*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ ꨄ Ɗan...ɗano 🤫😢........ Unexpected and Surprising 🔥💥 Our official trailer for the incoming ƘARSHEN ƘADDARA.... 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. This Book is dedicated to you *NA'EEMERH SULAIMAN SARAUTA NIMCY LUV* 1&2 ★... The writer's of MIKIYA TA DABAN DUNIYARMU RAMIN KURA KAREN BANA ƘAUNA BIYU JALAAL AREEF SO DAN RAYUWA DUHU na dukan DUHU And Now ƘARSHEN ƘADDARA ★ ꨄShin ta ina ya kamata ace ma na fara muku ne?,saboda nasan kan kowa ze kulle ne da tambayar ta ina ƙaddara take da ƙarshe???. Ehhhh lallai kuwa wannan nazartaccen littafin yaci suna mu ƙira shi da suna ƘARSHEN ƘADDARA. Saboda ita kanta ƘADDARAR tana gwada zuciya ne, ba don ta karya ba, A ahh sai don ta shirya ka zuwa wani mataki mafi ƙololuwar girma da daraja, don Kalmar ƙaddara bata gama garin mutane bace. Ita kanta yawaitar ambatar kalmar ƙaddarar tana zama ne tamkar ana mana washin KWAƘWALWA neeee. Se dai da yawan mutanen da ƙaddarar ke ci sukan tambaya kansu da cewa. _Amma me yasa ita ƙaddarar take cin mutane marasa laifi?_ Sedai amsar anan itace abinda ALLAH ya rubuta zai faru da rayuwar ɗan Adam, komai ƙarfin halinsa, komai tsarinsa, komai wayonsa. Dole akwai wani labarin dake sanja hakan kwarai, Anan ina son mu sani cewar wannan kaddara ce abin da ALLAH Ya rubuta, hakan na nufin babu wanda zai kauce masa kenan, duk kuwa iya gudunka duk iya saurin ka, sedai mu sani ba nufin ALLAH bane ya zaluncemu ba. Sedai mu sani cewar ALLAH yana da hikimarsa nayin hakan a cikin duk abinda yaga dama, Domin Ƙaddara tana koyar da mu abubuwa da dama… ★.. Ta farko- Rayuwa ba ta tafiya yadda muke so sai dai yadda ALLAH Ya so. Ta biyu- Kowane abu da ke faruwa ko da zafi yake, to tabbas akwai alheri a cikin hakan idan akayi hakuri aka jure, Ta uku- Mutum ya kasance mai haƙuri da godiyar ALLAH kan duk lamarin daya gindaya masa, saboda duk lokacin da kaddara ta same ka kayi hakuri kayi juriya ka kumayi gwagwarmaya karka taɓa bari ka sare don hakan yana cikin jarrabawarka shima. Mutane da yawa suna fuskantar tarin ƙalubalai a cikin rayuwa, wasu rashin lafiya ne, wasu kuwa rashin aure ne, wasunmu kuma suna fama da talauci ne me zafin gaske, saboda kar bawa yaga tarin ƙalubalai na bebeye dashi yaga kamar cewa ko duniyar tana mantawa dashi ne, to maganar gaskiya anan ita ce ba kai kaɗai bane, duk wanda ka gani me rai a cikin wannan duniyar to lallai tabbas yana fuskantar ƙalubale, sedai na wani yafi na wani tsanani... ALLAH yana gwada bayinsa da hanyoyi daban-daban ne domin ya ga wanene zai yi haƙuri, wanene zai ci gaba da yin addu’a. ƘADDARA bata nufin ka zauna babu ƙoƙari. A’a, Ka yi ƙoƙarinka, ka nemi ilimi, ka nemi arziki, ka nemi aure, saidai sakamakon na hannun ALLAH ne. Sabo da manyan mu sukan ce damu kada mu bari rayuwa ta koya mana baƙin hali. Idan ƘADDARA ta rufe ƙofa guda, tana buɗe wata da kuka bai bari mu gani ba... ꨄ Kada ka bari ganin wani yana samun nasara ya sa ka watsar da damar da kake da ita. Abinda ALLAH ya ƙaddara naka ne, to kuwa lallai naka ne don nasarar ka ba zata taɓa wuce ka ba. Ka nemi Albarkar iyaye, kuma ka nisanci hassada,duk ƙanƙantarta kuwa. Amma kuma kada ka taɓa barin ka gayyato bakin ciki cikin rayuwarka, ‎ kada ka zama me aje nauyin da wani ya ɗora maka shi, kada kuma ka bari kalaman wani ya dameka, ‎Kar ka taɓa bari kunci, baƙin ciki da damuwa su sama matsugunni su zauna a zuciyarka tamkar baƙon da yasamu gurin zama. ‎ ‎Me yasa zaka ɗauki nauyin kalaman wani? ‎Me yasa zaka aje abin da ya faru da kai ka maida shi ciwo a zuciyarka?...... ‎‎Idan kana cikin jinya, ko kana fuskantar ƙalubale da barazana ka ringa tuna abu ɗaya, ‎ALLAH baya gwada bayinsa don ya hallaka su, amma Sai don ya gafarta musu, ya ɗaukaka su ya kuma koya musu ƙarfi da gwagwarmaya tamkar RAYUWAR AMEENERH SHEHU USMAN.... ‎ Tabbas ‎akwai darussan rayuwar da ba zaka taɓa koyarsu cikin nishadi da Jin daɗi ba sai ka shiga ƙunci. ‎To me zai sa ka bari damuwa ta fara cinye zuciyarka idan ba za ta warware komai ba? ‎Damuwa ba ta kawo mafita sai dai ta ƙara nauyin zuciya. ‎Ka saki zuciyarka ka bar komai a hannun ALLAH, ‎ka kuma dage da addu’a. Domin ALLAH yana tare da kai fiye da yadda kake zata.A wannan zamanin ‎ƙaddara idan ta same ka, kaddara ce. Amma idan ta faru ga wani namu, sau da yawa mu kan dauke ta ne a matsayin iskanci ko kuskure. A fahimtar gaskiya a duk duniya dan adam bashida na biyu ba kowa bane yake iya gane asalin zahirin mene ne ƙaddara acikin rayuwar mutum Rayuwa da kake gani a waje ba ita ce cikakkiyar rayuwar zuciya ba. Tun daga ranar da aka halicci zuciya a cikin jiki, ALLAH ya bai wa mutum ikon sarrafa tunaninsa, Daga nan ne ya zama ba kowa ne zai iya fahimtar damuwa ko farin cikin wani gaɓa daga cikin rayuwarmu ba, Saboda haka idan ka ga wani yana rayuwa cikin ƙalubale, ka sani ba lallai ka fahimci abin da yake ciki ba, Idan ba za ka iya taimaka masa ya fita daga halin da yake ciki ba, kuma ba za ka iya saka shi cikin addu’arka ba, to mafi alherin shi ne ka bar shi cikin mutunci ba tare da sukar rayuwarsa ko halin da yake ciki ba inda ZAN BA KA SHAWARA.... To shi ne ka guji zama da Mutane masu yawan janjanin magana, domin ba tare da sanin kaba suna rage maka ƙarfin zuciya ne, su kuma iya hana ka ci gaba. Hulɗa da su na iya mayar da rayuwarka wuta, domin kullum suna kallon ɓangaren mara kyau na rayuwa, suna yaɗa damuwa da rashin kwarin gwiwarka. ★Amma idan ka kusanci masu godiya da yarda da ƘADDARA, zaka ga rayuwarka ta cika da nutsuwa da farin ciki, Mutane masu zuciya mai kyau suna ƙarfafa ka, suna sa ka kaɗa baki da murmushi harma su wanzar da farin ciki cikin rayuwarka, suna kuma nuna maka cewa rayuwa tana da daraja duk da ƙalubale sun cinye ta, to waɗan nan mutanen su ne abokan tafiya na gaskiya, domin suna kallon alheri a dukkan yanayin da kake a ciki, suna kuma karfafa ka ka ci gaba da neman nasara tare da gwagwarmaya. Domin sune rayuwa ta yar dasu, mu zaɓi irin mutanen da muke hulɗa da su. waɗanda idan ka zaɓi masu kuka, zaka sha wahala. Idan ka zaɓi masu godiya, zaka sami kwanciyar hankali ne da nasara, don haka mu kusanci masu son farin ciki da nasararmu, domin su ne za su taimaka mana har zuwa lokacin da zamu gina makoma mai kyau. To amma duk hakan baya faruwa se anyi hakuri da ƙaddara, domin duhu baya dawwama, haske zai zo duk runtsi, ‎Abin da ya same ka bai wuce rubutacciyar ƙaddara ba, sedai me???. Wata ƙaddarar da kuɗinmu muke sayenta. Ehhhh lallai tabbas da kuɗinmu muke sayenta... Saboda muna fifita addinin kiristoci fiye da namu a wannan zamanin. Shin ba kun matsu kuji ta yanda muke sayen mummunar ƙaddara da kuɗinmu ba?,mu kuma zaɓeta da kanmu da hannuwanmu ba?, To nidai AMMEY LAYLERH nace babu ruwana AMEENERH SHEHU USMAN wacce akafi sani da *DR MEENERL itane zata banbance mana me hakan ke nufi.... Kun shirya a kafta???.... _Kun shirya jin ta yadda da kanta ta zaɓa mummunar ƙaddarar?, ta hanyar kin bin dokoki da darajar dake cikin aure?, ta fuskanta tarin ƙalubalai masu tarin yawa, cikinsu kuwa har da ƙaddarar AURE AUREN mazan data dinga yi mabanbanta?, Ƙaddarar Fyaiɗen da rashin daraja AURENTA da ya hau kanta, wannan shi ne matakin farko kuma shi ne wasa farin girkin nata_. *Kun shirya jin ta yadda ƙaddarar nata zata zo ƘARSHEN kuwa?*. Dan dai idan nace *ƘARSHEN ƘADDARA* is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta *ƘARSHEN ƘADDARA* ba zan iya cewa an barki a baya SIS. Don It is going to be a hit, that I promise you. Saboda tafiyar *ƘARSHEN ƘADDARA* da banbanci da sauran littattafai na baya, yeah banbancin kuwa ma shi ne about 90% na littafin ƘARSHEN ƘADDARA is based on true life events ne, musamman daga farkon sa zuwa gaf da ƙaresunsa, karshen sa ne kawai zai zama fiction ta yacce zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shi ne from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share ruwan hawaye, so get ready to do both💃🤸......... ♡♡♡ ꨄ Tsaye Matashiyar matar da kallo ɗaya za ka yi mata, ka fahimci shekarunta na aihuwa ba zasu wuce Ashirin da biyu da yake gogayya da rayuwarta ba, tsaye take gaban Madaidaicin mirron ɗakinta me kyau da tsari, wanda yake a gyaren da kallon farko zakama ɗakin da wacce take tsaye gaban mirron ka tabbar da cewar me tsafta ce, tun daga yanayin yadda ɗakin nata ke a tsaftace tsaf, jikinta kuma na ɗaure da wani blue towel se faman shafe shafe take yi kyakkyawar fuskanta, wacce take ɗauke da zallar farin cikin fitanta aiki na farko yau da zata fara, wanda kai da ganin yadda take cikin farin cikin zaka tabbatar da cewar lallai wannan aikin nata me girman matsayi ne a cikin ranta, soson powdern dake hannunta take sake goggawa chocolate ɗin fatar fuskanta, wacce ta zarta mu ƙirata da baƙa sedai bata kai mu ƙirata da fara ba kuma, wannan dalilin yasa muka bata chocolote ɗin kai tsaye. Lipstick ta sake ɗauke tana gogoma lips nata wanda take suka ɗauki shining na kyau da sheƙin abinda aka goga musun, eyeliner ta sake ɗauka tana gyara eyelashes nata again kuma tana ci gaba da gyara duk abinda be mata ba, har zuwa dogon wuyanta shima da take sake gyareshi da soson powdern. Ta ɗan ɓata lokaci me nisa a nan tsaye a wurin, kafin ta miƙe ta nufa gaban wedrop nata me shida, irin me madubi da katifar nan ba laifi suma sun yi kyau babu ƙarya, kayan ta shiga bi da ita tana research da idanunta na wanda ya kamaci ace ta saka, haka har idanunta suka sauƙa akan wata lafiyayyar abayarta black, wacce take ta cikin kayan lefenta ce kuma bata taɓa sakata ba, don haka kai tsaye takai hannunta tana tare kayan dake ƙasa da sama kasancewar rigan itane a tsaƙiyan kaya, ahankali ta janyota bayanta ta ɗan gyaggyara kayanta da suka zamo wosu kuma suka yi ciki. Zame towel ɗin dake jikinta tayi bayan ta zira wata sitred riga daga jiki linor, kana ta ɗora abayar tare da komawa gaban madubi tayi Rolling kanta da vail ɗin da bai kai ya kawo ba na abayar, tsaf kuwa tayi kyau ta kuma karɓu cikin shigan daya mata wani kalan kyau na musamman. Turaren dolcy nd gabbana ta feshe ilahirin jijinta dashi, kana ta wuni nufi ƙofa tana taku ɗay ɗay kamar bata taka ƙasa ba, tin kafin takai ƙofar parlourn ta take famar kwala ƙiran. "Baby!Baby!!Baby!!!" Tana ci gaba da tunkarar ɗakinsa tana sake tunkaro ƙofar bedroom nashi, tana ci gaba da mitar ta "Haba Baby har yanzun baka tashi bane mun makara fa?" Tayi maganar tana wani ɗan zazzaga parlourn irin a matse ɗin nan take, "To wllh sedai ka biyo napep don Wllh nidai tafiyana zan yi....." Takai ƙarshen zancen nata tana kaiwa zaune saman kujerarta me kyau, ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani jijjiga jiki. Babu jimawa sega takun tafiyarsa nan na tunkaro inda take zaunen, zama yayi kusa daf da ita yana ɗan kishin gida daga zaunen da yakai, fuskansa da murmushi sosai ya ce. "Kai My luv yanzun duk wannan zumuɗin fara aikin ne haka?, to yanzun dai a taimakeni da abinci don yunwa nake ji...." Fuskanta ta saki kaɗan tana miƙewa,babu jimawa se gata ta dawo hannunta riƙe da cooler na abincin data yi tin farar safiya, ajje musu tayi tana buɗe cooler'n kai tsaye ƙamshin couscous ɗin data ma lafiyayyen haɗi na dukar hancinan su. Wani ɗan lumshe idanunsa yayi yana sake jin ƙaunar matar nasa na sake bebeye shi, ta iya komai na cikin rayuwa tin daga kama kan kula da kanta, Mijinta, cikinsa, haƙƙinsa, da duk wasu al' amura nashi. Saƙƙowa yayi yana me furta. "ALLAH yama Meenoh na albarka, ya saka miki da gidan aljannarsa mafi tsada..." Wani kallo ta masa wanda ya saka shi kusan sarƙewa da yawun da ya taho kai tsaye daga cikin maƙoshinsa, don shi kaɗai yasan iriyar masifar ƙaunar da yake ma wannan baiwa tashi, gaba ɗaya jinta yake a ko ina na jikinsa, jinsa yake daga kanta ya gama aure IN SHA ALLAHU, domin duk abinda yake so yi masa take kai tsaye babu shamaki, a natse sukaci abincinsu cike da ƙaunar junansu... ruwan swan suka sha me sauƙin sanyi kasancewar ita da kanta ta saka musu dokar hana shan ruwa bame sanyi ba sosai, daga nan ya miƙe yana ce da ita _just 15 minutes_ kanta ta ɗaga mishi tana sakar masa murmushin daya kusan kashesa da ransa, da yar sassarfa ya nufi bedroom nata don babu jimawa kuwa se gashi ya dawo sanye cikin tattausan shigar shadda brown color, wacce ta masifar amsar nasa jikin, don sosai daga ita har shi suke da wani irin sahihin kyau me sanyi da nutsuwa, ba wai irin me ɗaukar hankalin nan... Kallonta yayi daga sama zuwa ƙasa ganin yacce ya tafi ya barta haka take, don haka yace "Baby ya naga ke baki shiryo bane?" Kallonsa tayi ta kuma kalla shigar dake jikinta tana miƙewa tsaye, tsadaddar wayarta me ƙirar _TECNO POP 9_ ta ɗauka tana cewa. "Kaga muje don ALLAH Ya Ahmad lokaci na ƙurewa kaga wannan shi ne karo na farko kar inji a makare...." Tayi maganar tana ƙoƙarin ficewa a parlourn, hannunta ya ɗan jawo yana dawo da ita baya, cikin komawa seriously nashi yace. "Yanzun don ALLAH Meenoh ke idan na ƙyaleki seki fita a hakan?" Cikin yanayi na ɗan fusatuwar data soma tace. "So what idan na fita a hakan Ya Ahmad?, kalla ka gani a suturce nake fa!, ko kuwa illa ka gani tattare da shigan dake cikina?, ya zaka fara abu kamar wani wanda be waye ko ya shiga class ba?" Ta ƙarasa maganar tana fita a ɗan kamar fusace, da sauri ya biya yana bama zuciyarsa hakuri akan cewar wannan ɗin ba komai bane sharrin shaidan ne. Lokacin da yake fitowar kuwa har me gadi na ƙoƙarin buɗe mata get zata fita ta tara napep, saurin dakatar dashi yayi yana isa ya kamo hannunta cikin nasa yana kallar tsaƙiyan cikin idanunta yaje... "Oya les't go!, ko in na barki kin fita ke kaɗai kinsan hospital ɗin ne?, kuma wurin wane zakije?..." Se ya ɗan shiru daidai lokacin da yake buɗe mata gefen me mazan banza a motar, shi kuma yana komawa driver sit ya zauna, Ahankali yakai hannunsa yana lakatar dimple nata da yake gefe guda yana cewa. "Bestien Besty rigima..." Daga haka yaja motar tasa me ƙirar GLK bugun 2025/2026 suna barin harabar gidan, hannunsa na cikin nata ɗaya yake driving ɗin wa'azin Marigayi *SHEIKH MUHAMMAD AUWAL NASEER ALBANY ZARIA* Na tashi a cikin motar me suna *IN KASAN WATA* Sabo da sosai yake son wa'azin Malamin, sabo da matuƙar feɗe gaskiyar sa da yake yi.... Haka har suka isa katon private Hospital ɗin da anan ne yayi duk wasu cuku cuku ya nema mata aikin nata, tin da suka shigo cikin harabar asibitin take kallar tsari da yanayin ta aka tafiyar da ginin wurin kawai na yi mata hundred percent. Ci gaba da bin komai da ido tayi a cikin zuciyarta tana ayyana lallai Ahmad na manyan mutane yana kuma da hannu da manyan, in banda hakan ta yaya ita AMEENERH SHEHU USMAN ta taɓa zata ko tsammatar cewar zata taɓa aiki a ko me kama da wannan asibiti ne, amma se gashi sanadiyyar Mijin nata yau wai ita ce da aiki a wannan tsadaddar asibitin da a da sedai ta hangeta daga nesa nesa, wanda koda a tunani bata taɓa kawo cewar zata zama ɗaya daga cikin ma'aikatan asibitin ba, don ta san cewar ko aikin zatayi tofa sedai ta ƙare a na gwamnati, wanda inta sama aikin ana gwamnatin ma kenan ita nata yayi kyau, amma se gashi yau ata sanadiyyar Mijin nata yau gata a matsayin ma'aikaciyar asibitin, Ikon ALLAH fa kenan, Lallai ta sake yarda cewan Ikon ALLAH shi ne gaba da komai. Wata doguwar ajiyar zuciya ta kawo lokacin da yake farkar da ita daga tunanin data ɗan shilla. Ƙafanta dake cikin wani vk shoe ta fara zirowa me laushi sosai plat me kalan jikin miski, kafin ta fito a natse tana buɗe kofofin hancinta ta shaƙi iskan cikin asibitin da kyau idanunta a lumshe, zagayowa yayi daga mazaunin nasa yana dawowa ta setin da take, tare da kama murfin motar ya zuba mata kyawawan idanunsa, wani numfashi ta ɗan shaƙa tare da buɗe idanunta tar kuwa se akan Babyn nata, wata iska me ɗan nauyi ya fesar yana sarƙe hannunsa a ƙirji tare da sakar mata da wani tsadadden murmushinsa me kyau. "Les't go idan DR. Meenerl ta gama abinda take yi...?" Taji muryan mijinta abin sonta da bata taɓa haɗa shi da kowa, wanda suke yau kimanin watanni Bakwai kenan da aure, amma idan ka kallesu zaka iya shan cewa sun kai irin fin shekarun nan ne a auren, bawai don zaka gane hakan bane ata siffar jikkunansu, A ahhh sedan ta iriyar shaƙuwar dake tsakanin nasu, amma kai idan har ta suffar jikkunan nasu ne tsaf zaka iya ƙiransu ma budurwa ne da samrayinta. Fitowa tayi suna jerewa a tare suka soma tafiya suna ƴar firarnsu suna ƙaramar dariya ƙasa ƙasa, duk wanda suka haɗu dashi a hanyar kuwa seya sake waywayensu koda ya wuce, don yanda suka matuƙar dace da juna. A gaban wani babban office suka tsaya yana zaro wayarsa ƙirar iphone ya saka ƙira a wata number, wayar second yayi yana datse ƙirar, babu jimawa sega wata nurses ta ƙaraso tana musu iso, gaba tayi suka take mata baya har zuwa babban parlourn dake cikin office ɗin, ruwa da lemu ta kawo musu tana ajjewa gabansu bayan ta sake gaidasu, fita tayi ta wata ƙofan daban can kuma babu jimawa sega wani hamdsome guy ya fito sanye cikin labcoat na likitoci sky color, wuyansa rataye da Patient screening hannunsa cikin handglov kansa da surgical cap, zama yayi kujeran dake fuskantar su fuskansa da murmushi sosai, "Barka da zuwa abokina, na ɗan ɓata muku lokaci ko?" Yayi maganar yana miƙa masa hannu tare da sake cewa yayi hakuri wata Surgery ce ya shiga ta gaggawa, "Ba komai DR BILAL" yace masa yana dawo da dubansa kan Meenal. gáidashi a mutumce tayi duk da bawai ta san shi bane ko ta taɓa ganinsa da mijin nata, bayani ya masa game da cewar ita ce Meenal ɗin. Kansa ya ɗan shafo yana cewa "Okay to Ma sha ALLAH, zamu duba mu gani duk dai takaddun nata da kyau, amma duk da aka zan sake gwada ta ko na mako guda ne. Kuma daga gobe In sha ALLAHU zata fara zuwa, yanzun kuma za'a mata interview ne..." Yay maganar yana jan landline ta parlourn ya saka ƙiran wata babbar likita, babu jimawa wata gaggaɓar mata ta iso, nuni ya mata da Meenal yana ce da ita, "Dr pooja jeki da Meenal zaki mata interview a fannin surgery...." Cikin harshen turanci ya mata bayanin kasancewarta Christian ce, fuskanta da yanayin da murmushi me kyau ta kama hannunta cewa "les't go My freind!" Murmushi ta nata tana mara mata baya suka fita, shi kuma suna yin hannu yace zai je wurin aikinsa don har kamar ma yayi late. Har parking car's ɗin DR BILAL ya raka AHMAD.... Lokacin da Dr pooja ke can tana ma Meenal interview tuni shi har ya jima ma da barin cikin hospital ɗin baki ɗaya, kuma Alhamdulillah sosai tayi ƙoƙari dan tiyatan Ɓera ne tayi, kuma cikin ikon ALLAH bayan allurar baccin da akama ɓeran ta masa tiyatan cikin taka tsantsan da kuma tsoro, amma cikin iko na Ubangiji tana kammalawa sega ɓeran nan na motsi harma yana ƙoƙarin tashi ya gudu, wata nannauyar ijiyar zuciya daga ita har Dr pooja ɗin suka saki ita tana godiya wa ALLAH,ita kuma tana cewa. "THANKS JESUS...." daga nan suka ci gaba da ƴan ababuwa har ƙarfe sha biyu da kusan rabi, kafin ta ɗebeta suna komawa office ɗin Dr BILAL, sedai tin kamin Meenal ɗin ga kawo kanta taga Dr pooja ɗin tayi hanzarin yowa baya tana dafe goshinta da zuciyarta, na irin alamar nasha da kyar ɗin nan kafin kuma taga lokacin data furta thanks jesus, ta motsawar mukwallonta, tana kama hannunta suna saurin barin wurin, suna yin ta bayan window me girma, tsaiwa tayi bayan ta saki hannun Meenal ɗin dake ganin Ikon ALLAH, "Thanks god Sir MAJEED!! be ganmu ba...." Ta furta tana sake sakin wata ijiyar zuciyan. office nata ta wuce da Meenal ɗin, suna isa ta saka ƙiran Dr BILAL. Nan take bashi labarin ai taje zata shiga office nashi ta tarar da Sir MAJEED a ciki yau dai jesus ya tseratar da ita, dariya bame yawa ba Dr Bilal ɗin dake tare da Sir MAJEED ɗin har kusan daf ya saki, can ƙasa ƙasa yana satar kallon inda MAJEED ɗin ke zaune daya wani sha mur sosai yana cike wasu takaddun da shi ne abinda ya kawo shi cikin asibitin da seya kusa shafe rabin shekara be leƙo taba,dan hakan nema yasa ba kowa ne ya masa cikakken sani a matsayin me hospital ɗin ba, mafi yawancinsu ma sukan danganta asibitin data Dr Bilal ɗin ne, idan kuwa kaga mutum ya masa farin sani a cikin asibitin to kuwa tabbas babbane me girman matsayi kamar dai Dr pooja ɗin da ta ganshin a yanzun, wanda mamakin ganin san da tayi har yaso bata mamaki, wanda ita a karan kanta sau da dama takan sha mamakin yadda aka yi Majeed ɗin ke mata kwarjini bayan kuma schoolmate nata ne, tare suka yi karatu a ƙasar Oxford amma yanzun ya wani girme mata ya zama magidancin dole, duk da dai dama magidancin ne kuwa, harda ƴar sa ƴar kimanin 7 year's. Fesar da iska daga bakinsa Dr Bilal yayi yana datse ƙirar bayan kallon da yaga Majeed ɗin na jifarsa dashi, komai kuma be ce masa ba, wanda dama yasan hakan cewa zata faru tin da hakan shi ne kusan ɗabi'arsa. Miƙewa yayi yana nufar hanyar barin office ɗin, seda yaga yakai har bakin ƙofar kana ya masa gwalo yana cewa. "Maye dai yaci kansa banza miskilin tsiya da baƙar zuciya, yanda mutum yaƙe baƙi haka ma zuciyar tirr da MAJEED DAWOUD ISHAQ...." Yana kai nan ya fice a guje daga office ɗin baki ɗaya,ɗan yasan tsaf shi idan ya tashi yaɓo tashi baƙar maganar ze kusan kashesa da ransa. Kai tsaye office na Dr pooja ya wuce saɓunta gaisuwa tsakanin su suka yi, yana amsar document ɗin da pooja ɗin ke bashi, dubawa yayi yana cewa ta kwana ma gidan sauƙi bara kawai ya bema Majeed ya shigar da file ɗin cikin jadawalin list na ma'aikatan asibitin, seda Dr pooja ta ɗan waro ido har tana gaza yin shiru tace. "You don't see any problem with that, do you Dr?" Murmushi yayi yana fita kawai dan ya fahimci tsaf pooja ɗin zata bashi ciwon kan da Majeed ɗin ke yawan cewa tana bashi. A lokacin da yaje masa da zancen duba file ɗin daya masa wani kallo yana ma turar da laptop ɗin dake gabansa gefe daban, kafin ya wani kalle sa yace. "Kai me yasa ba zaka shigar ba,halan ka haɗu da cutar kuturtace bana da masaniyar hakan, to bara kaji indai se na shigar da wannan cikin jadawalin list ɗin ne, to kuwa ko waye sedai ya mutu be sama aiki anan ba...." Daga haka yasa kansa yana ficewarsa, ko ina be kalla ba ya shige motarsa yana ma yin reverse yabar cikin asibitin. Ƙarfe biyu daidai Ahmad ya dawo asibitin suka wuce bayan ya sake jaddada godiyansa ga abokin nasa Dr Bilal, har gaban motarsu ya sake rakasu daga ita har shi suna sake jaddada godiyar su, tana cewa ya sake miƙa mata godiyarta ga Dr pooja. Daga nan kai tsaye gidan Hajiyarsa yakai Meenal ɗin, duk kuwa da yanda gabanta ke faɗuwa da haɗuwar nata da hajiyar san, don tasan bame kyau bace, amma bata nuna masa komai ba har suka isa gidan, hong yayi get man ya buɗe musu get ɗin yana cilla hancin motar nashi cikin haraban gidan nasu, Motar Abbansa daya gani a gidan ne ya bashi tabbacin yau babu inda ya fita kenan, duk da dai dama be ganshi a Company ba, wanda da ya zata ko wani wurin yaje, ashe duk ko ina ne ma beje din ba. Ajiyar zuciya me kyau na ziran da tayi itama tayi ganin motar Abban, don tasan ko babu komai ta kuɓuta daga bakaken maganganun hajiyar Ahmad ɗin.... Da sallama ɗauke a bakunansu daga ita har shi suka shiga parlourn gidan, wanda mutane uku ke zaune a babban ƙaryataccen parlourn, magidancin jarida ce ɗauke a hannunsa yana dubawa, yayin da magidanciyar matar ke zaune tana fuskantar plasma da ake haskaka labaran Duniya, se wata matashiyar da ita kuma ke kwance saman 3siter tana lallatsa wayarta, wanda sallamar su Ahmad ɗin ya saka gaba ɗaya attention nasu dawowa kansu ciki kuwa harda hajiyar da tana kallon sa tare da Meenal take ta ɗauke kanta bata sake kallar inda suken ba. Zaune matashiyar ta miƙe tana gyara hulan dake kanta dake ƙoƙarin zamewa, fuskanta da fara'an ganin Meenal ɗin ta miƙe tana nufosu tana cewa _Oyoyo Meenally'n babban Yaya...._ ta isa gare su tana rumgume Meenal ɗin da ita ma ta rumgume Fatiman, A kunyace ta ƙaraso tsakiyan parlourn tana ɗurƙusawa gaban Abba da yake tace da ita ta koma saman sofa, gáidashi ta shiga yi a girmame tare da Hajiyar da take wani amsata a ciccure, wanda hakan ma tasan albarkacin Abba ne taci, se lokacin kuma Ahmad ɗin ke ƙarasowa cikin parlourn shima yana zama daga ƙafafun Abban nasa ya gaida shi, kafin ya juyo a natse ga mahaifiyar nasa, "Hajiyata barka da rana, fatar kin wuni lafiya...." A daƙile ta amsa may da "Lafiya Alhamdulillah" kawai tana ɗauke kanta daga garesa. Fatima ce ta Abba yace ta wuce dani ɗakinta,hakan kuwa yamin daɗi ba kaɗan ba muka wuce abin mu, babu jimawa sega Ya Ahmad ya shigo mana da abincin da na tabbata ni ya kawowa ma. Da ido na masa alamun ya ka min haka?, shima da idon yamin alamu da sabo da hakan hakkinane... Murmushi kawai nayi kuma kamar abin haɗin baki muka saki dariya a tare, be zauna ba ya fita sakamakon shigowar ƙira cikin wayarsa ya fita, dake tayi salla a can asibitin se kawai ta zauna sukaci abincin, koda suka kammala kwanciyar ta tayi a gadon Fatiman take nannauyar bacci yayi awon gaba da ita, wanda ta jima yi, don se bayar la'asar sosai ta tashi sallarn ta fara yi kuma zuwa lokacin Fatima bata nan, wanda take da tabbacin Islamiyya ne ta tafi, fita tayi zuwa parlourn Hajiyar, har lokacin Abba na zaune a parlourn amma babu Ahmad, Hajiyar kuma bata parlourn sema motsinta data fara juyowa a kitchen don haka kai tsaye ta nufa kitchen ɗin, A ɗan tsorace ta mata sannu tana ce da ita ta kawo ta mata aikin, wani banzan kallo ta wurgo mata tana jan tsaki tare da nuna mata hanya alamar ta bar mata wurin, "Don ALLAH kiyi hakuri Mami ban san abinda na miki ba wllh..." A wani irin fusace kuwa ta juye tace. "Baki san abinda kika min ba?, tun da ke muna fuka ce gadon munafurci taya ya zaki san abinda kika min kuwa, tin da kin gama mallake min ɗa babu kowa a gabansa in ba ke ba, gashi yau watanni Bakwai kenan da aurenku, ban ga alamar komai tattare dake ba, halamar sedai aci aje masai kenan ke ba matar ƙaruwa bace out....." Ta wani ƙarashe maganar nata da tsawa tana korar ta a kitchen ɗin, wani abu me kama da ruwan hawaye ne taji sun ciko idonta, don haka babu musu ta fice, sa'an ta ɗaya Abba baya parlourn don haka ta shige ɗakin Fatima ta zauna a gefen gadon ta tana dafe kanta da hannayenta. Jin Shigowar Hajiyar har ɗakin Fatiman ne ya saka gabanta yayi wani irin faɗuwa, yawun bakinta na ƙafewa ƙaf, take taji kanta ya sara mata, don haka a cikin zuciyarta ta shiga nanata kalmar INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN... Tamkar sauƙar aradu haka taji muryan Hajiyar tana cewa. "Wllh³ bazan taɓa son ki ko na amsheki a matsayin surukuwata ba Meenal, sabo da na tsanake!, bana sonki!, bana ƙaunarki, gaba ɗaya so kawai kike ki haukatar min da yaro baya da aiki se naki,yanzun fa duba har aiki ya samo miki a asibitin *4&4 SPECIALIST HOSPITAL* wanda ni nan babu kalan roƙon da ban masa ba akan ya samowa Fatima amma yaƙi, se gashi ke dake ke kece ya samo miki tashin farko, ko shawartana beyi da maganar ba, sabo da ga makiyiyarsa se yanzun naji ya a faɗama ubansa ni ban kai ba, ban kuma isa ba...., To ki sani wllh se nayi duk me iyuwa na rabaki da Ahmad kamar yadda kike nemar rabani dashi kema....." Fuuuuu daga haka tasa kai tana ficewa har wani hucin bala'i da masifa take. Kuka tayi me rai da lafiya a wurin tana roƙon ALLAH ya ganar da Hajiyar Ahmad ta gane gaskiya, tana nan zaune har bayan sallar magrib amma hawayen be dena zubo mata ba, jin motsin kamar za'a shigo ne ya sakata saurin faɗawa toilet ɗin Fatima ta wanko fuskanta tana gyara yanayin ta sosai, don tasan Ahmad ne , tin da taji shigowar Fatima da kuma lokacin da Hajiya ta dakatar da ita daga shiga ɗakin ta aiketa makota. Idanunsa ya zuba mata da kallon farko ya gane cewar kuka tayi, zama tayi a sofar dake daf da gadon Fatiman kwara ɗaya, inda ya ƙaraso har wurin a natse daf da ita yana zama tare da janyo ta jikinsa. "AMEENERH?" Haka taji ya ambata sunanta da full name nata kafin ya sake jefa mata tambayar "lafiyanki kuwa? Ko wani abu akayi miki?" Tsaye ta miƙe sannan calmly ta goge hawayen idonta da bayan hannunta daya sake zubo mata, kanta ta jinginar a jikinsa tace. "Babu abinda aka yi ya Ahmad bacci nayi, kuma kasan idan nayi bacci tsakanin sallar la'asar da magrib da ciwon kai yawanci nake tashi..." Ta faɗa da sanyin murya and I can swear I saw him relaxed. Kanta ya ɗago bawai don ya gama yarda ba wani abu Hajiyarsa ta mata ba, fuskar sa cike da concern ya furta. "Kin tabbata?" Yana saka idonsa cikin nata don sake tabbatar da hakan. Vail nata dake gefe a tashe ya ɗauko mata yana ɗora mata samar kanta yaje suje. Babu musu kuwa ta bi bayansa don dama hakan take ta jira tin ɗazun, koda suka fito babu kowa a parlourn don dama Abba be dawo ba, yasan kuma dama ba sosai ya fiye dawowa idan yayi sallar magrib ba se anyi isha'a yake dawowa gaba ɗaya. Hannunta ya kama ya nufa sashen Hajiyarsa da ita, wanda gabanta keta sake faɗuwa amma babu yacce ta iya ko tace ba zata ba, haka ta bishi tana zaune samar darduma suka isa, sallama yayi bata amsa ba taci gaba da laziminta, tsugunne yakai gabanta yana ce da ita zasu wuce. Da hannu ta masa alamar suje duk da beji daɗi ba amma haka yaja hannun Meenoh ɗin nashi suna wucewar su. Gidan gaba ya buɗe mata ɓangaren me zaman banza ta shiga ya rufe ya zaga ya shiga driver sit yana tada motar suka bar gidan. A wurin gashin wasu zabbi ya tsaya fita yayi babu jimawa se gashi ya dawo hannunsa ɗauke da ledoji biyu, ɗaya ta gashin zabbin ce, ɗayar kuma fruits ya sai musu kasancewar yaga kamar na gidan sun kusa ƙarewa. Sannu ta masa tana amsar ledojin ta miƙa ta baya, daga nan yaja suka wuce gida, be shigo gidan ba ya fita don baya son ya shigo beyi sallar isha'a ba, shima kusan irin Abban nasa ne, yafi gane idan yayi isha'a ɗin ya shigo gidan shima, ita ce ta shiga da ledojin ta ware fruits ɗin a fridge ta rage wasu zabbin ma ciki don tasan da safe ba sai ta musu girki ba, ta ware musu kuma wanda zasu ci idan ya shigo. Karfe tara saura ya dawo, wanka ta taya shi ya fara yi kafin su fito cikin shigar kayan shan iska, don itama tayi bayan tayi sallah'n isha'a. Se baza ƙamshinsu suke, a natse suka kammala cin nama da youghout ɗinsu kafin su zauna suna kallar Film na HAQ a tare a laptop nashi, don duk Film sabo daga fito yake sauke musu su kalla. Har wajajen sha biyu saura kana suka kammala suna ta mayar da yacce film ɗin yayi kyau, ya kuma tsaru, don ba ita mace ba ko shi kansa da yake namiji Film ɗin ya taɓa masa zuciya, gashi kuma akan addinin Musulunci aka yi Film ɗin, har yacce wasu mazan ke wulaƙanta matayensu na gida idan sun ƙara aure, da yacce Ƴaƴan wacce ake zalumta suke ƙin iyayensu maza, saboda kuntatama mahaifiyarsu da ake, haka dai sukayi ta maida yadda suka tsara Film ɗin. Ɗan kwantar da kansa a kan kafaɗarsa yayi, wanda ya saka Meenal ɗan juyowa ta kallesa, shima kallon nata yayi yana wani kashe mata idon daya sakata lumshe nata, matso da fuskansa daf da nata yayi zata ɗan koma baya kaɗan yakai hannunsa ya kama waist nata daya saka ta jin yirrrr, tsigan jikinta na tashi bakinta yama kissing yana cewa. "In sha ALLAHU bazan taɓa kasancewa miji irin Abbas ba, don zalumcinsa yayi yawa, ya kuma cuci Yami Ghautam da yawa tare da yaranta. Idonta ta sake lumshewa tana jin tabbaci akan duk maganganunsa akan ta, ta kuma yarda dashi samm bata da haufi akan mijin nata, daga nan ya tashi da ita suna wucewa bedroom nasu, don har ta fara bacci a jikinsa, kwantar da ita yayi shima yana kwanciyar gefen ta tare da janwota yana shigar da ita cikin jikinsa, ta buɗe baki da niyar masa magana ya haɗe bakin, dole ta tsaya da kyau tana bashi kulawan daya kamata, sune har wajajen karfe ɗaya da rabi basu yi bacci ba, seda suka tsaftace jikinsu kana suka kwanta tana lafe a jikinsa tana sakin ijiyan zuciya me ɗan zurfi. Daga nan wani daddaɗan bacci me cike da SO da ƘAUNAR da suke ma junansu ya kwashe su, washegari har kusan a makare suka tashi, don se a gida ya jasu sallar subhi. Daga nan basu komawa tayi ƴan gyare gyarenta ta sake gasa musu namansu na jiya suka karya dashi, sedai yau ɗin ma dai kalan jiya da doguwan riga ta bubu ta fito, se sani ƙaramin vail, har ze mata magana kawai ya kyaleta suka fita. Ajje ta yayi yau be shiga cikin asibitin ba ta wuce ita kaɗai..... _Byu byu hayya hayya ya take ne?, fatar dai wannan ɗan littafi nawa ze amsu a wurin ku, kamar yacce kuka saba amsar duka littattafaina..._ _Idan naga reactions naku akan littafin zan fara sakinsa nan bada jimawa ba IN SHA ALLAHU....._ _ALLAH yasa wannan salon labarin da muka sanja ya muku, don labari ne akan irin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin gidajen rayuwar aurenmu zahiri da kuma baɗininsu, da yacce wasu mutanen su da kansu ke siyar ƙaddararsu da kansu da kuma hannayensu...._ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. _My NAINERH TARH, My Ƙaunar ƙaunata My aminiyar kwarai mutuniyar kirki Uwar yaro na Mubeen kuma this Book for you, gashi ya iso gareki da zafi zafinsa fa💃🤸_ Page 3&4 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Tana isa cikin asibitin kai tsaye office na Dr pooja ta wuce, wasu ayyuka ta ɗan bata ita kuma tana yin ɗakin wata me haihuwa da aka kawo, tun cikin dare ta kasa haihuwar da kanta shine ma abinda yasa take tunanin ko C/S ma kawai za'a mata, don tana matakin ƙarshe ne don tana 1/cm haihuwa a koda yaushe, amma gashi abu ɗaya ake fama tin wajajen karfe 7 gashi kuma yanzun har goma na nemar wucewa ma, labcoat nata ta zira da handglov a hannunsa ta sake