Laraba tare da mai kwalliya. Duk da kasancewar ita ba mai son kwalliya ba ce kamar Sidra. Amma yanzu kam ba ta isa ta ce ba ta son kwalliya ba. Hijabinta ta cire wani ni'imtacen ƙamshi na tashi daga jikinta. "Bari na yi sallah lokacin sallah ta yi ." Ba ta jira cewar kowa ba ta nufi bathroom don sauro alwala Sai da ta gabatar da sallar sannan ta dawo kan su. Zama ta yi dadai lokacin da wayarta ke ringing, ta duba ta ga Ya Sayyadinta ne ke kiran wayarta. Murmushi ta yi za ta ɗaga sai Gwaggo Laraba ta karbi wayar ta kashe ta gabaɗaya ta ce. "Ki tsaya a gama da sauri ba lokaci, kina gani gidan ya fara cika da jama'a ko?" Mai kwalliyar ta buɗe akwatin kayan kwalliyar ta dubi Nadra ta ga ba ita ba ce ta kira ta, hasalima wacce ta kira ta fara ce ita kuma wanann baƙa ce. Kallon Gwaggo Laraba ta yi ta ce . "Ko dai ba gidan ba ne?" "Nan ne kar ki damu wannan ce za'ayi wa wacce ta kira ki Sidra ce ita ce ƴar wannan." "Okay." Ta faɗa a takaice ta fara yin aikin da ta kawo ta yi. Nan ta tsantsara wa Sidra kwalliya wanda ya yiasifar yi ma ta kyau kamar ba ita ba. Sannan aka ɗauko ma ta kayan Sidra wanda dama shi za ta saka a lokacin. Sai dai an ɗan sake ba tela ya sake buɗa ma ta faɗin kayan kasancewar Nadra ta fi Sidra diri da cikar halitta. Karba ta yi ta shiru tare da taimakon mai kwalliyar ta shirya ta, ta yi ma ta ɗaurin Ɗankwali. Nan ƴan uwa suka dinga ɗaukarta photo, ita dai har lokacin ba ta saki jiki ta ba, ta rasa dalilin dai zai saka a ce saboda Sidra ba ta nan ta maye gurbin ta. Ga shi an ce ba yanzu za ta dawo ba, ita dai addu'ar ta Allah yasa kafin karfe huɗu ta dawo, don idan ba ta dawo ba to ita kam ba za ta iya maye gurbin ta a wajen Dinner party ba. Ta ya ya za ta fito ta tsaya tare da Fahad kai ba zai yiwu ba ma. Ita kadai take saƙa da warwara har ta ji ana cewa karfe biyu ya yi yanzu za'a daura aure. Tsintar kanta ta yi cikin faɗuwar gaba da tsoro. _Fahad_ Kwance yake a bayan motar ya jingine bayansa da jikin motar, sanyi A.C da ƙamshin turarensa ke tashi a cikin motar. Mukhatar da Aluyi sun saka shi a tsakiya, Kabir na zaune a gefen direba wajen me zaman banza Suna ba shi baki tare da kwantar ma sa da hankali, don sun san yana cikin damuwa. Har aka karasa kofar gidan surukan nasa bai buɗe idanunsa ba. Kowa ya fito ya bar sa a cikin motar. "Ko sai mun fito da kai ne?" Cewar Mukhtar yana kallonsa yana Murmushi. "Hana Majidaɗi ka saki ranka ma na sai ka ce wanda aka yi wa auren dole?" Harararaa Fahad ya yi tare da cewa . "To idan ba auren dole aka yi ma ni ba na soyayya ne?" Ya faɗa yana ziro fararen ƙafarsa wanda ke cikin takal ki ƙirar kamfanin Prada, takalmar baƙi ne. Yana sanye da farar shadda gezna wanda aka yi ma sa aiki da baƙin zare riga da wando har da babbar riga. Ya fito yana gyara zaman babban rigarsa. Kansa sanye da bakin hula, hannunsa ɗaure da tsadadden agogonsa na Rolex Day-Date 40 (president watch) wanda ya zauna a hannunsa kamar don shi aka yi . Duk wanda ya kalle shi zai gane shi ne angon domin ya sha banban da kowa a wajen. Zuwan su ba jimawa aka fara shirye-shiryen ɗaurin auren. Ɗaurin aure ne da ya tara manyan mutane na gida da waje. Manyan kusoshin gwamnati da da saraki da ma su mulki, har da shahararrun ƴan kasuwa . Mutane suna ta yi wa Fahad fatan alkhairi ana taya shi murna, sai dai ya yi kokarin ganin damuwar da yake ciki bai shafi walwalarsa ba. Yana nan zaune ba abinda yake yi sai tunanin Sidra sam ya kasa dalilin da ya sa ta aikata ma sa haka, duk ikirarin da take yi na tana son sa har za ta iya yin haka? Bai ankare sa an ɗaura ma sa auren ba sai da ya ji an dafa sa ana taya shi murna. Bayan an gama an tashi ana ta ma sa fatan alkhairi ana ɗaukar hotuna. Daga nan Baba ya ce wa Fahad su shiga shi da abokansa su su gaida surukansa Haka kuwa aka yi da shi da Mukhtar, Khabir da Aliyu suka shiga cikin gidan. Falon Abba wanda shigowar su kenan shi da ƴan uwansa da abokansa. Suka durƙusa suka gaishe su tare da yi ma su godiya da ba su ƴa da aka yi . Daga nan kuma suka nufi main falon gidan, suka ga jama'a mafi yawansu ƴan uwa ne. Tun da suka shiga gidan kansa a ƙasa yake har suka durƙusa suka gai da dangin Amaryar. Kasancewar ba kowa ya san angon ba, kuma duk wani abin rabo da za'a raba wanda yake da photon Sidra da Fahad ba'a raba ba don kada jama'a su gan shi tare da Sidra a photo a fahimci wani abu. "Ina angon yake?" Wata Dattijuwa ta tambaya, Haidar ya nuna ma sa Fahad da ya sunkuyar da kai tun da suka shigo. "Ma sha Allah kyakkyawan saurayi kuwa ta samu, Allah ya ba ku zaman lafiya mai ɗore wa da zuri'a ma su albarka. Yadda muka zo taron biki Allah ya sa nan da watanni tara mu zo taron suna." Amin aka amsa ana sake rangaɗa guɗa wanda Fahad yake jin samuwar har cikin kansa. Nan suka yi ma sa nasiha sosai sannan ya mike su ma abokan nasa suka mike, in da suka nufi part ɗin Umma. Har lokacin tana cikin bedroom ɗin ta ita da wasu ƙawayenta. Gwaggo Laraba dake falon ita da jama'a ce ta shigo don kiran Umma ta zo ga ango ba abokansa Gabadaya suka fito ita da ƙawayenta, angwayen suka gaishe su suka sa ita dai Ummar karfin hali take yi, hade ɗaya damuwar halin da Nadra z ga shiga ciki take yi. Sanin irin son da Sidra ke yi wa Fahad, da yadda Fahad ke son ta. Ita Nadra da ba ce yana son ta ba ya za ta yi musamman da ta san halin Halin Nadra da dabi'arta ya sha banban da na Fahad. Har suka gama gaisuwar suka tafi ta kasa magana tausayin Nadra kawai take yi . Sallama suka yi ma su suka tafi . A hanya ma kasa magana da juna su Fahad ya yi, domin su kadai suke ta firar su. Suna isa gidan tun a harabar gidan ana ganinsa aka fara rangaɗa guɗa. Abokan wasan sa na tsokanarsa bai bi ta kansu ba ya yi wucewarsa part ɗin sa. Bai tsaya falo ba ya shiga bedroom ya mirza key ya rufe ya cire takalminsa da hularsa, sannan ya cire babban rigarsa ya cire rigar ciki. Ya saura sai farin singileti a jikinsa. Agogon hannunsa ya kwance ya kwanta a saman tangamemen gadonsa. . Yana jin ana knocking amma ya share bai bude ba har suka gaji suka bar shi. Abinci da aka ajiye masu da abun sha kowa ya fara ɗibar abinda ke ransa yana ci. Suna nan sai ga wasu abokan na Fahad sun shigo cikin falon. _Nadra_ Ta sha kyau iya kyau kamar ba ita ba, baƙar fatarta mai matukar kyau da ƙyalki sai shinning take yi. Ga kayan ɗinkin riga da siket na less ta saka a jikinta, cikin kayan da Fahad ya siye wa Sidra ne wanda kudinsa zai kai kimanin dubu ɗari biyu. Sai arkar gold da ta saka kunne da wuya, har da warwaro da zobe. Kasancewar ta ba mai son nuna jiki ba kuma less ɗin sun kama ma ta jiki ya saka ta saka babban gyale, duk da Hijabi ta so sakawa sai da Gwaggo Maimuna Yar Abba ta hana ta. Shi ne fa ta saka babban Hijabin kasancewar ba kowa ya san cewa Sidra ba ta nan ba ya saka wasu da suka san ba Nadra ke aure ba ya saka suka tambayar ina Sidra take, ita kam sai sai ta ce ma su tana nan dawowa ta fita ne, wasu kuma sai ta sanar da su cewa ta tafi gyaran jiki ne. Mamaki wasu ke yi ace yau ɗairin auren amma a ce ta je gyaran jiki, me ya saka ba ta yi da wuri ba Ƙawar Nadra ɗaya ce wato A'isha Humaira, ta zo tana sanye da hijabi da niƙab a fuskarta. Tana zaune kusa da Nadra suna firar yadda Sidra ya tafi wani wajen ta dade ba ta dawo ba. Har lokacin sallah la'asar ta yi suka tashi Nadra ta shiga ta ɗauro alwala, sannan A'isha ta shiga. Suna zaune suna azkar din yamma sai ga ƴar Gwaggo Laraba, wacce ba za ta wuce sa'ar Nadra ba ta shigo ta ce. "Dama Mama ce ta ce na duba ko kin yi sallah mai kwalliya za ta zo ta yi ma ki kwalliyar zuwa Dinner party kafin ango ya ƙaraso tare za ku tafi da shi." Zumbur ta mike tsaye tare da cewa. "What?" Wani kallo ta yi wa Salma kafin ta ce . "Waye zai je Dinner party? Allah ya kiyaye, ni duk ire-iren waɗan nan wurare ban taɓa zuwa ba, duk wani taro in dai ba walima ba ce to ba zan tafi ba ballantana q ce na je a madadin Aunty Sidra, a jira idan ta dawo su je ta yi amma ba zan iya ba, I try my best but ba zan iya zuwa Dinner party ba." Ta fada kamar za ta yi kuka. Salma ta fit don ta sanar wa Mahaifiyar ta abinda ya faru. _Fahad_ Har karfe uku da rabi bai fito ba, da ya ga lokacin sallah ta yi na ya shiga bathroom ya ɗauro alwala ya fito Nan suka cigaba da firarsu .Ganin karfe uku da da rabi ta yi ne ya saka suka je suna knocking. Daidai lokacin shi ma zai fito don zuwa masallaci. Shi ma sai a lokacin ya lura da abokinsa Sadik daje ƙasar Canada ya iso. Rungume juna suka yi sanan suka fita tare don duk sun yi alwala a bathroom dake falon. Gabɗaya suka je masallaci, suka bi jam'i aka yi sallah. Bayan an idar a tare suka fito suka koma ciki. Daidai lokacin ne Yar Fahad Aunty Rahama ta shigo. Dukkanin su suka gaishe da ita don duk sun san ta don Fahad na zuwa da su gidanta . "Se Aunty Babba." Cewar Sadik yana dariya . Kallon su ta yi tana cewa. "Lokacin Dinner party ya kusa ku je ku saka shi ya shirya bana son Afrikan time." "Wai ya ce b zai je Dinner party din nan ba an fasa yi ." "Akan me wanna ai zandan banza ne, dole a yi shi kamar yadda ka tsara tun farko, idan zai cire wa kansa damuwa ya rungumi ƙaddararsa." Tana fadar haka ta shiga bedroom, yana zaune a bakin gado ya yi shiru cikin tunani Dafa kafaɗarsa t yi ya ɗago kai ya kalle ta. "Tashi ka shirya ku je ka ɗauki Amaryarka ku je wajen Dinner party." Kwaɓe fuska ya yi kamar zai yi kuka, kafin ya buɗe baki zai yi magana ta ce. "Ba na son jin komai, kuma na fahimci matsalarka, ka yi abinda na ce maka kawai." Dole ya tashi ba tare da ransa ya so ba ya nufi bathroom, sai da ta ji saukar ruwa alamar ya fara wanka sannan ta fice. Don dama su matan sun shirya zuwa reception ɗin . _Ma'eesha_ Tana zaune a ɗakin tun da ta idar da Sallah ta yi azkar ba ta tashi ba, tana tunanin hanyar da za ta samu dubu hamsin ta biya kudin hayar gidan nan. Ga shi ta yi ma sa alkawarin yau za ta bashi kudin. Sallamar makaho ta ji ya shigo, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba. Shigowa ya yi ya zauna kafin ya ce . "Ina kwana?" Sai a lokacin ita ma ta ce ma sa . "Ina kwana?" "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah." "Ya zaman hakuri da rashin barci." "Ai Ni na yi barci kai ne dai ka kwana a zaune kana ma ni fifita ." "Ke ma ba barcin kika yi ba, na ji kina ta motsawa." Tunani take yi 1k ya rage ma ta idan ta siyo abin da za su ci shi kenan ba ta da komai. Wani tunani ta yi kafin ta ce. "Zan fita na je na siyar da wayata ko zan samu na biya kudin hayar gidan nan, kuma sauran canjin mu samu na cin abinci da dan abun buƙata da ya dace. Shiru ya yi kafin ya ce . "Idan kika siyar haka za ki zauna ba waya?" "Ai wayoyina biyu ne da ni, zan siyar da babbar na rike ƙaramar ina amfani da shi. Na san kudin zai yi yawa . Don wayar miliyan daya da dubu ɗari biyar aka siya mun, ko miliyan ɗaya idan na siyar zan samu abubuwa da yawa da zan siya ma su sauƙin kuɗi, kamar karamar katifa labule kayan aiki da kuma kayan abinci." Shiru ya yi kafin ya ce . "Allah ya tsare ya dawo dake lafiya ya sa ki samu abin da kike nema." "Amin ya Allah, bari na je kafin mai karɓar kudin hayar ya zo ya yi Mani sallama." Tana fadar haka ta tashi dama rigar Abaya ne a mijinta baƙa. Rolling kanta ta yi da mayafin abayar sannan ta dauki handbag ɗin ta da wayoyin ke ciki ta fice. *Maman Ihsan ce.* 090 5327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣6️⃣ Tana fadar haka ta tashi dama rigar Abaya ne a jikinta baƙa. Rolling kanta ta yi da mayafin abayar sannan ta dauki handbag ɗin ta da wayoyin ta ke ciki ta fice ba tare da ta san in da ta dosa ba. _Aunty Rahama_ Tana fita daga part ɗin Fahad ta nufi part ɗin Mama. Tun kafin ta karasa jikin kofar bedroom ɗin take ta jin muryar kanwar mahaifiyar su wato Hajiya Jummai mahaifiyar Farida. "Ai shi kenan ku shirya ku tafi wajen Dinner ni dai ba in da zan je a yanzu haka. Don Yaya na gama gane cewa ba ki ƙaunata ba ki ƙaunar ƴata. Saboda Fahad Farida ta bar garin ta ta bar iyayen ta da kowa na ta ta dawo nan gidan da zama, ba don komai ba sai don ta samu kusanci da Fahad. Amma yaron nan ya yi kamar bai gane tana son sa ba. Da ta gaji da bayyana ma sa irin son da take ma sa ya wulakanta ta, kuma kina cikin gidan nan kun san me ke faruwa. Yanzu yarinyar da ya ƙwallafa rai a kanta an ce ta gudu ta bar gidan iyayen ta. Madadin ya zo a bashi ƙanwarsa ya aura shi ne ya je aka ba shi kanwar yarinyar ya aura ko? Sanadin Haka ga Farida can kwance na kasa gane kanta, ba sunan da take kira sai na Yaya Fahad." Murmushi Mama ta yi tare da cewa . "In ban da abin ki Jummai ai ni abun farin ciki ne a wajena a ce ga ɗana zai auri ƴar ƙanwata. Amma ya ce baya son ta to ya za mu yi? Ba dole a bar shi ya auri wacce take so." Hajiya Jummai za ta sake wata magana ta ga Mama ya tsuke ma ta fuska tana dauke kai alamar ba ta son zancen, ga hankulan mutane ya dawo kansu. Mama fita ta yi daga cikin dakin tana tarbar baƙin da ke zuwa a lokacin. Kasancewar Yamma ta yi lokacin da za'a je Dinner party ya yi mutane suka fara shirye-shiryen zuwa Dinner party. Ankon fari da baƙi suka yi . White an black. Mata suka sanya ankon nasu material fari da baƙi ne sun yi kyau sosai. Bangaren Fahad ma zuwa lokacin samari ne cike da falon nasa, su na sun yi ankon yadi na fari mai ratsin baƙi a jiki. Gabɗaya kalar yadin suka sanya ba abinda ke tashi daga cikin falon sai waƙar bikin Fahad da aka yi da sunan Sidra. _Aunty Rahama_ Ita ma ta shirya cikin ankon nata ɗinkin doguwar riga, tana rike da hannun ƙaramar ƴar ta mai suna Zahrah yar shekaru uku a duniya. Part ɗin Fahad ta nufa don ta tabbatar ya shirya ganin karfe biyar ya kusa yi. Da sallama ta shiga cikin falon, Sautin waƙar da bikin kawai ke tashi wasu na rawa yadda wakar ke ma su dad'i. Hanyar bedroom ɗin Fahad ɗin ta nufa sai suka haɗu a corridor. Shi ma angon ya yi dressing White and black. Yana sanye cikinsu tsadadden Suit ɗin sa baƙi, da farin shirt a ciki, ya sanya farin glass a idanunsa. Ƙafarsa sanye cikin cikin takaninsa cover shoe mai baƙi ƙirar Louis Vuitton mai ƙamshinsa mai dadi ke tashi daga jikinsa. Hannunsa ɗaure da tsadadden agogonsa, ya yi masifar kyau wanda ya kara fito da ajinsa da kwarjininsa. "Tabarakallah ma sha Allah, tsarki ya tabbata ga uban gijin da ya halicci wannan kyakkyawan angon." Sai a lokacin ya lura da ita,kallonta ya yi fuska ba walwala . "Na gaji da ganin wannan murtuƙewar taka haka, har yanzu kana tunanin Sidra ko?" Bai ce komai ba ya kau da Kai gefe yana kallon wani wajen daban. Don haushin kowa ka yake ki a cikin Rayuwarsa "Ka rungumi ƙaddararka a yadda ta zo maka Fahad. Don Allah ka yi kokarin cire Sidra daga cikin rayuwar ka, ka ɗauka ita ba matarka ba ce Nadra ce matarka. Dama can hakan Allah ya tsara, wata ba ta auren mijin wata, haka kuma wani baya auren matar wani. Ka rungumi Nadra ka yi irin rayuwar da ka tsara yi da Sidra da ita, ka ba ya kulawar da kake ba wa Sidra ka ƙunace ta kamar yadda ka ƙauna ci Sidra." Girgiza kansa ya yi yana cewa. "Ba na iya tunanin zan yi haka Sunyi Rahama." Saboda ba ka son ta ko?" Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sai ya ji muryar ta tana sake cewa. "Saboda ita ba fara ba ce iya ɓaka ce ya saka ba ka son ta masai Sidra baƙa ko?" "Ba wannan ne kawai matsalar ba, ita wanann yarinyar sam ba ta waye ba, ta cika sanyi da yawa ga ta da zubin munafukai, ta dinga sunkuyar da kai wai ita mai kunya ni ba na son mace mai kunya, yadda kina san wata mutumiyar da can baya haka take sam ba ta waye ba. Wallahi ba na jin zan iya rayuwa da ita ba." Murmushi Aunty Rahama ta yi tana cewa. "Wannan ba matsala ba ne, kai za ka iya canz ta ta koma yadda kake so? Kai za ka koya ma ta son ka da irin rayuwar da kake so matukar bai sabawa addini ba. Don haka ka saki ranka don Allah ka daina wanann haɗe rai da kake yau rana ta musamman ce a wajanka ba ka ga yadda kowa ke farin ciki saboda kai ba, to kai me zai sa ka kasace cikin bakin ciki?" Murmushi ya yi wanda iya fatar bakinsa ta tsaya sannan ya yi wa Zahrah Baby alamar ta zo. Da sauri ta saki mahaifiyar tata ta nufi wajen uncle Fahad ɗin ta ta rungume shi. Hannunta ya rike suka nufi falon Sunyi Rahama n jaddada ma sa wasu sun wuce ya je su dauki Amarya su tafi. Da to kawai ya amsa har ya karasa suke gaisawa da sauran wadanda suka zo ma sa . Daga nan ne kuma aka fara fita don zuwa wajen Dinner party. Shi ma fitowa ya yi suna tafiya yayin da Zahrah Baby ta nufi mahaifiyarta ganin za ta shiga wani motar. Fahad kuwa wajen sabuwar motarsa wacce ya siya bai fara hawa ba sai yau, da burin yau ne zai fara hawanta shi da Sidra ashe ba haka ba ne shi da Nadra zai hau ta. Wasu daga cikin abokan ango motarsu na cikin gidan suka shishshiga wasu kuma na su na waje ne suka dinga fita zuwa wajen motocin. Wata galleliyar mota ƙirar Lamborghini urus ya nufa wanda yana ƙarasawa wajan motar sai ga diraba ya bude ma sa bayan motar, bayan ya shiga sannan ya rufe da hanzari direba ya nufi mazauninsa ya yi wa motar key suka bar gidan. Jingina bayansa ya yi da jikin motar sit ɗin motar ya lumshe idanunsa ƙamshinsa da sanyin ac ke ratsa kowane sashe na motar. A ƙofar gidansu Nadra direban ya yi parking don ya san inda za su fara zuwa kafin su tafi Dinner party. Yana ƙarasawa ya ga motoci na barin wajen. _Nadra_ Bayan an gama yi ma ta wani kwalliyar ne aka fito da kayan da za ta saka. Karɓa ta yi ta warware kayan ta juya gaba da baya ta kalle shi da kyau sannan ta ce. "Yanzu Wai wannan kayan kuke tunanin ni Nadra zan saka?" Gwaggo Laraba da mai kwalliyar sai wata ƙanwar Umma daje ɗakin suka kalle ta. Kafin su yi magana ta ce . "Ku duba fa ku gani kayan ko hannun arziki bai da shi hannun ƙarani ne ga shi gaban rigar irin mai bayyanar da ƙirar halittar mace ne, wato shape ɗin ƙirjinta, don an yi ma sa gidan breast . Yanzu dama ranar da Aunty Sidra suka fita da Yaya Fahad ta ce za su je siyan rigar da za su yi Dinner party da shi wannan kayan suka siyo? A yanzu a matsayin ta na matar aure ne za ta saka wannan kayan ta fita cikin jama'a ana kallonta? Shi ma Yaya Fahad da suka fita zaɓen kayan ya san wannan kayan suka zaɓo zai bar matarsa ta saka ta shiga cikin jama'a maza da mata?" Ƙawar Umma mai suna Hajiyayye ta kalli Nadra ta ce. "Daughter ki yi hakuri ki saka ku tafi ga angon can a mota yana zaman jira da?" Kwaɓe fuska ta yi tare da cewa . "Ba zan iya saka wannan kayan ba?" Yar Abba Gwaggo Maimuna ce ta daka wa Nadra tsawa ta ce. "Za ki saka ku tafi ana jiran ki ko sai na ɓata ma ki rai yanzu?" Kasancewar Gwaggo Maimuna tana da zafi sosai ko Abba shakkarta yake yi, family ba wanda baya tsoron ta. Gwaggo Laraba dai ba ya ce komai ba, don ita ma ta ga rashin dacewar kayan a wajen mace mai kunya wacce ta saba shigar mutunci da kamala ba za ta iya saka kayan nan. Kuma ta ga laifin Fahad wanda aka ce shi da Sidra suka zaɓo kayan, wani irin rashin sanin ya kamata ne ya bari matarsa ta shiga jama'a da wannan kayan, idan Sidra ba ta da hankali ai shi yana da wannan ai ba wayewa ba ne, tana tsaka da wannan tunanin ta ji muryar Gwaggo Maimuna na cewa. "Nadra idan ba ki saka kayan nan kun tafi ba wallahi yanzu zan saka a danne mani ke na saka ma ki kayan nan ta karfin tsiya, ita Sidra da za ta saka me kika fi ta ne, ko ita ma ta san ciwon kanta ba sai ke ce mai sanin ya kamata, to sannu uztaziyya." Gwaggo Laraba za ta yi magana kenan sai Gwaggo Maimuna ta ce . "Ki yi Mani shiru Laraba idan aka biye ma ki yarinyar nan ba za ta saka kayan nan ba, don ba zan iya lallaɓa ta da kike yi ba, tun dazu sai bata wa mutane lokaci take yi ana ta jiranta." Ba yadda Gwaggo Laraba ta iya saboda Gwaggo Maimuna yayarta ce, kuma ko mahaifun Nadra ne idan ta yi magana baya yi ma ta gardama don haka ta jinjina wa Nadra kai tana ma ta murmushi alamar ƙwarin guiwa. Don haka Nadra ta saka kayan wanda ya yi masifar yi ma ta kyau, sai dai sun kama ta duk shape ɗin ƙirjinta ya fito da hips ɗin ta ma su ɗaukar hankali. Dogowar rigar irin wanda bayansa je sharar ƙasa ne idan tana tafiya. Kuka take son yi sai Gwaggo Maimuna ta ce. "Ki haɗiye kukan nan kar ki kuskura ya fito waje." Jin haka ya fasa kukan ta haɗiye shi mai kwalliya ta gyara ma ta in da hawayen ya zubo. Ita ma kayan nata white and black ne, don rigar dari da baƙi ne sai mayafin kamar net da ka daura ma ta ne fari zalla. Sarƙar gold ɗin ta aka saka mata a kunne da wuya sai hannu da yatsu wato warwaro da zobe. Da aka saka ma ta. Sai wani takalmi mai tsawo sosai da tsini ta saka. Wanda tsinin takalmin ya yi yawa. Kuma dama ita ba ma'abiciyar saka dogon takalmi ba ne duk, takalmi mai tsawo ba ne flat shoe take saka wa. Haka ba yadda ta iya ta zira ƙafa tana kallon su yayin da mai kwalliyar ke yi ma ta hoto. "To sai ki fita ki je ga angon nake can yana jiran ki." "Ango na muka Gwaggo?". Sai a lokacin Gwaggo Maimuna ta san cewa ta saki layi. "Au angon Sidra nake son cewa fa." "Ni wallahi da ta dawo na yanzu na huta da wannan masifar, ga shi wani gyaran jiki ne tun safe har yamma ba ta dawo ba?" "Za ki wuce ko sai na ɓata ma ki rai?" Tafiya take yi a hankali kasancewar ba ta iya tafiya da irin takalmimin nan ba. Salma ƴar Gwaggo Laraba ke bin bayanta za ta taka ta wajan motar, don ƙawar ta A'isha Humaira ta wuce gida bayan ta yi sallar la'asar. Yana zaune a bayan motar har lokacin idanunsa a lumshe suke. Kamar an za ce ya biɗu lumtsatstsun idanunsa ya sauke su akan ta ta jikin mirror ya hago ta tana tafiya kamar wacce take tausayin ƙasa ta nufo motar . _Makaho_ Bayan fitar Ma'eesha da ne ya samu ya kwanta a saman zanin da ta shimfida ma sa, sakamakon rashin rarcin da bai yi ba, don ko na mintuna biyar bai yi ba, ta sakamakon kwana da ya yi a zaune yana aiki. Yi wa Ma'eesha tare da kore ma ya sauro. Yana kwance a saman zanin yana tunani sabuwar rayuwar da za su yi da Ma'eesha. Lallai dole ya tashi ya nemi abun yi saboda ya rike ta duk da ya san cewa ba zai iya ɗauka ɗawainiyar ta ba bisa la'akari da irin rayuwar da ta ta so ta saba da shi, da kuma abincin da ta saba ci da irin ruwar da ta saba sha da makwancinta da suturarta da mayyukan shafawarta da turarruka da ta saba amfani da su. Ta ya Ma'eesha za ta zauna da shi. A tunaninsa ba za ta yarda ta zauna da shi ba, ya ɗauka za ta ci mutuncinsa ne ta wulakanta shi ta sa ya sake ta amma sai ya ga ba ta dauki rayuwar da zafi ba ta rungume kundin ƙaddararta, ta yarda tare za su yi karatun tare za su yi hadda sannan kuma tare zasu koka. Tabbas samun mace irin Ma'eesha a wanann zamanin sai an bincika. Yana ta tufka da warwara har barci ya yi awon gaba da shi nan kwance akan zanin da ta shimfida ma sa . _Ma'eesha_ Tana fita daga cikin gidan ta tari mai keke nape, bayan ya tsaya ya kalle ta ya ce "Hajiya ina zuwa?" "Mallam ka san in da ake siyen waya na hannu?" "Eh na sani Hajiya, sai sai gaskiya ba su siye da daraja ba, yadda kika san ɓarayi haka suke, za ki siye waya da tsada amma su siye shi a wulaƙance. Amma idan kika je siye a wanensu tsada za su yi Maki." "Mu je ka kai ni lalura ce ta saka zan siyar." "To mu je amma ba lallai sun fito ba don sai karfe tara zuwa goma suke fitowa ." "To mu je idan sun fito na siyar za ka kai ni kasuwa na yi soyayya sai mu kwashi kayan ka kai ni gida." "To Bismillah." Ta shiga suka ɗauki hanyar zuwa kasuwar. Cikin ikon Allah suna ƙarasawa sai ga wani yana kokarin bude shago, da alama shi kadai ne ya fara fitowa . Kashe kake nape ya yi ya yi ma ta jagora yana cewa. "Mu je Hajiya." Tana bin sa a baya suka shiga shagon da sallama. Mai shagon ya amsa yana kallon su. "Me kuke so?" Ma'eesha ta ce "Waya zan siyar Mallam?" "Wace irin ce?" "Iphone 15 ne." Sai da ya tsaya ya kalle ta da kyau daga sama har ƙasa ya kare ma ta kallo ya tabbata ba ta yi kama da wacce za ta kawo ma sa wayar sata ba. "Kawo mu gani." Handbag ɗin ta ta buɗe ta ciro wayar ta ba shi sannan ya karba ya duba da kyau. Kafin ya kalle ta ya ce. "Na gaji zan siye ta Naira dubu dari huɗu 400k." Wani kallo ta yi ma sa ta ce. "Mallam ka san nawa aka siya mun wayar nan kuwa? Ko wata biyu ba'a cika ba da mahaifina ya siya ma ni ita miliyan daya da dubu ɗari biyar na kawo ta yanzu za ka siye ta a wulaƙance?" "To Hajiya ai ma na siye da daraja idan wasu na Naira dubu dari uku da hamsin za su siye ta, waya ko yau kika siye gobe kika kai kasuwa sai ta karye kin sani." "Ban sani ba don ban taɓa siyar da waya ba sai sai na kyautar, wanan karon ma ƙaddara ce da ba za ka ganni a nan ba." "To gaskiya zan siye ta dubu ɗari huɗu da hamsin." "Don Allah ka kara Mallam wallahi matsala ce ta saka na siyar da wayar ba komai ba, lalura ce." "Na sani don daga ganin ki kina cikin matsala, don haka zan tausaya ma ki na dutse dubu ɗari biyar 500k idan bai yi ma ki ba ki dauki wayarki ki tafi ." Shiru ta yi tana mamakin wannan son zuciya a ce a cikin wata biyu ka yi asarar miliyan ɗaya ko rabin kudin ba za'a baka ba." "Ka siye ko 700k ne mana." "Ba wanda zai siye wayar nan a haka don sai a daɗe ba'a samu mai siye ba." Sanin ba ta da wani zaɓi kuka tana bukatar kuɗi don ba ta da shi ya saka ta ce. "Kawo kuɗin." "Me nape ya yi saurin cewa. "Hajjya kada ki siyar da wayar nan ki koma da abun ki gida ki yi hakuri." Murmushin takaici ta yi tana cewa. "Dole ne na siyar da wayar ba na da wani zaɓi ne." "To ki jira wasu su zo sai ki yi ma su tallah." "Ko sun zo farashi daya muke siyan kaya." "Gaskiya ba ku da imani." "Kar ka faɗa mani maganar banza akan sana'a ta, daga ganin ka ma kai karere ne.Hajiya iya dubu ɗari biyar idan ba ki siyar ba sai Anjima." "Kawo kuɗin." Ta fada kamar za ta yi kuka. Ta cire sim da memory card, sannan ta sauke email ɗin ta dake kan wayar, ta goge komai sannan ta bashi wayar?" "Cash zan baki ko na yi na ki transfer?" "Cash za ka bani." Ya ba ta bandir na dubu ɗari guda biyar ta karba ta zuba a handbag suka fice da mai nape Bayan ya tayar da nape ya ce " ina za mu je." "Kasuwa za ka kai ni?" "Wace kasuwa?" "In da zan samu kayan ɗaki ma su sauƙin kuɗi. Kamar katifa, pillow da sanin gado leader carpet da labulaye sai sauran kayan aikin da ba'a rasa ba." "Okay Hajiya Allah ya kai mu lafiya." Da haka ya dauki hanyar da zai kai Ma'eesha ta yi siyayya. _Nadrah_ Tafiya take yi kamar mai jin tsoron ƙasa, don tsakanin ya ba ta wuyar tafiya, bugu da kari ga kayan jikinta da ta kasa saukewa a cikinsa. Abun ya hadu ma ta biyu ga kaya ga takalma, duk sun takura ma ta. Hannayen ta biyu ta saka tana kare ƙirjinta wanda rigar aka yi shi da gidan breast. Karon farko kenan a rayuwarta da za ta fita babu hijabi ga shi kayan ba yadda take so ba. Ta cikin mirror Fahad ya kalli yadda take kare ƙirjinta tana tafiya kamar za ta faɗi, gajeren tsuki ya ja yana mai jin takaicin yanayin yadda take yi don za ta iya kunyata shi a gaban jama'a, ga manyan baƙin da abokansa da suke masa kallon wayayye mutum mai ji da kai da aji. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣7️⃣ Ta cikin mirror Fahad ya kalli yadda take kare ƙirjinta tana tafiya kamar za ta faɗi, gajeren tsuki ya ja yana mai jin takaicin yanayin yadda take yi, don za ta iya kunyata yi don za ta iya kunyata shi a gaban jama'a, ga manyan baƙin da abokansa da suke masa kallon wayayye mutum mai ji da kai da aji. Dauke idanunsa ya yi ransa ya na ɓaci, a hankali take tafiya har ta karaso wajen motar. Da sauri Direban ya fito ya buɗe mata murfin bayan motar ganin za ta buɗe. Kallonta ta yi ya gaishe ta da cewa. "Ina wuni Madam?" "Kai kawai ta jinjina ma sa ba tare da ta iya amsa wa ba." Shiga bayan motar ta yi bakinta ɗauke da sallama. "Assalamu alaikum." Idanunsa na kan wayarsa bai kalle ta ba ya amsa sallamar ciki-ciki wanda ita kanta ba ta ji ya amsa ba shi kadai kawai ya ji kayansa. Bayan ta zauna ne direban ya rufe murfin motar, ba abinda ke tashi a motar sai sanyin A.C da ƙamshin turarensa. Duk da cewar tana cikin ɓacin rai da takaici amma haka.n bai hana ta ta gaishe shi ba." "Ya Fahad ina wuni?" Kamar ba zai amsa ba har ta fidda ran zai amsa sai ta ji ya amsa da. "Kina lafiya?" Ta amsa da Alhamdulillah kanta a sunkuye. Direban ya ja motar suka bar gidan. Sun ɗan fara tafiya ta kalle shi ta ce. "Ya Fahad?" Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. "Na ga kamar kana cikin damuwa ko?" Bai ce ma ta komai ba sai dai ya ɗauka yadda ya saki ransa ba wanda zai gane yana cikin damuwa, tun da ita da yake ma ta kallon ba ta da wayau ta iya karantar yanayinsa ashe tana da wayau. Kuma kowa zai iya karantar yanayinsa. Kallon kayan dake jikinta ya yi wanda ya siya wa Sidra ne last week tare, hatta sarƙar gold ɗin da su warwaro da ɗan kunnen duka seti ne ya siya ma ta. Bai ce ma ta komai ba kuma kamar bai ji tambayar da ta yi ma sa ba. Sun yi nisa da tafiyar ne duk ta damu da kayan da za ta shiga cikin jama'a da shi, ta kalli jikinta ta fara maganar zuci wanda ya fito fili ɗin ba ta yi don ya ji ba. 'Mtswww, wannan wane irin iskanci ne ba in da zan fita da kayan nan na shiga cikin jama'a, don ni ba ƴar iska ba ce. Haba sai ka ce ba ƴar musulma ba Aunty Sidra ta zaɓo kayan nan a matsayin kayan da za ta shiga jama'a bayan an ɗaura aure tana matar aure? Kodayake ba laifn ta kaɗai ba ne har da laifin shi Mijin nata ta ya ya Yaya Fahad zai yarda ya siye wannan kayan matarsa ta saka sai ka ce wanda baya da kishin matarsa, zai so a kalli matarsa a haka cikin wanann shigar, kalli rigar ko hannun arziki babu ga ta an yi gaban rigar kamar na bra duk siffar kirjin mace a bayyane yake. Wallahi da na san har da wannan tsinannen Dinner party za'a ce wai na je a madadinta da islamiyya na wuce. Na samu lada da wannan bidi'ar da zan je. Ga Aunty Sidra har yanzu ba ta dawo daga gyaran jikin ba ta je da daɗe duk ita ta jawo Mani wannan abun. Idan Allah ya kai ni ranar aurena da Ya Sayyadina walima kawai za mu yi ayi lectures kan aure mallamai su yi wa'azi amma ba wannan bidi'ar. Ko ya Sayyadina idan ya ganni haka sai ransa ya ɓaci.' Fahad idanunsa na kan wayarsa ne amma duk maganar da take yi a kunnensa, ita ba ta san a bayyane ta yi maganar ba. Kuma yanzu ne ya tabbatar da cewa iyayenta ba su faɗa ma ta cewa an ɗaura auren da ita ba, to amma ai da sun sanar da ita musamman da suka san akwai saurayin da take so wato Ya Sayyadi. Shi kansa Fahad ya san Ya Sayyadi kuma Ya Sayyadi ya san shi shi ma. Saboda sau tari idan ya zo wajen Sidra ya kan ga Ya Sayyadi tare da Nadra kullum cikin jallabiya yake da hula taɓa ni ka ji hadisi yana zuwa ne da tsohon babur nasa kullun. Har Sidra ta yi ta faɗa wai me na sama zai ci ballantana ya ba na ƙasa Nadra ta rasa wa za ta so sai wannan abar da ba lallai ya iya ɗaukar ɗawainiyar ta ba, in ban da kuɗin Laraba da ke kai wa islamiyya me yake da shi. Ta tsayar da mai kuɗi ta aura cikin ma su son ta sai wannan ya Sayyadin mai gemu kamar na bunsuru, har wata rana Fahad ya yi Sidra faɗar abun da take yi wa Ya Sayyidi. Yana tsaka da tunanin baya wayar ta fara ringing, sai dai har ta katse bai ɗaga ba. Aka sake kiran ɗayar wayar nan ma bai ɗaga ba. Ta na kallonsa ta gefen ido a zuciyarta ta ce. "Sun haɗu sun dace, don ita ma Sidra haka za'a dinga kiran wayarta ba za ta ɗaga ba sai ta ga dama. Tana ganin an kawo wajen gabanta ya tsananta faɗuwa. Ita ma za ta iya fita a haka ba. Musamman da ta hangi cikar da aka yi, don ma ba ta shiga ciki ba. Kowa white and black ne maza da mata. Motar na tsaya wa sai ga mutane sun nufo motar ma su ɗaukar photo da ma su ɗaukar video wasu da wayoyinsu wasu da Camera 📷. An tsaya ana jiran fitowar Amarya da ango. _Ma'eesha_ Mai keke napep ɗin bai dire ta a ko ina ba sai gaban wasu shaguna dake bakin titi. "Hajiya yanzu ba'a fito a kasuwa ba, don sai zuwa karfe tara ko goma idan kina son wasu kayan da kike so za ki iya samun su a nan, idan kin kai su gidan sai mu dawo na kai ki kasuwa." "Okay." Ta faɗa tana fitowa shi ma ya kashe keken ya zare key sannan ya bi bayanta. "Shagon katifa ne da su pilows ake siyarwa, ta siye madaidaicin katifa ba mai girma ba, ta siye pillow guda biyu ta biya kuɗin, ma keke napep ɗin ya ɗaure katifar da pillow ya ɗaura a keke nape ɗin, sannan ta shiga shagon dake kusa da wanda ta siye katifa. Ta siye zanin gado kala biyu da labule guda biyu, sannan ta siye leader carpet, saboda ta san shi ne mai sauƙin kuɗi. Za su wuce sai ta ga shagon dake kusa da in da ta yi siyayya. Ana siyar da kayan kitchen. "Ka ga bari na shiga can na duba abind da zan buƙata." "To Hajiya." Daga nan ta nufi cikin shagon don ta ga kayan da take buƙata. Tukunya guda biyu ta cire gefe mai ɗan girma da karami, sai ta siye tukunyar suya sannan ta siye set ɗin food flask mai guda uku a kwali ta siye cokular cin abinci guda shida na cin taliya wato fork guda uku, ta siye plate na cin abinci ma su fadi guda huɗu ma su zurfi ƙanana guda hudu da service spoon, sai babban tire sai kofin shan ruwa huɗu na shan shayi ko kunu guda huɗu. Ta siye rariya da cikakin girki Lissafi aka yi ma ta ta biya kuɗin sannan mai napep ɗin ya ɗauki kayan da ta siyo ya saka a bayan keken. Sannan ta tuna da robar zuba ruwa wato duram ɗin roba ta siye da bokitin roba guda biyu da baho madaidaita biyu da robar ɗiban ruwa. Ta gama abinda za ta siya ta yaya wannan bangaren. Sannan ta shiga ganin keken ya ya cika da kaya yawa. "Mallam mu je ka kai ni gidan idan na ajiye sauran kayan sai mu dawo ka kai ni in da zan siye kayan abinci sai ka mai da ni gida ." "To Hajiya Allah ya kai mu lafiya." Da Amin ta amsa , daƙyar da ita gane layin, don dama dai ta san sunan unguwar, amma layin ne ya ba ta wahalar gane wa sakamakon lungu ya yi yawa a unguwar. A ƙofar gidan ya sauke ya tsaya sannan ya fito daga ciki yana fito da kayan. Kasancewar ba kaya ma su nauyi ba ne, ya saka yana ajiye wa tana ɗauka tana kai wa cikin gidan. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin gida. Daga cikin ɗakin ta ji muryarsa ya amsa ma ta da "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Ya fito rike da sandarsa ta jagora, sai dai ya canza kayan jikinsa ba wanda ta bar shi da shi ba ne, wannan farare ne su ma yadi ne ma su sauƙin kuɗi wanda aka cewa Yi shirunka maraya. "Ma'eesha kin dawo ne?" "Eh." Ta fada tana ajiye katifar wanda aka ɗaure su da filo a hannunta a saman barandar. Komawa ta yi ta ɗako sauran kayan, sau uku tana fita tana kwaso kayan kafin ta gama ta kalle shi ta ga ya yi tsaye yana rike da sandar jagoransa. Kansa a ƙasa kamar mai karantar wani abu. "Ban gama siyayyar da zan yi ba, mai napep na jira na a waje, zan koma na karasa sai na dawo na nema ma na abun da za mu yi breakfast. Don yanzu karfe goma ake nema, ni dama ina kai karfe goma sha ɗaya ko sha biyu ban yi breakfast ba, don haka kai nake tunani." Murmushi mai ciwo ya yi tare da cewa. "Ma'eesha ke nake ji da sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki a ciki, ni kada ka damu da ni, wata rana sau ɗaya nake cin abinci a rana. Ko ina jin yunwa ba na da mai bani abinci, sau ranar da Allah ya saka naje gidanku idan mahaifiyarki ta bani nake ci, duk da ta ce na dinga zuwa kullum ina cin abinci ba na iya wa, sai dai duk sati nake kai mata ziyarar juma'a wato duk ranar juma'a, ranar ne nake ci na ƙoshi , wata rana ai ke take saka wa ki zuba Mani wanda zan tafi gida da shi, Allah ya jiƙanta da rahama ya sa aljanna ce makomarta, halinta nagari ya bi ta." Kuka ne ya suɓuce wa Ma'eesha tuna mahaifiyar ta da Fahad ya yi ma ta, ji take ina ma tana da dangin mahaifiya da can za ta tafi ko ta samu sassauci abinda yake ranta. Ita kanta ba ta san yaushe ne za ta daina kukan mijin marainiya ba, amma tana ji a ƙasan ranta wata rana za ta yi dariya. Sallamar mai daidaita sahun dake jiranta ya sa ta goge hawayenta da sauri ta fice daga gidan ba tare da ta sake magana ba. "Ka yi hakuri na bar ka kana jira na ko?" "Ba matsala." Ya fada yana yi wa keken burki suka bar kofar gidan. Ganin tana ƙwalla ta cikin mirror yake kallonta ya ce. "Hajiya lafiya?" Sai sa lokacin ta lauba fuskarta ta ji hawaye ke bin fuskarsta Da sauri ya goge. "Ba komai Mallam." "Anya kuwa ba komai?" "Eh." "To na ga kina kuka ne duk na damu." Murmushin takaici ta yi tana cewa. "Kawai na tuna da mahaifiyata ce." "Allah sarki ki Allah ya jikanta da rahama." "Amin na gode." "Rayuwa kenan Allah ya ba mu guzurin cin ma su." "Amin ya Allah." Ta fada tana kau da kai gefe tana kallon titi. Still hawaye ne dai ke yi ma ta zarya wanda duk yadda taso dakatar da hawayen ta kasa hakan . "Yana kallonta ta madubi ya ce. "Aunty na ki yi hakuri Allah ya jikanta." Ai kamar ya ce ta ci gaba dai ji ta yi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya wanda tun daga kasar zuciyarta take jin ƙuna da raɗaɗin rasa mahaifiyarta, ga wani sabuwar rayuwa da ta tsinci kanta a ciki mai cike da ƙalubale, haƙika mutuwar mahaifiyarta ya durƙusar da duk wani motsi nata, ya gurguntar da tunanin gobenta. Wannan sabuwar rayuwa da ta shiga tamkar hanya ne mai cike da kwazazzaba da ƙayoyi. Jin yadda take kuka kamar za ta shiɗe ne ya saka hankalinsa ya tashi ya yi parking gefen hanya . *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣8️⃣ Ai kamar ya ce ta ci gaba sai ji ya yi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya wanda tun daga kasar zuciyarta take jin ƙuna da raɗaɗin rasa mahaifiyarta. Ga wani sabuwar rayuwa da ta tsinci kanta a ciki mai cike da ƙalubale, haƙika mutuwar mahaifiyarta ya durƙusar da duk wani motsi nata, ya gurguntar da tunanin gobenta. Wannan sabuwar rayuwa da ta shiga tamkar hanya ne mai cike da kwazazzaba da ƙayoyi. Jin yadda take kuka Kamar za ta shiɗe ne ya saka hankalinsa ya tashi ya yi parking a gefen hanya. Ya juya ya kalle ta sai ya ga ta jaɗa kanta guiwarta, wato ta ɗora ƙafarta tana cigaba da kuka. "Hajiya ki yi hakuri don Allah addu'ar ki take buƙata ba kuka ba. Domin wannan kukan ba zai amfane ta ba." Ɗago kanta ta yi ta goge idanunta sa suka yi jajir sannan ta ce. "Mu tafi." Kunna nape ɗin ya yi sannan ya fara tuƙi a hankali don shi ma jikinsa ya yi sanyi sosai, yana son ya tambaye ya amma yana tsoeon amsar da za ta ba shi. Musamman da ya ga wayar da ta siyar ya san wace irin waya ce. Sannan ga shi yanzu bayan ta siyar da wayar irin kayan da take siye, kuma yadda ya ga take yi kamar ita ce za ta yi amfani da kayan, ga gidan da ta kai kayan sam gidan bai dace da ita ba. Har suka ƙarasa kasuwa ba wanda ta sake yin magana s cikinsu. Bayan ya yi parking a In da ya dace ne ya zauna ciki. Ta kalle shi ta ce. "Mallam ko za ku je ka taimaka ma ni ban taɓa shigowa kasuwar ba, don ban san ta ina zan bi da ake siyar da kayan abinci kamar su shinkafa da sauransu." "Okay mu je na nuna ma ki na ha kamar ke baƙuwa ce a garin." Ya yi maganar ne don ya tabbatar da abun da ke ransa, ita kuma ba ta ce ma sa komai ba. Har suka ƙarasa wani layi. "Yauwa Hajiya ga wani shagon za ki iya samun komai a ciki." "Toh na gode Allah ya saka da alkhairi." Da Amin ya amsa sannan suka shiga cikin shagon da sallama a bakinsu. "Assalamu alaikum " Wa'alaiki Salam warahmatullah." Cewar wani matashin saurayi dake kusa da su. Don shagon babban shago ne mutane biyar ke sigar da kaya a ciki har da Alhaji me shagon yana zaune kan kujera yana lissafa babban calculator. Matashin saurayin ya ce . "Me da me za'a kawo?" Ya yi maganar yana ajiye ma ta plastic chairs ta zauna tana ma sa godiya. Bayan ta zauna ta ƙare wa shagon kallo dake da masu siyen kaya a ƙalla za su kai mutane goma. "Ka bani karamin buhun shinkafa, da katon ɗin taliya da makarani kowane guda ɗaya." Ta yi maganar tana nuna ma sa kalar wanda take so. Ya dauko shi kafar da taliyar da macaroni ya ajiye ma ta . "Ka kawo ma Ni buhun semolina da kuma cus-cus." Ta ce ya kawo ma ta wani madaidaicin galan manja da man gyaɗa, sai wake mudu biyar. Sannan ta saka shi ya kawo ma ta ledar Maggi know da kuma star, sai gishiri da su kayan ƙamshi . Sannan ta ce a kawo kwalin indomie. Total aka yi ma ta ta biya sannan mai napep ɗin ya ɗauki kayan tana bin sa a baya rike da wanda za wanda za ta iya ɗauka. Suka nufi wajen keke napep ɗin. Bayan sun saka kayan a baya ne ya kalle ta ya ce "Ki zauna a ciki bari na kwaso sauran kayan." Ba musu ta shiga ta zauna ya koma ya kwaso sauran kayan , sau biyu yana ki komawa. A na karshe sai ga shi ya dawo tare da Alhajin nan mai shagon, wanda da dukkan alamu shi ne mamallakin wannan shago. Washe ba ki ya yi ma ta yana cewa. "Ƴan mata ya za ki tafi bayan kin sace ma ni zuciya." Kallo ɗaya ta yi ma sa ta dauke kai. Murmushi ya yi tare da cewa. "Da alama wannan ƴan matan akwai jin kai, to a jiƙaina ko lambar waya a bani ba " Kallon mai napep ɗin ta yi ta ce. "Mallam mu tafi ma na." "Don girman Allah ki saurare ni." "Matar aure ce ni." Ta fada a takaice. "Subhanallah don Allah ki yi hakuri ban sani ba." Daidai lokacin mai napep ya ja suka bar wajen. "Yauwa na mance ina buƙatar Gas ƙarami kamar 3kg." "To Hajiya zan kai ki in da za ki samu, ko za ki hada da murhun gawayi saboda yau da gobe wata rana Gas zai kare ba za ki iya fita ba sai ki zuba gawayi ki cigaba." Ita dai ba ta san yadda za ta yi amfani da shi ba, amma ta amsa mai da to. Ya kai ta ta siye Gas, a wajen da ta siye aka cika ma ta shi da Gas.sannan ya kai ta inda ta siye murhun gawayi da kuma wani ɗan ƙaramin buhu da aka zuba gawayi, ta siye ya ɗauka ya saka ma ta suka bar wajen. "Mallam ina zan samu kayan miya?" Daga cikin keken ya nuna ma ta . Ya zauna yana jiranta. Ba jimawa ta dawo da manyan ledoji guda biyu cike da kayan miya, sannan ta kalle shi ta ce. "Bari na siye dankalin turawa a can ." Ta juya ta siye dankalin turawa da ƙwai kiret daya sannan ta dawo, ya ja napep suka bar wajen." "Yanzu ina za mu je?" Gida Mallam za ka kai ni " _Nadra_ Ganin yadda ka zagaye motar da take ciki sannan ga ma su ɗaukar photo da video sun zagaye su ne ya saka ta kasa yunƙurin fitowa . Sai sake noƙewa take yi ba ta ma da niyyar fitowa. Direbansa ne ya zagayo ya bude ma sa bayan motar, a hankali ya ziro ƙafarsa ɗaya waje, sai da ya ɗauki seconds kafin ya dake ziro da ɗaya kafar waje. Sannan ya fito cikin takunsa na ƙasaita fuskarsa ba yabo ba fallasa. Daidai lokacin Aunty Rahama ta karaso wajen tana Murmushi. Da ido ta ma sa alamar ya riko hannunta su karasa wajan a tare. Zagayawa ya yi gefen da take ya yi ƙasa da kansa saitin fuskarta ya yi magana ta yadda ita kadai za ta ji. "Ko sai an fito da ke ne, ka da ku kuskura ko da wasa ki yi mani gidadanci anan, na san ki kamar bagidajiya haka kike, ina mamakin yadda zama da Sidra bai saka kin waye ba. Nan cikin jama'a ne akwai manyan mutane nan da suka halarci wannan taron har daga ƙasar waje wasu suke, ka da ki kunyata ni, be careful." "Ƙwalla ce ta cika ma ta idanu." "Kada ki mani kuka anan." Ya faɗa yana ciro hankaci cikin aljihun Suit ɗin sa ya goge ma ta ƙwallar. Tafi wasu suka hau yi don an ɗauka kalaman soyayya yake yi ma ta musamman da fuskarsa ke daf da tata. Tana fitowa daga cikin motar aka fara watsa ma su wani fure mai ƙamshi. "Ma sha Allah." Aunty Rahama ta fada lokacin da ta yi tozali za Nadra. Kasa ɗaga ƙafa Nadra ta yi sakamakon hangen jama'a da suke a cike a wajen, ga wasu na ɗaukarta video da photo. Ganin ta coge tana tunani ya saka ya sakala hannunsa cikin nata. A bazata ta ji lalluasan hannunsa cikin nata hannun. "A'uzubillahi minash a shaiɗani rajim." Ta furta tana kallon sa a razane, shi kam bai kalle ta ba yana kallon tarin jama'ar da bai yi zaton gani ba. Koƙarin kwace hannunta take yi ta kasa. Saboda riƙon da ya yi ma ta ba na wasa ba. Ba yadda ta iya haka ta dinga binsa kamar Raƙumi da akala. Sai dai kamar za ta yi kuka cike da shagwaɓa take cewa. "Yaa Fahad please ka sakar ma ni hannu ba kyau haramun ne namiji ya taɓa wacce ba maharramarsa ba, ba Aunty Sidra ba ce ni ce fa Nadra haramun ne." Bai kalle ta ba ya yi kamar baya jin ta. Ana ta watsa ma su fure me ƙamshi ana ma su feshi. Jin yadda idanun mutane ke yawo a likita ya saka ta fara kokare kare jikinka ta hanyar ɗan shigewa jikinsa ta yadda ba za'a ga ƙirjinta da take ɓoye wa ba, wanda bai tsaya kusa da su ba zai ɗauka ta haɗa jikinsa da nata ne, amma a zahiri sun dai yi kusanci amma jikinsu bai haɗu ba, sai dai har lokacin yana rike da hannunta cikin nasa. Kuma yana tafiya a hankali ganin yadda take tafiya ita ka sai yake bin ta a haka. MC na bayani yana sanar da idowar amarya da ango ga wani sanyayyen kiɗa na tashi a hankali. Har suka ƙarasa wajen zamansu suka zauna , ana ya saukar su photo. Kowa dake wajan kayan jikinsa White and black ne maza da ma ta. Taro ya kai taro jama'a da ba'ayi zato ba sun zo. Waƙar auren na tashi sai dai abin da ya ba Fahad mamaki ya san dai waƙar auren da sunan Sidra aka rera, amma yanzu sai ya ji sunan Nadra ne ba na Sidra ba, duk da wakar ɗaya ce sunan kawai aka canza, bayan shi ba abinda aka canza daga sunan iyaye da dangi duka suna nan. Fahad ya san wannan ba aikin kowa ba ne sai Aunty Rahama. Ita ce za ta saka ayi wannan a kankanin lokaci. Kamar yadda ka tsara haka aka yi aka kira abokin ango ya zo ya bayar da tarihin rayuwar ango da halayyarsa. Daga nan aka bukaci ƙawar Amarya ta fito ta ba da tarihin rayuwar Amarya. A nan ne Nadra ta daga kai saboda ta san saboda ta san ba wata ƙawar da take da ita da ya wuce A'isha Humaira kuma ba ta zo wajan nan ba. Dama Khadijah ƙawar Sidra ce za ta bayar da labarin Sidra. Yanzu kuma tun da an fasa auren da Nadra ai ba zai yiwu ƙawar Sidra ta zo ba. Ga mamakinta sai ta ga Khadijah ƙawar Sidra ta fito ta zo ta tsaya. Haɗa idanu suka yi ta sakar ma ta murmushi. Sai dai Nadra ta kawar da mamaki ne lokacin da ta tuna cewa ai labarin Amarya za ta bayar amarya kuma Sidra ce, dole za ta bayar da labarin Sidra, dama duk cikin ƙawayen Sidra ba wacce hankalin ta ya kwanta kamar Khadijah. Don tana ba ta shawara na kwarai tare da fada ma ta gaskiya. Shi ya sa ba wuya sun yi faɗa ita da Sidra saboda fadar gaskiyarta. Cike da mamaki Nadra take kallon Khadijah ƙawar Sidra, jin ta ta ambaci sunan ta ba sunan Aunty Sidra ba kila tarihin rayuwar Nadra take bayar wa . Sai dai ba ta ce komai ba kuma ba ta kawo komai a ranta ba. Aka buƙaci amarya da ango su fito, nan fa Nadra ta noƙe ta ƙi fitowa, ganin take-taken ta ya saka ya riƙo hannunta, don idan ba haka ya yi ma ta ba ya san ba tashi za ta yi ba. Janyo ta ya yi ya rike hannunsa cikin nata har suka fito cikin tsakiyar taron. Ana ma su liƙin kuɗi ita da ƙokarin kare ƙirjinta take yi da hannayenta guda biyu. Don abinda ya sa ta kara tsanar kayan saboda ƙirjinta da aka yi kamar na bra a tsuke kuma ga baby hannun arziki a jiki. Ganin za ta rungume hannaye kamar mai jin sanyi ya saka ya yi saurin rike hannun nata yana rawa ana watsa ma su kuɗaɗe ƴan dubu-dubu har da ɗari biyar-biyar. Mama da su Aunty Rahama da sauran danginsa sai liƙi ake yi ma sa. Farin ciki ya lulluɓe Mama sai liƙi kawai take yi wa surikar tata. Don Nadra ta ji ta shiga ranta haka ma Aunty Rahama sai ɓarin kuɗi take yi, da sauran dangin Fahad. Bayan dangin ango sun koma wajen zamansu sai ga dangin Amarya sun fito su ma. Su Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna da saran dangin Abba da ƙawayen Umma. Bayan sun ma sun yi ma su nasu liƙin sai abokan ango suka fito. Nan fa Sidra ta kasa nutsuwa ganin samari matasa ne irin Fahad Ke ta yi ma su liƙi. Ga Fahad ya ki sakin hannuwanta yadda yake rawa da ita ne ya saka ita ma idan ka kalle ta za ka yi zaton rawar take yi . Ga takalmin ta gaji da shi kasancewar ita ba ma'abociya saka dogon takalmi ba ne, baya ta yi kamar za ta fadi sai ya yi saurin riƙo ƙugunta ya dawo da ita ta fado jikinsa. Ba ta san san da ta kwantar da kai a ƙirjinsa ba saboda tsoron faɗuwar da za ta yi da dogon takalmin da ke ƙafarta. Ta yi lamo a ƙirjinsa ta rintse idanunta tana jin yadda gaban ta ke faduwa. Dariya ta ba shi yadda take da tsoro haka har ya yi murmushi yana kallon fuskanrta nan aka dinga tafi ana ɗaukarsu photo wanda hakan ya sa ta dawo cikin cikin nutsuwarta, da sauri ta raba jikinta da nasa. Daga nan kuma aka fara daukar photo amarya da ango da sauran jama'a, dangi da abokan arziki. Baga gama ba gajiya ya saka Nadra barin wajen ta nufi wajen zamanta ta zauna. Daga nan kowa ya dinga zuwa yana dibar kalar abinci da abun sha da yake so. *Abuja* Satin Muryar Sidra ke tashi a cikin madaidaicin falon tana tsaye rike da kugu cike da masifa take kallon ƙawar tata Sady baby. "Amma wannan ma su raunin hankali ne, wasa da hankalinmu ya yi ko me?" "Ki hanyar da hankalinki ƙawata ba..." "Dalla rufe ma ni baki wani kwantar da hankali zan yi, bayan na ga alamar mafarkina ba zai zama gaskiya ba, sanin kanki ne cewa burina na samu ɗaukaka na yi suna fiye da yadda waccen sakaryar da ta wulakanta ni saboda ta yi samu suna. Burina na rama wanda a dalilin haka na gudu ranar aurena da masoyina na bar kowa nawa don na samu cikar burina." "Wallahi ya ce wai ai tun shekaran jiya aka yi ba mu zo akan lokaci ba bar an gama ta tacewa sun zaɓi wata, ya kuma tabbatar ma ni da cewa da a ce kin zo da ke za'a zaɓa saboda duk kin fi su haɗuwa kuma ya san za ki iya, lokaci daya za ka ki yi suna don babban kamfanin ne fa suke ɗaukar ƴan tallan." "Aikin baza da wofi wallahi ni kin cuce ni kin sa na bar aurena na zo nan, da yanzu an ɗaura Mani aure da Fahad, dole na koma Kaduna a yammacin nan na roki iyayena gafara gobe a daura Mani aure da masoyina ba zan yi biyu babu ba." "Biyu babu kam ai kin yi shi, ba ki ga tsunsu ba ki ga tarko kin ɓarar da damarki." "Akan uban me kike magana ke kuma?" Ta jiy maganar a fusace. Mika ma ta wayar ta yi tana cewa "Ga shi ki kalli yadda wannan bikin da Khadijah ta tura Mani." A wulaƙance Sidra ke kallonta kafin ta karbi wayar ta fara dubawa. Photon farko shi ne in da ta ga Nadra kwance a kirjin Fahad ta rungume shi, yana kallon fuskarsa yana murmushi. Sannan ta kalli in da suke tafiya yana rike da hannunta tana shigewa jikinsa sai na ukun in da suke rawa Ga mahaifiyar Fahad da Aunty Rahama na ma su liƙi tana dariya. Sakin wayar ta yi tana dafe kanta da ta ji yana sara ma ta ga wani duhu da take gani. Tana girgiza kai tana cewa. "No no no ba impossible ta ya Abba da Umma za su aiki ta haka, ko Fahad ba zai yarda da wannan abun ba, kawai editing ne aka haɗa amma Fahad nawa ne ni kaɗai ba babu macen da ta isa ta raɓe shi ban ga bayanta ba." Wata budurwa ta karaso ta ajiye masu faranti da Fruits da wuƙa. "Magana ta gaskiya dole ki hakura ya zama mijin ƙanwarki." Wuƙar dake hannunta ta dauka tana nuna wacce ta yi maganar tana cewa "Idan kika sake fadar haka sai na kashe ki." Ganin ba ta da hankali ya saka ta ce. "Allah huci zuciyarki na bar ki lafiya." Wuƙar dake hannunsa ta fara yankar hannunta tana ta surutai cikin ficewar hayyaci. Yadda jini ke zuba ya sa hankalin Sady baby tashi ta ce . "Meye haka Sidra za ki illata kanki fa, ba ki ganin yadda jini ke fita daga jikinki?" "Wallahi ba zan iya rayuwa ba Fahad ba ba wacce za ta raba ni da shi ki ce karya ne bai auri ƙanwa..." Jiri ne ta ji yana ɗibarta ta zube wajen akan kujera. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page0️⃣9️⃣ Jiri ta ji yana ɗibarta ta zube a wajen akan kujera. Sady baby ta yo kanta tana kiran sunanta, sai a lokacin ta fahimci ashe suma ta yi. Ganin ba kowa a falon ya duk sun watse ta nufa fridge da kanta. Ruwa ga ɗauko mai sanyi ta yayyafa ma ta. Wani ajiyar zuciya ta ja kafin ta fashe da kuka. Idanunta a rufe take cewa. "Sady ina fatan ba gaskiya ba ne ko? Na san yadda Fahad Majidaɗi ke so na ba zai iya auren wata ba, na taho nan da zumar idan ba na nan za su ɗaga bikin zuwa lokacin da zan dawo sai a ɗaura ma ni aure da shi ko?" Cikin kwantar ma ta da hantdady ta ce. "Ba komai wannan fa ƙsrya ne ba gaskiya ba ne, ki daina saka damuwa a ranki ke ma ki. San wannan zamani da muke ciki fuska kawai za'ayi amfani da shi aje a haɗa kamar a tare suka dauki photo. Ki cire s ranki ke fa da bakin ki kika ce Fahad na son ki zai hakura har sai kin dawo kafin ayi bikin auren naku." Ba dai ta gamsu ba haka ta dai yi shiru don kanta na matsa wani irin ciwo ne mai tsanani. "Bari na kira wata nurse dake kusa da mu, ta zo ta dubs wannan raunin da lima ji wa kanki da wuƙa. Tana fadar haka ta fice daga falon zuwa kiran nurse. Sidra ta dafe kanta dake ma ta ciwo sosai sannan ta kwantar da kai tana lumshe ido zuciyarta cike da tunanin Fahad, tana tuna ƙamshinsa mai saka ta nutsuwa da shauƙi. _Nadra_ Tana zaune a mazauminta Fahad na gefenta yayin da mutane ke zagayowa su tsaya bayansu ana ɗaukarsu photo. Yayin da mafi yawanci suna zuwa su ɗebi kalar abincin da suke son ci da kalar ruwan da suke so sha. Ita dai Nadra ga ta nan ne kamar me jin sanyi . Har aka gama ciye-xiye da lashe-lashe. Sannan aka zo wajan yanka cake suka ta so don yanka xaket, a nan ne ya sake ganin aminiyar Sidra wato Khadijah. Ya yi mamakin yadda ta fito take fadar halayyar Nadra bayan ita kawa ce ga Sidra. To me ta zo yi? Wani makirin murmushi ya yi saboda ya san dole za ta tura wa Sidra abinda ke faruwa wajen wannan bikin, kuma yana da yakinin cewa yadda Sidra ke mahaukacin son sa dole za ta ji zafi a ranta idan ta ji ya aure ƙanwarta. Duk da ba ya da tabbacin zaman nasa da Nadra. Don haka ya kalli Khadijah dake ma su video tabbas Sidra za ta gani zai aikata abun da idan Sidra ta gani zata ɗanɗani ɓacin rai kwatankwacin yadda ta saka ya ji shi ma. Zai tabbatar ma ta kamar bai ji haushin abinda ta aikata ba Hannunsa ya ɗaura saman na Nadra tana kokarin janye hannunsa bai ba ta damar hakan ba. Ya rike hannunta suka fara yanka cake. Ƙasa-ƙasa da murya ta fara magana tana cewa . "Yaya Fahad ka daina taɓa jikina ba na so ni ba Sidra ba ce, haramun ne Please ka daina." Kamai bai ji ta ba bayan sun yanka cake ɗin aka dinga yi ma su tafi ana ɗaukarsu photo. Sanin ba ba za ta yi abinda yake so a wajen ba, da kuma kokarin ɓata ran Sidra don ya san za ta gani.. Suna yankawa ya riƙo hannunta dake rike da cake, zuwa bakinsa ya kai ta ciyar da shi ana ma su photo, sauran na bakinsa sai ya tallabo gefen fuskarta da hannayensa biyu, sauran ba bakinsa ya haɗe bakinsa da nata wuri guda na cikin bakinsa ya tura ma ta a bakinta, take wajen ya ɗauki sowa da ihu ana tafi. Nadra mutuwar tsaye ta yi saboda mamaki da al'ahabin Fahad Majidaɗi. Wai yau ita ce wani namiji da ba mijinta ba ya haɗe bakinsa da na ta waje ɗaya yana tura ma ta abinda ke cikin bakinsa a tsakiyar jama'a ko kunya baya ji a gaban kowa zai iya aikata hakan har iyayen sa na wajen. Lallai yau ta kara tabbatar Fahad mara kunya ne lamba ɗaya. Barin wajen ta yi ta koma mazaunin ta. Kanta a sunkuye tana goge ƙwalla. Ana kiran sallar magrib aka tashi daga taron, Amarya da ango suka nufi wajan motarsu. Kunyar abinda Fahad ya ma ta ya saka ta kasa daga kai ta kalli kowa. Direbansa ya yi saurin bude ma ta murfin motar ta shiga ta zauna. Daga nan ne ta fashe da kuka shi kuma yana can yana sallama da abokansa. Har ya dawo ya shiga motar tana kuka. Kallonta ya yi cike da takaici ya ce. "Ke me aka yi ma ki za ki saka mutane gaba kina kuka?" "Kan me za ka aikata ma ni haka?" Ƙyasta yatsunsa biyu ya yi ya ba da wani sauti wanda hakan ya saka diraban ya fita da sauri ya ba su waje, don ya gane uban gidan nasa na bukatar sirri ne." "Kin ɗauka abun da na yi ma ki da son raina na yi ma ki ne, in ban da ƙaddara da ba ta riga fata ke kin isa ma na rike hannunki ne? Ba ki da wannan ajin da zan iya taɓa jikinki. Dole ne ta saka na aikata hakanna farko saboda biyayyar iyaye, na biyu don na ƙuntata. Amma ba don haka ba ko kallo ma kin ishe ni ne, ma ta masu class da waye wa ma ban kalle su b ballantana ke da kike..." Kuka ta fashe da shi tana cewa. "Ya isa ya ishe ni haka, ba sai ka ci mun mutunci ba, na ji ban ai matsayin..." Tsawar da ya daka ma ta ne ya saka ta haɗiye sauran maganar, ke har kin isa ki dakatar da ni ina magana, last warning da zan Maki shi ne kada ki sake daga Mani hannu idan kina mun magana idan ba haka ba sai na ɓalla hannunki, don ma kin samu na taɓa jikinki har kike ma ni wani zancen banza dole ce ni ma ki sani ba don ƙaddara ba ba ki kai matsayin ba kuma ba za ki kai ba, dama wancan shashashan ustaz ɗin ya dace da ke ba ni ba " Ya yi maganar yana saukd Glass ɗin motar ya yi dirban alama ya zo. Zuciyarsa cike da takaici me ya saka ma ya sa wa iyayen yarinyar nan ya amince ne, sai yanzu take jin haushin kansa, ya dai san baya son ta to ta ta zai zauna da ita. Har suka ƙarasa gidan ba wanda ya yi magana a cikinsu. "Get out in my car." Ya daka ma ta tsawa, da sauri ta fice tana kuka. Gajeren tsuki ya ja yayin da suke barin gidan. *Ma'eesha.* Suna ƙarasa wa ƙofar gidan hangi makaho na fitowa daga cikin gidan hannunsa rike da kayan aikinsa na gyaran takalma. Tun daga nesa ta hango shi yana tafiya hannunsa ɗaya yana rike da kayan aikin gyaran takalminsa daya hannun rike da sandarsa ta jagora. Yana jin mai nape ya tsaya a ƙofar gidan ya tsaya. Fitowa ta yi daga cikin nape ɗin tana kallonsa da kayan aikinsa dake hannunsa. Kafin ta dauke idanunta lokacin da mai keke nape ɗin ke ma ta magana. "Hajiya sai kin samu wanda zai taimaka ma ki ya shigar ma ki da kayan cikin gidan." "Ba damuwa ka ajiye kawai ka yi tafiyar ka zan nemo wanda zai taimaka ma ni." "Idan ba damuwa zan shigar ma ki da shi ciki." "A'a ka bar shi kawai ka yi tafiyar ka zan shigar da kayan." Wani kallo mai nape ɗin ya yi ma sa kafin ya ce. "Kai kuma daga ina, kana makaho har da sandar jagora ne za ka iya ɗaukar kayan nan da wani ido za ka ga in..." Ma'eesha ta dakatar da shi ta hanyar cewa. "Ya isa Mallam don yana makaho ba shi ke nufin kasashshe ba ne, to shi ne maigidan ya ce ba sai ka shiga ba don haka maganarsa ta zauna." Wani kallo ya yi wa Ma'eesha na mamaki da al'ajabi kafin ya kalli makaho ya ce. "Dama da kika ce ke matar aure ce daga gaske ne, kuma wannan ne mijin naki?" "Eh shi ne mijin nawa sai aka yi ya ya?" "Amma Hajiya a yadda kiken nan a ce makaho kike aure faƙiri ko dai asiri ya yi ma ki ko kuma auren manufa kika yi ne?" Ba ta tanka ma sa ba ta buɗe jakarta ta ga 100k ya rage ma ta, ta ciro 10k ta mika wa mai nape ɗin ta ce. "Na gode za ka iya tafiya ." Washe baki ya yi sannan ya shiga ciki yana ma ta godiya ya bar wajen. Makaho ne ya dauki karamin buhun shinkafar a hannu ɗaya, ɗayan hannun ya ɗauki katon ɗin taliya da na macaroni da cus-cus. Da mamaki take kallonsa har ya shiga gidan ta bi bayansa tana kallon ikon Allah. Ba ta yi mamakin ɗaukar kayan ba, saboda yana da ƙira irin na zaratan jaruman maza, don jikinsa ma a murɗe yake kamar irin mazan da suke yawan motsa jiki suna daga ƙarfe. Amma yadda ya ke tafiya haka nan ne ya ba ta mamaki. Sai da ya gama ta kalle shi ta ce. "Ta ya ka iya tafiya haka nan ba tare da ka yi karo da komai ba?" Murmushi ya yi ya ce. "Na riga na karanci yanayin gidan bayan fitar ki sai da na auna ta hanyar tafiya na san taku nawa zan yi da idan na kawo saitin ƙofar dakin na sani." "Ina za ka je yanzu?" "Zan je ne ko Allah zai sa na samu wani abun, gyaran tsakani nake zuwa?" "Ta ya kake gane kalar takalmin da za ka san irin foolish ɗin takalmi fari ko baƙi?" "Idan aka kawo ni kan tambaye wani kala ne, kafin na san irin kayan aikin da zan yi amfani da shi, duk countener dada nake amfani da su daban-daban ne na san na fari da na baki da kowane kala, iska tsinke wa ne idan na laluba ina gane wa sai na ɗinke." "Ka hakura da fita don ina son mu yi gyaran dakin nan, za ka dinga ko mika Mani wani abun ne idan na ba ka ka rike za ka iya ko?" "Zan iya in sha Allah." Daga nan ya fita ya shigo da kayan aikinsa. Ita kuma ta shiga ciki ta fara fito da trolly ɗin kayanta. Har ya ajiye a barandar. Sai ya koma gefe ya tsaya. Shara ta fara yi ta kwashe sannan ta shimfida leader carpet da ta siyo ya cika ɗakin ya yi kyau sosai. Sannan ta shiga da ƴar madaidaiciyar katifarta ajiye a inda ya dace. Sannan ta shimfida zanin godon ta sanya rigar pilow a pillow biyu da ta siyo ta jera. Duk da kasancewar tana da mai yi ma ta gyaran ɗaki da wankin toilet amma hakan bai sa mahaifiyar ta ta bar ta haka ba ta koya ma ta ba, don ita ke gyara wa Mahaifinta ɗaki. Labule ta ɗauko guda biyu na koda da window, a jikin bangon ɗakin ta samu ƙusa ta buga labulen na kofa da na window. Sannan ta kalle shi ta ce. "Ko za ka iya shigo ma ni da kayan nan duka?" Kai ya jinjina ta ɗaga labulen ta sakala a jikin kofar. Haka ya dinga shigo da kayan tana nuna ma sa in da zai ajiye, da zaran ya kai wajen za ta ce ma sa ya yi ya ajiye. Har aka gama shigo da komai. Kitchen ɗin fale-fale dake tsakar gidan ne ta ce ma sa ya dauki karamin buhun gawayin ya ajiye a ciki tare da murhun gawayi. A barandar ta ajiye ƙaramin Gas da ta siyo ta ce. "Ka yi a hankali kar ka karaso ta nan gefen na ajiye Gas zan yi girki." "To in sha Allah." Shiga ciki ta yi ta buɗe kwalin tukwane da ta siyo, ta ciro ƙaramar ciki ta kunna gask ta zuba ruwa. Sannan ta ɗauko tabarma ta shimfida a gefe ta ce. "Ka zauna ma na " Sai da ya laluba ya ji inda tabarmar take sannan ya zauna a gefe. Ita kuma ta dauko kujerar tsuguno na roba da ta siya ta zauna akai. Sallama suka ji daga waje ana yi. Makaho ya amsa sallamar yana mikewa tare da ɗaukar sandarsa. "Wa'alaika salam warahmatullah." Ya amsa yana nufar kofar gidan. "Mallam Iro mijin Larai Dillaliya ne ya zo amsar kuɗin haya." Jin haka ya saka Ma'eesha cewa. "Ga kuɗinsa ka kai ma sa na san shi ya zo amsa." Ta yi Maganar tana shiga ɗaki ta dauki handbag ɗin ta. "Ana zuwa ." Makaho ya yi maganar yana daga murya yadda Iro zai ji shi. 50k ta ƙirga ta ba shi yayin da kudin ya rage ma ta saura dubu arba'in. Yana ganin makaho ya ce. "Khalifa Barka da safiya." "Barka dai Mallam Iro ya al'amura?" "Alhamdulillah." Kudin ya mika ma sa ya karɓa ya kirga ya ga sun cika. "Ma sha Allah kudi sun cika, amma fa akwai dubu biyar da ya kamata Ku ba Ni da dillanci. Amma na yafe ma ku." "To mun gode Allah ya saka da alkhairi ya sa la fi haka." Da Amin ya amsa ya ma sa sallama ya bar gidan. _Nadra_ Da kuka ta shiga ciki kai tsaye ta nufi ƙofar ɗakinsu ta shige, kan gado ta faɗa tana ci gaba da rusa kuka. Gwaggo Laraba ta bi bayan ta da sauri. Kan gadon ta nufa in da Nadra ke kwance ta kalle ta tana ɗaga ta . "Nadra lafiya me ya faru?" "Ba a gaban idanunku kuna kallonsa yana taɓa jikina duk da haka bai ma sa ba sai da ya tallabo fuskata ya haɗa bakinsa da nawa ya tura mun cake a cikin bakina, ba wanda ya yi ma sa magana ko ya hana sai sai tafa ma sa ake yi. Sannan kuma don na ma sa magana rashin dacewar abun da yake ma ni don na daga ma sa hannu wai idan na sake daga ma sa hannu sai ya karya hannun har yana zagin saurayi na wai wancan shashashan ustaz ɗin ne ya dace da ni, wallahi Ya Sayyadi ba shashasha ba ne mutum ne mai tsoron Allah da kiyaye dokokin Allah ba kamar shi da yake take dokokin Allah ba yana taɓa macen da ba matarsa ba. Wallahi Gwaggo ba namijin da ya taba rike ko da ƙumbata amma shi lokaci ɗaya ya zo ya..." Dariyar da ta ji daga bakin kofar ne ya saka ta dakata tana kallonta fuska a murtuƙe. Wata ƴar Gwaggo Laraba ce take dariya ta ce. "Yanzu ma aka fara ba ki yi kuka ba tukuna." Wani kukan ta saka saboda dariyar ya ƙular da ita, sai da Gwaggo Laraba ta Kore ta Sannan ta ce wa Nadra ta tashi ta yi wa wanka ta yi sallah. Bayan kamar mintuna talatin ta shigo ta samu Nadra akan sallaya. Wasu kaya ta ajiye ma ta wanda Nadra na ganin kayan ta mike tsaye tana cewa. "Wannan ai kayan da Sunyi Sidra za ta saka ne idan za'a kai ta gidan mijinta, ko har ta dawo ne?" "Ba na son yawan tambaya ki shirya cikin wannan kayan ki fito Falon Abbanki yana kiranki." Haka kawai ta tsinci kanta da mummunan faduwar gaba wanda ba ta san dalili ba. Wayar Sidra ta gwada kira still switch off. Zama ta yi bakin gadon taba kallon tsadadden leshin da kudinsa zai kai Naira dubu ɗari biyu. Da set na ɗan kunne da sarƙa siriri na Gold. _Fahad_ Yana zaune a falo shi da iyayensa. Baba, Mama, Aunty Rahama sai mahaifiyar Baba wacce ake kira da Inna. Mama ce take faɗa tana cewa "Zancen banza waye za ka ajiye wa ita a nan? Wato saboda ba ka son ta ko? Ina ce a baya da muka ce a gyara ma ka part ɗin ka ka zauna da ita ka ce ba za ka zauna da matarka a family house ba. Saboda za'a saka ma ka idanu a takura ma ku. Wato saboda wacce kake so ta gudu ita wannan tun da ba son ta kake yi ba shi ne za ka ce wai kada a kai ta sabon gidan da ka yi niyyar zama da matarka ka fasa ko? Sannan za ka ce a kawo ta a ajiye a family house bayan a baya ka nuna ba ka so ko? To ba ka isa ba yadda ks hana gyara gidan aka kai ma ta kaya gidan iyayenta suka jera kaya tun shekaranjiya ba wanda zai je ya kwaso kayan nan, kuma dole ka zauna da ita a gidan, to uban waye za ka bar wa gidan ya zauna?" Ina ta amsa da cewa . "Kila har yanzu yana jiran ita waccen da ta gudu ta dawo ne ya saka ta a ciki, don alama ya nuna haka." " Baba ya yi saurin cewa. "Haba sai ka ce ba Musulmai ba ta ya ya zai auri wa sannan ya auri ƙanwa kamar maguzawa? Ko maguzawa ai ba za su yi haka ba." "Idan ma tana cikin zuvuyarka ka cire ta don ko saki Nadra saboda Sidra ba wanda zai yarda ka aure ta." Cewar Aunty Rahama tana kallon Fahad da ta hade fuska kamar bai taɓa dariya ba. Tashi ya yi ya bar ma su ɗakin suka bi shi da kallo, Mama ta raka shi da harara don har ga Allah tana ƙaunar Nadra. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣0️⃣ Tashi ya bar ma su ɗakin suka bi shi da kallo, Mama ta raka shi da harara don har ga Allah tana ƙaunar Nadra. Baba ya kalli Mama ya ce. Matuƙar yau iyayen yarinyar nan suka kai ta gidan mijinta to ki tabbatar bai kwana a gidan nan ba." Jinjina kai Mama ta yi tare da cewa. "In sha Allah." _Makaho_ Yana zaune a tabarmar da Ma'eesha ta shimfiɗa ma sa ya ji muryarta tana cewa. "Ba ri na je na siyo bread a shagon dake nan kusa da mu." Bai tanka ma ta ba ita ma ba ta jira cewarsa ba ta yi ficewar ta. Ba ya jima ba ta dawo da bread a leda da gwanhwanin milo da na madara. Ta ajiye har ga Allah ta ji dadin siyayyar da ta yi, ba don ta yi tunanin siyar da wayar ba su da ba ta san yadda za ta yi ba. Duk da cewar a yanzu ma hankalin nata bai kwanta suka ba, saboda ta san yau da gobe duk abinda ta siyo za su ƙare ya za ta yi ne ina za ta samu wasu kuɗaɗen har ta sake siyo ma su wani ba. Don ta tabbatar makaho ba iya ɗaukar nauyin gidan zai yi ba, don wannan gyaran takalmin da yake yi ba ta tunanin shi kansa zai iya ɗ sa ɗaukar nauyinsa da shi ballantana ya dauki nata nauyin. "Ma',eesha." Ta ji ya kira sunanta lokacin da ta kashe Gas ɗin. "Na'am." "Don Allah ki daina yawan fita ko wane lokaci yanzu yai kin fita sau nawa a gidan nan?" Shiru ta yi tana kallon da kafin ta ce. "Idan ina buƙata abu za ka aje ma ni yaron da zan aika ne?" "Meye amfanina ina gidan da sai kin fita?" "Na ding aikenk kenan?" "Wa ya fi cancanta ya fito ya nemi abun da ake bukata tsakanin ni da ke?" "Kai ka fi cancanta amma gani nake za ka wahala ga sanda ga kaya a hannun ka." "Kin manta haka nake fita neman na abinci, hannu daya riƙe da sandar hannu daya riƙe da kayan gyara. " "Shi kenan dama na mance ban siyo ruwa ba sai ka je ka siyo." Ta ciro ɗari biyar ta bashi ya karba. "Wannan nawa ce?" "Ɗari biyar ce, yanzu tsarin zai canza kamar yadda rayuwa ta ta canza. A baya bottle water nake sha, amma yanzu ba na da halin da zan cigaba da shan sa, ko da na siya yanzu nan da kwana biyu zai gagare ni don haka yanzi zan koyi shan ruwan pure water. Wannan ɗari biyar ka siyo ma na bag ɗaya wato jaka dayatina tunanin bai wuce dari biyar ba." Ya fita don siyo wa ta bi shi da kallo har sai da ya fice sannan ta ɗauko ƙwai guda huɗu ta ta ɗan jajjaga bayan ta wanke ƙaramin turmi ta daka magi ta yanka albasa, sannan ta ɗauko fry pan ta wanke sannan ta zuba mangyaɗa ta soya. Da sallama ya shigo gidan ta amsa tana miƙe wa ta karbi jakar ruwan dake hannunsa, ya ƙaraso ciki sai da ya ji ya taɓa tabarmar da sandarsa sannan ya gane ya ƙaraso wajen. Bayan ya hau tabarmar ne ya zauna tare da yin Bismillah. Kofuna biyu ta dauko na shan shayi ta ajiye bayan ya wanke da cokula. Ruwan shayin ta zuba wa kanta da nasa ta zuba sugar da milo da madara, ta fifita dai da ya rage zafi ta ajiye ma sa a gabansa da plate ɗin da ta saka ma sa soyayyen kwai ciki ta ajiye ma sa bread. "Ga breakfast ɗin ka nan a gabanka." Sannan ta haɗa na ta ta koma kan tabarmar ta zauna a gefensa. "Na gode Ma'eesha Allah ya biya ki fa gidan aljanna." "Amin ya Allah." Ta amsa tana cigaba da cin abincin ta. _Nadra_ Tana zaune a falon zuciyar ta cike da mamaki da ɗan firgici. Duk abinda take gani a gidan yana gudana tana ɗaukarsa ne na yayarta Sidra ba ta taɓa tunanin ita ce Amaryar ba. Abba dake zaune kusa da kujerar dake kusa da Nadra dake zaune saman Centre carpet, fuskarsa cike da tsananin tausayin ƴar tasa mai biyayya da bin Umarninsa akan komai. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir ya ce. "Nadra yau ce ranar da rayuwarki za ta sauya." Nadra ta kalli fuskarshi idanunwanta cike da rashin fahimta tana kallon jama'ar falon ɗaya bayan ɗaya. Idanunta suka sauka akan kakarta mahaifin Abba, sai Gwaggo Maimuna Yar Abba sai Gwaggo Laraba ƙanwar Abba. Sai Yayan Umma wato Alhaji Bashir. Kafin ta mai da dubanta kan Abba. "Nadra yau aka ɗauara aurenki ba tare da na shawarce ki ko jin ra'ayin ki ba, saboda ina da yaƙinin cewa ba za ki taɓa watsa ma ni ƙasa idanun ba." A firgice take kallon su ta ce. "Me kuke nufi wace ce Amaryar?" Abba ya dube ta cike da kulawa da nauyi ya ce. "Sidra ta gudu Allah ya kare ta a duk in da take. Amma ki sani rayuwarki aka ɗaure yau." Nadra ta ji shiru na ɗan lokaci zuciyarta ta yi ma ta nauyi kamar dutse. Ƙwalla ce cike a idanunta ba zato ba tsammani zuciyarta ta fara fahimtar cewa ita ce Amarya. Ta taɓa kafafuwan Abba cikin tsanani ruɗani da firgici. Zuciyarta na bugawa da karfi. Sai ta ɗaga kai ta yi addu'a a cikin zuvuyarta. "Allah ka bani ƙarfin fuskantar wannan sabuwar rayuwa , ka sa na zama mai haƙuri da biyayya." Kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciyar mai sauraro. Cikin wannan yanayi Nadra ta san cewa babu koma baya, kuma dole ta rungumi a abun da ya zo ma ta. Shin ma waye mijin da aka ɗaura ma ta auren da shi? Tambayar dake kai komo a zuciyarta kenan. Sai ta ji muryar wan Mahaifiyarta Alhaji Bashir yana cewa. "Dama kana naka ne Allah ya gana nasa. Dama can Allah bai ƙadarto cewa Sidra ce matar Fahad ba sai ke, don haka ki rungum..." Kukan da ta fashe da shi ne ya saka kowa dakata wa yana kallonta. Kuka take yi wanda ke fitowa can a kasar ranta. "Ki yi hakuri Nadra na san za ki ji abin a baibai, amma ki sani ba ni da wani zaɓi da ya wuce hakan. Na gayyaci jama'a na tara su an zo daga garuruwa mabanbanta gari ya waye ana jiran rana ta yi a daura aure amma sai Sidra ta nemi tozarta ni da kunyata ni ta nemi zubar ma ni da ƙima a idanun jama'a. Da wani idanu zan kalli jama'ar da na gayyata zuwa auren ƴa ta na ce ma su an fasa daurin auren ƴata ta gudu? Hakan ba zai zubar mani da ƙima ba? Ke kadai ce na san cewa za ki iya kwaso ma ni ƙima ta da ƴar ki ta nemi zubar wa. Tun da na haife ki daga ni har mahaifiyar ki muna alfahari da ke, ba ki taɓa saɓa ma na ba, don haka ba na sa ran wannan karon za ki aikata wani abun da ba daidai ba. Na roke ki da Allah ki..." Cikin sauri ta ce . "Abba ka daina roƙo na don Allah ba abinda za ku aikata akaina ku roke ni Ko da hakan na nufin mutuwa ta ce, Abba dan Allah ka daina roƙo na sai na ji kamar na gaza zama ƴa gagari ce a gare ku. Na amince akan duk hukuncin da kuka yanke akaina. Amma Yaa Fahad fa Sidra yake so kuma ita ma na san tana tsananin son sa idan ta dawo ta tarar da..." Abba ya kira sunanta a kausashe. "Nadra!" Ɗagowa ta yi ta kalle shi da idanunsa da suka yi jajir saboda kuka ta ce. "Na'am Abba." "Daga yau ba na son sake jin sunan Sidra a bakin ki, a cikin gidan nan ma na hana a kira sunan ta, ba zan yi ma ta baki ba amma na cire ta daga cikin mu, ki ɗauka ba ki da wata ƴar uwa a raye Sidra ta mutu a wajen ki." Kuka ta saka sosai tana rokon Abba ya yafe wa Sidra amma bai saurare ta ba. Sai ya tashi tsaye ya kalli Nadra ya ce . "Allah ya yi ma ki albarka ya kare ki a duk in da kike, yadda kike wa iyayen ki biyayya Allah ya sa ƴaƴan da za ki haifa su yi ma ki fiye da yadda kika yi mana. Allah ya zaunar da ke lafiya da mijinki ki yi ma sa ladabi da biyayya kome ya daka ki to kiyi masa matuƙar bai saɓawa addinin Musulunci ba, aljannarki na kasan ƙafansa idan ya daga ki shiga kada ki mance da wannan." Yana fadar haka ya fita daga falon kamar zai yi kuka, don ba zai iya jurar ganin Nadra n kuka tana rokonsa akan wani abu bai yi ma ta ba, amma wanann karon ba ya jin zai saurare ta akan zancen Sidra. Sauran jama'ar dake falon kowa nasiha sosai suka ji ma ta akan zaman aure da hakuri da rayuwar aure. "Dare na yi ya kamata a ɗauke ta a kai ta gidan mijinta." Cewar Gwaggo Maimuna tana kallon Ammi. Ammi ta ce . "To me kuke jira ku tafi a raka ta ma na ga jama'a can a falo suna jiran ku fito, ga motaci jere a waje." Gwaggo Laraba ce ta ja hannun Nadra da ta kudundune cikin babban mayafin da aka yafa mata. Part ɗin Umma suka shiga suka same ta ita da ƙawarta Hajiya Turai tana rarrashinta, ganin dunya saka Umma ta yi saurin goge hawayenta. Kukan Nadra ne ya kara tsananta ta nufi Umma ta shige jikinta ta rungume. Kuka suke yi du duka biyin. Duk yadda Umma ta so rike kukanta kasa wa ta yi, haka kawai take jin tausayin Nadra ga Sidra da ba su san halin da take ciki ba, damuwa sun yi ma ta yawa. Kula take yi sosai tana ƙankame Nadra kamar za'a ƙwace ma ta ita. Ammi ce ta shiga ganin halin da suke ciki ta ce "Me nake gani haka, ke da za ki ma ta nasiha a wuce da ita gidan mijinta shi ne kike kuka?" Da ƙyar aka ɓanɓare Nadra a jikin Umna suka fita da ita tana kuka tana kiran sunan Umma. Hankalinta ya tashi musamman da ta ji jikin Umman da zafi alamar ba ta da lafiya. Tana ji tana gani lokaci daya rayuwarta ta juye sama zuwa ƙasa ƙasa zuwa sama. Ko da wasa ba ta kawo wannan ranar ba, ba ta yi tsammanin nan kusa za'ayi aurenta ba kuka da saurayin ƴar ta wacce take ƙauna yake ƙaunarta. Amma yau ita ce za'a ɗauka akai gidan Fahad a madadin Aunty Sidra. Kuka take yi sosai tana ji tana gani aka saka ta a ɗaya daga cikin motocin da suka zo ɗaukar Amarya. Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka saka ta a tsakiya. Sauran dangi suka shiga cikin sauran motocin, sai dai ba ƙawar amarya ko ɗaya, kasancewar ba ƙawarta da ta san da zancen auren, ko A'isha Humaira da ta zo ta dai zo ne a matsayin bikin Sidra ba wai ta san ƙawarta ce aka aurar ba. Sauran yan matan na dangi da kowa sai da motacin suka kwashe su zuwa gidan Amarya. _Fahad_ Kwance yake a bedroom ɗin sa yana jin yadda abokansa Sadik da mukhatar suke ta yi ma sa knocking ƙofar, amma bai yanka ma su ba sai ma pillow ya saka ya dora a kansa alamar baya son ƙarar ƙofar. "Fahad please open the door." Cewar Mukhtar yana bugun kofar. Sadik cikin ƙuluwa da wulaƙancin da Fahad ke yi ma su tun ɗazu ya ce. "Wai kai wane irin wulaƙanci kake yi wa mutane ne tun ɗazu, sai faman bin ka make yi ka fito mu tafi a raka ka ɗakin amarya ka share mu ka mayar da mu ƴan iska idan ba za ka je ba ai sai ka sanar da mu." "Sau nawa na fada kowa ya watse, sauran sun tafi ku ma ku tafi ba in da zan je Allah ya ba mu alkhairi." Cikin takaici suka fito kowa ya nufi motarsa suka bar gidan. _Nadra_ Har suka isa katafaren gidan Fahad ba ta daina kuka ba. Motacin duka suka shiga cikin compound ɗin gidan. Babban gida ne sosai mai girman gaske ga manyan fitilu da suka haska gidan ya koma tamkar rana ne ba dare ba. Faɗar kyau da tsaruwan gidan ma ɓata lokaci ne, gini ne na alfarma kuma na zamani. "Fito da ƙafar dama." Cewar Gwaggo Laraba tana riko hannun Nadra dake kuka. A hankali ta yi Bismillah ta fito da ƙafar dama. Tana rike da hannunta suka nufi main door nan ma ta ce ma ta ta shiga da addu'a. Ta dan jira kafin ta ga ta saka ƙafar dama ta shiga ciki. "Ma sha Allah." Shi ne kalmar da kowanen su yake faɗa wasu a zuciya wasu a fili. Ɗaya daga cikin manyan kujeru dake downstairs aka zaunar da ita. Yayin da suka dinga shiga suna leƙa ko ina na gidan suna yaba kyawun gidan. Daga karshe dai suka kai Nadra ɗakin da ya kasance mallakinta ne a downstairs. Saman katafaren gadonta suka zaunar da ita. Nan suka dinga yi ma ta nasiha sosai da da kuma kara nuna ma ta mahimmancin haƙuri. Sannan suka yi ma ta Sallama suka fice, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Hakan ya saka suka dawo suka dinga rarrashinta. Ganin kukan na ta ba na tsaya wa ba ne ba ne. Sallama suka yi ma ta suka ce da safe za su dawo. Suka bar gidan suna ta santin kyawun gidan. _Mama_ Tana zaune ita da Aunty Rahama da ƙanwar Mama mahaifiyar Farida wacce suke kira da Aunty Jummai. Farida na kwance a jikin Mahaifiyarta tana sharar ƙwalla. Aunty Rahama ce ta kalli Farida tana cewa. "Ki yi hakuri Farida wannan kukan ya isa, Allah ya zaɓa ma ki ma fi alkhairi, idan Allah ya nufa ke matar Fahad ce wata rana sai ki ga Allah ya karkato da hankalinsa zuwa gare ki ya aure ki, auren nan nasa ba wai yana nufin ba ya da damar auren ki ba ne, ai namiji mijin mace huɗu ne." Haka Aunty Rahama ta dinga rarrashinta duk da ta san cewa ba yadda Fahad zai yarda ya auri Farida saboda ba ya son ta kwata-kwata amma ta faɗi haka ne don ta kwantar ma ta da hankali. Mama ne ta kalli Rahama ta ce . "Ki je ki duba ko sun tafi don karfe goma da rabi yanzu, don motocin da suka kai Amarya tuni sun dawo." Rahama ta miƙe kenan sai ga kiran Sadik ta shigo wayarta. Amsa kiran tayi bayan ta ji sallama ta ce . "Sadik kin kai abokin maku ne?" "Ina fa Aunty, rashin mutunci ya ma na muka bar shi." Nan ya sanar da ita yadda suka yi da shi. Kuma ya kira ne don a je a saka shi ya tafi kada ya bar yarinya ita kadai a gidan.Bayan sun yi sallama ta kashe kiran wayar. Nan ta sanar da Mama yadda suka yi sai Mama ta dauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa a kashe. Don haka ta mike fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part ɗin Fahad. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *🎉Happy new year*🎉 Ina ma na barkan shigowa sabuwar shekarar 2026 lafiya. Allah ya ba mu zaman lafiya mai ɗore wa a ƙasar nan. https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣1️⃣ Nan ta sanar da Mama yadda suka yi, sai Mama ta ɗauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa , don haka ta miƙe ta fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part ɗin Fahad. Ba kowa a fakon sai sanyin A.C dake tashi a falon. Bedroom ɗin sa suka nufa Mama ta fara buga ƙofar da ƙarfi. A tunanin Fahad su Sadik ne ba su tafi ba, don haka a fusace ya fara magana. "Wallahi idan ba ku rabu da ni ba zan tafka ma ku rashin mutunci idan na fito." "To Bismillah ma ta mutunci kawai." Muryar mahaifiyarsa da ya ji ne ya saka shi zaro idanunsa waje. "Ya Salam. Mama ce?" Tasowa ya yi cikin rashin kuzari ya zo ya bude kofar ɗakin. Kallonsa ta yi fuska a tamke ta ce "Me kake yi har yanzu da ba tafi gidanka ba ka bar baiwar Allah ita kaɗai." Har ya buɗe baki zai yi magana sai Mama ta ɗaga ma sa hannu alamar dakatar wa. "Ba na son jin komai, mintuna goma kada ka sake yi a cikin gidan nan ba ka tafi ba." Tana gama fadar haka ya juya ta fice, yayin da Aunty Rahama ma ta mara ma ta baya suka fice a tare. Kamar zai yi kuka haka yake ji. Key ɗin motarsa ya ɗauka, sai system ɗin sa da wayoyinsa ya nufi hanyar fita zai fice. Har ya murɗa handle ɗin kofar zai fice sai ya juya yana ƙare wa ɗakin kallo sannan ya dawo ya kashe komai na dakin . Ficewa ya yi zuwa farlon nan na ya kashe duk wani kaya na Elections sannan ya fice. Kai tsaye wajen motocinsa ya nufa, ya shiga ɗaya daga ciki bayan ya ajiye laptop dinsa a kujerar zaman banza. Sannan ya yi wa motar key bayan maigadi ya wangale ma A ya bar gidan. _Makaho_ Suna zaune bayan sun gama yin breakfast, ruwan tea ya shanye amma bai cinye bread da ƙwai ba. Tattara kayan ta yi ta haɗa su a can gefen kayan wake-wake da suka ɓata. "Ma'eesha me kike yi ne?" "Ba komai wake-wake zan yi." Sandarsa ya ɗauka ya karasa in da yake jin motsinta ya ce. "Ba ri na wanke je ki kawai." "A'a ba za ka iya ba." "Ba abinda za ki iya yi wanda ni ba zan iya ba, domin nakasa ba kasawa ce " Lalube ya fara yi har ya ji in da kayan suke , tana kallonsa yana wanke wa yana ɗauraye wa har ya kammala. Ta kwashe kayan ta je ta jera su a in da ya dace. Bayan ya shigo ɗakin ne ya ce ma ta . "Yanzu me zan yi ma ki?" "Ba komai na gode." "Na san ke ƴar hutu ca ba ki saba da ayyuka ba, ma su aiki ne suke yi ma ki aiki, to don me ba za ki bari na taya ki ba ?" Gajeren murmushi ta yi ta goge ƙwallar da ya cika idanunta ta ce. "Haka ne, duk da ma su aiki ke yi ma ni aikin komai amma hakan bai saka Mahaifiyata koyar da ni ba. Ta na cewa ba lallai mijin da zan aura ya so a ce mai aiki ce ke yi ma sa gyaran ɗaki ko girki ba. Wani namijin sai matarsa kawai take yi ma sa hidima." Kasancewar ta buga labule ta shimfiɗa leda ta ajiye katifar ta gyara. Ba wani aikin da ya rage. Hakan ne ma ya sa ta tuna ina z ta damu room freshener spray ko turaren wuta ta turaran wuta da za ya sa a ɗakin ya yi ƙamshi , dole ta nemo ba z ta iya zama daki ba ƙamshi. "Ba abun da zan yi ma ki kafin na fita, kada na fita kuma ki buƙata wani abu." "Kada ka damu girki ne kawai kuma Anjima kaɗai zai ɗaura, kuma ba aikin ka ba ne." "To ba kaya ma su datti da zan yi ma ki wanki?" "Babu." Ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa. "To zan je na zagaya ko Allah zai sa na samu." "Ka huta kawai da yawon gyaran takalmin nan ga rana, kuma ba kudin kirki ba?" "Kin fi so ba zauna ke ce ɗauki ɗawainiya ta ne, ke ce mijin ni ne matar, ba zan iya ba" "Amma yanzu wanan uwar rana fa, gyaran ma kamar nawa ake gyara takalma?" "Idan tsinkewa ce Naira hamsin nake ɗinke wa, amma idan sauran gyararrakin ne ya danganta yanayin aikin." "Please ka bar shi ka hutarwa kanka, a ƙalla muna da abincin da zai kai mu watanni uku muna ci, to me ye na wahalar da kai cikin wannan ranar ka yi ta yawo, kudin da ba na kirki ba, da babban sama'a ce ma da sauƙi. Amma wanann sana'ar ba..." "Kin raina sana'ar ko? Kina ganin kamar asara ce ko? Duk wanda kika ga ya yi nasara a rayuwa, to akwai tarin asarori da faɗi-tashi da karyewar jari da ya fuskanta waɗanda ba ka gani ba. Sai dai asara ba ta hana shi ci gaba da neman nasara ba, faɗuwa ba ta hana shi sake yunƙurawa ba, karyewar jari bai karya masa zuciya ba. Wahalar da kike sha a yau, ita ce farashin nasarar da kake so ta tabbata gobe. Domin duk nasarar da ba a wahala wajen tabbatar da ita ba, ba ta ƙarko." Ya ɗauki kayan aikinsa ya fice ba bishi da kallo. Huɗubar mahaifiyarta take tunawa, in da take cewa . "Ya ke ƴata Ki zaɓi namiji mai kyakkyawan zuciya, komai matsayinsa, komai kuɗinsa ko rashin kuɗinsa. A cikin gaskiyar rayuwar aure, za ki gane cewa kasancewa cikin babban gida ko tarin kuɗi mai yawa ba su da muhimmanci kamar yadda ake tunani. Za ki fi son wanda za ki iya tattauna komai da shi, wanda kuma zai zama uba nagari ga ’yayanku, wanda ba ya yaudara, wanda za ki iya amincewa da shi. Iyali masu farin ciki ba su da farashi. Kada ki ji tsoron auren namiji da ke cikin hanyar gyara kansa. Amma ki guji na miji marar sana'a kuma bai damu ya tashi ya nema ba." Wayarta ta ji yana ringin ta duba ta ga ƙawarta ce Nasreen Ibrahim. Tana ɗaga wa ta ji muryarta cikin tashin hankali tana cewa. "Ƙawata kina ina?" Ɗan jim ta ji kafin ta ce. "Lafiya?" "Na zo gidanku ne nake jin wani zancen da ya ruɗa ni akan kin yi aure." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Kina ina yanzu?" "Ga ni a ƙoafar gidanku ." Ta cikin wayar ta ji muryar Laila na cewa. "Nam ba gidansu ba ne ki je can in da take yanzu ita da musakin faƙirin mijinta can ne gidanta yanzu." "Laila kika dake ma ni wanta magana anan wallahi dai na ci uwar ki a wajen nan." "Ba dai uwa ta ba Wallahi, cire wayar Nasreen ta yi za ta yi cikin Laila sai ta gudu ciki tana cewa . "Shegiya ce ni da zan tsaya ki dake ni? Mai ƙirar samudawa ai sai ku kashe ni. Wacce kike zuwa wajen ta yanzu ba ta nan dai a koma in da take mun kora ta ni da uwata. "Ku jira na ku sakamakon." Cewar Jamil yana watsa ma ta wani mugun kallo. Tura ba ki ta yi tana cewa "Yaya Jamil kawar Aunty Ma'eesha ce za ta dake ni." Bai ko saurare ta ba ya nufi motarsa. Jin Muryar Nasreen na cewa. "Ma'eesha ban gane wannan kwatancen naki ba, idan na kawo titin zan kira ki sai ki fito ki shiga da ni cikin layin, don ban zo da Driver ba ni nake yin driving ɗin." Jin haka ya saka Jamil tsaya wa yana kallon tana yana cewa. "Ba ni ita Please ta yi Mani kwatancen sai mu tafi tare." " Jin haka ya saka Ma'eesha cewa "Wallahi kuka zo da shi gidana ba zan yafe ma ki ba." Jin haka ta ce. "Ba zan zo da shi ba kar ki damu." Daga haka ta kashe kiran ta kalli Jamil ta ce "Ka yi haƙuri ba ta yarda na je da kai ba, amma next week zan kira ka sai ka zo mu tafi tare ka ga ni yanzu ba ta yarda na je da kowa ba." "Ba damuwa ki gaishe ta zuwa next week ina jirab kiran naki." Daga haka ya shige motarsa ita ma ta shiga tata motar suka bar gidan a tare. Horn ya danna ya tsaya kasancewar shi ne a gaba, ita ma ta tsaya . "Ban lambar wayar taki ko?" Ya fada bayan ya sauke glass din mota tasa. Ta karanta ma sa lambar sannan ta ja motarta ta bar wajen zuciyata cike da tarin tambayoyi. Kwatancen da ta faɗa ma ta nan ta je ta tsaya a gefen titin, ba ta ga Ma'eesha ba, can ta hango ta tana ƙarasowa wajen motarta. Sai dai kallo ɗaya ta yi wa ma'eesha ta ga ta rame ma ma ta a cikin kwanaki biyun da ba su haɗu ba. Tana zuwa ta buɗe front sit ta zauna tana yi ma ta sallama. Amsa wa ta yi tana ma ta kallon mamaki,sai dai ta haɗiye tambayoyin ta ta yi wa motar key ta ni hanyar da ta ga Ma'eesha ta fito. Tana nuna ma ta hanyar tana bi har suka ƙarasa ƙofar gidan. A tare suka fito ta ga Ma'eesha ta buɗe ƙofar ta shiga, ita dai Nasreen mamakin ta ƙara hausawa yake yi . "Bismillah shigo ciki." Ta yi magana lokacin da ta shiga ɗakin. Da sallama Nasreen ta shiga cikin ɗakin, ta tsaya tsaye tana ƙare wa ɗakin kallo. Ba ta zauna ba duk da Ma'eesha ta ce ta zauna saman katifar. "Zaman me kike yi a nan, wannan kangon wanda bai kai na a ce kina kiwon karnuka a ciki ba?" Ta yi maganar tana karewa ɗakin kallo, sannan ta fito taskar gidan tana kare ma sa kallo, hatta banɗaki da kitchen ɗin fale-fale dake tsakar gidan sai da ta leƙa. Sannan ta dawo ta kalli Ma'eesha dake zaune a bakin katifa ta ce. "Lafiya kike zaune a wannan kangon kuma me kike yi?" "Zaman aure nake yi ." Da mamaki take kallona ta ce. "Zaman aure kuma?" "Eh." Ta ba ta amsa ba tare da ta kalle ta ba. "Wani irin zaman aure kuma da waye mijin naki?" "Zaman aure da kowace macen aure take yi a gidan mijinta." Dafe kai ta yi tana cewa "Am confused about how..." Kukan da ta saka ne ya saka Nasreen kasa ƙarasawa maganar da ta yi niyyar faɗa, domin kuwa tausayin ƙawar tata ce ta saka ita ma ta rungume ta suna yin kukan tare ba tare da ta san komai ba. Tsawon mintuna suka ɗauka suna kuka ba mai rarrashin wani, kafin Nasreen ta zame jikinta daga na Ma'eesha, tana goge ma ta hawaye ta ce. "Me yake faruwa ne, na san ni da ke ba mu ɓoye wa juna komai, don Allah ki sanar da ni kar ki saka kaina ya buga." Nan Ma'eesha ta ba ta labarin komai, tun daga farko kar karshe. Ba abinda Ke tashi sai sautin kukan Nasreen tana tausayin ƙawarta. "Amma Allah ya tsine wa Mamy albarka. Allah ya sa ta shiga wuta, wallahi wannan matar ba za ta ga annabin rahama ba. Gabadaya ta juye wa Daddy tunani sai abinda ta ce. Allah ya jikan Mummy." "Amin ya Allah." Ma'eesha ta faɗa tana goge hawayenta. "Yanzu shi wanann makahon ne zai iya riƙe ki?" Ma'eesha ba ta ce komai ba, don ba ta san amsar da za ya ba ta ba. "Yanzu ke sai kika yarda?" "To ya zan yi Nasreen?" "Ai ba yadda za'ayi a haɗa ki da wannan nakasashen talakar musaki. Haba ke ba za ku nema wa kanki ƴanci ba?" Murmushin takaici ta yi ta ce. "To ya zan yi tun da mahaifina ya aurar da ni ga wanda ya ga dama, ba na da wani zaɓin da ya wuce rungumar kundin ƙaddarata." "Haka ne, amma wannan ai bai dace da ke ba, ta ya ya za'a aurar da ke ga wanda na san ko kuɗin kayan kwalliyarki ba zai iya siye ba ballantana abincin da za ki ci, abun takaici wai sadakinki dubu uku kacal ko kaza yanzu ai ba za'a ce dubu uku ba ballantana mutum, ba kayan lefe ba komai, wanann ke ce kika sigar da wayarki kika kama haya kika siyo abincin da za ki ci kin san wannan auren ba alkhairi a cikinsa. Don haka ki tattara kayan ki yana zuwa ku ci mutuncinsa ki saka ya yi ma ki saki uku, ki zo mu tafi gidanmu ki zauna a can na san iyayena za su karbe ki, kin ga ba ki da kowa a garin nan ba ki san dangin mahaifiyar ki ba, sannan yanzu tun da hakan ya faru ba ki isa ki tafi wajan dangin Daddy ba, don sai abinda ya fada a family suke ɗauka." Ta yi maganar tana tattara kayan Ma'eesha da ta gani a waje, tana saka wa a cikin trolly ɗin ta. "Ba in da zan je." Da mamaki take kallonta. "Da gaske ba in da za ki je?" "Eh haka na ce." "Saboda me?" "Saboda zaman ibada nake yi." Nisa wa ta yi kafin ta ce. " Duk talaucin mijina zan yi haƙuri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi nawa ba duk sunansu mazajen aure, zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito in nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma boye shi, da zama cikin kima da mutunci, shi ne alkhairi, Idan mijina yana bakin ƙoƙarinsa wajen kula da ni, to zan riƙe shi da kyau. Idan na bar shi, ban san wanda zan haɗu da shi ba, ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni ba zan yi haƙuri na zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna rayuwa cikin jin daɗi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buɗa musu. Ba zan fitar da rai daga rabona, arziƙi na Allah ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba a sami duniya ba, insha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira. Zan kula da mijina, danginsa sun zama dangina, zan kama darajata mu rufawa juna asiri. Mu kula da juna cikin mutunci da biyayya.Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farinciki yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ƙauna." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣2️⃣ "Duk talaucin mijina zan yi haƙuri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi nawa ba duk sunansu mazajen aure zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito na nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma ɓoye shi da zama cikin kima da mutunci shi ne alkhairi. Idan mijina yana bakin ƙoƙarinsa wajen kula da ni to zan riƙe shi da kyau, Idan na bar shi, ban san wanda zan haɗu da shi ba. Ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni zan yi haƙuri zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna rayuwa cikin jin daɗi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buɗa musu. Ba zan fitar da rai daga rabona arziƙi na ALLAH ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba'a sami duniya ba, in sha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira. Zan kula da mijina da danginsa sun zama dangina. Zankama darajata mu rufawa juna asiri,zani kula da iyalanki cikin mutunci da biyayya. Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farin ciki yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ƙauna." Gabadaya kalaman ta ɗin sunana kashe wa Nasreen jiki, don haka ta ce. "Kina son sa kena?" "Ba sonsa nake yi ba, ina tausayinsa ne." "Kin tabbata iya tausayi ne kawai?" "Na tabbata don ba na jin komai a zuciyata game da shi, abu ɗaya na sani shi ne tausayinsa da nake ji a zuciyata." "Ke ce abar tausayi ba shi ba." Kafin ta fuskanci Ma'eesha da kyau ta ce. "Tausayi rabin soyayya ce, amma muje zuwa." Ta yi maganar tana ciro wayarta ƙirar iphone a cikin handbag ɗin ta. Sannan ta ce. "Ya maganar cousin brother na, da kika yi wa alƙawarin aure, kin dai san irin son da Abdul yake ma ki, ya ki kowace mace yanzu haka gobe zai dawo daga ƙasar Canada da mararin zuwa ganin ki, kin san kin yi ma sa alkawarin yana dawowa za ki gabatar da shi a wajen Daddy. Kin san ba kasar nan zai ajiye ki ba can ƙasar..." Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga ma ta hannu. "Ya isa haka nan Nasreen, ya za ki zo kina ma ni wani zancen tsohon saurayina bayan kin san cewa yanzu ni matar aure ce, ko mace ɗaya na auren maza biyu ne?" "Ba ta auren maza biyu kuma ina son na ceto rayuwar ki daga halakar da kike ciki ne, ki auri attajiri ɗan attajirai wanda ya mutu a ƙaunar ki wanda zai jiyar dake farin ciki da jin daɗi ba wai in da za ki zauna kika wahala ba. Look at you yadda kika koma a kwana ɗaya duk kin bi kin fita hayyacinki, nan da wata ɗaya ba za ki ganu ba. Na tabbata har yanzu ke budurwa ce ba abinda ya shiga tsakanin ki da wanann makahon don haka ki rabu da..." "Nasreen tashi ki tafi sai anjima." Kallon mamaki take yi ma ta kafin ta ce . "Ma'eesha ni kike kora daga in da kike, duk shaƙuwa da amincin dake tsakaninmu?" "Nasreen matukar kika cigaba da fadar mugayen kalamanki tabbas zan yi ma ki abun da ba ki yi zato ba. Na rungumi kundin ƙaddarata ban yi jayayya da hukuncin Allah ba na dogara gare shi kuma na san ya isar ma ni, kada ki sake yi Mani magana makamancin wannan, idan kuma ba haka ba za mu samu Matsala." "Ki yi hakuri Allah ya huci zuciyarki, me ya yi zafi, duk wanda ya ce zai haɗiye gatari ɓota zan riƙe ma sa." Daga nan suka shiga wata firar daban. Ganin rana ta yi ma'eesha ta ce. "Me zan girka ma ki ?" "Duk abin da ya samu." Tukunya ta wanke ta ɗira girki bayan ta fitar da gas din ta ajiye shi a baranda. Jallop ɗin taliya da dafa ma su wanda ya ji kayan lambu da bisashen kifi. A plate daya ta zuba ma su ta saka fork guda biyu. Ganin Ma'eesha ta dauko pure water ta zuba a plate ya saka Nasreen kai hannu ta taɓa. "Ya na ji ba sanyi?" "To a wane fridge zan saka ya yi sanyi? Ke ni fa duk yadda rayuwa ta zo ma ni haka zan rungume ta." "Bari na fita na nemo don wallahi ba zan iya ba." Tana fadar haka ta miƙe tana ficewa daga ɗakin. Ma'eesha ta rufe abincin tana jiran dawowarta. Zuwa can ta dawo bakinta ɗauke da sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Shigowa ta yi rike da bakin leda ta siyo bottle water guda biyar da maltina guda biyar ma su sanyi. Daga nan suka fara cin abincin. Bayan sun kammala ne sai ma'eesha ta kwashe kayan da aka ɓata ta je ta wanke su tas. Ita kuma Nasreen dama can a gidansu mahaifiyar ta ba ta saka ta aikin komai , sai dai ma su aiki su yi ma ta komai, don haka ba abun da ta iya. Ma'eesha kuwa wani lokacin Mahaifiyarta za ta ce ma su aikin su bari Ma'eesha ta yi saboda mace ce ita gidan wani za ta je wata rana. Bayan ta gama wanke-wanken ne ta saka ruwan ɗumi a wuta ta ke ta yi wanka, da ta fito ne ta ɗauara alwala don yin sallar azahar. Bayan ta idar Nasreen ma ta fito da niyyar yin alwala, yamutse fuska ta ji lokacin da ta ga banɗakin, duk da ba datti amma ita gani take yi ta fi karfin ta shiga wannan banɗaki. Alwala ta yi sannan ga shiga ɗakin, don ko da ta shiga har ma'eesha ta idar da sallah. Nan ta ba ta wuri ita ma ta yi sallar Mayyukan shafawarta ma ma su kanshi da tsada ta shafa. Sannan ta shafa turare sannan ta shirya cikin riga da siket na atamafa, ta yi daurin Ɗankwalinta mai kyau, ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa da man leɓe. "Hmmm yanzu ko kin yi kwalliya aikin banza ne fa, don da wani idanun zai gani ballantana ya yaba ya san cewa kin yi kyau." Tsuke fuska ta yi ganin haka ya saka Nasreen cewa . "Tuba nake yi. Ba zan sake ba." Daga nan ne wayar ma'eesha ya yi kara, bayan ta duba mai kiran ne sai ta katse kafin ta yi danne-danne a wayar kafin ta ajiye wayar gefe. Daga nan suka ci gaba da fira, sai wayar Nasreen ta yi ruri. Gani. Mai kiran ya saka ta yi Murmushi tana cewa . "Barka da warhaka yallaɓai." Daga cikin wayar ta ji muryarsa yana cewa. "Barka dai ya kike ?" "Lafiya lau Alhamdulillah. Tun jiya nake kiran lambar ƙawarki tana ringin ba ta ɗaga wa, sai na sake kira na ji a kashe, yanzu ma na kira ba ta ɗaga ba da na sake kira ina zato ma ta ji blocking ɗina ne. Kuma saboda ita zan shigo ƙasar gobe, da ba don haka ba sai nan da watanni uku zan dawo ƙasar." "Yaya Abdul ka yi haƙuri da Ma'eesaha kawai." "Ban gane ba, ko dai ta samu wani ne ta yar da Ni?" "Hmmm." "Ban gane hmmm ba talk to me." Ya ji maganar cikin wata irin murya mai cike da karaya. "Ma'eesha ta yi aure jiya, don haka ka zauna ƙasar Canada ka gama abun da ya kai ka." "Ke b na wasa da ke kada ki fara yi a yanzu." "Ba karya nake yi ma ka ba, wallahi wallahi da gaske nake yi ta yi aure." Wani sauti ta ji daga cikin wayar kafin ta ji shiru. Cikin sanyin jiki ta ajiye wayar tana mai tausaya wa cousin brother nata. Dan ba ta mance wa sanadin ta ya haɗu da ma'eesha. Wata rana da ya kammala karatun master digiri ɗin sa ya dawo ƙadar ya biyo gaida mahaifiyar Nasreen nan ta ga Ma'eesha ta zo wajan Nasreen ya nuna yana son ta, ita ma ta amince ma sa suka fara soyayya da Abdul. "Wai yana kiran wayarki baya shiga." "Eh na yi blocking ɗin sa ne. Don bai dace na dinga waya da shi ba." "Allah ya kyauta." Da Amin ma'eesha ta amsa ba tare da ta kalle ta ba, kanta a sunkuye da alama tunani take yi. Da misalin karfe huɗu saura kwata ya shigo da sallama a gidan. Gabadaya suka amsa ma sa, Muryar mutane biyu da ya ji ya tabbatar ma sa cewa ma'eesha ta yi baƙuwa. Yana rike da sandarsa ta jagora Da hannu daya ɗaya hannun kuma yana rike da basket da ma su gyaran takalmin ke yawo da shi. Ya ɗaura wani bakin leda a saman kayan aikin." "Sannu da dawowa." "Yauwa Ma'eesha sannu da gida. Baƙuwa kika yi ne?" "Eh ƙawata ce sunan ta Nasreen." Nasreen ta zuba ma sa idanu tana ƙare ma sa kallo. Tabbas makanta ce kawai cikas ɗin sa sai kuma talauci domin da ace na makaho ba ne kuma ba talaka ba ne za ta iya cewa ƙawarta ta yi mijin nuna wa Sa'a. Domin kuwa ya hadu iya haɗuwa ta ko ina baya da cikas, don ba za'a hada shi da Abdul ba, domin ya yi ma sa zarra nesa ba kusa ba ya fi shi duk wasu qualities da macen da ta san kanta za ta bukata daga wajen ɗa namiji. Taɓa ta da Ma'eesha ta yi ne ya saka ta dawo duniyar tunanin da ta lula. Jin muryarsa mai amo ta yi yana cewa. "Sannu da zuwa ina wuni." "Lafiya lau ya ƙokar" "Alhamdulillah." Ta amsa tana ɗauke kai daga kallonsa. Ma'eesaha ta karbi kayan hannunsa ta shiga cikin ɗakin, da lalube shi ma ya shiga ya zauna jan tabarmar da ya ji ya taka. "Sannu da dawowa ya rana?" "Sannu da imani Ma'eesaha, ya hakuri da rayuwa?" "Alhamdulillah." "Ba ri na kawo ma ka abinci ko?" "A'a sallah zan yi . Sai na dawo masallaci." Ya yi maganar yana ciro ledar da ya dawo da shi. "Ga tsarabar yalo na kawo ma ki ko za ki iya ci?" "To na gode Allah ya kara budi." Cike da jin dadi ya amsa duk da ya san ba cimar su ba ne, ba Apple da ta saba ci ba ne. Tashi ya yi tana cewa. "Na ba ka buta ne?" "Eh na gode." Suka fito ta miƙa ma sa buta cike da ruwa. Ya sa ya nufi banɗaki ya shiga. Bayan ta fito ne ta damu wuri a gefe ya yi alwala ya fice zuwa masallaci. Ledar yalon ta buɗe ta zuba a mazubi ta wanke, sannan ta dawo da zauna kusa da Nasreen tana cewa. "Ƙawata ko kin iya ci?" Taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Ai ko ke ba ki iya ci ba ballantana ni." Daga haka ta cigaba da danne-danne a wayarta. Ma'eesha ba ta sake bi ta kanta ba ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki. Ɗaci da ta ji ne ya saka ta ɗan yamutse fuska sannan ta haɗiye. Nasreen na kallona ta gefen idanu ba ta ce komai ba, zuwa can ta mike tana cewa. "Zan tafi gida sai wani lokacin." "To na gode ki gaida su Mom don Allah." "Za ta ji." "Ba za ki tsaya ki yi sallar la'asar ba." "Idan na je gida zan yi." Tana tsaye bakin ƙofar tana kallon Nasreen har sai da ya ga tashin motarta sannan ta saki kofar ta koma ciki. Buta ta ɗauka ta shiga banɗaki ta yi tsarki sannan ta fito ta daura alwala. Tana alwala tana jin muryarsa mai amo yana rera karatun sallah a masallacin, da alama shi ne liman ɗin. Bayan ta idar da alwalar ta shiga dakin ta gabatar da sallar la'asar. Addu'o'i ta yi ta yi azkar na yamma daga nan ta kwanta a saman sallayar. Bayan kamar mintuna talatin ya shigo gidan da sallama. Da lalube ya kai bakin kofar ya yi sallama ta amsa tana tashi zaune. In da ya saba zama ya laluba wato kan tabarma ya zauna tare da Bismillah. "Ƙawarki ta tafi ne?" "Eh ya tafi." "Allah sarki, Allah ya kai ta gida lafiya." Maltina da ruwa ta ajiye gabansa ta ce. ,Ga Maltina nan da ruwa na ajiye ma ka, bari na kawo abinci." "To na gode amma ki bar abincin nan, sai zuwa dare." "Me ka ci da rana." "Ba komai dama ni ban saba cin abinci sau uku ba, sau biyu nake ci wata rana ma idan ban samu sau biyu ba idan na ci na rana zuwa dare ruwa kawai zan sha na kwanta." "Wanan ya wuce yanzu akwai sai ka ci idan babu ne sai ka san cewa babu ka yi hakuri. " "Ba na jin yunwa bari na sha wannan kawai kada ku damu." Daga nan ba ta sake magana ba ta koma ta kwanta a saman sallayar. "Bari n je na yi wanka." "Okay bari na zuba ma ka ruwa na kai ma ka." "Don Allah ki huta na gode, zan iya ɗiba da kaina, ai na gama sanin kan gidan, bayan kin ke kasuwa ai har fita na yi na dauko jakar kayana. Na san komai na gidan nan, ba na bukatar ki yi ma ni wani aiki sai dai ni na ji ma ki." "Ai lada nake nema kuma aljannata nake nema." "In dai Aljanna ce in sha Allah za ki shige ta Ma'eesha, Allah ya yia ki albarka ." Da Amin ta amsa ta koma ta kwanta. Bayan ya ɗebi ruwa ya kai banɗaki ya dawo wajen kayansa zai ɗauka, kasancewar ya san shi ba ya gani ita kuma tana ganinsa ba zai iya cire kaya a gabanta ko ya canza ba, don haka ya dauki kayan da zai saka da sabulu ya fita ya je banɗaki da su. Bayan ya yi wanaka a banɗaki ya goge jikinsa ya sauka kaya ya fito bayan ya zuba wanda ya cire a cikin bokitin wankan . Ruwa ya ɗeba ya sa ido ya wanke kayan ya shanya. Sannan ya koma dakin, ta daga kai ta kalle shi ta ga ya sauya kaya. "Ina kayan da kika cire na wanke ma ki?" "Ka bar shi na gode." Duk da dama tana tunanin wanki na ba ta wuya, don ba ta saba ba sai dai a wanke ma ta, ma su wanki ke wanke ma ta. Ko underwears ɗinta a warahing machine take wanke wa . Idan na cire, yau dai ta wanke underwears ɗinta banɗaki da ta cire bayan ta ji wanka. Lalube ya fara yi ganin ya matsa ta ce ba basket da ta zuba nan bayansa, ta dauka ta fita bayan ta bashi sabulu, ya je ya wanke ma ta su y shanya ma ta kayan. _Sidra_farkawar ta kenan daga barci ta farka da kuka, sakamakon mafarkin da ta ji wai an kai Nadra gidan Fahad da ya gina da sunanta, irin tsarin da take so, kuma ga kayan ɗaki da kayan kitchen ɗin da aka je aka zuba da sunan ta sun zama mallakin Nadra. Da kanta ta nuna wa Umma irin funitures da take so aka yi order daga ƙasar waje, sannan Abba ya ba ta kudi je Dubai ta siyo irin kayan kitchen da take so, yanzu shi ke nan an mallaka wa Nadra kayan kitchen ɗin ta da kayan ɗakinta da kuma mijinta.? "No ba zai yiwu ba wallahi, na san wannan duk aikin Ammi ce ita ce za ta ziga Abba akan ya ƙwace komai nawa ya ba Nadra. Dama ba ta ƙauna ta kullun cikin zagina take yi wai ni ba na da kunya da tarbiyya kullum Nadra ce ya yarinyar kwarai a wajen kowa wannan karon zan nuna kowa rashin tarbiyyar da suke kira. Mani za su gan shi muraran kuma ziryan, wallahi ba zan yi biyu babu ba, ba zan rasa burina da nake da shi ba sannan kuma na rasa mijin da nake so ba, ba zan yi biyu babu ba wallahi sai dai ayi mutuwar kasko." "Ba ni wayarki.." Ta yi maganar tana kallon Sady baby, ta mika ma ma ta wayar ta shiga TikTok account ɗin abokin Fahad Sadik. Na ci karo da videos ɗin bikin Fahda da Nadra. Da in da yake ba ta cake daga bakinsa zuwa na ta, rintse idanunta ta yi tare da kokarin cilli da wayar sai Sady baby ta yi saurin karbe wayarta. Don ta san idan ran Sidra ya ɓaci idanunta rufe wa yake yi. Ta fama hannunta dake zubar da jini tana cewa. "Wallahi ba zan haƙura da Fahad ba, domin nawa ne shi ni kaɗai, ruwa da iska ba abinda zai ma ni shamaki da abun so na ciki kuwa har da ita Nadra, zan iya aikata ma ta komai don na mallake sa." Kallon ta da tsoro Sady baby take yi kafin ta ce. "Ko da hakan na nufin bakin cikin ƙanwarki ce?" "Ko da hakan na nufin mutuwarta ne." Ganin yadda take zubar da jini ya saka Sady baby kokarin taimaka ma ta, amma ta fisge hannunta tana cewa . "Sai na aikata abinda ke raina in dai akan Fahad ne?" "Na sani Sidra za ki iya, ko me kika ce za ki aikata na san za ki iya. Amma ba ki ga yadda kike zubar da jini ba ne?" *Maman Ihsan ce.*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣3️⃣ "Na sani Sidra za ki iya, ko me kika ce za ki aikata na san za ki iya. Amma ba ki ga yadda kike zubar da jini ba ne?" "Ban damu da jinin ba, kuma bam ji zafin hakan ba, amma kuma abinda aka yi ma ni na raba ni da Fahad shi ne ya fi yi ma ni zafi." Nan ta dinga rarrashinta sosai da ba ta baki har ta hakura ta yi shiru da surutun nata. "Ba ni wayata." "Me za ki yi da ita, bai kamata ki kunna waya yanzu ba." "Ina bukatar jin Muryar Fahad." "Kada ki kira shi da wayarki, domin kuwa ba mu san abun da za mu ce ya faru da ke ba har kika bar gida. Ki kira shi da wata lambar don gudun tonuwar asiri ki." Ta yi magana tana mika ma ta wata karamar waya a hannun ta. Karba ta yi ta saka lambar wayar Fahad kasancewar tana da lambar wayarsa a cikin kanta . _Fahad_ Driving yake yi zuciyarsa babu daɗi, sam bai taɓa kawo ranar nan da za ta zo ba wai zai tare a sabon gidansa ba tare da Sidra ba. Yana driving ɗin kamar wanda zai ɓalle sitiyarin motar. Saboda yadda ya rike shi da ƙarfi, har yanzu ya kasa gane dalilin da ya saka Sidra ta aikata haka bayan ya san tana tsananin son sa. Wayarsa dake gefe ya kalla da idanunsa da suka canza launi zuwa ja ya yi, ganin baƙuwar lamba ce ya saka bai ɗauka ba. Sidra dake jiran ya dauka ko ta ji muryarsa ta cire wayar daga kunnenta don ta san ba lallai ne dama ya dauka ba. Sai da ta yi masa 3 missed call bai ɗaga ba, sai a na huɗun ne ya ɗaga wayar na ajiye ya yi picking call ɗin ba tare da ya yi magana ba, yana jiran me kiran ya yi magana. Jin shiru ya katse wayar don ita ma Sidra ta ƙi ta yi magana. Dama shi haka yake in dai bai san me kira ba to ba zai yi magana ba sai dai ya katse kiran wayar. Hawaye ne suka wanke ma ta fuska ta juya ta kalli ƙanwarta ta ce. "Kila yana can tare da ƙanwata ko? Me yiwuwa ma yana nanne da ita? Kuma zai iya yin sex da ita ko?" Sai a lokacin Sady baby ta yi magana ta ce. "To me zai hana shi yin sex da ita tunda matarsa mallakinsa ce kuma an kai ma sa ita har gida, ai ba kowane lafiyayyen namiji zai iya kau da kai a daren farkonsa ya kyale matarsa ba." Kuka ta saka tana dora hannu aka . "Wayyo na shiga uku na lalace, kai ba zai yiwu ba na san ba zai taba son ta ba, ba na fata wata alaƙa ta autatayya ta shiga tsakaninsa da Nadra domin ba abinda zai yi da ita ni yake so ba ita ba." A gaban tangamemen gate ɗin gidansa ya yi parking ya tsaya yana danna horn. Security ya leƙo ganin maigidan ne ya saka ya koma da sauri ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya shiga da matarsa. Parking lot ya nufa ya yi parking, sai da ya kwashe mintuna ashirin ba a cikin motar bai fito ba. Ganin shiru ya saka security biyu da ke harabar gidan ɗaya ya karasa wajen motar yana knocking glass ɗin. A hankali Fahad ya dago da kansa da ya kwantar a sitiyarin motar sannan ya zuge glass ɗin motar. "What happened?" "Am sorry sir, are you okay?" "Am okay." Ya faɗa yana kokarin fitowa daga cikin motar yayin da security ya bar wajen. Don sun ga ya ɗauki lokaci bai fito ba ne ya saka suka fara tunanin ko wata matsala ce ko bai da lafiya ne. "Wayoyinsa a hannunsa ya nufi main door ya tura ya yi sallama ciki-ciki wanda ko kawai wani a falon ba jin sallamar zai yi ba. Ƙamshin turaren wuta da room freshener spray suka yi ma sa sallama. Ba tare da ya kalli ko ina ba ya nufi upstairs ɗin. A hankali ya tura ƙofar falonsa ya shiga, wayoyinsa ya ajiye saman Centre table sannan ya zauna a daya daga cikin lafiyayyun kujerar da suka yi Falon ƙawanya. Jinginar da bayansa ya yi da jikin kujerar. Wayarsa ce ta soma ruri ya duba ya ga Mama ce ke kiransa. Sai da ya sauke ajiyar sanan ya daga kiran wayar. "Mama." Ya fada cikin shagwaɓa murmushi ta yi Murmushi irin tasu ta manya ta ce. "Ka isa gidan lafiya?" "Uhm." Ya faɗa kamar ba ya so yin magana. "Shagwabar ce ta motsa ko?" Bai ce komai ba idanunsa a lumshe yana rike da wayar. "Ina Nadra take." "Ban sani ba amma ina tunanin tana ɗakinta." "Kai kana ina?" "Ina ɗakina." "Me za ka yi yanzu." "Zan yi wanka ne na kwanta." "Fahad." "Na'am Mama." "Yanzu ko dabba ce aka kai ma ka gida aka ajiye ta ai ka duba lafiyar ta ko?" "Tana lafiya Mama." "Ka je ka haɗa ni da ita a waya. Nan da mintuna biyar zan kira ka." Tana fadar haka ta katse kiran wayar. Fuska babu walwala ya mike ya nufi ƙofar fita, dama kofar falonsa da kofar falonta suna kallon juna ne. Hannunsa ya daura saman handle ɗin kofar ya buɗe ya shiga da sallama ciki-ciki. Ba kowa a falon sai kanshi da sanyin A.C dake tashi . Bedroom ɗin ta ya nufa ya shiga da sallama. Tana kwance a saman gado ta kudundune mijinta wuri ɗaya sai ajiyar zuciya take sauke wa. Da alama ta ci kuka har ta gaji. Ƙamshin turarensa ne ta ji ya saka ta ɗago kanta ta zuba ma sa kumburarrun idanunta da suka yi ma ta nauyi saboda tsabar kuka. Shi ma idanunsa ya a zuba ma ta ba tare da ya yi magana ba. A hankali ta mayar da idanunta ga kanta dake bala'in sara ma ta da ciwo. Wayarsa ce ta yi ruri yana ganin Mama ce ya karasa bakin gadon ya miƙa ma ta wayar bayan ya yi picking call ɗin ya saka a handsfree. "Assalamu alaikum." Cikin disashshiyar muryarta da ta disashe da kuka ta amsa da. "Wa'alaiki Salam warahmatullah. Ina wuni ." Duk da ba ta san waye ke magana ba amma zuciyarta ta ba ta cewa " Mahaifiyarsa ce . "Wa'alaiki Salam warahmatullah Nadra ya kike?" "Alhamdulillah." "Daga jin muryarki kin sha kuka sosai, ki yi hakuri kin ji komai muƙaddari ne daga Allah, Fahad shi ne mijin ki ki yi hakuri ki zauna da shi a matsayin mijin ki, idan ya yi ma ki wani abun da ba daidai ba ki kira ni ki faɗa ma ni, ni ce mahaifiyar sa zan dauki mataki akansa kin ji Daughter." Cikin Muryar kuka ta ce. "To Mama." "Yauwa Allah ya yi ma ki albarka kin ji." "Amin Mama." Ta fada tana goge hawayen da ke ma ta sintiri a idanunta. "Zan ce ya tura ma ni lambarki sai ya tura ma za mu yi magana da safe." "To Mama." "Kin ci abinci kuwa?" "Ba na jin yunwa." Tun karfe nawa kika ci a abinci?" "Tun da rana." "To yanzu ki samu ki ci abinci zai kawo ma ki. Sai da safe ko?" Daga nan ta mikawa wa Fahad wayar ya karɓa yana karawa kunnensa. Kafin ya yi magana ya ji ta ce. "Ka siya ma ta kaza ne?" "Wace kaza kuma Mama?" "Ka fita ka je ka nemo kaza ka kawo ma ta ba ta ci abinci ba." Tana fadar haka ta kashe wayarta. Jiki ba karfi ya fice daga dakin ya koma nasa ɗakin ba tare da ya sake kallon in da take ba. Key ɗin iya ɗauka ya fida daga cikin gidan ransa babu dad'i. In da ake gashin kaji ya tsaya. Ba tare da ya fito daga cikin motar ba ya yi horn wanda ya janyo hankalin daya daga cikin ma su aiki a wajen. Ya ƙaraso wajen daidai lokacin da wayar Fahad ta sake ringing. Ya yi picking still bai yi magana ba don ya san lambar ɗazu ce. "Ka kawo mun kaza guda daya da fresh milk guda biyu." Maganar sa ya sauka a cikin kunnen Sidra dake rike da wayar tana jiran ya yi picking. Katse wayar ta yi tana fashewa da kuka. "Wai fa kaza ya zo siye da fresh milk, ita zai kai wa su ci kenan? Kazar da kowane ango ke siya wa matarsa a daren farkonsu shi ne ya siya ma ta. Kazar ba shi da idan ta ci sai ta biya kenan fa." Lokaci daya ta rikice da kuka wanda hakan ya saka Sady baby rarrashinta. "Ba zai yiwu ba dole na bar garin nan gobe na koma Kaduna, duk abinda zai faru ya faru amma sai Fahad Majidaɗi ya dawo mallakina." _Makaho_ Bayan ya idar da sallar isha'i daga masallaci gida ya nufa. Don karfe tara ne yanzu, sai sa ya tsaya ya yi karatun Alkur'ani mai girma. Da sallama ya tura kofar fale-falen gidan ya shiga Daidai lokacin tana fitowa daga wanka daga ita sai towel da ta ɗaura rabin cinyarsa a waje suke. Sai ƙamshin shower gel din ta take yi. Amsa ma sa sallama ya ji ta yi tana ma sa Barka da shigowa. Ya amsa yana lalube har ya ji ya kawo bakin kofar sannan ya shiga da sallama. Lokacin akwai wutar nepa, Tsane ruwan jikinta ta ke yi ganin shi makaho ne ba gani yake yi ba ya sa ta warware towel ɗin ta shafa man shafawar ta ta shafa. Zama ya yi kan tabarmar da ya kan zauna , har ta gama shafar ta ta saka turaren ta ma su kamshi sannan ta saka kayan barci ta . "Ka yi hakuri ina shirya wa ne." "Ba komai Ma'eesha." "Na ga abincin nan ya rage ne ya sa ban yi sabon girki ba kada ya zama ɓarna." "Kada ki damu Ma'eesha ba wani yunwa nake ji b." "Kar ka ce haka tun breakfast ba ka ci komai ba, ta ya mutum zai yi ta zama da yinwa ana rayuwa da yunwa?" Murmushi ya yi tare da cewa. "Ba iya abinci muke buƙata don mu rayu ba, muna buƙatar mu riƙa ji a ranmu cewa akwai wanda yake sonmu, yake fahimtarmu, yake taya mu alhini a lokacin damuwa, yake fahimtar maganar da ke ranmu a lokacin da muka yi shiru, yake fahimtar damuwarmu a lokacin da muka rufe ta da murmushi. Mutum zai iya jure talauci, ya yi haƙuri da yunwa, amma ya kasa jure rashin masoyi mai kulawa. Kalma ɗaya mai daɗi da masoyinka zai gaya maka za ta iya haska tsakiyar zuciyarka da sanya maka farin ciki da natsuwa a lokacin da kake fuskantar ƙalubalen rayuwa." Ƙwalla ta goge yayin da take ƙokarin ajiye ma sa abincin a gabansa. Sannan ta kawo ruwa da Maltina ta ajiye ma sa. Ya fara cin abincin kenan suka ji sallama daga tsakar. Amsa wa ta yi sannan ta janyo hijabi ta saka daidai lokacin da ake ƙara bude murya an rangaɗa wata uwar sallamar. _Nadra_ Yana fita daga dakin ta saka sabon kuka Har ya dawo ba ta daina ba . Cikin kuka take cewa. "Sidra ina kika tafi kika bar ni a muhallin da bai dace da ni ba. Ke kika dace kina nan don Allah ki dawo zan tafi na bar ma ki komai naki ne, wannan gidan gidan tamkar gidan aro ne a gare ni, ki dawo na bar ma ki gidanki mijin ki komai na ki ce ni ba mazauniya ba ce." Ƙamshin turarensa da ta ji ya haifar ma ta da faɗuwar gaba. Dara-daran idanunta da suka kumbura ta kalle shi da su Wani kallo yake yi ma ta wanda ya sa ta faduwar gaba. *Ku yi hakuri da wannan*🙏🏻 *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣4️⃣ Wani kallo yake yi ma ta wanda ya sa ta faɗuwar gaba. Da sauri ta ɗauke idanunta daga kallonsa ta mayar kan yatsun hannunta tana wasa da su. A hankali ya ƙaraso gaban gadon hannunsa rike da faranti da ya ɗora rabin kaza akai, sai dayan hannun nasa wanda ya rike robar fresh milk da glass cup. "Ki zauna da kyau." Tsintar kanta ta yi da bin Umarninsa. Bayan ta tashi daga kwancen da take ta yi kanta a ƙasa har lokacin ba ta daina hawaye ba. Sai lulluɓe jikinta da mayafinta take yi. "Ga shi nan ki cinye shi, ko na kawo ma ki tea ne?" Ma ta girgiza ma sa alamar alamar a'a. _Sidra_ Bayan ya ci kuka ta ƙoshi ne sai ta kalli Sady baby tana cewa. "Yanzu dama namiji baya da kunya?" "Tofah, me aka yi ne?" "Wallahi In fada ma ki siyen kaza ya tafi kazar amarci wanda a sani na idan ta ci kazar nan fa kin san me zai biyo baya." "To sai aka ce ma ko sai zai yi abu da ita ne zai siya ma ta kaza?" "Yau ne fa daren farkonsu hakan yana nufin yana da lokacin ta kenan, ban taɓa tunanin hakan daga wurin Fahad Majidaɗi ba. A baya fa shi da kansa idan kika fahimce shi za ki ga kamar ya tashi Nadra ce. Musamman da yake ganinta kullum cikin dogon hijab da yadda take sunkuyar da kai sai yake ce ma me ya sa ƙanwata take yin abu kamar munafuka ce shi baya son haka. Sai na ce ma sa wai kunya ce nan. A lokacin ya ce baya son mace mai kunya haka ba zai iya auren duk mace mai wannan yanayin ba, amma da ke namiji munafiki ne har da zuwa siyen kazar amarci." Hawaye ma su zafi ta goge tana cewa "Ba zan zauna a garin nan ba, dole na tafi na koma Kaduna gobe, na tari yaƙin dake gabana." "Ba za ki hakura da Fahad ɗin nan ba kuwa Sid?" "Ba zan zan iya ba Sady baby ba zan iya ba ƙarya da ciwo. Ba abinda ya ragu cikin son da nake ma sa. Gajeren murmushi Sady baby ta yi kafin ta ce. "Sai dai addu'ar da za ki yi kada wani abu na autatayya ya shiga tsakaninsa da Nadra. Domin idan wani abu ya shiga har ya yi sex da ita a wannan daren komai zai lalace ma ki, domin hakan na nufin sun zama abu ɗaya ne shi da ita. Musamman idan ya kasance ita virgin ce, to saboda samun ta da cikakken budurcin ta ko ya ya ne sai ya ga darajarga da ƙimar ta a idanunsa. Kuma ba zai taba mance wannan halaccin nata ba, ke ɗaiɗaikun maza ne fa suke sakaci da irin wannan mace domin shi ne saka ta yi daraja a idanunsa. Amma idan ya ga cewa ya aure ki ya fahimci ke ba virgin ba ce wallahi duk son da yake yi ma ki sai ya ragu mutuncin ki zai zube a idanunsa Sosa da sosai." Ta yi maganar tana kallon Sidra wacce ta yi mutuwar tsaye kamar ba ta jin ta . "Shi kenan komai zai lalace na tabbata Nadra virgin ce, saboda ita mai tsoron Allah ce, mai horo da bin Umarninsa da hani ga saɓonsa, ba za ta taba bari a raba ta da mutuncin ta ƴa mace ba. Infac ma ba in da take zuwa daga guda sai makaranta, ko kawaye bata da aji sai wata yarinya daya A'isha Humaira. Ke ko za mu fita da ita sai da dalili ba iri na ba ce mai yawan tsiya ko satar hanya ina ji na fita, kuma idan na yi satar hanya na fita duk da tana ba ni shawara na daina amma duk da haka tama rufa ma ni asiri wajan iyayen mu ta ce ina ɗaki ina barci." Goge hawaye ta yi ta ce. "Bari na sake kiransa ." "Kada ki kira shi ki ji abun da zai tayar ma ki da hankali." Ba ta saurare ta ba ta kira lambar Fahad Majidaɗi. _Fahad_ Shigowarsa ɗakin kenan ya miƙa wa Nadra ruwan shayin da ya haɗo ma ta duk da ta ce ba ta so. Miƙa ma ta shayin ya yi daidai lokacin da wayarsa ta so ma ruri, sai ya duba still numbern da aka kira shi da ita ne. Ya ɗaga daidai lokacin da da Nadra ya kai kofin da ke hannunta bakinta ta kurɓi tea, jin zafi ya sa ta saki wata ƴar ƙara wanda ya sa Fahad ɗan rikicewa ya ce. "Am sorry na yi ma ki shi da zafi ko?" Nan ma aka yi katarj da Sidra ta ji su kuma sai zuciya ta ake kitsa ma ta wani abun daban. Don haka sai ta katse kiran wayar zuciyar ta na tafarfasa sosai da sosai. Kuka da nadamar barin gida ya zo ma ta lokaci guda, ta kalli Sady baby ta ce. "Ba na faɗa ma ki tun da ya je siyen kazar kazar nan na san me hakan ke nufi . Yanzu fa ihunta na ji ta yi tana ƙara shi ma daga jin muryarsa a rikice yake har yana ce ma ta sorry ya yi ma ta shi da zafi ko?" Ta ɗora hannu akai tana kuka mai tsuma zuciya. Allah wadaran halin maza wallahi, Nadra karamar yarinya ce fa dududu shekarunta 18 amma shi ne har ba zai iya kawar da kai akanta ba. Ai ba sa'ar aurensa ba ce. Don ko da aka haife ni sai da Ummanmu ta sake haifar yara guda biyu suna mutawa kafin aka haife ta ita ce ta rayu ai ko kusa da ni ba ta kai ba. Don na ba ta shekaru bakwai a duniya. Don idan ba ki manta ba yanzu ina 22 years ne ita kuma yanzu take 18 ai ba kusa ni da ita. Kuma wallahi ba ta isa ta raba ni da Fahad ba shi ma munafiki ya ba ni mamaki." Nan da dinga sambatu ita kadai a ba wanda ya tanka ma ta. Kafin ta kalli Sady baby ta ce. "Za ki iya saka diraba ya mayar da ni Kaduna gobe da safe?" "Eh amma ki bari zai kai ni wani waje da safe zuwa karfe goma za mu dawo na san kin shirya zuwa lokacin ko?" "Har karfe goma?" "To ya za'a yi fitan nawa ya zama dole ne, kuma idan ya tafi kai ki da motar ba yadda zan yi." Jinjina kai ta uku tana cewa. "Shi ke nan zan jira karfe gomar." "Yauwa ƙawar arziki, kaya ce da na yi order matar ta kira zan je na karɓa shi ya sa, amma muna dawowa zai kai ki har gida." Godiya ta yi ma ta sannan ta Sady baby ta fice ta bar ma ta dakin bayan ta karbi wayarta. _Ma'eesha_ Tana saka hijabi akan kayan barcin na ta ta fitq waje don duba mai sallama. Don Muryar mace ce ta ji ba ta namiji ba. Ba kowa ba ce fa ce Larai Dillaliya wacce makaho ya fara kai Ma'eesha gidan ta kasa zama ciki ta ce za ta kama haya. Ita dai Ma'eesaha ba ta gane ya ba , amma Larai sai washe baki take yi tana jin daɗi. "Sannu da zuwa." "Yauwa sannu amaryar Khalifa ya kuke ya Khalifa?" Jin haka ya saka Ma'eesha ta yi tunanin cewa. Ko Larai dangin Khalifa ne. Don haka da fara'a ta ce. "Bismillah shigo ciki ma na." Ta yi gaba Larai na bin bayanta suka shiga ɗakin. Da sallama suka shiga Larai Dillaliya ta kalli gaban Khalifa makaho ta Maltina da bottle water. "Ma sha Allah." Sannan ta kare wa ɗakin kallo ta ga komai sabo ne ba tsoho ba, sai ta fara tunanin dama akwai canji a hannun yarinyar kenan. Sai dai ba ta ji dadin haka ba, don ta fahimci yrinyar ta fiye kayan bukata. Ta dauka ba su da komai ne sai ta ce ma ta tana siyen kayan saka wa da takalmomi da handbag ta siye a wulaƙance don ta fahimci komai na yarinyar mai tsada ne kuma kamar tana cikin matsala ko nawa aka ba ta za ta karba. Muryar Khalifa ta ji yana cewa. "Ina wuni?" Sai a lokacin ta daina kalle-kallen da take yi ta ce. "Lafiya lau Khalifa ya amarya?" "Alhamdulillah." Daga nan ba wanda ya sake magana. Ma'eesha ce ya mike ta kawo ma ta ruwa ta ajiye ma ta. Ta dauki plate za ta zuba ma ta abinci kenan sai ta ji Muryar Makaho na ce wa. "Baiwar Allah lafiya a daren nan ko?" Don sarai da ya ji muryar ta ya gane ta. "Am dama na ce bari n zo ne don na ga kamar za ku bukaci kuɗi sai na siyen abun da amarya ke da su, kamar ko akwati haka da kayan saka wa da takalmomi da handbags da sarƙa da ƴan kunne da sarƙa duk...," Tsawar da Ma'eesha ta daka ma ta ne ya ba ta mamaki ta mike da sauri . "Tashi ki fita!" "Ban gane ba daga taimako?