nufar delivery room ɗin da matar ke ciki, tin kafin ta kai ga ƙarasa shiga room ɗin take jin ihu da salatin matar na tashi, goshinta ta dafe tana ƙarasa shiga da ɗan hanzarin ta, handglov ɗin dake hannunta ta sake gyara zamansa tana kai hannunta ƙasan matar dake kwance saman gadon masu haihuwar nan, ganan dai kan jaririn ya ɗoso sedai daga uwar har yaron ko yarinyar dake cikin cikin kowa fafatuwar tsira da rayuwarsa yake, ita tana son taga tayi duk me iyuwa ta yunƙura koda ta numfashi ne abinda ke cikin cikin nata ya sama damar fitowa, shi kuma dake cikin shima yunƙurin yaga ya fito ɗin yake, wata nurses ta ƙora Damaga kan ta haɗo mata allurar naƙuda kawai tama matar, kanta matar ke jijjigawa gafa ɗaya gumi ya gama jiƙeta sharkaf, da kyar ta iya samun bakin furta. "Karku daura min ruwan naƙuda ina da sugar da hawan jiniiiiii...... San...sa...sa....san...nan...ina da raunin zuciya....." Duk wannan abin da take yi cikin fusgar numfashi take da haki.. gaba ɗaya ta gama saddakarma rayuwar ta gama sallama cewar shikenan ita nata ajalin yazo, don haka ta shiga adda'a 'o'i masu kyau da girma idanunta na ƙoƙarin lumshewa, su kuma gaba ɗaya ma ɗakin sun rasa abinda ya kamata su mata, don haka kawai Dr pooja ta fita babu jimawa se gata hankali a matukar tashe da file na saka hannun mijin matar dake can haraban asibitin yana ta safa da marwa yawa me dawafi. Abinda ze baka ma dariya ƙafansa ɗaya da takalmi ɗayan kuma babu faɗi yake. "Don ALLAH NA'EEMERHTOU karki tafi ki barmu!, ki taimaki rayuwar yaran mu dake dani Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" haka yake ta famar ambata gaba ɗaya shima ya gama jiƙewa se kace shi ne me haihuwar, gefe can kuma dashi wasu mata ne biyu kowannensu ya buga uban tagumi kowa da abinda ke damunsa. A can ɓangaren Meenal shigar Dr pooja office ɗin ta hankali tashe da kuma fitar ta ne itama ya tashi hankalin ta, don haka ta mara mata baya, bayan ta ɗora labcoat da handglov a hannunta koda ALLAH yasa zata iya musu da wani temako ne haka, gaba ɗaya zuwa lokacin kuwa har Dr pooja ta kammala duk wani shiri nata na fara surgical ɗin, harma an nufi surgery room da matar. Lokacin da take kaiwa ainihin room na Surgery room ɗin har pooja ta ɗora Scissors nata saman cikin matar da numfashin da take shaƙa ma na Oxygen ne, don tuni rauninta yayi ƙasa sosai dole se da taimakon oxygen zataci gaba da numfashin. "Wait a minute, ma'ame..." Haka Dr pooja ta tsinkayi muryan Meenal, dakatarwar kuwa tayi tana isowa ita kuma. Cewa tayi pooja ɗin ta taimaka mata da sabuwar rezor, seda ta sake risinar da kanta tana juye baki cikin yaren Ingilishi tace da ita tayi haƙuri ta shiga cikin hurumin da ba nata ba, ba komai tace da ita, don haka kai tsaye ta saka sabuwan rezor ɗin tana ɗan yankar ƙasan matar, da komai bata ji ba sakamakon allurar kashe jikin da aka mata, oxygen ɗin dake hancin matar Meenal ta zare kaɗan tare da ɗan ɗago kan matar kamar zata zaunar da ita ta kuwa takarkare ta saki wani zazzafan numfashin dake kumshe cikin bakinta ya fashe, wanda dama ita Meenal ɗin hakan take son samu daga matar, daga ƙirji zuwa cikinta ta ɗan danna tare da sake mata irin ta ɗazun bayan ta mayar da ita ta sake ɗago ta, aikuwa a wannan karon ma ta sake yin irin na ɗazun, haka har suka yi karo uku, ana huɗun kuwa tayi wani kyakkyawan nishin da kai tsaye ya taho da yaron dake cikin, hannunta ta saka duka biyun tana ƙarasa janyo yaron ya fito kuwa da assalatunsa, wato kuka irin na jarirai sabuwan haihuwa, suluf haka matar taji jikinta ya koma kamar wacce aka sauƙe mata cutar shekara da shekaru, tana meda wasu numfarfashi, kafin ta tafi zuwa duniyar sumewa... Dama tasan za'a yi hakan duk da cewan bata taɓa amsar haihuwa ba amma kuma Alhamdulillah tana da kyawawan da bata mantuwa, don wannan ɗin duk cikin interview ɗin da aka musu ne na irin dabarun haihuwar da tayi gaddama, kuma Alhamdulillah tayi nasara wanda dama se irin kamar ana daf da yima mutum operation ɗin ake son yin hakan, wanda ita da classmate nata sun sha gwada hakan akan kansu da numfashin da suke gumtsa su fesar idan an zame oxygen ɗin, kamar yadda tayi tama matar. Dr pooja ce ta rumgume ta tana furta "Ohhh jesus Today I saw a young lady who was thoughtful and knew her job well.Thank you Jesus.... Thanks u Maanol....." Dake haka tin jiyan take ƙiran ta dashi wato Maanol ɗin. Ko kafin kace mene se gashi tuni har an gama shelanta wa duka sauran Dactor's ɗin dake cikin hospital ɗin cewa ga wata ƴar baiwar likita sun samu me matsakaicin year's. Cikin ƙanƙanin lokaci se gashi sunan Dr Meenerl Shehu Usman na nema yin shura tun a matakin farko, da kansa Dr Bilal ya ziyarci wurin ya kuma zauna da sauran Dactor's tare da Meenal kan fikirar da tazo musu da ita, nan kuwa ta tashi ta ringa musu bayanai daki daki, wanda daga ƙarshe suka gane cewar lallai ashe ba se iyaka private school's bane suke jajircewa wajen koyar da ɗalibansu ba, nan mijin matar ma ya bada wasu kuɗi masu ɗan gwaɓi yace na likitar data ceci rayuwar matarsa ne da kuma abinda ke cikin ta,duk da kuwa kasancewar tana a Cold room ne. Wato ɗakin sanyi amma kuma ai tana ci gaba da shaƙar numfashin daba na oxygen ɗin bane, ga kariyar da aka haifa ɗin tazo cikin ƙoshin lafiya abinta, dake dama tun a lokacin ta gama wa matar ɗinki,don haka yaci gaba da kulawa da marasa lafiya a fannin haihuwa, kowa se kaji yana don ALLAH a ƙirawo masa Dr Meenerl shima tazo ta taimake shi, wanda ita abin ma yake ɗan bata dariya, wato ma ita ne zata temakesu ba ALLAH, ko dan ance me ciwon haihuwa tamkar zautacce haka yake komawa, duk abinda yazo bakinsa faɗa yake. Ba itane ta koma gida ba yau se wajejen ƙarfe 7:30pm, tin kuma 7:15am data fito. Dake dama tayi waya da Ya Ahmad ɗinta cewar yau kar ya biyo da wuri se after magrib ze biyo ya ɗauketa, SO shi kuma lokacin Hajiyarsa ce tayi ƙiransa dole haka ya tafi yace ta biyo napep amma karta yarda ta hau machine... Koda ta dawo ta tarar ya dafa musu farar shinkafa da yaji, ta wani cunkule ƙaramin bakinta kuwa don ita ba Sosai take son farar zallar shinkafa da may da yaji haka ba, har ƙara ya musu couscous ko noodles da egg, haka bayan tayi wanka tana ƙananun ƙunƙunai tana komai ta tuttura abincin... Wayarta ta ɗauka bayan sallarn isha'a ganin be shigo ba ta shiga WhatsaAp nata da duk wunin yau bata hau ba, da test messages na Shareefah ƙanwarta kuma babbar aminiyarta ta fara cin karo, don haka ta shiga, voice note ne don haka ta kunna tare da kaiwa kunnenta ta saurara. Wata ijiyan zuciya ta sauƙe lokacin data kammala sauraran voice note ɗin, kafin itama ta fara mata nata voice ɗin. _Look Shareefah ina son ki kwantar min da hankalinki kinji, ki kuma ci gaba da haƙuri bana son kika sanya wata damuwa daban a cikin ranki, kinsan koda ace da ran Ummanmu ba zata so ganinki cikin damuwar hakan ba, kuma Baffa yana daidai gwargwadonsa a kanmu tsakanin mu da gwaggo Sadiya, kuma ke ba karatun ki ma kike ba, don ta hana ki abinci kuma se yaya ina ce kusan duk bayan 2 weeks nake saka miki kuɗi a account naki?_ daga nan ta tsaida voice ɗin, babu jimawa kamar da 5 minutes sega wani voice ɗin na Shareefah'n ya sake faɗo mata. _Aunty Ameenatou ba wai rashin hakuri ko rashin kaiwa zuciya nesa bane, kin san ni ina son naga anyi komai cikin tsakani da ALLAH, bana son cuta ko zanba da zagon kasa irin na gwaggo Sadiya, matar nan makirace wllh, bayan rashin bani abincin da bata yi ina jinta ranar tana cema Baffanmu wai na dena cin abincin gidan, haka ta ɗebo kwanukan abinci kusan na kwanaki biyar ta dire a gabansa wai bana cin abincin ya tuhumeni wai a ina nake samar kuɗi?, kin ji fa, karki ga yadda baffan kuma ya wani rutsani wai in faɗa masa inda nake samar kuɗin, alhalin gidansu Yaya Jafaru nake shiga inci wajen mamarsu......_ wata doguwar ajiyar zuciyan dai again ta sake sauƙewa a cikin zuciyarta tana ayyana wai se yaushe gwaggo Sadiyan zata san cewa Annabi ya faku ne?, se kuma zuwa yaushe zata gane gaskiyar dake bayan ƙarya?. Wani voice ɗin ta mata tana ce da ita taci gaba da haƙuri zata ma Yaya Sadeeq babban ƴaƴansu kenen maganar, kuma itama yanzun ganan wasu ƴan kuɗaɗe zata turo mata daga wanda mijin matar nan ya bayar a bata, shi ne ta raba uku ta ɗauki kaso ɗaya biyun ta ce su Dr pooja ɗin su kasa suma, gashi alert nata na wata har ya shigo mata wajen dubu ɗari huɗu da arba'in da biyar. Dake su haka al'adansu yake a ranar da kaje aiki a washe garin ranar alert naka ke faɗo maka. 100k ta turo mata take aiko sega saƙon godiya nan daga ƙanwar nata harda kukanta, da cewar lallai ita ce uwa mahaifiyar da suka rasa itace kuma bangonsu se kuwa Yaya Sadeeq da shima ba'a barinsa a baya, duk da kasancewar ba wata gwaggwaɓar sana'a ke gare shi ba, amma kuma kusan kullum cikin rufin asirin ALLAH suke,don kusan shi ne ke ɗauke da gidan mahaifin nasu, kai tsaye suna kammala maganarsu da Shareefah ɗin ta laluba No na Yaya Sadeeq ɗin buga ɗaya ana biyu kuwa ya katse shi ya ƙirata, ɗan murmushi kawai tayi,don tasan dama ba wai ɗagawar ze yiba, amma kuma ze biyu tunda kamar hakan na masa nuni ne da tana son yin magana dashi kai tsaye, tana cikin wannan tunanin ƙirar nasa ya shigo mata, answering call in tayi tana kai woyar kunnenta. Gaidasa tayi yana tambayar lafiyanta, komai normal tace masa kana tace ta saka masa ɗari biyar a opay nasa ya sake data jarinsa, tif yaji wata wuta ta ɗauke masa duk da dai ba wannan ba ne karo na farko da take tura masa kuɗin ba, duk da kuwa kasancewar baso yake ba yace ta bari alhakin kulawa dasu na a hannunsa ne, wata numfashi me ɗan zafi ya furzar yana ce da ita a ina ta samu kuɗi har haka?, da har tashin farko ta saka masa dubu ɗari biyar?. Wata ƴar ƙaramar dariya tayi tana cewa. "Laaa Ya Sadeeq kana manta cewa yanzun na fara aiki ne halan?" "Kuma daga fara aikin naki shi ne har kina sama uban wannan kuɗin haka?" Fuska ta ɓata tana cewa. "Amma ai na faɗa maka cewar babbar asibiti ce, kuma tashin farko su suke fara biyar ma'aikatansu sabbi,kuma ƙarshen watar ma Dr pooja tace zasu sake sakamin 200k...." Wata yar gubtuwar murmushi yayi yana cewa. " Su kuwa wannan waɗan da irin masu kuɗi ne haka, da tashin farko su hankaɗo miki uban kuɗaɗe haka?, kana kuma ƙarshen wata ma su sake biyar ki har 200k?...., kuma halan ALLAH dai ma yasa kin shawarci Mijin naki, don a wannan fannin na sanki farin sani ba shawara kikayi da kowa ba, duk abinda ya miki kawai kike aiwatarwa..." Tsaye ta miƙe daga zaunen da take tana wani tura micil ɗin bakinta gaba tare da cewa. "To shi in na bashi ma me zeyi da kuɗi?, nasan ko da ace na bashin ma ba amsa ze yiba ai...." Sosai daga ta can ɓangaren Ya Sadeeq ɗin ya haɗe ransa yana cewa ze dawo mata da kuɗin nan lallai ta tabbatar ta fara shawartan mijinta kafin kowa, tin kafin ta ce komai ya datse ƙirar sega alert nan na kuɗinta na dawo mata har da ƙarin dubu ɗarin da take da tabbacin Shareefah ta faɗa masa shi ne ya haɗa ya dawo mata dashi, duk da tasan cewar bawai ze amsa na wurin Shareefah ɗin bane yayi ta aljihun sane, wanda tasan yanzun haka ya gama budget na abinda zeyi da kuɗin sa... Ɗakinta ta nufa tana wani huhhura hanci sama,ita ala dole yayan nata ya ɓata ranta, kwanciya tayi saman lafiyayyen bed nata idanunta lumshe, tana son yaƙar zuciyarta akan ta ringa bijirema duk abinda take raya mata, ta sani sarai cewar ita bame sauki bace, ba kuma me ƙyaliya bace ga duk wanda ya shiga gonar ta, sedai in mutum yaga bata tankashi to lallai ya kai ya kawo girmansa take gani,mutumcinsa take gani ko na wani nasa, kamar dai Hajiyar Ahmad da ita ma nashi mutumci da albarkacin take ci da har take yaɓa mata duk maganar data gadama kuma ta kyaleta. Duk zuciyarta take jin a cunkushe badon an mata komai ba sai don kawai dawo mata da kuɗin da Ya Sadeeq yayi. Tana nan a haka har bata san Ahmad ɗin ya shigo har nan bedroom ɗin ba, sedai taji hannunsa a shoulder nata kana ta ankare, zaune ta tashi tana ɗora kanta akan kafaɗarsa bakin nan a tinzire kamar wata ƙaramar yarinya, "Meke faruwa da Rayuwar Ahmad Junaida Haris haka?, wanda me gangancin ne yayi ƙoƙarin taɓa farin cikinsa kuma?" Seda ta haɗiye abinta ke son ɓallo mata ruwa don se da Ya Sadeeq ɗin yace da ita, _Saura kuma in yazo kice masa ga abinda ya faru wacce bata iya kalmasa zance ko kalamanta ba...._. Makut ta sake haɗiye maganar tana tauneta da ƙarfin tsiya kana tace. "Ba kai bane kaki dawowa da wuri ba!, kuma ka dafa min shinkafa farar da kason ban fiye sonta hakan ba...." Jikinsa ya shigar da ita yana cewa. "Wannan shi ne dalilin?, shi ne kuma musabbabin fushin naki Bestie?" Se ya dakata tare da ɗan janye ta daga jikinsa yana kama kunnensa da kokarin sauƙa yayi kneel down, tayi saurin tarosa tana wani famar zazzare fararen idanuwanta. Kana ta kai hannunta samar bakinta tana me furta. "A ah Babyn Baby kayi haƙuri ka kuma rufamin asiri maza su kaini ba mata ba, in ma hukuncin ne ai ba irin wannan ya kamaci ace ka amsa ba, irin haka...." Tayi maganar tana ɗagosa ta kama gefen kuncinsa ta ɗan ciza kaɗan ba da yawa ba. Fuskanta ya ɗan tallafo ya mara marin wasa yana jijjiga fuskan suna sakin dariya kusan a tare. Bayansa ta juya tana ɗurƙusan dashi ta haye bayan wani shauƙin ta hau bayan mijin nata na kamata. "Ohhh Bea bayan yayan naki kikeson ɓallewa ya dena samar na moro ko?, ke baki san kin ƙara lukucewa bane halan...." Tam fa an taɓo ta, don ta tsani taji yace ta fara lukucewa tace masa yaka cewa ta fara zama ƴar duma duma kawai, amma ita ina take son wani girma. Dariya yayi yana cewa "Tuba nake wane ni inji kare da yaga kura maza hau bayan kine, da ma don inyi ta goyaki ALLAH ya min shi ne auki haka...." Gefen kunnensa ta kama ta ɗan ciza tana cewa, "ALLAH Ya Ahmad ɗin nan ka fiye tsokana, za kayi ta zaga gidan nan dani har nayi bacci a bayanka wannan shine hukun cin naka. Dan waro idonsa yayi da riƙe haɓa yace, "Nie kuma in kikayi baccin waye ze kula dani har inyi nawa baccin cikin salamar?" Seda ta cakulkuli wuyarsa kana tace. "ALLAH mana..." Ɗan sakin ta yayi kamar ze kayar ya ce "Naki wayon ban isa ba wllh, kin gama saƙƙo nayi missing ɗumin jikinki duk wunin yau... Se kuma ya wani haɗe rai kamar ba shi ba yana sake furta. "Gaskiya wannan aikin na son shiga haƙki nafa Baby, iyaka jiya da yau har kulawanki ya fara raguwa daga gareni anya zamu seta kuwa da wannan aikin?...." Yayi maganar yana fara tafiya da ita a jikinsa zuwa nasa ɗakin tana cakulkulinsa tana cewa babu abinda ya isa ya shiga ƙarkashin kulawan da suke bama junansu, har suka kai bedroom ɗin nasa, kafin su kai kuwa gaba ɗaya ta gama susuta jikinsa da ababuwan data ringa masa, ga hannunta ɗaya na cikin rigarsa data ziro bayan ɓalle boturan gaban rigan da tayi, don haka suna isa bedroom ɗin suka zube yana fara kunnata itama, duk dai dama a kunnen take, indai zata jita a jikinsa to kuwa lallai babu zaman lafiya a gangar jiki da ruhinta, har se sun ziyarci juna. Amma se ta fara masa rakin ita ya kyaleta ta gaji da yawa ƙafafunta sun yi tsami, ko ta kanta be bi ba yaci gaba da abinda yake har se da yaji shi ontop kana ya sarara mata yana janyota jikinsa ya shigar yana sauƙe mata numfashinsa me ɗumi a gefen wuyarta, ita kuma ganan shatin kwanciyar hawayen da suna dinga gangaro mata. Sedai suka jima sosai kafin su tashi su tsaftato jikinsu kana suka dawo suka kwanta, bayan sun san gyaggara gadon. Can gabanin asuba ya sake nemarta inda taso zamewa ta gudu amma ya sake nuna mata bata isa ba, haka ya sake biyar buƙatansa da ko Sallah yau ɗin ma wuce su tayi, karfe shida saura kana ya ja su Sallah'n. Aikuwa tayi kwanciyar ta taƙi fita musu dinner murmushi kawai yayi yana fita yaje ya soya musu bread da kwai. Da ruwan bunu, koda ya dawo seda ya fara yo wanka kana ya tadata yace ta fito suyi dinner karta makara. Wankan tayi itama sama sama kana ta fito cikin wata ash jallabiya ta mata, wacce ta amshi surar jikinta kwarai, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ta zauna sukayi dinnerh ɗin, seda suka kammala tsaf kana ya fuskanceta yace. "Yanzun yauma fisabilillahi Meenal yau ɗin ma haka zaki fita?, anya kuwa kina son ci gaba da fita wannan aikin naki?" Tsaye ta miƙe tana dubar shigar nata kana tace. "Haba Ya Ahmad mana, kar ka neda kanka wani ɗan kauye mana, yanzun miye laifin shigana don ALLAH? Se dai in kaine ba ka son zaman lafiyan...." Daga haka ta suri jakarta tayi waje fuuuuu.... Da wani kalan daskararren kallon mamaki al'ajabi rudu ya bita. Kafin yayi ƙarfin halin miƙewa tsayen shima ya bi bayanta, sedai me wayam babu ita har ma ta fice kenan?... Duk yacce zuciyarsa taso ingizo hasalarsa fili kin yadda da hakan yayi, yana ajje ta a matakin mata uziri ne kawai. Don haka yama motarsa key ya tashe ta yana fita daga haraban gidan. Sedai kome kama da ita a hanyar be gani ba don haka yayi wucewarsa gun nasa aikin tin da yasan ita ba yarinya bace, ta kuma san inda ta nufa, haka ya tafi yana ta tunanin sabbin halayenta daga ranar fara aikin nata zuwa wayewar yau da yake na uku a fara fitan nata, a cikin zuciyarsa yake ayyana lallai da akwai matsala kenan indai har tace a haka zasu ci gaba da tafiya. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauƙe yana karanto Hasbinallu wani'imal wakeen... Meenerl kuwa yau se aikinta yafi na jiya yawa don har sun sau mata ragamar fara aikinta gadan gadan, harma sun gama tsara mata time table na lokutan aikin nata, a sati tana aikin tin daga safe har zuwa yamma sau uku, daga yamma zuwa safe sau biyu. Koda ta koma gida take bashi labarin be ce mata komai ba, har ya fara gudanar da aikin nata, a memakon shigar da take ya sanja sema sake ɓauɗewa da take, amma se ya tattarata duk gefe guda yaga iyaka nata gudun ruwan, itama kuma bata damu ba haka har suka cinye tsawon wata guda kenan a hakan, idan tayi bacci yakan ɗauka wayanta time to time bawai don yana zargin tana sedan kawai tsaro da kariya, baya shiga duk abinda ya danganta family issue nata, be kuma taɓa kamata da aikata ba daidai ba, sedai yakan tsinci video's nata tsilli tsilli duk ranar da take da kwanan asibiti tana yar rawa abinta, wanda take yi a tiktok seta yi sev nashi akan wayan,seta goge daga tiktok ɗin da dama a private account nata yake. Amma na yau ɗin se yafi na koda yaushe daga masa hankali don kuwa daga ita se wata sky ɗin rigan baccinta iyaka gwiwwa kanta babu kitso a tubke ƙasar ƙeyarta, ga hannun bra nata nan ɗaya ya fito koda saninta kodai akasin hakan, se ya shigawa WhatsaAp nata ze tura a wayanshi amma se wani abu ya ɗauki hankalin sa a cikin wayar nashi, wato kamar sabbin status da sunan _BESTIEN BESTY_ ke ɗauke dashi, don haka kai tsaye ya shiga status ɗin ya kalla, video'n daya gama kalla yanzun ne tayi status dashi, duk da kasancewar ta saka hoton love ta kare jikinta amma kuma ai be dace ba, inta kare ƙasan saman kuma fa?, nan ya shiga na biyun yaga ol de same da wancan ɗin, shi wannan da tana yi har kamar wulgawar wani namiji ya gani da kayan likitoci sanye a cikinsa. Guda uku ne don haka na ƙarshen tana tafiyane tanayi tana sanye da kayan ta na aiki ta a video ɗin, view na mutanen da suka kalla ya duba, yaga sama da mutum goma sha biyar har sun kalla, cikin kuwa harda classmate nata, fitowa daga wurin status ɗin yayi yana duba na farko farkon da suka fara mata message, nan ya kalla na Yayanta Sadeeq da shi kai tsaye cewa yayi Lallai lallai maza maza ta sauƙe status ɗin, bata bashi amsa ba duk da ganan taga message nashin, daga nan yaga group na school mate nasu saƙonni nata shigowa, don haka se hankalin sa yafi karkata wurin kawai ya shiga, shi dai wannan video ɗin da tayi status dashi ne wata daga cikin freind nata da suka kalla ta tura musu, a ƙasan video ɗin ta rubuta. _Gafa mutuniyar an fara ɗaukan haske...._ Mutum na farko kuma daya fara magana akan video ɗin na miji ne, me suna Hasheem Al'asan, shi ne yace. _Ohhh ALLAH Yarinyar nan wai dama zata waye haka?, kodan No wonder daga yanayin tsiwa da rashin kunyar tama, idan kuma aka haɗe da kalan mijin data samu lallai dole ne ta numfasa itama...._ Se na biyu shima dai namijin ne inda shi kuma yace. _Wooo Malam yarinya ta gama timbatsa ba, ta zama wata se kace renon madara da A/C....._ se ta ukun kuma macece ita kuma tace. _Shegiya nera wato dai shi kuɗi da jin daɗi babu abinda baya saka mutum aikatawa ci gaba dayi da kyau hakan ma India'n girl...._ namiji ne ya sake tag na hoton yace. _Je kaya alaji, gaskiya sa hijjab ma duniya, da yarinya kullum a cikin manyan kanya,amma da dukkan alamu mijin nan nata na shagwaɓata da yawa..._ _Yo ba dole ya shagwaɓata ba ya sama wanga ganima haka, dole ai yayi ta bata tana kwashewa ita kuma...._ Wani kalan rumtse idonsa yayi ganin duk cikin maganganun babu na kirki, babu kuma wanda aka samu ya ce tayi ba daidai ba, se dai masu yabon tama. Dubawa yayi yaga itama group admin ce a group ɗin, don haka kai tsaye ya goge video ɗin, tare da exit kanta daga cikin group ɗin gaba ɗaya, yana fitowa ga mamakinsa duk da kasancewar lokacin wajen karfe ɗayan dare ne se yaga wani guy har ya biyota private yace. _Haba India'n girl ya zaki mana haka uyhmmmm?, bafa mu riga munyi saving video ɗin nan a wayoyinmu ba kika goge?, kana kinyi left daga cikin group ɗin, halan Mijin kine yasa ki fita ko???, Hhhhhhh yayimin dai-dai ta wani fannin kuma be kyauta min tin da duk mun sakan kance bamu yi sev na video ɗin cikin wayoyin muba, ita kuma waccen Yar Is ɗin data ɗora na mata magana naga bata online, dama ita kowa yasan kasa ce uwar yan bacci, amma zuwa safe na mata magana ta turomin, in kuma zaki bani zan yi farin ciki da hakan, daga Jinior Ahlam kd_ take wani mummunar ɓacin rai ya sake kume zuciyarsa, kai tsaye ya rubuta masa. _Come to your senses and calm down, otherwise I may mislead you or end your life in prison, be careful..._ Daga haka yayi block nashi yabi yarinyar data ɗora video ɗin, yace mata. _ The biggest mistake you will ever make is to forward this video to someone else, because I will look at every possible connection between the two of you and I will have you arrested, an arrest like forever, so be careful, From Meenal's husband Shehu Usman_ Daga haka ya kashe wayan yana fita a ɗakin zuciyarsa na tururi da kuna akan wannan abin data masa, don haka cikin ransa yake raya dole ya nuna mata kuskurenta a wannan karon. Da safe ta farka ta ganta ita kaɗai babu ma alaman ya kwana a ɗakin, se kawai ta taɓe baki ai dai ko babu komai ta tsira daga takurawansa da ba sosai yake barin tayi wani baccin kirki ba. Don haka wanka tayi tayi sallan subhi ta shirya cikin shigar wasu riga da wando palazzo's cubeb. Se ta kawo wani himar irin robo robo ɗin nan ta ɗora kan palazzo's ɗin ta fito, bayan ta dudduba wayanta bata kalla ba, baya parlour ko kitchen don haka kai tsaye ta bishi zuwa dakinsa sedai nan ɗin ba baya nan, gaba ɗaya baya gidan don haka cikin hanzarin karta yi let wurin aikinta ta ɗiba cake da biscuit ta zira a handbang nata ta fita, yau ma ba aikin dare bane da ita don haka tana isa ta kama aiki. Amma time to time tunanin wayartan da bata gani ba kan fado mata, bayan sallar zuhr dai ta gasa samar nutsuwa ta amshi wayar pooja ta ƙira No nashi, amma yana ta ring be amsa ba, short message ta aika masa cewar ita ce yayi answering call nata, kamar da 2 minutes ta sake kira amma No answer. Dole ta haƙura ta kyaleshi tana ayyana baƙar zuciyar ta motsa kenan. Se wajajen 8 na dare take komawa gida lokacin harya jina da shiga gidan shi, yana zaune a parlour yana kallo ta shigo a gajiye sosai, a gabansa ta zube dama takarmi da guntun shimar nata a hannu ta shigo dasu. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana kuma ƙoƙarin zame kanta daga jikinsa data ɗora, kanta ta ɗago ta kalleshi tana furta... "Besty yau duk me ya faru ne?, banga woyana ba na ƙira ka data Dr pooja har test messages na ma amma No answer lafiya kuwa?..." Hummmm ya kawo wani gauren numfashi yana ƙarasa zamar da ita daga jikinsa yace. "Yanzun kin kyautama kanki kenan meenor?, duba kalan shigar da kika fita dashi, ina ma laifin kici gaba da saka bubu ɗin kina fita dasu kiyi rolling vail na kayan, bayan haka yanzun ke abin birgewa ne a gareki kiyi video da karamar riga har kiyi status dashi, wasu can su ɗauka su ɗora a group naku da kuke haɗe maza da mata uyhmmmm?. Duk sabbin halayen da kike ta bijiromin dasu inata ƙoƙarin shanye wa sabo da ina SONKI Meenal, amma duk na miye waɗan nan ababuwan?...." Kanta ta dafe tana furta "Ohhh shit dama nayi tunanin hakan wllh" se kuma ta taso gaba ɗayanta tana shigewa jikinsa tace "I'm so sorry Dear, Amma ai naga na kare jikin nawa, kuma ma ai nake kallar hakan ba laifi bane, ni wllh ma sabo da kai ne nayi video's ɗin, idan kana wasu ababuwan se kace wanda be gama wayewa kodai yake da ƙarantar wayewar kan.... Tin da ta fara maganar yake kallonta da kaifafan idanunsa ko fiftawa bayayi, wato ma ita hakan ba komai bane a wurinta, har yana faɗa mata abinda tayin ba daidai bane amma take ƙiran sa me ƙarancin wayewa?, Lallai ya riga yayi saken da Meenal ɗin ta gama rainasa. Amma duk da hakan se ya danni zuciyarsa yana ɗago fuskanta ya riƙe a cikin tafin hannuwansa ya furta. "Ki gyara!, ki sake halaye da ɗabi'unki Meenor!, ina SONKI ba zan iya ɗaukar waɗan nan sabbin halayen naki ba, Pls ki taimaki wannan zuciyar dame zuciyar...." Yayi maganar deep down na bugun zuciyarsa na sake ƙaruwa, daga yanda take lafe a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke beating very fast akai akai. Tashi tayi ta nufa ɓangarenta wanka ta fara kafin tayi sallan magrib da isha'a da batayi ba duk ta haɗe su a lokacin, wasu riga da wando masu taushi ya saka tana baje jikinta ta turare ta nufa ɓangarensa, zuwa lokacin har ya bar parlourn,yana kwance idonsa bisa p.o.p na ɗakin yana kalla kamar me nazartan wani abu daga cikin sa, be ji shigowarta ba sejinta kawai yayi a jikinsa ta wani faɗo masa, ƙanƙameta yayi da hannunsa yana cusa kansa cikin wuyarta ya wani shaƙi numfashin daya tafi may da mayen ƙamshin ta me bala'in rikitasa. Anan wurin ya zubar da duk wasu makaman yaƙinsa yayi yaƙin gaskiya da gaskiyar da babu saussauci ko sauƙi na ragwanta tattare da shi, amma kuma akwai sanya nutsuwa da nishaɗin hakan tattare da lamarin. Washe gari babu aiki weekend ne, don haka daga shi har ita suka mora wunin ranar da ƙaunar junansu, tuni harya mayar mata da wayarta bayan ya sake roƙon ta da karta sake don ALLAH. Washegari daya kasance Lahadi kuma ta tambayi gidansu,don kawai kewar Shareefah da tayi da kuma Yaya Sadeeq ɗin ta, sha biyu daidai ya sauƙeta a gidan yace after isha'a ze dawo ɗaukanta. Wata leda ya bata yace ta shiga musu da ita, godiya ta masa yana shirin komawa motarsa sega Yaya Sadeeq ɗin ma ya fito tare da Baffansu, fasa shigar yayi yana dawowa ya tsugunna ya gaida Baffan dake tai masa godiya, kafin ya bama ya Sadeeq hannu su gaisu yana jan sa cikin motar shi kuma Baffan suna komawa ciki shida Meenal ɗin, babu jimawa sega Ya Sadeeq ɗin shima ya shigo kafin Gwaggo Sadiyan data matsu da a buɗe ledan ta muskuto tana cewa a buɗe ledan mana.... Komai babu wanda yace mata taja ledar daidai damin kuɗi sabbin ƴan ɗari biyar biyar na faɗowa, daidai kuma da shigowar Shareefah tare da Bilkisu wacce take ƴa ga gwaggo Sadiya, duk su biyun a guje suka taho suna rungumeta da faɗin..... "Oyoyo Yayarmu🫂...." Suka faɗi kowa na sake rungumeta da murna, a cikin ledan kuwa kayan fruits ne da nama me uban yawa, kuɗin kuma pakege ne da 100k dake da Yaya Sadeeq a wurin shi yasa gwaggo Sadiyan ta tura kuɗin ga Baffa tana cewa. "Kai Ma sha ALLAHU babu abinda zamu ce da wannan yaro se godiyar ALLAH, ALLAH dai ya saka masa da alkhairinsa ya bashi masu masa shima, Malam kawo dubu biyar se Bilkisu ta sawo lemu muci da naman...." Ya Sadeeq ne ya buɗe aljihun gaban rigansa ya zaro 2k ya bama Bilkisun yace ta amso na hakan ai ze isa, duk da bata so hakan fa amma haka ta kyale bayan yasha wata uban harara a fakaice. Daga nan ya Sadeeq ɗin da Baffan suka fita don ƙirar sallar karfe ɗayan da ake ta kira, suna fita gwaggo Sadiya taja wata tsuka tana tashi ta bar musu wurin, wajajen ƙarfe uku shiru shiru Meenal taga ba'a ɗora sanwar dare ba, don haka ta fito bayan ta yi shara a gidan ta sake tarar da gwaggon nayi... "Sannu da gida gwaggo amma ai nayi sharar ɗazun babu jimawa." In wurin ya tankata to ita ma ta tanka, yi tayi kamar ta juya se kuma dai ta danni zuciyarta ta sake cewa. "Gwaggo me za'a ɗaro a gidan ne?" Meenerl ɗin ta faɗa tana me sunkuyar da kanta kasa, saboda sanin halin mebi yanzun ma ba wai ya zama lallai bane ta tanka mata. Gwaggo Sadiyan kuwa data wani ɗan ya nutsa fuska kafin cikin halin ko in kula ta ce.... "Dake da can ma ai kene kike min aikin ko?..." Da idanu kawai Meenal ta bita kafin ta sauƙe ajiyar zuciya, kafin ta dawo daga duniyar tunanin daya faɗa, ta tsinkayi muryan gwaggon nasu na cewa.... "Sumumu kasau, rasa kunya ɓeran tanka...." Tasan da ita take amma se komai bata sake ce mata ba ta nufa Dakin Shareefah bayan ta sauƙe wata ƙaƙkafar ajiyar zuciya, kafin a hankali kuma wasu abu me kana da siraran hawaye masu sanyi taji suna zubowa daga cikin idanunta, tana tunowa da Mahaifiyarsu, Ammeyn su mutum me nagarta da sanin ya kamata, da haka ta koma ɗakin nasu ta kwanta wani abu me kama da kewa na taso mata irin na uwar da aka rasa mahaifiya kuma jigon rayuwarsu..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. Page 5&6 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Shigowan Ya Sadeeq ne ya cilasta mata tashi zaune, tana sake goge idananunta, tambayar ta yayi ko wani abu ne aka nata, se ta ce A ahhh don Shareefah bata nan tana Islamiyya, shi yasa ta kwanciya se kuma ta tashi da ciwon kai, dake duk wanda yake tare da ita yasan hakan, yasa sau da tari idan ire-iren waɗannan ababuwan suka faru take ɓuya a bayan hakan, Sosai ya fuskanceta yace. "Wato ke babu me faɗa miki ki yarda ko Meenal?, waɗan nan sabbin ababuwan kenan da kika zaɓarma kanki kuma ko?, ki sani ita kanta shiga ta mutumci kima da daraja take ƙarama mutum a idon duniya, amma in dai burinka ka burge mutanen to ki sani bawai zaki taɓa burgesu bane, se dai ƴan uwanka dabbobi, kuma ko babu komai ai kin kare daraja da kuma martabar auren Ahmad dake kanki, ke yanzun baki kai munzilin da zaki zauna kima kanki da kanki faɗan ta nutsu ba?, to ki sani wllh³ duk sanda Ahmad ya sake samuna da magana me irin haka sena sassaɓa miki wllh, idan kika yi woni abun yanda kika san goyon jakai haka kike, shin ina addi da karatu da nutsuwarki suke je?,ina Sanin yakamanta yake?, ina wannan kunya da kamun kan naki suke?, ina hasalin wannan AMEENEERH SHEHU USMAN ɗin take? Wannan me kunyar, me kare mutumci da martaba da kimar jikinta?, Ko kuwa kina manta cewar... _A hijab is a traditional head covering, usually a scarf, worn by many Muslim women to cover the hair, neck, and sometimes chest in accordance with Islamic principles of modesty. Derived from the Arabic word hajaba ("to conceal"), it serves as a sign of faith, piety, and privacy. While often worn voluntarily, it is legally mandated in some places and restricted in others?....... kina manta cewar The Muslim hijab is a head covering worn by many Muslim women as an expression of modesty, faith, and identity, typically covering the hair, neck, and shoulders while leaving the face visible. It serves as a, voluntary or, for some, involuntary, daily practice derived from Quranic principles of modesty ne Meenal?....Ko kuwa shima kina mancewane da cewar Shi Hijjabinki mutumcinkine? Ki sani kalmar *HIJJABINKI MUTUMCINKI* wata magana ce ta hikima a harshen Hausa da ke nuna cewa sanya hijabi ba kawai umarni na addini ba ne, yana ɗaya daga cikin ginshiƙan mutunci, daraja, da kamun kai na ko wacce mace musulma. Ta inda har wasu fassarori na wannan jigon saka hijab ALLAH ya bamu kamar... Kariya da Daraja, Hijabi yana kare mutuncin mace da kiyaye ta daga kallon banza, wanda hakan ke ƙara mata daraja a idon al'umma da kuma duniya. Ita kuma kanta alamar Kunya, Yana nuna mana cewar mace tana da kunya da kuma kiyaye dokokin ALLAH ne. Kana kamun kai!, Sanya shi yana nuna cewa mace ta girmama kanta, don haka wasu ma za su girmama ta inji Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, sannan Mutunci!!!. Mutuncin mace yana tattare da yadda take suturce jikinta da kuma ɗabi'unta ne inji ALLAH (S.W.T.) A takaice, ma'anar ita ce: *Hijabinki shi ne mutuncinki da darajarki* shi ne ke kuma kike son ɓarar da naki mutumcin ameenatou?, kike son kamar kinyi jayayya ne da hukuncin Alqur'ani da hadisi ne tabbatacce tun daga Rabbil Izzati?, Ki gyara don ALLAH ki gane ameenatou idan kuma saɓanin hakan ya kasance to kiyi kuka da kanki baga kowa ba, ki kare haƙƙin ALLAH da auren dake kanki se ALLAH ya kare ki da kariyarsa shi ma...." Tun da ya fara mata Maganar zuciyarta ke wani kalan tafasa da ƙuna, wato ashe dama shi yasa Ahmad ya dage se ya kawo ta gidan da kansa?, ashe dama don ya haɗa ta yayan ta ne?, aikuwa wllh ze san ita yama haka, wllh seya gane kuskuren daya tabka na haɗata da yayan nata, fita kuma da duk shigar data ga dama yanzun ta fara. Ko kafin ya dawo tuni har ta hau napep ta tafi, ba tare data tsaya tayi sallama da kowa dake gidan ba, kai tsaye asibiti ta wuce se wajajen taran dare kana ta koma gidan, duk kuwa wunin ranar daya jima yana mata a waya, amma ko sau ɗaya bata ɗaga ba, domin taga idan ta tsaya wasa se Ahmad ya kaita ƙasa warwas. Ita kuwa ta rantse daya kaita ƙasa kara tayi duk me iyuwa ta nuna masa cewar ɗin *Kainuwace dashen ALLAH* bana *Mutum ba*, koda ta dawo lokacin yana parlour amma haka ta tsallake shi ta wuce ɓangarenta, tana kuma shiga ta kulle ta yadda bema isa shigowa inda take ba. Washe gari koda ta tashi iyaka cikinta ta dafa abinci, nan ma be tanka taba, ya rabu da ita, don yaga yau ba shirin fitar ma tattare da ita duk da kasancewar Monday ce, don riga da wando ne a jikinta trouser se vail da tayi Rolling dashi, ga wani eye glasses data maka a ido, ci kanka bata ce dashi ba kamar yacce shima be ce mata ba, amma ga mamakinsa se yaga ta fito ɗauke da handbang nata da wayarta, sokoko ya tsaya kallonta don ganin yau kuma da abinda ta fito, ganin dai tabbas da gasken gaske fitar ne zatayi ya saka shi saurin shan gabanta, yana me furta. "Meenal ina zakije da wannan shigar dake jikinki?...." Cak ta dakata tana me furta. "Wurin aikina mana ko kana da matsala da hakan ne?, ko kuwa yau ɗin ma gidan zaka je ka sake haɗa ni da yayana???..." Tayi maganar ranta ɓace zuciyarta na sake fusatuwa sosai akan abinda ya matan. Numfasawa yayi ya ce.... ★.. "Ke yanzun saboda nace ki ringa suturta jikinki shi ne kikace bara ki nuna min ƙarshe na kenan ko?, to shikenan Meenal kiyi duk abinda kikaga ya dace da rayuwarki, nikam na gama nawa na kuma fita haƙƙin ki,kije rayuwarki ce, kiyu duk yacce kikaga dama da ita fine. Tun da hakan kika zaɓarma kanki rashin daraja da kimarki....." Aikuwa dama kamar jiransa take tace. "Nayi na kuma zaɓa hakan Ahmad!!!, na ji na kuma gani wannan ɗin rayuwar tawace ba ta wani ba, don haka a barni inyi duk yacce naga damar yi da ita, kai a jakin tunaninka don kaje ka haɗani da yayana shikenan ka gama ne?, to ka sani fita da duk kayan dana ga dama wannan rayuwata ce, kuna yanzun na fara..." Da kallo na hasalin mamaki al' ajabi yake kallarta kafin ya sama zarrar cewa... "Kiji tsoron ALLAH ameenatou!, AMEENERH kiji tsoron haɗuwarki da Ubangiji ya zata kasance?, ki guji haɗuwarki da UBANGIJINKI wllh... Nie dai ALLAH ya gani nayi iya yin da nai, amma abin ya gagara kin kasa sanjawa har yanzun...." Dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu tace. "Kaga dakata Ahmad!, wai Don ALLAH wannan mummunar alkaba'in da kake ta yi a kaina kana tunanin kai uwata ne ko kuwa ubana?, nace da zai kamani koya bani tsoro?......" Ɗan ja da baya yayi don se ya kalla wannan ɗin kamar ma Meenoh ɗin sa bace? Yana me furta. "Subhanallahi ameenatou Ni ina matsayin mijinki shi ne kike gaya min wannan maganar???" Wani mugun tsuka taja tana fisge car key na motar dake hannunsa ta yi compound na gidan nasu, ja da baya da baya ya fara yana dafe kansa yana rasa kalmar daya kamaci ace ya fara ambata a matsayin wacce zata bashi nutsuwar da yake nema kai tsaye... A lokacin da take barinsa nan da mutuwar tsayen da yayi ita tuni har tama motar key dake dama ta iya tayi reverse tama bar gidan baki ɗaya, cikin wannan dai shigar da bai dace ba samm ace matar Aure ne ta fita dashi, kai ko budurwarma indai tasan daraja da kuma kima da mutumcin kanta ba zata fita da shigan ba. Tana ɗaukar titin ta saki waƙar *SOJA BOY* Ta _ƘAUNA NA BAKI_ . Yacce kukasan itane tayi wakar haka take binta har wani rausaya da sakin kan motar take. Idan wakar ta ƙare ta sake dawo da ita on repeat. Tayi nisa sosai motar ya tsaya cak, taki gaba da kuma ki baya, don haka dolen dole bata da yacce zata yi dole ta saka ƙiran numbern sa, sedai baya ɗagawa saboda baya ma kusa da wayar ne, ga wani ƙara da motar ta ɗauka yi taje ɗuuuu ɗuuuu ɗuuuuu. Dole ta fito ga wayar da Dr pooja ke famar mata akan cewar tayi maza ta ƙaraso wata tiyata ce ta sauri zata shiga. Gaba ɗaya ta rasa yacce zata yi don haka ta saka ƙiran Dr pooja ɗin tace mata wllh motar tane ta sama matsala, amma INSHA ALLAHU tana gaf, tana nan tsaye kamar anyi tofin ala tsine a wurin babu motar data wulga, can sega wata mota nan ta ɓullo kiɗa se famar tashi yake a cikin motar kan gari, irin ta arnan nan. Har motar ta wuce ta ɗan yo baya kaɗan tana dawowa da baya daya har inda take tsayen, mutane huɗun dake cikin motar duk suka firfito suna tambayar "Ƴan mata lafiya kuwa?, kamar temako kike nema ko?" Ɗaya daga cikin su ya tambayeta, wayarta dake hannunta da car key na motar ta ɗan gyara riƙon su tana me furta. "Ehh motar ce ta ɗan sama matsala wllh..." "Ok to mu gani ko zamu iya temaka miki mana..." Wannan na farkon again ya sake faɗi, gaba tayi tana buɗe musu gabar motar su kuma suna isowa suka fara kamar alamar dudduba mata. Kafin cikin su wani yayi hanzarin fakarta ya shaƙo wuyanta, wani kuma ya riƙe hannayenta suna kaita ƙasa. Ihu ta saki tana me furta..."INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN ³ ku cika ni mana me zaku min, kuji tsoron ALLAH Matar aure ce ni,wllh nie Matar aure ce ku rufa min asiri ku ƙyaleni....." Haka take faɗi sedai babu me jinta, se ALLAH'n data riga ta take dokoki da ƙa'idojinsa. Don haka se ya barta da iyawarta ya gani ko zata iya yaƙar kanta daga miyagun mazan da dama kamar tana tallata jikin nata wa su ne. Firkici da tsoron abinda taga suna shirin aikata mata ne ya sumar da ita..... Yana zaune duk a parlourn ya gaza tabuka komai, ko ta kan ƙiranta be bi ba duk da cewar yaga miss call nata wajen uku, amma se bi ba, ga zuciyarsa dake bugawa time to time da tsananin karfi. Yana nan a zaunen wayar ya sake shigo masa, lokacin ma an ɗan ja lokaci sosai akan baya, don haka ya rarrashi zuciyarsa ya ɗaga din tana daga zaunen, sedai jin muryan wani da daban saɓanin Meenal ɗin ne ya saka shi furta "Lafiya kuwa?" Daga ta can ɓangaren aka ce "Kai ne Mijin me wannan wayar ne?" Cike da tsantsan tashin hankali ya ke cewa... "Ehhh ni ne wllh ni ne wani abu ya faru da ita ne?, accident ta samu ne....?" Daga ta can aka sake ce dashi dama mun kwaci matar kane hannun wasa yara a gefen titi sunyi mata fyaiɗe...... Yanzun haka tana kwance a asibitin da take aiki...." Wani kalan zabura yayi yana ja da baya ya miƙe ya na cewa.... "Eyeeee Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³ fyaiɗe???...." Kafin ɗif ɗif ya datse ƙirar wata juwa da jiri na kwasar shi da Hajijiya.... *Around 4:20 Pm* Ahankali slowly ta shiga buɗe idanunta da taji sun mata nauyi loƙaci guda, ɗan lumshesu ta sake yi tana ƙoƙarin saita kanta da dawowa cikin sense nata, ga wani nauyin da taji kanta da idanunta nayi na bala'i, gaza ƙarasa buɗe idanun nata tayi, sakamakon ahankali ahankalin da ababuwa suka soma yowa zeroying brain nata. Highlighting abinda ya faru da ita ta shiga yi tana ƙiran _Hasbinallu wani'imal wakeel_ adai cikin zuciyar nata taci ga da cewa _ba gaskiya bane wannan mafarkine baze taɓa yiwuwa ba na sani?, tabbas ba gaskiya bane hakan bazai taɓa faruwa dani ba...., Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!" Kalaman da take ta famar nanatawa kenan da muryarta wacce ke rawa ba kuma ta fita sosai, wanda ya saka hankalin Shareefah dawowa gare ta dake zaune se famar ɗauke kwalla take, don ita kaɗai ce a wurinta, Yaya Sadeeq yace babu ruwansa da duk abinda ya faru da ita. Ganin yacce take ne ya saka ta saurin miƙewa ta nufa fita don ƙirar Dr pooja da tace data farka ta ƙirata, se dai suna shigowa bata ko numfashi alamun ta sake somewar kenan, don haka kai tsaye wasu nurses ta kira suna turata a gadonmarassa lafiya....Direct emergency room aka wuce da ita domin abin nata na nemar fin ƙarfin tunaninsu suma, daga ta farfaɗo seta kuma suma tun kafin wani lokaci. After 20mn. Gaba ɗaya hankalin Shareefah ya sake tashi tun da aka shiga da Yayar tata take ta famar safa da marwa a bakin ƙofar emergency room ɗin, daga can gefe kuma Ya Ahmad ɗin ne da shi ɗin ma yake tsayen ya gaza tafiya, sedai baya kusantar inda take amma kuma ya gaza tafiya ya barta. Inda kowannensu da irin abunda yake saƙawa acikin rai da zuciyarsa.saidai banda ita da tunani da kuma nutsuwar zuciyarta suka kau, don sun jima da barin jikinta suna tafiya wani wuri na daban, wanda take cike da tarin fargaba acikin ranta dangane da makomar auren yayar nata, wanda indai zata tuna hakan ne ke sanadiyyar saka hawayen dake cikin idanunta kasa tsayuwa. Around 6:30 pm. Har zuwa wannan lokaci suna tsaye bakin emagency room ɗin, sunƙi matsawa ko ina bayan sallarn da shi yaje masallaci yayi ita kuma tayi anan dandanin wurin. Haka kuma har zuwa wannan lokacin doctors ɗin dake cikin emergency room ɗin, suma basu fito ba suna can suna kokarin saita tunani da natsuwarta da se sun samu kamar zata dawo daidai seta sake birkice musu, duk yanda suka so control matsalan amma abun yaci tura, Ganin abun na ƙoƙarin fin ƙarfinsu ne kuma ya saka su yanke hukuncin wucewa ita ICU kaitsaye, saboda acanne zata fi samar kulawa fiye da nan ɗin ma, gashi daɗi da ƙari ko babu komai yau Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ na cikin asibitin, wanda a da ita ce wacce zata yi aikin, rashin ta ya saka dolen dole Dr pooja ma Dr Bilal waya ta sanar duk abinda ake ciki, shi kuma baya gari lokacin yaje wata interview ta manyan Dactor's, don haka kai tsaye ya ƙira gida ya sanarma Abban MAJEED ɗin ana son ganinsa maza maza a cikin asibitin, wanda kai tsaye yasan in ba hakan ya masa ba bazai taɓa zuwa ta sauƙi ba, kuma har lokacin yana cikin ICU ɗin. Acan ɓangaren Shareefah kuwa har zuwa lokacin tana wajen emergency room ɗin a zaune tayi jigum ta manna kanta da jikin bangon ginin, daga ta can kasar raunatacciyar zuciyarta kuwa sunayen ALLAH kawai take ta famar ambatowa, cike da saka duk wani fata da kuma burin ta akan Yayar nata, Kan zuwa yanzun kuwa kan kuma zuwa lokacin da abin ya faru ta zubar da hawaye masu yawan gasken da basa da adadi, har saida cikin idanunta sukayi jajur suna mata wata kalan zogi da kuma zafi, fyaiɗe ba?, fyaiɗen ma wa Matar aure?, shin tayaya mutane zasu ringa tunanin duniyarmu zata zauna ƙalau, alhalin kuma ɓarna a ban ƙasa tayi yawar da bata da adadi ko iyaka?...... Tana nan zaune har bata san iyaka adadin da ta sake ɗauke ba taji kamar motsin buɗe kofa, wanda ya saka ta ɗagowa hakanan taji zuciyarta na bugawa, wannan dalilin yasa ta tsurama ƙofar fitowan rinannun idanuwanta, wanda kai tsaye ganinta na sauƙa akan *Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ*, dake ta famar wani kalan bala'i yana yima Dr pooja tsawa ran nan a matuƙar ɓace, fuskarnan da dama take ɓaka ta sake rinewa, amma fa bawai baƙi irin na muni ba, irin na hasalin masu jin daɗi da kuma kwanciyar hankalin da suka gama ratsawa, haka ya wuce wanda ya saka Dr pooja ɗin jan burki a gaban Shareefah ɗin. Tana me ƙoƙarin zare handgloves ɗin dake hannunta... "Dr yaya jikinta ?, ta farfaɗo?bata dai sake somewar ba ko???" Haka Shareefah'n keta famar jeroma Dr ɗin tambaya, cike da fargaban kada agaya mata cewar har yanzun bata a daidai nata bata cikin sense nata. Ajiyar zuciya me ɗan zurfi Dr pooja ɗin ta sauƙe, kana cikin son kwantar mata da hankali tace.... "Jikinta yayi worst sosai ne, wanda firgicin abinda aka mata ne ya sakata sumewar da tayi, har hakan ke ƙoƙarin taɓa brain nata amma In sha ALLAHU zata sama sauƙi da izinin Ubangiji.... Ta kai ƙarshen maganan tana me kallon Shareefah'n dake ɗibar kamanni sosai da Meenal da ta tsare ta da idanunta sosai tana kallonta, dukansu shiru sukayi gaba ɗayansu, yayin da itama gefen Dr pooja ɗin tsananin tausayi da ƙaunarta ke mugun kamata. Wasu irin zafafan hawaye ne suka sake gangaroma Shareefah'n daga cikin idanunta, zuwa kan ƙuncinta, cike da raunanta haɗi da rashin ƙwarin zuciya ta koma ta sake jingina jikinta da bango... Rashin Ammeynsu na dawo mata sabo fil, ta tabbata da ace tana raye da tuni tana nan rungume da kan Meenal ɗin suna raba ciwon tare... Da sauri tayi hanzarin ɗago kanta jin kamar an sake buɗe ƙofar da aka shiga da Yayar nata, wasu nurses mata ne guda biyu suka fito da yayar nata a gadon marasa lafiya.Ganinsu da tayi ne kuma yasa har kamar a ɗan zabure tayi kansu, saidai kasancewar kuma suna sauri sosai ne, yasa ta kasa cimmusu saboda dakatar da ita da ɗaya daga cikin nurses ɗin tayi, bisa dole haka ta tsaya akan ƙafafunta dake rawa, daga can nesa tana zubawa fuskar Mijin Yayar nata ido, da har lokacin ya gaza tafiya shima,sedai dishi dishi take kallonsa saboda ruwan hawayen da suka cika mata idanu. A cikin zuciyarta take sake jin tsananin tausayin Yayar nata acikin zuciyarta, sai takejin cewa tamkar Yayar tata zata rasa damar ci gaba da kasancewa a karkashin inuwar Mijin nata, tana jin ya zatayi da irin wannan rayuwar da take shirin fuskantar ta a cikin rayuwar auren ta?, Haƙiƙa ta sani cewar Yayar nata mutum ce wacce take kamar tinzirarriya, wacce idan aka hanata abu to ita kuma kamar a lokacin ne ma ake ingiza ta gashi wannan abin ɗin, Hakan kawai da take hasasowa ne ke saka karya mata zuciya, hakan yasa ta sake damƙe hannunta ɗaya dake cikin ɗaya a bayyane cikin raunin murya tace.... "Allahumma La sahala illama ja’altuhu sahala, wa’anta taj alul hazna iza shiyta hasla, Yah ALLAH ka taimake mu!, Ya ALLAH ka kawo mana ɗauki da agajinka ka kawo mana mafita a cikin wannan halin da muke ciki, ka dubemu da idon rahama ya Rahman ya Arrahaman Rahimin!!!......" Ta ƙare maganan tana kuka hadi kuma da ware idanunta, cikin wani kalan damuwar dake sake shigarta take cewa.... "Hasbunallahu wani'imal wakeel!!!" Tana kamar zata shiɗe daidai da isowar Ya Sadeeq daya biyo bayanta, don bai zata abin ze kai haka ba, kuma dama shima yana da zafin zuciya da kuma riƙe abu a zuciya. "Shareefah!" Ya ƙirayi sunan ƙanwar nasa cike da damuwa da tashin hankali, yana tallafo fuskarta dake ɗauke da tsananin damuwan halin da yayar nata take a ciki, yanda yaga hawaye caɓa caɓa akan fuskarta ne ya sake tashin hankalin sa. Kafin a sanyaye ta ɗago cikin muryan kukan dake ƙoƙarin sake kufce mata ta kamo hannun yayan nata, kafin cikin sigan bayyana tsananin rauni da damuwarta tace. "Ya Sadeeq ka taimakeni banason in rasa Yaya Ameenatou......" Daga yanayin yanda tayi maganan cikin muryar kuka ne yasa idanun Yayan nasu cikowa da nashi hawayen shima, Saboda yafi kowa sanin iriyar tsananin SO da ƘAUNAR dake tsakanin Shareefah ɗin da kuma ameenatou ɗin. Hannunsa yasa ya ɗan dafa kafaɗanta cike dason kwantar mata da hankali yace. "IN SHA ALLAHU babu abinda ze faru da Meenal, wannan ɗin ma kamar kuskuren tane ta amsa daga Ubangijin ta, idan tana da rabon shiriya daga wasu daga cikin halayenta shikenan ta rabauta ranar gobe kiyama..... Jiya jiyar nan na gama magana akan ire-iren shigar da take yi wanda be dace, amma haka ta kaɗa kunnenta maganganun nawa suka wuce ta bayan kunnenta, ita rudin sauran Dactor's na ɗibarta, da yin duk abinda suka ga dama, wanda a yanzun mafi yawancin abinda Dactor's sukafi yi kenan, duk shigar da suka ga dama daga Matan Aurensu har ƴan matan cikinsu, suna ɗaukar hakan a matsayin wata waye wace ta zamani da tazo musu, se dai suna aikata kuskure ne ba tare da sanin suba, lokaci suka nema kuma ALLAH ya basu sedai su sani. Daga lokacin da shi wannan lokacin ya gama kare musu daga nan na ALLAH ke farawa, don faɗin sane hakan domin shi da kansa yace....Yaku bayin ALLAH, ku ji tsoron ALLAH, tsoro na gaskiya domin tsoron ALLAH shi ne ginshiƙin rayuwa mai albarka, shi ne hasken da ke shiryar da zuciya a cikin duhun duniya, Ku kusanta kanku gareni ku nisanci duniya, domin duniya tana wucewa ne kamar mafarki. Abin da muke gani yau gobe zai zama labari tabbas, duk wata ɗaukaka zata barmu, dukiya za ta bar mu!, mukami zai gushe mana, kamar yadda in mun mutu mutane za su manta da mu. Amma aikin da muka yi domin ALLAH shi kaɗai ne zai tsaya tare da mu a kabari, ya kuma ci gaba da ribanya bayan koda ta hanyar kwatance da halaye na gari ne, yana cewa kada mu yaudari kanmu da buri, alhalin mutuwa ko ƙaddara basa taɓa tambayar shekaru ko matsayi da girman ikon mutum , aikinsu kawai suke gudanar akan duk wanda ya bari son zuciya da duniya suka gama rinjayarsa. Inda yake mana nuni da kamar yanda da yawan wasu mutanen sun fita daga gidajensu da safe lafiya lafiya ne, amma ba su dawowa da yamma sabo da amshi abinsa. Ko anan ya kamaci ace duk bawa me tunani me kyau ya tsaya nazartan shin, me na tanadar ma kaina wa ranar da za mu haɗu da ALLAH?, se dai kash bamu tunanin hakan sabo da duniyar kaɗai muka sa gaba, inda yake cewa da zaku gyara zukatanku kafin tsayuwa ranar hisabi, Ku kuma yawaita istigfari, ku kuma koma ga mahaliccinku da tuba na gaskiya, ku darajanta jikkunanku da kun sama babban sakamako a ranar gobe kiyama, kuyi gaggawar tuba a gareni domin ni me gafara ne, ku dena koyi da shigar arna, koyi koyi da abinda addininku ya baku ba na wasu ba, dana azartaku da manyan hijjaban da zasu kare duk haufi naku a ranar gobe kiyama.... Amma Meenal taki ganewa Shareefah, ra'ayin nasara sun rinjayi nata ra'ayin, tabbas wannan aikin nata be jawo mata komai ba face taɓewa da lalacewa mara ƙarshe da kuma tushe... Ashe don ALLAH yace ka suturce jikinka ba ni'ima bace, yanzun ni nan dake dake nan wurin,duk mun tsaida hujja a kanmu, ita Rayuwar duniyar da muke kallo tamkar zubin dashi ne, iyaka kirki ko zunubin da muka aikata su zamu samu, domin kuwa dama ALLAH (S.W.T) cewa yay mana damu, rayuwar mu ta nan gidan duniya kamar mun zo munyi shuka ne, can kuma shi ne ranar abinda zamu girba , amma duk da zuciyoyinmu sukan rinjayi ra'ayoyin mune daga tafarki na gaskiya zuwa tafarkin ƙarya da burge wasu dabbobin mutanen da sune ALLAH ya ware ya mana misali dasu...... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³ yake nanatawa tare da Baffa dake tsaye daga bayansu tin farkon fara maganar nasu, se Dr pooja dake tsayen itama gaba ɗaya tsigar jiki da jikinta na wani kalan rawa, a duk lokacin da zata ji ana wa'azi, ko tunasarwa me irin haka. Gyaran muryan Baffansu su ne ya saka kukan Shareefah dakatawa, nuni ya mata da Dr pooja take kuwa itama ta fuskanta halin da take ciki, kai tsaye ta fara ƙoƙarin tallafa mata duk da itama tallafin take. Suna haka sega wata nurses mace nan ta iso wurin tana amsar pooja ɗin suka fara tafiya. Kai tsaye kuma Shareefah'n ta miƙe tana ma su Baffa jagoranci zuwa ɗakin da Meenal ɗin ke kwance amma ta cikin glas, don babu damar shiga ko waye kuwa in aka ɗauke ma'aikatansu. Wata guntuwar kwalla Baffa da Ya Sadeeq suka ɗauke kusan tare, har dama Ya Ahmad da tin isowar Baffan yake biye dashi, sedai baya da bakin da ze iya buɗewa balle har yayi magana, ganin hakan ya saka Baffan kyaleshi ya hutayye ma zuciyarsa, duk da kasancewar bawai ma sanin takamaiman makomar auren Meenal ɗin suka yiba...... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. Page 7&8 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ.... Sunfi ƙarfin 30 minutes tsaye a wurin kafin Ya Sadeeq ya lalubo hannun Baffansa cikin nasa tafin, cikin dauriya da son danne raunin dake son taso masa game da ƙanwar tashi yace. "Muje gida Baffa!" Don ya lura da yanda jikin Baffan nasa ke rawa, ganin hakan ya saka Baffan kallon Shareefah shima yace da ita. "Muje gida!" Kanta ta girgiza masa wanda taji kamar ze faɗo ƙasa na tsananin damuwar da take ciki, da kuma yunwar dake ƙoƙarin illatata ba tare da sanin taba,don ita samm a babin yau ɗin nan komai mancewa tayi dashi bare wani abinci da ta gama ɗaukarsa ƙaramin alhaki. "Zan tsaya anan Baffa!, Yaya Meenal zata iya farkawa a koda yaushe likitoci zasu bukaci wani nata a kusa!, kuje gida ni ina nan tare da Yaya Meenal...." Ta faɗa idanunta a soye don jin ƙaddarar yayar tata take kamar tata ce, "Kuje gida Shareefah ke macece kuma yarinya ƙarama, zan kula da ameenatou kuje....." Haka duk su ukun suka tsinkayi muryansa, wanda a kallon farko baka isa cewa shi ne yayi maganar ba, daga yanayin yadda fatar bakinsa take a bushe raƙayau, babu kuma wata alamar da zata nuna maka cewar shi ne yayi maganar... Taku ɗaya ana biyu ta ƙara tana tsaiwa a gaban mijin Yayar nata tace. "Kai ne zaka tafi ka barni, domin Ni nafi chanchanta da kulawa da Yayata...." Ba kallonta yake ba sema baya kaɗan da yana yana sake harɗe hannunsa a ƙirji yace, "Ni nafi chanchantar kulawa da ameenatou Shareefah, kina da buƙatar kaɗaicewa ki sama nutsuwa haka nan kema...." Idanunta da suka sake cika taf da hawaye tace "Ni babu inda zana je, sabo da ni macece ƴar uwarta zanfi bata kulawan da tafi buƙata!" "Ni kuma Mijin tane ni ne zanfi kowa bata kulawar da kowa be isa bata ita ma Shareefah!" Daga ya kamo hannun Ya Sadeeq da suka jima da zama status shi da Baffa yana tsaida shi gabanta yace. "Ku tafi........" Ya Sadeeq ɗin ne tamkar wani gunki ya ɗamko hannun Shareefah ɗin ganin yadda take jujjuya masa kai alamar ya barta. Babu yacce ta iya, babu kuma yacce zata yi dole yaja hannunta suka tafi, ta tafi tabar Yayar tata a cikin wayuyacin halin da take a ciki. A cikin rai da ruhinta tana ayyana ba laifin yayarta bane, laifin wulaƙantattun wasu mazan irin ƴan iskan garin nan, ba laifin shigar dake jikinta bane, ba laifin ta bane, ba laifin ta bane, laifin wasu mazajen ne masu son zuciyoyinsu, in banda haka daga ganin mace a hanya shikenan seku haike mata?, dolen dole laifin ba nata ba ne, ko tashi sayayyarsa ALLAH yayi mazan ze kama... Haka take ta jujjuya maganganun ita da zuciyarta. Tin da suka bar wurin Ya Ahmad ya sake jingina da jikin ginin wurin se a lokacin wani abu me kama da dawowa hayyaci ya same shi, wani kalan rumtse rinannun idanunsa da soye yayi ƙafafunsa na fara rawa, ya fara bi yana dafe bangon dake ginin wurin, jikinsa da gaɓoɓinsa na kamar ana ruru musu wuta ne ata jikinsu, isowar Dr Bilal ne ya temaka masa, sabo da Dr pooja da tayi waya dashi ta labarta masa yacce ake ciki, amma bata faɗa masa ainihin abinda ya faru da Meenal ɗin ba ta ɓoye hakan a iyaka zuciyarta, se kuma Sir MAJEED da tayi kuskuren sanarma wa, wanda yace daya saka tsarkakan hannuwansa ya duba ta shima ya kwashi nashi rabon tagomashin zunubin, ƙara ya barta ta mutu, da uban wa yace karta kare martabar aure da addininta... Shi ne fitowar nan da yayi yana ta balbalin bala'insa har Shareefah ta gansa. Shi da kansa ya temaka ma Ahmad ɗin ya miƙa shi ɗakin jinya ya kwantar dashi, tare da auna jininsa da yaga yayi mummunar hawa, drip ya fara ɗaura masa da masa alluran bacci zuwa can dare ya gani, idan har be sama pain Relief ɗin da ake buƙata, se a san yacce za'a yi dashi, bayan ya masa wasu allurai. Ga jikinsa da har wani hucin zafin yake fitarwa tsabar yadda yake amsar kidan dake sake rikita jiki da zuciyarsa, ga daga cikin kansa ji yake kamar ana masa bikin mahaukatan aljanu a cikin tsakiyar kan nasa, sannu a hankali tunaninsa ya fara janyewa yana nesa nesa dashi alluran da aka masa na fara rinjayar kai da tunaninsa, wani wahallen barcin da har a cikinsa mafarkan Meenal ɗin ne kawai a cikinsa, Meenal ɗin da yake ɗaukarka a matsayin DUNIYARSA, se gashi sama ta ka ta meda wannan Duniyar tasa ba komai ba, domin ta gama rugujeta tass babu komai a cikin ta se tarun wasu ababuwan da bai gama tantance ko sanin ko meye su ba.... *Meenerl* "DON ALLAH DA DARAJARSA KU ƘYALENI, KU RUFA MIN ASIRI NI....NIE MATAR AURE CE, KARKU AIKATA HAKA GARENI NA HAƊAKU DA GIRMA DA ZATIN DA MAHALICCINMU YAKE DASHI....!!!" Da sauri ta wani kalan dafe kanta tare da ƙoƙarin son ganin ta motsa idanunta ko yaya ne, amma hakan na ƙin faruwa sakamakon abubuwan da suka faru da ita ne kawai keta famar dawo mata a sabbin su.... "ALLAH ba zai taɓa ƙyale kaba, ku sani har da ku da kuka bashi goyon baya, zaku hulaƙanta!, za kuyi dana sani, ƘARSHENKU ba zai yi kyau ba, domin kun keta kima da darajar addininsa...." Ta sake faɗar kalmomin domin ita a tunanin ta har zuwa lokacin a hannunsu take, "Kin makaro Ƴan mata, domin rising naki be amsu ba, uban wa ze ganki da shigar dake jikinki ya yarda ke *MATAR AURE CE?*, to ki sani idan ma ke MATAR AUREN CE se mun keta haddin ki, tun da shigar dake jikinki ita ce ta rinjayi ra'ayina a kanki har na kware miki, dole inyi abinda na gama ƙyasa shi a cikin zuciyata, dole ne in kwashi ganima yau...." Kalmar mutumin da fuskarsa ba zata taɓa goguwa a cikin idanunta ba ya faɗi hakan, yana fara yayyage kayan dake jikinta, dukansa da yaƙushinsa ta fara amma ba abin komai ba..... Da ganan sak komai nata ya tsaya shikenan nan wannan shi ne MAFARIN..... Kanta ta riƙe ahankali taci gaba da processing farkawanta na farko!, da sumewar data ringa yi haka komai ya shiga dawo mata daki daki cikin kanta, wani kalan rumtse rinannun idanuwanta da suka kasa buɗuwa tayi, ga zuciyarta dake mata wani kalan zogi da ɗacin da ita kaɗai ce tasan iriyar ukubar da take amsa daga hakan, yanzun shikenan hakan yana nufin sun gama da ita kenan? Sun keta hijjaban dake lulluɓe da igiyar AURENTA kenan?, Yanzun shikenan Ya Ahmad rabuwa da ita zeyi kenan?, shin yana inama?, a wanne hali yake yanzun?, tasan duk inda yake baya ƙalau wllh, shi take son gani!, so kawai take ta gansa. Kanta taci gaba da jujjuyawa tana riƙe da kanta muryanta a kasa can sosai take wasu maganganu... Ƙarar tsoki taji an saki, kafin wata fusatacciyar murya ta biyo baya ta hanyar furta kalmar *"IDIOTS"* Bata san murya ko fuskan me maganar ba, don haka ta tattaro duk wani sauran kuzarin da take da tare da ambaton sunan ALLAH, tana buɗe idonta da a disashe suka ƙarasa kalle mata baya da gilmawar inuwar koma waye ɗin, bata zurfafa ko cilasta kanta ba, ta sake jan idanun nata ta kulle wasu zafafan hawaye su biyo bayan hakan. Sosai take ƙoƙarin dannar zuciyarta kasancewarta macece ita me dauriya, da shanye ko wanne irin ciwo da raunin dake cikin zuciyarta idan taso,don haka ko a yanzun ma take ƙoƙarin ganin ta danne hakan saboda ta taso yaƙi hakan. Wani kalan rumtse rinannun idanuwanta tayi a karo na babu adadi tana lallasar zuciya da gangar jikinta dake son bijire mata. Ita da kanta ga shiga bama kanta ƙwarin zuciyar shanye hakan ta fuskanta rayuwar da kyau, ta kuma yi gwagwarmaya tukuru wajen gyara rayuwa da gobenta. Don haka tayi luff idanunta lunshe, A yayin da ruhi da zuciya da gangar jikinya suke samun nutsuwa da hutu, mizanin yadda numfashinta ke sauƙa akan tafukan hannayenta tana tarar ruwan hawayen ƙarshen da In Sha ALLAHU ta gama zubar dasu kenan akan ƘADDARAR data afka mata, Kai bama iyaka ƙaddarar yau ɗin taɓa da duk wata sabuwar da zata zo mata cikin wannan duniyar zata jure, ta kumyi gwagwarmaya da yakar hakan, tafukan hannayenta dake riƙe da fuskanta da hawayen ke ci gaba da bi ta gefe da gefen fuskarta suna sauƙa a cikin tafukan hannayen ta rumtse, wanda take jinsu kamar ɗigar dalma a cikin zuciyarta, haka zafinsu ke ƙara birkita kanta da tunanin ta suna ci gaba da zana mata tabon ƘADDARAR da take kallar kamar ita da kanta ta sema kanta hakan. Wanda kai tsaye idan da ace wani zai iya tambayarta miye sanadin ƘADDARARTA?, Da kuwa kai tsaye zata ce dashi ita ce, wanda rashin bin dokoki da ƙa'idojinsa suka jaza mata, wanda taurin zuciya da zafinta da rudin zamani suka bi suna haɗawa duka waɗan nan abubuwan wuri guda su cakuɗe mata, harma suka mata taron dangin daya jata zuwa ga ƙaddarar ta, tabbas ta yarda ta kuma amince ita ɗin tamkar *MISALI CE* da ALLAH ya bar ma ƴan baya a kanta, tamkar kuma *IZINA CE* gamai hankali da tunani. Wannan yasa da wani kalan gudun ceton rai da fitar numfashi take ƙoƙarin danne zuciyarta daga son faso ƙirjinta da take son yi ta fito, wanda tama kanta alƙawarin cewa IN SHA ALLAHU ba zata taɓa barin hakan, ya zama shi ne destiny ɗin ta ƙaddarar data yi wa rayuwarta dabaibayi wajen fitar numfashinta na ƙarshe ba. Wanda zuwa lokacin wajen ƙarfe biyu na dare ne, Amma har yanzu hawaye bai daina zubowa daga Idanunta ba,kamar yadda lokacin ke wucewa haka hawayenta ke ƙaruwa maimakon raguwa ma.... Wannan hali da take a ciki ne ya sake haddasa bugun zuciyarta ya karu wani zazzafan zazzaɓin kai tsaye na kai mata farmaki, hakan ya saka Dactor's biyun dake duty saurin ƙarasowa gadonta suka danna mata allurar bacci, wanda da farko fin ƙarfin allurar nasu tayi ma, har seda wata data kasance musulma ce ta taimaka da tofa mata wasu adda'o'i kana baccin ya ɗauke, sedai masu cike da wasu muggwan mafarkai wa rayuwar... Ƙarfe goma a cikin asibitin tama su Baffa dukansu tare da gwaggo Sadiya da Bilkisu, sedai basu faɗin musu hasalin abinda ke faruwa da Meenal ɗin ba, kawai sun ce bata jin daɗi ne, wanda se da ƙyar gwaggo Sadiyan ma ta yarda ta biyo su, don da cewa tai bata zuwa jinyar lallauyi dai kowa tana kansa, se ita ce dan raki da lalacin tsiya daga fara laulayin zata fara tara ma kanta jama'a da mutane. Se kawai suka bita a hakan suka taho, don su duka ukun suma kansu alƙawarin bisne hakan a iyaka zuciyoyinsu IN SHA ALLAHU. Zuwa lokacin kuma Alhamdulillah ta dawo daidai ɗin ta sakamakon kwarin gwiwa da zuciyar da ta ringa bama kanta. Har ma an dawo da ita normal room da kowa ze iya shiga ya ganta... Shigowar Baffanta da Yayan ta da ƙanwarta dasu gwaggo Sadiyan ne ya saka ta binsu da rinannun idanuwanta tana kallarsu kamar wasu sabbin halitta, zama daga ƙafafunta Shareefah tayi a natse tana dafa kafaɗar Yayar tata ahankali, wanda ya sata ɗagowa a sanyaye ta juyo tana kallon Shareefah'n da jajayen idanunta da suke rine sosai har lokacin, Shareefah'n bata ce bata ce komai ba har na wani ɗan lokaci suna zazzaune a hakan, kafin Gwaggo Sadiya ta miƙe tana me furta. "To Ameenatou ALLAH ya sauwaƙe, dan tafiya zanyi, ni ban san a gidan makoki muke ba mun zauna munyi jigum jigum kamar wasu masu damuwa ko wanda iftila'in rayuwa ya afkawa... Bilkisu taso mu tafi dan zamu biya ta gidan Inna Marka mu dubata...." Da wannan Bilkisun ta miƙe tana kallar Meenal ɗin don da zuciya ɗaya take ƙaunarta tace "ALLAH ya sawwaƙa Yaya ya baki lafiya..." Suka fita daga ɗakin ya rage se iyaka su, Suna fita ta buɗe idonta da suke jajir tace "Baffa ka yafe min, kaga abinda ya faru da rayuwata ko?, don ALLAH ka yafe min Baffa...." Be kalleta ba yace. "Ai ba yafiyana ya kamaci ace kin nema ba Ameenatou!, domin kuwa ba ni ne kikama laifin ba, yafiyar mijinki da ubangijin ya kamaci ace kin fara nema, domin kuwa su kika saɓamawa..." Shareefah ce ta miƙe tsaye tana isa ga mahaifin nasu, har gaban ta kai ɗurƙushe ta ce "Don ALLAH ka yafe mata Baffa wllh ba zata iya ɗaukar waɗan nan abubuwan ba...." Seda ya danne tuƙiƙin dake ƙoƙarin taso masa kana yace. "Zata iya mana, tin da ita ne ta saya hakan da kuɗin ta..." Yaya Sadeeq ne yace. " Zata gaza ɗauka Baffa zuciyarta me rauni ce..." Tsaye ya miƙe don kar suga abinda ke son ciko idanunsa yace. "Dole zata iya ɗauka mana, domin duk tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa kan doka, Ta san da ba zata iya ɗaukan bane har ta murzawa idanunta toka tayi fatali da dokokin ubangiji da kuma Mijin ta?..." Yadda Baffan ke maganar kaɗai ya isa tabbatar maka da cewar baƙin cikin da tashi zuciyar take ciki me girma ne, Meenerl dake kwance daga saman gadon marasa lafiyar kuwa, wani lumshe idanunta a hankali tayi , wasu zafafan hawayen data bawa damar sakkowa ya shiga sauka saman fuskarta, wani iri nauyi zuciyarta ke sake ɗauka da fitinannen ciwo, wani irin abu take ji me zafi da raɗaɗi, ji take dama ace ana iya meda hannun agogo baya da ta dawo da hasalin rayuwarta ta da can bayan nan, sedai lokaci ya gama nasa alƙalancin sedai batun tuba da miƙa lamura ga ALLAH kuma. Fitar Baffan ne ya saka kukan da take ta ƙoƙarin dannewa kufce mata, tana kuwa fasa shi da azabar da yake taho mata daga cikin ƙarƙashin tsakiyar ƙirjinta, saurin dawowa gare ta Shareefah tayi, tana tallafar kan yayar nata tare da soma karanto duk adda'ar da tazo bakinta, don ta sama sassaucin abinda ke zuciyarta ya ragu, Cikin iko da buwayar Ubangiji kuwa se gashi adda'o'in na ratsa ta sosai tare da sanyaya zuciyarta. Kafin cikin natsastsiyar kalama da natsuwa Shareefah ta ce... "Ki sani! Babu wani abinda zai faru sai da izinin ALLAH mai girma Yaya!, Tabbas na yarda da ƙaddara kuma koda ace kina yawo da mafi girma a cikin sutturu ne tin da ya ƙaddara hakan a cikin kaddararki seta same ki, sedai sanadin kawai da kika faɗa tarkonsa na shaidan, wajen rashin ƙarasa suturta jikinki da rashin daraja ƙa'idojin da Ubangiji ya gindaya a cikin rayuwar aure. Kiyi hakuri Yaya Meenal, kiyi hakuri ki kuma yi joining wannan ƙaddarar,ki kuma roki ALLAH gafarsa ze kafarta miki, domin kuwa shi ya ce. idan wani lokaci mai tsanani da wahala ya zo a cikin rayuwarku, kafin komai ku sani cewa ALLAH yana da manufa da dalilinsa na zuwan wannan al'amarin dake tare daku, kuma ku tuna cewa na ɗan ƙanƙanin lokaci ne abin zai zo ya wuce ɗin, tamkar ba'a taɓa yin saba.... Yaya Meenal I know da zan ci gaba da ce miki wani abu, domin duk kalmomin da zanyi amfani dasu kin fini saninsu, I know kuma bana da kalmomin da zan baki baki wajen sanyaya zuciyarki a wannan lokacin!, Kamar yanda babu wanda zai iya kashe wutar da ke balbala acikin Rai da Ruhinki sabo da But trust me, I can imagine your pain akan kaina, amma kuma babbar gudun mawar da zan baki a matsayina na Ƴar uwar da kika kasance Yaya kuma Uwa a gareni shi ne, kawai zance ki dage da haƙuri da kuma dannar zuciyarki da fawwalama ALLAH duka lamuranki. In sha ALLAHU Lokacin da baki tsammani ba, Zai sauya miki damuwarki zuwa farin ciki mara iyaka. Tamkar yadda yake juya dare izuwa rana....." Kukan dake ƙoƙarin kufce mata ta danne tana sake tallafar Yayar tata da take jin ta tamkar uwa a gare ta, Don haka