* "Kin ga jin zo wajen ki neman taimako ne?" "Ba ku zo b amma na san sai kun zo wata rana, sai kun zo wata rana kuna nema ma da kanku. Don wannan makahon mijin naki Makaho ba ya iya ɗaukar ɗawainiyar ki zai yi ba. Don Allah na tuba ai ba na tunanin cewa a yini ɗaya yana haɗa Naira ɗari biyar. Tun da kuma ha ba kowa zai ba wa maka..." "Mallama tashi ki fita kafin na ba ki mamaki a gidan nan, dama abun da ya kawo ki kena" Jiki ne rawa Larai ta mike ta bar gidan. Ranta ya ɓaci kasa magana, illa iya kai ta kawar da komai ta yi shirin. Bayan ta yi shirin kwanciya barci duk da tana jin zafi haka dai ta rufe ƙofar ɗakin. Ba zai yiwu ma ta a ce wa makaho ya zo su kwanta tare ba, Hakazalika ba ta jin ta yi ma sa adalci idan ta bar shi ya kwanta ƙasa kan tabarma. Don haka sai ta rasa yadda za ta yi don ita ma ba za ta iya kwanciyar a ƙasa ba. Amma sai ta yanke shawarar bari shi makahon ya bi zaɓin abun da ke ransa. Idan ya hau katifar ya kwanta kusa da ita ba za ta hana shi ba, don haka ta kalle shi yana zaune kamar wanda yake tunanin wani abu ta ce . "Ni zan yi barci sai da safe." "Jinjina kai ya yi yana cewa. "Allah ya tashe mu lafiya." Da Amin ta amsa ma sa sannan ta yi addu'ar kwanciya barci ta kwanta abun ta. Kashe hasken wayarta ta yi don dama shi ta kunna. Duhu ya gauraye ɗakin . Sai dai ta kasa barci kwata-kwata sakamakon zafin da ta ji ya addabe ta . Don ta saba kwanciya cikin sanyin A.C nan kuma zafi da sauro ne suke addabar ta suna kuka. Sosai ta rikice tana ta mutsu mutsu. Jin motsinta ya yi yawa baya. Kamar awa ɗaya da kwanciyar ta ya saka ya kira sunanta. "Ma'eesha lafiya, ko zafin ne ke damunki" Kamar za ta yi kuka ta ce. "Na kasa barci wallahi." "Kamar jira yake yi ya taso da lalube ya ƙaraso wajan katifar yana cewa. "Ki yi hakuri na yi ma ki fifita kin ji?" Yana nan zaune gefen katifar ya ce ta bashi abun fifita. Tashi ta yi ta je ta nemo ma sa ta kawo ma sa bayan ta kunna fitilar wayar. Tama ba shi ta kashe ta kwanta. Daga nan ya dinga yi ma ta fifita ba daɗe wa barci ya yi awon gaba da ita. Shi kuma yana nan zaune har ya soma gyangyaɗi, sakamakon rashin barci jiya da bai yi ba ya kwana juya yana ma ta fifita ga yau bai yi ba har dare ya raba yana ma ta fifita. Idan ya daina take cikin barci za ta ji zafi na shig busowo za ta fara motsawa shi kuma da ya ji motsi zai cigaba. Farkawa ta yi ta ga shi zaune yana yi ma ta aikin fifita. Ta tuna haka jiya ya kwana zaune yana ma ya fifita. Sai ta ce. "Am ka bari ya isa haka nan na gode." "Ba za ki iya ba." "Sanyi nake ji ka bar shi kawai." Sanyi a yanzu ko ba ku da lafiya ne?" "Lafiya lau nake amma na gaji da fifitar ne ya na sa na ji sanyi." Daga haka ya daina ita kuma ta kudundune cikin sani har kabta da ƙafarta na ciki. Ta rasa yadda za ta yi tausayinsa ya sa ce ma sa haka amma ba wai don tana jin sanyin ba. Tana addu'ar a ranta Allah zai kawo ma ta mafita. *Wace ce Ma'eesha?* Ma'eesha Ibrahim Khalil, shi ne cikakken sunanta. Ibrahim Khalil shi ne cikakken sunan mahaifinta. Mahaifiyarta kuma sunanta Saliha. Ibrahim ya haɗu da Saliha ne a gidauniyar tallafawa marayu wanda mahaifinsa Shamsuddin ke daukar kusan rabin ɗawainiyar marayun. Duk lokacin da Alhaji Shamsu kan shigo gidan marayun tare da Ɗansa Ibrahim Khalil yake zuwa. Ya kan taya mahaifinsa raba wa marayun kaya da sauran abun bukatunsu. Wanda anan ne Ibrahim Khalil ya ga Saliha ya ji yana son ta. Lokacin da ya sanar wa mahaifinsa zancen auren Saliha mahaifinsa ya nuna jin fadinsa domin shi mutum ne mai son marayu da tausaya ma su. Sai dai Ibrahim Khalil ya fuskanci ƙalubale daga wajan mahaifiyarsa kan rashin amincewar ta da auren Saliha. Saboda an yi bincike ba'a san daga ina ta fito ba wai ba ta sani ba ma ko ba ƴar Sunnah ba ce. Wata kila cikin shege aka haife ta ta aka jefar da ita. Sai da Mahaifin Khalil ya tsaya tsayin daka sannan aka yi auren Ibrahim Khalil da Saliha. Ta tare a gidansa dake nan cikin garin Kano. Zama suke yi cikin soyayya da ƙaunar juna. Yana son ta saboda nagartar ta, don tana da hakura juriya da hangen nesa. Alhaji Shamsuddin yana son sirikar tasa ganin yadda Ɗansa ke son ta, sai sai tsakanin ta da uwar mijinta ce kadaran kadahan. Ba ta nuna ma ta soyayya kuma ba ta nuna mata tsana. Bayan shekaru ɗaya Allah ya albarka ce su da haihuwar ƴa mace. Ranar ya kasance ranar farin ciki ne a gare su. Farin ciki a wajen Ibrahim Khalil da Saliha ba'a magana. Haka ma Alhaji Shamsuddin, ya yi farin ciki sosai, ɓangaren Hajiya A'isha ma ta yi farin ciki sosai duk da ba ƙaunar Ma'eesha take yi ba amma tana ƙaunar Ma'eesha. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ma'eesha na girma har ta isa shiga makaranta aka sanya ta makarantar kuɗi. Sai sai duk weekend akan kai ta gidan kakannin ta ta yi hutu. Don Hajiya takwarar Ma'eesha ce ta tsara haka duk weekend sai an kai ma ta takwarar ta can gidanta ta yi ma ta kwana biyu. Idan kuma ana cikin hutu can take ma ta weekends. Haka rayuwa ta cigaban da tafiya har Allah ya raya Ma'eesha ta kammala primary school. Kuma har lokacin iyayen ta ba su saka samin wata haihuwar ba. Sai dai arzikin Ibrahim Khalil ya kara bunƙasa, don kasuwancinsa saidai yake samun cigaba. Har wata rana Saliha ta samu Ibrahim Khalil da zancen za ta fara kasuwanci ita ma. Sai ya nuna ma ta ai mahaifinsa ma ya yi maganar ta fara kasuwanci har ya ce ta ke ta fadi sana'ar da take so zai ba ta jarin da za ta fara. Ta yi farin ciki sosai washegarin ranar dama ya kama weekend ne za su je su kai Ma'eesha gidan kakannin nata, don haka suka tafi tare da ita. A nan ne surukin nata ya tambaye ta wace sana'a take son fara wa, nan ta sanar ma sa cewa ko kowace sana'a ce za ta iya. Nan ya fara ba ta zunzurutun kuɗaɗen da za ta fara sana'a da su, ya ce ta fara da siyar da atamfofi da leshi da su shadda da material. Nan ta fara sana'a nan da nan Allah ya sa ma ta albarka ta bunƙasa. Ta fada haɗo wa har da takalmomi da haka da su sarƙa da ƴan kunne. Don a yanzu haka manyan shaguna ne guda biyu yake da su a kasuwa wanda ake kula ma ta da su. Kuma ta samu mutane ma su amana dake kula da su. Ma'esha na ta shekaru goma sha uku ta sauke Alkur'ani mai girma aka yi ma su walima. Tarbiyya daidai gwargwado ta samu daga wajan mahaifiyarta. Ma ta mai karamci da Dattaku ku , ta san ya kamata ga ta da hakuri juriya da hangen nesa. Duk da kasancewar tana da masu ma ta aiki a gida hakan bai sa ta bar Ma'eesha sakaka ba tarbiyya ba, don ta koyar da ita duk wasu aikace-aikace aikace na gidan da girki da komai, wai a cewar ta ƴa mace ce gidan wani za ta je ba kowane namiji ke son mai aiki na ma sa komai ba musamman kula da ɗakinsa da kuma yi ma sa girki. Don haka take saka ya tama shiga cikin ma su aikin suna girki tare da Inno wata Dattijuwa dake yi wa Mummy aiki, matar akwai hankali kuma jininsu ya hadu da Ma'eesha. Har ma'esha ta kai shekaru goma sha takwas iyayen ta ba su sake samun haihuwa ba. Kuma a lokacin ne ta kammala karatun secondry school. Kuma a wannan lokacin Daddynta ya siya ma ta mota. Aka koya ma ta driving ɗin motar har ta iya wanda lokacin ne Daddy ya so tura ta ƙasar waje ta yi karatu a can amma Mummy ta hana. Ta ce gara yarinyar ta ta zauna a gabanta tana kallon ta hankalin ta zai fi kwanciya akan ta je can wata ƙasa da ba ta san tarbiyya da ɗabi'ar da za ta koya ba, ita dai a bar Ma'eesha a gabanta tana kallon halin da take ciki don ƴa mace tana da rauni. Don ta ba wa Ma'eesha tarbiyya mai kyau ba ta yarda da yawon gidan ƙawayenta. Ƙawarta daya ce a duniyar nan sai dai abokan karatun ta. Wata rana Mummy ta fito daga gida tana bayan mota direba zai fita da ita zuwa kasuwa ta duba kayan da babu. Don yanzu har Dubai take fita siyen kaya. Sai ta ga wata mata rakuɓe kusa da gidansu ita da yar biyu saurayi daya sai budurwa guda ɗaya. Ba ta ce komai ba suka wuce, bayan ta dawo za ta shiga gida tana bayan motar, still su ta fara gani, sai wannan matar ta rugo da sauri ta nufi motar, ganin haka ya sa Mummy ta ce wa direban ya tsaya. Bayan ta sauke gilashin motar ne ta ce. "Baiwar Allah lafiya daga ina haka, yaranki ne can?" Ta daga kai kawai ta kasa magana, da ƙyar ta iya cewa . "Ki taimaka ma na da abinci yunwa, tun jiya ba mu ci komai ba ni da yara na." Tana gama fadar haka ta zube a wajen a sumammiya, yayin da saurayi da buduwarwar suka ƙaraso kanta suka kiran sun Mamy, buduwarwar har tana kuka. Da sauri Mummy ya fito cikin motar tana salati. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣5️⃣ Tama gama faɗar haka ta zube a wajen a sumammiya, yayin da saurayi da budurwar suka ƙaraso kanta suka kiran sunan Mamy, budurwar har tana kuka. Da sauri Mummy ta fito tana salati. "Baiwar Allah lafiya?" Direban ne shi ma ya fito daga cikin motar yana cewa. "Suma ta yi ya kamata mu yayyafa ma ta ruwa watakila ta farfaɗo." Da sauri Mummy ta ce . "Kawo ma na ruwan ko?" Da sauri ya bude murfin motar ya dauko robor ruwa ya zo ya yayyafa ma ta, ajiyar zuciya nauyi ta sauke sannan ta fashe da kuka tana cewa. "Yauwa wayyo na shiga uku na lalace ku taimaka ma ma da abinci." Jin haka ya saka Mummy ta ce . "Ba damuwa mu je ciki za ku ci abinci." Laila ta kama mahaifiyar ta ta da taimakon ta ta tashi tana rike da hannunta. Mummy ta ce wa direban ya ja motar zuwa ciki ita za ta karasa shigowa da ƙafa . Ya shiga cikin motar ya ya tayar suka bi bayansa da ƙafarsu, budurwar na rike da Mahaifiyarsu. Bayan Mummy ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga da sallama ta ce su shigo. Suka shiga ciki kowa ya zauna akan Centre carpet. "Haba ku tashi ku zauna akan kujera ma na." Mummy ta fada tana Murmushi. Suka hada baki wajen cewa. "A'a nan ma ya yi." Ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta kira ta ba ta umarnin kawo abinci wa ɓakin. Mau aikin ta gaida su ta wuce don cika umarnin matar gida. Ba jimawa aka cika ma su gabansu da kayan ciye-ciye, ta yi servin ɗin su abincin da za su ci. Sannan ta zuba ma su farfesun a cikin bowl huda uku kamar yadda ta zuba ma su abinci. Kasancewar ta hana mai aikin ta zuba ma su abinci da lemu. Ta koma ɗakinta ta basu wuri don su sake su ci abincin. Tana barin wajen jiki na rawa kowa ya dauki plate ɗaya na abincin suka hau ci cikn haɗama. Nan da nan suka cinye suka ɗauki farfesun shi ma suka cinye suka shanye romon da lemu suka sha ruwa. Laila ta buɗe ƙular ta ha sauran abinci ta kara masu duka suka cinye suka lashe plate. Bayan sun shanye lemu sun sha ruwa ne suna zaune sai ga Mummy ta fito da fara'a tana ma su sannu da zama. Nan suka hau yi ma ta godiya. Horn ɗin mota suka ji a bakin gate, nan fa nan maigadin gidan ya bude gata. Motar ta cinno kai ta shiga cikin nutsu ake driving motar. Bayan an yi parking motar ne sai mamallakiyar motar ta ziro fararen ƙafarta ta fito daga cikin motar. Hannunta daya riƙe da makullin motar ɗayar hannun kuma rike da handbag ɗin ta. A hankali take tafiya kamar mai jin tausayin ƙasa. "Hajiya Ma'esha kin dawo?" "Eh na dawo ina wuni?" "Lafiya lau ya karatun?" "Alhamdulillah." Daga nan ta shiga cikin ga gidan ta tura kofar falon da sallama. "Assalamu alaikum" Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin wannan matar da yaranta ke kiranta da Mamy. Amma sai ta dake ta karaso ciki ta gaida Mummy. "Ina wuni Mummy?" "Lafiya lau kin dawo?" "Eh Mummy na gaji." Murmushi ta yi sannan ta ce . "Ba ki ga baki ba ne?" Ma'eesha ta kalli Mamy wacce ta ji sam matar ba ta kwanta ma ta ba. "Ina wuni?" Washe baki ta yi tana amsa wa Ma'eesha gaisuwar. Sai ta kalli dayan saurayin za ta gaishe shi ya yi saurin cewa. "Ina wuni ranki ya daɗe." Murmushi ta ɗan yi sannan ta amsa ma sa cikin fara'a, sai budurwar ita ma ta gaishe ta, ta amsa ma ta cike da fara'a. Matar ta kalli Mummy ta ce . "Hajiya taimaka ma na za ki kamar yadda Allah ya rufa ma ki asiri mu ma ki rufa ma na." "Me kike so na taimaka ma ki da shi in dai bai fi ƙarfina ba zan yi ma ki in sha Allah." "Ba mu da wajen zama, gidan hayan da muke ciki maigidan ya Kore mu saboda ba mu da kuɗin da za mu biya shi na haya, ga mijina ya rasu yara biyun nan nake da su to ba abun yi tun da ba su damu damar yin karatu ba. Don Allah Hajiya ki taimaka ma na ko za ki samar ma na wajen da za ki raɓa mu za mu dinga yi ma ki aiki dukkan mu, ko ba ki biya ki komai ba in da za ki ba mu abincin da za mu dinga ci muna so Hajiya." Ta karasa maganar tana fashewa da kuka. Cikin tausaya wa Mummy ta ce kar ki damu ba aikin da muke bukatar ayi mana , ma'aikata sun ishe mu, amma ba na da ikon ba ki wajen zama a gidan nan ba tare da izinin maigidan ba. Amma za ku zauna a B.Q na gidan nan kafin ya dawo sai a san abun yi." Gabadaya suka haɗa baki wajen yi ma ta godiya suna farin ciki da wannan ni'imar da Allah ya yi ma su. Mummy ta kalli Ma'eesha ta ce. Tashi ki kai su BQ ɗakin da ba kowa sai su zauna a ciki. "To Mummy." Cewar Ma'esha ta fada tana mikewa tsaye, duk da dai hankalinta bai kwanta da lamarin mutanen ba. Ba yadda za ta yi ne ta hana mahaifiyar ta taimaka ma su amma jiki ta ya ba ta akwai wani abu mara daɗi da zai faru da su a dalilin mutanen nan. Tana gaba suna bin ta a baya har suka ƙarasa BQ ɗin gidan. Ta bude kofar ta shiga suka bi ta a baya. Madaidaicin falo ne da ɗakuna biyu a ciki da toilet da kitchen dake nan cikin dakin. Akwatin set ɗin kujeru a falon ɗakina biyu suka kowane akwai katifa a ciki. Fitowa ta yi ta bar su suka ta jin daɗi suna yaba wajen. Part ɗin su ta koma ta samu Mummy na waya Da Daddy, sai da ta bari sun gama sannan ta kalli Mummy ta ce. "Mummy hankalina bai kwanta da wannan matar ba, don Allah idan taimakon su za ki yi ki ba su kudi su je su nemi haya su zaiuna, ki ba su kuɗin da za su ja jari amma ba na son zaman su a nan." Shiru Mummy ta yi tana nazarin maganar ƴarta, ita dai iya sanin ta da Ma'eesha ba ta da ƙyamatar mutane duk yadda suka kai ga lalacewa kuwa. Ta san darajar Ɗan Adam Sosai, amma sam ta rasa dalilin da ya sa hankalinta ya kasa kwanciya da mutanen nan. Cikin sigar rarrashi ta ce. "Shi kenan zan yi tunani akan hakan, amma ba kya ganin ita nan ta nemi mu ba ta ta zauna ba wai a ba ta kudi ta je ta nemi haya ba?" "Eh na sani Mummy, amma ba ta da hujjar cewa anan dole za ta zauna, ai taimako ne ko gida aka ba ta a wata unguwar za ta zauna ai." "Je ki huta za mu yi maganar daga baya." Tashi ta yi ta nufi bedroom ɗin ta cikin sanyin jiki. Haka nan su Mamy suka ci gaba da zama cikin gidan, ba abinda suke yi a cikin gidan, kullun da safe ma su aiki za su mai ma su abincin breakfast a part ɗin. Sannan da rana ma a kai ma su can part ɗin haka dare za'a kai ma su . Ranar da suka cika sati daya a ranar ne Daddy ya dawo daga tafiyar da ya je. Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya huta ne Mummy ta ba shi labarin Mamy da yaranta da yadda suka yi . Kallon ta Daddy ya yi tare da cewa. "Kin san daga ina suka fito ne?" "Ban sani ba wallahi, amma dai abu ɗaya na sani shi ne suna bukatar taimako kuma na taimaka ma su." "To yanzu ya kike son a yi da su?" "Duk yadda ka ce haka za'a yi yallaɓai." Murmushi ya yi sannan ya ce. "A'a duk yadda kika ga ya dace sai ki yi na ba ki wuƙa da nama." "To me zai hana mu zauna da su a nan gidan?" Ɗan jim ya yi kafin ya ce . "Nan gidan kuma?" "Eh yallaɓai, na ga kamar tana son zama nan ne, don ba ta ce a ba ta wani gidan ko kuɗin siyen gida ko haya ba. Sannan kuma ai tana can BQ ba nan za ta zauna kusa da mu. " "To ai ba ta da zaɓi muhalli take nema da Abinci, idan ta samu ko ina ne ina ne ai buƙatar ta dai ta samu mu abun da take nema." "Haka ne, amma zan so a ce ta zauna kusa da mu, tana da yaro saurayi idan bai yi karatu ba sai a saka shi kasuwanci. Macen kuwa sai a saka ta a makaranta." "Shi ke nan Allah ya mana jagora." Da Anin ta amsa daidai lokacin da Ma'eesha ke ƙarasowa fakon hannunta da karamar jaka ta fito daga wajan kakarta da ta je yi ma ta weekend. Ganin Dad ɗin nata ta saki jakar cike da murna ta karasa wajensa ta rungume shi. "Daddy yaushe ka dawo ba wanda ya sanar da ni?" "Yau na dawo Mamana ya kika bar su Hajjaju." Da yake sunan da suke kiran da shi kenan. "Hajjaju na can na bar ta da masifarta." Mummy da Daddy a tare suka yi dariya. "Daddy idan na masifa ba ta za ta ce wai na je na kwaso sauran kayan na dawo gidan nan da zama?" "Yaushe aka yi hakan?" Cewar Mummy tana kallon Ma'eesha, duk da ta san cewa Hajjaju ba ta ƙaunar ta har yanzu kuma ba ta nuna ma ta tsana yanzu, domin soyayyar da take yi wa jikar ta ya ɗan saka ya shafi mahaifiyar ta. Domin tana ƙaunar Ma'eesha sosai kamar ranta, ko don Ma'eesha kadai ce jikarta ɗaya da ta fito daga tsatson tilon Ɗants guda ɗaya da ta mallaka a duniya, ga shi ɗan nata shi ma Ma'esha kadai ya mallaka a duniya. Don haka tana ƙaunar Ma'eesha amma ta kasa ƙaunar mahaifiyar Ma'eesha har yanzu , amma tana amsa mata ba yabo ba fallasa idan ta zo gaishe ta sai dai ba ta wani sakin jiki da ita. Ita ma kamata Mummy yanzu abun ya daina damunta. "To ai ba wani abu idan kin koma gidan nata da zama?" Cewar Mummy tana Murmushi. "To idan na koma can da zama ku fa ai ba ku fa kowa a nan, sai ku zauna haka daga ku dai ma su aiki?" Murmushi Mummy ta yi tana cewa. "Daga mu sai ma su aiki mana, to su ba mutane ba ne, ga kuma ƙarin wasu ƴaƴan na samu saurayi da budurwa." "Ok ina suke?" "Baƙin da kika raka su BQ nake nufi." Take fara'ar dake fuskarta ta ɓace ɓat. "Mummy please a ba su wani gidan su zauna can a ba su abinci, amma jikina ya na ba ni zuwansu gidan nan ba alkhairi ba ne.," "Ban san me ya sa ba ki ƙaunar mutanen nan ba." Shiru Ma'eesha ta yi don a ya san me za ta ce ba. Don haka ta mayar da hankalinta ga Daddy ta ce. "Daddy me ka dawo ma ni da shi tsarabar tafiyar ?" "Mamana komai na kawo ma ki sai abin da ba ki so ne kawai ban siya ba." "Thank you so much Daddy." "You are welcome ." Daga nan rayuwa ta cigaba da tafiya a hankali sabo da shaƙues ya fara shiga tsakanin Mummy da Mamy. Don ta sa Daddy ya kai Jamil kasuwa a ɗaya daga cikin shagunan ta yana siyar da kaya. Laila kuma an saka ta a makarantar secondary school kasancewar ta gama primary. Sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakanin Mummy da Mamy wanda kullum a bangaren Mummy mamy ke wuni kullun suna tare, Mamy kan bar BQ ta zo nan main house din su yi ta fira da da Mummy. Tun Ma'eesha ba ta sakin jiki da Mamy har yau da gobe yadda Mamy ke jan ta a jiki ta saki jiki da ita amma ba sosai ba. Wata ranar talata da misalin karfe biyar na yamma Mummy ta dawo daga kasuwa, sai dai ba tare da dirbanta take ba ita kadai ce take driving. Don ranar direban bai da lafiya yana gida ta ce ya huta. Kasancewar yanayin unguwar ba yawan mutane da yawa. Tana tsaka da tafiya ta ga mutum ya tsaya a gaban motarta, cikin azama ta taka birkin motar. Su biyu ne suka zagayo gefen me zaman banza ya zauna yana nuna ma ta wuƙa yana cewa. "Ki bi umarnin da zan ba ki." Daidai nan ɗayan ya shiga bayan motar ya zauna suka nuna ma ta hanyar da za ta bi, wanda ba ta da wani zaɓin da ya wuce bin maganar su. Duk hanyar da suka nuna ma ta nan ta bi har suka shiga unguwar da ba mutane don sabbin gine-gine ne a unguwar su ma ɗaiɗaiku ne ba da yawa ba. "Tsayar da motar." Ta tsayar suka fito suna waige-waige. Fitowa suka yi sannan suka ba ta umarnin ta fito ita ma. Fitowa ta yi tana rokonsa da kada su cutar da ita. Don ba ta san nufin su akanta ba, sun yi yi haka ne don su kawo ta wajen da na mutane su kashe ta ko sun yi haka ne don su yi ma ta ƙwace. Tana ganin wata zabgegiyar wuƙa da suka fito da ita ya sa ta ruga a guje, ganin haka suka mara ma ta baya a guje suka bi ta. Tana cikin gudu duk ta gaji ga numfashinta kamar za su ɗauke ta ji ta yi karo da mutum a gabanta. Sai a lokacin ta lura da mutumin da ta yi karo da shi. Saurayi ne maji ƙarfi yana da siffa irin na zaratan maza. Bayansa ta laɓe tana rike rigarsa ta baya, domin ba za ta iya cigaba da gudu ba. "Saurayi don Allah ka taimaka ma ni kada su cutar da ni." Dariya samarin da suka biyo ta suka yi sannan ɗaya ya ce. "Ta ya makaho da ba ya gani zai iya taimaka ma ki?" Sai a lokacin ta lura da sandar jagoransa dake hannunsa, sannan ga wani baƙin gilashi da ya sa a idanunsa. Cikin dakakkiyar murya ya ce . "Ku bar wajan nan." Dariya suka sake yi kafin ɗaya ya ce. "Kai makaho ja sandarka ka yi gaba kafin na ƙarasa illata ka." Cike da ƙwarin guiwa Makaho ya ce wa Mummy. "Kwantar da hankalinki ba abin da da suka isa su yi ma ki." Daidai lokacin ɗaya saurayin ya yi kukan kura ya nufo makahon a fusace, yayin da makahon ya ji yakin gudunsa ya ɗaga sandarsa daidai yana kawo wa ya buga ma sa Sandar a kai, wanda ya sa ya faɗi ƙasa yana birgima. Ɗayan ma na ganin haka ya zo da karfinsa, nan ma makahon ya yi bugu ɗaya ya yi ma sa shi ma ya zube a wajan. Ganin haka ya sa ta ce. "Mu je ka bar wajan nan kar su tashi su illata ka." Ta faɗa cike da tsoro. "Sai sun ɗauki tsawon lokaci kafin su koma daidai. Ki wuce ki bar nan." "Kai kuma fa?" "Kada ki damu da ni." "Ba zan bar ka anan ba, don Allah ka zo mu ke ka ji." Haka ya bi bayanta suka isa wajan motarsa ta bude ma sa gefen mai zaman banza ya shiga. Da sauri ta ja motar suka bar wajan tana godewa Allah. "Ya sunanka." "Khalifa." "Na gode da cetona da ka yi. Mu je gidana duk abinda kake bukata zan ba ka ko meye, zan kai ka asibiti a yi ma ka aikin idanunka ko da ƙasar waje ne." "Haka idanuna suke, haka aka haife ni ba aikin da za'ayi ya bude kuma." "Ayyah na ɗauka lalura ce ta same ka." "A'a." Ya ba ta amsa a takaice. Ba wanda ya sake magana har suka isa gidan, ta danna horn maigadi ya bude ma ta ta shiga da motar zuwa parking space ta yi parking. "Hajiya ni zan koma gida, ba na bukatar komai." "To na ji mu je ka gaisa da iyalina ga mijina ma ya dawo ƴata ma ta dawo ina son na ma su bayanin komai a gabanka." Daga haka suka fito tana gana yana bin ta da sanadar jagoransa suka shiga ciki. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣6️⃣ Daga haka suka fito tana gana yana bin ta da Sandar jagoransa suka shiga ciki. Da sallama ta shiga falon, Daddy da Ma'eesha dake zaune a falo suna jiran dawowarta suka mike suna ma ta kallon mamaki. Ganin yanayin ta da kuma wanda take tare da shi. "Lafiya kuwa Mummy, yanzu Daddy ke shirin kiran wayarki sai muka ji ƙarar motarki." Murmushi ta yi tare da cewa. "Na auna arziki ne yau." Da sauri Daddy ya mike tsaye yana kallonta. "Subhanallah ba abun da ya same ki ko?" Murmushi ta yi ta ce "Ba komai Daddyn Ma'eesha Allah ya kare ni fa ya tura mun wannan bawan Allah ya taimake ni." Sai a lokacin ne suka lura da Makaho, cikin sakin fuska da fara'a Mummy ya kalli Makaho ta ce. "Ƙaraso ma na Bismillah." Sai a lokacin Makaho ya karaso ciki ya zauna a saman carpet. Nan Mummy ya ba wa Daddy da Ma'eeaha labarin duk abinda ya faru da ita a hanya da haduwarta da makaho. Sun jinjina lamarin sosai nsannan Daddy ya ɗebi kudi ya mikawa Makaho yana cewa. "Ga wannan kudin ka damu na kashe wa ko?" Hannu ya daga ɗaga alamar ba zai karɓa ba. Nan Mummy da Daddy suka yi suka yi ya karba kudin amma sam ya ce ba zai karɓi ko sisi daga wajan cikin kudin da suka ba shi ba. Mamaki suka yi ga shi makaho kuma bai yi kala da wanda yake da kudi ba. Don sai da Mummy ta kare ma sa kallo. Kuma ta rasa me za ta bashi da zai kaba a matsayin tukuicin ceton ranta da ya yi. Abinci ta saka Ma'eesh ta kawo ma sa. Sai dai ya ce ba zai ci ba. Kallon Ma'eesha dake rike da tire da ta kawo abinci Mummy ta yi kafin ta ce. "Mayar da abincin ki hada ma sa take away ya tafi da shi." "To Mummy." Ta faɗa tana nufar hanyar kitchen, don dama ba kowane lokaci Mummy ke sanya ma sai aiki yin abu ba, wani lokacin Ma'eesh take saka wa. Daddy ya kalli Makaho ya ce. "Bawan Allah ya sunanka?" "Sunana Khalifa." "Ma sha Allah, amma me ya saka ba ka karbi kuɗimda la ba ka ba, ko sun ji kadan ne?" "A'a Alhaji ba haka ba ne, na yi komai saboda Allah ne, idan na karbi kuɗin ku ai ya zama kamar na kudi kuka biya Ni, kuma ba na yi don ku biya ni ba ne na yi saboda Allah ne." Murmushi Mummy ta yi tare da cewa. "Iyayen ka suna raye?" "A'a ba sa raye Allah ya yi ma su rasuwa tun ina yaro." "Yanzu a ina kake zaune?" "Gidan wasu bayin Allah ne sauka ba ni ɗaki nake zaunar fisabilillah." "Za ka iya zama da mu a baka ɗaki can bangaren mazan da ke mana aiki?" "A'a Hajiya na gode ki bar shi kawai." Jinjina kai ta yi kafin ta ce. "Ina neman wata alkfaea a wajen ka." Faɗi ina dai bai fi ƙarfina ba in sha Allah zan yi ma ki." "So nake kullun ka dinga zuwa gidan nan ka na karɓar Abinci." "Eh to kada na ce a'a ki ga laifina komai na ƙi karba, amma dai zan dinga zuwa duk ranar juma'a in sha Allah ina karbar abinci ko na ci." "Sauran ranakun da?" "Ba tabbas zan iya zuwa. Amma idan na damu sarari jefi-jefi za ki dinga ganina" Daidai lokacin Ma'eesha ta karaso rike da leda da ta hadi take away da abin sha da su snacks." Mummy ta karɓa ta miƙa ma sa ya yi godiya ya nufi hanyar fita daidai lokacin Mamy ta shigo tare da Laila suka yi sallama. Gabadaya suka amsa ma su sallamar. Laila na ganin makaho zai fita ta ce. "Yaushe mabarata suka fara shigowa har cikin gidanmu ne?" Cak ya tsaya wanda kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka san cewa ransa ya ɓaci. "Ni na mabaraci ba ne, duk da cewar ina da makasa to ba kasashshe ba ne, ina d abun yi kira na aka yi dole na zo gidan nan, kuma ban zo gidanku don a wulakanta ni ba. Na ɗauka gidan karamci da sanin darajar Ɗan adam na zo." Ma'esha ta yi saurin cewa. "Ƙwarai kuwa gidan karamci da sanin darajar Ɗan adam ka zo, kuma ka ga yadda muka karrama ka, ita wacce ta yi ma ka maganar ba ƴar gidan nan ba ce cin arziki ta zo, ka yi haƙuri Yaya Khalifa." Har ga Allah ya ji dadin zancen Ma'eesh sai dai bai ce komai ba ya fita. Hatta Daddy da Mummy ba su ji dadin zancen da Laila ta yi wa makaho ba, kuma sun ji dadin hakurin da Ma'eesha ta ba shi, duk da ba su so ta ce Laila ba ƴar gidan ba ne don kar ta ji ba daɗi. Mamy kuwa ta ji haushin zancen ma'eesha ko kadan ba ta so a ce An yi maganar cewa ƴaƴanta ba ƴan gidan ba ne, tamkar gori Ma'eesha ta yi wa ƴar ta. Fuu Laila ta nufi kofar fita za ta fice Mummy ta kira ta. "Laila zo nan." ",Ta karasa gaban Mummy tana kumbure fuska." "Kada ki sake irin abun da kika yi yanzu, ki dinga daraja Ɗan adam ban da wulaƙanci ko cin zarafi akan wata nakasa da yake da ita. Ko da a ce haka ne bai kamata ki fadi haka ba. Ko a ina kuma ga mutum duk yadda yake ki daraja shi kada ki wulakanta shi Ɗan adam daraja ne da shi, ba wai idan ka taka wani matsayi sai ka dinga wulakanta mutane ba." Naj ta ba su labarin Khalifa Makaho da yadda ya taimake ta. Mamy ta jajanta ma su sannan ta yi Dady Barka da dawowa suka koma part ɗin ta ita da Laila. Ran su a ɓace don idan aka ɓata rana Laila dai Mamy ta taya ta fushi. Suna zuwa BQ Laila ta fada kan kujera tana kuka. Mamy ta janyo ta ta rungume. "Yanzu wai ni ban wuce gori a cikin gidan na ba, kullum cewa kuke na ɗauka nan gidanmu ne amma kalli abun da ma'eesha ta yi ma ni s gaban wannan Makaho." "Ki kwantar da hankalinki lokaci kadan ya rage daga Ma'eesha har uwar ta za su bar ma na gidan da me gidan dai yadda muka yi da shi. Ko kin mance abun da ya kawo mu nan ne?" "Ban mance ba, amma sai yaushe za mu yi ta zama a haka ne?" Lokaci kadan ya rage za su zama tarihi a gidan nan, nan ba da dadewa ba ke ce matsayin Ma'eesha yayin da ni kuma zan maye gurbin mahaifiyarta a wajen Alhaji." Dariyar mugunta suka saka su duka wanda sautin dariyar ya da ba su ji sallamar Jamil ba. "Assalamu alaikum." Shiru ba wanda ya amsa sai dariya suke yi Ya shigo ya tsaya gabansu sannan suka yanke dariyar da suke yi. "Lafiya wannan dariyar ai ta wuce na Musulunci." "Ina ruwanka." Mamy ta faɗa don ko da wasa ba za ta bari Jamil ya san shirinta, don ba halinsu daya da shi ba ta sani. Ɗakinsa ya wuce ba tare da ya sake cewa komai ba. Don har ga Allah ya tashi halin mahaifiyar tasa. *Washegari* _Ma'eesha_ Ta fito daga cikin bedroom ɗinta tana gyara mayafin abayar da ta yi rolling kanta da shi. Sanye take cikin doguwar rigar Abaya mai ruwa ƙasa. Hannunta rike da makullin motarta . Part ɗin Mummy ta nufa da niyyar yi ma ta sallama, tun kafin ta karasa ta hango Mamy tana barin part ɗin Daddy cikin sanɗa alamar rashin gaskiya. Da mamaki take tambayaar kanta. 'Me Mamy ta zo yi nan part ɗin, sannan duk falo bai ishe ta ba ko ɗakin Mummy shi ne za ta zo part ɗin Daddy me ta zo yi. Ga Daddy baya nan ya fita.' Ƙofar bedroom ɗin Mummy ta yi knocking aka ba ta izinin shiga sannan ta shiga da sallama. "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Mummy ta amsa yayin da take nannaɗe sallaya kasancewar sallar walaha ta idar. "Wai har kin fito zuwa gidan su Nasreen ɗin kenan ?" "Eh Mummy da ita na kwana ba ta da lafiya sosai." "Allah sarki, Allah ya ba ta lafiya." "Amin ." Ɗan jim ta yi har sai da Mummy ta tambaye ta. "Lafiya alamar kina da damuwa ko?" "Mummy ." "Na'am." Ta amsa tana tattara hankalinta kacokan kan Ma'eesha. "Me Mamy take zuwa yi nan na?" Cikin nuna gajiya da zancen Ma'eesha kullun na cewa ba ta son zaman Mamy a gidan." "Wai me bayin Allah suka yi ma ki ne Ma'eesha? Ban san ki da mugun hali na rashin son jama'a ba." "Wallahi da na ga Mamy tana sanɗa tana barin part ɗin Daddy ." Da sauri Mummy ta kalle ta tana cewa Ban gane ba wai ita da kanta kika gan ta a part ɗin mahaifinki?" "Eh." Ta amsa a takaice cike da damuwa. "Mummy me ya kawo ta ne?" "Ina zan sani don ban ganta ba. Me yiwuwa nan za ta shigo ta ɓace hanya kin san iyakar ta falo take tsaya wa." "Wannan fa sanɗa take yi alamar ba ta son wani ya ganta." Cikin kawar da zancen Mummy ya ce. "Idan kin je gidan su Nasreen ki gaida ma ni da mahaifiyarta." "Za ta ji." Har za ta wuce ta dawo ta ce "Mummy ba ki tunanin wani mugun abun take ƙoƙarin aikatawa ne?" "Me ya sa kika ce haka.?" "Haka zuciya ta ke raya ma ni." "To ki saƙa alkhairi a zuciyarki." Cikin sanyin jiki ta yi wa mahaifiyarta sallama ta fice daga part ɗin. A falo ta tarar da Mamy tana zaune tana kallonta ta washe baki. "Ƴan matan Mummy ina zuwa haka?" "Gidan ƙawata." "Da motarki za ki tafi?" "Eh." "Am na ce ba?" Sai Ma'eesha ta tsaya tana kallon ta don jin me za ta ce. "Ki dinga fita da Laila tana ganin gari ita ma ko za ta san jama'a." "Yanzu ina sauri next time za mu tafi tare." Ba ta jira cewar ta ba ta fice daga falon. A parking space tana kokarin yin parking motarta kenan ta ga wata sabuwar mota ta shigo cikin gidan. Ba kowa ba ne face Abdul saurayinta da yake mutuwar son ta. Bude murfin motar ya yi ya fito daga nasa motar ya nufi nata motar. Tsaya wa ta yi tana kallonsa da mamaki don ba ta san ya shigo kasar ba. "Kina mamaki ko?" Saukar yaushe a garin?" "Yanzu, ko gida ban je ba daga airport nan na fara zuwa na ga sanyin idanuwana." Murmushi ta yi tare da cewa . "Sannu da zuwa, shi ya sa na ji garin na ƙamshin Egyptian, ashe mutanen Egypt ne." Dariya ya yi tare da cewa. "Yanzu daga ƙasar Canada nake ." "Ma sha Allah. Ya kamata ka je gida ka huta kafin ka zo nan k" "Korata kike yi?". Dariya ta yi tana cewa. "Ba haka ba ne, kawai na ga ba ka je gidan ka huta ba ai." "Okay." Ya buɗe bayan motar ya fito da wasu manyan jakuna guda biyu ya ba ta. Kin karba ta yi sai da ya nuna ɓacin ransa ta amsa tana godiya. "Ba zan bar kasar nan ba sai an sanya ma na ranar aure da ke, don haka ki sanar da Daddy zan zo na gaishe shi." Daga haka ya shiga motarsa direba ya ja suka bar Wajen. Ba ta kai kayan gidan ba sai ta saka bayan motarta ta yi wa motar key ta bar gidan sai ta kama hanyar gidan su Nasreen. Ma'eeha na barin gidan Mamy ta hango abincin Daddy a a dinning table. Tashi ta yi ta kwance haɓar zaninta ta ciro wani kulin magani a leda ta kwance. Sai ta barbaɗa a cikin miyar abincin Daddy ta motsa shi sannan ta motse ta bar wajen bayan ta rufe ta bar wajen in da ta ga Mummy tsaye a falon *Maman Ihsan ce.*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣7️⃣ Tashi ta yi ta kwance haɓar zaninta ta ciro wani kulin magani a leda ta kwance. Sai ya barbaɗa a cikin miyar abincin Daddy ta motsa , sannan ta rufe ta bar wajen in da ta ga Mummy tsaye a falon. Sai ta hau kame-kame cikin rashin gaskiya ta ce. "Dama Wai fridge nake so na ɗauko ruwa na sha." "To ai ga fridge nan a bayanki ko kin manta ba a dinning area fridge yake ba." "Lah ko me ya hau kaina na nufi can oho, bari na je na ɗauko kawai." Ta nufi fridge ɗauki ruwa roba guda ta ta dawo falon ta zauna. Ita ma Mummy zama ta yi ba tare da ta kawo zargin komai a zuciyarta ba, duk da maganar da Ma'eesha ta yi ma ta kuwa. "Ko abinci za ki kara ci ne akwai shi a kitchen fa." Cewar Mummy tana kallon Mamy. "A'a Hajiya ba abinci nake bukata ba, ai an kai ma na ga shi can na baro shi ba mu cinye ba, Allah dai ya saka ma ku da alkhairi ya ƙara arziki, mun gode sosai." "Haba don Allah ki daina yi ma na godiya, ai mun zama ɗaya." Ƙarar horn ɗin motar Daddy suka ji da ƙarar bude gate ɗin gidan. "Bari na tashi na tafi tun da maigidan ya dawo ko?" "Tashi kuma ki zauna ma na na ga kallo kike yi ai, na manta ban fada ma ki ba za mu tafi aikin Umrah cikin satin nan in sha Allah." Washe baki Mamy ta yi tana cewa. "Alhamdulillah Allah ya kai ku lafiya ya karbi ibada?" "Ke da Alhaji za ku tafi ne?" "Mun saba duk shekara tare da shi da Ma'eesha muke zuwa mu uku, amma wannan karon ba zai samu zuwa ba ni da Ma'eesha kawai za mu tafi, shi ma wata ƙasar zai tafi." "Allah ya tsare ku za mu sha kewa." Dariya Mummy ta yi tana cewa. "Idan Allah ya kai mu za ku je aikin Hajji ke da yaranki duka." Kukan farin ciki ta saka tana yi wa Mummy godiya, ita kuma tana cewa ta daina kuka. Daidai lokacin da Daddy ya shigo da sallama. "Subhanallah me ya faru ne take kuka?" "Don na yi ma ta albashir ɗin zuwa aikin hajji ita da ya ranta shi kenan fa." Murmushi ya yi ya ce. "Ikon Allah , ai addu'a za ki yi ba kuka ba." Yana gama fadar haka ya nufi part ɗin sa, duk kukan da Mamy ke yi bai hana ta satar kallon Daddy ta kasan idanunta ba. Mummy ta bi bayan mijinta ganin cewa Mamy ta yi shiru. Da harara ta raka ta sanan ta mike ta nufi BQ. Ko da Mummy ta shiga part ɗin ta ta samu Daddy ya fara rage kayan jikinsa zai yi wanka. Ta taimaka ma sa ya cire kayan sannan ta haɗa ma sa ruwan wanka. Kafin ya fito ta cire ma sa jallabiya mai gajeren hannu, kasancewar in dai yana gida to ya fi saka jallabiya. Ya fito ta taimaka ma sa ya shirya cikin jallabiyar ganin yanayinsa ta san a gajiye yake. "Ka gaji ko?" Murmushi ya yi yana cewa. "Bari kawai aiki ne ya ma ni yawa tun safe har yammacin nan." "Allah sarki mu je ka ci abinci ka huta na san ba ka ci komai ba." "Haka ne, a tare suka nufi dinning area yana jin kansa na ɗan sara ma sa. Abinci ta zuba ma sa ya ci ya sha lemu da ruwa. Kallon time ya yi. "Ya kamata a ce Ma'eesha ta dawo gida haka nan, tun yaushe ta kira ni zancen zuwa gidan ƙawarta da ba lafiya shi ne ba ta dawo ba." "Za ta dawo in sha Allah. Ka san ba ta daɗe da wucewa ba, ka dawo kuma ka san ba ta da ƙawar da ta wuce Nasreen." Duk da haka sai da ya kira waya ya ce ta dawo gida. A ranar sai ga Khalifa Makaho ya zo gidan, kamar yadda Mummy ta ce ya dinga zuwa kowace rana, amma bai zuwa kowace rana sai dai duk sati yana zuwa. Ziyarar juma'a, bayan an yi sallar juma'a daga masallaci yakan je gidan ya kaiwa Mummy ziyara. Kuma takan karrama shi sosai da sosai a cika ma sa gabada da abinci kala-kala da abun sha. Wata rana har take away take yi ma sa. Kamar kullum yau juma'a ya zo gidan, bayan maigadi ya bude ma sa ƙaramar ƙofar m *Bayan sati ɗaya.* A ranar ne su Mummy da Ma'eeha suka wuce ƙasa mai tsarki don yin umara. Shi kuma Daddy nan da kwanaki biyar, zai tafi ƙasar da zai je don gudanar da harkokin sa.Farin ciki ya cika zuciyar Mamy saboda yanzu ne lokacin da za ta shirya mummunar kudirin ta kai. Don yanzu wani sabon salo Mamy ta tsiro da shi, sai ta bar BQ da sassafe ta zo man main house din ta ce da ma su aiki su dinga dafa abinci na su kaɗai, ita za ta dafa nata ita da yaranta da na maigidan wato Daddy. Ba yadda suka iya haka suka zuba ma ta idanun take yin abun da ta ga dama. Abincin Dady kuma kullum safe da dare sai ya barbaɗa ma sa magani a ciki. Gabɗaya ya canza kamar ba shi ba. Tafiyar da zai yi ma ya ce ya fasa zuwa. *Bayan sati biyu* Motar da ta ɗauko su na tafiya akan titi suna baya direban na zaune mazaunin sa yana driving hankali kwance. Cikin damuwa Ma'eesha ta ce. "Mummy tsawon sati ɗaya kenan ba mu ji daga Daddy ba, kuma yana ƙasar nan, abun ya ba ni mamaki shi bai kira ba kuma idan mun kira baya ɗaga wa." "Kar ki damu me yiwuwa aiki ne ya ma sa yawa." "Ba na tunanin akwai aikin da zai ma sa yawa da har zai saka shi ya mance da iyalansa. Yanzu haka na ɗauka za mu gan shi a airport ya zo ɗaukar mu." "Ki yi ma sa uzuri Ma'eesha." Daga haka ba wanda ya sake yin magana har suka ƙarasa gidan. Horn direban ya yi maigadi ya bude ma sa kofar gate ɗin ya shiga ya yi parking. Abun da ya kara ba su mamaki ganin motocin Daddy duka a wajen. Sauran ma'aikatan gidan suka ƙaraso suna yi ma su sannu da zuwa. Mummy ce ta amsa ma su, don Ma'eesha gabaɗaya hankalinta ya koma ga mahaifinta so take yi ta gan shi ta kuma ji dalilin da ya sa ya share su na tsawon kwanaki. Direban ne ya shigo ma su da kayansu, suna shiga cikin falon ba kowa sai sanyin A.C dake tashi a falon. Sautin dariya suka ji yana fitowa daga ɓangaren Daddy. A tare suka juya suna kallon ɓangaren Daddy wanda daga nan suke jin dariyar . Da mamaki suke kallon Mamy tare da Daddy suna fitowa daga ɓangarensa tana rike da jakarsa, alamar tafiya zai yi. Mutuwar tsaye suka yi suna kallonsa. Wanda shi ma su yake kallo sai dai ba za ka iya shaida halin da yake ciki ba. Cikin rawar baki Ma'eesha ta ce. "Daddy." Ba tare da ya kalli kowa cikin su ba ya ce. "Kun dawo?" "Ba su iya amsa ma sa ba, shi ma bai sake cewa komai ba ya nufi hanyar fita, Mamy na binsa a baya tana ta wani shu'umin murmushi. "Yauwa zan yi tafiya maybe zuwa next week zan dawo." Sai a lokacin Mummy ta yi karfin halin cewa. "Alhaji ba na ganin dacewar abun da na gani a yanzu, me wannan matar take yi a part ɗin ka?" "Oh haba!" Ta jingina kai sannan ta ce. "Meye tsakanin ku da har za ta fito tana yi ma ka rakiya?" "Kamar yadda kike matsayin matata a gidan nan to haka ita ma matata ce ita auren ta nake yi." Rintse idanunta Mummy ta yi sakamakon wami zafi da raɗaɗin kalmar da Daddy ta ki shi kamar an watsa mata ruwan dalma a zuciyar ta. Ma'eeha kam tamkar saukan aradu haka ta ji. "Alhaji yaushe hakan ya faru ba tare da sanina ba." "Ke uwata ce da dole sai na yi shawara dake wajen aiwatar da abun da na yi niyya?" Jinjina kai ta yi tare da yin murmushi da ya fi kuka ciwo ta ce. "Haka ne, Allah ya sanya alkhairi." "Amin, dama ke kika kawo ta kin san halinta kun saba da juna don haka ki karbe ta ku zauna lafiya don ba zan juri tashin hankali da kishin hauka da wasu matan ke yi idan mijinsu ya kara aure." Yana fadar haka ya fice shi da Mamy tana ma sa Allah ya tsare. Ma'eesha kuwa sulalewa ta yi a wajen tana kuka, ganin mahaifinta ko kallon arziki bai yi ma ta ba, bayan san cewa ita ce sanyin idanunsa. Yana masifar son ta baya son ɓacin ranta, amma yau an wayi gari ko kallo ta ba yi ba bayan tsawon kwanaki da suka shafe ba su ga juna ba. Mummy ta yi kokarin danne abun da take ji ta hau rarrshin Ma'eesha. Suna nan da na Mamy ta dawo tana taunar cingum. Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗaura tana danna waya tsadaddiyar wayarta sabuwa fil. Mummy ta kalli Mamy ta tuna ranar da ta zo ƙofar gidan neman taimako ita da Jamil da Laila. Wai yau ita aka wayi gari ta aure ma ta miji. Kuka sosai Ma'eeha ke yi ranta na ma ta zafi. "Aure dai an riga an ɗaura ba yadda mutum zai yi da ikon Allah, ni ma ba son raina ba ne aka aikata hakan. Alhaji ne ya matsa." Daga haka ta yi shiru tana ƙwalawa daya daga cikin masu aikin gidan kira. "Inno! Inno! Inno!" "Na'am Hajiya." Ta amsa tana fitowa, ganin Ma'eeha na kuka hankalin ta ya tashi ta nufi Ma'eesha tana tambayarta lafiya. Tsawar da Mamy ta daka ma ta ne ya saka ta ɗago da sauri. "Inno!" "Na'am." "Aikin da na saka ki kin gama ne?" "Eh Hajiya." Daga nan ta kama Ma'eesha suka nufi ɗakinta da ita. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, a cikin gidan, abubuwa marasa daɗi na faruwa. Bangaren Daddy ma gabadaya ya tattara hankalinsa ya mayar kan Mamy da yaranta, su ya mai da madubin sa. Sam bai damu da Mummy ba ballantana ƴarta ɗaya tilo a duniya. Da abun ya ishe Ma'eesha wata rana da ta je week end gidan Hajiya Turai ta kakarta sai take sanar da ita halin da suke ciki a cikin. Amma sai ta tarar da Hajiyar ita ma ba ta da labarin cewa wai Ɗanta da ta haifa ya iya yin aure ba tare da ya sanar da su ba. Daka jiran zuwa nasa take yi a baya kullum zai zo ya gaishe su, amma tun da ya auri Mamy bai je ya gaishe ta ba. A cikin kwanakin nan ne Mummy ta dinga fama da rashin lafiya. Yau lafiya gobe ciwo. Sai dai duk rashin lafiyar ba ta bari a kai ta asibiti ba, a cewar ga wai ciwon ba na asibiti ba ne. Ga Daddy ya fita ba zuwa ƙasar. _Makaho,_ Kasancewar yau juma'a ne kuma daga masallaci gidan su Mummy yake son zuwa don ya gaishe da Mumm. Kasancewar sun tafi aikin Umara ya san dai yanzu sun dawo. Don haka bayan ana idar da Sallah kai tsaye ba gidan su Mummy ya nufa don gaishe su kamar yadda ya saba. Doguwar tafiya ya yi kafin ya ƙaraso gidan. Sai da ya sa hannu ya shafa gate ɗin gidan ya tabbatar gidan ne kafin ya yi knocking. Maigadi ya bude kofar ya ga Makaho ne ya ce. "Ma sha Allah makaho ne ke tafi?" Bai tanka ma sa ba ya yi gaba yayin da maigadin ya bishi da harara. "Wannan mishkilancin naka Allah ya ga abin da ya gani da ya hana wa jaki ƙaho. Ana ma sa magana yana share Mutane wannan da yana da kudi da an ga gadara." Makaho kam bai ma san yana yi ba ya nufi cikin gidan. Daga bakin kofar falon yake knocking, ɗaya da cikin ma su aikin ta fito . Ganin shi ne ya sa ta ce. "Bari na sanar da su. Tana shiga ta yi sallama sai aka amsa ma ta tare da ba ta izinin shiga. Ta shiga Mummy na barci Family doctor nasu ma hi ma ta ƙarin ruwa. Ƴar aikin ta kalli Ma'eesha ta ce . "Aunty wannan makahon da ke zuwa ranar Friday ne ya zo " "Okay Ina zuwa." Bayan ƴar aikin ta fita da kamar mintuna biyu sai Ma'eesha ta tashi ta fita ganin Mummy na barci. A hankali take tafiya har ya buɗe kofar falon. Yana tsaye a ya jingina bayansa da bango . Tana daga kanta ta sauke idanunta a kansa. Ya nunkuyat da kai ƙada ya haɗa kai da Sandarsa. Cikin siriryar murya Ma'eesha ta yi masa sallama. Ya ɗago kansa kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣8️⃣ Ya ɗago fuskarsa kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana. "Wa'alaiki Salam warahmatullah." Ya amsa ma ta cikin muryarsa mai amo. "Ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ka shiga ciki." Tana gaba yana bin ta a baya dama idan ya zo bangaren baƙi Mummy ke cewa a kai sa. Bayan ta tura ƙofar falon n ta shiga ne shi ma ya zo ya shiga yana mai yin sallama. Sai da ya ɗan laluba ya ji kujera sannan ya zauna da Bismillah. Ina Mummyn taki take ne?" Cikin sanyin murya ta ce. "Ba ta da lafiya." "Subhanallah me ya same ta?" "Zazzaɓi ne." "Allah ya ba ta lafiya." "Tana ina ne?" "Tana bedroom ɗin ta. Ita ce ta ce na shigo da kai." "Allah sarki, Allah ya ba ta lafiya." "Amin ya Allah." Ta amsa tana mai nufar ƙofar fita ta ce. "Bari na kawo ma ka abinci ko?" " A'a ki bar shi kawai tafiya zan yi, na zo ne dama na gaishe ta." "Ka yi hakuri ka zauna zan kawo ma ka abinci ko a cikin take away ne dan idan Mummy ta ji ban kai ma ka abinci ka tafi haka nan ba za ta ji dadi ba." Tana fadar haka ta fice daga falon. Ba jimawa ta dawo da leda mai ɗan girma ta mika ma sa. "Ga shi na zuba ma ka abincin da abun sha sai snacks." "To na gode Allah ya kara arziki ya ba Mimmy lafiya ." "Amin ya rabbil izzati na gode." Ya mike ya fice daga falon tana binsa a baya. Ya nufi hanyar fita ita kuma ta shiga falonsu cikin matsanancin faduwar gaba da sanyin jiki wanda ta ji ya dirar ma ta lokaci guda. Mamy ne a falon tana waya, amma tana ganin Ma'eesha ta yi saurin katse kiran wayar ta ajiye wayar tana kau da kai. Ma'eesha dai ba ta kalli gefen da take ba kai tsaye bangaren mahaifiyarta ta koma. Ta same ta idanunka a lumshe tana tuna yadda Daddy ya canza ma ta, kamar ba mutumin da baya son ɓacin ranta ba, kamar ba wanda yake shiga damuwa idan ba ta da lafiya ba, amma yau ga ta kwance ko ya zo sai dai ya tsaya daga bakin kofar ya yi ma ta magana baya shigowa ciki. Kuma duk a sanadiyar matar da ta taimaka da zuciya ɗaya a a rayuwa. Matar da ta ɗauke ta kamar ƴar uwa take ƙaunarta da zuciya ɗaya. Kalli rayuwar nan abar tsoro ce. A hankali ta bude idanunta akan Ma'eesha tana tausayin rayuwar da yarinyar za ta fuskanta bayan babu ita a duniya. Don ba ta da in da za ta je, Daddy ya ma ta shamaki da danginsa, dole ta zauna gidan ubanta. Kuma ba za ta yi rayuwar farin ciki da jin dadi ba. Dama a ce ta aurar da ita ga miji nagari da ba ta da wani damuwa, ta san tana zaune gidan mijinta ba za ta zauna a wannan gidan ba. Ta kira sunanta a hankali. "Ma'eesaha." "Na'am Mummy." "Kar ki sa a ranka duk wanda kike tare dashi a yau ba zai iya rabuwa da ke a gobe ba, dan haka karki sa rai da mutum kowa ki so shi saffa-saffa. Saboda wanda muke tare da su yanzu anjima babu su. Ɗan adam yana iya rabuwa da ke a duk yanda kike da shi, shi ya sa da kowa ma ki zauna da shirin rabuwa da shi ko wane ne, ke dai ki zauna da kowa da zuciya ɗaya, duk wanda ya tafi ko ba yanzu ba wata rana sai ya ga amfanin ki ko ya tuna ki saboda son da kila ma sa da ALLAH da kuma zaman da kika yi dashi dan Allah. Allah ya sa ki dace duniya da lahira, Allah ya haɗa ki da masu son ki da zuciya d'aya wa 'yanda suka san kina sonsu, Allah ya raba ki da wanda duk yanda za ki so su ko daidai da rana ɗaya ba su tuna kin taɓa sonsa ko ka ta6a masa alkhairi ko wani abu naki a rayuwa, in dai mutum ya samu wata dama kai ma sai ya rabu da kai saboda yana ganin ya fi 'karfin ka shi ya sa sai Allah ya kwace daman shi kuma saboda shi da zuciyan kowa yake amfani. Allah ya haɗa ki da masoyan gaskiya." Cikin sanyin jiki ta ce. "Amin Mummy." Mummy idanunta a kafe kamar tana kallon sama, sai Ma'eesha ta ce. "Mummy na ba shi abincin ya tafi da shi ya ce yana godiya a gaishe ki da jiki." Ta yi maganar tana riko hannun mahaifiyarta, sai ta ji hannunta ya saki yaraf. Gabanta ya tsananta faɗuwa fargaban ya ƙaru. Ta kira sunanta sau uku shiru, don haka tana kokarin fita ta kira Inno kenan sai ga Inno ta shigo. Da sauri ta karasa bakin gadon tana kallon Mummy. Shafe ma ta idanun ta yi tana hawaye. Sannan ta kalli Ma'eesha dake kallon ta kamar wata sokuwa ta ce. "Sai dai mu yi hakuri Allah ya yi wa Mummy rasuwa ta riga mu gidan..." Tim ƙarar da ta ji ne ya saka ta juya da sauri, nan ta ga Ma'eesha kwance ta sume a wajen. Ihu ta saka wanda ya janyo hankalin Mamy dake zaune a falo. Kuma daidai lokacin ne Daddy ya shigo falon. Yana jin abun da Inno ke fada ya yi hanzarin nufar ɗakin . Wajen Mummy ya nufa ya duba ta sosai ya tabbatar rai ya yi halinsa ya sa shi lulluɓe ta har da fuskarta yana mai zubar da hawaye. Yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya da ya mayar ya canza wani abu. Ruwan sanyi ya ɗauka a cikin fridge dake cikin dakin, ya watsa wa Ma'eesha. Ba ta farfaɗo ba har da aka yi sau uku sannan ta farfaɗo tana matsanancin kuka. Faɗa wa ta yi jikin mahaifiyar tata tana kuka mai tsuma zuciya. Tana rungume da gawar tana surutai. "Mummy ta za ki tafi ki bar ni cikin wannan duniyar mai cike da tarin kalubale? Mummy ba zan iya ba, ke ce gatana, ban san ya zan yi ba. " Haka ta dinga ihu tana sambatu Inno na rarrshin ta. Mamy kam ko magana ba ta yi ba ta juyabta bar ɗakin. Daddy ya kira mutane ya sanar da su. Lokacin da Alhaji Shamsuddin ya ji labarin rasuwar Inno ya shiga tashin hankali sosai ba kadan ba. Yana tuna rayuwar da ta yi a gidan marayu da yadda take yi ma sa addu'a idan ya kawo ma su abu. Dole ya shirya ya bar ƙasar dak da cewar yana fushi da ɗan nasa Daddy. Domin gabadaya sauyawar da Daddy ya yi ya shafe su har da su ma. Domin ya daina kiran su a waya ko sun kira baya ɗaga wa. Ba don komai ba yake ma su haka sai don sun nun ba sa son auren nan fa ya yi musamman da bai sanar da su ba sai bayan bikin da yadda Ma'eesh ta ba su labarin yadda auren ya kasance, da kuma wace ce ita Mamyn da yaranta da zo da su. Dalilin haka ya saka Mamy ta ce wa Daddy ya hana Ma'eesha zuwa gidan kakannin nata tana week end. Duk yadda Daddy ke tsoron iyayensa yanzu ba ya yi sai tsoron Mamy da bin umarnin ta. Sai abun da ta ce yake yi. Ko da Hajiya ta yi ma da maganar Ma'eesha ta daina zuwa week end gidanta ya ce wai ta daina zuwa daga yau ya raba ta ya gidan ya kuma yi wa Ma'eesha gargadi sosai akan zuwa gidan kakannin nata har cewa ya yi bai yafe ma ta ba. Nan da nan labarin rasuwar Mummy ya karade unguwar. Ta yi jama'a sosai har daga wasu unguwannin da dama sun zo . Bayan an yi ma ta sutura za'a kai ta makwancinta anan Ma'eesha ta dake rike cewa har tana kokarin fita waje za ta bi su Sai da Inno ta rike ta. Daga nan ta sai ta liƙe wa Inno a jiki, don ko kakarta Hajiya Turai ba ta lyarda ta je kusa da ita ba, saboda Daddy ya yi ma ta iyaka da ita. Ta canza kamaar ba ita ba, gabadaya ta yi sanyi duk da cewa dama ita ba mai hayaniya ba ce. Har aka yi kwana bakwai ba ta wani iya cin abinci, Inno ke kokarin ba ta abinci ba ta ci sai dai ta sha ruwan tea idan ta matsa ma ta ma ne take sha. Kasancewar ba ta da dangin uwa na uban ma Mamy ta sa Daddy ya yi ma ta shamaki ita da danginsa. Ba ta taɓa jin ciwon rashin dangin uwa ba sai yanzu, da tana da su to ba shakka can za ta je ta nemo su. *Bayan sati ɗaya* Yau juma'a ya yi daidai da ranar da Mummy ta cika sati biyu da rasuwa. Gidan kamar ba gidan mutuwa ba, sai harkokin su suke yi, idan aka cire Ma'eeha da Inno. Don su ne ka kalle su har yanzu ka san suna cikin damuwa. Sai kuma Jamil babban yaron Mamy shi ma mutuwar ta shige su, amma iya su ne suka da mu sauran sai a hankali. Haka dai rayuwa take ta tafiya . *Bayan sati Uku.* _Makaho_ Tafiya yake yi rike da sandarsa ta jagora ya tsaya a ƙofar gidan su Ma'eesha. Maigadin baya nan don haka direba ne zaune a bakin gate ya ji ana ƙwanƙwasa kofar ya buɗe. Ganin makaho ne ya ce . "Mallam Khalifa kana lafiya?" Don haka ya ji Mummy da Ma'eesha na kiransa da Khalifa ba su ce ma sa makaho. "Ya amsa da lafiya lau ya ƙoƙari?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Ya haƙurin Hajiya kuma?" Cewar Makaho. Direba ya ce. "Haƙuri namu ne duka." Daidai lokacin mota ta yi horn sai Direban ya bar makaho ya tafi ya bude gate. Laila ce ta shigo da motar ta yi parking space. Idanunta ya sauka akan motar Ma'eesha dake gefe. "In sha Allah wata rana sai na raba ki da wannan motar ta zama mallakina. Wato saboda ke ƴarsa ce ya siya ma ki tsadaddiyar mota, amma ni kuma ya siya ma ni mai sauƙin kuɗi. Mu ba je zuwa komai ma sai na raba ki da shi ba iya motar ba." Fitowa ta yi tana yi wa Khalifa wani ƙasƙantaccen kallo ta ce. "Shi kuma wannan makahon me ya kawo gidan nan, bayan wacce ta ce ya dinga zuwa ta mutu sai dai idan kabari zai bi ta can ta bashi abincin da take ci." Muryarta kawai Khalifa ya ji ya gane ita ce ranar ta yi ma sa maganar mabarata. Kafin ya yi magana sai Direban ya ce. "Ina ganin wajan Hajiya Ma'eesha ya zo." Laila ta yi ɗan jim sannan ta ce. "Ma sha Allah." Daidai lokacin Mamy ta fito tana kallon su kafin ta ce. "Lafiya kika tsaya a nan?" "Wai ina ganin baƙon Ma'eesha ne." Sai a lokacin Mamy ta lura da Makaho, ta kalle shi sama da ƙasa. Wasu kuɗaɗun kaya ne a jikinsa ma su arha, dai hula taɓa ni ka ji hadisi da ya sanya a kai, sa hankali silifas a ƙafarsa. Wani tunani ya zo wa Mamy ta yi dariyar mugunta ta ce . "Wajen Ma'eesha ka zo ko?" "Eh na zo ne na yi ma ta ta'aziyya da bankwana don daga yau na gama zuwa gidan nan, tun da Hajiya Allah ya karbi abinsa Allah ya jikanta da rahama. Direba ne kawai ya amsa da Amin. Kallon Direban ta yi ta ce. A kai shi ɗakin baki, yanzu zan tura ma sa ita . Daga haka ya bar wajen Laila ta mara ma ta baya. Suna shiga falon ta damu Daddy ta ce . "Dama Alhaji akwai maganar da nake so mu yi ne." Ya ajiye wayarsa ya ce "Ina jin ki." "Ya kamata a tausaya wa yaron nan kullum sai zuwa zance yake yi, tun uwar na da rai har ta rasu , bayan rasuwar ma kullun yana zuwa ɗebe ma ta kewa yanzu haka ga shi can ɗakin baƙi." "To ai Ma'eesha ta fi karfinsa makaho ne fa." "Kamar ya ta fi karfinsa makaho ba mutum ba ne, ai idanunsa ne kawai ba sa aiki, amma idan aka aura ma sa ita an samu lada taimako ne ai za ta taimaka ma sa tunda ita mai kula da gida tana gani, kuma idan suka haifi yara ita ce mai kula da su ba shi ba." Shiru ya yi cikin rashin yarda da zancen, ganin haka ta ɓata rai cikin bayar da umarni ta ce. "Ina son daga yau juma'a gobe Asabar a ɗaura auren makahon nan da Ma'eesaha." Shiru ya yi tana tunani ta sake cewa. "Ko ba ka ji ba ne?" "Na ji shi ke nan duk yadda kika ce haka za'ayi." Laila dake tsaya tana jin su ta wuce ɗakinta cikin farin ciki. To ba damuwa ka je ka sanar da ski gobe ya nemi sadaki ya kawo a ɗaura ma su aure, idan bai da kudin a bashi sadaka kawai kowa ya huta. Don gobe ko ana ha maza ha mata sai an ɗaura wa yarinyar nan aure da makahon nan." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page1️⃣9️⃣ To ba damuwa ka ke ka sanar da shi gobe ya nemi Sadaki ya kawo a ɗauara ma su aure, idan bai da kuɗin a bashi sadaka kawai kowa ya huta. Don gobe ko ana ha maza ha mata sai an ɗaura wa yarinyar nan aure da makahon nan." Da mamaki Daddy ke kallon ta amma ya kasa yi ma ta musu. Don duk abinda take so ko ta furta sai ya tsinci kansa da bin Umarninta ko da ba ya son hakan, amma ba ya iya yi ma ta gardama. "Ka tashi mu ke ka same shi ya san da zancen." Tashi ya yi ba don ya so ba sai don zuciyarsa na azalzalarsa da ya bi umarninta. Ko da ta tura ƙofar falon baƙin ba ta yi sallama ta shiga, a tunaninsa Ma'eesha ce amma yanayin takun ƙafarta da kuma ƙamshin turaren ya ji ba irin na Ma'eesha ba ne. Muryar Daddy da ya yi sallama ya saka shi ya amsa da. "Wa'alaika Salam warahmatullah. Daddy Barka da rana." "Yauwa Barka dai." "Khalifa sunan ka ko?" "Eh Daddy." "Kana da mata ne?" Sai da ya ɗan yi jim yana mamakin dalilin tambayar kafin ya ce. "Ba na da mata Daddy." "Shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama." Cewar Mamy tana Murmushin mugunta. "Na ba ka auren Ma'eesha gobe ka nemo sadaki ka kawo za'a ɗaura ma ka aure da ita." "Sai da ya kike tsaye daga zaunen da yake, tsabar mamaki da al'ajabi." ",Daddy Ma'eesha ba sa'ar aurena ba ce, ta fi ƙarfina, ni fa makaho ne, faƙiri wanda ba shi da cin yau bare na gobe, ta ya zan iya ɗaukar ɗawainiyarta, bayan ina makaho ballantana a ce zan iya yin wani aikin da zan riƙe ta." Mamy ta yi saurin cewa. "Ba mutum ke yi ba Allah ke yi, baƙin da Allan ya tsaya baya hana ma sa abincin da zai ci. Kai dai ke nemi sadaki ka kawo ko nawa ne, idan ma ba ka samu ba ka zo za'a ba ka ita Sadaka." Tana gama fadar haka ta ce "Ko ba haka ba Alhaji, sannan a wannan masallacin za ka so kafin sallar azahar, don ana idar da sallar sai a ɗaura aure kawai." "To na gode Allah ya saka da alkhairi." "Mu je Alhajina." Cewar Mamy tana jan hannunsa ganin ya karaya kamar ba yadda zai yi ne. Suka fice suka bar shi cike da mamaki. Yana cikin wannan mamaki ne ya ji sallamar Ma'eesha cikin siriryar muryarta. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam warahmatullah." "Sannu da zuwa ina wuni?" "Lafiya lau Alhamdulillah." Ya amsa yana tunanin abun da mahaifinta ya ce ma sa. Kafin ya buɗe baki ya ce. "Ya ƙarin haƙurin Mummy." "Alhamdulillah." "Allah ya jiƙanta da rahama ya sa Aljanna maɗaukakiya ce makomar ta. Sannu da imani kin ji Ma'eesha." "Amin na gode." Ta amsa tana goge ƙwalla. Muƙe wa tsaye ya yi yana cewa. "Dama na zo ne na yi ma ki ta'aziya tare da sallamar bankwana, don ba zan sake zuwa gidan nan ba, dan wacce ta kawo ni nake zuwa yanzu babu ita a doron duniya. To me zai da na ci gaba da zuwa, sai dai kuma yanzu Daddy ne ya zo da wani al'amari mai girma." "Wane Daddy ya zo da al'amari mai girma?" Ji ya yi ba zai iya fada ma ta ba, don haka sai ya ce. "Cewa ya yi na zo gobe." "Ma sha Allah, to sai ka ci gaba da zuwa ai tun da ya baka dama. Bari na je na kawo ma ka abinci." "Ba na jin zan iya cin abinci yanzu." "Okay bari na kawo ma ka snacks da lemu ka tafi da su ." Tana gama faɗar haka ta fice, bai tsaya jiran ta ba shi ma ya fice, don ya shiga damuwa sosai. Ko da ya dawo ta yi mamakin rashin ganinsa, ta tambayi maigadi ya ce ya ga ya fice. Komawa ciki ta yi ta tarar da Daddy zaune shi kaɗai. Bayan ta yi masa sallama ta ce tana son gobe ta je saloon, kai ya jinjina ma ta kawai ya kasa magana . _Makaho_ Yana barin gidan su Ma'eesha ya nufi unguwar da yake , kasancewar masallaci yake kwana dama. Bayan an idar da sallar la'asar ya keɓe shi da limamin masallacin ya sanar da shi abun da Daddy da Mamy suka ce na ba shi auren Ma'eesha. Mallam Liman ya yi mamaki sosai ba kaɗan ba, kasancewar ya san cewa Ma'eesha ita ce ƴa ɗaya tilo da Alhajin ya mallaka, to wane dalili zai sa ya aurar da ita ga makaho talaka. Ya san cewa za ta sha wuya sosai ba kadan ba, ya kuma san wannan ba an yi ba ne dan farin cikin yarinyar sai dai bakin cikinta. "To yanzu na ga a masallaci kake kwana, to kana da ɗakin da za ka ajiye ta ne?" "Ba na da shi ." Ya fada cike da damuwa. "To akwai wani gidan haya nawa da nake da shi, akwai wani ɗaki guda ɗaya can ƙarshen cikin gidan. To zan ba ka ka zauna da ita a ciki sai dai ba'a shafa siminti ba, zan saka a yi wata dabara da za ku zauna cikin rufin asiri." "To na gode Allah ya ƙara arziki." "Amin ya Allah, kana da kudin sadaki?" "Sun ce wai na je ko nawa ne na kawo, idan ba na da shi ko sadaka za su bani, don haka zan duba ƴan kudin da nake turawa ko nawa ne zan bayar." Addu'a da fatan alkhairi Mallam Liman ya yi ma sa Sannan makaho ya sa nemi alfarma yi ma sa wakilci ya karba ma sa auren Ma'eesha ya amsa ma sa . A yammacin ranar Mallam Liman ya tura iyalinsa ta je ita da maƙociyarsu suka je da buhun siminti aka shimfiɗa suka yi ƴan dabaru sannan suka ja kofar suka tafi. A daren ne Mallam Liman ya kai Makaho gidan nasa har ɗakin da za'a saka Ma'eesha ya raka shi. Godiya sosai ya yi masa suka fito a tare. Washegari aka ɗaura auren Khalifa da Ma'eesha akan sadaki Naira dubu uku da Khalifa ya bayar. Ɗaurin auren da ya ba wa jama'a mamaki da al'ajabi, kamar Alhaji Ibrahim Khalil ne zai aurar da ƴar sa ɗaya tilo ga wani makaho kuma faƙiri. Ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki ya ke sanar wa da Mamy kuma komai, wanda duk maganar da yake yi na auren a kunnen Inno. Wacce ta kaɗu da jin zancen, ta shiga kitchen tana goge hawayenn tausayin Ma'eesha. Wayarta ta fara tunanin ɗauka ta kira Ma'eesha ta sanar da ita kada ta dawo ta gudu. *Cigaban labari* Ƙarfe huɗu na asuba Ma'eesha ta farka daga barci da take yi. Sautin muryarsa mai amo ta ji ta ji yana karatun Alkur'ani mai girma. Yana zaune saman sallaya da alama sallama sallah ya idar. Sauraron muryarsa take yi yadda yake ba wa kowane harafi hakkinsa, yana karanta suratul Yasin. Lumshe idanunta ta yi tana jin wani sanyi da nutsuwa na ratsa ta. Ya idar ya kama wata surar. Har sai da aka kira sallar assalatu ya juya bangaren da Ma'eesha ke kwance kamar wanda idanunsa suke gani. Ita kuma sai ta yi saurin lumshe idanunta kamar mai yin barci da gaske, ko ta mance makaho ne baya gani oho. Tashi ya yi ya karasa bakin katifar bayan ya yi lalube. Da ya ji ya taɓa pilow ne ya bubbuga pillow ɗin a hankali. Dama ba barci take yi ba hasalima ta buɗe ifsnunta da ta ji takun tafiyarsa. "Ma'eesha." "Na' am." "Ki tashi ki yi alwala ki yi sallah lokaci ya yi ." "To zan tashi." "Allah ya baki iko." Ya fada yana laluben Sandar jagoransa. Bayan ya taɓa ta ne ya saka ya ce. "Ni zan tafi masallaci." "A dawo lafiya." Tashi ta yi tana jin alamar cizon sauro a jikinta. "In sha Allah gobe ba zan manta ba zan siye maganin sauro in sha Allah. Ko ma na nemi zanin sauro." _Nadra_ Ta kasa haɗa idanunta da nasa saboda wani irin kwarjinin da yake yi ma ta. Sai ta ya kamar za ta kalle shi sai ya kasa saboda kaifin idanunsa gare ta. Kallon ta ya yi ba yabo ba fallasa ya ce. "Ki shanye shi duka, ki ba ni kofin." "Gabaɗaya tea din jinsa take kamar tana shan magani. Bakinta ba daɗi don jin zazzaɓi take yi ma a jikinta, ga kanta dake bala'in sara ma ta, kuma baya rasa nasaba da kukan da ta sha. Hawayenta ya gani yana sauka a hannunta da take rike da tea. "Wai ke kuka baya yi ma ki wuya ne, yanzu me na yi ma ki daga ba ki abinci shi ne za ki dinga yi ma ni kuka?" Kai ta girgiza ma sa alamar a'a. "To me aka yi ma ki na kuka ne haka?" Shiru ba ta ce komai ba. "Saboda an aurar da ba ke ba ga wancan ustazun ba ko?" Shiru ta yi ma sa ko motsin kirki ta kasa yi tana dai rike da kofin a hannunta. "To idan ma don ba'a ba ki wanda kike so ba ne ya saka kike kuka to ai ba ke kadai ke da kuka ba, ni ma da kukan zan zauna na yi ta yi, saboda masoyiyata Sidra da nake so ta gudu aka aura ma ni ke kin ga ni na sai na zauna mu yi kukan tare ko?" Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga ya zuba ma ta rikitatun idanunsa yana kallon ta. Kafin ya ci gaba da cewa . "Ban taɓa kawo wannan ranar a tarihin rayuwata ba." Cikin kuka ta ce . "Yaya Fahad." "Na'am." Ya amsa yana kallon ruwan tea dake hannunta, don kazar ma ta ce ba za ta iya ci ba. "Ina neman wata alfarma a wajen ka." "Ina jin ki?" "Na san kuna son juna kai da Aunty Sidra, kuma ban san dalilin da ya sa ta tafi ranar aurenku ba, amma na san tabbas za ta dawo. Kuma soyayyar da take yi ma ka ba za ta iya cire shi daga cikin zuvuyarta ba. Ina son duk ranar da ta dawo matukar ta nuna tana son zama da kai to ka sauwaƙe ma ni sai ka aure ta, ni ma na je na auri Ya Sayyadina." Shiru ya yi yana kallon ta kafin ya ce. "Na ji alfarma da kika nema, zan yi ma ki ɗayaba cikin biyu. Ma'ana zan sake ki sai ki je ki auri Ya Sayyadi da kike so, amma ban ma ki alƙawarin Auren Sidra ba." Za ta yi wata magana kenan ya ɗaga ma ta hannu. Dole ta yi shiru. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Gud night." Ya fita daga cikin ɗakin bayan ya rage hasken ɗakin ya ja ma ta kofar ɗakin ya rufe. Ajiye kofin shayin ta yi ta fashe da kuka mai cike da ƙunci. "Ta ya zan iya za zaman gidan nan da aka gina da sunan Yayata, na yi amfani da kayan ɗakin da ka ajiye da sunanta, sannan na yi amfani da kayan lefenta sannan na mallaki masoyinta da tafi kauna fiye da komai a rayuwar ta, yau a ce shi ne mijina anya za ta fahimce ni kuwa da wani ido zan kalle ta ?" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣0️⃣ Ta ya zan iya zaman gidan nan da aka gina da sunan Yayata,na yi amfani da kayan ɗakin da aka ajiye da sunanta, sannan na yi amfani da kayan lefenta, sannan na mallaki masoyinta da ta fi ƙauna fiye da komai a rayuwar ta, yau a ce shi ne mijina za ta fahimce ni kuwa da wani ido zan kalle ta. _Fahad_ Yana komawa part ɗin sa kai tsaye ya nufi bedroom, bai tsaya ko ina ba sai bathroom. Don shi baya gajiya da yin wanka. Kayan jikinsa ya cire ya tsaya jikin babban madubin dake cikin bathroom ɗin, ffaɗan ƙirjinsa ya zuba wa idanu yana kallon zanen Tattoo da ya sa aka yi ma sa , daga gefen ƙirjinsa har zuwa damtsen hannunsa. An yi ma sa zanen butterfly da kuma sunan sa haɗe da na Sidra. Wani ɗaci ya ji a ƙasar ransa ji yake yi ina ma a ce zai iya goge wannan zanen Tattoo dake jikinsa da ya goge ko ya daina ganin sunan Sidra a jikinsa. Wanka ya yi don shi akwai shi da yawan wanka sosai. Almost 30 minutes ya ɗauka yana sakawar wa kansa ruwa kafin ya yi wanka da shower gel din sa mai ƙamshi. Towel ya ɗaura a ƙugunsa dai wani ƙarami da yake tsane ruwan kansa da shi. Gaban dressing mirror dake cikin bedroom dinsa ya tsaya. Yana kallon kansa a jikin madubin, da alama shi mutum ne mai yawan don kallon kansa a madubi. Body spray ɗin sa ya shafa sannan ya shiga cikin closet ɗin sa. Bai sanya wasu kaya ba sai wando three-quarter fari da ya saka, ya zo ya hau saman tangamemen gadonsa ya haye daidai lokacin da wayarsa ta soma ruri. Dubawa ya yi still number wayar ɗazu ce, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma dai kuma ya ɗaga har lokacin bai yi magana ba. Jin shiru ya saka ya kashe wayar gabaɗaya ya kwanta. _Sidrah_ Gabaɗaya daren ranar ba ta yi barci ba sai kuka da ta kwana tana yi. Ta yi danaasanin tafiya ya bar aurenta, ga shi yanzu ta yi biyu babu, ba ta ga tsunsu ba ta ga tarko. Ita ba ga samun abinda ta fito nema ba don yin suna da ɗaukakar da take so ta yi. Sannan auren da ta tsallake ta baro da niyyar idan ta koma ta ba iyayenta haƙuri su haƙura da sake saka ranar ɗaurin auren sai ga shi an maye gurbin ta da ƙanwarta. Ko da a mafarki yadda ta san Fahad wayayyen mutum ɗan gaye ji da kansa ba zai taɓa amincewa ya karbi Nadra ba, amma abun mamakin sau ta ga ya amince da ita yarinyar da yake cewa kamar ba ta waye ba shi ne ya amince ya aura. Har yana iya keɓe wa da ita kenan a wanann daren, wa ya san me suka yi? Wannan tunane-tunanen ne ya hana ta barci yake saka ta zubar da hawaye. Fatan ta gari ya waye ta ɗauki hanyar komawa gida. Ta roki iyayenta kuma dole Nadra ta bar ma ta Fahad Majidaɗi. _Nadra_ Bayan fitar Fahad daga ɗakin ta dinga riskar kuka kamar ranta zai fita. Don har sai da ta ji kanta na sara ma ta kamar zai fashe sannan ta yi shiru, don idanunta ko gani ma ba ta yi saboda tsabar kumburin da suka yi ma ta. A haka ta ƙudundune waje guda da misalin karfe ukun dare ne barci ya yi nasarar ɗaukarta. Da misalin karfe biyar na asuba wayarta ta fara ƙara kamar yadda ta saita ta. A hankali ta motsa tare da kokarin bude kumburarrun idanunta da suka yi ma ta nauyi sosai. Addu'ar tashi daga barci. Ta tashi zaune tana dafe kanta da hannayenta biyu, dan ciwon kan nata sosai ya ƙaru. Saukowa ta yi daga saman gadon tana rike da kanta ta nufi bathroom ɗin dake cikin ɗakin. Tana shiga ta ji jikinta na rawa sanyi take ji sosai. Tana kakkarwa ta tashi daga duƙen da take, ta lallaɓa ta yi wanka da ruwan zafi sannan ta sake amfani da ruwan ɗumi ta gabatar da alwala ta fito ɗaure ta towel. Da kyar take yin tafiya har ta karasa cikin closet. Komai na kayan sabo ne a ciki. Tun daga kan kayan lefe har da kayan da aka ɗinka wa Sidra wanda iyayen su suka ɗinka ma ta, sai waɗan da Fahad ya kawo ma ta ya ce sun burge shi ne. Cikin kayan da aka kawo ma ta daga gida ta duba bayan ta saka underwears sai sai sun matse ta kasancewar ta fi Sidra cikar halitta. Don ta fi Sidra nono da hips. Dan ko tela ma idan zai yi ma su ɗinki na Nadra yakan fi na sidra kaɗan. Don haka pant ɗin dai ta saka ya shiga ma ta, amma bra bai shiga ba don rabin nononta a waje suke kuma sai ya maste ta, kasancewar da sunan Sidra aka ajiye komai to komai size ɗinta ne ita kuma ba ta da nono Sosai ƙanana ne da ita. Don haka Nadra ba ta wahalar da kanta Wajan saka bra din ba ta bar nononta haka nan, kasancewar nonon nata irin ma su kan tasa ɗin nan ne a tsaye suke ƙyam. Wata doguwar rigar material mara nauyi ta saka bayan ta sa turare sannan ta saka dogon Hijabinta ta ɗauki sallaya ta fito ta shimfiɗa. Sallar nafila ta yi kafin ta yi sallar asuba ta zauna tana azkar. Duk da kasancewar ta mai yawan karanta Alkur'ani ne da safe amma Yau kam ba ta jin za ta iya karatun Alkur'anin nan da ta saba. Kwanciya ta yi a nan saman sallayar da ta yi sallah. Don ciwon kanta nan nan ba ta daina jin sa ba, ga sanyi tana ji. Don haka sai ta ƙudundune kanta cikin Hijabin a nan saman sallayar ta yi barci. Da misalin karfe takwas na safiya a cikin ɗan barcin da ya ɗauke ta ne ta ji ƙamshin turarensa ya ziyarci hancinta. Wani faɗuwar gaba ta tsinci kanta a ciki. Duk da ba ta son bude idsnunta da suka yi ma ta nauyi amma sai ta ɗan tashi zaune daga saman sallayar ta kalle shi da kyar. Sanye yake da farar jallabiya a jikinsa ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana kallon ta. Daidai lokacin da wayarta dake kan gado ta soma ruri, tana son ta miƙe amma ta kasa. Sai ta ga ya nufi gadon ya ɗauki wayar. Sunan da ya gani a screen ɗin wayar yana yawo shi ne an rubuta YA SAYYADINA. Sannan aka saka emojis na love da kuma emoji na heart a gaban sunan. Miƙa ma ta wayar ta yi ba tare da ya yi magana ba. Kuma ya tsaya a saman kanta. Har kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan ta ɗaga tare da yin sallama. "Assalamu alaikum Ya sayyadi" "Wa'alaiki Salam warahmatullah ya Sayyadata." Shiru ba ta sake magana ba, sai dai tana da yaƙinin Fahad ɗin ma ya ji maganar Ya Sayyadi, dan wayar sauti na fita wanda ke kusa da kai zai ji maganar na cikin wayar. "Sayyadata an watse taron biki lafiya ko?" Ban samu zuwa..." Sai kukanta ya ji ta fashe da shi. "Subhanallah, subhanallah ya sayyada me ya faru ne, ki faɗa ma mi make faruwa ne?" Ya faɗa a ruɗe saboda jin kukanta. Fahad ya karbi wayar daga hannunta ya ce. "Kai daga yau kada ka sake kiran wayar nan?" "A'uzubillahi me ya haɗa Sayyada da rijalu kuma, ke sayyada waye Wannan kuma? Subhanallahi A'uzubillahi minash shaiɗani rajim ƙato da wayar Sayyada da sanyin safiyar nan. Wa'iya zu billahi a'uzu billahi." Cike da takaici Fahad ya ce. "A'uzubillahi akanka. Kai bari na yi ma ka gargadi na karshe, idan har ka sake kiran wayar nan sai na sa an koya ma ka hankali, za ka san waye Fahad Majidaɗi." Da sauri Ya Sayyadi ya ce. "Fahad Majidaɗi da na sani mijin Sidra?" Bai ba shi amsa ba ya ce. "Ina mai maka gargadi wallahi ranar da ka sake kiran wayar nan duk inda kake a faɗin ƙasar nan sai na saka an kamo ma ni kai, ban damu da wanzuwar soyayyar dake tsakanin ka da Nadra ba, amma a halin yanzu ta yi ma ka nisar da ba zai ka iya kamo ta ba, watakila dai nan da lokaci kaɗan idan na sallame ta za ka iya zuwa gidansu ka ci gaba da alaƙa da ita ko ka aure ta wannan ba damuwata ba ce, amma a halin yanzu tana ƙarƙashina kam ƙarya ne na bar ka ka yi wata alƙa da ita, idan za ka iya jira ka je ka ci gaba da jiranta har zuwa lokacin da za ta fito, amma kam sake kiranta bayan tana ƙarƙashin iko na shi ne kuskure ma fi muni da za ka tafka a rayuwarka." Yana gama fadar haka ya katse kiran wayar tare da yi wa Nadra wani mugun kallo." "Ke!?" Ya kira sunanta da kakkausar murya. Idanunta da suka yi nauyi ta daga ta kalle shi da kumburarrun idanunta. "Idan kika sake magana da wani ƙaton gardi a cikin gidan nan bayan kin san akwai igiyar aurena a kanki sai na shayar da ke madaran mamaki." Ba tare da ya sake magana ba ya fice rike da wayar a hannunsa bai ba ba ta wayar ba. Kuka ta sake fashe wa da shi wanda ya ƙara sa wa ta ji kanta na barazanar tarwatse wa. Yana zuwa falon ya ji ƙarar ƙararrawar ƙofa, sauka downstairs ya yi ya nufi ƙofar ya zai buɗe. _Makaho_ Ko da ya dawo daga masallaci sallar asuba ƙarfe bakwai na safiya. Zuwa lokacin Ma'eesha ta kammala aiyukan gidanta. Ta gyara ɗaki ta share ta yi mopping ta yi wanke-wanken ta wanke toilet sannan ta yi wanka. Dadai lokacin da ta fito da Gas da za ta hada ma su abun breakfast kenan ta ji sallamar sa ya shigo gidan. Ta amsa ma sa sallamar ya shigo ta zuba ma sa idanun tana kallonsa. Sai da ta durƙusa cikin girmamawa ta gaishe shi duk da baya ganinta. "Ina kwana?" "Lafiya lau Mar'atusaliha." Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah, sannu da ƙoƙari Allah ya saka ma ki da gidan Aljanna Firsausi." "Amin ya rabbil izzati." "Me kike yi ne haka, na ɗauka za ki kwanta sakamakon juya ba ki samu isasshen barci ba jiya." "Ai na yi barci kai ne dai ya kamata ka wanta ka huta ko za ka samu barcin da ba ka samu ka yi ba." "Ni da zan fita neman na kai ne zan kwanta na huta?" "Wai nawa kake samu a rana wajan gyaran takalmin da kake yi ?" "Eh to mutane da yawa ba sa yarda su ba ni aiki, kasancewar ni makaho ne ba na gani to ba sa yarda su ba ni aiki, sai su ce wai ba aikin da na iya, sai su kai wani wurin, amma wasu na bayar wa sai dai ba su da yawa. Abun sai sa'a ne wata rana ma bai wuce na samu ɗari biyu wata rana dari biyar amma ban taba samun dubu ɗaya ba. Shi ya sa nake ganin cewa ba zan iya riƙe ki ba, ban cancanci na ajiye mata ba, saboda ba na da halin ciyarwa da me zan ciyar da ke? Sam na kasa dalilin da ya sa iyayenki suka aura ma ni ke, bayan kin saba da cin abinci mai kyau mai tsada, ruwan sha mai tsada sutura mai tsada kayan kwalliya ma su tsada ta ya zan iya yi ma ki duk abubuwan da kika saba da su?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Dama haka rayuwa ta gada, ba komai yake tafiya a yadda yake a da ba." Haka ne Ma'eesha, amma na rasa gane me kike son ki ci ma wa a rayuwa, ko me kike so ki zama meye burin ki?" Murmushi ta yi kafin ta ce. "Ina son na zama mace tagari mai tsoron Allah a fili da ɓoye, tare da biyayya ga manzon Allah mai biyayya ga iyayenta ɗari bisa ɗari da kyautatawa, mai biyayya ga mijinta, idan ya hana ta hanu, idan ya sa za tayi. Wacce take ɓoye adonta ga mazan waje, ta bayyana shi ga mijinta. Wacce take da kunya, gaskiya, adalci da tausayin mijinta. Wacce ba munafuka ba, ba ta sharri dan ta jingina karya a mijinta. Mace mai girmama iyayen mijinta da yan uwansa saboda Allah mace mai gudun duniya da neman na kanta kamar Nana Khadija. Mace mai tallafawa mijinta da dawainiyar gida kamar Nana Fatima. Mace mai kishin mijinta kamar Nana Aisha." Allah sarki ƴar aljanna, yanzu kina ganin za ki iya karɓa ta a matsayin mijin aurenki, za ki rayu da ni a cikin kowane hali?" "Me ya saka ka yi Mani wanan tambaya?" "Saboda na ga kin fi ƙarfin na, ke ba ajina ba ce kin wuce sa'ar aurena, a matsayina na nakasashshe miskini ta ya ke da kika rayu cikin daula da wadata za ki iya zama da ni?" "Me za hana na zauna da kai idan ƙaddarar aurena da kai ne Allah ya tsara?" Ba na son na fita daga cikin salihan bayi ma su godiya da duk abin da Allah ya aiko ma su da shi? Mai daɗi ko mara daɗi, ma su jiran ƙaddara duk daɗinta duk raɗaɗinta su haɗiye ta, ko ba ka san cewa Allah ya fi mu sanin abun da ya dace da mu ba?" Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Haka ne?" Murmushi ta yi kafin ta ce. "Ina son ka ba ni tarihin rayuwarka ban san kowa naka ba, ina son sanin Asalinka?" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣1️⃣ Ina son ka ba ni tarihin rayuwarka ban san kowa naka ba, ina son sanin Asalinka. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Yanzu aiki kike yi, ki ci gaba da yin aikinki idan muka b zauna ba ki aikin komai ni ma ba na komai sai na baki." "To shi kenan, bari na haɗa ma na breakfast." Shiga cikin ɗakin ya yi ya bar ta nan tana kiciniyar ɗora girki. Tana nan zaune ta ga ya fito daga ɗakin rike da wasu kayan a hannunsa, da alama wanka zai shiga. "Ka bari na sa ma ka ruwan zafi ka yi da shi don akwai sanyin safiya." Murmushi ya yi tare cewa. "Ma'eesha kenan, ni da na saba da ruwan sanyi me zai dame ni kuma yanzu? In dai wannan ne na saba da shi kar ki damu kanki, babu irin rayuwar da ban gani ba." "Na sani amma ya kamata ka san cewa tsakanin da da yanzu akwai banbanci, da ba ka da aure ba ka da wacce za ta dafa ma ka ruwan zafi ka yi ji wanka, yi yanzu Allah ya ba ka ya kamata ka san cewa akwai banbanci tsakanin lokacin da kake da aure da yanzu. Yanzu fa ɗan gata kake mai cikakken iko, ka saka ayi ka haka a hani ai kuwa ka ga da banbanci ko?" "Haka ne." "To ba ni mintuna biyar kaɗai zan dafa ma ka ruwan zafi yanzu." Zama ya yi akan dangaramar ƙofar ɗaki ta zuba ruwa a cikin tukunya ya yi zafi sannan ta juye ma sa cikin bokitin ta mai ma sa har cikin ɓanɗaki." "Na mai ma ka ruwan cikin banɗaki." "Na gode ma ki Ma'eesha Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa sannan ya shiga banɗaki, ta fara kiciniyar haɗa ma su breakfast. Bayan ya gama ya fito sanye da wasu kayan a jikinsa, waɗanda ya cire kuma suna a hannunsa. Kallonsa ta yi sannan ta ce. "Wai me ya saka da ka yi wanka kake saka kaya ne, kar ka damu ko da ba ka gani na ai idan za ka canza kaya zan fito daga cikin ɗakin na ba ka wuri ka shirya ne, amma ace daga yin wanka ba ka tsane jiki ba kuma ba ka shafa man shafawa ba kawai sai ka ɗauki wasu kaya ka saka?" "Za'a daina in sha Allah." "Da ya fi." Ta faɗa tana mai cigaba da fere dankalin turawar da take yi. "Bari na tso na ba ka man shafawa da turare ka shafa." Ta mike ta bishi cikin ɗakin. Man shafawar da ta ba shi ya shafa ne ya shafa ya kuma ya shafa turaren da ta ba shi. Tana nan zaune ya fito yana yana cewa. "Aikin me zan yi ma ki ne na fara yin yanzu kafin na fita ." "Ka fita ina?" "Neman na kai mana." "Yau da alama za'ayi rana a garin nan, ka je kana ta wahala a cikn rana bai fi ka samo Naira ɗari biyar ba. Don haka cinikin yau na siye zan ba ka Naira dubu ɗaya ka ga ai na ba ka fiye da cinikin da kake yi ." Ga mamakin ta sai ta ga ya tsuke fuska alamar ransa ya ɓaci. _Fahad_ Kafin ya karasa bakin ƙofar har an dake danna wata ƙararrwar. Yana bude ƙofar ya ga ƙanwarsa Rumaisa ce rike da basket na abinci. Sai wasu ƴan mata guda biyu tare da ita, yan matan duk danginsu ne da suka zo biki daga wani garin. Basket ɗin abinci ne a hannun Rumaisa. A tare suka haɗa baki wajen cewa. "Yaya Fahad ina wuni?" Bai amsa ma su gaisuwar da suke yi ma sa ba, hannu ya mika wa Rumaisa alamar ta ba shi basket ɗin hannunta. Ta mika ma sa ya karba zai mayar da ƙofar ya rufe ta ji saurin cewa. "Yaya Please za mu ga Amarya." Tsuke fuska ya yi kafin ya ce. "Wani lokacin za ku ganta." Marairaice fuska suka yi suka hada baki wajen cewa. "Yaya Please." Rumaisa ta ɗora da cewa . "Kuma dama Mama ta ce idan mun zo mu shiga mu gaishe ta mu ce kuma tana gaishe ta." Sauran suka hada baki wajem cewa. "Eh haka ne." Ba su hanya ya yi alamar su shiga ba tare da ya ce komai ba. Suna shiga ya mayar da kofar ya rufe. Suka Zazzauna a fakon kan kujerun dake downstairs. Upstairs ya haye sannan ya ajiye abincin a dinning table ya nufi ɗakinta. Kuka take yi har lokacin tana kuɗudune kan sallayar. Ba ta ji shigowarsa ba sai ƙamshin turarensa da ta ji ya ne ya sa ta tsaida kukan nata, ta ɗago kumburarrun idanunta ta kalle shi. Tana ɗan dafe kanta. "Tashi ki fito ƙannena suka zo kawo abinci Mama ta ce su gaida ke idan sun zo." Tashi ta fara yinƙurin yi tana cije lips din ta na ƙasa. "Ki shiga bathroom ki wanke fuska ba na bukatar sake ganin wannan hawayen." Bathroom ta shiga ta wanke fuska kamar yadda ya umarce ta. Bayan ta fito ne ya yi hana tana bin sa a baya suka fita. A tunaninta suna nan upstairs ne, ganin ya nufi downstairs ta na tafiya a hankali tana jine lips sakamakon ciwon kan da ya sa ta gaba. A hankali take tafiya tana sanye da hijabinta har ƙasa sai flat shoe dake ƙafarta. ",Zuba ma su idanu suka yi suna kallon su. Musamman Nadra da da duk wanda ya kalle ta ya san tasha kuka. Cike da ƙarfin hali take tafiya don har wani jiri take ji. Daf da za su sauka daga matattakalar kenan ta ji kanta na juyawa ta yi kamar za ta faɗi. Ganin haka ya saka ya yi saurin rike ta ya ga ta yi luu za ta yi baya. Cikin zafin nama ya taro ta ya ɗaga ta cak ya koma da ita sama ba tare da ya karasa da ita wajen su Rumaisa sun gaisa ba. Kallon kallo aka fara yi tsakanin Rumaisa da cousin sister ɗin ta guda biyu da suka zo tare. Ɗaya daga cikinsu ce ta saka dariya yana cewa. "To fa, Yaya Fahad ya ɓaro aiki kenan, to amma ba an ce baya son ta ba? To ya hakan ta faru?" Rumaisa ta kalle ta tare da cewa. "Me kenan ya faru?" "Ba ki ga alamar Yayanki ya sha romon amarci ba daren jiya, ki kalli yadda idanunta suka kumbura tsabar kuka, sannan tafiya ma ta kasa yi sai da ya ɗauke ta." Cike da tausaya wa Rumaisa ta ce. "Allah sarki." Ɗayar wacce ba ta yi magana ba ta ce. Ku ga fa da yake cewa baya son auren har jiya fa da ƙyar Mama ta saka shi gaba ya bar gida, da cewa ya yi ba zai zo nan gidan ba Sa sanya ga ɓacin ran Mama sannan ya zo ya tare, amma da ke namiji munafiki ne har ya iya azabtar da ƴar mutane ta kasa tafiyar don jaraba. Gabaɗaya suka saka dariya da shewa. Dadai lokacin ne suka ji ƙamshin turarensa suka juya suka kalle shi. "Ku tashi ku tafi kun zo kuna ma ni ihu a gida." Kamar suna jira kowacce ta mike suka nufi hanyar fita. Komawa ya yi sama ya shiga kitchen ya haɗa ma ta tea sannan ya nufi ɗakinta don kai ma ta, ya dawo ya zo dinning ya ɗauki basket ɗin da Mama ta aikio ma su da shi, sannan ya ɗauki plate a kitchen ya wanke da cokali sannan ya koma ɗakinta. Food flask ɗin ya bude ɗaya, farfesun kan rago ne, ya zuba ma ta. Sai ya bude wani ya ga wainar shinkafa ce sai miyar taushe daban. Tea ya miƙa ma ta. "Karɓi ki sha." Ba ta jin shan komai don haka ta ce. Ta girgiza ma sa kai ba tare da ta yi magana ba., "Ba na son sake maimaita magana ɗaya." Ya faɗa cikin tsare gida. Karɓa ta yi ta fara sha. "Na kawo ma ki bread?" Kai ta girgiza alamar a'a, sai ya miƙa ma ta farfesun. Da ƙyar ta iya cin guda uku ta ajiye. Bayan ya karbi kofin da plate ɗin ne ya fice da su, sannan ya dawo tare da magani a hannunsa. Ruwa ɗauka a cikin fridge dake nan cikin ɗakin. Ya ɓalli magani ya ba ta sannan ya zuba ruwa a glass cup ya ba ta ta sha. Jingina ta ji da kan filo da ke kan gadon, ba tare da ta kwanta ba. Fita ya yi daga cikin ɗakin bayan ya ɗauki basket ɗin abinci ya fita da shi ya ajiye a dinning table. Bedroom ɗin sa ya nufa ya ciro wayar Nadra da ta karɓa ya kunna yana dubawa. Ba ta amfani da social media sosai don what's up kawai ya ga tana yi, ya shiga ya duba shi ma daga ƴan uwanta sai ƙawarta da Ya Sayyadi ne suke yin chatting da shi. Ba ta da groups har wurin text message sai da ya duba. Nan ma ya ga ba wani abu ba rashin daidai da take yi. Ya tuna idan ya karbi wayar Sidra ita ce TikTok, Instagram, Facebook, twitter da sauran su, ga tarin groups kamar Hauka groups ɗin na na maza da mata ba wai iya mata zalla ba. Kuma bai ga group ɗin ƙaruwa ba ko na faɗakarwa sai irin su. Manyan mata, ƙasaitattun mata, mata ma su aji, ma su ji da kansu, wayayyun mata. Da sai sauran su. Amma nan wayar Nadra ya ga ba ma kullun take hawa what's up din ba, wa'azuzzuka na ma manyan malamai ne suka cika wayar video da Audio. Kashe wayar ya yi gabaɗaya ya bude side drawer ya saka ta a ciki. _Rumaisa_ Bayan direba ya ajiye su a gida ne suka fita duka su uku ne dama suka je gidan. Rumaisa, Rahina da Sahiba. Suna fita daga motar jikinsu na rawa suka shiga cikin falon. Nan suka ga gabaɗaya mutanen gidan suna falo har da ɓaƙi da suka zo daga wasu garuruwa. Dariya suka shiga suna yi gabaɗaya mutanen suka mayar da hankali suna kallon su. Inna wato kakar su Fahad ta kalle su ta ce . "Waɗan nan sabbin mahaukatan fa?" Sahiba ta yi saurin cewa "Wallahi ba hauka ba ne Yaya Fahad ko?" "Me ya yi Fahad ɗin?" Cewar Hajiya Jummai mahaifiyar Farida. Rahina ta ce. "Jiya nan ya dinga cewa baya son auren nan, har sai da aka kore shi daga gidan nan ya tafi wajan Amaryarsa. To ga Amarya can idanunta sun kumbura tsabar kuka tafiya ma ba ta iya yi sai ya ɗauke ta kinga yadda ta koma yake wani tarairayarta ko tafiya sai ya ɗauke ta Allah ya sa bai illata ta ba." Rahina ta yi maganar kasancewar bazawara ce ta yi aure shekara ɗaya auren ya mutu. Gabɗaya falon aka yi shiru Mama ko ta yi farin cikin jin haka yayin da bakin ciki ya kama Hajiya Jummai saboda tana taya ƴarta Farida kishi. Farida ko kasa haɗirye ƙincinta ta yi sai kawai ta tashi ta bar wajen tana kuka Dinning area ya nufa ya zauna ya ci waninar da Mama ta kawo ya sha farfesun kaɗan sannan ya tashi. Yana shiga bedroom ɗin sa ya ga wayarsa na ruri. Ya duba ya ga Mama ce. Ɗauka ya yi tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." Daga xan bangaren ta amsa tare da cewa. "Ya kuke?" "Alhamdulillah." "Ya Nadra take ƙannenka sun ce ba ta da lafiya ko?" "Eh haka ne." "To ka kula da ita, ta zauna cikin ruwan zafi ba wanda zai kuma yi ma ta illa ba, sannan ka bar ta ta huta a ƙalla ko na sati ɗaya ne kar ka takura ma ta, don Allah ka bi ta a hankali, na tabbata da daren jiya ka bi ta a hankali da ba za ta jigata haka nan ba." Shiru ya yi bai iya cewa mahaifiyar tasa komai ba, don bai gane in da zancen ta ya dosa ba,kafin ya yi magana ya ji ta katse kiran wayar. Maganganun nata ne suka fara yi ma sa yawa a ƙwaƙwalwarsa. Me zai saka ta zauna a cikin ruwan zafi, kuma akan me zai ɗaga ma ta ƙafa na sati ɗaya. Mama tana magana ne kamar ya kusanci Nasra alhalin ba abinda ya shiga tsakaninsa da ita. To me ya saka ta ce haka. Ya san dai haka nan kawai Mama ba za ta ji zargin wani abu a tsakaninsu da Nadra ba. Tuna zuwa ƙannensa da suka yi kawo ma su breakfast ya sa shi tunanin akwai maganar da suka yi. Mai yiwuwa don sun ga alamar ta sha kuka ne, to me zai saka su faɗi abin da ba su da tabbas akan sa. Daga nan ya tashi ya shiga bedroom ɗin sa. Kayan jikinsa ya rage ya shiga wanka. Yana tsaye yana kallon kansa a madubi kamar yadda ya zame ma sa ɗabi'a. A da idan ya ga Tattoo dake jikinsa ya kalli sunan Sidra da butterfly yakan yi Murmushi. Amma yanzu ji yake yi da zai iya da ya goge sunan daga jikinsa. Ji yake yi kamar ya samu reza ya ya kankare fatar jikinsa. Wanka ya yi da shower gel din sa mai ƙamshi sannan ya ɗaura towel ya fito yana tsane ruwan kansa. Man shafawarsa ya shafa ya fesa body spray ya shiga closet ɗin sa. Shirya wa ya yi cikin ƙanan kaya farar Tshirt mai tsada da wando jeans, ya duba ɓangaren takalmominsa kambas masu tsada, saidesigner sneaker ya saka a ƙafarsa shi ma fari ya ɗaura tsadadden agogonsa Rolex GMT- master ll pepsi sannan ya fesa turarensa Bleu de Chanel (farfum) duk wanda ya gansa ya ga gentleman na gaske mai tsafta da kuma classy. Fitowa ya yi daga cikin closet ɗin ya ɗauki wayoyinsa da makullin motarsa ya fice cikin takunsa na ƙasaita. Har zai wuce sai ya tuna da ita ya koma ɗakinta _Maeesha_ Ganin makaho ya tsuke ne ya ba ta mamaki don ita a fahimtar ta ba ta san ta jmyi ta yi wani abu na rashin daidai ba. "Ka yi hakuri idan na faɗi wata magana da ba ta yi ma ka daɗi ba." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "Ma'eesha mutane suna raina sana'ar nan da nake yi ba na jin daɗi, domin ni albarkarta nake nema. Amma yau ke da kanki kike raina sana'ar? "Ka yi hakuri ba yadda ka fahimta ba ne, ni so nake ka huta saboda ana rana, ina tausaya ma ka ne shi ya sa na ce kudin da kake samu bai fi ɗari biyar ba zan ba ka dubu ɗaya ka zauna ka huta a gida." "Ba na so ki rike kudin ki ni zan fita na nemi gumina da kaina. Ba son raina ba ne na zauna a ce kina ɗaukar nauyin da ya rataya a kaina, na san ba zan iya ɗaukar nauyin ki ba, amma ina son ɗaukar ko da kwatankwacin nauyin ki ba, zan kwatanta, domin ma wata rana zan yi alfahari da cewa na yi wa matata wani abun kuma ta karɓa ta yi amfani da shi. Ki yi hakuri idan kin ji ba daɗi kinji ƴar aljanna ." Murmushi ta yi tana cewa. "Allah ya buɗa ma ka hanyar samu mijina." "Amin matata." Tea ta haɗa ma sa ta bashi bread sai soyayyen dankalin turawa da ƙwai. Suna ci suna ɗan taɓa fira sama-sama. Kafin ya ce. "Yanzu Ma'eesha idan aka wayi gari kayan abincin da kuma siyo sun ƙare, musamman waɗan nan na ku na gayu da kika saba ci kuka ya kasace ba na da kuɗin siya ma ki irin su fa?" "Ba damuwa Allah ke ciyar wa ba mutum ba, duk abinda Allah ya hore ma ka ka kawo zan karba na yi godiya ga Allah, tare da maka addu'a buɗi daga wajensa. Nan suka cigaba da fira har suka kammala sai da ya yi niyyar yi ma ta wanke-wanke ta hana. Dole ya fita bayan ya ɗauki kayan aikinsa na ɗinkin takalma. Yana tsaka da tafiya ya ji kamar ana binsa bayan ya yi nisa da layin, kuka da dukkan alamu mota ce ke bin bayansa. Jin hakan da ya ji ne ya saka shi ya tsaya daga tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya, wata baƙar mota ce tinted glass. Bayan ya fita daga layin ne ya shiga wani layi sai ya tsaya cak da tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya daga bin sa da take daidai lokacin da ya saki sanadar hannunsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣2️⃣ Bayan ya fita daga layin ne ya shiga wani layi, sai ya tsaya cak da tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya daga bin sa da take yi daidai lokacin da ya saki sanar hannunsa. Sannan ya saki kayan aikinsa na gyaran keke. A fusace ya juyo bayansa tamkar mai gani, yayin da matuƙin motar ya yi arba da shi dai ya figi motar a guje tamkar mai gani. Jin motar ta bar wajen Khalifa Makaho bai yi magana ba ya lalubi sandarsa da basket na kayan aikinsa ya yi wucewarsa in da za shi. Ya ɗan yi tafiya mai nisa sannan ya ƙarasa bakin wata karama titi. Da sallama ya ƙarasa wajen, yayin da wasu dake wajan suka amsa tare da cewa. "Ka iso Khalifa?" "Eh ina kwanaku?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Mutane ne a wajen duk da ba sosai ba, don wajen karamar titi ne, kuma akwai hanyar da za ta sada ki unguwar masu kuɗi wanda hanyar suke bi zuwa cikin unguwanninsu. Ba Makaho ba ne kaɗai a wajen, akwai mutane ma su kananan sana'o'i a wajen suke zaune. Akwai mai siyar da yalo a wajen, da mai siyar da kifi gangariya a wajen da wani mai baro dake sigar da Aya sai wata mace mai suyan awara a wajen, daga gefe kuma ga mai shinkafa da wake da mai da yaji. Duk suna wajen saboda babban bishiyar mangwaro ce a wajan ta yi inuwa mai fadi. Nan ne wajen sana'ar Khalifa nan take zama ƙasan bishiyar. Wata rana kuma yakan bar wajan ya yi ta yawo yana neman wanda takalminsa ya tsinke. Mai awara ta kalli Khalifa ta yi Murmushi dama ta saba tsokanarsa a wajen. "Kyakkyawa ya kake?" Ta fada tana Murmushi. "Kyakkyawa don Allah ka dinga sakin fuska ma ma kai kenan fuska ɗaure tamau ba murmushi ba dariya kamar wanda aka aikawa saƙon mutuwa." Bai tanka ma ta ba kamar kullum dama baya tanka ma ta ita ma ba ta fasa tsokanarsa. Mai siyar da yalo ne ya yi magana ya ce. "Wai ke Laure ba za ki ƙyale wannan bawan Allah ba ne, kullum sai kin dame shi da surutu, kuma baya tanka ki ." "Ilu mai yalo ka bar ni, ina son ya yi magana ce na ji muryarsa. Ka san Allah makatntar nan tashi ce kawai cikas ɗinsa. Amma da ba don makaho ba ne wallahi ba na aure shi ko da bai da kudi kuwa. Don ko kyakkyawar surarsa na kalla zan ji daɗi saboda ya haɗu iya haɗuwa rashin idanunsa ne matsalarsa, kuma gaskiya ba zan iya auren makaho ba, don makantar idanun ai mutuwar tsaye ne ba zan iya ba don wahala zan yi da kai. Amma wallahi kana da siffar da kowace mace za ta so ka." Shi dai Khalifa bai ce komai ba yi ya yi kamar bai ji ta ba. Tunanin Ma'eesha yake yi, ga wata da ba ƴar kowa ba ƴar talakawa tana cewa tana son sa amma ba za ta iya auren makaho ba. Ta ɗauki makantarsa a matsayin kasawarsa. Amma Ma'eesha gata can ƴar masu kuɗi wacce ta taso cikin kudi da gata da kayan more rayuwa kamar ta amma ba ta ɗauki makantarsa a matsayin kasawarsa ba a haka take son da take faranta ma sa rai ba ta damu da makantarsa ba tana rayuwa cikin farin ciki da walwala. Bai san lokacin da ya yi wani sanyayyen murmushi ba tare da sanya ma ta albarka a zuciyarsa. Wani matashin saurayi ya zo wajen sakamakon hangen kayan gyaran takalmin da ya yi ne ya zo. "Ina mai gyaran takalmin?" Khalifa ya ce ma sa baki nan." Ya kalle shi ya mika ma sa takalmin daga ɗan nesa da shi. Sai ya ga yana lalube yana cewa. "Ina takalmin yake bawan Allah ka matso kusa mana." Ganin yana lalube ya saka shi cewa. "Ban gane ba wai makaho ne yake lalube ko me? Bai ma ganni ba ko?" ",Eh makaho ne amma ya iya aiki sosai zai yi ma ka yanzu." Cewar Ilu mai yalo yana kokarin karbar takalmin don ya mikawa Khalifa. "Dalla Mallam bar ni, hauka nake yi ne, ko na yi ma ka kama da mahaulaci ne da zan ɗauki takalmi na ba wa makaho salon ya mayar ma ni da takalmin nakasashshe kamarsa ko? Wannan nakasashshen sai dai ya nakasa tsakalmi ba dai ya gyara ba." Yana fadar haka ya figi takalmimsa yana barin wajen. Cike da tausayinsa Ilu mai yalo ya dafa kadarsa ya ce. "Kar ka damu abokina Allah ya sa ba rabonka ba ne, Allah zai kawo ma ka rabonka ka ji." Murmushi ya masa tare da cewa. "Ba komai." _Nadra_ Tana nan zaune saman gadon sakamakon zufa da ta ji ya karyo ma ta bayan maganin zazzaɓi da Fahad ya ba ta. Ta ji ba wani ciwo garau take ji. Hakan ya saka ta cire hijabinta ta ajiye a gefe. Ta ji kewar gida tana son ta yi magana da Umma da Abba amma ga Fahad ya karɓe ma ta waya Tana nan zaune ta yi jigum sai ta ga an turo kofar dakin, ta daga kai ta kalle shi ta ga yana shigowa kai tsaye. Da sauri ta janyo hijabinta ta na sakawa tare da ƙudundune jikinta waje ɗaya. Mamaki ya cika shi ganin yadda duk ta taburce wurin saka hijabinta bayan tana da riga a cikinta ba wai tsirara take ba, kuma bayan haka nan ai shi mijinta ne halak ɗin sa ne ko da ya ganta tsirara ba ai ta halatta a gare shi amma sai wani noƙe wa take yi cikin hijabi. Zuba ma ta idanun ya yana tsaye hannayensa suka biyu cikin aljihun jeans ɗin dake jikinsa. Jin ba ta sake jin takusana ba kuma bai yi magana ba sai ta ɗaga kai ta kalli in da yake. Idanunta ne suka sarƙe cikin nasa. Ya zuba wa kyakkyawar fuskarta idanu, sam ba ta kama da masoyiyarsa Sidra. Don ita Sidra fara ce sol kuka fuskarta doguwa ce idsnunta madaidaita hancinta dogo ne sai bakinta wanda shi ma madaidaici ne ba za ka kira ta mai ƙaramin baki ba kuma ba za ka kira ta mai babban baki ba. Ita kuma wannan Nadra baƙa ce amma baƙinta mai kyau ne irin mai sheƙin nan fatarta tana glowing ne, round face ne da ita, don fuskarta a zagaye yake, idanunta dara-dara ne hancinta dogo ne haka bakinta ma ƙarami ne laɓɓanta pink ne don a zahirin gaskiya ta fi Sidra kyawun fuska, sai dai kasancewar ta baƙa ba kowa ke ganin kyawunta kamar yadda ake ganin kyawun nata ba Ita kuma Sidra hasken fatarta yake kara haska ta don ita Sidra doguwa ce ba ta da cikar halitta sosai saɓanin Nadra dake da hips da kuma manyan nono. Amma kasancewar kullun tana cikin hijabi ya sa ba'a ganin dirin jikinta, ita kuma Sidra ba ta saka hijabi mayafin ma sai ta ga dama take saka shi. Tura baki ta yi ganin yadda yake kallonta kuma kamar tunani yake yi. Kara ƙanƙame jiki ta yi cikin Hijabin tana tura baki. "Ya jikin na naki?" "Da sauƙi." Ta fada tana sunkuyar da kai ƙasa." "Me ke ma ki ciwo yanzu?" "Ba komai." Jinjina kai ta yi kafin ya ce. "Akwai abun da kike buƙata ne?" "Ba komai." Daga haka ya nufi hanyar fita, sai ya juyo ya ce. "San fita na san Mama za ta aiko ma ki da abinci." Daga haka ya nufi hanyar fita ya fice daga ɗakin. Daga haka ya nufi kofar fita in da ya nufi parking space, motorsa ya nufa ya shiga. Tun kafin ya danna horn maigadi ya wangala ma sa gate ɗin gidan. Yana fita ta mike ta fara ƙokarin gyara ɗakin. Toilet ta wanke sannan ta zo ta gyara ɗakin tas. Falo ta nufa kai tsaye duk da ba wani gyara amma haka ta gyara shi, sannan ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke ta gyara shi ta goge wajen da ya dace. Ɗakinta ta koma ta yi wanka ta fito mayyukan shafawar da ta gani an jera ma ta ma su tsada ta shafa, sannan ta saka underwears don singileti ta saka da wando ta duba kayan ta rasa wanda za ta saka. Domin ita tana son saka rigar Abaya ce ko kayan da ya ke rufe jiki kuma ta sake a ciki ba tare da ta takura ba. To nan kayan kuka duk kaya ne da Fahad ya siya da sunan Sidra don irin kayan da take son sakawa kenan ma su kama jiki, sai kuma na gida wanda iyayen su suka siya ma ta ta kai wa tela duk irin kayan da take so ta saka aka yi ma ta. Rasa kayan da za ta saka ta jan tsuki cike da takaici. Wani riga da siket ta saka duk da ya kama ta amma sai ta bar shi kasancewar ta san za ta saka hijabi. Hijabi ta dauka ta saka sannan ta fita zuwa falon. Ba ta wuce mintuna biyar ba ta sauka downstairs. Kallon gidan take yi wanda ya haɗu iya haɗuwa. Komai na gidan na musamman ne, gini ne mai kyau da tsari na zamani. Tuna Sidra ta yi kawai sai ta goge ƙwallar da ta ji ya cika ma ta idanun. "Ƴar uwa ina kika shiga ne, me ya sa kika gudu kika bar takarda meye dalilin hakan. Ga ni a gidan da ya dace a ce kece kike ciki tare da masoyinki Yaya Fahad. Don Allah ki dawo akan lokaci Abba da Umma suna fushi da ke." Ta yi maganar tana goge hawayenta. Ƙarar ƙararrawar ƙofa ta ji ya saka ta gyara zaman Hijabin jikinta ta nufi ƙofar ta buɗe. Cike da murna ta ce. "Gwaggo Laraba." Ta rungume ta tana dariya. Sannan ta kalli saura mutanen duk danginsu ne da suka zo daga ƙauye bikin auren. Cike da murna ta tarbe su ta yi ma su iso zuwa ciki. _Ya Sayyadi_ Tun da Fahad Majidaɗi ya yi masa gargaɗi akan Nadra ya kasa ƙwaƙwaran motsi. Shin me ye zai saka Fahad da da yake auren Sidra ya ma sa haka, yana da wannan ikon da zai ma sa barazana. Me ya taka ne ko iyayen Nadra sun san da zaman sa amma ba su ma sa shamaki da ita ba sai shi bare a wajenta, kawai don yana auren Yayarta. Har yana cewa zai saka a Kamo shi duk in da ya shiga a faɗin ƙasar nan. Jiki ba ƙwari ya shirya cikin jallabiya da ɗagaggen wando ƙwaurin ƙafarsa a waje. Babur ɗinsa ya ɗauka ya tayar ya nufi gidan su Nadra. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣3️⃣ Babur ɗin sa ya ɗauka ya tayar ya nufi gidan su Nadra. A ƙofar gidan ya tsayar da babur ɗinsa sannan ya tsaya yana danna horn. Maigadin na jinsa ya share shi har sai da Direban ya yi magana . "Ba ka ji ana horn ba ne?" "Rabu da ɗan wahala." "Waye wai?" Direban ya sake tambayar maigadi. "Oh kai ba ka gane ko waye ba, ai ni tun da na ji wannan ƙarar babur ɗin kamar an tayar da injin ɗin markaɗe na san wannan Ustaz ɗin ne dake son Nadra. Ni idan ba shi da tsarin idanun ba ina shi ina neman aure a wannan katafaren gidan. Ai ruwa ba sa'an Kwando ba ne, yana talaka da shi ko sutura arziki bai da ita kayansa fa kala uku ne jallabiya uku yake da su daga wata fara sai baƙa da wata Blue su kenan kayan nasa sai hular taɓa ni ka ji hadisi da wani takalmin robarsa da ta so ta yi ma sa yawa." Dariya direban ya saka yana cewa. "Kai Mallam Musa ba ka da dama, haka ka sa wa Ya Sayyadi idanu?" "Ba dole ba, saboda ina jin takaici a ce wai kamar ƴa a gidan nan ba ƴar aiki ba ƴar ma su gida a ce ita yake so. Ita kuma Nadra da yake ba ta damu da rayuwar duniya ba kuma ba ta duba girma da ta fito ba amma ta yarda ta karbi soyayyarsa haka zai zo ta fito har ta kawo ma sa ruwa da Abinci. Idan da Sidra ce ya isa ya ce yana son ta ai wargi ma wuri yake samu." Dariya direba ya yi ya ce. "Har ka tuna ma ni ranar da Sidra ta mare shi saboda ya bugar ma ta mota ." Maigadin ya saka dariya ya ce. "Dama ita Sidra ai ba ta da hakuri ban san yadda aka ji aka fasa auren Sidra ba aka ɗaura da Nadra." Kafin ya yi wata magana suka ji ana buga gate ɗin gidan da ɗan ƙarfi, hakan ya saka maigadi ya tashi da sauri yana cewa. "Waye ke damun mutane a wajen?" Ya faɗa yana buɗe karamar ƙofar. "Assalamu alaikum warahmatullah." Ya faɗa yana miƙa wa Maigadi hannu don su yi masabaha. Maigadin ya mika ma sa hannu tare da cewa "Wa'alaika Salam." "Ma sha Allah, ya lokaci ya kuma aiki?" "Ga shi Muna ta yi." "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora." "Bai amsa ma sa ya ce. "Ustaz ka shigo." Ya fada yana ba shi hanya, ya shigo da babur ɗin nasa ciki ya ajiye a harabar gidan daga gefe. Sannan ya ƙarasa wajen da Direban yake suka gaisa. Maigadin ya ce . "Ka zo ka yi bankwana da mu ne?" Cikin rashin fahimta Ya Sayyadi ya ce . "Bankwana aka me fa?" "To dama me za ka sake zuwa yi a nan, tunda wacce kake zuwa dominta ta yi aure." Wani kallo ya yi wa Maigadi kafin ya ce. "Amma ba ka cikin hayyacinka ko? Yarinyar da babu wanda take so sai ni ne ta yi aure? Wannan da'ifin labari ne bari na je na ji sahihin labari daga bakin da baya ƙarya. Ya tafi zuwa cikin gidan yana tafiya kamar zai kife a ƙasa. "Assalamu alaikum." Daidai lokacin da LUBE mai aiki ta buɗe kofar, ganinsa ya sa ta gaida shi, bai amsa ba ya ce ta sanar da Abba ya zo yana son magana da shi. Ta nufi part Abba ta same shi shi da Gwaggo Maimuna da Ammi. Ta gaishe su sannan ta sanar da su saƙon ya Sayyadi. Sai da suka kalli juna Abba da Gwaggo Maimuna sannan Abbabyq ce a sanar shi ya shigo. Bayan ya shigo ya gaida su suka suka amsa cike da kulawa. Nam yake sanar da Abba Fahad Majidaɗi ya yi masa rashin mutunci har da ka sa barazanar idan ya sake kiran wayar Nadra sai ya sa a ɗauko ma sa shi a fadin ƙasar nan, wai idan bai daina ba ba shi ne kuskure mafi muni da zai tafka a rayuwarsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Abba ya sauke sannan ya ya yi wa Ustaz ɗin takaitaccen bayanin abin da ya faru, sannan ya bashi haƙuri akan cewa ba su da wani zaɓi ne da ya wuce su aura ma sa Nadra a madadin Sidra. Ba za su bari alsu kunyata ba a idanun duniya mutuncinsu ya zube taron da jama'a suka zo wasu daga wasu garuruwa a ce sun watse haka nan ba tare da an yi ɗaurin auren da suka taro domin sa ba. Kuka wiwi Ustaz ke yi na rashin Nadra da ya yi a rayuwarsa, yarinya mai hankali da tarbiyya, wacce ta so shi duk da tana gidan ma su rufin asiri shi kuma gidan talakawa ba ta ƙi shi ba, ya san ba zai samu mace kamar Nadra a rayuwarsa ba. Ba tare da ya cewa kowa komai ba ya nufi kofar fita yana kuka har da majina. Ammi ta raka shi da harara don dama ba ƙaunarsa take yi ba. Kullum sai ta zuga Nadra akan ta Kore shi amma ba za ta yi ba sai dai kasa ta yi ma sa murmushi. Dama daga Ammi sai Gwaggo Maimuna suka rage a gidan, don su Gwaggo Laraba da sauran dangi sun tafi gidan Nadra su ga gida kuma su yi ma ta sallama don gobe za su watse zuwa garuruwansu. _Sidra_ Ta gama haɗa kayanta a cikin akwatin kayanta tana jiran Direban da zai kai su Sady baby ya zo ya ɗauke ta su kama hanyar Kano. Amma sai ta ji shiru tun da suka fita da sunan zai kai su Sady Unguwa ya dawo shiru. Ta kira wayar Sady baby bai shiga ba. Don ba ta son shiga motar haya, don haka ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta ta jira su. Ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta jira su har sai sun dawo. _Fahad_ A kofar gidan Mahaifinsa ya tsaya yana yin horn ɗin motarsa, yanayin sannan horn din da Maigadin ya yi ne ya gane cewa Fahad ne ya iso. Da gudu-gudu ya nufi gate ɗin gidan ya wangale ma sa. Parking lot ya nufa ya yi parking motarsa. Gidan har yanzu akwai baƙin da suka zo bikin don ga motocinsu nan a jere. Fitowa ya yi daga cikin motar yayin da ma'aikatan gidan ke gaishe shi. Ya amsa ma su ba yabo ba fallasa. Tun daga ƙofar da zai sada ka da falo yake ji yo hayaniyar ƴan matan da ke cikin falon. Firarsu kawai suke yi suna dariya. Mirɗa handle ɗin kofar ya yi ya shiga wanda ƙamshinsa kaɗai ya isar da saƙon zuwansa. Kowace ta nutsu suka fara gaishe shi, ya amsa ma su ba yabo ba fallasa. Ya kalli Rumaisa ƙanwarsa da Rahina da Sahiba da suka je gidansa suka dawo suka ce wai Nadrah ba ta iya tafiya ya kasance ta. Ganin kallon da ya yi masu ne suka sha jinin jikinsu. Daidai lokacin wayarsa ta yi ringing. Ya duba ganin abokinsa Sadik ne ya saka ya yana cewa. "Ya aka yi ne?" Maganar mintuna biyar suka yi sannan ya katse kiran wayar . Ko da ya duba bai ga su Rumaisa da Sahiba da Rahina ba sun sulale sakamakon ganin kallon da ya jefa ma su. Sauran ƴan matan duk ba garin suke ba zuwa bikin suka yi. Amma duk ƙannensa ne. Part ɗin Babansa ya nufa in da ya same shi tare da kawunsa. Gaishe su ya yi sukaasa sannan suka ɗora da yi ma sa nasiha akan zaman aure da hakuri. Bayan ya bar part ɗin ya nufi part ɗin ya nufi part ɗin Mama. Farida ce kawai a falon daga ganin idanunta ta sha kuka sosai. Idanu suka haɗa da sauri ta ɗauke kai tana juya ma sa baya. Shi ma kansa ya sani Farida na tsananin son sa da ƙaunarsa amma shi baya son ta, bayan so na ƴan uwantaka da yake yi ma ta ba wani abu a ransa. Da a ce bayan guduwan Sidra iyayen ta ba su bashi Nadra ba to da zai iya auren Farida. Amma a yanzu kam baya jin zai iya aurenta kuma. Ƙarasa wa ya yi ya zauna kusa da ita. Ta zuba ma sa idanunta tana kallonsa kamar za ta cinye shi. Kafin kuka hawaye ya fara zuba a idanunta sharr kamar an bude famfo. "Ki yi haƙuri kin ji." Tashi ta yi a guje ta bar falon ta nufi ɗakin dake kusa da na Mama. Daidai lokacin Mama ta fito ita da Aunty Rahama. Bayan sun gaisa ne Mama ta ce. "Ya za ka fito ka bar ƴar mutane ita kaɗai bayan ka san condition ɗin da take ciki?" Ka tashi ka koma zuwa gobe iyauenka za su zo ganin gida don jibi suka ce za su tafi, don yau suka ji niyyar zuwa amma na ce su bari sai gobe." Ya dai yi shiru ba tare da ya sake yin magana ba. Kallon Baby Zahrah ya yi wacce take ma sa dariya tana kiran uncle. Alama ya ma ta da ta zo ya zaunar da ita kusa da shi wanda ganin haka ya saka Mama cewa. "Fahad ba ka da niyyar tafiya ko? Ai bai kamata ma ka bar gidan ba, ka je ka haɗa ni da ita a waya ko ka bani lambar wayar ta. Sanin cewa ya karɓe wayarta ya saka ya ce . "Ba ta da waya." "Kamar ya ba ta da waya?" "Eh wayar ta ɓace ne." "To ka siya ma ta wata wayar yau ɗin nan ka tafi ma ta da shi, na san dole za ta so yin magana da iyayenta." "To Mama." Aunty Rahama ta ce . Da take ganin kamar rashin fahimta ce don ita ba ta yi tunanin cewa ƙanin nata zai kusanci Nadra ba wanda daren juya daƙyar ya tafi yana fushi. Ganin shi ma bai ce komai ba ita ma ta yi shiru amma tabbas tana da shakka akan hakan don ta fi kowa fahimtar ƙanin nata. Sallama ya masu sannan ya nufi part ɗin baƙi ya gaishe da kowa. Sai dai ƙanwar mahaifiyarsa Hajiya Jummai mahaifiyar Farida ce ta share shi ba ta amsa ba, shi ma bai damu ba ya yi ficewarsa _Ma'eesha_ Tana ɗora girki ta ji sallama daga kofar waje, ta amsa yayin da da take kwarara amai ta taimaka ma ta da ruwa kuma ta gyara wajan a gidan Mallam Liman da aka ba Makaho ɗaki. Da fara'a ta tarbe su suka shiga cikin ɗaki ta shimfida ma su tabarma. Bayan sun gaisa ne ta kawo masu ruwan pure water guda biyu. Nan Dattijuwar take gabatar ma ta da kanta ashe ita ce matar da ta ga za su bar gidan lokacin da Ma'eesha ta fice Makaho na bin bayanta take tambayar makaho ina za su je ya ce suna zuwa. Yana girki suna taɓa fira don ganin su ne ya saka ta canza tukunyar ta saka babba. Kafin ta gama Dattijuwar da jikarta mai suna A'isha suka yi ma ta sallama za su tafi. Ta yi daga da su akan su tsaya ta gama girki su tafi da shi amma ba su zauna ba. Da ta kammala ta zuba a food flask sauran da ya rage ta zuba a wani food flask shinkafa da wake ne jallop wanda ya ji bisashen kifi. Tun karfe biyu take jiran Khalifa ya dawo ya ci abinci shiru. Har karfe huɗu sannan ya dawo. Ta yi ma sa ƙorafin rashin dawowa ya ci abinci akan lokaci. Ƙarshe ma ta ce ya gama su tashi su ke ta siya masa karamar waya. Ta sanar da shi zuwan Baba mayar Liman da jikarta da suka yi. Bai so ba haka ta matsa ma sa dole ya yarda suka shirya za su fita don ta siya ma sa karamar waya. Da zai ɗauki sanadar jagoransa hanawa ta yi ta ce sai dai su tafi haka nan ita ce ƴar jagora. Duk da bai so ba amma baya son yi ma ta gardama don tana da ƙima sosai a idanunsa. Hakan ko aka yi bai rike sanda ba ita ce ta rike ma sa hannu suka fita. Tana sanye da doguwar rigar Abaya blue ta yi rolling kanta da mayafin abyarta sannan ta saka facemask da farin glass a idanunta. Hannunsu na sarƙe cikin na juna suke tafiya duk wanda ya san Khalifa a unguwar sai dai ya saki baki yana kallon su da mamaki. Ganinsa tare da wannan zugegiyar budurwa tana rike da hannunsa suke tafiya. Sai dai idan har ba idanunta karya suka yi ba ta hangi wata motar a gabansu wani na zaune gefen me zaman banza yana ɗaukarsu hoto. Cike da mamaki ta yi niyyar nufar motar sai ta ga an figi motar a guje an bar wajen. "Ka ga wanda ya ɗauke mu photo?" Ta yi tambayar tana kallon Khalifa. "Ni da ba idanu gare ni ba da wani idanun zan kalle su?" Har suka je wani shagon siyar da waya ta siya masa wata karamar waya keypad, duk da ba ta da isasshen kuɗi amma dole ta cire dubu goma ta siya ma sa karamar waya, da sim card mai register Ka san me ya sa na siya ma ka waya?" "Ban sani ba don da wani idon zan yi amfani da shi?" "Ai bai da wahalar koya, ni zan dinga kiran ka idan ba ka gida lokacin cin abinci idan ya yi ba ka dawowa Sai ka zauna da yinwa shi ya sa na siya ma ka da zaran na gama garki zan Kira ka sai ka zo ka ci abinci. Zan nuna ma ka wajen da za ka danna da zaran ka ji ƙara sai ka laluba ka danna wajen ka kara a kunne daga nan za ka ki murya ta." Bayan sun tsallaka titi kasancewar ba wani nisa da unguwar su. Suka kama hanyar dawowa gidan wayar da ta siya masa na cikin jakarta, tana tuna mutumin da ta ga suna daukar su photo a waya ɗazu su waye su me ya sa suke bibiyar su? Daidai lokacin wayar ta ya soma ringing ta duba ta gani ƙawarta Nasreen ce. Ta ɗaga tare da sallama. Daga can bangaren ta ji Nasreen na cewa. "Abdul ne zai yi magana da ke ta wayata tun da kin yi blocking ɗin sa." "A kan me zai yi magana da ni?" "Akan yana son ki cika masa alkawarin auren da kika yi ma sa, kuma dama shi ne ya dace da ke ba wannan musakin ba." A fusace ta ce . "Nasreen za mu samu matsala da ke wanda ba za mu taba komawa kamar da can baya ba. Kuka ki ja wa shi wanda ya aiki ki kunne ya fita a sabga ta. Wani irin jahilci ne zai saka ya fara neman matar aure, ko mace na auren maza biyu..." Maganar nata maƙalewa ya yi sakamakon ganin wato motar ta tsaya gabansu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣4️⃣ Maganar nata maƙalewa ya yi sakamakon ya yi sakamakon ganin wato motar ta tsaya gabansu. A hankali ya sauke glass ɗin motar yana sakar ma ta murmushi. "? Yaya Jamil." Ta furta cike da mamakin ganinsa a unguwar su, shi kuma tun ranar da Nasreen ta kira ta a waya bayan ta je gidansu ya so ya zo tare da Nasreen sai dai ba ta bashi damar hakan ba. Don haka ya matsala wa Nasreen akan ta kawo shi gidan amma ta ƙi sai dai ta yi ma sa kwatance. "Ma'eesaha wancan ranar kin bar gida a cikin fushi kina kuka, na so ki tsaya ki saurare ni amma ba ki tsaya ba. Yanzu ina neman arzikin don Allah ki taimaka ku shigo na ajiye ki a gidanku idan ya so sai mu yi magana." "Yaya Jamil ina ganin mutuncinka don haka ka bar nan unguwar kafin na saka yara su yi ta jifar motar nan sai sun farfasa ma ka gilashin motar." Murmushi ya yi tare da da fitowa daga cikin motar ya kalle ta yadda ranta yake ɓace ya ce. "Idan kin saka an fasa kanki kika yi wa Asara. Domin ɗaya daga cikin motocin da mahaifinki ya mallaka ne na ke amfani da ɗaya. Kuma sakin kanki ne cewa ke kaɗai ya mallaka a duniya. Yau idan ƙasa ta rufe idanunsa ya zama babu shi ke ce mamallakiyar dukiyar da ya mallaka babu wanda ya isa ya canza hakan. Ko Mamy mahaifiyata tuminin takaba akwai za ta samu, ni da Laila da muke Agola ba'a maganar mu. Don haka ki yi hakuri ki zo mu tafi gida na zo ne na ba ki haƙuri a madadin mahaifinki da mahaifiyata." "Yaya Jamil na daɗe da rasa mahaifina yanzu ba na da kowa a wanann duniyar sai mijina shine fitila ta, domin la kira kowa kansa ya sani da rayuwarsa. " Ta ji maganar tana damƙar hannun makaho za su fara tafiya ya sha gabanta da sauri ya ce. "Ki tsaya ki saurare ni Ma'eesaha, kin ga ni ba ni na yi ma ki laifi ba mahaifiyata ce ta yi ma ki laifi kada laifinta ya shafe ni, laifin wani baya shafar wani Ma'eesha. Sai a lokacin makaho ne ya yi magana ya ce. "Ki bar shi ki ji da me ya zo?" "Babu wani abun alkhairi da zai zo da shi, domin kuwa babu alkhairi a tattare da su. Daga ranar da mahaifiyata ta taimake su daga rana ta janyo su inuwa me suka aikata ma ta jefa ta a ranar suka..." "Ya Isa haka nan Ma'eesha ki wuce mu tafi." Kamar jira yake dama hannunsa na rike da nata ne. Take suka fara tafiya yayin da mamaki ya cika zuciyar Jamil, wato duk tana daraja mijinta tun da har ya ba ta umarnin ta wuce su tafi lima take ta wuce ba musu ko gardama. Kenan hakan na nufin ta karɓe shi a matsayin mijin aurenta ne. Jinjina kai ya yi tare da cewa. "Ni ina can ina faɗi tashi wajan Daddy da Mamy don su raba auren ma don na yi zaton ba za ta taba yarda da auren ba, nayi zaton za ta saka ya sake ta don ta fi ƙarfinsa, amma sai na gansu tare da alama wani wajen suka Fito." Shiga motarsa ya yi ya fara bin bayansu ta juyo ta kalli motar amma ba ta damu ba sai ta ci gaba da tafiyar da take yi. Har suka isa ƙofar gidan ta ciro ɗan makulli daga cikin handbag ɗin ta ta buɗe. Bayan ta buɗe ne ta ja hannunsa suka shiga bakinsu ɗauke da sallama. Suna shiga daidai lokacin motarsa ta karaso . Fitowa ya yi daga cikin motar yana ƙarewa gidan kallo yana jinjina wanan al'amari. Wai kamar Ma'eesha Ibrahim Khalil ce take rayuwa a cikin wanan akulikin gidan. Yarinyar da mahaifinta ke da manyan gidaje na alfarma a garin nan, mutumin da yake kyauta da gidaje da motoci wanda ko gidajen da ya raba wa masu ma sa aiki kamar direba maigadi da sauransu to mahaifin Ma'eesha ya siya ma su lafiyyun gidaje amma a ce ƴarsa ɗaya tilo a duniya tana rayuwa a cikin wannan gidan da bai wuce a ce tana kiwon karnuka ba. Amma ita ke rayuwa a nan lallai ma'eesha Allah ya ba ta karfin zuciya. Yana tsaye yana kallon ƙofar fale-falen da suka bude suka shiga. Ya ƙsrasa bakin kofar gidan yana sallama. "Assalamu alaikum." Daidai lokacin da ma'eesha ke fitowa da tabarma daga cikin dakin ta ji sallamar sa a kofar gidan. Makaho ne ya amsa ma sa sallamar yana kokarin mikewa "Please kar ka fita ka rabu da shi idan ya gani da tafi." Ta fada tana rike hannunsa. "A'a Ma'eesha ki yi hakuri wannan bawan Allah ba shi ya yi ma ki laifi ba, ki sauraren shi laifin wani baya shafar wani, don haka ki daina hukunta shi da laifin da mahaifiyarsa ta aikata." Ya fadi haka yana zame hannunsa daga rikon da ta yi masa ya ɗaiki Sandarsa ya nufa hanyar fita. Yana fita ya ce. "Waye ke sallama?" Jamil ya ce . "Ni ne wanta Jamil." "Bismillah ka shigo ciki." Ya yi maganar yana yin gaba yayin da Jamil ya take ma sa baya. _Nadra_ Farin ciki duk ya lulluɓe ta sakamakon ganin ƴan uwanta sun zo. A nan falon dake downstairs suka zauna. Durƙusawa ta yi ta gaida dangin nata cikin farin ciki.sannannta mike suka gaisa da ƴan matan dangin nasu. Sai tsokanar ta suke wai ta canza a cikin kwana ɗaya ne me Fahad ɗin ya ba ta ne, ita dai ba ta tanka ma su ba. Ruwa da lemu ta kawo ma su ta na shirin zuwa kawo ma su cincin sai Gwaggo Laraba ta ce. "Me kuma za ki kawo ma na?" "Cincin ne zan kawo ma ku." "A'a cincin da muka baro shi a gida." "To bari na je na ɗoraa ku girki don na ga Akwai komai na bukatar." Daidai lokacin aka danna ƙararrawar ƙofa. Dama tana sanye da dogon Hijabi kamar yadda ya zamar ma ta al'ada. Tana buɗe wa ta ga Rumaisa ƙanwar Fahad ce sai dai wannan karon iya kaɗai ce. Murmushi ta sakarwa Nadra tana cewa. "Antynmu ya kike ?" Ta faɗa tana Murmushi. Duk da kasancewar ta girmi Nadra sosai amma ba ta da girman kai. Nadra ma murmushi ta sakar ma ta tana yi ma ta sannu da zuwa . Rumaisa ta amsa tana shigewa cikin falon ɗin ta hangi baƙi. Ta shiga da fara'a tana gaida jama'ar da ta gani a falon fuskarta ɗauke da murmushi. Suka amsa ma ta cikin sakin fuska da walwala. Kallon Nadra ta yi ta ce. "Ga abinci Mama ta ce a kawo ma ki ." "Okay to na gode a gaishe ta." "Za ta ji." Ta faɗa nufar hanyar waje bayan ta yia su sallama. "Am ba ki ji ba." Nadra ta faɗa tana kallon Rumaisa kasancewar ba ta san sunan Rumaisa ba ta dai san sunanta ba. Rumaisa ta juyo tana kallon Nadra ta ce "Da ni kike yi?" "Eh, dama basket ɗin da kika kawo da safe ne nake so ki tafi da su." "Okay." Nadra ta haura upstairs ta nufi kitchen don ɗauko basket da food flask ɗin da aka kawo da safe. Dama kafin ta wanke su sai da ta fita ta kai wa masu gadi da sauran ma'aikatan gidan. Bayan ta kawo ne ta ce. "Ga shi ." "Sunana Rumaisa." Jinjina kai Nadra ta yi tana Murmushi. Daga nan ta yi ma ta sallama ta tafi. Dama ta bar direba a mota yana jiran fitowar ta. Tana fitowa suka bar gidan. Bayan tafiyar ta ne Nadra ta ce . "Ga abinci nan an kawo, na san zai ma isa don na ga da yawa kamar ta san za ku zo." "Dama ta samu ma na, dole wasu za su zo yau su ganki musamman danginki." Gwaggo Laraba ta faɗa tana karantar yanayin Nadra. Don ta lura jikina a sanyaye yake. Kallon ƴarta ta yi mai suna Amal ta ce ta zuzuzba abincin ta ba wadanda za su ji. Ita kuma sai ta ja hannun Nadra tana cewa. "Muje na ba ki sako ko?" Nadra ta miƙe suka nufi upstairs. Har cikin bedroom ɗin Nadra suka shiga ta zaunan a saman gadon sannan ta nuna wa Nadra gefenta ta ce ta zauna kusa da ita. Ba musu ta zauna Kamar yadda ta umarce ta. Sai ta riko hannun Nadra ta ce . "Daughter akwai matsala ne?" Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle. "Idan akwai matsala ko sanar da ni, sai na san ta ina da za'a ɓullowa lamarin." Ƙwalla ne ya cika idanunta a hankali ta ce . "Ummata." "Ummar ki kuma?" Jinjina kai ta yi ta ce. "Ya jikinta." Ta ji sauƙi ta warware, yanzu haka ma ta yi ta kiran wayarki ba ta shiga ." "Eh ya amshe ma ni waya." "Ya amshi wayarki saboda me?" Nan ta ba ta labarin duk abinda ya faru. Shiru ta yi tana nazari kafin ta yi ajiyar zuciya ta ce. Eh mu ne muka mance ba mu sanar da shi Sayyadi zancen auren naki ba. Amma yanzu na san dole ya sani. Sannan zan ya ma ki wata magana ɗaya. Kada ki sake yi wa Fahad zancen Sidra." Da sauri ta kalli Gwaggo Laraba ta ce . "Idan ta dawo ai sai a daura ma su aure ta zo ta zauna ni kuma na je na auri ya Sayy..." Mugun kallon da Gwaggo Laraba ta yi ma ta ne ya saka ta yi shiru. "Ke dakata! Ba na son shashancin banza, ko da Sidra ta dawo to sai dai ta auri wani namijin ba Fahad ba, domin dama wani baya auren matar wani haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka ki sa wa rabi cewa zaman aure kika zo ba wai kin zo da niyyar wata rana ki fita ki ba wa wata mijin ki da gidanki ba ne, don ba za mu taba aurawa Fahad Majidaɗi Sidra ba, bayan ya aure ki, don haka ki kama mijinli ki yi ma sa biyayya sau da ƙafa. Ba mu kawo ki nan dan ki fita wata rana ba. Sannan kada na sake jin sunan Sayyadi a bakinki ko tunaninsa. Ki cire shi a ranki dama can ba mijinki ba ne." Jinjina kai ta yi hawaye na bin fuskarsta. Dosa Gwaggo Laraba ta yi ma ya nasiha mai ratsa zuviya da wasu shawarwari kan dabarun zama da miji. Wasu magungunan mata da na gyaran jiki Gwaggo Laraba ta fito da su daga cikin jakarta sannan ta yi na ta bayanin yadda za ta sha kowane. Karɓa ta yi ta ajiye su. Sai ta ga Gwaggo Laraba ta fito da wani kula a cikin leda ta buɗe kazar amarya ce guda aka dafa ma ta da romonta, daga gani ta ji sassaken magani . Sai da Gwaggo Laraba ta saka ta gaba ta ci rabin kazar ta sha romon maganin sannan ta ajiye sauran da niyyar kafin su tafi sai ta saka ta ta cinye sauran. sannan suka koma downstairs, don har sun gama cin abinci. Daidai lokacin ne suka ji horn ɗin mota. Bayan kamar mintuna biyar aka turo ƙofar falon tare da sallama. Fahad ne ya shigo ya durƙusa cikin girmamawa ya gaida su Gwaggo Laraba. Upstairs ya haura zuwa part ɗin sa. A falo ya zauna kan kujera ya faɗa duniyar tunani. A can falo Gwaggo Laraba ta ce wa Nadra ta tashi ta je ta sami mijinta ta kai ma sa ruwan sha. Jin haka sai da gaban Nadra fadi, amma sai dake. Gwaggo Laraba ta tashi ta ce. "Mu je kitchen ɗin." Tashi ta yi ta bi bayansa kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki. Suna shiga ta fuskanci Nadra ta ce. "Wato ba ki ji huɗubar da na yi ma ki ba ne? Na ce da zaran ya dawo ki dinga tashi kina tarbarsa, sannan ki bashi ruwa ya sha idan yana da buƙata. Sannan idan wanka zai yi ki taimaka ma sa. Yanzu ɗauki ruwa da cup ki kai ma sa, sannan ku tambaye shi ko akwai abun da yake buƙata ki kai ma sa ko ki yi masa⁷." Sannan kuma ki daina daka wannan dogon hijab kamar mai takaba ya isa haka nan, daga ke sai mijinkine idan an yi baƙi maza ." Faranti ta ɗauka ta dauki ruwa roba guda da glass cup ta fito ta nufi upstairs. Knocking ta yi a kofar falon sai dai ji shiru. Sai da ta sake yi sannan ta ji ya ya ba ta izinin shiga sannan ta shiga. Yana zaune kan sofa a ƙasan ƙafarta ya fara dauke idanunsa, yatsunta da suka sha lalle ne kawai ake iya gani. Don dogon Hijabinta har ya rufe ƙafarta. Ɗauke idanunsa ya yi ya mayar kan wayarsa yana daddanna wa Har ƙasa ta durƙusa ta ce. "Sannu da dawowa." Share ta ya yi kamar bai ji ta ba ya ci gaba da danna wayarsa. Duk da haka dai ta sake cewa. "Ina wuni?" Nan ma shiru ya ma ta bai amsa ma ya ba. Glass cup ɗin da ta ajiye ne ta buɗe robar ruwa ta tsiyaya ma sa ta mika ma sa ta ce. "Yaya ga ruwa." Ta yi maganar tana mika masa cup ɗin. Sai a lokacin ya ɗago kansa ya sauke idanuntsa kan kamilalliyar fuskarta. Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, da sauri da janye idanunsa saboda kwarjininsa. Kamar ba zai karɓa ba sai kuma A hankali ya mika hannunsa ya karɓa tare da cewa. "Thank you." Ya faɗa yana kai ruwan bakinsa ya sha. "Mama ta aiko ma na da abinci na kawo ma ka ne?" Kai ya girgiza sannan ya ce. "Am okay, you can go." Tashi ta yi nufi ƙofar fita ta fice. *Maman Ihsan ce* 09065327995 https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣5️⃣ Tashi ta yi ta nufi ƙofar fita ta fice. Sai dai bayan ta fita kafin ta rufe ma sa ƙofar ya ce. "Come here." Dawowa ta yi ciki ta tsaya tana jiran me zai ce. Kallon Hijabin da ke jikinta ya yi ya tuna duk sanda zai ganta da hijabi ne ko da ya je zance ne a wajen Sidra. Sai ya ɗauka ko don saboda zai shigo ne duk da ita wance yake zuwa wajan nata ba ta saka wa. Har wata rana suna hira da da Sidra a falon saukar baƙi sai ga Nadra ta zo wuce wa ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan dage part da dogon Hijabinta idanunta ya sauka akan Fahad da Sidra da suke zaune a kujera mai zaman mutum biyu, hannunsa sarƙame cikin na juna ta kwantar da kanta a kafaɗarsa suna kallon wani abu a wayarsa. Girgiza kai kawai Nadra ta yi don ta sha ganinsu rike da juna kuma manne da jikin juna girgiza kai kawai ta yi tana taɓe baki ta zo za ta wuce bayan ta gaida Fahad sai Hijabin ya ja kofin ruwan da Sidra ta ajiye wa Fahad. Ruwa ya zube ran Sidra ya ɓaci har tashi za ta mari Nadra Fahad ya dakatar da ita ta hanyar cewa. "No." "Ka bar ni na koya ma ta hankali tun da ba ta da shi kullun tana cikin hijabi kamar mai fita takaba, wani namiji ne zai yi sha'awarki a haka? Yarinya kamar wata bagidajiya sai ƙauyanci, ban ga ranar da yarinyar nan za ta waye ba." Sai a lokacin da kalli Yayar tata ta ce. "Aunty Sidra Indai wayewa irin ta ku ne ba na buƙata wayewa ta addinin Muslunci nake buƙata bar ni a haka ban saɓa wa Allah ba." A fusace Sidra ta wanke wa Nadra fuska da mari wanda sai da ta durƙusa wajen tana kuka. "Ni za ki yi rashin kunya wani saɓon Allah na yi ko saka hijbi da suturta jiki ne tsoron Allah da ba na da shi? Sau nawa ma su daka hijabin suke aikata ɓarna wanda wacce ba ta saka wa ba za ta iya yi ba?" Tashi ta yi tana kuka ta bar part ɗin. "Wai me ya saka kin fiye zafin rai ne?" "Don Allah Mallam kar ka sake ɓata ma ni rai, ya za'ayi ta Mani rashin kunya na ƙyale ta?" Ta yi ma sa maganar cikin ɓacin ran da take ciki. "Ba'ayi ma ni tsawa ki iya bakinki ki san kalaman da za ki dinga faɗa mani, idan ba haka za mu samu matsala da ke." Jin haka ta sassauta murya tana bashi haƙuri. Tari da ta ɗan yi ne ya dawo da shi duniyar tunanin da ya lula. Ya kalle Nadra da kyau wacce ko a mafarki bai taba tunanin ita ce za ta zamo matarsa ba Sidra ba. Maida idanunsa ya yi kan wayarsa cikin muryarsa mai amo ya ce. Ba na buƙatar sake ganin ki da hijab matuƙar ba wai namiji ne ya shigo gidan nan ba ko kuma za ki fita zuwa wani waje. Okay?" Kai ta jinjina ma sa sannan ta fita daga ɗakin. Kitchen ɗin ta koma in da ta tarar da Gwaggo Laraba tana ƙara gyara wa wasu kayan wajen zamansu. Ganinta ya sa ta dakata ta ce. "Abinci za ki kai ma sa?" "A'a cewa ya yi ya ƙoshi na tafi." Shiru Gwaggo Laraba ta ce. "Dole fa sai kin yi hakuri, domin har yanzu akwai tabon da Sidra ta yi masa a cikin zuciyarsa. Domin ba daɗi a ce ranar aurenka matar da kake so ta gudu ta bar ka. Kin ga dole har yanzu ransa ya kasace a ɓace. Ke ce za ki yi ƙokarin dasa ma sa soyayyarki a zuciyarsa. Ta hanyar kyautata ma sa, dama ita zuciya an halicce ta ne bisa ga son wanda ya kyautata ma ta, da kuma ƙin wanda ya munana ma ta. Shin ya nuna ma ki tsana ne ko hantara ?" Kai ta girgiza alamar a'a kafin ta ce. "A rayuwar aure ko soyayya, akwai abu guda da ya kamata mace ta gane, Ko wani namiji yana da irin nasa hali.Kuma yadda yake sonki, haka yake nuna fushinsa idan wani abu ya bata masa rai, ba wai saboda baya sonki ba ne, a’a, saboda ya damu da ke sosai ne.Don haka ke dai ki fahimci irin namijin da kike tare da shi Idan mijin kirki ne, zai yi fushi saboda yana son ki gyaru, ba don ya cutar da ke ba Idan mai saurin ɓacin rai ne, ki gane cewa yana magana ne da zuciyarsa, ba wai yana ƙin ki bane.Idan mai shiru-shiru ne, fushinsa yakan zama nesa da magana, amma zuciyarsa tana cike da damuwa, Idan mai gaskiya da tsauri ne, yana fushi saboda ya san abin da ya dace da abin da bai ya dace ba. Idan mai tausayi ne, fushinsa zai zo da nutsuwa, amma zai so ki gane kuskurenki ba tare da ya takura miki ba, a kowane hali, rarrashi na mace shi ne sirrin da ake so mace ta sani.Ki saurari damuwarsa ba tare da tsawatarwa ba. Ki nuna masa kin gane abin da ya dame shi. Ki yi magana cikin ladabi da natsuwa.Ki yi masa nasiha cikin taushi, ba da jayayya ba, Ki nuna masa kulawa, ko da da kananan abubuwa ne.namiji baya buƙatar mace cikakkiya, yana buƙatar mace mai fahimta. Jinjina kai Nadra ta yi cikin gamsuwa ta ce . "Gwaggo Laraba baya sakar ma ni fuska fa." "Ya ma ki wani abu ne yanzu da kika kai ma sa ruwa?" "Cewa ya yi wai kada na sake saka hijabi in dai ba wani namiji zai shigo ba ko fita zan yi." Murmushi Gwaggo Laraba ta yi sannan ta nuna ma ta yadda za ta zuba da shi da kuma kiyaye abinda baya so. Sai yamma suka shirya za su bar gidan suna fita harabar gidan dama motoci biyu suka zo da su na Gwaggo Laraba da ta Abba daya wacce daya daga cikin ƴan matan ta yi driving. Daidai lokacin Fahad ya dawo daga sallar la'asar ya ga suna shirin tafiya. Sallama ya ma su sannan ya ce Nadra ta zo ta karɓar ma su saƙo. Ko da ta ke 200k dubu ɗari biyu ya ba ta ya ce ta ba su yana ma su Allah ya kiyaye hanya. Ta zo ta ba su suka yi ma ta godiya tare da cewa ta isar ma su da sakon godiya suka tafi. _Ma'eesha_ Sallamar Yaya Jamil da na mijinta ne ta san cewa ya shigo da shi ne. Don haka ya tsuke fuska ta tashi daga kan tabarma ta koma kan kujerar tsuguno yayin da Makaho ya zauna a gefen tabarma shi ma Jamil ya zauna. "Ki girma baƙonki hadisin Manzon Allah (s.a.w) ne." Cikin sanyin murya ta ce. "Yaya Jamil ina wuni?" Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya amsa mata cike da farin ciki ta sauko. Tashi ta yi ta je ta kawo ma sa ruwan pure water guda biyu ta ajiye ma sa. Wanda ya san cewa yanzu ne ta fara shan pure water. Don a gidan su ruwan roba ake sha. Shi kan shi tun ranar da suka zo gidan su Ma'eesha suka ji sallama da kowane ruwa sai na roba. Bayan ya sha ruwan pure water leda ɗaya ne ya kalli Ma'eesha ya ce. "Ina mai ba ki haƙuri a madadin mahaifiyata, na san ta cutar da rayuwar ki cutarwa mafi muni ..." Kasa karasa maganar ya yi ganin yadda ta mike zumbur. "Yaya Jamil na roƙe ka dan girman Allah ka tashi ka tafi ba sai ka sake dawowa ba, kuma ba na bukatar ka sake jin an tayar mani da wannan zancen ya riga da ya wuce cutarwa dai an ya mana sai dai sakayyar Allah." Tana faɗar haka ta shige daki tana fashewa da kuka. Tana shiga ɗakin Jamil ya cire kuɗi 100k ya ce wa makaho ga kudi nan ya ba wa Ma'eesha amma makaho ya ƙi karba saboda ya ji tsana da ɗaci da a cikin Muryar Ma'eesha ya san ba za ta so kudin ba don haka ya ki karba. Sai ya mayar da kudin cikin aljihunsa sannan ya cire 3k ya ce ka ba ta wannan kudin sadakinta ne da ta ki karba shi ne na karɓa a hannun Laila hakkinta ne ka ba ta." Wannan kam makaho ya amsa suka yi sallama ya fita. Ma'eesha na jin fitar Jamil ta fito daga cikin ɗakin ta zauna waje. Wayar da ta siyo wa Makaho ne ta ciro ta buge wayar don battery akwai caji. Ta saka sim card ɗin da ta siya ma sa ta mika ma sa, nan ta dinga nuna ma sa yadda zai danna idan an kira shi waya. Ta gwada kiran wayarsa sai ta ga ya iya ɗaga kiran kamar yadda ta koya masa kiran na shigowa sai ya ɗaga ta ji muryarsa shi ma ya ji tata muryar. Sai da aka kira sallar magrib sannan ya tashi ya tafi masallaci. Ita kuma ta kunna gas kasancewar spaghetti sauce za ta yi ma su. Da misalin karfe takwas da kwata na dare suna zaune a waje ta shimfida ma su tabarma, kasancewar ta fesa maganin sauro sai suka janyo ƙofar ɗakin ta rufe. Spaghetti sauce din suke ci suna Shan zobo da ta haɗa ma su ta siyo ƙanƙara. Kasancewar akwai wutar nepa ya saka ta ƙirƙiri wanke-wanke shi kuma yana yi ma ta ɗauraya. Bayan sun gama ne ta buɗe ɗakin kafin ta ɗaura towel ta shiga wanka. Tana fitowa shi ma ya shiga don yin wanka da kanta ta kai ma sa ruwan wankan a banɗaki bayan ya shiga sannan ta nemi ruwan yin alwalar kwanciya barci. Tana shiga ɗakin ta fara goge jikinta, ga hasken nepa ya gauraye ɗakin sai dai rashin fanka, Allah ya sa yau garin ba wani zafi. Yana shigowa ta tana gama shafa mai. Kasancewar ta san cewa shi makaho ne ya saka ta warware towel ɗin a gabansa ta yi tsirara ba komai a jikinta . Under wear ta saka wata singileti ce da wandonta wanda ya tsaya rabin cinyarta ya tsaya ma ta. Hula ta saka ta yi shirin kwanciya barci ta yi don haka ta kalli in da ya ke tsaye ya ga ashe ya cire rigar da ya yi wanka da ita, jallabiya ya saka ta kalli inda yake zaune kan tabarma da yake kwanciya sai ta ga rashin dacewar hakan ya dinga kwana kan tabarmar ita kuma ta 'na kwance kan katifa mai taushi. Cikin sanyin jiki ya ce. "Ka zo mu kwanta tare saman katifar za ta ishe mu sai mu kwanta tare a saman katifar ka daina kwana a ƙasan tabarmar. " Ko ranta gama maganar ta juya sai ya ga jikinsa na rawa yana jijjiga Da sauri ta mike tsaye tana nufi in da yake tana kiran sunan shi cikin tashin hankali. *Maman Ihsan ce* 09065327999 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣6️⃣ Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi in da yake tana kiran sunan shi cikin tashin hankali. Kansa ya dafe yana cije leɓe sakamakon kansa da yake jin kamar zai zai tsage. Har lokacin jikin nasa na rawa kafin ka ce me jikinsa ya yi zafi sosai . Hankalin Ma'eesha tashi ya yi saboda jin zafin da jikinsa ya yi . Rasa ya za ta yi da shi ta yi ga jikinsa sai rawa yake yi. Ta duba time ta ga karfe goma sha ɗaya na dare ne a yanzu . Ga shi ita ba ta da kudin zuwa asibiti ballantana ta ce za ta kai shi. Don kudin da ke hannunta bai ba su wuce 3k ba, ga kudin abun hawa da za ta kashe kuɗi. "Sannu ko,bari na je na nemo ma ka magani." Ta ji maganar tana saka doguwar rigar Abaya ta saka ta yafa mayafin abayar ta ɗauki 3k ɗin da suka rage ma ta ta fice daga ɗakin. A hankali ta bude ƙofar fale-falen ta fice daga gidan nan tana waige-waige ya sa ta nufi wajen me shagon dake kusa da su. Ganin ta a rude ne ya dakatar da maso son shigowa shi ya fito . "Haniya lafiya?" Mijina me bai da lafiya Bƙan san ina j sa za kawo ma sa magani ba." Cikin tauSaya ya ce. "Allah sarki,bayan, Garba dake syar da magani sai dai shi ne ke siyar da magani a nan kusa. Yanzu kam na san ya tashi tun da karfe goma sha sha ɗaya ta yi, don shi karfe goma yake rufe Chemist. Yanzu Sa dai ki je ɗayan layin na san Emeka yanzu yana nan." Cikin damuwa ta ce. "Ta ina zan bi?" Kwatance ya yi ma ta nan da nan cikin zafin nama ta bar wajen ta kama hanyar da yake tunanin ya kwatanta ma ta. Dare ya yi ƙafa sun ɗauke ba mutane da suke kai da kawo. Tsaya wa ta yi kayan layin dake kke kusa da na su Har nunfashi take maida wa, kamar wacce ta yi tare gudun tsere. Ga duhu ba wutar nepa yanzu suka ɗauke don haka duhu ne ya mamaye garin ba ko daya. Ba irin unguwarsu ba ne, da ko dare ne yana mamaye da hasken fitilu. Tana nan tsaye ta rasa ina za ta kai sai ta hangi wani mutum na dosowa . Yana zuwa ta tambaye shi sai ya nuna ma ta ashe ma tana kusa da wajen. Ta karasa shi ma yana gab da rufe wa har ya fito sai ga ta. Komawa ciki ya yi yana tambayar ta me take so. Bayani ta yi ma sa ya haɗa ma ta magunguna sannan ta amsa tana tambayar sa kuɗin ya ce dubu ɗaya ne, ta mika masa ta kama hanyar tana gudu-gudu sauri -sauri don hankalinta a tashe yake ba ta san wani hali za ta same shi a ciki ba. Har ta karasa ƙofar gidan ba ta daina gudu-gudu ba. Tana shiga ta rufe kofar gidan da sakata sannan ta shiga ɗakin. Can ta hango shi ya mirgina ƙarshen gadon kusa da katifarta sai rawar sanyi yake yi . Tana ƙarasa wa ta durƙusa a gabansa tana yi ma sa sannu. Ya amsa da ƙyar kafin ta ɓallo magungunan bayan ta ɗauko ruwa ta ba shi magungunan, daƙyar ya iya hadewa sakamakon jin jikin da yake yi. Ya dunƙule a ƙasan ɗakin sai ta ce akwai sanyin ƙasa saboda robber carpet ne ya hau katifa ya kwanta. Sam ya ki yarda ya hau katifa sai da ya ga ta na ma sa magiya sannan ta taimaka ma sa ya kwanta saman katifar jikinsa na rawa kansa kamar zai tsage gida biyu. Addu'a ta yi ma sa sannan ita ma ta hau kan katifar ta kwanta gefensa tana yi masa sannu, kafin ta janyo wani zanin gadon ta lulluɓe su da shi. _,Nadra_ Bayan ta yi sallar isha'i tana nan zaune akan sallaya kaɗaici ya ishe ta, Alqur'ani mai girma ta ɗauka tana karatu, sai karfe tara na dare sannan ta ajiye ta yi sallar shafa'i da wuturi. Bayan ta idar ta yi addu'a ne sai ta rage kayan jikinta ta shiga bathroom don yin wanka. Ta fito daga wanka kenan ta ta nufi closet ɗin ta. Tana neman kayan barcin da za ta saka. Sai dai cikin rashin sa'a akwatin da aka loda kayan barcin a ciki duk ba rigar arziki da ta ga za ta iya sakawa. Domin dama Sidra ita ce ta zaɓi kayan barci da take so sannan Fahad ya biya kudin aka zuba su cikin akwatin kayan lefe. To duk rigunan irin waɗan da za'a ce da su da babu kusan ɗaya suke don irin ma su shara-sharan nan ne wanda komai na jikin mace a bayyane suke. Kuma ba su wuce rabin cinya ba, ma su tsawon sune waɗanda suka kai guiwa. Nadra ta dafe kai cike da takaici. Don iya kayan barcin da ta saba amfani da su riga ne da dogayen wanduna. Ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta saka tun da ta san na kowa ne zai ganta da shi ba, idan ta shige cikin bargo ta rufe jiki ta shi kenan. Don haka kawai ta ɗauki wani riga iya kar ta guiwa ta saka, bayan ta shafa turare ta saka pant. Don dama bra din duka ba wanda ya yi ma ta don size ɗin Sidra ne ita kuma tafi Sidra girman nono. Don haka ba ta wahalar da kanta ba ta saka rigar kawai ba tare da bra ba dan rigar irin mai hannun singiletin nan ne kuma tana da ƙoƙon bra don haka daga gabar rigar za ki ɗauka bra ta saka. Sannan ta daka dogon Hijabinta ta fito daga cikin closet ɗin ta zauna bakin gado. _Fahad_ Bayan sallar isha'i ya nufi complex ɗin da ake siyar da wayoyi ya siya wa Nadra tsadaddiyar waya ƙirar Samsung. Bayan ya ba su A.T.M card ɗin sa sun cire kudin yana fitowa kiran Mama ya shigo wayarsa. Sai da ya shiga cikin motarsa ya ajiye ledar wayar gefensa sannan ta ɗaga kiran wayar. "Hello Mama." "Kana lafiya?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ina Nadra." "Tana gida." "To ka yi sauri ka koma kafa kaɗaici ya yi ma ta yawa. Sannan ka biyo ga abinci ka wuce da a shi." "Okay gani nan zuwa." Ya katse kiran wayar a zuciyarsa yana mamakin yadda mahaifiyarsa ke ƙaunar yarinyar. Bai shiga da motar cikin gidan ba ya bar ta waje ya shiga ta karamin ƙofar bayan ya yi knocking maigadi ya ga shi ne ya wangale ma sa kofar gate ɗin da sauri. Gabaɗaya suna zaune a falon gidan daga ma su gidan har baƙin da suka zo bikin ba su koma ba. Don gobe kowa zai tafi Idan aka cire Hajiya Inna wato kakar Fahad, don ta ce sai ta kwana biyu za ta koma. Don haka kowa na fakon manya da yara don a ƙalla za su kai su goma sha biyar. Da sallama ya shiga wanda ba wanda ya ji sallamar sa sakamakon fira da suke yi. Kamshin turarensa ne da a kullum shi yake isar da saƙon wanzuwar sa a wajen. Abokanan wasan sa na ta tsokanarsa shi dai bai tanka ma su ba. Gaisuwar ma a taƙaice ya yi ma su. Zama ya yi a inda Rumaisa ta tashi ta ba shi wajan akan kujera mai zaman mutum biyu. Dama ita da Farida ne suke zaune a wajen. Sai ya zaune gefen Farida kallo ɗaya ya yi ma ta ganin yadda take cika tana batsewa ya share ta bai ko sake kallonta ba. Mama ce ta ce. "Ya jikin Nadra ɗin ta warware Mama." Karaf kakarsa dama ba kunyar zaro zance take yi ba ta ce. "Ƙarya kake yi munafuki yaushe ta isa warware wa yarinyar da ka ce ka far ma ta ko tafiya ba ta iya yi shi ne za ka ce ta warware?" Cije laɓɓansa na kasa ya yi cike da takaicin tsohuwar, sai ta ci gaba da cewa. "Na ina ce bayan an ɗaura ma ku auren da ita ka ce ba ka son ta tafiya ma gidan naka wajan matar ka ce ba za ka je ba sai da aka saka ka dole shi ne kana zuwa ka haike ma ta shi ma cikin ba ka son ta ne ko?" Yana jin yadda idanun ta ke yawo a jikinsa ya san ba mai yi ma sa kallon ƙurillar nan sai Farida, don haka ya ɗaga kai ya kalle ta karaf suka haɗa idanu, ta kau da kai tana harararsa. Dariya ta so ba shi ya danne ya mike yana cewa Mama ta bashi abincin zai wuce . Nan take shaida ma sa cewa baƙi za su zo ganin Amarya gobe saboda jibi za su koma garuruwansu. "Allah ya kai mu." Ya faɗa ba tare da ya sake magana ba. Rumaisa ce ta kawo ma sa basket na abincin ta na cewa. "Ko na kai ma ka mota ne?" "Amsa kawai ta yi ba tare da ya ce ma ta komai ba ya yi ma su sallama sannan ya kalli Mama. Ganin kallon ya sa ta gane akwai magana,. don haka ta tashi ta bi bayansa. A harabar gidan suka tsaya ya kalle ta cikin damuwa ya ce. "Mama wai me ye makomar wannan Auren ne?" "Ban gane ba." "Mama yarinyar nan fa ba wai son ta nake yi ba ita ma ba wai tana..." "Me ya saka ka amsa wa iyayen ta a lokacin da suka yi ma ka tayin aurenta?" "Saboda ba zan iya ce ma su a'a ba za su ji ba daɗi. Kuma ni..." Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar dakatar wa kafin ta ce. "Ka je dare na yi za mu yi magana daga baya." Ba ta jira cewarsa ba ta juya ta koma ciki. Daga gani ranta ya ɓaci da jin zancen nasa. Cikin sanyin jiki ya ya nufa gate ɗin gidan da basket ɗin a hannunsa. Bayan ya ajiye a bayan motar ya yi wa motar key ya bar layin. Ƙarfe tara da mintinan arba'in ya yi horn a ƙofar gidansa. Maigadin ya wangale ma sa gate ɗin ya shiga da motar zuwa parking space. Ya yi parking motar a parking lot ya fito rike da kwalin wayar sannan ya buɗe bayan motar ya ɗauko basket ɗin abincin ya nufi cikin gidan. Handle ɗin kofar ya murɗa ya shiga da sallama a bakinsa. Ba kowa a falon dake downstairs. Sai ƙamshin room freshener spray ke tashi. Kai tsaye ya haura upstairs ɗin. Nan ya ganta ta fito daga kitchen ta nufi ɗakinta. Motsin shigowarsa ne ya saka ta juya ta kalle shi. Shi kuma takaici ya ishe shi sakamakon sake ganinta da zumbulrlen hijabin da ya hana ta saka shi a cikin gidan matukar ba baƙin maza ne ko fita za ta yi ba. Wato ta raina maganarsa kenan . Fasa shiga dakin ta shi ta juyo ta nufi in da yake ta durƙusa cikin girmamawa ta karbi basket ɗin hannunsa tana ma sa sannu da zuwa . Dinning area ta nufa da basket ɗin ta ajiye a saman dinning table. Zama ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon yana kallon ta har ta karaso in da yake, ta buɗe baki za ta yi magana ta ji muryarsa yana cewa. "Ban hana ki saka hijabi a cikin gidan nan ba?" Sai a lokacin ta tuna amma sai sai a cikin wannan aniyar rigar barcin dake jikinta ba, don banbancin rigar da shi da babu kusan ɗaya suke. "Ba kya jin magana ko?" Kai ta girgiza ma sa alamar a'a. Miƙewa tsaye ya yi bayan ya ajiye kwalin wayar da ya siya ma ta a Centre table. "Ke kenan kullun cikin hijb a gida hijab a waje hijab makaranta hijab kasuwa hijabi kin kasa tantance in da ya dace a ce kina saka hijab ko?" Kafin ta yi magana har ya zare hijabin daga jikinta ya rike a hannunsa. Mutuwar tsaye ya yi sakamakon sakamakon arba da ya yi da kyakkyawar surar jikinta cikin figigiyar rigar barci da ba ta da maraba da babu. Yayin da ya ji kamar an zare masa laka daga jikinsa, sam bai yi tunanin haka ba. Yayin da ita kuma ganin yadda yake kallon jikinta ne ya saka ta yi saurin shigewa jikinsa ta ƙanƙame shi yayin da ƙafafunsa suka fara rawa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Wannan ƙirƙirerren labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suka ko hali ya zo ɗaya to a gafarce ni ba da niyyar yin hakan na yi ba. Arashi ne me kashe auren wawa *SADAUKARWA* Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku masoyana na *MAKAHO NE* Fans group ina jin daɗin comments naku da tarin addu'arku a gare ni Allah ya bar ƙanuna much love Page 2️⃣7️⃣ Yayin da ya ji kamar an zare ma sa laka da jikinsa, sam bai yi tunanin haka ba. yayin da ita kuma ganin yadda yake kallon jikinta ne ya saka ta saurin shigewa jikinsa ta ƙanƙame shi yayin da ƙafafunsa suka fara rawa. Wani yanayi da bai taɓa riskar kansa a ciki ba ya ji shi a yau. Tun daga tafin kafarsa har tsakiyar kansa yake jin wani abu na fisgarsa. Ita kam sai hawaye take yi don wani irin kunyar da ba ta taɓa jinsa ba a rayuwarta sai yau, ji take yi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki ta nitse haka take ji. Cikin kuka ta ce . "Yaya Fahad Please ka daina ba na so." Da ƙyar ya iya fisgo zance ya ce. "Me na yi ma ki na taɓa ki ne?"ya yi magana yana ɗaga hannayensa biyu sama alamar ba ruwansa. Kuka ta saka ma sa wanda ya sa shi cewa. "Me na yi ma ki da kike ma min kuka? Ina kece kika rungume ni, don haka ki sake ni ma na." Cikin kuka ta ce. "To idan na sake ka ai za ka ga jikina ne." "To ya kike so na yi?" "Ka rufe idanunka sai na sunkuya na ɗauki hijabi na na saka." "Makaho ne ni da zan rufe idanuna.?" Sai kuma ya ga gwanda ya rufe idanun nasa domin su rabu lafiya da ita, don idan ba haka ba komai zai iya faruwa a yadda yake jin kansa. Rufe idanunsa ya yi wanda ya sa ta yi sauri. Sakinsa ta durƙusa ta dauki Hijabin ta saka. Aguje ta bar wajan ta nufi bedroom ɗin ta ta rufe tare da murza key. Zubewa ya yi kan kujerar yana mayar da numfashi. Dade kansa ya yi cike da takaicin kansa yadda ya kasa controlling kansa akanta. Tsawon mintuna biyar yana zaune ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi kafin ya iya tashi ya shiga cikin bedroom dinsa. Wayarsa dake aljihunsa ya ciro sannan ya cire agogon hannunsa. Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga bathroom cikin rashin kuzari. Yana tsaye cikin bathroom yana kallon faffaɗan ƙirjinsa zuwa damtsen hannunsa. Ta cikin mirror dake cikin bathroom ɗin sa. Takaicin wanan zanen Tattoo yake ji ba wai don komai ba sai don sunan Sidra da ya sa aka zana ma sa da photon butterfly. Tauna lips din sa ya yi kamar zai fasa shi cike da takaici yake kallon zanen da ya fito a kyakkyawar farar fatarsa wanda kallo ɗaya za ka yi fatarsa ka san cewa yana kashewa wa jikinsa kuɗi. Kansa ya sakarwa shower na tsawon mintuna talatin wanda ba abinda yake tunani sai kyakkyawar surar Nadra. Ya raina yarinyar gani yake yi ƙwaila ce ita sai ga shi gabaɗaya ya susuce. Tsawon mintuna talatin ya ɗauka yana sakarwa kansa ruwa kafin ya yi wanka ya fito. Body spray kawai ya shafa bayan ya tsane ruwan jikinsa . Wando three-quarter fari ya saka ba tare da ya saka riga ba ya kwanta haka nan. Sai sai barci ya gagara ɗaukarsa. Har sai tsakiyar dare barci ya in nasarar ɗaukarsa. _Nadra_ Tun da ta samu ta kufce daga hannun Fahad ta rufe ɗaki kan gado ta faɗa. Kuka take yi tamkar ya yi ma ta wani abu, bayan ko taɓa ta bai yi ba. Ƙudundune kanta ta yi a cikin bargo tana hawaye. A haka barci ɓarawo ya yi nasarar ɗauke ta. _Makaho_ Tun da Ma'eesha ta kulluɓa ma su bargo bayan ya sha magani . Jinjina ya daina rawar jiki amma amma sai dai kansa har lokacin yana jin sa kamar zai rabe gida biyu. Dafe kansa yake yi yana karanta duk addu'ar da ta zo bakinsa. Ma'eesha sai jera ma sa sannu take yi kamar ta zubar da hawayen tausayinsa. Har sai karfe biyun dare kafin ya ji wani zufa ya keto ma sa. Har zuwa lokacin Ma'eesha ba ba ta yi barci ba. Tsabar tausayinsa. Sai da ta ga yana zufa sannan ta kai hannu saman goshinsa ya ji zazzaɓin ya sauka ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala a zuciyarta. A cikin kunnenta ta ji ya yi ma ta raɗa. "Na gode Allah ya yi ma ki albarka ya saka ma ki da gidan Aljanna." "Amin ya Allah." Ta faɗa tana Murmushin jin daɗi ta kwantar da kanta a saman ƙirjinsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, idanunsa ma suna da kyau da ɗaukar hankali sai sai a juye idanun suke. Gyara kwanciyar ta ta yi sa sakan faffaɗen ƙirjinsa yayin da take jin wani sihirtaccen ƙamshin da ya saka ta faɗuwar gaba. Sai ta dake ta dinga cusa kanta a ƙirjinsa saboda ƙamshin ya yi ma ta daɗi. A haka barci ya ɗauke ta a saman ƙirjinsa Sai sa ya tabbatar barcin ya yi nisa sannan ya zame ta daga jikinsa a hankali, ya kwantar da kanta kan filo. Tashi ya yi ta je ya watsa ruwa sannan ya ɗauro alwala ya zo ya gabatar da sallar nafiloli sannan ya koma kan tabarmar da yake kwanciya ya kwanta ba tare da ya koma kan katifar Ma'eesha ba. Wanda shi ma nan take ya yi barci wanda lokacin karfe uku na dare ne. _Nadra_ Sai karfe huɗu na asuba ta farka ta je ta ɗauro alwala ta yi sallolin nafila har alfijir ta keto ta shi ta yi raka'atanil fijri. Aka kira assalatu ta tashi ta je ta yi sallar asuba ta zauna yin azkar. Da karatun Alkur'ani. Tana son ta fita zuwa falo amma kuma kunya take ji ta haɗu da shi, don haka ta fara wanke toilet Sannan ta gyara ɗakinta ta yi saka turaren wuta. Falo ta nufa tana addu'a Allah ya sa baya nan, cikin rashin sa'a kuwa tana buɗe ƙofar karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna. Juyawa ta yi da a sauri za ta koma ciki sai ta ji muryarsa mai amo ya ce. "Come here." Ya faɗa babu wasa a fuskarsa. *Kuyi hakuri da wannan ba na da caji ne alƙawarin da na yi na tuna ya sa ɗan yi shi*🙏🏻 *Maman Ihsan ce*✍️ Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣8️⃣ Juyawa ta yi da sauri sauri za ta koma ciki sai ta ji muryarsa mai amo ya ce. "Come here." Ya faɗa babu wasa a fuskarsa. Ba yadda ta iya haka ga dawo cikin takunta na nutsuwa ta karasa gabansa, durƙusawa ta yi ta motsa laɓɓanta cike da karsashi ta ce. "Ina kwana?" Banza da ita ya yi kamar bai ji ta ba, har ta fidda ran zai yi magana ta ji ya ce. "Dodo kika gani da za ki gudu ko meye?" Kai ta girgiza alamar a'a. "Me ya saka ba ki jin magana ne?" "Tura baki gaba ta yi kafin ta ce. "Ina jin magana." "Ban ce ki daina zama mani da wannan ƙaton nan a gida ba." "Na saba da shi ne?" "Dole ki daina don ba na nuƙata." Ya faɗa cike da izza. Ba ta ce komai ba ta miƙe tsaye sannan ta ce. "Zan shiga na gyara ma ka ɗaki ." Bai yi magana ba ya yi kamar bai ji ta ba, ita ma ba ta sake cewa komai ba ta nufi ɗakin nasa. 'Ma sha Allah.' Ta faɗa a zuciyarta sannan ƙarasa ciki tana ƙarewa falon kallo. Don falonsa kalar fari ne hatta kujeru da Centre carpet da Centre table da labulaye tiles komai fari ne Bedroom ta nufa nan ma ya haɗu sosai komai dake cikin ɗakin white colour ne komai fari ne na ɗakin kama daga kan fenti labulaye, tiles, carpet, gado, mirror bedside drawer, zanin gadon, bargo, closet ɗin sa komai fari ne kuma da alama mutum ne shi mai tsafta. Toilet ta fara da shi don shi ma nasa fari ne komai na ciki. Duk da tsaf yake kamar an wanke shi amma haka ta wanke shi tas sai ƙamshi yake yi sannan ta fita zuwa bedroom ɗin sa. Gyara gadon ta yi ta sannan ta gyara ɗakin ta share ta yi mopping, room freshener da ta gani ta fesa a ɗakin sannan ta nufi hanyar fita. Falonsa ta gyara ta gyara ta saka ƙamshi sannan ta fita zuwa babban falon. Kamar yadda ta bar shi zaune haka ta same shi zaune sai dai wannan karon laptop ne a gabansa yana danne-danne. Falon ta zo tana kokarin gyarawa ya mike tare da laptop dinsa a hannunsa ya nufi nasa bangaren. Ledar da ya shigo da shi ta ɗauka za ta kawar ya juyo ya ce wayarki ce na siya ma ki, anjima zan kai ki a yi i ma ki register na sim card. Kafin ta ce komai har ya rufe kofar. Buɗe ledar wayar ta yi ta ciro kwalin wayar, ba tare da ta buɗe kwalin ta ga wayar ba ta mike tsaye ta fara gyaran Falon. Sai da ta gama tsaf sannan ta sauka downstairs ta gyara falon ta goge komai ko ina tsaf hatta toilet dake cikin falon sai da ta wanke ta kunna turaren wuta da sannan ta haura upstairs nan ma ta saka turaren wuta . Tana shirin komawa bedroom ɗin ta kenan ta ji ta ji ƙarar ƙararrawar ƙofa. Sauka ta yi ta je ta buɗe, sai ta ga Rumaisa ce da basket a hannunta. Murmushi suka sakarwa juna kafin Rumaisa ta ce . "Barka da safiya Aunty?" "Don Allah ki daina ce ma ni Aunty ki kira ni da Nadra, don kin girme ni ni ce ya kamata na kira ki da Aunty." Murmushi Rumaisa ta yi ta ce. "Ko na girme ki yanzu ke ce sama da ni, sabi'oda Yayana kike aure kenan kin zama Yayata." Mika ma ta basket ɗin ta yi tana cewa. "Sauri neke yi sai Anjima kuma." "To don Allah ki ce wa Mama ta daina aiko ma na da abinci mun gode sosai, zan fara shiga kitchen da kaina." Kai Rumaisa ta jinjina tana cewa. "Zan fada ma ta in sha Allah." Sallama suka yi ta juya ta tafi ita kuma ta shiga da abincin ciki, a dinning table ta ajiye ta shiga bedroom nata. _Ma'eesha_ Farkawa ta yi da asuba cikin barci take ta laluben katifar ko za ta ji shi, amma sai ta ji wayam ba alamar mutum a kusa da ita, bayan ta san a jikinsa da ta kwanta. Kunna torchlight ɗin wayanta ta yi sai ta hango shi can kan tabarma da yake kwanciya akai ya kwanta ya dunƙule jikinsa waje ɗaya. Mamaki ya kama ya kama ta domin ita dai a iya saninta yadda ta yi masa gata ta kawo shi kan katifa ta lulluɓe shi amma bai masa ba ya tashi ya koma kan tabarma. Taɓe baki ta yi daidai lokacin ne kuma aka kira sallah. Shi ma kiran sallar ne ya farkar da shi ya buɗe juyayyun idanunsa wanda suke ajuye sai dai ba sa da amfani tun da baya gani da idanun. Ƙoƙarin tashi ya fara yi ta yi sauri ta sauka tana miƙa ma sa sandarsa. "Ga sandarka nan." Ta mika masa sandarsa ya karba tare da cewa. "Na gode Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa tana ɗaukar buta ta ba shi buta. "Ya jikin naka?" "Na ji sauƙi." "Allah ya kara sauki." "Amin na gode, matata maganin kukana." Bayan ya yi alwala ya je masallaci yayin da ita kuma ta yi sallar ta a gida. Sai karfe bakwai ya dawo daga masallaci zuwa lokacin har ta kammala breakfast. Doya ta soya ma su sai ta yi source ɗin ƙwai. Da ruwan Lipton wanda ya ji kayan ƙamshi. Don kudin da suke hannunta sun ƙare ƴan canji ne suka rage ma ta. Ruwan Lipton kawai ya iya sha bai ci doyar ba, hakan ya saka ta damu Kasancewar ta san ruwan Lipton ba zai ɗauke shi ba. "Ko na siyo bread ne na haɗa ma ka tea ka sha?" "Kada ki damu hakan ya ishe ni, ba na jin cin wani abu a bakina ne." Cike da tausayawa ta ce. "Ayyah sorry." Kai kawai ya jinjina ma ta ba tare da ya yi magana ba. "Bari na je na kawo ma ka maganininka." Tana fadar haka ba ta jira cewarsa ba ta tashi ta ɗauko ledar maganinsa ta ba shi. Pure water ta fasa ta zuba a cup ta bashi . "Ka sha maganin sai ka kwanta ." Ta fada tana ɓallo ma sa maganin ta bashi, ya karba ya sha. "Zan yi wanka." Ya faɗa yana dafe kansa. "Okay bari na kai ma ka ruwa." Tashi ta yi ta je ta haɗa ma sa ruwan wanka ta kai ma sa banɗaki. Yana zaune ta dawo ta ce. "Na kai ma ka ruwan a banɗaki." "To na gode Allah ya yi ma ki albarka." Amin ta amsa yayin da da shi kuma ya fara lalube cikin jakar kayansa. "Me kake nema?" "Jallabiyata." "Okay bari na duba ma ka." Kafin ya yi magana sai hannunsa ya kai kan jallabiyar sakamakon tana da santsi ne ta fita daban da sauran kayan, hakan ya saka da ya kai hannu yake gane abinda ya taɓa. Ɗauka ya yi ya yayin da ita kuma ta fita daga ɗakin. Bayan fitar ta sai ya cire kayan jikinsa ya saka jallabiya. Kayan da ya cire ya fito da su yana cewa. "Ina son na wanke kayan kafin na shiga wanka." "Saboda me za ka yi wanki bayan ba ka da lafiya ?" "Kar ki damu zan iya yi." Nan ta dai suka fara jayayya akan za ta wanke masa ma sa shi kuma ya hana ya ce shi zai wanke. "Kana son na samu lada?" "Eh sosai kuwa Ma'eesha." "To idan har kana son na samu lada to ka bar ni na yi wankin kayan ka domin lada za'a rubuta ma ni." Hakan ya saka ya ce. "Ke me ya saka idan zan wanke ma ki kike hanawa?" "Saboda ni na fi cancanta na yi ma ka ba kai za ka yi mani ba." "Ni kuma ba na son ki wahala bisa la'akari da gidan da kika fito ba ki saba da waɗan nan aikace -aikace ba." Murmushi mai ciwo ta yi tare da cewa. "Haka ne, ka yi gaskiya, tabbas ban saba ba don ma su aiki ke yi ma ni amma hakan ba yana nufin ban iya ba ne. Don haka ko da a ce mijina kana da kudi ka aje ma su aiki to ka sani duk wani aiki naka ba zan taba bari ƴar aiki ta yi ba domin kwaɗayin ladan da zan samu wajan kyautata ma ka." "Kin tabbata?" "Of course, ka jira lokaci za ka ce na faɗa." Murmushi ya yi kafin ya ce. "Wani lokaci zan jira kuka yaushe lokacin zai zo, na so na ga wannan lokacin." Kallo da ta yi tana ɗauke ƙwallar da ta ji ya gangaro ma ta da yatsanata ta ce. "Lokaci yana tafiya a hankali ga masu jira, yana gudu da sauri ga masu tsoro,yana zama dogo sosai ga masu korafi, yana zama gajere ga masu murna, Amma ga masu ƙauna lokaci shi ne madawwamiya." Cikin sanyin jiki ya nufa banɗaki ba tare da ya yi magana ba, saboda yanayin maganar na ta tana gab da yin kuka. Domin ya ji ƙuna a cikin kalamanta. _Nadra_ Ta gama shirinta zuwa register da zai kai ta na sim card ɗin da zai siya ma ta. Haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki domin ta san ko ba komai za ta ji Muryar Umma da Abba. Fitowa ta yi dan sanar da shi ta shirya, baya Falon don haka sai ta yi knocking da a ƙofar falonsa. Jin shiru ya saka ta yi tunanin cewa yana cikin bedroom ɗinsa. Don haka ta tsaya bakin bedroom tana knocking. Izinin shiga ya ba ta ta tura ƙofar bedroom ɗin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Yana tsaye a gaban dressing mirror ɗaure da towel a ƙugunsa ta shigo. Ganinsa haka nan ta juya da sauri tana barin ɗakin. Ta jikin mirror ya kalle ta ganin yadda ta fita kamar wacce ta ga abin tsoro take guduwa. Tsane ruwan jikinsa ya cigaba da yi. Ita kuma ba ta tsaya ko ina ba sai bedroom ɗinta. Don saura kadan dogon Hijabinta ya haɗe ma ta ƙafa ta faɗi, sai Allah ya taimake ta ba ta fadi ba. Tana nan zaune bayan wasu ƴan minutes ya shigo sanye da farin yadi mara nauyi. Sai ƙamshin turarensa yake tashi a jikinsa. Ganinsa ya sa ta mike da sauri tana kallon sa cike da fargaba, ganin take yi kamar wani laifi ta aikata ma sa ganinsa da ta yi ɗaure da towel. "Ke." Kallonsa ta yi ganin yana kallonta ya saka ta ɗauke idanunta da sauri. "Ina ganin akwai motsi a cikin kanki ko?" Ba ta gane me yake nufi ba don haka ta ce. "Motsi a cikin kai kuma?" "Eh ina nufin ba ki da cikakken hankali ko?" Tura baki ta yi tana kau da kai. Da kika shiga ɗakina me ya saka kika fita a guje?" "To da ka san ba ka da kaya a jikinka me ya saka ka bari na kalle ka haka nan ai bai dace ba." Mamaki ta bashi don haka ya ce. "Shekarunki nawa?" "Goma sha takwas." '18 years no wander ta fiye shirme da yawa, ashe akwai tazara tsakaninta da Sidra, don Sidra yanzu shekarunta ashirin da biyar, an dauki yarinyar da ba ta gama mallakar hankalin kanta ba an hada ni da ita.' Tsuki ya ja a fili wanda sai da ta ɗaga kai ta kalle shi. Sai ta ɗauka shigar da ta yi masa ɗaki ne ya ba shi haushi, don haka ta ce. "Ka yi haƙuri zan kiyaye." "Za ki kiyaye me?" "Ba zan sake shigar ma ka daki haka nan ba ganka ba kaya a jiki ba wannan ma akasi ne." Dafe kansa ya yi ya rasa ya zai nuna ma ta daidai da ba daidai ba. "Kina zuwa islamiyya?" ",Eh mana har walima fa sai da na yi." "Me aka sanar da ku akan hakkin aure?" Shiru ta yi kanta a ƙasa, ya ce "Akwai inda aka ce ma ku ya haramta don miji ya kalli matarsa ba kaya ne ko kuma shi ya kalle ta ba kaya sun aikata wani babban laifi ne?" Girgiza kai ta yi alamar a'a. Sannan ta ce. "An ce mu dinga rufe tsiraicinmu." "Okay to waye aka ce ku baiyana wa tsiraicinku ?" Tura baki gaba ta yi tana kau da kai. "Ni ma ban sani ba." "Okay to bari na nuna ma ki yau za ki sani." Ya faɗa yana nufo tana ja baya, da sauri ta ce. "Mazajen aurenmu ne za su iya ganin surar jikinmu." Ta fada kamar za ta yi kuka, shi kuma ya yi dariya ya ce. "Oh ashe kin sani kike yi kamar wata..." Rurin wayarsa ya saka ya dakata da maganar da yake yi ya duba ganin Mama ce ya ɗaga da sallama. Bayan sun gaisa ne ta cikin wayar take sanar da shi zuwan dangin mahaifinsa zuwa Anjima. Ya ce to ya sani zai kai Nadra ta yi register layi ne ya siya ma ta waya. Mama ta ji daɗin hakan sai sanya masa albarka take yi, ta ce ya ba Nadra su gaisa ya ce tana cikin dakinta idan ta fito zai kira. Ya fadi haka ne don ya ga ta kasa motsi kunya ta ishe ta ba lallai ta yi maganar ba. "Ki same ni a mota." Yana fadar haka ya fice daga ɗakin, ita ma ta bi bayansa. Tsaye ta gan shi a ƙofar fita, tana fitowa ya rufe kofar, har lokacin ba ta yarda ta kalle shi ba. Motar da ya nufa ta bi bayansa, direbansa ya taso ya zo ya buɗe ma sa bayan motar ya shiga ita ma ya bude mata dayan gefen ta shiga sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa, ya yi wa motar key suka bar gidan bayan maigadi ya wangale ma su gate. *ABUJA* _Sidra_ Ta fito daga cikin gidan hannunta rike da handbag ɗin ta da wayarta. Wajen motar dake harabar gidan ta nufa. Direban ya saka trolly ɗin ta a but motar yayin da ta zauna bayan motar. Fuskarta ba walwala duk yadda Sady baby ke ta yi ma ta magana ba ta wani kula ta ba, don haushin ta take ji. Kasancewar ita ta ba ta goyon bayan abinda ta aikata, a lokacin da Khadijah ke hana ta gani take yi Khadijah ba ta ƙaunar ta, sai ga shi sanadin biye wa Sady baby komai ya lalace ma ta. "Ƙawata Sa mun yi waya, don Allah ki yi hakuri kuma da za ki bi shawara ta ki hakura da Fahad tun da an bashi ƙanwarki ya aura." "Fahad nawa ne ni kaɗai babu macen da za ta mallake shi sai ni kuma zan iya aikata komai a kansa, babu wanda ya isa ya ma ni shamaki da abun so na ciki kuwa har da ƙanwata Nadra" Ta fada cike da ƙasaita. "Direba mu tafi sauri nake yi." "Allah ya tsare hanya." "Amin idan kuma har wata matsala ta biyo baya to fa ki sani ba zan ɗauki fansa ta akanki ba zan taɓa saurara ma ki ba ko kaɗan." Direba ya ja motar suka bar gidan suka kama hanya don zuwa Kaduna. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page2️⃣9️⃣ "Amin. Idan kuma har wata matsala ta biyo baya to fa ki sani zan ɗauki fansa ta akanki ba zan taɓa saurara ma ki ba ko kaɗan." Direba ya ja motar suka bar gidan suka kama hanya don zuwa Kaduna. Amma a zuciyarta fargaba ce ta yadda za ta tunkari iyayenta da maganar dalilin da ya sa ta gudu ranar ɗaurin aurenta. Tabbas ta san mahaifnta na da zafi, idan ya dauki zafi ya hau to saukowarsa abu ne mai matukar wahala cikin sauƙi. Sai yanzu take nadamar wasikar da ta rubuta ta ajiye, domin kuwa da ba ta rubuta ta ajiye ba za ta iya ƙaryar cewa sace ta aka yi yanzu aka sake ta. Amma wannan wasikar shi ne babban kuskuren da sai yanzu ta san ta tafka ta. Cike laɓɓanta ta yi tabbas ba za ta tunkari gidansu ba sai ta fara zuwa wajan ƙawarta Khadijah ta ba ta shawarar yadda za ta yi, wanda a baya ta yi kokarin hana ta guduwa amma ta kasa. Wayarta wacce har yau take kashe ta kalla sai ta kau da kai tana kallon hanya. _Fahad_ Yana zaune a bayan motar Nadra na gefensa , idanunsa na kan wayarsa yana danne-danne ya ce. "Za mu yi baƙi yau, dangin mahaifina ne za su zo ganin ki zuwa anjima." "To Allah ya kawo su lafiya ." Ba wanda ya sake yin magana a cikinsu har suka ƙarasa office na kamfanin MTN don ya siya ma ta sim kuma ta yi register. Suna parking a wajan da aka tanada don ajiye motoci direban ya fito da sauri ya bude ma su bayan motar . Suka fito sai ga wani mutum sanye da Suit ya ƙaraso in da suke cike da girmamawa ya ce wa Fahad. "Ambassador Barka da zuwa." Hannu Fahad Majidaɗi ya mika ma sa suka gaisa. Sannan ya kalli Nadra ya ce. "Madam Barka da zuwa." "Ina kwana?" Ya amsa sannan ya ma su jagora zuwa ciki. Ba ɓata lokaci aka yi ma ta duk abinda ya dace, gabɗayansu san san waye Fahad. Har da ihsani ya yi ma su sannan suka bar wajen suka kama hanyar gida. Ganin sun kusa zuwa ta hanyar da zai sada Nadra da gidan iyayenta ta kalle shi ta ce "Don Allah ka kai ni gida na ga Umma ta ko na mintuna biyar ne." Ka kallonta bai yi ba ballantana ya amsa ma ta. Har suka wuce hanayar unguwar tana kallon hanyar idanunta na cikowa da ƙwalla sakamakon ba ta da lafiya ko ranar auren a kwance take. Horn direban ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga da motar, parking space ya nufa ya yi parking sannan ya fito ya bude ma su. Bayan sun fito ne ya rufe sannan suka shiga ciki. Bayan sun haura upstairs ne ya kalle ta ce. "Ki haɗiye wannan hawaye naki na faɗa ma ki, idan kuma kukan kike sha'awar yi zan saka ki yi mai dalili." Ya faɗa yans jinjina kai alamar tabbatar wa. Na fada ma ki muna da baƙi idan kika kuskura kika aikata abun da zan ji kunya akan akan gidadanci suka bar gidan nan sai na hukunta ki a cikin gidan nan" Tura baki ta yi tana magana ƙasa-ƙasa tana cewa. "Ni kam ba bagidajiya ba ce, idan mutum baya irin rayuwar da kuke yi sai ku dinga ma sa kallon bai waye ba, to ba na son wayewar ta ku." "Me kike cewa ne?" "Ba abinda na ce da kaina nake magana." Ta faɗa tana kallon wayar dake ajiye a Centre table, ta dauki wayar ta tuna ba ta yi ma sa godiya ba. Ta kalle shi ta ce . "Na gode Allah ya saka da alkhairi ya ƙara ma ka buɗi." Tana fadar haka ta shiga ɗakinta da wayar a hannunta. Shi ma ɗakinsa ya wuce. Tana shiga ta daka sim card ta yi settings komai, tana gamawa ta ga ya tura kofar ya shigo mika ma ta kati ya yi ba tare da ya ce komai ba. Karɓa ta yi ta ga recharge card ne na 10,000 ya siya ma ta cike da murna ta yi godiya ya fice bai amsa ma ta ba. _Makaho_ Bayan ya fito daga wanka hannunsa ɗauke da bokitin ya ajiye a tsakar gidan. Ma'eesha na zaune a tsakar gidan ta ce. "Ka yi a hankali." "Na gode." Ya faɗa yana laluben ƙofar ɗakin kafin ya shiga da sallama. Sai bayan kamar mintuna talatin ta shiga cikin ɗakin da sallama a bakinta. Ya amsa ma ta yana zaune kan tabarm kansa a ƙasa. "Lafiya dai ko ciwon kan ne?" "Ba komai." Shiru ta yi kafin ta ce. "Zan je can bakin layi na dawo?" "A dawo lafiya?" Ya amsa ma ta sannan ta ɗauki gyalen ta yafa ta fice daga gidan. 2k ya rage ma ta a hannunta ga shi yanzu mijin baya jin dadi tana son ta siya ma sa nama ta ɗan yi masa farfesu ko zai ci tun da ya kasa cin abinci. Dubu ɗaya ta cire ta siye naman dubu ɗaya ya rage ma ta dubu ɗaya. Abun da ba ta yi tsammani ba shi ne ganin naman dubu ɗaya yanka biyar ya yi ma ta cikin sanyin jiki ta dawo gidan tana tunanin wanan. 1k da ya rage ma ta idan ya kare ya z su yi, ga shi tana son ta siye Omo da sabulu na wanki. Kafin ta shiga gidan ta tsaya wajen me shagon ta fiye Omo na ɗari biyu da dabulun wanki na ɗari uku aka ba ta canjin Naira ɗari biyar. Ta koma gida gidan in da ta tarar har ya yi barci, don cikin magungunan da aka ba shi akwai wanda zai saka shi barci. Gass ta kunna ta ɗora tukunya ta haɗa ma. Sa farfesun naman wanda ya ji kayan ƙamshi. Ko ɗaya ba ta ci ba ta zuba masa a bowl ta rufe ta ajiye ma sa. Jira take yi ya tashi ko zai samu abinda ya saka a baki, domin rashin cin abinci da bai yi ba ya dame ta _Nadra_ Sabuwar wayarta da Fahad Majidaɗi ya siya ma ta Samsung Galaxy S23 ultra wayar kudinta ta kai kimanin miliyan ɗaya da dubu dari biyu 1,200,000. Kallon wayar take tana Murmushi cikin ledar wayar ta duba ta zaro idanu sakamakon ganin zunzurutun kuɗin wayar wanda ba ta yi zato ba. Umma ta kira don ta ji muryarta amma sau biyar kiran na katsewa ba'a ɗaga kiran ba, sai ta saka lambar Abba ta danna ma sa kira, kasancewar ta haddace lambobin wayar a cikin kanta. Abba ya ɗaga kiran wayar tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." "Abba." Ta faɗa muryarta na rawa kamar za ta yi kuka. "Nadra ke ce?" Kai ta jinjina kamar yana ganinta. "Kina lafiya?" "Lafiya lau Abba." "Ma sha Allah, ina mijin naki?" "Yana ɗakinsa?" "Ba wata matsala ko?" Hawaye ta goge kafin ta ce. "Abba nan zan cigaba da zama da shi har zuwa lokacin da Aunty Sidra za ta ..." Tsawar da Abba ya daga ma ta ne ya saka ta fashe da kuka. Tabbas ta san cewa mahaifinta na da zafin zuciya kuma wannan alama ce da ke nuna har yanzu yana fushi da Sidra." Jin sautin kukanta ya saka ya sassauta murya cikin sigar rarrashi ya fara magana. "Nadra, ashe ba na faɗa ma ki cewa kada ki sake yi ma ni maganar Sidra ba, ki mance da ita tun da ta guje mu ta zabi wasu akan mu to ki ɗauka ta mutu. Na san mancewa da ita ba, amma wannan ne karo na karshe da za ki yi ma ni maganar ta. Tabbas ta so ta kunyata ni ta tozarta ni a idanun duniya Allah ya sa ke ce kika fidda mu kunya , hakika ina alfahari da ke Allah ya yi ma ki albarka ƴaƴanki za su yi ma ki fiye da yadda kika ma na." "To Abba." Ta faɗa tana goge hawaye. Kiran wayar Farida ne ya shigo wayar Fahad, nan take sanar da shi sun ƙaraso suna harabar gidan. Nan yake sanar da ita yana zuwa. Fita ya yi in da ya same su a harabar gidan, ƙannin mahaifinsa ne da yayyunsa, sai da wasu dangin mahaifinsa, sai Rumaisa da ta yi ma su jagora Da Farida wacce ta na ce sai ta zo ita ma. Duk da mahaifiyarta Hajiya Jummai ta hana ta zuwa don kada ta zo ta ga abun zai ɓata ranta. Motoci uku suka yi don sun kai su goma sha biyar. A falon dake downstairs suka yada zango. Sai ya gushe su cike da girmamawa abokanan wasansa na tsokanarsa Farida ba ta shigo ba ta tsaya a harabar gidan tana ƙarewa gidan kallo. Tana ina ma ita ce aka kawo wannan gidan a matsayin mayar Fahad Majidaɗi. Cike da ƙunar rai ta shiga falon tana karewa falon kallo. Tabbas ya tsaru gidan Fahad gida ne da kowace mace mai hangen nesa za ta yi fatan ace ita ce matar gidan. Bayan sun gaisa da kowa ne ya kalle su ya ce "Mu haura sama sai ta fito ku gaisa ko?" Ya fadi haka yana haurawa upstairs ɗin wacce ganin haka ya sa Farida ta bi shi a baya. "Yaya." Ta faɗa cikin shagwaɓa wanda ya sa ya tsaya daidai kofar ɗakin Nadra. "Ya aka yi ne Farida, kin gama fushin naki?" Hararar wasa ta yi ma sa tana cewa. "Duk ranar da aka ce na mutu to son ka ne ya yi ajalina." Basar da ita ya yi kamar bai je me ta ce ba, daidai lokacin da zai shiga ɗakin Nadra ta yi saurin rike hannunsa suka shiga tare. Da sallama a bakinsa suka shiga ita kam ko sallamar ba ta yi ba. Hannunsa na cikin na Farida suka shiga, shi a ganinsa ba wani abu ba ne kamar yadda Rumaisa ke rike shi haka Farida ke ma sa duk da kasancewar ita ba maharramarsa ba ce akwai aure a tsakaninsu. Daidai lokacin da Nadra ta ɗago kai tana kallon ƙofar, ta sauke idanunta a kansu ta yi saurin goge hawayenta. Hannunsu dake sarƙe cikin na juna ta kalla sannan ta kalli fuskar Farida sai ta ga ba ta san ta ba kuma ba Rumaisa ba ce wacce suke uwa daya uba ɗaya, iya saninta Rumaisa ce kawai ƙanwarsa. Harara mai cike da tsana Farida ke jifan Nadra da shi. Nadra kam ba ta ma san tana yi ba, dan kallo ɗaya ta yi ma ta ta kalli hannunta da take rike da na Fahad ta ɗauke kai. Wayar Fahad ce ta fara ruri ya kalli Nadra ya ce. "Sun iso suna falo." Daga haka ya daga kiran wayar yana mai zame hannunsa daga cikin na Farida. Fita ya yi daga ɗakin yana amsa wayar. Farida ta tsaya ta rike ƙugu tana ƙare wa ɗakin Nadra kallo. _Ma'eesha_ Bayan ta gama duk wasu aikace-aikace da take da su har wankin kayan ta da na Makaho sai da ta wanke su. Ta shiga ɗaki ta same shi zaune ya haɗa tagumi. "Ka tashi ?" Ta fada tana zama a gefensa. Hannun ta ta daura a saman goshinsa zuwa wuyansa ta ji ba zafi. "Alhamdulillah da alama ka ji sauki ko?" Kai kawai ya jingina ma ta ba tare da ya ce komai ba. "Na san kana jin yunwa ko?" "Eh." Ya faɗa a takaice. "Bari na kawo ma ka abin da za ka ɗan fara ci." "Bari na wanke baki." Ya faɗa yana mikewa tsaye. "Ina na ajiye Sandar tawa ce?" "Ga shi nan gabanka ai bai yi nisa da kai ba." "kin san ban gani nake yi ba, kuma ban laluba ba." "Allah sarki wata rana za ka gani, in sha Allah wata rana idanunka za su buɗe ka ganni ka ga yadda wannan duniyar ta mu take." Ɗan jim ta yi kafin ya ce . "Ba na jin zan iya gani, domin Wannan lalurar da ita aka haife ni, kin san kuka duk wata lalura in dai har da ita aka haife ka to ba wanda zai iya ba ka magani ko aiki ka samu lafiya. Sai dai wadanda suka samu lalurar daga baya ne to ana iya dacewa." "Ikon Allah ya fi gaban mamaki." Fita ya yi ya je ya wanke baki, ko da ya dawo ta ajiye ma sa farfesun naman nan da ruwa sai lemu na gora da take da shi ajiye. Da sallama a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, don haka ta amsa tare da cewa "Na ajiye ma ka abinki ka yi a hankali." Ta fada tana rike hannunsa da taimakonta ya zauna. ƙamshi ya daki hancinsa ya yi shiru kafin ya ce. "Me kika dafa." Farfesun naman rago ne." "Ina kika samu nama?" Murmushi ta yi tare da cewa. "Siya na yi ma na, ina zan samu nama?" "Na ɗauka kudin ki ya kare." "Eh ya ƙare yanzu haka ma ɗari biyar ne ya rage ma ni." Dafe kansa ya yi tare da furta kalmar. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un." Ga ni yake yi ya gaza tun da har kudin hannunta suka kare bayan ɗawainiyar da take yi na gidan da shi kansa, yanzu ina zai shiga ya fita don samawa kansu mafita, yadda kudin suka kare haka wata rana ma kayan abincin da ta ajiye ma su a gida za su ƙare." Ganin lokaci ɗaya ya shiga cikin damuwa sosai daga jin kuɗinta sun ƙare ta ce. "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, a cikin tafiyar rayuwa babu wanda ba ya fuskantar ƙalubale. Wani lokacin abubuwa sukan yi zafi har mutum ya ji kamar ya kasa, ko kuma ya fitar da rai, talauci, rashin aikin yi, bacin rai, ko rashin lafiya na iya sanya zuciya ta yi nauyi, amma babban sirrin samun natsuwa shi ne haƙuri. Komai yayi zafi maganinsa Allah hakuri ba yana nufin gazawa bane, yana nufin jiran lokacin da Allah ya sanya maka ne cikin natsuwa da yaƙini.Ka tuna dukkan waɗanda suka yi nasara a rayuwa sun sha wahala kafin su sha daɗi, Wahalar yau ita ce labarin gobe. Watarana idan ka waiwaya baya, za ka yi murmushi ka ce Alhamdulillah, domin duk waccan wahalar ta zama tarihi. Kada ka bari halin da kake ciki yau ya sa ka manta alkawarin Allah ci gaba da hakuri, ci gaba da addu'a, kuma ci gaba da aiki tukuru, Allah ya sa mu wanye lafiya, ya kuma canza mana kuncinmu zuwa farin ciki." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣0️⃣ "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, a cikin tafiyar rayuwa, babu wanda ba ya fuskantar kalubale. Wani lokacin abubuwa sukan yi zafi har mutum ya ji kamar ya kasa, ko kuma ya fitar da rai, talauci, rashin aikin yi, ɓacin rai, ko rashin lafiya na iya sanya zuciya ta yi nauyi. Amma babban sirrin samun natsuwa shi ne hakuri, Komai yayi zafi maganinsa Allah haƙuri ba yana nufin gazawa ba ne, yana nufin jiran lokacin da Allah ya sanya maka ne cikin natsuwa da yaƙini.Ka tuna dukkan wadanda suka yi nasara a rayuwa sun sha wahala kafin su sha daɗi wahalar yau ita ce labarin gobe. watarana idan ka waiwaya baya, za ka yi murmushi ka ce Alhamdulillah, domin duk waccan wahalar ta zama tarihi, kada ka bari halin da kake ciki yau ya sa ka manta alkawarin Allah. Ci gaba da hakuri, ci gaba da addu'a, kuma ci gaba da aiki tukuru. Allah ya sa mu wanye lafiya, ya kuma canza mana kuncinmu zuwa farin ciki." Cike da burgewa yake sakin murmushi saboda kalaman ta na hikima da burge wa, wanda ke sanya da cikin shauƙi a duk lokacin da ya ji fararen zantukanta ma su daɗin saurare, yakan tsinci kansa cikin farin ciki. "Bismillah ka ci kada ya yi sanyi." "Ke kuka fa?" "Kada ka damu na riga na ci nawa naka ya rage." Shiru ya yi kamar mai yin wani nazari kafin ya ce. "Ina son yau na lallɓa na fita na san ko ba yawa dai zan ɗan samu. Akwai wasu canji a aljihun wata rigata ina ganin za su iya kai ɗari uku ki riƙe su duk da na san ba waya amma ba za ki rasa abun siye ba. Tun da ni ba na siyan komai ballanta na yi amfani da kuɗin." "Jinjina kai ta yi tare da cewa "To Allah ya sa ma su albarka." Da Amin ya amsa sannan Don haka iya guda uku ya ci ya ce ya ƙoshi, ta ce za ta rufe ma sa zuwa Anjima ya ce A'a. Ya ishe shi. Dole ta bar shi ita sai ta cinye sauran . Cewa ya yi zai zo ya shirya ya fita, ita ce ta hana shi ta ce sai ya gama warware wa bai kamata ya fita a haka ba. Ta ce masallaci kawai za ta iya barinsa ya tafi. _Farida_ Matsawa ta yi dab da Nadra tana kallon ta cikin idanu bayan ta gama ƙarewa ɗakin kallo. Wanda kallo ɗaya za ka yi ma sa ka san cewa iyayenta ma sun yi bajinta sun siya ma ta kaya ma su tsada kama daga furniture har komaib dake cikin ɗakin . Taɓe ba ki ta yi kafin ta ce. "Amarya ta ango." Nadra dai ba ta tanka ta ba, don tun da ta lura da mugun kallon da Farida ke ma ta ne ta gane ba arziki ya kawo ta ba. Idanun Farida ya sauka akan sabuwar wayar Nadra da Fahad ya siya ma ta. Zare idanu waje ta yi tana mamaki kafin ta ce. "Au har matsayinki ya kai ya siya ma ki wayar Samsung Galaxy S23 ultra wayar da kuɗin ta ya kai miliyan ɗaya da dubu dari biyu ko fi ma?" Baƙin ciki takaici ya ishe ta, wayar ta ɗauka tana dubawa, irin wannan wayar ita ce take mafarkin mallaka a yanzu. Burinta da samu wayar, sai dai ta yi mamaki yadda take tunanin Fahad ba haka ba, a baya da ta ji sanyi a ranta lokacin da ta ji an ce ba da ɗin ransa aka yi ma sa auren ba baya son yarinyar. Sai dai hankalinta ya tashi ne da su Rumaisa suka faɗa cewa Fahad ya yi karɓi budurcin Nadra har ta kasa tafiyar Sa bya ɗauke ta. A wannan lokacin ta ji guiwarta ya yi sanyi. Ta ji ta sare sai kuma yanzu da ta ga wayar nan da ya siyo ma ta . "Nadra kike ko wace ce oho dai, bari na ba ko wani labari. Ni sunana Farida kuma ni ƴa ce a wajan ƙanwar mahaifiyar Fahad. Kuma soyayya muke yi da shi, ke a taƙaice dai sabada mu yi kusanci da juna me ya je ya ɗauko ni daga wajan iyayena ya kawo ni gidansu don mu shaƙu da juna soyayyar mu ta yi karfi kuma..." Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon tura ƙofar da aka yi aka shigo. Kallon su ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya ce. "Lafiya kuwa?" Murmushi Farida ta yi ta ce. "Lafiya lau ina gabatar ma ta da kaina ne." "Why not ki bari ku tafi can gaban kowa sai ku yi gabatar wa an bar su zaune suna jira." Nadra dai ko kallonsa ba ta yi ba ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sanye da hijabinta har ƙasa wanda suka dawo da shi daga yin register na sim card. Da sauri ya rike hannunta wanda sai da ta ji faɗuwar gaba. Kallon su Farida ta yi wacce ta ji kamar ya soka ma ta mashi ne a ƙahon zuciya. "Farida ki je muna zuwa." Kamar ta yi ta kurma ihu haka take ji, q fusace ta fita. Kallon Nadra ya yi ya ce. "Ke wai ba na faɗa ma mi kada ki sake sanya hijabin nan ba. Da muka dawo ne ban cire ba." Kai tsaye ya ce. "Cire Hijabin nan." Ba musu ta cire, doguwar riga ce a jikinta na atamafa ɗinkin ya zauna ma ta cif a jikinta, atamfar irin me aikin nan a jiki ce kuma ta ji Stone work. Sun ɗan kama ta amma na sosai ba, kallonta ya fara yi wanda cikar halittar ta ke ba shi mamaki a iya shekarunta. "Haka zan fita? Ban saba ba fa." "Daga yanzu dole ki saba." Mintuna biyu ba ba ki kada ki bari na dawo na tarar da ke a cikin ɗakin nan ba tare da kin fito ba." Yana gama fadar haka ya fita daga cikin ɗakin. Tana nan tsaye ta ga lokacin da ya ba ta ya kusa cika, kuma ya hana ta saka hijabi ba t da wani zaɓi dole ta fito Suna nan zaune suna fira suna yaba kyawun gidan Fahad, shi kuma idanunsa na kan ƙafa yana jiran ta fito kafin su yi ƙorafi. Ƙarar ƙofar ya sa suka juya suka kalle ta. "Ma sha Allah." Wasu daga cikin su suka faɗa. Don tabbas Nadra ba ta da makudan tana da kyau da kuma diri mai ƙyau sai dai a ce ma ta baƙa ce ita. Kanta a ƙasa cikin natsuwa da kunya take takun ta. Shi kansa ya kasa ɗaukeidanunsa daga kanta, domin shi kansa idan ya ganta ba hijabi sai ya yi ta kallonta saboda surar jikinta mai ɗaukar hankali ne. Durƙusa wa ta yi ƙasa ta fara gaiahe su suna amsawa. Ƴan matan da su Rumaisa suka gaiahe ta a matsayin ta na matar Yaya. Kitchen ta nufa ta buɗe fridge ta ɗebo bottle water da lemukan roba sai da ta ciki tire sannan ta kai ma su ta ajiye ma su. Sannan ta kawo ma su cincin da dubulan da Alkaki ya yawa . Kitchen ta koma tana tunanin me za ta sarrafa ma su mai sauki ne. Ta duba kitchen ɗin duka akwai komai na buƙata. Sanin spaghetti ya fi sauki ya sa ta fara ƙokarin girka ma su. Nam da nan kuwa ta fara ma su girki ɗin . Ƙamshin turarensa ya da ta juya bayan ta blending na kayan miya. "Me za ki yi anan?" "Girki zan yi ma su." "Ba bukatar sai kin yi ma su girki don a yadda kiken nan da ƙauyanci ba wani girkin da kika iya, ki zo ki kawo ma su kwamacalar da za ki saka a yi ta magana akai. Idan sun tafi ki girka iya cikinki ke kaɗai." Maganar ta yi ma ta zafi amma sai ta yi Murmushi ta ci gaba da aikinta. Ƙamshi har cikin falon wata daga cikin matan na cewa "Sai mun ci girkin amarya kafin mu tafi. Shi dai Fahad na mamakin taurin kai irin na Nadra yake yi, wato ba ta daina ba ta ci gama da yi kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa ma su jallop ɗin spaghetti da ya ji kayan lambu da bisashen kifi. Sai Pepe chiken don kan gas biyu ta yi amfani da su. Babban food flask ta zuba ciki ta kawo ma su . Sannan ya kawo ma su Pepe chiken. Ta ƙara kawo ma su ruwan sanyi da lemu, sai plates da forks ta kawo ma su suna ta yi ma ta godiya . Miumushi ta yi tana cewa. "Ba komai, ku yi hakuri don ban san da zuwan na ku da wuri ba." Rumaisa ce ta dinga zuba ma su taliyar da pepe chicken ɗin . Don ganin suna da yawa ya saka Nadra ba ta kai ma su dinning table ba. An zuba wa kowa Rumaisa ta kalli Fahad ta ce. "Yaya daga yanzu in dai Aunty Nadra na wuri Sai dai ta za ta zuba ma ka abinci." "Am okay." Ya faɗa ya tashi ya koma can gefe kan sofa yana danne-danne a wayarsa. Shi a ganinsa ba ta iya girki ba kwamacala ce kawai . Sai ya ji kowa na santin abincin. "Aunty Ashe haka kika iya girki mai daɗi?" Murmushi kawai ta yi don ba sabon abu ba ne don a yaba girkinta. Don ko gida duk ranar da ta yi girki sai an fi ɗokin cin girkin nata fiye da na Sidra. Farida ce kawai ba ta ci abincin ba ta koma gefe tana danne-danne a wayar ta. Bayan sun kammala Rumaisa da sauran ƴan matan suka gyara wajan suka yi wanke-wanke. Har lokacin Fahad bai ci komai ba, don ko breakfast na safe bai yi ba. Sai karfe shida suka bar gidan. Nadra ta ba ƴan matan turarurruka iyayen kuma ta ba su dubu hamsin 50k cikin kudin sadakinta da aka ba ta. Bayan fitar su Fahad ma ya bar gidan, ba shi ya dawo ba sai karfe goma na dare. Yunwa duk ta addabe shi, don ba wani abun da ke cikinsa in ban da biscuits da lemu. Ɗakinsa ya nufa kai tsaye, a gajiye ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom. Wanka ya yi ya fito sanye da rigar wanka. Bayan ya shafa turarrukansa ne ya sanya wando three-quarter Blue da farar singileti. Ji ya yi ba zai iya kwana bai ci abinci ba, ga shi ko da ya je gidan Mama daddare nan ya ce a kawo ma sa abinci cewa ta yi ya je matarsa ta ba shi. Shi kuma baya iya cin abincin restaurant daga na mahaifiyarsa sai sai kuma ya yi ta fama da kayan snacks. Bai da zabi dole ya nufi part ɗin Nadra don yunwar yake ji sosai. Da sallama ya shiga ɗakin nata, tana zaune kan sallaya sanye da hijabi tana karatun Alkur'ani. Karfe goma da mintuna arba'in lokacin, tana karanta suratul Maryam. Zama ya yi bakin gadon nata har ta kai karshen surar. Don dama ta kusan idar wa. Juyo wa ta yi ta kalle shi yana zaune abakin gadon. "Sannu da dawowa." Kai kawai ya jinjina ba tare da ya amsa ma ta ba. "Please ki nema mani abun da zan ci yinwa nake ji." "To me kake so na girka ma ka?" "Komai mai sauƙi dai da ba zai ɗauki lokaci ba." "Na dafa ma ka indomie ne don ya fi sauƙi." Bai tanka ma ta ba, tashi ta yi ta je ta ajiye Alqur'ani ba tare da ta cire hijabinta ba ta fita zuwa kitchen. Don ita ta saba da saka hijabinta mancewa ma take da wai ya hana ta. Daga nan zaune da yake ya ɗan kishingiɗa ya kwanta kan gadon, ƙafarsa na ƙasa yaba kallon saman ɗakin. Lumshe idanunsa ya yi cike da gajiya nan da nan barci ya ɗauke shi a nan saman gadonta. _Maeesha_ Da misalin karfe goma na dare ta gama shirin kwanciyarta. Tana sanye da rigar barci iya guiwarta.Makaho kuma ya fito daga wanka kenan. Hannunsa rike da sandarsa ɗayan hannunsa kuma rike da kayan da ya cire, ya saka jallabiya. Da alama a cikin banɗakin ya sauya kayan jikinsa. Da sallama ya shigo Cikin ɗakin. "Assalamu alaikum" "Wa'alaika Salam." Ta amsa tana mai zuba ma sa idanun kasancewar akwai hasken wutar lantarki nepa sun bar ma su wuta. Zama ta yi a saman katifar tana kallonsa "Akwai abun da kake bukata me yanzu?" Ta tambaye shi sakamakon barci da ke idanunta tana son ta kwanta. "Ba na buƙatar komai, Allah ya yi ma ko albarka." "Amin ya Allah." "Ka zo ka kwanta saman katifar." "Ke ina za ki kwanta idan na kwanta saman katifa?" "Zan kwana ni ma a katifar mu kwanta tare ai ba wani abu ba ne matarka ce ni fa ta sunnah to mene ne don nun kwanta a wajen ɗaya, na tausaya ma ka ne fa saboda ganin ba dadin kwanciya ƙasan kake ji ba, sannan kuma ba isasshen lafiya ce da kai ba. Idan na ce na bar ma ka katifar ni ma ba zan iya kwanciyar a ƙasa ba jikina ciwo zai yi, ka sani ba wai sai an sanar da kai ba ma'aurata muke to me ye dalilin ka da ba ka son ka raɓi jikina, ba wai ina son wani abu ya shiga tsakanina da kai ba ne don Mun kwana a shimfida ɗaya amma na duba dacewar hakan ne sakamakon ba mu da wajen kwana sai wannan kayifar don ko bargo ma da za ka ji taushi babu. Amma sai gudun haka kake yi, na saka ka ka kwana tare da ni ranar da ba ka da lafiya bayan na yi barci ka zame jikinka ka sauka ka bar ni me hakan ke nufi? Ba akan daidai nake ba kai ne kake kan daidai?" _Sidra_ Da misalin karfe takwas na dare motar da ta kawo ta ta faka a ƙofar gidan Mahaifinta. Sakamakon motar ta k lalace a hanya ya saka suka yi dare. Sallama ta yi wa mai motar yayin da ya fito ma ta da trolly ɗin ta tana jansa ta nufi bakin gate ɗin. Knocking take yi kafin maigadi ya ce . "Waye a wajen." Ba ta tanka ba har ya taso ya bude. Ganin ita ce ya sa ya bude baki cikin mamaki ya ce. "Hajiya Sidra Kece daga ina?" Ba ta duba darajar farin gemu da ya haife ta ba ta ce. "Daga gidanku." Baki ya sake yana kallonta don bai yi mamaki ba kadan ne daga rashin mutuncinta, Don har marinsa ta taɓa yi. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣1️⃣ Baki sake yake kallon ta don bai yi mamaki ba, kadan ne daga rashin mutuncinta, don har marinsa ta taɓa yi. Da idanu yake kallonta har ta ɓace wa ganinsa. A hankali ya fara tuna wata rana ta dawo daga unguwa tana danna horn ɗin mota tana jiran ya bude ma ta gate. Shi kuma ya zagaya banɗaki sai da ya gama uzirinsa ya fito da hanzari ya wangale ma ta gate ɗin gidan. A guje ta shigo da motar kamar za ta bi ta kan Baba maigadi da motar. Ita ce ke driving sai Nadra dake zaune wajen me zaman banza. A fusace Sidra ta fito daga cikin motar ko kashe motar ba ta yi ba, Nadra ce ta kashe motar ta zare key. Baba maigadin yana kallon Sidra ta nufo shi a fusace sai da ya tsorata. Cikin kwantar da murya ya ce. "Ki yi hakuri Hajiya ina banɗaki ne lokacin..." Kafin ya kai karshen zancen ta ɗauke shi da mari wanda sai da ya yi baya kamar zai fadi. Tsoro da firgici ne ya bayyana akan fuskar Nadra. Idanunta cike da ƙwallar tausayin tsohon ta ce. "Baba don Allah ka yi haƙuri na san ba ta kyauta ba ɓacin rai ne, ba ta iya sarrafa fushinta ne." Ta yi maganar tana ɗauko ma sa hularsa da ta fadi ƙasa.Kallon Nadra ya yi tare da cewa. "Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa sannan ta sake ba shi hakuri ta nufi cikin gidan wanda Sidra ta riga ta shiga. A falon ta tarar da Sidra ita kaɗai sai huci take yi. "Aunty Sidra sam ba ki kyauta ba, ta ya ya za ki dubi wannan dattijo da ya haife ki za ki iya ɗaga hannu ki mare shi?" "Na mare shi akan me zai bar ni cikin mota ina jiransa? Ba aiki yake yi ba albashi ake biyansa ?" "Amma wannan ba shi zai ba ki lasisin da za ki taka wanda yake ƙarƙashinki ba, domin ɗan Adam daraja ne da shi kuma..." "Shut up!" Ta sakawa Sidra tsawa tare da cewa. "Ki fita a sabga ta idan ba haka ba wallahi yanzu zan ma ki marin da ya fi wanda na masa." Tana fadar haka ta nufi ɗakinsu ita kuma Nadra ta nufi part ɗin Ummansu. Sauran ma'aikatan gidan da suke gefe suna kallon yadda Sidra ta faɗawa Baba maigadi magana su ma suka shiga taitayinsu don na Baba mai gadi ma sauki ne. "Ita kuma wanan daga ina kamar wata korarriya ta dawo a wanann daren?" Direba ne ya yi maganar, sai mai ba wa fulawa ruwa ya ce. "Ai ta yi wa kanta sagegeduwa don da yanzu ita ce a gidan miji cikin rufin asiri, amma yanzu ga shi ta dawo ta tarar da mijin da take so ya auri ƙanwarta." Nan dai suka dinga firan Sidra a tsakaninsu. _Abba_ Tsaye yake a ɗakin Umma yayin da Ammi ke ta fama da Umma akan ta ci abinci amma ta ƙi ci. Don tun lokacin da ta yi arba da wasikar da Sidra ta rubuta ta ajiye ta gudu. To daga nan ba ta sake lafiya ba, abinci ma sai na matsa ma ta take ci. Saboda tana cikin tashin hankali na rashin sanin halin da ƴarta take ciki, ba ta san hannun waye za ta faɗa ba, kuma ba ta san in da ya shiga ba, don ko anan haka kawai idan suka fita unguwa daga ita har Nadra to Umma ba ta taɓa samin nutsuwa da sukuni har sai ta ga sun dawo gida hankalinta yake kwanciya, amma yau ga shi an wayi gari ba ta san in da Sidra ta tafi ba ko sanin halin da take ciki ba. Abba ya kalli mahaifiyarsa da take ta fama da Umma ya ce. "Ammi ta sha maganin ta kuwa?" "Ina fa ta sha Abdallah wannan yarinyar taka wallahi mu dai ba ta taɓa yi ma na rana ba, Allah ya wadaran halin Sidra ga shi ta saka mahaifiyarta ta cikin halin jinya, me yiwuwa tana can hankalinta kwance. Tun da yarinyar nan take ba abun arzikin da ta taɓa yi ma na, akan me za ki damu da yar da ba ta damu da ke ba, idan ta damu dake za ta tafi wani wajen ta bar ki ne?" Duk a cikin jikokina Sidra ce ta fita Zakka wallahi da ina da dama da na..." Sallamar ta da turo ƙofar da ta yi ne ya saka sauran maganar Ammi maƙalewa. Tana kallon Sidra da maɗaukacin mamaki, a hankali ta ce . "Sidra!" Umma dake kwance tana fama da jinya ta buɗe idanunta tana ƙokarin tashi zaune. Abba ya haɗe fuska kamar zai yi Aman wuta yana ma ta kallon bakin ciki da takaici. Trolly ɗin hannunta ta sake ta ƙaraso gabansu tana kuka. Tana ƙoƙarin zubewa akan guiwar ta kenan cikin zafin nama da tafasar zuciya Abba ya saka ƙafa ya yi balla da ita wanda sai da kanta ya haɗu da bango Ya bugu, ta zube a wajan tana sakin Maryan kuka. "Tashi ki bar mani gida tun kafin zafin zuciya ta ɗebe ni na yi ahalinki." _Ma'eesha_ Har ta gama zancen da take yi makaho bai tanka ma ta ba. Ita mamaki ma yake ba ta, meye a ciki don sun kwanta a katifa ɗaya tana matarsa yana mijinta. Ba ta gama mamaki ba ta ga ya kwanta akan tabarmar ya shafa addu'o'i a jikinsa ya juya ma ta baya. Takaice ya ishe ta don sai yanzu take nadamar yi ma sa magana da ta yi akan su dinga kwanciya a katifa ɗaya, sai ya ɗauka ko tana bukatar kasancewa da shi ne a shimfiɗar ma'aurata wanda abu ne mawuyaci ne ga mace budurwa kuma Hausa Fulani. 'Ba zan sake yi ma sa magana akan ya zo su kwanta a katifar ba in sha Allah.' Daga haka ta kwanta tana ta mita cike da takaici har barci ya ɗauke ta. _Nadra_ Indomie ta dafa ma sa wanda ta yi wa haɗi sai ya ji kayan lambu su carrot da sauran su ta dafaffen ƙwai da naman kaza. Ta ɗora plate ɗin indomie a tire ta rufe da wani plate ta saka fork sannan ya saka bottle water me sanyi da kofi . Cikin natsuwa take tafiya a hankali ta nufi ɗakinta don ba ta ji motsin fitowar sa ba da alama har yanzu yana ciki kenan. Ko da ta shiga da sallama a bakinta, ba ta ji ya amsa ba don dama shi sai ya ga dama take magana idan bai ga dama ko kana ma sa magana ba zai tanka ma ta ba. Stool ta janyo ta ɗira tire ɗin a gabansa. Ga mamakinta sai ta ga ya yi barci. Kamar ta tayar da shi kuma sai ta fasa tayar da shi. Don ba ta san yanayinsa ba, ba kowa ke son idan yana barci a tayar da shi ba, don haka ta fasa tayar da shi. Tsaye take tana kallonsa ta rasa ya za a'a yi. Don haka ta fara ƙokarin shiga wanka don ita ma barci take son yi. Hijabin jiki ta ta cire ta ninke shi ta ajiye a saman sallayar. Bathroom ta nufa don yin wanka. Wanka ta yi da shower gel ɗin ta mai ƙamshi sannan ta zuba wani turaren da Gwaggo Laraba ta kawo ma ta ta ce ta dinga zuba wa a cikin ruwan wanka yana da kanshi mai dadi kuma yana kama jiki ya daɗe yana kamshi a jikin mutum. Towel ta ɗaura a kikinta wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyarta, sai ta fito sam ta mance da wai Fahad na cikin ɗakin. Gaban dressing mirror ta tsaya tana goge jikinta da wani ƙaramin towel tana goge ruwan jikinta. A hankali ya fara bude idanunsa a cikin barci da ya ɗauke na mintuna. Saman ɗakin ya kalla kafin ya tashi daga zaunen da yake a hankali ya sauke idanunsa akan ta. Tana tsaye ta gama goge jikinta. Idaninsa na sauka a kanta sai da ƙirjinsa ya buga da ƙarfi. Tun daga kan zara-zaran yatsun ƙafarta yake kallonta Yana sama da idanunsa har zuwa santala-santalan cinyoyinta da suke sheƙi ga alamar cikar hips ɗin ta a bayyane. Kallonta yake yi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara. Man shafawarta take shafawa hankali kwance tana rera wakar larabci. Bayan ta shafa man a hannayen ta ne sai ta fara ƙokarin zame towel ɗin jikinta. Kamar an ce ta kalli madubin sai ta hango Fahad ya zuba ma ta rikitatun idanunsa yana kallonta. Da sauri ta mayar da towel ɗin da take ƙoƙarin kwancewa ta janyo hijabi da sauri ta zura ta rufe jikinta. Kau da kansa gefe ya yi cike da takaicin rashin kwancewar towel ɗin ba ta yi ba. Don baj taɓa ganin mace mai diri da ta jan hankalinsa ba kamar idan ta kalli Nadra ba hijabi a jikinta. Ko dai ta san cewa tana da sura mai jan hankali ne ya sa take rufe jikinta kullun cikin hijabi. Tabbas yarinyar ta kusan ruɗar da shi, amma saboda mishkilancin irin nasa ya basar kamar bai kalle ta ba. Fuska ba walwala ya kalle ta cikin tsare gida ya ce. "Ina abincin?" Kallon stool ɗin da ke gabansa ta yi tare da cewa . "Ga shi nan, na ga kana barci ne na ajiye ma ka." "Ina barcin zan ci da kina ajiye kika kama gabanki ?" "Ka yi hakuri na ɗauka ba za ka so na tayar da kai ba ne." "Okay." Ya faɗa yana miƙe wa ya nufi kofar fita ya fice daga cikin ɗakin. _Sidra_ Wani azababben zafi ne ta ji ya ratsa tana zaton kanta ma ya fashe. Duhu ta fara gani ga wani jiri da take ji yana ɗibarta daga kwancen da take. Muryar Abba ta ji cikin kakkausan marya ya ce "Ba na bukatar sake ganin ki a cikin gidan nan, ki tashi ki koma inda kika fito, ki je wajen da ya fiye ma ki nan." Cikin kuka ta ce. "Abba ka yi hakuri ka yafe ma ni wallahi sharrin shaidan ne." Idan ba ki tashi kin fita ba sai na illata ki kuma na saka a yi waje da ke yanzu kuwa." Sai a lokacin ta yi kokarin kiran sunan mahaifiyarta mai tausayin ta. Uwa mafi uba ko da Uba sarki ne." "Umma ki taimaka ki saka baki Abba ya saurare ni." "Ba abinda zan saurara ki tashi na ce. Sai a lokacin ta ji sautin kukan mahaifiyarta, don kuka ne ya ƙwacewa Umma q wanann lokacin. "Umma don Allah ku saurare ni, ki saka banki Abba ya sauko." Kallon kakarta ta yi tana cewa. "Ammi please ki saka banki ɗanki ne Abba yana ma ki biyayya kuma..." Kafin ta rufe baki Ammi ta ce . "Ko kashe ki zai yi ba zan ce komai ba mara mutunci kawai." "Na ji ko ba za ku yafe ma ni ba don Allah ku daura ma ni aure da Fahad idan bai aure Ni ba zan iya rasa rayuwata." Mamaki ne ya kama kowannen su domin kuwa da alama ba kukan nadamar abun da ta aikata take yi ba. Kuma babu nadama a tattare da ita, ba ta yi nadamar wuce wa ta bar iyayenta cikin tashin hankali ba, ba ta damu da halin da suka shiga ba a'a ita ta saurayin ta take yi ma. Cikin takaice Ammi ta ce . "Ai sai dai ki mutu domin Fahad yana can tare da matarsa Nadra." Kuka ta sake mai haɗe da kururuwa Abba ya ja ta ƙeee taka ihu bai saurare ta ba sai da ya kai ta har baƙin gate bayan ya ce maigadi ya buɗe ma sa gate ya cilla ta waje. Sai ga Ammi ta cillo ma ta handbag ɗin ta da trolly sun rufe gate ɗin ta ciki. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣2️⃣ Kuka ta sake mai haɗe kururuwa Abba ya ja ta ƙeee tana ihu bai saurare ta ba sai da ya kai ta har bakin gate, bayan ya ce wa Maigadi ya buge ma sa gate ya cilla ta waje. Sai ga Ammi ta cillo ma ta handbag ɗin ta da trolly sun rufe gate ɗin ta ciki. Kuka sosai Sidra ke yi tana tuna ranar haɗuwar su ta farko da Fahad. Ta fito daga cikin super market tana tsaye tana magana da wata ƙawarta da suka daɗe ba su haɗu ba sai yau da ta zo shopping. Sady baby ta kalli Sidra ta ce . "Na gaji da zuwa gidanku tun da ke ba ki zuwa gidan mutane dai dai ayi ta zuwa gidanku Ni ma na kama kaina." Sidra dake sanye cikin fitted gown na less ɗinkin ya zauna ma ta a jiki less ɗin dari ne da ratsin golding sai ƙaramin gyale golding colour da ta rataya a gefen kafaɗarta sai baƙin glass da ta saka a idanunta tana jingine a jikin motarta sai ta buɗe bayan motar ta saka ledar siyayyen da ta yi, kallon Sady baby ta yi ta ce. "Ki yi haƙuri ƙawata wallahi Abba da Muna ba su bari muna yawon gidajen ƙawaye, Khadijah ƙawata kawai suke bari na je ita ma sai da dalili. Wata galleliyar mota ƙirar Lexus ( Lc series higher trims) ce ta ƙaraso wajen kyawun motar da tsaruwarta ya saka hankalin wadanda ke wajen ya koma ga motar. Hatta Sidra da ke sanye da bakin glass idnsunta na kan motar, sai dai ba za ka taba gane me take kallo ba. Murfin motar mamallakin motar ya buɗe, a hankali ya ziro fararen ƙafuwansa waje wanda yake sanye da takalmi kambas masu tsada ƙirar Gucci sneakers. Kafin ya fito yana sanye da tsadadden kaya na alfarma Tshirt mai tsada da wando jeans. "Fahad Majidaɗi kenan, I like the guy." Cewar Sady baby tana kallonsa. Jin shaka ya saka Sidra cewa. "Kin san shi ne?" Ba ta amsa ma sa ba, don gabaɗaya hankalinta ya koma kan Fahad. Cikin takunsa na ƙasaita yake taku har ya shiga super market. Sai da ya shiga sannan Sidra ta ce . "Waye wanan guy din?" Sady baby ta ce . "Sunansa Fahad Umar Majidaɗi. Shi Ambassador ne Yana wakiltar ƙasarsa ne a ƙasar America (united state) yana yawan zama a ƙasar America , yana aiki a matsayin hadin gwiwa tsakanin tsakanin Nigeria da America. Yana jagorantar harkokin diplomasiyaz yana ƙarfafa dangantakar ƙasar da yake wakilta, da kuma kulawa da al'amuran ƴan ƙasarsa da suke zaune a American yana Magance matsalolin siyasa da tattalin arziki tsakanin ƙasashen guda biyu." Murmushi Sidra ta yi kafin ta ce . "Yana ƙoƙari." "Na taɓa nuna ma sa ina son sa ya yi rejecting ɗina." Cewar Sady Baby cike da takaici Murmushi Sidra ta yi wanda ita kadai ta san ma'anarsa . Sallama Sady baby ta yi ma ta ta shiga motarta ta bar wajan. Sidra ta matsa jikin motar Fahad ta jingina tana jiran fitowarsa. Ba jimawa ya fito tare da wani ma'aikacin super market din ta riko ma sa kaya. A bayan motar ya saka ma sa Fahad ya dunƙule kudi ya ba shi, zagayawa ya yi wajen direba sai ya ga Sidra ta jingina da mirgina motar tana waya, tana pretending kamar da gaske. "Wallahi Umma na gaji sosai ga Direban bai dawo ba yamma ta yi ban san yadda zan yi ba ga shi ba na iya shiga abun hawa na kasuwa." "Excuse me." Ya faɗa kamar wanda aka yi wa dole. Sai ta yi kamar ba ta ji ba, kamar za ta yi kuka take magana akan rashin abun hawa. Kafin ta katse wayar ta kalle shi ta yi Murmushi. "Oh sorry." Ta fada tana matsawa. "Nevermind." Ya ba ta amsa yana kokarin shiga motar. "Oh Allah yanzu ya zan yi na koma gida." Kin haka ya ce. "Ki shiga na kai ki idan ba za ki damu ba." "Toh na gode." Ta fada tana mai zagayawa mazaunin direba ta shiga ta zauna. Tsawon lokaci mintuna ba wanda ya yi magana kafin ta ce . "Na gode fa." Bai amsa ma ta ba yana driving ɗinsa. "Da ana samun mutane irin ku marasa girman kai masu saukin kai ai da an gode." Sai a lokacin ya kalle ta yana cewa. "Ke ce mutum ta farko da ta ce ina da sauƙin kai wai ba na da girma kai, kowa cewa yake ina ji da kaina ke kika fita daban." Dariya ta yi tana cewa . "To ma sha Allah na zama ta daban a wajen ka." Kwatance ta yi masa ya kai ta har ƙoafar gidansu. Za ta fice ta ce. "Sai yanzu ta daban za ta sake ganinka." "Duk sanda kike bukatar gani na in dai ina kasar za ki ganni." Ya faɗa yana miƙa ma ta katinsa ta yi godiya, sai da ta jira wucewarsa ta shiga cikin gidan,. Direban su ta ba key ɗin motarta ta sanar da shi in da zai je ya dauko motar sannan ta shiga ciki. Tun daga nan ta ke kiran Fahad a waya suna gaisawa har wata rana ya zo ya bayyana ma ta yana son ta. Ranar kamar za ta zuba ruwa ƙasa ta sha , daga nan suka ƙulla soyayya cike da kulawar juna, in dai yana ƙasar yana yawan zuwa ko da bai daɗe ba. A hankali Sidra ta share hawayenta bayan ta gama tunanin ranar da suka fara haɗuwa da Fahad tana dafe kanta inda ta bugu da dukan da Abba ya yi ma ta. "Ba zai yiwa a raba ni da shi ba Fahad nawa ne dole ya saki Nadra ya aure ni." Da ƙyar ta tashi ga dare ya yi ta nufi bakin titi kasancewar ba nisa da gidansu da gidan Gwaggo Maimuna. Tana ganinta ita ma ta kore ta don ta dauki zafi kamar yadda ƙaninta Abba ya dauki zafi. Daga nan sai ta nufi gidan Gwaggo Laraba lokacin karfe goma sha ɗaya na dare. Gwaggo Laraba ta yi ma ta faɗa sannan ta kira Abba ta ba shi haƙuri akan ya yi haƙuri. Kwancewar shi ne dama da Gwaggo Laraba ya yi ma ta fada ya ce idan ba ta kori Sidra ba ta bar gidan nan idan ba haka ba sai ta hadu da ɓacin ransa. Ba ta da wani zaɓi dole ya ce ya tafi. A ranar Sidra ta ga tashin hankali sosai ba kaɗan ba. Ƙarshe ta yanke shawarar zuwa gidan iyayen Fahad don ta nemi alafarmar Baban Fahad ya je ya roƙi Abba ko Allah zai sa ya hakura kasancewar yana jin kunyar Baban Fahad yana ganin ƙimarsa. Ƙarfe ɗayan dare ta yi ba abun hawa ga shi dama ba da motarta ta tafi Abuja ba. Yanzu na ina take ta mota. Ƙarfe ɗaya da kwata ta isa ƙokar gidan su Fahad a jikace sakamakon dogon tafiyar da ta yi . _Makaho_ Bayan ya tabbatar da Ma'eesha ta yi barci don dama shi ma ba barci yake yi ba idanunsa biyu. Tashi zaune ya yi tare da lalubar sandarsa ya ji ya riko ta ya mike tsaye. Hanyar ƙofar ya nufa yana lalube har ya buge sakatar ya fita daga cikin ɗakin. Bayan ya ɗauro alwala ya zo ya fara sallolin nafila. Ba shi ya kwanta ba sai karfe uku na dare. Yana zaune kan sallaya yana addu'o'i kafin ya shafa. Kwanciyar sa ya yi wanda ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi. Kiran sallar asuba ya farkar da shi daga barcin da ya soma ɗaukarsa. Fita ya yi daga ɗakin ya nufi banɗaki. Wanka ya yi ya fito ya yi alwala sannan ya koma dakin. Jin tsit sai saukar numfashinta ya tabbatar ma sa da cewa . Har yanzu barci take yi ba ta farka ba. Kayan jikinsa ya sauya zuwa wata jallabiya kafin ya nufi in da katifar da Ma'eesha ke kwance. Pillow ya buga yana kiran sunanta. "Ma'eesha." A hankali ta bude ida wanda daka a lumshe suke kamar bairci. "Na'am." "Lokacin Sallah ya yi ni zan shiga Masallaci, ki tashi ki yi sallah. ,"toh" Ta fada hana tashi daga zaunen da take. Fita ya yi shi ma ya je masallaci yayin da ita kuma ta gabatar da sallar a gida. _Fahad_ Bayan ya bar indomie da Nadra ta dafa ma sa ɗakinsa ya koma. Kwanciyar rud da ciki ya yi yana cije lips ɗin sa ba tsakiya. Ba abinda ke ma sa yawo a kansa sai yadda ya ga Nadra ɗaure da towel. Gabaɗaya abun ya tsaya masa a cikin kansa ya yi kane-kane ne. Cike da takaici ya ce . "Oh Fahad wai tunanin me kake yi haka ne, ba dai waccen ƴar karamar yarinyar je neman birkita masa ƙwaƙwal. Da sallama ta turo kofar ɗakinsa ta shigo, bayan sallamar da ta dinga yi a bakin ƙofar falon Yana jin sallamar amma bai bude idanunsa ba kuma bai tanka ba . Tire ɗin ta ajiye wanda ta jera ma sa abincin akai . "Ga abincin nan na kawo maka." Kamar ba zai amsa ba kafin ya ce "Okay thank you, sai da safe za ki iya tafiya." "To Allah ya ba mu alkhair." Har ta kai bakin ƙofar ta ji ya ce . "Zo mana." Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya fadi, don haka ta juyo cikin sanyin jiki ta karasa wajensa. "Ina za ki je?" "Kai ka ce na tafi ." "Okay kuma yanzu na ce ki dawo" Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce . "A nan ɗakin za ki kwana." Ya faɗa kamar ba shi ya yi maganar ba. _Makaho_ Dawowarsa daga masallaci kenan ya yi sallama, Ma'eesha na zaune a barandar ƙofar ɗaki tana hada ma su abun breakfast a gas ta amsa sallamar da ya yi . Cikin sanyin murya ta ce . "Ina kwana?" Ya amsa da lafiya lau ya aiki ya ƙoƙari ?" "Alhamdulillah, ya karfin jiki?" "Alhamdulillah." Sallama suka ji yaro ya yi ya shigo. Suka amsa ma sa ya ce "Wai ana sallama da Ma'eesha." Cikin mamaki ta ce. "Waye ?" Yaron ya ce . "Wani ne ya zo da mota yana waje." A tunanin ta Yaya Jamil ne, amma duk da haka yya ce. "Ka je ka ce waye?" Yaron ya fita ba jimawa ya dawo ya ce. "Wai ya ce saurayinki ne Abdul ya dawo ." Mamaki da al'ajabi ya kama ta ya aka yi ya san tana nan , shin ba ta yi blocking nasa ba kuma ta fada ma sa ta yi aure. Tashi ya yi cikin ɓacin rai ta dauki hijabin ta ta saka ta lallai makaho ta ce. "Ina zuwa don Alaihi minti biyu." Daga haka ya nufi kofar gidan ta fice. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣3️⃣ Daga haka ta nufi ƙofar gidan ta fice. Wata baƙar motar ce ta hango a ƙofar gidan, tinted glass ne ba ta iya hango na cikin motar. Amma shi yana ganinta ya bude murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar yana kallonta da maɗaukacin mamaki a fuskarsa. Don ko da Ma'eesha ta faɗa ma sa a waya cewa ta yi aure bai yarda ba, sai da ya tambaye Nasreen ta faɗa ma sa gaskiya ne, daga nan ya matsa ma ta akan sai ta bashi address na Ma'eesha. Da farko ta hana ma sa sakamakon Ma'eesha ta yi ma ta gargaɗi akan haka wanda har da barazanar cewa idan ta sake ma ta zancen Abdul ko kuma ta ƙara ƙalubalantar auren za ta rabu da ita. Amma sai Abdul ya ruɗe Nasreen da maƙudan kuɗaɗe wanda ya sa ta ba shi address n gidan. A tunanin ta ba zai gane gidan ba saboda yanayin unguwar ta talakawa ne kuka gine-ginen gidajen ba wani tsari ne da su ba. Fuska Ma'eesh ta ƙara tsuke wa kafin ta isa wajensa. "Abdul meye haka, me ka zo yi a nan bayan na faɗa ma ka cewa ni yanzu matar wani ce, amma saboda rashin sanin darajar aure ya sa za ka zo kofar gidan matar aure ka ce a yi ma ta sallama ta fito?" Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce. "Wai yanzu Ma'eesha Ibrahim Khalil ce ta dawo haka? Look at you, kin yi baƙi kin rame duk wanda ya san ki a baya idan ya ganki yanzu ya san kina cikin wahala. Wannan rayuwar ba ta dace da ke ba, ba za ki iya ba kuma ba ki saba ba. Don haka wannan musakin mijin naki kuma faƙiri ki sa ya sake ki ki zo mu je ki cika ma ni alkawarin aurena da kika yi. Zan ba ki jin dadi da kwanciyar hankali zan mayar da ke..." "Ya isa haka Abdul!" "Kina da baƙin da za ki hana ni na yi magana ne? Bayan a baya ina ma ki kallon mai gaskiya ashe ba haka kike ba, bayan kin yi alƙawari ki saɓa an ba ki amana kin yi ha'incin? Ko kin manta ke da kanki kika yi ma ni alkawarin aure? Ke fa kika ce da zaran na dawo daga ƙasar Canada na dawo Nigeria za ki tura ni wajan mahaifinki na gama da shi a yi zandan aure kawai sai da na kira ki a waya ki ce ma ni wai kin yi aure haka yarda da amana take, bayan kin yi ma ni alƙawarin aure ashe yaudara kika shirya, Ni ina can ina tsara mana rayuwar da za mu yi bayan auren mu idan na ɗauko kin mun bar Nigeria, ashe sha sha sha kika mayar da ni ko?" Goge hawayen dake kan fuskarta ta yi kafin ta ce . "Ni ban zamo daga cikin munafukai ba da suke ɗaukar alƙawari su saɓa ko kuma su yi karya ko su ci amana. Ban yi ko daya daga cikinsu ba." "To idan ba ki yi ba me ya sa kika yi aure bayan kin yi ma ni alkawari?" "Ni ma kaina ban san da zancen aurena ba kwatsam lokacin ɗaya ake shaida ma ni wai an ɗaura ma ni aure ba tare da sani na ko shawara da ni ba ballantana neman yarda ta. Ka ga ta ina nake da laifi akan hakan?" "To na ji ba ki da laifi amma ai Nasreen ɗin ta fada Mani wanda kika aura musaki ne kuma faƙiri to me ya sa za ki yarda ki zauna da shi? Ai kin fi karfinsa nesa ba kusa ba, ai zaren ba kalar yadin ba ne. Kina da ikon da za ki saka ya sake ki ko ta ƙarfin arziki ko ta tsiya tsiya , bai isa ya yi jayayya da ke ba, idan kuma ba za ki iya saka wa ya sake ki ba ki bar ni da shi ina da hanyoyi da yawa da zan saka ya rabu da ke ko yana so ko baya so ki bar ni da shi." Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar dakatarwa kafin ta ce. "Ba ruwanka da shi?" "Da mamaki yake kallon ta kafin ya ce. "Kar dai a ce wai son sa kike yi, kina nufin kina son makaho mabaraci ina fatan dai ba ki taɓa bari ya raɓi jikinki ba?" A fusace t ce. "Abdul!" Sai da ya kalle ta da kyau bai amsa ba ya dauke kansa yana kallon gefe. "Ka fita a sabga ta domin yanzu ni matar aure ce, kuma zaman aure nake yi na ibada har abada ba don na fito wata rana ba. Khalifa mijina ne har a aljanna in sha Allah, ina son mijina ba abinda zai saka na rabu da shi mutuwa kaɗai za ta raba ni da shi, idan ka sake zuwa ƙofar gidan nan wallahi sai na tafka ma ka rashin mutunci, don sai na sa yara sun dinga jifanka da duwatsu sun farfasa ma ka mota. Wanda bai san darajar aure ba. Makirin murmushi ya saki kafin ya ce. Kika ce ba abun da zai sa ki rabu da shi ba ko? Sai kuma kika ce mutuwa ce kaɗai za ta raba ki da shi to ai ko akwai abun da zai raba ki da shi ɗin domin kuwa mutuwar rigar kowa ce kuma mutuwar tana nan tana jiransa idan kin isa sai ki hana mutuwar zuwa gare shi. Kuma ki jira ni ina nan dawowa gare ki Yana faɗar haka ya juya ya bude murfin motarsa sai dai kafin ya shiga ya juya ya kalle ta ya ce. "Kalli yadda kika rame kika yi baƙi kika lalace ba wanda zai gan ki yanzu ya ce wai Ma'eesha Ibrahim Khalil ce ta dawo haka." Yana gama faɗar haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key ya bar ta nan tsaye. Hawaye duk sun gama wanke ma ta fuska. Hanyar shiga gidan ta nufa ta shiga cikin sanyin jiki. In da ta bar makaho tsaye a nan ta same shi. _Nadra_ Da mamaki da kuma fargaba take kallon Fahad, Majidaɗi jin ya ce wai a nan za ta kwana. Tsaye take tana kallonsa yana cin abincin sa hankali kwance. Duk yunwar da yake kira yana ji bai cinye rabin abincin ba. "Ka ce anan zan kwana?" "Eh ko kina da matsala ne?" "Eh ina da ita." "Okay meye matsalar?" "Ba na iya barci tare da wani a kusa da ni." Dariya ta so ba shi anan sai ya danne. Tsaye ya mike yana cewa . "Amma ai ke sa Sidra ɗaki ɗaya kuke kwana ko?" "To ai ita Yayata ce." "To ni ma ai mijinki ne?" Cike da yarinta ta ce. "To ai kai ba wai mijina ba ne, ka ga ka ce wai za ka rabu da ni ya Sayyadi ya aure ni tun da ba ka sona shi kuma yana so na. " "Idan kika sake kira mani sunan wannan mutumin ba?" "To ka yi hakuri." "Okay na ji zancen rabuwa da na ce ma ki za mu yi lokaci nake jira." Kafin ta yi magana ma ya ce. "Ki ɗauke kayan nan ki kai kitchen, ki dawo da shirin barci ina jiran ki" Tura baki ta yi ta ɗauki kayan ta fice daga ɗakin Tana ajiye kayan kitchen da sauri ta nufi ɗakinta ta saka key ta mirza ta ciki . Ita kaɗai take magana a zuciyarta. 'Tab ai na gane nufinsa wato ya ce baya so na kuma zai sake ni ne nan gaba na je na auri Ya Sayyadina. Amma shi ne zai ce na je na kwana ɗakinsa ya yi Mani wayau ya kwashe albarkatun jikina sannan ya sake ni lokacin da zama fanko sannan zai bar wa Ya Sayyadi fanko, to ta Allah ba taka ba, masoyina mai so na tsakani da Allah ne kadai zai samu budurcina ba kai...' Maganar ce ta maƙale sakamakon jin ƙamshinsa da ta yi, gane gabanta ya faɗi ta juya ta kalli ƙofar. Tsaye ta gansa yana ma ta wani kallo da ta kasa gane ko na mene ne. Yana kallon ta yana kuma kokarin hana zuciyarsa shin da take so, don tabbas tun da ya lyalle ta ɗaure da towel gabɗaya kansa kwance a kanta. Matsanancin sha'awarta yake yi, sai dai yana kokarin hana kansa zuwa gare ta. Musamman da ya san cewa ba ya jin son ta a ransa, kuma idan har ya ya aikata wani abu da ita raina shi za ta yi, don kallon ƙaranar yarinya yake yi ma ta, a ganinsa raini ne zai ja wa kansa kuma yana ganin ya fi karfin haka nan a wajen ta yana ganin ba ta da ajin da zai haɗa jikinsa da nata. Tsuki ya ja cike da takaici ya harare ta sannan ya fice daga ɗakin. Ganin haka ya saka Nadra ta yi Murmushi tare da cewa. "Alhamdulillah na ji dadin wannan girman kai da ji da kai da kake da shi. Ya gani yana so amma Jin kansa da mishkilanci ya hana shi ya nuna, hakan ya Mani kyau kai kuma ya yi ma ka muni." Haka ta kwana zuciyarta fara tas. _Sidra_ Karamar door din gate ɗin ta ƙwanƙwasa, security dake bakin gate ɗin gidan ya duba agogo ya ga karfe ɗayan dare. Don haka daga cikin ya ce. "Waye?" Ta waje ta ce "Ni ce." "Kece wa?" "Ni ce Sidra matar da Fahad na gidan nan zai aura." "Tofa yallaɓai da ya yi aure abin sa." "Eh ƙanwata ya aura." "To ai ba nan ya zauna da ita ba ki je gidansa ma na." "Wajen mahaifinsa na zo, ka ce ma sa wai Sidra Abdullahi Maitama ce ta zo wajensa." "Gaskiya yanzu dare ya yi Alhaji na barci ba zai yiwu na tayar da shi ba." "Don Allah ka taimake ni ka sanar da shi ba zan iya kwana a haka ba ga ni a waje wani abu zai iya samu na, ba ni da in da zan je." Daidai lokacin ne wayar security ya yi ringing, ya duba ya ga maigidan ne, ya dauka cikin girmamawa ya ce . "Barka da dare yallaɓai." "Ka bude ma ta gate ta shigo ciki." Abun da Alhaji ya faɗa kenan sanan ya lashe kiran wayar. Dama lokacin Alhaji Umar Majidaɗi bai yi barci ba, ya gama duba wasu document kenan yana shirin kwanciya ya duba CCTV camera ya ga Sidra tana tsaye jikin gate ga trolly ɗin ta a gefenta tana magana da maigadi. Duk da ba wai ya gane ko wace ce ba amma tabbas ya san cewa ya san fuskar yarinyar ya taɓa ganinta amma ba zai tuna ina ba ne ya san ta. Bayan ya ba security damar shigowa da ita ne ya juya ya kalli kan gadonsa da Mama ke barci. A hankali ya kira sunanta yana shafa fuskarta. Bude idanunta ta yi a kansa ta ce . "Alhaji lafiya kuwa?" "Ki je ki bude main door akwai yarinyar da ta zo yanzu, tana tare da trolly me yiwuwa daga wani gari take dare ya ma ta a hanya." "Wace ce ita?" "Ba zan iya tuna wace ce ba amma na san za ki gane ta ke, mu tafi tare." Shiru Mama ta yi kafin ta sauko daga kan gadon ta saya hijabi suka fita shi kuma Bana yana sanye da jallabiya a jikinsa. Bayan security ya ba wa Sidra damar shigowa ta shigo tana kalle-kallen don gidan ko ina fitilu ne. Main door ta nufa tana tsaye tana shakkar yadda za ta buga ma su kofa, sai ta ga an bude kofar. Baba da Mama ta gani tsaye suna kallonta. Durƙusawa ta yi tana kuka yayin da Mama ta ce. "Sidra?" Sai a lokacin Baba ya gane ta . Cikin kuka ta ce. "Baba dan Allah ka taimake ni Abba ya kore ni, ƴan uwansa na sun kore ni ba na da wajen zuwa, dan Allah ka taimake ni ka ba shi hakuri ya yafe ma ni na koma gida." Shiru Baba ya yi kafin ya ce. Yanzu ransa a ɓace yake akan abin da kika aikata , ba zai saurare kowa ba, don haka ki zauna a nan zuwa wani sati idan na dawo daga ƙasar Germany zan je na roƙe shi ya yafe ma ki." "Na gode Baba Allah ya saka da alheri. " "Amin ya Allah, gobe da safe zan bar kasar idan na dawo sai kin fada mani in da kika je da kuma dalilin da ya sa kika tafi kafin na je na roƙe shi." Kallon Mama ya yi tare da cewa. "Hajiya a kai ta ɗakin baƙi a ba ta abinci ta ci ta kwanta." "To Alhaji " Mama ta fada tana cewa Sidra. "Tashi mu tafi." Baba ya nufi part ɗin sa yayin da Mama ta yi wa Sidra jagora zuwa daya daga cikin ɗakunan da suke saukar baƙi. Daki ne wanda aka komai da komai na buƙata gado wardrobe mirror T.V da fridge. Ga toilet a ciki. Mama ta kalli Sidra ta ce. "Nan za ki zauna, bari na kawo ma ki abinci." Daga haka ta fita don zuwa kitchen, ruwan semovita ya rage a cikin kula kuma tuwon da zafi da da miyar egusi da ya ji nama da ganda. Kawo wa Sidra ta yi sannan ya ce . "Akwai ruwa da lemu a fridge, don dama an zuba komai saboda baƙi da suka wuce yau." Godiya Sidra ta ya wa Mama sannan mama ta fita. Dama yunwa take ji ta buɗe fridge ta dauki bottle water da lemu ta wanke hannu ta ci tuwo. Bayan ta gama ne ta ajiye kayan q gefe ta shiga bathroom ta yi wanka. Ta fita ta sanya kayan barci ta kwanta. *Washegari* Bayan Nadra ta gama aikin gyaran gidan da ta saba yi ya rage ɗakin Fahad ya rage ta gyara. Kitchen ta nufa don ɗora breakfast sai ta ji alamar tafiyar mutum. Tana juyawa ta gan shi yana fitowa ɗakinsa hannunsa rike da waya yana cewa. "Ka yi hakuri Baba na macen yau ne tafiyar ta ka, da na kawo ma ka ita ka ganta. Amma duk da haka akwai sauran lokaci bari mu zo yanzu sai ta gaishe ka kafin ka tafi." Daga nan ya katse wayar ya karasa kitchen ɗin . Yana tsaye bakin kofar kitchen ɗin ta juyo suka hada idanu ya kalle ta daga sama har ƙasa. Kuma lokacin ma hijabi ne a jikinta. Durƙusawa ta yi ta gaishe shi cikin girmamawa. Bai amsa ba ya basar da ita. Cigaba ta yi da kokarin wanke tukunya za ta kunna gas ya ce . "Ki je ki shirya za mu je ki gaida Baba zai yi tafiya da safen nan." "To." Ta ce tana ajiye tukunyar ya fito ita ma ta bi bayansa. Ɗakinsa ya nufa ita ma ta nufi ɗakinta. Rigar Abaya ta saka kasancewar kayan lefen ba hijabi ko ɗaya, kasancewar Sidra ba ta saka hijabi. Ita kuma hijabin da ta zo da shi dama guda ɗaya ne na jikinta da ta zo da shi. Don ko kayan gidan iyaye Sidra ba ta ɗauki hijabi ba. Ganin babu hijab ya saka Nadra ba ta da wani zaɓi saka Abaya mai ruwan ƙasa ta yi rolling kanta da mayafin abayar. Ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa sai lips glow ta yi kyau ta fito kamar baƙar balarabiya. Handbag ɗin ta ta dauka ta saka wayarta a ciki da wasu ƴan kuɗaɗe cikin na sadakinta ne ta ɗauka.ta zo wajen ɗaukar takalma, sai dai duk takalmomin zaɓin Sidra ce don dogaye ne ma su tsini, wanda ita kuma Nadra ba ta iya tafiya da dogon takalmin ba. Tana tsaye tana neman mafita ya shigo ɗakin, kallonta ya yi ganin ta shiga har handbag ta dauka ya ce. "Me kike jira?" "Takalmin da zan saka nake nema. Ƙarasowa ya yi ya kalli takalmomi da ke wajen da sun kai kala goma sha biyar ya ce. Duk takalmin da suke nan ba wanda ya ya ma ki, sun yi amma suna da tsini ba zan iya tafiya da su ba." Hannu ya saka ya ɗauki wani bakin takalma ya ajiye q gabanta. "Ki koyi tafiya da su daga yau." Za ta yi magana ya wurga ma ta wani kallo wanda ya saka dole ta yi shiru ta saka haka nan, tafiya ta fara yi kamar mai tausayin ƙasa. Ya yi gaba tana binsa a baya suka fice . Har ya suka fito ya rufe kofar gidan yana zaune cikin motar yana jiranta ta karaso tana tafiya kamar mai yanga. Yana zaune a mazaunin direba ta shiga ta zauna gefensa. Ba tare da wani ya yi magana cikin su ba ya yi wa motar key suka bar gidan. *Mamman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣4️⃣ Ba tare da wani ya yi magana cikinsu ba ya yi wa motar key suka bar gidan. Driving yake yi cikin nutsuwa yana kallon hanya, har suka ƙarasa gidan bai ce uffan ba, haka ita ma ba ta ba har suka ƙarasa bakin tangamemen gate ɗin gidan. Horn ya yi security ya zo ya wangale ma sa gate ɗin gidan, ya shiga ya yi parking lot. Kusan a tare suka fito daga cikin motar, ma'aikatan gidan da suke nan suka fara gaishe su, Fahad ɗin kam bai amsa ba ita Nadra ce take amsawa cikin girmamawa kasancewar ta ga duk sun girme ta. Tafiya take yi a hankali sakamakon takalmin da ba ta saba amfani da irin su ba. Ƙararrawar ƙofar ta danna, sai ga ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta zo ta buɗe ma su ƙofar. Ganin Fahad da Nadra ya saka ta gane cewa ita ce Amaryarsa. "Sannu da zuwa yallaɓai ." Bai amsa ba sai kokarin shiga ciki yake yi, ganin bai amsa ba kuma dama sun saba da halinsa. Cikin sakin fuska ta gaida Nadra. "Sannu da zuwa Aunty." Murmushi Nadra ta sakar ma ta tare da cewa. "Yauwa Barka da safiya ya kike?" "Alhamdulillah." Part ɗin Mama Fahad ya nufa. Ba kowa a falon Maman don haka ya nufi bedroom ɗin ta. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Cak ya tsaya yana rike da handle ɗin kofar sakamakon ganin Sidra tana gaisawa da Mama. Take fuskarsa ya sauya kamar wanda zai yi aman wuta. Take ya juya ya fice daga ɗakin. Mama na ganin haka ta san cewa saboda ganin Sidra ne ya ɓata masa rai. Don haka sai ta bi bayansa tana cewa Sidra tana zuwa . Lokacin da ya fito Nadra na zaune a falon ita kaɗai. Bai kalle ta ba ta nufi part ɗin Baba, da kallo ta bi shi tana mamaki mai ya canza yanayinsa lokaci ɗaya. Mama na fitowa ta ga Nadra zaune a falo, murmushin jin daɗi ta sake tare da cewa. "Daughter dama tare kuke?" Murmushi Nadra ta yi tare da sauka daga kan kujerar cikin girmamawa ta gaida Mama. Ita ma ta amsa ma ta cike da farin ciki da jin daɗi.. Hannunta Mama ta riƙe sannan ta ce . "Mu je ki gaida Babanku kafin ya wuce ko?" Tashi Nadra ta yi Mama na rike da hannunta suka nufi part ɗin Baba. Yana zaune a falo sakan kujerar yayin da Fahad ke zaune a kukerar dake fuskantar Baba sai Farida da Rumaisa da suka saka Baba a tsakiya kowa tana fadin abinda da zai dawo ma ta da shi. Mama ta turo kofar ta shigo da sallama, Nasara ma sallama ta yi gabaɗaya . "Ga Daughter ɗin ka ta zo gaishe ka." Murmushi Baba ya yi tare da cewa. "Ma sha Allah, Daughter ƙaraso mana ." Cikin sanyin jiki take tafiya ta karasa gabansa ta durƙusa ta gaishe shi. "Ina kwana Baba?" "Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah." Tashi daga ƙasa ki hau saman kujera, ba ki ga ƴan uwanki duka a sama suke zaune ba, ba ruwan mu fa ki zauna duk ɗaya ne." Sai a lokacin ta kalli Fahad, Rumaisa, Farida da duka suke zaune a saman kujera, sai sai ita ba za ta iya ba, don haka ya zauna a kasa saman Centre carpet ta ce . "A'a Baba nan ma ya yi." Mama ma ta saka baki ko za ta hau sama ta ƙi yarda ta zauna a ƙasa. Lokaci guda ta sake shiga ran Mama da Baba. Ruamisa ce ta kalli Nadra cike da tsokana ta ce. "Matar Yaya ina wuni?" Nadra ta kalle ta ta ce . "Ina wuni Aunty Ruamisa?" "Ba na ce ki daina ce ma ni Aunty ba ni ƙanwarki ce tun da ƙanwar mijin ki ce ni ai na zama ƙanwarki ka ajiye zancen na girme ki." Murmushi kawai Nadra ta yi ta kalli Farida da ke ma ta kallon banza, ba tare da damuwa ba ta ce. "Ina kwana?" "Lafiya." Ta amsa a daƙile. Murmushi Mama ta yi ta ce ce kin gane kowa ko?" Ta nuna Rumaisa ta ce. "Wanan ita ce kanwar mijinki ita ke bin sa sunanta Rumaisa." Sannan ta nuna Farida ta ce. "Wannan kuma cousin sister ɗin mijinki ce ɗiyar ƙanwata ce sunan ta Farida, a nan gidan take zaune tare da mu." Kai Nadra ta jinjina sannan ta ce. "Na gane Mama." "Mu je mu yi breakfast kafin ka rasa jirgi ko?" "Haka ne, to Bismillanku." Daga haka suka mike tsaye ban da Nadra, sai da Rumaisa ta ja hannunta suka fara tafiya a tare. "Ki saki jikinki matar Yaya." A dinning table suka hallara dukansu Baba ne ya yi magana ta ce. "Ina Sidra ba ta tashi ba ne?" Jin sunan Sidra sai da gaban Nadra ya faɗi, amma ba ta yi magana ba ta yi shiru. Ma ce ta ce. "Ta tashi har ta shigo ɗakina." Kafin wani ya yi magana ne suka fara jin takun takalmi ƙwas ƙwas ƙwas. Gabaɗaya suka juya suna kallon mai zuwa. Sidra ce sanye da sanye da doguwar riga English wear tana tafiya idnsunta na kan Fahad sam ba ta lura da Nadra ba. Kallo ɗaya ya yi ma ta ya dauke kai tare da kau da kansa gefe yana tsuke fuska. A zubure Nadra ta mike tsaye cike da jin daɗi ta nufi Sidra tana cewa. "Aunty Sidra, kece? daga ina? Yaushe kika dawo kina lafiya?" Ta karasa gare ta ta rungume ta ƙam a jikinta tana sakin kuka. Murmushi Sidra ta sake wanda ya tsaya iya saman lips ɗin ta. "Aunty ina kika je kika bar mu cikin tashin hankali, Umma har rashin lafiya ta yi." Sidra dai ba t ce komai ba, ganin Nadra za ta sake jefo ma ta wata tambayar wanda kuma ba ta son ta amsa ma ta a gaban kowa ya saka ta ce . "Zamu yi magana anjima, yanzu mu je mu yi breakfast." Murmushi Nadra ta yi tana goge hawayan da ya wanke ma ta fuska. Garin cikin kawai take ciki sakamakon ganin ƴar uwar ta cikin ƙoshin lafiya. Zama suka yi a saman kujera yayin da Nadra gabaɗaya hankalinta na kan Ƴarta. Ita kuma Sidra idan ta ga alamar Nadra za ta yi ma ta magana sai ta girgiza ma ta kai alamar a'a. Sakamakon ba ta so ta jero ma ta wasu tambayoyin da ba za ta iya amsa ma ta su a gaban ahalin gidan Majidaɗi ba. Babu abun da Fahad yake hangowa a cikin idanun Sidra sau sallar soyayyarsa. Shi kuma ya ɗaukar wa ransa alkawarin sai ya musguna ma ta ya cusa ma ta baƙin ciki _Ma'eesha_ Ganin makaho tsaye yadda ta bar shi ne ya saka ta saka wa ranta cewar bai ji komai na maganar da suka yi da Abdul. Kallonsa ta yi duk da lokacin da ta kalle shi sai da gabanta ya faɗi, sakamakon ganin fuskarsa cikin irin yanayin da ba ta taɓa ganinsa ba. Da ƙyar ta iya magana ta ce . "Am dama kana nan tsaye ba ka zauna ba har yanzu." Bai tanka ta ba kamar tana magana da dutse. Ganin haka ta saka ta janyo hannunsa ta zaunar da shi a saman tabarma. "Mijina lafiya kuwa na ga yanayinka ya sauya?" Shiru bai ce uffan ba karshe ma tashi ya yi ya shiga ɗaki, sandarsa da yake dogarawa yana tafiya ta ƙalla tana sauke ajiyar zuciya. Bin bayansa ta yi zuwa cikin dakin ta ga yana laluben jakar kayansa. Ya ciro wasu kaya sannan ya zuge zip ɗin. Gane wanke zai yi ya saka ta fita da sauri, ruwan zafi da za ta hada ma su tea da shi ta juye a bokiti ta sirka da ruwan sanyi ta kai ma sa banɗaki. Ko da ya fito yana laluben bokiti sai ta ce. "Ranka ya daɗe na kai ma ka ruwan banɗaki." Bai ce komai ba ya nufi banɗakin da kayan da ya ciro a jaka. Wani ruwan zafi da dafa tana kokarin hada ma su shayi da bread. Don yau babu ƙwai kuma ba ta da kuɗin siyen ƙwai dan kudin ta sun ƙare daga ita dai ɗari biyar da ya rage ma ta. Ya fito daga wankan ya canza kaya wanda ya cire kuma ya zo zai ɗebi ruwa zai wanke ta yi saurin cewa. "Ka bar shi zan wanke." "Na gode amma zan yi da kaina." "Ni kuma ba zan bari ka yi da kanka ba, ko ba ka so na samu lada da albarkar da ke tattare da yi wa miji wanki ne?" Bai ce komai ba ya lalubi sandarsa ya shiga ɗaki daidaito lokacin da take haɗa tea. Fitowa ya yi da kayan aikinsa na gyaran takalma zai fita. Kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka karanci damuwa da yake ciki. Ganin ya nufi hanyar fita bai yi ma ta sallama kamar yadda ya saba ba ne ya saka ta ɗauki kofin tea da ledar bread ta nufi kofar fita ta bi bayansa da sauri. Shan gabansa ta yi ta kafa ma sa kofin a baki tare da cewa. "Bismillah ka sha ko kadan ne kada ka fita ba ka ci komai ba." Kau da kansa gefe ya yi ya ce. "Ina azumi." "Azumi shi ne ba ka faɗa ma ni ba?" "Na macen ne ki yi haƙuri." "Ko na ɓsta ma ka rai ne ka gafarce ni tuba nake kaina bisa wuyana." "Ba komai kada ki damu." "To Allah ya tsare ma ni kai ya kare ma ni kai, Allah ya kusanta ka da halal ya nisanta ka da haram, Allah ya haɗa la da alkhairinsa ya nisanta ka da sharri dan albarkacin nabiyyun rahmati." Haka kawai ta ji kaso hamsin na damuwar da yake ciki ya ragu, cikin murya mara amo ya ce . "Na gode." Daga nan ya fice daga gidan tana kallonsa lokaci ɗaya take murmushi kuma take kuka ta ce. "Alhamdulillah ala kulli halin." (A rayuwar aure ko soyayya, akwai abu guda da ya kamata mace ta gane: Ko wani namiji yana da irin nasa hali Kuma yadda yake sonki, haka yake nuna fushinsa idan wani abu ya ɓata masa rai.Ba wai saboda baya sonki ba ne, a’a, saboda ya damu da ke sosai,Don haka ke dai ki fahimci irin namijin da kike tare da shi. Idan mijin kirki ne, zai yi fushi saboda yana son ki gyaru, ba don ya cutar da ke ba. Idan mai saurin ɓacin rai ne, ki gane cewa yana magana ne da zuciyarsa, ba wai yana ƙin ki bane, Idan mai shiru-shiru ne, fushinsa yakan zama nesa da magana, amma zuciyarsa tana cike da damuwa, Idan mai gaskiya da tsauri ne, yana fushi saboda ya san abin da ya dace da abin da bai dace ba. Idan mai tausayi ne, fushinsa zai zo da nutsuwa, amma zai so ki gane kuskurenki ba tare da ya takura miki ba, a kowane hali, rarrashi na mace shi ne sirrin da ake so. mace ta sani, Ki saurari damuwarsa ba tare da tsawatarwa ba, Ki nuna masa kin gane abin da ya dame shi. Ki yi magana cikin ladabi da natsuwa,Ki yi masa nasiha cikin taushi, ba da jayayya ba,Ki nuna masa kulawa, ko da da kananan abubuwa ne. Na Miji baya buƙatar mace cikakkiya. Yana buƙatar mace mai fahimta.) _Nadra_ Suna cin abinci amma ita kasa cin abincin kirki, zuciyarta fara tas ta ji ma ta ƙoshi, burinta ɗaya ta keɓe da Sidra ta ji me ya faru da ita. Bayan sun kammala breakfast Baba ya kalli Nadra ya ce . "Daughter ina fatan ba matsala ko?" Kai ta sunkuyar tana Murmushin ta ce . "Ba komai Baba." "Ko akwai magana ne mu keɓe kafin ta tafi?" "A'a Baba ba komai." "To ba abinda yake ma ki da bakya so? Kada ku dubi idanunsa." "Ba komai Baba." Sai a lokacin Fahad ya ce . "Baba ni ba za ka tambaye ni ba sai ita?" Dariya Baba ya yi yana cewa. "Ba zan tambaye ka ba, dan wannan baiwar Allah ba za ta ma ka laifin komai ba." Gabaɗaya suka saka dariya ban da Sidra. Baba ya kalli Nadra ta ce . "Daughter zan ba ki gift na aure da na so washegarin auren na ba ki abubuwa suka saka na manta." Kallon Fahad ya yi ya ce . "Ka kai ta wajen Alhaji Murtala mai siyar da mitaoci ta zaɓi duk irin motar da take so ." Gabaɗaya suka saka dariya suna taya ta godiya in ban da Sidra da take yin yaƙe (masomin kuka) Nadra ta rasa mai za ta ce sai hawaye, nan aka hau yi ma ya dariya. Sallama Baba ya yi masu ya wuce yayin da Fahad ya dauki jakar Baban suka fita tare dan yi ma sa rakiya. Daga nan kowa ya watse Mama ta nufi part ɗin Baba dan ta gyara ma sa. Ya rage saura Sidra, Nadra, Farida da Rumaisa. Farida sai kallon banza take yi wa Nadra kafin ta mike ta nufi ɗakinta. Sidra ta nufi ɗakin Mama don can ta bar wayarta sai ta shiga ɗakin dan ta dauki wayar. Ganin haka ya saka Nadra ta bi bayanta. Bayan Sidra ta dauki wayar ne sai ga Nadra ta shigo . Kwallonta Sidra ta yi ta ce . "Lafiya ?" "Lafiya kau Aunty, dama wata tanabya zan ma ki." Taɓe baki Sidra ta yi kafin ta ce. "Ki ajiye tambayoyin ki Sai kin fara amsa ma ni nawa tambayoyin tukuna." Gyara tsayuwar ta ta yi kafin ta ce. "Yanzu Ashe ƙanwa na iya cin amanar Yayarta?" Cikin rashin fahimta ta ce . "Wace kanwa kike magana akai?" Nuna ta da yatsarta ta yi kafin ta ce. "Ke nake nufi maciya amana, yanzu ke da kanki za ki iya cin amanata?" "Aunty Sidra ta ina na ci amanarki?" "Wace ce matar Fahad a yanzu haka?" "Ni ce amma wallahi sunan dai ina matarsa ce kawai." Tsuki Sidra ta yi kafin ta ce. "Ko da a ce ba na nan yadda kika san ina masifar son Fahad ko da kin ga za'a aura ma sa wata ke me tsaya ma ni ne, amma abun takaici ke ce da Kanki kika aure shi. Hawaye ne ya wanke ma ta fuska ta ce . "Wallahi ban san komai ba, ban san abun da ke faruwa ba a ranar auren, ban san cewa kin gudu ba, cewa aka yi kin tafi gyaran jiki, har aka daura aurena da Yaya Fahad ban san da ni aka daura ba, komai ɓoye ma ni aka yi, sai bayan da aka kammala komai dare ya yi ne ake sanar da ni komai. Ba na da wani zaɓi Aunty Sidra, ba zan iya jayayya da hukuncin iyayena ba kin sani, sanin haka ya saka Abba ya aurar da ni ba tare da shawara da ni ba. Kuma ba zaman aure na mata da miji muke yi ba sunan dai an yi auren..." Shiru ta yi sakamakon ganin Fahad ya shigo ɗakin. Nadra ta goge hawayenta ta ƙarasa gaban Fahad ta ce. "Yauwa Yaya Fahad ka sanar da ita komai ka sanar da ita ban ci amanarta ba, ka sanar da ita ba wani abu da ya shiga tsakani na da kai, ai ko hannuna ba ka taɓa rike wa ba ko?" Wani wulaƙantaccen kallo Fahad ya wurga wa Sidra, kafin ya dauke kai ya kalli Nadra ya saki wani mugun murmushi sannan ya ce. "Haba sweet heart meye na damuwa akan abun da bai da mahimmanci? Ki daina ɓata ranki ko don ajiyar babyn da na ba ki." Ya yi maganar yana shafa cikinta ya kashe ma ta idanun ɗaya. Ba ta gama fita daga mamakin Fahad ba sai da ta ji saukar tattausan laɓɓanta akan pink lips ɗinta. Zaro idanu ta yi lokacin da ta ji bakinsa a cikin nata yana ma ta wani irin tsotsa kamar wanda ya samu sweet. Sidra zare idanunta ta yi wanda ta fara ganin Fahad da Nadra bibbiyu yana kissing ɗin Nadra cike da ƙwarewa. Kanta ta dafe da ta ji kamar yana barazanar tarwatse wa, cikin tashin hankali ta dafe bangon ɗakin yayin da wayar da ke hannunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa. *Naman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SANARWA* Wannan ƙirƙireren labari ne, ban rubuta ta ba shi dan wani ko wata ba, idan suka ko hali ya zo ɗaya to a gafarce ni arashi ne mai kashe auren wawa. *SADAUKARWA* wannan shafin sadaukarwa ne ga members na MAKAHO NE FAN GROUP, da kuma MAMAN IHSAN NOVEL GROUP ina matuƙar godiya da ƙauna fa kuma tarin addu'o'i da kuke yi ma ni na gode Sosa Allah ya bar ƙauna much love😘 page3️⃣5️⃣ Sidra zare idanunta ta yi wanda ta fara ganin Fahad da Nadra bibbiyu yana kissing ɗin Nadra cike da ƙwarewa. Kanta ta dafe da ta ji kamar yana barazanar tarwatse wa, cikin tashin hankali ta dafe bangon ɗakin yayin da wayar dake hannunta ya suɓuce ya faɗi ƙasa. Nadra ganin abun take yi kamar a mafarki ta fara ƙoƙarin raba bakinta da nasa amma dai ya riƙo ƙugunta ta manna da jikinsa ya zagaye ƙugun nata da hannu ɗaya ɗayan hannunsa kuma ya tallabo ƙeyarta da shi. Sosai yake kissing ɗin bakinta ya ziira harshensa cikin bakinta yana ma tsotson harshenta a hankali, duk yadda Nadra ta so ƙwatar kanta ta kasa. Fahad kam tsintar kansa ya yi a wani baƙon yanayi, take ya fara jin ƙafafunsa sun daina ɗaukarsa. Daidai lokacin Sidra ta fice daga ɗakin tana tana jin kamar zuciyarta za ta tarwatse. Yana jin ƙarar buga ƙofa alamar ta fita daga ɗakin ne ya saki zare bakinsa daga cikin na Nadra tare da sakin ta. Idanunsa har sun fara canza launi zuwa ja. Hawaye ne ya gani yana bin fuskar Nadra. Bai kula ta ba ya nufi hanyar fita, har ya kai hannu zai bude handle ɗin kofar ta ji ya ce "Idan har na sake jin kin yi wa Yayarki makamancin maganar da kika yi ma ta yanzu sai na ba ki mamaki. Ko da wasa kada ki sake nuna ma ta cewa ba rayuwar aure muke yi kamar kowace mata da miji ba. Akan me za ki faɗa ma ta irin zaman da muke yi ?" Cikin kuka ta ce . "Saboda tana son ka ta damu da auren da muka yi har tana ce Mani maciya amana kuma ba haka ba ne." "To tun da ba haka ba ne meye na damuwa.?" "Ta shiga wani hali saboda aurena da kai tana son ka kai ma kana son ta." "Ba na ɗin ta kuma!" Ya faɗa yana dakawa Nadra tsawa wanda yanda ta firgice. "Kada na sake jin kin ce ina son ta, daga ranar da ta gudu a ranar aurena da ita na cire ta daga cikin rayuwata. Domin Fahad Majidaɗi idan ya bar abu ya bar shi kenan har abada. Ba na dake waiwayarsa, har gaban abada kada ki yi tunanin Fahad Majidaɗi idan har ya bar abu zai dawo ya dauke shi ba. Har gaban abada idan ba bar waje ko wani abu kada ki yi tunanin zai dawo gare shi a karo na biyu, idan har na riga na yi nisa ba na jin kiran kowa, ajina ya wuce da mace za ta bar ni a lokacin da ta ga dama Sannan ta yi tunanin idan ta dawo zan waiwaye ta a karo na biyu. Ga ƴan mata da suke haukar so na kamar za su yi hauka akaina ban kula su ba ita ta samu na kula ta har za ta bar ni a lokacin da ta ga dama Sannan ta dawo na karɓe ta? Ajina ya wuce nan." Cikin kuka da takaici Nadra ta ce . "To shi kenan nima ai ba sona kake yi ba, haka zalika Ni ma ba sonka nake yi ba. Don haka ka sake ni." Wani banzan kallo ya yi ma ta ya ce . "Wannan ne karo na karshe da zan ji kin yi ma ni zancen saki idan ba haka ba zan ba ki mamaki. Idan ba dan darajar mahaifinki da ya ba ni ke ba kuma ba zan iya cewa ba na son jininsa ba, ai ba ki kai macen da zan so ba ballantana har ace na aure ki. Ba ki da wanann ajin." Nisawa ya yi kafin ya ce . Yana gama fadar haka ya fice daga ɗakin ya bar ta cikin takaici da baƙin ciki Zubewa ta yi akan guiwar ta tana fashewa da kuka wanda ta kasa gane wani abu ne ya fi yi ma ta zafi a cikin biyun da ya yi ma ta. Shin wulaƙancin da ya yi wa Ƴarta Sidra ce ya fi ɓata ma ta rai ko kuma cin fuskar da ya yi ma ta ita kanta. Abubuwan nan guda biyu ne suka taru suka cunkushe ma ta a zuciya. Fahad ko da ya bar ɗakin sai ya ga ba kowa a Falon, don Sidra ko da ta fito tana kuka ɗakin da aka sauke ta ne ta shiga. Fahad kam part ɗin sa dake gidan ya nufa. Dan bai ɗebi kayansa dake gidan ba. Wasu ya siya dama ya zuba a can gidan nasa da ya tare da Nadra. Sai dai fa ya tsokano wa kansa abinda yake kwance sakamakon runguma da sumbatar Nadra da ya yi don ya ƙuntata wa Sidra ya jawo wa kansa, domin ciwon mara ne ya turnuƙe shi, sai dai bai yi ma sa yawa ba. Yana shiga part ɗin nasa kiran waya ya yi da wasu manyan gwamnatin ƙasar, bayan sun gama tattaunawa ne ya kakkaɓe gadonsa wanda kullum sai Ruamisa ta gyara ma sa shi kamar yadda ya ba ta umarni. Laptop ɗinsa ya ɗauka da niyyar ya yi wasu aikace-aikace amma ya kasa wani feelings ne yake taso ma sa wanda bai taɓa jin irinsa ba. Ya yi nadamar abun da ya yi wa Nadra domin shi ne ya saka shi cikin wanann halin da yake ciki. Yana zaman zamansa ya janyo wa kansa abun da ya dame shi. Ruwa mai sanyi ya ɗauka ya sha sannan rage kayan jikinsa ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa. Almost 30 minutes yana sakarwa kansa ruwan sanyi ko ya ji sassaucin abun da ke damunsa amma shiru ba wani canji illa ma ƙaruwa da abun yake yi _Nadra_ Bayan ta gama kukan da take yi ne ta mike ta nufi ɗakin da Sidra ta sauka. Da sallama ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga , tsaye ta same ta dai Safa da marwa take yi a cikin ɗakin. Kallo ɗaya za ka yi ma ta kasan ranta a ɓace yake . Wani mugun kallon da ta yi wa Nadra sai da gabanta ya faɗi. Ta dake ta ce "Aunty Sidra don Allah ki saurare ni mintuna biyu don Allah." Jin ba ta ce kina ba ne ya saka ta ce . "Ke kanki shaida ce ban taɓa yi ma ki karya ba ko?" Banza ta yi da ita tana cika da batsewa. "Ki yarda da ni wallahi tallahi da gangan ya yi abin da ya yi, da gaske nake yi ko hannuna bai taɓa rike wa ba, ballantana ya yi wani abu. Yau ne kawai dai ya yi a gabanki don ki ki haushi amma ba gaskiya ba ne ba wani ajiyar da ya yi tun da ba a ruwa zan jiƙa ciki na sha ba. Yau ya fara sumbatar..." Wani bakin ciki ya lulluɓe ta ba za ta iya bari Nadra ta karasa maganar ba, don haka ta dakatar da ita. "Yanzu kin tabbatar bai taɓa taɓa ki ba?" Kai ta jinjina ma ta alamar tabbatar wa, kafin ta ce. "Ina son ki yi ma ni wani alƙawari yar uwata." Kai ta jinjina kafin Sidra ta ce . "Tun da har ba wani abun ta ya shiga tsakanin ki da shi alma ce ta ce wa baya son ki, don da yana son ki da tun ranar da aka kai ki ba zai bar ki ba, amma tun da ya bar ki alama ce ta nuna baya son ki baya bukatar wani abu naki, kin ga da yake yana so na ai da ni ce aka daura auren da ni da wallahi ba zai ƙyale ni haka kawai ba. Don haka ina so na sani shin ke kina son sa ne?" Ta yi maganar cike da fargaba kada Nadra ta kamu da son Fahad. Ɗin ta tabbatar ba macen da za ta ce ba ta son sa. Kai Nadra ta girgiza alamar a'a kafin ta ce . "Ba namijin da na taɓa so kamar Ya Sayyadi." Ɓoyayyar ajiyar zuciya Sidra ta sauke kafin ta ce . "To ki taimake ni kin ga ni ma zan taimake ki." "To Aunty ta ya ya ?" "Za ki taimaka ma ni na samu Fahad ni ma na taimaka ma ki ki samu Ya Sayyadi." Dafa kafaɗar Nadra ta yi kafin ta cigaba da cewa. "Ina son ki shafa kwallin rashin mutunci, ki ci wa Fahad mutunci ki addabi rayuwar sa, kullum tashin hankali na yau daban na gobe daban na Anjima daban har sai ya ji ba zai iya ba ya sake ki, kin ga daga nan zan nemo ma ki masoyinki ki aura." Shiru Nadra ta yi tana tunani kafin ta ce . "Aunty Sidra kin fi kowa sanin halina, ko wanda yake ƙasa da ni ne ba zan iya yi ma sa rashin ballantana wanda yake sama da ni." "Dalla can wawuya ce ke dama, idan ba haka kika ma sa ba ai ba zai sake ki ba, don yana tsoron ya saɓawa iyaye." "To shi yana tsoron ya saɓawa iyaye ya yi ma su biyayya sannan ni na saɓa wa Allah da kuma iyaye? Bayan mijina ne dole n yi ma sa..." "Shut up munafuka dama can sonsa kike yi shi ya sa kika ce ba za ki iya ba?" Kuka take yi tana cewa . "Wallahi ba haka ba ne, amma kar ki manta a islamiyya an karantar da mu cewa babu biyayya ga abun halitta wajan saɓa wa Allah. Allah ya ce mace ta yi wa mijinta biyayya aljannarta tana ƙasan ƙafarsa amma ke kina neman saka ni na saɓawa Allah. Idan dai akwai wata hanyar da zan samu ya sake ni ki kawo ta amma ban da wannan wallahi ba zan iya ko da harararsa ba ballantana..." "Ya ishe ni, munafuka na gano ki to ki sani Fahad nawa ne ni kaɗai kuma zan iya aikata komai akan sa ki rubuta ki ajiye, zan so hakan Aunty Sidra Allah ya daidaita lamura su koma daidai fatan alkhairi." Tsuki take tana kallon rigar jikin Sidra da takalminta kafin ta ce. "Macijiya kwai wacce ba ta ramin kanta sai wani ya gina ta shige ciki. Wato gidana da mijina da kayan sakawa ta da takalmomina duk kin mallake ko, komi da daka siya da sunana sun zama naki ko? Tsabar munafurci ke da ba ki iya tafiya da irin wannan takalmin ba shi ne yanzu kike sakwa don ki ja hankalinsa ko?" "Ba na da wani zaɓi ne saboda su kawai ne a gidan, shi ne ma ya sa na saka. Ki yi hakuri in sha Allah Fahad zai dawo gare ki don na tabbatar yana son ki ɓacin rai ne ya sa yake ma ki haka. _Ma'eesha_ Tun da ta raka makaho bakin kofa ta bashi tea ya ce yana azumi haka ta dawo cikin gidan cikin sanyin jiki. Duk ta shiga damuwa sakamakon halin da ta gan shi a ciki, ta rasa me yake yi ma ta daɗi ne . Me ya sa ta ga yanayinsa ya sauya lokaci guda? Kuma lokacin da ya dawo daga masallaci ba haka ya dawo ba. Canzawarsa dai bayan ta dawo daga waje ne sakamakon kiran da Abdul da ya yi ma ta ta fita waje don ta amsa kiran da ya yi ma ta. To ko dai ya ji maganar da Abdul ke fad'a ne akansa ya da ransa ya ɓaci? To ai kuma yana cikin gida bai kai ya ji zancen su ba, dai dai idan ya bi bayanta zai iya jin komai. Idan har kuma bai bi bayanta ba to tabbas fitar da ta yi daga gidan zuwa kiran da Abdul ya yi ma ta ne ya ɓata ma sa rai. Ta kudirin niyyar koma mene ne za ta bashi haƙuri, don ba ta ji dadin yanayinsa da ya sauya ba. Ita ma kanta ba ta iya cin bread ɗin ba, tea da ta haɗa ma sa bai sha ba sha ba ne ta dauka ta sha sannan ta fara tattare kayan ta gyara ta ka gyara wa ta wanke na wanke wa. Bayan kamar awa ɗaya da fitarsa ne ta ɗauki waya ta lalubo lambar wayarsa ta danna ma sa kira. _Makaho_ Lokacin yana tsaka da ɗinkewa wani takalmi. Bayan ya gama ɗimkewa ya mika masa sai saurayim nan ya ce. "Nawa ne kuɗin naka?" Makaho ya ce. "Naira ɗari ne." Sai da saurayin ya duba ya ga ba kowa a kusa, don ma su siyar da abu da suke wajan ba wanda ya fito, sai ya mikawa Makaho naira goma ƴan biyar guda biyu ya ce. "Ga Naira ɗari nan ƴan hamsin guda biyu ne." Ya karbi Naira goma a matsayin ɗari ya saka aljihu. Waysrsa dake ringing ya ɗauka ya laluba ya danna yadda Ma'eesha ta koya ma sa. Sannan ya kara a kunne tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce . "Kana lafiya?" "Alhamdulillah." Ya amsa yana Murmushin. "Ya ibada?" Ta tambaya tana Murmushi, ya amsa da walwala wanda ta saka ta ji dadin ya sake. Suna cikin fira sai ga mai suyan awara dake tsokanar makaho ta iso. Ganin yana waya ta ce . "Alhamdulillah mun yi waya kenan ko? Shi ne ba ka amshi lambar wayata ka kira ni mun yi fira ba ko?" Take ɗan fara'ar dake fuskar Ma'eesha ta ce . Ta ce to sai Anjima ka Kula da kanka." Daga haka ta katse kiran wayar. _Fahad_ Ganin ba sarki sai Allah kuma zai iya cutuwa ne ya saka shi nema wa kansa mafita. Dole ya kira Nadra ta zo dan ita kadai ce mafita a gare shi. Ita ce maganin matsalar da. Don ba ya jin zai iya cutar da kansa bayan yana da mafita. Tura ma ta text message ya yi ya ce. *Ki zo ki same ni a part ɗina yanzu nan ina jiran ki.* Jin shiru ne ya saka shi kiran wayar ta, sai dai wayar na ta ringing ba ta daga ba. Dan ita Nadra wayar na cikin handbag ɗin ta handbag ɗin na falo ita kuma tana dakin Sidra. Jin ba ta ɗaga ba ne ya kira ƙanwarsa Ruamisa. _Rumaisa_ Tana zaune a ɗakinta suna kallon wani series a laptop ita da Farida, wayarta ta yi ringing a tare da faida suka kalli wayar. Ganin Fahad ya sa Farida ta dauke kai, Ruamisa ta daga tana cewa. "Hello Yaya." "Ki kira mani Nadra ta zo ta same ni a part ɗina." Shiru ta yi kafin ta ce . "Ba na tunanin ta san part ɗin ka fa " "Okay ki rako ta bakin ƙofar ke ki koma ta shiga ciki ina jiranta." Ya yi maganar yana cije lips ɗin sa. Tashi tsaye ta yi sai Farida ta ce. ",ina za ki je?" "Yaya ne ya ce na kira ma sa matarsa ta same shi a part ɗin sa." Taɓe baki ta yi tare da jan tsuki. Rumaisa ta fita daga ɗakin tana zuwa farko ta ga Nadara na fitwua ɗakin Mama. Sanar da ita ta yi sakon Fahad ta yi wanda ba gardama ta bi bayanta suka nufi part ɗin sa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣6️⃣ Rumaisa ta fita daga ɗakin tana zuwa falo ta ga Nadra na fitowa ɗakin Mama. Sanar da ita da ita ta yi saƙon Fahad ta yi wanda ba gardama ta bi bayanta suka nufi part ɗin sa. Daidai lokacin Inna kakar Fahad ta fito daga part ɗin ta. Ganin sun nufi part ɗin Fahad ya da ta ce wa Ruamisa. "Ke kuma ina za ki je ɓangaren?" "Mai bangaren ne yake ciki." "Yaushe ya shigo." "Ya zo sallame Baba ne." "Tofah wani lokacin Shi Umarun zai tafi can ƙasar?" "Ai ya tafi kina barci, ya ce kada a tashe ki ne saboda kina barci wai zai kra wayarki." "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yau ga mugun hali, a gidan Ɗana kuma a ce zai yi tafiya saboda mugun hali irin na uwarku ba ta tayar da ni ba?" Ɓata rai Rumaisa ta yi kafin ta ce. "Ba laifin Mama ba ne, shi fa Baba ne ya ce ba ki son kina barci a dinga tashin ki, kuma fa ba ki so fada kike yi." "To ƴar bantan uba, yanzu da gulma ce ai za ki zo ki tayar da ni." Ta yi maganar tana kallon Nasra ta ce. "Ita kuma wanan baƙar bafullatanan daga ina take?" Kallon Nadra Rumaisa ta yi kafin ya ce . "Matar Ɗan gidanki ce." Washe baki ta yi tana cewa. "Ma sha Allah yaushe ta zo, ina shi Fahad ɗin?" "Yana part ɗin sa ya ce na kira ma sa ita ne?" "To je ku dawo sai mu gaisa kin ji amarya?" Durƙusawa Madra ta yi cikin girmamawa ta gaida Inna, ta amsa ma ta cikin farin ciki da walwala. Part a upstairs part ɗin yake nan suka bi, sai dai Ruamisa ta lura da yadda Nadra take tafiya . Don haka ta ce . "Aunty ya dai" Ta yi tambayar tana kallon ƙafarta, sai ta ɗauka ko salo ne da yanga. Murmushi ta yi tare da cewa. "Matar Yaya wannan tafiyar yangar duk na zuwa wajan Yaya ne?" Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Da suka isa daidai kofar falon ta ce. "Bismillah ki shiga yana ciki." Cikin ɗan tsoro ta ce. "Mu je ki raka ni don Allah." Dariya ta yi kafin ta ce. "Ban gane ba, tsaronsa kike yi ko me, a gidanku ai daga shi sai ke, ni ce nake raka ki?" Ƙoƙarin danne tsoronta ta yi tana ƙirƙiro murmushi ta ce. "Na gode." Jinjina kai Rumaisa ta yi bayan ta mayar ma ta da martanin murmushin da take yi kafin ta ce. "Sai kin fito." Tana fadar haka ta juya ta nufi hanyar barin wajen. Da sallama Nadra ta buɗe ƙofar falon. Ba kowa sai sanyin A.C dake ratsa ko ina a Falon. Wata kofar ta kalla wacce take tunanin nan ne bedroom ɗin sa. Ƙarasawa ta yi baƙin kofar ɗakin ta kai hannu za ta yi knocking ta fasa. Tana nan tsaye ta kasa ƙwaƙwaran motsi kafin ta samu ƙwarin guiwa da za ta iya shiga kasancewar an ce yana son ganinta ne. Duk da haka sai da ta yi sallama kafin ta tura ƙofar ɗakin da sallama a bakinta. "Assalamu alaikum." Yana tsaye ɗaure da towel abƙugunsa. Yana tsaye a gaban dressing mirror ya ɗan sunkuya hannayensa biyu ya dafa dressing mirror ɗin. Shigowa ta yi ta cikin mirror ta kalle shi sau ɗaya ta kau da kanta da sauri. Sakamakon ganinsa daure da towel a ƙugunsa. Kanta ta sunkuyar ta ƙasa ta kasa daga kai ta sake kallonsa a karo na biyu. Shi kuma yana nan yadda yake lips na ƙasa a cije ya lumshe idanunsa yana sauraren zuciyarsa. Baya son ya aikata abun da zuciyarsa ke azalzalarsa amma ba ya da wani zaɓi. Jin shiru ne ya saka ta ɗago kai ta kalli inda yake. Ta jikin mirror suka haɗa idanu wanda ya sakar ma ta da faɗuwar gaba, sakamakon ganin yadda idanunsa suka sauya. Tattoo ɗin da ke gefen ƙirjinsa zuwa damtsen hannunsa ta kalla, sai sai ba ta iya gane me aka rubuta na ba sai sai ta ga zanen butterfly. Shi kuma ganin cikin idanunta ma su ɗaukar hankali ya sake assasa yanayin da yake ciki. A hankali ya juyo idaninsu a cikin na juna, kasa jure kallonsa ta yi ta rintse idanunta. Ba zato ba tsammani ta ji ya ɗaga ta cak kamar wata baby. Ba shiri ta buɗe idanunta saboda abu ne da ba ta yi zato ba, zaro idanun ta ba yi ganin ya nufi gadonsa da ita ya dire ta a tsakiyar gadon. Sai a lokacin idanunta ya sauka akan sunan Sidra da aka rubuta ma sa da zanen Tattoo. Ƙoƙarin tashi daga kan gadon ta fara yi ya yi ma ta rufa da ƙirjinsa take ta sakar ma ta nauyin jikinsa. Bakinsa ya haɗa da nata ya fara ba ta zazzafar kiss cikin ƙwarewa. Mayafin abayar dake kanta ya cire yana shafa lalluasan gashin kanta. Ɗaga ta yi yi ya zuge zip ɗin rigar Abayar dake jikinta. Kasancewar zip ne a gaban rigar daga sama har ƙasa. Kasancewar ba ta saka bra don duk ba size ɗin ta ba ne, ƙaramar singileti ta saka wanda duk da ba bra amma nononta s tsaye suke ƙam . Take ya sake rikicewa ya fincike ƴar singiletin take na shanunta suka bayyana wanda suka sake ruɗa shi sun tsaya ƙam ba su rankwafa ba . Take ya fara tsotson nononta kamar jaririn da ya kwana biyu bai sha nono ba, yana shan ɗaya yana murza ɗaya. Kuka ta sakar ma sa don ta ga abun da ta girmi tunanin ta. Sosai yake sarrafa ta yadda ransa ke so, ita kam sai kuka take yi tana girgiza ma sa kai . Shin kam tuni ya gama rikicewa kanta. Kuka ta sakar ma sa mai sauti lokacin da ta ji ya zare pant ɗin jikinta. Shi kam gabaɗaya yana jin kansa ne a wata duniyar. Sarrafa ta kwai yake yi ya taɓa can ya tsotsi can. Towel ɗin jikinsa ya warware ya wanda hakan ya sa ta ƙara tsorata sosai don tun da take a rayuwar ta ba ta taɓa ganin tsaraicin ɗa namiji ba sai yau. Ganin Fahad ɗinsa a fili. Ba ta sake rikicewa ba sai da ta ji ya kama hannunta ya kai a saman Fahad ɗinsa. Tana jin hannunta da ya ɗora a saman Fahad ɗinsa ta ji ta rike abu kamar itace. Tana kokarin zare hannunta sai ta ji ya rike hannunta a jikin Fahad ɗin sa. Yayin da bakinsa ke cikin nata yana na ta wani irin tsotsa tun daga kar lips nata har harshenta . Yatsarsa ɗaya ya sa a ƙasanta cikin Nadra ɗin ta wanda ya sa ta saki ƴar ƙara. Shi ma jin fatar da ta tare wajen ne hakan ya tabbatar ma sa da cewa. Ita cikakkiyar budurwa ce, haka kawai ya tsinci kansa a cikin shauƙi da annashwa. A hankali ya zare bakinsa ya yo ƙasa da kansa zuwa wuyanta kar zuwa ƙirjinta. Sai wani gurnani yake yi da numfashi. Sun ɗauki lokaci a haka kafin daga baya ta ji wani abu a cikin hannunta da ya rike Fahad ɗinsa na zubar wa. Ɗumin da ta ji ne ya saka ta kalli hannunta wanda sai a lokacin ya saki hannun . Ta kalli hannun da sauri ta ga maniyinsa ne a cikin hannun. Yamutse fuska ta yi cike da ƙyanƙyami ta ce. "Spam ?" Tissue paper ya yago a bedside ya miƙa ma ta. Tura baki ta yi har lokacin tana hawaye. Karɓa ta yi tana goge hannunta da ya zuba ma ta ruwan sparm. Kuka take yi har lokacin wanda ya ɗaga idanunsa ya kalle ta ya ce . "Me na yi ma ki da zafi har kike ma ni kuka" Just wasa dake fa na yi ba komai ba amma kike ta kuka. Ina ga fa sex na yi da ke fa sai dai ki suma. " Ba ta tanka ma sa ba ta cigaba da kukanta. "Ba na son kuka ko wani hayaniya, zafi kawai na rage ba wai na samu yadda nake so ba ne, idan kuma kukan kike so to yanzu nan zan mayar da ke cikakkiyar macen aure sai ki yi kukan mai dalili." Jin haka ya sa ta yi shiru tana haɗiye kukan domin kuwa ɗazu yatsa kawai ya sa a cikin ƙasan ta sai da ta ji zafi ballanta ya saka manta wannan abun da take gani kamar an dasa itace. Towel ɗin jikinsa ya daura ya nufi bathroom. Don tsarkake jikinsa, yayin da ta haɗiye kukan tana tsoron ya aikata ma ta abun da ya faɗa idan ba ta ma sa shiru ba. _Jamil_ Tun da ya je gidan Ma'eesha ya ga yadda take rayuwa cikin wanan akulikin gidan, ga mahaifinta attajirin da je bayar da kyautar gidaje ga wasu, amma ƴarsa ce a wannan rayuwar. Ga shi ya je ya bata kyautar kudi b ta saurare shi ba, laifin Mahaifiyarsa ya shafe shi. Kudin sadakinta kawai makaho ya amsa. Ko da ya koma gidan ya tarar da Daddy a falo, sallama ya yi Daddy ya amsa kafin ya ce . "Na je gidan Ma'eesha." Da sauri Daddy ya kalle shi kafin ya kau da kai ya cigaba da harakar gabansa. Tashi ya yi ya nufi ɗakin Mamy , bayan sun gaisa ya kalli yadda ta koma ta rame . Tabbas ga ta cikin dukiya amma ba ta da walwala da kwanciyar hankali . Ko Ma'eesha da Makaho sun fi ta kwanciyar hankali. "Mamy lafiya kuwa na ga tun da Ma'eesha ta bar gidan nan ba ki da walwala." Harara t watsa ma sa. "Ba na ce ka daina kiran Mani sunan wacce yarinyar a nan ba?" "Na daina Mamy , amma ki sani akwai ranar nadama lokacin da ba zai ma ki amfani ba. Yanzu haka ba ki da kwanciyar hankali, ita Ma'eesha da kike ganin kun ƙuntata ma ta na tabbata ta fi ki kwanciyar. hankali. Kwanciyar hankali shi ne abin da duk mai rai ke nema. Ba kuɗi ne ke samar da shi ba, ba matsayi ko suna ne ke kawo shi ba, ba kuma aiki ko wahala ke hana shi ba, Kwanciyar hankali kyauta ce daga Allah sai ka ga mara lafiya ko talaka, amma zuciyarsa cikin nishaɗi, hankalinsa kwance. Wani mai lafiya da wadata kuma yana jinsa tamkar a kurkuku, saboda tashin hankali da ƙuncin zuciya. Idan Allah ya azurta ka da kwanciyar hankali, to ka sami babbar ni’ima da kuɗi baya iya saya. Kuma ku sani, da ambaton ALLAH ne zuƙata ke samun natsuwa, Kuma nisantar ambaton Allah shi ne ke jawo rayuwa mai ƙunci. Kamar yadda Allah ya faɗa." Mikewa tsaye ya yi kafin ya ce. "Ya Allah Ka azurta mu da kwanciyar hankali, a zuciyarmu, a rayuwarmu, a dangantakarmu da bayinka, da duk inda muka tsinci kanmu. Amin." Yana gama fadar haka ya wuce . Ya tarar da Daddy na hawaye a Falon, sai dai bai ce komai ba ya ficewar da gidan zuciyarsa na ma sa zafi . _Ma'eesha_ Kasancewar ta san yau makaho na azumi bayan ta gama ma sa girkin bude ba ki, sai ta dauki ɗari biyar da ya rage ma ta tana son ta siyo ma sa dabino. Wayarta ta dauka don ta kara shi ta nemi izinin fita sai ta ga ya shigo gidan da sallama. Tashi ta yi ta karbi kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa . Ya amsa cike da jin dadi yana ma ta ya gida. "Alhamdulillah, gida ba daɗi saboda ba ka nan gidan dubu ya mamaye shi, amma yanzu tun da ka dawo haske da abnuri ya mamaye gidan ." Murmushin jin dadi tmya yi kafin ya yi magana ta ce . "Dama zan siyo ma ka dabino ne na dawo " "To mu je na taka ki." "To amma ka ajiye sanda dai na rike ma ka hannu." Haka aka yi ta rike ma sa hannu suka fito daga gidan tana jin gabanta na faɗuwa. Suna tska da tafiya ta ga haske na haska su kasancewar Yamma ce likis. Tana juyawa ta ga wasu maza guda biyu cikin mota suna ɗaukarsu photo. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣7️⃣ Tana juya wa ta ga wasu maza guda biyu cikin mota suna ɗaukar su photo. Cak ta tsaya da tafiyar da take yi ta ɗan zuba ma su idanu. Dai dai ba ta iya shaida ko su waye. Sakamakon fuskarsa sanye da mask sannan kuma sun sanya bakin glass a idanunsu. "Ka ga wasu maza guda biyu ɗaukar mu photo fa suke yi." "Da wani idanun zan kalle su na gane su ?" "Ki rabu da su mu tafi kawai mu je mu dawo?" "Amma kana ganin haka kawai za su dinga daukar mu photo ne, bayan ga mutane nan ba wanda suka ɗauka sai mu?" Madadin ta ta tafi in da za su tafi sai ta nufi motar daidai lokacin da suka ja motar suka bar wajen. Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, amma zuciyarta na cike da tarin tambayoyi. Su waye waɗan nan kuma mene ne dalilin da ya saka suke ɗaukar su photo? Haka ranar da suka fito daga siyan waya aka dauke su photo ita ta shi . Har suka ƙarasa wajan me dabino ta siya na ɗari biyu sai pure wayar mai sanyi ta siye na Naira ɗari. Shi ya karba ya riƙe sannan suka kama hanyar gidan. Suna shiga ana kiran sallar magrib. Tabarma ta shimfida ma sa a barandar kofar ɗakin sannan ta gabatar ma sa da kayan bude baki. Sai da ya wanke baki sannan ya ci dabino da ruwa ya tafi masallaci. Tashi ta yi ta gabatar da sallar magrib ita ma har lokacin hankalinta ya kasa kwanciya da waɗan nan mutane . Sai da aka yi sallar isha'i ya dawo ita ma lokacin ta idar da sallar. Suna zaune a ɗaki ta zuba ma sa abincin a plate, tuwon shinkafa ne da miyar kuɓewa . Sai kunun tsamiya da ta dama ma sa bai sha ba ya tafi masallaci. Sai yanzu ya sha kadan, tuwon na kadan ya ci ya ce ya ƙoshi. Ta lura shi ba mai son cin abinci ba ne, haka ta dinga lallaɓa shi kamar ƙaranin yaro don ya ci tuwon da yawa. Har ta samu ta ɗan kara kuma ta ji dadin hakan sosai. "Sai lallaɓa ni kike yi kamar wani ƙaramin yaro ko?" "Idan ban lallaɓa ka ba wa zan lallaɓa? Allah sarki ina ma zan ga karamin yaron da zan lallɓa?" Ɗan jim ta yi kafin ta kuma cewa. "Ina masifar son yara wallahi, idan na ga jariri hannun uwarsa sai na ƙi dama ni ce da babyn. Ka san Allah ina son na ga ranar da Allah zai azurta mu da babys ranar zan iya barci kuwa?" Ta yi maganar cikin shauƙi sosai Shiru ya yi bai ce komai ba, kafin ya ce. "Ni a gani na a yadda muke cikin wannan halin bai kamata a ce mun tara zuri'a ba." Ya yi maganar ya saka hannu a aljihu don ya ciro kudin da ya samu. Ya san daga haka zai kawar da zancen. "Cinikin yau duka-duka Naira ɗari biyar ne." Ko ɗaya fito kudin ya mikaa ta da hannu biyu ta karɓa. Sai dai tana dubawa ta ga Ɗari biyu ne madadin dari biyar da ya ce. "Dari biyu na gani." Cikin mamaki ya ce. " Ɗari biyu da kika ce?" "Ƙwarai kuwa haka na gani." Shiru ya yi kafin ya ce. "Wai me ya sa cuta ta yi yawa a wannan zamani da muke ciki ne, idan Allah ya ɗora wa mutane lalurar makanta sai hakan ya saka dogaro wajan cutar da shi?" Cikin tausaya wa ta ce . "Ka rabu da shi kansu suka cuta ba kai ba." Nan dai ta cigaba da kwantar ma sa da hankali har ya bar zancen, amma zuciyar sa na mamakin ha'inci na mutane. Kuma duk hakan ya faru ne sakamakon yau da ya fara zuwa kuma da safe ya yi cinikin kafin abokan zamansa su fito. "Allah ya sa ma su albarka." Ta fada tana jingina da bango ta lumshe idanunta. "Na san kuɗaɗen da suke hannunki sun ƙare ko?" “Ɗari biyu ya rage." "To Ma'eesha Allah ya kara rufa ma na asiri." "Ni ina ganin buhun gawayin da na siyo na ajiye a kitchen zan fara ɗaura shi a leda ina siyarwa, zan yi wa maƙota talla su dinga zuwa suna siye." "Gawayi kuma ?" "Eh mana ai ya fi a ce mun zauna haka nan, rayuwa ba za ta tafi ma na a haka ba, idan kayan abincin da muke da su suka ƙare waye zai ba mu ? Mutanen yanzu kansu kadai suka sani, wannan gyaran takalmin naka ba iya ɗaukar mu zai yi ba, amma idan na kulla ya kare sai na dinga siya ina ɗaurawa." "To shi kanan Allah ya taimaka ya yi jagora." "Amin ya rabbil izzati." Ruwan wanka ta kai masa banɗaki ya yi kafin ya shirya ita ma ta shiga ta yi wankan. Ko da ta fito har ya gama shiri . Karfe goma sha daya suka kwanta, ita tana kwance a katifa shi yana kwance a tabarma, kamar yadda ta yi wa kanta alkwari ba za ta sake ce ma sa ya kwanta a katifar ba kuwa ba ta sake ba, shi ma bai damu ba. _Fahad_ Fitowarsa daga wanka kenan yana sanye da bathrobe a jikinsa. Yana goge kansa dake jiƙe da ruwa, ya kalli gadon sai ya ga ta dunƙule ji jikinta wuri guda ta lulluɓe da bargo. Jajayen idanuna ta kalle shi shi ma ita yake kallo kafin ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Tashi ki je ki yi wanka." Banza ta yi masa ba ta motsa daga in da take ba. "Ko na yi ma ki wankan ne?" Nan ma shiru ba ta motsa ba "Okay bari na yi ma ki to." Jin haka ya saka ta kara rufe jikinta da bargon tana cewa. "Ka daina kallo na zan tashi na yi da kaina." Murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce . "Meye kuma ban gani ba yanzu? Ai duk wata kunya ta ƙare." Takaici ya sa ta fara kukan shagwaɓa. Ya bar wajan ya nufi bathroom ɗin. Ba jimawa ya fito sanye da farin towel sabo da ya cire daga ledarsa Miƙa ma ta ya yi sai da ta shigar da shi cikin bargon sannan ta ɗaura ta fito daga cikin bargon. Towel ɗin me girma ne Tana sauka ya cire sanin gadon da bargon da kayan da suka cire duka. Jallabiya ya saka a jikinsa bayan ya shafa turare ya saka boxer . Tana shiga banɗakin tsarkake jikinta ta yi sannan ta yi wanka ta dauki wani towel ta daura . Tana fitowa ya shiga da kayan da ya kwashe kan gadon. A warahing machine ya fara wanke kayansa da na ta sannan ya zuba sannan ya zuba su zanin gadon. Bayan ta tashe ruwan kanta ta duba ba ta ga kayan da ya cire ba. Ba abayarta ba mayafin. Tsaye ta yi tana jiran fitowarsa. Yana fitowa ta ce " kayana fa ban gan su ba." Share ta ya yi kamar bai ji ta ba ya nufi hanyar fita. Da ido ta bi shi tana tura baki. Downstairs ya sauka in da ya tarar da kowa a falon, Mama, Inna, Rumaisa, Farida, sai kuma Sidra. Ƙamshinsa ya bayyanar ma su da isowar sa wajen . Inna da ta gama jin labarin da Mama ta ba ta na Sidra da Baba ya ce ta zauna sai ya dawo. Fahad ya kalli Rumaisa ta ce . "Ɗauko ma ni kayanki kala ɗaya ki kawo ma ni." Gabaɗaya suka kalle shi cikin rashin fahimta musamman Ruamisa ta ce . "Ban gane ba." "Da wani Yaren na yi na ki magana, ki ɗauko kayanki cikin dogayen rigunan da na siyo ma ki a kasar Egypt last two weeks ." "Okay." Ta fada tana nufar ɗakinta. Inna ta kalli Fahad ta ce. "Me za ka yi da kayan saka wa na mata kuma?" "Nadra za ta saka?" Kalmar da ya daki zuciyar Sidra kenan ta kalle shi ba shiri. Inna ta ce . "Me ya samu kayan da ta zo da shi?" Share ta ya yi kamar bai ji me take cewa ba. Jin ya yi banza da ita ne ta fara ma sa masifa wai ya kawo amarya don ta gaishe su amma bai bari ta gaishe su ba ta ƙunshe ta a ɗaki. Ta in da take shiga ba ta nan take fita ba. Har Rumaisa ta ta kawo ma sa kayan ya karba ya haura sama. Hankalin Sidra ya kasa kwanciya gabaɗaya ta rasa sukuni tana addu'a Allah ya sa ba abun da take tunani ba ne. Yana shiga ya mika ma ta kayan riga ce doguwa tana da tsaga gefe da gefe da wando dogo dai mayafin madaidaici. Banɗaki ta shige don ta sauya kayan, ya taɓe baki ya bar ɗakin. Waya ya amsa yana magana yana kallon T.V dake aiki. A cikin wayar yana magana ne kan tafiyar da zai yi America zuwa gobe. Bayan ya katse kiran wayar ne ya shiga bedroom ya same ta ta gama shiri, kayan sun karbe ta sosai sun yi ma ta kyau har ya kasa ɗauke idanunsa akan ta. Don dama kayan sun burge shi ne ya siya wa Rumaisa ita kuma ita kuma Sidra ya san ba ta san kaya ma su rufe jiki ne bai siyo ma ta ba. "Mu je ki gaida Kakata tana can tana tambayar ki." Ya yi gaba ta bi bayansa tana tafiya a hankali. Takun takalmin Nadra ya jawo hankalin mutanen Falon, suka ga kayan da Fahad ya karba ne a jikinta. Sai a lokacin kunya ya kama ta sakamakon kayan jikinta. Don kobdabya kawo ma ta kayan ba ta san daga ina ba ne amma ta san kowa dake Falon nan ya san cewa ba kayan da ta zo da shi ba kenan, yanzu sun san abinda suka aikata kenan. Wani kunya ya lulluɓe ta kamar t ƙasa ta tsage ta shiga. Jin ta tsaya cak ya saka ya ce . "Lafiya ?" "Yanzu idan suka kalle ni da wanann kayan ba wanda na zo da shi ba za su gane abun sa muka aikata ko?" Sai da ya danne dariyarsa sannan ya ce . "Eh sun san komai da na zo karɓar kaya sun tambaye ni na ce ke ce kika ce na ba ki hakkin ki na aure." "Hawaye ya wanke fuskarta ta juya da sauri za ta koma sama. Cak ya dauko ta yaba saukowa downstairs. Duk yadda ta so sauka haka bai ba ta wannan damar ba. Sai da ya sauko ya dire ta a ɗaya daga cikin kujerun Falon. Ganin za ta mike ne ya saka ya yi saurin zaunar da ita yana murmushi. Mama ta ce . "Lafiya ?" Fahad ya ce . "Wai ba za ta zo ta zauna tare da ku ba sai dai ta tsaya da mijinta." Kunya ya sake rufe ta ya fice daga gidan yana dariya. "Kar ka damu Daughter na san halinsa tsokanarki yake yi na sani." Ta yi maganar tana nuna wa Nadra kusa da ita , kamar tana jira ta mike ta koma jikin Mama ta kwantar da kanta kan cinyar Mama kamar yadda Umma ke yi ma ta idan sun yi faɗa da Sidra. Fahad ne ya dawo ya kalli Mama ya ce. "Gobe in sha Allah zan tafi America." Mama ta ce. "To ita kuma Nadra fa tare da ita za ka tafi? "Idan za ta bi ni sai mu tafi tare da ita." Sidra ta girgiza ma ta kai alamar ta ce a'a. Cikin sa'a kuka ta yi saurin cewa "Ba zan bi shi ba zan zauna a nan gidan kafin ya dawo ko kuma ba koma wajen su Umma." Mama ta ce "A'a Daughter ba za ku je wajen Umma ba sai dai ki zauna nan kafin ya dawo sai ki koma gidanku." Shi dai bai ce komai ba ya bar falon. Bai dawo ba sai bayan magrib ya shigo da set na akwati. Kaya ne ya siyo wa Nadra wadanda ya fahimci za ta iya saka wa. Akasarin su dogayen rigunan Abaya ne da hijabai yadda ya san tana son kaya, sai flat shoes da handbag ɗin da underwears wanda ya san za su yi daidai size ɗin ta. Part ɗin sa ya kai kayan bayan ya nuna wa Mama da Inna kayan kafin ya kai part ɗin sa. Inna ta fara fadar cewa tsabar almubazzaranci ga kayan lefe ne zai je ya kifi wasu kayan. Bai kula ta ba ya fita don yin sallar magrib. Text message ya tura wa Nadra ganin ta tare a dakin mama. *Ƙarfe goma na dare na yi ki yi ma su sallama ki koma part ɗina tare za mu kwana kafin gobe idan na tafi za ki iya kwana a dakin da kika ga dama.* Tana kwance a gadon Mama bayan ta yi sallar isha'i ne ta ga message ɗin nasa. Tura baki ta yi tana cewa. "Ni ba ƴar iska ba ce da zan je kwana dakinka bayan abun da ka yi ma ni da safe." Kamar ya san me take cewa sai ga wani message. *Idan ba ki zo ba zan biyo ki ne ko a gaban Mama ne ba ruwana da kunya.* Bayan ta karanta tana hawaye ta ce. "Na shiga uku. Wallahi zai aikata bai da kunya." Yana gama tura ma ta messages ɗin. Ya siye gasashshen kaza ya siye fresh milk ya bar wajen. _Makaho_ Yana dawowa daga wajan da yake gyaran takalmin daidai kan kwanar da zai sada shi da hanyar unguwarsu wata baƙar motar ta tsaya a gabansa. Wasu maza masu ƙirar samudawa ne suka fito su biyu, suka ɗauke shi suka saka shi a bayan motar bayan sun toshe ma sa baki da hannu kafin ya yi wani yunkuri, a guje motar ta bar layin . Wata mota dake can gefe ta mara ma su baya a guje. *Maman Ihsan ce* 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣8️⃣ Wasu maza ma su ƙirar samudawa suka fito su biyu. Suka ɗauke shi suka saka shi a bayan motar bayan sun toshe ma sa baki da hannu kafin ya yi wani yunkuri, a guje motar ta ta bar layin. Wata mota dake can gefe ta mara ma su baya a guje. Motar da ta fahimci ana binta ne sai Direban ya ce wa mutanen nan guda biyu da suke rike da Makaho cewa. "Wancan me motar na fahimci bin mu yake yi fa?" Ɗaya daga cikin mutane biyun ya ce. "Ka san yadda za ka yi ka ɓace wa ganinsa." Ya yi maganar yana shaƙawa Khalifa hankaci a hancinsa. Wan da ya ya sa Khalifa ya a yi luu ya zube a kan kujerar." Sai suka sake shi suna kallon motar da aka ce yana bin su. Daidai lokacin ne kuma wayar ɗaya daga cikinsu ya yi ringing. Suna dubawa suka ga uban gidansu ne yake kiran wayar. Amsawa ya yi yana cewa . "Sai oga, aiki ya kammala muna hanya, sai dai mun fahimci wata baƙar mota tana nan tana bin mu, tun da muka dauke shi take bin mu ina kyautata zaton sun ga lokacin da muke dauke shi ne suka bi mu?" Daga can ɓangaren ya ce . "What's? Ta ya za ku yi sakaci haka bayan na faɗa ma ku yadda za ku gudanar da komai, to bari ku ji ku tabbatar kun tsere ma su domin idan har kuka yi sakaci aka kama ku to har da kanku kuka yi wa don ba zan taɓa bari miliyoyin da aka biyani akan aikin makahon nan ya tafi a kansa ba na rasa su." Cikin tabbatarwa ya ce . "Kafa ka damu boss ba mu taba ma ka matsala ba kuma ba za mu fara kan wannan ba." Ogan na jin haka sai ya ce. "Good job." Ya katse kiran wayar. Gudu suke ya kamar za su tashi dama don sun kama hanyar barin unguwannin da ke da mutane. Yayin da su ma motar da take bayansu dai ƙara gudu suke yi don su ga sun tarar da su. Su biyu ne a cikin motar wanda yake zaune mazaunin direba sai kuma ɗayan yana zaune gefen wajen me zaman banza. Wanda ke zaune gefen wajen me zaman banza ya kira wata lamba, sannan ya kara a kunnensa. Bayan an ɗaga ne ya ce . "Hello sir" Ta cikin wayar ya ji an ce . "Hello ya ake ciki ne ina fatan ba wata matsala ko?" "Akwai matsala yallaɓai." Ɗan jim ya yi kafin ta ce . "Meke faruwa?" "Wallahi wasu ne suka ɗauke shi suka saka shi a motarsu suka bar wajen a guje." Tsawa ya daka ma su yana cewa . "Meye amfanin ku da har za ku yi sakaci da wasu za su samu damar ɗauke shi ba ku dakatar da su ba?" "Wato abu ne da ba mu yi zato ba, ya dawo daga inda ya saba zuwa ya dauki hanyar gidan da yake zaune kenan sai suka ritsa shi suka tura shi a cikin motar da karfi wanda Kafin mu yi wani yunƙuri tuni sun bar wajen. Amma muna biye da su in sha Allah dai mun cin ma su" "Ita yarinyar da kuka kuna ganinsu tare da ita fa?" "Ita tana gida shi kaɗai ne suka kama." "Okay me ya alaƙarsa da yarinyar ne?" "Abun da har yanzu ba mu tabbatar ba kenan, amma bayan kuɓutar da shi za mu iya gano dangantakar da ke tsakaninsu da ita ." Yana fadar haka sai ya ji an katse kiran wayar. Daidai lokacin ne kuma suka nemi motar gabansu suka rasa. Sakamakon sun zo mararraba ce, hanayar ta rabu hudu suka rasa in za su bi , dan ba su san in da za su bi ba, mikewa ne ko kuma damar su za su bi ki hagu. Gabaɗaya sun rasa in da za su tafi, ga shi mota daya suka fito da ita ballantana ace su rabu wani zai iya hangen su. Sai dai kawai suka mike ba tare da sanin Ina motar gabansu ta yi ba _Ma'eesha_ Ganin har na kira sallar magrib makaho bai dawo ba ne hankalin ta ya fara tashi. Domin ta san baya taɓa kai wa magrib bai shigo ba. Don haka sai ta kira wayarsa. Tana jin yans riginging amma ba'a ɗaga ba. Sai ta dake kira a karo na biyu ta ji wata baƙuwar murya da ba ta taɓa jin sa baya ɗaga kiran wayar yana ka ta sallama. Gaban ta ne ya yi mummunan faduwa amma sai ta dake ta amsa sallamar. "Wa'alaika Salam, ina mai wayar." Hajiya tafiya nake yi akan hanya na ji ƙarar wayar, ko da na duba sau na ga kina kira,kafin na daga ta katse sai yanzu da kika sake kira." Cikin tashin hankali ta ce. "Ba ka ga wani makaho a wajan wayar ba?" "Ba kowa sai kayan gyaran takalmin da suke watse a Wajen." Hawaye ne ya wanke ma ta duka ta ce . "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un. Bawan Allah kana ina ne yanzu?" Ya yi ma ta kwantancen farkon layin ta ce. Ita matar me wayar da kayan gyaran takalmin ne ga ta nan fitowa . Katse wayar ta yi ta daki hijabi ta saka sannan tana fita gudan sauri -sauri gudu-gudu. Har ya karasa wajan. Tun daga nesa ta hango mutane za su kai biyar a waje ɗaya, ga kayan gyaran takalmin Khalifa nan na a waje ɗaya. Tana ƙarasowa ta ce "Don Allah ina kuka ga ya bi da ya zubar da kayansa a nan." Ta yi tambayar tana kallonsu, wanda ya ba ta wayar ne yake cewa. "Ga wayar da kayan ki tafi gida zai dawo." Ta karaɓa tana kallonsa kamar wata sokuwa." Ɗaya daga cikinsu ne ya ce. "Kada ka ɓoye ma ta komai matasa ce fa. Hajiya ki yi addu'a Allah ya bayyanar ma ki mijinki, domin wasu ne suka zo da mota suka saka sa ciki da karfin tafiya Kanta ta dafe tana cewa. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, ina suka kai shi?" "Allah masani sai dai duk yadda aka yi wadannan mutanen criminals ne dan ba su yi kama da jami'ai ba." Goge hawayenta ta yi ta ce. "Na gode Allah ya saka ma ku da alkhairi." Tana gama fadar haka ta nufi gida rike da kayan aikinsa da wayarsa a hannunta. Tana zuwa gidan ta ajiye kayan aikinsa ta fito dan zuwa police station ta kai report. Duk da ta san ba ta da kudin da zai kai ta ya dawo da ita, ɗari biyun da makaho ya ba ta ne wadanda aka cuce shi aka ba shi a matsayin ɗari biyar. Jin kiran sallar isha'i ya sa ta dakata sai da ta gabatar da sallar isha'i kafin ta wuce bayan ta yi ma sa addu'o'i. Sannan ta rufe gidan ta kama hanyar zuwa Ofishin ƴan sandan. Sai da ta kai bakin titi sannan ta tsaya. Mai keke nape ta tare da sanar da shi ya ƙai ta police station ya sanar da ita kudin ta ɗari uku za ta biya, amma sai ta roke shi ya taimaka ɗari biyu take da shi. Ya ha kekensa ya tafi wai shi ba zai iya zuwa a dari biyu ba. Haka ta dinga tare ma su keke kusan su uku ba su dauke ta a ɗari biyu ba. Hawaye ne ya dinga ambaliya a saman fuskarta kamar an bude famfo. Bayan hannunta ta sa tana goge hawayenta kafin wani tunani ya fado ma ta a rai. "A.S.P." ASP Nasir Yusuf Wani tsohon saurayinta ne wanda ya taba nuna yana son ta a baya ita kuma ta nuna ba ta son sa. Saboda nacin son da yake yi ma ta ne har ta yi blocking nasa a waya, sakamakon yawan kira da messages. A gidan ma ta ce wa Maigadi idan ya zo ya ce ta bar ƙasar. Da haka ya hakura da ya fahimci ba ta son sa. Tana tsaka da tunanin sai wani mai nape ya tsaya yana cewa. "Hajiya tafiya ne?" Ta sanar da shi police station da zai kai ta ta kuka roke shi ya kai ta dari biyu take da shi. Ganin tana cikin tashin hankali ya sa ya kai ta a haka nan. Bayan ya sauke ta ne sai ta ba shi kudin ta ciri wayar ta ta yi unblock ɗin A.S.P Sannan ma sa kira ta yin sai ta ji ringing ɗin wayar a bayanta. Ta waiga ta gan shi sanye da kakinsa na aiki yana kokarin shiga motarsa. Wayar ya ciro ya duba yana kallon sunan da mamaki, a hankali ya furta. "Ma'eesha." Katse kiran ta yi ta karasa wajensa daidai lokacin da yake kokarin bin kiran nata. _Fahad_ Bayan ya siye kaza da fresh milk park ya nufa in da suka saba zama su shaƙata su da abokansa. Suna zaune su biyu Sadik da mukhatar suna ganin motarsa suka taso suka ƙarasa wajan , kasancewar ya sanar da su ba zai zauna ba. Sadik ya shiga gaban motar yayin da Mukhatar ya shiga baya. "Ya aka yi ne Ɗab America har an gama cin amarcin ne?" Cewar Sadik yana kallon Fahad. Mukhtar dake baya ya ce . "Wai kamshin me nake ji ne a cikin motar nan, har da tsaraba ka kawo ma na ne?" Ya yi maganar yana kallon kazar. "Ba sai ka ci ba tunda da kudinka na siya." Mukhtar ya yi dariya yana cewa . "Wai amarya ana siyo wa wannan kazar? Shegen sama ashe za ka sauko da wuri haka? Ai da cewa ka yi ba ka so har kana fushi da mutane shi ya sa yanzu na ga an..." "Ya isa haka nan Mallamai, ba ruwanku, sallama na zo mu yi ba na da lokacin ɓatawa." "Da Nadra za ka tafi ne?" Cewar Sadik yana kallon fuskar Fahad." "Why not ka je da ita ? Amma ka ce bayan kun yi aure can za ka zauna da matarka." "Eh lokacin Ban san ita ba ce a lokacin Sidra ce zan aura kuma ita ta ce can za ta zauna ita da Nigeria sai ta zo ziyara. Ita kuma wannan da yake akwai duhun kai a tattare da ita cewa ta yi ba za ta je ba." Nam suka ɗan taɓa fira Kafin suka yi sallama da juna suka fito ya bar wajen su ma kowa ya shiga motarsa suka bar wajen kowa ya kama hanyar gidansa. _Nadra_ Tana zaune a dinning table suna cin abinci ita da iyalan gidan. Duk wani motsi nata akan idanun Sidra take yin sa. Musamman ganin irin wayar da Nadra ke amfani da shi ya tashi. Musamman da ta ga lokaci lokaci tana duba wayarta. Ita kuma Nadra sakon Fahad ne ke sake ba ta mamaki. Bayan sun kammala cin abinci lokacin karfe tara ne sai Sidra ta ja hannun Nadra suka shiga ɗakinta. Suna shiga ta tura ƙofar tana cewa. "Ƙanwata wayarki sabuwa ce ko?" Tana Murmushi take maganar yadda za ta bugu cikin Nadra ta faɗa ma ta. "Eh sabuwa ce Yaya Fahad ya siya ma ni ita." Sai da ta ji wani abu ya soki ƙrjinta kafin da daidaita kanta ta ce. "Na ki ya ɓace ne?" "A'a shi ya karba ya siyo ma ni wannan ." "Okay amma dai ya kamata a ce kina kiran masoyinki a waya Ya Sayyadi kuna gaisawa, saboda ya san da cewa kuma jiransa shi ma ya jira ki." Zaro idanunta waje ta yi ta ce. "Rufa ma ni asiri ranar da Ya Sayyadi ya kira ni a waya sai da Yaya Fahad ya masa gargaɗi mai haɗe da barazana na tabbata ba zai sake waiwaya ta ba. Amma kin ga da zaran Yaya Fahad ya sake ni shi kenan sai ja je na sanar da shi, amma yanzu ba daidai bane na kira shi." Harararta ta yi a fakaice ta ce. "Okay to yaushe zai sake ki?" "Ya ce kada na sake yi ma sa zandan saki, idan lokacin ya yi da kansa zai sake ni. Wai idan na sake maganar sai ya ba ni mamaki." "Ba ana ba ki shawara ba ki dauka ba, kina masa sanyi da yawa dole ya raina ki. Muga wayarki." Ta shiga wajen kira ta ga ba su taba magana da Fahad a waya ba kamarsa ma ba ta yi servin ba, sai dai ya kira ta yau ba ta ɗaga ba. Sai ta shiga wajen message ta ga messages da ya tura wa Nadra. Nan ne hankalin Sidra ya tashi sosai. "Kina nufi ɗakinsa ya ce ki ki kwana tare da shi?" "Eh Ni ma haka na message ɗin ." "Kuma ba ki taɓa kwana daki daya da shi ba ko?" Kai Nadra ta daga ma ta kafin ta ce. "Ɗazu da ya karbi kayan Rumaisa ya kai ma ki ne ya yi ma ki?" Shiru ta yi kafin ta ce . "Ba abinda ya yi Mani?" "To shine zai zo karɓar ma ki kayan? Sannan kika dinga noƙewa kuna jin kunya sai da ya dauke ki?" Ta yi maganar kamar za ta dake ta, kafin ta kwantar da murya tana cewa . "Kin ga Fahad ba son ki yake yi ba, wayau zai ma ki ya cuce ki ya kwashe albarkatun jikinki sai ya mayar da ke fanko ya wulakanta ki ya ce ki je ki auri ya Sayyadi. To shi Sayyadin wawa ne?" Shiru dai ta yi ba ta ce komai ba. "Yanzu ki tashi ki je ɗakin Mamansa ki kwanta ki yi barci a dakin, kuma ki kashe wayarki." Sallama ta yi ma ta ta fito don zuwa dakin Mama. A hanya ta kashe wayarta sannan ta shiga ɗakin da sallama. Turus ta yi ganinsa tsaye a ɗakin yana magana da Mama yayin da ita kuma take yanke Fruits. Hanyar fita ta nufa Mama ta ce ma sa. "Ba za ka sha Fruits din ba ne?" Kallon Nadra ya yi kafin ya ce . "Mama ki ba Nadra ta kawo mani, idan zan kamata zan sha. Good night." "Okay to Allah ya tashe mu lafiya." *Wata kila na kara ma ku page ɗaya zuwa dare, idan ban samu dama ba to sai dai na ce mu hadu bayan sallah idan Allah yasa muna cikin ma su yawancin rai, don ba na posting cikin azumi fatan alkhairi*🤗 *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page3️⃣9️⃣ Ba za ka sha Fruits ɗin ba ne?" Kallon Nadra ya yi kafin ya ce. "Mama ki ba Nadra ta kawo Mani idan zan kwanta zan sha. Good night." "Okay Allah ya tashe mu lafiya?" Mama na gama fadar haka ya fice daga cikin ɗakin. Kallon Nadra mama ta yi kafin ta ce. "Daughter lafiya kuwa?" Ƙokarin ƙaƙaro murmushi take yi kafin ta ce. "Ba komai Mama." Kallon ta take yi tare da nazartar yanayin ta kafin ta ce . "Na ga ba walwala a tare da ke ne, idan akwai wata matsala ki faɗa ma mahaifiyarsa ce ni, ina da ikon da zan saka shi ya canza." "Ba komai Mama." Ta yi maganar tana zama ƙasa saman carpet. Mama ta kalle ta ta ce. "Bari na gama yankaa ku fruits ɗin sai ki wuce ma ku da shi." Shiru ta yi gabanta na faɗuwa kafin ta ce. "Mama zan kwana a ɗakinki?" "Ɗakina kuma Nadra?" Kai ta ɗaga alamar eh tana wasa da yatsun hannunta. "Kar ki damu in dai kwana a ɗakin nan ne sai ya ishe ki. Amma ba yau ba sai gobe idan mijinki ta tafi America. Na so a ce tare kuka tafi amma kika ce ba za ki je ba, duk da cewar akwai rashin sabo da rashin shaƙuwa a tsakanin ke da shi sakamakon yadda auren ya zo ba yadda muka yi tsammanin sa ba. Amma duk da hakan ki saki jiki da mijinki a haka za ku shaƙu da juna ku saba, idan da wani abu da yake yi ma ki wanda bai dace ba ko ba ki so to kada ki ɓoye ma ni komai, ko yana hantarar ki ko wani abu da bai dace yana yi ma ki ba a tsakanin ki na matarsa to ki sanar da ni in sha Allah zan yi wa tufkar hanci. Nisawa ta yi kafin ta ce. "Rayuwar aure dai da mutunta juna, Idan aka rasa mutunta juna a cikin kowace irin alaƙa, alaƙar soyayya ce ko abota, hatta alaƙar zumunta, za ta mutu ne. ta koma tamkar gangan jiki bayan an zare rai. Koda a zahiri ana tare, amma kowa zuciyarsa ta ware." Sosai Mama ta yi ma ta nasiha da bada shawarwari kafin ta ce. "Tashi ki tafi wajen mijinki sai da safe." Jinjina kai ta yi cikin sanyin jiki ta mike ta karbi bowl ɗin fruit ɗin ta fita tana yi wa Mama sai da safe. Murmushi Mama ta yi cike da ƙaunar Nadra ta ce. "Allah ya tashe mu lafiya." Da haka ta fita daga dakin zuciyarta cike da fargaba da kullum abun da zai iya biyo wa baya. A hankali take tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a cikin ciki haka take tafiya. Matattakalar ma a hankali take taka step ɗin har ta isa ƙofar shiga falo. Nan ta tsaya cak ta kasa taɓa ƙofar tana rike da bowl ɗin fruits ɗin a hannun ta Har tsawon mintuna biyar kenan take tsaye wanda a karshe ta san ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta shiga ko don Fruits ɗin da Mama ta ba ta don ta kai ma sa. Knocking ɗin ƙofar t fara yi amma sai ta ji shiru tsawon lokaci bai ba ta izinin shiga ba. Fahad kam yana zaune yana aiki a system ɗin sa. Kum yana jin tana knocking amma y share ta. Ɗin shi a ganinsa ya kamata a ce ta shigo kai tsaye ne ba sai ta jira ya ba ta izinin ba. Sai da ta gaji ne ta yi sallama tana tura ƙofar ɗakin. Ganinsa zaune da ta yi jan kujera yana danna system ɗin sa ya ba ta mamaki. Wato yana zaune kum yana ganin ita ce amma ya share ta. Tura ƙaranin bakinta gaba ta yi daidai lokacin da ya ɗago kai ya kalle ta. Rufe system ɗin ya yi tare da kallonta wanda ita ma ya yi daidai da lokacin da ta kalle shi. Tashi ya tsaye ya yi daidai lokacin da ta ajiye bowl ɗin kan Centre table dake gabansa. "Ina wuni lafiya." Ta gaishe shi tana mai ɗan durƙusawa. Bai amsa ba kamar kullun da idan ta gaishe shi dama baya amsawa. Ledojin da ya shigo da su ne ya ɗauko ya ajiye saman Centre carpet Zama ya yi yana mai ce ma ta. "Kawo mun Fruits ɗin nan." Ta dauki bowl ɗin ta karasa gabansa ta ajiye. "Zauna." Ya umarce ta yana ciro kaza ɗaya daga cikin ledar. Nan ya baje ma su ita yana mai furta. "Bismillah." Gabanta ne ta ji ya fadi sai sai ya dinga nanata kalmar innalillahi wa'inna ilahir raji'un a zuciyarta. Ganin ba ya da niyyar saka sannu ya saka ya yago cinyar kazar yana nufar bakinta da shi. Girgiza kai ta yi tana kallon ƙasa. "Kada ki yi ma ni gardama akan komai a wannan daren kin ji." Ɗago kai ta yi tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba. "Ina son ki kasance mai biyayya a gare ni matukar dai ban saɓon Allah na umarce ki da ki aikata ba, don haka duk yadda na so ko na yi da ke ki kasance mai biyayya a gare ni kamar yadda na san an yi ma ki nasiha akan biyayya ga umarnin miji ko? Kai ta jinjina ba tare da ta yi magana ba, cikin sanyin jiki ta jinjina kai. Sake ba ta kazar ya yi ta kasa ci sai sai ta saka hannu ta karba sannan ta ci , tun da ta ci cinya ɗaya ba ta ƙara ci ba ta ce ta ƙoshi. Fresh milk ya zuba a cup ya ba ta ta karɓa ta shanye. Shi ma bai wani ci ba ya tattara kayan ya nufi kitchen dake cikin part ɗin nasa. Bayan ya dawo ne ta ji ya kama hannunta ya miƙar da ita tsaye, ƙokarin zame hannunta take yi amma ta kasa. "Mu je mu yi wanka ko?" Gabanta ya faɗi wanda sai da ta kalle shi ba shiri. "Na yi wanka." "Eh mu sake yi." Ƙwalla ya cika idanunta ta kalle shi ta ce. "Ni fa zan iya yin wanka tare da kai ba." "Okay ki je ki fara yi ." Ya yi maganar yana jan hannunta har zuwa cikin bathroom. Da kansa ya hada ma ta ruwan wank sannan ya fito ya janyo ma ta kofar. Set ɗin akwatin kayanta da ya siyo ma ta ya buɗe. Sanin halinta ba ta sun saka kananan kaya ya sa ya fito mata da riga da wando sai dogon Hijabi da za ta yi sallah. Bayan ta gama ne sai ga ta ta fito ɗaure da babban towel da da kuma wani ta lulluɓe da wani towel ɗin. Tsaya wa ta yi ta kasa ƙarasawa tsakiyar ɗakin. Kallon ta ya yi tare da kau da kansa gefe ɗaya kafin ya ce. "Kin ɗauro alwala?" "Eh." Ta bashi amsa a taƙaice. "Okay ki shirya ga kayan barci nan na fito ma ki da shi." Ya fadi haka yana nufar ƙofar bathroom ɗin ya shiga. Kamar tana jiran ya shiga bathroom don haka cikin sauri ta shirya cikin kayan barcin da ya ajiye ma ta, don dogon wando ne har ƙasa, duk da dai bai fito ma ta da underwears ba amma gudun ya fito ya same ta haka nan ta saka kayan da sauri. Dogon Hijabin da ya ajiye ma ta shi ta ɗauka ta saka. _Ma'eesha_ Tana ƙarasawa gaban A.S.P Nasir Yusuf kiran wayar ta ya shigo wayarsa. Kallon wayarta ya yi kafin ya kalli fuskarta kasancewar akwai hasken fitilu a Wajen. Da mamaki yake kallonta daga sama har ƙasa mamaki bayyane akan fuskarsa. "Ma'eesha?" Ya kira sunan ta da alamar sigar tambaya. Kasa amsa ta yi hawaye na sintiri a idanunta. Wanda hakan ya ɗan tashi hankalinsa ganin yadda take kuka kuma da dukkan alama tana cikin tashin hankali. "What's happening with you?" Kukan ta ci gaba ta yi kafin ta durƙusa a gabansa akan guiwoyinta . Ganin haka ya sa ya kai hannu zai riko ta ya tayar da ita tsaye, sai ta yi saurin janye hannunta tana watsa ma sa wani kallo wanda hakan ya saka ya mike tare da mayar da hannayensa a cikin aljihun wandonsa. "Kin tayar ma ni da hankali matuƙa ganin halin da kike ciki, ko dai an yi garkuwa da ke ne kika kuɓuto kika fara zuwa wajen mu?" "Nasir don Allah ka taimake sa ka ceci rayuwarsa makaho ne shi baya gani, kuma baya da gata idan ba Allah ba." "Kin ga ki kwantar da hankalinki ki yi ma ni bayanin komai yadda zan fahimta. Shin wane makaho daga ina kike kuma su waye suka kama Makahon?" "Mijina ne makahon ban san su waye suka ɗauke shi ba, amma bayan na kira wayarsa sakamakon jin sa shiru da na yi. Sai wani ya dauki wayar yake sanar da ni Inda ya tsinci wayar. To bayan na je wajen ne shi ne ake sanar da ni wata mota ce ta ɗauke shi ta gudu da shi ana zaton criminals ne." A.S.P Nasir Yusuf sagale ya yi yana kallon ta, don tun kalmar farko da ta ce mijinta ne ya saki ƙirjinsa duk da ya san cewa ba wai tana son sa ba ne, amma muna kalmar bai ji daɗinsa ba kamar yadda kowane mai rai da numfashi yake ji idan wacce take so ya ji ta ji aure. Amma sai ya dake bai nuna damuwa ko wani abu ba, hasalima ya ƙaƙaro murmushi yana cewa. "Ma sha Allah, ashe yanzu matar aure ce ke. Yanzu na ji bayanin ki mu shiga ciki ki shigar da report na ɓatar nasa." Yana fadar haka ya nufi hanyar komawa cikin station. Bin bayansa ta yi ta goge hawaye dake idanunta. Bayan sun shiga ne ya sa aka ɗauki report nata, kafin Asp ya ce ta je gida za su yi bincike in sha Allah. Kuka ta saka ma sa tana cewa. "Ta ina zan koma gida bayan ban san halin da mijina yake ciki ba?" Kin ga ki kwantar da hankali in sha Allah za mu yi bincike za mu gano shi. Yanzu dare ya yi ki koma gida in sha Allah a daren nan za mu fara bincike." Sai da ya yi fama da ita sannan ta yarda za ta tafi kan gobe sai ta dawo ta ji halin da ake cik. Amma kafin ta tafi ya nemi ta bayar da photon makaho, ƙaramar wayarta ta bayar bayan ta lalubo ɗaya daga cikin hotunan da take ɗaukarsa wanda bai na san tana yi ba. Don wannan yana zaune ne akan tabarma bayan ya cire bakin glass dake idanunsa ya lumshe idanunsa yana jingine da bango. Bayan sun cire tura photo cikin na'urarsu ce suka ba ta wayar . Tana fitowa waje ta fara tunanin abun yi don, don ko sisi ba ta d shi da za ta hau motsa ya koma gida. Tsawon mintuna biyar tana tsaye cikin rashin sanin madafa ta fara tafiya ta nufi hanyar komawa gida, duk da ta san ba lallai ta iya yin doguwar tafiya a ƙafa ba. Ta yi tafiya kamar na mintuna goma sai ta ji horn ɗin mota a gefenta, sai ta waiga ta ga motar ASP Nasir Yusuf ne ya tsaya. Sai ta karasa wajan motar yayin da yake dauke glass ɗin motar. "Ya na ga kina tafiya a ƙafa ina motarki take?" "Ban zo da ita ba." "Okay idan ba damuwa ki zo ba sauke ki a gida ko?" "A'a ka bar shi kawai na gode." "No kada mu yi haka da ke, ki shigo kin ga dare ya yi ko?" "LBa tare da ta sake wata magana ba ta buɗe gaban motar wajen me zaman banza ta shiga. Ba ta yi magana ba "Wace unguwa kuke?" Ta fada ma sa sa sunan unguwar. Bayan sun kai unguwar kasancewar ASP Nasir bai taɓa shiga cikin unguwar ba ya yi mamaki ganin yanayin unguwar na marasa ƙarfi, wanda bai kamata a ce kamar Ma'eesha Ibrahim Khalil ƴa ɗaya tilo ga attajirin irin Alhaji Ibrahim Khalil ke rayuwa a ciki ba. Wanda ko da a ce Direban ko mai gadinsa ne zai iya ba su lafiyayyan gidan da za su zauna ballantana a ce ƴarsa ce ke rayuwa a unguwar. Daƙyar motar je bin hanayar yayin da mamaki fal a zuciyar ASP Nasir amma ya kasa magana. Sai da suka kai kofar gidan zuwa lokaci n karfe sha ɗaya na dare ne. Bayan ta sanar da shi sun iso ne ta ɗan kalle shi ta ce . "Na gode Yaya Nasir Allah ya saka da alkhairi ya sa ka fi haka." "Ina ne gidan mijin naki?" Da hannu ta nuna ma sa kofar gidan, ya kalli gidan da mamaki ya ce . "Anya ke ce kuwa Ma'eesha da na sani?" "Eh ni ce ɗin dai da ka sani ikon Allah kenan ya fi gaban mamaki. Alhamdulillah ala kulli halin." "To amma me ya...? Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar dakatarwa kafin ta ce. "Don Allah kada ka tambaye ni komai, sai da safe." Ta buɗe murfin motar ta fita ya bi ta da kallo har ta shige cikin gidan. _Nadra_ Tana nan tsaye a har Fahad ya fito daga cikin bathroom ɗin. Ɗaure yake da towel a ƙugunsa sai wani karamin yana tsane ruwan kansa. Kallo ɗaya ta yi masa ya kau da kai da sauri gabanta na tsananta faɗuwa. Closet ɗin sa ya shiga ciki. Tana nan tsaye har ya fito sanye da farar jallabiya sai zuba ƙamshi yake yi. Sallaya ya shimfida ma su sannan ya zuba ma ta rikitatun idanunsa. "Bismillah." "Na yi sallah ni." "Ni ma na yi wanann nafila ce za mu yi." Take gabanta ya tsananta faɗuwa sai yanzu ta fara gane manufarsa. Narai-narai ta fara yi da idanu tana shirin yin kuka. Bai kalli fuskarta ba cikin bayar da umarni ya ce . "Ke nake jira ki zo mu yi sallar." A hankali ta karasa wajen sallayar tana hawaye. Sallah raka'a biyu suka gabatar bayan sun idar ya yi masu addu'a sanan ya rike goshinta ya yi addu'a. *Maman Ihsan ce.* 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page4️⃣0️⃣ Sallah raka'a biyu suka gabatar bayan sun idar ya yi ma su addu'a sannan ya riƙe goshinta ya yi addu'a. Bayan ya gama ya cire hannunsa tare da nazartar yanayin ta. Jikinta har rawa ya fara yi kuma zuciyarta cike da tsoro take a wajan . "Zan tafi ɗakin Mama na kwana a can." "Ko saboda me za ki je can ki kwana?" "Kawai dai zan tafi ne." "Ba ki da hujjar zuwa dakin Mama ki kwana bayan ga ɗakin mijinki nan ya fi cancanta ki kwana. Ita ma Mama da ace Baba na ƙasar part ɗin sa za ta kwana tare da shi." Hawaye ne ya fara zarya a saman fuskarta wanda hakan ya saka ta sunkuyar da kanta ƙasa . "Me na yi ma ki na kuka ne kuma?" Kai ta girgiza alamar a'a kafin ta cigaba da cewa. "Ni dai ba zan kwana tare da kai ba tsoro nake ji." Wani dariya ya yi kafin ya ce. "Tun yanzu har kin fara jin tsoro na, to za ki huta ai ƙasar zan bari gobe in sha Allah. Amma kafin nan sai na more." Kafin ta yi magana ya ɗaga ta cak ya nufi tangamemen gadonsa da ita a hannu. Kuka mai sauti ta sakar ma sa tana cewa . "Yaya Fahad Please kada ka yi ma ni komai ba zan iya ba." "Calm down ba abun da zan yi ma ki kina ji na ko? Ki kwantar da hankalinki. Idan kuma ba haka ba ke ce za ki sha wahala." Da sauri ta goge hawayenta tana cewa. "Za ka bar ni na yi barci ." "Eh amma sai kin nutsu." Jin haka ya sa ta sake ƙudundune jikinta cikin Hijabin dake jikinta. Juyawa ya yi ya nufi closet ɗin sa. Tana nan tana raba idanu ta gan shi ya dawo babu riga a jikinsa sai wando three-quarter fari. Har ta ɗauke idanunta daga kallonsa sai ta yi sairin dawo da idanun ta gefen ƙirjinsa zuwa damtsen hannunsa an yi zanen Tattoo har da sunan Sidra da hoton butterfly. Tsaya wa ta yi tana kallon Tattoo ɗin da sunan Autyn nata. Rage hasken ɗakin ya yi bayan ya haura saman gadon. Janyo ta jikinsa ya yi ya haɗa ta da jikinsa. Sannan ya zare ma ta hijabin dake jikinta ya sake manna ta da jikinsa. Buɗe ba ki ta yi da niyyar yin ihu hakan ya ba shi damar saka bakinsa cikin nata ya fara kissing ɗin ta. Hawaye kawai ke ambaliya a idaninta, tsawon mintuna biyar ya ɗauka yana tsotson bakinta kafin ya zare bakinsa a hankali. Ya mayar da fuskarsa cikin wuyanta yana shinshina, hannunsa ɗaya kuma ya zira cikin rigarsa yana shafa fatar jikinsa. Nan hankalin sa ya kara tashi saboda laushin fatarta. A kiɗime ya raba ta da kayan barci da ke jikinta. Shafar ta yake yi ta ko ina tun daga saman ta har ƙasanta, dukiyar Fulaninta a tsaye ƙyam ƙyam kamar an hura balloons. Hankalinsa ya kara tashi cikin rawar jiki ya kai bakinsa ya fara tsotson dukiyar Fulaninta kamar jaririn da ya kwana biyu bai sha nono ba. Yana tsotson ɗaya yana murza ɗaya . Sarrafa ta yake yi ta ko'ina tun daga samanta har ƙasanta. Lokaci ɗaya ya ƙara gigicewa ya fita hayyacinsa, sai wani gurnani yake yi kamar wani zaki. Duk yadda Nadra ta so kwatar kanta a hannun Fahad kasa wa ta yi, don ganin ba za ta ba shi hadin kai ba ne ya sa ya sakar ma ta nauyin jikinsa. Ta yadda ba za iya iya tashi ba. Kuma har lokacin kuka take yi tana roƙonsa kada ya kasance ta ba ta so amma baya jin ma tana magana . Tsoro da fargabar ta ya kara tsananta ne lokacin da ta ji ya fara karanto addu'ar saduwa da iyali. Duk da cikin duhu ne amma hakan bai hana ta girgiza kai alamar a'a ba. Hawaye duk ya gama wanke ma ta fuska ya jiƙa filon ta take kai. Wani gigitaccen ƙara ta saki na azaba, ture shi ta dinga yi da hannayenta duka biyu iya ƙarfinta amma ta kasa. Wani ƙarar ta sake saki wanda ya fi na farkon saboda lokacin ne ya sake ratsa wa cikin jikinta. Ihun da ta yi na biyu shi ne ya karaɗe ilahirin gidan. Sai dai babu wanda hankalinsa ya kawo wajen sai Sidra. A figice ta mike tsaye daga kwancen da take cikin tashin hankali ta ɗora hannu akai tana cewa. "Shi kenan na shiga uku ni Sidra, me kunne na ya ji yo ma ni ne?" Kamar yanda wacce aka zabura ta mike ta fice daga dakin a guje. _Makaho_ Bayan sun shaƙa ma sa powder da ya sa ya fita hayyacinsa bai sake sanin kansa ko in da suke ba. Don a hankali ya ji kansa na juyewa yana ganin duniyar na juya ma sa . Doguwar tafiya suka yi ba wanda ya yi magana kafin wani ya yi magana ya ce. "Wai su waye suke bin mu a baya ne?" Wanda ke zaune a baya da suka saka makaho tsakiya ne ya yi maganar. Direban ya ce . "Ban san su waye ba, sai dai ina fatan ba jami'an tsaro ba ne, don idan su ne akwai matsala babba." Matsalar me bayan mun ɓacewa ganinsu, ai ba wata matsala. "To idan ba wata matsala me zai saka take muna ɗaukarsa muka saka a motar take su ma suka ma ta ma na baya ko wajan ba mu bari ba sun bi mu, idan ba jami'an tsaron ba ne hakan yana nufin waɗan nan mutanen suna ba wa makaho kariya kenan." Direban ne ya yi maganar yana jinjina kai, kafin ya dora da cewa "Ko su waye tabbas kariya suke ba shi ba tare da saninsa ba." "Haba dai wani irin kariya za su ba shi wanann makahon da ba shi da gata bai da wani tsayayyen mutum da zai tsaya ma sa ne za'a sami ma su ba shi kariya?" Direban ya ci gaba da cewa. "Abun da yake ba ni mamaki kenan amma ko ka mene ne ta faru dai ta kare." Sauka suka yi daga saman titin suka dauki wata hanya. Bayan gari n don ba gine-gine a wajan ko alamar mutane. Daidai wani gidan gona suka yi parking motar a wajen gate ɗin. Suna gama parking wani mutum dogo yana da ƙiba ya fito daga gida gidan gonar. Kai tsaye motar ya nufa wanda ganinsa ya sa duk suka fito sai makaho dake kwance a bayan motar. Buɗe ma sa murfin motar aka yi ya kalli Makaho, sannan ya sune yaran nasa ɗaya bayan ɗaya ya ce. "Aikin ku ya yi kyau." Ya yi ma su alamar jinjina da hannunsa. Sannan ya ciro wayarsa a cikin aljihunsa, wata lamba ya danna wa kira kafin ya kara wayar a kunnensa. Bayan sakanni ya ji murya daga cikin wayar ana cewa. "Ya ake ciki ne sun iso?", "Eh sun iso." "Okay Ina son ka ɓatar da shi ya bar duniyar gabaɗaya. Zan tura maka cikon Naira miliyan goma." Daga haka ya katse kiran wayar daidai lokacin da wata mota ta iso wajen a guje. Kallo ɗaya suka yi wa motar nan suka gane ita ce wacce ta bi bayansu bayan sun ɗauki makaho, sai dai bayan suna ganin kamar sun tsere ma ta ne ashe ba haka ba. Wasu gardawa ne guda biyu suka fito daga cikin motar. Yayin da ogan wadanda suka sato Makaho yake kokarin ciro bindiga daga cikin aljihun wandonsa. Cikin ƙwarewa da zafin nama wannan da suka zo ƙwatar makaho ya yi saurin Harbin hannun wando ya ciro bindiga wanda hakan ya saka ya saki bindigar ya durƙusa a Wajen. Sauran mutane biyun kuwa suna ganin an karbi ogan nasu sai suka ruga a guje, sai dai dukkannin su biyun ba wanda ya tsere domin sai sa aka harbi kowa a ƙafa. Take suka zube suka kasa tafiya sai ihu. Shi kuma ogan ya yi saurin ɗaukar bindiga da niyyar harbi sai aka dayan hannun kuma wanda ya ɗauko bindigar da shi. Nam ya saki ƙara ya kwanta don suka hannun akwai harbi ƙafarsa ma . Take ya fara ihu yana roƙon taimaka ma sha a bar su da kansu kar su kashe su. Wajen motar da makaho ke ciki suka nufa. Nan suka gan shi kwance a bayan motar. Suka ɗauko su sannan suka saka shi a cikin motarsu suka bar wajen. Suna barin wajen kira ya shigo wayar ogan sai sai ba hannun da zai ɗauki kiran wayar da shi. Sau uku ana kira ba hannun ɗaga wayar, shi sauran yaran nasa kuma duk an harbi ƙafarsu. Makaho na kwance a bayan motar amma ya kasa ko da motsi ne, sai barci kawai da yake aikin yi. Su biyu suna gaba yayin da shi kadai ke kwance a bayan motar . Wanda ke zaune a kujerar me zaman banza ne ya kalli wanda ke driving ya ce. "Na kira sir na faɗa ma sa ko?' Kai ya jinjina ba tare da ya yi magana ba, sai bayan wasu sakanni kafin ya ce . "Sam na kasa gane dalilin da ya sa waɗan nan abubuwan." Ya yi maganar cike da takaici. Daidai lokacin wanda aka kira a wayar ya ɗaga tare da cewa. "Assalamu alaikum." "Wa'alaika salam, sir mun samu kuɓutar da shi amma yanzu baya cikin hayyacinsa." Ɗan jim ya yi kafin ya ce . "Ina fatan ba su cutar da shi ba ko?" "No sun dai bugar da shi ne kawai, kuma Allah ya sa muka je akan lokaci ba tare da wani abu ya faru da shi ba ko sun yi ma sa wani abu." "Gud job." "Thank you sir." Ya faɗa yana kallon wanda ke driving ko zai yi Magana, girgiza ma sa kai ya yi alamar a'a kafin ya ce . "Sir mu mayar da shi gida ne yanzu?" "No ku bari ya dawo cikin hayyancinsa zuwa gobe sai a kai shi." "Okay sir." Daga haka ya katse kiran wayar yana sauke ajiyar zuciya . _Ma'eesha_ Bayan ASP Nasir ya kai ta kofar gidan ta shiga gida sai ta ga gidan ya ma ta ƙunci da duhu. Wani irin kewar makaho take yi, duk da ba ta ci komai ba amma ba ta cikinta take yi ba. A hankali ta mayar da kofar gidan ta kulle bayan ta saka sakata. Tsaya wa ta yi tana kallon gidan na wasu mintinan kafin ta shiga cikin dakin bakinta ɗauke da sallama. Kayan jikinta ta cire ta je fito waje bayan ta ɗaura towel ta kuma daka hijabinta. Kasancewar akwai wutar nepa gidan da haske. Ta dauka bokiti ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki don yin wanka. Ba jimawa sai ga ta daga wankan, ta dauki buta ta yi alwala sannan ya shiga ɗaki. Bayan ta saka kaya ne ta ɗauki hijabinta ta hau kan sallaya . Sallolin nafila ta yi tare da yi wa mijinta addu'ar Allah ya kuɓutar da shi ya ƙare shi a duk in da yake . Sannan ta yi karatun Alkur'ani mai girma. Ba ita ta kwanta ba sai karfe biyun dare sannan ta kwanta . Ga wani tsoron gidan da take ji. A ranar ba ta iya lashe haske ba ta bar shi a kunne. Sannan kuma ba ta yi barcin kirki ba har asuba ta yi . Kewar makaho ne fal a zuciyarta, don pilow da take kwance a kai duk ya jike da hawayenta. Kuka take yi na tausayin mijinta da rashin sanin halin da yake ciki. Da asuba ta tashi da ciwon kai sakamakon kuka da rashin isasshen barci da suka hadu ma ta . "Adaddafe ta tashi ta kunna gas, ruwan ɗumi kadan ya yi wutar gas din ta yi low. Sakamakon ƙsraewar da gas din ya yi . "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un." Shi ne kalmar da ta furta sakamakon ta san ba ta da ko Naira biyar a hannunta. Ballantana ta zuba gas, dai dai gawayin da take da shi wanda ba ta san ma yadda ake kunna murhun gawayi ba. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ page4️⃣1️⃣ Shi ne kalmar da ta furta sakamakon ta san ba ta da ko Naira biyar a hannunta. Ballantana ta zuba gas , ga dai gawayin da take da shi wanda ba ta san ma yadda ake kunna murhun gawayi y. Kashe gas din ta yi ta juye ruwan a bokiti sannan ta shiga banɗaki don yin wanka. Bayan ta fito ne ta ɗaura alwala ta shiga ɗaki, dai dai lokacin ne nepa suka dauke wuta. Duhu ya mamaye ɗakin, sai ta tuno da zancen makaho da yake ce ma ta shi ba wani banbanci a wajan sa da akwai wutar NEPA da idan babu, saboda duhu yake gani duka ko wani lokaci. Wayarta ta laluba ta kunna torchlight sannan ta saka kaya ta yi sallar raka'atanil fijri. Kafin aka kira sallar assalatu ta gabatar da sallar asuba. Tana idar da sallar asuba ta zauna tana karatun Alkur'ani mai girma. Kafin gari ya waye sannan ta yi azkar din safiya ta . Addu'a sosai ta yi wa mijinta kafin ta tashi ta fita. Wanke-wanke ta fara yi bayan ta gama ne ta fara gyaran ɗaki. Daga nan ta fito ta gyara gidan. Mutun hawayi Ta ɗauka tana kunnawa amma bai kama ba. Kamar za ta yi kuka da kasa takaici ga shi duk kayan jikinta sun yi baƙin ha88i8wayi duk sun ɓaci da gawayi Dole ya saka ya je ta canza kayan jikinta, hijabi ya saka. Ka tsaye gidan da aka kai ta ta ƙi zama kafin suka kama haya. _Nadra_ Ba ƙaranin wuya ta sha a hannun Fahad ba a wannan daren. Shi ma kansa ya ji a jikinsa. Don Nadra ba abinda ba ta yi ba don ta ƙwaci kanta a hannun Fahad. Ganin Fahad bai ba san tana yi ba gabaɗaya ya gigice akanta sai sambatu yake yi ma ta har da daka ma ta albarka yake yi tare da godiya na tsare mutuncinta na ƴa mace. Nadra jin azabtar ta yi yawa ne ya saka ta kai ma sa duka da cizo har da yagushi don duk ta ji ma sa ciwo a fatarsa ta ji na sa ciwo har da cizo ya sha. Amma hakan bai sa ya saurara ma ta ba. Tsabar azaba sai da Nadra ta sume ma sa a wannan daren . Don bai yi la'akari da cewa ita budurwa ce ba. Yai ne karo na farko da ta taɓa sanin Ɗa namiji, sannan kuma shi za ɗauki tsawon lokaci yana wahalar da rayuwarta. Sai da ya samu natsuwa sosai kafin ya bar ta ta mirgina gefe yana mayar da numfashi. Zuwa lokacin karfe uku na dare ne. Shi a tunaninsu Nadra ta gaji da kukan ne ya saka ta yi shiru bai yi tunanin cewa sumewa ta yi ba. Da sauri ya shiga bathroom ya yi wanka ya tsarkake jikinsa Ba tare da ɓata lokaci ba ya yi wanka ya tsarkake jikinsa ya fito. Ka yi tsaye closet ɗin kayansa. Fitowa yayi daga cikin closet ɗin ya kunna hasken ɗakin, kwance ya gan ta ba ta motsi kuma ba alamar numfashi. Ga jini nan a jikinta. Dafe goshinsa ya yi tare da cewa. "Ya Allah." Ya ma rasa me zai yi lokacin da ta karasa baƙin gadon. Ɗan girgiza ta ya yi ya ga ba ta numfashi. Ga shi irin jinin da ya gani ya tayar ma sa da hankali. Dole ya nemi taimako Don bai san yadda zai yi da ita ba. Ruwa ya yayyafa ma ta amma ina ba ta farfaɗo ba, don haka hankalinsa ya kara tashi ya nufi ƙofar fita. Downstairs ya nufa wanda tun kafin ya karasa sauka yake ji yo sautin kukan Sidra. Tana zaune a kan sofa sai kuka take yi ta haɗa kanta da guiwa . Kin motsi an saukowa ta ɗaga kai ta kalle shi da idanun ta da suka rine suka yi ja. Kallo daya ya yi ma ta ya dauke kai ba tare da ya ce komai ba . Part ɗin kakarsa Inna ya nufa da sauri. Knocking yake yi a kofar bedroom ɗin ta, cikin barci ta ji bugun ƙofa. "Waye?" "Dan Allah Inna ki zo da sauri." Jin Muryar Fahad ya saka mike da sauri tana kunna hasken torch light din wayar ta. Domin ta san ba lafiya ba duk yadda aka yi . Buɗe ƙofar ta yi tana kallonsa ta ce. "Lafiya kuwa Majidaɗi?" "Ki zo don Allah Inna." Ba tare da ta sake wata magana ba ta bi bayansa zuciyarta cike da fargaba. Suna zuwa falo ta kalli Sidra dake kuka ta ce. "Me ya same ta ne.?' Ta yi tambayar tana kallonsa . "Inna ki zo don Allah." Ya ja hannunta suka nufi upstairs ɗin. Daga falo ya tsaya ya ce ma ta ita ta shiga ciki. Duk da ba ta san mene ne dalilin sa ba haka ta shiga ciki zuciyarta cike da wasu-wasi. Tana shiga idanunta ya sauka akan Nadra dake kwace kan gadon ga jini a ƙafarta har ya ɓata zanin gadon. ",Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. La'ilaha ilallahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi wasalam. Cikinta ne ya zube. Ka yi sauri ka..." "Ba cikin da take da shi Inna. A taƙaice dai yau ne daren farkon mu da na kasance da ita." Abubuwa biyu suka haɗu wa Inna lokaci guda, farin ciki da kuma baƙin ciki. Farin cikin na kusantar ta da ya yi, na biyu kuma na baƙin cikin yadda Fahad ya yi wa Nadra daga gani ta sha wahala sosai." Ba ta yi magana ba ta ɗauki wayarta ta ta kira lambar wayar Mama. Bugu biyu a na uku ta ɗaga tana cewa. "Inna lafiya kuwa?" "Wani lafiya Ɗan ki yana neman yin kisan kai." Ras gaban Mama ya faɗi ta tashi a firgice tana cewa. "Me ya yi Inna?" "Ki zo ɗakinsa ki gani." Da sauri ta diro daga kan gadon ko takalmi ba ta samu damar saka wa ba ta fice zuciyarta cike da fargaba abun da za ta tarar. A falo ta samu Sidra na kuka kamar za ta tsaya wajenta amma hankalinta na kan kiran da Inna ta yi ma ta. Fahad kam tun da ya ji tereren da Inna ta yi ma sa na kiran Mama sai ya ji kunyar Mahaifiyarsa. Don haka kafin ta zo ya sulale ya nufi part ɗin baƙi na gidan. Inna tana nan tana jiran isowar Mama. Da sallama Mama ta tura ƙofar ta shiga, ba kowa falon don haka ta nufi bedroom ɗin. Nan ta ga Inna tsaye kafin ta yi magana ta hangi Nadra kwance a gadon kamar gawa. Sai da zuciyarta ta harba. "Me ya same ta haka ta zubar da jini?" "Ba dole ba saboda rashin imani irin na ɗanki kalli yadda yayi wa wannan ƴar ƙaramar yarinyar aika-aika kamar ya samu guzuma." Sai da ƙwallar tausayin Nadra ya cika idanun Mama, cikin sanyin jiki ta karasa gaban gadon tana cewa. "Inna don Allah ki taimaka ma ta mana." "Ai dole na taimaka ma ta na kira ki ne ki ga abin da ke faruwa." Inna ta kalli Mama ta ce. "Ina zuwa bari na je na hado ma ta magungunan da za su taimaka ma ta yadda za ta warke da wuri kuma raɗaɗin ciwon zai ragu kuma za ta koma ta matse. Tana faɗar haka ta juya ta fice. Mama ta karasa gaban gadon tana kallon fuskanta da ta bushe da hawaye idanunta sun kumbura. Cike da tausayin yarinyar Mama ta shafa gefen fuskarta tare da cewa. "Kiyi hakuri Daughter, Allah ya ma ki albarka." Mamaki take yi saboda Rumaisa da Sahiba sun sanar da ita cewa Fahad ya kusanci matarsa har ba ta iya tafiya to dama karya suke yi ko me? Fridge ta buɗe ta ciro robar ruwa ta zuba a bakinta ta fesa wa Nadra a fuska da ƙarfi. Wani gawurtaccen ajiyar zuciya ta sauke tare da fashewa da kuka tana cewa. "Ya Fahad wallahi zan iya mutuwa." Tana fashewa da kuma mai tsuma zuciya, daidai dai lokacin da Inna ta shigo cikin ɗakin. Mama ta kalli Inna ta ce . "Ta farfaɗo." "Ma sha Allah, yanzu na haɗa magungunan na ɗora a wuta ki duba a cikin kitchen dake cikin part ɗin nan idan tkya tafasa ki zuba a roba ki kawo mana a banɗaki." Jin muryoyin su ne ya saka Nadra ta gane ita da su waye a ɗakin. Kuka ta saka masu tana rike hannun Inna tana cewa." "Inna ki taimaka ma ni ba zan iya tashi ba, wajan Ummata zan koma." Ta yi maganar tana sake rufe jikinta da bargon da Fahad ya ɗan rufa ma ta. Mama ta je duba maganin inda ta tarar yana tafarfasa. Ta juye a wani roba dake cikin kitchen ɗin ta ta bar sayyun magungunan a tukunyar. Ta kashe gas din ta fito ta wuce zuwa bathroom na Fahad ta ajiye . Inna ta biyo bayanta ta karba ta zuba a roba mai faɗi. Sannan ta zuba wani garin magani dake hannunta. Sannan ta fita Mama ma ta fice . "Za ki iya tafiya?" Cewar Inna tana kallon Nadra. "Mu taiamaka ma ta dai ." Mama ta fada tana budar bathroom, ba jimawa ta fito rike da babban towel ta mikawa Inna. "Ki ɗaura ma ta Inna." Inna ta amsa ta shigar da shi cikin bargon sannan ta ɗaurawa Nadra. Sai da suka rirriƙe ta ƙafarta na rawa ta taimakon su suka kai ta banɗaki. Daga nan Mama ta fita daga bathroom ɗin. Bayan Inna ta tabbatar da ruwan ya yi daidai yadda take so ta zaunar da Nadra a ciki. Wani azababben zafi ta ji ya ratsa ta wanda ya sa ta saki ihu. Tana shirin miƙewa tsaye kenan Inna ta danna ta a cikin ruwan wanda hakan ya saka ta sakin kuka tana girgiza kai. Cikin tausayawa Inna ta ce. "Na san akwai zafi sosai amma idan kika ɗaure wannan ruwan maganin zai taimaka ma ki wajen warkewa da wuri kuma zai sa ku koma ki matse yadda za ki sake martaba a wajen mijinki." Ita kam ba ta ma san me Inna ke cewa ba sai aikin kuka kawai da take yi. Sai da ta ɗauki mintuna talatin a cikin ruwan kafin Inna ga canza ma ta ruwa, sai da ta tabbatar da cewa ta haɗa ta yadda ya kamata sannan ta ce ma ta ta yi wankan tsarki. Ko da Inna ta fito ta tarar da an cire wannan zanin gadon an sauya wani sabo. Tana tsaye tana jiran fitowar Nadra, sai wayarta ya soma ruri, tana dubawa ta ga Fahad ne, tana dagawa ya ce. "Inna idan kun gama ga magani nan na ajiye ma ta." Jin haka ya sa ta gane cewa shi ne ya shigo ya gyara gadon ya ajiye magani. Nadra ta fito ɗaure da towel babba a jikinta. A hankali take tafiya ta ji saukin jikinta sosai don tafiyar ta fi ba ɗazu kyau. Da kanta ta ɗauko doguwar riga a cikin akwatin kayan da Fahad ya siyo ma ta. Rigar ba ta da nauyi sai pant da ta saka. Kanta ne ke ciwo ga wani barci da ke fisgarta. Da taimakon Inna ta kwanta a kan gadon yayin da Inna ta ja ma ta bargo tana yi ma ta sai da safe ta fice. Lokacin karfe huɗu da kwata na asuba. Dai da barci ya dauke ta sannan Inna ta bar part ɗin. Duk abinda ke faruwa akan idanun Fahad dake kallon su ta wayarsa. Lokacin da ya ga Inna ta fice shi na ya bar part ɗin baƙi ya dawo part ɗin nasa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* Page4️⃣2️⃣ Duk abin da ke faruwa a kan idanun Fahad dake kallon su ta wayarsa. Lokacin da ya ga Inna ta fice shi ma ya bar part ɗin baƙi ya dawo part ɗin nasa. _Makaho_ Kwance yake a wani katafaren ɗaki, wanda aka ƙawata shi da kayan alatu Yana kwance saman wani haɗaɗɗen gado wanda aka shimfida tsadadden zanin gado. A hankali ya fara motsawa, hannun sa ya sa ya dafe kansa dake tsananin sara ma sa. Wani baƙon ƙamshi da sanyi ne yake ratsa shi. A hankali ya kai hannunsa yana shafa in da yake kwance. Jin laushi ya sa ya tashi zaune yana lalube. Har kan royal bed ɗin ya shafa ya tabbatar akan gado yake, kuma ba katifar Ma'eesha ba ce. A hankali abinda ya faru ya fara dawo ma sa a kai. A zabure ya miƙe tsaye yana lalube. Ji ya yi an rike ma sa hannu tare da cewa. "Ka yi a hankali don Allah jikinka ba ƙarfi." Cikin ɓacin rai ya ce. "Meye matsalar ku da ni ne?" "Ba mu da matsala da kai gaskiya, hasali ma ceton rayuwarka muka yi daga wajen waɗan da suka kama ka, da ba don mun je a kan lokaci ba da sai sun kashe ka." Shiru yi yi na ɗan lokaci kafin ya nisa ya ce. "Mutuwa lokaci ne, duk wanda ya mutu kwamansa ne suka ƙare, duk yadda suka so kashe Ni idan kwanakin mutuwa ta ba su cika ba ba su isa su kashe ni ba ko babu ku kuwa, haka kuma idan kwana na suka ƙare ko second ɗaya ba zan kara a duniya ba zan tafi, don haka idan mai kisa ya yi hakuri wanda zai kashe zai mutu. Don haka yanzu zan koma gida na san waɗan da suka damu da ni suna can cikin tashin hankali da damuwa na rashin gani na." "A gaskiya ka yi yi hakuri yallabai ba zai yiwu ka fita cikin wannan daren ba, sai da safe in sha Allah za mu mayar da kai cikin aminci ." Table da aka jera abinci ya janyo ma sa ya ajiye ma sa a gaba. "Ga abinci nan, a gabanka, idan ka mike hannun damarka kuma toilet ne ko da kana bukatar shiga ciki sai ka shiga." Juyawa ya yi ya bar ɗakin ba tare da ya sake yin magana ba. Kamar yadda ya ce ma sa kofar toilet na ta hannun damar sa haka ya mike yana lalube har ya ji kofar sannan ya tura ta ya shiga. Ba jimawa ya fito da alama alwala ya ɗauro ya fito. Yana fitowa ya ji an ce "Ga sallaya nan." Aka rike ma sa hannu zuma saman sallayar. "Karfe nawa yanzu ?" "Karfe biyu dare ne?" Bai sake yin wata magma ba ya fara gabatar da sallolinsa. Bayan ya idar da sallolin ne ya ya yi addu'o'i sannan ya tashi. Ya sake jin Muryar mutumin na cewa "Allah ya karba ya bada lada." "Bai amsa ma sa ba ya ji ya rike ma sa hannu yana cewa Suka karasa bakin gadon sannan ya zauna sannan ya janyo ma sa karamin table da aka jera ma sa abinci akai. "Bismillah ka ci abinci." "Ba zan ci komai ba." "Me ya sa yallaɓai?" Kwanciyarsa ya yi ba tare da ya ce ma sa komai ba, domin ya san cewa Ma'eesha na can cikin damuwa ba za ta iya cin abinci ba, don haka shi ma ba zai ci abinci ba." Duk yadda aka dinga rarrashin sa bai motsa ba, dole ya fita ya bar ma sa ɗakin. _Ma'eesha_ Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan. Cike gidan yake da mata da yara. Wasu Na hura wutar murhu wasu na share kofarsu wasu na wanke-wanke wasu na zaune ba sa komai yayin da yara kuma suna wasa. A hankali ta sauke idanunta kan kofar ɗakin da makaho ya kai ta a matsayin ɗakinta, wanda ta kasa zama, har lokacin yara na zaune kofar dakin sun jeru a dama Po suna bayan gida. "Lale marhaba da zuwan matar makaho." Cewar Larai Dillaiya kenan. Baba ta fito daga ɗakinta tana washe baki ta ce. "Amarya sannu da zuwa, ke ce da safiyar nan?" Murmushi Ma'eesha ta yi tare da durƙusawa ta yi ta gaida Baba. Ta amsa mata cike da farin ciki. Ta gaida sauran matan gidan suka amsa mata cikin dakin fuska. Baba ta yi murmushi ta ce. "Ƴata ko za mu shiga daga ciki ne?" Ma'eesha ta kalle ta tana murmushi ta bi bayanta suka shiga ciki. Bayan ta shimfida ma ta tabarma ta zauna ne ta ce. "Yanzu kuwa Liman ya fita yana cewa wai ya ji ana raɗeraɗen an kama Khalifa mijinki juya da yamma, shi ma bai sani sani ba sai yau a masallaci yake ji da asuba. Har ya ce na je na duba ki. Ina shirin fita ne sai na ji na uryar ki." Murmushin karfin hali Ma'eesha ta yi kafin ta ba ta labarin abun da ya faru, kafin ta kara da cewa. "Yanzu ina jiran ɗan anjima ne na koma wajen ƴan sanda. Amma kafin nan ina son ki bani aron jikar ki A'isha ta nuna mani yadda ake kunna wutar murhun gawayi ne." Dariya sosai Baba ta yi kafin ta ce. "Ba ki iya ba ne dama?" "Eh ban ma taɓa gwadawa ba sai yau, na fi gane wa Gas ne don shi na taso na gani a gidanmu." Cike da tausayinta Baba ta ce. "Allah Sarki rayuwa kenan, wannan ma zai wuce in sha Allah." Ta mike ta fita waje tana kiran Mahaifiyar A'isha. Matar ta shigo dakin Baba suka kara gaisawa da Ma'eesha, kafin Baba ta ce . "Ina A'isha?" "Ba ya dawo daga islamiyya ba amma yanzu na san suna hanya." "To dama za ta je ne ta taya Matar Khalifa wani aiki a gidanta." Daidai lokacin A'isha ta yi sallama ta shigo cikin gidan. "Ma sha Allah gata nan ta dawo." "Assalamu alaikum." Ta yi sallama ƙofar ɗakin kakarta ta shigo. Ganadaya suka amsa mata ta shigo ciki, tana ganin Ma'eesha ta faɗada fara'ar ta ta ce. "Aunty sannu da zuwa." "Yauwa A'isha ya kike?" "Lafiya lau Alhamdulillah." Daga nan ta gaida kakarta da mahaifiyarta. Sannan Baba ta ce ta je ta taya Ma'eesha aiki." Jakarta da Alqur'ani ta ajiye ta bi bayan Ma'eesha suka fice bayan Ma'eesha ta yi ma su sallama. Suna tafiya suna fira a hanya duk da dai Ma'eesha ƙarfin hali kawai take yi, damuwar dake zuciyarta ma kaɗai ta ishe ta. _Fahad_ Shigowarsa kenan bayan ya bar part ɗin baƙi. Tsaye yake yana ƙare ma ta kallo. Karon farko a rayuwarsa ya ji wani abu game da ita a zuciyarsa. A baya baya jin komai akanta a zuciyarsa, amma a yanzu da wani mu'amala ta shiga tsakanin sa da ita sai yake jin ta a gefen zuciyarsa, tabbas ba zai iya cewa ya kamu da soyayyar ta ba amma kuma ya ji yana tausayin ta a zuciyarsa. Sam ya kasa gane dalilin da ya sa har ya ji ya kwaɗaitu da son kasancewa da ita ba. Wanda ko bayan aurensu bai taɓa saka wa a ransa akwai ranar da wata mu'amala ta aure ya haɗa shi da ita ba, kwata-kwata babu wanann a tsarin zamantakewarsa da ita ita, amma lokaci ɗaya komai ya sauya ya ji ba zai iya hakuri da ita ba. Shafa gashin kansa ya yi har zuwa gefen kwantaccen sajensa zuwa gemunsa. Yana jin nishaɗi sakamakon tuna yadda ya tsinci kansa a yanayi dai bai taɓa jinsa a ciki ba sai dalilinta. Ta mallaka masa mutuncinta da ƙimarta da darajar ta na ƴa mace, wanda a wannan zamanin ba kowace mace ba ce ke kai mutuncinta gidan aurenta ba. Murmushi ya saki yana nufar bathroom. Jallabiyar jikinsa ya cire yana tsaye gaban madubi yana kallon jikinsa. Idanunsa suka sauka akan damtsen hannunsa zuwa gefen ƙirjinsa da ke da sunan Sidra. Ɓacin rai ya ji ya ziyarce shi lokacin guda. Shower 🚿 ya sakar wa kansa idanunsa suna sauya kala zuwa ja. Take ɓacin ran da Sidra ta cusa ma sa ya dawo ma sa sabo. Har ya gama ya ɗaura towel da wani karamin towel a hannunsa yana tsane gashin kansa. Alwala ya ɗauro ya fito daga bathroom ɗin. Jallabiya ya saka ya ya gabatar da sallolin nafila. Sai da aka kira sallar asuba ya tashi zai tafi masallaci ne ya kalle ta. Yana son ya tayar da ita amma yana tsoron tashin ta. Fita ya yi ba tare da ya tayar da ita ba ya nufi masallaci. Cikin barci ta ji ana sallah a masallaci, Kasancewar ta saba tashi a daidai wannan lokacin, to da zaran lokacin sallah ya yi duk nauyin barcin da ke kanta sai ta farka daga barci. Tashi ta yi daga kwancen har lokacin tana jin jikinta na ma ta ciwo sosai, sai dai ƙasanta ya rage zafin da yake yi ma ta. A hankali ta fara tafiya ta nufi bathroom. Gasa jikinta ta sake yi da ruwan ɗumi sannan ta yi wanka ta fito Wata doguwar riga mara nauyi ta saka ba ta tsaya sa komai ba ganin Lokaci sallah ya tafi. A daddafe ta yi sallar asuba ta yi wasu azkar ɗin sannan ta koma ta hau gado ta kwanta. Don ko karatun Alkur'ani da ta saba yi kowace safiya yau ba ta samu damar yi ba ta shige cikin bargo. Lokacin da gari ta fara haske Fahad ya dawo daga masallaci. Part ɗin Mama ya nufa ba ta falo, sallama ya yi yi a kofar bedroom ɗin ta. Tana zaune saman sallaya ta amsa ma sa. Ya shiga ya gaishe ta, ta amsa ma sa tana yi ma sa ya jikin Nadra. Kasa amsa wa ya yi don kunyar Maman ya ji. "Bari ba je na shirya saboda sauran awanni biyu jirgin da zan bi ya tashi." Ya yi maganar yana miƙewa. Jinjina kai Mama ta yi tana cewa. "Haka ne ka san jirgi baya jira." Hanyar fita ya nufa ta bishi da kallo kafin ta cigaba da abun da take yi. Part ɗin Inna ya nufa ya same ta saman sallaya ta koma barci. Fita yayi ya nufi part ɗin sa. Har ya fara taka step ɗin sai ya ji a jikinsa ana kallonsa. Juyawa ya yi suka yi idanun biyu da Sidra. Tana tsaye sanye da kayan barci kanta ba hula ta zuba masa idanun ta kamar za ta cinye shi. Ga idanun sun kumbura alamar ta ci kuka. Ɗauke kansa ya yi ya fara taka matattakar har yana tsallaken stepe. Yana shiga bedroom ɗin ya same ta kwance ta fara barci. Sai dai da alama ta yi sallah, don ya ga sallaya da hijabinta in da ta yi sallah ba ta ɗauke ba. Trolling bag ɗin sa ya dauka ya fara saka kayan da ya san zai buƙata a can. Ya haɗa komai har da system ɗin sa. Wanka ya shiga bathroom ya yi ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya sai zuba ƙamshi yake yi. Time ya duba ya ga lokacin tashin jirgi sauran awa ɗaya da rabi. Idanunsa ya sauke akan ta lokacin da take gyara kwanciya tana yamutse fuska kamar za ta yi kuka. A hankali ya karasa bakin gadon ya zauna a gefen ta. Bargon da ta rufe jikinta da shi ya yaye shi. Tana barci ne amma kamar ba ta jin dadin jikinta. Tura baki gaba take yi tana ɓata rai. Wani abu ya ji ya fisge shi wanda hakan ya saka ya kai bakinsa saman nata ya fara tsotsa. A firgice ta bude idanun ta tana sauke shi akansa. Tuna azabtar da ta sha ya saka ta saka ma sa kuka. Kokarin tashi take kokarin yi ya ma ta rumfa da ƙirjinsa. Nan ya shiga sarrafa har ya raba ta da rigar jikinta, da pant ɗin dake jikinta Cikin kukan tausayin kanta take cewa. Sosai yake wasa da ita yana tsotsa duk inda ya ga dama ya shafa in da yake so. "Yaya Fahad wallahi wajen yana mun zafi, bai ma san me take cewa ba ya fara gigice ma ta. Ganin yana ƙoƙarin cire kayan jikinsa ne ya saka ta rintse idanunta tare da sadaƙar wa tata ta ƙare. Lokacin da ta ji yana karanto addu'ar saduwa da iyali ta saka kuka. Lokacin da ya shige ta ne ta rasa hawaye da bakin kuka, don bakin kukan ma ba ta same shi ba. Sai da ya yi awa ɗaya kafin ya saurara ma ta. Ganin saura mintuna ashirin da biyar jirginsa ya tashi ya saka ya fada banɗaki da saur. Sauri-sauri ya yi wanka ya fito yana tsane kansa. Closet ɗin sa ya shiga ya shirya cikin wasu kayan. Time ya duba yana sauri ya ɗaura agogonsa ya fesa turare. Ganin saura mintuna sha goma sha biyu ya kalle ta cike da tausayi, ta galabaita shi kansa y san bai kamata a ce bayan ya kasance ta daren jiya yau da safe ya sake ba kara ma ta wani zafi kan zafi ba. Idanunta sun canza sun yi ja. "Am sorry." Ya fada a ƙasan maƙoshinsa wanda shi kaɗai ya ji kayansa. Trolling bag ɗin sa ya dauka da wayoyinsa yana barin ɗakin da sauri. Suna zaune a main falon gidan suka juya suna kallonsa. Inna, Mama, Farida, Rumaisa. Idanun Farida a kansa tana kallon tabon dake gefen wuyansa. Da sauri ta mike tana cewa "Me ya same ka?" Shafa wajen ya yi ya tuna cizo da yakushin da Nadra ta yi masa a daren jiya. Shaidar farcen ta ne a gefen wuyansa. "Kar ki damu ba wani ciwo ba ne." Kallon Mama ya yi ya ce . "Saura mintuna goma zan iya rasa jirgi." "Ai da na ji ka shiru n dauka ka fasa ne." "A'a zan tafi, Inna ki duba yarinyar nan don Allah ba ta da lafiya." Wani kallon ta ma sa kafin ta ce . "Me kuma ka yi ma ta?" "Ba komai." Daga nan ya fice suka tashi suna mara ma sa baya. Direba na wajan mota yana jiran fitowarsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* Page4️⃣3️⃣ "Me kuma ka yi ma ta?" "Ba komai." Daga nan suka tashi suna mara ma sa baya. Direba na wajen mota yana jiran fitowarsa. Yana hangen su ya karasa ya karbi trolling bag ɗin Fahad ya saka a bayan motar. Cikin hanzari ya yi ma su sallama ya shiga motar. Umarnin taka Motar da sauri Fahad ya ba shi, don haka a guje yake taka Motar suka kama hanyar airport. Su Mama ba su koma part ɗin su ba suka nufi part ɗin Fahad kasancewar ya ce Nadra ba ta da lafiya. Farida ba ta so zuwa ba amma ganin Inna ta ce su je su gaishe ta ya saka suka bi bayanta gabaɗaya. Ba kowa a falon don daman ba su yi tsammanin ganin ta a nan ba, bedroom ɗin suka shiga nan suka ganta dunƙule cikin bargo sai hawaye take yi. Kallo ɗaya Inna da Mama suka yi ma ta suka fahimci Fahad ne ya yi sake yi ma ta waya aika-aika. Cikin ruɗewa Rumaisa ta karasa bakin gadon tana cewa. "Aunty me ya same ki dama ba ki da lafiya ne mayar Yaya?" Ta yi maganar tana kokarin jan bargon da take rufe ciki. Da sauri Nadra ta rike bargon tana girgiza ma ta kai alamar a'a. Hakan ya sa suka fahimci babu kaya a jikinta. Mama ta ce wa Rumaisa "Duba cikin kanta ki ɗauko ma ta riga mara nauyi ta saka." Bayan ta ɗauko rigar ne Mama ta kalli Farida da Rumaisa ta ce. "Ku ba su wuri Inna za ta taimaka ma ta anjima sai mu shigo Mu duba su." Cike da takaici Inna ta ce . "Wallahi da zan ga Fahad yanzu nan ba abinda zai haka ban samu madaki na dake shi ba, wani irin rashin imani ne wannan? Ƙaramar yarinya ka addabe ta tin jiya har yau ma ba ka bar ta ta huta ba saboda rashin imani?" Cike da takaici Farida ta bar ɗakin tana nadamar shigowar ta ɗakin. Rumaisa ma ta mara ma ta baya suka bar part ɗin suka koma downstairs. Sidra ce zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon . Su ma suka zauna ba wanda ya yi yi magana. Mama ce ta zo ta wuce su ta shiga part ɗin ta. Cikin takaici Farida ta ce . "Wallahi Yaya Fahad ya ba ni mamaki, ban taɓa tunanin ajinsa da jin kansa zai sauke su a kan wannan kucakar yarinyar ba. Wacce sam ba ajinsa ba ce ba ta dace da shi ba, ki duba irin matan da suke son sa yake wulakanta su suke kai kansu amma ya kare a wannan ƙaramar yarinyar da ko..." Kafin ta kai ƙarshen maganar ta ne ta ji Sidra ta saka dariya tana cewa. "Iska na wahalar da mai kayan kara, ai ki sani Fahad ba kya gabansa bai ma san kina yi ba, ko can dama ba kya gabansa ballantana yanzu da yake da ma ta. Don haka ina mai baki shawarar ki nemi mijin da yake son ki ki aure shi, tun da har tsawon shekaru da kuka yi da shi a gidan nan ba ki iya janye hankalinsa daga wata mace ba har ya kai wannan matakin to ta ki ta ƙare." Wani kallo Farida ta yi wa Nadra kafin ta ce. ",Ke kuma a su waye, matarsa ko yar matarsa? Ko kuma budurwarsa ko surukarsa ko tsohuwar budurwarsa? Na kasa gane a wani mataki zan ajiye ki. Sai dai na san abu ɗaya shi ne har yanzu kina mutuwar son Fahad duk da yana auren ƙanwarki? A gurɓataccen tunanin ki zai auri ƙanwarki ya aure ki ne, ko kuma kina shirya planning yadda za ki fitar da ita ne ke ki shiga?" Wani murmushi Sidra ta yi wanda ita kadai ta san ma'anar sa, kafin ta kalli Farida ta ce. "Lokaci ne zai sanar da ke manufa ta." "Hmmm ai lokaci sakarai ne ya kan tafi da mahimman abubuwa." Dariya Sidra ta yi kafin ta ce . Kuma yakan tafi da sakarkarin burkan wasu, ke kanki kin san cewa babu macen da Fahad yake so sama da ni a wannan duniyar. Domin ni da kansa ya ce yana so na ba ni ce nake bisa yake wulakanta ni ba, kina mace ai abun kunya ne a wajen ki a ce kin kasa janyo hankalin ɗa namiji gare ki har sai wata daga waje ne za ta ɗauki hankalin..." Kasa ƙarasawa ta yi sakamakon ganin Mama na zuwa. Sidra ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa cikin dakin fuska da walwala. Har za ta wuce sai ta ce. "Ya na ga kamar fuskar ki a kumbure har da idanun?" Murmushi Sidra ta ƙirƙira kafin ta ce "Sanyi ne idan ina mura hakan na faruwa da ni." "Ayyah sorry, za ki je asibiti ne ko magani za'a kawo ma ki sai ki sha?" "Mama Gara na je na ga likita." "Okay idan kin shirya direba sai ya kai ki." Jinjina kai ta yi alamar gamsuwa sannan Mama ta bar wajen. _,Nadra_ Sosai take yin hawaye na takaicin abun da Fahad ya ya yi ma ta. Sai da Inna ta sake gasa ma ta jikinta sosai sannan ta bar ta ta ce ta yi wankan tsarki. Tana wanka tana zagin Fahad a cikin zuciyarta har ta gama . Towel babba ta ɗauro a ƙugunta tana tafiya a hankali yayin da ɗaya ke kanta. Zama ta yi gaban dressing mirror 🪞 ta shafa man shafawarsa. Daidai lokacin innat ta shigo cikin ɗakin da faranti a hannunta d Ka jera breakfast. Nadra ta yi nisa cikin tunani ba ta ma san ta shigo ba. Ta shiga duniyar tunanin abun da za ta cewa Sidra. Don tun da har ialahirin jama'ar gidan nan suka zo don duba ta to tabbas Sidra ma ta san abinda ke faruwa. Da wani ido za ta kalle ta ne bayan ta roƙe ta akan kada ta yarda da Fahad ta bar ma ta shi kuma ta amince ma ta. Kuma ba lallai Sidra ta gane cewa ba yadda ta iya ba ne. Ta roƙe shi Allah Annabi akan ya bar ta bai saurare ta ba "Tunanin me kike yi ne?" Murmushi ta ƙaƙaro kafin ta ce. "Ba komai Inna." Ganin gashin nata a jiƙe ya sa Inna ta duba kayan akwatin da Fahad ya siyo wa Nadra. Nan ta yi kiciɓis da hand drayer ta mika wa Nadra. "Karɓi ki busar da wannan dogon gashin kanki, yaushe zai bushe har ki shirya?" Murmushi ta yi ta karba tana yi wa Inna godiya. Bayan ya jona a jikin socket ta busar da gashin kanta ta ɗaure su ne ta mike ta ta nufi set na akwatin kayan ta fito da wata Abaya da underwear ta saka . Dama yunwa take ji don haka ta cika cikinta sosai. Sannan Inna ta bar part ɗin _Ma'eesha_ Tana kallon yadda A'isha ke haɗa gawayi cikin murhun gawayi, har ta ce wa Ma'eesha idan akwai Leda ta ba ta. Ma'eesha ta memo ledoji ta kawo ma ta ta ga yadda ta ƙyasta ashana a jikin ledar ta hura wuta. Bayan kamar mintuna biyar ne dai ga wutar ta fara garwashi. Ma'eesha ta ɗauko tukunya ta wanke ta ɗora a wutar. "Yauwa A'isha ko kin san yadda ake ɗaurin gawayin siyarwa?" "Gawayin siyarwa kuma Aunty?" "Eh, ina da buhu ɗaya ina son na ƙulla na dinga siyarwa." "Eh na sani." "Yauwa mu je ki nuna mun." A tare suka shiga kitchen dake tsakar gidan A'isha ta juye gawayin a ƙasa. Kallon Ma'eesha ta yi kafin ta ce . "Kin siyo leadar ƙulla gawayin ne?" ,Shiru ta yi don ba ta yi tunanin wannan ba, ga shi ko Naira biyar ba ta da shi. Kasancewar A'isha yarinya mai wayau ce ta karanci yanayin Ma'eesha ta ce. "Ɗari biyu ake ɗaura gawayin yanzu, kuma dama ni ma kullum ina siya ta ɗari huɗu idan zan yi sana'a ta, don haka bari na siyo ma ko ledar da ɗari huɗun nan idan an gama ƙulli sai na ɗauki gawayin ɗari huɗu." Ɓoyayyen ajiyar zuciya Ma'eesha ta sauke kafin ta ce . "To A'isha na gode." Daga nan ta fita don siyo gawayin. Bayan ta dawo ne ta ce wa Ma'eesha ta ta kawo ƙaramin roba ko kwano da za su dinga awo da shi . Ta kawo kwano uku ta ce wanne zai yi, sai A'isha ta zabi daya daga ciki ta ce zai yi daidai. Haka kuwa aka yi tana aunawa tama zubawa Ma'eesha na ɗaure bakin ledar.j Kuma ta kan tashi tana duba girkin da ta ɗora a wuta. Har suka gama suka ƙirga, kuma Alhamdulillah an samu riba sosai. Don lokacin da Ma'eesha ta siye buhun gawayin dubu bakwai ne kuma yanzu an ɗaura na dubu goma sha ɗaya a ciki. Duk kayan jikinsu ya yi baki musamman A'isha da ta yi zaman zubawa. Kallon Ma'eesha ta yi tace. "Aunty ki dinga neman tsohon zani idan za ki daura saboda ɓata jiki." "To A'isha na gode, ki tsaya ki yi wanka ma na." "A'a yanzu xan je gidan na yi ." Don haka sanya zuba ma ta jallop ɗin taliyar da ta dada a kula ta ba ta ta kai gida. Sannan ta ce ta dauki gawayin kudin ta na dari hudu ta kuma kara na ɗari huɗu, sai dai sam A'isha ta ce ba za ta amsa ba duk yadda ma'eeha tayi hakuri ta bar ta. Bayan fitar Aisha Ma'eesha ta shiga banɗaki don yin wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin atamfa Holland riga da zani. Ta zauna t hada tagumi cikin yanayin sanin madafa. Ga shi ASP ya ce sai sun yi bincike zai kira ta. Ga yunwa tana ji amma ta kasa cin komai. _Makaho_ Tun da ya idar da sallar asuba ya zauna yana karatun Alqur'ani, da safe ya yi azkar din safiya. Yana zaman jiran shigowar daya daga cikin mutanen da suka kawo shi nan. Jin shiru ya saka shi ya mike tsaye bayan ya lalubi sandarsa. Da lalube har ya gano in da ƙofar ɗakin yake, ya ha ƙofar amma sai ya ji ta a datse, wato an rufe da key kenan. Don haka ya hau dukan ƙofar don a zo a bude ma sa ƙofar. Amma sai ya ji shiru ba alamar za'a zo a bude ma sa kofar, cikin fusata yake dukan ƙofar wanda hakan ya sa ɗaya daga cikin mutanen zuwa ya buɗe ƙofar. Tun kafin ya yi magana dai MAKAHO ya ce . "Ku mayar da ni inda kuka ɗauko Ni." Gajeren murmushi Mutumin ya yi kafin ya ce . "Kar ka manta mun sanar da kai a hannun waɗan da suka yi garkuwa da kai. Kuma da dukkan alama kashe ka suke da niyyar yi, ba don Allah ya sa mun je akan lokaci da yanzu babu kai a duniyar nan." "Ba ni hanya na fita !" Ya fada a kausashe. "Okay ina zuwa." Ya faɗa yana lalubar wayarsa a aljihu, bayan ya fito da wayar ne ya ya nemi wata lamba ya danna kira. Bugu biyu aka ɗauka daga can ɓangaren aka ce. "Assalamu alaikum " "Wa'alaika Salam." "Ina fatan ba wata matsala kuma, yana cikin ƙoshin lafiya ko?" "Eh yallaɓai, ya tayar da hankali akan sai ya koma gida ne." "Okay ba damuwa a mayar da shi gida cikin aminci." "Okay sir." Daga nan ya katse kiran wayar ya kalli makaho ya ce. "Za ka iya zama ka yi breakfast kafin mu tafi?" "Ba zan iya ba." Ya faɗa ransa a ɓace. Murmushi Mutumin ya yi kafin ya kira wata lamba ya ce su fito da mota za su mayar da shi gida. Kallon Khalifa ya yi ya ce. "Za ka iya tafiya ko na rike ka?" "Ka tafi ina bin ka a baya." Daga haka ya yi gaba yayin da Khalifa Makaho ke bin sa a baya ta hanyar jin sautin tafiyar takalminsa. A harabar gidan suka tarar da wata mota mai tinted glass tana jiran su, mutane biyu ne a cikin motar, direba dai kuma wani da yake da wajen me zaman banza. Wanda ya fito da Khalifa ya bude murfin bayan motar ya ce wa Makaho ya shiga, bayan ya laluba ya shiga ne shi ma ya zauna a gefen sa. Direba ya tayar da motar yayin da security ya wangale ma su gate ɗin gidan. Suna tafiya wanda ke zaune gefen direba ya ɗan juya ya kalli makaho ya ce "Ya kamata ka zama mai taka tsantsan wajen sanin inda za ka dinga zuwa da kuma lokutan inda kake fita. Sannan wace ce wannan yarinyar da kake zaune gida ɗaya da ita me ye alaƙar ku f ita?" Tsuke fuska Khalifa ya yi kafin ya ce. ",Ina ruwan ku da ita? Ki tsaya matsayin ku Mallamai." Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa suka ajiye shi ƙofar gida suka kama hanya suka koma. Tsaye ya yi rike da snadar jagoransa na tsawon mintuna biyu, kafin ya ɗaga ƙafarsa cikin sanyin jiki ya doshi ƙofar gidan. Ya kai hannu zai tura ƙofar falefalen kenan ya ji sheshsheƙar kukanta na tashi. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan✍️ *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION* Page4️⃣4️⃣ Tsaye ya yi rike da sandar jagoransa na tsawon mintuna biyu, kafin y ɗaga ƙafarsa cikin sanyin jiki ya doshi ƙofar gidan. Ya kai hannu zai tura ƙofar falefalen kenan ya ji sheshsheƙar kukanta na tashi. Take ya ji jikinsa ya kara sanyi duniyar ta yi ma sa zafi, babu abun da ke cikin zuciyarsa sai tausayin Ma'eesha. Ya san tana cikin matsin rayuwa, ta taso cikin hutu da jin dadi, sam ba ta san wani abu wai shi matsin rayuwa ba sai a dalilinsa gani yake yi ai duk saboda shi yake fuskantar wannan ƙalubalen. Yarinyar da ta tashi cikin ƙererren gida cikin hutu da jin daɗi, gidanta ɗakinta A.C motarta A.C ga ma su yi ma ta aikin duk hidimar da take so ta ci lafiyyaen abinci ta sha ruwan roba da duk wani nau'in abun sha da yake so. Amma yanzu rayuwa ta juye da ita wai ita ke rayuwa cikin wannan akulkin gidan. Cikin zafi da sauro. Ƙwalla ce ya ji ta ciko ma sa idanunsa ya yi Saurin ɗauke ta da sauri sannan ya tura ƙofar gidan da sallama a bakinsa. Ba ta san ya shigo ba tana can ɗaki tana kuka. Har ya isa bakin ƙofar ɗaki. Ya yaye labulen ɗakin ya yi shiga da sallama a bakinsa. Kamar daga sama ta ji sallamarsa, a firgice ta ɗago kai tana kallonsa. Gani take yi kamar gizo ne yake yi ma ta don haka sai ta mayar da kai ta haɗa da guiwarta ta cigaba da rera kuka. "Ma'eesha." Ya kira sunan ta cikin nitsatstsiyar muryarsa. Wanda jin haka ya saka ta tashi da sauri ta faɗa jikinsa ta rungume shi. Ƙam ta haɗe jikinta da nashi ta ƙanƙame tamkar wani ne zai ƙwace ma ta shi. Kwantar da kanta ta yi a ƙirhinsa tana cigaba da rera kuka. Bayanta yake bugawa alamar rarrashi. Ajiyar zuciya ta sauke cike da samun mutuwar da ta daɗe ba ta ji ta ba. Wannan ne karon farko da jikinta ya hadu da na shi. Ji take yi kamar su dauwama haka har ƙarshen rayuwarsu. Tsawon mintuna goma suna a haka kafin ya janye jikinta daga nasa kafin ya ce. "Ki yi haƙuri ki daina wannan kukan haka nan, ya isa don Allah na dawo cikin ƙoshin lafiya ba abun da suka yi ma ni." Da gaske ba a bun da suka yi ma ka, ka tabbatar? To me ya sa suka dauke ka idan ba komai za su yi ma ka ba , meye amfanin hakan? Kana lafiya ba abinda ke yi ma ka ciw?" "Ina lafiya ba komai ba abinda ke yi ma ni ciwo kada ki damu." Ta dinga duban jikinsa ko za ta ga wani tabo amma babu, ta tabbatar ba abinda ya same shi ta saki murmushi tana cewa. "Alhamdulillah, na gode Allah ba abin da ya same ka." "Yunwa nake ji Ma'eesha ban ci abincin da suka ba ni ba." "To zauna bari na kawo maka abinci." Ta zaunar da shi bisa tabarma jikinta har rawa yake yi wajen zuwa zuba masa abinci. Ta zuba ma sa jallop ɗin taliyar da ta dafa, da kuma ruwan Lipton. W gabansa ta ajiye bayan ta tabbatar da ruwan Lipton ɗin ya yi daidai yadda zai iya sha sai ta kafa ma sa kofin a baki tana mai yin Bismillah. Ba musu ya bude baki yana sha. Kafin ta fara ba shi taliyar a baki. Yana ci har sai da ya ƙoshi. Ta sa baki ta fasa ledar pure water ta bashi ya sha. "Alhamdulillah." Ya furta yayin da ita kuma ta ce . "Ma sha Allah." ",Ke kin ci abincin kuwa?" "Yanzu dai zan ci tun da na gan ka cikin ƙoshin lafiya." Tausayin ta ya sake shigarsa cikin sanyin murya ya ce. "Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa tana fara cin abincin. *America/Washington DC* _Fahad_ Ambassador Fahad ya isa America da babban buri, ya wakilci Nigeria cikin gaskiya da mutunci. Tun farkon aikinsa yana nuna ƙwarewa da hikima wajen tattauna wa da shugabanni. Yana ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka tsakanin kasashen guda biyu. Ko da ta isa ƙasar shi kansa ya kasa samun mutuwar zuciya kan abun da ya yi wa Nadra. Ya kamata a ce ya kula da ita amma bai damu damar hakan ba. Ga kunyar iyayen nasa da yake ji, shi ya sa ya kasa kunna wayarsa ballantana ya kira Mama. Don ya san tabbas sai ta yi ma sa fadar abunda ya aikata. Hakan ya saka har dare ba bai samu damar kiran kowa ba har ya kwanta ya yi barci. Da Asuba ya tashi a gidansa dake America, ya zauna shiru yana shan coffee yana kallon saƙonnin da suka shigo daga Nigeria . A yau akwai muhimman taro da zai halarta. Da safe ya shiga ofishin jakadanci cikin nutsuwa. Ma'aikatansa suka gaishe shi cikin girmamawa. Ya fara duba takardu da rahotanni. Yana tambayar su game da matsalolin da ƴan Nigeria ke fuskanta a Amurka. Da rana ya je wani babban taro tare da jami'an gwamnati. A wajan taron ya yi magana cikin hikima da nutsuwa, yana kare muradun ƙasarsa. Duk wanda ya saurare shi zai fahimci matashin mutum ne ma mai ilimi da wayewa. Sai yamma ya koma gidansa a gajiye. Bayan sallar Isha'i yana zaune a falonsa da laptop ɗinsa da ya zuba wa idanu. Gajeren murmushi ya yi lokacin da ya kalle ta ta fito daga toilet tana ɗaure da towel. Ganin yadda ta tura baki ne ya ba shi dariya, kallon lips ɗin ta ya yi yana tuna irin tsotsan da ya yi ma sa. Yana kallon ta har ta shiga closet ɗin sa ta shirya, Inna na zaman jiranta ta fito ta ba ta breakfast ta fara sha. Daga nan ya rufe laptop ɗinsa ya lalubo wayarsa. Lambar Mama ya dannawa kira har ta katse ba ta ɗaga ba, a kira na biyu ne ta ɗaga tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam. Barka da warhaka Mama." "Yauwa Barka dai ya aiki?" "Alhamdulillah." "Sai yanzu ka ga damar kira kuma an kira ka baya shiga?" "Afuwa Mama ina tsoron ki yi ma ni faɗa ne." "Faɗa kam dole ne na yi ma ka shi, saboda ka yi a abun da za'a yi ma ka faɗa. Kai da bakinka ka faɗa ma ni cewa kai ba ka son yarinyar nan da aka aura ma ka ita, za ka sake ta ne ta je ta auri wanda take so. To akan wani dalili ne zai sa har ka yi gigin saduwar aure da ita idan ba ka son ta, ko ka canza shawara ne?" Duk da ita mahaifiya ce da nauyi ta yi ma sa wanann Maganar amma hakan ya dace don yanzu ba ta fahimci in da ya sa gaba ba." "Mama ni fa har yanzu ba na jin son yarinyar nan a zuciya ta. Kuma abun da ya faru tsakani na da ita ba yana nufin na fara son ta ba ne, kar ki manta ma su bin karuwau ai ba don suna son su ba ne, kawai suna biyan buƙatar su ne dan kau da sha'awar su da zaran sun biya buƙatar su shi kenan, wannan ba soyayya ba ne. To haka abinda ya faru tsakanina da Nadra wannan ai ba shi ne soyayya ba. Kawai dai na biya buƙatar kaina ne saboda ita ce kadai Allah ya halatta ma ni na kusance ta ba tare da na saɓa ma sa ba. Mama da ba don gudun aikata zunubi ba idan kika ga wayayyun ƴan matan da suke bi na ina guje ma su ai ko kallo wannan yarinyar ba ta ishe ni ba. Har yanzu na kara rabuwa da ita ne saboda mutuncin iyayenta amma ba wai don ina son ta ba. Yanzu abu guda na sani yanzu yake ɗan damuna daga jiya zuwa yau. Tun lokacin da mu'amalar aure ya shiga tsakani na da ita na ji na daina jin haushinta, yanzu tausayinta nake yi, ga shi tun da na zo ƙasar tunanin yarinyar ya ƙi barin zuciya ta har sai da na kalle ta na ji nutsuwa anya yarinyar nan ba mayya ba ce ta lashe ma ni kurwa a daren gabaɗaya tunanin ta nake yawan yi na kasa gane me ya sa." Murmushi Mama ta yi mai cike da ma'anoni kafin ta ce. "Wato saboda ba ka da kunya ni mahaifiyarka kake yi wa waɗan nan zantuka ko?" Dariya ya yi ya ce . "Mama yanzu fa ba zamanin baya muke ba, idan ban sani jiki na faɗa ma ki abun da ke raina ba da qa zan yi? " "Hmm" "Yauwa Daddy ya ce na kai yarinyar nan ta zaɓi motar da take so, tafiya ta kama ni ba tare da na shirya ba, don haka zan kira Aunty Rahama a waya su tafi tare da ita sai ta zabi wacce take so." "Okay ba damuwa, amma sai zuwa gobe ko jibi idan jikinta ya kara warware wa." Fira suka ɗan taɓa sannan suka yi sallama ya kashe kiran. _Sidra_ Shirya wa ta yi cikin riga da siket na leshi, ɗinkin ya kama ta yayin da duk surar jikinta suka kasace a bayyane. Shirin mayafi ta rataya a gefen kafaɗarta. Tana rike da handbag ɗin ta da wayarta a hannunta. Sai zuba ƙamshi take yi tana taku ɗai-ɗai da dogon takalmin ta ma su tsini, sai zuba ƙamshi take yi. A haka ta fito zuwa falon, Mama ce tare da Inna suke zaune a falon. Jin takun takalmi ya sa suka juya suna kallon gefen, a hankali take taku sautin takalmin na bada sautin ƙwas ƙwas ƙwas. Kayan jikinta Inna ta kalla ta taɓe baki tare da cewa. "Gwada da Allah ya sa jikana bai auri wannan yarinyar ba. Wani hanin ga Allah baiwa ne, sai Allah ya bashi kamilalliyar yarinya mai kunya." Mama dai ba ta ce komai ba har Sidra ta ƙaraso wajen. "Barkan ku da hutawa." Ta fada tana zama kan kujera. Mama ce ta amsa da . "Yauwa kin fito ko?" "Eh Mama." "Okay bari na sanar wa direba ya kai k" "No Mama na fi son na yi driving da kaina." "Okay, bari na ba ki mukullin motata." Mama ta tashi ta nufi ɗakinta don ɗaukowa Sidra Sidra mukullin motarta. Daidai lokacin Aunty Rahama ta yi sallama ta shigo, tana rike da hannun Baby Zahrah. "Wa'alaiki Salam warahmatullah. Ku ne a gidan yau ma saboda ba ku gaskiya da yawan fita ko?" "Eh na zo gaida ƙanwata ce Rumaisa ta kira ni ta sanar da ni wai Nadra tana nan gidan kuma ba ta da lafiya. Na ce mun yi waya da Mama amma ba ta faɗa ma ni ba." "Kai Rumaisa akwai gulma, Allah ya shirye ta." Mama ta faɗa tana mikawa Sidra key din motarta. Ta karba tana cewa. "Aunty Rahama Ina wuni?" "Lafiya lau Sidra kin zo duba ƙanwarki ce?" "Uhmm" Ta furta tana nufar kofar waje . Da kallo suka bi ta Inna ta ce. "Wa ya faɗa ma ki duba kanwar ta zo? "Nan Inna ta ba Aunty Rahama labarin korar da Mahaifin Sidra ya yi ma ta da yadda ta zo Babanku ya ce idan ya dawo zai kai ta ya ba wa Mahaifinsu haƙuri." "Allah ya kyauta." Aunty Rahama ta faɗa ta durkusa tana gaida Mama, sannan ta gaida Inna. Baby Zahrah ta zauna kan ƙafar kakarta. "Ina Nadra take ne?" Mama ta ba ta amsa da cewa. "Tana can ɗakin Yayanku?" "Can aka kai ta?" Inna ta yi saurin cewa. "Can dai jarababben ƙanin naki ya kai ta. Yarinyar da yake ta ikirarin baya so to tana can ya karɓi budircinta ya bar ta cikin wahala." Murmushi kawai Sidra ta yi ba tare da ta ce komai ba. _Nadra_ Tana zaune a bakin gado ta yi tagumi tana tunani, me ya sa har yanzu Aunty Sidra ba ta nemi in da take ba, me ya sa har yanzu ko wayarta ba ta kira ba. Wayarta ta ɗauka ta lalubo lambar Aunty Sidra ta danna ma ta kira. Daidai lokacin da Sidra ta shiga motar Mama tana shirin yi wa motar key kenan sai kira ya shigo wayarta. Ganin Nadra ce sai da ta yi tsuki kafin ta ɗaga ta ce. "Ya aka yi ne?" "Assalamu alaikum." Nadra ta yi mata sallama cikin sanyayyiyar muryarta. "Aunty kina cikin gidan nan kuwa?" "Idan ba na ciki akwai inda kika aike ni ne?" "Allah ya ba ki haƙuri. Dama na ga shiru ne ban gan ki ba tun shekaranjiya." "Me ya hana ki saukowa ƙasa?" "Ba na da lafiya ne?" "Me ya same ki?" Shiru ta yi ta kasa cewa komai. Dariyar bakin ciki Sidra ta yi kafin ta ce. "Wato na zo na gaishe ki ko hamshaƙiya mandiya farkar me gari." Ƙwallar da ya cika ma ta idanun ne ya samu nasarar zubowa. "Ya aka yi kika yi shiru munafuka maƙaryaciya maciya amana, kin yi zancen karya, kin yi alƙawari kin saɓa na yarda da ke kin ci amanar yardar da na yi ma ki. To ki sani wallahi wallahi wallahi ki sani ja da baya ga rago ba tsoro ba ne sake shirin faɗa ne. Don wanann abun ya shiga tsakanin ki da Fahad kar ki ɗauka na haƙura ina nan akan baka na dole ki tattara tsumman rayuwarki ki bani wajen da kike da zaman wuccin gadi." *Maman Ihsan ce.*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *SADAUKARWA* Wannan shafin sadaukarwa ne gare ki masoyiyar arziki AMMEY LAYLERH alkhairin Allah ya kai gare ki a duk in da kike. Allah ya bar zumunci masoyiya 🥰 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣5️⃣ Ya aka yi kika yi shiru, munafuka maƙaryaciya maciya amana, kin yi zancen karya kin yi alƙawari kin saɓa, na yarda da ke kin ci amanar yardar da na yi ma ki. To ki sani ja da baya ga rago ba tsoro ba ne sake shirin faɗa ne. Don wanann abun ya shiga tsakanin ki da Fahad kar ki ɗauka na haƙura ina nan akan baka na dole ki tattara tsumman rayuwarki ki ba ni wajen da kike zaman wuccin gadi." Cikin kuka Nadra ta ce. Aunty Sidra don Allah ki saurare ni ba yadda kike tunani ba ne, wallahi na fi kowa bakin cikin wannan abun da ya faru , ba da..." Salla rufe ma ni baki, da a baya ne idan kika fada Mani magana zan yarda, saboda na san ba kya yin ƙarya. Amma yanzu kin canza." "Wallahi ba karya nake yi ma ki ba, ba da son raina hakan ta faru ba, ko da kika ce na je ɗakin Mama na kwanta can na nufa. Ina zuwa ne na tarar da shi a cikin ɗakin Mama. Shi ya ce wa Mama ta ba ni fruit na kai ma sa. Na ce wa Mama ɗakinta zan kwana ta hana ni wai sai gobe idan mijina ya tafi. Ta ba ni fruit na kai ma sa. Kai ma sa da na yi ne ya ba shi damar isar da manufarsa a kaina. Ba yadda zan yi na yi iya ƙoƙarina don ganin na ƙwaci kaina amma ya fi ƙarfina bai bani damar hakan ba." Ta karasa maganar tana gunjin kuka. Cike da takaici Sidra ta ce. "Ko ma dai mene ne Fahad nawa ne dole ki bar ma ni shi. Majiya da ba ta ranmin kanta sai wani ya gina sannan ta shige." Tana faɗar haka ta katse kiran wayar tare da yi wa motar key ta bar gidan. Cikin sanyin jikin Nadra ta ajiye wayar tana cigaba da rera kuka. _Daddy_ Zaune yake a ɗakinsa ya saka hoton Mummy da Ma'eesha yana kallo. Ƙwalla ne suka cika ma sa idanunsa. Ya saka hannu ya goge . Shi sam ya kasa gane dalilin da ya saka baya iya taɓuka komai a cikin gidansa. Baya da kataɓus sai abun da Mamy ta ce yake zartarwa. Ga shi rashin Matarsa uwargidansa da ba ta duniyar da kuma rashin tilon ƴarsa da ya mallaka a duniya ya aurar da ita ga musaki faƙiri yana ji yana gani amma ya kasa komai. A hankali ya bude baki ya furta sunan Ma'eesha. "Ma'eesha. Ki yafe ma ni, ina ji a jikina ba daidai nake ba, kuma na san ban kyauta wa rayuwarki ba, na cutar da ke, na yi ƙoƙarin hana zuciya aikata hakan na kasa." Sai ya fashe da kuka. Motsin shigowa ɗakin da ya ji ne ya sa shi yin shiru ya kasa magana. Kansa a sunkuye ta shigo ɗakin, idanunta akansa ta na nazarin sa. "Alhaji." Ya kasa ɗago kai ya kalle ta. Ta kira sunan a kausashe wanda hakan ya saka shi ya ɗago kai ya kalle ta da sauri. "Yau ma keɓewa ka yi kana kuka ko?" "A'a Hajiya ba kuka nake yi ba." Taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Idan ma kukan kake yi wannan matsalar ka ce, ka je ka yi ta yi kai ne a damuwa. Yarinya tana gidan mijinta cikin kwanciyar hankali me ye za ka damu kanka?" Idan ita da damu da kai ai da ta zo ko sau daya ne ta duba ka. Amma ita ma sai ta zaɓi zama da wannan Makahon mijinta akan ka, da ba don haka ba ai da ta zo nan gidan idan tana son ganinka. Amma duk ka yi bi ka damu da ita bayan ba ta damu da ka kai ba." Ta karasa drawer da yake ajiye kuɗi ta ɗebi iya son ranta ba tare da ta ce ma sa komai ba ta fice. Da ido ya bi ta har ta fita daga cikin ɗakin. Tana fita ta nufi ɗakin ƴar ta Laila, wacce yanzu ita ke cikin ɗakin Ma'eesha. Wanda ya zama mallakin ta a yanzu. Tana kwance akan tangamemen gadon ta ɗora ƙafa daya kan ɗaya tana chatting. Inno wacce a baya ita ce mai yi wa Ma'eesha aiki, kamar gyaran ɗaki wankin toilet wankin kayanta da abin da ba'a rasa ba. Inno ta fito daga banɗaki bayan ta gama wankewa daidai lokacin da Mamy ta shigo cikin ɗakin. "Hajiya na sake wankewa." Yamutse fuska Laila ta yi tare da cewa. "Wannan karon ma idan na shiga na ga bai ma ni ba Tanko zai ɓaci. Fita ki bar mun ɗaki." Mamy ta raka ta da harara tana cewa. "Munafuka ta yi ta sunkuyar da kai ƙasa." Inno dai ba ta ce komai ba, tana takaicin yadda Laila sa'ar ƴar cikinta take wulakanta ta. Sau uku tana wanke banɗaki amma sai ta ce bai fita ba ta sake wankewa Ga shi haka za ta bar banɗakin da ƙazanta ko pad ta cire idan tana period nan take ajiye ma ta sai dai ita idan ta je wanke wa ta ɗauke. Ko period take yi nan za ta bar alama sannan ta kira Inno wai ta je ta gyara. Idan ko ta cire kaya nan za ta zubar da su ƙasa sai inno ta kwashe. Wanda lokacin da Ma'eesha take ɗakin ba za ka taba gane cewa tana period ba idan ya cire kaya sai dai ta ajiye a inda suka dace. Mamy ta kalli Laila ta ce . "Ga kudin na san dubu ɗari uku sun ishe ki ko?" Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ni har yanzu na kasa samun gatan da Ma'eesha ta samu a cikin gidan nan. Ita lokacin da take nan ai miliyoyin kuɗaɗe ne a account ɗin ta sai dai tayi ta zara tana bukatar ta, ki duba ranar da aka aura ma ta makahon nan irin miliyoyin kuɗin da aka cire a account ɗin ta. Amma ni kullum idan ina bukatar sai dai na yi magana ki ɗebo dubu ɗari biyu ko uku ki ba ni." Daga ƙafarta ta yi cikin sigar rarrashi ta ce "Ki kwantar da hankalinki da sannu zan saka ke ma ya bude ma an ki account ya zuba ma ki kuɗaɗe. Yanzu na kasa gane kansa ne kullum ckikin ƙunci yake. Kuma kin san Ma'eesha tun tana karama suke tara ma ta kudin lokaci guda ba ne suka saka ma ta." "To ina su gwala-gwalan nata da kika ce za ki kawo ma ni." Cikin damuwa Mamy ta ce. "Har yanzu na kasa gane in da ya ajiye gold din nan." Cikin takaici Laila ta tashi ta figi kudin ta zuba a handbag ɗin ta ta fice daga dakin bayan ta ɗauki wayarta. _Makaho_ Yana zaune a tabarma a barandar kofar ɗakinsu. Ma'eesha na zaune a gefen sa ta zuba ma sa idanu tana kallonsa. Ji ya yi a jikinsa ana kallonsa don haka ya ce. "Wannan kallon fa ba mene ne?" Murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce. "Idan ban kalli mijina ba waye zan je na kalla?" Dariya ya yi kafin ya ce . "Ba wanda za ki kalla sai ni kuwa, saboda ni ne na ki. Ni ma Allah ya nuna ma ni ranar da idona za su bude na kalli Matata farin ciki na." "Amin ya Allah." Ta faɗa tana murmushi, zuciyarta cike da farin ciki. Haka kawai take jin kanta cikin nishadi da farin ciki da walwala. Ɗan yamutse fuska ta yi tana cije lips ɗin ta. Tuna date ta yi ai yanzu ne lokacin period nata. "Inna lullahj wa'inna ilaihi raji'un." Shi ne kalmar da ta fada a cikin zuciyarta. Domin ita kadai ta san irin wahalar da take sha idan tana period. Don tana jin jiki sosai. Ga shi ko Naira biyar ba su da shi a cikin gidan nan, ballantana ta yi tunanin siyen magani da alluran da ake yi ma ta. Sallama suka ji yaro ya yi daga ƙofar gidan. Sai suka amsa a tare yarin ya shigo. "A bani gawayi na ɗari huɗu." Cewar yaron yana miƙa ma ta ɗari huɗu ƴan ɗari biyu guda biyu. Daga gidan Mallam Liman yake kasancewar A'isha ta yi wa Ma'eesha tallar gawayin wajen mutanen gidansu. Tana rike da mararta ta dafa su da hannu biyu. Ga yaron tsaye yana miƙa kuɗi. Ta kalle shi da idanunta da suka fara canza kala, kafin ta yi karfin halim cewa. "Aje kudin nan ka je ka ɗauka a wancan kitchen ɗin." Yaron ya ajiye ya nufi kitchen don ɗauko gawayin. Jin yadda ta yi magana ya sa Makaho cewa. "Ma'eesha lafiya kike kuwa?" Gudun ta tayar ma sa da hankali ya saka ta yin murmushi mai sauti ta ce . "Ba komai kada ka damu." Ta yi kokarin ganin murya ta ba ta yi raunin da zai gane ba . Yaron yana sai anjimanku, Makaho ne ya iya amsa ma sa. Makaho ya ce. "Kika ce idan anjima na ba ki labarin abun da ya faru bayan an sace ni ko? Yanzu zan ba ki labarin komai har zuwa dawowa ta." Tana jije lips cike da ƙarfin hali da dauriya ta ce. "Mu bari zuwa wani lokacin, yanzu bari na shiga na ɗan kwanta. "Kamar ba ki da lafiya." "Lafiya ga ƙalau." "Na san sai ba kya barcin yamma, don ke ma kin san bai da alfanu." Ba ta iya sake yin magana ba a daddafe ta shiga ɗakin ta zube kan katifa ta fara murƙususu tana hawaye. _Sidra_ Tana fita direct unguwar su ƙawarta Khadijah ta zame. A ƙofar gidan ta dinga danna horn. Maigadi ya leko bayan ya ga ko waye ne sa sai ya buɗe ma ta gate ɗin gidan. Bayan ta yi parking ne ta fito da sauri kasancewar ta san daidai wannan lokacin Mahaifiyar Khadijah ba ta gida ta je wajen aiki. Haka ta faɗa cikin falon a guje tana kuka. Khadijah na kwance kan kujera tana chatting kallo daya ta yi ma ta ta ɗauke kai, ci gaba da abun da take yi ta yi ba tare da ta kula Sidra ba. Ganin haka Sidra ta fisge wayar daga hannun Khadijah ta yi jifa da wayar saman ɗaya daga cikin kujerun da suke falon. Murmushin takaici Khadijah ta yi kafin ta ce. "Na san wannan ranar tana zuwa. Ranar da za ki zo kina yi ma ni kuka ba, irin haka na guje ma ki amma kika ƙi saurara ta kuma biye wa shawarar Sady baby. Ga shi yanzu ta kai ki ta baro. Gani kike yi kamar ita ce mai ƙaunarki, ko kiran ki na yi ba ki ɗaga wa, ranar da za ki gudu ba yadda ban yi da ke ba ko saboda mutuncin zuri'ar gidan ku da tozarta su da za ki yi. Amma kika ƙi saurara ta. Kin ɗauka za su jira ki ne sai kin dawo kafin a sake maganar daurin auren ko?" Murmushin takaici ta yi kafin ta ce. "Sai kuma kika yi saɓanin fahimta ya kasance aka aura ma sa ƙanwarki a madadin ki. Kuma na ji dadin hakan dama ita ce ta dace da shi." "Lallai Khadijah yau na san cewa ba ki so na ba ki ƙaunata, abun har ya kai haka? Ni kike taya wa farin ciki.?" "Da kin saurare ni hakan za ta faru ne?" "Duk wannan ya isa, so nake yi ki ba ni shawarar da zai sa Fahad ya zama mijina." "Wani kallon ba ki da hankali Khadijah ta yi ma ta kafin ta ce . "Kin taɓa ganin in da aka haɗa ya da ƙanwa zaman kishi su auri namiji daya su zauna matsayin kishiyoyi? Mu fa musulmai ne ba maguzawa ba." "Amma idan ya saki ƙanwa ko ta mutu zai iya auren yayarta ko?" "Eh zai iya. Amma an fi yi idan ƴar uwa ce ta mutu zai iya auren ƴar uwarta, amma idan ya sake ta ne tana raye akwai kunya ki auri mijin ƙanwarki." Wani kallo Sidra ta yi ma ta kafin ta ce. "Kunya, gaba na ba shi ba baya ba. Kuma duk hanyar da zan sai na bi shi wajen ganin na mallaki Fahad kamar yadda na sa wa raina cewa nawa ne shi kaɗai har gaban abada." "Hmmm Allah ya shirye ki." Ba ta sake magana ba ɗauki wayarta ta kira lambar wayar ƙawarta Sady baby. Bugu ɗaya ta daga tare da cewa. "Ƙawata." Sidra ba ta amsa ba ta ce. "Kina ina ne?" "Ina nan Kaduna." "Okay gani nan zuwa." "Allah ya sa lafiya don ni tsoron ki nake ji " "Ki kwantar da hankalinki mafita za ki ba ni." Tana gama fadar haka ta dauki handbag ɗin ta. Ko kallon Khadijah ba ta sake yi ba ta fice daga falon . Da kallo Khadijah ta bi ta tana yi ma ta addu'ar shiriya. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣6️⃣ "Ki kwantar da hankalinki mafita za ki ba ni." Tana gama fadar haka ta ɗauki handbag ɗin ta. Ko kallon Khadijah ba ta sake yi ba ta fice daga falon. Da kallo Khadijah ta bi ta tana yi ma ta addu'ar shiriya. "Allah ya shirye ki Sidra. Da na ga kin shigo kina kuka na dauka nadama kika yi ashe ba haka ba. Dama mahaukaci ba zai taɓa warkewa ba sai dai ya ji sauƙi." _Ma'eesha_ Tun da ta shiga ɗaki ta kwanta sakamakon canjin yanayin da ta ji ne ya sa Makaho shhga damuwa. Ya san ba haka take ba, duk da baya ganin ta amma ya san akwai abun da ke damunta, ko don yanayin maganar ta ma. Hankalinsa ne ya ji ya tashi domin baya son damuwarta, kullum yana son ganin ta cikin walwala, kamar yadda itaa take kokarin ganin ta faranta ma sa rai. Kullun zuciyarta cikin bakin ciki da damuwa take amma ta kan ari murmushi ta yafa a saman fuskarta don ganin ta ɓiye bakin cikin da take ciki. Domin akwai ciwo a zuciyarta. Musamman kan mahaifinta. Wani tausayin ta da ƙaunarta ya ji ya ƙara ginuwa a zuciyarsa. Ba kyawun fuska kawai namiji yake nema a soyayya ba. Akwai wasu abubuwa masu girma da suke gina zuciyarsa da kwanciyar hankalinsa. Idan mace ta fahimci waɗannan, zata iya rike soyayya cikin hikima. Girmamawa Girmamawa shi ne ginshikin zuciyar namiji. Namiji yana jin darajarsa ne ta yadda mace take mu’amala da shi, a gaban mutane da a ɓoye. Idan mace tana girmama shi, tana sauraron ra’ayinsa, tana kuma kula da mutuncinsa, hakan yana kara masa kwarin gwiwa da jin cewa yana da matsayi a rayuwarta. Rashin girmamawa kuwa na iya kashe soyayya ko da akwai kauna. Biyayya (cikin hikima da mutunta juna) Biyayya ba bautar mutum ba ce, a’a fahimta ce da haɗin kai. Namiji yana son mace da zata iya bin shawararsa, ta nuna yarda da jagorancinsa a wasu al’amura, musamman idan yana kokarin alheri a gare ta, Idan mace tana ta gardama a kowane lokaci, hakan na iya kawo zuciyarsa tayi nesa da ita, amma idan tana nuna biyayya cikin hankali da mutunci, hakan yana gina zaman lafiya. Fahimta da goyon baya rayuwar namiji tana cike da nauyi da ƙalubale. Yana bukatar mace da za ta fahimce shi, ta tsaya masa a lokacin wahala, ba wacce zata kara masa matsin lamba ba.Lokacin da ya gaji ko ya shiga damuwa, yana bukatar wanda zai kwantar masa da hankali, ya ji cewa ba shi kadai bane. Goyon baya daga mace yana kara masa ƙarfi da kwarin gwiwa a rayuwa. Idan namiji ya samu girmamawa, biyayya cikin hikima, da kuma fahimta daga wacce yake so, zuciyarsa zata zauna lafiya, soyayyarsa kuma zata kara zurfi. Soyayya tana dorewa ne idan bangarorin biyu suna bawa juna abin da zuciya ke bukata. Sandarsa ya laluba ya tashi a hankali ya fara tafiya har ya ji ya taɓo kofar ɗakin. Da sallama a bakinsa ya yaye labulen ɗakin ya shiga. Tana kwance akan katifarta ta dafe mararta tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta. Sosai idanunta ke tsiyayar da hawaye tana ambaton sunan Allah. Dama kowace mace akwai yanayin da period nata yake zuwa duk wata. Ita Ma'eesha takan yi fama da ciwon ƙasan cikinta kuma ciwon na ma ta tsanani. Lokacin al’ada, mace na iya jin abubuwa daban-daban a jikinta da kuma zuciyarta saboda canjin hormones. Da farko, yawanci ana jin ciwon ƙasan ciki (cramps), wanda wani lokaci yana iya zuwa har baya ko ƙafafu. Wasu matan ciwon nasu yana da sauƙi, wasu kuma yana iya zama mai tsanani. Haka kuma ana yawan jin gajiya da kasala. Jiki yana iya yin nauyi, kuma mutum ya fi son hutawa ko kwanciya. A bangaren yanayi kuwa, ana samun sauyin hali (mood swings). Wani lokaci mace na iya jin haushi, ko damuwa, ko kuma ta ji kuka ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba. Wasu kuma suna fama da ciwon kai ko ciwon jiki gaba ɗaya. Haka kuma ciki na iya kumbura (bloating), wanda ke sa a ji kamar ciki ya cika ko ya yi nauyi. Akwai kuma sha’awar wasu abinci (cravings), musamman kayan zaki ko abinci na musamman, kuma wani lokaci yunwa na ƙaruwa. Amma ya kamata a sani cewa ba duk mata suke jin abu iri ɗaya ba yana bambanta daga mutum zuwa mutum. "Ma'eesha lafiya kike kuwa?" Cije lips ɗin ta ta yi ta goge sun hawaye tana kokarin daidaita nutsuwarta da muryarta. "Na'am ka shigo?" Ta amsa cikin sanyin murya. Lalubar katifar ya yi ya karasa kai ya lalubo hannunta. "Me ke damun ki?" " Ba komai barci zan yi." "Amma kin san barci a irin wannan lokacin na yammaci ba kyau ko?" Kuka ne ya ƙwace ma ta sai ta faɗa jikinsa tana sakin wani sabon kuka. Kwantar da kanta ta yi a faffaɗar ƙirjinsa tana ci gaba da kuka. Shi kuma hankalinsa ya tashi zuciyarsa ta yi ma sa nauyi. Take idanunsa suka sauya zuwa ja. _Nadra_ Tun bayan da ta gama waya da Sidra ta take riskar kuka. Kuka take yi sosai ta rasa me ke yi ma ta daɗi. Daidai lokacin Aunty Rahama ta yi sallama ta shigo cikin ɗakin. "Subhanallah, me ya samu ƙanwata ce take kuka haka?" Sai a lokacin Nadra ta lura da ita ta yi saurin goge hawayenta. Ƙarasawa ta yi ta zauna gefenta, sannan ta dafa kafaɗarta ta ce. "Nadra." Sunkuyar da kai ƙasa ta yi tare da cewa "Ina wuni Aunty." "Lafiya lau ya kike ya jikin?" "Alhamdulillah." Ta amsa cikin sanyin murya. "Me ke damun ki ne kike ta kuka?" "Ba komai." "A'a akwai komai kam." Shiru Nadra ta yi ba tare da ya sake yin magana ba. Aunty Rahama ta kalle ta cike da ƙaunarta ta riko hannunta cikin nata cikin hikima ta ce . "Ina son ki dauke ni kamar ƙawar ki." Kallon ta Nadra ta yi cike da mamaki ta ce. "Ke fa babba ce." Dariya ta yi kafin ta ba ta amsa da cewa "Ai ba sai sa'arki za ki yi ƙawance da ita ba, ko wacce ta haife ki za ki iya ƙawance da ita ballantana wacce ta girme ki. Kasancewar ina matsayin yar mijinki ba yana nufin ki dinga jin kunya ta kina ɗauka ta sirikar ki ba. Ki ɗauke ni kamar ƴar uwarki ta jini. Na san cewa kina cikin damuwa idanunki ma ya nuna hakan. Idan bakin ki ya ɓoye damuwar da kike ciki to idanunki da da fuskarki ba za su yi karya ba. Na san dole akwai damuwa ki faɗa ma ni zan ba ki shawara. Kuma na yi ma ki alƙawari ba wanda zai ji abun da muka tattauna. Ko mahaifiyar da ta haife ni ba za ta ji komai ba, zan rike ma ki sirrinki domin ina ƙaunarki fisabilillah. Shiru Nadra ta yi domin kuwa tana buƙatar wanda za ta fada wa damuwar ta ko ta yi shawara da ita. A duniya dama mutane biyu ne abokan shawarar ta . Ummanta ce sai kakarta Ammi. To ga Umma kwance ba lafiya, ta ya za ta iya faɗa ma ta abun da zai tayar ma ta da hankali, sai kuma kakarta Ammi ,to ita kuma idan ta sanar da ita ta san za ta sanar wa Abba ne sai sun saka Sidra ta bar gidan nan. Amma ta ji hankalinta ya kwanta da Aunty Rahama. Shin ta faɗa ma ta damuwarta ko ta yi shiru? _Sidra_ Gudu take yi a saman titi kamar wacce za ta tashi sama. Tana driving tana jin ƙuna a ranta. A cikin ƙanƙanin lokaci ta isa gidan Sady baby. A waje ta yi parking motar ta sannan ta tura ƙaramar kofar ta shiga. Madaidaicin gida ne sai motoci guda biyu a harabar gidan. Knocking ɗin kofar falon ta shiga yi. Ta kai mintuna biyu har ranta ya ɓaci sai ga Sady baby ta buɗe ƙofar wani saurayi ya fito, kallo daya Sidra ta yi ma sa ta ɗauke kai. Murmushi Sady baby ta yi ma ta tana cewa. "Babban yarinya kin iso ?" Ba ta tanka ma ta ba ta shiga cikin falon. Taɓe baki Sady baby ta yi tabi bayan Sidra. Suna zama kan kujera Sidra ta watsa ma ta harara tana cewa . "Kin ga abun da kika janyo ma ni ko? Ga shi a dalilin bin ki na ina neman rasa Masoyi na wanda nake mafarkin mallakarsa a matsayin mijin aure na. To abinda ba zan yarda da shi ba kenan. Dole na same shi ta kowace hanya." "Yanzu ya kike so a yi?" "Na mallaki Fahad Majidaɗi." Shiru Sady Baby ta yi kafin ta ce. "Ƙanwarki da yake aure fa?" "Ya rabu da ita ya aure ni?" "Kina ganin iyayen ki da iyayen sa za su yarda da hakan kuwa?" "Ban damu da amincewar su ko akasin haka ba, abu ɗaya nake buƙata shi ne amincewar Fahad. Ko da ya amince idan iyayen sa suka hana shi fa zai hanu. Saboda yana da biyayya. Ko ƙanwarki ai ba don yana son ta ya aure ta ba, ya yi biyayya ne kawai. Hanya daya za mu bi shi ne Fahad ya amince da auren ki ya saki ƙanwarki, sannan iyayen ki da iyayen sa ba za su iya hana wa ba za su yi shiru kamar ba sa ganin komai. Amma hakan zai faru ne ta sanadiyar aikin da wani Mallami zai yi ma na." Wani kallo Sidra ta yi Sady baby kafin ta ce "Ni na je wajen wani neman taimako?" Girgiza kai ta yi kafin ta ce. "Is not possible." "To idan ba haka ba ban hango himmatuwar cikar burinki ba. " Wani dariya ta yi kafin ta ce . "Ba wani Boka ko Mallam da zan je wajen sa, domin duk maƙaryata ne, a baya sun yi ma ni aiki ba abinda na gani, kuma na saka wa raina ba zan sake bin kowane Boka ba." "Rally?" Kau da kai Sidra ta yi kafin ta ce . "Kawo wata hanya amma ban da wannan." "Okya ina da wata hanyar da za ki iya cika burinki na raba Fahad da Nadra amma ba lallai iyayen sa su yarda ya aure ki ba, kuma su iyayen naki ba za su ba ki auren sa ba." "Na yarda in dai zai rabu da ita, saboda idan ina kallon ƙanwata a matsayin matarsa zuciyarta za ta yi bindiga ne." "Okay raba su ba abu ne mai wahala ba, saboda ba wai suna son juna ba ne , dukkansu sun yi biyayya ne." "To ya za'ayi ?" "Na san yanzu baya kasar idan ya dawo sai ki zo mu fara shirya planning yadda shirin zai tafi cikin tsari." _Umma_ Zaune take a falonta tayi tagumi lokaci zuwa lokaci take goge hawayen da ya cika ma ta idanu. Kallon Abba wanda ya murtuke fuska take yi. "Abban Sidra." Ko kallon ta bai yi ba ballantana ya amsa. Sai da ta sake fada a karo na biyu sannan ya fara magana a kausashe "Sau nawa na faɗa ma ki ba ni da ƴa mai wanann sunan, ita ba ƴa ta ba ce a yanzu, daga ranar da ta zubar ma ni da ƙima na cire ta daga cikin zuri'ata. Na sha faɗa ma ki kada ki sake yi ma maganar yariyar nan kin kasa dainawa ko?" "Ba'a canza wa tuwo suna duk in da za'a je a dawo kai ne uban Sidra ba wanda ya isa ya sauya hakan. Ai hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar da shi." "Idan hannuna zai ruɓe tuni zan yanke shi na yar tun kafin ya fara cin sassan jikina." Cikin damuwa Umma ta ce. "Yanzu yadda ka kore ta ba ka tunanin halin da za ta je ta saka kanta a ciki? Kora ba shi ne mafita ga yaran da suka aikata kuskure a rayuwarsu ba, saboda za su iya shiga wani halin da ya fi wanda suka shiga aka kore su, don Allah ka bari a kira ta ta dawo." "Kin san wani abu?" Abba ya tambaya yana kallonta "Sai ka faɗa." "Daga yau kada ki sake tayar ma ni da wanan zanen." Yana gama fadar haka ya fice ya bar ta. Umma na kuka ta nufi part ɗin Ammi tana sa ran samun sassauci idan ta yi wa Abba magana a matsayin ta na mahaifiyarsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣7️⃣ Umma na kuka ta nufi part ɗin Ammi tana sa ran samun sassauci idan ta yi wa Abba magana a matsayin ta na mahaifiyarsa. Ammi da ke zaune tana waya da Gwaggo Laraba ta ji kukan Umma ta kashe wayar. Cikin tashin hankali ta ke cewa Umma. "Ke lafiya?" Cikin Muryar kuka Umma ta ce. "Don Allah ki saka baki Mahaifin Sidra ya yafe ma ta ko za ta dawo gida." Tsuki Ammi ta ja tana cewa. "Ba zan taɓa saka baki Abdullahi ya dawo da wannan gantalalliyar yarinyar ba." "Haba Ammi ke fa mahaifiyarsa ce ke, kuma ke kadai na san cewa za ki iya yi ma sa Magana ya saurare ki. Da zaran kin saka baki shi ke nan." "To ba zan saka baki akan wannan yarinyar ba, idan ya ga dama ya yafe ma ta wannan ra'ayinsa ne ta dawo ban damu ba, idan bai yafe ma ta na kuma ta yi ta zama a duk in da take. Akan me za ki damu da yarinyar da ba ta gujin ɓacin ranki. Yarinyar da ba ki isa ki saka ta ko ki hana ta ba, yarinyar da ba za ta faranta ma ki ba sai dai ta baƙanta ranki.Ni ba ruwana da sabgar ta tun can dama, ballantana yanzu. Ki shawo kan mijinki idan ya yafe ma ta shi ke nan." Cikin sanyin jiki Umma ta bar ɗakin Ammi ta rasa tudun dafawa. _Maeesha_ Murƙususu take ta yi a jikin Makaho cikin azabtar ciwon da take ji. Makaho kuwa jin yadda take yi ya san tana cikin mawuyacin hali ne. Alluran da da ya kamata a ce ta yi shi tun last month ne ba ta yi ba, wanda hakan y saka ta cikin wannan halin. Kasancewar dama alluran *Depo-provera* ne da yake yi kowanne wata uku amfanin alluran dama ana yin sa wajen rage ciwon mara lokacin haila muka yana daidaita haila idan tana da matsala, ciwon haila na raguwa sosai. Kuma alluran tana da tsada sosai fiye da painkillers. Ta san cewa ba za ta iya jure ciwon marar da take yi ba, don rashin kwanciyar hankali da nutsuwa ya sa ta mance da cewa duk wata uku alluran ke aiki, ga shi tun last month ya dace ta je likita ya yi ma ta amma ta kasa. Ta san cewa ba ta da kudin da za ta yi alluran kuma ba za ta iya jurewa ba. Cije lips ɗin ta take yi wanda sai da ta ji gishiri-gishiri alamar ta fasa lips ɗin ta da hakori ne. Wayarta ta laluba a nan kan katifar bayan ta zame jikinta daga na Makaho. Lambar wayar ƙawarta Nasreen ce ta nemo ta danna ma ta kira. Bugu biyu ta ɗaga tare da cewa. "Hello ƙawata ya aka yi ne?" Yadda ta ji saukar numfashin Ma'eesha ya sa ta ce . "Are you okay." Ba ta ba ta amsa ba sai sheshsheƙar kukan da take yi. Hakan ya saka Nasreen ta katse kiran wayar, dama tana driving ne za ta koma gida. Don haka ta juya akalar motar zuwa hanyar unguwar da Ma'eesha suke . A cikin mintuna goma ta iso kofar gidan, daidai lokacin da makaho ke rarrashin ta yana cewa maganin me zai siyo ma ta. Sallamar Nasreen ne suka ji wanda Makaho ne ya iya amsa wa. Cikin ɗakin ta shigo ganin halin da ƙawarta take ciki ya sa ta ji tausayin ta. Don a baya lokacin da ta ce wa Ma'eesha ta rabu da makaho ba sa'ar aurenta ba ne sun dan samu rashin fahimta, musamman da Nasreen ta ba Abdul adireshin gidan Ma'eesha ya zo ran Ma'eesha ya sake ɓaci da Nasreen. Sai yau da ta kira ta a waya. Ganin kayan jikinta ya fara ɓaci ya sa ta gane halin da ƙawarta ke ciki. "Oh my God." "Nasreen ta faɗa tana dafe goshi." "Mu je ki gyara jiki mu tafi asibiti." Ta taimaka ma ta ta tashi suka fita har banɗaki ta kai ta, sanan ta fito ta duba bokiti ta dauka sai a lokacin ta lura da ruwan zafi dake kan murhun gawayi. Don haka ta ɗebi ruwan zafin ta sirka ya ɗan yi ɗumi sannan ta kai ma ta a banɗaki. Bayan ta ajiye ma ta ta fito yana ƙarewa gidan kallo tana mamakin yadda Ma'eesha ke rayuwa a cikin wannan akulkin gidan. Wanda ko maigadin gidan uban Ma'eesha ya fi karfin wannan gidan. Taɓe baki ta yi tana cewa. "Idan ta gaji ko ta ga uwar bari da kanta za ta saka ya sake ta, na san dole za ta zo ta same ni da wanan zancen. Muje zuwa. Yanzu da ta dawo gidan mu kamar yadda na ba ta shawara da yanzu tana cikin rufun asiri, da gangan na ki taimaka ma ta da kudi na bar ta sai wahala ta koro ta. Tsuki ta ja a ƙasan ranta, zuciyarta cike da takaici. Motsin Ma'eesha dake fitowa tana dafe bango ne ya sa ta fito. Taimaka ma ta t yi suka shiga ɗaki. Akwatin kayanta ta buɗe ta duba pad wato audugar mata, da pant ta ba ta ta saka da ƙyar. Doguwar rigar material ta ba ya ta saka sai hijabin da ta saka. "Wani asibiti za ki kai ta?" "Ko ma wane asibiti ne ni na san wanda zan kai ta kuma ni zan kashe kuɗin ko nawa ne duk da ba a wuya na hakkokin ta suka rataya ba, idan ban da kankanba ina kai ina Ma'eesha alhalin ba za ka iya daukar ɗawaini..." "Ya isa haka Nasreen, ban kira ki dan ki ci zarafin mijina ba, yana da hakkin sanin in da za mu je, ke ƙafata ƙafarsa ko..." "Really? Kina cikin ciwon ma bakinki ba zai iya jure aci Mutuncinsa ba, tun da na zo kin kasa magana, amma akan mijinki kin yi karfin halin magana duk da maganar daƙyar take fita ma ki." Cikin jigatuwa Ma'eesha ta ce . "In dai akan kare mutuncin mijina ne zan yi." Cikin sanyin murya ya ce . "A'a Ma'eesha ki ji da kanki, ku tafi Allah ya dawo da ku lafiya ya yaye ma ki lalurar da ke damunki." "Idan tare da kai ba na fasa zuwa." Sanin halin Ma'eesha ya sa Nasreen ta ce. "Ku fita mu je." Sandarsa ya laluba suka fita a tare. Duk da bai so bin su ba, amma bai so zuwa ba don dai Ma'eesha ta ce dole sai da shi za su tafi. Bayan motar ta bude ma su da taimakon ta Ma'eesha ta shiga ciki har lokacin tana dafe da kasan mararta tana hawaye. Makaho ya zauna gefenta yana ma ta sannu . Nasreen ta yi wa motar key suka bar unguwar. Wani tsadadden asibiti suka nufa. Asibitin da Ma'eesha ke zuwa ganin likita. Daidai lokacin kuma Doctor Irfan likitan da yake duba Ma'eesha ya fito daga office ɗin sa. Ganin Ma'eesha ya sa ya tsaya yana kallonta da mamaki ya ce. "Hajiya Ma'eesha lafiya?" Kallo ɗaya ya yi ma ta ya gane matsalar, don haka ya ce . "Me ya hana ki zuwa akan akan lokaci?" Wai Nurse mata biyu ya kara ya da suka shigar ma sa da Ma'eesha ciki Kallon Makaho ya yi kafin ya ce . "Yaushe aka fara bari mabarata suna shigo ma na asibi..." Kasa karasa maganar ya yi sakamakon jin Muryar makaho. "Ni ba mabaraci ba ne, ban taɓa nema a wajen kowa ba, don ina makaho ba shi zai ba ku damar wulakanta ni ba, ba don lalura ba ine zai kawo ni asibitin nan?" "Doctor tare muke da shi kada ka damu." Bai sake magana ba ya bar wajan don zuwa duba Ma'eesha. Wani ma'ikacin asibitin ne ya zo wuce wa, ganin Makaho ya sa ya taimaka ma sa ya zauna, kasancewar akwai kujerun zama a wajen. _Nadra_ Haka nan take jin za ta iya yarda da Aunty Rahma. Don ta rasa da waye za ta yi maganar ta ji sanyi. Kallon Sunyi Rahama dake sakar ma ya murmushi ta yi kafin ta ce. "Aunty wai da gaske na ci amanar Aunty Sidra?" "A'a ba ki ci amanar ta ba, waye ya ce kin ci amanar ta?" "Na ga yata ce uwa daya uba ɗaya, kuma ita ce take soyayya da Yaya Fahad suke son juna, wata ƙaddara ta saka ta bar garin a ranar aurenta da Yaya Fahad. Ita a tunanin ta idan ta idan ta tafi za'a dakatar da ɗaurin aure sai bayan ta dawo sanann za'a ɗaura. Amma iyayenmu suka kasa hakuri suka ce ba za su fasa daurin auren ba sai sai za su ɗaura da ni a madadinta. Wallahi Aunty Rahama ban san cewa aure na aka daura da Yaya Fahad ba, na ɗauka cewa da ita aka ɗaura ma su, sai dare ake sanar da ni wai ta gudu an maye ma sa gurbinta da ni. Ba ni da yadda zan yi ba dan yi jayayya da hukuncin iyayena ba, dole na yi masu biyayya. Na zauna da shi da niyyar idan ta dawo ya sake ni ya zauna da ita, saboda tare suka tsara rayuwarsu. Amma bayan ta dawo sai na lura da ita take son sa amma shi kamar ya fitar da ita daga rayuwarsa. To tun da har yanzu tana son sa ai bai dace a ce na cigaba da zama da shi ba ko?" Dariya sosai Aunty Rahama ta yi kafin ta ce. "Ke ba ki son sa ne?" Tura baki gaba ta yi tana cewa. "Ni ina da wanda nake so?" "Auzubillahi. Kina da aure kina maganar akwai wanda kike so? To ki daina ba kyau." "Shi ma Yaya Fahad ɗin fa baya so na, da kansa ya ce zai sake ni wai na je na auri shashashan wanda yake so na, Ya sayyadi yake kira da shashasha." Yadda ta yi maganar ne ya sake ba Aunty Rahama dariya sosai. "To na ji, amma ya fada ne ba zai sake ki ba." "Wallahi da kansa ya ce zai sake ni kuma ba da wasa yake yi ba, baya so na sai ya dinga ce ma ni wai ban waye ba bagidajiya ce ni, sanann Aunty Sidra tana ca ma ni wai Yaya Fahad baya son bak'ar mace sai fara kamar ta. "Ƙarya ne wannan , shi a familynsa ba bakake ne , ko mahaifinsa baki ne da sai ya tsane shi ko ya?" Shiru Nadra ta yi kafin ta ce. "Ki taimake ni ya sake ni sai ya auri Aunty Sidra." "Ba zai yiwu ba, Fahad na da ɗabi'a daya, idan ya so abu bai same shi a lokacin ba to abun ya kan fita ransa duk son da yake yi ma sa kuwa. Ko aka ja masa rai kafin a ba shi abu to yakan yi zuciya da shi ne. Don haka idan ba wani karfin ikon Allah ba to ya hakura da Sidra kenan. Kuma na tabbatar zai so ki kuma ke ma za ki so shi. Ba don yana ƙanina ba ne amma na tabbata ba macen da Fahad zai ce yana so ta ce ba ta son sa karya ne, don ya hadu ta kowane fanni, ke ba ki jin son sa?" "Tab ni kan ba na son sa kuma ba zan taba son mutum mugu mara imani irinsa ba." "Fahad ba mugu ba ne, abun da ya ma ki kowace mace cikakkiyar budurwa takan tsinci kanta a yadda kika tsinci kanki, sai dai ya danganta da yadda kowane namiji yake zuwar wa matarsa. Na san bai kyauta ba tun da ya tafi ya bar ki a cikin wanan halin, amma ki yi ma sa uzuri ba haka kawai y tafi ba, tafiyar dole ce ta kama shi." Nisawa ta yi kafin ta ce . "Ya jikin naki?" "Da sauki." "Ma sha Allah, an ce na kai ki za ki zabi motar da kike so, Baba ne ya ba su ki gift." "Aunty ba sai na je ba na ba ki zabi kowacce ne kika samu indai ta yi ma ki to ta yi ma ni." "Kin ba ni zaɓi?" "Eh." "To shikenan sai kin ga sako, sannan zan kawo ma ki wasu sabulai na wanka da maiyukan shafawa da wasu magungunan gyaran jiki da za ki dinga amfani da su." "Gyaran jiki kuma su ne har da na sha?" ",Eh haka suke, anjima zan dawo in sha Allah. Ko akwai abun da kike so ne?" "Ba komai na gode." Sallama ta yi ma ta sannan ta fice daga ɗakin. A ranar da yamma sai ga Aunty Rahama ta kawo galleliyar motar da ta zaɓawa Nadra,sai ɗaukar idanu take yi. Sannan ta shako manyan ledoji guda biyu na kayan gyaran jiki na ciki da waje. Daidai lokacin Sidra ta yi horn maigadi ya wangale ma ta gate, ta shigo da motar Mama da ta fita da ita, idsnunta ta sauke akan galleliyar motar dake sheƙi da daukar idanu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣8️⃣ Daidai lokacin Sidra ta yi horn maigadi ya wangale ma ta gate, ta shigo da motar Mama da ta fita da ita , idanunta ta sauke akan galleliyar motar da ke sheƙi da ɗaukar idanu. Cike da mamaki ta furta . "Mercedes Benz G Class ?" Ba ta gama cika da mamaki ba sai da ta ji muryar Aunty Rahama na cewa. "Sidra ga motar ƙanwarki ta iso." Cike da basarwa da kokarin danne bakin cikinta take murmushin yaƙe. "Ta yi kyau sosai na taya ta murna." Tana faɗar haka ta karasa wajan motar. Mota ne da mata ke so, tana da karfi sosai da nuna Class (matsayi) Ƙare wa motar kallo ta yi duk da ba z ta iya cewa ga kudin motar ba, amma ta san cewa an kashe miliyoyin kuɗi. Aunty Rahama ta fito da ledojin kayan gyara da ta siyo wa Nadra. Sidra ta bi ta da kallo har ta shiga ciki sannan ta mara ma ta baya, sai dai idanunta na kan Sunyi Rahama sakamakon ganin ta zagaya ta ƙofar da zai shigar da ita part ɗin Fahad ba tare da ta ji cikin main falon gidan ba. Cije lips ɗin ta na kasa ta yi kafin ta tura kofar falon ta shiga ciki. Da fara'a Aunty Rahama ta shiga cikin part ɗin Fahad. Kayan da ta siyo ne ya ya ma ta bayanin yadda ake amfani da su . Key din motar ta karkaɗa wa Nadra. "Motarki ta iso Farin ciki Nadra ta nuna kafin ta yi wa Aunty Rahama godiya. Sai da ta tabbatar ta saka Nadra ta fara shan magungunan nan na gyaran jiki sannan ta bar ta. Downstairs ta nufa da niyyar sanar wa su Mama motar Nadra ta iso. Mama da inna ne kawai a main falon suna fira. Sallamar Sunyi Rahama ne ya ba su mamaki don ba su san ta dawo gidan ba. Bugu da kari kuma ga shi ta fito daga part ɗin Fahad. "Ke dama har yanzu kina cikin gidan nan?" Cewarsu Inna bayan ta ɓalli goro ta tauna. "A'a yanzu na dawo, na kawo wa Nadra motarta ne?" "Ma sha Allah." Inna da Mama suka hada baki wajan fadar haka. Tashi suka yi Inna na mita ciwon ƙafa da take yi ya sa ta gaba. Suna isa harabar gidan sai ga Rumaisa da Farida sun shigo gidan. Su biyu ne a bayan motar yayin da direba ke driving nasu. Suna fitowa suka ga su Mama wajen motar Nadra suna addu'ar Allah ya kare ya sa ya more. Farida kam ko wajan ba ta karasa ba ta yi shigewar ta ciki yayin da Rumaisa ta karasa wajen motar cikin farin ciki. "Wow wanann motar na mata ma su aji ne. Na taya ta murna wallahi dama ni ma a siya ma ni irinta." _Ma'eesha_ Tana zaune bayan an kammala ma ta allura ne Nasreen ta shigo. Kallonta ta yi da alama ta samu saukin ciwon marar da ke damunta. "Ƙawata ya jikin naki?" "Da sauƙi" Murmushi ta yi tana cewa. "Na ga alama ai." Doctor ne ya kalle ta ya ce. "Za ku iya tafiya yanzu. Amma ki dinga kula sosai, sai nan da wata uku sai ki sake dawowa." "To Doctor na gode sosai." Nasreen ne ta kalli Doctor ta ce. "Shi ke nan ko?" "Eh ai ba wani abun da ya rage kin riga kin biya kuɗin." Godiya suka yi ma sa, suka fice. A in da Makaho ya zauna a suka same shi, Ma'eesha ce ta karasa in da yake zaune ta yi ma sa sallama. Ya amsa yana miƙewa tsaye rike da snadarsa. "Ma'eesha ya jikin naki." Murmushi mai sauti ta yi tare da cewa. "Alhamdulillah na ji sauƙi sosai sai abun da ba za'a rasa ba." Farin ciki ne ya ziyarce shi ya furta kalmar Alhamdulillah. A tare suka fito Nasreen na gaba su suna baya sun jera a tare suna tafiya. Bayan sun shiga motar ne Nasreen ta yi wa motar key suka bar asibitin. Har ƙofar gida ta sauke su, suka fita ta yi ma su sallama, Khalifa ya nufi cikin gidan, Ma'eesha ta tsaya tana yi wa Nasreen godiya sannan ta shiga gidan, Sa da ta shiga Nasreen ta ja motarta ta bar kofar gidan. *BAYAN SATI ƊAYA* Baba ya dawo daga tafiyar da ya yi da kwana biyu kenan ya ce wa Sidra ta shirya don ya kai ta ta ba wa Abba hakuri. Ita kam ba ta so hakan ba don tana zaune gidan ne saboda Fahad. Tana so da zaran ya dawo za ta ɗana tarkon da take ganin shi ne tsakanin da zai kai ta ga masoyinta Fahad Majidaɗi. Ba yadda ta iya haka ta shirya cikin shiga ta kamala da mutuntaka. Don ranar hijabi ta sanya a saman doguwar rigar amtamfar da ke jikinta. Sallama ta yi wa mutanen gidan in da Nadra ta rako ta har wajen motar Baba. Sai da suka bar gidan ta koma ciki tana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Abba ya yafe ma ta. Sai dai addu'ar ta ba ta karɓu ba, domin Abba shafa ma idanunsa toka ya yi ya ce sam ba zai karbi Sidra ba ya riga da ya yafe ta a matsayin ƴarsa. Duk yadda Baba ya kaɗa ya ya raya Abba ya ƙi. Domin shi kaifi ɗaya ne, idan ya faɗi magana ya fada kenan ba zai taɓa sauya wa ba. Sidra har ga Allah ta ji dadin hakan a zuciyarta sai dai ba ta bari hakan ya faru ba, don dai kukan karya take yi. Don Abba bai faɗa wa su Umma zancen zuwan na Baba ba, saboda ya san Umma za ta tayar da hankalinta. Don haka a ɓangaren baƙi ma ya sauke Alhaji Umar Majidaɗi. Duk wani motsi na Sidra Abba na lura, domin ya san wace ce Sidra shi ne mahaifinta. Ya fahimci duk wannan kukan wasan kwaikwayo ne, ba ta yi nadama ba murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi lokacin da ya ga tana murmushi. Ita kuma ba komai ya saka ta yin murmushi ba, sanin cewa za ta koma Familyn Majidaɗi, dole ne ta samu kusanci da Fahad da familynsa. Haka Baba ya dawo da ita gidansa, ya yi wa iyalansa bayanin yadda suka yi da Abba. Ya ce Sidra za ta ci gaba da zama a gidan ba wani lokaci har zuwa Allah ya sazuciyar Abba ya yi sanyi. Ya kuma nuna ma su yanzu an zama daya kasancewar ko ba abota yanzu akwai surukantaka aure ya haɗa an zama dangi. Ga Nadra nan tana matsayin sirikar gidan kuma Sidra yarta ce. Haka rayuwa ta cigaba da gudana a cikin gidan, Sidra ta saki jiki da Nadra ta ja ta a jiki sosai, ta nuna ba komai yayin da ta gama duk wani shirin da za ta aiwatar dawowar Fahad kawai take jira don ta aiwatar da shirinta. Don yadda take jin haushin Nadra da kishinta yanzu ta daina ji. Don ta lura kamar Nadra ba ta gaban Fahad bisa la'akari da ko kiran wayarta baya yi. Ko messages baya tura ma ta, hakan ya sa ta ji sanyi a ranta tana ganin ai ba ta gabansa. Saboda kullun sai sun yi waya da ƴan gidan, wata rana ma video call suke yi, zai gaisa da Mama, Baba, Inna, Rumaisa, da Farida. Ko tana Wajen ba zai taɓa cewa a ba ta waya ba, kuma ba zai taɓa tambayar ta ba. Hakan na damun Mama amma ba ta taɓa yi ma sa Magana ba ta zuba ma sa idanu, ta san ta in da za ta kama shi. Ita kanta Nadra hakan na ma ta ciwo a zuciya, duba da yadda ya yi ma ya ya saka kafa ya bar ƙasar bayan ya san tana cikin mawuyacin hali, bai taɓa tambayar ta ya jikinta ba ballanta ya yi ma ta sannu. Amma tana addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya za ta ba shi mamaki. Haka take ta rayuwa a gidan ba tare da ta nuna tana da damuwa ba. Ga kayan gyaran jikin da Sunyi Rahama ta kawo ma ta Inna tana sa ma ta idanu don ganin tana amfani da su. Sabulai ma haka da su take amfani har da man shafawa. Hakan ya sa ta yi kyau fatar jikinta sai ƙyalli take yi ta yi kyau kamar ba ita ba, baƙar fatarta dama mai kyau ne sai ta kara kyau. Sai dai abin da ba ta sani ba duk abin da take yi akan idanunsa take yi, don yana kallonta daga can in da yake. Idan ya dawo yana zaune baya komai zai yi ta aikin kallonta, duk abinda take yi. Yana mamakin yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba. Haka zai shagala yana kallonta, musamman da yawan tunanin yarinyar ke addabar sa. Haka nan kawai begen ganinta yake yi da son jin muryarta, Mama jin kansa ya hana ya kira wayarta ko ya ce ba ta waya su yi magana. Amma tunanin tariyar ya hana ta sukuni. *BAYAN WATA UKU* Ana gobe Fahad zai dawo ƙasar ne ya kira waya ya sa Mama ta sa ma'aikata su je su gyara ma su gidansu. Mama ta gama sauraren sa tana kare da waya a kunnen ta kafin ta ce . "Yaushe kake so a gyara ma ka gidan?" "Yau nake so, sanan Rumaisa ta bi su ta gyara ma na bedroom." Shiru kawai Mama ta yi tana tunanin yadda za ta ɓullo ma sa akan halin ko in kula da ya nuna wa Nadra. _Ma'eeaha_ Tana zaune gaban murhun gawayi ta haɗa tagumi, tunanin ta a abun da za su saka wa cikinsu take yi. Tun jiya ba su da abincin da za su ci, kuma ba su da kuɗin siye. Don hatta gawayin da za ta kunna babu ya ƙare. Tashi ta yi ta shiga ɗaki ta dauko farar leda sosai wacce suka siye garin kwaki rabin mudu. Shi suka sha jiya daddare suka kwanta. Yau da safe suka sha koko wanda ko sugar babu. Garin ta ɗiba a kofi ta ɗauki ɗaurin gyaɗar hamsin da ya rage, ta raba gyadan gida biyu ta ɗauki rabi sannan ta ƙulle sauran. Bayan ta jiƙa garin ta zuba gyaɗa tana sha tana ɓata fuska kamar mai shan magani. Sallamarsa ta ji yo daga ƙofar gida bayan ta kammala shan garin. Ta amsa ma sa tana yi masa sannu da zuwa. Ya shigo gidan hannunsa ɗaya rike da sandarsa dayan hannun kuma rike da basket kayan gyaran takalminsa. "Sannu da zuwa." "Yauwa ya gidan?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Karɓar kayan gyaran takalminsa ta yi ta ajiye gefe. Sannan ta ɗebo ma sa ruwa ta ba shi ya sha. "Ya kasuwan?" Ta tambaye shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa. "Alhamdulillah zan ce, amma yau kam ma kamar jiya, ko mutum ɗaya bai kawo gyaran takalmi ba haka ba gaji da zama na dawo." Murmushi ta yi tana cewa. "Ba komai, kada ka damu duk abin da ba ka samu ba to ba rabonka ba ne, Allah ya kara ma na wadatar zuciya." "Amin Ma'atussaliha Allah ya yi ma ki albarka." "Amin mijina." Sauran garin rogo da ta rage ne nake sha bari na jika ma ka naka." Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya sake magana ba, amma kallo ɗaya za ka ma sa ka gane cikin damuwa yake. Garin ta jika ma sa ta kawo ma sa bayan ta zuba ma sa sauran gyaɗa. Bayan sun gama sha ta ce . "Dama ina son na sanar da kai an kwantar da mahaifiyar Rumaisa asibiti, idan ka amince zan je na duba ta." "To bari na yi wanka sai mu tafi tare." Ya fadi haka yana miƙewa tsaye. Ta zuba ma sa ruwan wanka ta kai ma sa banɗaki.. Kofuna da suka yi amfani da shi ta wanke ta koma ta zauna. Tana nan zaune kan tabarma har ya fito wanka ya shiga ɗakin, sai da ta tabbatar ya shirya ta shiga da sallama. Kayan jikinta take kokarin ragewa lokacin da ya fice daga ɗakin. Yana zaune a barandar kofar ɗakinsu rike da sandar jagoransa, ta fito ta yi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar rigar Abaya mai ruwan toka, ta yi rolling kanta da mayafin. Fitowa ta yi hannunta rike da wayarta. "Na shirya yallaɓai." "To ranki ya daɗe." "Ka san ba mu da kuɗin abun hawa ko?" "Ba damuwa zan iya tafiya a ƙafa ke nake tunani." "Mu je ai ba mu da nisa da asibiti. Amma fa ka ajiye sandar nan zan rike hannunka har mu tafi." "To ba Kya jin kunyar idanun mutane?" "To ba mijina ba ne?" "Eh haka ne, amma ai su iyayen ƙawarki fa?" Ɗan jim ta yi kafin ta ce. "To rike sanadarka mu tafi." Ta yi maganar tana dariya. A tare suke tafiya gwanin sha'awa, har suka kai asibitin kasancewar ba su da nisa da Asibitin da unguwar su. Kasancewar Nasreen ta yi sanar da ita in da aka kwantar da mahaifiyarta ya sa ta nufi wajen kai tsaye. Mahaifiyar idanunta biyu Nasreen na ba ta magani tana sha. Sai wasu mata guda biyu. Da ƙawayen Ma'eesha su uku. Sai kuma mahaifin Nasreen. Bayan sun gaishe su tare da yi ma su ya jiki suka amsa cikin dakin fuska. Kasancewar duk sun san Ma'eesha kuma sun ji labarin auren nata da makaho. Don haka suka zuba ma ta idanu suna yi ma ta kallon tausayi. Khalifa ya ma su sallama ya fice yana jiran Ma'eesha har sai ta fito su tafi. Ganin kallon da ake ma ta ya sa ba shiri ta yi masu sallama za ta tafi. Mahaifin Nasreen ya ba ta 10k ta ki karba sai da ya nuna ɓacin ransa ta amsa tana godiya. Ta yi farin ciki da kuɗin kasancewar ba su da kudi ba su da abinci. Ko da ta sanar wa makaho ya ce Allah ya saka da alkhairi. Bayan fitowar su daga cikin wata ɓakar mota ta fara bin bayan su. A hankali motar ke tafiya tana bin su, sai dai matukin motar ya yi parking motar ya fito yana bin bayansu, kasancewar hanyar da suka bi mota ba za ta iya bi ba, don hanyar tafi sauri ya sa ba su bi titi ba. Sai dai hanyar ba mutane sosai. Idan sun ɗan yi tafiya kadan makaho sai ya tsaya. Kafin ya cigaba da tafiya. Ita dai Ma'eesha ba ta ce komai ba. Daidai lokacin da wani mai keke nape ya biyo ta gabansa. Makaho ya sa hannu ya tare shi, sai ya tsaya yana cewa. "Ina za ku je?" "Ma'eesha ki shiga ya kai ki gida." Da mamaki ta kalle shi kafin ta ce. "Kai kuma fa." "Kada ki damu zan kula da kaina." "Ba zan bar ka kai kaɗai ba." Tsawo ya daka ma ta yana cewa. "Na ce ki shiga!" Yadda ya daka ma ta tsawa sai da ta firgita ba ta san lokacin da ta shige ba. Tana shiga ya yi wa mai nape alama da hannu ya tafi, take ya ja keken suka bar wajan. Suna tafiya ya cire baƙin glass ɗin dake idanunsa ya juya bayansa cike da karsashi yana jifan mutumin da ke bin su da wani mugun kallo wanda da sai da hantar cikinsa ta kaɗa. Baya ya fara ja kafin ya juya zai gudu, tsalle ɗaya Makaho ya yi ya dira a gabansa. Shaƙo wuyansa ya yi cike da ƙaraji yake cewa . "Kai har kana da zarrar da zan ka dinga bibiya ta?" Idanunsa sun firfito waje saboda shaƙar da ya yi ma sa. Daidai lokacin wayar mutumin dake gaban aljihun rigar suit ɗin sa ta fara ruri. Sake shi ya yi sannan ya zaro wayar dake gaban aljihun suit ɗin mutum yana kallo. MADAM shi ne sunan da ta bayyana akan screen din wayar. Amsa kiran wayar ya yi sannan ya yi ma sa da alama ya yi magana. Kafin ya yi maganar suka ji muryar me kiran na cewa. "Ka ga fitowan su daga asibitin ko har yanzu suna ciki, sannan na ce ka yi mani bincike akan yarinyar da ka tura ma ni photon su kwanaki ta rike ma sa hannu suna tafiya, meye a tsakanin su, kuma shi da yarinyar ne yau ma suke tare ko wata ce daban?" "Duk ita ce Madam." Ya yi maganar yana kallon idsnun makaho. "To ka tabbatar daga yau zuwa gobe ka samu duk wasu bayanai kafin ka bar garin nan." Cike da ɓacin rai da takaici makaho ya cije leɓansa na kasa wanda sai da ya Fahe jini ya fito." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page4️⃣9️⃣ Cike da takaici da ɓacin rai da takaici makaho ya cije leɓansa na ƙasa wanda sai da ya fashe jini ya fito. Sannan ya saka hannu ya katse kiran wayar mutumin. "Duk wani shirin ku ina sane da shi, kuma duk bibiya ta da kake yi na sani, daga kai har sauran mutanen da suke bibiya ta na san komai, ni ba shashsha ba ne. Wato har ka tura ma ta da photon mu ko?" Shiru ta yi yana kallonsa da idanun sa da suka kaɗa suka yi ja. "Wato kai ne me zarrar da kake bibiya ta ko? Har ja ɗauki photon mu ka tura da shi ko? Akan aikina ma sai an saka ma ni idanu ?" Cike da tsoro mutumin yake kallonsa, ganin da ya yi ya ma sa kama da mayunwacin zaki. "Idan har kana son rayuwarka da ladiyarka to ka fita daga cikin wannan sabga, domin kuwa shine zamanka lafiya, idan ba so kake yi na binne ka da ranka ba. Idan kuma kaƙi ji ka cigaba da bibiya ta ko yarinyar da ka ganni da ita , sannan ka nemi sanin alƙar da ke tsakanina da yarinyar ka sanar ma na ta to fa ka sani shi ne kuskure mafi muni da za ka tafka a rayuwarka." "Ka gafarce ni yallaɓai ni ma umarni nake karɓa ba yin kaina ba ne." Cikin ƙaraji makaho ya ce . "Shi ya sa na ce ma ka ka daina." "Ba zan iya ba yallaɓai domin ina dai akan Madam ne raina fansa ne a gare ta." Wani gajeren murmushi makaho ya yi kafin ya ce . "Shi ke nan za mu gani." Ya yi maganar yana saka ƙafarsa ɗaya ya kwashe ƙafafuwan mutumin wanda hakan ya saka ya zube a saman guiwoyinsa da ƙarfi, wanda sai da ya saki wata ƙarar azaba, don ji yake ba yi kamar guiwoyinsa sun daina aiki." Makoho yana huci ya bar wajen, yana mai mayar da baƙin glass din sa ya ɗauki sanadar jagoransa ya fara tafiya yadda makafi ke yi. Tun mutumin na ganinsa har ya ɓacewa ganinsa, har lokacin ya kasa miƙewa ya tashi. _Ma'eesha_ Sam hankalin ta ya kasa kwanciya, ganin yadda makaho ya shi ne ya daka ma ta tsawa cikin wata iriyar Muryar da ba ta san yana da ita ba. Da ba ita ya yi wa ba ko ba a gabanta aka yi ba da sai ta ce ba Khalifa mijinta ba ne ya yi ma ta wannan tsawar. Don za ta iya cewa ko mijinta ko yatsa aka saka ma sa a ba su ki ba zai an iya cikawa ba, amma yau ta ga a abun da ya ba ta mamaki sosai ba kadan ba. "Hajiya ina za mu je ne?" Ta yi zurfi cikin tunani sai da ya sake magana sannan hankalinta ya dawo jikinta, ta sanar da shi in da zai kai ta, don dama ba su da nisa da Asibitin da suka je. Bayan ya sauke ta ƙofar gida ne cikin kudin da mahaifin Nasreen ya ba ta ciki ta ba shi dubu ɗaya, ya ba ta canji ɗari biyar kasancewar ita kadai ya ɗauka. Ƙofar gida ga nufa ta bude kofar langalangan su ta bude . Ta shiga gidan bakinta dauke da sallama. Zama ta yi saman barandar ɗakin ta haɗa tagumi. Tana jiran shigowarsa. Jin shiru ne ya sa ta kira wayarsa don ta ji lafiyarsa amma sai ya kasance wayar na gida. Don ta ji sautin wayar a cikin ɗaki. Hankalinta ya kasa kwanciya tuna kwanakin baya an sami waɗanda suka yi garkuwa da shi, cikin ikon Allah ya kuɓuta. Har ta ji an kira sallar Magrib sannan ta tashi ta yi alwala ta fara gabatar da sallah. _Makaho_ Da Kafa ya ƙaraso unguwar yana tafiya yana saƙa abubuwa da yawa aransa. Yana shigiwa unguwar ana kiran sallar Magrib, don haka ya tsaya ya gabatar da sallar Magrib a cikin jam'i a masallaci ya yi sallah. Bayan an idar jama'a sun fara watsewa me Mallam Liman ya karasa gaban Makaho. "Assalamu alaikum Mallam Khalifa." "Wa'alaikium Salam Mallam Liman kai ne?" Liman ya mika masa hannu akan su yi masabaha. Bayan sun gaisa ne Mallam Liman ya bar Khalifa zaune, har lokacin ɗaxu yake ji. A ransa. Don haka ya fara karatun alƙur'ani mai girma. Kuma ya ji sa'ida a cikin ransa, don kaso hamsin na baƙin cikin da yake fama da shi ya ragu. Bayan an yi sallar Isha'i ne ya tashi ya nufi hanyar gida. Da sallama ya shiga cikin gidan. Ma'eesha dake zaune kan sallaya ta fito da sauri tana kare ma sa kallo. Kasancewar akwai wutar nepa. Hannayen sa duka biyu ta rike tana cewa. "Kana lafiya ko? Me ya faru ne ka ce na dawo kai na ga ka tsaya? Bayan cewa a tare suke tafiya kafin y aikata wannan abu . "Kada ki damu kawai na tausaya ma ki ne ya saka na yanke shawarar je ki Hau keke nape ni zan je da ƙafa. "Amma me ya sa za ka wahalar da kanka bayan akwai kudi a hannuna?" "Kada ki damu na dawo cikin ƙiahin lafiya. Don a masallacin unguwar nan ne na yi sallar Magrib sa Isha'i. "Alhamdulillah." Ta faɗa tana ja ma sa hannu suka shiga cikin ɗakin. Bayan sun zauna a tabarma ne ta kalle shi tana yi ma sa sannu. "Ka san ba mu da abinci a gida nan , lokacin da na dawo gidan ba na da nutsuwa da na girka ma na wani abun. Amma yanzu bari na siya indomiee na girka ma na zai fi sauki." "Sannu da ƙoƙari Allah ya ma ki albarka." Sai a lokacin ta lura bakin Khalifa ya fashe. Cikin tashin hankali ta kai hannu ta kan fuskarsa tana cewa . "Subhanallah me ya same ka ne?" "Kada ki damu ina cikin ƙoshin lafiya. Kamar za ta yi kuka ta ce. Bakinka da ya kumbura." "Eh ba damuwa ba zafi ai, hakori na ne ya ya datse leɓen." "Haba mijina kamar ƙaramin yaro ne mai z ka datse baki haka?" Bai ce komai ba, ita ce ta tashi tana cewa ina zuwa yanzu xan dawo." "Ina za ki je a daren nan." "Zan siyo indomie ne nan shagon waje." Jinjina kai kawai ya yi ba tare da cewa komai ba.. _Nadra_ Tana zaune a part ɗin Fahad kamar yadda ya bar ta har tsawon wanan lokacin ita ke rayuwa a ɓangaren. Kasancewar ta har yanzu ta kada sake wa da mutanen gidan sosai. Tana yi ma su kallon surukai take yi ma su. Sallamar Mama ce da Aunty Rahama suka shigo falon. Bayan ta amsa ma su sallama. Ba ta yi mamakin ganin Aunty Rahama ba kasancewar ta ji ana firan daowarasa kuma sai shirye-shirye ake yi a cikin gidan. Gaishe da Mama ta yi ta amsa sannan ta gaida Aunty Rahama. Ita ma ta amsa tana ƙara jinjina kayan gyaran jikin da take kawo ma ta. Mama ta kalli Aunty Rahama tana cewa. "Ki tabbatar da ta tattara komai na ta an mayar da su ɗakina, sannan ita ma ta biyo ki kamar yadda na ce." "To Mama, ki ɗan turo ma na daya daga cikin ma su aikin nan ko da Laraba ce ta zo ta taya mu kwashe kayan." "Kin san baya son ma su aiki na shigar ma sa ɗaki ko?" "Eh ta tsaya ƙofar falo." "Okay." Mama ta amsa tana fita. Aunty Rahama ta kalli Nadra ta ce. "Yar gatan Mama, Mama ta ce ku tattara komai na ki za ki koma ɗakinta da zama. Ki yi Sauri za mu fita." Cikin fadin ciki Nadra ta fara tattara duk abin da ta san nata ne." Aunty Rahama ta fara fita da akwatunan kayan tana kai wa bakin kofar falo,sai Laraba ta dinga ɗauka. Sai da suka gama fitar da komai sannan Laraba na kashewa tana sauka da su sannan suka fito. Kai tsaye ɗakin Mama suka nufa suka tarar ta jera akwatunan a in da ya dace Da sallama suka shigo Mama ta amsa sannan ta ce. "Ya kamata yanzu ku tafi ko?" "Eh Mama yanzu za mu tafi." Ta juya tana kallon Nadra kafin ta ce . "Ƙanwata shirya za mu je gyaran gashi kuma ayi ma ki lalle." "To Aunty Rahama na shirya hijabi kawai zan saka." "Okay saka mu tafi." Dogon hijabinta ta saka, kasancewar yanzu ta daina saka dogon hijabin da ta saba sakawa a gida. Hakan ya faru ne saboda taimakon Aunty Rahama don sai da ta yi da gaske sannan Nadra ta daina yawo da hijabi a gida. Don gara ta dinga bayyana adonta ga mijinta ba kullum zama da hijabi kamar mai takaba ba. Bayan ta shirya suka fita tare, a motar Aunty Rahama suka je. Gidan sai ƙamshi girke-girke ake yi na tarbar Fahad. Bayan kamar awanni biyu da fitar su ne suka dawo gidan. Bayan an tsara wa Nadra Lalle me kyau zaben dukawar baƙi da ja aka yi ma ta. Dai gyaran gashi kasancewar ba ta cika son kitso ba ita. Sosai ta yi kyau ga gashin ya zubo sai sheƙi da wani kanshi take yi. Wanka ta yi addu'a lokacin da ake kokarin zuwa ɗauko shi a airport. Da taimakon Aunty Rahama ta shirya tsaf, cikin wani tsadadden leshi ɗinkin riga da siket ya ɗan kama ta, ya zauna ɗagwas a jikinta. Ta so saka Abaya Amma Aunty Rahama ta hana ta ce ta bar shi wanan ya fi ɗaukar hankal, kuma ba kowane namiji a gidan. Dole ta bar shi. A don ranta ya so ba . Wani turare ta fesa ma ta a jiki wanda shi na musamman ne. Horn suka ji daga bakin gate wanda hakan na nuna sun iso, Rumaisa da Farida suka je tarbon sa,. A tare suka fito daga bayan motar sun saka shi a tsakiyar suna ta farin ciki. Mama da Sidra ne a falon suna farin ciki da shigowarsa. Sidra ma ta ci kwalliya cikin dogon rigar atamfa ɗinkin fitted goun ɗinki ya matse ma ta jiki. Yana shigiwa suka mike tsaye ya karasa ya Side hug ya yi wa Mama sannan ya karasa wajen Inna dake zuwa ita ma ya yi ma ta yana dariya. Sidra ta gaishe shi ya amsa a yabo ba fallasa. Sannan ya nufi part ɗin sa da tunanin ko Nadra na can. Su Rumaisa suka bi shi da kayan part ɗin sa suka ajiye a falo. A tunanin sa Nadra na bedroom amma ya ga ba ita ba komai nata. Bincike ya yi a CCTV camara ya ga komai. To ina suka kai ta ko dai tana sabon gidansa ne da aka gyara jiya. Da wannan tunanin ya yi wanka ya fito, shirya wa ya yi cikin ƙananan kaya sai zuba ƙwmshi yake yi . _Ma'eesha_ Kafin ta je ta siye indomie sai da ta fara zuwa Chemist ta siye wa makaho Khalifa magani na rage zugin ciwo sannan ta tsaya ƙofar wani gida da ta ga an ɗaura gawayi a leda suna ajiye a kofar gidan. Ta siye gawayin wajen yaran da ke kofar gidan sannan ta nufi shago ta siyo ma su indomie da ƙwai biyu ta nufi gida. Ta same shi a tsaye a tsakar gidan rike da sandarsa, ya amsa sallamar da ta yi. "Lafiya na gan ka tsaye haka?" "Bayan ki zan bi na ji ko lafiya daga nan zuwa Wajan me kanti siyen indomie na ji shiru, shi ne na ce bari na bi bayan ki ko lafiya kika daɗe?" "Na ke Chemist na siye ma ka magani ne, na tsaya na siye gawayi kafin na zo wajen mai Indomie." "Allah sarki to na gode ƴar aljannah." Murmushi ta yi ta ajiye kayan a kofar ɗaki, maganin kuma ta mika ma sa shi . "Me zan taya ki da shi ne?" "Ba komai ka zauna ka huta idan na gama sai kawai ka ci." Kujera ta ajiye ma sa a tsakar gidan tana cewa. "Bari na ajye maka kujera ka huta muna fira har na gama." Ta taimaka ma sa ya zauna kan kujerar, ita kuma tana huta wuta har ya tashi ta wanke tukunya ta ɗira ta zuba ruwa, da kayan Hadi, ƙwani ɗin ma ta saka shi bayan ta wanke su don su ma dafaffe za su ci ƙwan. Har ta gama suna fira sai dai ta lura tun da ya dawo baya da walwala da alamar damuwa a tare da shi. Sai dai ta danganta hakan da ciwon da ke bakinsa ne. Har ta gama ta ɗora ma su ruwan wanka da za su yi idan sun kammala cin abinci. Pure water ta ɗauko cikin leda ta ajuye ma su, sannan ta shimfida tabarma ta ajiye abincin jan tabarma ta taimaka ma sa ya dawo kan tabarma ta ajiye ma sa abincin a gabansa. Suka fara ci don dama ta riga ta ɓare ɓawon ƙwan, baya jin cin abinci amma haka ya daure ya ci sakamakon idan bai ci ba za ta shiga danuwa, shi kuma baya son damuwarta. Bayan sun gama ta ba shi magani ya sha da ruwa. "Bari na zuba ma ka ruwan wanka ko?" Tashi ya yi ya shiga ɗakin ya duba kayansa ya ciro jallabiya wacce idan ya yi wanka ita zai saka a banɗakin. Koda ya fito ta hada ma sa ruwan ta kai ma sa, shiga ya yi ita kuma ta fara wanke-,wanke. Bayan ya fito ita ma ta shiga ta yi wankan nata. Yana ganin ta fito ya fito cikin ɗakin don ya ba ta damar shirya wa ta saka kaya. Da kallon mamaki take bin sa har ya fice. Ta rasa gane dalilin da zai saka a duk lokacin da za ta cire kaya ko za ta saka kaya sai ya fita ya bar ma ta ɗakin. Bayan shi ba gani yake yi ba to meueye amfanin fitarsa tun da bai da idanun ganin jikinta. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣0️⃣ Da kallon mamaki take bin sa har ya fice. Ta rasa gane dalilin da zai saka a duk lokacin da za ta cire kaya ko za ta saka kaya sai ya fita ya bar ma ta ɗakin. Bayan shi ba gani yake yi ba to meye amfanin fitarsa tun da bai da idanun ganinta. Rigar barci ta saka riga riga ce iya guiwarta ba ta da hannu sai na singileti ta saka sai turaren da ta fesa. Fitowa ta yi ta gan shi tsaye ya jingine sandarsa a bangon ɗakin ya tura hannayensa duka biyu cikin jallabiyar da ke Jikinsa yana kallon sararin samaniya. Da dukkan alamu ya yi zurfi cikin tunanin da yake yi. Kallonsa ta yi na wasu daƙiƙu kafin ta ƙarasa wajensa tana murmushi. "Lafiya ka zo nan ka tsaya kuwa?" "Lafiya lau, me kika gani?" "Na ga daga fitowa ta wanka ka yi saurin fitowa daga ɗakin." "Na ba ki waje ki shirya ne." "To ni ban damu da ka fito ko kana nan ba, domin ko na cire kaya a gabanka ai ba gani na kake yi ba to me ye amfanin fitowarka?" Murmushi kawai ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa. "Mu koma ciki to." Ta yi maganar tana jan hannunsa zuwa cikin ɗakin ɗayan hannun ta ɗauki sandarsa. Tunani yake yi a zuciyarsa yadda Ma'eeha ta kamu da son sa. Duk da ba ta san shi waye ba daga ina ya fito, duk da nakasar sa da halin talauci da yake nuna ma ta ba ta taɓa nuna ma sa wani abu da zai tabbatar ba ta son sa ba, kullun halin da take nuna ma sa a aikace shi ne nuna soyayyar ta a gare shi. Zama suka yi a tabarmar da yake kwanciya akai. Tana fuskantarsa duk da shi kansa kasa yake kallo don daga ita sai rigar barci wacce ko gama rufe guiwarta ba ta yi ba. Kuma kanta ba ɗankwali babu ta tufke gashin kanta. Wayarta ce ta soma ruri ta ɗan mika hannu ta dauki wayar. ASP Nasir ne ke kiran wayarta. Sam ita ta ma mance da shi, kuma ta san kiran nasa yana da nasaba ne da zancen ɓatar mijinta da ta kai rahoto, tun da ya ce za su yi bincike zai su neme ta. Har wayar ta katse tana tana tana tunani, har sai da Makaho ya ce ma ta. "Ba kiran wayarki ake yi ba?" "Eh kira ne ya katse." Daga haka bai sake yin wata magana ba, sai wani kiran ya sake biyowa baya. Ɗaga wa tayi tare da yin sallama. "Assalamu alaikum warahmatullah." "Wa'alaiki salam." "Ina wuni ASP ." "Lafiya lau, ya kika ji da fargaba?" "Alhamdulillah." "Kin ji ni shiru ko, to sai dai na ce ki kara hakuri muna nan muna bakin iya ƙo..." Murmushi da ta yi ne ya saka ya yi shiru, don ya san in dai Ma'eesha da ta zo station na su cikin tashin hankali tana kuma na ɓatar mijinta ce bai kamata yanzu ace tana wannan murmushi ba sai dai idan ya dawo su ba su sani ba." "Ya dawo gida ne?" "Eh ya dawo gida yanzu haka yana kusa da ni." Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ya ce. "Na taya ki murna." "Na gode sosai." "Idan ba damuwa zan iya tambayarki ?" Ta san zancen da zai ma ta, saboda ta ga mamaki da tarin tambayoyi akan fuskarsa ranar da ta je kai rahoton ɓatar mijinta. Don haka ta ce na sa. " Yanzu barci nake ji." "Okay good night and sweet dreams." Daga haka ta kashe kiran wayar. Ta kalli Makahon mijinta ta ce. "Police ɗin da na kai ma sa rahoton ɓatar ka ne yake kira na." Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce . "Amma da dukkan alamu ba ranar da kika kai rahoton ba ne kika fara saninsa. Dama can kun san juna kuma akwai alaƙa a tsakanin ku." Kallon mamaki take yi ma sa yadda ya iya fahimta cikin sauƙi. Shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da cewa. "Lokacin da na ɓata har wajen police kika je kai rahoto." Murmushin ta yi kafin ta ce. "A lokacin da ka bata na shiga tashin hankali sosai ba kaɗan ba, na shiga makamancin tashin da na shiga lokacin da na rasa mahaifiya ta. Domin a wanan duniyar ba ni da kowa sai kai ka na mayar fitila ta kuma madubin dubawa ta, idan na rasa ka ban san inda zan tafi ba. Don ba zan iya rayuwa ni kaɗai ba, mahaifiyata Allah ya dauke ta, mahaifina ya juya ma ni baya. Ya nuna baya bukatata danginsa na sun juya ma ni baya. A baya duk da kakata Hajiya Turai da ta haifi Babana ba ta son mahaifiya ta, amma ni tana so na sosai, amma lokacin da mahaifina ya juya ma ni baya ita ma sai ta juya ma ni baya. Ban san inda dangin mahaifiyata suke ba, ban san in da zan samo su ba." Ta yi maganar tana goge hawayen da ya gangaro ma ta. "Ita mahaifiyarki ƴar ina ce?" Tamabayar da ya yi ma ta kenan yana jin ba dadi a zuciyarsa. "To an ce dai ƴa gidan marayu ta tashi, a ziyarar da kakana je kaiwa gidan marayu yana raba ma su kaya da abinci ne wata rana suka je da mahaifina gidan marayun in da ya ga mahaifiyata ya ce yana son ta. Wanda dalilin haka ya sa kakata Hajiya Turai ta tsani mahaifiya ta saboda rashin sanin asalinta." Kamar an fama ma ta in da ke ma ta ƙaƙayi sai kuka take yi har da sheshsheƙa. Shi ya ma rasa me zai ce ma ta da in da zai rarrashe ta. Don shi sam bai iya rarrashin da daɗaɗan kalamai ba. Ɗan bubbuga bayanta ya yi alamar rarrashi, a hankali take dauke ajiyar zuciya. Bayan wasu mintuna ta ce "Har yau ban san tarihin rayuwarka ba, daga ina ka fito su waye iyayen ka suna raye ko ba su raye ban sani ba. Kuma ya kamata na san komai game da mijin da nake aure. Idan ƴaƴan da aka damu da su ne ko aka san danginsa ai ba za'a taɓa aurar da su ga Mutumin da da ba'a san asalin ko waye shi ba an yi bincike ina danginsa suke ba. Amma ka ga ni ba su damu da ko ɗan yankan kai ne ba sun ba da ni sun huta." Ta yi maganar cikin ƙunar rai. Tunawa ta yi da yadda Mamy ta shigo rayuwarsu, da yadda Mummy ta karɓe ta ba tare da sanin mugun nufin da ta zo da shi ba Yau da gobe ba ta canja kowa, sai dai yau da gobe na bayyana ma ka haƙiƙanin mutane. A hankali take tuna rayuwar ta ta baya tana zubar da ruwan hawaye. Shi ma Makaho a nasa bangaren tunanin da yake yi daban ne Soyayya na bukatar wani matsayi na karfi da kulawa tana bukar ɗauakar ɗawainiya ba wai kawai rabon damuwa ba. Shi kam zai iya cewa ta wannan ɓangaren ya gaza yin duk waɗan abubuwa. Amma ita har yanzu ba ta taɓa ganin gazawarsa ba. "Ka ɗan bani taƙaitaccen tarihin rayuwarka ma na." Sai da ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya dake bai nuna hakan ba. "Na tamabaye ka kwanakin baya akan sanin asalinka amma ba ka sanar da ni ba, kuma ya kamata na san da wa nake zaune, kamar yadda ka san tarihin rayuwata ban ɓoye ma ka ba, wanda ko yau ka tamabaye ni wani abu a shirye nake da na sanar da kai." "Babu wani abun birgewa a cikin sanin tarihin rayuwata, ba na son tunawa ne shi ya sa ban sanar da ke ba, ki bari idan lokaci ya yi zan sanar da ke." "Haba wani lokaci kuma zai yi, aure fa muka yi ya kamata na san wani naka ko wani abu naka." Shiru ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara magana. "Sunana Khalifa kamar yadda kika sani, Ni na fito ne daga Jahar Maiduguri a wani ƙauye muke rayuwa da iyayena da dangina duka a kauyen muke. Ina nufin kowa nawa yana cikin ƙauyen. Ni dama ko da aka haife ni da laluran makanta aka haife ni, ma taso ina raywai ni kaɗai ne ba tare da abokai ba, kasancewar ba na gani sai dai idan yara na wasa na kan je nisa da su na zauna ina sauraren su. Don ni ne na fari sai ƙanina guda ɗaya da nake da shi. Mukan yi wasa da shi a gida musamman idan mahaifiyarmu ta hana mu fita takan ce mu yi wasa mu biyu a gida, hakan ya sa ƙanina ya daina fita wasa shi ma. Sai dai shi an saka shi makarantar boko wanda Ni kuma iya makarantar islamiyya aka saka ni. Ina da shekaru ashirin wani iftila'i ya faɗawa ƙauyen mu na rikicin ta'adda ci in da aka kashe mafi yawan ƴan ƙauyen mu. Daga baya kuma gobara ta tashi a kauyen in da aka yi asarar rayuka da yawa har da iyeyena da ƙanina da sauran dangina na uwa da na uba. A ƙwauyen ɗaiɗaiku ne ba su da yawa. Daga nan kowa ya dinga watse wa ana barin ƙauyen, wanda ni ma na bi sahun wasu har na tsinci kaina a garin nan. Kuka sosai Ma'eeha ke yi tana tausaya ma su, sai dai ita tana da abu ɗaya, idan mutum ƙarya ya faɗa taka ji a ranta cewa ƙarya ne, shi ya sa lokacin da Mummy ta kawo Mamy gidan nan ba ta goyi bayan ta ba, kamar ta san abun da ke faruwa a kasar zuciyarta. Haka wannan labarin na makaho duk da ta tausaya ma sai dai a kasar ranta, take ji kamar kada ta amince don haka ta ce. "Wannan maganar da ka yi Mani na tarihin rayuwar ka idan na gane cewa ƙarya ne to ka sani za mu samu matsala da kai. Na tsani karya da cin amana, idan mutum ya yi ma mi daya daga cikin su ma nakan ji na tsani mutum. "Kina tunanin ƙarya na yi ma ki?" "Ban ce ka yi ma ni karya ba, na dai faɗa ma ka ne don ka sani." _Fahad_ Zaune yake a dinning table shi da mutanen gidan, an loda ma sa kalolin abinci. Inna, Baba, Mama, Rumaisa, Farida, sai kuma Sidra. Sai kalle-kalle yake yi ya rasa ta ina Nadra za ta ɓullo. Mama na lura da yanayinsa kuma ta harbo jirginsa. Tsakuran abincin kawai yake yi ya kai wa baki amma ba wai don ya shirya cin abincin ba ne. Sidra kan idanunta kur akansa ta zuba ma sa idanu kamar za ta cinye shi. Sautin takalmi ne suke ji alamar ana zuwa waje da suke. Da sauri Fahad ya juya yana kallon wajen. Aunty Rahama ce da Nadra suka gani suna nufar dinning table idanun Fahad kur akanta ko ƙyafta idanun baya yi. Da sallama suka ƙaraso wajen, gabadaya suka amsa ma su sallamar. Zama suka yi kan kujeru biyu da suke jere wanda ba kowa akai. Nadra ta gaida su suka amsa ma ta, yayin da ɗaya daga cikin ma su aikin ta fara sevin din su. Ko da wasa ba ta ɗaga kai ta kalli in da Fahad yake ba. Shi kuma idanunsa na kanta, tambaya kasa yake yi. Ya aka yi ta yi wani haske ta washe, ga fatarta sai ƙyalli take yi, ta kara cika ta zama babbar mace. Ɗaga kansa ya yi ya kalli Mama, yaga shi take kallo. Kansa ya mayar kasa yana cigaba da cin abinci nasa. Nadra ma ba wani cin abincin kirki ta yi ba ta tashi ta nufi ɗakin Mama. Yana ganin ta shiga cikin ɗakin, ya mike tsaye yana cewa. "Alhamdulillah." Farida da Rumaisa suka ɓata fuska Farida na cewa . "Ya ba ka ci abincina ba, Ni na dafa ma ka abincin don na burge ka fa?" "Ayyah sorry anjima ki ɗumama ma ni zan ci." Murmushi ta yi tana cewa. "Zan saka ma ka a microwave oven na kawo ma ka shi." "Yaya nawa fa ba ka ci ba." "Ke ma har da ke?" "Jinjina ma sa kai ta yi." "Me kika dafa ma ni?" "Faten doya." Yadda ya yamutse fuska ne ya saka mutanen dake wajen yin dariya. Takaici ta ji wanda ganin haka ya sa ya ce. Zai ci ita ma. Wanda hakan ya sa ta saki ranta ta daina jin haushi. Hankalinsa na kan Nadra da ta nufi part ɗin Mama. Don haka part ɗin ya nufa kai tsaye. Tana zaune kan kujera tana tana chatting da wata mata da Aunty Rahama ta haɗa su a waya, ita ce Aunty Rahama ke siyen kayan gyaran jiki a wajen ta tana ba wa Nadra. Kuma Aunty Rahama ta sanar wa matar halin da Nadra ke ciki. Kuma matar tana ba ta shawarwari. Wanda ta taimakon su ne ma Nadra ta daina sigar manyan hijabai da take yi a baya. Yanzu ma tana sanar wa matar ne dawowan Fahad. Duk da tana son ta rabu da shi ne sa koda yayarta na son da har yanzu, sai dai matar da Aunty Rahama suna ɗora ta akan hanyar da za ta mamaye zuciyarsa ne. Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar ma ta da faɗuwar gaba, wanda hakan ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi. Yana tsaye ya zuba ma ta Mayun idanunsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page 5️⃣1️⃣ Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar ma ta da faɗuwar gaba, wanda hakan ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi . Yana tsaye ya zuba ma ta mayun idanunsa. A hankali takowa ya fara yi zuwa gabanta cikin takunsa na ƙasaita. Miƙewa tsaye ta yi sai dai ta kasa kallon cikin idanunsa. Har sai da ya matso dab da ita. "Ba ki ga na dawo ba ne?" "Na gani." Ta faɗa tana kallon gefe fuskarta ba walwala." "Okay kin ganni amma ba ki iya gaishe ni ba? Saboda kin raina ni ko saboda me? Saboda kin ga gadon barcina ko?" Kafin ta yi magana Mama ta turo ƙofar ta shigo. "Lafiya?" Komawa bayan Mama ta yi tana kuka, shi kuma ya saki baki yana kallonta da mamakinta. "Me ka yi ma ta?" "Ba abun da na yi ma ta. Na zo ne na sanar da ita ta tattara kayanta za mu koma gidanmu." Wani kallo Mama ta yi ma sa kafin ta ce . "Ta tattara me?" Sanin ba magana mai daɗi zai fito daga bakin Mama ba ya sa ya juya ya fice daga ɗakin. Don baya son Mama ta yi ma sa fada gaban wanan yarinyar. Tana fita Mama ta kalli Nadra wacce daga kukan shagwaba zuwa na gaskiya, sakamakon jin Fahad ya ce za su koma gidansa wanda ita kam ba za ta so hakan ba. "Mama zan zauna tare da ke ba zan bi shi ba." "To kada ki damu kina tare da Mamanki ." Nan ta cigaba da rarrashinta har sai da ta saki jiki. "Shiga ɗaki ki kwanta ki huta." "Ba musu ta nufi bedroom ɗin Mama dan ta kwanta. Sai da Mama ta ga shigarta sannan ta nufi ƙofar fita. A corridor da zai sada ka da part ɗin Mama ta same shi tsaye ya rungume hannu a ƙirji ya zuba wa ƙofar idanu. "Lafiya kuwa?" "Mama wai me kike nufi da ni akan wanan yarinyar ne, na ga ta takan raina ni ne sannan kina goyon bayanta." "Au haba? Zaginka ta yi ko me?" "Na shirya ta zo mu koma gida." "Ba in da za ta je." "Saboda me Mama?" "Tun da ka bar ƙasar nan ka tafi daidai da sau ɗaya ka taba kiran ta a waya ka ji lafiyar ta? Ko ka taɓa tamabayar wani cewa ya take, ba ka san da ita ba sai yanzu da ka dawo ne take da amfani a wajen ka? To bari ka ji ka tattara naka ka koma kai kaɗai dama can ka ce ba son ta kake yi ba." Tana faɗar haka ta nufi main falon gidan. Kallon ƙofar ɗakin Mama ta yi kafin ya karasa ya tura ƙofar, ba ta falon sai ya nufi bedroom kai tsaye. Kwance take a saman gadon Mama ta juyawa ƙofar baya. A hankali take tafiya cikin ɗakin, har sai da ya karasa dab da ita sannan ta ji ƙamshinsa. Tsoro ne ya kamata tana kokarin ja da baya ya yi saurin janyo hannunta ya riƙe. Tsuke fuska ta yi tana kau da kai, da mamaki yake kallonta ganin yadda ta murtuke fuska. "Yaushe kika raina ni har haka ne?" "Tun ranar da ka nuna ma ni ko kai waye." "Ni?" Yayi tamabayar yana nuna kansa. "Yaya Fahad me kake tsammanin gani daga gare ni? Na yi farin ciki da murnar dawowarka? Idan ba ka sani ba ka sani ba na farin ciki da dawowarka ba na ƙaunar ganin fuskarka a kusa da ni." "Da gaske?" Kai ta jinjina ma sa alamar eh. Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce. "Why?" Kamar tana jira ta fashe ma sa da kuka tana cewa. "Ka mance da abun da ka yi ma ni a daren da za ka tafi? Ka mance azabtar da ka gana ma ni, babu imani da tausayi ka saka ƙafa ka bar ƙasar nan ba tare da ka iya bude baki ko sannu ka ce ma ni ba ballanta ka taimaka ma ta ni? Kai kawai kanka ka sani ko na mutu buƙatar ka ta biya ko? Ka bar ƙasar ba ka da damu da halin da nake ciki ba ballantana ka kira ka tamabaye lafiyata akan halin da ka saka ni, amma kake tsammanin zan yi farin ciki da dawowarka?" Ta karasa maganar tana kukan da yake fitowa daga ƙasar ranta, wanda ke nuna ƙuncin da zuciyarta ke ciki. Shiru ya yi yana kallonta, wato abun da ya yi ma ta ya tafi ta rike shi a ranta duk tsawon watannin da ya yi a can, dama tana jin haushi da baya kiran wayarta kenan ko ya tambaye ya take. Shi kansa ya san bai kyauta ba, amma kuma ya zai yi . Janyo ta ya yi a jikinsa ya rungume yana bubbuga bayanta alamar rarrashi. "Ko ban ta fi ba idan ina ƙasar ba abinda zan iya yi ma ki, domin ko ina nan Innar dai da na kira ma ki ita ce zan sake kira ma ki ita. To banbanci da ina nan ko ba na nan, sannan da ban kira ki ba kin damu da ni ne, ko kin taɓa cewa bari ki kira ni ko tura ma ni saƙo?" Tsabar takaici ture shi ta yi daga jikinsa tana ja baya, wato har yanzu girman kan nasa da jin kansa yana nan ba abun da ya sauya. Wato ba zai ba ta hakuri ya yarda ya yi ma ta laifi ba ko, sannan tsabar ya raina ma ta wayo ita ce za ta kira shi . Ganin ta tura shi ta cigaba da kuka ya share ta ya yi fice daga ɗakin. Don shi baya jin zai iya ba ta haƙuri.. Goge hawayen ta yi ta na mamaki girman kai da jin kai irin na Fahad Majidaɗi. Har ya fita ya dawo ya kalle ta ya ce. Ki shirya mu koma gidanmu anjima." Ina za fice Daga cikin dakin. _Makaho_ Har karfr goma sha biyu ba dare suna fira da Ma'eesha, ita kanta ta san cewa ba su taɓa dadewa suna fira irin na yau ba. Ganin karfe goma sha biyu ya yi ne ya sa Ma'eeha ta rufe ƙofat ɗakin. Nan kuwa zafi ya fara yi ma su sallama. Wanda ya sa ya Ma'eesha jan gajeren tsuki , Makaho ya ce "Me ya faru ne kike tsimi?" "Zafin nan ne yadda ya addabe mu." "Kada ki damu za ki yi barci me daɗi." Kan katifarta ta nufa ta hau sai da ta yi addu'ar kwanciya barci sannan ta kwanta . Kwanciyarta ke nan ta ɗauki mefeci a gefen filon sannan ta kashe hasken da ta kunna, dama torchlight ɗin wayarta ce ta kunna. Tana ɗan fifita idan barci ya kama idanun nata sai ta saki mafecin ya faɗi, daga nan kuma zafi zai sa ta farka ta kasa barci. Ji ta yi ana lalubarta cikin barci, cikin tsoro ta ce. "Yaya Khalifa?" "Na'am ba ni mafecin na yi ma ki fifita." Sai a lokacin ta saki aniyar zuciya tana cewa. "A'a ka bar shi kai ma na san barci kake ji." "Kada ki damu ba na jin barci, idan ma ina ji to zan kwanta." Ba musu ta mika masa mafecin, ya fara yi ma ta fifita wanda ya sa nan da nan barci me daɗi ya ɗauke ta. A daren ranar bai rintsa ba kwana ya yi yana yi ma ya fifita kamar yadda ya saba yi ma ta. Ita har mamakin yadda baya barci take yi. Ai dare mahutar bawa ne, ko ta hana ta ce ya yi barci baya yi. Da Asuba ne ta farka daga barci tana mamakin sa. "Ma'eesha kin tashi ne?" "Eh na tashi sannu da ƙoƙari." Wanka ya je ya yi sannan ya ɗauro alwala ya wuce masallaci. Ita ma wankan ta yi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba. Sai da safe karfe shida da rabi ya dawo gidan. Ƙamshin girkinta ne ya yi ma sa sannu da zuwa. Ruwan Lipton ne wanda ya ji kayan ƙamshi take dafa ma su, don ta siyo kayan tea da biredi wanda ta siyo a shago da safiyar nan. "Assalamu alaikum warahmatullah." "Wa'alaika salam warahmatullah. Sannu da zuwa." "Yauwa sannu da ƙoƙari Ma'eesha ." Tabarma ta shimfida ma sa tana cewa. "Ga tabarma nan daga cikin baranda na shimfida ma ka " Ta ja hannunsa zuwa wajen tabarmar ya zauna, sannan ta durkusa cikin girmamawa ta gaishe shi, ya amsa ma ta cikin farin ciki da sanya albarka. Ruwan shayin ta zubaa sa da madara pick powder na sachet da milo sachet ɗaya ta zuba sugar kadan ta ba su shi. Dole ce ta saka yake cin abinci a gidan, ba wai don komai ba sai don gani yake yi da kunya ya zauna mace ke ciyar da shi. Ita ma ta zuba na ta ta zauna gefen sa tana sha Bayan sun gama ta ce "Alhamdulillah . Ka ga jiya ba mu da abincin da za mu ci ba mu da kuɗin siye, amma yau Allah ya rufa ma na asiri ko?" "Haka ne, Allah ya kara rufa ma na asiri duniya da lahira." Ya faɗa yana kokarin tashi. "Yau zan fita da safe." "Lafiya dai ko?" "Lafiya lau, kin san wata rana akan samu kasuwa da safe ne kawai." "To Allah ya bada sa'a ya sa a samu abun da ake so." "Amin ya Allah. Na yi wanka kafin na tafi sallar asuba bari na tafi yanzu." Ta mike ta ɗauko ma sa basket kayan gyaran takalminsa, har kofar gida ta raka shi sai ta ba shi kayan tana yi masa addu'ar Allah ya tsare ya bada sa'a. *ABUJA* Wata hamshaƙiyar mara ce mai kimanin shekaru hamsin. Tana sanye da wani tsadadden leshi a jikinta. Kunnenta da wuyanta ɗan kunne ne da sarƙa na gold. Lokaci zuwa lokaci takan kalli mutumin da ke gefenta wanda yake sanye cikin suit. Cikin ɓacin rai ta miƙa ma sa hannu alamar ya ba ta, mika ma sa wayar da ke hannunsa. Ta karɓa ta fara duba wa hotunan Makaho ne tare da Ma'eesha. Wanda aka ɗauke su lokuta mabanbanta na farkon wanda aka ɗauke su ne da suka fito tana rike da hannunsa ranar da za ta siya ma sa waya. Da kuma wanda aka ɗauke su ranar da za su je asibiti gaida mahaifiyar Nasreen har ya sa Ma'eesha ta shiga keke ya ma sa duka. Ranta a ɓace take kallon mutumin wanda ake kira da Jimoh ta yi kafin ta ce. "Yanzu dan ya gano kana bin bayansa shi ne ya yi ma ka wannan shaƙar?" "Ai Madam da ba don kiran wayar da kika yi ma ni ba da Allah kadai ta san abun da zai ma ni, kin ga yadda ya dimfaro ni kamar mayunwacin zaki?" "Me suka je yi asibitin? Sannan kuma har yanzu ka kasa gano wace ce wanan yarinyar da kuma abun da ke tsakaninsu da ita?" "Ban gano ba sai dai akwai wani a unguwar da suke an ce shi ya ba su hayan gidan da suke zaune a ciki shi da yarinyar." "Okay, a unguwar da suke zaune shi ma a anan yake da zama?" "Eh a nan yake da zama , sai dai ina jin tsoro." Wani kallo ta yi ma sa saboda ta san me zai ce. "Tsoron me kake ji?" "Kada ya sake kama ni a karo na biyu, Madam yaron nan naki fa ba shi da sauki." "Wancan karon ma ai sakarcin ka ne ya saka ka bari ya gan ka, kai ba ka san yadda za ka iya takunka ba?" "Yarinyar dai maƙura ce a wajen kyau, sai ka ce aljana ce ita?" Da sauri ta kalle shi ta kuma kalli hoton dake wayar ta zuba wa fuskar Ma'eesha idanu tana kallon kyakkyawar fuskarta wacce kyawun yarinyar sai da ya firgita ta. Ta kalli hannunsu dake sakale cikin na juna, shi yana sanye da baƙin glass ita kuma tana sanye da doguwar rigar Abaya. Tsuki ta ja kafin ta ce. "Kuma ba ka tunanin cewa ita yarinyar abokinyar aikinsa ce?" "Madam ba na tunanin abokinyar aikinsa ce domin a tarihi Jalaluddeen baya aiki da kowa, shi kadai yake aikinsa duk hatsari aikin kuwa." "To ka ce a wani gida yake zaune da yarinyar ko?" "Ƙwarai kuwa." "To me ya sa wanann karon bai kama hotel ba?" "Madam a farko a hotel yake zaune daga baya ne ya daina kwana a hotel yake kwana a gidan shi da yarinyar." Kallon mamaki take yi ma sa kafin ta ce . "Kana nufin a gida ɗaya yake kwana da yarinyar?" Ƙwarai kuwa Madam sai kin ga gidan, gida ne na ƙasƙantu miskinai, kai wannan ma ba zan kira shi da gida ba sai sai akulki ko kango. Don wallahi ko gidan da kike kiwon karnuka ya fi wanan gidan sau dubu." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Yaushe Jalaluddeen ya zama haka? Rabon da ya kira ni a waya ma na mance kuma ko na kira shi baya shiga. Amma na san inda zan bi na san komai." Ta yi maganar tana haurawa upstairs, ba dadewa ta fito riga da handbag da mayafinta, da hannu ta yi wa Jimoh alamar su tafi. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 5️⃣2️⃣ Ta yi mahada tana haurawa upstairs ba daɗewa ta fito riƙe da handbag ɗin da mayafinta, hannu ta yi wa Jimoh alamar su tafi. Suna fita ta rufe ƙofar direbanta na ganinta ya taso da sauri, ta ɗaga ma sa hannu cike da izza, dole ya koma. Jimoh na bin ta a baya ta nufi wata tsadaddiya mota ta nufa yana bin ta a baya, key din motar ta mika ma sa ya karba ya bude ma ta bayan motar ta shhga ta zauna. Zagayawa ya yi mazaunin direba ya shiga ya yi wa motar key, horn ya yi maigadi ya wangale ma sa gate suka bar gidan. _Fahad_ Yana fita daga part ɗin Mama part ɗin Baba ya nufa, saboda ya san shi kadai ne idan ya yi ma sa Maganar komawarsu gidansu zai ce su tafi ba tare da Mama ta yi gardama ba. Don ya lura yanzu Mama so take ta hana ma sa matarsa. Da sallama ya shiga falon Baba, cikin sa'a kuwa ba kowa sai shi kaɗai yana duba wasu documents. Baba ya amsa ma sa sallamar yana cewa. "Ambassador kai ne ?" "Eh Baba." Ya zauna saman Centre carpet ya yi shiru. Ganin shirun da ya yi ne ya sa Baba fahimtar akwai magana a tare da shi. Tattara hankalinsa wuri ɗaya ya yi ya ce. "Kamar akwai magana a bakinka ko?" Ɗan sunkuyar da kai ya yi kafin ya ce. "Dama ina son mu koma gidanmu ne?" "To In ban da abun ka wanan ai ba wani abu ba ne, ka ɗauki matarka kawai ku tafi ma na." "Am dama dai Mama ce na ga kamar ba za ta amince ba." "Kan wani dalili za ta hana ka ɗaukar matarka?" Wayarsa ya dauka ya lalubo lambar wayar Mama ya danna ma ta kira. Bugu biyu ta ɗaga tana yi ma sa sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam, ki zo part ɗina ina son ganinki." "To Alhaji." Ta kashe kiran wayar tana kallon Aunty Rahama da Inna da suke firar kallon da Fahad ke bin Nadra da shi suna dariya. "Bari na je Alhaji na jira na." Tana faɗar haka ta mike don zuwa amsa kiran wayar Baba. Koda shiga falon Baba ta tarar da shi da Fahad ne a falon. Tun da ta shigo kansa yake a ƙasa ba ta kawo cewa shi ne ya zo da Baba da wata maganar ba. Zama ta yi kan kujerar da Baba yake zaune, kujera mai zaman mutum uku ne. "Barka da hutawa Alhaji." "Yauwa Barka dai ya gidan?" "Alhamdulillah." Shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da cewa. "Yaushe Fahad da matarsa za su koma gidansu ne, tun da ya dawo ai zamanta ya kare a nan sai ta koma ɗakin mijinta ko?" Kallon Fahad Mama ta yi ta gane cewa shi ya kawo wa mahaifinsa zancen. "Au har ka kasa jurewa ka kawo ƙarata ne tun yanzu? Ashe ba za ka iya jure wa ba, da wuri haka?" "To wane dalilin zai sa ki hana ma sa matarsa ma?" "Alhaji idan na ba ka labarin abun da yaron nan ya yi wa yarinyar nan za ka goyi bayana. Ni na yanke shawarar ma gara ya sake ta kawai tun da ba son ta yake yi ba." "Subhanallah me ya kawo wanan zancen kuma? Ba na son na sake jin makamancin wannan zancen, Fahad ko da wasa idan ka saki Nadra za ka hadu da mummunan ɓacin raina." "Alhaji ka tsaya ka saurare ni ina da dalilin da ya sa na ce ya sake ta. Aure ibada ne amma idan da cuta barinsa halal ne." "Wacce hujja kike da ita da za ki ce ya saki matarsa." Murmushin takaici ta yi kafin ta ce. "Hujjoji ma nake da su ba hujja ba. Hujjata ta ɗaya yaron nan da bakinsa ya ce baya son yariyar nan zai sake ta, na biyu na sanar da kai abinda ya yi ma ta a ranar da ta kwana a ɗakinsa, sannan ya saka ƙafa ya bar ta cikin halin jinya bai taɓa kiran wayarta ya tambaye ta jikinta ba. Kuma bai taɓa kiran wani ya tamabaye ya jikinta ba, tsawon watannin da ya yi a can mulkin nuna waya bai taɓa tamabayar ta ba. Sai yanzu da ya dawo ya ce ta bi shi saboda zalunci to ba za'ayi wannan da ni ba, ba zai iya yi ma ta adalci ko tausaya ma ta ba." Shiru falon ya ɗauka na tsawon mintuna biyu kafin Baba ya ce. "Fahad ba ka kyauta ba gaskiya, ba'a haka, ai ko dabba ce ka siyo ai ka dinga duba lafiyar ta, idan ba ka nan dole ka nemo mai kula da ita ballantana bil'adama. Ta ya za ka wofantar da yarinyar da aka ba ka amana? Ban tsammaci haka daga gare ka ba." Sai a lokacin ya daga kansa yana cewa. "Baba don Allah ku yi hakuri, ba yadda ake tunani ba ne, duk da ban kira ya kuma ban tamabaye kowa ita ba amma ina kula da ita duk wani motsi nata akan idanuna take yin sa, ina kallonta, kuma na tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya. Gabadaya hankalina yana kanta tun da na bar ƙasar nan." Shiru suka yi suna sauraron sa kafin Baba ya ce. "Ka faɗa ma ni gaskiya meye ra'ayin ka akan wannan yarinyar ? Ba na son a takura wa kowa a cikin ku, shin za ka iya zama da ita a matsayin matar aurenka kuma ka kyautata ma ta da yi ma ta adalci ba cuta ba cutarwa? Shin kana son ta ?" "Baba ban sani ba ko son ta nake yi yanzu, na dai san a baya da aka aura ma ni ita ni kan ji haushi da takaici ko ganinta ba na son yi, a duk lokacin da na ganta sai na ji raina ya ɓacj na dinga jin haushin Sidra. Saboda ita ce ta ja faruwar komai. Amma daga baya ɗan zaman da na yi da Nadra na fahimci ta fi Nadra nagartar da kowane namiji yake buƙata daga wajen ƴa mace. Domin ta fi Sidra hankali da nutsuwa, tarbiyya, haƙuri juriya da hangen nesa, kuma tana aiki da ilimin ta na Addini. Waɗan nan ɗabi'un nata da na fahimta ya sa na daina jin haushin da nake ji na aura ma ni ita, kuma na san duk namijin da ya samu mace mai ɗabi'un nan da na lissafa tabbas ya zaɓawa ƴaƴansa uwa tagari. Na san cewa a baya da nake soyayya da Sidra i na duba hasken fata da ƙyale-kyale ne amma yanzu na fahimci ba shi nake bukata ba, nagartacciyar mace wacce za ta yi yarda waɗan da suka isa da ita su yi ma ta tsawa ta bi umarnin iyayenta ko mijinta nake buƙata. Ba ma mance huɗubar Mahaifinsu lokacin da Sidra ta gudu bayan mahaifinsu ya ba ni Nadra a madadinta sai yake sanar da ni cewa. Ya san ya yi ma ni sakayya da wacce zan ci jin dadin zama da ita, idan da Nadra nake so ba zai taɓa ba ni Sidra a madadinta ba, amma tun da Sidra ce to ya ba ni Nadra ba zan taɓa nadamar aurenta ba, domin ya san cewa zan fi jin dadin zama da ita akan Sidra. Kuma na zauna na yi tunani na ga cewa idan har Sidra na girmama iyayenta ba za ta taɓa guduwa a ranar aurenta ba, hakan na nuna rashin ɗa'a da biyayya ce ga iyaye. Amma ita Nadra duk da tana da wanda yake so kuma sun tabbatar za ta yi biyayya ga umarnin su sun isa da ita ya sa suka aurar da ita ba tare da amincewar ta ba. Wanda ko da aka sanar da ita ba ta bijire ma su ba ta yi ma su biyayya ta zauna da wanda suka zaɓa ma ta. To ire-iren waɗannan tunanin na yi na ji na daina jin haushin aurenta kuma ɗabi'un yarinyar suka burge ni. A yanzu ban sani ba ko ina son ta amma kuma na san cewa zan iya zaman aure da ita ta zama uwar ƴaƴana in sha Allah na ɗauki ƙaddarar da Allah ya rubuto ma ni cewa ita ce matata ba Sidra ba." Hannu Mama ta ɗaga tana godewa Allah da ya amshi addu'ar ta cikin gaggawa, kullum addu'ar ta Allah ya karkato da hankalin Fahad kan matarsa. Murmushi Baba ya yi ya ce . "To Hajiya za'a iya ba shi matarsa?" "In sha Allah, yanzu ma kuwa don sai yanzu hankalina ya kwanta." _Makaho_ Bayan sun yi sallama da Ma'eesha yana ta tafiya akan hanya har ya iso bakin titi. Kai tsaye ya nufi wajen da yake zama yana yin aikinsa na gyaran takalmi. Zaman sa na jimawa sai ga wasu motoci sun fito daga layin da ke tsallaken da su makaho ke sana'a. Motoci ne guda biyu ɗayar irin na ɗaukar kaya ne amma bayanta a rufe yake. Ɗayan kuma motar ce baƙa ce mai tinted glass ba'a ganin wanda ke ciki . Tun da motocin nan suka fito ya zuba ma su idanu ta cikin glass wanda ba wanda zai ce ga abun da yake kallo. Direban motor kaya ce ta tsaya daidai in suke ya yi parking, wanda hakan ya sa bakar motar dake bin motar a baya ita ma ta tsaya. Direban babban motar ya fito yana cewar. "Mallam gyaran mun takalmin nan yanzu sauri nake yi." Ya yi maganar yana miƙa wa makaho takalmin. Ganin makaho yana ɗan lalube ne ya sa ya ce . "Kai ba ka gani ne?" Mai yalon dake kusa da makaho ya ce. "Eh baya gani makaho ne amma ya iya aiki sosai." Zai yi magana kenan sai wanda ke cikin bakin motar ya fito yana cewa. "Wani irin sakarcin ne wanan za ka tsayar da mu akan titi bayan ka san ba mu da lokaci ko?" "To ya kake so na yi so kake idan mun sauka na fara tafiya ba takalmi ga shi daji za mu je idan ƙaya na taka fa me za ka ce?" "Ba abun da zan yi amma ka sani idan har ka bari kolayen nan suka fito kai ne a cikin hatsari da ka ɓata ma na lokaci, nawa ne takalmi da ba za ka siye sabo ba?" "Kolayen ai duk an siye su sai mun tafi za su zo ta Wajan sannan kuma idan zan siye takalmi ai ba nan zan samu ba sai na je wani wajen da za mu ɓata lokaci." Wayar direban motor kaya ce ta yi ringing, ya dauka yana cewa. "Afuwa oga kaya za su isa cikin aminci ba matsala, dama wani Kolo ne yake son ba mu matsala amma yanzu shi ma an siye shi ya shigo daga ciki." Daga nan ya katse kiran wayar yana cewa. "Wai har yanzu Makahon nan bai gama gyaran takalmi ba ne?" Daidai lokacin ne Makaho ya Miko ma sa takalminsa ya karba yana dubawa. "Ikon Allah Makaho mai basira, lallai idan mun dawo zan neme ja muna da takalmin da muka tara sun tsinke." Ɗari biyar ya ba makaho ya karba yana cewa . "Nawa ne nan?" "Ɗari biyar ce." "Ba na da canji?" "Bai ma san yana yi ba tuni ya shiga motar ya yi ma ta key." Mai siyar da Yalo ne yake cewa . "Rabon ka ce." Kallon mai Yalo ya yi kafin ya ce. "Ina zuwa zan je na dawo." "To Allah ya tsare." Barin kayan aikinsa ya yi a wajen ya tafi da sandarsa. Can nesa da wajen ya tsaya sai ga wani mai nape ya zo ya tsaya a gabansa. Shiga yayi suka bar wajan. Kai tsaye wani hotel suka nufa in da Makaho ya fito ya bar mai nape din zaune ciki yana jiransa, don ko sandarsa bai ɗauka ba a cikin keke nape ɗin ya bar shi. Cikin hotel ɗin ya shiga ba tare da ya yi wa kowa magana ba, sama ya haura sama. Ɗaya daga cikin ɗakunan ya sa key ya buɗe ya shiga ciki. Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga bathroom don yin wanka. Almost 30 minutes ya ɗauka yana sakarwa kansa shower 🚿, kafin ya gama wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani karami yana goge ruwan kansa. Man shafawa mai sanyin ƙamshi ya shafa har ya ɗauki turare zai shafa sai ya yi wani tunani ya fasa shafawa ya ajiye. Ƙananan kaya ya saka wando three quarter fari ya saka da farar riga. Gudun A.C ya ƙure sannan ya hau saman lafiyayyen gadon ya kwanta, ba jimawa barci me daɗi ya yi awon gaba da shi kasancewar daren jiya bai yi barci ba kwana ya yi yana yi wa Ma'eesha fifita. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣3️⃣ Ƙananan kaya ya saka wando three quarter fari ya saka da farar riga . Gudun A.C ya ƙure sannan ya hau saman lafiyayyen gadon ya kwanta. Ba jimawa barci me daɗi ya yi awon gaba da shi, kasancewar daren jiya bai yi bari ba kwana ya yi yana yi wa Ma'eesha fifita. Sai da lokacin sallar azahar ya yi sannan ya farka, ya yi awa huɗu yana barci. Bathroom ya sake faɗawa ya yi brush da toothpaste ya yi wanka ya fito ya shirya cikin jallabiya fara. Fita ya yi don zuwa masallacin da ke cikin hotel ɗin. Har zuwa lokacin mai nape ɗin da ya kawo shi yana nan yana zaman jiran fitowarsa. Sai dai a lokacin mai nape ɗin ya gama cin abinci a cikin takeaway yana shan ruwa. Sai da aka idar da sallar sanann ya koma cikin hotel ɗin. System ɗin sa ya ɗauka yana shigar da wasu bayanai. Manyan wayoyinsa da ke ajiye a saman table ya ɗauki daya ya kunna. Wata lamba ya lalubo ya kara a kunne, bugu daya aka ɗaga. "Hello sai yau ka ga damar a same ka a waya kenan." Murmushi mai sauti ya ba yi wanda ya ba fito har ta cikin wayar. Kafin ya ce. "Ina hotel a ɗakin da ka sani." Daga haka ya katse kiran wayar kafin ya ɗauki ɗayar tsadaddiyar wayarsa ƙirar Samsung Galaxy Z fold 5 farashin wayar ya kai miliyan biyu da dubu ɗari shida. Irin wayar da ake lanƙwasawa ce ta koma ƙarama idaaka buɗe ta kara girma. shiga what's up ya yi yana duba tarin saƙonnin da suka shigo ma sa, na wasu ya buɗe, na wasu bai bude ba. Har zai aje wayar sai ya shiga bude saƙon da ya ga messages nata ya fi na kowa yawa. YASMEEN shi ne sunan da ya furta kuma sunan ne a jikin wayar da ya yi Seve da shi. "Messages ne barkatai wasu photon ta ne kawai tana hawaye, wani kuma emoji ne na kuka, wasu kuma voice message ne tana nuna damuwa na rashin ji daga gare shi ba kira ba saƙo. Messages na karshe da ta tura ba ta yi magana ba sai rera ma sa kuka kawai take yi. Bai ma ta reply ba ya kashe wayar ya ajiye kawai. System ɗin sa ya sake ɗauka ya shigar da wasu bayanai. Daidai lokacin aka fara knocking ƙofar. Tashi ya yi ya je ya bude kofar . Tashi yayi ta bude kofar nan ya ga Abokinsa da ya kira ya sanar ma sa yana hotel ɗin. "Khalid." Ya fada a saman leɓensa. Murmushi Khalid ya yi yana cewa yau dai ga ni ga *Senior intelligence officer*. "Dama ba ka gani na ne?" "Yanzu kam wa ke ganinka ai sai sai wanda kake tare da su." Wayarsa ce ƙarama wacce Ma'eesha ta siya ma sa ta soma ruri a cikin aljihun kayan da ya cire na wanda ya zo da su. Kallon kayan Khalid yake yi daidai lokacin da ya ga Khalifa ya ɗauki wayar, sannan ya duba ya san mutum ɗaya ce za ta kira shi a wayar. "Nurul ƙalb" Sunan da ya fito kenan don da wannan suna Ma'eesha ta yi Seve number ta da shi a wayar. "Assalamu alaikum." Daga can ɓangaren ta sa da wa'alaika Salam. "Mijina ya kake?" "Lafiya nake matata." "Ma sha Allah, ga abincinka na ajye ma ka don Allah ka dawo ka ci kada ka zauna da yunwa ka ce sai yamma." Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce. "Kada ki damu ni ba na jin yunwa." Nan dai da ƙyar ya shawo kanta ta hakura akan idan ya dawo da yamma sai ya ci. _Nadra_ Tana zaune a falo a falon Mama sai ga Sidra ta shigo ta same ta. "Ƙanwata kina zaune ne ke kaɗai?" "Eh, sannu da shigowa Aunty Sidra." "Yauwa sannu." Zama ta yi a gefenta tana ma ta murmushin yaƙe. "Sai ga Fahad ya dawo ko?" "Eh Aunty." "Kin yi magana da shi ne?" "Eh cewa yayi wai na tattara kayana mu koma gidansa." Sai da gaban Sidra ya fadi amma sai ta dake ba ta nuna tashin hankalin take ciki ba "To ke me kika ce ma sa?" "Cewa na yi ba zan koma ba, don Mama ma ta goyi bayana ta ce ba zan koma ba." "Da kyau, yanzu ya alƙawarin da kika ɗaukar ma ni?" "Aunty Sidra ai ban ɗaukar ma ki alkawarin komai ba." Wani kallo ta yi ma ta kafin ta ce. "Lokacin da na ce ma ki ina son Masoyina har yanzu ke da kanki kika ce ba son sa kike yi ba biyayya kika yi wa iyayen mu, na ce ki taimaka ma ni ya sake ki ya aure ni ni ma zan taimaka ma ki don ki auri Ya Sayyadin da kike so?" Jinjina kai Nadra ta yi kafin ya ce. "Eh tabbas mun yi haka, amma da kike ce ma ni wai sai na yi ma sa rashin mutunci da fitsara na dinga wulakanta shi sanann na dinga waya da tsohon saurayina dole zai sake ni a lokacin na ce ma ki ba zan iya aikata abu ɗaya da kike so na aikata ba. Ba don ko komai ba ke kanki shaida ce ko kare ne ba zan iya wulakanta shi ba, ballantana Ɗan Adam, ko kin manta cewa da duk wulakancin da kike yi wa ma'aikatan gidanmu da zaginsu da kike yi har ki ɗaga hannu ki mari mutanen da a haife sun haife ki me nake yi a lokacin. Kuka fa nake yi. Da a ce zan iya aikata hakan da a kan Waɗanda kike aikata wa zan yi. Ya kamata ki yi amfani da ilimin da Allah ya ba ki wajen tuna cewa Yaya Fahad mijina ne yi ma sa biyayya wajibi ne saɓa ma sa tamkar na saɓawa umarnin Allah ne. Tabbas na yi iya taimakon da zan yi ma ki wajen ganin ya sake ni ya aure ki, tun kafin wani abu ya shiga tsakanin mu na roƙe shi da Allah cewa tun da ba so na yake yi ba ke ni ma ba son sa nake yi ba ya taimaka ya sake ni ya aure ki tun da kin dawo kuma kina son sa shi ma yana son ki ya aure ki. A lokacin yake sanar da ni cewa zai sake ni amma ko ya sake ni ba zai taɓa auren ki ba, tun da har kika iya guduwa a ranar aurenki da shi. Tun a lokacin ya cire ki daga rayuwarsa, idan har ya nemi abu bai samu a lokacin da ya so ba ya fitar da abun kenan daga cikin rayuwarsa. Shi idan ya juya wa abu baya taɓa waiwayarsa har gaban abada." "Ƙarye ne , ƙarya ne wallahi.Fahad nawa ne ni kaɗai, kuma sai na raba ki da shi na aure shi." ",Zan yi farin ciki da haka, fatan nasara." Nadra ta faɗa tana murmushi. Daidai lokacin Mama ta shigo da sallama. Ganin yadda suka yi cirko-cirko ya sa ta kalli Sidra da ta tsuke fuska ta ce. "Lafiya kuwa?" "Lafiya lau Mama." Ta faɗa tana aro murmushi ta yafa a kan fuskarta. Ba dai gamsuwa Mama ta yi ba, amma sai ta bar zancen tana cewa. "Shiga bedroom ki tattara kayanki ki zo ki bi mijinki ko kuma gidanku." Daga Sidra har Nadra sai da ƙirjinsu ya buga a tare. Ganin yadda ta kwaɓe fuska ne ya sa. Mama tsuke fuska don kar ta kawo ma ta wasa. "Mama don Allah ki bar ni a nan." "Okay to je ki roƙi Babanku shi ya zartar da hukunci ba ni ba." Hawaye ya fara yi ma ta sintiri akan fuska tana cewa. "Shikenan na shiga uku ni Nadra." Janyo ta Mama ta yi ta zaunar da ita a gefenta, sannan ta riko hannunta cikin nata, cikin sigar rarrashi ta ce. "Meye abun tashin hankali kuma ƴata, ina ce da can ai kike zaune da shi kafin kuka dawo nan?" "To ai lokacin..." Sai ta yi shiru ta kasa cewa komai. Murmushi kawai Mama ta yi don ta san dalilin Nadra yanzu. "Kar ki damu ba komai in sha Allah, komai ya wuce da yardar Allah. Idan ya yi ma ki wani abu da ba daidai ba, ko abin da kika san ba ki so to ki yi sauri ki ɗauki wayata ki danna ma ni kira, za ki ga hukuncin da zan ɗauka." Mama ta lura da Sidra ta ga rashin jin daɗin da ta shiga yanzu -yanzu. Kuma ta fahimci har yanzu tana son Fahad ba ta fitar da shi daga cikin rayuwarta ba, duk kuwa da Kasancewar yanzu yana auren ƙanwarta ce. "Mu je ta taya ki tattara kayan yamma ta yi." Ta yi maganar tana jan hannun Nadra. "Yi zamanki Mama bari ba taya ta tattara kayan." Aunty Rahama ta yi maganar tana shigo wa hannunta riƙe cikin na Baby Zahrah. "Dama ba ki tafi gida ba?" "Eh na je kaeɓowa Nadra saƙo ne dama ." Ta yi maganar tana jan hannun suka nufi bedroom ɗin Mama. Sidra kam ficewa ta yi daga cikin ɗakin ba tare da ta yi wa kowa magana ba. Murmushi kawai Mama ta yi ta girgiza kai. Aunty Rahama na taya ta shirya kaya tana sake ba ta shawarwari. Hatta kayan gyaran jiki ta fito da su a cikin handbag ɗin ta ta saka ma ta cikin wata ƙaramar jaka. Sannan ta ciro wani ƙaramin roba da ke da wani hadin ta bude murfin goran ta ce. "Karɓi ki sha." Girgiza kai kawai ta yi alamar a'a. Amma ganin ba wasa a fuskar Aunty Rahama ya sa ta karɓa ta shanye. Sauran kayan duk ta yi ma ta bayanin yadda za ta yi amfani da su. Bayan sun ja akwatunan zuwa falo ne ma su aikin gidan suka kwashe su suka fita da su bisa umarnin Mama. Direban Fahad ya jera akwatunan a bayan mota. Fahad ya nufi part ɗin sa dan ɗaukar wasu abubuwan bukatar. Tsarabr da ya kawo ma su daga America ya sanar wa Rumaisa ta fito da su tare da bayanan na kowa. Part ɗin Baba ya nufa in da Mama ma ta ja hannun Nadra suka nufi part ɗin. Nan Baba ya yi masu nasiha sosai Nadra na kuka tana jinjina kai. Shi dai Fahad bai ce komai ba kansa a ƙasa. Bayan Baba ya gama ne Mama ma ta ɗaura da nata, Inna ma ta shigo ta ɗaura da nata nasihar. Sallamar su aka yi kasancewar zuwa lokacin ina shirin kiran sallar Magrib ne. Suna fitowa falo suka tarar da Aunty Rahama da Rumaisa, sai Farida wacce ita ma ba walwala a tare da ita. Ita kuma Sidra fitowar ta kenan saboda kada a yi tunanin halin da take ciki ya sa ta danne zuciyarta ta fito don yin sallama da ƙanwarta . Nadra na hawaye ta yi ma su sallama, har Aunty Rahama na ma ta dariya tana cewa. "Wai kuka sai ka ce amaryar da aka ɗaurawa aure yau." Rungume Sidra ta yi tana cewa "Aunty..." Sauran maganar ta kasa furta wa kuka ya ci ƙarfinta. Sai da Sidra ta yi yaƙi da zuciyarta sanan ta ƙaƙaro murmushin yaƙe tana bubbuga bayan Nadra. Don idan ta ce za ta yi magana to asirin zuciyarta ce za ta tonu. Da kyar Aunty Rahama ta ɓanɓare Nadra daga jikin Sidra. Fita suka yi aka yi ma ta tsakiya har wajen motar, Farida ce kawai ba ta motsa daga ina da take ba. Direba na gaba Fahad na zaune a bayan motar, Aunty Rahama ta bude ma ta bayan motar ta zauna gefensa. Idanun Sidra na kan Fahad ta zuba ma sa idanu. Shi kuma idanunsa na kan wayarsa da yake sarrafa ta ta cike da ƙwarewa. Direba ya ja motar suka bar gidan. Sanyin AC da ƙamshi ne ke tashi a cikin motar, sai kuma sheshsheƙar kukanta. Yana jin kukan har a cikin ransa ya fahimci yadda take ji, amma jin kansa da mishkilancinsa ya sa shi ya basar da ita kamar bai san tana yi ba. Ji ya yi kukan na hawa ma sa kai, daidai ana kiran sallar Magrib. Umarnin tsaida motar ya ba direban, bayan ya yi parking motar ne ya ce wa direban ya fita su yi sallah. Ya yi maganar yana fita. Direban ma fita suka bar ta a cikin motar. Ruwa suka ɗauka suka yi alwala, daidai za'a tayar da sallah suka shiga jam'i aka yi sallar tare da su. Sai da suka idar da sallar sannan suka fito zuwa lokacin kanta har yana ciwo sosai yake sara ma ta. Don haka ta dakatar da kukan da take yi sai dai sheshsheƙa take yi. Har suka ƙarasa kofar gidan tana ajiyar zuciya. Horn horn direban ya yi maigadi ya wangale ma su gate suka shiga.a parking space ya yi parking motar. Sannan ya zagayo yana buɗe wa Fahad bayan motar ya fito. Sannan ya zagayo ya buɗe wa Ma'eesha. Ma'aikatan gidan suka ƙaraso suna yi ma su Barka da dawowa. Fahad ne ya amsa Nadra tuni ta nufi hanyar shiga ciki. Tana tura kofar ta ji a rufe, don haka ta tsaya ta jingina da bango kanta na sara mata idsnunta a rufe. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣4️⃣ Tana tura ƙofar ta ji a rufe, don haka ta tsaya ta jingina da bango kanta na sara mata idanunta a rufe. Karasowa ya yi ya bude ƙofar dama jira take yi don haka ta faɗa cikin falon. Hijabinta kawai ta cire ba ta karasa upstairs ba ta tsaya a downstairs ta yi amfani da toilet dake cikin falon Alwala ta ɗauro sannan ta fito ta sanya hijabinta a nan ta ɗauki sallaya ta shimfida. Kasancewar ko ina fesa yake an gyara . Tana isar da sallar ta kwanta a nan saman sallaya. _Makaho_ Bayan ya gana waya da Ma'eesha ya shawo kanta ta hakura da zancen ya dawo gida ya ci abincin rana. Abokinsa Khalid na ma sa kallon Mamaki kafin ya bude baki ya ce. "Jalaluddeen." Ba tare da ya kalle shi ba ya ɗaga ma sa gira ɗaya alamar ya aka yi. "Kai da wa kake waya?" "Ba ruwan ka da ita?" "Yaushe muka fara ɓoyewa juna sirrin junan mu ne?" "Da Ma'eesha nake waya." "Wace ce ita na ji tana kiran ka da mijina?" "Au hakan da ja ji bai zana ma ka alaman cewa Matata ba ce ita ?" "Jalaluddeen ka san me kake faɗa kuwa? Na ɗauka bincike da aikin sirri ya kawo ka garin nan sai ka ɓige da aure? To ya za ka yi da Yasmeen da ka bari tana can tana zaman jiran ka?" Bai tanka ma sa ba ya yi kamar bai ji shi ba. Ya cigaba da cewa. Iyayenka sun san cewa ka yi aure a nan?" "Ba wanda ya sani." "Okay ina fatan ka aure ta ne iya na tsawon zaman da za ka yi a garin nan, da zaran ka kammala aikin ka za ka sake ta ka koma ga Yasmeen ko?" "Na san ba abin da ya kawo ka kenan ba, so ka yi abinda ya kawo ka ka tafi ina da abun yi." Mamaki da takaici ya cika zuciyar Khalid, wai aure ba tare da sanin kowa ba. Tashi ya yi ya fice ba tare da ya sake kallon in da yake ba. *WAYE MAKAHO?* Jalaluddeen Kabir Arzika shine cikakken sunansa. Sunan mahaifinsa Alhaji Kabir Arzika (Dad) sunan mahaifiryasa Hajiya Fatima, (Mom)Suna zaune ne a garin Abuja. Alhaji Kabir Arzika baban ɗan kasuwa ne da yana da kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki ana fitar da su waje. Mahaifiyarsa Hajiya Fatima kuma Babbar likita ce tana da babban asibitin nata na kanta mai suna *Jasad international hospital* Jamaluddeen shi ne babban Ɗan su da suka haifa. Lokacin da suka haifi Jalaluddeen yana da shekara ɗaya ɗaya mahaifiyarsa ta samu wani cikin da ke matuƙar ba ta wahala tana laulayi sosai wanda ba ta iya komai sai an yi ma ta. Wannan dalilin ya sa ƙanwar Alhaji Kabir mai suna Maryam wacce ake cewa (Ummee) wacce dama shekaru biyar da aurenta ba ta taɓa haihuwa ba ta ɗauki Jalaluddeen ta yaye shi a wajenta ta rike shi kamar Ɗanta. Yayin da Dad ke cigaba da kula da Mom. Jalaluddeen yana wajen ƙanwar Mahaifinsa. Lokacin da Jalaluddeen ya cika shekaru biyu aka saka shi a makaranta. Lokacin Mom dinsa ta haifi cikin da yake saka ta wahala, ta haifi Ɗa namiji sunan sa Sadik. Har Mom ta haifi Sadik Jalaluddeen na wajen ƙanwar Dad ba ta dawo da shi wajan mahaifiyarsa ba. Sai dai su je ziyara tare da Ummeensa su gaida Mom da Dad su dawo. Har Allah ya ba Ummee ciki ta haifi Ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Yusuf.Ta haɗa su ta rene su tare ba ta taɓa banbanta su hasali ma soyayyar da take yi wa Jalaluddeen ya fi son da take yi wa Yusuf yawa. Allah ya jarebe ta da ƙuanar Jalaluddeen tun da aka haife shi, ballantana da yanzu yake hannunta sai ƙaunar ra ƙaru. Kusan lokaci ɗaya Mom da Ummee suka sake haihuwa, Mom ta haifi Sadiƙa da sati biyu Ummee ta haifi Yasmeen. *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣4️⃣ Tana tura ƙofar ta ji a rufe, don haka ta tsaya ta jingina da bango kanta na sara mata idanunta a rufe. Karasowa ya yi ya bude ƙofar dama jira take yi don haka ta faɗa cikin falon. Hijabinta kawai ta cire ba ta karasa upstairs ba ta tsaya a downstairs ta yi amfani da toilet dake cikin falon Alwala ta ɗauro sannan ta fito ta sanya hijabinta a nan ta ɗauki sallaya ta shimfida. Kasancewar ko ina fesa yake an gyara . Tana isar da sallar ta kwanta a nan saman sallaya. _Makaho_ Bayan ya gana waya da Ma'eesha ya shawo kanta ta hakura da zancen ya dawo gida ya ci abincin rana. Abokinsa Khalid na ma sa kallon Mamaki kafin ya bude baki ya ce. "Jalaluddeen." Ba tare da ya kalle shi ba ya ɗaga ma sa gira ɗaya alamar ya aka yi. "Kai da wa kake waya?" "Ba ruwan ka da ita?" "Yaushe muka fara ɓoyewa juna sirrin junan mu ne?" "Da Ma'eesha nake waya." "Wace ce ita na ji tana kiran ka da mijina?" "Au hakan da ja ji bai zana ma ka alaman cewa Matata ba ce ita ?" "Jalaluddeen ka san me kake faɗa kuwa? Na ɗauka bincike da aikin sirri ya kawo ka garin nan sai ka ɓige da aure? To ya za ka yi da Yasmeen da ka bari tana can tana zaman jiran ka?" Bai tanka ma sa ba ya yi kamar bai ji shi ba. Ya cigaba da cewa. Iyayenka sun san cewa ka yi aure a nan?" "Ba wanda ya sani." "Okay ina fatan ka aure ta ne iya na tsawon zaman da za ka yi a garin nan, da zaran ka kammala aikin ka za ka sake ta ka koma ga Yasmeen ko?" "Na san ba abin da ya kawo ka kenan ba, so ka yi abinda ya kawo ka ka tafi ina da abun yi." Mamaki da takaici ya cika zuciyar Khalid, wai aure ba tare da sanin kowa ba. Tashi ya yi ya fice ba tare da ya sake kallon in da yake ba. *WAYE MAKAHO?* Jalaluddeen Kabir Arzika shine cikakken sunansa. Sunan mahaifinsa Alhaji Kabir Arzika (Dad) sunan mahaifiryasa Hajiya Fatima, (Mom)Suna zaune ne a garin Abuja. Alhaji Kabir Arzika baban ɗan kasuwa ne da yana da kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki ana fitar da su waje. Mahaifiyarsa Hajiya Fatima kuma Babbar likita ce tana da babban asibitin nata na kanta mai suna *Jasad international hospital* Jamaluddeen shi ne babban Ɗan su da suka haifa. Lokacin da suka haifi Jalaluddeen yana da shekara ɗaya ɗaya mahaifiyarsa ta samu wani cikin da ke matuƙar ba ta wahala tana laulayi sosai wanda ba ta iya komai sai an yi ma ta. Wannan dalilin ya sa ƙanwar Alhaji Kabir mai suna Maryam wacce ake cewa (Ummee) wacce dama shekaru biyar da aurenta ba ta taɓa haihuwa ba ta ɗauki Jalaluddeen ta yaye shi a wajenta ta rike shi kamar Ɗanta. Yayin da Dad ke cigaba da kula da Mom. Jalaluddeen yana wajen ƙanwar Mahaifinsa. Lokacin da Jalaluddeen ya cika shekaru biyu aka saka shi a makaranta. Lokacin Mom dinsa ta haifi cikin da yake saka ta wahala, ta haifi Ɗa namiji sunan sa Sadik. Har Mom ta haifi Sadik Jalaluddeen na wajen ƙanwar Dad ba ta dawo da shi wajan mahaifiyarsa ba. Sai dai su je ziyara tare da Ummeensa su gaida Mom da Dad su dawo. Har Allah ya ba Ummee ciki ta haifi Ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Yusuf.Ta haɗa su ta rene su tare ba ta taɓa banbanta su hasali ma soyayyar da take yi wa Jalaluddeen ya fi son da take yi wa Yusuf. Ko mihin Ummee wato Abbee yana ji da Jalaluddeen kamar shi ya haife shi. yawa. Allah ya jarebe ta da ƙuanar Jalaluddeen tun da aka haife shi, ballantana da yanzu yake hannunta sai ƙaunar ra ƙaru. Kusan lokaci ɗaya Mom da Ummee suka sake haihuwa, Mom ta haifi Sadiƙa da sati biyu Ummee ta haifi Yasmeen. Haka rayuwa ke tafiya Mom na kula da Asibitin ta, Ummee na na zuwa ƙasashe irin su Dubai China tana kasuwancin ta. Haka rayuwa take ta tafiya Jalaluddeen, Sadik, Yusuf da a ƙasashen waje suka yi karatu har master digri yayin da matan kuma Yasmeen da Saddiƙa suka yi karatun su a nan gida Nigeria don iyayen sun ce ba su yarda ƴa mace su tura ta wata uwa duniya ta yi karatu ba. A yanzu haka kowa na aiki a cikinsu Jalaluddeen yana aiki a Department of state services(DSS) yana rike da baban muƙami na Senior intelligence officer. Yayin da Sadik kuma Doctor ne yana aiki a asibitin mahaifiyarsu (Jasad international hospital) Yusuf kuma Lauya ne mai zaman kansa. Saddiƙa da Yasmeen kuma yanzu suke karatun Master digiri. Jalaluddeen wanda aka fi sani da Makaho shi ne Senior intelligence officer a hukumar DSS . Yana jagorantan manyan bincike, yana da iko kan wasu jami'ai, ana ba shi muhimmin missions, albashinsa da alawus suna da yawa sosai . Kuma shi ke jagorantar ayukkan kama criminals, yana shiga aiki da kansa ba dole sai a office ba. Yana da horo na musamman (Fightings spaying tactics) Yana samun kudi sosai sirrin alawus. Ƙwararre ne wajan shiga mutane ya yi mu'amala da su ba tare da an gane shi ba. Yana canza rayuwa a duk yadda ya so yana rayuwa kamar talaka sai yadda ya so, yana samun kudi sosai saboda shiga haɗarin aiki da yake. Yana da allowance na sirri, kuma yana samun lada daga manya missions. Babban jami'i ne yana shiga hatsari da kansa. Yana daya daga cikin manyan jami'an Department of state services field operations commander da aka fi yarda da shi wajen aikin sirri. Yana da shugabanni guda biyu da ke sama da shi. Director General (DG) Sai kuma Deputy Director su ne manyan shugabanni a sassa daban-daban. Aikin da ya kawo shi garin Kaduna ba wani binciken wani Attajirin mutum ne wanda yake safarar makamai, yana shigo da bindigogi a ɓoye yana siyar wa ƴan ta'adda Sunan mutumin Alhaji Mamman Daula) yana taimakawa talakawa ana ganin girmansa, amma ba wanda ya san cewa yana safarar makamai. Wannan dalilin ne ya sa Jalaluddeen ya zo garin Kaduna ya yi ɓadda kama a matsayin makaho kuma mai gyaran takalmi. Gidan Alhaji Mamman Daula na kusa da in da makaho ke gyaran takalmi yana kula da duk wani shige da ficensa yana hada rahoto. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page 5️⃣5️⃣ Gidan Alhaji Mamman Daula na kusa kusa da in da makaho ke gyaran takalmi, yana kula da kula da duk wani shiga da ficensa yana haɗa rahoto. Wata rana wajan bin bayan daya daga cikin yaran Daula ne ya ga ana ƙoƙarin Illata Mummy mahaifiyar Ma'eesha, wanan dalilin ya sa ya fasa yin abun da ya kai shi ya taimaki rayuwar Mummy ta dauke shi a motarta har zuwa gidanta. Shi ya sa ko da Mummy ta ce ma sa ya dinga zuwa yana karbar abinci ba saboda komai yake zuwa ba sai dan yana sa idanun ya ga ko ana bibiyar rayuwar ta ne ya ba ta kariya. A cikin lokacin kuma Allah ya yi ma ta rasuwa. Mamy ta sa Daddy ya ba shi auren Ma'eesha don rayuwarta ta tagayyara ba tare da ta san ko waye shi ba. _Nadra_ Tana nan kwance a wajen saman sallaya har aka kira sallar Isha'i sannan ta tashi ta gabatar da sallar Isha'i. Har lokacin tana jin ciwon kai sai dai karfin halin da take yi. Tana idar da sallar Isha'i nan ta sake kwanciya kan sallayar, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Shi kam ko da ta dawo daga masallaci salar Isha'i nan ya gan ta kwance a saman sallaya tana barci. Tunawa da ya yi ba ta ci abinci ba ya sa ya ɗauki key din motarsa ya fice daga gidan. Gasashshiyar kaza ya siyo ya dawo gidan, bayan ya yi parking ɗin motar ya fito hannunsa rike da ledar kazar. Bayan ya huta kofar falon ya shiga ne ya rufe ƙofar. Upstairs ya haura da ledar ya ajiye a dinning table. Ya buɗe fridge ya ciro yoghurt a fridge ya ajiye a dinning table. Downstairs ya sauka ya karasa in da take kwance a saman sallaya. Durƙusawa ya yi ya daga ya cak ya haura sama da ita . Yana tsaka da taka step ɗin ta farka. A hankali ta bude idanunta shi kansa ya ji jikinta da zafi, tsuke fuska ta yi tana cewa. "Ka sauke ni" Bai saurare ta ba sai da ya kai falonsu da ke upstairs. Akan kujera ya dire ta ganin yadda ta tsuke ma sa fuska shi ma ya murtuke fuska ba wasa ya ce. "Tashi ki je ki yi wanka ki fito ki ci abinci ki sha magani." "Ni na ƙoshi kuma ba abinda ke damuna da zan sha magani ai." Ta yi maganar a tsiwace, Kallonta yake yi don bai taɓa tunanin tana da bakin tsiwa ba, don ba ta taɓa yi a gabansa ya gani ba. Cikin bayar da umarni ya ce. "Umarni na ba ki ki yi abun da na ce, idan kuma kika ƙi yi to fa ki sani zan shigo na ɗauko ki da kaina ne." Yana faɗar haka ya zauna a saman sofa yana ɗaukar wayrsa dake saman Centre table. S hankali ta tashi ta fara tafiya cikin sanyin jiki, idanunsa na kan waya, amma sam ba wayar yake kallo ba har yanzu idanunsa na kanta, a hankali take tafiya har ta shige. Yana sake mamakin yadda fatarta ta washe ta yi haske kuma ba na bilicin ba, ga fatarta sai ƙyalli da sheƙi take yi, ga wani sihirtaccen kyau da ya ga tana da shi wanda a baya sam bai gani ba. Cusa hannunsa ya yi cikin gashin kansa yana yamutsawa. *Abuja* _Ummee_ Sunan barin gidan ita da Jimoh wanda ke driving ba tare ta ya san in da suka nufa ba ya ce. "Madam ina za mu je?" Ba ta ma ji shi ba, hankalin ta na jan photon Makaho da Ma'eesha in da z su je asibiti da inda zasu je siyen waya tana rike da hannunsa, sai na ukun ranar da suka fita siyen Abu a cikin unguwar nan ma tana rike da hannunsa, fuskarta ɗauke da murmushi wanda ya kara bayyana tsantsan kyawunta. "Madam ina za mu je?" "Ya sake maimaita wa yana kallonta ta cikin madubin dake jikin motar "Gidan Yayana." Ta yi maganar tana ajiye wayar saman cinyarta. "Yanzu akan kana bibiyar sa shi ne ya yi maka shaƙar mutuwa?" ",Eh Madam dama da suka shiga asibiti ne na tsaya suka fito, bai juya ba amma wai ya san ina bin sa, shi ne ya tare na nape ya sa yarinyar ta shiga, bayan sun wuce ya juyo kaina. Jinjina kai ta yi tana cewa. "Ina mamakin yadda Jalaluddeen ya canza, wanda ko baya garin kullum sai mun yi waya duk yawan da wahalar aikinsa, amma wannan karon sai ya yi sati bai kira ni ba, kuma idan na kira wayar ba ta shiga. Na san hakan na da alaƙa da wannan yarinyar ne. Jinjina kai ta yi ba ta sake magana ba har suka isa gidan Alhaji Kabir Arzika. Horn motarsu ta yi, sai da security ya leƙo ta karamar kofar, ya tabbatar da su waye kafin ya bude ma su gate ɗin gidan. Shigar su kafin su kai parking lot ta sa Jimoh ya yi parking motar a harabar gidan. Fitowa ta yi a cikin motar yayin da ma'aikatan gidan ke gaishe ta, ta amsa ma su sama-sama saboda ranta a ɓace yake. Jimoh ya zauna cikin motar yana jiran fitowarta. Door bell ta shiga dannawa ba kakkautawa, cikin ma'aikatan da suke aiki a falon ta nufi ƙofar ta buɗe da sauri, don daga jin yadda aka danna ƙararrawar ƙofar sun san ba na lafiya be ne, zubawa suka yi suna gaishe ta, ba ta ama sa sai dai ta tamabaye su da. "Dr ta tafi asibiti ko tana ciki?" "Tana ciki." Suka amsa ma ta a tare. Kai tsaye ta nufi part ɗin Mom, bakin kofar ta yi knocking. Mom tana sauri za ta je asibiti sakamakon ana bukatar ta a asibitin cikin gaggawa. "Waye?" "Ni ce." Ummee ta faɗa cikin ɗaga murya. Mom cikin mamaki ta ce . "Hajiya Maryam da safiyar nan? Bismillah shigo." Ta faɗa daidai lokacin da take saka wayoyinta a cikin handbag. After dress ta saka saman kayan dake jikinta. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki Salam warahmatullah. Hajiya Maryam ke ce da safiyar nan?" "Eh." "Allah ya sa lafiya." "Ina fa lafiya dama ina tafe ne jan zancen Jalaluddeen." Sai da gaban Mom ya fadi don ta ɗauka wani abu ne ya faru da Ɗan nata ma fi soyuwa a zuciyarta. Dan duk da ba ita ta reni Jalaluddeen ba ba a hannunta ya tashi ba amma ta fi jin soyayyarsa fiye da Sadik da Sadiƙa, ko don yana Ɗan ta na fari ne oho. "Me ya faru da Jalaluddeen din." Ta faɗa cike da fargaba kasancewar ta san yanayin aikinsa yana da hatsari. "Ba abinda ya faru da shi." Ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke. "Tun da yake bai taɓa tsallake kwana ɗaya bai kira ni ba, amma yanzu sai ya yi sati kafin ya kira ni, kuma ko na kira wayrsa ba ta shiga, kuma na san kowane aiki ya tafi ina jin motsin sa, hankalina ya tashi na sa a je garin da yake a bincika ma ni ko yana lafiya, sakamako binciken da aka yi ma ni yana tare da wata yarinya ce a taƙauce ma gida ɗaya yake kwana da yarinyar gidan ma ɗaki daya rak a cikin gidan, wanda ba za'a kira shi gida ba sai dai kango. Kullum yana tare da ya yarinyar suna yawo hannunsa sarƙe cikin na juna suna yawo a gari." Shiru Mom ta yi kafin ta ce . "Why ki yi magana da shi ya yi ma ki bayanin komai, duk da na san ba zai aikata wani abun da ba daidai ba." "Wani magana bayan na faɗa ma ki tsawon sati ba na samun wayarsa, amma ke na san kullun yana kiran wayarki." Wani kallo Mom ta yi na ta kafin ta ce. ",Wa ya faɗa ma ki kullum yana kiran wayata." "Ai ba sai an faɗa ma ni ba, tun ranar da ya gane cewa ke ce mahaifiyarsa ba ni ce na haife shi ba ya fara rawar ƙafa akanki komai sai ya ambaci sunanki ni ya rage..." Dakatar da ita Mom ta yi ta hanyar ɗaga ma ta hannu,. "Dakata Hajiya Maryam, kar ki soma kawo wani zancen da bai da tushe, har kina zargin kullun sai ya kira ni a waya? Ko kuma kina son ki ce ma ni tun da ya gane ni ce uwarsa yake ƙaunata ko me? To ke idan sati yake yi ya kira ki a waya ni yau kwana goma kenan bai kira wayata ba, na yi ma sa uzurin yanayin aikin da yake yi ne ya sa haka, zanen cewa ta gane ni ce na haife shi yana so na ba ta taso ba. Dan har yanzu irin alkawar da yake ma ni na matar kawunsa haka yake ma ni ban ga abun da ya sauya ba, sai dai a cikin zuciyarsa. Don haka daga ranar da kika ɗauki Jalaluddeen kika tafi da shi na bar ma ki shi na yi addu'ar cikin da nake da shi Allah ya sauke ni lafiya. Na bar ma ki shi a lokacin ne saboda na ga Allah bai ba ki haihuwa ba, ni kuma yana ɗan shekara ɗaya na samu wani cikin. Hatta dangina na sanar da su cewa na bar ma ki Jalaluddeen har abada kada su saka shi a lissafin dangi kuma kada wanda ya sanar da shi ni na haife shi. Haka aka tafi yana ma ki kallon Mahaifiya yana ma Ni kallon Matar kawunsa. Ban so ya sani ba. Har wata rana ya zo gaishe da Alhaji da ya yi rashin lafiya ya tarar da ƴar ƙanwata ya fara son ta suka fara soyayya, na yi farin ciki da haka amma sai kika nuna ba ki son haɗin ya rabu da ita, ni ma na ce ya rabu da ita tun da mahaifiyarsa ba ta so haka ya hakura da ita. Kina bijiro ma sa da zancen za ki haɗa su aure da Yasmeen yarinyar da kika haifa da cikinki, hankalinsa ya tashi domin ya dauka uwa daya uba ɗaya suke, ke ce kika sanar da shi ba kece mahaifiyar sa ba wanda a lokacin ya san ni na haife shi. Ya amince da auren Yasmeen ko da kika sanar da ni addu'ar fatan alkhairi na yi ma ki, ban taɓa ce ma ki komai ba duk hukuncin da kike zartarwa akan Jalaluddeen ba na damuwa Ɗan ki ne kuma yana ma ki biyayya irin ta uwa, bai saba da ni kamar yadda ya saba da ke ba, bai gama sanin dangina ba ko ya zo gidan nan a matsayin baƙo yake zuwa ya gaishe mu ya ba tafi, don haka ki daina zargin na san komai da yake aikatawa ba abun da nasa ni ki nar ni na ji da abun da ke gabana, marasa lafiya na jira na a asibiti." Cikin ɓacin rai Ummee ta ce . "Ba zan taɓa yarda da wannan zancen naki ba, duk abinda Jalaluddeen yake aikatawa kin sani, don tun da ya gane kece uwarsa ya canza ma ni yanzu da a baya ne ba zai iya kwana bai ji murya ta ba. Yanzu ya daina jin magana ta, da yana jin magana ta da ba zai saka ƙafa ya bar garin nan ba tare da an yi bikinsu ba, ga shi yanzu da an yi bukin tun last month tun da an gama shirin komai, ya tafi na tsawon watanni ya fifita aikinsa akan aure." Ta karasa maganar ta na fice wa daga ɗakin. Mom dafe goshi ta yi tana zama bakin gadon. Ummee tana fita falo ta hadu da Dad yana saukowa. Dama Yaya kana ciki . Kallon ƙanwar tasa ya yi yana murmushi "Eh ina ciki Maryam,.lafiya dai ko?" "Ba lafiya ba gaskiya." "Subhanallah me ya faru?" "Gabadaya Jalaluddeen ya canza, ka duba ana saura wata ɗaya aurensa ya bar garin nan ya ce nan da sati Uku zai dawo, sati Uku shiru wata wata uku shiru har yanzu ba ba wanda ya san me yake yi.A taƙaice ma tare da wata mace yake a can." "Kin ga Maryam ki kwantar da hankalinki, har ya gama aikin da ya je yi ne sai kuma ya sa kansa wani aikin, idan ya kammala zai dawo. Duk satin da ya dawo a satin za'a ɗaura ma sa aure in sha Allah. Mace da kika ce kuma watakila tana taimaka masa ne wajen gudanar da aiki." Za ta yi wata ƙorafin ya ɗaga ma ta hannu don ya san halin ƙanwar tasa ba ta raina abun magana, kafin ya ce. "Ɗan ki yana jagorantan manyan jami'ai, tsara yadda za'a gudanar da bincike ko leƙen asiri, tattara da nazarin bayanan sirri. Bayar da rahoto ga manyan shugabanni, taimaka wa wajan tsara tsaron ƙasa. Shugabannin sa na son sa saboda kaifin basirarsa da hangen nesa, sirri da juriya, jarumtaka da riƙon amana. Ƙwarewar nazari da yanke shawara." Ɗan ki ba gamagarin mutum ba ne, ba za ki samu lokacinsa a daidai wanann lokacin ba, ki yi ta yi ma sa addu'a Allah ya kare shi a duk in da yake." "Amma har da matarka ba ta san halin da yake ciki ba take ɓoye ma ni?" "Maryam kada ki kawo wanan a ranki, domin kuwa Dr ta yi ma ki kawaici da sadaukarwa, shin ta taɓa nuna ma ki wata alama da ke nuna ita ta haifa Jalaluddeen?" Kai ta girgiza alamar a'a. " Ko ta taɓa nuna tana da iko akan Jalaluddeen?" Nan ma kai ta girgiza alamar a'a. Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce. "Ko kin san cewa lokacin da Jalaluddeen ya haɗu da ƙanwar Dr a gidan nan ya nuna yana son ta ba karamin farin ciki Dr ta yi ba, ganin Ɗan ta zai auri ƴar ƙanwarta . Amma kika nuna iko da isa kika ce bai isa ya aure ta ba kin zaɓa ma sa ƴar ki. Haka ya hakura ya yi ma ki biyayya, Dr ba ta nuna damuwa ba. To me ya sa yanzu kike tuhumar ta a kan lamarin Jalaluddeen bayan ba wata shaƙuwa ce tsakanin su ba, in fact bai fi shekara da sanin cewa Dr ta haife shi ba, wanda bayan sanin bai zo gidan nan sama da sau uku ba." Shiru Ummee ta yi sannan ta sauke ajiyar zuciya. "To Yaya ni zan tafi sai anjima." "Allah ya tsare ki gaida Mutanen gidan." Daga haka ta fice daga falon in da ta sami Jimoh yana jiranta. Dad ya nufi ɗakin Mom, da sallama ya shiga, yadda ya ga ta hada tagumi ya san zantukan ƙanwarsa ne suka taɓa ta. Zama ya yi gefenta ya yana cewa. "Dr har kin shirya?" "Eh na shirya." Ta fada tana kokarin saka farin gilashi a idanunta. "Ki yi hakuri da abun da Maryam ta yi, kin san ba ta da fahimta ne, amma in sha Allah na san ba wata matsala." Cikin damuwa ta ce. "Ni ba ni ce na fitar da sirrin cewa ni ce mahaifiyar Jalaluddeen, ita ta fasa sirrin ta hanyar ba shi auren ƴar ta, ban taɓa saka baki a lamarin da ya shafi Jalaluddeen ba, ita ce take yanke hukunci kan al'amuran shi kame yadda uwa ke yi wa ɗanta. Iyaka ta da shi daga gaisuwa . Sai idan azumi ya zo yake jido ma na kayayyaki na abinci da na sakawa da kyautar kudade, daga nan kuma sai wata shekara. Na san cewa shi yake ɗauke da nauyin gidanta cin su sha da sutura duk a wuyansa yake ya dauke ma su Wannan. Duk shekara sai sun je Umara duka shi ke yi, hatta dangina mijinta da Jalaluddeen yake kallon dangin ubansa ya kai da yawan su Makkah sun sauke farali, dangin ja sun ci moriyar dukiyarsa ne? Duk kawaici da alkunya da nake nunwa ba ta gani har za ta zo tana tuhuma na akan Ɗan da na haifa?" Dad ya san ranta ne ya ɓaci ɗin idan ba haka ba sama da shekara talatin da uku ba ta kiran Jalaluddeen da Ɗanta . *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣6️⃣ Dad ya san ranta ne ya ɓaci dan idan ba haka ba sama da shekara talatin da uku ba ta kiran Jalaluddeen da Ɗanta . "Ki yi haƙuri Dr " "Ya wuce amma ka ja wa ƙanwarka kunne." "In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba." A tare suka fito daga ɗakin in da ma'aikatan gidan suka jera breakfast a dinning table. Ba ta ko kalli dinning area ba ta nufi hanyar fita. "Dr ki tsaya ki yi breakfast ma na." "Ba lokaci ana jira na, zan yi a can." Daga haka ta fice ya raka ta har wurin motarta, da kanta take driving cikin nutsuwa ta bar gidan. _Makaho_ Yana kammala abun da zai yi da misalin ƙarfe uku da rabi ne ya miƙe tsaye. Kayan jikinsa ya cire ya saka kayan da ya zo da su a jikinsa. Duka wayoyinsa ya ajiye a nan, ya tafi da guda biyu ƙananu. Ɗaya na amfani domin aikinsa ne ɗaya kuma Wanda yake waya da Ma'eesha ne. Baƙin gilashinsa ya saka sannan ya saka takalmin soso da zo da su. Ya kashe komai da ke ɗakin sannan ya fito daga ɗakin. Har lokacin wanann mai nape na zaman jiransa, sai da ya fito ne ya shiga suka bar wajan. Nesa kaɗan da wajan aikinsa ya ajiye shi, kafin ya fito ya ɗauko sandarsa ya cigaba da dogarawa yana irin tafiyar da yake saba yi. Wajen sana'arsa ya ƙaraso da sallama, suka amsa ma sa, Bello me yalo yana yi ma sa sannu da dawowa kafin ya ce. "Na ga ka daɗe lafiya dai ko?" "Alhamdulillah wajen ne da nisa." "Allah sarki sannu." Gajeren murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Yana nan zaune sai ya ga wata mota ta gifta kan titin. Makaho ya cire tsohuwar wayrsa daga cikin aljihu, ba waya ce irin ta kowa ba, waya ce ta aikinsa. Ya yi magana ƙasa-ƙasa a cikin wayar yake cewa. "Target ya motsa." Daga ɗaya bangaren aka amsa da . "Kar ka bari ya ɓace." Sai ya koma ya cigaba da gyaran takalmin da yake gyarawa kamar babu abun da ya faru. Daga haka ya ɗan miƙe kasancewar yana da Ɗan tazara tsakanin sa da sauran mutane da suke Zaune kowa na sana'ar sa. Kiran sallar la'asar ce ta saka ya ajiye komai ya tashi yana cewa. "Bello don Allah taimaka ma ni da buta na yi alwala." Kasancewar suna ajiye ruwan sallah a bokiti mai murfi. Mai suyan awara dake kusa da su ta kalli Makaho ta ce. "Wallahi shi ya sa Khalifa kake ƙara burge ni, ba ka wasa sa ibada." Bai ce da ita Komai ba illa ya yi gajeren murmushi. Bello ya kawo ma sa ruwan,.sai ya karkace hannu yana laluben gefen da ba nan butar take ba, sai da Bello ya rike hannunsa yana cewa . "Ga ruwan nan." Ya karba yana godiya. Gefe ya ma tsa ya yi alwala kafin ya ce . "Jama'a ku tashi mu yi sallah lokaci na wuce wa yanzu za'a tayar." Wasu sun tashi wasu kuma ko a jikinsu. Bayan an idar da sallah ya fito daga masallacin gabaɗaya mai suyan awara ifanunta na kansa, tana ganin ikon Allah, cikkaken namiji mai cikar zati da haifa ya hadu ta ko ina sai dai jarabtarsa makanta da talauci. "Bana son yawan kallo." Ta ji maganar kamar daga sama, wanda sai da ganinta ya faɗi. Cike da mamaki ta ce. "Khalifa waye ke kallo ka?" "Ban san ko waye ba, amma ina ji a jikina ana kallona kuma kallo na ƙurilla." Wanda yake faci daga can gefe ne ya bude baki ya ce. "To meye abun kallo a jikin naka, nakasar za'a kalla ko me?" Kafin ya yi magana mai suyan awara ta ce. "Namiji ƙira da cikar zati , kyau da kwarjini." "Dalla rufe wa mutane baki Mallama ina kwarjini ga makaho?" Ya faɗa a fusace, dama yana jin haushi yana son me awara ba ta son sa, kuma ta yi ta yawan kallon makaho tana jan sa da fira duk da ba wani kula ta yake yi ba. Sai dai yana burge ta amma ba ta jin za ta iya soyayya da makaho talaka. Mai Yalo da ya sa baki yana nuna wa Mai faci ya daina abun da yake yi , wanda shi kuma Makaho ya ya ɗauki kayan aikinsa ya tafi. Don idan ya tsaya tabbas zai iya illata wannan mutumin kuma za'a san shi waye. _Ma'eesha_ Ta yi wanka tana jiran dawowar mijinta don tana ta damuwa tun karin safe bai ci komai ba, kamar ta sani kuwa dama bai ci komai ba, don ko ruwa bai sha a hotel ɗin ba. Da sallama ya shigo cikin gidan, ta ɗago kai ta kalle shi tana amsawa da . "Wa'alaika salam warahmatullah." Ta mike fuskarta ɗauke da fara'a ta karbi kayan hannunsa tana yi ma sa sannu da zuwa. "Yauwa ya gidan." "Alhamdulillah." Hannunsa ta riƙe ta taimaka ma sa ya zauna a tabarmar da ta shimfiɗa. Zama ya yi ta kawo ma sa pure water mai sanyi da ta siyo a kanti ta zuba a jug. Ya sha ruwan yana yi ma ta godiya. Abinci ta kawo ma sa yana ci tana yi ma sa fifita har ya gama. A hankali ya furta " Alhamdulillah." Murmushi ta yi tana cewa . "Ma sha Allah." Kallonsa ta yi na wasu second kafin ta ce . "Am na ce ba." "Me kika ce ranki ya daɗe?" "Na ce maganar sace ka da aka yi fa har yanzu hankalina bai kwanta ba, saboda rashin sanin manufar ma su satar naka, ga shi kai ba gani kake yi ba ballantana idan ka ga wani abu da bai ma ka ba ko makamancin abun da ya faru da kai ka nemi taimako a kowane waje kake. Idan ka fita gidan nan hankalina baya kwanciya sai na ga dwowar ka, ba na so na rasa ka a duniyata da ba na da kowa sai kai." Ta karasa mgana tana zubar da hawaye. "Kada ki damu in sha Allah ba abun da zai same ni." Sallamar mace suka ji daga kofar gidan, suka amsa yayin da ya tashi ya shiga ɗaki kafin mai sallamar ya shigo cikin ɗakin. Wata mata ce maƙociyarsu ta shigo gidan. "Sannu da zuwa." Ma'eesha ta faɗa cikin sakin fuska da walwala. "Yauwa sannu baiwar Allah." Matar ta faɗa tana zama a ranarma tare da ajiye madaidaiciyar jakar hannunta. Gaisawa suka yi kafin matar ta ce . "Sunana Bilikisu maƙociyarki ce duk da ba ki shiga jama'a ballantana a saba da juna." "Haka ne, in sha Allah zan shigo." Duka maganar da suke yi yana jin su daga cikin ɗaki, ita matar ba ta san cewa mijin Ma'eesha na gidan ba, don haka ta ce . "Talla na kawo ma ki ga su nan, kayan gyaran aure ne magungunan mata ma su kara ni'ima da Ɗanɗano " Shiru Ma'eesha ta yi tana tunani, ita me za ta yi da waɗan nan kayan, ita da ba ta da ko sisi, ko tana da kuɗi ma ai ba za ta siye ba, meye amfanin su mijin da ko hannunta bai taɓa rike wa ba ballantana wata Mu'amalar aure ya shiga tsakanin su. Don sai dai ita ta rike hannunsa amma shi bai taɓa rike hannunta ba, ta lura ko jikinta bai so ya haɗu da nasa, take zai zame jikinsa ta rasa dalili. Maganar matar ce ta dawo da ita cikin hayyacinta . "Wanne kike so ga su nan na fito ma ki da su." Ma'eesha ta kalli magunguna daga na kwali har na roba ga sunanyen su nan da yadda ake amfani da su. Murmushi ta yi kafin ta ce. "Allah ya kawo kasuwa." "Haba baiwar Allah ai yanzu mata ba sa zama ba gyara, idan kina da kyawu sai ki kara da wanka, yadda oga zai samu gamsuwa yadda ya kamata" Murmushi ta sake yi kafin ta ce . "Ina da su da yawa ne idan na siye wasu yanzu za su yi ma ni yawa ne." "Shi ke nan tun da haka kika ce, amma bari ba ba ki wasu kayan kyauta idan kika yi amfani da su da kanki za ki biyo ni." Magunguna ta dauka kala uku sai wani turare ta ba ta su kyauta. Ba ta da wani zaɓi don haka ta karba tana yi ma ta godiya. Fitar matar kenan sai ga Nasreen ta shigo da sallama. "Assalamu alaikum Matar Khalifa na nan?" Murmushi ta yi tana cewa . "Ina zan je ƙawata." Zama ta yi gefenta tana cewa. "Daga unguwa nake na ce bari na biyo na duba ki." "Allah sarki aiko na gode. Ya jikin Mama?" "Mama ta ji sauƙi sosai." "Ma sha Allah, Allah ya kara lafiya." "Amin ya Allah." Kallon magungunan ta yi kafin ta ce. "Tofah, Ma'eesha kayan mata kike siya?" Ba ta tanka ma ta ba ta dai yi murmushi. "To a dai bi a hankali a san irin abun da za'a dinga sha." "Ke ba fa sha nake yi ba, idan akwai macen auren da kika san tana sha kwashe ki kai ma ta." "Ban gane ba ke meye na siye to." "Ba siya na yi ba, ba ni ta yi kuma ba zai ma ni amfani ba kamar yadda ke ma ba zai ma ki ba." Cikin tashin fahimta Nasreen ta kalli Ma'eesha ta ce. "Ni da ba matar aure ba ke kuma ai kina da miji." "Hmmm sunan dai ina da miji ne kawai amma ba wani mu'amala ta aure ya taɓa haɗa ni da shi." Da mamaki ta kalle Ma'eesha kafin ta ce "Duk watannin da kuka yi ba wani abu da ya shiga tsakanin ki da shi kuna kwana daki ɗaya? Ko bai da lafiyar mazantaka ne?" "Ban sani ba wallahi. Kuma kin san wani abu?" "Sai kin faɗa." "Ina matuƙar so na ga na samu ciki, saboda ina son yara a rayuwata , burina na ganni rungume da baby na." "To ba ki tunanin a cikin wannan rayuwa da kike ciki za ku iya ɗaukar ɗawainiyar baby?" "Za mu iya domin Allah baya ɗorawa bawa abun da ya fi ƙarfinsa. Kuma ba mu fatan dauwama cikin wanann halin da muke ciki." "Okay yanzu kafin ki yi tunanin cikin da kike so ki fara tabbatar da lafiyar mijinki, idan kuna haɗa jiki wuri guda yanayinsa baya sauya wa?" "Ai baya yarda mu hada jiki da juna, da zaran na hada jiki da shi zai zame da sauri, ke ko kwanciya baya yarda mu yi a shimfiɗa ɗaya." Sai da Nasreen ta yi dariyar mai isarta kafin ta ce. "Ina da tabbacin lafiyarsa ƙalau, kuma yana nisanta kansa daga ke ne saboda baya son wani abu ya shiga a tsakanin ki da shi. Don idan da bai da lafiya ne ba zai damu dan kun hada jiki ballantana ya nisanta kanki da shi, kin ga alamar yana tsoron abun da zai iya biyo baya ne, sai dai ban san dalilinsa na yin hakan ba." Shiru Ma'eesha ta yi kafin ta ce . "Ba damuwa sai mu tafi a yadda yake so, don duk yadda nake son haihuwa ba yadda za'ayi ina ƴa mace da aka sani da al-kunya na kai kaina wajan namiji ." "Ba za ki kai kanki ba amma ai mace ce ke, akwai hanyoyi da yawa da za ki iya saka shi ya kawo kansa gare ki ba tare da ya shirya wa hakan ba." Murmushi ta yi kafin ta ce. "Bari na faɗa ma ki a kunne ." Ta matso dab da Ma'eesha ta matso da fuskarta saitin kunnen Ma'eesha, ta fara yi ma ta magana cikin raɗa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page5️⃣7️⃣ Ta matso dab da Ma'eesha ta matso da fuskarta saitin kunnen Ma'eesha, ta fara yi ma ta magana cikin raɗa. Wani kallo Ma'eesha ta yi ma ta kafin ta ce. ,"Ke ni za ki kai ki baro? Wallahi ba zan yi ba sai dai mu yi ta zama a haka, matukar sai na bi wannan hanyar da kika zo ma ni da ita." "To shi kenan tun da haka kika ce." Fira suka ɗan taɓa kaɗan kafin ta miƙe bayan ta ciro kayan kwalama da ta zo ma ta da su. ice cream ne da au Chocolate ta ajiye ma ta, sallama suka yi ta fice daga gidan,.ita kuma ta ɗauki ledar kayan da kuma kayan matan da maƙociyarsu ta kawo ma ta su ta shiga ɗakin. Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin , ya amsa mata ta kalle shi ta ce. "Lafiya ka zauna a ɗaki?" "Na ga kin yi bakuwa ne shi ne na ba ki waje ku gaisa." "Ayyah maƙociyarmu ce ita." "Ayyah me ta zo yi ne?" Kallon magungunan ta yi wanda shi ma kallon magungunan yake yi, wanda kallo daya ya yi wa magungunan ya ɗauke kai, kuma ya san me magungunan ya ƙunsa amma kasancewar kallon makaho take yi ma sa ya sa ba ya san magungunan yake kallo ba, don duk firar su har da na Nasreen ya ji su. Murmushi ta yi kafin ta ce. "Kawai ta zo wai mu gaisa ne da ita kasancewar ban taɓa shiga maƙota mun gaisa, da na zo ya kamata na je na gaida su. Bayan matar ta fita ne Nasreen ta zo ita ma akan hanya yake har ya tafi." "Ya jikin Maman nata?" "Da sauki ta ce." "Ma sha Allah, Allah ya kara ma ta lafiya." "Amin ya Allah." "Bari na je masallaci Magrib ta gabato." "Okay bari na zuba ma ka ruwa a buga." Daga nan ta fita daga dakin don zuba ma sa ruwa. _Nadra_ Bayan ta yi wanka ne ta saka kayan barci riga da wando farare na su taushi da santsi , wandon dogo ne shi , ta tufke gashin kanta sannan ya saka hula. Har za ta yi taurin akbar kwanta kuma sai ya tuna da gargadin da Fahad ya yi ma ta. Don haka sai ta ba nufi ƙofar fita daga ɗakin. Yana zaune a falo hannunsa rike da waya yana sarrafa ta, tana fitowa ya tsaya yana kallonta sosai, domin kuwa ta yi ma sa kyau sosai fiye da yadda yake tunani, ga kayan barcin su.n zauna ma ta ɗagwas kamar saboda ita aka yi kayan. Fuskarta a tsuke take, ganin ya tashi ya nufi dinning area ita ma ta tashi ta bi shi. Ba ta zauna ba ya saka ma ta naman kaza a plate ya zuba ma ta yoghurt a glass cup. "Zauna ki ci ki sha magani." "Na ƙoshi." Ta faɗa tana hade rai. Ɗaya kai ya yi ya kalle ta da kyau , kafin ya ce. "Ba na son gardama kuma ba na maimaita magana dayay, kar ki bari na sake yi ma ki magana. Zama ta yi tana tura ba ki , ga shi yunwar take ji amma kuma taurin kanta ya hana ta zauna ta ci. Ganin kallon da ya yi ma ta ne ya saka ta fara ci kamar za ta yi kuka . Sai da ta ci kusan rabi ta ce ta ƙoshi. Kofin gabanta ya yi ma ta nuni da shi, ta ɗauki yoghurt din ta shanye. Magani ya ba ta ta karba kamar za ta yi kuka, sai da ta shanye ta bar kasar Wajen. Da ido ya bi ta har ta shiga cikin ɗakinta. Shi ma ya ci sauran wanda ya rage sannan ya kwashe kayan ya kai kitchen. Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka ya yi shirin barcina ya kwanta kan lafiyayyen gadonsa don yin barci. Ita ma tana komawa ɗakinta ta wanke baki ta ɗauro alwala sannan ta kwanta barci. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Amma shi kam Fahad a nasa ɓangaren ba haka ba ne, domin ya kasa barci sai tunanin Nadra ya saka shi gaba. Lokaci zuwa lokaci yake jan tsuki ya kasa gane dalilin da ya sa yarinyar nan ta yi kane-kane a cikin zuciyarsa. Yarinya sai ka ce Mayya. Sai cikin dare barci ya yi nasarar ɗauke shi. _Ma'eesha_ Kamar yadda ya zame ma ta al'ada kullum sai Khalifa Makaho ya yi ma ta fifita take iya barci yau ma haka ne, yana tsaka da ma ta fifita barci ya yi awon gaba da ita. Yana ganin ta yi barci ne ya yi sauri ya je ya ɗauko wata ƙatamar fanka a cikin kayansa, ya bude fankar ya ja ta ta ɗan yi tsayi sannan ya kunna ya ajiye ma ta. Wani abu da ba ta sani ba, a duk lokacin da take yin barci Makaho kunna ma ta fanka yake yi ya fice daga gidan. Yakan je ne ya gudanar da bincikensa cikin dare. Saboda mutanen da yake yin aikin a kansu a dare suka fi yin harkokinsu. Don haka ne ma idan Ma'eeha ta yi barci yake ajiye ma ta fanka ya fice. Sai tsakiyar dare shiyoyin ƙarfe ƙarfe uku na dare yake dawowa, don a cikin awanni biyu yake kammala abun da ya fita da shi yake dawowa. Kuma ita ba ta san da fankar a cikin gidan ba, don ba taɓa ma sa kaya take yi ba. Bayan ya ajiye ma ta fankar ya cire kayansa ya sauya daga manyan kaya zuwa ƙananan kaya. Na'urar ɗaukar sauti ya ɗauka ya maƙala a jikinsa sannan ya ɗauki ɓoyayyer wayarsa ta zuwa aiki ya bar gidan. Nan Ma'eesha ta cigaba da barci ba tare da ta san baya gidan ba. Sai zuwa can da misalin karfe uku da rabi ya dawo gidan. Cikin sanɗa yake tafiya ya shigo cikin ɗakin. Wasu takardu ya ɗauka a cikin kayansa ya yi rubutu a jiki, ya shigar da wasu bayanai, kafin ya tashi ya karasa in da take kwance tana barci . Fankar ya dauke ya kashe sannan ya yi saurin zama a gabanta yana yi ma ta fifita . Baya karfe huɗu ta cika ne ta farka daga barcin, ganinsa ta yi zaune yana yi ma ya fifita, karɓe mafecin ta yi tana cewa. "Wai Yaya Khalifa me ya sa ba ka tausayin kanka ne?, Ta ya mutum ya zauna tun daga farkon dare har ƙarshen dare bai yi barci ba yana zaune, ko so kake yi ka samu wani ciwon mu shiga uku." "Na saba babu abun da zai same ni." "A'a barci ma lafiya ne ga jikin mu, yanzu ka kwanta na awa ɗaya idan ƙarfe biyar ta yi zan tayar da kai ka je masallaci ka yi sallah." Ganin yadda ta dage har tana ɓata rai ne ya saka shi dole ya amice zai kwanta, ganin yana ƙoƙarin zuwa kan tabarmarsa ne ya saka ta rike hannunsa tana cewa . "To ai yanzu ba kwanciya zan yi ba ballantana ka ce ba za ka kwanta tare da ni ba. Ka dawo kan katifar ka kwanta kai kaɗai ne za ka kwanta." Murmushi kawai yayi sannan ya hau kan katifar ya kwanta. Nan ta dinga yi ma sa fifita cikin mintuna goma barci ya yi awon gaba da shi. Tana yi ma sa fifita na tsawon awa ɗaya sannan ta fara tunanin tayar da shi don lokacin sallah ya gabato. Kyakkyawar fuskarsa ta zuba wa idanu tana kallonsa, sannan ta kira sunan sa a hankali. "Yaya Khalifa, Yaya Khalifa, Yaya Khalifa." A hankali ya amsa yana mai tashi zaune bakinsa da salati. "Ka yi hakuri ka ji dadin barci , na ga lokacin sallah ta yi ne shi ya sa." "Ba komai na gode Allah ya yi ma ki albarka." Da Amin ta amsa sannan suka fito daga ɗakin don lokacin sallah ya yi . _Sidra_ Tun da ta ga Fahad ya bar gidan da Nadra ranar ba ta iya barci ba, hankalinta ya kai ƙolololuwar tashi. Duk ta firgice ta fita hayyacinta musamman da ta ga yadda Fahad ke ta rawar ƙafa akan Nadra yayin da ita ki kallo ba ta ishe shi ba. Shirya wa ta yi ta nufi gidan Sady baby dan ta ba ta shawarar yadda za ta ɓullowa lamarin nan. Sallama ta yi wa su Mama da sunan za ta je gidan ƙawarta ba ta da lafiya. Duk da Mama ba ta son yawan fitar da Sidra ke yi sai dai ba ya da yadda za ta yi ta hana ta fita. Mama ta kalle ta ta ce. "Direba zai kai ki ko kuma ke za ki yi driving motar da kanki?" "Mama da kaina zan yi driving." "Okay ki ɗauki key din motar ga ta can, amma don Allah kada ki daɗe." "To Mama in sha Allah." Ta yi maganar tana nufar centat table in da Mama ke nuna ma ta key din motar . Fita ta yi daga cikin falon kafin ta kira wayar Sady baby. Daidai tana ƙarasawa wajen motar ne Sady baby ta ɗaga wayar tana cewa. "Hello ƙawata." Sidra ta ce kina gida ne?" "Eh ina gida ina fatan komai na tafiya daidai." "Hmm gani nan dai zuwa." Daga haka ta katse kiran wayar ta bude murfin motar ta shiga Sady baby ta tashi daga cikin saurayin da suke tare kan gado tana cewa "Ka bar gidan nan kafin ta zo ta same ka." "Wace ce ita da kike tsoron ta haka.?" Dariya ta yi kafin ta ce . "Ba tsoron ta nake yi ba, infact ma amfani da ita nake yi wajen cimma burina na mallakar Namijin da nake so na yake rayuwa da shi." Ya sauka daga kan gadon Yana cewa. "Wani namiji ne wannan?" "Fahad Majidaɗi." "Fahad Majidaɗi fa kika ce?" "Ƙwarai kuwa shi, shi ne Namijin da na dade ina so a rayuwata, wanda na san shi tun kafin Sidra ta san shi, a takaice me ni na sanar da ita ko waye shi da kuma irin son da nake yi ma sa. Wata rana mun haɗu da ita a wajan shopping muna magana sai kawai ga motar Fahad ga ƙaraso wajen. Nake sanar da ita ina masifar son sa amma ya wulakanta ni, madadin ta taimaka ma ni shi ne ta kutsa kanta gare shi, da na ga har suna shirin aure ni kuma ba zan taɓa bari ta mallake shi ba sai dai ni ya sa na ba ta gurguwar shawara, don na ga tana masifar son ta yi suna ta ɗaukaka, na muna ma ta damar zai wuce ta don wata shahararriya ta wulakanta, na yi amfani da damar na sa ta gudu ranar aurenta don rasa shi Ni kuma ba mallake shi. Amma cikin rashin sa'a iyayenta suka ba shi auren ƙanwarta a madadinta." Jinjina kai ya yi tana maida rigar jikinsa ya ce . "Tab shi ya sa sheɗan ya jinjina wa kaidin mace, to ga shi kin rasa ita ma ta rasa." Dariya mai sauti ta yi kafin ta ce. "Ban rasa ba, yanzu haka ina amfani da ita ne wajan ganin ta raba ƙanwarta da Fahad, na ba ta shawarar yadda za ta raba su, idan suka rabu ita ma na tona asirinta wajen iyayensu da shi dole ba za ta rayu da shi ba ka ga na buga wasa na yadda nake so" "Amma ai ba lallai ya so ki ba." "Na san hanyoyin da zan bi dole ya so ni." Ta yi maganar tana nuna ma sa kofar fita, ba musu saurayin ya fice yana jinjina kai Tashi ta yi ta faɗa bathroom don yin wanka. Bayan ta fito ta saka doguwar riga daidai lokacin da ta ji shigiwar motar Sidra. Ta window ta leka ta hange Sidra na fitowa daga cikin motar, sakin baki ta yi tana kallon motar wacce ta san cewa motar Sidra ba ta kai wannan tsada ba. Taɓe baki ta yi tana karasa shirya wa cikin sauri . Sallama Sidra ta hi tare da shogjwa cikin falon, zama ta yi kan Kujera daidai lokacin da Sady baby ta fito tana ma ta murmushi. Oyoyo ƙawata." Ta faɗa tana rungume Sidra tare da ƙaƙaro murmushin dole. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Pqge5️⃣8️⃣ Ta faɗa tana rungume Sidra tare da ƙaƙaro murmushin dole. "Sannu da zuwa ƙawata ya kike ya hakuri da rayuwa?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah." Zama ta yi gefenta tana cewa. "Meye labari?" "Hmmm ke dai bari na kasa gaskata abubuwan da ke faruwa a rayuwata ji nake kamar mafarki nake yi ba gaskiya ba ne." Tashi Sady baby ta yi ta kawo ma ta ruwar roba da glass cup, zuba ma ta ruwan ta yi ta mika ma ta, karba ta yi ta sha . _Nadra_ Bayan ta tashi da safe ta fara aikace-aikacen gidan, bayan ta gama da sama ta koma zuwa falon ƙasa. Kasancewar tana da ƙoƙarin aiki ba ta gajiya da aiki ba ta da ganda. Ɗakinsa ne kawai ba ta shiga ciki ta gyara ba, sai ta shiga kitchen don ɗora breakfast. Sai karfe tara na safe ya fito ya ji ƙamshi na fitowa daga cikin kitchen ɗin. A falo ya zauna ta dauki system ɗin sa yana amfani da shi. Bayan ta gama ne ta fito dauke da babban faranti da aka jera breakfast akai . Jera su ta yi a dinning table din sanann ta hango shi zaune a falon. Ƙarasawa ta yi gabansa cikin sanyi jiki ta durƙusa ta gaishe shi. "Ina kwana." "Lafiya lau." Ya amsa idanunsa na kan abun da yake yi. Tashi ta yi ta nufi bedroom ɗin ta, ya bi ta da kallo, kamar ta san yana kallonta sai ta juyo suka haɗa idanu, kau da kansa ya yi yana jin takaicin kallon da yake yi ma ta har ta kama shi yana kallonta. Ɗakinta ta wuce kai tsaye ta nufi bathroom don yin wanka. Ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar material ɗinkin bubu. Sanyayyen ƙamshi ke tashi daga jikinta. Kai tsaye ta nufi falon. Yana in da ta bar shi. "Breakfast na jiran ka Yaya Fahad." Ta faɗa har yau ba walwala ko sakin fuska a tare da ita. Bai tanka ma ta ba kamar yadda ba ta saka ran dama zai tanka ma ta ba. Nufar dinning area ta yi don hada ma sa breakfast. Cikin nutsuwa take yin komai nata har ta shirya ma sa komai. Tana gama wa ya ƙaraso wajen ya zauna, cin abincin ya fara yi yana mamakin yadda ta iya yin girki haka. Ita ba ta wani ci komai ba ruwan Lipton wanda ta dafa shi da kayan ƙamshi kawai ta sha. Bayan ya gama ne ya kalle ta ya ce . "Idan kin gama za mu je gidanku mu gaida su Umma." Farin cikin da ta tsinci kanta ciki ne ya kasa ɓoyuwa, cike da farin ciki ta ce . "Na gode." Bai ce ma ta komai ba ya tashi har zai bar wajan ya ce . "Waye zai gyara mun ɗaki?" "To ina zuwa." Komawa falo ya yi ya zauna. Ita kuma ta fara tattara kayan da suka yi amfani da su ta kai kitchen, sannan ta dawo ta gyara wajan ta goge. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa, falonsa fes kamar yau aka gyara, daga nan sai ta nufi bedroom. Toilet ta fara wankewa , sannan ta dawo ta gyara ma sa bedroom ɗin har zuwa falo. Bayan ta gama ne ta fita zuwa kitchen don ta yi wanke-wanke. Gani ya yi aikin sun yi ma ta yawa don haka take a wurin ya fara tunanin ko a nema ma ta mai taya ta aikin gidan ne. Ɗakinsa ya shiga don shirya wa, wanka ya fara yi ya fito ɗaure da towel yana tsane kansa da wani karamin towel ɗin. Shirya wa ya yi cikin manyan kaya, tsadadden yadi mai ruwan sararin samaniya. Yadin irin mai taushi nan ne ya saka hula wacce ta dace da shigarsa. Sai zuba ƙamshin turare yake yi, ya saka takalmi baƙi wanda shi ma hulɗar ta sa baka ce . Fitowa ya yi daga bedroom ɗin sa ya nufi ɗakinta dan ya sanar da ita idan ta shirya ta same shi a mota. _Nadra_ Fitowarta daga wanka kenan tana ɗaure wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyarta. Nan ya yi tozali da ita wa da hakan ya saka ya tsinci kansa a wani yanayi ma daban. Wani abu ya ji ya tsara ma sa tun daga kansa har zuwa babban yasar ƙafarsa. Wanda bai san lokacin da ya karasa gabanta, wanda ita kam ba ta ma san ya shigo ɗakin ba sai da ta gan shi a gabanta yana kokarin janyo ta jikinsa neta lura da shi. Taga-taga ta yi baya za ta fadi sakamakon santsi tiles cikin zafin mama ya janyo ta jikinsa sannan ya ɗaga ga can ya nufa gadonta da ita a hannunsa. Kuka ta saka ma sa tana ture shi amma ko gezau bai motsa ba. "Ki kwantar da hankalinki kin ji ba zan cutar da ke ba, na yi ma ki alƙawarin zan rayu da ke har zuwa ƙarshen rayuwata, I love you Nadra. Ni za ka yi wa dadin baki saboda kana son ka mori jikina." "Wallahi ba dadin baki ba ne da gaske nake ba zan iya rabuwa da ke ba ina son ki." "To shi ne ban ga kana nuna ma ni so myayya ba sai yanzu?" "Kece ba ki bani dama ba tun dawowa ta kika sauya." Ya yi maganar da kyar yana yana cikin halin buƙatuwa da ita sosai. "Shi ne ba ka bani hakurin laifin da ka yi ma ni ba ko? Wato idan jikin nawa wata masifar ce na jiƙa na sha ko?" Jikinsa na rawa yana ƙara ƙanƙame ta ya ce. "Na ba ki haƙuri tuba nake ba zan sake ba, ni da kaina zan jiƙa kuma na shanye kin ji?" Duk da Halin tsoro da take ciki bai hana ta yi ma sa dariya ba, ganin lokaci daya ya canza ba wannan jin kai da yake da shi ko nuna isa da taƙama yana bin ta duk yadda take so. Tana rike da towel ganin yana ƙoƙarin warware ma ta shi. "Yaya Fahad kada ka gama morar jikina ka wulakanta ni ka sake ni kamar yadda ka ce, na san ba ka so na ka sake..." Ya rufe ma ta baki da yatsarsa ya ce. "Duk abun da na faɗa ma ki yanzu gaskiya ne, zan rayu da ke har ƙarshen rayuwata na amshe ki matsayin matata uwar Ƴaƴana." "To amma Sunyi Sidra fa?" "Kada ki sake kira ma ni sunan ta. Please ki ba ni hadin kai na samu abun da yake halaliya ta ba zan iya jurewa ba, kina da ilimin addini kin san hukuncin matar da ta bijirewa bukatar mijinta ko,?" Hankalinta ya kara tashi ta sani tana cikin tsinuwar Mala'ikun Allah amma ba za ta iya jurewa ba." "Ka yi hakuri tsoro nake ji." "Na gane kuma na yi ma ki alƙawarin ba zan dasu da ke ba sai da amincewar ki, amma ki taimaka ki bari na biya buƙata ta da ke ta hanyar wasa da ke ba tare da ba kusance ki ba har sai ranar da kika yarda." "Kai ta jinjina ma sa tana hawaye." Rintse ifanunta ta yi tare da sakar ma sa towel ɗin da yake kokarin janye wa . Bakinsa ya saka cikin nata bakin ya shiga tsotsa kamar ya samu sweet. Yana sarrafa albarkatun jikinta yadda ransa yake so, kasancer ita ma ta sakar ma sa jiki, sai dai ba abun da take tunawa kamar kalaman Aunty Sidra, su ne suke yi ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta. Tambayar kanta take yi shin ya za ta yi? Za ta saɓa wa umarnin Allah ne don ya faranta wa baiwar sa? Ko kuma umarnin Allah za ta bi ta samu lada? Babu biyayya ga abun halitta wajen saɓawa Allah. Wani yanayi ta sake riskar kanta a ciki jin yadda yake tsotsan dukiyar fulaninta kamar jariri yana murnza ɗaya. Tsawon lokaci ya dauke sarrafa ta, ita kanta ba ta san lokacin da ya cire kayan jikinsa ba kasancewar idanunta na a rufe, ba shiri ga bude idanunta sakamakon jin ya kana hannunta ya ɗora a sanadar girmansa. Cikin tashin hankali ta kalle shi za ta janye hannunta ya matse hannun ya rike yadda ba za ta iya cire hannunta ba. Zuwa can ta ji ɗumi a cikin hannunta, ta kalli hannun ta ga abun da ya zuba ma ta. Yamutse fuska ta yi kamar za ta yi kuka yayin da ta mika ma ta toilet peper ta karba tana goge hannunta. Sumbatar gishinta ya yi tare da cewa "Thank you." "Mu je mu yi wanka." Make kafada ta yi tana cewa "Ka tafi kai kaɗai." Murmushi ya yi ma ta ya tashi ya nufi bathroom ya tsarkake jikinsa. Ko da ya fito ta daura towel ɗin ta tana jiran fitowarsa. Ya fito ɗaure da wani towel ya nufi ɗakinsa. Ita ma wankan ta yi sanann ta fito tana gyara gadon ta tattara kayansa da suka yi takure. Shirya wa ta yi cikin Abaya mafi ruwan toka ta dauki handbag da wayarta ta saka takalmi flat shoe. Ta dauki kayansa ta nufi ɗakinsa. Ta same shi ya shirya cikin wata ɗanyar shaddar fara yana ɗaura tsadadden agogon hannunsa sai zuba ƙamshi yake yi. Ta cikin mirror suka haɗa idanu, da sauri ta ɗauke kanta tana sunkuyar da kai. "Ki saka su a cikin washing machine" Kai tsaye ta nufi bathroom ɗin sa ta zuba su ciki kamar yadda ya umarce ta haka ta yi sannan ta fito. Har lokacin ta ƙi yarda su haɗa idanu da shi, dan wani kunyarsa take ji sosai ba kaɗan ba. Key din motarsa da wayoyinsa ya ɗauka sai wasu tarkardu da alama daga can zai je wani wurin ne.' Shi ya rufe ƙofar shiga don ita tuni ta fice. A wajen parking space ya same ta tsaye don ita ba ta san da wata motar zai tafi ba. Ma'aikatan gidan na gaishe ta. Sai a lokacin take lura da motarta sabuwa wanda Baban Fahad ya siya ma ta, duk da ba ta san lokacin da aka kawo motar ba. Ganin tana kallon motar ya ce "Motarki ce aka kawo key na falo dan mun dawo sai i na ba ki ." Ya yi maganar yana buɗe ma ta gaban motar, ta shiga ta zauna sannan ya zagaya wajan zaman direba ya zauna, key ya yi wa motar suka bar gidan. Ba abun da ke tashi daga cikin motar sai ƙamshin turarensa da sanyin A.C kawai ake ji. Kallonta ya yi ganin har lokacin kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle sun yi kyau. Yana mamakin irin kunyar da Nadra ke da shi. "Nadra." "Na'am Yaya." "Kada ki sake kira na da Yaya domin ba Yayanki ba ne, yau na ji kalan dangi." "To me zan kira ka?" "Ki zaba ma Ni sunan da kika ga ya dace." "Ni ban san sunan da ya dace ba." "Okay to kira ni da Fahad." "Wallahi ba zan iya ba ." "To zaɓi suna na masoya ki saka mun. " "Kunya nake ji " Dariya ya yi yan cewa. "Da sannu sai na raba ki da wannan kunyar da kike ji." "Ta ya ya?" " Da sannu zan mayar da ke mara kunya." *Tab wallahi ba na son rashin kunya da fitsara." "Ba irin wannan rashin kunyar ba, irin kunyar nan nawa da kike ki zan raba ki da shi, don zai iya ciyar da ni." Ba su yi tafiya mai nisa ba ya ya yi parking a wani gabanb super market. Kallon wajen ta yi don ba ta san me yake sunyi w wajen ba. "Me za ki siya wa su Umma tsaraba da su Ammi da Abba?" "Ba na da kuɗi." Ta yi maganar kanta a ƙasa, don kam ba ta da kudi ko da suka yi aure kudin sadakinta ne kawai a hannunta, kuma ta ranar wajen sallamar baƙi da ta dinga yi. "Ba ni account number naki." Ba musu ta karanta ma sa account number ɗin. Shigowar alert ta ji na Naira miliyan uku. A firgice ta kalle shi don kudin sun yi ma ta yawa. Za ta yi magana ya ce . "Fito mu je." Yana faɗa ya fita daga cikin motar zuwa cikin supermarket ɗin. _Makaho_ Bayan ya fito da safe zai je wajen sana'arsa, hannunsa ɗaya rike da kayan gyaran takalminsa, ɗaya kuma rike da sandar jagoransa, sai sauri yake yi kasancewar akwai wani jami'in da zai zo karbar rahoto daga hannunsa. Kuma idan jama'a suka taru a wajan za su iya fahimtar wani abu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Pqge5️⃣9️⃣ Bayan ya fito da safe zai je wajen sana'arsa hannunsa ɗaya rike da kayan gyaran takalminsa. Ɗaya hannun kuma rike da sandar jagoransa, sai sauri yake yi kasancewar akwai wani jami'in da zai zo karɓar rahoto da daga hannunsa. Kuma idan jama'a suka taru a wajen za su iya fahimtar wani abu. Cikin ƙanƙanin lokacin ya isa wajen sana'ar sa, sai sai akwai mutane duk da bai yi tsammanin zuwan kowa ba. Ya gaisa da mai Yalo da sauran mutanen da suke wajan . Zama ya yi bakin aikinsa, sai ga wani karnin yaro ya kawo takalminnsa gyara. Karba ya yi ya gyara ma sa yaron mai kimanin shekaru shida a duniya. Bayan ya gyara ma yaron takalmi ne yaron ya ba shi dubu ɗaya ya ce . "Uncle ga shi ka ba ni canji." "Ya yi maganar yana miƙa ma sa dubu dayan da ke hannunsa. Karba ya yi yana cewa. "Nawa ne nan?" "Dubu ɗaya ne uncle." "Ba na da canji." Ya yi maganar yana miƙa ma sa dubu ɗayan." "To uncle Ina za mu samu canji." Murmushi ya yi saboda yaron ya burge shi ya ce . "ka tafi ba bar ma ka kudin gyaran." "To uncle na gode." Yaron ya tafi yana murmushi, mai faci dake gefe ya ce . "Dama canji ka nema ka karɓi ko Naira hamsin ce, don na san waye uban yaron nan yana da rufin asiri, kudin da yake samu a rana ɗaya sai ka yi wata ɗaya ba ka tara shi ba!" Bai tanka ma sa ba ya yi kamar bai ji shi ba. Wani mutum ya zo ya yi sallama . "Assalamu alaikum." Gabadaya suka amsa ma sa da . "Wa'alaika salam." "Na kawo gyaran takalmi ne." Ya yi magana yana nuna ma makaho tsakaninsa. Jarɓa makaho ya yi cikin hikima da basira da Allah ya yi ma sa ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro wani micro SD makaho ya manna shi a ƙasan takalmi da wani ƙarfe kamar ƙugiya a tafin takalmi. Cikin ƙwarewa ya manna shi da jikin takalmin ya nannaɗe shi da zare ya ɗinke takalmin. Miƙa ma sa ya yi tare cewa. "To yallaɓai na gama." "Nawa ne kudin aikin ka?" "Naira ɗari ce ." Ya ciro Naira ɗari daga cikin aljihun wandonsa ya a mika ma sa, makaho ya ba shi takalmin ya karba ya tafi . Yana barin wajen makahon ya kira waya yayin da yake shiga cikin motarsa. Ana ɗauka daga can ɓangaren ya ce . "Hello sir." Daga can ɓangaren aka ce . "Ka samu ganin Jalaluddeen?" "Eh yanzu haka ma bayanan suna hannuna ya ba ni." "Gud job, aikinsa yana kyau. Ka kama hanyar Abuja yanzu kada ka ɓata lokaci." "Okay sir." Ya faɗa yana yi wa motar key ya bar wajan . _Nadra_ Tana ganin ya ya fita bayan ya ce ta fito su je ta bishi ita ma. Zuciyarta cike da mamakin yadda Fahad Majidaɗi ya tura ma ta Naira miliyan uku. Ta saka a ranta za ta yi wa Ummanta siyayya da Abba har da Ammi. Suna shiga ciki ya ce . "Ki duba tsarabar da kika ga ya dace ki siya ma su." Jinjina kai ta yi har lokacin tana mamakin sa. Shi kuma ɓangaren kayan abinci ya nufa. Ita kuma tana bangaren wajen kayan sakawa. Atamfofi guda biyar da ɗaukarwa Ummanta. Da mayafaiya ma su kyau da tsada, sai sarka da Ɗan kunne ma su kyau kala biyu. Ta ɗaukarwa Abba shaddodi kala uku ma su kyau da tsada.. sai huluna da suka shiga da kowane kaya. Ta ɗaukarwa kakarta Ammi atamfa kala biyu ma su kyau. Bayan ta gama cire wa ta waiga ta kalli bayanta , sai ta ga Fahad ne yake kallonta . "Kin gama ne?" Kai ya jinjina ma sa alamar eh. "Okay mu je." Ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ya tura kayan da ta zaɓa. Ko da aka yi lissafin Kudin tana shirin bude handbag ɗin ta don ta fito da ATM card nata sai ta ga Fahad ya mika nasa ATM card ɗinsa. Kallonsa take yi da mamaki yadda ya tura ma ta kuɗi har Naira miliyan uku wanda ita a tunaninta da su za ta yi tsarabar iyayenta, amma sai ta ga ya biya. A bayan mota aka zuba ma su kayan,abun da ya kara ba ta mamaki shi ne yadda ta ga uban kayan abinci da ya siya aka zuba a motar, kama daga kan buhun shinkafa biyu buhun semovita biyu spaghetti da macaroni da cus-cusvhar zuwa indomie komai bibbiyu galan man ja da man gyaɗa haka aka tara komai har zuwa su maggi da kayan tea. Ta kasa magana har ya bude ma ta gaban motar ta zauna a gefen sa, sannan ya yi wa motar key suka bar wajen. Kasancewar ba su da nisa da wajan da suka yi siyayya da gidan Abba. A kofar gidan ya yi horn maigadi ya leƙo ganin Fahad ya magale gate ɗin yana ta fara'a. Ma'aikatan gidan da farin ciki suka ƙaraso wajen motar suna yi ma su sannu da zuwa. Don sunji kewar Nadra. Fahad ya fara fitowa sanann ya buɗe wa Nadra ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Baba maigadi da direban gidan da suke nuna farin cikin zuwanta. Cikin girmamawa durƙusa ta gaida su, suka amsa suna ma ta Allah sanya alkhairi ya ba su zaman lafiya. Ciki suka nufa yayin da ta ɗauki ledar tsarabar su Umma ta shiga falon. Fahad ya tsaya daga waje yana jiran a yi ma sa iso. Da sallama ta shiga ciki, ta yi Sa'a kuwa kowa na nan, Abba na gida bai fita ba, Umma na zaune a gefensa, sai Ammi dake kwance kan doguwar kujera mai zaman mutum uku. Gabadaya suka amsa sallamar fuskar kowa dauke da farin ciki. Nadra ta rungume Umma tana kuka. "Ikon Allah, to me ye abun kuka kuma?" Cewar Ammi tana mamakin Nadra. Ganin haka Abba murmushi kawai ya yi , don duk wanda ya kalli Nadra ya san ba ta cikin tashin hankali. Ta ciko ta yi kyau sosai. "Ina shi Fahad ɗin yake?" Kuka kawai take yi ta kasa magana. Su kuma sai dariya suke yi ma ta. Wacce ke yi wa Umma girki ne ta fito za ta je kasuwa, ta gaida Nadra lokacin da ta tsagaita kuka. Tana fita ta ga Fahad waje ta dawo take cewa . "Nadra kika bar mijinki waje ba ki ma sa iso ba?" Sai a lokacin ta tana da shi yayin da Ammi ke salati. "Ya kika bar shi waje kuma?" Cewar Abba yana miƙewa tsaye. Yana bude kofar ya ga Fahad yayin da Fahad ya durƙusa ya gaida Abba cikin girmamawa. Ya amsa cikin da farin cikin ganinsa, hannunsa ya ja suka shiga ciki. Ya gaida Ammi da Umma sannan ya kalli Nadra dake goge hawaye. "Ka ga sakaryar matarka kukan shagwaba take yi saboda ta ga Ummanta." Murjushi ya yi tare da cewa. "Umma ya karfin jikin?" "Alhamdulillah na ji sauƙi Fahad." ,"Allah ya kara lafiya." Ya faɗa yana kallon Nadra da take wani narkewa a jikin Umma.. Ruwa da lemu mai aikinsu ta kawo ma su. Fahad ya sha ruwan kawai . Abba ya kalli Fahad ya ce . "Ya aiki yaushe ka dawo?" "Juya na dawo Abba." "Ma sha Allah, Allah ya taimaka." "Amin ya Allah." "Yauwa a kara hakuri da Nadra ka san yarinya ce karama, don Allah ka kara hakuri da ita komai zai yi daidai." Kafin ya yi magana ne Ammi ta bude baki ta ce. "Wani hakuri zai yi da Nadra, ai Allah ne ke son sa da gata. Yanzu da ba don Allah yana son ka ba ai da waccen gantalalliyar ya bar ma ka a matsayin matar aure, da yanzu kana nan kana ta fama da ita kila da yanzu na zuwan ka sai ka kawo ƙarar ta. Amma da Allah ya so ka da rahama da kwanciyar hankali ya ba ka Kamilar yarinya ai da yanzu kana nan kana tagumi." "Umma ta yi shiru tana goge ƙoƙarin ɗauke ƙwallar ta ta je sun cika ma ta idanu. Fahad ya kalle ta cike da tausaya yana ayyyana girman soyayya irin ta uwa akan ƴaƴanta. Cikin sanyin murya ya ce . "Mama ki daina damuwa Sidra tana gidan Mahaifina cikin ƙoshin lafiya. Tana sakewa ta yi rayuwata da kowa, yadda ba mai takura ta a gidan nan haka adabi ma ba mai takura ma ta za ta yi rayuwarta yadda yake so , sai dai kewa da ba'a rasa ba. Jinjina kai ta yi tana yi wa Fahad murmushi ta ce. ."Allah ya yi ma ka albarka." Da Amin ya amsa yana miƙewa tsaye ya ce . "Ni xan tafi anjima zan dawo na dauke ta mu koma gidan." Addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya suka yi ma sa ya fice. _Makaho_ Kasancewar baya son abokan kasuwancin sa da suke sana'a tare su zarge shi ya sa wannan karon bai bar kayan aikinsa a wajen ba, kada su fara zargin ina yake zuwa . Don haka ya dauki kayan aikinsa ya yi ma su sallama da niyyar da wuce gida ne. Mai Yalo ya kalle shi ya ce . "Lafiya za ka tafi da wuri haka?" ",Eh to ba na jin dadi kaina ne yake ma ni ciwo zan je na keanta." "Subhanallah, Allah ya ba ka lafiya Mallam Khalifa." "Amin ya Allah." Mai suyan awara ta kalle shi ta ce "Sorry kyakkyawa Allah ya sauwake." Da yake ya san haka take kiransa ya amsa da Amin ya fara tafiya da sandarsa da kuma kayan aikinsa. Sai da ya yi tafiya mai ɗan nisa sannan ya tsaya cak, mai nape da ke bisa ya tsaya a gabansa, Nan da nan ya shiga suka kama hanyar hotel ɗin yake zuwa . Bayan sun isa hotel ɗin ne ya bar kayan aikinsa na gyaran takalmi da sandarsa ya shiga cikin hotel ɗin. Key din dakinsa ya karɓa sannan haura sama. Ɗakin ya bude sannan ya saka key ya rufe ta ciki. A.C ya kunna sannan ya nufi bathroom ya sakarwa kansa shower, 🚿 wanka ya yi sannan ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani karamin towel yana tsane ruwan kansa. Man shafawarsa ya shafa ya saka ƙananan kaya sannan ya karasa ya zauna kan kujera in da kayan aikinsa yake kan table, kama daga laptop ɗinsa da wayoyinsa suke . Wayarsa ya ɗauka ya lalubo lambar Ummee ya danna ma ta kira, don ya san halinta yanzu haka yana can ta tayar da hankalinta. *Abuja* Ummee na zaune a falo tana kwantar wa da Yasmeen da hankali, kan damuwa da ta yi na rashin ji daga Jalaluddeen. "Ummee tsawon kawanki kenan ban ji daga gare shi ba, yanzu idan muka yi aure haka zai dinga yi ma ni ya share ni ba kiran waya idan yana aiki? A gaskiya ni kan idan aka ɗaura ma na aure sai sai dai duk inda zai je ya yadu tare da ni." Kafin Ummee ta yi magana kiran Jalaluddeen ya shigo cikin wayar. Da sauri ga daga daga tana cewa. "Son lafiya tsawon kwanaki ba kira ina kiran wayrka ba ta shiga kuma ka kasa kira na ko? Ba ka tunanin halin da zan shiga ko don ba isasshen lafiya gare mi ba ko?" "Tuba nake Ummeena, yanayin aiki ne wallahi , kin san sau da taka tsantsan." "Duk da haka hankali na zai fi kwanciya idan ina jin motsinka. Na tabbatar kana lafiya." "Idan kin ji shiru lafiya kenan." Kamar ta yi ma sa Maganar yarinyar da aka ce yana tare da ita sai kuma ta fasa, ta bari sai ya dawo kafin ta ji daga gare shi. "Ummee kowa na lafiya ?" "Eh lafiya lau dai dai Yasmeen ce dai ga ta nan." Ta yi maganar tana mika wa Yasmeen wayar. "Subhanallah me ya same ta?" Tashi Yasmeen ta yi saboda kunyar Ummee ba za ta sake ta yi magana yadda take so ba." Sai da ta shiga bedroom ɗin ta ta zube a kan gado sannan ta shagwaɓe murya ta ce . "Hello" "Yasmeen ya kike ?' "Ba na lafiya fa Yaya Jalal." "Subhanallah me ya same ki?" "Rashin ganinka da ciwon son ka ne za su illata ni." "Subhanallah, ba na ce ki daina saka damuwa a ranki b" "Yaya Jalal damuwa dole ne, a satin da za'ayi bikin mu ka tafi wanda dalilin haka aka ɗaga bikin dai ka dawo, da yanzu nuna matsayin ma'urata ko?" "Haka ne, kin san komai na Allah ne kuma komai da lokacin sa, Allah ne bai yi ba a wancan lokaci." "Haka ne, amma na damu da rashin ka sosai, amma na san kai ba ka damu da rashina ba da ka dinga nema na a waya." "Ba haka ba ne, kina raina Yasmeen amma yanayin aiki ne ya sa ba ki samu na." Fira suka yi a ƙalla mintinan ashirin sannan ya ma ta sallama. Kafin ya katse kiran wayar ta ce. "Yaushe za ka dawo?" "Sai zuwa gaba." "I can't wait wallahi, sai dai na biyo ka in da kake." "Ko kin zo garin ina mai tabbatar ma ki wahala za ki yi ba za su ki ganni ba." "To Allah ya dawo mun da mai lafiya my Yaya Jalal" "Amin ya Allah " Cikin sanyin murya ta ce . "I love you." "Love you too." Murmushi ta yi wanda sai da ya ji sautin murmushinta sannan ya kashe kiran wayar. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce ✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page 6️⃣0️⃣ Murmushi ta yi wanda sai da ya ji sautin murmushinta sannan ya kashe kiran wayar. Zuciyarta fara tas ta ji muryarsa kuma ya mayarsa hankalinta ya kwanta. Ta fito fakon tana murmushi daidai lokacin da Yusuf ya dawo. Kallonta ya tsaya yana yi sakamakon ganin kwana biyu tana fama da ƙunci da baƙin rai, yau sai ya ga tana ta fara'a don haka ya ce. "Ummee wannan kuma fa farin ciki na mene ne?" Ya yi maganar yana zama kan kujerar da ke fuskantar Ummee yana jiran jin ta bakinta. Murmushi Ummee ta yi yayin da take karbar wayar da Yasmeen ke miƙa ma ta. "Bari kawai wai daga Yayanku ya kira waya shi ne duk na wannan farin cikin." "Okay Yaya Jalal ya kira waya yau kenan ?" "Eh yanzu muka gama magana da shi." Taɓe baki ya yi ya kalli Yasmeen ya ce . "Wallahi kina da aiki in dai Yaya Jalal ne kike ma irin wannan son " Kamar za ta yi kuka ta ce . "Haba Yaya Yusuf me ya sa za ka ce haka?" "Na ga son naki da kike ma sa ya fi wanda yake ma ki ne, infact ma Yaya Jalal baya da lokacin ki sai na aikinsa kuma..." Kafin ta karasa maganar da zai yi ne sai Ummee ta dakatar da shi "Ka ga Yusuf ka kiyaye ni kana ji na ko? Akan me za ka ce ba ya son ta? Ko an tilasta ma sa auren ta ne? Ina da kansa ya amince da zai aure ta ba wanda ya ma sa dole, ka fita a idanuna na." "Ummee ai ba cewa na yi baya son ta ba, na ce son ta ya fi na sa yawa." "To sai me ya yi ta fi ma na kai ina mai son naka take?" Dariya ya yi yana nufar bedroom ɗin sa. Daga nan ya lalubo lambar wayar Dr mahaifiyarsa ya kira. Sai dai wayar a kashe take kiran bai shiga ba, don lokacin tana ɗakin tiyata ne za ta cire wa wata mata baby a cikinta. Matar babyn ya mutu a cikinta har ya fara ruɓewa, shi ne Mom take yi ma ta tiyata ta cire gawar babyn. Ganin kiran bai shiga ba ya tura ma ta text messages. 'AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE KI MOM. NA KIRA WAYAR A KASHE NA SAN KINA HOSPITAL NE YANZU . FATAN KUNA LAFIYA.' Bayan ya gama turawa ne ya kira Lambar Mahaifinsa Alhaji Kabir Arzika. Sai dai shi na wayar a kashe. Tunanin kiran wayar Sadik ƙaninsa ya yi , sai dai shi kuma wayar na ringing ba'a ɗaga ba. Don shi ma Doctor Sadik yana duba marasa lafiya ne wayarsa kuma tana silen ya bar ta a office.. Lambar wayar Abbee ya kira suka gaisa kafin ya tamabaye shi aiki, ya amsa da Alhamdulillah. Daga nan suka ɗan taɓa fira, don shi ma Abbee ba karamin kewarsa ya ji ba. Don shi ma Jalaluddeen yana ƙaunar Abbee wanda sai daga baya ya gane ba shi ne mahaifinsa ba. Don Abbee ya nuna wa Jalaluddeen ƙauna kamar yadda Ummee ta nuna ma sa. Bayan sun ɗan taɓa fira ne ya yi ma sa sallama ya ajiye wayar bayan ya kashe. _Fahad_ Sai karfe biyar na yamma da Fahad ya kammala abun da yake yi zai je ya ɗauki Nadra. A kofar gidan ya yi horn maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga Shi sam ya mance da siyayyan kayan abincin da ya yi wa su Abba. Sai da ya yi parking ya da ma'aikatan gidan suka dinga ɗibar kayan abincin suna kai wa ciki. Abba saboda zuwan Nadra ya fasa fita ko ina, ya zauna ya ba ta lokacin da suna ta fita . Sun nuna jin dadin tsarabar da ta siya ma su suna ya godiya ga sanya ma ta albarka . Suna nan zaune a falon suka ga an fara shigo da kayan abinci. Mamaki ya kama su suna shirin yin tambaya dai diraban su Umma ya ce . "Mijin Nadra ya ce mu shigo da su ciki." Store aka ce su shiga da su ciki su ajiye . Mamaki da al'ajbabi ne ya kama su ganin yawan kayan abincin da ya siya ma su. Sai da suka gama shiga da su ya ba su kyautar kudi suna ta godiya . Da sallama ya shiga ciki. Bayan sun amsa na sa ya karasa ya gaida su. "Abba ya yi ma sa fadar kayan sun yi yawa ai. Ya ce ba su yi yawa ba ai yi wa kai ne. Godiya da sanya albarka suka dinga yi ma sa. Umma ta cewa Nadra ta dauki handbag ɗin ta da hijab su tafi. Marairaice fuska ta yi amma ganin yadda Umma ta murtuke ma ta fuska ya sa ta tashi ta dauki handbag ɗin da hijabi ta saka takalmi suka tafi. Tun daga ranar suka fara rayuwa mai daɗi, cike da nuna wa juna kulawa rayuwa. A ɗaki ɗaya s gado ɗaya suke kwana. Sai dai har lokacin Fahad bai sake yunkurin cewa zai yi sex da ita ba. Kamar yadda ya yi ma ta alkawarin cewa ba zai taɓa yi mu'amalar aure da ita ba sai ranar da ta yarda . Sai dai idan sha'awar ta ta motsa ma sa ya ɗan yi wasanni da ita ya rage zafi. Da zaran ta ga yana neman wuce makaɗi da rawa za ta saka ma sa kuka. Haka zai hakura ya ƙyale ta. Yau ma bayan ta kammala aikinta da yamma tana zaune a falo ya dawo gidan. Horn ɗin mota ta ji maigadi ya wangale ma sa gate ya shigo . Parking ya yi sannan ya fito ya shiga ciki. Tana zaune a falo ya dawo, yana ganinta ya tsaya daga bakin ƙofa ya ware ma ta hannu alamar ta zo gare shi. Ba musu ta tashi tana tafiya har ta karasa gabansa ta shige cikin ƙirjinsa ya rungume ta. Sumbatar ta a goshi ya yi daidai lokacin da wayarsa ta soma ringing. Ganin bakuwar lamba bai ɗauka ba, ya ja hannunta suka fara tafiya . "Sannu da dawowa." Sannu ki ya masa yana zama akan kujera ya zaunar da ita saman cinyarsa. Kiran aka aka sake yi ta kalle shi ta ce . "Ka ɗaga ma na ba ka san dalilin kiran ba." Bai ce ma ta komai ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya fara aika ma ta da wani zazzafan kiss. Ba ta hana shi ba sai na mayar ma sa da martani da ta fara yi . Zare bakinsa ya yi daga nata ya kalle ta da idanunsa da suka fara canza launi zuwa ja ya ce. "Nadra na gaji da wannan azabtar da ni da kike yi . Idan horo kike yi ma ni akan laifin da na aikata ma ki na horu haka nan ki tausaya ma ni ki ba ni hakkina. Na yi ƙoƙari ai a ce tun daren farkon da muka yi da ke a gidan Baba har yanzu? Kullun idan kika ga ina shirin biyan buƙata ta sai ki saka ma ni kuka? Haka zan haƙura na ƙyale ki. Ba ki tausaya wa halin da nake shiga? Don Allah ki amince ki bari mu raya sunna a wanann daren ki daina tsoro ba zan cutar da ke ba. Ita kanta ta san ya yi hakuri don haka ta ɗaga ma sa kai alamar ta amince. Cike da farin ciki ya kara ƙanƙame ta daidai lokacin da kiran wayar ta sake shigiwa wayarsa . Picking call din ya yi sannan ya saka a hands free. "Assalamu alaikum." Suka ji sallamar wani daga cikin wayar. "Wa'alaika salam." Ya amsa yana jiran ne na cikin wayar zai ce . "Kai ne Fahad Umar Majidaɗi?" "Eh ni ne." "To ga wata mara lafiya cikin mawuyacin hali take an kawo ta nan asibiti." "Wani asibiti?" "Wace ce?" "Sunan ta Sidra a wayar ta muka samu lambar ka saboda lambar take yawan kira duk da ba mu ga alamar kana amsa kiran nata ba " Nadra na ji an ce Sidra zumbur ta mike daga cinyarsa tana hawaye. Kallonta ya yi sannan ya ce. "Ga ni nan zuwa." Tana ganin ya mike tsaye ta ce . "Ɗin Allah zan bi ka mu tafi tare." Ta yi maganar tana kuka, sanin ba za ta zauna ba ne ya sa ya ce ta dauki hijabi su tafi . Tana hawaye ta saka hijabi ta bi bayansa suka fice daga cikin falon. Direbansa ya sa ya kai su yayin da su kuma suka zauna bayan motar yana rarrashinta. Bayan sun isa ne ya kira lambar da aka kira shi, aka sanar da su cewa tana Aminity word. Kai tsaye suka shiga suka gan ta kwance kamar gawa. Nadra ta Fashe da kuka tana tsige bakinta. Doctor ya kalli Nadra ya ce. "Wace ce ita?" "Ƙanwarta ce ita." "Okay ku same ni a office ɗina." Bin bayansa suka yi zuwa cikin officer din. Zama suka yi suna jiran jin me zai ce . "Ina iyayen ta suke ?" "Ba sa nan za ka iya sanar da mu kai tsaye." Farin glass din dake idanunsa ya cire ya kalle su daya bayan daya sannan ya ce. "Ina mai sanar da ku cewa ƴar uwarku Sidra ta kamu da cutar Heart fuilure, da Hausa ana kiran cutar da gazawar zuciya. Saboda zuciya ta daina aiki yadda ya kamata. Gazawar zuciya cuta ce dake faruwa idan zuciya ba ta iya tura jini yadda ya kamata zuwa ga sauran jiki. A yanzu haka cutar ta kai mataki mai tsanani (Advanced stage) zuciyar Sidra ta riga da ta yi nauyi sosai, idan ba ta samu kulawa ko magani ba to rayuwarta za ta iya ƙarewa a cikin watanni. Za ta iya mutuwa a cikin watanni, amma idan ta samu kulawa za ta iya rayuwa fiye da haka sosai. Musamman idan ta samu canjin ruyuwa, magungunan na musamman da kulawar likitoci. Idan har kuna son rayuwar ta ya yi tsayi sosai sai da taimakon ku, yawan saka ta farin ciki to zuciyarta za ta dinga samun sauƙi. Sannan ku dinga ƙara ma ta ƙarfin guiwa. Cin magani abinci mai kyau da kula da ita sosai . Saka ta farin ciki zai taimaka wa jikinta ya yi aiki daidai. Taimakawa ƙwaƙwalwa da zuciya. A guji ɓacin ranta ko shiga damuwa mai tsanani ballantana ta shiga halin bakin ciki ." Kukan da Nadra ke rike wa tun ɗazu ne ya ƙwace ma ta. Ta tausayawa Auntyn nata sosai . Ganin haka ya sa Likita ya dinga kwantar ma ta da hankali ta hanyar nuna ma ta cewa wannan fa hasashe ne. Tashi ta yi a guje ta fita ta nufi ɗakin da aka kwantar da Sidra. Shi kansa Fahad ya shiga tashin hankali sosai, amma ya aro jarumtaka ya yafa ya sa ba'a gane tashin hankali da yake ciki ba. Tashi ya yi ya bi bayan Nadra zuwa dakin da 'Sidra take. _Mom_ Bayan ta fito daga ɗakin tiyata ne ta shiga ɗakunan wasu marasa lafiya ta duba su. A gajiye ga koma office ɗin ta. Fridge ta buɗe ta dauki ruwan riba mai sanyi ta sha. Wayoyinta dake kashe ta ɗauka ta kunna su. Ganin saƙo ya shigo daga babban ɗanta Jalaluddeen. Jiki na rawa ta shiga bude messages ɗin. Bayan ta gama karantawa ne ta yi murmushi tare da furta "Allah ya kare ka ya ba ka nasara a rayuwa." Soyayyar Jalaluddeen na daban ne a zucuyar Dr, domin ta fi jin sa a zuciyarta fiye da sauran yaranta. Duk da cewar tun yana ɗan shekara ɗaya ta rabu da shi amma har yanzu tana jin sa a ranta ko don ba hannunta ya tashi ba ne oho. Ko ƙasar idan ta zo tana addu'a Allah ya sa ta zo gaishe su kafin ya koma. Bayan ta gama duba message ɗin ne ta danna ma sa kira. Bugu biyu ya ɗauka ta ji sallamarsa cikin muryarsa mai amo. "Assalamu alaikum." "Wa'alaika salam." "Mom ina wuni." "Lafiya lau Jalaluddeen ya kake ya aikin?" "Alhamdulillah Mom, na kira bai shiga ba da alama kina asibiti ko?" "Eh da zan yi operation ne na kashe wayoyin." "Okay Allah ya sa an yi a sa'a." "Amin ya rabbil izzati." "Ka yi magana da Umminka kuwa?" "Eh mun ji waya yau." "Okay amma ka dinga kokarin kiranta kullum ka san halinta in dai a kanka ne, dan dole take bari ka yi nisa da su, idan baka kiran wayarta ita ma ba ta samunka takan shiga danuwa sosai . "To Mom." "Ka yi waya da Yasmeen?" "Eh ita ma mun yi waya da ita." "Ba dai wata matsala ko?" "Ba komai. Na yi kewar gida." "To za ka bar aikin ka zo ka gan mu ne ki yaya?" "Eh zan zo na yi kwana biyu sai na dawo." "To Allah ya kawo ka lafiya ya kare ka ya ba ka nasara akan abun da ka sa a gaba." Cikin jin dadi yake amsawa . Sallama suka yi ya katse kiran wayar. Daidai lokacin kiran wayar Ma'eesha ke shogowa cikin karamin wayarsa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣1️⃣ Daidai lokacin kiran Ma'eesha ya shigo cikin karamin wayarsa. Sai da kiran ya katse sannan ya sake bi bayan kira. Kiran na shiga wayar ta ta ɗaga tare da yin sallama. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki salam." "Ina wuni ya aikinn?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ma sha Allah." "Ina fatan kina lafiya, kuma ba wata matsala ko?" "Gaskiya ba zan samu kwanciyar ba sai na ga dawowar ka gida?" Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce. "Ki kwantar da hankali in sha Allah ba wata matsala da za ta biyo baya. Gobe ma in sha Allah zan yi tafiya ta kwana biyu?" Cikin tashin hankali ta ce. "A'a, a'a, a'a don Allah, ina za ka je wa kake da shi?" "Yanzu ne nake jin labarin an samu wasu da suka dawo a ƙauyen mu,.ina son na je na duba ko akwai dangina a cikinsusu." Shiru ta yi kafin ta ce. "Amma ai bai kamata ka tafi kai kadai ba cikin halin da kake ciki, bugu da ƙari kuma ai ba ka da kuɗin mota." "Eh haka ne ba na da kuɗin mota, amma akwai motar ɗaukar kaya da za ta tafi Adamawa . Zan bi motar na zauna ko a samun buhuhunan kayan dake bayan motar ne?" "Shiru ta yi kafin ta yi wani tunani ta ce." "Ma su motar za su bari ka bi su ne?" "Eh suna bari ai, har mun yi magana da direba motar." "Gaskiya bai kamata ka tafi kai kaɗai ba sai dai mu tafi tare." "Bari na dawo sai mu yi magana." "Okay sai ka dawo." Daga haka nan ya katse kiran wayar yana tunanin hanyar da zai ɓullowa Ma'eesha. Tashi ya yi yana kokarin barin wajen hotel ɗin don zuwa shawo kan Ma'eesha. _Nadra_ Tana zaune saman kujerar gaban gadon da Sidra take kwance. Tana rike da hannun Sidra ta zuba ma ta idanun ta da suka rikiɗe zuwa ja sakamakon kukan da ta sha. Sidra tana barci ba ta ma san me ke faruwa ba, yayin da Fahad yake tsaye jingine da bango ya rungume hannayensa a ƙirji ya zuba ma su idanu. Turo ƙofar aka yi da sallama. Gabdaya suka amsa Nadra na ƙokarin goge hawayen da ke idanunta. Baba, Mama, Inna, sai kuma Rumaisa su ne suka shigo cikin ɗakin. Fahad ya yaushe su suka masa suna yi ma sa ya mai jiki. Sai kuma Nadra ta gaishe su suka amsa suna tambayar ta ya mai jiki. Tambayar ba'asi suka yi Fahad ya yi ma su bayanin da Doctor ya yi ma su. Tabbas hankalin su ya tashi matuƙa kuma sun tausaya wa Sidra. Baba ya kira Abban su Sidra yake sanar da shi halin da Sidra take ciki . Buɗar bakinsa ya ce Allah ya ba ta lafiya. Daga haka ya yi ma sa sallama ya kashe wayarsa. Baba yana matukar mamaki irin zafi da kafiya da Abba yake da shi. Kwanan Sidra uku a asibiti Nadra da Fahad ke tare da ita. Sai dai kullum sai su Mama sun zo gaishe su, kuma su suke aiko da abincin safe da rana da kuma dare. Ranar da za'ayi discharging nasu daga asibiti kowa na nan. Baba, Mama, Inna. Bayan likita ya ba su shawarwarin yadda za'a kula da ita da kuma da kiyaye ɓacin ranta ya kuma rubuta ma su magunguna. Sidra ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, ta san gidan Baba za ta koma wanda ba za ta so hakan ba, don haka ta kalli kowa sannan ta fara magana cikin sanyin murya. "Ina ji a jikina kamar ba zan daɗe a duniya ba, iyayena sun juya ma ni baya. Don haka ina son na rayu tare da ƴar uwata Nadra. Ina son na ganni a kusa da ita don idan na mutu ina tare da ita buƙatata ta biya, ta wani ɓangaren zan ji kamar ina tare da ajalinsa ne " Shiru ɗakin ya ɗauka na tsawon mintinan biyu ba wanda ya yi magana, kafin ta sake yin magana ta ce . "Baba, Mama, da kuma Inna, don Allah ku yi hakuri ban raina abun da kuka yi ma ni ba amma ina neman alfarma ku bar ni ta koma gidan Nadra da zama zan yi farin ciki da hakan." Caraf ina ta yi saurin cewa. "Ta ya ya za ki koma gidan ƙanwarki da zama? Nadra fa ƙanwarki ce ba Yayar ki ba, ai abun ba tsari." "Inna ku yi hakuri ku bar ta ta koma gidan nawa, tana son kasancewa da ni, kuma ga halin da take ciki ko kin manta abun da Doctor ya ce ne na a dinga yi ma ta abun da take so?" "Ke dalla maganar Doctor maganar Allah ce?" "Inna tun da ita ma ƙanwar ta goyi bayan hakan ki bar su kawai Allah ya ba ta lafiya." Shi dai Fahad bai ce komai ba ya kau fa kansa gefe. Nadra ta kalle shi ta ce. Yaya Fahad ka amince ta koma gidanka da zama? Zan yi farin ciki ni ma ita ma haka za ta yi farin ciki da hakan, a halin yanzu ba ta da wanda ya fi ni , Please ka amince ma ni." "Duk yadda kike so ki yi ai gidanki ne." Ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce ma ta ba ta shiga yi ma sa godiya. Ita dai Mama ba ta ce komai ba, amma fa dukkan alama ba ta so hakan ba. _Makaho_ Da sallama ya shigo cikin gidan. Ma'eesha dake zaune kan tabarma ta haɗa tagumi tana tunanin tafiyar da ya ce zai yi. "Amin wa'alaika salam." Ta amsa tana mikewa tsaye ta nufi in da yake. "Sannu da zuwa." Ta ce tana amsar kayan aikinsa dake hannunsa. "Yauwa sannu mar'atussaliha." "Ka zauna ga tabarma nan a gabanka." Ita kuma ta nufi ɗaki ta ajiye ma sa kayan shoe maker nasa. Pure watar dake cikin leda ta ɗauko ta kawo ma sa, sannan ta kawo ma sa abuncin da ta dafa. Shinkafa da wake da mai da yaji ta dafa. Ruwan ya fara sha sannan ya fara cin abincin. Tana yi ma sa fifita tana yi ma sa fira cike da shauƙi. Sai da ya ci kusan rabin abincin sannan ya yi hamdala tare da yi ma ta godiya . "Na gode Allah ya yi ma ki albarka ya kawo ranar da zan saka ma ki hidima da sadaukarwar da kika yi akaina." Murmushi ta yi tana cewa. "Amin Mijina. Dama ina son mu tattauna kan zancen tafiyarka ne, yanzu tafiya za ka yi ka bar ni ni kaɗai?" "Ki yi haƙuri Ma'eesha ba daɗewa zan yi ba zan dawo, in sha Allah ba zan wuce kwana biyu ba zan dawo." "To kana da tabbacin cewa su ɗin danginka ne wadan da aka ce sun dawo?" "Eh to ban sani ba sai na je na tabbatar." "Idan ba danginka ba ne fa?" "Sai na dawo mu cigaba da rayuwa a haka." "Idan kuma ya kasance su danginka ne za ka dawo ka ɗauke ni mu koma can ne da zama?" "Ba zancen komawa can da zama, domin garin da babu kwanciyar hankali me ake yi da shi? Ko su na ba barinsu zan yi ba za mu dawo nan ne su nemi sana'ar yi." "Amma ina tsoron zama gida ni kaɗai ba kowa a kusa da ni." Shiru ya yi yana nazarin abun yi kafin ya ce . "Zan yi magana da Mallam Liman ya taimaka ma na da jikarsa A'isha, na ga jininki ya haɗu da yarinyar sosai har takan shigo ko?" Jingina kai ta yi tana cewa "A'isha mutumiyata ce ita takan shigo ita da kakarta, lokacin da nake siyar da gawayi ita take ɗaura mun." "Haka ne, zan nemi Alfarma wajen Mahaifinta ." "To na gode." Ta faɗa tana murmushi. "Yauwa kina ji na ko?" "Eh ina ji." Ta tattara hankalin ta da nutsuwar ya zuwa gare shi. "Akwai wata mata da take ba wa mata tallafin kuɗi domin su yi kasuwanci, jiya mun je tare da abokan zamana na wajen sana'ar. Mun same ta ta kuma yi alƙwarin taimakawa ma na, wato za ta ba Matayen mu jarin da za su yi sana'a. In sha Allah ina saka ran kina ciki. Na bayar da sunan ki da lambar wayarki za ki iya jin kira kowane lokaci. Cike da farin ciki take kallon sa tana murmushi. "Allah ya sa mu ji alkhairi." "Amin ya Allah." "Bari na je masallaci idan na hadu da Mallam Liman zan sanar da shi komai . Ruwa a buta ta kawo masa a buta ya yi alwala ya nufi masallaci. A daren ranar bayan an gama sallar isha'i ya sanarwa Mallam Liman zancen A'isha . Kai tsaye ya amince ma sa tare da yi masa addu'ar Allah ya sanya alkhairi. Washegari tun da asuba ya yi wanka ya shirya. Ya nufi masallaci don yin sallar asuba. Ana idar da Sallah bai zauna Kamar yadda ya saba zama ba, kasancewa tafiya da zai yi. Duk wasu muhimman abubuwan da zai bukata dama tun cikin dare ya haɗa su a cikin jakar kayansa . Sai kayan sakawar sa kala ɗaya ya ɗauka, su ma kayan ya ɗauka ne saboda kada Ma'eesha ta yi magana kai. Ba ta yi kokarin haɗa ma sa breakfast ba kamar yadda ta so, shi kuma ya ɗauka saboda zai yi asubanci ne ba ta yi ba, yayin da ita kuma ta ɓangaren ta babu komai a gidan na ci ne da za su ci ya saka ba ta yi wani yunƙuri ba. Kuma ta san ko da ta faɗa ma sa babu abun da za su ci a gidan bai da kudi sai dai ya kara shiga damuwa. Don haka ya yi shiru ba tare da da nuna damuwa ba. Ta rike ma sa jakar yayin da shi kuma ya lalubi sanadar jagoransa ya fara tafiya. Suna zuwa kofar gidan ya haka ta fita ya ce ta koma ba sai ta raka shi ba. Gani take yi kamar idan ya tafi ba zai dawo ba. Har ya fara tafiya sai ta rike hannunsa, ya kalli hannun ya kalle ta. "Gani nake yi kamar idan ka tafi ba za ka dawo ba, ina tsoron wani abu ya same ka yadda ka bani labarin garinku na tsorata da shi, idan na rasa ka ya rayuwa ta za ta kasance a wanan duniyar fa ba na da kowa?" "Kina da kowa Ma'eesha, ki jira lokaci in sha Allah wata rana sai labari, na yi ma ki alkawarin zan nemo ma ki dangin mahaifiyar ki s duk in da suke a faɗin duniyar nan." Murmushi ta yi tana goge hawaye ta ce . "Ta ina za ka fara neman su? Wacce ko ita mahaifiyar rawa ba ta san komai ba akan ta, tun tana yarinya karama aka kai ta gidan marayun, wanda ita ma bude ido ta yi ta ga kanta a cikin gidan. Kada ka yi ma ni alkawarin da ka san ba za ka iya cika shi ba." "Zan iya ." Ya faɗa cike da kwarin gwiwa. Murmushi kawai ta yi don ta san ba abu ba ne mai sauƙi. Sai da ya tabbatar ya kwantar ma ta da hankali ta samu nutsuwa sannan ya yi ma ta sallama ya tafi. Yana tafiya rataye da jakar da ya karba a hannun ta fatan hannunsa da sanadar jagoransa. Tana kallon sa har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta koma cikin gidan tana fashewa da kuka. Yana fitowa daga layin kasancewar gari bai yi gama haske ba, don haka ba mutane. Wata baƙar baƙar mota ce take gefen titi, kai tsaye ya nufi motar, kafin ya karasa matuƙin motar ya fito da sauri ya zo ya bude ka sa bayan motar. Shiga ya yi sannan ya rufe masa murfin ya zagaya mazaunin direba ya shiga tare da yi wa motar key. Kai tsaye hotel suka nufa, yana shiga ɗakinsa ya yi wanka. Ya shirya cikin tsadaddun suit black shirt din ciki White me sai tie Black and white. Sai ƙamshin tsadaddun turarensa yake yi, ya daura agogon hannunsa ya sanya takalmi. Ba jimawa ya gama shirin sa. Sai dai ya canza jaka, ba wacce ya bar gida da ita zai tafi ba, sannan kayan da ya dauko a can gidan ma ya bar su a can bai zo da su ba. Wayoyinsa da mahimman abubuwan da zai bukata ya ɗauka. Wayarsa wacce Ma'eesha ta siya ma sa ce ya ɗauka yana kallon wayar kafin ya kashe ta. Futowa ya yi ya nufi motar kai tsaya, direban ya bude ma sa da sauri cikin girmamawa. Kai tsaye suka nufi airport, wanda isar su ba jimawa jirgi ya tashi. Direban ya juya da motar ɗin don komawa, bayan jirgin su ya ɗaga. Ba wanda ya sanar wa zancen dawowar sa, don haka ba wanda ya yi tunanin dawowarsa. Sai bayan saukar jirgin su ne ya fito daga cikin jirgin. Cike da mamaki da al'ajabi yake kallon motar gabansa. A hankali ba cikin motar ya ziro ƙafarsa wajen yana sakar ma sa sanyayyen murmushi. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣2️⃣ Sai bayan saukar jirgin su ne ya fito daga cikin jirgin. Cike da mamaki da al'ajabi yake kallon motar gabansa, a hankali na cikin motar ya ziro ƙafarsa wajen yana sakar ma sa sanyayyen murmushi. "Sadik?" "Na'am Yaya Jalal." "Wa ya faɗa ma ka tasowa ta?" "Babu na dai ritsa ka ne. Tun shekaranjiya da kuka yi waya fa Mom ka sanar da ita za ka dawo nan fa kwanaki biyu, shi ne yau na ce ko kwana ne sai dai na yi a airport amma sai na je na ɗaukoka." Ya yi maganar yana rungume Yayan nasa, hakan ya sa shi ma ya rungume shi . Sake juna suka yi yayin da da Sadik ya karɓi jakar hannun Jalaluddeen ya sa a bayan motar. Sannan ya bude wa Jalaluddeen gaban Mota wajen me zaman banza yayin da shi kuma ya zagaya mazaunin direba ya yi wa motar key suka bar airport ɗin. Yana tsaka fa driving yayin da shi kuma Jalaluddeen ya ya kunna wayoyinsa, amma bai kunna na wajen Ma'eesha ba. Hankalinsa na kan waya ne ya ɗago yana kallon Sadik, saboda ya san airport da gidan Ummee ba nisa, ya ci a ce sun karasa gida. Da mamaki yake kallon Sadik yana kuma kallon hanya,." "Kai Mallam ina za ka kai Ni ne?" "Gida mana." "Wannan ne hanayar gidan?" "Eh ma na, hanyar gidan iyayen asali ba na iyayen riƙo ba. Haka kawai kullum idan ka dawo daga tafiya sai ka sayka can?" "Sadik kana da rigima, yi ina kake so na sauka idan ba can ba?" "A'a gaskiya Yaya Jalal tun da Allah ya sa ka san cewa ba Ummee ba ce ta haife ka Mom ce ko? To ya kamata ko sau ɗaya ka yi ma ta abun da za ta ji cewa ita ma uwa ce tana da kai, ba komai ba nake so ka yi illa iyaka ka sauka a gidan kuma ka kwana tare da mu, mun gaji da sai dai ka zo ka gaishe mu na mintinan ka tafi. To yanzu ba wanann zuwan kana tare da mu dai gobe ka tafi can gidan. Amma fa ka kashe watoyin ka." Kafin ya yi magana har sun iso gidan Horn Sadik ya yi a kofar gidan , yayin da wani security taso ya wangale ma su katafaren tangamemen gate din gidan. Ya cinna hancin motar a katafaren gidan, kai tsaye parking lot ya nufa, in da aka tars manyan motoci na alfarma. Ke wajan . Fitowa ya yi bayan Sadik ya bude ma sa murfin motar Sadik ya ɗauki jakar kayansa suka nufi cikin gidan.. Ma'aikatan na ma sannu da zuwa ga hannu kwanan yake amsa ma su. Yana tura kofar tare da sallama. Mom wacce ta fito don uwa asibiti ta amsa tana kallonsa da mamaki. Don ba ta san ya iso ba, kuma ba ta yi tsammanin ganinsa a gidanta ba, don ko da ta faɗawa Sadik dawowar Jalal ta ɗsuka asibiti ya tafi ashe shi ɗauko Yayansa ya je ba. Ganin Sadik da jaka ya sa ta game cewa ɗaukimo Jalaluddeen ya tafi. "Mom ba ki ga yae8n ki ba, can na tafi na ce ko zan kwana a can sai na je na ɗauko shi na kawo shi nan zuwa gobe ya tafi can." "Yaushe wanna Gwaggon ta ku Maryam za ta bar shi ya kwana s nan." "Ba za ta san ya zo ba, ko ta sani ma menene ne ai ina ce nan ne guda. Mahaifinsa na asali ta isa ta hana shi shi ne?" "Amma yanzu ...." Sai ta fasa maganar da za ta yi . "Ya karasa har cikin falin Mom na kallonsa duk da ta ga ya nufo ta amma ba ta san nufin sa ba sai da ta ji ya rungume ta. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, shi ma wani ƙaunar mahaifiyar tasa ne yake Ratsa zuciyarsa . Ya durƙuda kasa ya gaishe ta, ta amsa tana tambayar da aiki, ya amsa da Alhamdulillah. "Ka je ka yi wanka ka fito ka ci abinci." "Ina Sadduƙa?" "Ta tafi school." Ya nufi ɗakin da ya ga Sadik ya kai ma sa kayansa. Ta bi shi da kallo tana jin ƙaunar ɗan nata har ranta. _Fahad_ Bayan an yi discharging na Sidra a asibiti ya dauke ta ita da Nadra zuwa gida, kamar yadda Nadra ta buƙata. Baba da Mama da Inna kuma suka nufi gida tun da Sidra ta ki yarda ta bi su kuma Nadra ta roki Fahad ya amince ta bi su, ba shi da wani zaɓin da ya wuce ya amince ko don farin cikin Nadra. Yana driving Nadra na gefen sa yayin da Sidra ke bayan motar. Shiru ba abun da kake ji a cikin motar sai sanyin A.C da mayen turaren da Fahad ke amfani da shi. Har suka karasa gidan kowa ya kasa cewa komai. Horn ya yi Maigadi ya wangale ma sa ƙofa ya cinna hancin motar a cikin gidan. Bayan ya yi parking ne Nadra ta fara fitowa daga motar, sannan ta bude wa Sidra ta fito. "Sannu Aunty." Ta faɗa cike da kulawa. A hankali Sidra ta fito tana jinjina ma ta kai ba tare da ta amsa ba. Kayan da suka dawo da su daga asibitin Nadra ta dauka a bayan motar. Fahad ya fito ba tare da ya ce komai ba ya nufi kofar shiga fakon. Sai sam babu walwala s fuskarsa . Bude ƙofar ya yi ya matsa gefe alamar su shiga ciki. Da sallama a bakin Nadra ta shiga Sidra na bayanta, shi kuma ya take ma su baya. Kai tsaye upstairs ya nufa suna bayansa ƙarar taka step ya ji ya juyo ya kalle su. Ganin alamar cewa a sama Nadra ke niyyar ba wa Sidra masauki ne ya sa shi cewa. "A ƙasa masaukin baƙi yake ko kin manta ne?" "Yaya Fahad Aunty Sidra ce fa Yayata ce?" "Na sani shi ya sa nake tunatar da ke a ƙasa masaukin baƙi yake, ba wai don yayarki ba ko Yayata ce ta zo a ƙasa za'a sauke ta. Nan saman iya na ma su gidan sai ɗakunan yaran da za mu haifa in sha Allah." Yana gama faɗar haka ya ci gaba da tafiya zuwa ɗakinsa ya shige. Murmushi Nadra ta ƙaƙaro don son ta kwantarwa da Sidra hankali ta ce. "Na tuna ma Aunty ba ɗaki a nan sai ƙasa mu sauka na raka ki?" Wani kallo Sidra ta yi wa Nadra kafin ta ce . "Ban gane ba ɗaki ba, ko kin manta ni na faɗi irin tsarin da nake so sannan aka bi tsarin da na so wajen gina gidan . Ko kin manta da suna na aka gina gidan? Ɗakuna biyar ne a ciki, ɗaki ɗaki ɗaya naki ɗaya nasa sauran ɗakuna uku ba kowa a ciki shi ne ba za ku iya bani ɗaya na, ta yadda za ku dinga jin motsina ba? Ba komai na gode." Tana faɗar haka ta juya da sauri ta fara sauka daga matattakalar kai tsaye ta nufi ɗakin baƙi ta shige da sauri. _Jalaluddeen_ Yana shiga cikin ɗakin ya zube kan tangamemen gadon dake cikin ɗakin. Sanyin A.C da ƙamshin room freshner na ratsa shi. Kasancewar Sadik ya gyara ma sa ɗakin. Sai da ya kwashe tsawon mintuna ashirin kafin ya mike ya fara rage kayan jikinsa. Bathroom ya shiga ya wanda shi ma kansa abun kallo ne, tsaya wa ya yi yana kallon kansa a jikin tangamemen mirror dake jikin bangon banɗakin. Shi kansa ya san ya ɗan rame. Daidaita ruwan 🚿 dake bathroom din ya yi daidai yadda yake so bai yi zafi ba kuma bai yi sanyi ba . Shower gel ya ɗauka ya yi wanka da shi. Dai fa ya kammala wankan sannan ya fito sanye da bathrobe sai wani karamin towel da yake goge ruwan kansa. Jakar kayansa ya bude ya fito da ƙananan kayan da zai saka. Ya shirya cikin ƙananan kayan da ya zo da su a jaka ya fesa turarensa mai ƙamshi. Babu tunanin da yake yi kamar na Ma'eesha yadda ya fito daga gidan take kuka. Tausayinn ta mai tsanani ne ya kama shi . Ɗaya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya lalubo wata lambar ya danna ma ta kira. Bugu ɗaya aka ɗaga daga can ɓangaren aka ce. "Barka da rana yallaɓal." "Barka dai Adamu ya kake?" "Lafiya lau sir." "Yauwa kamar yadda na faɗa ma ka za ka nemi mata guda biyu wadanda kake mu'amala da su, ka ba su Naira dubu ɗari biyar ₦500,000 su kai kuɗin zuwa ga gidan da na sanar da kai su faɗa wa matar gidan cewa tallafi ne wanda mijinta makaho ya sanar da ita za'a ba su." "Okay sir, yanzu ba sa nan sai zuwa yamma za su shigo garin, in sha Allah zuwa gobe da safe saƙon ka zai isa zuwa gidan da ka ce." "To na gode." "Ba komai Yallaɓal." Sallama suka yi ya katse kiran wayar. Yana ajiye wayar sai aka turo ƙofar da ƙarfi, ba kowa ba ce illa Sadiƙa ta shigo aguje ta shigo rungume shi cike da murna. "Yaya Jalala you are welcome." "Thank you." Sakin sa ta yi tana murmushi tare da cewa. "Wallahi yanzu Yaya Sadik ya kira ni yake sanar da ni, ai tuni na bar school na dawo gida saboda kai." Daidai lokacin Sadik shi ma ya shigo yana cewa "Food is ready." Gabadaya suka fita daga ɗakin suka nufi dinning area. Mom na zaune tana kallonsa yadda suka fito a jere fuskar kowannen su ɗauke da annuri. Farin ciki ne yake ji har kasan ranta. Masu aiki biyu ne tsaye a wajen suna jiran ma su gidan su buƙaci abun da za'a zuba ma su sai su zuba ma su. Sadik ne ya ja wa Ya Jalal kujera ya zauna sanan suka zazzauna. Ma su aikin ne suka yi serving na su bayan sun faɗi abun da suke so su ci. Kasa cin komai ya yi sakamakon tuna Ma'eesha da ya yi, shin ta samu abun da ta ci ko ba ta samu ba, don ya lura kwana biyun nan sai kame-kamen abinci take yi. Tsintar kansa ya yi cikin yanayi na rashin jin dadi wanda take komai nasa ya sauya. Tashi ya yi daga dinning area din ya nufi ɗakinsa. Da kallo suka bi shi ganin yadda ya sauya nan take. _Ma'eesha_ Bayan tafiyar mijinta ta zauna ta ci kuka ta ƙoshi, babu mai rarrashinta. Har sai da ta ji kanta ya fara ciwo sannan ta dakata, hatta idanun ta a kumbure suke. Gani take kamar za ta rasa shi, kuma su ma su motar duk da ya ce ma ta motar kaya ne a saman kaya zai zauna shin zai iya kula da kansa a matsayin sa na makaho a wanan doguwar tafiyar. Da wanan tunanin ta yini har rana ta fito ba ta yi breakfast ba. Bugu da ƙari ba ta da komai a gidan da za ta ci, kuma ba ta da ko sisi da za ta siya abun da za ta ci. Wasa-wasa har karfe biyu na rana ba ta ci komai ba, karshe ma zazzaɓi ne ya rufe ta ta kwanta saman katifarta. Wayar ta ta janyo ta lalubo lambar makaho amma switch off. A haka har ya fara rawar sanyi ta duƙunƙune kanta. Addu'o'i kawai take yi a cikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya yaye ma ta ya kare ma ta mijinta a duk in da yake. _Sidra_ Tana nufar ɗakin baƙi maganar Fahad ne ke yi ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta. 'Nan saman iya na ma su gidan ne dai ɗakunan yaran da za mu haifa in sha Allah.' Tana shiga dakin ba ta rufe kofar ba ta zube a ƙasa, Nadra da ta kasa motsi ta jiyo sautin faɗiwar abu timm. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t 🌲🌳🌿☘️ *TALLAH!* *DA MAGANI A GONAR YARO!!* *08089965176* *07084653262* *Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.* *Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.* *07084653262 ko* *08089965176* *SIYAN NAGARI!!!!!!* *A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH* 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣3️⃣ Tana shiga ɗakin baƙin ba ta rufe kofar ba ta a ƙasa. Nadra da ta kasa motsi ta ji yi sautin faɗiwar abu timm. Da hanzarin ta sauko daga matattakalar, ɗakin ta nufa kai tsaye har da ɗan gudun ta, tana shiga ta yi tozali da Sidra kwance ba ta motsi . Durƙusawa ta yi akan ta tana kuka tana jijjiga ta tare da kiran sunan ta . "Wayyo Allah na Aunty Sidra ki tashi don Allah Aunty Sidra ." Ta mike daga durƙuson da take ganin Sunyi Sidra ba ta mike ba ya sa ta nufi upstairs tama ihun kiran sunan Fahad. _Jalaluddeen_ Tun da ya kasa cin abinci a dinning area ya shiga ɗakinsa ya zauna kan gadon. Sai kuma ya mike ya tashi ya rufe kofar ta hanyar mirza wa kofar key ya bar key din a jikin ƙofar. Wayar da Ma'eesha ta siya ma sa ne ya ɗauka tare da lalubo lambar wayar ta. Kira ya danna ma ta zuwa lokacin gabansa ya ji yana faɗuwa. _Ma'eesha_ Tana nan kwance tana rawar sanyi ne ta ji ringing din wayar , duk da dai ba ta ga ko sunan waye ba amma dai ta lulubi wayar ta sannan wajen amsa kira tana kara wayar a kunne. "Assalamu alaikum warahmatullah." Ta ji saukar muryarsa mai amo a cikin dodon kunnenta. Ba ta san lokacin da ta bude kumburarrun idanunta ba tana cewa. "Wa'alaika Salam warahmatullah." Muryarta da ya ji ba ta fita sosai kuma tana wayar kamar wacce take a galabaice ya saka shi cewa. "Ma'eesha lafiya kike kuwa?" Da kyar ta iya cewa . "Lafiya lau nake kada ka sami damuwa ba komai." "Kamar ua ba komai bayan muryarki ma ta nuna cewa kina cikin mawuyacin hali , ba ki tana yi ma ni karya ba kada ki soma a yanzu ." Dafe kanta dake sara ma ta ta yi kafin ta ce. "Kaina ke ciki amma kada ka damu zan wartsake In sha Allah." "Kin ci abinci ne?" "A'a ban ci ba." Shiru ya yi kafin ya ce. "Ba abuncin ko?" "Eh." Ta ba shi amsa a taƙaice. Wanda take idanunsa suka sauya ya katse kiran wayar . Daya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya kira wata lamba, ana ɗagawa cikin bayar da umarni ya fara magana . "Adamu ba lokacin da zan tsaya jiran sai wasu sun dawo. Yanzu ba sai an jima ba ka nemi wasu matan guda biyu ja ba su saƙon ka sanar da su yadda za su yi sannan idan sun fito daga gidan ja biya su hakkin aikin da suka yi. A tare za ku je ka jira su a wajen gidan. Yana gama faɗar haka ya kashe wayarsa ya ajiye gefe, tausayi da kewar Ma'eesha suka addabe shi. Ma'eesha kam dama da kyar take amsa ma sa don haka ta saki wayar tana dafe kanta Bayan kamar mintinan arba'in kenan sai ta dinga jin sautin sallama a tsakar gidan , Da ƙyar ta iya amsawa da muryarta da ba ta fita sosai. Ta yunƙura ta tashi zaune, hijabiinta ta laluba ta saka, sannan ta dafe bango tana tafiya . Ta bude kabulen daidai lokacin daidai lokacin da suke sake yin sallama. Ta amsa suna haɗa idanu da matan guda biyu. "Sannun ku bayin Allah." "Yauwa sannu." "Nan ne gidan Khalifa Makaho?" "Eh nan ne." "To ina fatan ya sanar da ke zancen tallafin kuɗi da ake ba wa mata don su yi sana'a su dogara da kansu." "Eh ya sanar da ni ya bayar da sunana ina sha Allah za mu samu." "Haka ne." Wata karamar jaka suka mika ma ta suna cewa ta samu dana'ar da za ta yi don dogaro kai. "In sha Allah.." Ta karba tana yin godiya zuciyarta cike da murna Komawa ta yi cikin ɗakin ta juya kuɗin. Bandir ɗin Naira dubu ɗaya ne guda biyar, wato Naira dubu ɗari biyar kenan. Farin ciki ya cika ta ta ɗebi wasu daga cikin kuɗin ta mayar da saura.n a leda ta saka cikin akwatin kayan ta . Daidai lokacin ta ji sallame A'isha. Hamdala ta yi tana jingina da bango ta amsa sallama. A'isha ta shigo tana cewa. "Sannu Aunty ina wuni ." Ta amsa na ta sanan ba kuma ma ta dubu ɗaya ta ce . "Ki siyo mun milo da madara da sigar." "Aunty bread fa,?' "Ba zan iya ci ba ku siyo mun kawai na sha yunwa nake ji ban karya ba." ,"subhanah har rana ta yi?" "Ba na jin dadi ne." Da hanzarin A'isha ta fita daga gidan don zuwa siyo manta kayan tea. Ba jimawa ta dawo ta shigo da kayan tea din a cikin baƙar leda. Ta duba flaks cikin ikon Allah ta samu akwai ruwan zafi a ciki. Nan da nan ta haɗa ma ta tea. Ita ta taimaka ma ta ta je ta wanke baki, sanan ta ba ta ruwan tea ɗin ta sha. Kallon A'isha ta yi kafin ta ce . ,A'isha bari na kira Yaya Khalifa a waya na sanar da shi zan tafi asibiti." Ta ji maganar tana jingine jikinta da bangon ɗakin "To Aunty Ma'eesha." Lambar wayarsa ta lalubo ta danna ma sa kira amma ba ta shiga ba. Dai da ta gwada kira har sau uku kiran bai shiga ba, kallon A'isha ta yi kafin ta ce . "Wayarsa ba ta shiga bari ba aike ki Chemist ki ce ya haɗa ma ki maganin zazzabin maleria." Ta yi maganar tana janyo kuɗi ta ba ta 3k ta ce ta je da shi. Karɓa ta yi tana yi ma ta sallama ta tafi. "Ba jimawa sai ga ta ta dawo da ladar magunguna. Zuwa lokacin ta tarar har ta fara barci . Sai da ta tayar da ita sannan ta tashi ta sha magungunan ta ba ta canjin Naira ɗari biyar. Tana gama shan maganin ta kwanta barci ya dauke ta nan da nan. A'isha ta tashi ta awa taya ta gyaran gidan. Ba iya zazzaɓi ne ke damu ta ba, har da tafiyar makaho ya dame ta, domin kuwa kewar sa na daya daga cikin abun da ke sa tana jin wani iri a tare da ita . Shi ma a nasa bangaren haka ne, domin kuwa tun da ya tuna ya ya kasa cin abinci. Ji yake yi kamar ya rufe idanu ya tsinci kansa a gaban ta. Sai ya ji farin ciki da yake yi da tafiyar duk ya rasa. Duk da cewar yanzu yana a lafiyayen gida na alfarma. Ga komai da ake bukata na more rayuwa amma ji yake yi rayuwa a wancan. Akulkin gidan tare da Ma'eesha yake bege. *Jan hankali.* Wani lokaci mace tana jin kamar idan ta biya wa mijinta bukatu, yi masa girki kala-kala, gyara jiki, , ta tsaftace jikinta ciki da waje girmamawa, ladabi biyayya, kwantar da kai… to zata iya gamsar da mijinta 100%. Sai dai gaskiya ɗaya ce Mace ba za ta iya cika dukkan muradan mijinta ba, kamar yadda shima ba zai iya cika nata ba. Saboda dan Adam bashi da iyaka a bukata. Yau yana son shiru, gobe yana son hira. Yau yana son tuwo, gobe yana son noodles. Yau yana so ki zauna da shi sosai, gobe yana buƙatar sarari. Yau yana so ki yi masa magana da tausayi, gobe yana fushi saboda wani abu da ba ki yi ba, Zuciyar mutum tana canzawa. Rayuwa tana da nauyi. Ki yi niyyar kyautatawa saboda Allah, ba don yawan yabo ba. Ki fahimci cewa mijinki ba kullum yana buƙatar abu iri ɗaya ba, yau soyayya, gobe space. Ki gina kwanakinki da basira ki dinga karanta sauyin yanayinsa. Ki yawaita addu’a sosai. Saboda ko kina da niyyar gamsar da shi, idan ALLAH bai sa kin gane hanyar ba, zai zama kamar ba kya yi. Mace mai basira ba wadda ta iya komai ba ce, Ita ce wadda ta san iyakokinta, amma tana kokari da zuciya ɗaya. Ita ce wadda ta mayar da gida masaukin salama, ko da mijin yana da tabo. Kuma hakan yana da girma fiye da zama kammalalliyar mace. Girmama ƙoƙari shine soyayya. Shi kansa ya san tabbas Ma'eesha na son sa kuma so na haƙiƙa Knocking ƙofar da aka yi ne ya dawo da shi cikin tuanin da ya lula. Mom ce ta shigo da sallama , ya amsa ma ta yana zaune kan gado, yayin da ta zauna saman bed side tana karantar yanayinsa. "Wace ce ita?" Da sauri ya kalle ta yana mamakin tambayar da ta yi ma sa. "Na ce wace ce ita?" Nan ma sake kallon ta ya yi ya kasa cewa komai. "Mom wai akan wa kike magana ?" "Akan wacce kake tunani da har ka kasa cin komai saboda ita ." "Ni Mom ba wacce tunanin ta zai hana ni cin abinci." "Ga shi kuwa na gani." "Eh to ni wace mace zan yi tunanin ta bayan Yasmeen da kika sani, ita kadai ce." Ya yi maganar kansa a ƙasa ya kasa hada idanunsa da mahaifiyar tasa. Murmushi irin ta su ta manya ta yi kafin ta ce. "Idan har tunanin Yasmeen ne a cikin zuciyarka to da ka tashi yanzu ka karasa in da yake ka gan ta, saboda gari daya kuke a yanzu. To ya kamata ka sani ka cire tuanin kowace mace a zuciyarka ka san meye a ƙasa ba sai na faɗa ma ka ba. Ba ka isa ka fito da wani zancen wata mace bayan Yasmeen ba don haka kada ka fara abun da ka san ba zai yiwu ba." Wayar ta ta ɗauka ta danna kira bugu ɗaya aka ɗaga. "Kawo wa Yayanku abinci a ɗakinsa." Daga haka ya katse kiran wayar . "Ba jimawa sai ga Sadiƙa ta shigo da farantin abinci da aka ɗaura kan tire da robar ruwa ruwa da glass cup sai lemu na kwali. Mom ce ta karɓi abincin ganin haka ya sauko daga saman gadon ya zauna akan carpet dake ɗakin. Sadiƙa ta kalle shi ta ce. "Big bro are you okay?" "Am okay" Daga haka ta fita ta ba su waje . Abincin Mom ta ajiye ma sa a gabansa ita ma ta zauna tana fuskantar sa ta saka shi gaba kamar yaro. Sai da ya ci rabin plate ɗin abincin sannan ya sha ruwa lemu ma bai sha ba. Kallonsa take yi tana yi wa Allah godiya, domin kuwa rabon da ya kwana a gidan nan tun bayan da Gwaggonsa ta dauke shi yana ɗan shekara ɗaya, sama da shekaru talatin kenan bai sake kwana gidan ba sai yau. Sai dai ya so ya gaishe su ya tafi .Amma ta san hakan na da nasaba da rashin sanin ita ce mahaifiyarsa sai a cikin shekarar nan da zancen aure sa da Yasmeen ya fito. Kuma zuwa lokacin ba wani zama yake yi ba, ko, amma yanzu ga shi ita da shi nan ya fara sauka kafin ya je gidan Ummeen tasa. Horn ɗin mota suka ji sanan suka ji ƙarar buɗe gate. Hakan ya tabbatar ma su da isowar Dad. "Dad ne ya dawo ko Mom?" "Eh shi ne." Ta faɗa tana tashi ta dauki farantin da plate da ya ci abinci da shi. Ta fita daga ɗakin ya bi ta da kallo. _Fahad_ Ya rage kayan jikinsa kenan zai yi wanka daga shi sai gajeren wando da singileti. Nadra ta turo ƙofar dakin cikin tashin hankali. Da sauri ya juya ya kalli ƙofar ya ce . "Lafiya me ya faru!" "Aunty Sidra ce ta faɗi?" Shiru ya yi kamar bai ji ta ba, ganin ya yi shiru ta karasa dab da shi ta rike hannunsa tana kuka ta ce. "Ka taimaka ma na don Allah Yaya Fahad." "Ni fa ba na ƙaunar ganin wanan yayar taki na tsane ta, amma kin goyi bayan ta dawo gidanki ta zauna, ba yadda na iya Amma wallahi ba da son raina hakan ta faru ba." "To ba yadda zan yi ne shi ya sa, ta nuna nan take so kuma ga abun da Doctor ya ce a guji ɓacin ranta." Jallabiyarsa fara ya ɗauka ya ɗauka ya saka sannan ya nufa hanyar fita ta bi bayansa. Yana zuwa ɗakin baƙi ne ya ganta kwance ba ta motsi kamar wata gawa. Durƙudaws ya yi a gabanta ya zuba ma ta idanun na wasu sakanni kafin ya kalli Nadra ya ce. "Ba ni ruwa a fridge." Da sauri ta zuwa falo kasancewar fridge dake nan ɗakin a kashe yake. Nan da nan ta dawo da robar ruwa ta mika ma sa. Ya ɓalle marfin ya yayyafa ma ta amma shiru ba ta motsa ba, hakan ya sa ya ka ya watsa ma ta da ƙarfi wanda ya da ta ja ajiyar zuciya tare da rike hannunsa da ƙarfi tamkar wani zai kwace ma ta shi daga hannunta. Tsuki ya ja a ƙasar ransa kafin ya fusge hannunsa da ƙarfi ya fice daga ɗakin. _Jalaluddeen_ Bayan fitar Mom kenan ya tashi ya fice daga ɗakin shi ma. A falo ya tarar da ƙannen nasa suna zaune sun zubawa tangamemen plasma t.v wanda ya kusa rabin rabin bangon Falon. Sai sanyin A.C da wani sanyayyen ƙamshin turaren wuta da ke tashi a falon Ɗaya daga cikin lafiyayun royal chair dake Falon ya zauna. Kasancewar kujera ma i zaman mutum uku ce nan take Sadik da Sadiƙa suka taso suka zauna kusa da shi suka sanya shi a tsakiya. Fuskar kowannen su ɗauke da murmushi, Sadik ya ce " Yanzu fa daga gobe ka zama ango." Kallon rashin Fahimta ya yi ma sa ya ce . "Kai ba na son shirme fa, waye zai zama ango gobe." "Kai ma na Yaya Jalal, ai Dad ya ce duk ranar da ka dawo garin nan a washegarin ranar za'a ɗaura auren ka da Yasmeen kowa ya san da wanan zancen." " Wani gumi ne ya ji ya karyo ma sa shi da sanyin A.C dake ratsa falon. ,*Maman Ihsan ce✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣4️⃣ Gumi ne ya ji ya karyo ma shi duk da sanyin A..C dake ratsa falon. Ba wanda ya sake magana, su ma ganin yanaynsa ya sauya ne ya sa kowa . Mom ce ga karasa falon ta kalle shi ta ce.. "Ka zo ga Alhaji na son ganin ka." Ta faɗa tana nazartar yanayinsa. "To Mom." Ya amsa tana tashi ya bi bayanta don zuwa amsa kiran Dad. Yana shiga ya tarar da Dad da Mom zaune saman kujerar mai mai zaman mutum uku. Da sallama ya karasa falon ya zube a kan carpet ya gaida Mahaifin nasa. "Barka da dawowa Dad." "Barka dai Jalal ya kake?" "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ma sha Allah, ya kuma aikin?" "Alhamdulillah aiki sai an daure." Dariya Dad ya yi yana cewa . "Ya su Ummeen taka?" "Dad ai ban je can ba nan na sauka." "To fa, nan ka sauka?" "Eh na yi kewarku ne Dad." "Allah saekiy, Ummeen taka ta san kana nan." "Ban faɗa ma ta ba Wallahi, don idan ta sani za ta saka ni na koma gidan yau ne, ka san halin ta yanzu za ta iya aiko direba ya ɗauke ni idan ma ban tafi ba." Murmushi Dad ya yi tare de cewa . "Ƙwarai kuwa na san halin ta ba ta san ka yi nesa da ita sai dole. Shi ya sa ba ta ƙaunar wanan aikin da kake yi kullun cikin ƙorafi take. To amma idan ka yi aure ai dole ka bar gidan." "Yauwa Dad ka je kai da Mom kuwa kun ga yanayin tsarin gidan ko?" "Eh mun je gidanm ya yi kyau ma sha Allah, tsarin gidan kamar ba a Nigeria ba a kasar Turai aka yi shi." Cewar Mom tana dariya. Kafin ta ce . "Allah ya kara arziki ya kare ka a duk in da kake, gaskiya ka yi ƙoƙari irin wannan gidan haka?" ",Gaskiya kam Jalal ka narka dukiya a gidan nan Allah ya da yawan rai aka yi wa." Cewar Dad yana jinjina kai. Nan suka cigaba da fira har dare ya yi don karfe sha daya ne a lokacin. Kafin ya yi ma su sallama ya koma part ɗin sa. Wanka ya yi sannan ya kwanta kan gadon daga shi sai gajeren wando da singileti. Har ya dauki waya zai kira Ma'eesha ganin karfe goma sha daya da mintuna arba'in ya sa ya fasa don yana tunanin yanzu tana barci. _Nadra_ Tun da ta ga Sidra ta yi ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta ta saki murmushi tana goge hawayen da ke kwance a idanunta. Fahad da ya fice daga ɗakin ta zuba wa idanu har sai da ya banko ƙofar da ƙarfi sannan ta dawo da kallon ta kan Sidra. "Sannu Aunty Sidra."O Ba ta tanka ma ta ba ta kau da kai tana kallon yadda jikinta take jin sanyi. Don gabaɗaya Rigar jikinta sun jiƙe, kamar da gayya ne Fahad ya watsa ma ta ruwan. Ba tare da ta damu da yanayin yadda Sidra ta tsuke ma ta fuska ba ta kama hannunta ta janyo ta tana cewa. "Sannu Aunty ba ki ji ciwo da faɗuwar da kika yi ba? Ba abun da ya same ki ko?" Zare hannunta ta yi daga na Nadra tana kokarin barin wajen kenan sai Nadra ta riƙe ta tana cewa. "Bari na taimaka ma ki muje banɗaki daga nan sai ki yi wanka." "Ba ta ce ma ta komai ba, ta shige banɗaki ta bar ta tsaye. Nadra ta nemi mopping stick ta goge wajen da ruwan ya zube. Sannan ta sanya ma ta sabon zanin gado ta gyara gadon. Sidra na fitowa ta kalli Nadra ta ce . "Sannu da aiki." "Yauwa sannu Aunty ya jikin naki?" "Da sauki Alhamdulillah." "Ma sha Allah, duk da yamma ta yi bari na je na samu abun da zan sarrafa ki samu ki ci na san yunwa kike ji ko?" Kai kawai ta jinjina ba tare da ta yi magana ba. "Yauwa Aunty don Allah kada ku saka wa ranki wani tunani ko damuwa, maganar Doctor ba maganar Allah ba ne, don haka ina sha Allah muna tare da ke har jikokin ki sai mun gani. Kuma ina son mu je mu roki Abba ya yafe ma ki kura-kuranki ki koma gida ki ci gaba da rayuwar farin..." "Nadra!" Yadda ta kira sunan ta sai da gabanta ya faɗi. Ta kalle ta da sauri ba tare da ta karasa maganar da take yi ba. "Na'am Aunty." "Tun ba'a je ko ina ba har kin gaji da ni kina kora ta na koma gida na yi rayuwar farin ciki, saboda na zo gidanki gidan aro ko?" Cike da mamaki Nadra ke kallon ta tana nanata zancenta a zuciyarta, wato zancen cewa su je su nemi yafiyar Abba ne ba ta so ta ce tana korar ta . Sannan kuma me take nufi da gidan aro, wato duk da ba ta gaban Fahad da yanayin ta take nuna ma sa bai saka ta ta shiga hankalin ta ta fita daga lamarinsa ba, har yana cewa gidan aro. Murmushi kawai Nadra ta yi kafin ta ce. "Allah ya ba ki haƙuri Aunty ya huci zuciyarki ba haka nake nufi ba. Bari na je na nema ma na abun da za mu ci ki samu ki sha magungunan ki." Tana faɗar haka ta fice daga dakin tana murmushi. _Jalaluddeen_ Washegari da safe bayan sun kammala breakfast ya shirya don zuwa gidan Ummeensa. Sanye yake cikin cikin cikin cikin wani tsadadden yadi mai ruwan sararin samaniya. Ɗinkin ya zauna ma sa a jikinsa ya ma sa kyau. Sallama ya yi wa mutanen gidan gidan sannan Sadik da ya shirya zuwa asibiti ya dauke shi a motarsa, da niyyar idan ya kai shi gidan sai ya wuce asibiti daga can. Horn ya yi a ƙofar gidan, security ya leƙo ganin su ya sa ya wangale gate ɗin da sauri, kasancewar ya san motar Sadik. Bayan ya yi parking kusan a tare suka fito daga cikin motar . Ma'aikatan gidan na ganin Jalaluddeen suka nufo shi da sauri suna gaishe shi. Ya amsa ma su cikin sakin fuska da walwala. Suka nufi ƙofar da za ta sada su da ƙofar shiga babban falon gidan. Kararrawar ƙofar Jalaluddeen ya danna wanda ya sa gabaɗaya ilahirin jama'ar dake ciki suke kallon ƙofar cike da mamaki. Saboda sun san idan har suka ji yanayin bugun kararrawar Jalaluddeen sun san shi ne. Ummee da Abba sai Yusuf da suke a dinning table suna breakfast suke kallon ƙofar. Ma su aikin da ke falon ma suna kallon ƙofar suna mamakin yaushe ya dawo. Hatta Yasmeen da yanzu farkawar ta daga barci kenan ta ji ƙarar ƙofar masoyinta sai da ta miƙe zumbur. Da sauri Yusuf dake cin abinci a dinning area sai ya tashi kafin ma su aikin su buɗe har ya riga su isa ya buɗe. Cike da mamaki yake kallon Jalaluddeen ya ce. "Yaya Jalal kai ne yanzu haka?" Gajeren murmushi ya yi tare de cewa. "Ga shi kuwa kana gani." Ba su hanya ya yi suka shigo cikin sannan ya rufe kofar daidai lokacin da Yasmeen ta fito daga part ɗin ta. Daga ita sai rigar barci wacce ta tsaya iya guiwarta, kanta babu ɗankwali kanta babu ɗankwali sai kitso calaba da ke kanta. Ganin da gaske ba ƙarya kunnen ta yi yi ma ta ba ta nufe shi da gudu za ta rungume shi ya yi saurin dakatar da ita da hannu ya ce. "Koma ki saka kaya!" Ya faɗa babu wasa a fuskarsa . Da sauri ta juya tana tura baki Dariya Yasuf ya yi don ya san a fadin gidan nan Jalal ne kawai zai yi ma ta magana sau ɗaya ta aikata abun da ya umarce ta ba tare da gardama ba. Ummee ta kalli Jalaluddeen ta kalli Sadik dake rike da jakar kayan Jalaluddeen dake hannun Sadik. "Daga ina kuke haka da safiyar nan? Na san dai ba ka isa a ce har ka bar garin Kaduna ka iso nan ba ." Kafin ya yi magana sai Sadik ya ce . "Daga gidanmu yake, tun jiya ya iso na je na dauke shi a airport na yi ma sa bazata. Daga airport na kai shi gida ya kwana yanzu na dawo da shi gidansu." Ya yi maganar yana dariya. Su ma dariyar suka yi ban da Ummee. Kafin ta ce. "Son za ka dawo ko ka sanar ma na dawowarka sai dai na gan ka daga sama wasu ne ka sanar." 'Wasu?' Sadik ya faɗa a ransa yana mamakin Gwaggon tasu. Gaida su ya yi sama-sama ya ce zai tafi aiki yana sauri, daga nan ya fice daga falon. Yasmeen ce ta dawo sanye da rigar after dress ta saka hula a kanta. Cikin farin ciki ta ƙaraso wajensa da niyyar ta rungume shi. Da idanunsa kawai ya gargaɗe ta wanda gane nufin sa ya sa ta tura baki tana fushi. Zama ta yi akan kujera mai zaman mutum biyu dake Falon. Kasancewar ba wanda ya san abun da ya haɗa su ya sa Abba cewa. "Yasmeen ba ki ga Yayanki ba ne?" Kamar tana jira sai hawaye dariya Yusuf ya yi yana cewa. "An dai ji kunya." "Ke lafiya me yake faruwa ne haka, ba na son sakarci." "Ummee bar ta ni da ita ne." Jin haka ba su sake magana ba, ya gaida su cikin girmamawa, sannan Yusuf ma ya gaishe shi. "Tun jiya kake garin nan Son shi ne ba mu sani ba?" "Ummee ki yi haƙuri ke ma kin san ban saɓa sanar da tafiya ta ko dawowa ta ba, muna waya da Mom ne nake sanar da ita dawowa ta anan Sadik ya ji shi ne ya je ya taro ni." "To me ya sa da muka yi waya ba ka sanar da ni ba?" "Bayan mun gama waya da ke lokacin ban yi tunanin dawowa ba." Murmushi ta yi kafin ta ce. "You're welcome." Murmushi kawai ya yi yana kallon Yasmeen dake cika da batsewa. "Amma ya kamata ka canza wanan aƙidar taka Son, a ce ba ka sanar da kowa duk abun da ya shafe ka? Yanzu fa iyali kake shirin ajewa ko ba haka ba, duk rashin damuwa da mutane idan kana aiki dole za ka canza ko don iyalinka." "In sha Allah Ummeena." "Yauwa Ɗan gidan Ummeensa." Gabaɗaya suka saka dariya. Ta kalli jakarsa ta ce wa Yasmeen. "Kai ma sa jakarsa ɗakinsa." Ta ɗauki jakar ta nufi part ɗin nasa dake upstairs. Da kallo ya bi ta kafin ya kalli su Ummeen ya ce . "Bari na fito Ummeena." Murmushi ta yi kafin ta ce. "Ya aiki ya hanya?" "Lafiya lau Ummee aiki ba sauƙi." "Shi ya sa ba na son wanann aikin naka, ka ajiye shi ka fara kula da Kamfanin..." "A'a kin san kowa da hanyar cin abincin sa, na san dai saboda rashin zamansa ya sa ba ki son aikin." "Ki kwantar da hankalinki Ummeena." Ya faɗa yana nufar part ɗin sa. Yana tura ƙofar falon ya yi kiciɓis da Yasmeen dake ƙokarin fitowa. Kau da kanta ta yi gefe idanunta na kara cikowa da ƙwalla. Hannunta ya rike yana cewa . "Meye kuma na kuka?" "Ka daina so na ka daina ƙauna ta." Ta saki kukan da take riƙe wa , kafin ya kalle ta ya ce . "Me ya sa kike tunani na daina son ki?" "Ai a baya ba ka ƙyamata ta dai yanzu, da idan ka dawo za ka yarda na yi ma ka oyoyo idan na ji kwarara amma yanzu sai ka hana." Dariya ya yi kafin ya ce. "Da da yanzu ba daya bane Yasmeen, a baya ina na ki kallon jini daya ne ni da ke ina ma ki kallon Muharrama ta amma daga baya sai muka fahimci ba haka ba ne, daga ranar da na fahimta cewa ba Ummee ta haife ni ba na canza yanayin zamantakewar da nake yi da ke, domin akwai iyaka tsakanin mu. ga shi har ana shirin yi ma na aure, ai addini bai yarda na haɗa jiki da ke ba har sai kin halatta a gare ni. Ina fatan kin fahimce ni?" Kai ta gyaɗa ma sa alamar eh kafin ta ce. "Za ka raka ni wajen bikin ƙawata?" "Wata ƙawarki?" "Maryam da ka sani Aminiya ta." "Har bikin ya zo?" "Eh kuma mun shirya taro kowace za ta je da saurayinta ko mijinta, dama saboda ba ka nan na ce ba zan je ba, tun ja ka dawo dai mu tafi karfe biyar na yamma." Shiru ya yi kafin ya ce. "To Allah ya kai mu. Amma ba na son zuwa irin Wuraren nan fa." "Please Yaya Jalal ka raka ni." "Okay Allah ya kai mu." Da murna ta daka tsalle tana yi ma sa godiya. Fita ta yi daga part ɗin zuciyarta fara tas. Tsaye yake yana ƙarewa ɗakin nasa kallo wanda ya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu wani wadataccen haske a cikin dakin, ya ɗauki wani remote ya danna, take ɗakin ya gauraye da hasken wasu fitilu da suka ƙara ƙawata ɗakin. Tangamemen gadonsa wanda aka gyara ya kalla gadon circle ne a zagaye yake ba irin gamagarin gadon da kowa ya sani ba ne. Jakar kayansa ya ɗaura kan gadon ya cire wayoyinsa na aiki da kuma wacce Ma'eesha ta siya ma sa ya ajiye saman gadon ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom don yin wanka. Shower 🚿 ya sakar wa kansa yana wanka yana tuna yadda Ma'eesha take dafa ruwan zafi ta kai ma sa banɗaki ya yi wanka. Sauri-sauri ya yake yi ya fito domin ya kira ta a waya domin ya ji halin da take ciki. Ummee ce ta yi sallama ta yi knocking ƙofar ɗakin nasa, jin shiru ya sa ta tura kofar da sallama. Sai dai ta ga baya cikin bedroom ɗin nasa. Amma jin saukar ruwa a banɗaki ya sa ta gane cewa wanka yake yi. Har za ta fita sai ta ji ƙarar waya kamar calculator ta juya ta kalli wayar dake kan gado yana ruri. Kallon wayar ta yi cike da mamakin yadda aka yi mutum kamar Jalal yake amfani da wayar da talakawa ke amfani da su. Ƙarasawa ta yi jikin gadon tana kallon wayar. Ganin sunan da ke jikin wayar ne take kiransa wato MAR'ATUSSALIHA ya sa ta cika da mamaki. Kiran ya tsinke take wani kiran ya sake shigowa wayar, da sauri ta kai hannu kan wayar... *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣5️⃣ Kiran ya tsinke wani kiran ya sake shigowa wayar, da sauri ta kai hannu kan wayar da niyyar ɗauka sai ya riga ta ɗauka cikin zafin nama. Kallonsa ta tsaya tana yi yana sanye da rigar wanka kansa na ɗigar da ruwa da towel a hannunsa. Yana ɗaukar wayar sai kiran ya tsinke, ya kalle ta ya ce. "Ummee kina buƙatar wani abu ne?" "Wace ce mar'atussaliha?" "Abokiyat aikina ce ita." "Ba ta da wani suna se wannan?" "Tana da shi, amma haka ake kiranta saboda kyawun halinta da nagartarta." "Okay ka fito ka ci abinci na ga ba ka fito ba ne na biyo bayanka." "Ummeena yanzu na ci abinci a gidan Mom, sai zuwa anjima." "Okay ka huta, ko kana bukatar wani abu ne?" "Ba na bukatar komai Ummeena." Murmushi suka yi wa juna a tare sannan ta fita tana cewa. " ka kwanta ka huta kada ka takura kanka da zancen aikin nan." Yana dariya ya amsa sannan ya goge kansa da towel na hannunsa. Kiran Wayar ne ya bi ya danna ma ya kira . "Bugu biyu da ga tare da yin sallama cikin nitsatsiyar muryarta. "Assalamu alaikum warahmatullah." "Wa'alaiki salam warahmatullah Mar'atussaliha mayar mijinta." Murmushi mai sauti ta yi wanda sai da ya ji sauti nan cikin kunnensa. "Ina wuni' "Lafiya lau ya kike" "Alhamdulillah ga ni ina gama da kewar ka, har ciwo.n kai na yi sai da A'isha ta zo ga siyo Mani magani na sha. Bayan na tashi barci ne sai na ji sauƙi. "Ya Salam, to yanzu ya kike ji a jikin naki?" "Alhamdulillah na ji sauƙi sosai wallahi." "Ma sha Allah. To meye labari ?" "Labari mai daɗi kuwa." "Fada mani ina jin ki." "Wadanda ka ce za su ba mu tallafin nan ne suka kawo ma na kudi ma su yawa har Naira dubu ɗari biyar." "Cikin nuna jin dadi da murna ya ce. "Alhamdulillah Allah ya saka ma shi da alkhairi." "Amin Mijina." Yanzu abun da za'ayi ki ɗauki kamar dubi ɗari uku ki shiga da su kasuwa ki je ki siyo kayan abinci ma su kyau da inganci. Kamar yadda kika yi a baya lokacin da kika siyar da wayarki." "A'a wanan fa an ce mu yi sana'a ne aka ba mu jari." "Dubu ɗari biyu da ya rage sau mu yi shawarar sana'a da za mu yi idan na dawo ko?" "To shi kenan yadda ka ce haka za'ayi." Ka isa lafiya? Ka samu danginka cikin wadanda aka ce sun dawo?" "Ba sa ciki ba kowa nawa." Cikin sanyin jiki ta ce. "Allah ya bayyana ma ka su a duk in da suke, Allah ya haɗa fuskokin ku." "Amin na gode." "Yanzu yaushe za ka dawo?" "Ina ganin zuwa jibi motar da na biyo za ta dawo, don haka ita zan biyo." Fira suka tana daga bisani ya yi ma ta sallama ya kashe kiran wayar. _Nadra_ Tana barin ɗakin Sidra koma ɗakin Fahad, ta ji saukar ruwa a bathroom alamar yana wanka. Kitchen ta nufa don ɗora ma su abun da za su ci. Nan da nan cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa ma su jallop ɗin superghetti da ya ji kayan lambu da bisashen kifi. Sai farfesun kayan ciki wanda ya ji kayan ƙamshi. Bayan ta zuba a cikin kula ne ta kwashe su ta jera a dinning table. Daidai lokacin ana kiran sallar magrib kenan ta kammala. Fahad wanda ya fito da niyyar zai je masallaci ya ji ƙamshi girkinta. Tana kokarin barin dinning area suka hadu. Murmushi suka sakar wa juna kafin ya ce. "Sannu da aiki." Madadin ta amsa sai ta ce ma sa a dawo lafiya, kafin ta nufi ɗakinta. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar magrib. Tana nan jan sallaya ba ta tashi ba, karatun Alkur'ani take yi har sai da aka kira sallar isha'i ta tashi ta gabatar da sallar isha'i ta yi addu'o'i sannan ta mike tsaye ta cire hijabiñ da ya yi sallah da shi . Rigar material ne a jikinta ɗinkin doguwar riga ce. Kai tsaye ta nufi falonta daidai lokacin yana dawowa sallah. Nadfah yunwa nake ji." Kallonsa ta yi alamar ba ta bane sunam danya kira ta sa shi ba ne "Wa na ji ka kira ne?" "Ke na kira ma na, ba ki ji na ce Nadfah ba?" "Shiru ta yi tana nanata kalmar a ranta. 'Nadfah.' Wato farkon sunan ta na nasa ya haɗa kenan NAD+FAH =NADFAH. Nurmushi ta yi sakamakon sunan da ya yi ma ta daɗi sosai da sosai ta ce. "Ga abinci na jiranka. Mu je dinning area na zuba ma ka, daga nan sai na kira Aunty Sidra ta fito mu ci abinci ." Ji ya yi ransa ya ɓaci sakamakon kiran sunan Sidra da ta yi. Amma gudun kada ya ɓata ma ya rai tun da ya fahimci tana son ƴar uwarta sosai ya sa ya ce. "A gajiye nake ba zan iya fitowa zuwa dinning area ba please ki kawo mun nawa a ɗakina, amma fa dai kin taya ni ci." Ya yi maganar yana murmushi. "Ayyah sorry, to bari ba kawo ma ka ko?" Ta yi maganar tana wucewa don kawo ma sa abincin nasa. Shi kuma ya shiga cikin bedroom ɗin sa. Bayan kamar mintuna biyar sai ga ta ta dawo da ba tire a hannunta wanda ta jera abincin da abun sha da kofi da spoon. Yana zaune yana jiranta daga shi sai singileti da gajeren wando. Yana zaune kan sofa dake cikin bedroom ɗin nasa. Ajiyar abincin ya yi kafin ta janyo stool dake gefe ta ajiye a gabansa danna ta ɗora abincin. Jallop ɗin superghetti ne da ta dafa ya ji kayan lambu fa busashshen kifi. Ta zuba ma sa lemu da ruwa sannan ta ce. "Ina zuwa?" "Ai tare za ki zauna mu ci ." "Okay just 5 minutes zan dawo." Ta faɗa tana murmushi ta fice daga ɗakin hannunta rike da wayar ta. Ƙasa ta sauka ta nufi ɗakin baƙi. Nan ta samu Sidra na ta kai wa da komowa. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki salam." Zama ta yi bakin gadon tana cewa. "Sannu Aunty Sidra." "Yauwa sannu. Na ga kin dade baki dawo ba ko kina tare da Fahad ko?" "A'a Aunty da na bar nan kitchen na je ba yi girki, da na gama ne na aka kira sallar magrib na je na yi, kuma kin san baka tashi daga magrib sai na yi isha'i. Yanzu na fito don na tambaye ki nan zan kawo ma ki abincin ki ne?" "Ku a ina za ku ci?'" "Ya ce tare za mu ci a ɗakinsa?" Sai da ta ji zafi a zuciyarta kamar an watsa ma ta garwashin wuta kafin yi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta ce. "Yanzu zuwa wajansa za ki yi?" "To Aunty Sidra ya zan yi?" "Hmm yanzu haka za ki bar ni ki je can wajensa ki bar ƴar uwarki da take cikin halin jinya tana bukatar taimakon ki? Kuma kin san bai kamata ki bar ni na kwana ni ƙaɗai ba, saboda ba'asan me zai faru cikin dare ba ko ciwon nawa zai iya tashi ba kowa a kusa da ni, wata kila ma sai dai ki ga gawata da safe." Ta yi maganar tana fashewa da kuka. Cikin rauni Nadra ta rungume ta tana rarrashin ta. "Dan Allah Aunty Sidra ki daina fadar haka ba abun da zai same ki ina tare da ke in sha Allah." Tana gama faɗar haka ta fice daga cikin ɗakin yayin da Sidra ta zauna sai cika take yi tana batsewa. Ba jimawa sai ga ta ta dawo da tire a hannunta wanda ta jera wa Sidra abinci. "Aunty ga abincin nan ki fara ci kafin na dawo." Sai da ta buɗe ma ta abincin ta saka ma ta fork ta zuba ma ta ruwa da lemu sannan ta fice daga ɗakin. Da sallama ta shiga ta samu Fahad na zaune waya yake yi abincin na nan gabansa bai fara ci ba. Zama ta yi gefen sa tana kallon sa har ya gama wayar sannan ta ce . "Yaya ba ka ci abincin ba." 'Ke nake jira." Murmushi ta yi kafin ta saka fork cikin plate ɗin abincin. Shi ya dinga ba ta a baki har sai da ta ƙoshi. Ganin haka ita ma ta fara ba shi suna fira har ya ce ya ƙoshi. Tattara kayan ta yi ta kai kitchen ta wanke sannan ta dawo. Sanin halin ta yanzu za ta yi ma sa zancen Sidra ko ta ce za ta tafi wajen ta ya sa ya rufe ƙofar ya murza key. Za ta yi magana ya ce. "Na yi ma ki dukkan wasu alfarma da kika nema akan Yayar ki. To yanzu lokaci na ne, dama ai kin yi ma ni alƙawari kin tuna? Rashin lafiyar Yayarki ya tsayar da komai." Shiru ta yi tana tuna kalaman Sidra. Ba ta ankare ba ta ji ya ɗauke ta ya yi sama da ita, kai tsaye bathroom suka nufa. Wanka suka yi a tare sannan suka fito daga banɗaki ya naɗo ta cikin towel kamar baby. _Jalaluddeen_ Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma bayan ya dawo masallaci, wanka ya shiga ya yi sannan ya fito sanye cikin bathrobe (Rigar wanka) yana tsaye a gaban dressing mirror yana kallon kansa. Wayarsa ya ɗauka gaban dressing mirror ɗin wacce yake waya fa Ma'eesha. Kira ya danna ma ta bugu biyu ta ɗaga. Cikin zazzaƙar muryarta ta yi ma sa sallama . Sai da ya lumshe idanu cike da kewarta ya amsa ma ta sallamar. "Ina wuni mijina?" "Lafiya lau ya kike ya gidan?" "Gaskiya duka ba lafiya ba. Don ta ina zan yi lafiya ba ka tare da ni, sannan kuma gidan ma duhunsa nake gani domin fitilar dake haska ma ni gidan baya tare da ni?" "To ina fitilar ya faɗa ai sai ki neme shi?" "Kai ne fitilar ai, idan ba ka nan gidan Lami ne, sai yanzu nake jin maraici a tare da ni." "Kuyi hakuri zan dawo in sha Allah. Kin siya abincin ?" "Wani abinci ?" "Kin manta na ce ma ki cikin dubi ɗari biyar din nan ki cire dubu ɗari uku ki siye kayan abinci kamar yadda kika siye da kika siyar da waya." "To an ce mu yi sana'a ne, idan ba mu yi sana'ar ba kuɗin karewa za su yi." "Allah na nan, kuma ba haka za mu dawwama ba." "Na sani amma Allah ya ce ka tashi in taiamake ka, kai ga ka ba gani kake yi ba, ballantana na ce za ka yi sana'a da kuɗin, mutane cutarka kawai za su yi . Sai dai..." "Ma'eesha." "Na'am." Ta amsa tana sauraron abu zai fito daga bakinsa. "Ki yi abun da na ce ma ki." "To sh ke nan, yadda ka ce haka za'ayi ." Sallama ya yi ma ta ya katse kiran wayar. Ya shafa tsadadden man shafawarsa sannan ya shiga ciinin closet ɗin sa . Ba nunawa ya fito sanye da cikin rigar suit baƙa na cikin fari ya ɗaura tie Black and white. Sai ƙamshi yake bazawa. Ya ɗaura tsadadden agogon hannunsa. Wayarda Samsung Galaxy Z fold 5 wacce kuɗin wayar Naira miliyan biyu da dubu ɗari Shida. 2, 600,000. Ya saka a aljihun rigar suit ɗinsa. Bayan ya saka Safa da makami ne ya saka baƙin glass a idanunsa. Daidai lokacin Yasmeen ta yi knocking. Izinin shigowa ya ba ya ta shigo da sallama. Ya amsa ma ta ba tare da ya kalle ta ba, yana duba sako a cikin wayarda ta aiki. Reply ya yi sannan ya sa wayar a aljihun wandonsa. Kallon Yasmeen ya yi ta yi shirin ta cikin material fari da baƙi don shi ne ankon da suka yi . Ganin kayan ya matse ta ne ya sa ya ce. "Ki ke ki sauya kayan jikinki ?" Kamar za ta yi kuka ta ce . "Yaya Jalal wallahi wanan ne ankon ka yi hakuri don Allah." "Ban hana ki fita da kayan da suka matse ki ba?" "Ka hana?" "Ban isa ba kenan shi ya sa ba ki daina ba." "Wallahi ka isa ka yi yawa ma, amma wanan ne ankon kuma tailor din ne ba ni na ce ba." "Ki je ki saka after dress." Da sauri ta fita sanan ya nufi hanyar fita. A falo suka hadu ya yi gaba ta bi bayansa. Don Ummee ba ta gidan ma. Ɗaya daga cikin motocinsa wanda ya sa aka wanke ma da ne ya shiga. Ita ma ta shiga ta zauna gefensa, sai dai ba walwala a fuskarta ganin ta rufe adonta. "Ina ne wajen taron?" Ta sanar da shi tana ɓata rai. Kamar bai san tana yi ba ya yi wa motar key yayin da maigadi ya wangale ma su gate ya fice daga gidan. Kai tsaya wajen taron suka nufa. Ya yi parking a wajen da aka tanada na parking motoci. Daidai yana fitowa daga cikin motar suka yi idanu biyu da Nasreen ƙawar Ma'eesha, tana sanye da ankon irin na Yasmeen ,wacce fitowar ta kwanan daga wata motar da aka yi parking. Sakin baki ta yi tana kallon Jalaluddeen da matsanancin mamaki. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣6️⃣ Daidai yana fitowa daga cikin motar suka yi idanu biyu da Nasreen ƙawar Ma'eesha, tana sanye da ankon irin na Yasmeen, wacce fitowar ta kenan daga wata motar da aka yi parking. Sakin baki ta yi tana kallon Jalaluddeen da matsanancin mamaki. 