cikin wata irin muryan kwantar da hankali ta ci gaba da faɗin. "Ina son ki rungumi duka ƙaddarorinki da zuciya ɗaya, Ki bar komai ga ALLAH domin kuwa shike maganin kowacce irin damuwa da matsala, kana ki yawaita adda'a ki kuma tsarkake imaninki tare da komawa gare shi baki ɗaya, kiyi kokarin cire komai daga ranki duk da nasan da wuya,amma ina son daga wannan rana me kama da haka ki dena ɓata hawayenki akan kaɗɗararki dama ƙalubalan da zakici gaba da riska a gaba , kar kiyi kuka ki dena kuka Yaya domin kuwa ba'a ma ƙaddara kuka bata waje tayi aikinta ake, don kuka baya maganinta sedai karfin adda'a kan rage kaifinta, Bama da uwar da zata tsaya mana wajen dannar zuciyoyinmu, sedai muna da ALLAH shi tsai tsaya mana kin ji Yayata....." Takai ƙarshen maganar nata suna rungume juna su sake sakin wani sabon kukan a tare, sedai na Shareefah'n yafi nata tasirintuwa, don ita nata se ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukan nata,sautin da bashi da wani ƙarfi ko ƙarsashi da amo cikinsa ko misƙala zarratin,saboda rashin wadatacciyar garkuwar jikin da zata bata wannan damar,uwa uba kuma tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba,ta zubda hawayen har sai data daina sanin lokacin tahowarsu, har sai da idanunta suka fara gani dishi dishi tin a daren na jiya data raba kuka da kowa da numfashinta, wanda har daga karshe ta yanke tsammani daga samun dukkan ɗauki,ta kuma gama sallamawa ƙaddarar rayuwarta sedai a yanzun ƙanwar nata ta bata kwarin gwiwa sabuwa. Motsin taɓa ƙofar da akai ne ya saka ta buɗe jajayen idanunta, duk da cewar a hankali ne aka buɗe ƙofar ɗakin, haka nan zuciyarta ta bata tabbacin shi ne, Ya Ahmad ɗin tane, da jiya jiyar nan ta gama wulaƙanta aurensa dashi, amma yanzun wa gari ya waya?, ita ce, ita ce ta sani har gaban abada ita ɗin nan dai ce a ruwa. A hankali ta ɗaga kanta tana kuma sauƙe dubanta ga bakin ƙofar shigowar,duk da kuwa irin yadda gabanta ke mummunar faɗuwa wahala da iftila'in daya gama afkama rayuwarta me gigita hankalin taya gama riskarta, kai tsaye kuwa idonta ya faɗa cikin nashin. Shi da ita suka zubama juna ido kamar yau ce ranar farko da suka fara ganin juna,kowannensu da kalar kallon da yakema ɗan uwansa. Wanda a kallon farkon daya mata yana kallar yadda tashin hankali ya gama dabaybaye kyakkyawar fuskar nan tata, da har yanzun wani irin kyau na daban me matuƙar tasiri da fusgar hankalin da ya gagara gushewa shimfide saman fuskar tata,saidai kana kallonta kasan ba haka take ba,abubuwa da yawa sun canza wanna fuskar, tsakanin daren na jiya zuwa yau komai ya sanja lissafin fuskar nata, idanuwansa na a kanta ya fara takowa Mahaifinta na tako masa baya, raunin kalaman da Shareefah tayi na kamasu su duka, don suna tsaye sun kuma gama saurarar komai daga gare ta, wannan abu shi ya sanyaya duka jikkuna da zuciyoyinsu, kamar yadda suka gama ruguwa taurin zuciyar Ya Sadeeq ma anan ɗin, da yake zaune har lokacin ya gaza koda wanne kalan motsi, tabbas kalaman Shareefah haka suke kuma suna akan daidai, lallai duk abinda ya faru da bawa tin daga Rabbil Izzati ne yake, Koda ace kai ne ka fi kowa kare martabar da kimarka, idan har ALLAH ya rubuta hakan to kuwa se an samu ɓata garin da dolen dole su bata maka rayuwar a irin wannan gabar!, se dai kamar kuma yacce tace ɗin ne still, son zuciya da rudin zamani kan zama sila ko kuma ja gaba wajen bama shaidan damar afkuwar hakan. A wani kalan sanyin jiki dana zuciya ya ƙaraso gar gaban gadon yana kaiwa zaune inda Shareefah tayi gaggawar tashi ta bashi,ya zauna sosai yana fuskantarta haɗi da zuba masa idanunsa da suka janye sosai shima... Ganin hakan ya saka su Baffa fita dukansu amma kuma suna daga bakin ƙofar room ɗin, "Me kika yi haka ameenatou?, wanne kalar fentine ne haka kika gogama rayuwar aurenmu uyhmmmm?, kawai don biyema rudin duniya da zamani kika zaɓa lalata rayuwarmu mu duka biyun, da kuma ruguza yardar dake tsakaninmu!. Kina jin irin yadda nake ji kuwa a cikin ƙirjina?, ashe dama haka ƙaddarar take bata da sauƙi irin haka?" Ya ɗinke maganar nashi ne saboda rawar da bakinsa ya fara da haƙoransa, zuba masa jajayen idanunta dake a rine tayi kafin ta lumsh su, ragowar hawayen da basu samu damar zubowa ba suka gangaro mata kana ta buɗesu tarwai a kansa tace.... "Bana da tsumi ba kuma ni da dabarar hana faruwar hakan Ya Ahmad, Kamar yadda ban isa na fidda kaina daga gare kaba, nasan zuwa yanzun ka tsaneni ne Ya Ahmad, kayi hakuri kayi hakuri kayi ta yin haƙuri da bama zuciyarka salama, Ubangiji ya maka mace ta garin data fini nagarta!, da halaye masu kyau fiye dani, zanyi nesa sosai da rayuwarka kamar yacce kaima nasan za kayi nesa da tawa rayuwar!!!, Sedai ka tayani adda'ar koda ace bana raye, to ina son ka tayani da Adda'ar hana duk wanda yamin haka nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa,Ya kuma girbe fiye da abinda ya shuka min.... Saurin rufe bakinta yayi da hannunsa yana jijjiga mata kai, kafin Yace... "Ina sonki Meenoh!, bazan iya rabuwa dake ba, kuma banajin zan daina SO da ƘAUNARKI don wata ƙaddara ta gilma tsakaninmu, zan ci gaba da zama dake ameenatou!, kuma bana son wannan maganar ta fita ko ina daga mu se su Baffa, Sedai se kin yi hakuri kin kuma jurema zaman, don kuwa se na gama jinyar zuciya da kaina kafin komai ya dawo mana dai-dai gwargwado iyaka abinda naga naga zan iya, ba zan rabu dake ba INA SONKI ina ƘAUNARKI Meenal........" Sosai ta buɗe ido da baki da hanci tana kallarsa da wani kalan yanayi, kafin bakinta na rawa ta ce... "Har yanzun kana jin zaka iya ci gaba da zaman aure dani Ya Ahmad?, bayan na gama take aurenka dake kaina, wasu kuma sun gama wulaƙanta martaba da yardar dake cikin auren namu amma har yanzun kake jin zaka iya zaman auren dani?...." Kansa yake ɗan jujjuya mata kafin Yace... "Kifar taso da abinda ya riga da ya gama faruwa, ki ɗauka hakan a wani issue ne na daban daya shafi interest nawa da kuma naki kawai, ki dena sako ko danganto wani a ciki domin zuciyata ba zata ci gaba da jure hakan ba...." Wani kuka ta saka tana ɗamke hannunsa dake cikin nata take furta. "Na gode!, na gode ALLAH, Alhamdulillah ko yanzun ALLAH ya ɗauki raina na gode masa...." Rumgumeta kawai yayi domin bazai iya ci gaba da saurarar kukan taba, daga nan Dr pooja ta shigo ta sake dudduba jikinta ta haɗa mata magani ta basu sallamar da ita ce da kanta tace a basu, Sosai Baffa da Ya Sadeeq suka ta yima Ahmad ɗin godiya don duk dama zullumin hukuncin da zai yanke a kanta suke da tsoron kar ace ya rabu da ita, Se da suka musu rakiya har gida kana Baffa ya sake jaddada godiyarsa ga Ahmad kana suka bar gidan.... Bayan tafiyar su Baffan sun jima zaune a wurin zaman kurame kafin tayi kundin balar sake nemar yafiyarsa gare ta, Komai bai ce mata sema tashi da yayi ya bar mata parlour ya shige bedroom nashi, don kansa wani bala'in ciwo yake masa, koda ta bishi taji ya rufe ɗakin kanta kawai ta jinginar da jikin ƙofar tayi kukanta me isarta a wurin, kafin taja ƙafafunta ta nufi bedroom nata, kwanciya tayi zuciyarta na wani kalan mata bugu da tafasa, ƙarfe biyu bayan tayi Sallah ta fito tayi girkin rana, ɗakinsa ta leƙa daga a rufe ta woje alamar ya fita kenan, kaɗan ta ɗan cakali abincin itama ta ture ta koma tayi wanka ta ɗauki Alqur'ani tayi karatu, har kusan yamma sosai tana nan zaunen kafin ta tashi taje ta meda na dare, bayan ta kammala tayi sallar magrib, ta sake karatun Alqur'ani tsakanin magrib da isha'a, wajajen tara taji alamun shihowansa gidan, tayi hanzarin fitowa jikinta da himar har ƙasa, daidai lokacin yake ƙarasa bayyana a cikin parlourn, sannu da zuwa ta masa ya amsata da hannunsa yana ƙoƙarin wucewa, cewa ta mishi ga abincinsa yace ya gode amma ya koshi, bata ji daɗi ba amma haka ta danne ta kyale shi, kana ta mara masa baya zuwa ɗakinsa, Sedai ya dakatar da ita ta hanyar ce da ita tayi haƙuri yana bukatar balance ne sosai, don haka ta dawo parlourn jikinta a matuƙar sanyaye, seda dare ya tsala sosai kana tabar parlourn, koda ta shige bedroom nata bata kwanta ba Alwala tayi ta fuskanta alƙibla, ta fara jero sallolin da bata san iyakar su ba, har aka ƙira asuba, A hankali ya turo ɗakin nata don tada ta tayi sallar subhi ɗin, Sedai ganinta a zaunen da yayi ne ya saka shi fita be ƙaraso ba, wajan shida ta fita ta ɗora musu brekfast. Lafiyayyar Doya da kyau ta musu, da lemun kwakwa, a gurguje taje tayo wanka kana tazo ta zauna cikin parlourn tana jirar fitowar sa, babu jimawa kuwa se gashi ya fito da brifcase nashi a hannunsa ta fita aiki, saurin miƙewa tayi tana isa gare shi yay hanzarin janyewa ya koma gefe guda, kanta ta sunkuyar ƙasa ta gaida sa, amsata yayi sama ² tace dashi ga breakfast yace da ita ya gode zeci a woje. Kusan a wannan karon kam daskarewa a tsaye tayi, shin me yake nufi ne wai, ko dama shi ne haƙurin da ya ce se tayi? In sha ALLAHU zata yi za kuma ta jure da Ikon ALLAH... Tin tana kallar kamar zata iya jurema yanayin, har hakan ya fara fin ƙarfin tunani da kuma kanta, don takai ta kawo ko zama ya dena yi inda ta zaune, tayi kukan tayi adda'ar amma duk a banza, abinci kuwa dama tuni ta dena yi dashi, don ko tayi Sedai ta tayin asara tana bama getman ya rabama almajirai, abinda ya sake bata mamaki kuma shi ne da sati ɗaya da faruwan abun ya zo mata da zancen zata iya ci gaba da aikinta tace ta dena ta haƙura har gaban abada, komai daga haka be sake ce mata yaci gaba da rayuwarsa, har takai ta kawo gidan ma yanzun kafin ta tashi ya fita, lokacin da zai dawo kuma tayi bacci, inda sosai hakan ke damunta, har take jin ƙara kawai ya rabu da ita idan har hakan shi ne mafi alkhairinta, saboda da wannan matsalar nasu har Shareefah seda ta tuntuɓa da lamarin, kai tsaye kuma tace da ita ta ƙara hakuri akan wanda take yi, In sha ALLAHU komai zai wuce, gama hucewar ne be yiba. Tin Dr pooja na ƙirar ta har ta haƙura, inda daga ƙarshe take jin kyakkyawan labarin musluntar Dr pooja ɗin, wacce ta musulunta a hannun Baffansu a masallacin ƙofar gidansu, a yanzun haka tana amsa sunan AYSHA ne, tayi murna sosai da jin lamarin na musuluntar da tayi, Ta inda take sake godema ALLAH ma shi ne da bata da komai, idan kuma ta tsaya ta tsai da ranta rashin samun cikin da batayi ba a tin farkon Aurensu har zuwa yanzun kan damunta, se dai shima ta barma ALLAH lamarinta, haka sukaci gaba da gudanar da rayuwar Aurensu, ba tare data sake fuskantar kowa da matsalar ta ba, har kimanin 2 Months, gashi ma har suna kokarin shiga na uku... Masu iya magana sukan ce a duk lokacin da wani abu ya tunkaro ɗan Adam yana yi masa barazana da rayuwarsa, sai yaga kamar duk duniya babu wanda ya kai shi shiga tsananin rayuwa. Har takan kai wasu ƙarancin imanin fara fafutar nemarwa kansu mafita ta kowacce siga ce kuwa domin kawar da ita wannan matsalar da yake fuskanta. Kamar yadda ya kasance a cikin rayuwar Meenal a ƴan tsakan kanin lokutan da suke wucewa a cikin rayuwar aurenta da Ahmad. Lallai ta sake yarda da wannan maganar da ake yawan cewa. Ciwon da ya addabi hannu idanu yake hanawa bacci. Idan ido bai yi bacci ba to lallai dukkan jiki ba zai huta ba. Jikin da rashin hutu ya yiwa sarƙa kuwa yana tattare da ƙarantar kuzarin kare kansa daga bullowar wasu cututtukan ne, Kamar yacce sannu a sannu wani irin ciwon da bata san ko ainihin na minene ba ke famar wajiga rayuwarta, Ta kuma sake yarda da ake cewa idan bamu magance ciwon hannun ba, da sannu sannu shi dai wannan ciwon zai iya kama ragowar sassan jiki ko kuma ya bayar da ƙofar samuwar cutar da tafi ta hannu. Sannu a sannu rayuwarta ke ci gaba da gudana cikin kunci a gidan Ahmad, ga ciwon dake ƙoƙarin kaita ƙasa amma tana gwada jarumtarta akan hakan, har tana daukar hanyar wata guda kenan da wannan jinyar, wanda a zahiri na gaskiya ba haka hasalin lissafin yake ba, wannan jinyar alamu ne bayyanuwar cikin haihuwa a jikinta, sedai tsananin kunci da damuwar da take ciki be saka ta fuskanta hakan ba, ko daga yanayin sanje sanjen da take samuwa daga wasu sassa na halittar jikinta, se dai idan aka ce tashin hankali to anan nufin gaba da komai kenan, don babu cikakkiyar nutsuwar da ya kamaci ace ta tsaya duba ko tantance yanayin da take a ciki ba... Ranar da ba zata taɓa mancewa da ita ba a cikin rayuwarta itace ranar wata LAHADI, ranar ta tashi ne kamar ba ta kai labari ba, gaba ɗaya tin daga kamo daren ranar har kamo la'asar ɗin ranar haka ta wuni a kwance ko ruwa kasa zama a bakinta yayi, tana daga kwancen a yadda take ta fara ƙoƙari da yunƙurin miƙewa, da shigowar Ahmad sassan nata da rabon daya shigo shi har ta manta, gaba ɗaya ya gama fitar da ita daga cikin rayuwarsa tun faruwar wancan lamarin, ko zama kusa dashi be sake bari tayi ba. Kin kallar inda take kamar ko da yaushe, kamar yaga dogon zunubin da ze iya kifewa koya halakar dashi, haka ya dubeta yace tayi maza ya shirya ta fito yana jiranta a mota, tambayarsa tayi lafiya ina kuma zai kaita, wayarta yace ta duba Dr pooja (AISHA) tayi ta ƙiranta amma ta gaza taƙi amsawa, ƙoƙarin komawa kwancen data yunƙura ta tashi take, tana ce dashi..... "Babu inda zani Ahmad!, ai na faɗa mata bana jin daɗi ne, ko kuwa duk Dactor's ɗin dake cikin asibitin basu isa ba se lallai dole ni naje???, Haba Ahmad da wanne kake son inji, na baka hakuri kaki ka haƙura ka fita a cikin rayuwata, ka dena sakewa dani ka dena kusantata, komai daɗa lalacewa yake, memakon ace samun sassauci nake, Bayan kuma na baka hakuri na baka hakuri, don girman kayi hakuri mana..." Tsaiwarsa ya gyara yana fuskantar da kyau yace. "Wanene ya gaya miki ban haƙuraba?, Idan da ban haƙura ba da tin tuni kin jima da tafiya gida!, kinga yanzun dai wannan a matsayin umarni da kuma temakon rai zakiya, kasancewar weekend na babu yawaitar manyan Dactor's duk se ƙananu shi yasa suka biyo ta hannu nama, Dr Bilal ne yamin waya don shi ashe ma baya 9j ɗin ne......... Da kyar ta yunƙura tana shigewa bathroom, babu jimawa ta fito babu laifi kuwa taji ƙarfin jikinta sosai, don haka ta zira doguwar hijjabarta har ƙasa ta fito ta same shi cikin motarsa. Karatun Afid muhd taj ya saka musu, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa asibitin, tin daga yanayin tsaron da aka bama hospital ɗin ta gane cewar lallai wani babban ne ko ɗan gidan wani kusar ne me jinyar, tana isa ta shiga wani room ta sanja kayanta zuwa na surgery, hannunta da handglovs idanunta da glasses fari ta nufi ICU inda nan ne me jinyar yake, Dactor's biyu ne suka mara mata baya ta shiga, tana isa Dr Aysha dake kan majinyancin ta bata hanya, isa tayi gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta ta saka hannu kenan da niyar amsar tiyatar idanunta ya sauƙa akan................... _To fa shin akan mene ko waye idanun Dr Meenerl ya sauƙa?..._ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. Page 9&10 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Wannan fuskar da ba zata taɓa mancewa da ita ba, ita dai wannan fuskar data mata fyaiɗe ta kuma wargaza rayuwar aurenta. Ta raba da da daraja da kuma kimarta, don haka bata san lokacin data saki Scissors ɗin dake hannunta tana zare glass ɗin ta jefar a ƙasa, tare da handglovs da hannunta ke ciki, bakinta ta toshe da duka wannuwanta tana fitowa daga ICU ɗin, idanunta na ƙoƙarin rufewa ko ganin gabanta bata yi, saboda dishi dishin da take kalla, kanta na mata wani kalan masifa da bala'in bugu na ƙafar ya zazzago ƙasa, ganin yadda ta koma lokaci guda ne ya saka nurses biyun dake tare da ita saurin mara mata baya suna tambayar lafiyanta kuwa?, Komai ƙin ce musu tayi har seda ta danga da lafiyayyun kujerun dake center na asibitin, irin na zaman jiran marasa lafiyar nan, babu jimawa sega Dr pooja (Aysha) ta bayyana a wurin tana cewa "Lafiya kuwa Maanol, meke shirin faruwa haka?, naga ma har kin cire uniform ɗin tiyatar?" Idanunta da take suka sanja launi ta ɗago tana kallar pooja ɗin tace, "Sabo da bazan taɓa iyama wannan mugun mutumin tiyatar bane...." Ɗan ja baya Dr pooja ɗin tayi ta ce. "Sabo dame Maanol?" A matuƙar tsawace ta ce. "Sabo da shi ne mugun mutumin daya min fyaiɗ....... Bama ta ƙarasa ba sabo da tsabar yadda ta sarƙe har numfashinta na kamar zebar gangar jikinta... Ga idanunta daya fara ja baya yana lumshewa kamar zata sume... "Subhanallahi Dr Meenerl!!!........... Ɗaya daga cikin Dactor's ɗin ta faɗa don babu wanda ya lura da yanayin sanjawa yanayin nata, don haka Dr pooja tayi saurin tallafota amma tana zamewa ta ma mike ta shige wani daki ta bugo wani kalan masifar kuka na taso mata, akan wani gadon marasa lafiya ta faɗa kukan na kufce mata da tari wanda tarin na fitowa sega jini ya faɗi gudul, zuciyarta ta danne gefenta da hannunta tana ambatar. "Hasbinallu wani'imal wakeen ³" babu jimawa sega Dr pooja ɗin ta sake biyota riƙe da wayarta a hannunta, miƙa mata wayar tayi tana saka ta a handsfree, kamar sauƙar aradu haka taji saukar muryan Ahmad yana bata umarnin Lallai lallai tayi aikin nan, "Wallahi bazan yi ba Ahmad, ba zan iya ba...." Daga ta ɗauka wayar nata tana dokata da ƙasa ta tarwatse kuwa take, zama Dr pooja ɗin tayi tana tallafota ta ce. "Haba Dr Maanol!, kiyi hakuri mana ki fara ceton lafiyarsa, ya kike abu kamar wacce baki san dokokin asibitin nan ba?...". "Wllh babu wanda ya isa ya saka ni yin wannan tiyatar da dai nayi masa ya sama lafiya yaci gaba lalata auren mutane ƙara ya mutu ko babu komai an rage mugun iri." Takai ƙarshen maganar nata zata miƙe, saurin dawo da ita zaune Dr pooja tayi tana sake furta. "Haba mana Maanol yanzun idan ya mutumin nan ya mutu kuma fa?, kin san iyayen yaron nan zasu iya kaimu ƙara kotu fa...." A ɗan zuciya tace "To bazan yi ba, na gaya miki bazan mai aikin nan ba, SO duk ku rabu dani sabo da ba'a dole...." Suna cikin haka sega shigowar wata Matashiyar mata a ɗan burkice, kallo ɗaya zaka mata ka gane cewar bata a hayyaci da nutsuwarta sosai. Har ta zarta su ta dawo tana me furta, "Ina ne inda ɗana yake?...daga yanayin yadda hankalinta yake a tashe ne ya saka su gane cewar uwar yaron ce, don haka kai tsaye nurses ɗin dake gefe da ita tace "Nan ne...." Tana mata nuni da ɗayan ɗakin dake ta bayansu ta glasses,don ɗakin da suke ta fado kai tsaye. Babu jimawa kuma se gata ta dawo tana balbala masifa da bala'in... "Where Are You The Dactor's?, kina ina?, tana ina?, me kike nufi ne?, so kike ki kashe min ɗa ne?, shin dama ba biyanki ake ba?, ko kuwa ba aikin ki bane?, to maza ki tashi yanzun ki duba min yaro!!!, Dan wllh² idan ya mutu sena nuna miki irin ƙarfin ikon da muke dashi a ƙasar nan, kin ji ko maza ki tashi kije ki duba min yaro....." Gaba ɗaya tin da ta fara maganar nata da hargowa take, gaba ɗaya bata cikin hankalinta....... Tsaye Meenal ɗin ta miƙe ta saka idonta cikin tsaƙiyar na matar bayan ta nuna ta da yatsa tace, "Bari kiji in gaya miki indai akan wannan dabbar ɗan naki ne!, to ba zan masa aikin ba!, in kuma anayi doke to bismilla ki sani inyi mu gani?... Wani ihun daya kusan cika harabar wurin tayi tane me furta. "Ƙarya ne!, Ɗan kwara ɗaya ya mutu? Wllh ƙarya ne kuna ina.....ina....ina...ina me asibitin yake?, yana ina Wllh sena sa an ɗaureku idan ɗana ya mutu baku duba shi ba...." Tafiya zata yi tayi hanzarin shan gabanta kamar za tayi kuka kuma ta ce. "Dan ALLAH kiyi hakuri ki duba min shi, shi ɗaya tal ne dani...." Wasu hawayene suka zubo mata tace bazan taɓa iya duba ɗan ki domin shi ne ya ruguza yardar dake cikin aurena, ya lalata min gobe na!, ya kuma illata rayuwata,illar da bata da ƙarshe har gaban abada..... Hannun Meenal ɗin matar ta kama tana shirin kaiwa tsugunne amma Meenal ɗin tayi hanzarin fizge jikinta daga gare ta, cikin ɗaga murya matar tace. "Don ALLAH baiwar ALLAH ki fara duba min yaron nawa!, in yaso in warware ko....ko...kome kike so se...se....se.... Ayi Don ALLAH kiyi hakuri......" Takai ƙarshen maganar nata ta na zubewa ƙasa tana ci gaba da kuka, se ga fitowar wani Dactor nan yana share zufar dake zubo masa, kansa matar tayi da gudu tana me furta, "Ya farfaɗo?, kun duba min shi?..." Kansa yake girgiza mata kafin ya furta. "IS GONE MA'AM, Sedai muce ALLAH ya masa raham..... Ai tin kafin ya ƙarasa maganar nashi ta wani fasa uban ihun da kaff asibitin seda ta ɗauka, ta zube ƙasa tana kururuwar sun kashe mata ɗan ta, kafin kuma kamar wacce aka zabura ta lalubo wayarta kai tsaye ta saka ƙiran numbern mijinta, wanda ƙasar ma, sedai dirarsa ƙasar kenan dake dama yau ɗin ze dawo. Ya a daga wayar ta fasa masa wani uban kuka tace... "Asi....asi....asibitin....4&4 sun kashe mana shi!!!!, sun kashe mana Sameer ɗin mu, sun rabamu dashi, sun ki masa aiki, sunki kulawa dashi har ya mutu Alhaji...." Ɗif ɗif ɗif Haka ƙarar datse ƙirar da aka yi daga ta can ɓangaren me wayar, cikin abinda be gaza 30 minutes ba sega jiniyar ƴan sanda da sojoji sun gama karaɗe ilahirin asibitin, gaba ɗaya jami'ai suka ma hospital ɗin ƙawanya kamar irin za'a kama mutum dubu ɗin nan masu laifi, Cikin mugu mugun tashin Dr Aysha ta ƙira Bilal take sanar masa halin da suke ciki, cikin mugun tashin hankalin da yake jin kaf rayuwarsa be taɓa shiga bane yaji ya shiga a lokacin, gashi baya ƙasar baki ɗaya, ga MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ma da yake da tabbacin shima baya ƙasar, don haka ƙirar Daddyn MAJEED ɗin kai tsaye ya saka yana sanar masa abinda ke faruwa, wanda daidai lokacin da Dr Majeed ke ƙoƙarin cire sau cikin dake ƙafarsa da sauƙarsa kenan a ƙasar, shigowarsa kuma ƙasar kenan, don haka ya dakata cak shi be cire ba shi kuma be saka ba, wani Gwauron numfashi mahaifinsa ya sauƙe yana ce dashi shi kawai ya huta bara yaje yaji da matsalan, kansa ya girgiza masa yana zira sawu cikin nasa, kai tsaye ya sake fita cikin wata lafiyayyar motarsa ta *LAMBORGHINI* wacce ba'a fiye samar kalarta a Nigeria ba, sabo da kuɗin masu nauyin da motar ke lasa, gata wata a wani shafe, wacce ni kuwa AMMEY LAYLERH nace ehhhh lallai yaci a ƙira ta da sunan Lamborghini ɗin,domin kuwa a lamgwamen take, kalarta ma daka kalla kasan ta daban ce ba irin sauran motocin daka saba gani bane, irin su jeef, marcadez benz, toyota highlander, dadai sauransu to wannan ba kalarsu bace.... Tin daga kan yadda yaga an zagaye asibitin nashi ransa ya sake masifan ɓaci na ƙarshen ƙarshe, dan haka da wani mugun gudu ya danna kansa cikin ainihin compound na asibitin, jami'an dake tsare asibitin duk suka yo kansa, sedai bayyanuwarsa akan diga digan sane ya saka su ja baya da alamun mamakinsa me girmar, Me kuma ya kawo *BILLIONAIRE MAJEED DAWOUD ISHAQ?* Wannnan asibitin a cikin irin wannan lokacin?, kallo ɗaya ya musu kai tsaye yana kutsa kansa cikin ainihin ginin asibitin. Dr pooja kai tsaye ya ƙira ya tambayeta tana wanne room ne, cikin rawan jiki ta sanar masa room ɗin da suke, don dama rufe su ne tayi don gaba ɗaya jami'ai sun gama kewaye wurin, don ma sa'ar su ɗaya ƙofar bluetfroof ce, shi ne taimakon da ALLAH ya musu, amma in ba dan haka ba da tuni an gama bandarsu nama ɗanye, gaba ɗaya kusan Dactor's ɗin a ɗakin, don haka ya nufo room ɗin drectly... Bayyanuwarsa ya ankarar da jami'an dake zagaye da wurin, da da farko har sun nufo shi sedai suma ganin nasa ne ya saka su jan birki daga inda suke, shi kuwa Alhaji Kabeee mahaifi ga yaron daya rasu suna can shi da Matarsa Hajiya Madinah suna aikin kuka, sun saka shi a tsaƙiyarsu babu abinda suke se kuka. Da wani spire key yayi using ya buɗe ƙofar, kuma ya barta buɗe in yaso me shigar ma ya shiga. Dr pooja ce ta gama koro masa duk abinda ya faru, har kan case na fyaiɗen da mutumin ya ma Meenal ɗin bata ɓoye ba, don baya da wata mafita kuma a yanzun daya wuce fadar gaskiya. Tana gama bashi jawaban ya wuni juyo ga Meenal ɗin yana zuba mata shegun idanunsa masu kama dana mayu,lolz inji Meenal ba inji LAYLERH..... ★.. "WHO IS SHE'S??" Shine kawai abinda ya fara tambaya kafin komai.... "You..." Wata daga cikin nurse da jikinta ke rawa ta sake nuna masa Meenal ɗin a karo na biyu bayan bayanin da Dr pooja ta masa... .....Fin sama da 5 minutes kenan da suka zuba juna idanu, suna kallon tsaƙiyar idanun junansu babu ko ƙyaftawa, yayinda sauran Dactor's ɗin kowa ke sake shan jinin jikinsa daga yanayin kallon tsana da ƙamar da yake jifarta dashi, da wani kalan ɗan iskan salo ya wani juya mayan oily ayes ɗinsa dake kanta masu matuƙar haske da kyau, kafin ya wani kauda fuskarsa gefe yana mai furzar da wani irin hucin ɗumin da zuciyarsa ta ɗauka, Sai kuma ya sake dawo da idanun nasa a kanta cike da barazana da isa da basarwa ya furta, "WHO ARE YOU?" Yi tayi kamar bama tasan ALLAH yayi ruwansa a wurin ba, sakamakon tsohon miƙin da aka famo mata na daga cikin rayuwarta. Cikin ihu ya wani buga mata tsawa yana sake furta... "Who are you? Tell me who you are, answer me who you are?..." Haka yake ta famar nanatawa don ganin kalan renin hankalin da take son zuwar masa dashi. Ita kuwa a nata ɓangaren duk da yacce yake maganar nashi cikin tsawa be sa ta ɗago ba, bare yasa ran zata tanka mishi. Sema sake riƙe kanta da tashi tana jin duk wasu hargagi da kalamansa ɗaya bayan ɗaya suna mata wani irin amsa kuwwa da tartsatsi a cikin kunnenta, har kan nata na kamar ze rabe gida biyu ko ya fashe mata haka take ji, domin gaba ɗaya komai da take gudun ya dawo mata sabon ne ya dawo mata. Ga wani irin zafin lokaci gudan daya game ilahirin gwaɓɓan jikinta, yana narkar nata da duka wasu gwaɓoɓin dake jikinta da ƙasusuwanta tamkar zasu narke.... "You won't answer me?..." Ya sake faɗa cikin gizago da tsawataccen sauti mai cike da fusatuwa, har yana bugar desk ɗin dake gabansa. Wanda ya sakata miƙewa tsaye tana sauƙema fuskarsa zazzafen marin da yazo masa a matuƙar bazatar da ya saka kowa rufe bakinsa dake wurin, musamman ma Dr pooja da tafi kowa dake wurin sanin irin ƙarfn iko da matsayin da yake da. Jikinta wani irin rawar zafin dake cigaba da ratsata tun daga saman kai har yatsun ƙafafunta, duk da yanayin da take ciki da kuma yadda jikinta ke fitar da wani kalan hucin masifar zafi seda ta bude lips nata, cikin wata irin dakiya da jarumtar da ta aro ma kanta ta shiga nuna shi da hannu tace.... "Idan baka san daraja da martabar mace ba to lallai kayi gaggawar zuwa ka koyo!, Kai waye da akan wannan dabbar mutumin har kaka cira min sauti?, Ba mace ba ce ta haife ka?, ko kuwa baka da ƴan uwa Matan ne?, yanzun idan da ƙanwar kace a cikin irin wannan halin da nake ciki zaka mata haka? Uyhmmmm zaka tambaye ta akan me yasa taƙi duba mutumin daya wulaƙanta mata rayuwa, Ni nasan daraja da kuma mutumcin kaina, wannan ma na baka warning ne don gaba ka kiyaye...." Tin da ta fara maganar a karo na farko kenan daya wani kauda kansa gefe guda. Kafin kuma ya wani ɗan yamutse fuska da ɗaureta yana maida hankalinsa a kan sauran Dactor's ɗin da sukai jugum-jugum suna kallar ikon ALLAH. Se kuma ya sake ɗauke kansa daga kallonsu ya sake dawo da kansa gare ta, kafin yayi taku ɗaya ana biyu ya wani tsaya nesa da ita yana wani huhhura hanci sama. Se kuma ya wani kaɗa yatsun hannunsa biyu ya ce. "Da kyau! ai ban san kin iya wa'azi har haka ba, da tuni na yi magana an baki loud speaker sai ki faɗawa jakuna irin ki cewar zaki shelanta musu kin iya wa'azi....amma ba *ABDOUL-MAJEED DAWOUD ISHAQ BAAAA...* Domin shi tin kafin a san za'a yi halittar ki a cikin duniyar ya gama sanin DARAJAR MACE da kuma kimarta, Amma ba wai wake wake wata ba, Duk inda aka ce MACE, to ana nufin kamila wacce ta gama sanin DARAJA da KIMAR kanta, ta hanyar suturta jiki da kare martabar addinin Musulunci, da bin duk yacce tsarin Addininta ya gama shar'anta mata wannan ita ce MACE, ba wa sauran dabbobi irin ki masu fakewa a cikin rigar musulunci suna cin dunduniyarsa ba!!!...." Bibbiyu idanunta suka fara gani, saboda wata ƴar banzar juwar da taji tana nemar kai ta kasa, wata shiryayyar ciwon zuciya kuma na nemar illata rayuwarta ta raba da numfashi da gangar jikinta. Goshinta ta dafe idanunta na ci gaba da lumshewa duk yacce take son sake gasa da yaɓamar wata baƙar maganar amma tunanin ta be rinjayi hakan ba. Se ma tafiya da tayi luuu baya zata faɗi, Zaro ido Dr pooja tayi tana isa gabanta da sauri ta tarota jikinta tana ɗan dukan fuskarta tana me furta "Are you Okay kuwa Maanol?" Cikin fusgar numfashi da wahala ta buɗe bakinta dake karkarwa tace. "No...no I'm feeling fine is an Fever headache headache headache..... Haka taci gaba da ambatar headache ɗin idanunta na sake lumshewar, "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN ³ Sorry let Me tell for Husband" tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa tsaye don ɗauko wayar Meenal ɗin ta ƙira mijinta, amma se ta saka hannunta ta riƙo hannun pooja ɗin tana ɗan girgiza mata kai, kafin cikin ƙarfin hali ta tattaro jarumta ta ce "No I don't call him. Leave me alone.Pleaseeee......." wani numfashi mara sauti ya fita daga bakinta taja ijiyar zuciya shikenan.... Daidai nan kuma jami'an da MAJEED ɗin daya jima da fita ya basu damar shiga suka faɗo room ɗin, Idon Hajiya Madina akan Meenal da bata motsi ya fara sauƙa, don haka cikin ihu tace su ɗauke ta gata nan. Ita ce ta kashe musu Ɗa, duk yacce Dr pooja ke basu bakin akan su barta su ƙyaleta amma bata numfashin itama ƙiyawa sukai, kattan majiya ƙarfin jami'ai biyu su kayi kanta da niyar ɗauka amma uwar tsawar da aka daka musu ta dakatar dasu, shi ne daya dawo ɗaukan car key nashi ya tarar mazan na shirin daukarta ya dakatar dasu ta hanyar buga musu tsawar da ba iyaka jami'an ta razanar ba har da sauran jama'ar wurin. "All of you get out of here. I don't want to see anyone like you in my hospital again..." Wannan tsawar daya sake buga musu ne ya saka su fara zare jiki ɗaya bayan ɗaya, kafin ya taka a hankali zuwa inda take kwance jikin pooja ya zari car key nashi da cikinta ya fice. Se da yakai daf da ƙofan fitan ya ce. "Follow her" yana ƙarasa ficewar kai tsaye. Gadon marasa lafiya Dr pooja tare da wata nurses suka ɗora ta suna fita da ita zuwa ɗakin da tasan can ya nufa, sedai ga tarin mamakinta baya nan ɗin kuma, duk inda ta san zata ganshi bata gan shin ba, dole ta dawo ita da sauran Dactor's suka fara bata taimakon gaggawa. Dr Majeed ɗin kuwa yana fita kai tsaye babban office ɗin sa da sunan DR MAJEED DAWOUD ISHAQ, ke rubuce a jiki ya budeyya shige ya kuma rofo, ta yacce baka isa shiga ko gane yana ciki ba. Yana tsaƙiyar room ɗin wayarsa na fara ringing ta hanyar flashlight ɗin dake motsi yana kunna kanshi da kashewa dan wayan na silent ne, wani zaro wayar yayi a matuƙar fusace zai jifa da ita, sai dai ganin sunan me ƙiran ne ya saka sa saurin amsa wayan ganin Mahaifinsa ne, kunnensa yakai wayar cikin sese ta natsuwa da yanayin sa yana Daddyn nasa sallama cike da girmamawa. Ta can ɓangaren a natse shima mahaifinsan ya amsa yana tambayar sa yacce ake ciki, se da ya fesar da wata iska daga bakinsa kafin yama mahaifin nasa bayanin duk abinda ke faruwa, har zuwa tafiyar da jami'an suka so yi da yarinyar, se da ya sake fesar da wata iskan kana ya ce. "The girl is pregnant..." Yayi maganar wani irin rauni na ziyartarn zuciyarsa, sabo da duk lokacin da zai ga mace mai ciki gani yake kamar zata mutu ne ita ma da Cikin dake jikinta irin AMEENATOU ɗin sa, a duk lokacin da zai ga mace da ciki wani kalan rauni kan zuciyarci zuciyarsa har ya gaza ɓoye shi wannan raunin nasa.... Saurin yanke wayar yayi jin yacce numfashinsa ke fara sama sama, duk yacce kuwa mahaifin nasa keta famar ambatar.. _Majeed kana lafiya² kana lafiya kuwa?_ saboda yasan duk inda yake ba'a daidai nashi yake ba. Bayan ya datse wayar mahaifin nasa ne ya jinginar da kansa da jikin ginin. Yana tuno rayuwar da suka yi da ameenatou ɗin sa cikin SO da ƘAUNAR junansu me tsanani, amma lokaci guda ta tafi ta barsa cikin lokacin da suka fi buƙatarta shi da Ƴarsu AYLA data haifa masa, tana shirin sake haifa musu na biyun ta mutu ita da cikin, ta tafi ta barsu cikin kewar da har yau basu sama wacce ta maye musu gurbin wannan kewar ba, ta barsu da ciwon rashin ta, wanda har yau ba'a sami wacce ta cike musu gurbin wannan ciwon ba. Ta barsu da tsoron da har a yanzun be gama barin su ba. Ta tafi ta barsu da ababuwa da yawan da har basu sama masu basu garkuwa daga waɗan nan ababuwan ba.... Musamman yaga mace da ciki hakan yafi komai daga hankali da tunaninsa. Adda'ar duk da tazo bakinsa ya fara karantowa yana jin lallai zai tsaya mata akan duk abinda ya tunkaro ta, ciki kuwa koda hakan na nufin ze jefa kansa cikin matsala ne. Sabo da kusan duk lokacin da suke zaune da ameenatou ɗin sa takan ce dashi. _ABU AYLA!, a duk lokacin da zaka ga mace me ciki, abar a tausaya mata ce, domin duniyarta tana rabewa zuwa gida biyu ce, ƙafarta ɗaya na duniya, ɗayar kuma na lahira ne, a koda yaushe zata iya mutuwa ko kan cikin ya girma, ko kuma tana gaf da haifesa ta mutu ita da abinda take ƙoƙarin taga ta haife ɗinnn, Ina jin a jikina nima kamar ba zan kai labari ba!, domin kuwa ni kaɗai nake jin abinda nake ji a cikin jikina, idan na mutu abu na farko da zaka fara min, shi ne taimakon masu ciki a duk lokacin da zaka kalle su cikin matsala, abu na farko da zaka Duba a gare su to ni ce!!!, ka ɗauka cewar ni ce ke cikin wannan matsalar, sabo da wasu mazan basa da imani, a daidai gaɓar da ya kamaci ace suna tausayama mace idan tana da ciki, to wasu kuma a daidai ita wannan gaɓar suke samun damar ƙuntata mata saboda da basu ke ɗauke da wannan nauyin ba.... A duk lokacin da zaka ga mace me ciki a cikin matsala kwatankwacin wacce na lissafa maka to ni ce!, Ni ce!!, Ni ceee Abu Ayl....._ Wani kalan ƙara ya saki me tafe da salati yana katse tunanin iyaka haka nan. Don idan yace hannun agogon sa ze dawo dashi baya ababuwan da yawa suna da yawar da jumiri da lokacin ba zasu tsimaya ba... Bedroom ɗin dake office ɗin ya wuce yana sakarma kansa ruwa me sanyi sosai... Tsaye yake ƙarƙashin showern ruwan kuma naci gaba da dukan jiki zuwa kansa, domin ganin abin yake tamkar mafarki ne yake yi, gani kuma yake tamkar idan ya buɗe idanunsa zega a mafarkine ashe hakan ke faruwa. Ameenatou ɗin sa ba rasuwa tayi ba, zata dawo suci gaba da rayuwarsu kamar baya, Ruwan daya taro acikin tafukan hannayensa ya watsa akan kyakkyawar fuskarsa, lokaci ɗaya kuma ya saki wani irin ajiyar zuciya tare dajan dogon numfashi. Gaba ɗaya kuma kwantattun gargasan dake jikinsa na mimmiƙewa... Dafe jikin bangon bayin yayi yana yin wani irin shiru. Wanda shirun da yayi kuma wannan ɗin alamace ta samun nutsuwar gangar jiki da kuma brain ɗin sa, na amsar rashin nata da yayi da hannu bibbiyu domin haka ƙaddararsu ta gama tsara musu ba zasu tsawon rayuwa a tare ba, Kafin ahankali kuma ya janye jikinsa daga gaban classic glass shower ɗin, ruwan da suka shigar masa ido kuma nasa wani abu ciccikowa a cikin idon. Wata nannauyar iska ya fesar daga bakinsa yana nemar kalmar ALHAMDULILLAH ya aza akan laɓɓansa, Jiƙaƙkun kayan jikinsa ya zare yana zarar wani sabon towel ya ɗaura, inda drower'n kasan yake ya nufa da yake da wasu kaya anan ɗin, wasu labcoat sky blue ya saka a natse cikin mutuwar da jikinsa ya gama yi, yana zirawa ya kwanta akan doguwar kujerar office ɗin take wani nannauyar bacci yayi awon gaba dashi, masu cike da mafarkan yarinyar da wannan shi ne gani na biyu daya taɓa mata, da kuma Ameenatou ɗin sa da take ce masa lallai ya kula da ameenatou don ita kaɗai ce macen da ze samu a madadinta.... A wani kalan mugun firgice ya farka sunan ALLAH ɗauke fal a bakinsa, wani gumin tashin hankali na tsatstsafo masa ilahirin gangar jikinsa. Time ya duba yaga bakwai har ta gota,don haka yayi hanzarin miƙewa ya fado bathroom ɗin ya fito ɗaure da alwala. Masjid ya wuce daga nan be dawo ba ya wuce gida..... ★.. Gudu sosai yayi a motar a ganinsa gudun ko shi ne zai rage zafin dake ƙoƙarin faso ƙirjinsa ya fito, saida yayi tafiya mai ɗan nisa kafin yayi parking motar agefen titi, hanunsa dake ɗan rawa ya sanya ya bugi steering motar, tare da furzar da wata iska daga cikin bakinsa me zafi, wata loca dake jikin motar ya jawo haɗe da ciro goran ruwa, ɓalle murfin goran yayi haɗe da kafa goran abakinsa, be ɗauke bakinsa ba har seda ya tabbatar da ya zuƙe ruwan dake cikinta kana ya zare gorar yana jifa da ita, Wani numfashi ya fesar Ahankali nauyin da ƙirjinsa yayi a da na ɗan raguwa, ɗago kansa yayi ya kalli madubin dake cikin motar, da sauri ya kauda kansa gefe saboda kamar gimlawarta ne ya gani, jiyayi zuciyarsa tayi wani irin karyewa har wasu abu na ciko idonsa, kifa kansa yayi ajikin steering motar, baisan ya zaiyi da rayuwarsa ba, haka kuma bai san baƙar ƙaddarar dake son sake kusanto kanta gare shi ba, Bayan Ameenatou yay wani auren. Ya auri Ramlah xiyar shaibah, ƴar hasalin Dubai, ita ma mutuwar tayi da cikin 7 Months a jikinta, ya zo ya auri Fareedah.... Ita ma ta mutu dai wajen haihuwar babu ita babu abin cikin, daga nan ya yafe Aure daga cikin rayuwarsa gaba ɗaya, sabo da be shirya sake fuskantar wani kalubalen ba, duk gudunsa da sauri da taka tsantsan ɗin sa, amma hakan be hana mataye har uku sun mutu a hannunsa ba, kula da zurfafa bincikensa akan hakan amma hakan kuma be sake hana rashin matayensa biyun da ya sake bayan ita ba. Shi yasa a duk lokacin da zai ga mace da ciki kallon wacce ta gama rayuwa yake mata ɗago kansa yayi yana zuba rinannun idanunsa akan jikin steering motar, idanunsa ne suka sakeyin ja kamar an watsa musu garin barkono, Ga tiririn da zuciyarsa keci gaba dayi a cikin rai tunanin sa yana jin bayajin cewa kuma zai iya zama da kowacce mace a cikin duniyarnan, Motar ya kunna yaci gaba da tafiya kai tsaye yana buga hong a babban get ɗin gidan su. Buɗe masa get man yayi shi kuma ya danna hancin motarsa ciki, tamkar me jinya haka ya fito a motan yana tafiya a hankali, A kuma hankalin ya saka zara zaran yatsun hannunsa ya murɗa Handledoor na kofar babban parlourn gidan, yana sanya kansa cikin babban parlourn ta tura kansa ciki. A hankali yake takawa zuwa ainihin ɓangarensa, ya kai ƙafarsa kenan kan stairs ɗin Benensa ya jiyo muryar uwar da tayi sanadiyar kawo shi cikin duniyar. Cak ya dakata yana dedeta yanayinsa kwarai se dai be juyo ma a samar laɓbansa ya furta. "Sannu da gida Ummieh!" Ya ce kawai yana shirin hayewa samar... Sedai ya dakata ne sakamakon muryar abu mafi tausayi da soyuwa a cikin duniyarsa AYLA... Da gudu ta isa gare shi tana rungume ƙafafunsa bayan ta jefar da ƴar Teddy'n dake hannunta ƙasan floor'n. Gaba ɗaya ya shanye duk yanayin dake tare da shi, kafin ya juyo yana rage tsawonsa daidai nata yana sakar mata murmushi yana kama fuskarta yace. "How is your night Baby AYLA?" Wani ɗan jujjuya ido yarinyar tayi kafin takai bakinta ta sumbaci goshinsa ta ce.... "THANKS GOD I'm fine..." Ɗan janye ta baya yayi yana kallar shigar ta, don wannan yana ɗaya daga cikin kamar aikinsa, sabo da lumonia ɗin da take ɗauke da ita. Wata ijiyar zuciya ya sauƙe ganinta sanye da wando da riga na sanyi, da takalmi cover sedai kan babu hula se gashinta dake rito a bayanta irin na uwarta, hannunta ma da safan hannu...... Ɗan murmushi ya mata kafin yace "Babyn Papa tana lafiya?" Ɗiɗɗige tayi tana sake kissing goshinsa ta ce... "Today is not a happy day for me.." Tayi maganar tana wani shagwaɓe fuskarta. Dan zaro idonsa waje yayi yana me cewa. “Ohh Dear Papa what Happen?" "PAPA is this good for you?" Gefen kunnensa ɗaya ya ɗan kama yana me sake cewa. "Ohh to ni kuma ɗan Ummiensa mi ye nayi kuma?". "Ka dawo ka sake tafiya ko kallarka ban yi ba!..." "Ohhh SO sorry na dena cutie " daga nan ya kama hannunta suna hayewa sama. Se da aka ƙira sallan isha'a suka fito tare da ya wuce masjid tare da Daddynsa. Koda ya dawo dinner ma sama sama yayi ya haye sama bayan ya musu sallama, yana isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom, wanka yayi tare da ɗauro alwala kana yafito, dogon wando na bacci ya sanya babu da vest, kwanciya yayi akan makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa yana faɗawa wata duniya ta daban. Bacci barawo gaza ɗaukan sa yayi se daf da asba, amma hakan be sa ya makara sallar ba, yana dawowa ya sake komawa bacci me nauyin da be sama ma daren jiya na sake ɗaukarsa. 10:30am. Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa masu ɗauke da zara zaran gashi asamansu, kai tsaye ganinsa na sauƙa akan agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin, cike da nutsuwar daya samu ya zuro ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, bathroom ya shiga babu jimawa ya fito da alaman wanka ya yo. Tsab ya gama shirya kansa cikin wani lallausan yadi, ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi da kama jiki, combat shoe ya sanya aƙafarsa haɗe da ɗaura agogon Apple a hanunsa na dama, sosai yayi kyau bana wasa ba, ahankali ya isa gaban mirror yana ɗora kyawawan idanunsa ya kalli kansa acikin madubin. shi kansa yasan cewar shi cikakken kyakkyawan Namiji ne mai aji da kuma ɗaukar hankali. Haka ya tsaya sosai gaban madubin yana kallar kansa, Kafin ahankali ya sauƙe idanunsa ƙasa yana nufar wayarsa me ƙirar Galaxy S50 ya jefa cikin aljihun kayan dake jikinsa, yana sa kai ya fice daga cikin ɗakin..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. Page 11&12 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ A ƙasa ya tarar da Ummiensa da ƙanwarsa Ikleemerh, dama AYLA wacce ke lafe jikin Ummiensa. Idanunsa ya lumshe da sake buɗe su akan Ayla ɗin dake jingine da jikin Ummien tana mata rigima, domin bata jin daɗi lumonia ɗin tane ke nemar tashi. Sakamakon hunturun da aka tashi dashi, gashi jiya da dare ba tare da sanin Ummien ba taje ta sheƙama jikinta ruwan sanyi, Shi yasa yau bata wani tashi da kuzarinta da ƙarsashin taba kamar kullum, Shi ne ma yasa ko school bata je ba duk da kasancewar Monday ce yau ɗin. Suna haɗa ido yaji wani irin raunin da ganinta ya sake haifar masa na ƙoƙarin taso mar, Ayla kuwa da ganin Papa ɗin nata ne ya sanya ta a farin ciki ne ta taso da gudu zuwa wurin sa, hannayen sa kawai ya buɗe mata domin ya san mine take shirin yi, tsamm ya rungume Babyn nasa zuciyarsa na masa wani mahaukacin bugu, Jin yadda jikin yarinyar ya saki, ga wani ɗan banzan sanyin da gaba ɗaya jikinta ya ɗauka. "Paapa" haka ta ƙirayi sunan shi cikin maraitacciyar murya.wanda hakan ya sanya Majeed ɗago haɓarta ya zuba idanunsa cikin muryan shirin yin kuka tace. "Paapa na dena wasar ruwan, kuma ma I hate him!, tin da yake sani jinya." Yanda tai maganar a hankali cikin rauni ne yasa kaɗan ya rage zuciyarsa bata fito waje ba, amma ya daure cike da son nuna jarumta yana ƙara ƙanƙameta sosai a cikin jikin sa. Kafin ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya, yana jin gaba ɗaya komai na nemar cinkushe masa. dole ne yana buƙatar ƙara ƙadaice kansa, domin gudun kada iyayen sa su fahimci rauni da kuma halin da yake ciki, zare ta yayi daga jikinsa samm baka isa kai tsaye ka fahimci halin da yake a ciki ba, amma a baɗini da zaka ga irin tarin raunikan dake chunkushe a cikin zuciyarsa, da kuwa tabbas saika tausaya masa. Da wani kallon zallar tausayin ɗan nata Ummeh ta shiga binsa dashi, A cikin zuciyarta tana jin inama ace wani na iya ɗauke damuwar wani, da kuma ciwon wani,da ita kuwa tabbas ita ce uwa ta farkon ta zata fara ɗauke duk tarin abubuwan yaron nata, ba tare da ko shi kansa ya san da hakan ba. Idanunta ne ya ciko da hawayen tausayin ɗan nata. Maganar Ayla ne ya sake katse duk tunaninsu da tace. "Papa shike nan nima zan mutu ne irin na Maama narhhh ko???" Da sauri Majeed ɗin ya rufe mata bakinta shima yana danne nashi bakin da ɗaya hannun sa da yaji kukan shima na dab da subce masa. da sauri Ummiensa ta miƙe daga wurin da take tana faɗawa kitchen itama, Ikleemerh ce tayi ƙarfin halin isa gare ta tana shirin ɗaukarta daga wurin mahaifin nata, dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kansa, rungume kanta yayi sosai yana tunawa da Ameenatou mahaifiyar ta, Wanda yake mata wani irin mahaukacin SO da ƘAUNAR da be taɓa tsammanin zema wata halitta bayan taba. Ɗaukarta tsam yayi yana yin woje da ita bayan ya furta mata. "Ba zaki mutu ba In sha ALLAHU Ummiena...." Dake sunan ummin ameenatou ɗin tace yasa mata, wanda shi kuma da ita ya niyar yima takwarar, amma tace ita dai ya saka sunan ummien, idan ta sake haifa musu wata Babyn ya saka nata sunan amma ummien first kafin ita. Kai tsaye wajen parking manyan motocin gidan ya nufa, wata Black Bentley ya faɗa tana jikinsa yake driving zuwa hospital. Yana zuwa shi da kansa ya wuce da Ayla wani special room ya ɗaura mata ruwa, bayan wani lokaci ya cire mata ya ƙira wani Dr Saif ya kwanta yace ya zuƙi jininsa ya ƙarama Ayla da nata yayi ƙasa sosai, ana dibar jinin nasa ya miƙe zaune tare da ziro ƙafafunsa ƙasa ze sauƙa, saurin dakatar dashi Dr Saif ɗin yayi yana me furta. "Zaka ɗan huta ne Sir. Domin akwai buƙatan ka huta ɗin, zan maka allura ne.... Da hannunsa yayi amfani wajen dakatar da Dr ɗin daga dogon sharhin da yake koro masa, kafin cikin zurfin murya yace. "Bana buƙata...." Daga haka ya fice bayan ya ƙira pooja yace ta kula da Ayla. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa, zuciyarsa na masa bugun da bai san kona minene shi ba, Sedai yana zuwa yaga bata nan, ya jima yana ta dube duben inda zai ganta amma be gani ba, duk da zurfin cikinsa amma se da ya magantu ya tambaya wata nurses, "Mr MAANAL FA?...." Da farko da nurses ɗin daburcewa tayi don bata san wacece kuma Mr MAANAL ɗin ba, har seda ya dafe goshinsa kana yace... "Dr ameenatou...." Jikinta na ɗan rawa da bakinta tace. "Mijinta ya zo ya tafi da ita...." Rumtse idonsa yayi yana rike kansa dake ɗan sara masa yana soma haɗa hanya ya fice a room ɗin. Drectly office nashi ya wuce yana zubewa saman doguwar kujera, Kai tsaye wani hawaltaccen bacci nayin gaba da shi, masu cike da kalan wasu surkullen mafarkai marasa kan gado.... Wajajen sha biyu ya farka a firgice sakamakon wani irin mummunan famarkin da yayi, Rumtse Idanunsa yayi gamm tare da ƙara ƙankame jikinsa wuri guda,a ƙalla ya ɗauki sama da minti uku zuwa biyar kafin ya saki ajiyar zuciya. Amma baiyi motsin kirkiba balle kuma ya iya furta wata kalma. Sosai mafarkin ya firgita shi, in banda tsuma babu abinda jikinsa ke faman yi sai uban zufar dake yanko masa ta ko ta ina. Idanunsa da suke a lumshe ya ware tare da ƙurama wuri guda ido tamkar Anan ne za'a faɗa masa fassarar mafarkin da yai. Kafin ahankali ya riƙe kansa da hannuwansa biyu da yake jin tabbas yana gaf da samun matsala, indai har zaici gaba da shiga irin wannan attack ɗin. kwanciya yayi daga jikin sofar don gani yake daya koma ɗin mafarkin da yai zai kuma maimatuwa ne. "Ya Rabb" ya faɗa yana ci gaba da adda'o'i cikin ransa... Ya dau lokaci zaune a hakan kafin ƙarar shigowar ƙira cikin wayar nasa ya sanya shi buɗe idonsa da suka gama galabaituwa sosai, Ahankali ya janyo wayar tare da shafa screen nata, take kyakkyawar Pics na Ayla ya bayyana. ganin sunan Dr Bilal ne ya sanya shi ɗaukan wayan ba tare da yace komai ba yayi shiru. Kamar da 3 minutes ya janye wayar daga kunnen bayan ya furta. "Karka dawo ka tabbata a airport ɗin indai se nazo ɗaukar kane...." daga nan ya shige bathroom babu jimawa ya fito ɗauke da alwala, kai tsaye yana fita zuwa masallacin da ake daf da shiga sallar ma. Bayan idar da sallar ya nufa ɗakin da ya kwantar da Ayla, yana tafe yana duba Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa a nutse, don ƙa'idar sace yin komi akan loƙaci tamkar yanda ya gama gindayama kansa, don aganinsa bashi da loƙacin ɓatawa lokaci lokacinsa, komi yana yinsa ne akan loƙacinsa ba tare da wani ya shiga cikin woni ba, donshi mutum ne mai tsananin bin kowacce ka'ida acikin dukka lamuransa da taka tsantsan, kai tsaye har an zare mata jinin da aka sa mata an gyara ta harda wanka, ɗaukanta kawai yayi bayan ya furta ma Dr pooja ɗin "Thanks!" A samar lips nashi ya fice da ita, be ko bi ta kan office nashi ba ya wuce wurin motarsa. Seda ya fara kwantar da ita dake bacci take har yanzun be gama sakin taba, ya zaga ze shiga driver sit kenan sega Bilal nan ya nufo wurin yana masa tsiya, "Banza da wani bauɗaɗɗen halinsa, da baka ɗauko ni ba gani na kawo kaina se ka mutu...." Ko kallar inda yake bai yi ba ya faɗa cikin motar yana mata reverse yabar wurin. Kansa kawai Dr Bilal ɗin ya girgiza a ransa yana cewa. _ALLAH ya taro ka ABDOUL-MAJEED...._ daga nan yayi cikin asibitin..... ★.. Tun da ya ɗauko ta daga Asibitin ta rufe kanta a ɗaki take kuka, kuka irin wanda ke gasa da soya zuciyar me yin sa, kukan baƙin cewa wai ita AMEENEERH SHEHU USMAN yau ƙaddara ta tsara mata ke ɗauke da ciki!, cikin wanda ya mata fyaiɗe tin da ganan watan cikin huɗu da kwana biyar ɗin da abin ya faru, ta gwada paisoning ɗin kanta yafi sau uku, idan ta tuna ko ta mutu bawai ta huta ko ta tsira bane, Wannan dalilin yasa ta gama tsarama kanta za ta tsaya ta fuskanta rayuwar, tayi gwagwarmaya ta jure ta daure ta cinye duk wani maɗacin da duniyar da abinda ke cikinta zata basu, ta gode ALLAH da tin da abin ya faru ko sau ɗaya Ahmad ɗin be taɓa koda kwatankwacin kusantarta bane, Idan kuma ta tuna cewar zasu rabu ne a duk lokacin da cikin jikinta ze bayyana tana jin kamar ba zata iya jurema hakan ba. Ahmad ɗin da tunda ta rufe kan nata yake ta famar Safa da Marwa kamo ɗakinta kamo ɗakinsa, yana cewa ta buɗe masa don ALLAH!, ta buɗe ze yafe mata komai, ze dawo suci gaba da gudanar da rayuwarsu irin ta baya, ze manta komai, ze shafe komai kamar komai ɗin kuwa be taɓa faruwa ba. A lokacin da maganganun nasa ke dukar cikin kofofin kunnenta kuwa kukanta tsananta yake, tana jin ta gama yafe kanta ta kuma haramta daga gare shi, yin Duniyar yayi ta buɗe masa amma ta ƙi ya, Dole ya kira Ya Sadeeq yazo har gidan amma taƙi saurar kowa daga cikinsu, Ina samm bata jin zata iya buɗe musu wannan ƙofar, ko kuwa so suke ta buɗe tace musu ciki ne da ita?, cikin da ba na mijin taba?, haba abin yayi munin da bata jin zata taɓa buɗe musu wannan ƙofar a dai daidai wannan lokacin ɗin.Suna tsaka da wannan danbarwar sega ƙarar jiniyar ƴan sanda nan ta gama karaɗe ilahirin gidan baki ɗaya, wanda jiniyar gaba ɗaya ba ƙaramin tasar hankulansu yayi ba,se dai banda ita. Don jima tayi kamar an yaye nata dala ne bisa kanta, tasan zasu tafi da ita ne bisa mutuwar mutumin da tasan ita ce sanadin hakan. A ruɗe Ya Sadeeq da Ya Ahmad ɗin suka isa ga harabar gidan, Suna zuwa wani baƙi murjejen ɗan sandan da kana kallonsa kasan babu imani tattare da shi yace. "Ina mai laifin kisan take?" Wani kalan mugun shock ne ya ziyarci Ya Sadeeq da bai san da zancen komai ba. Don haka ya duba Inspector ɗin tare da furta. "Ƴallaɓoi ko dai kun yi ɓatan kai ne?" Jajayen idonsa Inspector ɗin ya zaroma Ya Sadeeq ɗin yace. "Ba nan ne gidan AMEENEERH SHEHU USMAN ba?, Matar AHMAD IBRAHIM SHAREEF?" tin da ya kama hasalin cikakken sunanta Ya Sadeeq ɗin ya gama sallama wa, Kafin ya juya ga Ahmad ɗin don yana buƙatan ƙarin haske dangane da maganar kisan da tazo masa a matuƙar bazata kwatsam lokacin guda. A takaice Ahmad ɗin ya bashi labarin abinda ke faruwa daga jiya zuwa yau, har musabbabin ƙiran da ya masa ɗin kuwa. Jikin Ya Sadeeq ɗin ne ya fara wata kalan rawan tashin hankali. Kafin ya kalla Inspector ɗin yace. "Ƴallaɓoi zaku iya tafiya dani, domin wacce kuka zo wurin nata bata da lafiyar da ko fitowa da kanta ba zata iya ba, amma ni yayan tane, zaku iya tafiya dani duk hukuncin daya kama nata a min ciki kuwa koda rataya ce...." "Gani nan da lafiyana Sir!, ni zaku kama domin kuwa ni ce mai laifin!!!..." Haka baki ɗayansu suka tsinkayi muryan Meenal ɗin data fito da fuskanta duk abin hawaye ya gama bushewa, idanunta tsabar kuka kuwa sun zurma sunyi ciki. Ahmad ne yayi hanzarin shan gabanta yana me furta. "Wa ya baki umarnin ki fito?" Kai tsaye tambayar da ya fara cilla mata kenan, "Sabo da ni aka zo nema!, kuma ko da ace ban fito ɗin ba dole zasu fito dani........" Ta sake faɗi tana ƙoƙarin nufar kwalawan. Kyakkyawar Garkuwa Ahmad ɗin ya bata ta hanyar tare gabanta da yayi daga shirin miƙa kanta ga kwalawan da dake, Zuciyarsa harya fara tafasa yace "Zaki koma ne ko se na saɓa Miki?" Ya sake faɗi daidai janye san da wani police yayi daga gabanta. Ya Sadeeq ne ya iso gabansu yana sake shiga tsaƙiyar police ɗin da ita. Cikin ɗan yanayin fusata yace."Na ce muku da nine wanda zaki tafi ba ita ba amma" Ganin renin hankali da wasa da aikinsu da duka su biyun ke yi ne ya saka Wannan ƙaƙƙarfan police ɗin buga musu tsawa, yana me furta "I like that..." Daga haka yama macen dake tare dasu inkiyar ta kama Meenal ɗin, hakan kuwa akayi ta kamo hannunta tana zira mata Onka. Wani irin rinewa idanun Ahmad yayi zuciyarsa na ƙoƙarin masa bindiga. Kafin ya isa gabanta ya ce. "Abin da kike zaɓa kenan?, kariyar da muke shirin baki kika ture Meenal?, Kika zaɓa tozartamu da ƙasƙantar damu a idon duniya?...." Ya faɗi hawaye na zubo masa. Hannayenta duka biyun dake cikin onkar ta sa tana goge nata kwallar da ya ciko nata idon, kafin cikin ƙarfin gwiwwa da yaƙi ni tace. "Ko da ace ban yi hakan ba bazan taɓa tsira ba Ya Ahmad, dole gaskiya tayi halinta, dole komai ya bayyana, Me bi wannan ita ce zata iya zama magana ta ƙarshe da kai Ya Ahmad, domin kuwa na san koda na fito bayan gaskiyar komai ya gama bayyanuwa doke zaka rabu dani, domin abinda ke ɗauke a jikina da kasancewar sa ɗan duma ko an ɓoye se ya bayyana. Abinda kawai nake buƙata daga gareka shi ne Adda'a da fatan Alkhairi, tare da Adda'ar zaɓin abinda shine mafi Alkhairun mu garemu. Tabbas dukkan ayyuka suna tabbata ne da niyya,kuma Lallai ko wanne mutum yana samun sakamako ne na abinda yayi niyyar, Ubangijii ALLAH yana gani kuma shi ne wanda zai bani kariya, karka ji komai, domin nie a yanzun babu abinda nake jin ɗin kuwa... Face na bayyana gaskiyar abinda yake akwai ciki kuwa harda bayyana cikin dake jikina daya kasance na wannan dabbar ne...." Ji da ganinsa ne suka nema ɗaukewa lokaci guda, me take nufi da cikin jikinta?, tana nufin ciki ne ke ɗauke a cikin cikin nata irin na haihuwar ɗan mutum dai?, me ya sa shi da ita bata taɓa fada masa ba?, me yasa be taɓa lura da hakan ba da suna zaune gida guda har cikin yayi wannan watannin a jikinta be sani?, Haba No wonder ranar yayi ta kallarta, ramar tayi yawa, zafgewar bici ace ta iyaka damuwar da take a cikinta bace, shi kuwa me yasa be tsaya ya fuskanta matarsa ba, me yasa fushinsa gare ta har ya bari yaja lokaci haka?..... Kansa ya riƙe yana ɗan jujjuyawa yana ambatar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un a cikin kansa. Idanunsa na dishi dishin lumshewa yake ja baya yana cewa kar ta masa haka, karta yarda ta sako maganar cikin nan, nashi ne!, na shi ne!!, Ze amsa yana son ta yana son duk wani abu daya kasance tsatson tane.... Yana ji yana gani suka tafi da ita, tafiyar da ita ce farko da kuma ƙarshen rayuwa da duk wani farin cikinsa, tafiyar data tafi ta barshi na har abadan da dama ta riga ta gama ambata mishi, Kuka ya saki a wurin tamkar wani ƙaramin yaro yana buga kansa da jikin biyar settline ɗin dake tsakar compound ɗinsu, Ita kuwa zuwa lokacin idanunta sun gama ƙaiƙashewa sun bushe babu alamar hawaye, domin zun riga da sun gama zubar da iyaka ruwan da zasu gama zubar wa ɗin, sun soye kuma yanzun sun ƙaiƙashe, bata jin kuma akwai abinda ze sake sakata kuka yanzun. Da kanta tana layi tana komai ta shige cikin motar suka buga suka bar gidan da ita. Ya Sadeeq ne yayi hanzarin yin kan Ahmad ba wai dan shima tashi zuciyar na cikin sauƙi da nutsuwa ba, sedan haƙurin daya gama bata ya jure ya taya ƙanwar tashi gwagwarmaya, ya taya ta yaƙin har se inda ƙarfinsa ya kare shi ma. Ciki ya shige da Ahmad bayan ya ƙira gidansu ya sanar da iyayensa abinda ake ciki, kafin kiftar ido sega mahaifinsa a gidan, wannan ne ya saka Ya Sadeeq ɗin tafiya shima domin ya fara binciken Inane inda aka kai ƙanwar tashi. Se dai duk wata HEADQUARTERS ɗin daya sani dake cikin garin KANO ya gama zagayesu, se dai babu ita babu me ko alamarta. Sosai hakan ya tashi hankalin sa goshin zuhr ya isa gidansu, Daga yanayin yacce mahaifinsa ya ganshi a jigace ne yasan cewar ba ƙalau ba, seda ya fara shan ruwan da Baffan ya bashi ɗan huta kaɗan kana yake tambayarsa ko lafiya?... Kora masa bayanin duk yacce ake ciki yayi, se dai ya ɓoye zancen cikin da yaji ta furta kuwa, tin da bai da tabbacin hakan ne koba haka ba, ALLAH sarki take Baffa shima ya shiga wani kalan zallar tashin hankalin da ba'a sa masa rana. Kafin ka me se gashi har ya haɗa kan almajiransa ya saka su sauƙar Alqur'ani me girma, cikin gidan ya wuce yake gwaggo Sadiya ta dafa shinkafa jallop kamar kwano uku, tana gunguni tana komai ta miƙe ta ɗora don wllh ita ta tsani wannan saka aikin na Baffan, da sai kana zaune kwatsam se ɓallo maka da aiki bayan kana murna ka kammala naka, gashi babu damar musu don duk tsiyarta tana shakkarsa ai, ɗan kwalin dake ƙoƙarin zame mata ta gyara tana cewa. "Se ka bani kuɗin kayan miyar ai dubu uku..." Ganin kuma yana kallonta da kanta yasa ta tsargu don haka tace "To ai kowacce kwana kayan miyar dubu take ci, amma ba sai ka bada kuɗin mai da magi ba muna dasu...." Ta ƙare maganar da susar kan da kana kallarsa kasan bana gaskiya bane, don kar a gano ƙaryar data labta ne. Kansa kawai ya jijjiga ya fiddo ukun harda ƙarin ɗariya biyar yace ganan yacce zefi isa ma, yasa kansa ya fita. Yana fita ta ƙira Bilkisu dake daki ta bata 1500 bayan ta zare dubu biyu, tace a mata malkaɗe bashi ɗaya kulli uku na ɗari biyar biyar gida uku, iya zallar tattasai da da tarugu. Shimar nata ta koma ta ɗauko a cikin ranta tana ma Ummar nata fatan shiriya, don duk maganar da suka yi tana jin su. Fita tayi taga gidan har ga gota Baffan nata da sai da ta masa sannu ya ƙiranta, wanda se da ya saka gabanta faduwar ko tambayar ta baffan nasu zaiyi, duk da dai bawai hakan yake mata ba. Tsugunne takai tana cewa "Baffa gani!" Dubu ɗaya ya zaro daga cikin aljihunsa yace ta taho da ciyawan shayi ta ɗari biyar ta dafa mishi shayi me ɗan dama, bayan ya tambayeta ai suna da sugar tace ehhhh kana yace to ta riƙe ɗari biyar ɗin, godiya ta mishi tana miƙewa ta tafi aikar nata. Babu jimawa ta dawo ta wuce ta bama Ummun nata markaɗen, kafin itama ta nema tukunyanta me kyau me ɗan girma ta ɗora, koda uwartata ta tambayeta me zata yi, tace Baffa ne ya sakata dafa masa shayi, yi tayi kamar tayi magana amma kuma ta fasa tana ɗaukan wata babban tukunya itama ta ɗora. Kafin kace me sega gidan ya ɗauki ƙamshin girkin gwaggo Sadiyan, ita kuwa tuni dama Bilkisu ta gama dafa shayin ta juye a wata babbar cooler. Ta nemi wankakkun ƙananun kofuna ta ɗora a kai ta ajje daga bakin ɗakin Baffan nasu ta shirya a gurguje ta wuce Islamiyya, ita kuma dama Shareefah tana school dake Monday ce tana can ba kuma zata dawowa ba se Friday, weekend kawai take zuwar musu. Bayan idar da sallar la'asar Baffa ya saka manyan almajirai fitowa da abinci da shayin da aka dafa, nan gardawan ciki suka ringa zuzzuba musu abincin da shayin, bayan sun kammala ci aka kuma taruwa aka yi adda'an ALLAH ya kawo musu komai da sauƙi... ★.. Tafiya yake cikin yanayin da kai baka isa ainihin gane masa ba, domin kuwa wannan moody face ɗin nashi da kullum haka zaka ganta babu murmushi balle dariya, ita ba'a ɗaure ba ita kuma ba'a sake ba. Gaba ɗaya tin da ya kama kallar labaran maka yarinyar da tayi sanadiyar mutuwar ɗan gidan senator Garba Aliyu na Yaya a kotu, yaji hankalin sa ba'a kwance ba. Ya rasa abinda yake masa daɗi haka kawai kawai, a ransa tunani yake don me yasa ba asibitin zasu kai ƙaran ba?, ai ba iyaka yarinyar bace likita a cikin asibitin, me yasa basu kai kowa ba se ita? Sune jerin tambayoyin da yake tama kansa. Gaba ɗaya lissafinsa nemar kufce masa yake akan al'amarin, gani yake idan har be shiga cikin case ɗin ya kwatarma da yarinyar ƴan cin ta ba to shima yana da nashi kamisho ɗin zunubin ne. Wayarsa ya fidda ya saka ƙiran Dr BILAL lokacin da yake kaiwa zaune cikin motarsa, lokacin kuma wajajen tara da rabi ne na dare. Wayan nata ring baya ɗauka don haka kai tsaye kawai yama motan key ya fita daga gidansu. Asibitin ya nufa directly, Lokacin da ya isan kuma goma saura, ganin motar Dr Bilal ne ya bashi tabbacin yana cikin asibitin kenan, kai tsaye office na Dr Bilal ɗin ya nufa ganinsa da yayi zaune gaban computer yana ta famar aiki ne ya saka shi jan tsuƙa, ya ƙaraso ya zaune yana janye computer ɗin dake gabansa yace. "Uban me kake da kana kallar ƙirana baka daga ba?" Wani kallo Dr Bilal ɗin ya watsa masa yana furta. "Aikin daka aiken ɗan renin sense kawai, bani computer na woni aiki me muhimmanci nake, ƙirarka kuma ban gani ba ne Malam...." Seriously ya dawo yana fuskantar Bilal ɗin, kafin cikin ɗan ƙaramin sautu yace. "Ƙarin bayani zaka bani game da ita...." Daidai nashi Dr Bilal ɗin ya dawo yana me furta. "Game da?..." Don shi ma bai gane ko waye yaje nufi a kai ba. "Ita yarinyar da case na su sen Garba Aliyu ke kanta...." Wani numfashi Bilal ɗin yaja yana me furta yanzun ma shi ne aikin daya riƙeni, don da magribar nan Yayanta yazo cikin asibitin yake tambayana game da ita, wai kwalawa sunje har gidan mijinta sun tafi da ita, kuma ya duba duk wata headquarters na ƴan sanda bai sama labarin taba, bayan tafiyansa nima nake kallar labaran kama ta ɗin da aka yi shi ne ma dalilin da yasa na yi busy kenan..." Wata iska daga cikin bakinsa ya fesar tare da miƙewa tsaye, yana cewa "Kafin zuwa wayewar gari kayi gaggawar gano inda suka ɓoyeta,nd kuma shi ina banzar mijin nata yake da har zasu shigar masa har cikin gida su tafi da ita, da ba zai dakatar dasu ba...." "Yayi duk yacce zeyi dan ya bata kariya shi da Yayan nata dana ce maka yazo, amma Ita yarinyar ne ta ƙi aminta har ta bayyana kanta gare su...." Kafaɗunsa ya ɗaga alaman bashi da damuwa ya fice, shi dai abu daya kawai yasan zai tsaya mata akai shi ne kare martaba haƙƙinta na wacce aka zalumta... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. Page 13&14 _YA ALLAHU ME IKON ZARTAR DA HUKUNCINKA AKAN KOWANNE RAI ME NUMFASHI, GASHI A YAU WASU SUN TAƁO MAKA NI MARYAM WANNAN BAIWAR TAKA DA BATA DA GATAN KOWA SE NAKA, DON HAKA NAKE KAWO MAKA KUKANA AKAN DUK WANI MUNAFIKIN DAKE SON GANIN BAYANA, DA HAƊA MIN TUGGU DA MUNAFINCI AKAN MAGANGANUN DA NI BAN SAN NA FAƊE SU!, YA ALLAH KA SAKA MIN, KA KUMA BI MIN HAƘƘI NA AKAN KOMA WAYE... ALLAH KA TSAYA MIN ADUK WANI LAMARIN DA ZAI TASO IRIN HAKA, DOMIN NI KAI NE GATANA KUMA ABIN DOGARO NA, DONNI DA KAI NA DOGARA BAWA KO WANNE KATO KO KATUWARBA,YA WADUD KA SHIGA CIKIN LAMARIN..._ _KU KUMA MUNAFIKAI KUJI TSORON ALLAH WLLH ,IDAN KUMA BURINKU WANI YA TOZARTANI TO KU SANI IN SHA ALLAHU BA ZAKU TAƁA GANIN BAYANA BA DA IKON RABBIL ARSHIM AZEEM... DA WATAN AZUMIN ALLAH KUN TASHI HANKALI NA KUN KUMA SA HANKALI NA YA TASHI BA KAƊAN BA, KUJE KUMA NA BARKU DA ALLAH, SHIRUN KUMA DA NAYI BA INA NUFIN NA TSORATA BANE, KAWAI BANA GAGGAWAR ƊAUKAR MATAKI NE DA KAINA, INA BARMA ALLAH YA ZARTAR DA NASHI IKON NE, DOMIN NASAN IN YA TASHI YAFI NAWA ƘARFIN IKO KO MATAKIN DA ZAN ƊAUKA,DON HAKA KUCI GABA DA GASHI ALLAH YANA KALLON KU BABU RUWAN AMMEY LAYLERH 🤸💃_ ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ A can gidan su ameenatou kuwa da kuma Mijinta Ahmad tabbas sun kwana suna baƙin ciki da alhinin iftila'in daya faɗama Meenal ɗin a daren jiya, tabbas sun sake yarda da ake cewa zaɓi guda ɗaya mara kyau a cikin rayuwarka na iya janwo maka shekaru na gajiyawa da nadamar rayuwarka na har abada, Shi sa masu iya magana suke cewa ka zama mai taka tsantsan aduk wani al'amarin daya danganci rayuwarka. Domin rayuwar tana jujjuyawane cike da tarin abin mamaki da al'ajabi, ta yanda wani lokacin zaka shiga kwanakin da suke nauyaya maka rai,har kayi tunanin ba zasu taɓa ƙare maka ba. Har ka wayi gari wata rana kana son kayi sabuwar rayuwa, sedai lokaci ba zai taɓa baka wannan damar ba, domin shi da kansa lokacin ba zai taɓa baka damar hakan ba,don lokacin daka gama ɓatawa na baya ba za su taɓa dawo maka ba, ta yanda wani lokacin karshen abu shi ne farkon nutsuwar zuciya. Kamar yadda masu hikima suke yawan cewa, karka jira ƙofa ta buɗe bayan ta rufe maka, sannan ka gane babu rufewar data fito daga ALLAH face tana ɓoye da alkhairinsa akan ta. Abu na farko daya kamaci ace kowanne bawa ya gane anan shi ne ka sani cewar, abu na farko daya kamata ka fara yafewa shi ne ka koya daga kuskurenka don ka sake gyara kuskurenka harma kaci gaba da ƙoƙari. Kada kabar kuskurenka ya zama sarƙar yanke ƙauna,ka mai dashi gyara zuwa matakin gaba na ingantacciyar nasarar ka, don masu iya magana sunce, Rashin nutsuwa yana farawa ne daga nisantar mutum da ALLAH, tsoron ALLAH kuma shi ne sirrin kowanne farin ciki na gaskiya..... Idan har duniya da abinda ke cikinta suka soka da gyara to maza kayi gaggawar gyarawar kuwa, idan kuma ta ƙiƙa to ko zata sake baka wata damar seka sha baƙar wahala da fafutuka sannan. Daga nan labarin ameenatou ya fara..... Yanda taga daren wannan rana haka taga wayewarsa masu cike da almara da irin ƙarfin iko na Ubangiji, lallai idan har bawa beji tsoron mahaliccin saba to kuwa yaji tsoron hukuncinsa, don idan yaso ka da ramane fa kuskuren saɓa masan da kai ke farawa tin daga nan gidan duniya, idan har shi wannan bawan me zuciyar nagartane seya gyara, nadamar rayuwa da dana sanin biyema son zuciya da kuma rudin zamani shi ne abu na farkon daya farawa dirar mata, A cikin zuciyarta take zubar da hawaye bawai don yana fitowa daga cikin idanun taba, A ahhh yana daga can cikin zuciyarta yana mata illar da tafi zubar shi azaba, cinnaku da kukan sauro sune abu na daya fara addabar rayuwarta, wanda take jin kamar ta sare da rayuwar ta huta haka nan, Sedai kuma kamar yacce hausawa ke cewa wahala bata kisa sedai asha baƙar hawala a hannunta, tuna wannan kawai da tayi ne yasa har taji a ranta cewar sauyin rayuwa da munin ƙaddara ba zata taɓa barin su kaita ƙasa ba, bare sauyin rayuwar data samu kanta kwatsam a ciki besa taji zata sarema rayuwar ba, sai ma wani ƙarfin imani dana zuciyar karɓan kowacce iriyar ƙaddarar da tazo mata da hannu bibbiyu, wannan kwana ɗayan da tayi a cikin cell a kulle da har a da take jin kamar ba zata iyaba, saboda rayuwa ce da ko a idon zuci bata taɓa ko tunanin hasasoma kanta ba ko da a mafarkin tane da. Rayuwar data tsinta kanta a ciki se taji tama tata rayuwar nauyin da kamar ba zata kai labari ba. Amma ƙarfin imanin daya shigeta na danne hakan take. Hasken daya haske mata idanune ya sakata motsawa tare da kare fuskanta da duka hannuwanta biyu, Wata police macece tace ta fito se famar wani kukkumbura take tana cika tana batsewa, domin ku su duka jami'an ba hakan suka so ba daga yarinyar, don da a son samu ne se ta samu kamar kyakkyawar sati guda cif a kulle ba tare da ko sauron waje yasan inda take ba, sedai wanda ta tarar a cikinsa amma kash wani ya musu kutse a cikin tarkon nasu, wanin da suke da tabbacin tsaf ze iya saka a dakatar