'Khalifa Makaho?' Ta faɗa a ranta idanunta akansa. Tabbas ya shiga ruɗu sakamakon ganin aminiyar Ma'eesha. Amma dai ya dake ya basar kamar bai taba sanin ta ba. Yanayinsa ba zai taba nuna halin da ya shiga ba, amma tabbas ya yi nadamar zuwa wajen nan. Kau da kansa ya yi ya rufe murfin motarsa ya yin da Yasmeen ta fito ta zagayo gefensa tana murmushi. "Mu shiga ciki." Ta yi maganar tana rike hannunsa suka fara tafiya. Dariya Nasreen ta yi har yana tafa hannu tana kallon su har suka shige ciki. _Fahad_ Bai sauke Nadra ko ina ba sai tsakiyar gadon. Daga nan ya haura saman gadon shi ma ya ja ma su bargo ya rufe su. Towel din jikinta ya warware za ta yi magana ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Hannu ya kai jikin kan gadon ya rage hasken ɗakin, take duhu ya mamaye ɗakin. Tsoro da fargaba suka ziyarce ta amma idan ta tuna huɗubar da Aunty Rahama ta yi ma ta sai ta fara kokarin kawar da tsoron da take ji. Bakinsu ya haɗe waje guda ya fara aika ma ta da zazzafar kiss, wanda babu ɓata lokaci ta fara mayar ma sa da martanin abun da yake yi ma ta. Take saƙon ta ya fara isa gare shi ya kuma yi tasiri a jikinsa. Tsawon mintinan shida suka dauka suna yi tsotson bakin juna cikin raɗa ya ce . "I love You Nadra." "Love You too Yaya Fahad." Hannunsa ya sa ya shiga shafa fatar jikinta daga sama har ƙasa ta ko ina a jikinta. Musamman ƙirjinta da yake cike da dukiyar Fulani masu ɗaukar hankalin mai kallon su. Ya kai bakinsa ya fara tsotson su har jikinsa na rawa kamar mazari. Ita kanta yau ta ji tana bukatar mijinta, don magungunan gyaran da Sunyi Rahama ke ba ta ne yake yi ma ta aiki. Don ba karamin ni'ima ya sakar ma ta ba. Duk ta gama jiƙewa. Sai da suka kai junan su ƙololuwar buƙatuwa da juna sannan ya karanto addu'ar saduwa da iyali ya shige ta. Sai da suka yi ihu tare ita na zafin da ta ɗan ji shi kuma na daɗi ya yi. _Sidra_ Jin Nadra shuru ba ta dawo ba ya sa Sidra hankalin ta ya tashi. Don yanzu ta fara tsorata da wanan lamari. Don tabbas ta fara hango soyayyar Nadra a idanun Fahad kamar yadda ta ga soyayyar Fahad a idanun Nadra. Ta tasa yaushe ne suka kamu da soyayyar juna. Don kama yanzu ba tsana ko ƙiyayyar ɗaya daga cikin su akan ɗaya. Haka kawai ta ji jikinta bai ba ta ba wanda hakan ya sa ta tashi da sauri ta fita daga ɗakin. Ta baya ta zagaya daidai saitin window na ɗakin Nadra jin shiru ne ya sa ta zagaye ta window na ɗakin Fahad. Abun da kununuwan ta suka jiyo ma ta ne ya yi sanadiyar ɗaukewar numfashinta na wucin gadi. Domin numfashin su take ji gami da gurnanin mai haɗe da ihu da Fahad ke yi ya wanda hakan ya sa Sidra shhga tashin hankali. Toshe bakinta ta yi dan kada sautin kukan nata ya fito ta bar wajen a guje. Ikon Allah ne ya kai ta ɗakinta wanda shigar ta kenan ta faɗa kan gado tana fashewa da matsanancin kuka mai ƙona zuciya. "Shi kenan ta ƙare mun na shiga uku na lalace. Ya mafarkina ke shirin rugujewa lokaci daya ne? Dama na zo gidan nan ne don na kwashi bakin ciki da kunci?" Kai ta girgiza da sauri tana cewa. "Ina ba zai yiwa ba Wallahi hakan ba za ta faru ba, Nadra ba za ta taba yin nasara ni kuma na fadi ba. Saboda ba abun da ta fi ni da shi." Haka ta dinga kuka tana Surutai ita kaɗai kamar wata mahaukaciya. _Nasreen_ Cike da mamaki da al'ajabi na Khalifa Makaho da ta gani a wajen taron Centre ta ciro wayar ta a jaka. Lambar ya wayar Ma'eesha ta lalubo ta danna ma ta kira, sai dai cikin rashin sa'a har sau biyu tana kiran wayar Ma'eesha ba ta ɗaga kiran wayar ba. Saurayin da suka zo tare ne ya ce . "Lafiya kuwa?" Sai da ta yi dariya sanan ta ce . "Kada ka damu, ƙawata ce aka yaudara aka cuce ta nake son sanar da ita gaskiyar da ba ta sani ba." "Ban gane ba." "Ba za ka gane ba dama. Ka manta kawai ba zai amfane ka da komai ba." Tana gama faɗar haka ya ja hannunta suka shiga cikin wajan taron. Suna shiga ciki ta hangi Angon na dosowa wajan Jalaluddeen, yana isowa ya rungume shi yana cewa. "Jalaluddeen kana ƙasar nan dama?" "Wai dama kai ne kake aure yau?" "Eh ma na na ɗauka saboda ni ka zo." "A'a rakiya kawai na yi ban san mai ne ango ba ma." " Tun da muka gama karatu fa ba ku sake haduwa ba ko? Mun hadu ma na sau ɗaya a ƙasar Canada." "Haka ne to ya aiki ya iyali?" "Ban yi aure ba har yanzu ina dai kan hanya." "To ma sha Allah, Allah ya kawo lokaci na alkhairi." Daga nan suka rabu ango ya koma wajen da aka tanadar dan shi da amaryarsa. Yayin da Jalaluddeen ya koma ya zauna kusa da Yasmeen. Yana zama sai ya lura da Nasreen na ɗaukar su photo. Ya basar kamar bai ganta ba. Ana ta Shagali mawaki ya waƙe amarya da ango an yi rawa da waka. An yi wa amarya da ango liƙin kuɗaɗe ciki kuwa har da Jalaluddeen. Don ba karamin kudi ya yi ma su liƙi ba kuma ƴan dubu ɗaya ne kuɗin da ya yi ma su liƙi. Bayan wani lokaci an fara cin abinci yayin da kowa ke cin abin da ransa ke so ne Nasreen ta zagaya ta wajan Amarya. "Ke kalli wancan Mutumin kin san shi ne?" "Ta yi maganar tana nuna ma ta Jalaluddeen wanda ke kare da waya a hannunsa tana magana." Dariya ta yi sannan ta ce "Okay Jalaluddeen kike nufi ki? Kin ga handsome guy kin ƙyasa ko? To ki cire rai domin ana shirin aurensa kwanan nan ne. Da ba don tsaiko da aka samu ba su da yanzu ya dade da angocewa ba." "Ba sunan sa Khalifa ba? Sanan yana gani ba Makaho ba ne?" Sai da ta yi dariya kafin ta ce "Wani Khalifa kuma wani Makaho kuma? Ko dai ya yi ma ki kama da wani ne?" "Ba wani kama na tabbatar shi ne kuma sai na toni asirinsa ." Dariya kawai ta yi don tana yi wa Nasreen kallon wacce ba ta cikin hayyacinta. Kafin a tashi taron Jalaluddeen ya ce wa Yasmeen ta tashi su tafi yamma ta yi. Ba musu za su bar wajan duk idanun Nasreen nan kan su. Ita kanta ta matsu su bar wajan saboda ta lura da yadda Nasreen ke yi wa Jalal kallon ƙurilla wanda ya da ran Nasreen ɓaci. Don kishinsa take yi, a tunanin ta Nasreen na kallon Jalaluddeen ne saboda tana son sa. Har sun yi nisa ta juyo ta watsawa Nasreen wani banzan kallo mai haɗe da gargadi sannan ta bar wajan. _Mamy_ Cikin tashin hankali take bincike a cikin ɗakinta. Gabaɗaya gwala-gwalai da ta tara babu ko ɗaya, hatta kuɗaɗen da take ɓoyewa a ɗakinta ba ko sisi. Cikin tashin hankali ta nufi in da ta ajiye ƙadarorin Dady. Kasancewar yanzu baya da kataɓus a gidan sai abun da ta ce ya da ta karɓi takardun fiye da ƙadarorinsa da ta mallaka. Wasu ma sunan Ma'eesha ne a jikin takardun. Ɗora hannu ta yi a saman kai tana fadin ta shiga uku. Domin ta san ba mai shigo ma ta cikin ɗaki sai Laila. Ita kadai ce take shigo ma ta ɗaki don ko Jamil bai cika shigo ma ta ɗaki ba. Cikin tashin hankali ta lalubo lambar wayar Laila ta danna ma ta kira, sai dai har ya katse ba ta ɗaga ba. Sau uku tana kira ba ta ɗaga ba. "Allah ya sa yarinyar nan ba ta salwantar da ƙadarorin nan ba." _Laila_ Tana zaune a gaban motar Taj ta kalle shi ta ce . "Wai yaushe za mu bar ƙasar nan ne mu tafi ƙasashen da aka ce yawon shaƙatawa. Sannan kuma yaushe ne za mu yi auren?" "Kada ki damu idan kin gama tattaro duka dukiyar muka tara su na tabbatar za mu ishe mu mu yi rayuwar mu a can ba tare da har jikokin mu sun yi talauci ba." "To zan dai sake bincikawa amma na tabbatar na kawo ma ka kaso saba'in na dukiyar gidan." "Ba iyakar su kenan ba ki sake gwada wa ki tabbatar kin gama kwashe komai kuɗaɗe da kadarori da gwala-gwalai. Ba kin ce yanzu ba komai a wajen Dady ba duk Mamy ta amshe komai?" "Eh na kawo ma ka duk wasu takardun duk rabi na takardun sunan ƴarsa Ma'eesha ya saka, kuma yanzu na Mamy ta raba shi da ƴarsa Ma'eesha ka ga ba mai gadon dukiyar ko?" "Mu za mu gaje su mu je mu yi bushasha" "Don Allah kada sai na gama tattara komai na mallaka ma ka don mu je mu yi rayuwar mu a can kamar yadda ka ce daga baya ka juya ma ni baya ka guje ni" "Haba ni ba bututu ba ne, ki daina tunanin hakan ?" Murmushi ta yi tare da cewa. "I love You?" "Love you more." Kallon takardun da ta kawo na sa yau ya yi sannan ya ce. "Ana jira na zan iya tafiya?" "Eh za ki iya sai gobe idan mun hadu sai mu sake tattaunawa." Fitowa ta yi daga cikin motar ta shiga motarta wacce a baya mallakin Ma'eesha ce kafin su raba ta da shi . Tana fita ya fara duba takardun sannan ya kira Jalaluddeen a waya." Lokacin Jalaluddeen na driving za su koma gida shi da Yasmeen, ya ga kiran yaron aikinsa ya shigo wayarsa. Parking ya yi a gefen hanya sannan ya fito daga cikin motar ya bar Yasmeen a ciki. "Hello Taj." "Hello sir, barka da yammaci sir." "Yauwa Barka dai , an kara samun wasu abubuwa daga yarinyar ne?" "Eh Yallaɓal ga wasu takardun nan yanzu ta kawo, wasu sunan Ma'eesha ne a jiki, wasu kuma sunan Mahaifinta bai Mallaka ma ta su ba." Jinjina mai Jalaluddeen ya yi kafin ya ce . "Da kyau Taj aikinka ya yi kayu, dama na san za ka iya shi ya sa na saka ka. Ka ajiye takardun zuwa jibi zan dawo sai ka kawo ma ni su na haɗa su tare da waɗan can da ka karɓo.." "Okay Sir." "Yanzu a cikin waɗan nan takardun da ka kawo ma ni ba takardar Kamfani a ciki?" "Gaskiya babu." "Zuwa gobe ka bincike ta ta nemo ma ka wannan takardar, don Ma'eesha ta taɓa ba ni labarin kamfanin, duk da ya zama mallakin Mahaifiyarta ne shi mahaifin dama ko da ya siye kamfanin fama kamfanin ya mutu sai an raya shi, kuma amma takardun suna gidan duk yadda za'ayi ka saka ta nemo wannan takardar." "Ina tunanin daga ita har Mamy ba su san da kamfanin ko takardun su ba." "A yadda suka mayar da Dady ba zai ɓoye ma ta komai ba, don haka ka sa ta nemo shi yana da mahimmanci sosai." "Okay sir, in sha Allah zan saka ta kawo su." Sallama suka yi ya katse kiran wayar sannan ya shiga motar ya yi ma ta key ya fara tafiya. Kallonsa Yasmeen ta yi ganin lokaci daya yanayinsa ya sauya sai ta fasa ma sa maganar da ta yi niyya, don ta san halinsa idan ransa ya ɓaci ba za ta ji dadi ba, barinsa shi ne mafi sauki." Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana, horn ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shigar da motarsa ciki. Satar kallonsa ta yi kafin ta ce . "Thank you my husband to be..." Kallon ta ya yi ta fita da sauri tana murmushi. Tura hannunsa ya yi cikin suman kansa yana yamutsawa. Sannan ya kifa kansa kan sitiyarun motar. Tsawon mintuna biyar har motar Abbi ya shigo direban Sa ya yi parking ya buɗe ma sa ya fito. Har zai wuce ciki ya lura da motar Jalal da ke kunne. Ya karasa jikin motar ya yi knocking glass ɗin. Sai a lokacin Jalal ya ɗago tare da sauke glass ɗin motar. Ganin Abbi ne ya sa ya bude murfin motar ya fito. Cikin kulawa Abbi ya ce . "Son kana lafiya dai ko?" "Alhamdulillah Abbi ." "Ka tabbata ba wata matsala?" "Bo komai Abbi kawai dai na gaji ne." A tare suka jera suka shiga cikin gidan suna fira. *Washegari* Suna zaune a babban falon gidan suna fira. Abbi, Ummee, Jalaluddeen, Yusuf, da kuma Yasmeen. Fira suke yi cikin nishadi, kafin suka ji horn ɗin mota. " Ganin karfe uku ne ya sa Ummee cewa. "Ko Yaya ya iso ne?" Ta yi maganar tana kallon Abbi. "Ina ganin ya iso don lokacin da ya faɗa kenan yanzu." "Lafiya dai ko Abbi?" Cewar Yusuf yana kallon Abba. "Lafiya lau Alhamdulillah, abun farin ciki ne ma za mu ƙulla." "Alhamdulillah. Wani abun farin ciki muka samu?" "Muna son gobe a ɗaura auren Jalal da Yasmeen yake so a tattauna." Da sallama Dad ya shigo cikin falon suka amsa ma sa, sannu da zuwa suka yi ma sa dukansu. Ya amsa sannan ya zauna suka gaisa. Ummee da kanta ta jawo ma sa abun sha ya sha sannan ya yi gyaran murya. "Duk da ba na da lokaci ina kan hanya ne, sai dai sanin gobe ne Jalaluddeen zai tafi ya sa na zo." "Haka ne Yaya." "Cewar Ummee." "Don haka rashin sanin cewa idan ya dawo washegari za'a ɗaura ma su aure. Na ɗauka cewa sai ya kammala aikinsa zai dawo, to sai aka samu akasi ba yadda na yi tunani ba ne, don haka ya kuke gani." "Kawai a ɗaura ma su aure ya tafi da matarsa kowa ya huta!" Cewar Ummee tana kallon Yayan nata. "A'a ku bari a ji daga bakinsa duk yadda ya ce haka za'ayi. " Cewar Abbi yana kallon Jalaluddeen. "Son ya ke ce shin a ɗaura ma ka aure kana da ra'ayin tafiya da matarka ba za mu takura ma ka ba?" "Abbi ina neman alfarma a yi hakuri a bari na karasa aikin da na je yi idan na dawo sai a ɗaura auren ko da kuwa ranar da na dawo ne." _Nasreen_ Bayan an kai amarya gidanta ta samu isasshen natsuwa sun koma masaukin su sannan ta dauki waya ta kira lambar wayar Ma'eesha. Bugu biyi ta ɗauka cikin nitsatsiyar muryarta ta yi ma ta sallama. "Assalamu alaikum ƙawata." "Rike sallamar ki ina son ki saurare ni da kyau." Cikin mamaki Ma'eesha ta ce. "Ikon Allah sallama bushara ne da saƙon aminci, amincin shi ne ba ki so?" "Duk ba wanan ba, ina mijinki yana gida?" "A'a ya yi tafiya." Sai da Nasreen ta yi dariya sosai kafin ta ce . "Idan kika wayi gari wanda yake tare da ke kika yarda da shi kika ba shi amana ya ci amanarki ya yi ma ki karya fa?" "Ba sai kin tambaye ni ba, na tsani ƙarya na tsani yaudara na tsani mai aikata su ko ma waye! Ai ke ma kin sani ba na son ƙarya idan na kama mutum da wanan halayyar zan iya rabuwa da shi kin sani. Amma me ya sa kika yi ma ni wanann tambaya?" "Amsar yaba tare da ni ko ba faɗa ma ki ba za ki yarda ba dan idanun ki sun rufe, amma idan na zo na nuna ma ki video da photo hakan zai tabbatar ma ki da gaskiyan lamari, ki gode wa Allah da na je biki a Abuja don zuwan ki ne." Daga haka ta katse kiran wayar yayin da Ma'eesha ta bi wayar da kallo cikin rashin gane in da zancen nata ta dosa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣7️⃣ Na tambaye ka wace ce ita ba ka sanar da ni ba, yanzu ka shirya faɗa ma ni ne?" Juyo wa ya yi ya kalle ta ya n da take ƙaraso wa cikin ɗakin. Zama ta yi gefensa ta dafa kafaɗar sa tana cewa. "Na ji an ce uwa tana iya karantar idanun ɗanta, tabbas na yarda da wanann domin kuwa tun ranar da ka iso garin nan na lura da hakan. Amma sai ka ce ma ni ba haka ba lokacin da na tambaye ka, har na yi ma ka maganar nan ka nuna ma ni cewa ba komai." Shiru ya yi ya dauke kansa daga duban mahaifiyar tasa don ta yaya zai iya sanar da ita cewa yana da mata bayan ba su suka sura ma sa ita ba ba su san da zancen ba. Tabbas wata zuciyar na ingiza shi akan cewa ya sanar da ita komai amma yana gudun abun da zai je ya dawo. Don haka a ƙasan ransa ya ji cewa gara ya bari idan ya kammala aikinsa da ya kai shi can garin ne sai ya dawo tare da Ma'eeha ya ajiye ta gidan Mom tare da gabatar da ita ya sanar da ita komai. Zuwa lokacin ita ma Ma'eesha zai fara sanar da ita ko shi waye kafin ya sanar da danginsa. Da wanan tunanin ya saki murmushi yana cewa. "Mom kin dawo?" "Na dawo ya kake ya mutanen gida?" "Suna lafiya lau Alhamdulillah." "Ma sha Allah. To meye labari ?" Ta faɗa tana zuba ma sa idanu . "Mom ba komai fa kamar yadda na ce, idan ma akwai zan sanar da ke idan lokaci ya yi?" Jingina kai ta yi tare da cewa . "Allah ya kawo lokacin na alkhairi." "Amin ya Allah." Shiru ne ya biyo baya kowa da abun da yake ransa, kafin ta katse shirun ta hanyar cewa. "Gobe ne tafiyar taka ko?" "In sha Allah." "To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya ya kare ka a duk in da kake ya ba ka nasara." "Amin ya Allah Mom. Na so na a ce na ƙara kwana biyu saboda Sadik ya kai ni wajen dangin ki da ban san su ba mu ga juna da su. Musamman mutanen Katsina ya dace na gan su har da wanann rigimammiyar tsohuwar da nake jin labarin ta wajen Sadik. " Dariya ta yi tana cewa. "Mahaifiyar tawa ce rigimammiyar tsohuwar sau nawa ka ganta ?" "Na gan ta ai lokacin da kika taɓa samun accident din nan ta zo a lokacin har ta addabi jama'ar asibiti idan an ce ta yi shiru ta fara masifa." Dariya ya yi suka cigaba da fira har Saddiƙa ta yi sallama ta shigo ɗakin. "Wato Yaya ka shigo ko ka neme ni ko?" "Afuwa sis ya kike, ina Sadik." "Yanzu ya shigo ya ce bari ya yi wanka ya zo ya same ka. " "Ke kina gidan dama?" "Eh ina nan kawai dama na shiga ɗaki ne ina jiran shigowar Mom, da ba fito Dad ke sanar da ni kana ciki." Zama ta yi kan carpet tana cewa. "Zan iya zama ayi firar da ni?" "Eh za ki iya ma na, tun da gulma kike son ji." Dariya Jalal ya yi yana kallon yadda take tura ba ki. Zuwa can ta ce. "Yaya Jalal wai ka fasa auren Yasmeen yanzu sai ka dawo tafiya kuma, to me ya sa bayan ni da ita duk mun gama sanar da kowa zancen ga shi har kuka sai da ta yi." "Ai na san giulma ce ta kawo ki nan yanzu." "Mom na tambaye shi ne fa na ga ƴar uwata ƙawata na cikin damuwa na rashin auren da ya sa aka ɗaga, ya bar ƙawata cikin damuwa da zullumi." "Kar ki damu sis komai lokaci ne, idan Allah ya kawo ranar sai ku ga komai sai ya zama tarihi, na fi son na kammala abubuwan da na saka a gaba a halin yanzu." "To Yaya Jalal Allah ya taimaka ya yi jagoranci." "Amin ya Allah." Sadik ya shigo da sallama a bakinsa, suka amsa ma sa ya gaishe da Yaya Jalal kasancewar tare da Mom ya dawo aiki shi. Zama ya yi suka cigaba da fira cikin farin ciki da nishadi har karfe sha daya na dare ta yi ba su sani ba. Daidai lokacin Yusuf ya shigo ɗakin da shi da Dad. Bayan sun yi sallama sun shigo ne Jalal ya kalli Yusuf yana cewa. "Har ka dawo ne?" "Eh yanzu fa karfe goma sha daya na dare." Duk sun yi mamaki sosai ba kadan ba, don ba su yi zaton lokaci ya tafi har haka ba. Sallama Jalal ya yi ma su amma kafin nan sai da ya turawa Sadik kuɗin ma su yawa a account din sa ya ce ya yi siyayyan gida kayan abinci da kayan bukata. Godiya da sa albarka Mom da Dad suka yi ma sa sannan ya yi ma su sallama, har wajen motat Yusuf suka raka su, sai da suka bar gidan suka koma ciki, sai dai zuciyar Mom na ayyana ma ta akwai abun da Jalal ke ɓoyewa. Ko da suka koma gida Ummee da Abbee na zaune a falo suna sai Yasmeen da ke can gefe. Da sallama suka shigo yayin da Abbee ke cewa . "Yauwa ga su nan ƴan halak sun bayyana, hankalinki ya kwanta?" Kallon su Jalal ya yi yana cewa. "Ga Ummeenku ta damu ba ku dawo da wuri ba ga dare ya y,i har za ta kira ku na hana ta na ce dare ya yi na san duk in da kuke yanzu za ku dawo. Ya su Dad din da Mom." "Kowa na lafiya suna gaishe ku." Cewar Yusuf yana zama kan kujerar mai zaman mutum ɗaya. "Son ba wata matsala ko?" Ta yi maganar tana kallon Jalaluddeen. "Ba komai Ummeena, in sha Allah kuma tafiyar safe zan yi." "Ba damuwa Allah ya kai mu ya tsara mun kai a duk in da kake ." "Amin Ummeena." Abbee da Umme suka tashi suka shiga ciki yayin da Jalaluddeen ya tashi ya koma gefen Yasmeen ya zauna. "Meye matsalar ki." Shiru ta yi ma sa tana wasa da wayarta. "Ki yi hakuri na fahimce ki, ni ma nan da kika gani dole ta sa na ɗaga auren saboda na fi son idan na kammala aikina na dawo sai ayi auren hankali na ba zai rabu biyu ba. " Cikun karaya ta ce. "Na ga kamar gujewa auren kake yi ne." "Wa?" Ya faɗa yana fito fito da idanunsa. "Kai ma na Yaya Jalal." "Wane ni? Waye za'a ba sa zugegiyar mace kamar ki ya ce baya so.." Madadin ta sauko sai ta sake tunzura tana cewa. "Wato ba ka ni aka yi ba cewa ka yi kana so na ba ko? Na sani ba sai ka nanata ma ni ba na san kai ba ka ce kana so ka ba aka ba ka ni." "Ya Salam ba haka nake nufi ba, kada ki juya mun zance ki fahimce ni." Tashi ta yi tana kuka wanda ya san kukan baya rasa nasaba da burin da ta ci na auren wanda shi kuma ya ruguza shirin nata. Bedroom ɗin ta ta nufa tana kuka. Bin bayanta ya yi zuwa ƙofar bedroom ɗin nata, ya tura ya ji ta rufe da key ta ciki. Barin wajen ya yi Yusuf ya bi shi da kallo yana dariya, hararar sa ya yi ya wuce bedroom ɗin sa. Ita kuma jin bai yi ta knocking yana roƙon ta ta bude ma sa ƙofar ba ne ya saka ranta ya kara ɓaci. Yana shiga cikin bedroom ɗin sa ya ci karo da kiran wayar Ma'eesha na shigowa cikin wayarsa. Kiran ya bari ta katse sannan ya bi bayan kiran nata. "Assalamu alaikum warahmatullah." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya amsa ma ta. "Wa'alaiki salam warahmatullah mar'atussaliha." Murmushi ta yi cike da nishadin jin muryarsa. "Na'am mijina ina wuni." "Lafiya lau Alhamdulillah ya karfin jikin?" "Na warke dama zazzaɓin rashin sanin halin da kake ciki ne tun da na ji muryarka na warke." Murmushi ya yi yana mai jin dadin kalamanta da suke kwantar ma sa da hankali. "Me kika shirya mun za ki tanadar ma ni gobe idan zan zo?" "Komai da na san kana so na tanadar ma ka shi ." "To godiya nake mar'atussaliha, Allah ya yi ma ki albarka ." Da Amin ta amsa ma sa , daga nan ta ce ma sa . "Bari na bar ka haka nan na san ba kudi ne da kasa ba ballantana ka saka kati a waya." "Waye ya ce ma ki ban da kudi ?" "Na san a yadda ka yi tafiyar nan ba ka da kudi ai. Ms ce ba?" "Kika ce me?' "Na ce ko za ka samu wanda ke da account number sai ka tur mami na saka kudin da Z ka karamar mota. Kasancewar da za ka tafi wata babbar motar kaya fa ka bi na san ka sha bakar wahala sosai to hakan ya sa na ce bari na tura ma ka kuɗin motar cikin kuɗin tallafin da muka samu." "A'a kada ki damu wanann karon ba babbar mota zan bi ba, ƙaramar mota zan bi na samu wadan da suka bani kudi na san za su ishe ni." "To shi kenan Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah ya dawo mun da kai lafiya ." "Amin ya Allah na gode sosai Allah ya ma ki albarka ." "Amin mijina." Sallama suka yi sannan ya katse kiran wayar yana tunanin idan ya tashi gobe yin da jirgi zai bi kuma ki awa daya ba zai cika a jirgi ba zai isa, don haka ya yanke shawarar zai sauka a hotel ɗin sai zuwa yamma ya isa gida gudun kada ta zarge shi. Da wannan tunanin ya kwana. _Nadra_ Bayan ya gama ayyukan gidan kamar yadda ta saba, ta share ko ina ta gyara, ya saura daura ɗakin Fahad wanda ta san yana kwance tama jira ya tashi. Kitchen ta shiga don haɗa ma su breakfast, nan da nan ta kammala ta je ta yi wanka. Riga da siket ta saka na atamfa wanda ya zauna ma ta ya yi ma ta kyau sosai a jiki. Ɗakimsa ta nufa ta ji saukar ruwa a bathroom, hakan ya tabbata ma ta fa yana wanka kenan. Ɗakin Sidra ta tafi ta tarar da ita har ta yi wanka ta shirya cikin ƙananan kaya riga da wando. "Ina kwana Aunty." "Lafiya lau." Ta amsa ma ta ba yabo ba fallasa. "An tashi lafiya ya jikin naki." "Da sauki Alhamdulillah." "Ma sha Allah, Allah ya kara ma ki lafiya.," "Amin ." "Dama na gama haɗa breakfast ne shi ne na zo na kira ki za ki fito ne ko na kawo ma ki naki a nan?" "A'a zan zo nan na ci tare da ke." "Okay to mu je. A tare suka fita har suka haura sama , a dinning area suka karasa in da Nadra ta ja ma ta kujera don ta zauna ." "Bisimillah ki zauna ina zuwa ." "Me zan zuba ma ki Aunty?" "Ke ma kin san na fi Shan tea da safe da soyayyan ƙwai da hankalin turawa." Murmushi ta yi ta fara hada ma ta tea ta haɗa ma ta komai da komai da take buƙata. "Bari na je na duba ko Yaya Fahad ya gama shirya wa." "Hmmm da alama dama can kina son Fahad munafurci ne ya sa kika nuna ba ki so ko, yayin da kika ma ni alkawarin cewa za ki rabu da Fahad ni kuma ya aure ni shi ne kika yi kane-kane , amma ku saurari abin da zai biyo baya daga ke har shi mayaudarin ." Daidai lokacin suka ji ƙarar buɗe kofa kamar mutum ba fitowa. Ƙamshin turarerensa ne ya fara iso wa gare su. Yana sanye cikin suit farar takaminsa baki da farin glass da yake sanye da shi. Sai da zuciyar Sidra ta buga amma kallo ɗaya yi ma ta ya dauke idanunsa daga kallon ta . Ganin hannunsa time da wasu file ne ya saka Nadra ta mike tsaye tana cewa . "Barka da fitowa Yaye Fahad." "Barka dai Nadfah." Ya faɗa yana rungumo ta jikinsa, kunya ce ta lulluɓe ta don ta tabbatar Aunty Sidra na kallon su. "Kokari. Zame jikinta ya yi yana ce w. "Bisimillah ka zo ka yi breakfast." ''ina sauri ne ana jira na yanzu n nan idan Na dawo zan ci." Jinjina kai tai ta yi tare da cewa a dawo lafiya. "Ba za ki raka ni ba.?'" Ya yi maganar yana nufar hanyar sauka yana kuma cewa . "Aunty Rahama za ta zo anjima ." Cikin farin ciki da jin dadi ta ce Allah ya kawo ta lafiya. Yana fita wayarsa ta fara ruri, Aunty Rahama ce take kiransa. Ya daga yayin da ya isa wajen motarsa. "Hello Aunty Barka da safiya." "Barka dai ya kake ya Nadra." "Muna lafiya duka." "Na ga message naka kana sanar da ni Sidra na gidanka, yanzu haka su Mama suka bar ta?" "Eh wallahi abun ya dame ni." "Ka kwantar da hankalinka ina nan zuwa wallahi yau sai ta bar gidan nan, sai dai ta koma gidan ubanta ko yanka naman jikinta zai yi sai dai ya yi. Kai kafin ma na zo ma sai na biya na sanar da iyayenta halin da ake ciki kuma na sanar da su yau sai ta bar gidanka." Cike da gamsuwa ya jinjina kai yana yi ma ta godiya, sallama suka yi ya katse kiran wayar ya shiga motarsa tare. Da yi wa motar key ya bar gidan. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣8️⃣ Cike da gamsuwa ya jinjina kai yana yi ma ta godiya, sallama suka yi ya katse kiran wayar ya shiga motarsa tare da yi wa motar key ya bar gidan. Nadra kam zama ta yi suka fara yin breakfast. Bayan kamar mintuna ashirin suna zaune wajen sai ga text message ya shigo cikin wayar Nadra. Ganin sunan Fahad ya sa Sidra ta yi saurin ɗaukar wayar da sauri kafin Nadra ta ɗauki wayar. Bude messages ɗin ta yi ta fara karantawa kamar haka. *Hi my Nadfah ya kike? Am sorry na bar gida ba mu yi gaisuwar safe yadda ya kamata ba ana jira na ne shi ya sa. Ya gajiyan daren jiya na gode sosai zuma ta. Tabbas daren jiya kin jiyar da wanan majidaɗin daɗi mara misaltuwa thank you so much, I love you more than anything* Sidra na gama karantawa sai zuciyarta ke tafarfasa ta juya ta kalli Nadra ta ga ita ma kallon ta take yi. Don dama ta ji ba daɗi daukar ma ta wayar da ta yi. Don haka ta fara jifar Sidra da wani kallo mara misaltuwa. "Munafukar banza kawai ke sa muka yi za ki rabu ma ni da saurayi na amma kika yi shiru kika sakar ma sa jiki jiki har ya kika samu kansa ko?" "Aunty Sidra maganar gaskiya ya kamata ko hakura da Yaya Fahad tun da ba shi kadai ne namiji a wanann duniyar ba. Matar mutum kabarin sa, wata ba ta auren mijin wata hakazalika wani baya auren matar wani, aure nufin Allah ne shi. Ban taɓa tunanin zan zauna inuwar aure da Yaya Fahad ba, haka shi ma bai yi zaton ni ce zan zama matarsa ba, amma da Allah ya ƙaddara ba ga shi mun yi aure ba muna zaune lafiya ya yarda da ƙaddarar sa ya karɓe ni matsayin abokiyar rayuwarsa, ni ma haka na yarda da shi a matsayin abokin rayuwata. To ke me ya yasa ba za ki yarda da ƙaddara ba a matsayin ki ba musulma ki nemi zaɓin Allah. A gaskiya da ba na ƙaunar Yaya Fahad amma a halin yanzu ina jin sa har ƙasar raina, ban san yaushe ne na kamu da son sa ba amma tabbas na san yanzu ina son sa. Shi ma yana so na don haka ki haƙura ki fauwala wa Allah lamuranki zai taimake ki, don Yaya Fahad bakya gabansa ko ganin ki ba ya son yi, kamar yadda ya ce idan ya bar abu ya bar shi kenan har abada ba zai dake waiwayar sa ba to haka ne. Fata na Allah ya ba ki mijin da ya fi Yaya Fahad." Tana faɗar haka ta tashi da niyyar za ta bar wajen, ita ma Sidra ta yi saurin mikewa tare da cewa . "Ni kike faɗa wa wadan nan maganganun saboda na zo gidan aro?" "Aunty Sidra wannan gidan ba gidan aro ba ne gidana ne na har abada sai mutuwa ce z ga fitar da ni daga cikkin...." Kafin ta mai zancen maganar ta Sidra ta ɗaga hannu da niyyar kai wa Nadra mari. Cike da zafin nama Nasara ya yi saurin riƙe hannun Nadra salqfin ta ce . "Kada ki kuskura hannu ki taɓa jikina, domin yanzu ba da ba me. Kika mare Ni sai na rama wallahi sai dai mu yi kare Juni biri jini wallahi." Cike da mamaki take kallon Nadra domin ba wacce ta sani ba ne, ba wacce ta saba rayuwa da ita ba ne, domin da ita ce, ba wacce ta saba zagi har ta mare ta ba ce, sai dai yi kuka ta ba ta hakuri. Ba wacce ta saba ba ce. Yau wata ce take gani a gabanta ba waccen Nadra ba ce." Nadra ta tashi ta bar wajan dan ta fara gajiya da magana ɗaya da Yayan take yi ma ta. Kullum zuga ta take yi akan ta rabu da Fahad ta yi ma sa wulakanci ko zai yi zuciya ya sake ta. Ita kuma ba za ta iya ba gaskiya ba za ta iya ba domin saɓawa Allah ta sabawa Iyayenta don ta faranta wa Aunty Sidra ba. Saman gadonta ta faɗa tare da sakin kuka , gabaɗaya ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta, ga shi lokaci guda ta kamu da soyayyar Fahad ba tare da ta shirya wa hakan ba. Ga Aunty Sidra ta ƙwallafa wa ranta dole sai da shi za ta rayu. _Aunty Rahama_ Bayan ta gama shirin ta na zuwa aiki yara shi an kai su school ne ta fito daga gidan. Driving take yi a motar cikin nutsuwa duk da ta makara da zuwa aiki amma da safen nan ne take da tabbacin cewa za ta samu Abba a gida. Tana isa ƙofar gidan ba ta yi horn ba ta fito daga cikin motar, knocking ƙaramar ƙofar ta yi nan da nan maigadi ya taso ya buɗe. "Barka da aiki Mallam." "Yauwa Hajiya ina kwana?" "Lafiya lau, Alhaji yana ciki kuwa ko ya fita?" "A'a yana ciki?" Ya yi maganar yana matsawa gefe don ba ta hanyar shiga. Ta shiga ciki har zuwa ƙofar falon za ta yi knocking kenan dai ga Abba ya bude kofar zai fito. Tana ganinsa ta durƙusa cikin girmamawa ta ce. "Ina kwana Abba.?" "Lafiya lau, Rahmatuko ?" "Eh Abba." "To suna ciki ki shiga ni za fita?" "Ai wajen ka na zo Abba." "To bisimillah shigo." Ya yi maganar yana komawa ciki Aunty Rahama ta bi bayansa. Da sallama suka shiga falon Umma da Ammi dake zaune a falon suka amsa. Aunty Rahama ta gaida kowa cikin girmamawa sannan ta zauna ta kalli Abba ta ce. "Da farko dai Abba ba maganar Sidra zan yi ma ka ba kasancewar ba ka son a yi zancen ta. Amma ina son sanar da kai ne matuƙar ba ka dawo da Sidra gidanka ba to haƙiƙa za ta kasance barazana ce ga rayuwar auren Nadra." Da sauri suka kalle ta cike da mamaki, Abba ya shiga tashin hankalin jin cewa rayuwar auren Nadra zai iya samun tangarɗa akan Sidra." "Meke faruwa?" Cewar Ammi tana kallon Rahama. "Sidra ta dage ba za ta zauna a gidan mahaifin mu ba sai gidan Nadra a halin yanzu a can gidan Nadra take zaune wanda na san zaman dole matsala za ta biyo baya." Nan ta ba su labarin abun da ya faru daga rashin lafiyar Sidra har zuwa komawar ta gidan Fahad. "Ta ina hakan za ta faru wallahi na tabbatar ba alkhairi ne zai kai Sidra gidan Nadra ba sai don ta kashe ma ta aure, dama tana jin baki cikin an aura wa Nadra Fahad. Abba kasa magana ya yi illa ya dauki wayarsa ya kira ƙanwarsa Laraba. Bugu biyu ta daga ya fara magana cikin ɓacin rai da takaici "Laraba ina son idan kin gama abun da kike yi ki tafi gidan Maimaina ku hadu ku je gidan Nadra ku dawo da Sidra gidana ƙafarta ƙafarku, tana can ta tare a gidanta." Daga haka ya katse kiran. Wayar, daidai lokacin Aunty Rahama ta yi ma su sallama ta tafi. Idanun Abba kawai za ka ƙalla ka san cewa ransa a ɓace yake . _Jalaudeen_ Fitowa ya yi daga cikin gida yayin da gabaɗaya mutanen gidan suka fito don yi ma sa rakiya.. Mota ɗaya za su tafi airport da ita, miyar Yusuf ce "Yusuf ya shiga mazaunin direba yayin da da Jalaluddeen ya zauna gefensa. Bayan motar kuwa Abbi da Ummee ne a baya sai Yasmeen da take zaune a gefen Ummee. A hankali suke tafiya yayin da Yusuf ke cewa. "Amma idan ka dawo wanan karon shi ne dawowar ka ta kammala aikin ko?" "In sha Allah, don na riga na gama haɗa bayanan da zan haɗa, kama su shi ne abun da ya rage, da kuwa wasu abokan harkar ta su da nake so na tabbatar." "Allah sarki bro kana kokari ma Allah ya bada nasara." "Amin ya Allah." "Umme da Abbi suka hada baki wajan amsa wa. Har suka isa airport fitar fitar aikin nasa suke yi. Bayan sun fito daga motar ne Yasmeen ta tsaya a gabansa tana ma da wani kallo mai wuyar fassara. Komawa ya yi gefe wanda gane abun da yake nufi ya sa ta bi shi ta tsaya a gabansa fuska ba walwala. Murmushi mai sauti ya saki kafin ya ce . "Yasmeen rigima ko gaishe ni fa ba ki yi ba." Shiru ta yi masa wanda ganin haka ya sa ya ce . "Okay." Yana kokarin barin wajen. Rigarsa ta rike tana girgiza kai. "Me zan yi ma ki bayan fushi da ni kike yi?" "To ka tsaya na daina." Zuba ma ta idanu ya yi ya rungume hannayensa a ƙirjinsa. "Kin ga na fahimce ki ba yadda kike tunani ba ne, na ina nuna ma ki halin ko in kula ba ne, kawai dai yanayin aiki ne ya sa ba na da lokacin da zan dinga kiran ki ko kuma ke ki kira ni ki same ni. Amma ai ba dole sai ta haka nan ne za ki yarda ina son ki ba, ita soyayya a zuciya take, fatan kin fahimce ni, kina zuciyata kowane lokaci kowane hali kar ki manta da wanan ." "Son lokaci ya yi fa jirgi baya jira." Ya ji Muryar Abbi yana ma sa magana. Wayarsa ya ɗauka ya yi ma ta transfer na kudi a account din ta sannan ya ce. "Sai mun yi waya ki kula da Kanki." Murmushi ta yi sanan ta bi bayansa suka koma wajen da su Abbi ke jiran su. _Nadra_ Bayan kukan da ta yi akan abun da Sidra ta yi ma ta ne sai barci ya ɗauke ta a wajen. Kasancewar daren jiya ba ta yi isasshen barci ba. Sidra kuwa mamaki da al'ajabi ya hana ta cewa komai kuma ta kasa barin wajen. Mamaki take yi shin har ta yi lalacewar da Nadra za ta kalli idanun ta ta yi ma ta magana yadda ranta yake so? Shin sanyi ta yi ne? Ina zafin nata yake, yarinyar da idan ta yi ma ta abun da bai yi ma ta ba za ta ɗaga hannu ta mare ta amma yau ta rike ma ta hannu yayin da take da niyyar marin ta? Sanann ta faɗa ma ta zancen da ranta yake so. Tabbas tura ta kai bango dole ta nema wa kanta mafita kuma ba ta jin za ta iya hakura da soyayyar Fahad. Tsawo lokaci ta ɗauka a wajen ba ta motsa ba, har aka dinga danna ƙararrawar ƙofar, ba ta ji ba daga farko Sakamakon ta yi zurfi a duniyar tunanin da ta lula. Daga baya ta sauka downstairs ta nufi kofar da niyyar budewa a tunanin ta Fahad ne Nadra ta sanar da shi abun da ya faru. Sai dai tana buɗe kofar mutanen da ta gani tsaye a bakin ƙofar ne suka saka hanjin cikinta kaɗawa. Ja da baya ta yi tana kallon Gwaggo Maimaina da ke jifanta da wani mugun kallo, dama tana tsoron ta kasancewar ita ma tana da zafi sosai . "Ja da baya ta cigaba da yi yayin da Gwaggo Maimaina ta finciko wuyar rigarta tana cewa. "Munafuka me ya kawo ki zama gidan ƙanwarki, kashe ma ta aure kike so ki yi ko?" Nan ma girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Tattara kayan ki yanzu ki zo mu tafi." "Gaskiya ba in da zan ta..." Kafin ta kai karshen zancen Gwaggo Maimaina ta wanke ma ta fuska fa marin da ya sa ta hantsilawa. Ita dai Gwaggo Laraba ba ta ce komai ba ta yi shiru tana kallon su. "Har kina da bakin magana eye fitsararriya mara kunya. To wallahi tun da ubanki ya ce ki dawo gida wallahi sai kin tafi." "To wai shi ya kore ni daga gidansa, kuma kuma danginsa har gidajen ku na ce kuka kore ni sannan wasu sun karɓe ni ina zaune a gidansu a ce na tafi? Sai dai idan wadanda suka ce na zo na zauna suka kore ni daga gidansu shi ne zan tafi ." "Ƙarya kike yi Sidra ƙafata ƙafarki sai kin tafi kin bar gidan nan ehe!" Gwaggo Laraba dai ba ta ce komai ba ta haura sama ta nufi ɗakin Nadra. Knocking ta yi ta ji shiru sai ta tura kofar da sallama a bakinta. Hango Nadra ta yi kwance saman gado tana barci, ga busashshen hawaye a idanunta da alama sai da ta ci kuka kafin ta yi barci. Cike da tausayin ta Gwaggo Laraba ta karasa cikin ɗakin. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page6️⃣9️⃣ Hango Nadra ta yi kwance saman gado tana barci, ga busashshen hawaye a idanunta, da alama sai da ta ci kuka kafin ta yi barci. Cike da tausayin ta Gwaggo Laraba ta karasa cikin ɗakin. "Ta san wanann hawayen ba zai rasa nasaba da Sidra ba, domin kuwa ta ɗan Fahad da wuya ya saka ta kuka. Don ko farkon aurensa da ya nuna baya son ta bai saka ta kuka ba ballantana yanzu da yake son ta. Sunkuya wa ta yi tana shafo fuskarta daidai in da hawayen ya bushe. A hankali Nadra ta buɗe idanunta ta sauke su akan Gwaggo nata. "Gwaggo ke ce ko mafarki nake yi ?" "Ni ce Nadra ba mafarki kike yi ba. Tashi zaune ta yi wasu sabbin hawaye na zubo ma ta . "Daina zubar da hawayenki kin ji?" Ai kamar ta ce ta kara ne don kuka ta saka ma ta wiwi. Cikin tashin hankali ta zauna bakin gadon tana rungume ta tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi. Ajiyar zuciya take saukewa kafin ta fara magana cikin rauni. "Gwaggo meye lafin ƴaƴan da suka yi biyayya ga iyayen su wajen cika ma su burin su? Ya sa hakan zai janyo ma su ƙasƙanci da wulaƙanci a duniyar ma'abota sadaukarwa? Shin laifina ne ko kuma ni ce na ce Abba ya aura ma ni Yaya Fahad ballanta har Aunty Sidra ta ɗora alhakin hakan a kaina?" Kuka ne ya ci karfinta wanda hakan ya saka Gwaggo Laraba sake rungume ta. "Gwaggo wallahi Yaya Fahad baya son Sidra yanzu ya tsani ganinta ko maganar ta baya so ina yi ma sa, tana zaune a gidan nan ne don saboda na nemi hakan daga gare shi, wanda shi kuma ba zai ki amince wa bukatata ba. Da a ce na ga yana son ta ko kuma zai iya auren ta wallahi zan hakura na bar ma ta shi su yi rayuwar auren su kamar yadda suka tsara. Amma shi ya ce ya hakura da ita har abada ba zai iya auren ta ba. To meye amfanin na bar ma ta shi bayan ba aurenta zai yi ba?" Ɗan bubbuga bayanta Gwaggo Laraba ta yi tana cewa. "Daina kuka ya isa haka nan kin ji, ai ba zai taɓa yiwuwa ba ne a ce ya sake ki sannan ya zo mu ba shi auren Sidra ba, idan ba rashin hankali irin nata ba da rashin tawakkali irin nata ba ai hakan ba mai yiwuwa ba ne." Nadra ta share hawayenta sannan ta kalli Gwaggo Laraba ta ce. "Gwaggo me za ki ci ne daga ma ki ne?" "Hutar da Kanki Nadra mun zo ɗaukar Sidra ne bisa umarnin mahaifinku." "Abba ya yafe ma ta ne ko?" Ta yi tambayar cike da farin ciki, dama ita birninta bai wuce Abba ya daina fushi da Sidra ya yafe ma ta ba. Don fushin iyaye masifa ne akan ƴaƴan su. A tare suka fito daga ɗakin suka sauko downstairs daidai lokacin da Gwaggo Laraba ta tasa Sidra a gaba tana jan akwatin kayan ta . Cikin girmamawa Nasara ta gaida Gwaggo Maimaina , ta amsa mata cike da murna. "Nadara ya hakuri da rayuwa ya mai gidan?" "Lafiya lau Alhamdulillah ya fita." Kallon Sidra dake jifanta da wani kallo ta yi kafin ta ce. "Aunty Sidra da alama Abba ya sauko ya yafe ma ki,na yi farin ciki da haka, Allah ya..." "Dalla rufewa mutane baki munafuka, kin sanar da shi ina gidanki saboda a fitar da ni da..." Ba ta kai ƙarshen maganar ta ba Gwaggo Maimaina ta finciko wuyar rigarta ta hankada ta waje, sai da ta faɗi. Sannan ta koma ciki ta dauko akwatin kayanta ta fito da shi. Gwaggo Laraba na biye da ita a baya Nadra na n take ma su baya. "Daughter juya ki koma gida Allah ya yi ma ki albarka, ku gaida mijin naki idan ya dawo." Tana so ta yi wa Sidra magana amma ta kasa, don ko ta faɗa ma ya cewa ba ita ce ta samar da Abba zaman ta gidan ba yarda za ta yi ba. Don haka ta yi shiru idanunta na cika da ƙwalla, har direba ya ja motar suka fice daga gidan. Komawa ta yi ciki tana rusa kuka wanda ita kanta ba ta san ko na mene ne ba. _Ma'eesha_ Da taimakon A'isha wacce ta taya ta aiki ta gudanar da komai. Girki kaloli suka yi saboda tarbon Makahon mijinta. Bayan sun kammala ne ta zuba a kulolli tana kiran dawowarsa. Kasancewar ya ce ma ta garin da nisa dai yamma zai iso. Ta zuba wa A'isha ta ce ta ɗauka ta tafi da shi gida, sannan ta ba ta kudi 5k cikin kuɗin tallafin da aka kawo ma ta. A'isha na barin gidan dai ga Nasreen ta yi sallama ta shigo kamar an jefo ta daga sama. "Assalamu alaikum ina Ma'eesha take ?" "Wace'alaiki Salam warahmatullah . Lafiya wannan kiran haka Nasreen." Ba ta ce komai ba ta janyo hannun Ma'eesha suka shiga cikin ɗalo . Ita dai ma:eesha ya tsaya na kallon ikon Allah. Wayarta ta danna sai ga photon Makaho shi da Yasmeen. Sannan ta ga video shi da Yasmeen ta rike ma da hannu sune tafiya . Sai ta ga na washehari. "Na gani amma gaskiya Allah ya yi halitta kin ga wani kamanni da na gani? Gaskiya kamar ta yi yawa." Wani banzan kallo Nasreen ta yi ma ta kafin ta ce. "Wani irin kamanni to ba wani kama wanan mijinki ne Khalifa Makaho ." "Ba yadda haka. Za ya yiwu mijina makaho ne baya gani kuma tallka ne wanda idan muka samu abun da muka ci na yau na gobe sai mun nema, ba don da Allah ya rufa ma na asiri muka samu kudin tallafin nan ba har muka samu wadata ai da sai dai kawai hamdala. Ki duba wanan na jikin hoton hutu da jin dadi sun nuna a jikinsa. Ki dubi ko kayan jikinsa sun fi karfin miliyan ɗaya, kalli takalmin da agogon sa, kalli wayarsa fa kalli motar da ya fito ciki a ƙalla za ta miliyan ashirin. Don Allah ki bar wannan zancen mara tushe." "Ba yadda za'ayi kama ta yi yawa haka, ki bude idanun ki da kyau , wanda duhu da makantar zuciya ta sa kike yi wa kallon haske. Ni dama tun ranar da na fara ganinsa bai yi kama da mutumin da ya sha wahala ko kuma wata gwagwarmayar rayuwa kamar yadda ya yi ma ki ƙarya ba. Domin hutu da jin dadi abu ne wanda ba sa ɓoyuwa. Duk wanda ya taso cikinsa sai ya nuna kansa. Mijinki ki kiyaye shi ba makaho ba ne, wata manufa yake da ita a Kanki da ya sa ya yi ma ki basaja a matsayin makaho, yana da wata mummunar manufa a Kanki ki zama mai taka tsantsan wajen kula da kanki, don gaskiya hankali na bai kwanta da shi ba maƙaryaci ne mayaudari ne..." "Ya isa!" Ta faɗa a tsawace. Wanda sai da Nasreen ta kalle ta da sauri . "Dan Allah ki tashi ki tafi idan abin da ta kawo ki kenan. Mijina mai gaskiya ne ba zai yi ma ni karya ba." Ba ta ce komai ba ta bude handbag din ta sanan ta ciro wasu hotuna guda biyu na kati da aka yi. In da yake zaune tare da Yasmeen da wanda yake fitowa daga cikin mota Yasmeen na rike da hannunsa. Ga waɗan nan ki ajiye a wajen ki za su yi ma ki amfani. Daga nan ta mike ta nufi bakin kofar fita sanann ta juyo ta kalle ta. "Na yi ma ki alkawarin sai ba binciko abun da yake ɓoye wa." Daga nan ta fice daga cikin gidan ranta a ɓace. _Jalaluddeen_ Bayan ya sauka a airport Taj ya je ya ɗauko shi. Kai tsaya ya bashi umarnin ya kai shi hotel. Ba su zame ko ina ba sai hotel ɗin da yake zama. Ba ɓata lokaci suka fito daga cikin motar Taj na rike da jakar uban gidan nasa. Suna shiga ciki ɗakin Taj ya ajiye ma sa jaka, cikin girmamawa ya ce . "Barka da dawowa sir." "Barka dai ya aikin da na saka ka komai ba tafiya daidai?" ",komai na tafiya yadda ka tsara. A yanzu haka ta kawo ma ni kaso ma su yawa a cikin dukiyar mahaifin Ma'eesha. A yanzu haka akwai wasu takardun da za ta kawo ma ni a cikin kwana biyu." Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa sannan ya ce. "Thank you, za ka iya tafiya." Taj ya fita ya bar masa ɗakin. Laptop ɗin sa na aiki ɗauka ya fara amfani da shi. Sai yamma ya shiga wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, wsyarsa wacce Ma'eesha ta siya masa ya fara kunnawa. Take kuwa kamar tana jira sai ga kiran Ma'eesha ya shigo cikin wayar. Amsa kiran ya yi tare da yin sallama. Ta amsa ma sa tare da cewa. "Ina wuni mijina." Murmushi mai sauti ya yi sanan ya ce . "Lafiya lau mar'atussaliha." "Kana ina ne yanzu?" "Yanzu motar mu ya sauka ga ni nan zan nemi abun hawa ba iso gida." "Alhamdulillah na gode wa Allah da ya dawo mun da kai lafiya. Allah ya dawo da kai gida." "Amin ya Allah." Daga haka ya katse kiran wayar. Sauri -sauri ya shirya cikin kayan yadinsa ma su arha cikin wanda ya saba sawa. Sannan ya dauki jakar kayansa da ya ajiye a hotel ɗin ya tafi Abuja da wasu. Sanadar jagoransa ya ɗauka da baƙin glass da aka fi sanain sa da shi. Sannan ya dauki jakar kayan ya ya fito daga cikin ɗakin rike da wayarsa ta wajen Ma'eesha. Takalmin soso ya saka da hularsa taɓa ka ji hadisai ya fito daga hotel ɗin . Yana fita zuwa titi ya tara mai keke nape, bayan ya sanar da shi in da zai kai shi. Shiga ya yi mai nape din ya ja keke nape ɗin suka bar wajen. Har ƙofar gidan ya sauke shi. Ya biya shi kudinsa sannan ya shiga cikin gidan bakinsa dauke da sallama. Ba ta tsakar gidan don haka ya ya shiga dakin yana dogara sandarsa. Tsaye ya yi yana kallon ta da mamaki, ganin yadda ya dinga sallama ya ji shiru ba ta amsa ba. Da a da ne yana sallama za ta fito ta tare shi. Abun da ta zuba wa idanu yake kallo, kara zaro idanun ya yi yana kallon hotunan da tasa a gaba tana kallo da maɗaukakin mamaki a kan fuskarta. Ɗago da jajayen idanunta ta yi tana ma sa wani kallo mai wuyar fassara. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣0️⃣ Tsaye ya yi yana kallon ta da mamaki,ganin yadda ya dinga sallama ya ji shiru ba ta amsa ba. Da ada ne yana sallama za ta fito ta tare shi, abun da ta zubawa idanu yake kallo , kara zaro idanun ya yi yana kallon hotunan da ta sa a gaba tana kallo da maɗaukacin mamaki akan fuskarta . Ɗago da jajayen idanunta ta yi tana ma sa wani kallo mai wuyar fassara.. Ganin kallon da take ma sa ne ya sake jefa shi cikin tashin hankali. Sai ya yi ya maza ya dake kasancewar tana yi ma sa kallon makaho ne ba ta san yana gani na shi ha sa ya share ya ɗaga murya yana ƙwala ma ta kira. "Ma'eesha !" Ma'eesha!" Ina kiks shiga? Ko tana banɗaki ne!" "Na'am gani nan a gabanka." "Gaba na kuma kuma?" Lafiya nake ha sallama ba ki amsa ba?" "Ka yi hakuri ban ji ba ne na tsaya kallon wani abun mamaki ne?" "Wani abun mamaki?" "Duba ka gani." Ta yi maganar tana nuna ma sa hotunan sa da na Yasmeen. In da ya fito daga motarsa Yasmeen ta rike ma sa hannu sa kuma,. Kallo ɗaya ya yi hoton ya cije lips din sa na ƙasa kafin ya ce. "To ni fa nake makaho fa wani idanun zan gani sai dai ki bani labari." "Mu bar zancen kawai, sannu da dawowa Mijina." Ta yi maganar tana karɓar jakar da ke hannunsa. Yayin da ya fara lalube da sandarsa har ya zauna kan tabarma da ke shimfide a ɗakin ya zauna. Yana lura da yanayin ta duk taa shiga ruɗu, ruwan sanyi da ke cikin jug wanda A'isha ta siyo ma ta ta ajiye a gamda sannan ta zuba a kofi ta mika masa. "Bisimillah ga ruwa ja sha.* Ta yi maganar tana kai ma sa ruwa saitin bakinsa ya buɗe ba ki ya sha har cikin ransa ya ji sanyi. "Na gode." Ya faɗa yayin da yake kau da kansa gefe. Hakan ya sa ta gane ya ishe sa Kenan. Ajiye kofin ta yi sannan ta ɗauko farantin da ta jera ma sa abici ta ajiye a gabansa. "Ga abinci wanne zan zuba ma ka?" Ta kalle shi tana murmushi tana tuna mutum na cikin hoton. Amma kasancewar ta yarda da mijinta ɗari bisa ɗari. "Na yi ma ka masa da miyar tasushe sanann ga tuwon semovita da miyar kuɓewa. Na san kana son su ko?" Murmushi ya yi yana sa ma ta albarka yayin da ya buƙaci ta saka ma sa tuwon ya ci. Har da kunun aya ta ta saka ma sa ƙanƙara ya yi sanyi ta zuba ma sa. Fitowa waje ya yi ya zauna saboda ɗakin zafinsa yake ji kamar gidan biredi. A tare suka ci abincin suna ci tana yi ma sa fira. Sai dai ya lura da cewa duk da Nasreen ta kawo ma ta pics din su da Yasmeen bai yi tasiri a wajen Ma:eesha ba, saboda ta yarda da shi sosai kuma ta yarda da kalaman sa. "Wai na tambaye ka ma na Yaya Khalifan." "Ina jin ki." Ya ba ta amsa cike da fargaban tambayar da za ta yi masa. "Wai dama ana ana samun mutane biyu da kamanni ɗaya, komai na su iri ɗaya kuma ba tagwaye ba ne?" "Eh ana samu sosai ma kuwa. Ai kowane mutum a duniya akwai irin sa a wani wurin?" Shiru ta yi kafin ya ce. "Da ace kana gani da na nuna na ka wani hoton wani mutum mai kama da kai kamar an tsaga kara." "Allah sarki, sai ya kasance ba na gani ballantana na san meye banbancin mu." "Wata rana in sha Allah idanun ka zai bude za ka fara gani tamkar yadda kowa ke ganin ka " "Allah ya nuna ma ni ranar da idanun mijina za su buɗe ya kalle Ni na kalle shi." "Amin ya Allah" Ya amsa ma ta da shi sannan ya tashi yana yi ma ta godiya tare da yaba girkin nata. Zai shiga ɗaki kenan ya ji muryarta tana cewa. "Kana bukatar wani abu ne?" "A'a lokacin sallar magrib ya yi zan je na yi sallah." "Okay Ina zuwa . Ya tsaya bakin kofar ga shiga ta dauko ma sa sandar jagoransa. Ta zuba ma sa ruwa a buta ya je ya shiga banɗaki. Bayan ya fito ya yi alwala ya ya nufi masallaci don yin sallar magrib. _Sidra_ Kuka take yi a bayan motar Gwaggo Laraba na gaban motar yayin da Gwaggo Maimaina ke baya ita da Sidra. Ba abun da ke tashi a cikin motar sai sautin kukan Sidra. Ba wanda ya kula ta ballantana ya ce ta yi shiru ko ya ba ta hakuri. Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana a cikinsu. Horn direban ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shigo da motar ciki ya yi parking. Gwaggo Laraba ta fito daga gaban motar yayin da Gwaggo Maimaina ke dakawa Sidra tsawa wanda ya sa dole ta fito, don ta san idan ta yi ma ta taurin Kai ba wani abu ba ne a wajen Gwaggo Maimaina sai ta gaura ma ta mari a gaban ma su aikin gida . Fitowa ta yi ta nufi hanyar shiga ciki fuuu. "Uban waye kika ajiye da zai ɗaukar ma ki akwatin kayanki?" Gwaggo Maimaina ta yi maganar ranta a ɓace.. Tura baki Sidra ta yi saboda ba ɗabi'ar ta ba ce ɗaukar kaya idan ta dawo ko ba nauyi sai dai ta saka a shigo ma ta da shi. Kamar za ta yi kuka ta zo ta ɗauki akwatin kayan ta shiga da shi ciki. Ko da ta shiga ta same su duka a falo. Abba, Umma, Ammi, Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimaina. Ta yi sallama yayin da take shiga ciki, gabaɗaya suka amsa ma ta. Kallon fuskar Abba yake sakawa hanjin cikinta kaɗawa. Ajiye akwatin kayan ta yi tare da zubewa akan gwuiwoyinta. Tsawon lokacin ba wanda ya yi magana a falon sai shiru. Kafin Abba ya bude baki ya yi magana. A baya na yanke hukuncin cire ki daga cikin zuri'a ta sakamakon abun da kika yi ma ni na kunyatawa da kuma tozarci. Ko sunan ki na hana a kira mun a cikin gidan nan, na zo kowa ya fita harkar ki. Amma abin takaici ashe kin koma gidan ƙanwarki da zama Nadra. Kuma na san zaman ki a gidan ta ba alkhairi ba ne. Sai kin haddasa ma ta masifa ita da mijinta, tabbas za ki addabi rayuwar su ne. Don haka na yanke hukuncin dawowar ki a cikin gidan nan. Kuma ko ƙofar gida ban yarda ki taka ki fita ba, sanan kuma nan da wata ɗaya zan aurar da ke sadaka ga duk wanda na ci karo da shi idan na tafi ƙauye a cikin satin nan." Yana gama faɗar haka ta ɗora hannu biyu akai ta rushe da kuka tana fadin ta shiga uku ta lalace, don Allah Abba ya rufa ma ta asiri kada ya ma ta haka, amma bai saurare ta ba haka ya fice daga gidan. Hararar ta Ammi ta yi tana cewa. "Wannan hukunci da Abdullahi ya ɗauka ya yi ma ni daidai wallahi. Ya ma yi ma ki sassauci ne albarkacin mahaifiyarki da kullum take cikin damuwa akan ya yafe na ki ki dawo. Darajar ta kika ci hukuncin ya tsaya iya haka, amma hukuncin da ya so ɗauka a kanki ai sai kin tsani kanki da kanki." Tana gama faɗar haka ta juya zuwa ɗakinta, ƴaƴanta Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka mara ma ta bayan. Aka bar Umma tsaye Sidra na durƙushe tana kuka tana roƙon Umma da ta ba Abba hakuri ya janye hukuncin da ya yi niyyar ɗauka kanta . Umma ta kasa cewa komai ta yi tsaye kamar wacce aka dasa, amma da zaran ka kalli cikin idanun ta za ka hango tsantsar tashin hankali da take ciki. _Daddy_ Yana zaune a bedroom ɗin sa ya saka hoton Mummy da Ma'eesha yana kallo yana zubar da hawaye. "Kiyi haƙuri Hajiya na kasa rike amanar da Allah ya ba ni. Ƴa ɗaya tilo da Allah ya ba ni ina ji ina gani aka waufantar da rayuwar ta amma na kasa cewa komai. Yarinyar da muka haife ta mika rene ta cike da so da ƙauna, muka yi burin inganta rayuwar ta da bata farin ciki mai ɗorewa. Sai ga shi lokaci daya abubuwa suka dagule. Na san cewa kafin rasuwar ki ban yi ma ki adalci ba, na tauye ma ki hakkin ki ga ƴar da kika haifa ina ji ina gani aka mayar da rayuwar ta zuwa matakan rugujewa. Ban san a wani halin take ciki ba. Wasu abubuwan duk ba na iya tuna su tun bayar zuwan Mamy da yaranta gidan nan. Ki yafe ma ni don Allah, Allah ya yi ma ki rahama ya sa aljanna Firdausi ce makoma a gare ki. Ma'ee..." "Alhaji!" Ya ji Mamy ta kira sunan sa a tsawace. Da sauri ya juya yana goge hawaye. Ƙarasowa ta yi cikin isa da taƙama ta ce. "Me kake yi da wanan hoton, kuma kukan me kake yi ne? Wani sabon mutuwa aka yi ma ka ne, ko Ma'eesha ce ta muyiy. Da sauri ya girgiza kai ya na cewa . "Ma'eesha na nan da ranta ba ta mutu ba in sha Allah." Taɓe baki ta yi tana cewa. "Ko ta mutu wa ya sa ni ko yunwa da wahala ta gama da ita, don wanan makahon mijinta ba wata sana'a da zai iya ba, sai sai idan bara za su dinga zuwa tare tana yi ma sa jagora. Ta yi maganar tana dariyar mugunta. Wani tsabar Mamy ya ji a zuciyarsa amma ba zai iya yi ma ta komai ba. "Alhaji." Ta kara sunan sa tana ɗauke hoton Ma'eesha da mahaifiyarta akan cinyarsa. Ajiye su gefe ta yi tana tabe baki. "Alhaji na ce ba wasu kuɗade ko dukiyar da suka rage a hannunka. Ka san yanzu girma ya kama ka ya kamata a ce kana hutawa Jamil ne yake kula da komai naka. Ko ba haka ba?" "Eh haka ne " Haka kawai ya tsinci kansa da bin umarnin ta. Duk abun da ta ce baya iya yi ma ta gardama. "Sauran wadanda ke hannunka ina so ka kawo su na bayar a kula da su ka huta ko saboda bawan jinin ka." Kai ya jinjina alamar gamsuwa da maganar ta. "Za ka bayar ?" Kai ya daga kafin ya ce . "Eh zan kawo." Murmushi ta yi tana cewa. "Bari na kawo ma ka coffee din ka ko?" Ta faɗa tana murmushi ta nufi hanyar fita tana cewa. "Ina zuwa ka jira ni yanzu." Ta fita tana murmushin cin nasara a ranta. Duk da ita kamata yanzu ta rasa meke ma ta daɗi a duniyar nan, ko barci cikin natsuwa ba ta iya wa. _Sidra_ Umma don Allah kada ki bari Abba ya yi ma ni auren dole ba zan iya zama ba Wallahi. Umma kauye fa ya ce zai aurar da ni, Umma ta ya zan iya rayuwar ƙauye ko na wuni ɗaya ba zan iya ba duk kyawu na da karatuna har matakin digiri a ce wai za'a kai ni ƙauye a bayar da aurena sadaka ga duk wanda aka ci karo da shi. !" Tana cikin wanan halin ta zube ƙasa sumammiya. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *SADAUKARWA GA* AMMEY LAYLERH *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣1️⃣ Umma don Allah kada ki bari Abba ya aura da ni auren dole ba zan iya zama ba wallahi. Umma ƙauye fa ya ce sai aurar da ni, Umma ta ya zan iya rayuwar ƙauye, ko na wuni daya ba zan iya ba. Duk kyawu na da karatuna har matakin digiri a ce wai za'a kai ni ƙauye a bayar da aurena sadaka ga duk wanda aka ci karo da shi!" Tana cikin wanan halin ta zube ƙasa sumammiya. Cikin tashin hankali Umma ta yi ihu tana kiran sunan ta, wanda hakan ya janyo hankulan su Ammi da yaranta suka shigo falon da hanzari. Ganin abun da ke faruwa ya sa suka fahimci dalilin ihun Umma. Gwaggo Laraba ce ta ɗauko robar ruwa a fridge ta yayyafawa Sidra. Wanda nan take ta ja ajiyar zuciya mai karfi. Sannan ta Fashe da matsanancin kuka. "Kukan me kike yi ai baki ga komai ba akan abun da kika aikata ." "Cewar Gwaggo Maimaina tana mata wani banzan kallo. Umma dai ba ta ce komai ba ta kama hannunta ta yi suka nufi bedroom ɗin ta. Suna dab da shiga ciki suka tsaya cak ba wanda ya ji ƙara ko fa taku daya. "Ba na buƙatar ta a tare da mu. Domin ganinta na ba na son ba yawaita kallon ta . Ɗin haka ta tattara kayanta ta bar part ɗin nan, ta koma ɓangaren baƙi da zama." Cikin takaici Umma ta ce . "Haba Alhaji ai hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar. "Ni kam tuni zan yanke hannuna na yar idan dai ya ruɓe, don idan ban yanke na yar ba tuni zai fara cin sassan jikina!" Yana gama faɗar haka ya juya ya nufi ɗakinsa. Umma ta saki Sidra ta bi bayan Abba a ɗakinsa. Yana tsaye ya juya wa ƙofar baya. Za ta yi magana ta ji muryarsa ya ce. "Dama ba abun da kike so kenan kullum kike roƙon na dawo da ita gida ba, to ta dawo me ya rage kuma?" Za ta yi magana ta ji ya ce . "Bissalam." Ta fita daga ɗakin ba tare da ta sake cewa komai ba, don ta fi kowa sanin halin mijin nata. Don haka ta bashi lokaci kafin ya huce don ta ga ɓacin ran da ke kan fuskarsa. _Makaho_ Wayarsa ta aiki ya fito da ita daga cikin jakarsa, lokacin Ma'eesha ta tafi gidan Mallam Liman kai wa Baba abinci. Waya yake yi da ogan sannan wajen aiki, nan take sanar wa headquarter din su yana kokarin kama daya daga cikin yaran Alhaji Daula. Fatan nasara ya yi ma sa daidai lokacin da ya ji sallamar Ma'eesha tana shigowa gidan . Da sauri ya katse kiran wayar ya kashe wayar ya sa a aljihun wandonsa. Sannan ya amsa sallamar da Ma'eesha ke yi. "Har kin dawo?" "Eh, ina kai ma ta na dawo saboda na bar mijina shi kaɗai. Kuna burina ko wane lokaci na kasance a kusa da kai, har ga Allah ni kan ji dadi idan na ganni a kusa da kai, a duk lokacin da ka fita daga cikin gidan nan sai na ji gidan ba daɗi, gidan ya yi ma ni duhu har sai ka dawo sanan zan ga haske da annuri a cikin gidan nan, kai ne duniyata idan na rasa ka ƙiyama ta ta tsaya." Ta yi maganar cikin rauni da damuwa. Ba abun da take tunawa kamar rayuwar da ta yi a baya tare da iyayen ta da suka rene ta cikin so da ƙauna. Ta kuma tuna yadda Mamy ta shigo rayuwar su ta ruguza ma su farin ciki. Hawaye ne kawai suke rige-rigen saukowa daga idanunta . Shiru Makahon ya yi yana karantar yanayin ta da damuwa da take ciki. Kafin ya mike tsaye da nufin fita sai ya tsaya ya kalle ta cikin wani irin murya ya ce. "Hakurin da kike ba a banza ba ne, ko wanne hawaye da kike zubarwa yana da daraja a wajen Ubangiji. Kowane numfashin da kike shakar juriya da jurewa, yana karuwa da lada. Wata rana za ki dawo ki kalli baya ki ga irin wahalhalun da kika sha, sai ki yi murmushi cikin hawaye kina cewa. "Lallai Allah bai taba barina ba." "Bar wa lokaci, domin lokaci magani ne. Kullum ki kasance da kyakkyawan zato ga Allah. Akwai tarin farin ciki da aka adana miki, sai dai yana buƙatar juriya da hakuri. Kada ki daina addu’a. Kada ki daina fatan alheri. Kada ki daina sadaukarwa. Hakkin ki ne ki ji daɗi, kuma UbangijinKi yana ganinki, zai baki alheri fiye da duk abinda kike zato. Ki ci gaba da hakuri, domin a ƙarshen dare haske yana zuwa. Hakurin ki zai zama hasken gobe in shaa Allahu." Kalaman sa sun yi ma ta daɗi sosai ba kadan ba, wanda har ba ta san lokacin da ta rungume shi ba tana ajiyer zuciya. Wanann ne karo na farko a rayuwarsa da mace ta rungume shi bai taba ta da jikinsa ba. Domin Ita kanta Ma'eesha da ba don halin damuwar ba da za ta tuna da zaran ta rungume shi ko ta haɗa jiki da shi take zai raba ta da jikinsa. Amma wanan karon ya kasa raba ta da jikinsa, sai ma rarrashinta yake yi ta hanyar bubbuga bayanta alamar rarrashi . Ita kanta ta san cewa wanan me karo na farko da ya bar ta har ta rabi jikinsa. Tsawon mintuna goma suna a haka kafin ya zame ta daga jikinsa ya ha hannunta har kan katifa ya ce ta kwanta. Ba musu ta kwanta kamar yadda ya buƙata sannan ya ce ta huta zai fita ya dawo. Jinjina kai kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba har ya fita tana kallonsa. Fitar sa ba jimawa sai ga Nasreen ta yi sallama ta shigo gidan . Tashi daga kwancen da take ta yi kafin ta ce da Nasreen ta shigo. Shiga Nasreen ta yi tana cewa . "Ina Makahon mijin naki yake?" " Banza ta yi da ita kamar ba za ta ce komai ba kafin ta ce. "Ba sunan sa Makaho ba sunan sa Khalifa ki san me za ki faɗa game da mijina a gabana." "Allah ko me miji, na ga ai makaho ne meye aibun da na faɗa ." Tashi ki fita kafin na yi ma ki abun da ran kowa zai ɓaci." "Haba ƙawata ki yi haquri don Allah na daina." Ma'eesha ba ta ce ma ta komai ba ta share ta. "Na zo ne dama ina neman shawarar ki, kin san ba na da abokiyar shawara sai ke." "Ina jin ki." " Ta faɗa tana kallon ta ba yabo ba fallasa. "Wannan saurayina da nake ba ki labari ya matsa akan zai fito mu yi aure, ni kuma ban gama cika burina ba ballantana na yi aure yanzu ke ma kin sani, kuma ina tsoron na rasa shi yanzu ya zan yi? Don har yanzu ban kai matakin da nake burin kai wa ba kafin na yi aure . Murmushi Ma'eesha ta yi kafin ta ce "Ko da kina da burin zama hamshaƙiyar ƴar kasuwa ko babbar ma'aikaciya, idan kin samu mijin aure kina da ƙananan sheka ki yi aurenki. Aure shi ne babban security ga mace, musamman wadda take da burika na gina kai. Idan kika yi aure, rayuwarki ta ɗauki saiti, za ki iya kaiwa duk matakin da kike so cikin nufin Allah. Mun ga dubban manyan mata, waɗanda duka sai bayan aure suka samu ɗaukaka. Don haka aure baya daƙile ɗaukaka, ko kashe mafarkai. Amma idan kika bar batun aure, kika mayar da hankali wajen gina kanki, to fa auren zai miki wahala. Ba wai ina nufin wahalar samun miji ba, duk da ita ma akwai ta sosai gare su. Babbar matsalar ita ce idan mace ta samu ɗaukaka kafin aure, aure yana mata wahala. Domin ta saba da rayuwar jin daɗi da sakewa, wataƙila ma ta kai matsayin da take umarni da hani, zai wahala ta sunkuyar da kai ta yi wa miji ɗa'a. Sa'an nan fa shi aure dole sai da ɗa'a, idan aka rasa ta, ko bai rushe ba, ba zai daɗi ba ita kanta ba za ta ji daɗinsa ba. Amma idan ta saba da biyayyar aure tun da ƙuruciya, zai wahala ɗaukaka ta canja ta. Sai dai wani dalilin daban. Idan na saurari ƙorafin manyan mata waɗanda ba su aure ba, ko ba su yi aure da wuri ba kan zamantakewar aure, ina gane suna da matsala, amma su kansu ba su fahimci mecece matsala tasu ba. Nisawa ta yi kafin ta cigaba da cewa. "Na taɓa misalta rayuwar aure da shiga aikin soja: Aikin soja, da ƙuruciya ake shiga, kamar tsakanin 18-25, a wannan shekarun mutum zai iya jure wahalar da ke cikinsa, idan ya saba to shi kenan, zai iya tsufa a ciki. Amma wanda ya girma, ya kai kamar 35-40, ba zai iya ba.. Ba wai rashin kuzari ba, tunaninsa ne ya girma, ba zai iya jurewa ba. To kamar haka aure yake. Allah ya datar da mu." "Amin ya Allah." Nasreen ta amsa cikin sanyin jiki tana auna maganar ƙawarta a mizanin hankali. Tabbas maganar Ma'eesha abun dubawa ne, sai dai tana bukatar yin nazari akai. Don haka ta yi ma ta sallama ba tare da ta sake cewa komai ba ta bar gidan . Driving take yi hankalin ta na kan tunanin kalaman Ma'eesha. _Makaho_ Kamar yadda ya tsara yau ne yake shirin kama ɗaya daga cikin yaran Daula. Don haka bayan ya yi wani bincike akan su ya san shige da ficen yaran da da komai ne ya sa bayan ta fito daga gida ya tsaya yana jiran fitowar abun harin sa. Dare ya rufe gari ya yi duhu sai hasken fitilu da suke haska titi da rauni. Makaho na tsaye bayan wata mota idanunsa na kan mutumin da ke tafiya cikin sauri, wato mutumin Daula daya daga cikin yaran sa. Mutumin ya bi wata karamar hanya, Makaho ya bi shi a hankali ƙafarsa ba sa amo don na wanda ke jin sautin ƙafararsa. Kwatsam sai mutunin nan ya tsaya cak. "Na san kana bi na a baya. *Jalaluddeen Kabir arziki *senior intelligence officer*" Zuciyar makaho ta buga da ƙarfi. Kafin ya ankara ya ji ƙarar mota ta bayansa an kewaye shi. Wani ya fito daga inuwa . "Ka yi kuskure Mallam mai gyaran takalmi.... *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣2️⃣ Zuciyar Makaho ta buga da ƙarfi, kafin ya ankara ya ji ƙarar mota a bayansa an kewaye shi. Wani ya fito daga daga inuwa. "Ka yi kuskure Mallam mai gyaran takalmi. A nan Jalaluddeen ya gane shirin sa yana shirin tonuwa. "A baya mun saka yaran mu sun je sun ɗaukoka a yayin da kake komawa gida bayan ka tashi wajan gyaran takamin ka n basaja. Sai dai cikin rashin sa'a jami'an ku na DSS suka bi yaran mu suka ceci rayuwarka. Amma duk da haka kake sake saka kanka a hatsari ko? To bari ka ji Alhaji Alhaji Daula ba zai kamu ma ka ba, hana da ɗaurin gidi har a wajen na sama da kai a ƙasar nan. Ya km Take sai duhu ya mamaye wajen na wasu sakanni wanda a daidai wannan lokacin Jalaluddeen ya shammmace su, tsalle ɗaya ya yi ya haura katanga tare da faɗawa ta baya. Haske ne ya dawo wanda a lokacin suka ga babu Jalaluddeen a tsakiyar su. Cike da mamaki suke ta waige-waige suna neman sa amma babu ko mai kama da shi. "Ina ya shiga ne?" Suka rabu suna neman sa, gabaɗaya suka zagaye yankin amma ba su gan shi ba. Shi kuma yana barin wajen hanyar gida ya koma, yana tunanin ya hakan ta faru. Alama ya nuna cewa a kwai mai yi ma sa zagon ƙasa a cikin jami'an su na DSS. Domin su kaɗai ya sanar da su inda zai je, to ya aka yi yaran Daula suka san da zuwan sa, dole akwai munafiki a cikin su. Amma ya gode Allah da ya tsira da rayuwar sa. Amma tabbas zai gano waye ya shirya ma sa wannan abun. _Fahad_ Wayar Nadra ya kira don ya ji muryarta, don tunanin ta kawai yake yi, don haka ya bar abun da yake yi ya nufi hanyar gida . Horn ya yi a ƙofar gidan nasa, yayin da maigadi ya fito ya wangale ma sa gate ɗin gidan . Bayan ya yi parking motar ne ya fito daga cikin motar yayin da maigadi ya ƙaraso wajen uban gidan nasa ya gaishe shi. Ya amsa ma sa yana nufar cikin gidan. Tura kofar ya yi ya yi ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama . Ba ta falon ƙasa sai ya haura sama. A tunanisa zai ga ta jera abinci a dinning table a daidai wannan lokaci. Amma sai ya ga ba ta jera komai b, kuma ba alamar ta yi girki ma. Bedroom din ta ya nufa kai tsaye, can ya hango ta ƙasan gado ta kudundune kanta a saman gadon. Da sauri ya karasa sanan gadon ya haura akai, sannan ya janyo ta jikinsa sai ajiyar zuciya take saukewa tana barci. "Subhanallah!" Ya faɗa yana taɓa jikinta. ,"Nadfah lafiya me ke damun ki?" Kuka ta saka ma sa wanda ya kara tayar ma sa da hankali. Rungume ta yi yana rarrashinta . E ya same ki?" ",Kai ne ka kira Abba ka faɗa ma sa Aunty Sidra na ganin nan?" Shiru yanayi yana kallon ta wato akan Sidra ta tafi shi ne take kuka. "Ba ni na faɗa ma ta ba, dai dai maybe Aunty Rahama ce, din ta kira nu da safe tana ta faɗa akan tashin dacewar hakan . Kuma na fahimci gaskiya take faɗa gara ta tafi za mu fi sakewa a cikin gidanmu. "Ta tafi tana jin haushi na sosai ta tafi ina son na je na fahimtar da ita." Da sauri ya kalle ta kafin ya ce . "Yaushe za ki je?" "Yau nake so na na je saboda ba na son ta kwana da ni a zuciyarta." Wani kallo irin na baki san net kike yi ba ya yi ma ta, kafin ya ce . "Zan ya tunani akai?⁷ Sake shigewa jikinsa ta yi tana roƙonsa, wanda wanda hakan ya haifar ma sa da kasala sosai a jikinsa. Da ƙyar ya yi magana ya ce.. "Too...too....too shi...shi...kanan zan kai ki." Ɗago da kanta dake sanan ƙirjinsa tana kallonsa jin yadda yake magana kamar wani ɗan koyon magana. Idanunsa ta ga sun kaɗa sun canza launi. "Ba ka da lafiya ne?" "Kai kawai ya jinjina ma ta alamar eh." Saurin tashi za ta yi daga jikinsa amma sai ya rike ta yana sake matse ta da jikinsa. "Akwai maganin da za ka sha?" Kai ya jinjina ma ta alamar eh. "Ina maganin yake na ɗauko ma ka?" Ya nuna ta alamar iya de maganin sa. "Ni kuma?" Ta faɗa yana nuna kanta da hannunta . "Ta ya zan zama magani? Yaya Fahad wasa kake yi ka tashi mu tafi magrib na gabatowa sai mu yi sallah a can." "In dai ban samu maganin ciwo na ba ko ɗakin nan ba zan iya fita ba ballanta na kai ki wajan wata kuma." "To ya kake so ayi?" "Ke ce maganin ciwo na, jikinki maganin yake ?" " Kallonsa ta yi ta gane jarabar sa ne ya motsa saboda ta rungume shi shi kenan ya shiga wanan halin. "To ka ga ai magrib ya gabato kuma kai idan ka fara ba ka gamawa da wuri za mu...." Haɗa bakinsa da nata ya yi yana aika ma ta saƙon sa kai wuyar karantawa. Ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta bashi hadin kai." Don haka ko da ya cire manta kayan jikinta ba ta yi yunkurin ma sa gardama ba, ta bar shi ya yi bidirinsa yana sarrafa jikinta yadda ransa yake so. Kusan mintuna ashirin ya yi yana wasa da jikinta, don ya fara rikice ma ta, kafin ya dauki hanyar shigarta yana karanto addu'ar saduwa da iyali. Duk sanda ya shige ta sai ya ji ta kamar sabuwa take sake zama ma sa. Har aka kira sallar magrib bai ma sani ba don yana can ya lula wata duniyar da ya lula, ita ce ma take sanar da shi lokacin sallah ya wuce fa ana sallar magrib amma ina bai ma san tana faɗa ba ya fice daga hayyacinsa. Sai da aka kira sallar isha'i sannan ya samu natsuwa ya mirgina gefe yana mayar da numfashi. Ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta janyo rigarta ta saka ta shiga bathroom. Cikin sauri ta tsarkake jikinta sannan ta fito ɗaure da babban towel a jikinta tana takaicin yadda sallar magrib ya wuce ba ta yi shi akan lokaci ba. Ko da ta fito ba ta gan shi a dakin ba, don haka ta shirya cikin rigar abaya ta saka hijabi ta fara gabatar da sallah. Shi ma a nasa bangaren ɗakinsa ya wuce ya tsarkake jikinsa ya yi wanka, sannan ya ɗauro alwala ya fito. Kasancewar ko masallaci an isar da sallar isha'i ya sa ya yi sallarsa a ɗakinsa bai fita ba. Bayan ya idar ne ya ya ɗauki key din motarsa da niyyar zuwa ya yi ma su take away, a bakin ƙofar ya hadu da ita tana kokarin shigowa ɗakinsa. Sanye da hijabi da wayarta a hannunta. Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ba tare da ta ce ma sa komai . Hannunsa daya ya sa ya ɗago da haɓar fuskarta suka hada idanu. Kashe ma ta ido ɗaya ya yi ta dauke idanun ta da sauri cikin jin kunya. "Wai wane kunya kuma ya rage a tsakanin mu ne iya zumata?" "Ni dai mu tafi." "Mu tafi ina?" Kwaɓe fuska ta yi kamar za ta yi kuka ganin yana son ya raina ma ta hankali. "Kai fa ka ce za ka kai ni idan..." Sai ya kasa karasa maganar tana kallon kasa. "Na ce zan kai ki idan aka yi me?" "Na manta ɗan tuna mun abun da ya faru, yaushe na ce za. Kai ki kuma idan aka yi me? Ba abun da na tuna mu je mu yi take away mu dawo gida mu huta. Kuka ta saka ma sa za ta koma ɗakinta, ya yi saurin riko hannunta yana cewa. "Am sorry na tuna abun da ya faru mu je na kai ki." Ya yi maganar yana dariya, ita ma dariyar ta yi duk da hawayen da ke idanunta. "Ki daina ɓata ranki domin ba na son ɓacin ranki ballanta zubar hawayenki sarauniya ta." "Ba na son ki yi wahala bari na ɗauke ki." Kafin ta yi magana ya dauke ta ya fara tafiya da ita, a hankali yake taka matattakalar benen har ya sauka zuwa falon ƙasa. Suna fita a jarabar gidan ta fara kokarin zamewa tana so ya ajiye ta sakamakon wasu ma'aikatan gidan da suke kallon su . Bai na ta damar ba har sai da ya kai parking space ya ce wa direbansa ya zo ya bude ma su bayan motar . Ɓoye fuskarta ta yi a ƙirjinsa saboda kunya. Har direban ya ƙaraso wajen da sauri ya bude bayan motar. Ya saka ta ciki shi ma ya shiga ya zauna gefenta. Direban ya shiga yi yi wa motar key suka bar gidan. _Makaho_ Bayan ya bar su mutanen Daula ya bar layin daidai yana kokarin fita daga wata bayan ya ji Harbin bindiga a damtsen hannunsa. "Ash!" Ya faɗa bayan Harbin ya shige shi. Sake yin harbi aka yi a karo na biyu, cikin zafin nama ya yi yi ƙasa ya tsallake Harbin. A guje ya bar wajen yana gudu ana bin sa da harbi har ya samu ya tserewa mai Harbin nasa. Yana gudu yana rike da hannunsa dake fitar da jini. Har ya isa gida inda ya tura ƙofar a hankali ya shiga ciki. Ɗaki ya shiga in da ya tarar da Ma'eesha na barci kamar yadda ta saba. Wani ƙaramin akwati ya ciro daga cikin jakar kayansa. Fita ya yi ya yana rike da hannuna ya ajiye akwatin a banɗaki. Sanann ya dawo ya ɗauki bokiti dake cike da ruwa ya kai banɗaki. Wani dogon wando ya ɗauka a cikin kayansa da niyyar idan ya yi wanka su zai saka. Karamin akwatin nan ya buɗe ya ciro wani abu kamar scissors ya sa a wajen Harbin, ya ciro bullet din bindigar, sai da ya yi ƴar ƙara na azaba wajan cire bullet din bindigar. Ya yi wanke wajen ya sa magani jinin ya tsaya ya rufe wajan sanan ya yi wanka. Yana fitowa ya ga Ma'eesha a tsaye a tsakar gidan tana kallonsa da mamaki. Pretending ya yi a matsayin sa na makaho wanda baya gani. Da lalube ya ajiye bokitim ya saka rigar sa ciki ya wuce ta a matsayin bai san da mutum a wajen ba. "Mijina lafiya kuwa?" Ta yi maganar tana kallon gefe ɗaya, saboda kallo ɗaya ta yi ma sa ta kawar da kanta gefe saboda ba shi da riga sai dogon wando sannan ga murɗaɗɗen surar jikinsa irin na jaruman maza bayyane a jikinsa wanda ke firgita ta. "Ma'eesha kece kika fito a cikin daren nan?" "Eh na farka ban gan ka ba ne ya sa na fito na duba ka." "Ki je ki kwanta wanka na fito yi." "Okay, Amma wankan a daren nan?" "Eh zafi nake ji ne na kasa barci. Ke ma zafin kike ji ne?" "A'a mafarki na yi akan ka wanda na ji tsoro na farka." "Ina lafiya ba abun da ya same ni je ki kwanta ki huta ina shigowa yanzu." Ya yi maganar yana dibar ruwa ya zuba a kayan da ya cire, zai wanke. "Ki shiga ciki ma na." Ba musu ta bi umarnin sa ta shiga ciki. Sai da ya wanke kayansa ya shanya sanan ya shiga cikin dakin . Tana zaune a kan katifar tana kallon ya shigo ta sunkuyar da kai kasa. Sai dai ta lura yanayin da yake ciki ya sauya. Riga ya saka ya fita ya ɗauro alwala ya zo ya fara sallar nafila kafin a yi sallar asuba. Sai da aka kira sallar asuba sanan ya tashi ya nufi masallaci. Ana idar da sallah ya fito daga masallaci ya dauki wsyarsa a aljihu ya kira lambar Taj. Bugu biyu ya ɗaga tare da gaida shi. Umarnin ya zo ya ɗauke shi ya ba shi. Daga nan ya fara tafiya da sandarsata jagora . A bayan layin suka haɗu ya dauke shi zuwa wani gidan. Bayan ya yi horn maigadi ya wangale ma su gate Taj ya ja motar zuwa ciki . Yana parking ya fito da sauri ya bude wa ubangidansa bayan motar ya fito ba tare da sanar jagoransa ba. Kai tsaye wani karamin ɗaki ya shiga in da aka manna allo da wasu rubuce-rubuce a kai . Kallon Taj ya yi kafin ya ce . "Akwai munafuki a cikin mutane mu, jiya an na sanar da cewa zan bibiyu mutanen Daula don na san shirin su, bayan na bibiye su sai suka shirya ma farmaka ta. Abun tambaya waye ya sanar da su shirina.? Sanan bayan na kuɓuta daga hannunsu a hanya an kai ma ni hari har an samu nasarar harbina kuma ba mutanen Daula ba ne cikin jam'an mu ne waye da wanan aikin?" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣3️⃣ Akwai munafukai a cikin mutanen mu, jiya na sanar da cewa zan bibiyu mutanen Daula don na san shirin su, bayan na bibiye su suka shirya farmaka ta. Abun tambaya waye ya sanar da su shirina? Sannan bayan na kuɓuta daga hannunsu a an kai ma ni hari, sanann an samu nasarar harbina kuma ba mutanen Daula ba ne na waye da wannan aikin?" Yaja hoton kan mutum ya zagaye shi sannan ya saka alamar tambaya a wajen kan. "Dole na gano ko waye domin farautar rayuwa ta ake yi, kuma ba wanan ne karo na farko da aka farmake ni ba. Sai dai na baya na yi tunanin mutanen Daula ne. Domin na dawo kenan daga wajan gyaran takalmi da yammaci, kan hanyata ta komawa gida ne suka farmake ni suka saka ni a mota. Sai dai cikin ikon Allah lokacin jami'ana da zan ba wa wasu bayanai suna kusa sun hange ni suna tunanin yadda za su tinkare ni saboda ba su iso akan lokaci ba har na gaji da zaman jiran su na kama hanyar gida. Sai Allah ya sa akan idanun jami'an mu abun ya faru suka bi wadan can mutanen har suka kuɓutar da ni bisa umarnin oga. Sannan na gano Harbin da aka yi ma ni ba daga Daula ba ne bullet din bindigar ya fito ne daga weapon serial number DSS stock ." Jalaluddeen (Makaho) ya juya ga gefe a wani allon yana nazari yayin da Taj ya tsaya yana kallon sa na ƴan saknni kafin ya juya ya kalli allon dake manne a bangon ɗakin, alamar bayanai da hotuna ne ke yawo akai. Kamar ana sake gina abun da ya faru ne a baya. Shiru ya mamaye ɗakin. Makaho ya matse sandarsa a hannunsa , zuciyarsa na bugawa a hankali amma cikin karfi. Ya ji wani abu a cikin kansa yana faɗa ma sa cewa. Abun nan bai tsaya ga kwanton ɓauna kawai ba." "Ka ce an sanar da su?" Taj ya maimaita tambayar Jalaluddeen a hankali kamar yana auna kalmomin. Jalaluddeen ya haura tsayuwar sa. "Eh duk abun da na tura ma su sun san shi kafin lokaci." Taj ya yi shiru na dan lokaci sanan ya ja numfashi mai nauyi. "Wannan ba al'ada ba ce." Jalaluddeen ya matso kusa da teburin da ke tsakiyar ɗakin. Yana jin kowane motsin iska. "Na riga na fara zargin akwai mutum a cikin tsarin mu." Jalaluddeen ya faɗa cikin murya mai sanyi. "Amma yanzu na fahimci ba zargi ba ne gaskiya ne." Taj bai amsa nan take ba. Sai ya ɗan juyo da kansa amma idanunsa bai kalli Jalaluddeen kai tsaye ba ya ce . "Waye kake zargi?" Tambayar ta yi nauyi fiye da yadda aka furta ta. "Duk wanda ya san motsi na " Wannan amsa ta Jalaluddeen ta sa dakin ya kara yin shuru. A waje iska ke kaɗawa tana bugun window dake ɗakin kamar tana kokarin fadar wani sirri. Daidaita lokacin wayar Taj ta yi ƙara, sai ya duba. Sakon ya fito ne daga wani lamba da ba'ayi seve ba. *Ya fara tambaya sosai, ku hanzarta kafin ta gano komai* Taj ya kalli sakon sannan ya rufe wayar da sauri. Jalaluddeen ya ɗan ɗago kansa. "Me ya faru?" Ya tambayi Taj. Shiru ne ya biyo baya kafin Taj ya ce. "Babu komai." Amma muryarsa ba ta yi daidai da kalmomin sa ba. Jalaluddeen ya ɗan matso gaba zuciyarsa ta fara nauyi. "Ka san wani abu?" Jalaluddeen ya tambaya a hankali. " Taj ya ɗago kai da sauri. "Me kake nufi?" Gajeren murmushi Jalaluddeen ya yi, irin murmushin da ba na daɗi ba. "Na koyi abu daya a wanan aikin." Sai kuma ya yi shiru bai sake magana ba. Shiru ne ya biyo baya kafin Jalaluddeen ya ce . "Za ka iya tafiya gobe za ku dake binciken." Taj ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa ya ji Muryar Jalaluddeen na cewa. ",Duk wanda ya fi sani na a nan shi zan fara zargi." Taj ya dakata da tafiyar da yake yi, kuma bai juyo ba. "Ka fara makara." Daga haka ya fita kofar ga rufe . Taj ya tsaya shi kadai a dakin yana tunanin yadda abubuwa suka sauya ma sa. A hankali ya ce. "Ba Taj ba ne... To waye?" Jalaluddeen yana tsaye a tsakiyar ɗakin sandarsa a hannunsa, tana rawa kadan . Kalmomin Taj ke yi masa yawo a cikin kansa kamar yadda iska mara nutsuwa. "Ka fara makara." Wanann kalmar tafi yi ma sa nauyi. Ya ja wani dogon numfashi ya mayar da hankali sa kan sautin da ke kewaye da shi. Agogo na tick tick a bango iska na shigowa ta window, da nisan motoci a waje. Sai ya ji wani ƙaramin sauti, sai ya ji wani abu kamar an motsa takarda a hankali. Jalaluddeen (Makaho) ya tsaya cak baya ganin komai amma kununuwan sa sun fi komai aiki. A hankali ya juya kansa zuwa teburin da Taj ya bar shi. Babu kowa a wurin . Amma jin sa yana ce ma sa, akwai wani abu da bai kamata ya kasance a wurin ba. Ya taka a hankali yana bin tebur ɗin da hannu. Sai ya taɓa wa wani abu, Fili ne wani karamin na'ura mai sanyi a saman tebur. Jalaluddeen ya tsaya . "Wace irin waya ce wanan ,?" Ya yi tambayar duk da babu mai ba shi amsa. Ya sa hannu ya ɗauka . " Na'urar ba ta da kara amma ta ɗan yi zafi kaɗan alamar ta daɗe tana aiki. Nan take ya fahimci an saka ma sa na'urar saurare a in da yake bincike . Zuciyarsa ta buga da ƙarfi . "Wato hakan na nufin duk abun da nake yi ana saurarena." Ya jefar da na'urar ƙasa ya taka ta da ƙarfi wanda sai da na'urar ta fashe. Daga wajen ya ji karar tashin Mota ta bar wajen a guje. Jalaluddeen ya juya da sauri amma ba su nan. "Sun riga sun ji ni." A lokaci guda wsyarsa ta yi ƙara, wanan karon ba Taj ba ne, wace lamba ce da bai san me ita ba. Ya ɗaga kiran wayar ba tare da ya yi magana ba. Jin shiru ya sa shi nufar hanyar fita don ya fice . _Fahad_ Kofar gidan su Nadra horn ya yi maigadi ya wangale ma su gate suka shiga ciki. Parking space ya yi parking motar sannan ya fito, Fitowar sa ya yi daidai da bude labulen window da Sidra ta yi daga nan ta hangi Fahad yana buɗewa Nadra karfin motar ta fito. Sai da numfashinbta ya yi kamar zai zau dauke. Ganin wani kallo mai cike da shauƙin so da Fahad ke aika mata, ita ma sai murmushi take yi ma sa. Cikin takaici ta dunkule hannu ta daki bangon ɗakin wanda ya sa ta saki ƙara saboda zafin da ta ji. "Wallahi ba zan bari ku yi farin ciki ba sai na farraƙa ku. Ba yadda za'ayi ku yi farin ciki ku bar ni cikin bakin ciki wallahi ko sama da ƙasa za ta hade ba sai na raba ku da juna kuma alkawari na ne wannan." Tana faɗar haka ya saki labule ta koma ta hau gado ta kwanta. Knocking Nadra ta yi a kofar falon shiga babban falon gidan. . "Ammi dake kokarin zuwa bude kofar, tana budewa ta ga Nadra da Fahad a tsaye. Cike da farin ciki ta ce . "Ku ne a daren nan haka lafiya?" "Lafiya lau mun zo gaishe ku ne." "Bisimillah ki shiga ciki ma na. Suka shiga ciki suka gai da Ammi sanan Nadra ta nufi ɗakin Umma tana ƙwala na ta kira . Abba ne ya fito daga part ɗin sa yana ganin Fahad ya sa ya saki murmushi yana cewa . "Fahad kai ne a daren nan, ina fatan dai ba wata matsala ko?" "Babu komai Abba muna zaune lafiya." Nan ya gaida Abba cikin girmamawa sannan ya shida Umma da ta fito yanzu tare da Nasara. Ta marasa wajen Abba ta ce . "Abba." "Na'am ƴar Abba ya faɗa yana rike hannunta suka Zauna a tare. Sai ta yi saurin zama kasa. "Ina Aunty Sidra ce ban ga ta fito ba ko ba ta ji zuwa ga ba ne." Ta yi maganar tana nufar dakin su. "Ki duba tana dakin baƙi." Cewar Umma tana kalli. Nadra. "Me take yi dakin baƙi kuma ko tana da bako ne?" Ba wanda ya amsa ma ta ita kuma ta nufi ɗakin. Da sallama ta shiga sai ta hango ta kwance kan gado ta ya tana lulluɓe cikin bargo. Ƙarasawa ta yi kamar ta tayar da ita amma ta fasa cikin rashin jin dadi ta ce. "Allah sarki Aunty na so mu yi magana ta fahimta da ke ki fahimce ni ko za ki daina jin haushi na. Kuma ba ba ki da lafiya bai dace na tayar da ke ba. Ko ba haka ba na san idan kina barci ba ki son a tayar da ke. Zan tafi Allah ya huci zuciyarki ya kuma ba ki lafiya." Daga haka ta fice daga cikin ɗakin. Sidra na jin fitar ta ta tashi zaune tare da bin kofar da ta fita da harara. Ko da ta fita ta koma falo ta samu Ammi ta kawo wa Fahad tuwon aljanna da miyar ɗanyar kuɓewa sai ƙamshin man shanu miyar ke yi. "Ga girkin uwar gida ka ci na san kana son shi, Allah ya sa Amarya ba ta cika ma ka ciki ba." "Yauwa Ammi Allah ya bar ma na ke, kamar ko kin san ban yi girki na take away za mu siya dama.," Wani kallo Umma ta yi ma ta mai sannan ta ce. "Take away Nadra kika ce fa? Yaushe kika zama haka? Abinci da za ku ci ke da mijinki ya gagare ki ? Wanan ba tarbiyyar d na koyar da ke ba ne?" 'Oh Allah ta ya zan fahimtar da su ne? Xan ce ma su na kasa girki ne saboda damuwar Aunty Sidra ko xan ce na kasa girki ne dan saboda jarabar Yaya Fahad ?' Tana tsaka fa tunanin ne ta ji Muryar Fahad na cewa . "Ba haka ba ne, ni ne na ce ta huta yau kawai na yi ma na take away, akin na ma ta hawa ita kadai a gidan nan." "Wanan ba dalili ba ne Fahadz kada ka yi kokarin kare ta. Aikin da Nadra ta saba da shi a gidan nan ai bai kai aikin gidan ka yawa ba, kawai dai lalacin da ba ta da shi a baya ne take so yanzu ta koya " Cewar Ammi tana kallon Nasara. Umma za ta yi magana Abba ya ce. "Ku bar ta haka nan in sha Allah ba za ta sake ba." Kallon Nadra ya yi yana cewa . "Ƴar gidan Abba kada ki sake bari mijinki ya tafi siyen abinci gidan abinci bayan kina da ran ki da lafiyar ki ba tare da wani baban uzuri ba." "To Abba in sha Allah." Tashi Abba ya yi yana cewa "Zan ɗan fita kika kafin na dawo kun tafi, Allah ya ma ku albarka sai da safe." Daga haka ya fice suna ma sa sallama. Umma ta tashi ta ba su wuri su ci abinci. "Ammi ma ta ce ina zuwa ." Barin wajen ta yi Fahad yana kallon yadda Nadra ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka . "Kukan me za ki yi, daga magana kin daki baki kina fadar zance waye ya san ba ki yi girki ba? Ke kika faɗa da bakin ki." Ya yi maganar yana ƴar dariya. Sanann wanke hannu ya fara cin tuwon. "Ki yi hakuri mu ci kin ji Nadfah. Ko take away kike so na siya ma ki a hanya?" Kai ta girgiza alamar a'a. "Okay to kaza fa za ki ci?" "Ba zan ci ba." Ta saka hannu suka fara cin tuwon a tare. _Jalaluddeen_ Bayan ya fito daga ɓoyayyen gidansa yana tsaye a ƙofar gidan ya ɗan tsaya yana sauraren bugun zuciyarsa. Murmushi kadan ya yi yana kara matse sandarsa dake hannusa. kai tsaye hanyar gida ya koma. Don ya san zuwa yanzu Ma'eesha za ta iya ɗaga hankalin ta. Ya san da ya zo da wayarsa ta yake waya da ita da tuni ta kira shi. Yana tafiya maganar Taj kawai ke aunawa a ƙwakwalwarsa da kuma na'urar saurare da ya gani a ɗakin. "Ka fara makara" *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣4️⃣ Bayan ya fito daga ɓoyayyen gidansa yana tsaye a kofar gidan ya ɗan tsaya yana sauraren bugun zuciyarsa. Murmushi kaɗan ya yi yana kara matse sandarsa dake hannusa. Kai tsaye hanyar gida ya koma dan ya san zuwa yanzu Ma'eesha za ta iya ɗaga hankalin ta l. Ya san da ya zo da wayarsa ta yake waya da ita tuni ta kira shi. Yana tafiya maganar Taj kawai yake aunawa a ƙwakwalwarsa da kuma na'urar saurare da ya gani a ɗakin. "Ka fara makara.!" Mai keke nape ya tare ya sanar da shi unguwar da zai kai shi. Har bakin layin su ya kai shi sanan ya ce ya dakata a nan zai sauka. Yana sauka kenan sai ya tambaye shi kuɗin sa, ɗari biyar ya ce ma sa kuɗin sa. Take ya zare dubu daya a cikin aljihun wandonsa ya mika ma sa. Yana mika ma sa ya kama hanya, mai nape ya ciro ɗari biyar da niyyar ba shi canji amma sai ya ga ya fara tafiya. "Mallam ga canjin ka!" Alama ya yi masa da hannu alamar baya son canjin. "Ikon Allah ga mutum Makaho har da sandar jagoransa amma ya bar canji haka kamar wani mai kudi?" Ya ja kekensa ya bar wajan yana sake mamakin wanan makahon. Cikin nutsuwa yake tafiya har ya karasa kofar gidan. Ya sa hannu ya tura kofar fale-fale bakinsa dauke da sallama. Da sauri Ma'eesha ta fito daga ɗaki yana sakin ɓoyayyen ajiyar zuciya. "Wa'alaika salam warahmatullah." Ta amsa tana murmushi. "Sannu da dawowa Mijina." Ta kama hannunsa ta taimaka ma sa ya zauna a saman tabarma . Sai sannu take jera ma sa kamar mai ciwo. Tashi ta yi ta kawo masa breakfast,kunun gyada ce ta yi sai ƙosai da ta soya. Kasancewar yanzu ta daina yin abinci kala-kala ko akwai saboda canjin rayuwa da ta samu kanta a ciki. Sai da ya sha kunun gyaɗar da ƙosai ya ƙoshi kuma ya ji dadin kunun sosai ba kadan ba. Bayan ta kwashe kayan tta dawo ta zauna gefen sa . "Mijina." "Na'am matata." "Ina fatan dai lafiya da na ga an isar da sallar ina ka dawo ba har gari ya waye lokacin da ka saba dawowa ya yi ba ka dawo ba, haƙiƙa hankali na ya tashi a lokacin musamman da na kira wayar ka na ji ga a kashe. Hankali na ta sake tashi kada a yi amfani da makantar ka a cutar da kai, ka san mutane idan suka ga mutum Makaho ne ba wuya za'a cuce shi ." "Kar ki damu ba abin da zai same ni in sha Allah. Na gode da nuna ƙauna da kulawa. Allah ya bar mu tare." "Amin ya rabbil izzati." _Fahad_ Bayan sun kammala cin abinci ne Nadra ta kwashe kayan ta je kitchen ta wanke su. Sannan ta shiga ta yi wa su Umma da Ammi sallama . Har ta kai bakin ƙofar fita daga dakin Ammi dai ta kira ta. Dawowa ta yi ta ce . "Ga ni Ammi." Wani leda ta miƙa ma ta tana cewa. "Karbi wanan kayan mata ne na gyaran zamantakewar aure. Ina so ki sha su. Wasu haka nan za ki sha ki yar da robar, wasu da madara za ki sha su . Duka dai an rubuta su za ki gani sai ki dinga amfani da su. "Kai Ammi dan Allah ki bar su ko wadanda Gwaggo Laraba ta ba ni ban gama sha ba, sanan kin kara ma ni wasu." "Eh nata daban nawa daban don haka karbi ki je ki yi ta sha ki zama ƴar gatan mijinta." Ba musu ta karba ta rike zuwa falo Ammi na bin ta a bayan ta suka tarar da Umma na yi ma sa sallama. Har wajen motat Ammi ta raka su in da Fahad ya ba ta kudi ma su yawa. Cike da murna ta koma cikin gidan bayan ta ga wucewar motarsu daga cikin gidan. _Sidra_ Bayan fitar Nadra sai ta tashi daga likimon da ta yi kamar mai barci . Wayarta ta ɗauka tana kuka ta sanar wa Sady babu abun da ya faru. Sady baby ta yi farin ciki kuma ta yi bakin ciki. Farinciki shi ne jin Nam da wata ɗaya za'a aurar da Sidra kuma ga ƙauyensu, bakinciki kuma shi ne jin yadda zaman Fahad da Nadra ya yi daidai suke zaman aure cikin soyayya da juna. "Daina kuka ƙawata, don Allah ya isa haka ki kwantar da hankalinki akwai wani Mallami da zan kai ki wajen sa aikinsa yana ci sosai, idan muka je kika sanar da shi matsalar ki to ki ɗauka bukatar ki ta biya kawai. Aikinsa kamar yankan wuƙa ne." "Ni fa Wallahi ban yarda da bokayen nan ba maƙaryata ne, karya suke yi mafi yawan maganar su." "Ke ba boka ba ne shi fa Mallam ne, ki kwantar da hankalinki bukatar ki ta mallakar Fahad za ta biya ki sa wannan a ranki." "Kai gaskiya hankali na bai kwanta da zuwa wajen boka ba Wallahi." "Wallahi ba boka ba ne gobe ki zo mu je za ki tabbatar da abun da nake faɗa ma ki ." ",Shi kenan zan zo duk da ban san yadda zan fito daga gidan ba. Abba ya tsaurara ma ni, idan ba damuwa ke ki je a madadina ma na." "In ji waye ya faɗa ma ki cewa zan iya zuwa a madadin ki, ai ke za ki je da kanki ya ganki, idan ya so daga baya zan dinga zuwa ina karɓo ma ki magani ko ba ki je ba. Yanzu ki yi dabara ki bar gidan nan gobe in sha Allah." Shiru ta yi tare da nazari kafin ta ce. "Zan duba yiwuwar hakan." Sallama suka yi ta katse kiran wayar tana tunanin hanyar da za ta bar gidan nan. *Bayan kwana biyu* _Nasreen_ Tana zaune ita da saurayin ta a wani tsadadden gidan cin abinci. Suna tattaunawa kan maganar auren su. Kamar an ce ta daga kai ta kalli kofar shigowa. Jalaluddeen ta gani tare da wani mutum wanda zai iya haifar ta. Dukkansu sanye suke cikin shigan Suit baƙaƙe. Sun zo sun zauna a wasu kujeru biyu da ke gefe ɗaya. Shi mutumin yana sanye da bakin glass a idanunsa yayin da Jalaluddeen bai saka glass ba. Kallon saurayin nata ta yi a dan firgice ta ce. "Sai anjima za mu yi waya ina sauri zan je wani wajen." Kafin ya yi magana har ta bar wajen ta fita da sauri. Mamaki ya kama shi amm ba wanda zai tambaya, don haka ya biya kudin abincin ya fice. Dama daga ita har shi kowa da motarsa ya zo suka hadu a wajan . Gudu Nasreen ke yi kamar za ta tashi sama, burin ta kwai ta isa gidan Ma'eesha. Tafiyar da za ta dauke ta Mintuna ashirin da biyar ta isa a mintuna goma sha biyar. Ko sallama ba ta yi ba ta shiga ƙwalawa Ma'eesha kira . "Ƙawata!" Da sauri Ma'eesha ta fito waje tana tambayar Nasreen lafiya. Ba ta tsaya bayani ba illa iyaka ta janyo hannun Ma'eesha tana cewa. "Zo mu je da sauri ba lokaci." Ganin yadda take jan hannun ta ne ya saka ta fisge hannunta tana cewa. "Anya kanki daya kuwa ?" "Idan muka je za ki gani." "Ba inda zan je ba tare da izinin mijina ba." "To wajan shi mijin ne za mu je." "Wai me ke damunki ne haka?" "Yau zan nuna ma ki asalin waye mijinki, za ki yarda cewa mutumin da na kawo ma ki photo na ce shi ne mijin ki amma kika ƙaryata ni to yau za ki tabbatar wanan shi ne mijin ki. Ba Lokaci mu je." _Mamy_ Zuwa yanzu ta rame ta fige ta fita a hayyacin ta sosai ba kadan ba. Don ko barcin kirki ba ta iya yi. Da zaran ta kwanta daddare to za ta kasa barci ne sai mafarkai barkatai da take yi a duk lokacin da barci ya yi nasarar ɗaukarta. Gefe guda kuma ga matsalar dake tsakanin ta da Laila. Din kullum sake rasa abubuwa suke yi a gidan. Ga shi ta rasa ta ina matsalar take . Ba ta zargin ƴaƴanta amma sai dai masu aikin gidan su take zargi. Ranar da ta dinga bala'i akan sai an fitar da kayan da aka ɗaukar ma ta . Haka ta dinga binciken ɗakin masu aiki amma ba ta samu komai ba. Abubuwa sun yi ma ta zafi ga shi bokan da yake ma ta aiki ya nemi maƙudan kudade a wajen ta saboda aikin da ya yi yana neman warware wa. Ya umarci da ta bayar da kuɗaɗen don ya sabunta aikinsa. Da kyar ta iya shawo kan Sidra ta yarda da cewa za ta bi ta su tafi gobe. _Alhaji Daula_ Zaune yake a tangamemen falonsa da waya kare a kunnensa yana magana. A tsaye bayansa kuma wasu murɗaɗɗun maza ne guda biyu. Sai da ya kammala wayarsa sanann ya juyo ya kalle su. "Yanzu yaushe contenar za su iso ne?" Ɗaya daga cikin su ya ce. "Yau da misalin ƙarfe biyu na dare za su iso ta jirgin ruwa." Jinjina kai ya yi kafin ta gyara zamansa ya ce. "To da zaran sun iso a raba makaman ga waɗan da suke jira kamar yadda aka saba. Sannan ku kasance cikin shiri saboda wanan Intelligence officer ya sa idanun su akan harkokin mu. Ku bi komai a sananu saboda yana da basira fiye da tunanin ku, na ji labarin waye Jalaluddeen sai kun yi taka tsantsan. "Na so mu ga bayansa kamar yadda muka yi wa sauran jami'an da suka nemi shiga gonar mu, amma shi mun gagara sanin sa sai daga baya." Cewar daya daga cikin yaran Daula. "Ka san shi yana da matuƙar lissafi ya ɓoye kansa wanda ba mu san shirin sa ba sai dai ya yi nisa a binciken da yake yi. Ya matukar iya basaja Yallaɓai yana da abubuwan da ya sani akan mu." Jinjina kai ɗaula ya yi sannan ya ce. "Ranar da kuka ritsa shi ai kasa kashe shi kuka yi, wai a ce duk yawan ku mutum ɗaya ya gagare ku har ya tsere ba mu sani ba, taron mara sa amfani kawai." Ya yi maganar cikin takaici. "Ka yi hakuri yallaɓal za mu shirya ma sa gadar zare zai faɗa." "Haka kullum kuke cewa, ku ne ma su shirya gadar zare karshe shi ba zai faɗa ba ku ne za ku fada ciki.." Ya yi maganar yana amsa wayar da aka kira shi. _Ma'eesha_ Kallon Nasreen take yi da maɗaukakin mamaki . "Ban gane mijina ba ina kika gan shi, ko dai can wajen gyaran takamin da yake zama ya yi?" Dariyar rainin hankali ta yi kafin ta ce. "Ko ma sai ina ne za ki ga ashirin waye mijinki ki san da waye kike zaune ." "Na san da wanda nake zaune Khalifa ne mijina dan asalin garin Maiduguri ko ina da wani mijin ne bayan shi." Sanin cewa duk yadda ta yi kokarin fahimtar da Ma'eesha ba za ta fahimta ba ne ta saka bin ta a hankali ta yadda za ba za ta bijire ma ta ba. "To amma ba jimawa na kira wayarsa ba ta shiga ." "Eh idan mun je can za ki gan shi kuma za ki ga abun mamaki ." Hijabi ta saka suka fita in da ta rufe gidan da makulli sannan ya shiga motarta da niyyar za ta kai ta wajen mijinta. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣5️⃣ Hijab ta saka suka fita in da t rufe gidan da makulli sannan ta shiga motarta da niyyar za ta kai ta wajen mijinta. _Makaho_ Yana zaune a tsadadden gidan cin abincin shi da ogan sa Assistant Director Sulaiman don bai yarda ya je ɓoyayyen gidan nasa sa ogansa ba, don a halin yanzu kowa abun zargi ne a wajansa. "Ka ce Harbin da aka yi ma ka ba daga mutanen Daula ya fito ba?" Jinjina kai ya yi yana kallon Ogan nasa kafin ya ce . "Ƙwarai kuwa ba daga mutanen Daula ba ne, ɗaya daga cikin mutanen mu ne suka harbe ni bullet din bindigar ya fito ne daga weapon serial number na DSS stock." Mamaki ne bayyane a fuskar ogan nasa kafin ya ce "To yanzu waye kake zargi?" "A halin yanzu kowa abun zargi ne a wajena musamman wannan da suka san shiri na. Shin kai Assistant Director zan zarga da nake tura rahoto office din ka, ko kuma zan zargi Deputy director ne wanda idan ka karanta rahoto kake tura wa office din Deputy director idan ya dace? Don na fahimci duk bayanan da nake aika wa da shi suna isa gaa su safarar makamai . Shin kai zan zarga ko wani a ofishin ka yana karanta rahoto kafin rahotanni su kai gare ka?" Ko kuma wani ne zan zarga cikin wadanda cikin manyan da suke mataki na sama?" Zuciyarsa ta buga wanda hakan ya sa ya juya bayansa. Zaro idanun waje ya yi hango Nasreen sa Ma'eesha. "Sir zan bar wajen nan yaxu kawai matsala." Kamar walƙiya haka ya bar wajen nan take. Sulaiman bai ce komai ba ya cigaba da cin abincinsa. Don dama shi Makaho ruwa kawai ya buƙata ya ce ba zai ci abinci ba. "Assalamu alaikum" Nasreen ta yi ma sa sallama yayin da Ma'eesha ke bayan ta. "Baba dama wani nake nema wanda na gani a nan tare da kai?" "Wai maganar me kike yi ne yarinya? Ba kowa da nake tare da shi ni kaɗai ne a nan wajan." "Baba da shekarun ka za ka yi irin wanann magana, na gan ku tare." "Yarinya don Allah ki bar nan ba na son hayaniya."" Ma'eesha ta ja hannunta suka fita waje. "Ba kin ce mijinki yana wajen gyaran takalmi ba?" "Eh yana can ma na." "Mu je wajen za ki ga baya wajen hakan zai sa ki yarda da ni.," Suka shiga motar Nasreen ta ja suka bar wajen aguje. "Wai gudun meye haka dan Allah idan ba za ki iya tafiya a hankali ba ki ajiye ni ko ki ba ni na yi driving a hankali." Ta yi maganar tana tuna lokutan da kullum idan za ta fita da mota sai Mummy ta yi mata maganar ta yi driving a hankali kada ta yi tuƙin ganganci. Kullum abun da Mummy ke yi ma ta magana akai kenan. Ƙwalla ne ya cika idanunta a hankali ta ce. "Allah ya jikan ki Mummy Allah ya kai haske kabarinki ." "Amin ya Allah." Nasreen ta amsa idanunta na kan driving da take yi. "Ina sauri mu karasa wajan da mijinki yake gyaran takalmi ne, ina mai tabbatar ma ki da cewa ko mun je yanzu baya wajen, shi ne dai wanda na gani a wannan gidan cin abincin da muka fito. " Shiru ya biyo kafin ta ce . "Na lura fa kina son mijin nan naki da yawa, me ya sa kike son sa a matsayin sa na makaho shi ba komai yake da shi ba faƙiri ne fa, ba kuma wai dukiya ba ballantana na ce saboda kuɗin sa ne. Ko kyawun surarsa ne ya rude ki?" "Ina son sa ne sabida Allah ba don wani abu ba, kuma yana da zuciya mai kyau, duk da na shiga damuwa lokacin da aka aura ma ni shi ba tare da sani na ba, sai dai Idan zuciya ta shiga damuwa, ta rikice, ta rasa natsuwa, babu wani abu da zai kawo mata sassauci kamar tunawa da Allah, ambaton Allah, da kuma roƙon Allah. Da kike maganar kyawu ya kamata ki sani. Kyau yana da matakai, mafi ƙasƙanci shi ne kyawun kamanni, matsakaici shi ne kyawun magana, mafi tsayi shi ne kyawun ruhi, mafi daraja shi ne kyawun hali, Amma mafi tsarkakarsu duka shi ne kyawun zuciya. Nutsuwar zuciya tana cikin abu biyu, Tawakkali, ka miƙa lamuranka ga masaninin dake riƙe da gaibi, yarda, ka yarda da tabbacin cewa abin da Allah ya zaɓa maka shi ne mafi alheri ne Mutumin da yake dogaro ga ALLAH, ba ya jin haushi idan bai samu abu ba, Idan kuwa ya samu koda kaɗan ne yana godiya, ba ya jin tsanani idan ya fuskanci ƙalubale, zuciyarsa tana da salama." Jinjina kai Nasreen ta yi kafin ta ɗan kalli Ma'eesha ta ce. "Tun da kike da shi ya taba furta ma kalmar soyayya? Ya taɓa cewa yana son ki? Dariya ta yi kafin ta ce . "Soyayya da aure suna bukatar hakuri, fahimta, da kyautatawa. Idan miji ya kula da mace tagari, shi ma zai zama hasken rayuwarta. Rayuwa ba ta da sauƙi, amma da kyakkyawan zamantakewa za'a iya cimma farin ciki da zaman lafiya. Gaskiyar soyayya tana bayyana ne a cikin aikace-aikace, ba kawai a cikin magana ba. Idan miji ya zama ginshikin farin cikin matarsa, domin ita haske ce a gare sa, kuma shi haske ne a gare ta." 'To ni dai shawara da zan ba ki tun yanzu ki koyi hakuri da rashin sa, domin shi za ki iya rasa shi a kowane lokaci." "Kada ki sake yi ma ni maganar nan ba na so." "In sha Allah, amma akwai ranar da za ki gasgatani." Bayan sun shigo unguwar ne Ma"eesha ta nuna wa Nasreen in da yake zaman gyaran takami. Suna ƙarasawa ta yi parking gefe. Da maɗaukacin mamaki take kallon Makaho yana zaune ba cikin kayan da ta gan shi ba, wato suit din jikinsa da ta gan shi da shi a can. Yanzu hanyan da ya bar gida ne da su wani yafi mai arha wanda ake cewa ka yi shirun ka Maraya. Da hula taɓa ka ji hadisi da ya saka. Sai takamin soso dake ƙafarsa. Saɓanin can da ta gan shi da tsadadden takaomi. "Yanzu dai ga shi wajen sana'arsa yana aiki. Wai me mijina ya yi ma ki da kike so sai kin raba ni da shi? Me ya yi ma ki ne a rayuwa? Don Allah ya isa haka kada ki sake kawo Mani magana akan mijina ko kina zargi da ya isa haka!" Nasreen ba ta ce komai ba ta yi wa motar key suka bar wajan. Murmushi Jalaluddeen ya yi tare da magana a zuciyarsa.. 'Yarinya ba fi karfin makircin ki na wuce sanin tunanin ki.' Tun da suka kama hanya ba wanda ya sake magana a cikinsu. Nasreen ta fara tsorata da shu'umancin Jalaluddeen. Duk shirin ta na shirin tona ma sa asiri sai ya wargaza shi. Ta ya ya ma a cikin kankanin lokaci kuma bayan ta tabbatar ya ga su ne a wajen shi ne ya bar wajen. Sannan sun biyo bayansa a kankanin lokaci ne har ya isa ya zo nan ya canza kaya ya fara aikin gyaran takami. Gudu fa ta kure a mota amma duk da haka sai da ta tsallake wannan ma? Cikin takaici ta buga sitiyarin motar da ƙarfi wanda hakan ya sa Ma'eesha cewa. "Sauke ni a nan zan karasa da kafata." Ba ta saurare ta ba ta cigaba da tuƙin da take yi. "Ki damu da abun da yake gabanki ya fi ma ki da ki tsaya zaman saka wa bawan Allah ido da neman ganin aibun sa. Ta ya daga ganin wani a wani gari ki ce mijina ne, sannan yanzu kin ga wani a tsadadden gidan cin abinci ki ce shi ne, mutumin da yake aiki tuƙuru dan ganin ya samu abun da ya kawo ma na ko ba yawa ne zai samu kudin zuwa gidan abincin nan? Sannan nawa ma yake samu a rana ɗaya, ku rabin abincin wajen nan baya da shi ko da zai kai sati yana aiki yana tara kuɗin. Ke burin ki ki raba ni da shi ko?" Murmushin takaici Nasreen ta yi sanan ta ce . "Wata rana yana zuwa wanda idan gaskiya ta yi halinta, ranar da za ki shiga tashin hankali da mamaki ranar da za ki zubar da hawaye kina nadamar rashin yarda da zance na yana zuwa. Ki rubuta ki ajiye wallahi sai kin yi nadamar ƙaryata ni da kika yi ." "Nadama, nadama fa kika ce." "Ai yanzu ma ga nadamar nan na yi na biye ma ki na fita daga gidan aure na ba tare da izinin mijina ba. Kin sa na shiga tsinuwar mala'ikan Ubangiji ina zaman lafiya ta. Kada ki sake kawo ma ni wani zancen akan mijina ya isa haka nan." Daidai lokacin Nasreen ta yi parking a kofar gidan, Ma'eesha ta bude murfin motar ta fita ba tare da ta yi magana ba. Tsawon mintuna biyar Nasreen na cikin motar tana tunani, kafin ta ja motar ta bar kofar gidan. _Sidra_ Washegari dama suka yi da Sady baby akan ta zo ta raka ta wajen Mallamin da yake ma ma ta aiki. Don haka ko da ta yi breakfast ta cewa Umma za ta shiga ɗakinta ta kwanta sai rana za ta fito. Don Umma ce kadai ke sakar ma ta fuska a gidan. Don haka ko da ta yi shirin fita ta ƙofar kitchen ta fice, ba ta bi ta gate ba sai ta bi kofar baya wanda an dade ba'a bude kofar baya wanda an daɓe ba'a bude kofar ba. Ta fita daga gidan ba wanda ya ga fitan ta. A bakin titi ta hadu da mai keke nape ta tare shi ya tsaya. Har za ta shiga sai ta ga wata mata da yara biyu a ciki. Da kin kalli matar kin san tana cikin matsin rayuwa bisa la'akari da kuɗaɗun kayan jikinta da na yaran. Kallon matar ta yi tana yamutse fuska alamar wacce ta ga abun ƙyama . "Tafi Mallam ba da kowasu irin mutane nake haɗa numfashi." "Ki yi hakuri Hajiya ba kusa sauke ta ai sai ja kai ki duk in da kike so." Ba ta saurare shi ba ta matsa gefe tana tsuki. Ganin haka ya ja nape ɗin sa ya bar wajen. Ma su nape sun kai biyar tana tare wa da ta kalli kayan jikinsu ta ga alamar ba ma su tsafta da kwalliya ba ne za ta ce su tafi. Sai Surutai take yi ita kadai. "Idan ba dole ce ta sa na yi satar fitar nan ba ai da na dauki key din mota na fita da waɗan nan kucakan mutane da nake gani." Tana nan har kiran Sady baby ya shigo wayarta, ɗagawa ta yi tana cewa . "Na fito daga gidan ina titi." "Ba abun hawa ne?" "Ba ki gan su ba wasu ƙazamai da su ko wanka ba su yi ballantana ki ji ƙamshin turarerensu." "Ina ruwan ki da kuma wankan su? Ke dai ba burin ki akai ki in da kike so ba? Dan Allah ki shiga ina jiran ki kafin gidanku su san kin fito." Suna gama magana sai wani ta tsayar. Ba laifi ya yi duk da ba yadda take iya ta samu ba. Haka ta shiga ciki tana yamutse fuska ta sanar da shi in da za ta je. Ko da ya sauke ta a kofar gidan Sady baby ta tambaye shi kudinsa ya ce ma ta dubu ɗaya ta fito da dubu daya a cikin jaka ta cilla ma sa kuɗin, sai kuɗin ya fadi kasa. Mai nape din ya juya ya kalli gabas da yamma kudu da areawa ya ga ba kowa a kusa da yake kallon su. Ya fito daga keke nape ɗin ya zaro wuƙa da ya soke a ƙugunsa. Ya saita wuƙan daidai saitin maƙogoronta fuskarsa a murtuƙe. Idanu Sidra ta zaro wajen cikin tashin hankali da tsoro. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣6️⃣ Ta fito daga keke nape ɗin, ya zaro wuƙa da ya soke a ƙugunsa. Fuskarsa a murtuƙe. Idanu Sidra ta zaro waje cikin tashin hankali da tsoro. "Sana'a ta nake yi ba Maula ba, na kawo ki in da kike so ki bani kuɗina cikin girmamawa." Cikin tsoro da fargaba ta ce. "Ka yi hakuri kada ka cutar da ni bari na ɗauko kuɗin na ba ka." "Ƴar wulaƙanci kawai na fi ki ɗanyen kai wallahi. Yanzu na ga dama sai na fassara ki a wajan nan na yi tafiyata." Yana sakin wuyanta ta duƙa ta ɗauki kudin ta mika masa, kaba ya yi ya shiga nape ɗin sa yayin da ita kuma ta faɗa gidan Sady baby q guje. Daidai lokacin Sady baby na zaune a falo tana waya, ganin yadda Sidra ta faɗo falon a guje ya sa ta katse kiran wayar da sauri ta nufi Sidra tana cewa. "Lafiya?" Kafin ya ba ta amsa ta leka harabar gidan ganin ba kowa ya sa ta karasa bakin gate ɗin, ta rufe da sakata sannan ta koma falo wajen Sidra. "Meke faruwa kika firgice haka?" Ba ta ba ta amsa ba sai dai ta nufi toilet dake cikin falon Sady baby. Don ta tsorata sosai cikinta sai da ya murɗa. Bayan ta fito ne Sady baby ta ce . "Wai meye haka ina ta tambayar ki ba ki ce komai ba kin saka ni cikin tashin hankali?" "Wallahi mai nape din ta ya ɗauko ni Ɗan daba ne shi da wuƙa yake yawo ban sani ba. Daga na jefa ma sa kudi shi kenan ya zaro wuka zai kashe ni, sai da na bashi hakuri ya sa na ɗauki kuɗin na mika ma sa ya ƙyale ni." Taɓa baki Sady baby ta yi kafin ta ce . "Allah ya kyauta." "Amin ya Allah ." "Za mu tafi yanzu ne ko sai kin huta?" "A'a wani hutu byNa na sanar da ke cewa satar fitar na yi kun sani." "Okay." Ta faɗa tana nufar bedroom ɗin ta, ba jimawa sannan ta fito sanye da ƙaramin gyale da key din motarta a hannun ta. A tare suka fita Sady ta rufe ƙofar falon da key sannan suka nufi harabar gidan. Sai da ta fara wangale gate ɗin gidan sannan ta shiga motar Sidra ma ta shiga ta ruwa miyar key ta fita daga gidan. Bayan ta fitar da motar waje ne ta fito ta rufe gate ɗin da key sannan ta ta koma cikin motar ta ja suka bar unguwar. "Wai ina maigadin gidanki ne?" "Na sallame shi saboda yana sa mun idanu a cikin Lamira?" Daga haka suka j yi nisa a tafiya ba wanda ya yi magana . _Makaho_ Da sallama a bakinsa ya shigo cikin gidan. Hannusa daya riƙe da sandarsa ta jagora, dayan hannun muka yana rike da kayan gidan takalmi. "Ma'eesha dake cikin daki ta ji dawowarsa ta fito amsa, da sauri ta karasa in da yake ta karbi kayan gyaran takami dake hannusa tana yi ma sa sannu da zuwa. Ya amsa ma ta yana bin bayanta zuwa cikin ɗaki. Da sallama ta shiga ta amsa sannan ta rike sabadrasa tana nuna ma sa tabarmar da zai zauna. "Ba sau kin wahalar da kanki wajen nuna ma ni wajen zama ba. Na riga na san komai da yake cikij dakin nan Zama ya yi t kawo ma sa ruwa. Pure watar bayan ta fasa leda ta zuba kofi Karba ya yi ya karba tare da yin bisimillah ya sha. Farantin da ta jera masa kulollin da ta zuba ma sa abinci ta kawo ma sa ta ajiye a gabansa. "Ga abinci ." "Na gode Allah ya yi ma ki albarka." "Amin ya Allah." Tana kallon da tana tuna zancen ƙawarta Yasmeen. Duk da ta san cewa Nasreen ba makaryaciya ba ce. Komai ta faɗa akan gaskiyar ta ne, to sai dai kuma wanan karon ba za ta ce Nasreen karya take yi ba illah iyaka ta ce ta dai yi ma dai yi ma sa kuskuren fahimta ne. Don ko a photon da ta gani ta san wancan na jikin photon wayayye ne ɗan boko, shi kuma wanan mijin nata ɗan gargajiya ne ko turanci bai iya ba. Sannan shi wancan da Nasreen ta nuna ma sa video yadda yake tafiya cike da izza da isa yayin da mijinta kuma tafiyarsa ma irin ba wadanda suka taso ƙauye yake yi, takunsa ba ɗaya ba ne da wancan. Duk da cewar dai Dukansu suna da ƙira irin ta jaruman maza. Ta cikin bakin glass dake idanun sa yake kallon ta, sannan ya cire glass ɗin ya juyar da kwayar idanunsa tamkar waɗan da basa gani da idanunz wato makafin da za ku ga idanunsu a bude amma bai da amfani. "Ma'eesha kina kusa kuwa?" Sai a lokacin ta dawo daga tunanin da ta faɗa tana cewa. "Ina kusa da kai, me kake bukata ne?" "Na ji kin yi shiru ne kamar ba kya wajen, lafiya kuwa ?" "Eh lafiya lau Alhamdulillah." "Kamar akwai abun da ke damun ki Ko?" "Eh to gaskiya ɗazu ƙawata Nasreen ta zo ta ce na raka ta wani waje. Na kira wayarka don neman izinin ka amma ba shiga , shi ne na raka ta ba tare da izinin ka ba. Ka yi hakuri ba yi farko da karshe kenan in sha Allah ba zan sake fita ba izinin ka ba ka ka yafe ma ni." "Ba komai kada ki damu." "Dama ka ce idan cikin unguwa zan siye abu ko kuma dai a ce gidan Mallam Liman zan iya zuwa ka lamunce ma ni ko?" Jinjina kai ya yi alamar eh haka ne. Abinci ta zuba ma sa ya fara ci, farar shinkafa ce da miyar stew da naman Sa wanda ta siyo a bakin layin su. "Allah ya sakawa bayin Allahn nan da alkhairi." Ta yi maganar tana tuna yadda suke abincin su ya kare ranar gari ta sha. Amma sai ga shi Allah ya aiko waɗan da suka kawo ma su tallafin dubu ɗari biyar ga shi yanzu suna cin abi mai kyau. "Wasu mutane kike magana akai?" "Waɗan da suka kawo ma sa kayan abinci nake nufi.." "Ayyah, ga shi yanzu shi muke ci. Allah ya saka da alkhairi." "Amin ya Allah." Daga haka ya cigaba da cin abincin yana da tuna Nasreen yana murmushi wanda shi kadai ya san Ma'anarsa. _Nadra_ Bayan sun bar gidan Abba suna kan hanyar su ta komawa gida ta kalli Fahad dake driving. "Yaya Fahad." "Wai ba na faɗa ma ki cewa ki daina kira na da Yaya ba ne? Ta ina na zama Yaya a wajen ki ? Ba na son kalar dangi." Murmushi ta yi kafin ta ce. "To ya kake so na kira ka?" "Ke ba ki san sunan da ya dace ki kira ni da shi ba ne?" "Gaskiya ban sani ba." "To ki bincika ki nemi suna mai dadi da za ki sakawa mijinki ." "To." Shiru ne ya biyo baya kafin ta sake kallon sa ta ce. "Ka san wani abu?" "A'a sai kin faɗa ina jin ki." "Ban samu yin magana da Aunty Sidra ba ko da na je tana barci, kuma ba na son na tayar da ita ka san ba ta da isasshen lafiya." Shiru ya yi bai tanka ma ta ba, ta juya da niyyar sake yi ma sa maganar Sidran sai ta ga ya murtuƙe fuska tare da yi ma ta wani kallon da ya sa gabanta faduwa , don haka ya ja bakinta ta yi shiru don ba fuskar da za ta sake yi ma sa wani magana. Har suka karasa gidan ba wanda ya yi wa wani magana. Ganin yadda ya sauya fuska ita ma ta yi fushi ta yi banza da shi ita ma. Yana gama parking ta fito daga motar ta wuce bakin ƙofar shiga falon. Dai sai dole ta sakavta tsaya sakamakon ƙofar a rufe kuma key ba hannusa. Shi ma yana lura da yanayin ta amma sai ya share ta, ya ɗan me take yi wa fushi saboda bai ba ta damar magana akan Sidra ba. Bayan tun ba yau ba yake faɗa ma ta idan suna tare ta daina kawo ma sa hirar Sidra baya so, sunan ta na baya son ji amma Nadra ya lura ba ta jin magana sai ta yi masa zancen Sidra dole. Bude ƙofar ya yi ta shiga da sauri, da ido ya bi ta kafin ya shiga sanan ya rufe kofar. Kashe komai na falon ƙasa ya yi sannan ya haura upstairs. Ɗakinsa ya nufa ya shiga, dama ita ma Nadra ɗakinta ta nufa ta shiga ta bude drawer ta ajiye magungunan mata da Ammi ta ba ta. Sawa ƙofar key ta yi tana tura baki ita a dole ya ɓata ma ta rai take fushi da shi. Cizon yatsa ta yi sai ta ji wani zaƙi kamar zuma a yatsar. Sai ta tuna da maganin matan Nam maybe akwai wanda yake zuba. Don haka ta fito da su ta ga wani robar zuma ne yake ɗan zuba wanda daga wurin murfi ne. Sai ta mayar da sauran shi kuma zumar ta zauna tana sha saboda dama akwai ta da son zaƙi. Sai da ta sha rabi sannan ta ajiye sauran. Wanka ta yi ta shirya cikin riga da wando na barci ta haura saman gadon kenan sai ta ji ƙarar an tura ƙofar an shigo . Da mamaki take kallon sa bayan ta rufe ƙofar da key sanan ya ajiye key a saman Side drawer. Wato tana da wani key din dakin kenan a wajan sa. Kwanciyar ta yi ta juya ma sa baya . Murmushi kawai ya yi ya kashe hasken ɗakin ya haura saman gadon tare da janyo ta jikinsa. _Ma'eesha_ Bayan ta gama duk ayyukan da ta na dare ta shiga wanka lokacin karfe tara na dare ne, ga hadari ya haɗu a garin sai iska ake yi. Ga banɗakin babu rufin sama wato ko rana ruwa da rana ake yi zai sauka kan mutum. Don katanga ce kawai aka yi. Tana tsaka da wanka sai ruwa sama ya faɗo da ƙarfi. Ga ruwan saman da sanyi sosai haka yake zubowa kanta. Ga shi ba ta gama wankan ba . Kuma ita ba ta son ruwan sama ya dake ta. Haka ta watsa ruwan ta fito waje da sauri, sauran ruwan fita watsa a ƙafarta bayan ta fito . Kafin ta kai ga shiga ɗakin ma haka ruwan ke fuskanta har ta shiga da sauri tana rawar sanyi. Yana tsaye a tsakiyar ɗakin wanda dawowarsa kenan shi ma ya cire riga daga shi sai dogon wando, ya kalle ta yadda ta fado ɗakin tana rawar sanyi. Tausayinta yake ji har cikin ransa yana addu'ar Allah ya kawo ranar da komai zai yi daidai sai ya ɗaga darajar ta a cikin mata ya mayar da ita tamkar zara a cikin taurari. Sai ya jiyar da cewa tafi kowace mace sava a duniya. Amma da sauran lokaci akwai babban kalubale a gabansa. Shin ma ta ya zai fuskanci iyayensa da zancen cewa ya yi aure ba tare da sanin su ba? Ya zai fuskanci zai fuskanci uwar da ta rene shi cike da so da ƙauna da kulawa wanda babu algusu da wanan maganar? Sanan ta yi ma sa kyautar ƴarta to ta ya ya zai iya sanar da ita cewa ya auri wata mace bayan ga ƴarta can na zaman jiransa. Jin sautin kat kar kat ne ya sa ya kalli Ma'eesha fa haƙurinta ke karkarwar sanyi jikinta ba rawa. Ga towel da ta yi wa ka da shi ya jikin shi ma . Kasancewar ta san ita kadai ce a ɗakin shi mijinta makaho ne baya gani ko da ma yana gani ba ta san ya dawo gidan ba ya sa ba tare da tunanin komai ba ta zame towel din jikinta ya faɗi ƙasa Gabaɗaya jikinta dai kaɗuwar sanyi yake yi, fito da idanunsa waje ya yi ganin ta tsaye jikinta na rawa babu komai a jikinta. "Ya Salam!" Ta faɗa kamar mai koyon magan a can ƙasar maƙoshinsa.Wutar nepa ce ta ɗauke a daidai wannan lokacin. Lalube ta fara yi inda za ta ga wayarta ta kunna torchlight. Ji ta yi ta faɗa jikin mutum wanda da alama shi ma ba riga a jikinsa, buɗe baki ta yi da niyyar yin ihu yaji saukar tattausan lips a fatar bakinta. Gabanta ne ya faɗi jin bakinta a cikin bakin wani mutum da ba ta san ko waye ba, a tunanin ta wani ne ya shigo ɗakin, don tun da take da mijinta bai taba rike ko da hannunta ballantana ya haɗa bakinsa da nata. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.k✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, ban yarda a sarrafa ma ni shi ta kowace hanya ba tare de izinina ba. Kuma ban yarda a karanta shi s YouTube ba tare da izinin ba, don haka a kiyaye! *SANARWA* Wannan ƙirƙireren labari ne, ban yi shi don cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi ne, mai kashe auren wawa Page7️⃣7️⃣ Gabanta ne ya faɗi jin bakinta a cikin bakin wani mutum da ba ta san ko waye ba, a tunanin ta wani ne ya shigo ɗakin, don tun da take da mijinta bai taɓa rike ko da hannunta ba ballantana ya haɗa bakinsa da nata. Jin yadda zuciyarta ke bugawa ya sa ya zare bakinsa daga cikin nata ya yi ma ta raɗa a kunne." "Mijinki ne." Sannan ta ɗan samu natsuwa a zuciyarta. Sake ƙanƙame ta ya yi a jikinsa ya xora bakinsa cikin nata tare da tsotsan harshenta a hankali. Jin yadda ƙafarta ke rawa ne ya sa ya ɗauke ta cak tare da ɗora ta kan katifar ya kwantar. Tsawon mintuna biyar suna a haka, duk da a tsorace take amma ba ta yi yunkurin hana shi abun da yake yi ma ta ba. Hannunsa ya da ya shiga shafar fatar jikinta. Wanda hakan ya da ya rikice jikinsa ya ɗauki rawa shafar ta yake ta ko ina daga samanta har ƙasa. Musamman ƙirjinta da suka ɗimauta shi, don a cike dukiyar fulaninta suke. Ya kai bakinsa ya fara tsotson ɗaya kamar jariri yayin da yake wasa da ɗaya yana murza shi son ransa. Ƙarar wayarsa ta aiki ne ya cika ɗakin wanda nan take ya dawo da shi cikin hayyacinsa. Cikin mutuwar jiki ya cire bakinsa da hannunsa daga Mamanta. Wani Gwauron numfashi ya sauke cikin kasala ya sauke cikin kasala ya sauka daga kan tatifar ya nufi kayan da ya cire, wayar na cikin aljihun rigarsa. Ɗaga wayar ya yi tana dab ta tsinkewa. Bai yi magana ba ya tsaya yana sauraren abun da na cikin wayar ke faɗa. "Okay gani nan zuwa." Ɗaya daga cikin yaransa ne ya sa shi ya kula da motsin mutanen Alhaji Daula. Ya godewa Allah da ya sa yaron ya kira shi a daidaita wannan lokacin, don har ga Allah ya yi farin ciki da kiran wayar nan ya dawo da shi hayyacinsa. Don gani yake lokacin da za su yi rayuwa irin na cikakkun ma'aurata bai yi ba. Har sai ta san waye shi, ta fahimci cewa Khalifa Makaho ƙarya ne, Jalaluddeen Kabir arzika shi ne gaskiyar mijinta. Shi ya sa lokuta fa yawa yake gujewa abun da zai sa ya haɗa jiki da ita saboda bai san iya inda abun zai tsaya ba a matsayin sa na lafiyayyen namiji. Duk da ya san ba ta jin dadin hakan amma bai nuna hakan ya dame shi ba. Sai dai ya saka a ransa har sai ta ksrɓe shi a yadda yake ta san komai game da shi ta amince da shi a yadda yake, sannan ya gabatar da ita ga iyayensa sun yarda sun amince da ita an yi shagalin bikinsu tare da sanyawar albarkar iyaye. To daga nan ne zai iya kusantar ta a matsayin matarsa su yi cikakken rayuwar aure kamar kowasu ma'aurata. Duk da ya san sai ya fuskanci kalubale daga wajan Ma'eesha da iyayensa amma ya shiryawa hakan lokaci yake jira. Kuma dole zai gargaɗi Ma'eesha ta kiyaye cire kaya a gabansa domin hakan zai iya sa wa ya watsar da ƙudirin sa na cewa sai ta san waye shi zai yi mu'analar aure da ita. Ga shi yanzu ma da ba don kiran wayar da ake yi ma sa ba ai da komai ya lalace ba yadda ya tsara ba. Ma'eesha kam dama a tsorace take da shi tuni ta nemi kaya ta saka. "Na ji ƙarar wata waya kuma ka amsa ka ce kana zuwa." "Eh wayar ce ina tafiya sai na ji ba taka abu, na laluba na ji waya ce, aka kira na ce na tsinta ce. To shi ne yanzu me wayar ya kira yake sanar da ni in da yake na kawo ma sa wayar." "A'a dan Allah kada ka fita daga cikin gidan nan, yanzu fa dare ne. Why not shi me wayar ka sanar da shi in da kake ya zo ya same ka ya karɓi wayarsa. Ta kunna torchlight ɗakin ya yi haske. "Na riga na ce zan kai ma sa " Fita waje ya yi bayan mintuna ya dawo da alama wanka ya yi. Sai ta kashe hasken wayar da sanin zai canza kaya. Shi ma ya san haka don haka bai damu ba ya shigo don ya sauya kaya. "Yanzu fita za ka yi?" "In sha Allah." Ya yi maganar yana lalubo wata rigar sanyi mai leda a jiki kuma tana da hula. Sai da ya fakaici idanunta ta soke bindiga a wandonsa. "Don Allah kada ka fita a daren nan.," "Kada ki damu zan kula da kaina, ki yi ma ni addu'a." "Ko na raka ka ne?' "Ba buƙata, ki kwanta ki huta ai yanzu kin daina jin sanyi ko, saboda jikina hita ne na ɗumama ma ki jiki ko?" Kunya ta ji kawai ta dukiyar da kai tana murmushi. "Sai na dawo ki kulle ƙofar zan buga ku bude idan na dawo." "Allah ya tsare ya dawo mun da kai lafiya." Da Amin ya amsa yana ɗaukar sandarsa ya fice daga ɗakin. _Sidra_ Bayan Sady baby ta yi parking motar a bakin titi ne suka fito suka karasa da ƙafa, sakamakon lungun mota bai iya shiga ciki. Suna zuwa ƙofar gidan ta ji gabanta ya faɗi kamar ta juya, wanda har sai da ta tsaya cak, amma Sady baby ta janyo hannun ta tare da yi ma ta alamar su shiga ciki. Gidan shi kadai ne a layin kuma gidan ya fita daga sahun jama'a don ya juya wa sauran gidajen baya, wato sai jama'ar da ke kusa da shi ba su ganin wanda ke shiga ko wanda ke fita. Cikin sanyin jiki ta bi Sady suka shiga cikin gidan. Ƙamin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyu, sai banɗaki da kitchen a gefe. Da sallama suka shiga cikin gidan, shiru ba wanda ya amsa sai Sady baby ta ƙarasa kofar wani daki tana sallama. Ya amsa sallamar ta shiga ciki, bayan kamar mintuna uku ta fito ta cewa Sidra ta shigo ciki. Shiga ta yi da sallama a bakinta ya amsa yana zaune a saman tabarma da wani faranti a gabansa. Ƙasa ne a cikin farantin, sai wata ƙwarays dake da ƴaƴan wuri a ciki. Daga gefe kuma magunguna ne da yawa da aka ɗaura aka ajiye. Sidra ta shigo tana yamutse fuska alamar tana jin wari. Kallon ta yake yi yana haɗiyar yawu kamar wani tsohon maye. Gefen Sady baby ta zauna ta buɗe baki ta ce . "Sannu Mallam." "Yauwa." Sady baby ta gyara zama ta ce . "Mallam wannan ƙawata ce tana so..." "Ki yi shiru ba sai kin faɗa ba, na san komai dake tafe da ita." Tsayawa suka yi suna sauraron abun da zai faɗa. "Wato sunanki Sidra kina da saurayi da kike mutuwar so Fahad sunan sa. Ƴar uwarki ce Nadra ta yi asiri ta janyo da hankalinsa wajenta, ke kuma ta yi maki kurciya kika bar gari , ta canzawa iyayen ku tunani suka sura ma ta saurayin ki, yanzu haka ma ko ganinki baya son yi ko?" Da maɗaukakin mamaki Sidra ke kallon Mallama jin yadda ya fadi sunan ta da na Nadra da Fahad, sanan abun da ya ba ta mamaki wai Nadra ta yi ma ta kurciya ta bar garin saboda ta auri Fahad. "Mallam dama Nadra son Fahad take yi kuma ita ta aikata ashirin da ta raba mu da shi? No wonder lokaci ɗaya daga wata ta ma ni wulaƙanci saboda ta samu daukaka na ji ba zan iya hakura ba zuciyata ta dinga azalzalata akan sai na ɗaukaka fiye da ita na rama wulakanta ni da ta yi, ashe ba yin kaina ba ne?" "Ƙwarai kuwa aikin asiri ne." "Aiko ba zan taba bari da samu salama a gidan Fahad ba sai na ɗauki fansa." "Kar ki damu ki ɗauka bukatar ki ta biya za'ayi ma ki ko ma mene ne kike so ayi ma ta. Ko kashe ta kike so a yi ko haukata ta kike so ayi duk zan yi, ke ko jemage zan iya mayar da ita." "A'a Mallam ba na son a yi ma ta komai kuma kada a canza ma ta halitta ko haukatarwa ballanta kashe wa. Kawai so nake yi ka raba su ya sake ta ta bar gidan kawai nake bukata. Sanan na maye gurbinta a wajensa da iyayen sa da nawa kowa ya kasa magana ka rufe bakin kowa." Jinjina kai ya yi sanan ya ɗora da cewa. "Akin akwai wahala idan kika bada haɗin kai komai zai zo da sauƙi." "Malam kudi ba matsala ta ba ne ka fadi miliyan nawa zan bayar." Shiru ya yi na wasu sakanni. "Ba wani kudi zan karɓa a gare ki ba, kawai za ki zo ki bani kanki ne kawai bukata za ta biya." Kallon rashin Fahimta ta yi ma sa kafin ta ce . "Ban gane na baka kaina ba!" "Wato budurcinki shi ne ladan aikin ki." A zauren ta mike tsaye tana yi ma sa wani kallo, kafin ta mayar da duban ta ga Sady baby, ta ga ba ta damu ba ko mamakin jin kalamansa. _Makaho_ Yana isa bakin wani daji dake gefen gari, sai ya tsaya cak ya duba agogonsa "Lokacin ya yi." Ya cigaba da tafiya. Bayan wasu mintuna tsohon sansanin ya bayyana a gabansa. Babu hayaniya, babu dariya, babu motsin da aka saba ji. Ya ɗan ɗaga gira ɗaya yana cewa. "Shiru ya yi yawa." Ya taka zuwa gaba. Kwatsam ya ji an ce. "Tsaya nan!" Muryar ta fito daga bayansa. Kafin ya juya gabaɗaya wasu mutane uku, suka fito daga gefen wani gini. Wasu biyu kuma suka bayyana daga duhu. Ya lumshe ido kaɗan "Wato haka ne." Wani dogon mutum ya fito daga cikinsu "Ka wahalar da mu sosai officer." Makaho ya yi shiru, mutumin ya yi dariya . "Ka yi tsammanin ba za mu gane ka ba, Makaho mai gyaran takalmi ?" "Na ɗauka wasan ya yi kyau." "Ya yi kyau amma baya isa." Mutanen suka matsa kusa da shi, ya kalli mutanen ɗaya bayan ɗaya. "Shugabanku yana ina?" Dogon mutumin ya yi murmushi. Sanan ya ce . "Har yanzu kana tamabaya?' "Eh har yanzu." "Nan take wani daga hagu ya yi kokarin cafke shi, sai ya kauce gefe mutumin ya faɗi ƙasa da karfi. "Ku kama shi" Gabaɗaya suka yo kan makaho, ya ja baya cikin sauri ya kauce wa na farko ya ture na biyun ya fadi ƙasa. Wani ya yi ma sa dirar mikiya daga baya amma sai ya juya akan lokaci. Hayaniya ta cika wurin, dogon mutumin ya zaro bindiga . "Ya isa!" Kowa ya yi shiruz ya daga bindigar zuwa kan Makaho. "Ka gama." Makaho ya kalle shi ba tare de tsoro ba. "Mutumin da ya tona ma ni asiri yana nan." Fuskar dogon mutumin ya sauya na ɗan lokaci ƙafan . Makaho ya yi murmushi. Dogon mutumin ya matse haƙora. "Kama shi!" Sai dai kafin wani ya motsa ƙarar tayoyi sun fara tashi daga wajen sansanin. Kowa ya fara waige-waige, sai hasken fitilun motoci ya zagaye wajen. Dogon mutumin ya zaro ido yana kallon makaho ya ce . "Me ka yi ?" Jalaluddeen ya gyara tsayuwarsa yana cewa. "Na zo ni kaɗai, amma ban ce ni kaɗai na shirya ba." Dogon mutumin ya kalli hasken da ke kara kusantowa, sanann ya kalli Makaho. "Ka yaudara mu." Makaho ya ɗan karkatar da kai . "Ba ni kaɗai na iya yaudara ba" "Ku tarwatse!" Dogon mutumin ya faɗa da karfi. Nan take mutanen suka fara gudu ta ko ina . Wasu suka nufi bayan gine-ginen sansaninsu, wasu kuma suka ruga zuwa cikin dajin dake bayan sansaninsu. Makaho ya lura da wani mutum dake sanye da baƙar hula, yana sulalewa zuwa wata karamar ƙofa dake bayan wani ɗaki. Zuciyarsa ta buga ya ce . "Shi ne." Tun kafin ya fara gudu mutumin ya ɓace ta ƙofar. Makaho ya kutsa tsakanin mutanen da suka rage a gabansa. Ka tsaya!" Mutumin bai waigo ba, ya shiga cikin wani dogon korido mai duhu, makaho ya bi bayansa. Ba abun da ake ji sai sautin amon takalminsu. Da ya fito daga ɗaya gefen koridon sai ya hangi mutumin a tsaye bakin wata ƙofa. A karon farko mutumin ya waiwayo, fuskarsa ta bayyana karkashin hasken wata. Makaho ya tsaya cak. "Kai..." Mutumin ya yi murmushi "Na yi mamakin tsawon lokacin da ka ɗauka kafin ka gane." "Kai ne shugaban?" "Ka yi tunanin zan zauna ina aika mutane ne kawai?" Makaho ya matso gaba tare de cewa. "An daɗe ana nemanka." "Kuma an dade ina kallonka." Shugaban ya bude kofar dake bayansa yana cewa . "Ka san mene ne kuskurenka mafi girma?" Makaho bai ce komai ba. "Ka yi zaton kai kadai ne ka iya farauta?" Ya shiga cikin ɗakin, Makaho ya bi shi, yana shiga dai ya tsaya cak. Babu komai a ɗakin sai teburi ɗaya a tsakiya. Akan teburin kuwa akwai hotuna . Hotunan makaho ne lokacin da yake gyaran takalmi, har ma da lokacin da yake shiga Masallaci, jikinsa ya ɗan yi sanyi . Shugaban ya tsaya a ɗaya gefen ɗakin yana cewa. "Na san kai tun ranar da ka shigo garin nan." Idanun makaho suka ƙanƙance. "To me ya sa ba ka kashe ni ba?" Murmushin Alhaji Daula ya yi tare da cewa . "Saboda ina so in ga iyakar abin da za ka iya gano wa. Shiru ya mamaye ɗakin na wasu daƙiƙu, sai kuma Daula ya yi magana a hankali . "Yanzu kuma ina so in ga yadda za ka fita daga wurin nan." Kafin makaho ya yi magana sai ƙarar kulle kofa ya ji daga bayansa "Klik." Ya juya da sauri ƙofar ta rufe, da ya sake waiwayo wa gaba shugaban ya ɓace. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065357995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣8️⃣ Ya juya da sauri da sauri kofar rufe, da ya sake waiwayowa gaba shugaban ya ɓace. Makaho ya juya da sauri zuwa ƙofar, ya ja makullinta ƙofar ta ƙi buɗewa. Ya sake gwadawa shiru. Sautin wata murya ta fito daga cikin lasifika ta fito da bai lura da lasfikan ba a cikin dakin. "Na ce ma ka ina son in ga yadda za ka fita." Jalaluddeen ya ɗaga kansa. "Ka fi son magana fiye da bayyana." Sautin dariyar Daula ta cika ɗakin , kafin ya bude baki tana cewa. "Har yanzu kana da ƙwarin guiwa kenan." Muryar ta katse shiru ya mamaye ɗakin, Makaho ya juya yana kallon ɗakin. Teburi, hotuna, katanga huɗu, babu window. Ya matsa kusa da Teburin, ya ɗaga ɗaya daga cikin hotunan a bayan hoton akwai wani karamin rubutu . "Ka daina kallon abun da ke gabanka." Ya ɗaga gira ɗaya, sanann ya ɗauki wani hoton ya juya bayan hoton, rubutun iri ɗaya ne, na uku ma haka, na huɗu ma haka . Duk suna ɗauke da saƙo ɗaya. Ya sauke hoton a hankali . "Daina kallon abun da ke gabanka." Idanunsa suka zagaye ɗakin, sai ya ɗaga kansa sama, a can kusa da rufin ɗakin ya hango wata ƙaramar buɗaɗɗiyar mashiga da iska ke ratsawa. Ya yi murmushi kaɗan. "To kenan." Ya jawo tebur zuwa ƙarƙashinsa, ya taka kujerar dake gefen teburin sannan ya mike, har yanzu bai kai ba. Ya yi tsalle ya kama gefen mashigar, ƙarfen ya yi ƙara, ya matse haƙora ya ja jikinsa sama. Da ƙyar ya kutsa cikin mashigar, ƙurar dake ciki tasa ya yi tari Ya cigaba da jan jikinsa s hankali, mashigar ta yi duhu sosai. Bayan wasu mintuna ya fara jin iska mai ƙarfi, alamar yana kusa da fita, ya cigaba can gana ya hango ɗan haske, da ya isa ƙarshenta ya cire wani tsohon murfi. Murfin ya faɗi kasa da ƙarfi, ya leƙa. Yana sah'man wani tsohon sito ne a bayan sansanin, ya sauko a hankali da ƙafafunsa suka taɓa ƙasa. Sai ya ji murya a bayansa. "Na san za ka samu hanyar fita." Ya juya nan take, ba kowa ba ne face Daula yana tsaye cikin duhu hannayensa a cikin aljihun wandonsa. Kamar dai tun farko yana jiransa a wajen. "Ka san me ya sa na bari ka fito? Saboda na gama abun da nake yi . Makaho ya kalle shi ba tare da ya motsa ba. Ƙarar motoci suka sake ji a kusa da su, murmushin dake kan fuskar Daula ya ɗauke, ya karkatar da kai yana sauraro. Sai ihu suka ji daga cikin sansanin . "Sun shigo wanann hanyar ku gudu!" Nan take hayaniya ta kaure mutanen Daula suka fara fita daga gine-ginen sansanin suna guje-guje. Daula ya zubawa Makaho idanun yana kallon sa da mamaki. "Kai ne ka shirya wanan tun farko?" Murmushi Makaho ya yi ya ce . "Ka ce kana kallona tun farko, amma ka manta cewa ni ma ina kallon ka?" Tashin hankali ya bayyana a idanun Daula, ya juya zai bar wajen da sauri, amma kafin ya yi wani yunƙuri hasken fitilu sun haske shi. Muryoyi suka fara bada umarni daga ko ina, mutanen kungiyar suka rikice, wasu suka jefar da makamansu suka gudu, wasu suka ɓuya. A cikin wannan rikicin ne Daula ya amfani da wanan damar ya ɓace cikin duhu. Makaho ya yi ƙoƙarin bin bayansa ya kuma fasa ya tsaya ya kalli sansanin, ya kalli mutanen da ake cafkewa, ya kalli motocin da suke wajen sanan ya sauke numfashi . Ya juya ya nufi wajan fitilu, wani jami'in ya ƙaraso wajen sa da sauri. "Sir! Kana lafiya?" Makaho ya share ƙurar dake jikinsa. "Ina lafiya." "Sir mun yi tunanin mun makara." "A'a." Ya faɗa yana sake duban duhun da shugaban kungiyar wato Daula ya ɓace. "Kun zo akan lokaci ." Jam'in ya kalli inda yake kallo sanan ya ce . "Sir shugaban fa?" Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin makaho ya ce. "Ya tsere." Jam'in ya ce." "Za mu bi shi?" Murmushi Makaho ya yi murmushin dake nuna cewa ya san wani abu. "Zai dawo." "Sir ta ya ka san cewa zai dawo?" "Zaro wata takarda ya yi daga cikin aljihunsa. Takardar da ya ɗauko daga ɗakin Daula. A takardar akwai adireshi ɗaya da kwanan wata, ya miƙawa jami'in. "Saboda yanzu mun san in da zai kasance nan gaba." Ya fara tafiya zuwa wajan motocin. A bayansa kuwa sansanin da ya kwashe watanni yana bincike a kansa yana rushewa a hankali. Duk da ya san wanan ba karshen yaƙin ba ne farko ne. *ABUJA* _Yasmeen_ Kwance take a katafaren gadonta na alfarma tana barcin ta hankali kwance. Tana sanye da rigar barci wacce ta tsaya daidai guiwarta. Wayarta ce ta yi ƙara wanda hakan ya sa ta ɗan yamutse fuska ta kai hannu ta hanyar karɓen wayar da katse kiran wayar ta hanyar danna power din wayarta. Sai da aka kira sau uku sannan ta ɗauki wayar da sauran barci a idanunta. "Hello waye yake damuna ina barci da safiyar nan ." Ta cikin wayar ta ji Muryar Aliyu yana cewa. "Ba shakka Hajjaju ki sha barci lafiya lau abun ki, kin dai san jirgi baya jira, kin saka na siya ma ki ticket daura mintinan talatin jirgi ya tashi kina barci." A zabure ta tashi zaune tana cewa. "Subhanallah ai lokacin ya kusa ban sani ba, na gode Aliyu." Daga haka ta katse kiran wayar ta diro daga kan gadon cikin hanzari. Bathroom ta faɗa don yin wanka, bayan ta saka hular wanka ta sakarwa kanta shower 🚿 Tana wanka tana waƙa cikin nishaɗi. Che che kule... Har ta gama wanka ta fito tana waƙa abun ta hankali kwance. "Nan da nan ta shafa man shafawarta da turare , har ta ɗsuko wasu riga da siket na leshi ta mayar tana cewa . "Yanzu yana gani na da wanan kayan zai fara masifa wai sun matse ni ba na son shigar mutunci. Wallahi Yaya Jalal ɗan yawa ne, ba don son da nake yi ma ka ba ai da tuni na rabu da kai na kama ɗaya daga cikin masoyans.," Doguwar rigar material ta daka ɗin kin bubu ne sai ta ɗauki karamin mayafi da ya shiga da kalar material ɗin. Ta ɗauki handbag ɗin ta mai ɗan girma ta daka kayan sawari ta kala ɗaya. Ta ɗauki abun da ta san za ta buƙata. Ta saka takalmi ta fito da sauri kamar wacce aka jefo ta faɗo falon. Ummee dake waya da ƙawata ta cire wayar daga kunne ta ce . "Ina zuwa naka kike sauri?' "Ummi zan je gidan Mom ce Saddiƙa na waje tana jira na, kuma can zan kwana." "Okay ki gaishe ta." Daga nan ta cigaba da wayarta da ƙawarta hankali kwance. Yasmeen na fita harbar gidan direba ya taso da sauri ganin alamar fita za ta yi kuma sauri take yi. "Hajiya ina kwana." Ya ɗan durƙusa yana gaishe ta.Banza da shi ta yi ba ta ko kalle shi ba ballantana ta amsa. Tana buɗe gate ɗin gidan ta ga Aliyu na jiranta. Bude gaban motar kawai ta yi ta shiga ta zauna gefensa. "Yanzu ke da ban kira ki ba da sai dai ki yi wani bikin jirgin , kin san kina da tafiya kika kwanta kina barcin asara." Wani kallo ta yi ma sa kafin ta ce. "Wani barcin asara?' ",Eh ma na su barcin bayan sallar asuba barcin asara ne." "Ba zan biye maka ba saboda ina cikin farin ciki zan je na ga masoyina Yaya Jalal nawa na kaina, da ba don wanan tsinannen aikin nasa ba ai da yanzu ina ƙarƙashin igiyar aurensa. Ya san za ki je wajen sa?' "Bai sani ba surprise zan yi ma sa." "Umme ta sani?" "Ba ta sani ba na yi ma ta ƙaryar zan je gidan su Mom na kwana ne." "Allah ya kyauta." Ba ta tanka shi ba har suka karasa Airport. Godiya ta yi ?masa sannan ta fita da sauri ta shiga ciki. Isar ta da mintuna biyar bakwai jirgin nasu ya tashi. _Ma'eesha_ Ba ta yi isasshen barci ba kasancewar mijinta ya fita da niyyar kai waya bai dawo ba. Tsoron ta kada a cutar da shi kamar ganin shi makaho ne ba gani yake yi ba. Kasa barci ta yi karshe dai ta fita ta ɗauro alwala ta zo ta fara sallar nafilfili tana yi ma sa addu'ar Allah ya kare shi a duk in da yake . Don ta kira wayarsa da ta siya ma sa ta ji wayar a gida. Wato bai je da wayar ba ya bar ta a gida. Har aka yi sallar asuba ta tashi ta gabatar da sallar asuba, sanann ta zauna zaman yin azkar din safiya. _Makaho_ Ko da suka shigo cikin gari ana kiraye-korayen sallar asuba. Har bakin layin unguwar ya ce su kai shi, suna zuwa ya ce kada su shiga ciki su bar shi nan kawai. Suka bi umarnin sa suka tsaya ya sauka suka yi ma sa sallama cikin girmamawa. Ba kowa a farkon layin kasancewar asuba ce yanzu duk wanda ya fito daga gidansa masallaci yake shiga. Ganin ana shirin tayar da sahu ya sa ya samu ruwa a masallaci ya yi alwala ya yi sallah. Bayan an isar ne ya yi addu'a sanan ya fice, yau bai tsaya jiran sai gari ya waye sanan ya tafi gida ba. Da sauran duhu ya bar masallacin. Da sallama ya tura ƙofar fale-falen ya shiga cikin gidan. Tana jin sallamarsa ta fito da hanzari tana cewa. "Kana lafiya dai ko? Ba abun da ya same ka? Ya aka yi ka daɗe daga kai waya? Su ne suka tsayar da kai?" Haka ta dinga jera ma sa tambayoyi ya ma rasa me zai ce ma ta . "Ina son zan yi wanka.' Ya faɗa kamar wanda baya son yin magana. "To akwai ruwan zafi bari na zuba ma ka " Da hanzari ta juya jikinta har rawa yake yi tana kokarin sa ma sa ruwan zafi. Da kallon tausayi yake bin ta ta cikin bakin glass dake idanunsa. Girgiza kai ya yi yana maganar zuci. 'Wahalar ki ta kusa ƙarewa in sha Allah, za ki yi farin ciki a rayuwarki.' Sai da ta kai ma sa ruwan sannan ta dawo ta ɗauki sabukun wankansa ta kai ma sa. Ɗakin ya shiga ya ɗauki jallabiya a cikin kayansa ya nufi banɗaki don yin wankan. Ita kuma ta fara kokarin neman abun da za ta haɗa ma su na breakfast. Sai da ya gama wanka ya fito tana ganinsa ta karasa gabansa da sauri Sannan ta yi ma sa jagora zuwa cikin ɗaki . Ita kuma ta koma ta cigaba da aikinta. Zuwa karfe takwas ta gama komai, ko fa ta shiga dakin ta same shi ya kwanta bayan ya sauya kayan jikinsa, yana dafe da kansa ya ɗora hannu kamar wanda kansa ke ciwo. Fita wajen ta yi ba tare da ta tayar da shi ba ta cigaba da aikin gida, har kayan da ya dawo da su ta wanke, duk da ta ji wata takarda a aljihun wandonsa sai ta cire ba tare da ta warware takardar ba, ta je ta ajiye ma sa a saman wajen kayansa. Ta cigaba da aikinta. Har ta gama ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, ɗinkin stone work ya karɓe ta ya zauna ma ta ɗagwas a jiki. Turarenta ta shafa wanda ta siyo lokacin da ya ce ta siyo kayan abinci da kudin tallafin da aka ba su. Don haka ta siyo turare kasancewar nata ya ƙare wanda ta zo da shi daga gidan Mahaifinta, sai dai wanda ta siya bai kamata bwancan tsada ba. Ta yi la'akari da matsayin ta na yanzu da na baya ba daya ba ne. Tana gama ɗaura ɗankwali ya bude idanunsa a hankali tare da sauke su a kanta. Ba ta ma san ya bude idsnu ba ta cigaba da shirinta, ta saka ɗan kunne da sarƙa har da warwaro. Kansa yana ɗan yi ma sa ciwo don haka sai ya sake lumshe yana cike lips ga jikinsa da yake jin yana na ma sa ciwo. "Sorry, ba ka da lafiya ne?" Bude idanunsa ya yi sakamakon jin tambayar da ta yi ma sa. "Lafiya ta kalau." Ya yi maganar yana tashi tare da jingine bayansa da bangon ɗakin. Kafin ya mike yana cewa . "Zan samu ruwa mai zafi ba yi wanka da shi?" "Eh na saka ma ka na san yanzu ma ya yi zafi." Ta yi magana tana tashi zuwa waja, shi ma tashi ya yi ya fita zuwa banɗaki. "Wanka ya yi da ruwan zafin da ta kai ma sa ko da ta fito ta jera abun breakfast a tsakiyar ɗakin. Da sauri ta tashi tana rike sandarsa tana cewa . "Ka yi a hankali na ajiye abinci kafa ka ci karo da shi ka zubar." Murmushi ya yi a ƙasan ransa ya raɓa yana bin gefe. Fita ta yi daga cikin ɗakin sai da ta daidaici ya gama shirya wa sannan ta shigo da sallama. Yana tsaye yana saka boturan gaban rigarsa. "Bisimillah." Ta janyo hannunsa zuwa gaban abincin sanan ta ce ya zauna. Zama ya yi ta zuba ma sa kunun gyada da ƙosai wanda ta yi ma su shi a matsayin abincin kalaci. Bayan sun gama yin breakfast ne ya yi hamdala yana cewa . "Na gode sosai Allah ya yi ma ki albarka mar'atussaliha." "Amin Mijina." Fita ta yi ta kwshe kayan da zummar wankewa. Sai wsyarsa dake cikin aljihun sa ya yi haske. Kasancewar wayar a silent take, gudun kada Ma'eesha ta kula da wayar ta fara zarginsa. Messages ne ya yi reply ya mayar ta ajiye. Bayan awa daya ya fito daga gidan, bayan ta ce ma ta zai je wajen sana'ar sa ne na gyaran takami. A kan hanya yana tafiya kamar an ce ya ciro wayar, sai ya ciro daidai lokacin da kiran Yasmeen ke shigowa wayarsa. Ɗaga wa ya yi tare da cewa. "Hello." Murmushi mai sauti ta yi . "Surprise!" "For what?" "Na biyo ka garin da kake yanzu na sauka daga airport ka zo ka ɗauke ni?" Ta faɗa cikin shauƙi. "Ke wai kin yi hauka ne?" "Wallahi Yaya Jalal da gaske nake yi, na zo na gan ka ne ." "Yasmeen kin san me kike faɗa kuwa?" "Wallahi na sani kawai na yi missing naka ne shi ne na zo na gan ka kai ma ka ganni." Dafe goshin sa ya yi cike da takaici. "To yanzu da kika biyo ni me zan yi ma ki.' "Ganina za ka yi ma na, ga ni q nan fa ban san kowa ba kuma ban san garin ba ka zo don Allah." Ta yi magana kamar za ta yi kuka. "Ki juya ki koka in da kika fito." Kuka ta saka ma sa wanda hakan ya sa ya ji wani iri a jikinsa, don baya son jin kukan mace. "To yanzu zan kira wani na ba shi lambar ki zai zo ya ɗauke ki, zai kai ki hotel ɗin da nake kafin na zo." Ya yi magana ransa a ɓace ya kashe kiran wayar. Lambar yaronsa ya kira ya sanar da shi in da take sanan ya tura ma sa lambar wayarta. Ya kuma sanar ya je reception din hotel ɗin ya karbi key ya ba Yasmeen zai kira su ya sanar da su zuwanta. Ya kira hotel ɗin ya sanar da su idan yaron sa ya zo da Yasmeen a ba ta key din ɗakinsa ta shiga. "Lallai yarinyar nan sai na koya ma ta hankali, don ba ta da lissafi sam a rayuwarta, duk abun da ya zo kanta za ta aikata ne ba tare da yin tunani ba." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page7️⃣9️⃣ Lallai yarinyar nan sai na koya ma ta hankali, don ba ta da lissafi sam a rayuwarta, duk abun da ya zo kanta za ta aikata ne ba tare da yin tunani ba." Fasa zuwa wajan sana'ar sa da ya saba zama ya yi saboda dama wajen na kusa da gidan Daula ne, yana zama wajen ne yana kula da shige da ficen Daula da mutanen sa. "Yanzu sun riga sun san waye shi har suna farautar rayuwarsa, cigaba da zama a wajan hatsari ne ga rayuwarsa. Don haka ya kira mai nape ɗin sa, kasancewar cikin jama'a yake, idan ya ce zai kira yaronsa ya zo da mota ya dauke shi za'a fara zarginsa. Yana nan in da yake ya kira mai nape din ta sanar da shi in da yake. Ba komawa mai nape ɗin yazo da sauri saboda ya san yau ranar sa'a ce a gare shi. Don duk ranar da ya kira shi hotel kawai yake kai sa ya jira shi ko a awanni zai kwashe bai fito ba yana zaman jiransa. Sai dai idan ya tashi biyansa ranar zai ba shi kuɗaɗen da zai kai sati ɗaya kafin ya tara shi. Yana zuwa makaho ya shiga cikin keken bayan ta fara shigar da sandar jagoransa da kayan gyaran takalminsa. "Yallaɓai ina wuni." "Lafiya lau Alhamdulillah." "Ya aikin ya ƙoƙari?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah, ai tun da na ga kiran ka na ce yau ranar sa'a ce a gare ni." Bai tanka ma sa ba idanunsa na kan tayi yana tunanin wani abun daban. *KATSINA* Wani babban gida ne na alfarma, kallo ɗaya za ka yi wa gidan ka san cewa an narka dukiya wajen yin sa. Girman gidan ya kusan kai wani unguwa guda. Idan ka shiga cikin gidan kamar Estate ne, saboda gine-ginen dake ciki zai tabbatar ma ka da cewa gidan gidan iyali ne. Don duka gidajen da dake wajen duka iri ɗaya ne, komai hatta fenti da tsarin gidajen iri ɗaya ne. Gine-ginen guda huɗu ne komai Iri ɗaya ne, sai dai akwai wani babba wanda ya fi sauran girma, amma tsarin ɗaya ne. Alhaji Sulaiman Musa shi ne asalin mamallakin wajan, yana da mata biyu Hajiya Amina da Hajiya Maryam. Sai mahaifiyarsa wato Dada da take zaune tare da su, duk da gidan na ta na wajan amma ba ta zama ta tare tare de babban Ɗanta. Don ta tsufa sosai sai rigima. Yara uku Dada ta haifa namiji ɗaya mata biyu, mijinta ya rasu ya bar ma su tarin dukiya, duk da cewar kafin ya rasu ya raba wa ƴaƴansa kashi mafi tsoka na dukiyarsa. Don hatta jaririyar da aka sace yau shekaru arba'in kenanƊa na farko shi ne Alhaji Sulaiman Sauƙi, sai kuma sai ƙanwarsa Dr Fatima da take aure a Abuja, sai kuma ƴar autar su wacce aka sace ta tun tana jaririya. Yau shekaru talatin da biyar kenan Alhaji Sulaiman baban ɗansu wanda yake da mata guda biyu Hajiya Safiya da Hajiya Saratu. Yana da yara guda biyar. Uwar gidansa Hajiya Safiya ta haifa ma sa uku duka maza ne. Barrister Haidar shi ne babba sai Captain Kabeer wanda shi soja ne sai Mujahid wanda yake kasuwanci yana kula da harkokin mahaifinsu ita kuma Amaryarsa Hajiya Saratu ta haifa ma sa mata biyu. Lubna, Jamila. Su kuma suna karatu a University . Sai kuma Dr Fatima tana can a Abuja tana aure tare da iyalanta ita ma. Ta haifi yara guda uku. Jalaluddeen, Sadik da Saddiƙa. Sautin hayaniya ne ya kaure a ƙofar gate ɗin daga waje, wanda ana jin hayaniya har a cikin gidajen su. Alhaji Sulaiman Sauƙi ya duba CCTV camera ya hango abun da ke faruwa wani tsoho ne, wanda ya yi ma sa kama da wanda ya sani amma ya mance ina ya san mutumin. Hayaniya ce ta kaure kasancewar security din da ke gadin gate ɗin har mutane uku ne. Dada ce ta fito tana salati tana kiran Sulaiman ina kake me yake faruwa kar dai ace hari aka kawo ma na mu shiga uku. Wayyo Allah ga shi Soja baya nan a gidan yau ya tafi wani gari waye zai cece mu?" Tana maganar tana kokarin shiga karkashin kujera. Sauti m dariyar da ta ji Barrister Haidar na yi ne ya sa ta leƙo tana kallon su. Alhaji na gaba tana bin sa a baya yana yi wa Dada dariya. "Kai ka shiga hankalin ka mahaifiyar tawa ce kake yi wa dariyar shaƙiyanci ?" "Sorry Dad tuba nake yi ba zan sake ba." Ganin Ɗan nata da jikanta sun fita ne ya da tsoron ta ya rayu. Hajiya Safiya suka fito tare da Hajiya Saratu su ma suka rufawa mijin nasu baya. "Me yake faruwa ne?" Cewar Alhaji yana tambayar ɗaya security din wanda shi yana daga cikin gidan ne. "Alhaji wani tsoho ne kamar mahaukaci wai dole sai ya shigo cikin gidan nan " Ɗaya daga cikin security ne yake sanar da, maigidan. Dubansa ya maida kan wanan abun kafin ya sake cewa . "Bawan Allah lafiya kuwa?' Ya yi maganar yana kallon yanda goshin tsohon nan ya kumbura ya ya ja kalmar ba na shi na ba." "Tashi ka shiga ciki sai mu yi magana ko?" To na gode Alhaji Allah ya kara arziki., Gabaɗaya iyalan gidan suka hadu a babban gidan. " Shiru kowa ya yi yana jiran jiran jin abun da zai ce.. "Hajiya ba ki gane ni ba?" Sai a lokacin Da ta ce "Maude kai ne?" Ta yi magana cike da mamaki, ba ta gane shi ba saboda shekaru sun ja. "Eh ni ne Hajiya." "Ban ga mijinki ba Alhaji yana raye kuwa?" "Ya riga mu gidan gaskiya." "Allah ya jikansa." Gabaɗaya falon aka amsa da Amin. "Hajiya ina yaranki Sulaiman da Fatima?" "Ga Sulaiman nan zaune Nam duka iyalansa ne, Fatima na aure a Abuja." "Ina ƙanwar Fatima da kika haifa?" Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce . "Kodayake ba mai wanan amsar sai ni da na yi tambayar duk da na zo a ƙurarren lokaci." Ɗaya daga cikin. Masu aikin ne ta kawo ma sa abun sha da abinci a babansa. "Ban gane me kike nufi da ka fi kowa sani ba." "Tabbas na zo ne na sauke nauyin da ke kaina kuma na roƙi gafarar waɗan da na zalinta ko ba su yafe ma ni ba zan samu sassauci a zuciyata. "Me ka sani game da sace ma ni ƴa da aka yi shekaru talatin da biyar da suka wuce?" "Hajiya ki gafarce ni domin ni ne na sace maku jaririya shekarau talatin da biyar bayan, na kai ta gidan marayun a garin kaduna da hannuna na fita da ita daga ɗakinki. Sai dai ba da son raina na yi haka ba dole ce ta saka na aikata haka.?" "What?!" Cewar Captain Kabir da yake shigowa falon mahaifinsa sanye da kakinsa na sojoji a jikinsa. Ganin fuskarsa ya tsorata maude. Dad ya lura da mahaifiyarsa ta sume a wajen ba ta motsi. "Dada?!" Ya karasa kujerar da take zaune cikin tashin hankali. Kowa ya yi kanta ban da Captain Kabir dake jifan maude da mugun kallon da ya kusa saka shi fitsari a wando. _Yasmeen_ Bayan Makaho ya tura yaronsa ya ɗauko ta kai tsaye hotel ɗin da ya kama ya kai ta. Har reception suka karasa ya yi ma su bayanin cewa Jalaluddeen ne ya ce ya kawo ta Kasancewar shi ma ya kira su daga can ya sanar da su a ba su key. Karba yaron nasa ya yi ya kai ta har ƙofar ɗakin ya mika ma ta key ya bar wajan. Bude ƙofar ta yi ta shiga tana karewa ɗakin kallo. Murmushi ta yi tana cewa. "Yauwa Ya Jalal yanzu na ɗan samu rabin nutsuwa kafin ka ƙaraso. Wayarta ta ɗauka ta kira wayar da sai dai har ta katse bai ɗauka ba har sau uku bai ɗaga ba. Karshe ma ta ji wayar a kashe. "Na san dai dole za ka zo ka same ni nan." Ta yi maganar cike da farin ciki na zuwa kusa da shi. Bakin gadonsa ta zauna tana tunani kafin ta tashi ta shiga bathroom don yin wanka. Wanka ta yi sa sabulunsa mai ƙamshi wanda ta jima tana wanka tana jin ina ma a ce an yi auren su tare suke yin wanka. Bayan ta gama ta fito daga toilet ɗaure da towel.tana rera waka a bakinta. Gabatanta na ya fadi sakamakon ganinsa tashe bakin ƙofar ɗakin yana aika ma ta da wani mugun kallo. *Ku yi hakuri da wanan ba na da caji.*🙏🏻 *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣0️⃣ Bayan ta gama ta fito daga toilet ɗaure da towel tana rera waƙa a bakinta. Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganinsa tsaye a bakin ƙofar ɗakin yana aika ma ta da wani mugun kallo . Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana tura baki tare da zancen zuci. 'Mutimin nan fa ɗan yaw ne yanzu zai iya wulaƙanta ni, na yi dogon tafiya saboda shi amma yana zuwa ya rasa me zai tarbe ni da shi sai mugun kallo da harara." "Ki saka kaya ina zuwa nan da mintuna biyar. Yana fadar haka ya fita daga bedroom ɗin ya koma ya koma falo ya zauna. Zama ya yi kan kkujera yana nazarin aikin da ke gabansa. Yana nan zaune sai ya daidaici ta gama, don haka dai ya mike ya same ta tsaye daga gani tana cikin fargaba ne. "Me kika zo yi?" "Na zo na ganka saboda na yi missing naka ko barci me dadi bana iya yi shi ne na zo na kanka?" "Ummee ta san kin zo?" "Ba wanda ya sani ce m ta na yi zan je gidan Mom can zan kwana, saboda na san ba za ta hana..." "Okay wannan shi ne dalilin da ya da kiks zo ba tare da kin yi tunani ba ko?' "Wallahi na yi tunani sosai da sosai Ya...." Za ki rufe ma Ni baki ko sai na tattaka ki a wajan nan wawuyar banza kawai." Da sauri ta kalle shi kin kalmar da ya kira ta da shi na wawuyar banza kawai . Ganin yadda ransa ke ɓace ne ya da jikinta yin sanyi sosai. Ita s gurɓataccen tunanin ta zai ji dadin zuwan da ta yi ma sa ne, amma dai ga shi ta ga ransa ne ya ɓaci. Kuka take kokarin yi amma ya daka ma ta tsawa tare da yi ma ta gargaɗin idan ta yi kuka dai ya ma ta dukan da kuka ma sai ya gagare ta. Tana ji tana gani ta haɗiye kukanta tare da nadamar zuwa wajensa da ta yi. Ya ma rasa me zai ce ma ta ko me zai yi ma ta. "Kin yi magana da wani ne daga gida a waya bayan kin sauka?' "Na kashe watoyina duka ba wanda zai same ni." *ABUJA* _Saddiƙa_ Tsms zaune a falo ita da Mom wacce dawowar ta kenan daga asibiti. "Mom next week ne wai bikin wata ƙawar mu ban sani ba sai yau, wai auren haɗi ne za'ayi ma ta ." "Ayyah to Allah ya sa na yi a sa'a." "Amin ya Allah. Bari na kira Yasmeen na sanar da ita ko tekun ta zai samu yi ma na ɗinkin ankon bikin." Ta yi maganar tana lalubo lambar wayar Yasmeen. Tama kira aka sanar da ita wayar a kashe. "Mom kin ga wayar a kashe yake, bari na kira lambar Wayar Ummee na ce ta haɗa ni da Yasmeen." Ta lalubo lambar wayar Ummee ta danna ma ta kira, bugu biyi Ummee ta ɗauka . "Hello Saddiƙa." "Ina wuni Ummee." "Lafiya lau ya Mom ɗin taku take?" "Tana lafiya lau." "To ma sha Allah." "Ummee dama ina son magana da Yasmeen ne na kira wayarta ba ta ɗaga ba." "Ban gane ba, shin ba ke ce kika zo kika ɗauke ta kuka tafi gidan ku ba ta ce za ta kwana can?" "Ummee duk yau ba mu yi waya da ita ba wallahi?" Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. To ina ta je har da ɗaukar kaya?" Ta yi maganar tana Katse kiran wayar, lambar wayar Yasmeen ta kira switch off. Hankalinta ya tashi sosai ba kadan ba. Kusan duk lambar wayarta ta kira bai shiga ba. Daidai lokacin Abbi ya shigo gidan. Ganin yanayin ta ya sa ya tambaye ta lafiya. "Wallahi Yasmeen ce ta ce za ta je gidan Yaya ta kwana, to ban kawo komai ba saboda duk gida ne. Har take sanar da ni Sadduƙa ta zo yana jiran ta a waje da motar Saddiƙan za su tafi. To sai yanzu Saddiƙan ta kira wayata wai tana so ta yi magana da Yasmeen ta kira wayarta ba ta shiga ba. Na tambaya ta ba ta gama gidansu ta ce duk yau ba su yi waya ba ballantana su hadu." "To ina ta shiga ne?" "Wallahi ban sani ba." Nan ta dinga kiran wayar kewayen Yasmeen da ta san za ta iya zuwa gidajen su amma kowa ya ce ba ta je ba. Abbi ya ce wa Umme ta zo su tafi, da hanzari ta shiga ta ɗauko mayafi a ɗakinta sannan suka fito. A jarabar gidan suka hadu da Yusuf suka sanar da shi abun da ke faruwa. A motarsa suka tafi har zuwa gidan Alhaji Kabir arzika, wato mahaifin Jalaluddeen Kenan. Ko da suka shiga cikin falon sun tarar da Dad da Mom suna tattaunawa akan maganar rashin sanin in da Yasmeen take, ga Saddiƙa ta shiga tashin hankali. Ta rakuɓe a gefen sa, sai kuma Sadik da ta tsaya a bayansu. Da sallama suka shigo ciki, suka amsa ma su fuskar kowannen su ɗauke da damuwa. Gaisawa aka shiga yi tare da alhinin halin da aka shiga. Tun safe ga shi har yamma ta yi ba labarin in da ta je. Ummee ta kalli Yayan nata ta ce. "Yaya ban san inda za mu samo ta ba?" "Kin kira ƴan uwanki kin tambaye su?" "Yaya ba za ta je can ba, don ba wani son shiga mutane take yi ba, ba taɓa zuwa dan ra'ayin kanta ba, duk ranar da ta je to ni ce na saka ta dole. " Caraf Saddiƙa ta ce. "Allah ya sa ba wajan Yaya Jalal ta tafi ba." Kowa sai da ya kalle ta, kafin Sadiƙ ya ce. "Kin yi hauka ne? Me zai saka ta je wajan sa?" "A duk lokacin da muke fira da da ita tana yawan cewa ji take yi kamar ta shirya ta je garin da yake ta same shi. Ko kuma ta ce wai kamar ta bude ido ta ga an kai ta gidansa matsayin matarsa." "Bari na kira shi a waya." Cewar Sadik yana fito da wayarsa daga cikin aljihunsa. *Kaduna* Cikin kuka da sangarta take magana. "Yaya dama na faɗa ma ka ba so na kake yi ba ni ce nake son ka, amma ka ce kana so na kai ma, ko sau daya ba ka taba nuna mun kana so na ba, kamar dai dole aka yi ma ka ba son ranka ba. Tun yaushe na iso garin nan da safe na iso amma sai yamman nan ka zo wajena." Kallon ta ya yi na wasu sakanni yadda take kuka sanan ya kalli abincin da aka kawo ma ta daga hotel ɗin wanda ko taba shi ba ta yi ba. Zai yi magana ya ji wayar da na vibrating ya ciro ya duba. Sadik ne ke kiransa a waya, ya ɗaga wayar ya ce. "Hello Sadik ya aka yi?" "Yaya wai Yasmeen ta zo wajenka ne?" Sai da ya ɗauki sakanni kafin ya ce amsa a taƙaice. "Eh." Salatin da Ummee ta yi ne ya sauka a cikin kunnen Jalaluddeen. Taune lips din sa na ƙasa ya yi yana jin sa wani iri. Dad ne ya yi wa Sadik alamar ya ba shi wayar. Karba ya yi ya kara wayar a kunnensa. "Jalaluddeen." "Na'am Dad ina wuni?" "Lafiya lau ya aiki?" "Alhamdulillah." "Ma sha Allah, ka saurare ni da kyau ina fatan kana ji na?" "Eh ina ji Dad." "Yanzu a ina kuke ne?" "Muna hotel a ɗakin da nake zaune." "To ban yarda Yasmeen ta kwana a hotel ba, yanzu ka ɗauke ta ka kai ta gidan abokina Alhaji Tanko ta kwana a gidan ka kai ta har wajan matarsa, zan yi ma sa waya na sanar da shi zuwan ku kafin da safe ka je ka ɗauke ta ka kai ta airport ta dawo. Ka ba ta wayar zan yi magana da ita ." Sai da ya saka wayar a handsfree sanan ya miƙa ma ta wayar. "Hello Dad ina wuni?" "Yasmeen ina ma ki kallon mai hankali ashe ba haka ba? Ta ya za ki yi tafiya har wani gari baki sanar wa kowa na?" "Dad idan na faɗa ba barina za'ayi ba shi ya sa kuma na..." Kunya ya hana ta karasa maganar da take son yi. "To ki kwantar da hankalinki next week in sha Allah za'a ɗaura ma ku aure, idan ya so duk in da za ki bi shi ba damuwar mu ba ne." Murmushin jin dadi ta yi yayin da Jalaluddeen ya yi tsinci kansa a wani yanayin da ya kasa gane me yake ji, sai dai jikinsa ya yi matukar sanyi da jin hukuncin da Dad ya yanke. Miƙa ma sa wayar ta yi tana kallon fuskarsa. "Kana ji na ko?" "Eh ina ji Dad." "Dama kai ne ka kawo uzurin sai ka karasa aikin da kake yi kafin ayi auren ku, kuma wanan aikin naka ban san ranar da za ka kare shi ba, don za ka iya saka kanka wani aiki kamar yadda wani aikin ka gama sannan ka saka kanka na Daula ba mamaki daga nan shi wani za ka shiga. To ko ka gama ko ba ka gama ba in sha Allah ranar juma'a za'a ɗaura auren ka da Yasmeen. Ka tabbatar ka bar garin Kaduna ka halarci bikin ka. Idan ya so bayan bikin ruwanka ne ka kai ta garin da kake ko ka bar ta nan, ya fi ma na kwanciyar hankali da ace tana satar jiki tana zuwa kuna haɗuwa." "Shi kenan Dad ." Abin da ya iya cewa kenan sannan sukayi sallama ya kashe wayar. *KATSINA* Bayan Dada ta fardaɗo daga sumar da ta yi ne ta kalli wanann mutumin sanann ta kalli kowa ɗaya bayan ɗaya kama daga kan Alhaji, Hajiya Safiya, Hajiya Saratu, Barrister Haidar, Captain Kabeer, sai Mujahid wanda shigowar su kenan shi da Lubna da Jamila . "Amma me na yi ma ka da ka raba ni da jaririyata wacce ba ta san kanta ba, ka nisanta da mahaifiyarta a lokacin da take buƙatata." Kuka ta fashe da shi tana tsinewa Maude. Tsohon maigadinsu wanda ya yi ma su gadi shekaru arba'in baya da ya wuce. "Allah ya ɗebe ma ka albarka la'anannen Allah mai raba ɗa da uwa. Wallahi ba za ka ga annabin rahama ba." Alhaji Sulaiman ne ya rarrashe ta akan ta ya shiru su saurare shi su ji da abun da ya zo. Da ƙyar aka iya shawo kanta ta yi shiru tana aika wa Maude da kallon tsana. Wanda shi kuma ya galabaita ruwa yake kallo yana son ya ɗauka robot ruwan ya jiƙa maƙoshinsa amma ya kasa sanda kunya. Fahimtar hakan ya sa Alhaji Sulaiman cewa ya ɗauki ruwan sanyi ya sha. Hannunsa har rawa yake yi wajen ɗaukar robar ruwar ya ɓalle marfin ya sha. Bayan ta ya sha ya numfasa ya ce. "Haƙika haƙƙin ku ba zai bar ni ba, don Allah Hajiya ku gafarce ni, na so a ce n samu mahaifin jaririyar da na ɗaike shi ma na roƙe shi gafara. Wato na kasance mutum mai son kansa da yawa da kuma son zuciya. Ba komai ne ya saka na aikata hakan ba sai son ganin na cire matata a cikin damuwa Wato a lokacin da wanan abun ya faru ina yi ma ku gadi tun kafin ki haifi haifi Sulaiman, lokacin da kika haife shi sai na ji kamar a ce ni ma na zama uba. Kasancewar matata ba ta taɓa haihuwa ba. Har kika haifi Fatima lokacin na je Kaduna wajen matata nake sanar da ita kin sake haihuwa. Take ji kamar ita ce ta haihu. Har kuka take yi kan rashin haihuwa hakan muke neman magani amma ba mu dace ba. A duk lokacin da nake kallon yaranki Sulaiman da Fatima suna wasa a gidan nan ji nake kamar na sace su na gudu. Ana cikin wanan halin sai na koma Kaduna dama idan zan yi tafiya nikan turo ma ku wani Ɗan uwa na ne ya zo ya yi ma ku gadi zuwa ranar da zan dawo. Wata rana da dawo bayan na kwashe watanni biyu ina can, ranar da na dawo sai ban ga Ɗan uwana dake gadi a bakin gate ba. Kasancewar na ji an tayar da sallah a masallacin da ke kusa da ku na san ya tafi sallah ne. Don haka na shiga gidan kai tsaye, sai na zagaya ta baya sai nake jin sautin kukan jaririya. Wanda na leƙa ta window a na ga jaririyar kwance kan gado. Take zuciya ta raya na ɗauke ta na kai wa matata da na baro tana jego amma ba jariri ba ta haife shi da rai ba. Sai kawai na zagaya saboda na san irin lokacin ba kowa gida Alhaji na kasuwa yara suna Makarantar boko. Na shiga na tura ƙofar a hankali, jin saukar ruwa a banɗaki na fahimci wanka kike yi. Na ɗauke ta da sauri na saka cikin wata babbar jaka na cire Safar ƙafarta na saka ma ta a baki gudun kuka ya fito. Har na fita maigadi bai dawo masallaci ba. A hanya na haɗu da wata mata na ce ma ta ta taimaka ta biyo ni ta rike jaririyar nan muna sauka a gare ki sai ta juya ta dawo mu je Kaduna zan ba ta ko nawa take so. Na ɗebi kuɗin da ke aljihuna ma su yawa na ba ta. Ta kalli jaririyar ta kalli kudin sai ta amince ta kebe ta muka tafi a matsayin ita ce mai jaririyar . Sai dai muna sauka a Kaduna ta nemi motar da zai koka Katsina ta shiga ciki. Na nufi gidana da jaririyar sai dai nuna zuwa na tatar da labarin mutuwar matata. Na shiga tashin hankali sosai. Na rasa yadda zan yi da jaririyar sai na kira abokina dake unguwar mu kuma yana aiki a gidan marayu, sai na mika masa jaririyar na ce ya kai ta gidan marayu ta tashi a can . Don ban isa na koma da ita wajan iyayenta ba . Wanan shi ne Abun da ya faru shekaru arba'in da suka wuce. Yarinyar da ya kamata ta tashi cikin gata da kulawar iyaye amma ta tsinci kanta a gidan marayu. Yarinyar da iyayenta suke taimakawa suke ciyar da bayin Allah ta tashi a inda sai an kawo taimako sanan ta samu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣1️⃣ "Yarinyar da ya kamata a ce ta tashi cikin gata da kulawar iyaye amma ta tsinci kanta a gidan marayu. Yarinyar da iyayen suke taimakawa suke ciyar da bayin Allah ta tashi a in da sai an kawo taimako sannan ta samu." Kuka ne yake yi yana tari wanda ko a hanya ka gan shi sai ka tausaya ma sa. "Daga na kuma sai me ya faru?" Captain Kabeer ya yi tambayar bayan ya ga tarin ya tsagaita ma sa. "Eh to nikan tambayi halin da yarinyar take ciki, yana sanar da ni tana cikin kishin lafiya . Har zuwa lokacin da yarinyar ta cika shekaru goma sha Bakwai, aka yi ma ta aure, hankali na ya tashi da na ji labarin, amma kasancewar na ji an ce shi wanda ya aure ta mahaifinsa ne yake ɗaukar nauyin kaso saba'in na gidauniyar marayun. Kuma sanannen mutum ne ya yi suna Mutumin kirki ne daga nan hankalina ya kwanta. Sau tari nikan ji kamar na dawo m ku da ƴarku tun da wacce na kai wa jaririyar Allah ya karɓi rayuwarta. Amma gani nake za ku hukunta ni don ban san matakin da za ku ɗauka a kaina ba. Ga shi dama ba wanda ya san ni na sace jaririyar, ko da muka haɗu da Ɗan uwana da na bari yana ma ku gadi na bugu cikinsa ta hanyar tambayar ya kuke ya yaran ku zuwan yanzu yaranki nawa? Sai yake sanar da ni iya Sulaiman da Fatima ne kun sake haihuwa aka sace jaririyar har yau ba'a san waye ya sace ta ba. Haka na cigaba da rayuwa ta duk da ba na cikin natsuwa yadda ya kamata har na yi wani auren matata ta haifa ma ni yara biyar. Duk da auren sake jefa ni cikin tashin hankali ya yi sakamakon bana da kwanciyar hankali ga matata masifafdiya mulkin sake sakani damuwa take yi. Ga bakin cikin yaran da na haifa da sam ba sa jin magana. A haka dai wata rana na ji labarin yarinyar da na kai gidan marayu har ta haihu ta haifi ƴa mace sunan jaririyar Ma'eesha, wato ita jikar taku ce Ma'eesha. Daga nan ban sake jin halin da suke ciki ba sakamakon mai sanar da ni Allah ya yi ma sa rasuwa. " Shiru falon ya ɗauka idan ban da ajiyar zuciyar da Dada ke yi, dama ita tana ji a jikinta ƴarta tana raye sai dai ba ta san in da za ta samo ta ba. Shi ya sa ko fa mahaifin yaran nata kafin ya rasu ya tashi rabawa yaransa dukiyarsa ta ce ya raba har da Babyn da aka sace wata rana Allah zai bayyana ma su ita, har yake cewa yau shekaru talatin da biyar ba wanda ya sani tana raye ko tana mace. Amma duk da haka ya raba aka ajiye ma ta kason ta yau shekaru biyar kenan. "Yanzu idan har muka je wajen shi mahaifin da ya aura wa Ɗan sa ƴar uwar mu za mu same shi yana raye?" Cewar Alhaji Sulaiman sauƙi. Tabbas yana raye sai dai baya ƙasar. Amma na tabbatar matarsa na nan garin Kaduna har gidansa na sani saboda ba ɓoyayyen mutum ba ne." Sai a lokacin Barrister Haidar ya yi magana ya ce . "Ina ganin ba can ya kamata mu fara dosa ba. Shi wanda ya kai yarinyar gidan marayu za mu je da shi, na san gidan marayun dole sai ya bayar da sunan sa da ranar da ya kai yarinyar da komai da photonsa an tabbatar shi ne kafin su ne za su hada mu da asalin wanda ya dauki yarinyar." Jinjina kai ya yi "Tabbas an yi haka sai da suka yi ma ni tambayoyi na samar da su tsintar ta na yi, sai da aka karbi sunana da passport ɗina aka yi cike-cike sanan suka karɓe ta, suna da ƙa'ida da tsari." "To me muke jira maza ku dauko motoci mu kama hanya!" Cewar Dada jikinta har rawa yake yi . "Kin ga ki kwantar da hankalinki Dada, yanzu yamma ta yi ki bari gobe da asuba mu za mu tafi ni da Kabeer da Haidar." Ɗaura hannu aka ta yi ta fashe da kuka . "Anya Sulaiman kana farin ciki da bayyanar ƴar uwarka kuwa? Ta ya zamu bari sai gobe sannan ka ce wai ba da ni za'a je ba to da waye za'a je idan na da uwarta ba?" "Ba haka nake nufi ba Dada, kin ga dare zai ma na a hanya kuma yanzu ba samun jirgi da zai tafi Kaduna ba zai yiwu ba. Don haka tun da ba wai an ganta ba ne, bincike za'ayi sai mun fara zuwa gidan marayun an bincika an tabbatar aka hada mu da mutumin ya hada mu da iyalansa muka tabbatar da gaskiyar magana sai a ɗauko ki ki zo ku mu kawo ma ki su." "Yanzu kana nufin kai da Soja da Lauya ne za ku tafi?" "Eh in sha Allah, daga baya sai ki ganta idan an tabbatar." Da ƙyar aka shawo kanta ta yarda akan za ta zauna , gobe sai su kama hanyar zuwa Kaduna tare da Maude da zai ma su jagora. BQ aka kai Maude ya zauna aka kai ma sa abinci da ruwa . _Nadra_ Fitowar ta kenan daga wanka tana ɗaure sa babban towel da kuma wani ƙarami a hannunta tana tsane ruwan da ke kanta. Handrayer ta jona a socket ta nusar da ruwan dake ya jiƙa ma ta kai. Man shafawarta ta shafa da turaren jiki mai sanyin ƙamshi. Dama ita ba ma'abociya yin makeup ba ne. Tana kokarin shiga closet ɗin kayanta sai ta ji ƙarar buɗe kofa, Fahad ne ya shigo bakinsa dauke da sallama. Ta amsa tana kallonsa, sanye yake da wando three quarter da ƙaramar riga sai ƙamshin turarensa mai daɗin ƙamshi yake yi. Ɗaya daga cikin akwatin kayan lefe ya ɗauko daga cikin closet ɗin. Ƙananun kaya ne a ciki, irin ma su nuna jikin nan da kuma marasa nauyi. Don wasu kayan ma gani take da su da babu duk daya ne . Tana kallon da ya fito da wata figaggiyar riga da siket. Rigar kamar bra take daga sama kasan rigar ma duk saukan rigar ba za ta rufe cibiya ba. Siket din kayan iya rabin cinya zai tsaya ma ta. Mika ma ta rigar ya yi tana cewa . "Daga yau idan ina gida irin wanan kayayyakin nake bukatar ki dinga saka ma ni ina gani. Dan gaskiya na gaji da ganin kullum cikin manyan kaya da Abaya. Ke da saka su sai dai idan fita za ki yi ko kuma ba na gidan . Idan kin ji sallamar baƙi ki saka hijabi kawai . Kallon kayan take yi ba ta karɓa ba, take sai jikinta ya yi sanyi sakamakon tuna Sidra da ta yi wacce da ba don ƙaddara ta ƙaddaro cewa ita ba matar Fahad ba ne da yanzu ita ce a matsayinta. Tuna yadda Sidra da Fahad suka je kasuwa suka yo siyayyan kayan ta yi, tana tuna yadda Sidra take ba Sady baby labarin irin kananan kayan da ta siyo wanda banbancin su da babu kadan ne. Da ƴan iskan kayan barcin da suka zaɓo ita da Fahad ma su bayyana jiki. Ko rigar da yake ba ta ba ta sake kallo ba don ta san shi da Sidra suka zaɓo shi don ta burge shi. Har ta buɗe baki da niyyar yi wa Fahad zancen Sidra sai ta tuna ya ce baya son tana maganar Sidra don haka sai ta fasa. Amma jikinta ya yi sanyi sosai tuna cewa wannan kayan fa da sunan Sidra aka siye shi ko ma ita ta zaɓe shi amma yanzu ita ce za ta yi amfani da shi. "Tunanin me kike yi?" "Ba komai." Murmushi ya yi yana cewa. "Ina fatan kin gane me nake nufi ko? Na fi son kananan kaya matata za ta dinga saka min dan haka ki saba." Shiru ya yi tana rike da kayan ba ta saka ba "Bari na saka ma ki tin da baki iya sakawa ba ." Jin haka ya sa ta yi saurin cewa. "Zan saka da kaina." ,"okay ina jiran ki a falo." Ya fada yana ficewa daga ɗakin . Dole ta bi umarnin sa ta saka kayan, amma sai ta ji ba za ta iya fita da shi ya ganta a haka ba. Sai ta ɗauki dogon hijqbi ta saka tana tafiya a hankali kanta ƙasa kamar munafuka. Jin ƙarar kofar ya sa ya juyo yana washe baki, take fara'ar fuskarsa ta ɗauke yana kallon ta cikin hijabi take ya tsuke fuska. _Sidra_ Da maɗaukacin mamaki take kallon matashin malamin. Duk da cewar ba zai haura shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba, amma ta yi mamakin jin kalamansa. Sanan kuma Sady baby ba ta damu ba. "Mallam ka san me kake faɗa kuwa ?" "Ke Mallama idan har zan yi ma ki aiki to fa ba zan karbi kudin ki ba, jikinki kawai nake so ki bani haɗin kai ku ga aiki da cikawa ." "Wai ƙawata ba ki ji me yake cewa ne? Wai sai ya yi lalata da ni fa?" 'Eh yi meye ai idan bukata za ta biya ba wani abu ba ne , ku tuna Fahda kike so ba kowa ba kuma za ki mallakar shi sai yadda kika yi da shi a rafin hannunki don haka ki Amince kawai kamar biya ma sa bukata shi ma ya ya ma ki aiki ki ga biyan buƙatar. Idan kuma ba ki aminci ba ba to ba wani Mallam da na sani sai dai ki koma gida ki je a kai kuma ƙauye a aura ma ki ɗan kauye ku je can ku ƙarata ki lalace. Tana faɗar haka ta fita waje ta janyo ma su ƙofa ta koma cikin mota tana jiran su gama abun da za su yi . _Jalaluddeen_ Tun bayan jin hukuncin mahaifinsa jikinsa ya yi sanyi da hukuncin, domin shirin sa ta gama wargaje wa shirin sa ya lalace. Kallon Yasmeen ya yi wacce farin ciki ya cika ta da jin zancen Dad din. "Za ki tashi mu tafi kuwa?" Da sauri ta tattara kayanta ta shirya tana murmushi. "Hankalinki ya kwanta ko?" "Abun da kike so kin samu hankalin ki ya kwanta ko?" Murmushi kawai ta yi ta nufa hanyar fita daga ɗakin ta fice. Sai da ya dauki sakanni sannan ya samu zarafin fita daga cikin ɗakin ya fice kai tsaye. Tana jiransa a gefe ya ganta daga nan suka fice a tare. Bayan ya ba d key din ɗakin ya yi gaba tana bin sa a baya har suka fice daga hotel ɗin . Kai tsaye gidan Alhaji Tanko Abokin Dad ya kai ta. Yana zaune a bayan motar shi da Yasmeen sai yaronsa dake driving motar . Shi ya nuna wa yaron hanyar gidan kasancewar ya taba zuwa sau ɗaya, wani zuwa da Dad ya yi ɗaurin auren ƴar Alhaji Tanko, ya kira Jalaluddeen ya sanar da shi yana garin, shi ne Jalaluddeen ya zo bisa kwantancen da Dad ya ma sa . Bayan ya yi horn a ƙofar gidan ne maigadi ya leƙo ya ƙaraso wajen motat ba tare da ya bude gate ɗin ba ta karamar ƙofa ya fito. "Assalamu alaikum." "Wa'alaiki salam." "Don Allah waye kai Yallaɓai an ce na tambaya ne?" "Jalaluddeen ne" Ya faɗa daga bayan Motar da yake . Da sauri Maigadi ya wangale ma su gate suka shiga ciki. Jalaluddeen ya fito bayan direban ya yi parking, ita ma ta fito riƙe da jakarta. Direban na bayan motar yana jiransu yayin da suka nufi main door din gidan . Ya kai hannu zai danna ƙararrawar kofar kenan sai ga ɗaya daga cikin ƴan matan gidan ta buge ƙogar za ta fito. Idanunta ya sauka akan Jalaluddeen, ta zuba ma sa idanu tana kallon sa ita ba ta matsa ta ba shi hanya ba. Sai da Yasmeen ta dawo ta tsaya gaban Jalaluddeen sanan wanan budurwar ta ɗauke ido yana barin wajen cike da kunya. Da sallama suka shiga Alhajin yana falo tare da matarsa . Bayan sun gaisa ya sanar da shi saƙon Dad, Alhajin ya ce Dad ya sanar da shi ba damuwa zai iya tafi gobe sai ya zo ya kai ta airport. Sallama ya yi ma su ya fita yayin da matar gidan ta ƙwalawa ɗaya daga cikin yarinya kiraz ta fito Nam ta sanar da ita je da Yasmeen ɗakinta su kwana zuwa gobe. Tashi Yasmeen ta yi ta bi bayan yarinyar wacce ta ɗauki kakar kayan . Jalaluddeen na cikin mota sai kiram Ma'eesha ya shigo wayar. Bayan ya ɗaga ne ta nemi izinin fita gidan Mallam Liman ana biki sam ta mance sai kusan yamma ta tuna shi ne ta kira shi da yamman . Ya ba ta izinin fita sanan ta yi godiya ta katse kiran wayar. Kai tsaye hanyar gida ya ce wa yaronsa ya kai shi. A bakin layin ya sauka ya dauki sandarsa a bayan motar ya yi wa yaron sallama sannan ta fara tafi zuwa cikin layinz don can baya ta sauka sau da ta tabbatar ba mai ganinsa ta fito da sauri. Tafiya yake yi cike da damuwa, ya so kafin a tayar da zancen aurensa da Yasmeen ya sanar da su auren Ma'eesha da ya yi, ga shi zuwan Yasmeen ta lalata ma sa shiri. A haka ya karasa cikin damuwa har cikin gidan, ba ta nan kasancewar ya san in da take ajiye key kan window ne sai ya ɗauka ya buɗe kofar. Ya shiga ciki tana safa da marwa a cikin ɗakin Vibrating na wayarsa ya ji daga cikin aljihu, ya ɗauka Dad ne, amma sai ya ga abokin sa Khalil ne . Ya amsa sallamar bayan ya daga wayar. Daga cikin wayar abokin ke cewa. "Ya na ji muryarka wani iri?" "Dole ka ji muryata wani iri ma na, wai ranar jama'a ne aurena da Yasmeen." "To me ye na damuwa bayan ka san da wanan zancen ba tun yau ba, ka sanar wa abokanmu kawai Malam . "Ba wanda zan sanar, dama ka san ba wai na fiye yawan mu'amala da aboka ba ne." Daidai lokacin da Ma'eesha ke shigowa gidan, sakamakon tuna zai iya dawowa ga yamma ta yi lokacin dawowarsa ne, don haka ba ta zauna s gidan bikin ba ta ma su Allah sanya alkhairi ta dawo don ta tarbi mijinta. Cak ta tsaya bakin ƙofar sakamakon jin muryarsa yana cewa. "Rabo na da wasu abokan fa tun da muka gama karatu a America ban sake haduwa da su ba, sai dai wani lokaci da na je London na haɗu da su Faisal a can . Sai kuma Ahmad da ya matsa sai na je bikinsa to a lokacin na tafi ƙasar Canada. Daga nan ban sake bi ta kansu ba, sai yanzu kawai dai na kira su na sanar da su cewa ranar Juma'a ne ɗaurin aure na da Yasmeen? Ba wani gayyatar da zan yi kai ma ɗan ka kira ni ne kuma ban ce ka ma ni gayya ba, ba abun da za'ayi daga an ɗaura auren shi kenan kowa ya watsa ba ruwana da wani events ko wani bidi'a." Kalamansa sun matukar gigita ƙwaƙwalwar Ma'eeha wanda ta ji wani jiri na ɗibarta ga numfashinta dake barazanar ɗaukewa. Kalaman da ta ji tana yi ne suke ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta kamar za su fasa ma ta dodon kunnen. "Dad ya ce na bar garin nan dole na koma Abuja na halarci bikin aurena da..." Kafin ya karasa maganarsa ya ji faɗuwar abu kada tim. Da hanzari ya daki wayar kasa ya fito da sauri, Ma'eeha ya gani kwance kada ba ta numfashi." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣2️⃣ "Dad ya ce na bar garin nan dole na koma Abuja na halarci bikin aurena da..." Kafin ya karasa maganarsa ya ji faɗuwar abu kasa "Tim." Da hanzari ya saki wayar ƙasa ya fito da sauri. Ma'eesha ya gani kwance kasa ba ta numfashi. Taune lips ɗin sa ya yi har sai da ya fashe jini ya fito, ya san ta ji komai kuma yadda ta ji ta wanan hanyar zai yi wuya ta fahimce shi. Ƙarasawa ya yi wajan da take ya dauke ta ya shiga ɗakin da ita. Ruwa ya yayyafa ma ta amma ba ta farfaɗo ba. Sau uku yana zuba ma ta ruwa ba ta farfaɗo ba. Don haka hankalinsa ya fara tashi ya ɗsuki wayarsa ya danna ma wata lamba kira. Bayan an ɗaga kiran wayar ne ya yi magana cikin bayar da umarni ya ce. "Ka zo karamin gidan da nake kwana yanzu-yanzu." Daga haka ya katse kiran wayar yana Safa da marwa a cikin dakin. Tsayuwar motar da ya ji a kofar gidan ne ya sa ya ɗauko hijab ya saka ma ta sanan ya dauke ta ya nufi hanyar fita daga gidan . Yaronsa na ganinsa ya bude bayan motar da sauri, yayin da Jalaluddeen kwantar da ita s bayan motar. Sanan ya koma ciki ya ɗauki wayarsa ya rufe gidan suka bar unguwar. A saman cinyarsa ya dora kanta yana kallon fuskarta. Wani tsadadden asibiti aka nufa da ita a nan cikin garin . Yana parking din motar Jalaluddeen ya fito da sauri ya dauke ta ya nufi ciki da ita . Emergency aka kai ta likitoci biyu suka tsaya a kanta. Sai Safa da marwa Jalaluddeen yake yi gabaɗaya ya rasa nutsuwarsa. Kiran sallar magrib da ake yi ne ya sa shi fita zuwa masallacin dake jikin asibitin. _Sidra_ Tana ganin Sady baby ta fita ta tsaya tana nazari . "Kin ga Mallama ba dole sai kin amince taimaka ma ki zan yi ki auri wanda kike so, ku yi rayuwa na har abada ki mallake shi sai yadda kika yi da shi, komai zai yi sai da izininki. Idan muka ba ki son shi ki haƙura kawai ma na ." "Ba zan iya hakura da Fahad ba." Jin ta yi shiru alamar amincewa ya yi murmushi yana shafa siririn gemunsa. Tura ƙofar ɗakin ya yi ya sa sakata ya rufe window. Tana ji tana gani ya umarce ta da ta cire kayanta, ba ta yi musu ba ta cire kayan kamar yadda ya buƙata. Idanunta ta rintse tana hawaye, a yadda ta tsara rayuwar ta da Fahad a daren farkon auren su amma yanzu duk ya rushe ga wani banza nan zai raba ta da mutuncinta na ƴa mace. Ƙara ta saki lokacin da ya shige ta da ƙarfi sakamakon azabtar da ta ji. Sanin asirinsa zai iya tonuwa ne ya sa ya saka hannu ya toshe ma ta baki, ta yadda muryaryarta ba zai fita ba. Hawaye kawai take ya babu sautin kukan baya fita ya toshe bakin. Sai da ya biya buƙatsrsa sanan ya bar ta nan kwance. Kayan jikinsa ya saka sannan ya kunna hasken ya ganta jini ya ɓata ma ta jiki. tishu fefa ya yago ya mika ma ta. "Karɓi ki saka cikin pant ɗin ki kada jinin ya ɓata ma ki kaya." Kakan takaici da nadama ta saki a lokacin da bai da amfani. Karɓa ta yi ta saka ta mayar da kayan jikinta, ba ta iya tafiya sosai haka ta ke ɗingisa ƙafa ta fita idanunta a kumbure. Sady baby na ganin tafiyar ta san aikin gama ya gama . Murmushi ta yi wanda ita kadai ta san ma'anarsa. Tabbas ta ji farin cikin rasa budircin Sidra, domin kuwa dama burinta ta ga rayuwar Sidra ta lalace. Ba ƙaunar Sidra take yi ba, hasalima tsanarta ta yi. Ba ta son ganin rayuwarta ta inganta. Bayan ita ma tana son Fahad din amma ko da ba ta son sa ba za ta bari ta ga rayuwarta ta yi kyau ba. Shi ya sa ta ba ta shawara ta gudu ranar aurenta gara ta samu ɗaukaka ta yi suna lokacin kowa zai ƙaunace ta fiye da yadda take, kuma hakan zai sa ta rama wulaƙanci da aka yi ma ta. Tabbas Sidra ta yarda Sady baby mai ƙaunarta ce yake ɗaukar shawararta. Duk da halin da ya shiga bai ishe ta ba sai da ta saka ta rasa budurcinta. Tafiya Sidra ke yi tana hawaye. Da sauri Sady baby ta fito daga motar ta taimaka ma ta ta shiga. Sanan ta bar ta cikin motar ta koma wajen Mallamin nata. Bayan kamar mintuna goma ta dawo ta ce. "Ya ce daren yau zai fara aiki akan Fahad din, jibi zan zo na karbi maganin da zan kawo ma ki ki yi amfani da shi." Ba ta ce ma ta komai ba illa hawayen da take yi . "Mu je na ajiye ki gida ne ko gidana za mu je?" "Gidanmu za ki kai ni." "Okay to, idan kin je ki gasa jikinki sosai da ruwan ɗumi ki zauna ciki, sanan ki bi kofar baya kada wani ya ga shiganki, ki tabbatar sai kin gasa jiki kafin ki fita wajan iyayenki, idan so samu ne ki kwanta kawai sai da safe." Ba ta ce ma ta komai ba ta cigaba da goge hawayenta, dansani take yi da ba amfani . _Jalaluddeen_ Har ya dawo masallaci sallar isha'i amma ba Ma'eesha ba ta farfaɗo ba, ganin yadda ya tayar da hankali ne ya sa suka kwantar ma da da hankali. Ko ruwa bai saka a cikinsa ba ballantana abinci . Da misalin karfe goma sha ɗaya na dare ne yana zaune s kan kujera ya zuba ma ta idanu. A hankali ta fara motsa ƙafarta sanan hannunta. Zuwa can ta sauke idanunta akansa. Tana kallon sa sai ta rintse idanunta da ƙarfi, hawaye na zuba a idanunta ba abun da take tunawa illah maganar Nasreen da take ta kokarin fahimtar da ita akan sanin waye asalin mijinta, amma sai take ganin laifin Nasreen tana kalubalantar ta ashe tana da gaskiya ita ce ta ƙi ta fahimce ta. Ganin ta farfaɗo ya saka shi sakin murmushi. "Ma'eesha sannu ko?" Wani takaici ne ya sake cika ta har ya fashe da kuka. "Ka yi nisa da inda nake ba na ƙaunar ganin ka, ka san yadda na tsani maƙaryaci da mayaudari kuwa? Ashe kai na kama da laifin da na fi tsana a rayuwata? Da a mafarki na yi wanan mafarkin idan na tashi sai na yi sadaka. Dama na faɗa ma ka duk ranar da na gane ka yi ma ni ƙarya za mu samu matsala, ƙarshen rabuwa ta da kai kuma ya zo. Dama Nasreen gaskiya take faɗa mun cewa kai ba Makaho ba ne basaja kake yi kama raina wa mutane hankali. Abun takaici ma har da ni da ban cancanci ka ɓoye ma komai ba. Na yarda da kai fiye da kowa. Kau da kanta gefe ta yi don ba ta so magana da shi. Ko ganinsa ba ta son yi. Ƙoƙarin tashi zaune take yi duk da kanta na Sara ma ta da ciwo amma ta daure, tana ƙoƙarin taimaka ma ta sai ta ɗaga ma sa hannu alamar dakatar wa. "Kada ka taɓa Ni!" Ta jingina da kyau sannan ta juya ta kalle shi cikin ido, cike da ƙunar rai ta ce. "Zan yi ma ka wasu tambayoyi ka ba ni amsa, wannan karon kafa ka kuskura ka ce za ka yi ma ni ƙarya." "Meye sunanka daga wani gari kake?" "Sunana Jalaluddeen Kabir Arzika, daga Abuja, kuma ni...?" Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar ya isa . "Da gaske kai Nasreen ta gani a Abuja tare da wata mace har ta kawo ma ni photon amma na ƙaryata ta bayan ka ce Maiduguri za ka tafi wajen wajen dangin ka amma ka je Abuja?" "Eh nine." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. Nasreen na yi nadamar rashin yarda da ke tun farko ku yi hakuri don Allah." Kauka ne ya ci ƙwrfinta, da zaran ya zo zai taɓa ta sai ta dakatar da shi da hannu. Ɗan tsagaita kukan ta yi kafin ta ce . "Maganar da na ji kana ya a waya da gaske ne ranar juma'a kai ne wanda za'a ɗaurawa aure ta wata mace? " Shiru ya yi kansa a ƙasa don amsar ta yi ma sa nauyi ya faɗa. "Faɗa mun kai ne?" "Eh ni ne amma wallahi ba da..." "Ya isa!" Ta daka ma sa tsawar da sai da ya yi mamaki. "Ba na bukar sake jin komai daga gare ka, iya abun da nake so na sani kenan kuma na sani, saura abu guda nake umartar ka da ka yi ma ni." "Mene ne shi?" "Ka sake ni saboda dama auren namu bai da amfani ba shi da banbanci da babu, sunan aure ne kawai amma ba rayuwar aure muke yi ba, yanzu na fahimci dama ba ja so na kana da wacce ja shirya rayuwar aure da ita, shi ya sa a zamantakewarmu ba ka taɓa nuna mun alamar soyayya ko wani abu da zan yadda kana so na ba. Don Allah ka sake ni." "Ba zan iya sakinki ba Ma'eesha, da za ki bani dama ki saurare ni mu fahimci juna za ki gane ..." "Ba za ka sake ni ba ko? To shi kenan za mu gani. Babu wani dama da xan ba ka na sauraren ka. Da a baya ne ko zan iya sauraren ka saboda na yarda ba za ka yi ma ni ƙarya ba, amma yanzu da gane gaskiya ne wallahi, wallahi, wallahi , ba wata magana da za ta fito daga bakinka na yarda da kai . Ban taɓa danasanin saninka a rayuwata ba sai yau. Na yi danasanin saninka a rayuwata , na yi nadamar zama da kai. Ban taɓa ganin ka da muni ba sai yau, ban taba jin muryar da na tsani ji kamar Muryar ka ba a yau na tsane ka wallahi,. Maƙaryaci, mayaudari...' Kula ne ya ci karfinta sosai har yake ihu tana dukan katifa tana kuka mai cin rai Doctor ne ya shigo yaga halin ta take ciki da yadda take cewa Jalaluddeen ya fita . Lura fay hakan ya sa ya ce ma Jalaluddeen ya fita. Yadda yake ta Surutai duk ta rikice ya da Doctor ya kira nurse ta yi ma ta allurar barci. Sai da ta yi barci sannan suka fita daga ɗakin. Lokacin karfe sha biyun dare. Doctor Kamal ya tafi gida ita nurse ta tsaya a asibitin. *KATSINA* Washegari Bsyan sun sun yi wanka sun yi breakfast suka shirya don zuwa Kaduna. Maude ma an kai ma sa breakfast ɗinsa da sabbin kayan da idan ya yi wanka zai saka, Alhaji Sulaiman ne ya aika ma sa da kayan nasa. Ya yi wanka ya shirya kamar ba shi ba. Ya fito yana jiran fitowar su. Captain Kabeer da Barrister Haidar ne suka fara fitowa. Maude duk da tsufarsa ya durƙsmusa yana gaishe su. Barrister Haidar ne ya amsa Amma Captain Kabeer ma ko kallo bai ishe shi ba ballantana ya amsa . "Amma ba dai da motata za'a tafi da wanan abun ba ko?" Cewar Kabeer yana yi wa Maude wani wulakantaccen kallo. "To Amma da motar ka Alhaji ya ce za mu tafi." "Wanan mutumin ba zai shigar ma ni mota ba wallahi sai dai motarka?" "Anya Kabeer ka san darajar Ɗan adam kuwa?" "Wani irin tambaya ne kake ma ni Yaya Haidar, shi ya san darajar mutane ne, da za'a ba ni dama sai na kashe shi. Amma bari mu gama abun da muke so dai ya gwammace mutuwarsa da rayuwarsa." Cikin Maude ya ɗuri ruwa wani tson wanan sojan ya shige shi lokaci guda. "Shi kenan a tafi da Motata, bari na je na ɗauko makullinta." Ya yi maganar yana tafiya zuwa ɗauko key din motarsa. Dadai sauran mutanen gidan na fitowa. Alhaji Sulaiman da Mahaifiyarsa yana sake kwantar ma ta da hankali. A gefe Hajiya Safiya da Hajiya Saratu ne , sai Lubna da Jamila. A baya kuma Mujahid ne wanda zai wakilci Alhaji Sulaiman yau a wani zama da za su yi da abokan Harkokinsu. "Ina kuma za ka tafi?" "Zan ɗauko key din motata ne." "Ba da miyar Kabeer za mu tafi ba " "Motata za ta fi bari na ɗauko ." "Kafin Ya yi wani magana har ya wuce da sauri." "Ko kuma baƙin halinsa ya sa ya ce ba za'a tafi ma sa da mota ba ,in dai Kabeer ne shi ya fi komai sauki a wajensa bai da mutunci." Cewar Dada tana tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa. Suna isa sai ga Haidar ya iso da key din motar, ya bude wa Mahaifinsu bayan motar ya shiga, sanan ya ce Maude ya shiga gefe. Yayin da shi ya shiga mazaunin direba. Kabeer ya zaune gefensa wajen me zaman banza. Allah kiyaye hanaya aka yi ma su tare da addu'a Allah ya bayyanar da su. Da amin suka amsa. Horn ya danna maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fita, har sai da aka rufe gate mutanen gidan suka koma ciki suna addu'ar Allah ya sa a gane inda suke cikin gaggawa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣3️⃣ Horn ya danna maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fita, har sai da aka rufe gate gate mutanen gidan suka koma ciki suna addu'ar Allah ya sa a gane in da suke cikin gaggawa. _Jalaludden_ Yadda ya ga rana haka ya ga dare. Domin gabdaya bai rintsa ba, ya shiga ɗakin da aka kwantar da Ma'eesha sama da sau goma yana duba ta amma tana barci. Har yanzu allurar barcin ke aiki a jikinta. Har ya kai ya zauna cikin dakin yana gadinta har aka kira sallar asuba ya tashi ya nufi masallaci. _Fahad_ Sake haɗe fuska ya yi ganin yadda Nadra take ƙarasowa wajen sa sanye da dogon hijabinta. Wato ya ba ta kayan da za ta saka ta zo in da yake shi ne ta ɗora wani hijabi a saman kayan. Tama ƙarasowa kanta a sunkuye kamar mara gaskiya. Miƙewa tsaye ya yi yana kallon ta ba ta yarda ta kalle shi ba. Hannunsa ɗaya ya sa ya zare dogon hijabin da ta saka, da sauri ta shige jikinsa ta ƙanƙame shi sosai. Saboda ita har ga Allah tana kunyar ya ganta cikin figaggiyar riga da ya ba ta. Murmushi ya yi sannan ya ɗauke ta ya zauna kan kujerar sanan ya ɗaura ta a saman cinyarsa. Kunya take ji har lokacin, sai ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. "Nadfah." Ya kira ta cikin sigar raɗa a cikin kunnenta. "Wanan kunyar ta ki fa tana cutar da ni wallahi. Kunyar me ya rage a tsakaninmu? Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba? Ba abun da za ki ɓoye ma ni wanda ban gan shi a jikinki ba ko ban san shi ba, na san ki ciki da waje har..." Hannunta ta sa ta toshe ma sa baki yana dariya. Cire hannun ya yi yana cewa. "To ka dena faɗa, ke ma ina son ki kasance a yadda nake buƙata ina son ki da dukkan zuciyata, i love You with all my heart." "Love you more..." "Na kusa komawa America next week zan koma in sha Allah, sannan ina so mu tafi tare da ke my sugar." Shiru ta yi tana tunani ba kowa ya faɗo ma ta a rai ba sai Aunty Sidra. Ita ce kullum maganar ta tana cewa idan ta tafi America ita dai Nigeria sai dai ziyarara don can za ta zauna da Fahad. Take yanayin ta ya sauya saboda tuna Sidra, sai take ji a ƙasan ranta kamar ita ce ta janyo komai da yake faruwa a yanzu. Hawaye ne ya cika idanunta. Tabbas ta san cewa tana son Fahad kuma ba ta san lokacin da soyayyan Fahad ya shige ta lokacin guda ba. Amma tana tausaya wa Halin da ƴar uwarta ta shiga a lokacin da ta rasa shi, wanda har yanzu ta san tana son sa amma ba yadda za ta yi. Ba zato ta ji ya kai harshensa a saman kumatunta yana lashe hawayen da ya wanke ma ta fuska. Sai da ya lashe hawayen sanan ya ce. "Kin san na tsani zubar hawayenki ko? Ba na son ɓacin ran ki ballantana har ki zubar da hawaye. Me ya sa kike son sa wannan majidaɗin ne ya ji ba daɗi? Idan tafiyar America ne ba ki so to ni zan tafi ni kaɗai ba zan tilasta ma ki abun da ba ki so ba." Ganin wani hawaye ne ya kai baki ya yana lashewa sai suka ji takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas, ana zuwa inda suke. Cire bakinsa ya yi daga fuskarta ya kalli wace isashshiya ce ta shigo ma su har falo na knocking ba neman izinin. Ita ma kallon ta ta yi sai da gabanta ya faɗi ta yi saurin ɗaukar hijabinta ta saka musamman ganin kallon tsanar da take jifanta da shi. _Sidra_ Bayan Sady baby ta sauke ta ta kofar baya na gidansu ne ta fito daga cikin motar tana tafiya a hankali. Leƙowa ta yi ta tana cewa "Zuwa jibi za ki ga sakamako aikin da zai yi ma ki, kuma zan je na karɓo ma ki wasu saƙon da ya ce zai ba ki." Ba ta ce komai ba, ta bude ƙofar bayan ta shiga cikin sanɗa. Sannan ta saka sakatar ta rufe. Sady baby ta ja motarta ta bar wajen, sai dai ba ta lura da wata motar da take bin su a baya tun lokacin da suka bar unguwar da suka je wajen Mallaminta. Sai da ta bar wajen sanan motar da ya biyo su tun daga can ya sauke baƙin glass ɗin motarta ya kalli gidan da kyau, sanan ya zagaya ta gaban gidan ya kalli gidan sannan ya ja motarsa ya bar wajan. _Ma'eesha_ A hankali ta buɗe idsnunta da suka yi ma ta nauyi ta sauke shi a kan fuskarsa. Cike da takaici ta rintse idanunta. "Kin farka ya jikin naki?" Idanunta a rufe kamar me barci amma ba barci yake yi ba. Kanta ke Sara ma ta kamar zai tsage gida biyu. Ga jikinta sam ba ƙarfi ko kaɗan a jikin nata. Wayarsa ce ta soma ruri ya fito da wayar daga cikin aljihunsa ya duba mai kiran wayar. Idanunta suka sauka an tsaddadiyar wayar tasa ta miliyoyin kuɗi. Lumshe idanunta kawai ta yi kamar tana barci . Ɗan matsawa gefe ya yi yana amsa wayar. Duk da a hankali yake magana amma tana jin abinda yake faɗa.. "Hello." Can cikin wayar ya ji muryarta tana cewa. "Gud morning my Sweet Yaya J." Cikin yanayin rashin son magana ya ce. "Kin shirya ne?" "Eh kai nake jira." "Ba zan samu zuwa ba zM turo a zo a ɗauke ki a kai ki airport." Kamar za ta yi kuka ta ce . "Please mu tafi tare ma na, ja ga dama ba mu yi tsare-tsaren bikin ba." "Kin ga ba na son magana, ki shirya a zo q ɗauke ki kada ki rasa jirgi." Daga haka ya kashe kiran wayar. Ya kira yaronsa da ya kai su gidan jiya, ya sanar da shi ya je ya ɗauko Yasmeen ya kai ta airport. Daga nan ya kashe wayar ya sa a aljihu, yana tuna diramar da Ma'eesha ta yi yana kuma tuanin yadda zai iya shawo kanta ta saurare shi . Tunani kawai take yi na neman mafita don shi ne a gabanta yanzu ba komai ba. Damuwa bata da amfani akan duk abinda ba ta da ikon koma wa baya ta canza shi, ko kuma ta hana faruwarsa, sai dai ta cinye ma ta lokaci, ta hana ta amfanar damarta ta yau wajen aikata abunda zai amfa ne ta a duniya da lahira. Za ta yi haƙuri, ta fuskanci al'amuranta ga Allah , zai kawo miki sauyi da mafita a mafi dacewar lokaci. Doctor ne ya shigo cikin ɗakin idanunsa akan Ma'eesha da ta lumshe idanu. Sanan ya kalli Jalaluddeen. "Assalamu alaikum." Jalaluddeen ya kalli Doctor dake shigowa sanan ya amsa sallamar. "Wa'alaika salam." Hannu ya ba shi suka yi musabaha sannan sannan ya ce. "Da alama ko barci ba ka yi ba ko?" Bai amsa ba idanunsa na kan Ma'eesha. "Ka ci abinci kuwa, na ga kamar kai ne mai jinyar jikin daga jiya zuwa yau har ka rame." Gajeren murmushi kawai ya yi nan ma bai amsa ba. "Ya jikin nata?" "Da sauki." "Ta farka kuwa?" "Da safen nan ne ta ɗan farka ta kuma rufe ido amma na tabbatar ba barci take yi ba." Doctor ya karasa wajan gadon ya ce. "Assalamu alaiki." "Wa'alaika salam." Ta amsa isanunta a rufe tana yamutse fuska tare da ɗan dafe kanta. "Doctor kaina kamar zai fashe nake ji." "Sorry, za ki samu lafiya in sha Allah. Bari wanda ya kawo ki ya taimaka ma ki ki tashi zaune sai ki wanke baki, za'a kawo ma ki breakfast ki ji sai ayi ma ki allura za ki samu sauki." Duk da halin da take ciki amma sai da ta ce "Ba na son ganinsa Doctor don Allah ya fita, sanan ka tura Mani nurse mace ta taimaka ma Ni zan yi wanka na yi sallah." "Na ga shi ya kawo ki, me ya sa ba ki son ganinsa? Meye alaƙar ku da shi?" "Ban san shi ba, taimaka ma ki kawai ya yi da ya ga na fadi, ya kawo Ni asibiti na gode ya fita don Allah ya kama gabansa." "Ka ji abun da ta ce Yallaɓai." Doctor ya yi maganar yana kallon Jalaluddeen. Bai ce komai ba ta fita daga ɗakin, wanda hakan ya sa shi ma Doctor ya fita don tura ma ta nurse kamar yadda ta bukata. Ba jimawa wata Nurse ta shigo ta taimaka ma ta ta shiga toilet ta yi wanka ta dauro alwala. Kayan hijira ta sake sakawa sanan ta bude kofar. Nurse din ta taimaka ma ta ta yi tafiya zuwa inda ta shimfida ma ta sallaya ta mika ma ta hijab ta yi Sallah. Fita ta yi sai ga ta ta dawo ta breakfast da aka jero a faranti . Tea da bread ne sai soyayyen ƙwai. Da kyar ta iya shan ruwan tea kadai sanan Nurse din ta yi ma ta allurar da Doctor ya sa ta yi ma ta bayan ta kwanta. Ba nunawa barci ya yi awon gaba da ita, da ba don maganin ya sa ta barci ba da damuwar da take ciki ba za ta iya bari ta yi barci ba. Bayan ta yi bacci Jalaluddeen ya shigo dakin ya tarar tana barci . Wayarsa ce ta yi ruri Mom ce ke kiransa . Ya daga tare da sallama . "Assalamu alaikum." "Wa'alaika salam warahmatullah. Na ji muryarka da damuwa." Murmushi mai sauti ya kirkiro sanan ya ce . "Ba komai Mom, barci na tashi ne" Ya yi maganar yana jin dadin yadda Mahaifiyar tasa ke lura da yanayinsa ko ba sa tare. "To albashirin ka!" "Goro" ya faɗa kamar an ma sa dole ya ɗauka zancen auren sa da Yasmeen za ta ma sa. "An gano ƙanwata da aka sace tun tana jaririya." "Ban gane ba " Sai ta tuna shi bai san zancen ba, saboda ba hannunta ya girma ba, kuma sau biyu ya taba zuwa Katsina ya gaida dangin mahaifiyar tasa. Sadik da Saddiƙa da suka tashi a wajen Mahaifiyarsu ne suka san labarin bacewar ƙanwar mahaifiyar tasu. "Mom ban gane ba." "Wato yara uku Dada ta haifa na farkon shi ne Yaya Sulaiman da ka sani mahaifin su Kabeer, sai ni nake bin sa, to akwai mace da Dada ta haifa bayan ni sai dai tun tana jaririya aka sace ta. An yi neman ta da cibiya har an gaji. Duk da mahaifin mu har ya rasu bai cire ran cewa tana raye ba wata rana za ta dawo. Ko da ya rabar ma na da dukiyarsa har da nata kason wanda dukiyar nan nan Yaya Sulaiman na kula da su. To yanzu zanen ya fito wai tsohon maigadin gidanmu a lokacin ya sace ta yanzu dai suna hanya zai kai su inda ya kai ta. Shi ne nake cewa tun da kana gari sai gobe za ka bar garin ka taya su neman inda za'a samo ta." Kallon Ma'eesha dake barci ya yi . "Mom ki yi hakuri ina da wani abu mai mahimmanci ne a gaba na, wanda ba zan iya barin sa ba. Amma tun da shi wanda ya sace ta ya san in da ya kai ta komai zai zo ma su da sauki ba za su sha wahala ba." "Okay ba damuwa, na sanar da su kana garin, ko da sun kira sai ka sanar da su uzurinka. " "To na gode Mom." "Ba komai, ka tabbatar ka gama abun da kake yi zuwa gobe, wanda ba ka samu damar ƙarasawa ba sai ka bari bayan auren naka sai ka yi. Ka tabbatar ka dawo gobe." "To Mom." Ya amsa yana kallon Ma'eesha. Bayan sun gama waya da kamar mintuna talatin sai ga kiran wayar Haidar ya shigo wayar Jalaluddeen. Amsa kiran ya yi ta hanyar sallama, bayan ya amsa ya ce . "Kana ina ne Bros ga mu a Kaduna." "Okay daidai ina kuke ne?" "Yanzu muke shigowa, na ji an ce hotel kake ko za ka iya sanar da mu?" Duk da baya cikin hotel ɗin amma sai ya sanar da su, ya san ba nisa da asibitin. Fita daga asibitin ya yi bai tsaya kiran waya a zo a ɗauke shi da mota ba ya tari mai nape. Yana isa hotel ɗin ya yi wanka sauri-sauri ya shirya cikin ƙananan kaya. Kira ne ya shigo wayarsa ya duba ya ga Haidar ne. "Barrister kun iso ne?" "Eh mun iso, Ni da Kabeer ne kawai muka zo, shi mahaifin mu ya tafi wajen abokinsa Sanatar garin nan shi da mutumin da ya san inda take yake. Ya amsa da ba damuwa , lambar ɗakin ya sanar da su sannan ya katse kiran wayar. Knocking aka yi ya ba su izinin shiga ciki. Suka gaisa sanan suka zauna kan sofa. "Me zan sa a kawo maku?" "Ba komai kada ka damu." Cewar Kabeer yana danne-danne a waya. Haidar ne ya gyara zama ya kalli Jalaluddeen ya fara magana . "Ka san zanen da ya kawo mu garin nan ko?" "Eh Mom ta kira ni ta sanar da ni, sai dai ba zan samu damar bin ku ba sakamakon wani uzurin da nake sa shi." "Ban yi mamakn jin haka daga bakinka ba, domin ba ka ɗauke mu ƴan uwan ka ba." Kabeer ya yi magana yana kallon wayarsa kamar ba shi ne wanda ya yi maganar ba. Jalaluddeen bai kalle shi ba ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai. Haidar ya kalli Kabeer ya ce. "Duk bai kai can ba." "Dama ni ban taɓa saka shi a cikin mu ba, duk da ba mu dade da sanin cewa muna da dangantaka da shi ba. Amma na tabbatar da dangin uwar da ta rike shi ne da ya bar abun da yake yi ya tafi. Amma wanan da muke nema fa da mahaifiyarsa da shi uwa daya Uba ɗaya, ana neman ta yana faɗin baya da lokaci? To shi kenan idan kuma har muka same ta na ga ka taka ƙafarka ka je Katsina sai na yi ma ka rashin mutunci!" Sai a lokacin Jalaluddeen ya ce . "Waye kai? Me kake da shi? Me kake taƙama da shi? To shi kenan ka rubuta ka ajiye ni Jalaluddeen sai na taka ƙafata cikin gidanku cike da isa da alfahari idan ka isa ka dakatar da ni." "Haka ka faɗa?" Banza ya yi fa shi ya miƙawa Haifar hannu tare da yi ma sa addu'ar Allah ya bayyana ta. Daga haka ya fice ya bar su a cikin ɗakin. Cikin takaici Kabeer ya ce . "Kana ganin wulaƙancin da ya yi ma na ko? Ba lafinsa ba ne kai da ka saka muka zo kai ka ja ma na wulaƙanci. Idan ba don ina duba dangantaka ba har ya isa ya faɗa mun magana na kyale shi?" "Kabeer ba ka da hakuri, ba ja san uzurin da ke gabansa ba, tun da ya fadi haka sai a tafi a haka ma na, meye na ɓacin rai a ciki, daga kai har shi kowa na ji fa izza da isa shi ya sa ba ku jituwa da shi." Bai ce komai ba ya tashi ta fita. Haidar ma ya bi bayansa suka fita a tare . Suna fita sai ga ɗaya daga cikin ma'aikatam hotel ɗin ya zo ya rufe ɗakin kamar yadda Jalaluddeen ya ba shi umarni." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣4️⃣ *Ku dinga haƙuri da typing error ba na samun lokacin yin editing.* Bai ce komai ba ya tashi ya fita. Haidar ma ya bi bayansa suka fita s tare. Suna fita sai ga ɗaya daga cikin Ma'aikatan hotel ɗin ya zo ya rufe ɗakin kamar yadda Jalaluddeen ya ba shi umarni. _Sidra_ A hankali take tafiya cikin sanɗa har ta shiga ta ƙofar baya na kitchen ta wuce zuwa ɗakinta ta cikin corridor da zai sada ta da ɗakinta. Ajiyar zuciya ta sauke ganin har ta shiga ba wanda ya ga shigowar ta Bathroom ta shiga ta haɗa ruwan zafi tana hawaye ta shiga ciki. Kuka take yi sosai ta yi nadamar abun da ta aikata. Sai da ta daure ta gasa jikinta sosai sannan ta yi wanka ta ɗauro alwala sannan ta fito. Doguwar riga ta saka tana jin ƙuna a ranta, ta tabbatar da a gidan aurenta ne mijinta na Sunnah ne da yanzu yana nan yana tausaya ma ta da lallaɓa ta kuma lada za ta samu. Amma wanan ga tarin zunubin da ta kwasarwa kanta, duk a dalilin soyayyar Fahad ta kai ta ga wanan halin. Sallah ta gabatar bayan ta idar ta mike dama ita ba mai yawan yin addu'o'i da azkar ba ne, ballanta karatun Alkur'ani. In da suka sha banban da Nadra Kenan. Domin Nadra akwai yawan addu'a da azkar da karatun Alkur'ani. Amma Sidra tana idar da sallah za ta tashi. Tana cire hijabinta sai ta hau saman gadon ta kwanta tana tunani. Umma ce ta turo kofar ɗakin ta shigo. Ba ta yarda sun hada ido da Umma ba don kar ta gane ta yi kuka. "Sidra." Cewar Umma tana zama bakin gadon. "Na'am Umma." "Ɗazu na zo na sanar da ke za mu fita da Ammi sai na yi knocking ba ki bude ba." "Eh Umma na yi barci ne, sannun ku da dawowa." "Yauwa sannu. Na tambayi ma su aikin gidan sun ce ba ku fito kin ci abinci ba lafiya?" "Umma na ƙoshi, na ci snacks dake cikin fridge." "Amma ba za ki ci abinci ba." "A'a Umma na ƙoshi ." "Akwai abun da ke damun ki." "Ba komai Umma ina lafiya." "Sidra." "Na'am Umma." Ya kamata ki shiga hankalin ki ki nutsu, hakika ina cikin damuwar hukuncin da mahaifinki ya yanke na cewa nan da wata ɗaya zai aurar da ke ga duk wanda ya ci karo da shi a ƙauyen su. Shawara ta ki fito da miji kafin lokaci ya kure ma ki. " "Umma duk samarin da suke cewa suna so na na wulaƙanta su, na kore su na yi masu gargaɗin na fi karfin su Umma. Har sai da ta kai ta kawo ana shakkar tara ta da maganar so. Ba wanda yake so na yanzu duk na watsa su saboda Fahad. Umma ba zan ɓoye ma ki ba har yanzu ina son Fahad kuma zan iya aikata komai don na same shi. Don wallahi Umma sai Nadra ta bar mun gidana da mijina." "Subhanallah!" Hawaye ta goge tana huci. "Wai ke ba za ki taba canzawa ba! Ke a matsayin ki na musulma ba za ki yarda da ƙaddara ba.?" "Ƙaddara! Ai Umma da tuntuni ƙaddarar ta zo ta hana ni haɗuwa da Fahad, sai da muka haɗu sannan ta ce za ta raba mu, ƙaddarar ma haƙuri za ta yi ta bar ni da shi wallahi." Da mamaki Umma ke kallonta. "Anya kanki daya kuwa?" "Umma komai ta faru komai ya lalace an mai matakin da zan iya tunzura Allah wallahi. Ba zan sadaukar da mutunci..." Kasa ƙarasawa ta yi don kada Umma ta gane ta aikata wani abun. Umma mamaki take yi ta ɗauka Sidra ta yi sanyi ne, ashe halinta yana nan ba abun da ya sauya. "Kina ji na ko?" "Eh ina ji." "Wanda ya bar wani abu da zuciyarsa ke so saboda Allah, Alkah zai musanya masa da abin da ya fi alheri a duniya da lahira. Idan zuciyarki tana son wani abu, amma Allah ba ya so, sai ki danne son zuciyar, ki hana kanki, ka fifita umarnin Allah da na Annabin sa a kan son ranki, to Allah zai saka maki da abin da ya fi shi alheri. Zai cika zuciyarki da imani, ya ba ki farin ciki da kwanciyar hankali da albarka a tare da lafiya a jikinki. A lahira, kuma Allah zai ba ki lada mafi girma da daukaka, wato Aljanna. Wannan alƙawari ne tabbatacce, babu kokwanto a cikinsa. Duk wanda ya gwada hakan da zuciya mai tsarkakakkiyar niyya, zai ga tasirinsa a rayuwarsa. Ki tsarkake niyyarki saboda ALLAH kawai, za ki ga abin mamaki daga falalarsa. Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana zuciyarsa bin son rai, to lalle Aljanna ita ce makomarsa. ALLAH Ya sa mu cikin waɗanda suke fifita yardarSa a kan son zuciyarsu, ya azurta mu da daidaito a duniya da rabauta a lahira." _Sady baby_ Sam ba ta lura da cewa akwai motar da take bin ta tun da ta bar wajen Mallam da Sidra ba. Har ta kawo Sidra gida yana bin ta har ya zagaya gaban gidan sannan ya bi Sady baby a baya. Tana shiga layin unguwar su kafin ya karasa gida ya sha gabanta da mota. Ba shiri ta taka burkin motar. Ya fito a fusace daga cikin motarsa sai huci yake yi. Sady baby tana fitowa daga motarta da niyyar yin tsiwa, amma ganin wanda ke gabanta da yanayin fuskarsa ta sa gabaɗaya gaɓɓan jikinta yin sanyi. Tas tas ta ji saukar maruka biyu a fuskarta wanda har ya da ta wuntsila ta faɗi ƙasa. Wani gishiri-gishiri ta ji a bakinta wanda hakan alama ce ta cewa bakinta ya fashe har ya fitar da jini. Kallon sa take yi sai numfashi yake yi kamar matashin ɓauna. "Ashe rashin imani ki har ya kai haka, anya ke mace ce kuwa ? Ina karin maganar da kuke yi cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne?" "JB ni ka mara??" "An mare ki, wallahi ji nake ma kamar na kashe ki kowa ya huta da annoba." "Au ni ce ma annobar? Sakayyar da za ka yi ma ni kenan?" "Akan me za ki yi ma ni haka? Akan me za ki kawo ma ni mace verging bayan ba haka muka yi da ke ba. Cewa kika yi yarinyar nan ita ma ƴar hannu ce tana mu'amala da maza, wanan dalilin ya sa na amince na yi ma ki wannan aikin ashe ba haka ba ne, yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce ba ta wani ɗa namiji da ya taɓa sanin ta sai ni. Akan me za ki lalata rayuwarta me ta yi ma ki haka da zafi?" Kafin ya yi wani magana wayarsa dake cikin aljihun wandonda ya yi ruri. Ya duba mai kiran wayar, ganin Yayansa ya yi tsuki sanan ya ɗaga. "Meye kuma?" "To mara mutunci ka zo yanzu ina son ganin ka." Muryar mahaifiyarsa ya ji saɓanin na Yayansa da ya yi zato." Kashe wayar kawai ya yi ba tare da ya amsa ma ta ba. Kallon Sady baby wacce bakinta har ya kumbura ya yi sannan ya fara magana cikin kakkausar murya. "Ki jira haɗurmu da ke." Daga haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key, sai da ya buɗe Sady baby da ƙura sanan ya bar wajen . Kuka take son yi amma bakinta ya kumbura ya kasa motsa shi sai hawaye kawai take yi . Tashi ta yi daga faɗuwar da ta yi, ganin har an fara kallonta jama'a ma su wucewa. Da ƙyar ta iya jan motar tana hawaye tana jin zafin abun da JB ya yi ma ta. Sai dai ba ta yi mamaki ba, dan idan ta tuna waye shi idan ransa ya ɓaci. JB. Cikakken sunansa shi ne Jabeer cikakken sunan sa. Wani sangartaccen ɗan ma su kuɗi ne a garin Kaduna. Mahaifinsa hamshaƙin ɗan kasuwa ne da yake kasuwanci har a kasashen waje. Sunan mahaifinsa Alhaji Kamil sai mahaifiyarsa Hajiya Karima. Su biyu iyayensu suka haifa yana da Yaya namiji mai suna Munnir. Tun tasowar Jabeer mahaifinsa ya sangarta shi sosai, saboda son da yake yi ma sa. Ko mahaifiyarsa tana kokarin ganin ta ba shi tarbiyya mai kyau amma son da mahaifinsa ke ma sa yake ganin kamar tana takura na yaronsa. Har yake ganin ba ta son Jabeer kamar ba ita ta haife shi ba. Don ba wanda ya isa ya yi ma sa faɗa ballantana duka, sai abun da ya ga dama yake yi. Hatta Yayansa Munnir bai isa ya ma da faɗa ko wani abun ba take zai kai kara wajen Mahaifinsu wanda shi kuma zai yi wa Munnir faɗa ya goyi bayan Jabeer. Karshe mahaifin nasu ya dauke shi ya kai kasar waje ya yi karatu a can sai ya gana saboda takurar da ake yi ma sa. Don baya son a kira shi da Jabeer dai dai JB.Wanan tafiyar ta kara lalata tarbiyyarsa bai ma tsaya ya yi karatu ba sai shashanci da harkar neman mata. Dole ta sa mahaifiyarsa ta je ta dawo da shi don dole. Driving yake yi yana jin kukan Sidra na dukan dodon kunnensa. Bai taba nadamar abun da ya aikata ba sai wanan karon. Ko don bai taba mu'amala da cikakkiyar budurwa ba ne sai kanta ya san budurci. Don duk ƴan matan da ya yi mu'amala da su to sune suke kawo kansu har wajensa. Amma kanta ya yi wa mace dole ba tare da sanin budurwar ba ce . Abokin Sady baby ne shi JB tun da ta ji labarin yadda yake sakarwa mata kudi bai san zafinsu ba ya sa ta shiga rayuwarsa. Suka zama abokai, kuma yana sakar ma ta kuɗi sosaiz har motar da take hawa da gidan da take zaune shi ya ba ta su. Dalilin abun da ya haɗa su da Sidra kuwa roƙonsa ta yi ya taimaka ya yi ma ta abun da take so, don ce ma sa ta yi Sidra za ta raba sunna ita kuma tana son ta dakatar da ita, ya yi basaja a matsayin Mallam su raina ma ta hankali kada ta je wajan wanda zai raba auren da gaske. Ta tsara abun da zai faɗa wa Sidra. Da ƙyar ya yarda akan cewa zai yi , ta samo gida da komai ta tsara ta kawo shi gidan sannan ta kira Sidra akan ta zo su tafi. _Ma'eesha_ Tana kwance saman gadonta bayan barcin ya sake ta sai kuma ciwon kai ya ma ta sauki shi ma. Ta bude idanunta da suka yi ma ta nauyi. Saman ɗakin ta fara kallo sannan ta kalli kofar ɗakin. Ganin ƙofar ɗakin a rufe ya sa ta lumshe idanunta . Daidai lokacin da Nurse ta shigo cikin ɗakin. "Assalamu alaikum kin tashi?" "Wace'alaiki salam warahmatullah." "Wace'alaiki salam warahmatullah." "Ƙanwsta kin tashi." "Na tashi sannu da ƙoƙari da ni." "Wani kokari? Ai wanda ya kawo ki yanzu ya ba mu dubi ɗari ya ce duk abun da kike bukata a siya ma ki ga kuɗin nan a hannuna, ko na ba ki ki rike a hannunki?" Shiru ta yi tana kallon kuɗin bandir ɗin dubu ɗaya ne ta fito da shi daga cikin handbag din ta. Sannan ta ɗauko wani dubu ɗarin ta ce . "Wannan kuma nawa ne ya ba ni kyauta. Gaskiya yana da kirki ya kike da shi ne." Ta yi maganar tana janyo kujera ta zauna tana farin cikin kuɗin . "Me da me kike bukata a siya ma ki?" "Ba na bukatar komai. Amma ki ciro dubu talatin ki ba Ni zan yi wani abun da shi." "Okay ." Ta yi maganar tana ciwo kuɗin, ga kirga dubu talatin fa sannan ta mika ma ta ." "Na gode ." Ƙadan pillow ta saka kudin sannan ta kwanta daidai lokacin da ya shigo da sallama. Ciki-ciki ta amsa yayin da Muryar Nurse din ga ya cika dakin ta amsa tana washe baki. "Barka da shigowa Yallaɓai." "Barka." Buɗe idanunta ta yi tana kallon yadda yake ta kowa cikin ɗakin cikin takunsa na ƙasaita. Tana tuna yadda yake dogara sanda yana tafiya kamar nakasashshe. Yanzu ga shi yadda yake tafiya irin na lafiyayyun maza. Ba abun da ke ma ta zafi kamar idan ta tuna wai ranar juma'a ɗaurin aurensa. Juyar da kanta ta yi ganin hawaye na shirin zubo ma ta. Bari na ba ku wuri Yallaɓai ." Da sauri Ma'eesha ta rike ma ta hannu tana girgiza kai Ammar a'a . Ganin haka ya sa ya ce . Ta zauna ba damuwa, duk da ba haka ya so ba. Ya so ya yi magana da ita sosai . "Ba wata matsala ko?" "Ba komai sir, yanzu za'a kawo na ta abinci ta ci sai na ba ta magungunan ta." "To ba damuwa bari na je masallaci daga nan akai wanda zan je na gani, amma nan fa awa daya in sha Allah zan dawo . Ki kula da ita sosai ." "In sha Allah, a dawo lafiya." Daga haka ya nufi kofar fita, bayan ya bude kofar sai da ya juyo ya kalle ta sannan ya fice . Yana fita ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito. Sallar azahar ta gabatar. Ganin Nurse din na cewa za ta kawo ma ta abinci ya sa ta ce ma ya ta bari zuwa anjima. Don ita ta san me ta shirya . "Aunty akwai nisa nan da kasuwa?" "Ba sosai ba nisan." "To don Allah ina son ki siyo ma ni wani hijabi ne." "Ba damuwa wani kala." "Fari nake so." "To bari na je na dawo, dama na tashi aiki wanda ya kawo ku ne ya ce na zauna na kula da ke ya biya ni." Daga haka ta fita . Wanda hakan ya ba Ma'eesha damar tashi daga saman sallayar da ta idar da sallah. Takalmi ta saka ta karasa wajan gadon ta cire kuɗin da ta amsa dubu talatin ta fice daga cikin dakin da sauri. Tana addu'a Allah ya sa kada ta hadu da Dr ko Jalaluddeen. Haka take tafiya kanta a ƙasa kada wani ya ganta ya gane ta. Cikin ikon Allah har ta fito daga asibitin ba wanda ya gane ta. Tana fita cikin asibitin ta rasa ina za ta je. Don ba ta da wajan zuwa, ba za ta iya komawa gidan aurenta ba. A fahimtar ta Jalaluddeen baya son ta, dole aka yi ma sa aka aura ma sa ita ba tare da yana so ba. Kuma bai ki tayin Dady da Mamy ba. Shi ya sa ya ajiye ta tsawon watanni da suka yi babu abu dayya da ya yi ma ta wanda za ta ce yana son ta. Bai nuna ma ta alamar so ba ko kaɗan, shi ya sa rayuwar aurensu ya daga banban da rayuwar auratayya da ta saba gani. Ashe yana nan yana neman macen da zai aura ita kuma ya mayar da ita banza. Kodayake ba laifinsa ba ne, an na shi ita a arhar banza bai sha wahala ba ya same ta, babu lefe babu kuɗin gaisuwa ko baiko dai kuɗin sadakin da aka ce ya bayar da dubu uku, wanda ko kaza ce za'a aura ma sa ta fi karfin dubu uku a yanzu ballantana mutum. Kuka ne ya ƙwace ma ta ta saka bayan hannunta ta goge. 'Tabbas ba in da zan tafi a halin yanzu, ban isa na je gidan Mahaifina ba. Haka kuma ba zan iya komawa gidan mijina ba. Don na tsane shi fiye da kowa da komai a halin yanzu. Ba na da kowa ban san inda dangin mahaifina suke ba na tafi wajensu na huta da wajan rayuwar. Na tsani zaman garin nan dole na tafi ko ma ina ne, barin garin nan ya zama ma ni dole ko zan sami sassauci.' Ta yi nisa cikin tafiyar da take yi ashe har ta kai titi ba ta sani ba. Kai tsaye ta hau saman titi ba tare da sanin ina take jefa ƙafa ba. Ihun jama'a ta kuma ƙarar taka birki da ta ji ne ya sa ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai kafin ta yi wani yunƙuri har motar ta ɗan ture ta ta fadi ƙasa. Rintse isanunta ta yi gabanta na tsananta faɗuwa. " Ke wata irin mahaukaciya ce za ki hau titi kai tsaye? Yanzu da wani abu ya faru fa?" Cewar Captain Kabeer yana kallonta a fusace. Barrister Haidar ne ya fito daga cikin motar cike da kulawa yake kallonta . "Sannu baiwar Allah ba ki ji ciwo ba ko?" Ɗago da dara-daran idanunta da suka canza launi zuwa ja ta kalle shi. Sai da zuciyarsa ta harba da ƙarfi sakamakon kallon fuskarta. Cikin sanyin murya ta ce. "Ku yi haƙuri don Allah, ba na cikin nutsuwata ne. Amma Allah ya kare ba abun da ya same ni." Da ƙyar ta iya jijina ma ta kai, tashi tayi ta kalli tsaddadiyar motar da ta kusan kaɗe ta. Cike da takaici Kabeer fara magana . "Dan Allah ka zo mu tafi Yaya, ana jiran mu fa, nan da gudan marayun ma akwai tazara." Bai tanka ma sa ba ya shiga motar ya tayar suka bar wajen. Don har an fara cunkoson ababen hawa. Ma'eesha kam mai nape ta tare ta ce ya kai ta tashar mota. "Wace tasha za mu je Hajiya?" "Kowace tasha da ake hawa mota zuwa garuruwa." "To bisimillah shigo mu tafi." Shiga cikin nape ɗin ta yi ya dauki hanyar kai ta tashar mota kamar yadda ta buƙata. Barrister Haidar bayan sun bar wajan suka nufi hanyar gidan marayun da aka sanar da su cewa su je mahaifinsu na hanyar shi da Sanata Zuwan su ya yi daidai da zuwan su sanata da mahaifinsu. Kusan a tare motocin nasu suka shiga cikin gidan marayun . In da aka tarbe su cikin girmamawa kasancewar an ga sanata a tare da su. Har office din shugaban aka je tare de Maude. Nan aka yi ma sa tambayoyi ya bayar da amsa da ranar da aka kai yarinyar da kayan dake jikinta da komai sai da ya bayar . Babu ɓata lokaci aka fara bincike don wanda ke kan kujerar a yanzu ba shi ba ne a lokacin da aka kawo ta. Don wancan shi wancan ma ya rasu wani ne yanzu da ke kai. Da ƙyar aka gano file din da bayanai kamar yadda Maude ya faɗa. Sai dai komai da tsari suke yi hatta ranar da aka dauke ta da wanda ya dauke ta yana cikin file ɗin. "Waye shi wanda ya dauke ta?" Yana daya daga cikin masu tallafawa marayun gidan nan dansa ya aura wa ita." Cewar shi shugaban. "Amma yanzu baya ƙasar nan yana jinya a kasar Egypt tsawon lokaci. Shi da matarsa , Amma shi Ɗan sa yana garin nan na san gidansa." "Ba damuwa mu tafi gidan Ɗan nasa." Motoci uku ne suka haɗu na sanata biyu da kuma na Haidar da suka zo da shi daga Katsina. Kai tsaye suka kama hanyar zuwa gidan Alhaji Ibrahim Khalil. _Nadra_ Kallon Farida da take yi ma ta wani kallon tsana ta yi na wasu sakanni sanan ta dauke kai. Tana ganin rashin dacewar abun da ta yi na shigo ma su gida kai tsaye ba izinin har cikin falo. "Farida!' "Na'am Yaya Fahad." Ta faɗa a shagwabe. "Wani irin dabbanci ne za ki shigo ma ni gida kai tsaye ba neman izini." Kuka ta saka ma sa ba tare da ta ce komai ba. "Nadra dai barin wajen ta yi ta ba su waje, don ta ga kallon da take yi ma ta. Dama ta san ba ƙaunarta take yi ba, kuma ta ji labarin ita ma son Fahad take yi shi ya sa take zaune a gidan tsawon shekaru sa saboda shi. Tana ganin Nadra na barin wajen ta fara magana . "Yaya Fahad yanzu shi ne za ka dinga yi ma ni faɗa a gaban matarka ko?" "Wani dalili zai saka ki shigo ma na gida kai tsaye Babu izini." "Yanzu dan zan shiga gidan ka sai na nemi izinin. Ai da yanzu Ni ce a gidan da ba don wanan..." "Ya isa!" Ya dakatar da ita don ya san halinta yanzu za ta iya cin mutunci ga Nadra. "Kuma ina nan akan baka na sai ka aure ni." "Kawai ba, ki ɗebo kayanki ki zo ki zabi daki daya mu zauna matsayin mata da miji kin ji ko?" Jin maganar banza da ya faɗa ma ta ne ya sa ta kau da kai tana magana kasa-kasa. "Da sannu za ka shiga hannuna Wallahi." "Me kika ce?" "A'a ba da kai nake yi ba." Wayarta ce ta yi ringing. "Hallo Mumsy ga shi." Tun da ya ji ta ce Mumsy ya san ƙanwar mahaifiyarsa ce wato mahaifiyar Farida. Tun da aka yi aurensa da Nadra bai yi magana da ita a waya ba. Don ko ya kira ta ba ta ɗagawa tana fushi da shi saboda bai auri ƴar uwarsa ba ya fita waje ya auri bare. Farida ta mika masa wayar, ya karba ya kara a kunnensa. "Assalamu alaikum." "Wa'alaika salam." "Ina wuni Mama." "Lafiya ya kake ?" "Alhamdulillah." "Dama ƙanwarka ce Farida za ta je karatu America tun da auren bai yiwu ba ta koma makaranta. To sai na ga tun da kana da gida a America sai ta zauna a gidanka hankalina zai fi kwanciya. Ba na son. Ta zauna in da ba wanda zai tsawatar ma ta ko da ta yi ba daidai ba. Amma na san za ka kula da ita ta yi karatu yadda ya kamata ." Shiru ya yi yana nazari kafin ya ce . "To ba damuwa Mama." "Yaushe za ka koma ?" "Sai next week." "To tafiyar za ta yi ma ku daidai kenan. Sai ku tafi tare ." "Allah ya kai mu." Sallama suka ya mika ma Farida wayar ya haura sama. Farida na ganin ya haura ta yi kasa da murya ta ce . "Mama ya ya haura sama." "To yanzu sauran aikin ya rage na ki, ba sai na koya ma ki ba, idan ya so wanan karon ma ki tsaya shashanci kada ki yi amfani da damarki akansa." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 *MAKAHO NE* *NA* Maman Ihsan ce✍️ *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️ (𝙅.𝙒.𝘼) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page8️⃣5️⃣ *End of book 1. Last free pages* *To yanzu sauran aikin ya rage naki, ba sai na koya maki ba, idan ya so wannan karon ma ki tsaya shashanci kada ki yi amfani da damarki." "Mama ba zan yi sake ba, dama ai saboda muna gida ɗaya ne ga mahaifiyarsa ga mahaifinsa, Sanan kuma ka ƙanwarsa Rumaisa hakan ya sa na nake ɗaga kafa ba na iya yin wani abun. Sannan kuma shi Fahad ɗin yakan share ni kamar bai gane me nake nufi ba. Sai da na fito na nuna ma sa irin son sa nake yi ma sa ne yake cewa wai Sidra zai aura. Mama sai da na yi kamar na bar gidan na dai daure na zauna, har aka fasa auren bayan gudun Sidra na saka rai zai aure ni shi ne matsiyatan iyayennta suka sura ma sa ƙanwar. Wallahi wanan karon Mama ba zan saurara ba ko kaɗan. Dama ba idan kowa akan mu idan mun tafi American daga ni sai shi wallahi idan har ban ja ra'ayinsa zuwa gare ni ba na daina amsa sunam mace." Sautin saukowa ta ji daga sama ya sa ta yi wa mahaifiyarta ta kashe kiran wayar . Nadra ce ta karaso wajen ta kalle ta da murmushi a fuskarta . "Aunty Farida ina wuni?" Banza ta yi da ita tana danne-danne a waya tana taunar cingam a bakinta. A takaice tunanin Nadra ta ɗauka ba ta ji ba ne, don haka ta sake gaishe ta a karo na biyu. "Mtswww" Tsukin sa ta yi ne ya tabbatar ma ta da cewa ta ji ta Msawar. E b za ga yi ba. Don haka sai ta juya ta koma sama. Da harara ta bi ta kafin ta ce. "Wallahi sai na yi maganinki sai zama da Fahad ya gagare ki." Ta faɗa da karfi don ta ji ta. Kuma ta yi nasara, domin maganar ya shiga kunnen Nadra. Murmushi kawai ta yi. Dama ta zo ne ta kawo ma ta abin sha da abinci. Amma tun da ta ga take-takenta ta san ba shan komai za ta yi idan ga ba ta ba. Don haka ta shige ɗaki ta yi kwanciyarta. Don dama daiurewa kawai take yi ciwon kai ke damunta. _Jalaluddeen_ Yana shigowa ɗakin ya ga Nurse din da ta bari ta kula da Ma'eesha hankalinta a tase. Kallo ɗaya ya yi ma ta ya gane tashin hankali da take ciki. "Me ya faru?" "Yallaɓai wallahi ashe dabara ta yi ma ni tana son fita ne." "Ban gane be meke faruwa ?" "Cewa ta yi na ba ta dubu talatin cikin kuɗin da ka bayar. Sanan ya ce na je kasuwa na siyo ma ta hijabi. Ko da na dawo daga kasuwar ban ganta ba. Ba ta cikin toilet na zagaye gabaɗaya asibitin nan ba ta ciki. Na sanar wa Doctor shi ne da ya yi bincike ya gano da ƙafarta ta fita bayan fitar da na yi." Bai iya cewa komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin. Wajen Doctor ya je don neman karin Bayan. Doctor ya nuna ma sa yanda ta fita ta hanyar CCTV camera da ya duba. Isso Jalaluddeen ya zaba wa computer yana kallon yadda take tafiya kanta a sunkuye alamar rashin gaskiya. Godiya ya yi ma sa sanan ya fito ya nufo inda ake parking motoci in da yanar yaronsa na jiransa. Gefen wajen me zaman banza ya zauna sannan direban ya ja motar suka bar wajen. Gidan da yake zaune tare da Ma'eesha ne ya umarci direba ya kai shi. Ko da direba ya yi parking kofar gidan Jalaluddeen ya fito ya shiga cikin gidan. Ba kowa gidan kamar yadda ya bar shi. Sai wayar Ma'eesha dake ajiye a tsakiyar ɗakin. Komai yana zaune a mazauninsa kasancewar ta mace mai tsafta. Wayarta ya durƙusa ya ɗauka, sanan ya karewa ɗakin kallo na wasu daƙiƙu sannan ya fito cikin sanyin jiki. Ya san ba za ta dawo gidan ba kasancewar tana fushi da shi. Har ta yi furucin saki da ta tsani ganinsa a rayuwar ta fiye da kowa. Hakan ya za na ma sa alamun cewa ba za ta zo inda yake ba. Sai dai to ina za ta tafi?" Abun da ya tsaya ma sa a rai kenan. Mutum ɗaya ce ta faɗo ma sa a rai wato Nasreen. Don haka ya fita da sauri ya bude murfin motar wajan zaman direba. Alamar ya fito ya yi ma sa da hannu. Ba musu ya fito. Jalaluddeen ya zauna mazaunin direba ya yi wa motar key suka bar wajen. Waɗanda da suka ga shigar da fitar sa mutane biyu suka bi motar da kallon mamaki. Kai tsaye ya ɗauki hanyar gidan su Nasreen yana sarrafa motar cikin ƙwarewa. Yaronsa dake zaune a gefesa yana son ya yi maganar cewa uban gidansa ya rage gudu amma ganin fuskarsa kawai ya ba shi tsoro, ya kasa yi ma sa magana. Domin yanayin da ya ga fuskarsa yanayi ne da tun da yake bai taɓa ganinsa ciki ba. A kofar gidan ya yi parking ya fito daga cikin motar. Ƙaramr door din gidan ya yi knocking. Maigadin gidan ya leƙo ya kalli Jalaluddeen ya kalli motar da ya zo da shi ne ya gane ba ƙaramin mutum ba ne. Hannu Jalaluddeen ya ba shi suka yi masabaha. Sanan ya nemi da wajen Nasreen ya zo. "To Yallaɓai bari a sanar da ita zuwanka." Ya koma ciki ba jimawa ya dawo ya sanar da shi cewa tana nan zuwa. Ba jimawa ta fito ta zuba wa bayansa idanu. Kasancewar ya juya baya yana tsaye jikin motar, ya ɗan kwantar da kansa a saman motar. Duk da cewar ba ta san ko waye na amma ƙirar jikinsa kaɗai zai tabbatar ma ka da cewa tsayayyen namiji ne. "Assalamu alaikum." Ta yi ma sa sallama. Ya amsa yana juyowa suna fuskantar juna. Da mamaki take kallonsa yadda ya zo kai tsaya ba tare da ɓadda kama da yake yi yana raina wa ƙawarta hankali ba. "Lafiya me ka zo yi nan ƙofar gidan?" "Ƙawarki nazo nema, na san ba in da za ta zo da ya wuce nan." "Tofah! daɗi na da gobe saurin zuwa, an zo wajen kenan, ta ga hanya yau ta gane shayi ruwa ne. Tabbas hakan ya ma ni dadi da ta gane ko kai waye, Alhamdulillah ko ba komai yanzu za ta tabbatar da cewa ba karya nake yi ma ta ba gaskiya nake faɗa ma ta. Kai wanda take kallo kamar waliyi kai ne ka yi ma ta karya." Girgiza kai ta yi tana murmushi. "Sai dai na tausaya ma ku daga kai har ita ababen tausayi ne, yanzu na san tana can cikin damuwa da bakin ciki, yadda ta tsani ƙarya da yaudara da cin amana. Ga Jsji ta kama ka da aikin aikata ma ta su. Tabbas na san shawo kanta ba abu ba ne mai sauƙi. Amma ko ba komai na yi farin cikin gaskiya ta yi halinta kuma..." "Ya isa, idan kin san inda za ta iya zuwa bayan wajenki to ki faɗa ma ni." "Ban sani ba, ka je can ka neme ta, yadda ka saka ta cikin halin da take ciki sai ka nemo ta ka shawo kanta." "Idan har kin san tana cikin gidan nan ki fito ma Ni da ita, idan kuma ba haka ba, kika bari na tabbatar tana ciki wallahi sai kin yi nadamar ƙaryar da kika yi ma ni." "Oh Allah, me zai saka na yi ma ka karya? Kodayake duk abun da mutum yake yi sai ya ɗauka kowa ma shi..." Tsawa ya daka ma ta wanda sai da hantar cikinta ta kada. "A halin yanzu raina a ɓace yake kada ki tunzura ni. Ina matata na tambaye ki." "Wallahi ban san in da ta tafi ba." Ganin yadda ta tsorata da yanayin ta ya tabbatar ma sa da gaskiya ta faɗa. Don haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key a guje ya bar ƙofar gidan. Tafiya kawai yake yi ba tare da ya san in da zai ganta ba. _Alhaji Sulaiman_ Horn motocin da sauke ciki suka yi a ƙofar gidan Daddy. Maigadi ne ya leƙo. Ganin manyan tsadaddun motocin da suka zo ƙofar gidan ne ya sa da sauri ya bude gate. Motocin suka fara shigowa cikin gidan . Daidai lokacin da Laila ta fito za ta je unguwa. Ganin irin motocin ya sa ta fadin . "Wow." Haidar da kabeer suka fara fitowa, ta zuba ma su idanunta ko ƙyaftawa ba ta yi. Alhaji Sulaiman da abokinsa Sanata suka fito tare, sai Maude da jikinsa ya yi sanyi, sai kuma daya ma'aikacin gidan marayun wanda ya biyo su. Barrister Haidar ne ya tura Maigadi a je a sanar da maigidan yana da baƙi. Daddy dake zaune da Mummy a falo sai kuma Jamil dake zaune a carpet. Maigadi ya shigo ya sanar da Daddy zuwan baƙin. Kafin Daddy ya yi magana har Mamy ta leka ta window. Ganin manyan motoci ne ya saka ta jijina kai tana yi wa maigadi magana. "Ka yi sauri ka shigo da su manyan mutane ne ba'a barin su a barin su haka." Zama ta yi tana jiran shigowar su. Da sallama suka shigo cikin falon, Daddy da Jamil suka miƙe suna yi ma sa sannu da zuwa . Suka shigo kasancewar set biyu ba kujera ne a falon don haka duk suka zauna akan kujera. Laila ma fasa fita ta yi ta shigo ciki din ganin abub da zai turewa buzu naɗi. Bayan an gaggaisa Mamy ga sa mai aiki ta kawo ma su ruwa da abun sha, sai ma'aikacin gidan marayun ya fara maganar abun dake tafe da su. Sannan ya gabatar da dangin Mummy ga su nan sun zo suna bukatar ganin ta ita da ƴaƴan da ta haifa. Gabaɗaya falon shiru ya yi kamar ruwa ya ci su. Daddy jikinsa ya gama yin sanyi. "Wato tabbas ni ce na auri ƴar uwarku kamar yadda kuka damu tabbaci hakan daga gidan marayun. Kuma mahaifina ya ɗauke ta ne bisa ƙa'ida. Muna zaune da ita har Allah ya albarkace mu da samun haihuwa, muka haifa ƴa mace mai suna Ma'eesha. Wanda a yanzu Ma'eesha tana da shekaru goma sha takwas zuwa sha tara. Kuma sai dai ina mai matukar ba ku hakuri ƴar uwarku ta rasu watanni huɗu da suka wuce." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un." Kalmar da suke furtawa kenan lokacin da suka ji labarin mutuwar. Jikinsu ya yi sanyi musamman Alhaji Sulaiman da ƴaƴansa. "To ina ƴar da ta haifa?" Nan ne kowa ya yi shiru don ba mai bakin ba da amsa a cikinsu. Sai da Alhaji Sulaiman ya sake tambaya a karo na biyu sannan cikin sanyin jiki Daddy ya ce "Ban san in da yake ba?" "What? Wanan ma ai zancen banza ne!" Kabir ya faɗa yana miƙewa tsaye. Ita kuma Laila da take tsaye ta bude baki cike da tsiwa ta ce. "Kamar ya zancen banza, nan ba wanda ya san inda take ku je can ke neme..." Kafin ta kai karshen zancen da take son faɗa ta ji saukar lafiyyaen mari wanda ya sa ta wuntsilawa ta faɗi, wani duhu take gani sannan da wani sautin shuu da take ji a kunnenta jin ta da ganinta ya ɗauke na wuccin gadi. Ƙaramar mara kunya, na sake jin kin yi magana a wajan nan." Gabaɗaya falon suka juya suka kalli Captain Kabeer wanda ya yi ma ta marin. "Mamy ina kike ba na ganin komai sai duhu." "Na shiga uku daga magana kake neman makantar mun da yarinya ka kashe ma ta kunne?" A hankali ganinta ya fara dawowa ta sauke isanunta akan Kabeer wanda ko shakka babu ta san cewa shi ne ya mare ta. Kuka take yi tana son ta yi wata maganar amma ta kasa. "Alhaji ka yi ma ni cikkaken bayanin komai domin mu san in da za mu ɓullowa bakin zare. Nan Daddy ya ba su labarin duk abin da ya faru bayan rasuwar mahaifiyar ma'eesha zuwa hukuncin da Mamy ta yanke na aurar da Ma'eesha ga makaho . Da yadda komai ya faru har zuwa ranar da makaho ya dauke ta suka bar gidan ba su sake saka su a idanu. "Wani unguwa suke zaune?" Cewar Alhaji Sulaiman da idanunsa suka kaɗa suka yi ja. "Ba wanda ya san unguwar da suke, ko shi kansa ba wanda ya san in da yake." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un." "Amma ka ɗauki ƴa ka ba shi, ba ka san shi ba ba ka san unguwar da yake ba? Dole na shigar da kara akan ku." "Wallahi ba llaifina ba ne, matata ta kawo shawara ni kuma duk da na ƙyamaci abun. A zuciyata amma na kasa hana ta. Duk hukuncin da ta yanke ba na iya cewa komai, duk da a zuciyata ina jin ba daidai ba ne amma ba ma iya cewa komai" "Wanan matsalarku ce idan muka shigar da kara akanku za ku nemo in da take." Mamy hankalinta ya tashi ta rikice . Shiru Falon ya ɗauka kowa ya kasa magana, yayin da ake yi wa Mummy kallon zargi. "Ko z mu iya ganin photon su?" "Eh za mu samu." Cewar jam'i ya nufi dakin da suke ajiye kayan ajiya. Don lokacin da Laila za ta koma ɗakin Ma'eesha fa zama duke kwashe kayan fa basu bukatar su. Suka kai can. Bayan Wai mijina dawo da photon dake manne a bangon ɗakin Ma'eesha.sai wani guda daya na Ma'eesha tana sanye da hijabi ranar da ta yi waliamar saukar Alqur'ani mai girms. Gabaɗaya suka zuba wa photon idanun. Barrister Haidar ya mike tsaye yana cewa. "Wallahi ita ce. Ita ce na gani ba kowa ba, ita ce wallahi na kusa kaɗewa da mota , har Kabeer na ma ta fadar ba ta da hankali ne. Ta ba mu hakuri ta tafi." "Da gaske kake faɗa? To ina kuka ganta kuma ina ta nufa a lokacin.?" "Wallahi ba mu sani ba, amma da dukkan alama tana cikin tashin hankali, yanayin ta ma ys nuns hakan, don idsnunta ma a kumbure suke." "Ko zu mu tafi, amma ku sani da ka amsa za ku amsa kira daga kai har matarka, duk in da kuka kai yarinyar nan sai kin fito da ita. Idan kuma ba haka ba sai kunyi nadamar mafi muni a rayuwarku." Daga haka suka fice daga gidan rai a ɓace.. _Ma'eesha_ Bayan mai nape ya sauke ta s tashar mota ne ta nufi cikin tashar. Wani ya ganta ya ce . "Tafiya za ki" "Eh." "Okay wani gari za ki je?" "Bauchi." "Okay to yanzu ga motar da ke kan layi ba ta cika ba za ki ɗan jira kaɗan." "Ba damuwa." "Bisimillah ga wuri ki zauna." Ya yi magana tana nuna ma ta wani benci dake gefe. Ƙarasawa ta yi ta zauna saman bencin. Kifa kanta a saman cinyarta ta yi tana kuka kasa-kasa. Abubuwa biyu ne suka taru suka cunkushe ma ta zuciya. Na ɗaya ƙwryar da ya yi ma ta na tsawon watanni ba tare da ya sanar da ita gaskiyar lamari ba. Na biyu kuma kishin auren da zai yi. Domin gani take yi ba sonta yake yi. A zaman da suka yi tare da juna. Domin a tunaninta ita ce take son sa amma ba shi ba. Bai ɗauke ta matar aure ba sai yanzu ne yake so ya auri wacce yske so. Sam ta kasa gane cewa yana gani tsawon watanni da suka yi a tare ba ta taɓa tunanin ba makaho ba ne. Sai yanzu wasu abubuwan suke zuwa ma ta akai. Ranar da ta cire kaya a gabansa jikinsa ya dinga rawa kamar mazari. Wanda ko da ta tambaye shi cewa ya yi baya da lafiya ne. Sha surar jikina ne ya kiɗima shi. Da kuma idan za ta cire kaya sai ya yi saurin fita ya bar ma ta ɗakin. Har wata rana ya ce ma ta ta daina cire kaya a gabansa duk da ba ya gani. Sannan ranar da aka yi ruwan sama tana wanka har ta shiga rawar sanyi ta tuɓe kayan jikinta. Ba ta ɗan yana ɗakin ba tana lalube ta ci karo da shi har ya rungume ta ya yi kissing nata. Ga abubuwa da yawa da ya kamata a ce ya zarge shi amma ba ta yi hakan ba. Kuka take yi kasa-kasa. _Haidar_ Yana rungume da photon Ma'eesha da na mahaifiyarta. "Ka san Allah ko Kabeer yarinyar nan ita na gani na kusan kaɗewa da mota." Captain Kabeer dake driving ya ce. "To me ya sa ka bari ta wuce?" "To wata hujja ne da ni da zan tare ta akan cewa ita muke nema? Duk da lokacin da na kalle ta sai da zuciya ta ta buga. Na ji wani abu a raina game da ita. Duk da cewar tana kama da Dada amma hakan ba yana nufin na ce lallai ita ba ce. Ya yi magana yana kallon ta sosai. Fara ce doguwa ba ta da ƙiba. Duban manyan idanunta ya yi har zuwa dogon hancinta da karamin bakinta. "Wallahi kamannin Dada ta ɗauka sai, wata kila ma tafi Fadar kyawu." _JB_ Horn yake dannawa ba kakkautawa wanda duk wanda yake gidan kama daga ƴan gidan zuwa ma'aikatan gidan kowa ya san cewa shi ne ya dawo . Hatta maƙotarsu idan suka ji wanan horn na rashin mutunci sun san shi ne. A guje maigadi ya wangale gate ɗin gidan dan kada ya ɓata lokaci JB ya tafka ma sa rashin mutunci kamar yadda ta saba. A guje ya shigo cikin gidan, bayan ya yi parking dai da ya kwashe mintuna goma a cikin motar bai fito ba. Ko da ya fito daga motar duk wanda ya kalle shi in dai ya san shi to ya san cewa yanayinsa ya canza da akwai abun da ke damunsa. Domin shigowarsa cikin gida ma kawai idan ka gani ka san cewa shi ne kaɗai ya fita Zakka a cikin gidansu. Tura kofar Falon ya yi ya shiga kai tsaye ba tare da ya kalli cikin falon ba ballanta ya ɗan su waye a ciki. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya tura ƙofar ya shiga ciki. Mahaifiyarsa wacce suke kira da Mimi tana zaune a falon tana tattauna wata magana ita da Yayansa Munnir. Da kallo suka bi shi domin sun ga yanayinsa ya sauya jikinsa a sanyaye yake. "Kamar wani abu na damun Autana." Nima haka na gani Mimi. Allah dai ya sa ba wata maganar ya ɗauko ta dame shi ba." Cewar Munnir din cikin damuwa. "Amin ya Allah, wallahi duk lokacin da Jabeer ya bar gidan nan ba na da kwanciyar hankali har sai na ga dawowarsa. Ga shi baya jin maganar kowa mahaifinsa ya riga ya ɓata shi duk yadda na so gyara shi abun ya ci turaz sai na gyara can sai ka ga ya ɓalle ta nan." "Addu'a za ki cigaba da yi ma sa Allah ya shirya shi." "Addu'a kam ina nan ina ta yi ma ku." "Dare ya yi ya kamata ka je wajan matarka" "Okay bari na je na ji meke damunsa kafin na tafi." Ya tashi ya nufi ɗakin Jabeer, yana kwance ya yi ruf da ciki ba abun da ke ma sa yawo a kansa sai abun da ya aikata wa Sidra. Kukan ta ne ya ke ma da amsa kuwa a kunnenta, abu biyu ya tsaya ma sa rai . Na ɗaya bai taɓa mu'amala da cikakkiyar budurwa ba sai kanta. Na biyu kuma yadda ba da son ranta ba bisa tilas ta amince da hakan. Wanda shi dai dai mace ta kawo kanta da kanta wajansa, kuma ya san duk ƴan hannu ne sun saba, ita kuma fa? Me ya sa Sady baby ta yi masa ƙaryar ciwa ita ma ƴar hannu ce kada ya damu. Bai taɓa nadamar yin zina ba sai yau. kusan a tare Yaya Munnir da mai aikin girkinsu suka nufi ɗakin Jabeer. Ita mai aikin gidan ta jera abincinsa a faranti za ta je ta kai ma sa. Tana shiga da sallama bai amsa ba hakan bai dame ta ba ta saba. Tana kokarin ajiye abincin sanan table dake gaban sofa ya daka ma ta tsawa. "Uban waye ya ba ki iznin shigo min ɗaki?" "Ka yi hakuri abincinka na kawo ma ka." ."idan ba ki ɗauke shi kin fita ba sai na tafka ma ki rashin mutunci banza jaka kawai" Ta fita da sauri ta san shi idan ta tsaya jayayya zai iya kai ma ta duka. "Assalamu alaikum warahmatullah" Munnir ya yi sallama ya shiga. Bai amsa ba idanunsa a lumshe. "Meke damunka duk ka canza?" "Mallam dalla ka fitar mun daga ɗaki, bayan ka gama munafurcinka wajen Mimi ka haɗa ni da ita sanan ka zo kana tambaya ta, to ban sani ba!" Nurmushi Munnir ya yi yana kallon ƙanin nasa yana cewa. "Kai kullum maganarka ina baya ka a wajen Mimi, to ka sani ba abinda nake faɗa mara kyau a gare ka, ka canza halinka idan ba ka ga Mimi ta so ka fiye da kowa ba.". Tashi tsaye ya yi yana yi na da wani kallon banza kafin ya ce "Mallam fitar mun daga ɗakin munafu..." "Tas" ya ji saukar mari a kumatunsa. Rintse idanunsa ya yi ya san ba kowa zai mare shi ba face Mimi ce. "Wai me ya sa ba ka da mutunci ne?" "Da kin ƙyale shi Mimi yana da damuwa na lura da hakan." "Idan yana da damuwa sai ya sauke kan mutane? Tun yaushe mahaifinsa ya dawo kasar nan, yana dawowa shi ya fara tambaya. Ina ka je ne tun safe !?" Bai tanka ma ta ba kuma baya da niyyar yin maganar. Ta bude baki zata fara masifa Mahaifinsa ya shigo yana cewa . "My son Ina ka je ne tun safe wayarka ba ta shiga?" Ganin halin da suke ciki ne ya ce . "Me kuma aka yi ma sa waye ya ɓata ma sa rai? Amma kun san ba na son ɓacin ransa a gidan nan ko? Me ya sa za ki yi ma sa faɗa hakan yaro ai ɗan hakuri ne." Cike da takaici Mimi ta bar ɗakin. Munnir ya mara ma ta baya suka fice. _Jalaluddeen_ Yawo kawai yake yi da mota s garin Kaduna ba tare da ya san in da zai nufa ba. Gefen hanya ya yi parking ga yinwa dake ɗawainiya da shi, wanda rabon da ya ci abinci tun jiya da rana. Kifa kansa ya yi a sitiyarin motar yana tunanin ina ya kamata ya tafi neman ta . Yau kadai gare shi, gobe dole ya koma Abuja bisa umarnin iyayensa. Magana ya fara yi shi kadai kamar wani zararre. "Ina kika tafi Ma'eesha, kewa kwanciyar hankalina, idan kina kusa da ni zuciyata tana samun salama. Ina godiya da Allah ya haɗa rayuwata da taki. Kullum ina kara son ki fiye da jiya. Murmushinki yana sa ranar tawa ta yi haske. Ba kyawunki kadai nake so ba ina son zuciyarki da kyawun halayenki. Ko da mun samu saɓani baya rage irin son da nake yi ma ki. Kece Aminiyata matar da nake son na raba rayuwata da ita har karshe. Ina alfahari da ke, kuma zan cigaba da kula da ke gwargwadon iyawa ta. Na gode da haƙurin ki da kuma ƙaunar da kika nuna ma ni. Ina so na zama wanda zai goge ma ki hawayenki tun kafin su zubo.Ina kike Ma'eesha?" _Fahad_ Dawowarsa gida kenan ya zauna akan kujerar dake Falon sama. Wani karamin box ne a hannunsa ya ajiye gefensa. Fitowar Nadra kenan daga kitchen za ta shiga ɗakinta ta ji ya kira ta . "Nadfah." "Na'am yaushe ka ka dawo.?" Ta yi magana tana karasowa inda yake . " Zo ki zauna kusa da ni." "Lafiya wanan kallo haka kamar za ka cinye ni?" Ya janyo ta ya zaunar da ita saman cinyarsa. "Ina kallon ni'imar da Allah ya ma Ni ne, wani lokaci har mamaki nake yi, me na yi da na cancanci samun mace kamar ki?" Ta yi murmushi. "Yau dai kana nema wani abu a wurina." Dariya ya yi tare da cewa "Ba komai nake nema ba, ina so ne kawai kisan cewa ina son ki ko da ban faɗa kullum ba zuciyata kullum tana fadin haka." "Ni ma ina son ka." "Ki yi ma ni alkawarin idan wani abu ya dame ki ba zaki yi shiru ba, ni ne abokin rayuwarki." "Na yi ma ka alkawari." Ya sumbaci goshinta. Sanan ya dauko wani karamin box din nan da ya dawo da shi ya ba ta . Karba ta yi ta bude. Ɗan kunne da sarƙa ne na gold, har da warwaro da zobe. Zaro idsnunta ta yi sanan ta rungume shi tana cewa. " Allah ya ba ni ikon faranta ma ka rai kullun." "Amin ya Allah, Murmushin ki nake so na gani kowane rana." Murmushi ta yi. "Tare de Farida za mu je America." Take murmushin dake kan fuskarta ta gushe. "Ya dai ko akwai matsala ne?" Murmushin karfin hali ta kirkiro tana cewa "Ba komai Allah ya kai mu." "Amin ya Allah. Don Mama ta ce ba ta yarda na bar ki a ƙasar nan ba tare da ke ba umarni ne ta ba ni." _Mamy_ Gabaɗaya sai sintiri take yi a falon ta, sakamakon rashin ganin Ma'eesha. Don Jamil ya faɗa ma ta cewa ya je gidan bai samu Ma'eesha ba an ce ba gidan suka kwana ba daga ita har mijin nata. Dama ta ki faɗa ne don ba ta son Ma'eesha ta hadu da dangin mahaifiyar ta. Musamman da ta lura manyan mutane ne karshen wahalar Ma'eesha zai kare. Shi ne ta tura Jamil ya je ya duba ko Ma'eesha na gidan ya je ya dawo ba ta nan. Cikin tashin hankali ya Jamil ya shigo falon yana cewa. "Dangin Mahaifiyar Ma'eesha fa sun shigar da kara akan ke da Daddy, yanzu haka ana bukatarku a offishin ƴan sanda." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un na shiga uku na lalace, yanzu ina zan nemo makahon nan a kama shi ya fito ma su da ƴarsu." *To Alhamdulillah, nan na kawo karshen littafin MAKAHO NE book 1, kuma shi ne free pages, book 2 kuma paid book ne. Normal group ₦500 ne posting sai ɗaya a rana. VIP group kuma 1k ne, posting sai biyu a rana, da ya zama complete shi ma kudinsa 1k ne. Sai s tura kudin ta wannan account number 2242538358 sai s tura shaidar biya ta wanan account number. 09065327995*