dasu a aikin nasu, dakatarwar kuma ta har gaban abada, domin shi kansa yaron nada wani irin karfin iko a cikin garin bare kuma azo kan mahaifinsa da yake kamar father's ne na manyan mutanen da duk suke jin sunkai a garin Kanon. Fatar bakinta tayi wani kalan bushewan da har tsagawan hawala tayi, idonta yayi zurfin da ya sake fitar da iyaka zallar jigatuwar da tayi, domin tin da suka wullota ko ruwa babu wanda ya bata bare abinci, domin sen Garba Aliyu na Yaya da Matarsa Haj Madina kamar kwangila kisan tane suka bayar suma. Shi ya saka ko a jiyan ziryan Yayanta biyu amma suka ce su bama su san wata me wannan sunar ko me kama da ita. Ana haka sega wannan Gabjejen bakin police ɗin ya fito, wanda sarai Ya Sadeeq ɗin ya gane sa don haka ya nufi wurinsa yana cewa don ALLAH ya taimaka ya faɗa masa inda Meenal ɗin take. Amma haka wannan police ɗin yay mirsisi yace shi baima taɓa ganin kome kama dashi ko wata can ba se yanzun daya fara ganinsa, Wannan abu shi ya sake rikita Ya Sadeeq ɗin, barin ma da sauran ƴan uwansa ma suka goya masa baya wai shi bama ya gari ai yanzu ya dawo, Nan fa suke neman haukata kan Ya Sadeeq ɗin... Tunanin wannan police ɗin ya dakata ne daga lokacin da wannan macen police ɗin take fitowa da Meenal ɗin, ɗago ƙananun idanuwansa da suke a matse kamar na ƴan Japanese yayi, yana sake tsayar da kallonsa akan Meenal ɗin da lokaci guda harta sanja saboda mummunar halin da take a ciki, ga yunwa da ƙishin da suka gama wajigata. Wata nannauyar ajiyar zuciya police ɗin yayi ganin kamar Wada damar ce ALLAH ya kawo musu, masu ƙarfin ikon faɗa da nera biyu sun haɗu akan case guda ɗaya, se yake jin a ransa cewar hakan ma kamar dama ce ALLAH ya kawo musu ta yanda zasu jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu a wannan gaɓar. Da wurin zama ya mata nuni yana sassauta zuciyarsa akan tsananin son abin duniyar da yake da. Zama tayi a inda ya nuna mata ɗin tana ta baza idon taga ta inda Mijinta ko Yayanta a cikinsu wani zai ɓallo, don tasan kaf duniyar babu masu zuwa wurinta daya zarta su. Se dai zama da kamar 30 minutes ɗin da tayi bata ga kowannensu daga cikin su ne ya sakata ɗaga kanta ta kalla police ɗin dake tsaye, mamakin Mutumin da kuma jin kansa na sake kashe sa, ehhhh mana ai dole yace jin kai mana yace a fito masa da yarinya kuma ta fito sama da 30 minutes be ce mata komai ba. Ta buɗe baki kenan da niyar tambayarsa a ina wanda ke ƙirar nata ya wani ɗago kansa yana wurgama Police ɗin wani mugun kallon da ko be buɗe baki yayi magana ba, idanunsa kawai sun isa isar da hukuncinsu ga mai laifi, don haka tin kafin ya furta masa wota magana ya bar wurin. Don kai tsaye ya gane spece or balance yake nema daga gare shi. Gabanta sosai taji yayi mummunar wata bugu da ganinsa kawai, me ya kawoshi wurinta?, miye kuma haɗinta dashi?, ama ina yasan tana nan ɗin, ko kuwa ya sake biyota har nan ɗin ne don ya sake wulaƙantata kamar ranar?. Maganar sa ce da wannan No nonsense muryan nashi ya sakata dakatawa cak daga tunanin nata. "Me ya sa kika biyosu?, bayan mijinki da yayanki sun yi ƙoƙarin baki kariya?" Haka maganar nashi ya sake dakar tsakar kanta da yake mata wani kalan mugun ciwon da take jin har kamar zai tsage gida biyu. Komai bata ce masa ba saima saka hannunta da tayi ta dafe goshinta da nufin ko zata ji sassaicin abinda ya riƙe mata kan, amma kuma sai taji ciwon kamar a tsakiyar kan yake, wanda taji kamar ma ba ciwon yake ba, kamar wuta ce ake hurawa a cikin kan nata da zafin ta yake saka gumi tsiyayowa daga cikin gashin kanta zuwa fuskar da ilahirin jikinka. Ba ciwon kan ne ya fi damunta ba, ciwon da zuciyarta ke mata ne yafi addabarta fiye da komai, se kuwa zafin kalamansa da tambayar daya mata ke sake taso mata, suna son wargaza sauran jarumtar da take jin tana da. Wani irin zafi take ji na taso mata daga cikin ƙarƙashin tsakiyar ƙirjinta irin mai kama da ƙaiƙayin nan, gashi tana lullube a ƙirjinta dan haka babu damar ta sosa ta bare tayi tsammanin samun sassauci daga suka da ƙaiƙayin da take matan. Don haka ta saka ɗayan hannunta ta dafe zuciyar tare da yin ajjiyar zuciya da nufin ko zata sama sassauci ko wani rangwame daga azabar da zuciyar ke mata amma sai taji tamkar kara kaikayin ne ma tayi.... A matuƙar jigace ta mike tsaye tana dafe da kan nata ta dube shi tare da cewa. "Stop it!, da duk wata baƙar maganar data saura wacce baka gama gaɗamin ma, domin a yanzun wannan zuciyar ba zata taɓa iya ɗauka ba ka temaka ka tafi ka barni Please!!!...." Shima tsayen ya miƙe ba tare daya kalla inda taken ba ya wani gumtsi iska ya kuma fesar duk a lokaci guda kafin ya wani furta. "Damn it!" ya fada da karfi sannan ya koma ya zauna a inda ya tashi yanzun. Kafin a natse ya dubeta tare da magana kai tsaye akan case ɗin da take cikinsa. Wani irin hope taji ya sake ratsa zuciyarta da jikinta don haka kai tsaye tace bata buƙatan taimakonsa yaje ya riƙe abin sa, amma ita a wurin mahaliccinta take nema, Ganin kamar zata bashi wahala ne yasa shi faɗa mata wata baƙar maganar da dolen dole yake da tabbacin seta amayar masa har fiye da abinda yake buƙatar ji daga gare ta, don yaga za tayi mugun taurin kai yarinyar. "Kar kiyi tunanin zan tsaya ɓata lokacina ne akan mace mara kima da daraja irin ki, me take dokokin ALLAH data aurenta, ki sani na shigo cikin maganar ne domin kawai a cikin asibitina case ɗin kisar ta faru, badon haka ba ke kin ma isa ki tsaya ko inuwar dana tsaya balle har kiyi tunanin raɓarta? IDIOTS....." A lokacin daya gama yaɓo mata maganar kuwa har bata san lokacin da jikinta ya soma rawa ba, duk yanda taso jurewa kuwa gazawa tayi ga hannunta ɗaya daya soma rawa. Ta riƙe hannun da ɗaya hannun da niyyar bashi kariya amma sai suke rawar a tare. Wannan ya saka ta haɗesu duk biyun ta rungume a ƙirjinta tare da jan dogayen numfashi sau uku ta hancinta, tana sakin ajiyar zuciya da niyyar calming nerves ɗin ta down ko dan ta sama damar ce masa yaje ta amsa hakan za kuma taci gaba amsar kowanne irin hukunci daga mahaliccin tane. Idanunta ta runtse tare da kokarin goge hawayen da kai tsaye taji sun zobo mata, wanda a daren jiya tayi tayi ya zuba yaƙi, se a cikin zuciyarta ya dinga kwarafniya, fara goge hawayen tayi amma wasu suna sake yin replacing ɗin kan su gare ta.... Abinda kawai take hangoma kanta a cikin idonta shi ne girman laifinta ga mahaliccinta da kuma Mijinta, fuskar Ya Ahmad da Ya Sadeeq ɗin ta kawai take hangowa a yadda ta baro su a tsakiyar compound na gidanta, don haka take jin ba zata taɓa barin zuciyarta ta yaudareta akan wani daban ba kuma, shi dama bata gama sanin ko shi waye ba?, daɗi da ƙari Ita Matar Aure ce babu hurimin wani yace zai shige mata gaba akan lamarin da ya faru da ita. Don haka cikin kwarin gwiwa ta soma tafiya ta barshi, Saboda aganinta hakan shi ne dai dai, hakan shi ne zai fi alkhairi gare su, barin ma data shafa cikin jikinta da shi ne silar komai,wanda zata iya rantsewa kamar motsinsa taji a karon farko ya mata.... Kuɗi sosai ya bama tarin police ɗin a matsayin na belinta da yayi har zuwa lokacin da za'a yi shari'an ba tare da sanin taba, kana yace idan har wani abu ya sameta koda kwarzanene se yayi sanadiyar rasa aikinsa, rasawa kuma ta har gaban abada kamar dai yacce Dpo ya tsammata ɗin kuwa. Daga nan ya wuce babu jimawa se ga Ya Sadeeq da Dr BILAL ya sanar dashi inda take ya kuma je anyi belinta. Lokacin tsaƙiyar ranace don irin sha biyu da rabi ɗin nan ce, gashi kuma ba laifi an tashi da ranar. A karo na biyun da akace ta fito cewa tai ta yafe ko waye. Har seda wannan mummunar baƙin police ɗin ya bayyana a gabanta kana ta nutsu ta kuma fito, ganin yayan tane ya sakata shigewa jikinsa kawai tana sakin kuka. Lallashinta ya shiga yi kafin ya jata ya zaunar kan wani plat chiar dake wurin, ruwa ya ɓalle ya bata da kuwa ta kafa kai bata janye gorar ba har se da ruwan ya ƙare, kana ya bari ta nutsu sosai kafin ya sama napep su wuce gida kai tsaye, ganinta ya kwantar da hankalin Baffa ba kaɗan ba nan Baffan yasa Bilkisu ta dafa mata ruwan wanka me ɗumi, har ban ɗakin dake tsakar gidan ta kai mata ruwan bayan ta dafa mata, wanko tayo sosai da gasa jikinta da kyau, kayan Shareefah ta saka jallabiya se kuwa gashi tudun cikin ya ɗan bayyana ta cikin rigar. Haɗe kanta da jikin gadon kawai tayi tana jin yadda zuciyarta ke tsanar cikin dake jikin nata kai tsaye da kuma ƙaunarsa na kasancewar a jikinta yake, haka duka abu biyun suka haɗe mata tsana da ƙaunar cikin jikinta,wanda ita dai ko a tarihin rayuwa bata taɓa jin SO da TSANA sun dirarma mutam lokaci guda ba se a kanta, shigowar mahaifinta dakin ne ya sakata sese ta natsuwarta tana zama daga ƙasan wurin. Cikin taushi da kuma lausasa murya ya dubeta cike da wani kalan matsanancin tausayinta me girma a gareshi, domin kusan ze iya cewa ita ce zuciyarsa kai tsaye. Don haka komai da zai shafi rayuwarta yake jinsa me girma na kuma daban a cikin rayuwarsa. Ahankalin cikin taushin murya yace..... "Kiyi hakuri ameenatou ki amsa wannan ƙaddarar, domin rayuwa ba zata taɓa ginamu kamar yacce muke so ba, harma abinda muke ganin yafi ƙarfinmu na iya zama abu mafi sauƙi da zarar munfi karɓi zaɓin da ALLAH ya mana, se kiga zuciyoyinmu sun sama nutsuwa ata sanadiyyar hakan... Ameenatou ina son ki saka a ranki cewar har yanzun rayuwarki na nan matuƙar kina numfashi!, duk wani zaɓi yana hannunki idan kika so ki sanja dole ne ki fuskanta matsalolinki da kanki, muddin zuciyarki naci gaba da aikinta na bugawa. Kin ga kenan har yanzun zaki iya sake *RUBUTA LABARINKI...*, Amma se kin fara fahimta da sanin cewar yin haƙuri yana kawo nutsuwa, yin godiya ga ALLAH yana ƙara ni'ima,yin adalci kuma yana samar da aminci da nutsuwar zuciya......" Se kuma ya ɗan fesar da wani huci me zafin da yaji yana nemar kuncushe ƙirjinsa. Kafin yaci gaba da fadin..... "Duk wanda yayi Adda'a sannan ya kyautatama ALLAH zato, to kuwa ya jira zuwan mafita daga gareshi zai sama ladan wannan jiran da kuma kyautata zaton da yayi, domin kyautata ma ALLAH zato da kuma tsammanin mafita daga gare shi suma ayyukan ibada ne, don haka kada jinkirin amsawa ya sanya ka sare!!!, ko kuma munana zato ga ALLAH, domin ALLAH yayi alƙawarin amsawa amma a lokacin da yace, don haka gaggawarka ba zata sanya ALLAH gaggawa ba... Ki wanke hawayenki da ruwan alwala,kiyi sallah, ki ɗaga hannayenki sama ki zayyanawa ALLAH damuwarki da buƙatarki. Idan zuciyarki tayi nauyi da damuwa ki sani Rahamar ALLAH tafi damuwarki yawa!, idan duniya ta matseki ki buɗe zuciyarki da tuba da istighfari.... Babu hanya mafi sauƙi na cire damuwa fiye da sujjuda a cikin dare, damuwa ba zata taɓa dawwamaba!, domin ALLAH yana tare da masu hakuri, ki riƙe alƙawarinsa domin shi ne da kansa yace... *INNA MA AL' USRI YUSRA* ki ɗaga hannunki ki kuma fuskanci sama ki ce.... *HASBINALLU LA'ILA HA ILLA HUWA,ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHIM AZEEM....* Zuciyarki zata huta!, za kuma ki sama nutsuwa, kwanciyar hankali kuma zata sama gurbin zama a cikin zuciyarki.... Ki sani tsoro ba zai taɓa gina mutum ba, sedai ya ruguza, domin ita kanta rayuwar ƙalubece. Amma ita nasara tana zuwar mana ne tamkar kiftawar ido,kamar yadda ajali ke zuwar mana kamar kiftawar idon shima. Anan ina son ki sani cewar damuwar da za'a barta a cikin kwakwalwa tafi kowacce kalar damuwa cutarwa, ki amayar duk abinda ke cikin zuciyarki ki kuma tsarkake ta tsarki irin na gaskiya da gaskiyar da ALLAH ke so, za kiyi albarka In sha ALLAHU....." Kuka sosai take yi wanda sautinsa ke fita da amo da kuma irin raunin dake bayyana me yin sa, Tsaye mahaifin nata ya miƙe hannuwansa a gadon bayan sa yace. "Ameenatou a yanzun kuka ba shi ne mafita ba.... Kiyi Adda'a ki kuma yi injoining na ƙaddararki In sha ALLAHU duk bayan wani tsanani sauƙi na bayansa.... Daga haka ya fita. Bakinta yake son buɗewa tama Baffan nata magana, ta masa godiyar Adda'a da nasihohinsa gare ta amma kukan daya sarƙe maƙoshinsa na hana mata hakan, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro, ta jima tana yi kafin ta share wata irin nutsuwa da sanyin kalaman mahaifin nata gare ta na ratsa ilahirin jikinta, kukan da ya zama mafarin buɗewan yin sa kenan a cikin rayuwarta, domin kuwa daga wannan tangarɗar daya faru da ita daga nan ƙaddarar ta fara. Tin da ta shige ɗakin sallace kawai ke fito da har aka yi isha'a, tin kuma data shigo gidan gwaggo Sadiya bata ko leƙo taba, Bilkisu kuma tana maƙarfi taje wurin dangin Ummanta wani biki da suke Malam ya hanata zuwa shi ne ta tura Bilkisun. Bayan sallar isha'a ɗin Ya Sadeeq ya shigo tare da Ya Ahmad har tsakar gidan, dake gwaggo ƴar duniyace harda su ahimfiɗa tabarma, a mutumce ya gaidata sega shigowan Baffan shima, ɗakin da Meenal ɗin ke ciki duk suka shige, wanda hakan bema gwaggo Sadiyan daɗi ba, don haka ta wani ja tsuka tana furta. "Munafincin banza..." Bata sake sarewa da lamarin ba seda ta sake ganin Ya Sadeeq da Ya Ahmad sun sako Meenal ɗin tsaƙiyarsu, ita kuma se famar share hawaye take, domin gani take da ba sai ta koma gidan Ahmad ɗin ba, don tasan koda ace ta koma ɗin taƙi kaɗan ne ƙaddara zata raba zaman nasu. Haɓa Gwaggo Sadiyan ta riƙe a bayyane tace. "Ji wata ƙaddarar liman da sket....." Wanda ya saka Ya Ahmad waywayenta banda sauran da ko kallo bata ishesu ba su duka, har bakin motarsu suka rakata ta shige gidan baya, duk yacce Ahmad ɗin yayi data shiga gidan gaba kuwa, ita kuma ta zaɓa gidan bayan ne yadda zata fi sakewa ta kwanta sakamakon cikinta dake mata wani kalan ciwo da marar ta. Koda suka kawo gidan yaso taimaka mata amma ta dakatar dashi ta yunƙura da kanta ta nufi cikin gidan, kai tsaye ɓangarenta ta wuce ta rufe babu jimawa kuma se gashi ya biyota har nan ɗin, zama yayi daga ƙasan da itama take daf, hannunta ya kamo cikin tafin hannunsa yana ɗago fuskanta kuma da ɗayan hannun, ga mamakinta ruwan hawaye ta gani kwance sharkaf a saman fuskarsa, hannunta dake cikin nasa ya ɗan damƙe, tare da soma magana.... "Komai kikaga ya faru da bawa dama can tin daga Rabbil Izzati ne hakan, don haka nake son ki fawwalama ALLAH duka lamurran, kana roƙon da nake son na miki da kuma Alfarmar da zaki min shi ne....." Se kuma wani kukan ya sake sarƙe maƙoshinsa ya kife kansa a jikin kafaɗarta yace. "Duk yin Duniyar da za'a yi akan cikin nan karki furta komai indai kinsan ba nawa bane zaki ce, naji na kuma gani har cikin zuciya ta na wuce zan kuma karɓi wannan ƙaddarar da duka hannayena biyun nan..." Yay maganar yana ware mata tafukan hannayen nasa. Kana yaci gaba da furta. "Nie banji ma a jikina cewar cikin nan ba nawa ne Meenorh, kwanaki biyar ɗin da kika ɗora ina kallar kamar hindawar wasu kalmomi ne kikai kika aza bisa watanni huɗun, na ji na gani koda ace ba nawan bane kada abinda yasa kika shigo da maganar wannan cikin kinji *ZUCIYAR AHMAD IBRAHIM SHAREEF.....*, mu roki ALLAH gafararsa!, mu kuma rokeshi da ya yafe mana kusakuranmu na baya, ya bamu juriyar ci gaba da gudanar da rayuwarmu kamar baya koma zarta hakan..." Kuka sosai take rerewa a jikin nasa kafin cikin muryan da kuka ya gama cinyewa tace..... "Ta ya kake tunanin ni zan yarda na yaudareka, bayan na gaza kare maka kaina martaba da kuma darajata data aurenmu?, Ya Ahmad na gode da kalan haliccinka gareni kuma bazan taɓa mantawa da wannan masoyin na gaskiya da gaskiya ba, Sedai banji a jikina cewar zamanmu zeci gaba da gudana a haka ba, koda ace zai ci gaba ɗin dole se kalmar saki ta shiga tsakaninmu naje nayi istibra'i na tsarkaka kaina daga dattin zinar dake tare dani. Sena haife abinda ke cikin kina na ware shi daban, domin kuwa bazan taɓa cakuɗashi da yaran da zamu haifa masu tsarki ba I LOVE U too much love Ya Ahmad......" Daga haka ta kwace jikinta a nashi ta shige bathroom tana rufewa duk yacce yata mata magiya da roƙon ta buɗe masa amma ta ƙiya, kuma take wanda bata san ya matsaya da iyaka tsayin da yake da ba, kukane irin na kai da kai ɗin nan, kukane da iyaka me yinsa kawai ne yasan illarsa ga lafiya da gangar jikinsa!, kuka ne irin na wanda ya gama sallamawa..... Sati guda cif suka shafe suna fuskantar azabtarwar da suka zaɓa suma junansu, taki aminta dashi, taki amsarsa a matsayin mijinta, domin tace masa ita ɗin a yanzun tamkar wata datti da zunubi ce, a kuma cikin waɗan nan satikan babu kalar barazanar da bata gani ba daga su sen Garba Aliyu na Yaya, Sedai ALLAH ya kan tseratar da ita daga jami'an ɓoyen da Sir MAJEED DAWOUD ISHAQ ya zuba musu a gaba ɗaya anguwar ba tare da sanin daga ina jami'an suke ba, ita kanta ba tare da saninta ko mijin taba, don wani lokacin se ya fita zuwa wurin aikinsa kana suke affecting na shiga gidan, ganin babu nasara ne ya saka Hajiya Madinah cewa kawai a shiga kotu, don haka kwana biyu bayan haka se gashi har office an kaima Ahmad takardar fara shari'an, tun da gidan babu dama shiga, wannan abu shi ya sake tada hankalin Ahmad daya dawo gida a birkice, Me makon ace shine zai kwantar mata hankali se ya zaman ita ce ke kwantar masa hankalin, cikin ƙwarin gwuiwar jin cewa zata fuskanta duk abinda ke tunkaro ta, wannan daren da mutane suka gaza runtsa bacci, yanda Ya Sadeeq yaga Wannan tsayin dare haka shima Ya Ahmad ya gani, ita ɗin ma haka ta gani sedai ita zamu ce ta raya daren da bautama mahaliccin ta kukanta, ta yi masa kirari ta kuma roke sa akan ya kawo mata mafita ya kuma zama gatanta.... Ko Baffa da Ya Sadeeq ya nasar dashi Adda'a kawai yayi akan batun yace ALLAH ya kai su lokacin, ɓangaren su Hajiya Madina ma duk sun gama har haɗa shedunsu akan cewar lallai Meenal ita ce sanadiyyar mutuwar yaronsu, wanda ranar juma'a za'a yi zaman, wacce ta kama saura kwanaki uku kenan a shiga Shari'an, sosai aka sake linka tsaron dake cikin anguwar wanda su kansu masu anguwar har mamakin hakan ya gaza barinsu,gashi kullum suna bakin aiki duk irin daren da zaka tsala zaka taddasu kiƙam ɗin nan. Sosai kan Ahmad ke ɗaukar hayaƙin shiga kotun da za'ayi, wanda se a daren washe garin ranar da za'a gudanar da zaman yake sanarma mahaifinsa IBRAHIM SHAREEF komai, sedai be musu zancen fyaiɗen ba, don a ganinsa ya wuce fannin tun da har yace Meenal ɗin karta yarda ta faɗa maganar fyaiɗen bare kuma cikin jikinta, sedai ya makaro kusan zamu ce, don kuwa a nata ɓangaren ta gama shirya duk wasu hujjoji nata ba tare da sanin kowa ba ta naɗe kayanta a kanta, ko lawyer ɗin da Ahmad ya ɗauko mata bakinta be jiba, duk kuwa da irin bugun cikinta daya ringa yi, amma haƙarsa bata cimma ruwa ba...... _To fa wannan shi ake ƙira da ana wata ga wata_ _Jama'a ya kuke tunanin wannan zaman ze wakana kuwa?, shin kuna jin wani ƙanshi ƙanshi koni kaɗai ce nake jiyo mana?_ _Wannan tafiyar fa itama da nata kalan salon da tazo mana shi, don na fahimta yanzun alƙalamin nawa nema yake ya faɗa kan iyaka ƙaddara da kuma ƙalubalen rayuwa Tabbas, to koma dai miye nidai AMMEY LAYLERH burina in nayi rubutun jama'a su amfana dashi_ _Nasan zaku ringa tunanin cewar ya alƙalamin yake nemar mana wasa da hankali ne ko?, zuwa yanzun nasan ko kowa be furta ba to kuwa abinda ke ƙumshe cikin rai da ruhinsa kenan..._ _Se dai ku sani cewar indai wasa da hankali ne Hhhhhhhhhhh badai zan ce komai ba amma dai akwai zatan da zakuyi tayi kuma na sanja salon tunanin naku kamar dai yacce aka saba, lolz 🤩 Ni kaina nasan banyi kamar wannan littafi ba, gashi dai labarin ba tsayi zeyi irin sosai ɗin nan ba, amma kuma nace sena rikita tunaninku, na gama assignment ta yacce zakuyi ta hasashe da tsammatar abinda be shi ke akwai ba, karfa ku manta sunan littafin ƘARSHEN ƘADDARA!!!. Kun ga kenan ai ƙaddarar ba ɗaya bace kenan ƙaddarorine da yawa....._ _Hhhhh to lolz 🤩 🤩 🤩 koma dai miye ku muje zuwa🤸🤸🤸💃💃💃💃💃💃🤸🤸🤸_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏.... Page 15&16 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Daga cikin motar da take zaune take ƙarewa harabar kotun kallo, wacce take cike da mutane kowa na harkan gabansa, wanda da dukkan alamu wata Shari'a ce aka gudanar me zafi, wanda ganan jama'a se famar mayar da yadda al' amarin ya kaya suke. Gaba ɗaya a yau ɗin data tsinta kanta a cikin kotun se take jin kamar zata sare ne, domin taki bama lawyer ɗin da aka kawo mata dama, wanda ita a karan kanta take son zamewa kanta da kanta lawyer kamar yacce Yami Ghautam tayi a cikin Film ɗin ta na HAQ wato ƙare Haƙƙi, za tayi iyaka yinta In sha ALLAHU itama har taga tayi nasarar da ikon ALLAH. Buɗe Motar da wata police tayi ne ya katse mata tunaninta, tana sanye cikin ɗamararta ta cikakkar ƴar sanda, hannunta da ɗan kulkensu wanda tin a daren jiya suka je har gida suka tafi da ita,sedai hakan bata faru se sune suka kwana a ƙofar gidan suma suka zama kamar body gurds nata ne, ita kuma ta a daga cikin gidan soye da zuciyar da tayi kwanan wasi wasi da fargaban ko me ze faru a cikin shari'an nasu. "Mrs Meenal zaka iya fitowa?" Christian police ɗin ta fadi, wanda ya sakata yunƙurowa tana zube kyawawan ƙafafunta da suke fess tayi, akan ta tsaya akan diga diganta tana fesar da wani gauron numfashi, Idanunta ta lumshe a can cikin zuciyarta ta furta.... _ALLAH kai ne ALLAH!, kai ne kuma buwayi gagara misali, UBANGIJIN da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Ya ALLAH na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko wace siga, amma ni ban damu ba sabo ni kaine GATANA kuma abun DOGARO NA!, na san ba za ka taɓa bani kunya har na tozarta a idon duniya ba.Ya ALLAH gasu nan sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu kai ma. Ya ALLAH ka nuna musu irin naka ikon na KUN FAYAKUN akan wannan shari'an!, Ta inda HASKEN dake cikin shari'an ya bama GASKIYA kariya ya shafe Ƙarya da sharrin dake cikin ta, Ya ALLAH ka zamana a bayana duk da ina da wanda suke tsaye a bayan nawa kuwa, amma ALLAH goyon bayanka nake buƙata, Ya Wadud!,UBANGIJINA ka iya mini badon iyawata kota wani na ba......._ tana kai nan ta soma tafiya cikin nutsuwa, Nan ƴan jaridu su kayo Caaaa a kansu wasu jami'ai biyun dake bayanta da aka rasa daga inda suka fito na bata kyakkyawar garkuwar da babu Yar jaridar data ko sake yunƙurin tun kararta, a nata ɓangaren kuwa tana tafiyar kawai amma Zuciyarta bugawa take duk lokacin da take sake tunkarar ƙofar shiga kotun, zuciyarta naci gaba da tsananta bugawa,tana fata da roƙon ALLAH ya shiga lamarin ta. Bayyanuwarta tsaye a gaban kotun ne ya saka wata hayaniya ɓarkewar da seda tayi yunƙurin kai hannunta da nufin toshe kunnuwanta ta tuna da Onka ɗin dake ɗaure da hannuwar nata, Wata tsawa ɗaya daga cikin lauyoyin dake zazzaune wani ya doka musu wanda ya saka kotun wani irin tsit, ta yanda har ba ka jin sauti da motsin komai face na ƙarar gudun A/Cn , gaba ɗaya mutanen sun kame sun zama kamar wasu gumaka tamkar kuma masu jiran wani sakamako. Kana sannan kotun ta sama nutsuwa har aka wuce da ita wurin da ake tare wanda ake tuhuma, gaba ɗaya kowa ya gama hallara a babbar kotun se dai anki fara gudanar da shari'an ne akan One Man ɗin da suke jira, wanda kowa be san ko wanene ba, kana babu mutumin daya san shi ko meye huriminsa akan Shari'a ɗin.... ★.. Tin bayar fitowarsa daga gida daya hau titi yake fuskantar kamar ana bin bayansa, gashi shi dama ba gwanin yawo da security ba don yace yawo da security ai na matsoratane masu raunin zuciya lolz 🤩 ba inji LAYLERH ba, Inji Majeed tin dai masu ɗan security ɗin nan daɗi ne dashi, ko kuwa yanzun mace Yaya Kuwait ɗin mu ÈÃGLÊ yana da tsoro🤸, kai tsaye ya ƙira security line na gidansu ya basu umarnin su biyo bayan shi akwai wata Black Bentley car ɗin dake bin bayansa da be gama yarda da ita iba kawai suyi kidnapping nata. Tun daga nesa yake hango irin uban tarin car's ɗin dake cike da harabarn kotun, wani murmushin gefen baki yayi tightly yana parking nashi ka ɗin a wurin da aka tanaja don ajje motoci. Bayyanuwarsa a wurin ne kuma yayi sanadiyar da iskan wurin ya sanja da ƙamshin daddaɗan out irin me sanyin daɗin nan, be san me yake ji game da case ɗin ba, abinda kawai ya sani tausayinta yake ji, yana tuna ameenatou ɗin sa ne, don haka duk wani taku ɗaya da zai yi sai ya ji ƙirjinsa yana amsawa, tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin da yake fitarwa me azabar daɗi da saka mutum yaji ya fara jin bacci take.... Alƙalin da ze gudanar da shari'an ne ya miƙe tsaye, tare da gyara farin yankakken gilashin dake idanunsa na ƙara ƙarfin gani, kafin yayi ɗan gyaran murya ya fara da cewa. "A yau data kasance ranar Juma'a wacce tayi daidai da _27/2/2026_ Zamu gudanar da Shari'armu akan laifin kisan kai, wacce ake zargin AMEENEERH SHEHU USMAN da laifin a cikin wannan KOOOTU!, tamu me albarka" Alƙalin yayi maganar yana buga ƴar hidimarsa, tsittttt kuwa kotun ya ɗauka shiru.... Nan ya umarci da lawyer ɗin dake kare ɓangaren iyayen yaron da aka kashe da su fara fitowa su gabatar da shari'ansu... Mutum ɗaya ne daga cikin lauyoyi biyun da suka diba ya miƙe tare da furta.... "Ya me girma me shariya sunana lawyer Ibrahimul-khaleel datti!, nine kuma lawyer ɗin da yake kare ɓangaren shari'an iyayen Sameer,akan Rashin tallafin da ɗaya daga cikin Dactor's na asibitin 4&4 suka kashe mana shi!!!!..." Ɗaya lawyer ɗin ne ya miƙe tare da ci gaba da faɗin.. "Kwarai kuwa yame girma me shari'a!, kamar yadda ɗan uwana Lawyer Ibrahimul- khaleel datti ya faɗi haka ne, domin a lokacin da iyayen Sameer suka kai shi cikin asibitin 4&4 lokacin daya sama accident aka kai shi can, amma se Dr Meenerl Shehu Usmanu taki amsar shi tin uwar yaron nayi da ranta har ya koma ga ALLAH, Na gode yame Shari'a...." Lawyer ɗin ya faɗi yana ɗan dukar da kansa ƙasa ya koma mazauninsa ya zauna.... Ɗan gyaran murya Alƙalin yayi tare da faɗin "Ina son ganin lawyer me kare haƙƙin DR AMEENEERH SHEHU USMAN" Tsit da shiru kotun ta ɗauka, kowa na son ganin ta inda lawyer ɗin da zai kare Meenal ze fito, ciki kuwa harda su Dr pooja dasu Dr Bilal, sedai shiru har na wosu ƴan mintuna babu alamar zai fito ɗin kuwa. Don haka Lawyer Ibrahimul-khaleel datti ya sake miƙewa yana me furta...."Tun daga nan ma sun bayar da shedar cewa lallai Dr AMEENEERH SHEHU USMAN ita ce sanadiyyar mutuwar Sameer Garba Aliyu na Ya...... Se dai kuma ya dakata ne da maganar a lokacin da nutsatsestsiyar muryan wanda zata bata zatansu ya karede ilahirin kotun, "Ina da ja nima yame Shari'a....." Cikin nutsatstsen kamala da wani kalan kwarjinin da yake da miƙe, tare da ɗan rausayar da kansa gefe yana me furta "SUNANA LAWYER MAJEED DAWOUD ISHAQ!, Lawyer me kare mutumcin Dr MAANAL, Me kuma kare Kima da darajar asibitin 4 4...." Tirƙashi!, wannan fa shi ake ƙira da tashin hankalin da ba'a sa masa rana, haka zuciyoyin mutane da yawa dake zazzaune a wurin suka fara furtawa, na kawai ganin MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin a matsayin wanda zai jagoranci shari'an, su kansu iyayen Sameer ɗin seda ƙirajensu ya buga da ganin bayyanuwar nashi, don kuwa a lokacin da suka ganshi a cikin asibitin se suka shiga taytayi da hankalinsu, wannan dalilin ya sanya suka sanja akalan wasar nasu zuwa kan Meenal ɗin ita kaɗai, wanda suke da tabbacin indai suka ce zasu buga wasar tare da shi ta hanyar tsomo asibitin sa ciki, to kuwa ba za su taɓa nasara akan case ɗin... Amma duk da hakan se suka fara karfafama kansu gwiwa, tun da suna da tabbacin bawai sanin ainihin takamaimain case ɗin yayi ba, amma kuma se sukaji woni zance na daban bama wanda sukay hasashen bane.... "15/9/2025 Itace rana mafi munin da Mr MAANAL SHEHU USMAN ba zata taɓa mantawa da ita ba, domin kuwa itace rana mafi munin da ta munana rayuwarta tun daga farkon ginata har zuwa wannan lokacin da nake tsaye a gabanka ya me Shari'a!!..... Se kuma ya fesar da iska daga bakinsa yana kuma sassauta teayneck ɗin dake wuyarsa kana yaci gaba da furta... "A lokacin ta sama ƙirar gaggawa daga cikin asibitin 4 4 akan wata tiyatar taimakon gaggawar da zata shiga!, wanda da farko ma har taki amsa ƙirar ne, sabo da kusan 4 months kenan data dena fita aikin nata, amma bisa maganar da Mijinta Ahmad Ibrahim Shareef da yayi ya sakata fitowa ba dan taso ba..." Alƙalin ne ya dakatar dashi yace yana buƙatan ganin Mijin Dr Meenerl.. wanda ya mike take yana fitowa, bayan ya risinar da kansa yace..." Tabbas anyi haka yame Shari'a!, domin kuwa ni ne da kaina na ɗaukota na kawota har cikin asibitin bayan na bata baki akan ta taimaki rayuwar dake cikin hatsari, kasanwar abokiyar aikinta Dr pooja ta ƙirata akan ta taimaka ga wata operation ta gaggawar data taso musu..." Shima daga nan Alƙalin ya dakatar dashi yana cewa ya koma inda yake, idan da buƙatar sake ganinsa ze masa magana, kana Dr pooja ta fito daya bukaci ya ganta itama, amma kafin nan se lawyer Ibrahimul-khaleel ya miƙe yana rusuna kansa yace.... "Ya me girma me Shari'a!, ba kwana kwana ce da bada labarai ya tara mu anan wurin ba, domin kuwa a ƙa'idar Shari'a babu kwana kwana ko wani dogon labari, kawai a tafi cikin shari'an daya tara mu kai tsaye..." Daga haka ya risinar da kansa yana komawa zaune, "uyhmmmm zaki iya magana" Alƙalin ya bama Dr pooja damar magana, wacce idonta ya cika taf da ruwan hawaye... "Kwarai Sir haka ne, kasancewar ranar babu da yawan Dactor's, Dr Bilal baya ƙasar, shima Dr Majeed daya kasance me asibitin baya ƙasar, ni kuma dake banyi ƙarfi sosai a fannin tiyatar ba ya saka sau da dama bana kasadar yinta, indai bata ɓangaren haihuwa bace!!!. Dake inda na karanta ɓangaren Radiology ne, shi yasa ban cika ganganci akan kowacce tiyatane, don haka na ƙira ta, kasancewarta kwararra a fannin ita, amma se tace min nayi hakuri ta ajje aikin ne kawai, wannan ya saka ni ƙiran Dr BILAL da baya ƙasar na sanar masa, wanda shi kuma ya ƙira mijinta kai tsaye daje aminin sane, shi ne dalilin daya kayo ta, wanda ni AYSHA wacce a da nake amsa sunan Dr Pooja Raju na musulunta, saboda wasu kalmomi na Yayanta Sadeeq da suka ratsani lokacin da yake mata nasiha...." Daga nan ta koma mazauninta ana sake buƙatan ganin lawyer Majeed. Se da ya sake risinar da kansa kafin yaci gaba da faɗin. "A lokacin data shiga tiyata room ɗin da niyar fara tiyatar wanda idanuwanta suka gane mata ne ya sakata sakin kayan aikinta, ta fito ranta ɓace ko ganin gabanta bata yi saboda ainihin abinda idanun nata suka ganar mata, ba kowa bane ba kuwa face Sameer Garba Aliyu na Yaya, Mutumin daya keta mata haddinta da daraja da martabar aurenta ta hanyar mata fyaiɗe...." Daga haka ya dakata yana kawar da kansa gefe, don bazai iya ci gababa kuma daga nan, ga wata irin hayaniyar da cikin kotun ya ɗauka. Wanda ya saka lawyer Ibrahimul-khaleel datti miƙewa a matuƙar fusace yace. "Tayaya akasan cewar Sameer yama Dr Meenerl Shehu Usman fyaiɗe?, ko dan kawai anga baya raye?, shi ne ake son renama alkalai da masu Shari'a hankali ta hanyar kirkiro ƙagaggen labari?, da wannan hujjar nake son wannan kutu me adalci tayi duba domin kawar da zargin da ake ma wannan yaro" yay maganar yana ɗan dukan table ɗin da yake kai.... "Saboda ina da shaidar hakan...." Lawyer Majeed ya sake faɗi shima daidai da lokacin da wannan shegen tight security ɗin nashi ke shigowa da zaratan samari har su uku..., wanda ya saka iyayen yaran da suka zo domin marama abokinsu Sen Garba Aliyu na Yaya baya suka miƙe ciki da kiɗimar uban me zai kawo yaransu kuma cikin shari'an... Alƙali ne ya bada umarnin ya tare su wurin da ake tsare masu laifin... Gaba ɗaya sun yi wujiga wujiga sedai babu alamar duka wa ko wannensu. "Waɗan nan sune shaidar yame Shari'a" Majeed ya faɗi yana isa har inda yaran suke, kana yaci gaba da cewa, "Nasan duk wanda yama Sameer Garba Aliyu na Yaya farin sani, to kuwa tare da waɗan nan yaran ne ya san shi, sabo da sune yaran dake mara masa baya wajen aikata kowanne kalar ɓarna..., Wannan sunan sa MUJAHEED, wannan kuma TAREEQ,shi kuma wannan CLEVER BOY..." Yakai ƙarshen maganar da rusunar da kansa bayan yace su ne zasu bada cikakkiyar shaidar komai daya faru a lokacin.... Nan suka shiga zayyano komai tin daga lokacin da suka taho bayan sun bugu a motarsu daga club ɗin da suka kwana, kawai sun zo gitta hanyar suka ganta tsaye alamar wani taimako take nema, har sanda suka isa gare ta da lokacin da shi Sameer ɗin ya musu inkiyar su zubar masa da ita, har zuwa kan magiyar data ringa musu tana kuka da kuma sumewar da tayi, wanda ada duk su huɗu suka so afka mata amma ganin bata numfashi ne ya saka suka gudu, gashi kuma gefen titi suke wani ka iya kamasu.... Tun daga lokacin da suka fara bada labarin suke kuka suna cewa wllh shi kaɗai yayi banda su ana tambayeta, don ALLAH a musu sassauci a sake su su tafi, har lokacin daya sama accident ɗin suka kaishi cikin asibitin da nan ne mafi kusa, abin mamakin kuma da ya sake bama kowa mamaki be wuce cewar da suka yi, daidai wurin da abin ya faru dai dai wurin sukayi accident ɗin, kuma shi kadai ya raunata, amma su duk basu yi komai ba... Haba sega ido yana fara rena fata, basu sake tsinkewa ba har se lokacin da Majeed ya bada umarnin sake shigo masa da wasu daga cikin jami'an da suka ringa barazana ga rayuwar Meenal ɗin, wanda wannan kuma duk aikin Haj Madina ne bama tare da sanin Mijin nata, har mutane ukun dake cikin wannan Black Bentley car ɗin data biyo bayansa suma.... Nan fa kowa yayi ɗifff an rasa me bakin magana, Se Haj Madina data mike tana rusa uban kuka tana cewa wannan duk cikin shirin Majeed ɗin ne, nan kuwa yace yana da wata hujjar ma, ya bama Alƙali CCTV footage ɗin dake yankin room's ɗin da komai ya faru, don dama ko ina da akwai, nan kuwa plash ta fara haska musu tin daga farkon kawo shin da su Muhajeed ɗin da suka yi, da shigar Meenal ɗin da fitowar, da zuwan Haj Madina ɗin, da irin maganganun da suka gayama juna, ciki kuwa har sanda Haj Madina ɗin ta fara bama Meenal ɗin bakin cewar ta taimaka ta fara duba mata yaronta in yaso koma miye ɗin ya biyo baya da bayyanuwar mijinta bayan da ALLAH yama Sameer ɗin cikawa.... Shike nan ƙurunƙus kan ɗan ɓera, don kuwa dai babu zance na gare kai yanzun... Alƙalin yayi gyaran murya da nufin yanke hukunci, amma suka sake tsinkayar muryan Meenal wacce tin da aka fara gudanar da shari'an kanta ke duke, Baffan tama haka tare da Ya Sadeeq.... "Ya me Shari'a ƙarar bata ƙare ba ai....." Tayi maganar tana bayyuwa gaban kotun, wanda ƙirjin Ahmad yayi wani kalan bugawa, don yasan maganar cikin ne za ta yi, shi kuma be shirya rabuwa da ita, be kuma shirya sake shirya amsar tozarci gaban dubban mutane ba, don kuwa zancen cikin nan da zata furta daidai yake da shi kuma fitar numfashinsa..... Kafin kiftar ido ya isa gabanta yana tin kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar cewa. "A ahhh Meenoh ba muyi haka dake ba, Pls don't forget kamar yacce na faɗa miki...." Raba jikinta da nasa tayi tana me furta. "A yanzu haka Ya me girma mai Shari'a sanadiyyar fyaiɗen da la'antaccen mutumin ya min ina ɗauke da cikin da yake daidai da lokacin da abin ya faru, wato wata huɗu da kwanaki 23 uku yau, wanda a ranar da accident ɗin ya faru dashi a ranar Dr pooja data bani taimakon gaggawa bayan sumewar da nayi bayan farfaɗowa na take cemin ina ɗauke da cikin wata huɗu da kwanaki biyar....." Wanda wata kalan hayaniya ta karaɗe cikin hol ɗin, ita kuma jikinta na ɗaukan wata wata tsuma, "Wanda Cutarwa da muzancin da wannan mutumi ya mi nake jin ba zan taɓa yafe masa ba!, Na so ace rayuwarsa bata ƙare ta cikin sauƙi da sassauci haka ba, naso ace se duniya ta gama wulaƙanta shi shi da macuta ma'intan iyayensa, ALLAH shi ne zai mini sakayya domin dama ni shi na barwa hakan tin faruwan abun..." Gaba ɗaya jikin Baffan ta se ya sake yin sanyin jin wai har da ciki ke gare ta kuma bana mijin taba na wanda ya fyaiɗen!, Ahmad ɗin kuwa jikinsa ne ya shiga wata kalan rawa idanunsa suka yi jajir ɗin tashin hankali, Ya Sadeeq kuwa sumar zaune yayi ba tare da kowa ya ankare ba. Kafin kuma kowa ya ankare ɗin ne Alƙalin yay gyaran murya a natse cike da tausaywa ga Meenal ɗin ya shiga furta. "A ta dalilin manyan hujjojin da mukaji da kunnuwanmu?, muka kuma gani da idanuwanmu zamu zartar da hukunci daidai da lefin kowa dake da hannu cikin rep na Dr AMEENEERH SHEHU USMAN, ciki kuwa har kalan barazana da tare tan da jami'an da suka yi ba bisa ka'ida da dokar aiki ba, za kuma mu hukunta harsu kansu jami'an da kuma hukuncin shi kansa yaron, ta yanda Yan baya za su ringa jin tsoron rep ga matan aure, dama yara ƙananan da muke samu case na rep akan su, ta yanda matasanmu masu tasowa zasu nutsu su ringa jin tsoron aikata lefin, domin dama ganin ba'a yanke hukuncin daya kamata ne yake basu kwarin gwiwar ci gaba da aikata miyagun ayyukansu babu Ƙaƙƙautawa... Ku sani daga rana me kama ta yau idan mun yanke hukunci ya zartu kenan, babu zancen beli, ko ƙaiyadewar kuɗi ku rubuta a dokance domin wannan ɗin kai tsaye umarnine daga *NI ALƘALI YAHAYA SHEHU ƊAN BATTA*, Na kuma yankema Iyayen Sameer Garba Aliyu na Yaya hukuncin ɗaurin shekara Goma Goma bisa laifin ɗan su da suke ƙoƙarin ɓoyewa, shakara ɗaya ɗaya kuma bisa bazaranar da suka sanya aka ringa ma Dr Meenerl tare da taran Million biyu, bisa ɗawainiyar renon ciki da kuma haifewar da Dr Meenerl za tayi, su kuma ɓata garin Yan sandar da wasu daga cikin ƴan siyasa ke yi na yanke musu hukunci ɗauri na shekara uku, gaba da ƙara in sun fito, Kana wannan kotu me adalci ta wanke AMEENERH SHEHU USMAN,bisa ga zargin kisan kan da ake tunanin tayi wa Sameer Garba Aliyu Na Yaya.... Haka yaci gaba da zartar da hukuncinsa har zuwa waɗan nan mutane ukun da suna yarin za suyi na 1 year's kawai. Yana gana yanke hukuncin nasa ya doka hidimarsa da kyau sosai domin ba kaɗan ba tausayin Meenal ɗin ya dirar masa take. Kafin kowa ya ankare sega Haj Madina isa ga Meenal, ta zube gabanta tana kuka sosai tana cewa don ALLAH ta yafe masa, ta kuma kula mata da cikin jikinta tana son ganin jinin Sameer a duniya, tana kukan tana komai tana furta wllh da an kashe Meenal ɗin da bata san da cikin Sameer a jikinta da bata yafewa kanta ba wllh haka tayi ta koke koken ta. Wani kalan kabbara mutane suka ɗauka domin ba ƙaramin mahaukacin cika kotun tai ba, kasancewarta babbar kotu ce kuma dama an gabatar da wata Shari'ar ne kafin wannan ɗin, Baffa ne ya miƙe wani jiri na ɗibarsa da nufin isa ga Ya Sadeeq da se lokacin ya lura da somewar da Ya Sadeeq yayi, se dai shi ɗin ma takunsa ɗaya ana biyun jirin dake ɗibarsa ya ɗibesa ya kayar. Jin faɗuwar abu a ƙasa, ya saka kowa kallar wurin ciki kuwa harda Meenerl, da ganin Baffanta zube a ƙasa ya saka zuciyarta wani irin buga mata, ta nufo wurin da niyar isa ga mahaifin nata, se dai itama taku biyun tayi jiri da harɗewan da ƙafafunta suka yi, suka ɗebeta suka kayar akan wani ƙarfe ta zube babu alamar numfashi tattare da ita, domin kuwa tashin hankula ba hankalin da take ciki ba, don dama sune suka fara bugar mata da zuciya.... Ahmad ne yayi kanta a gigice yana ɗagota yaga bata numfashi, ya kai hannunsa kan hancinta yaji bata numfashi, ya kama babbar yatsarta ta ƙafa yaji itama bata harbawa, don haka ya rungumota gaba ɗaya zuwa jikinsa,sedai abun da yaji hannunsa ya taɓa me ɗumi da ɗan ƙauri ne ya saka shi saurin kallar wurin, Gaba ɗaya jinine kwance ke malalowa daga ƙasanta me uban yawa, Ganin yadda al' amura suke nemar rikicewane ya saka hankali jama'a saje tashi, kotun kuma ta hargitse aka gaza countrol nata alƙali yayi iyaka ƙoƙarinsa amma kotun taƙi dawo wa daidai, Ga Haj Madina data fasa wani uban kukan daya sake jan hankalin kowa tana birgima tana cewa ta shiga uku ta lalace in cikin nan ya zube.. ita kuwa ya zata yi?, me kuma zata ce da rayuwar, tun da tana gani a gabanta taga ci ta ga rashi from grace to grass..... Ga nadamar daya sauƙar mata lokaci guda, wanda masu iya magana dama sukan ce Mai ido ɗaya baya taɓa godema ALLAH har sai yaga makaho.... Da tin farko bata ji nadamar ba har seda lokaci ya gama kure mata, wanda kuma a zahirin gaskiya hakan shi ake ƙira da a ɗauri kashi ko a ɓata igiya..... Motar taimakon gaggawa ce ta iso cikin kotun, zuwa lokacin har an cafke masu laifin, mutane kuma duk sun fice se tsiraru, Dr pooja kuma na tare da Meenal wacce take ma ALLAH roƙon cikin ya zube kai tsaye, don haka take wasu ƴan dabarun su na likitoci wanda take da tabbacin ko da akwai sauran cikin ze ƙarasa zubewa... Shi kuma Dr Bilal yana tare da Baffa da Ya Sadeeq, shi kuwa dama Majeed tuni ya jima da barin kotun baki ɗaya, tin kamin ta gama rikicewa. Kai tsaye aka yi hospital dasu don basu taimakon gaggawa. Ahmad da mahaifinsa kuwa bayan barinsu daga asibiti bayan sun bi bayan su Meenal ɗin suka wuce gida cike da jimama da alhinin hakan, Baban nashi ya wuce gida shima ya wuce nashi gidan don kansa wani bala'in sara masa yake, don abubuwan duk sun zo masa ne But I was shocked, really shocked dan da ƙyar ya kai kansa parlourn gidan, yana isa ya zube ya riƙe kansa dake barazanar fashe masa, Sedai zaman nasa babu jimawa se ga shigowar Mahaifiyarsa nan, wacce tin kan ta iso masifarta ta ƙaraso. Wani rumtse rinannun jajayen idonsa yayi yana jin yadda ƙirjinsa ke bugawa. "Kana ina baƙin maye, wanda mace ta gama jikawa ta wanke ta baka ka shanye,to wllh ka sani zaman ka ya zo ƙarshe kai da wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar..." Sake rumtse rinannun jajayen idanuwansan ya sake yana riƙe kansa daidai da isowar ta parlourn babu wata wata tana zuwa ta zabgesa da mari ta ƙara masa wani . "Mara zuciyar da babu ƙirji a jikinsa, har macen take ɗauke da cikin shege amma kaci gaba da zaman aure da ita, dake kai ɗan Akuya?, to wllh yanzu yanzu ba sai an jima ba seka saki wannan mayyar yarinyar, in kuma ba haka ba in tsine maka kabi duniya dan ubanka Ahmad..." Tayi maganar tana huci. Kansa ya ɗago yana kallon mahaifiyar nasa yace "Yanzu saboda da wata ƙaddara kawai ta gitta tsakani shi ne kike cewa in saki Meenal Mamy?, wllh ina son ta ba zan iya rayuwa ba tare da ita, don ALLAH ki sassauta min Mamy ki janye kalamanki, ki tuna cewar ƙaddara tana kan kowa, kuma kowa be isa shallakemata ba. Don ALLAH Kiyi haƙuri mubi komai a sannu..." Jefa masa takarda da byro'n dake hannunta tayi tana me furta. "Wllh idan har baka rubuta mata kalmar sakinta anan ba, to ka sani daga yau na yafe ka daga cikin yarana kai ba ɗan dana haifa bane, kuma in yi maka bakin da se ɗeɗeta goben rayuwarka Ahmad, za ka sa ko kuwa?..." Rarrafawa gareta yayi yana riƙo ƙafafun mahaifiyar nasa yana mata magiyar ta taimaka ta rabu dashi dashi ta janye kalamanta akansa amma ba zai taɓa iya sakin Meenerl ba, idan ya saketa wllh mutawa ze yi.... "ALLAH ya tsin....... "BY AMMEY LAYLERH ✍️.... 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏.... Page 17&18 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Ai tin kafin ta ƙarasa yay wani hanzarin amsar peper da byro'n, idanunsa na zubar da wasu ruwan hawaye masu ɗaci da ƙona zuciya yayi rubuta mata sakin ya bata, tana amsa taga ɗaya tak ya mata tace se ya jere mata ukun nan cif cif..... Duk yadda yaso data taimaka ta bar shi hakan, amma haka taƙi sema bakin data sake buɗewar da niyar sake tsine masan, ya sake rubuta mata saki ukun, kana ta fice da takardar sakin a hannunta tana huci......... Kai tsaye gidansu Meenal ɗin ta wuce wacce dawowarsu kenan daga Asibitin wannan fitila'in sakin ya sake riskarsu, komai bata ji ba game da sakin domin dama tasan zamansu dole ya ƙare Ya Ahmad ɗin,duk kuwa da iriyar ƙaunar junan da suke ma juna, amma tasan mahaifiyarsa ba zata taɓa barin hakan faruwa, se da ta tayi cin mutuncin da tijararta kana ta fice ga bar musu gidan ranta fesss yau dai ALLAH ya kawo mata hanya cikin sauƙi ta raba auren Ahmed ɗin da Meenerl, duk da kasancewar gwaggo Sadiya ba uwarta bace amma seda taji babu daɗi da ababuwan da suka faru da Meenal ɗin,amma kuma ko a fuska bata nuna mata ba, amma dake jajen ciki na munafunci ne shi ta mata, har da cewa ai ƙara da ALLAH ya ɓarar da cikin suma shi ne kwanciyar hankalinsu. Baffa kuwa da Ya Sadeeq ɗin idan hankalinsu yayi dubu to a tashe yake sakamakon sakin nan na Ahmad, wanda bayan sallarn isha'a ya ƙira Baffa ya ringa kuka yana cewa ya yafe masa haka ALLAH ya gama tsara iyaka rayuwar auren da za suyi kenan dama cikin 1 year's kawai, wacce ma saura 1 months su cika shekara ɗin cif da cif, kwantar masa da hankali sosai Baffan yayi yace ba komai Ubangiji yasa hakan shi ne mafi alhairinsu gaba ɗaya, Ya Sadeeq ma sosai yaji maganar sakin har cikin zuciyarsa amma kuma se ya fawwalama ALLAH shi ma, abu kamar wasa se gashi da dare Meenal ta gaza runtsawa, magabar sakin duk bata dameta se da tazo kwanciyar. Nan idanunta suka sake ƙaiƙashewa suka soye sabo da tsabar azabar da take amsa daga gare su, Idanunta ta rumtse ko zata ji sun rage daga zogin da suke mata, amma kuma ina babu damar hakan, sema jin da tayi kamar ba zasu iya buɗe mata ba, Wayar tane ta kawo haske alamar shigowar text message kasancewar a silent take, kamar ba zata ɗauka ba amma kuma ta miƙa hannunta da kyar tana janyo wayar, tana kallar test messages ne ta sake kife wayar ba tare data duba taga ko miye ba, don kai tsaye ta san MTN ne don su ne masu mata haka. Alwala ta miƙe ta dauro ta fito ta fuskanci alƙibla, bayan ta idar da sallolin data ringa yi ta ɗauka Alqur'ani ta hau karatu har zuwa sallan asuba, bayan ta idar da sallan asuba ɗin tayi adda'o'i masu kyau da girma kana anan wurin wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, wanda baya farka ba se wajajen sha ɗaya da rabi, wanka ta fito nan tsakar gidan tayi kana gwaggo Sadiya ta miƙa mata abin kari, kanta kawai ta jijjiga don ba zata iya cin komai ba adai halin da take ciki. Wayar tane ta shiga ruri tana ɗauka taga Maman Yasmin ce makwabciyarta, jiki a matukar sanyaye ta ɗauka wayar ta amsata.... "Meenerl abinda ya faru kenan?" Ta faɗi a raunace domin sosai suke mutumci babu laifi a zaman nasu, dake duk komai da komai be fita ba se a jiyan, zancen sakin kuwa tuni uban kowa har ya sani a cikin anguwar tasu, don yau wajajen karfe goman safe Maman Ahmad ta sake komawa gidan, taje da garada ta saka suka ringa fito da kayan Meenal ɗin har ƙofar gida, inda nan fa yan anguwar suka yi dafifi wasu cike da tausayin Meenal ɗin, wasu kuwa haka kawai suna mata ala ƙara ba tare data tare musu komai ba. A lokacin da dake wannan aika aikar kuwa a lokacin Ahmad ɗin na ciki yana jinyar zuciyarsa don ko gangar jikinsa da kyar take ɗaukarsa. Yana a wannan halin ya fito don jin kwarabniyar tayi yawa, a lokacin da yake kallar Mamyn nasa tana wannan aika aikar ƙiris ne ya sa zuciyarsa bata ƙarasa ficewa a gangar jikinsa ba, da kuma ya mata magana tace kul be rufe mata baki ba yanzu taci mutumcinsa. Shi ne ya koma gefe yay ƙiran Ya Sadeeq ya faɗa masa muryansa ko fita ba yayi sosai. Dan da nan kuwa sega Ya Sadeeq ɗin har ya ƙaraso da wata motar ɗibar kaya, har kuma lokacin Mamyn nasa nan kaf komai daya danganci Meenal seda ta fito da shi, haƙuri ya ta be Ya Sadeeq ɗin yace masa babu komai haka dama rayuwa ta gada. Daga haka suka hau kashe kayan Meenal ɗin suna zubasu cikin motar da yazo da ita ta wurin da yake aiki, koda yaje shagon waje Baffansu ya buɗe musu suka jibge kayan. Aka ware mata iyaka na sawarta kawai a gefe guda da nufin nan da kamar 1 week se a bata kar abun ya mata kusa da yawa. Bayan sun kammala wayar da Maman Yasmin ɗin har zata ajje wayar wani abu me kama da transper na kuɗi ya ɗauki hankalinta, don haka kai tsaye ta shige cikin sakon, kuɗi ne zunzurutun kudi har naira dubu ɗari biyar, me ɗauke da account na Ya Ahmad ɗin ta, jikinta na rawa ta fito daga cikin amoung balance nata messages ɗin dake ƙasar sakon kuɗin ya sake ɗaukan hankalinta don shima ɗauke yake da sunar Ya Ahmad ɗin, tana buɗe sakon bata san lokacin da kukan da tayi ta roƙon jiya su zubo mata ba se gashi kai tsaye na saƙƙo mata, kanta take dan jujjuya a cikin zuciyarta tana sake maimaita abinda sakon yake ɗauke dashi..... _Tun daga numfashishinmu na farko bayan wanzuwarmu a doron ƙasa,sakanni suke gangarawa cikin mintoci, hakan ne yake bayuwa zuwa ga kowacce Sa'ar dake shuɗewa. Badan komai ba sai dan ta samar da ranakun da muke kidaya makwannin da suke haifar da kowanne da kowanne watan da ke yiwa rayuwarmu giɓi, kwanci tashi nake lissafin watanni da tunanin rayuwarmu, har zuwa jerantuwar da lissafin shekarun da suka shige mana a baya, Amma idan na tuna cewar ALLAH baya buƙatarr fassara, yana ganin irin girman damuwarmu,yana kuma sane da irin girman ƙaddarar dake tare damu, kuma shi ne zai shirya bamu mafita kamar yacce yace kayan cewa. Tabbas In sha ALLAHU ba zaki taɓa tozarta ba meenoh!, Kiyi hakuri na rabu dake ba wai saboda kin sanja bane, Na rabu dake ba wai saboda na gaji dake bane, Na rabu dake ba wai dan akwai wata a rai na bane, shiru na kuma a gareki ba kiyayya bace, nisanta wa ta ba rauni bane,kawai ina yaƙi da zuciyata ne, ki gafartamin canzawar dana miki Meenoh a duk tsayin watannin da suka shude mana, ki kuma yafewa Hajiyata duk irin abubuwan data ringa miki wanda samm ni a karan kaina ko hakan bana son tunawa, ki ɗauka cewar wannan ɗin Ita ce ƙaddarar mu, zanci gaba da miki adda'ar Ubangiji yaci gaba da baki kariya a koda yaushe!, Ki ringa yawan tunawa kuma da cewar. Har abada akwai waɗan da zuciyarmu ba zata taɓa dena ƙaunarsu ba, saboda girman halaccinsu garemu na gode My Ameenatou......._ Tana karantawa wani kalan kuka ya taho mata a guje amma tayi hanzarin sanya hannunta ta toshe bakin. Wani kalan rumtse idonta tayi tana ƙanƙame wayar nata cikin jikinta, tana a wannan yanayin se ga shigowar Shareefah a guje da kuka ta faɗa jikinta, wani kalan kuka Shareefah'n ta saki tana rungume yayar tata cike da ƙauna da tausayi me tsanani, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" Meenal ɗin tayi ƙarfin halin kamawa tana maimaitawa don ƙanwar nata ta ɗauka. Aikuwa ta kama suka ringa maimaita har zuwa lokacin da zuciyoyinsu suka ji sun yi sanyi, "Mummunar ƙaddarar data sake samun mu Kenan Yaya?, haka ALLAH ya sake wanzar da ikonsa akan ki kenan?, ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALINNNN koda yaushe, zamu ci gaba da ambatar kalmar cikin kowanne irin yanayi In sha ALLAHU...., Kiyi hakuri In sha ALLAHU wannan ma zai wuce yaya.." wani murmushi me ciwo tayi a matsayinta na wacce take amsar roldin uwa ta shiga kwantarma da Shareefah'n hankali, cikin muryan da yayi laushi sosai take shafa gadon bayan Shareefah ɗin ta ce. "ALLAH ma ya tsare My freind,komai yazo mana cikin sauƙi da amincinsa, ciki kuwa ya fita duk da kuwa cewar naso kayana,amma bana da ja ko hukunci akan duk abinda Ubangiji na ya zartar a kaina. ALLAH Ubangiji ya sake zama gatan mara gata yaci gaba da shiga cikin al' amurranmu yana zame mana jagora a koda yaushe..." Haka taci gaba da kwantar ma da ƙanwar nata hankali har seda taji Shareefah ɗin na maida numfashi a hankali alamun barcin ya ɗauketa, har tana sauƙe ajiyar zuciya kana yaji hankalin ta ya kwanta sosai, Itama se tayi ƙoƙarin zame kan Shareefah ɗin ta mayar mata kan pillow da gefen kafadarta tayi, sedai cikin barcin Shareefah'n ta ƙara janyo yayar nata jikinta tana gyara kwanciyarta a jikinta amman idonta dai a rufe, shiru kawai tayi tana bin ƙanwar nata da tayi lif a jikinta tana sauƙe ajiyar zuciya, gashi bata son ta farka haka kawai take jin bata son ƙanwar nata da kowacce kalan damuwar da zata sake zuwar mata, koda da misƙala zarratin ne, barin ma kalan wannan ɗin da yazo musu hagunce, ba tare da sunyi zata ko tsammanin hakan ba.Tunani barkatai taci gaba dayi akan rayuwarsu har ƙarfe kusan biyar da rabi, kana ta shiga motsawa ahankali, shiru kawai tayi har ta gama tashi bata motsa ba, adda'ar tashi daga bacci tayi a hankali tana zare janye jikinta a na ta, ƙura mata Ido tayi ta cikin ɗan duhun magrib ɗin daya kawo kai. Duk da irin tsananin damuwar da yayar nata take ciki amma hakan bai hana Kyan nan nata fitowa ba, fuskan nan sai glowing na kyau takeyi ko ina kuma a jikinta fresh, kana ta miƙe ta shige toilet bayan tabi yayar nata da adda'ar gamawa da duniya lafiya. Duk abinda Shareefah'n keyi kuwa a ɓangaren Meenal ɗin tana jinta, shiru kawai itama tayi ƙaunar ƴar gudaliyar ƙanwar nata na sake kamata, tana kwancen idanunta a rufe har Shareefah ta fito daga wankan, itama se taji bata son tashin yayar nata ƙara ta barta ta ɗan huta ko taji rangwame da sassaucin abinda ke sukar zuciyarta. Ita kuwa Meenal dake daga kwancen idanunta lumshe har bama tasan taja lokaci har haka ba, se da taji anata ƙiraye ƙirayen sallar magrib, da sauri ta mike tana fita itama, alwala tayo tazo ta tada sallah bayan ta idar ta ɗan kishin gida saman dardumar. Lumshe idonta tayi ababuwan da suka faru na sake nemar dawo mata daki daki, saurin kawar da tunanin hakan tayi tana lalubar kalmar YA WADUD tayi ta maimaita da kuma HASBIYALLAHU LA'ILAHA ILLA HUWA, ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHEEM AZEEM.... Tana nan zaune har aka yi isha'a kana suka fita tsakar gida da Baffa ya leka da kansa har ɗakin yace su fito suci abinci, duk jikinsu babu me kwarin gwiwar cin abincin amma haka suka fito, ALLAH yaso ma bame nauyi bane, yau matar gidan bata ga damar yin tuwo ba, jallop ɗin taliya da maccaroni tayi, se ruwan shayin data haɗa musu dashi, plat guda aka zuba musu me ɗan girma Meenerl tayi hanzarin cewa a rage amma Baffa yace suci iyaka cinsu in sun yi sauran a bama ko almajiri ɗaya ne. Rabi kuwa basu ciba duk da cewar yadda taliyan tayi daɗi, shayin dai sun sha da ɗan yawa kana aka ɗan taɓa fira wacce mafi yawanci nasihohi suka fi yawa, sai wajajen tara da rabi kana suka yi sallama kowa ya nufi makwancinsa, nan fa yauma baccin nan yaso yama Meenal gaddama, don kuwa yace baisan zance ba, amma albarkacin Shareefah da Adda'ar data fara tofa mata sama sama har bata san lokacin da baccin yayi awon gaba da ita ba, ba tare data san sanda ya ɗauke tan ba. Washe gari suna tashi bayan sunyi sallar asuba suka sake komawa se wajajen bakwai suka tashi, tare suka fita zuwa tsakar gidan duk kuwa da yanda Shareefah taso Yayar nata ta sake hutawa amma tace ta barta, idan ta barta a ɗakin ita ɗaya bata jin daɗi ne, haka suka kama aikin gidan a tare, se Shareefah'n ta kama shara wanke wanke tace Meenal ɗin tayi musu abin kari, kitchen nasu ta shige ta ɗora musu farar taliya ƴar Hausa da manja, ganin yajin gidan se a slow ne ya sa tayi saurin daka me daɗi kana ta sake ɗora musu ruwan tea yaji kayan ƙamshi. Tana gama dafa musu tea ɗin ta juye a flask, kana ta gyara komai data bata ta ɗebi ruwan zafin data ɗora musu ya yawa ta shiga wanka, tana fitowa Shareefah ta shiga itama, bayan ta gama shafa mai wata doguwar riga ta zira ta yadi kana ta fito daidai shigowar Shareef. A zaune taga Baffansu saman tafarma, tsakar gidan nan yayi ƙal ƙal gwanin birgewar sharar da yasha, gefensa gwaggo Sadiya se famar hamma take tana wani murza idon daya bada alamun yanzu nema take tashi a baccin, ɗan murmushi kawai Meenal tayi tana ƙarasa fitowa cikin kaunar ta take ma Baffanta da baya taɓa ɓoyuwa a fuskata tace "Barka da safiya Baffa!". Murmushi yai me kyau yana me furta. "Barkanmu dai Ameenatou!, fatar kina lafiya?" "Lafiya ALHAMDULILLAH" ta bashi amsa tana tashi cilak ta ɗebo musu kayan karin, gwaggo Sadiyan ce ta zuzzubama kowa kana ta ɗauka nasu da niyar shigewa ɗaki, amma Baffa yace ta dawo ta zauna yana kwalama Shareefah ƙira kan tayi tayi ta fito, don ya santa da nauyi akan komai. Bayan sun karya kana suka miƙe suka nufi ɗakinsu. Kallon Shareefah dake shirin kwanciya Meenerl tayi data riƙe bakin ganin wai kwanciya ne ma za tayi, "Ke Shareefah baki san zaki iya makara ba?" Kallonta Shareefah'n tayi tare da cewa "Wai me kike nufi da nine Yaya Meenal?, nufinki daga zuwa yau ɗin shikenan se in ɗebi jiki in koma yau kuma?, cab wllh da sake, ai sena cinye satin nan tsaf tare dake..." Murmushi Meenal ɗin tayi me cike da dattako tace "Yanzu ke Shareefah ko wani yace ki zauna ki cinye satin seki yarda ki zauna karatun duk da aka muku ya tafi a banza?" Turo madaidaicin bakinta gaba tayi kana tace. "A tinaninki kenan ai, ga yawa ne nan ta waya zanka amsar duk lesson ɗin da ake mana...." "To ai shikenan, ke kuma ALLAH ya taro min ke..." ★.. Zaune suke a lafiyayyan palourn gidan nasu kusan dukansu , tin daga kan Ikleemerh Ummiensa,Daddy se Dr Bilal shima, kusan tin da suka zaune kowa shi kaɗai ake jira ya fito su fara dinner, amma haka suka share fiye da fin 30 minutes a zaunen da suke zamar jiransa, ita kanta Ayla ta gama matsuwar Papa'n nata ya fito, sedai hakan be sa ya fito ɗin ba, wanda har ƙiransa a waya se da Bilal yayi amma wayan a kashe, don haka Daddy kawai ya basu umarnin su fara cin abincin nasu kawai, Ɗan saurin kallon Daddy'n Ummiensu tayi jin yace su fara cin abincin wai, wacce take sanye cikin wani mayen lace ruwan ƙasa, an masa zane zane da sky sak mai matuƙar tsadar gaske wacce ta haska farar fatar ta, wanda kallo ɗaya zaka mata kasan cewar ita ɗin ba baya bace wajen tattali da kuma tsaftar jikinta, wacce zata kai shekaru 45/47 haka, Amma jikin ta bai nuna ba saboda tana da jiki nai kyau ga kuma uwa uba kulawar da yake samu, wanda kai tsaye ma ba ka isa cewar ita ne ta haifa wannan zabgegen matashin magidancin kamar Majeed ba. Shima kallonta Daddy'n yayi yana sakar mata murmushi mai cike da SO ɗin nan, "Afwan ummien Majeed, wato nace kar mu jira shalalenki shi ne kike wani tsare ni da ido" yayi maganar yana kallonta da itama take sake mayar masa da martanin murmushin tai tana masa wani kallo na ƙasan ido. Wayarsa ya ɗauka kai tsaye yana dokama Majeed ɗin ƙira, kai tsaye ya bashi umarnin ya fito ƙasa shi kaɗai suke jira, wani yamutse fuskarsa yayi shi fa badon Daddy bane da kansa ya ƙira shi wllh da babu inda yay niyar zuwa, bare wani cin abincin da sun san ba woni ci sosai yake ba, don ze iya fita yaje ya dawo ma ba tare dako ruwa yasha ba kaɗan kenan daga cikin aikinsa. Tamkar wanda yake gabansa haka Daddy'n ya gyaɗa kai kawai yana maida kallonsa ga ummien yace "Se a dai na min wani gani gani kuma ko Hajiya na ƙira Shalelen naki" ba'a ɗau wani lokaci mai tsayi ba kuwa suka fara jiyo takunsa daya ratso palourn, don haka tamkar wani bako ko wanda basu taɓa gani ba gaba ɗayansu suka zubama ƙofar shigowa palourn ido duk da kuwa sun san ko waye zai shigo ɗin kuwa. Cikin takun dake nuna ko a jikinsa ya shigo palourn, yana sanye da riga da wando masu taushi brown colour, saidai rigar irin armless ɗin nan ce ga ta kuma ya ɗan buɗe botir na gaban rigar guda uku, wanda hakan ya bayyana ƙirjinsa a waje, ƙafarsa sanye da versace slipper's masu taushi irin room parlourn nan, cikin takun jarumta ya karaso tsaƙiyar palourn bayan ya cire takalmin sa daga bakin grass carpet ɗin dake tsaƙiyar dining ɗin, binsa da kallo ummie tayi tana girgiza kanta ganin yanayin da har zuwa yanzun yake a cikin bame kyau bane, a natse yakai zaune kan farar chiar ɗin data saura yana me furta. "Evening Daddy" ba tare daya jira amsar saba ya juya ga ummien nasa ita ma yace "Evening Ummiena" kana Ikleemerh da Ayla suka shiga rige rigen fara gai dashi, ɗan hararansa Dr Bilal yayi yana kallon Daddy yace.. "Wato ni ka gama rainani nine ba zaka gaida ba ko?, Daddy Don ALLAH ban fi wannan yaron ba???." Dr Bilal ɗin ya faɗi yana wani turo bakinsa gaba, wanda yake ɗan gidan yayan Daddy'n ne, sedai iyayensa basa Nigeria suna Istanbul..... Wanda shi kuma kishin Majeed ɗin ne yasa yafi son zaman nan ɗin fiye da can, Wani kallo Majeed ɗin ya wurga masa kafin ya shiga motsa bakinsa kamar wanda ke tsoron yin maganar yace... "Koma dai miye ni ban yarda ba, sabo da karka manta ni har budurwar Ƴa gareni ƴar five year's wacce take ƙoƙarin shiga ta 6, ga kalla kuwa ta ina zan yarda cewan ka fini???.... Kuma ai ko makaho ya laluba yasan daidai, dan ubanka Yayan Fahaad shi ne Sa'a na bama Abdul-maleek..." Yayi maganar yana wani yamutse fuska kamar yaga kashi, kana ya shiga duba apple watch ɗin dake ɗaure a tsintaiyar hannun sa na hagu ganin pass 9 na ƙoƙarin shigowa ya kalla Daddy'n nasa da su har sun riga sun fara cin abincinsu yace "Zan iya tafiya?" Bayan yasha apple juice kawai. Shi dai Bilal in banda aikin hararansa babu abinda yake. Girar sa ta hagu ya ɗan sosa jin Daddy'n yace babu inda zai tafi sau yaci abinci, gwalo Bilal ya masa daya saka Majeed ɗin ɗaukan robar da yasha apple juice ɗin ya jefe shi da ita, kare jifar yayi da hannunsa yana dariya yana cewa ai ba shi yakar zomon ba... Da kyar ya iya cin kaɗan don a cunkushe yake jin jikin nasa kana yasha ruwa ya mike bayan yama Ayla peack a goshi, don yau itama ko ƴan maganar bata samu ba, wanda itama yarinyar ta san duk wani motsi nashi don haka se baya woni takura masa ba.... Kai tsaye ya mike ya nufa samar sa. Binsa da kallo cike da tausayawa ummien tayi, a ranta tana adda'ar ALLAH ya kawo ma ɗan nata mafita da ɗaukinsa.... Ayla da har ta fara bacci Ikleemerh ta ɗauketa suka wuce dakinsu, sallama Dr Bilal ya musu shima yana nufar nasa ɓangaren da yake guda shima. MAJEED Drectly yana isa ɓangaren nasa yakai zaune kan wata ƙerarriyar silver chiar. Yana kwantar da kansa da jikin kujerar, lallausar rigar amrless ɗin dake jikinsa ta wani lafe a dark shiny skin nashi, wanda kai tsaye ke bayyanar da asalin hutu da luxurious life ɗin da yake cikinsa. Fuskar nan kai tsaye dake bayyanar da kwantacciyar damuwar da yake a cikinta, tin daga lokacin daya fara ɗora idonsa a kanta. System ce a gabansa ya zuba mata fararen idanuwansa, wanda a zahirin gaskiya bawai kallon system ɗin yake ba ya tafi ne duniya irin ta tunani.Wani zazzafan numfashi mara sauti ya fesar jin,yanda zuciyarsa ke ci gaba da sake karta masa a karo na ba adadi. Gaba ɗaya kansa nemar juye masa yaje da tunanin Ameenatou ɗin sa, wacce har gaban abada yake jin bazai taɓa iya haɗa sonta dana ko wacce mace ba, duk wata macen da zai so to ta biyo bayanta. Duk da cewar Ƙaddara ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar ƙaddararsa, ta raba su rabuwa kuma irin ta har gaban abada ɗin nan , Wani gauron numfashi ya kawo yana sake zubama laptop nashi farare ƙal ɗin idanuwansa. Pisc na ameenatou ne tare dashi da sukayi a Goa bakin wani gaɓar ruwa, ga ɗan ƙaramin matashin cikin tanan daya bayyana tana sanye da wata faffaɗar rigar slik fara me kyau, da wando ash me faɗi shima kanta da farar hura daya zame sosai, ganan kwantaccen baki wulik ɗin gashinta ya bayyana da yake har gaban goshinta. Farar fuskarta me kyau ɗauke da murmushin da baya taɓa mantawa dashi, wanda suna shan ice cream ne ta shanye nata shi kuma yana cikin shan nashi ta warce masa tana masa gwalo fuskanta ɗauke da wadataccen murmushin ta me kyau, da komai da komai kalan nata ne Ayla ta ɗauko,duhun fatarsa ne kawai kega yarinyar farin ne kawai na uwar bata dauko ba, se maganan da suke sakk irin nashi da baki bakinta.... Pisc ɗin yake kalla a cikin laptop nashi idanuwansa har kalan bala'i bala'in yaji suke mai na tsananin damuwar da yake son cusama kansa, yasha zama irin haka idan abun duniyar suka ishe sa har kusan saɓo yake wani sa'in, amma kuma idan yay duba da yadda Ubangiji ke juya lamuransa daga kyawawa zuwa munana se ya sake jinjina lamari na ubangijin da babu kamarsa a duniya, dan kuwa shine kaɗai wanda ya isa yayi abinda babu wanda ya isa juya hakan. dan yana da tabbacin idan wani na juya ƙaddarar wani da tuni ya jima da fara juya nashi ƙaddarar, yasan kaf cikin duniyar nan ya tabbata babu abinda ya rasa a rayuwarsa se ita, se sauran mataye biyun da suka bayanta ma wato Ramlah da kuma Fareedah. Se dai wannan maganar ta *TUN RAN GINI* da tsarin ƙaddararsu ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wanne bawa nashi, amma duk da haka bazai gajiya ba wajen kaima ALLAH kukansa kan kawo masa mafitarsa cikin wannan hali da yake ciki. Janye fararen idanuwansa da sukai ja yayi a kan laptop ɗin a sanyaye kuma ya maida ya rufe yana sauƙe numfashi me zafin gaske, kana ya nufa bathroom,wanka yayo yayi nafila kana ya kwanta zuciyarsa cike da sake saken ababuwa.... Har besan lokacin da wani nannuya wahaltaccen bacci yin gaba da shi ba.... Meenerl.... Gaba ɗaya yinin ranar ta yau ta sake yinsa gata nan gata nan ne, barin ma makwafta da mutanen anguwa da suka ringa shigo mata jaje, wasu kuwa dama da gayya suke zuwa su yayyaɓa mata magana a matsayin jajantawa suke mata, har da masu ce mata ai tama godema ALLAH da cikin ya fita shikenan babu ita babi idda ko a yau taga damar sake wani auren za tayi, duk cikin masu zuwan babu wanda ya taɓa tankama, daga ƙarshe ma se ta wuce dakinsu se yamma kana ta dawo tsakar gidan, zama tayi tace Shareefah ta mata kitso, suna cikin kitson sega shigowar Bilkisu nan daga wurin bikin da taje. Ciki a sanyaye ta ƙaraso don ummar ta harta riga ta sanar mata da komai, wacce matuƙar tausayin yayar nasu ya sake rufeta da ganin nata kawai zai ne a gida. Idonta fall da ruwan hawaye ta zauna tana gaida yayar nasu tare da jajanta mata lamarin, da cewa ALLAH ya rufa asiri ya tsare gaba. Da Amin suka amsa ita da Shareefah sega fitowar gwaggo daga ɗakinta ta fara masifar wato ko wurinta ba zata shigo ba shi ne ta tsaya a wurinsu, da uban wani ne yace karta kama kanta ko ita ta aikata ne bare ace ita ce silar ƙaddarar nata. Babu daɗi samm haka Bilkisun ta miƙe tana sake bama Meenal ɗin hakuri, ko da aka yi sallar isha'a se aka fito tsakar gidan zaman fira bayan anci abincin dare. Se dai shiru shiru Meenal daga shiga daki ɗaukan abu har yanzun shiru, tun Shareefah da Bilkisu na saka ran fitowa Meenal ɗin har su hakura. Ita kuwa Meenal a nata ɓangaren tana shigewa ciki duk da ba barci take ji ba, se kawai tayi kwanciyarta don tun safiyar ranar take wani sukuku da ita kamar marar lafiya. Akan sallayan da tayi Sallah ta zauna tayi shiru tana istigifari ga ALLAH da Salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama, duk yanda tunani yaso ya bijiro mata saida ta kawar dashi kawai ta fawwalawa ALLAH lamarinta tasan duk rintsi yana tare da ita, a haka har bacci yaci ƙarfin ta ba tare data shiryama hakan ba. Cikin kwanaki uku amma anguwar ta gama haɗewa da zancen wannan zancen abinda ya sama Meenal ɗin, Nan kuwa mutanen anguwa harma da tsallakenta aka samu abin yamaɗiɗi a unguwar, Gaba ɗaya se suka sako Meenal a gaba har seda Shareefah ta yankama ɗaya daga cikin munafukan katin rashin mutumci kana sauran suka shiga taitayinsu, wannan abu da Shareefah tayi shi ne ya ɗan kwato Meenal ɗin daga munafukan anguwar. "Yahanasu...." Abban Ahmad ya wani irin ƙiran sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa dake wurin rawan jiki. Don ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Umman Ahmad ɗin keyi akan duk wani abu daya danganci Ahmad ɗin. Bakinta dake rawa ta buɗe da kyar tace "I'm sorry Abban Ahmad, wllh sharrin shaidan ne" Ta furta muryan ta na rawa sosai. "I said get out my friend! Nace ko?" Gaba ɗaya se jikin yaran nasu yayi sanyi ganin dai da gasken gaske mahaifin nasu ya rantse se tabar masa gidansa itama, in yaso se taji idan sakin da daɗi itama. Be sama labarin sakin data titseye Ahmad ɗin yama Meenal ba se a wayewar yau daya kasance kwanaki huɗu kenan da faruwar abun. Don haka yace itama wllh se ta bar masa nasa gidan se lokacin daya ne mata, domin dama ya jima da mugun gundura da halin nata, kawai yana dauke kai ne sabo da yaransu, to amma tun da ta nuna masa iyakarsa da cewar shi be isa ba to ya rantse a yau ba sai gobe ba seta bar masa gidansa. Ahmad ɗin idanunsa sunyi jajir ya nufa Abban nasa yana bashi hakuri shima ya buga masa wata tsawa yace ya fice ya bar masa gida. Fatima kuwa wani irin kuka take na nadamar halayen momin nasu marasa kyau. Ta buɗe baki da niyar sake bashi wani hakurin ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba, tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta ko sauran mafaka, Jiki a sanyaye Ahmad ɗin ya fice a parlourn nasu itama Fatima ta wuce nata ɗakin. Ita kuma Umman nasu da jikinta ke rawa ne ta wuce ɗakinta babu jimawa se gata ta fito da hijjab ɗin bata fiye yawan da shiba. Ganin daga se himar nata ne ya saka shi sake buga mata tsawa yana cewa maza ta haɗo kayanta a akwatu don ba nan kusa zai nemeta ba, har se lokacin data dawo da Meenal ɗakinta. Sosai ta sake razana da lamarin wata muguwar nadama na sake kamata, tana jin tsanar mugwayen halayenta da har yay sanadiyyar rabata da bugun numfashinta wato Abban, don ba ƙaramin mahaukacin SO take masa ba. Shi yasa ma take taka tsantsan da duk wani abinda ya shafe sa, amma se gashi yau saboda wata watsatstsiya can daban har yana mata barazana da nata auren, sosai ta sake jin tsanar Meenal ɗin a cikin rai da ruhinta. Babu jimawa se gata ta fito da akwatun ta taf da kaya ta fice tana jan majina, ido yayi fulin fulin tsabar kuka... Kai tsaye daga nan gidan su Meenal ɗin tama tsinke, taje ta sake yayyaɓa maganganunta san ranta, har da cewa yo dama ita yar malamai ba dole ubanta ya shiga tsakanin zaman lafiyarta da mijinta ba, daidai kuma Baffa ya kawo kansa lokacin da take faɗar kalaman nata, don haka ya ƙaraso yace da ita. Ta sani ita data koma gidan ɗan nata har abada, domin ta gama zaman aure dashi, tana nan zaune In sha ALLAHU se taga mijin Meenal ɗin zata aura ko ba jima ko ba daɗe, kuma taje duk abinda tayi kanta, se da Baffa ya mata tasss kana ya komar da Meenal ɗakinta da idanunta suka sake rinewa sosai, Runtse idanunta a karo na biyu tai tana ƙoƙarin kwatar numfashin ta dake barazana wa gangar jikinta. danne dukkan abinda ke yunƙuro mata tayi, tun da ga aurenta da Ahmad da irin baƙar tsanar da ummansa ke nuna mata haka kawai, har zuwa loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani, amma duk da haka baiwar ALLAH'r nan ba zata barta ta huta haka nan ba, se tayi ƙoƙarin mantawa da abu kana se wasu mutane su sake tado mata da danyen raunin da ya dauka hanyar warkewa.Lallai ta sake yarda duk inda Kalmar KADDARA take, lallai kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu yawan gaske a cikinta, domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwa juna. haka kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar ita ta amshi nata da hannu bibbiyu In sha ALLAHU, kamar yanda Baffan ta yasha ce mata Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin rayuwarsa game da duk abinda ALLAH ya riga tsara masa, to kuwa lallai kayi hakuri da duk abinda ALLAH ya tsara maka domin kuwa shi ne mafi alkhayri agareka. Sake Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake jujjaya mata. Maganganun Umman Ahmad ɗin na son haifar mata da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar hakan faruwa. Domin kuwa ita ɗin mutumce me tsananin ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama dama yay crossed nata mind ba, duk yadda maganganun suka so haukata kanta amma ƙin bama hakan dama tayi. Lumshe idonta tayi ta taji hawayen da suka tara nemar zubo mata, amma ta sake shanye hakan har tana jin yadda jinin jikinta ke wani irin harmutsawa tamkar ana aza wuta a jinin jikintan haka take ji, shigowar Shareefah ne ya sakata ɗago rinannun idanunta ta zuba mata, zuwa loƙacin kuma jikinta har rawa yake a mugun wahalce ta nufi jikin Shareefah'n , dama tasan ita ɗince ta biyo ta lallashi bayanta. Rungumeta kawai Shareefah ɗin tayi tana bata baki da haƙuri. Ganin duk yacce Shareefah'n tabi ta ruɗe ne ya sanya Meenal ɗin ɗan janye jikinta ana Shareefah 'n tare da ƙaƙaro murmushin dole wai duk don ta kwantar mata da hankali. Saidai zubowar ruwan wahayen dake yankar zuciyarta da bala'i bala'in zafi da ƙunar da suka kusa haifar mata attack take ne ya saka Shareefah fashewa da nata kukan itama, jin yadda jikin yayar nata ke jijjiga...... _The comments are dropping. 😔 ko dai baya muku daɗi ne? Naga ba comments ba reactions naku._ _Please don't be a silent reader. Comment, vote and share. Thank you 👏👏👏_ _Love you all my mutanena Amanana😘🫂_ _Put a smile on my face please. Vote, comment, and share My lovely friend's ana tare_ # Voice of the innocence # Team AMEENEERH SHEHU USMAN where Are You??? _Team Meenal wai kuna ina ne haka? meke meke shirin faruwa daku haka?_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏.... Page 19&20 ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ ƙarar data fasa ne ya saka Ya Sadeeq da Baffa da Bilkisu har dama gwaggo rige rigen shigowa dakin nasu. A sanƙame suka ganta jikin Shareefah ɗin gaba ɗaya jijiyar kanta sun gama fitowa sun yi ruɗu ruɗu. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Ya Sadeeq ya ambata shikenan abinda suke ta gudu ɗin ya faru, mutanen kan Meenal ɗin sun motsa, wani kalan tashi hankali muraratan kake kalla daga cikin idanun kowannensu, don kuwa jinya ce ta sau da tari ma sukan mance da cewar Meenal ɗin na ɗauke da ita, wanda suke kamar gadon mahaiyar tane tayo, idan tsanani yay tsanani suka tashi to sukan shafe tazarar kwanaki da suke ganin ace akai akai ɗin ne suke tashi, a wannan sanƙamen da take takan iya kaiwa har gobe uwar haka bata ko motsa ba, duk kuwa kalan ƙarfin adda'an da ake mata, idan suka tashi gaba ɗaya se hankalin kowa ya tashi, wannan shi ne karonta na uku kenan a tashin nasu, bata motsi bata numfashi babu alamar me rai tattare da ita. Se jijiyar babbar yatsarta kawai da take harbawa wanda shine zai baka tabbacin cewa tana da rai, a gabanta Ya Sadeeq ya zube yana amsar ta daga hannun Shareefah Baffa shima yakai tsugunne suna fara tofa mata adda'o'i masu kyau, har zuwa wani lokaci can cikin dare kana suka fita kowa ransa babu daɗi aka bar Shareefah da Bilkisu wacce da cewa yay gwaggo Sadiya ta kwana da ita tace wllh ba da ita ba, ita dai Bilkisun da taga zata iya bismilla to ga wuri na ta tsallake ta fita, su biyu kwana da ita a tsakiyar suna ci gaba da mata adda'a ɗin har bacci ya ɗauke su suma, bayan sun yi kukan sunyi har sun gode ALLAH. Ko washe gari haka yaran Malam suka ringa shigowa suna ma su Shareefah sannu dame jiki, ido duk yay jeme na alamar fita a hayyaci, Malam kuwa kusan kwana yayi zaune akan binciken ire iren matsalolin aljannu masu shige da nata, don haka da kyar ya samo wata hanya me ɗan tsauri. Da sassaucin abin ya tashi bayan Sallah a masallaci ya aiki Sadeeq Jigawa amso masa magungunan wurin hasalin tsohon malamin da ya koyar dashi. A asuba ɗin ya tafi sha biyu kuwa bata kai ba se gashi ya dawo da magungunan dana shaƙawa dana hayaƙi, wanda mafi ƙarfin cikinsu da saurin dawo da sinadaran ƙwaƙwalwa shi ne ɗan tumfafiyar da aka busar dashi a inuwa, tare da lafar ganyensa ɗaya da ɗan ɗaya se a rubuta _WALA YA HUDU HU HIFZU HUMA WA HUWAL ALIYUN ALIM, HASBINALLU LA I LA HA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHEEM AZEEM..._ SO za'a rubatasu ne a jimlamce matsayin kafa bakwai bakwai, idan ya bushe ya dake ya zama gari a shaƙama wanda yake fama da irin makamanciyar jinyar aljannu irin haka, ko me cutar farfaɗiya, to bi'izinillahi za'a sama waraka, se wasu manyan turarukan jinnul-Aashiq. Su zamfar su zauzau manyan turarukan jinnul-Aashiq ne, Shareefah fa ne ta shafe gaba ɗaya jikinta dashi wajen kala uku, kana ta kama hancinta tana cusa mata ciki, a take wata gigitacciyar hatshawa ta taho mata tana wani ƙoƙarin miƙewa a gigice, Ya Sadeeq da ya shigo yay hanzarin ɗamkar ta, wani ihun da kusan seda ya saka Baffa dake waje wurin almajirai kifawa, yayo gidan wasu maganganun da basu da kan gado ta shiga yi, tana wani jijjiga tana ƙoƙarin kwatar kanta daga mummunar riƙon da Ya Sadeeq ɗin ya mata, ahankali ahankali kuma jikinta ya shiga saki numfashinta na daidai ta koma yarab bayan a kan idonsu wani abu me kama da hayaƙi ya fita ta cikin goshinta. Wata ijiyar zuciyar data saka kowa sakin tashi shima ta saki tana laluben hannun Shareefah... Umman Ahmad kuwa a lokacin da ta kai gidan ƙanwar mahaifiyarta Hajja ta zayyane mata komai, dake Hajja ɗin ba kanwar lasa bace itama tayi kanta tana faɗan ina ruwanta da rayuwar auren yaron nata?, wannan abu shi sake tuƙe zuciyarta har munanan kalaman Mijin nata suka shiga dawo mata daki daki........ "Bana son kicemin komai Yahanasu domin kuwa komai ɗin ya isa haka nan!, Na riga da na gaji da munanan halayenki Yahanasu, wallahi kinji na rantsema awannan karon kam babu makawa se kin tafi, tin har kika saka ɗan ki ya saki matarsa alhalin yana sonta, yanzu ki dubi halin da yaron naki yake ciki ko tausaya masa ba zakiyiba, ke kuwa wacce iriyar uwa ce data fiye son kanta da yawa uyhmmmm?, Karfa ki manta kema kina da yara matan nan har biyu, akwai Amina ga kuma Fatima kuma ke kin ma yima kanki adalci kuwa har dan ita uwar mijin Aminan tana takurata itama ki ringa tsine mata?, kin ga ashe babu daɗi ma kenan, baki isa ƙuntatama ƴar wasu kuma ke kice naki Ƴaƴan su zauna ƙalau a nasu gidajen ba, ƙarya ma kenan never wllh. Don haka kema dole kiji irin raɗaɗi da baƙin cikin dake cikin tozarcin aure........." Haka kalaman Mijin nata ya katse ta a lokacin suna yin dinner da yaranta ta hanyar faɗan haka cikin wani irin mugun ɓacin ran da bata taɓa ganinsa a ciki ba.... A lokacin jajayen idanunta ta ɗago tana kallarsa cike da wani kalan mamakinsa. Wani irin tsannin baƙin cikin ne taji ya mugun turnuƙeta, babban abun takaicin ma shima shine a gaban yaranta ya mata hakan, ji tayi kanta na nemar zare mata don tsananin sarawan da yake mata kamar zai rabe gida biyu, a lokacin da take tunawa da maganganun nasa, tashi tayi ta bar parlourn wacce take madadin uwa a gare ta ko iya kallon gabanta batayi sabo da tsantsanr ɓacin ran dake cunkushe da ita, har tana fidda wani numfashi mai zafi. Haka ta wuce uwar ɗakan Mamar tata tana sharce hawaye, se gashi abu kamar wasa ko Fatima Abban ya hana zuwa inda uwar take, bare me dungurin uwar du ɗin Ahmad, wasa wasa har ta cinye satin farko ta shiga na biyu, idan ta ƙira wayarsa baya taɓa amsawa, tin da ya taɓa bata amsar cewa sai idan buɗar ido kawai yay yaga Meenerl ta dawo ɗakinta, kuma har gida ya sake zuwa shida Ahmad ɗin suka sake bama Baffa hakuri yace wllh babu komai, amma zancen kome kam babu shi, haka ma sun gode ALLAH ya amfana zaman da aka yi baya, Umman bata tashi aune ba se ganin katin ɗaurin auren Abban tayi ita da wata tsohuwar aminiyarta ta ƙut da ƙut, da duk wani tafarkin rashin kirki ita ke ɗorata akai ta aure mata mijin, aikuwa tayi kukan kura irin na mahaukatan nan ta buzanta taje har gidan ƙawar nata me suna Lubna suka kwashe tsiran karen mahaukaciya da ita, ta ce ita ai bata faɗa da mahaukata jahilai sedai da masu hankali. Aure ne kuma ta kwantar da hankalinta kamar anyi an gama ne ita da masoyinta IBRAHIM SHAREEF, tace mata babu boka babu malam kamar yadda ta sani a tsarin shedules nata, amma kuma tsantsanr makirci da kisiisina za suyi aikinsu da kyau, kuma ta zuba ido tayi kallon ikon ALLAH. Anan sema ta rasa bakin magana taje gida kuma zata ma Maman nata rashin m ta dakatar da ita ta hanyar mata tass,tace ai da lokacin da take bata shawarwari akan ƙawayen banza bata ji, gani take ma lokacin da ba ita ta haife ta bane take mata hassada, har takai ta kawo seda ta ɗauke ƙafarta cakk daga gidan Maman da itace ta reneta tin daga haihuwa, wacce uwarta na haihuwar ta ta mutu, wacce kuma a lokacin uban ita yahanasun da take aure yace ba zai riƙe taba shima rashin sa'a da baƙin halin jaririyar ya shafe sa ko ya kashe saba, ita ta rene ta shayar da ita amma daga ƙarshe sakamakon data bata kenan na tsameta daga cikin rayuwarta gaba ɗaya, se da iftila'in rayuwar data gama koya mata hankali ya sameta kana ta tuna da ita, bayan auren da sati biyu sega takardar sakinta har biyu daga mijin nata ya aiko mata har gida, yace tun da ta gaza dawo da Meenal ɗin dakin nata, afujajan ta isa gidan su Meenal gaba ɗaya ta fita a hayyacinta babu alamar kowacce iriyar nutsuwa tattare da ita, haka ta din gama Baffa kuka da magiyar ya taimaka ya ceci AURENTA Meenal ta koma ɗakin ta, wanda ita kuwa zuwa lokacin ma har ta gama zubar da komai taci gaba da gudanar da rayuwar ta yacce ta zaɓa mata. Ca yay da ita Meenerl da gidan Ahmad kan babu kome amma maganar aurenta da tayi yacce wannan zai taimaka mata da ƙarfin adda'a har mijinta ya dawo gareta, yace kuma ta gane tabbas su malamai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ta inda wani malamin yana kallar ana cutata diyarsa a gidan auren ta amma ko jarkar rubutu daya ba zai taɓa bata ba da sunan mallake wani, kuma itama yace babu rubutun da zai mata amma taje za taga ikon ALLAH In sha ALLAHU.... Duk se jikinta yayi sanyi ta ringa rokar tafiyar Meenal ɗin tace babu komai ita dama bata taɓa riƙe taba, don kowa yayi na fari kai nasa. Cikin kwanaki uku kuwa Malam ɗin ya ƙira Alhaji Ibrahim Shareef ɗin har ƙofar gidansa ya masa nasiha,yace kuma ya sani auren Meenal dama ALLAH yayi bame tsayi bane, kawai dai ita ta zama sila ne, wanda dama komai da yake faruwa a cikin duniyar yana da sila ko sanadi, yace indai don akan auren Meenal ɗin ne ba niyar juyama matarsa baya yayi ba to yayi hakuri ya maida ta,nan jikin Abban Ahmad ɗin yayi sanyi ya sake godema Baffan ya nufi gidansu Maman kai tsaye, anan gaban Maman ya sake ƙare mata tanadi ya kuma warware mata duk maganganun da uban wacce tafi tsana ɗin fiye da komai ya sanya shi amincewa ya dawo da ita ɗakinta, kuka ta dinga yi tana cewa sharrin zuciyane dana shaidan amma In sha ALLAHU bata sakewa ta tuba,tuba kuma na har gaban abada wllh. ALLAH sarki akace uwa uwace duk kuma inda ɗan uwa yake daɗi ne, haka kafin ta koma Maman ta sake bata wasu sirrika irin nasu na tsofin da da su suke kame zuciyar mazajensu, ta kuma sake mata faɗa da nasiha sosai kana ta koma gidanta. Sannu a hankali ta ringa sace zuciyar mijin nata duk da dama can ita ɗin ce a ciki, sedai rashin kirkin ta yasa ta fita a kan nasa, Gyaran kwanakin da kawai tasha a wurin Maman nata da adda'a 'oin data ɗorata akai suka fara tasiri, tuni ta sake janyo zuciyar mijinta gare ta, adda'o'i kala kala Maman ta bata, har da wani sirri data bata ganin yadda Ibrahim ɗin ya ɗan wazana Yar nata, tace ta nemi tsamiya cikin tafin hannunta biyu, wacce ba'a bare ɗin nan ba se da kanta ita ta ɓareta ta jika a cikin ɗan kofi haka, daga safe zuwa dare zata barta ta jika, idan dare yayi se ta ɗauko kofin data jiƙa tsamaiyar nan nata se ta karanta YA WADUDU, ƙafa bakwai, kowacce ƙafa ɗaya ta tofa a cikin ruwan, bayan ta kammala seta shanye ruwan ta ce da yadda ta bare wannan tsamiyar ta shanye ruwan ta haka ta ɓare zuciyar mijinta ta shanye, ta ce ta bata wannan sirrin ne kuma ba dan ta yi cuta ko tun kaho ba, ta bata ne kawai don ta kwato ƴan cinta daga wurin mijin nata da ƙawa ta mata kwace.... Kwarai ta bata sirrika da yawa masu kyau irin na gargajiya.... ★.. Ahankali jirgin ɗaya taso daga ƙasar Istanbul ya fara landing a babban filin jirgin Aminu Kano, ahankali fasinja suka fara fitowa zuwa lokacin daya sanyi kansa shima a natse cikin layin passingee's ɗin dake fitowa a natse. Wata iska ya shaƙa ta ƙasarsa da kusan 3 months kenan da baya cikinta, sakamakon damuwar data kusa haifar masa da ciwon zuciya ya saka Daddy'n tattarasa ya komar wurin Yayansa ABDOUL-MAJEED, da dama sunansa ne Majeed ɗin yaci, Kansa a ƙasa ya fara tafiya yanajin kamar wacce aka yi safarar zuciyarsa daga wata ƙasa zuwa ƙasar ne, Taku yake yi cikin natsuwa wanda kallo ɗaya zaka masa kasan cewar ehhhh lallai MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ba ƙaramin jarumin namiji bane, yanda yaje kan matakin girmansa daya ɗara samartajarsa, se dai kyaun jikinsa ke ɓoye hasalin shekarunsa. duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai sedai yanayin murjewan fata dana jiki kawai wanda hasalin Luxury da Luxury suka gama ratsawa, se dai Yanayinsa kaɗai zaka kalla ka tabbatar da cewan lallai ba lafiyansa lau yaje ba .Amma darajar addininsa hadi karamci da kuma tsananin kwarjinin sa suka shanye yanayin san na kowanne irin halin da yake a ciki, Toyota Camry TRD ɗin da tazo ɗaukarsa ya nufa, sedai ga mamakinsa Bilal ne tare da Ikleemerh dama Ayla. Rumgume Ayla a jikinsa yayi yana sakin wata wahaltacciyar ijiyar zuciyar kewarta da kawai yayi. Hannu Bilal ɗin ya basa suka gaisa, Ikleemerh ma ta gaidasa ya amsa cikin kulawa kai tsaye suka lula zuwa gida... Meenerl.... Alhamdulillah abubuwa sunci gaba da gudana cikin rayuwarta, inda dama bata da wata idda akan ta sakamakon barin cikin da tayi, sosai Baffa da yan uwanta sune ƙoƙari akanta,kafin kace me har masoya sun yi ca a kanta ciki kuwa harda samari don sunce ai sauta ga wawa ce, tin da ko shakera ba tayi da auren ba kuma ta fito, gashi ko haihuwa ba tayi na, sedai bata taɓa kula kowa har se da Baffanta ya mata magana, yace ta ɗauki dangana kuma ai dole zata yi auren ba wai ta ƙare shi bane da wannan ƙananun shekarun nata, kuka ta saka masa a lokacin tace ita Allah tsoron mazanma take, tsoron tayi zaɓen tumun dare take yi, nan su Yaya Sadeeq suka yi ta bata baki, ga nan ma wani nan cikin anguwarsu daya nuna yana son nata amma taƙi, don matarsa bata da mutumci suna na gaba gaba wajen aibantata a lokacin da wannan ƙaddarar ta sameta, don haka tace bata son shi, ita ta ma rasa ta yadda aka yi mutane suka san da maganar sakin nata, ita da tin da abun ya faru zata iya irga fitanta dududu be fi uku zuwa huɗu ba ƙarewa maza suka mata Caaaa aka. Se dai ana tsaka da wannan danbarwa se ga bayyanuwar Alƙalin daya mata Shari'a, wato ALƘALI YAHAYA SHEHU ƊAN BATTA shima ya faso cikin maneman nata, wanda tsananin tausayinta a karon farko ne ya addabi rayuwarsa, bayan ya bibiya lamarinta har ya gano mijinta ya rabu da ita, sedai beyi gaggawa don se wajen wata na biyar kana ya bayyana, wanda kai tsaye kuma ta hannun Baffa ya biyo ganin shi ba yaro bane, kawai ra'ayinta za'a tambaya masa ita in tana yin sa shikenan, wannan karamci da Baffan ya masa ne yasa har yake jin har abada ba zai taɓa mantawa da shi ba,a lokacin da Baffanta yake tinkararta da maganar se taji ta ɗan fi samun nutsuwa akan sauran mane man nata, don haka Baffan ya bashi umarnin fitowa yace ba da gaggawa haka ba, don yana son su fahimci juna kafin komai, don shi rayuwar soyayya yake son suyi bata alfarma ko ta girmama juna ba, don yana son soyayya sosai gaskiya, ɗan dudu du ba zai wuce 40 year's ba. Kuma jikinsa a gine yake daidai misali don haka ya fara zuwa zance, Maganar aikinta da ada har zata koma ta koma baya, ɗaukarta yake yana kaita wuraren shaƙatawa yadda zata sake sakewa dashi, ta kuma manta da giɓin dake cikin rayuwarta cikin sauƙi. ALHAMDULILLAH kuma sun fara fahimtar juna har tana jin sa cikin zuciyarta, Dake anan cikin Kanon yake anguwar SHARAƊA PHASE 0, kuma matansa biyu ata uku zata je, sedai ba gida ɗaya zasu zauna ba amma Baffanta yace inda hali ya haɗesu a gida ɗayan, sama yana da wadataccen gidan kawai dai dan kar ya zama kamar ya tauyi haƙkin tane ya saka shi ware mata gidan, amma se da ya sake tambayarta tace ba komai ALLAH ya basu zaman lafiya. 3 months ya saka bikin domin akwai buƙatan yayi wasu ƴan gyare gayre, ana saura 2 weeks bikin aka kawo lefen da ya bama koma mamaki don kowa be sha har wani laife ze mata ba, amma ga mamakin kowa se ga akwatu har guda biyar da kaya na kece raini a ciki, dede da wayar hannunta ya jima da sake mata ya sai iphone 13 pro max. Kuma gata hannunta Pop 9 Tecno, se ta barma Shareefah Pop ɗin nata ita kuma ta bama Bilkisu nata da itama babbace babu laifi, gwaggo Sadiya dai kada ran kada han haka take tsakanin nasu. Se ta ga dama take shiga lamarinsu in bata so bata shiga, amma su basa taɓa renata, ko kayan lefen ma a dakin gwaggo Sadiyan yake.... Kuma sunci gaba da mutumcinsu da Dr pooja har takan zo mata ma. A lokacin da ya dawo Risach nata ya fara yi amma yaga bata dawo wurin aikin ta ba, don haka se ya cire duk wani abu daya danganceta yaci gaba da rayuwarsa kamar baya, Sedai yafi bama aikin company'nsa ƙarfi fiye da hospital ɗin, gashi ma shirye shiryen bikin Ikleemerh suke suma nan da 3 weeks....... Kwanci tashi aka ce asarar me rai se gashi har ranar tazo, sosai Meenerl ta sake yin kyau na musamman wanda farin cikin wannan aure babu ya Shareefah don tana kallar kamar wahalar yayar nata ne ya yanke yazo ƙarshe se dai aka ce kashh?..... Cikin nutsuwa da aminci aka gabatar da komai cikin kwanciyar hankali,sedan tin da ake abun babu mahaifiyar Alƙali ko kaɗan. Ranar da aka ɗaura mata Aure da Alƙalin ranar saura ƙiris Ahmad yabar duniya, amma kuma yana nan yana Adda'ar ALLAH ya fito da ita in yaso komar da ita, tin da dama haramta auren ai yayi, kuma zuwa yanzun Ummansa ta sake musulunta dan har wurin bikin ma tazo, tana sake kuka tana cewa ALLAH yasa Meenerl ɗin rabon ɗan tace, su a nufin su kamar tayi Auren kisan wuta kenan ta fito se ya sake aurenta, a ranta take jin batayi wannan auren don ta fito ba, kuma ko babu komai hankalinta ya sake kwanciya da Alƙali Yahaya Shehu ɗin tin da ya ɗan manyanta yasan darajar sosai, ita kuma dama can ba son ƴan bama bakwai ɗin nan tayi ba, sedai idan ta tuna cewar cikin mata uku zata shiga gabanta kan faduwa time to time, amma data gayama Yaya Sadeeq shi kuma ya faɗa ma Baffa se ya saka wani ɗalibi mata rubutu na tsawon sati guda, kuma Alhamdulillah ta rage jin hakan, har sauƙa Baffa ya mata tun da yaga wani shirun baya isar wa, kuɗinta da Ahmad ya turo mata lokacin daya mata sakin nan dubu ɗari biyar ta bama Baffa ya sake mata kaya masu kyau, duk da be so amsa ba amma haka ta matsa masa. Ankai ta gidanta lafiya bayan da akayi sallar isha'a, wasu daga cikin dangi suka mikata bayan sun shan koke koke ita da da Shareefah, dan haka Baffa ya hana rakiyan da ita yace daga baya taje. Dake da wata ƴar uwar ummansu dake ƙauye aka mata rakiyan, seda suka miƙata wurin kishiyoyinta inda ɗaya ta amshesu a mutumce ɗayar kuma ko zama bata bari sun yi ba ta ce ALLAH basu alkhairi ala kuma kade fitina, daga haka suka wuce nata bangaren da ita, nasiha suka mata sosai har da gwaggo Sadiya kana suka tafi suka barta cikin kewarsu da zata yi. Zuwa can wajajen tara da rabi sega Malam ango ya shigo ɓangaren amaryar tasa, jikinsa se fidda daddaɗan ƙamshi yake me cike da nutsuwa, tanajin shigowarsa gabanta ya yanke ya faɗi, amma tayi saurin ambatar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un cikin ranta, zame babbar rigarsa dake saman kayansa yayi yana ajjewa kan madubinta ruwan zuma, zama yayi daga gefenta yana sake saɓunta mata sallar da yayi, a ɗan tsorace ta amsa tana gaida shi cikin sanyin murya, jikinsa ya ɗan jawo ta yana ƙoƙarin zame mayafin dake kanta ta ɗan riƙe jikinta na ɗan rawa, a kunnenta ya raɗa masa wai da kar zafi ya miki illa ne, ga solar gidan naku ta kallace ta laso min kuɗi masu ɗan nauyi, dariya tayi ƙasa ƙasa ya miƙe yana shiga toilet, ya ɗan jima be fito ba don da dukkan alamu lodi ya rage ga amarya kuma se ɗan doddone hanci take, don fufu ɗin nashi akwai ɗan wari ba laifi... Yana fitowa ta dena doddone hancin cewa yay tayo alwala itama, shi ga tayi se famar zuƙe numfashi take dan har lokacin da wari warin fufu ɗin da yayi. Akan darduma ta tarar dashi yajasu sallarn raka'a biyu adda'a sosai ya musu ta zaman lafiya, kafin ya janyo lafiyayyun ledojin kajin daya shigo da su, plat ta sama a cikin locer ɗin madubinta kana ta ɗaurayo a ban daki ya zuba musu me ɗan dama, ita dai se kallonsa take don ba zata iya ci da yawa ba, kaɗan kuwa taci ta koshi shi kuwa ya buɗe ciki kamar ba'a gaban amarya yake ba yaci yay ƙat yay gatsa kana ya wanko bakinsa ya haye gado, jikinsa ya janyo ta gabanta nata faɗuwa, a kunne ya raɗa mata. "Da dukkan alamu wannan amaryar raguwace matsoraciya ce kuma me rowa, don haka ango yau ya ɗaga mata ƙafa amma ban da gobe...." Daga haka ya shigar da ita jikinsa bayan ya rage mata kayan jikinta suka kwanta. Washegari daya fita sallan asuba be dawo ba, ashe ɗakinsa ya wuce ya kwanta ƙarfe bakwai kuma ya fita wurin aiki lokacin daya leƙo tana bacci, tana zaune wata dattijuwa ta shigo da kayan kari tace itace me aikin gidan, duk abinda take buƙata zata iya mata magana, godiya ta mata kana ta saƙƙo tayi karin, a ɗarare ta ce matar ta rakata ɓangaren matayen, ta farkon dai a wani yankwane ta amsa gaisuwar data mata, ta biyun kuma da fara'anta , har tana tsokanarta ashe ma ƙanwar tasu ƴar shila, a dole mijin su ya nemi daya zauce musu. Anan da ɗan jima kafin rana ta tasa ta koma ɓangarenta, kafin dare har ta ware tayi wankanta cikin doguwan riga ta bacci me kyau, kwanciya yayi sedai babu jimawa yace ya shigo kissing ɗin goshinta yayi ta biyo sa, dogon hijjab har ƙasa ta saka bayan ta sake feshe jikinta da turare da humra kana ta fito, yana parlour a zaune yana jiranta kana ya kama hannunta suka nufi ɓangarensa daya kasance shima daban, Suna zuwa ya zare himar ɗin yana tsokanarta yau babu ɗaga kafa fa, murmushi tayi duk yacce gabanta ke faɗuwa amma haka ta daure, kwanciya a saman gadonsa yayi da yake ɗan cif da cif yana janyowata, hannunsa ya saka ya kashe wutan dakin yabar dum light me haske kaɗan, ahankalin ya soma mata wasu abubuwan, tin yana binta a hankali har se da kansa ya kwace ya bita a yadda yake so, sosai ya wahal da ita a daren, ɗan wajen 3 round ya mata, inda tayi da masa kuka da magiyar ya kyaleta,wanda dama a ka'ida bazawara kwana uku ake mata, da safe sosai ya sake bata kulawa sedai be sake yunƙurin mata komai ba, sedai kin fita ko ina yayi yana tare da jikinsa don shi kaɗai yasan kalan abinda yaji, don haka ya sharirince wajen bata duk wata kulawarsa, se da ya fita sallar zuhr kana ta gudu ɗakinta, ALLAH ma ya so ta bata haɗu da kowa ba har ta shige ɓangarenta duk tana jin kunyar kanta, idan ta tuno yadda ya ta mata wasu surutai kamar wani yaro ba babba ba, anan tayi har isha'a duk da se da ya biyota amma taƙi yarda ta bisa, ko da dare kafin ya shigo harta kwanta tayi baccin ƙarya, don wllh ita kunyar binsa take ƙara shi yazo hakan se yafi, tana kwance taji turo kofarsa da ƴar ƙaramar sallama, yana sanye da jallabiya fara ya isa har inda take kwance, zama yayi yana ɗagowa kanta ya ɗora akan cinyarsa yana sauƙe mata wani numfashi me ɗumi, cewa yay mata yau ma anan zasu kwana kenan kamar ranar farkon ta, ai kuwa ya mike yana zare jallabiyar jikinsa, saurin rumtse idonta tayi ganin ashe daga shi se jallabiyar yake, cikin bargon da take ciki ya shige yana ƙanƙame ta a jikinsa, wutar abinda yaji jiya na sake taɓa kansa da motsa duk wani yanayinsa, kwanaki ukun daya mata sosai ya darzi amarcinsa babu ƙarya, yo ya sama ƴar shila, wacce da suna biyu yake kiranta koya ce mata Ƴar shila ko jaririyata. Zuwa lokacin har ta fara wayewa da kowa na gidan yaransa bakwai, manya hudu ƴan madaidai biyu se ƙaramar da tsakiyarunsa ke goyo,uwar gidan hudu ne nata kuma suna manyan, daga su kuma bata sake haihuwar ba, kasancewar shi da kansa yake baka tsari, in kana son haihuwar da yawa fine yace se yayi ta maka cikin, idan kuma baka so se kaje asibiti a sa ma planning ko allura, babban ɗan sa namiji ne yana Abuja da karatu, ita kuma wacce ke bi masa Nusaimah yar shekara sha shida se maza biyu, ba laifi suna da tarbiyya bakin gwargwado don Nusaimah ɗin ma shigowarta biyu ɓangaren nata..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 0810449315 *༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐* 𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ _𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_ Unexpected and Surprising 🔥💥 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏.... Page 21&22 *End of Last free Page's end🤗* # SingleAndThriving ♡ ♡ ♡ ♡ ꨄ Wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci riga da wando masu laushi. Kafin ta shiga fesa turare mai sanyi, bayan ta shafe jikinta da humra, tana cikin saka hula ya shigo yana sanye da pyjamasa blue colour sunyi matuƙar masa kyau, kallonsa tayi ta tarar da shima ɗin ita ya zuba ma ido. Sosai ya tsare ta da ido yana wani haɗiye yawun da yake neman sarƙe maƙoshinsa, ita kuwa gabanta se faɗuwa yake, don dama tunanin zuwa tirakarsa take don abin da kunya, wata numfashi ya ajje yana isa gabanta ya kamo hannunta ya tsotsi yatsarta ƙaramar, kafin ya rungumeta yana sakin ajiyan zuciyan kewanta da yayi. Wayarsa da yay ring ne ya saka shi rabata da jikinsa yana hanyar fita da hannu ya nuna mata ta biyo shi. Hijab kawai ta ɗora dogo akan kayan baccin dake jikinta ta nufi part ɗin nasa, baya palourn nasa hakan yasa direct ta nufi bedroom nasa, a zaune ta same sa a gefen gado yana danna waya. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta gabanta yana tsanan ta bugawa, a farkon gadon taja ta tsaya kanta a ƙasa tana wasa da hijab ɗin ta, sam bataji tahowar saba kawai sai hucin numfashinsa taji a fuskanta, hakan yasa da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa. Wani murmushi me kyau yai yana lasar lips ɗinsa, kafin yakai hannu ya zare mata himar ɗin dake jikinta, Ajiyar zuciya ya sauƙe yana kanainayeta gaba ɗaya a jikinsa. Sosai ya wani sake lafewa a jikinta wani daddaɗan ƙamshi na bugar masa hanci, ga wani kalan laushin da fatar jikin nata ke da, haba ai dole ne yake neman zaucewa akan wannan ƴar shila ɗin. Kai tsaye a gadonsa ya mata masauƙi shima ya kwanta bayan ya kashe musu fitila...... Washe gari ya rigata tashi sai da yai alwala sannan ya tashe ta, Hijab ɗin ta kawai ta ɗauka ganin ya fita don haka ta nufi hanyar fita, sai dai har takai ƙofa ta dawo a gurguje ta gyara masa gadon dakin ta fita. Sallah tai ta shige kitchen ta musu breakfast don yace kowa ta ringa girkinta kuma duk wacce take dashi itane zata ka abinci dashi, lokacin daya haɗe su ya musu nasiha...Breakfast ɗin ta ɗiba takai masa parlourn sa, sedai tana shiga ta tarar da Matarsa ta biyu me suna Raƙabiya ta wani hakimce a parlourn ita da yaranta uku, da ɗan murmushin yaƙen data ƙaƙaro ta iso tsakiyar parlourn tana ajje breakfast ta gaida ta a mutumce, wani tsuka tayi tace ta riƙe aunty'nta bata so zata iya ƙiranta da Raƙabiyanta ma fine, bata ce komai ba ta shige bedroom nasa don masa magana, a gaggauce ta gansa yana shiryawa tace lafiya ko wani wurin zashi?, yace mata wllh Mima ce bata da lafiya ze miƙa su hospital. ALLAH ya bata lafiya tace masa suna fitowa a tare se dai abinda ta tarar ne ya bata mamaki, da uwar da ƴaƴan ne gaba ɗayansu suke biki akan breakfast ɗin data kawo masa, shi ma sai da ya ɗan yi turus kana ya isa gabanta yana tambayarta ko miyeye dalilinta na cinye musu abinci, tana wani kwarkwasa tace... "Kasan jiya nace maka kwana mukai bamuyi bacci ba, shi yasa ko abincin na kasa tsayawa na mana..." A ɗan tsawace yace da ita kuma duk masu aikin gidan basu mata ba har se tazo ta nemi fitina?, wani ƙututun baƙin ciki ne taji ya ƙume don haka ta miƙe a fusace fuuuu taja hannun yaranta tana cewa tama fasa zuwa asibitin... Kwanci tashi aka ce hasarar me rai se gashi har sunyi wata huɗu da aure suna daf da shiga na biyar ma, kuma Alhamdulillah zuwa yanzun sosai take sakin jiki da Alƙali Yahaya,sedai har zuwa yanzu tsakaninta da tsaki yarunsa Indai sun haɗu su gaisa sama sama ta wuce itama ta wuce. Don ba ƙaramin kishi ne da ita da sam bata iya sarrafa shi, tsakanin ta kuwa da Uwar gidansa Hajiya Asma'u se son barka. Don tamkar ƙanwa haka ta ɗauke ta, duk da dai itama tana kishi da Meenal ɗin, ko dan sabo da yadda Mijin nasu hankalinsa yafi karkata akan Meenal ɗin, komai yace ita duk randa zai koma ɗakin ta uban kowa se yaga kalar rawan ƙafan da yake, amma duk sanda ze bar ɗakin nata kuwa kusan kowa se yasan yadda baya son ya baro ɗakin nata, in me girkin ma batai wasa ba ranar ko kallo bata ishe shi ba, amma fa idan ta tanka masa, don duk da hakan yana ƙoƙari sosai don abinda yake zasu daga yarinyar shi kadai yasan kayansa. To amma sedai takan danne hakan itama ta kuma yi adda'a, amma banda shugaba Raƙabiya da ake kwasar yan kallo da ita... Tin wajen ƙarfe tara saura yake zamar jiran shigowarta har gashi yanzun wajajen goma saura, don haka ya miƙe ya nufi Part ɗinta ya shiga ba kowa palourn kuma palourn a share yake sai dai ba wani ƙamshin da kullum baka raba parlourn dashi, bedroom nata ya nufa kai tsaye kwance ya same ta ta dugungune a cikin bargo, da sauri ya isa gaban gadon yana kaiwa zaune, hannunsa ya ɗaura a gefen wuyanta Jin zafi rau ne yasa shi faɗin "Baki da lafiya Meenal amma shi ne baki fada min ba?" Rintse idonta tai hawaye suka silalo tace "Daddy na ƙira ka ai amma bai shiga ba kuma wayar tawa ta mutu ban sa a charge ba" takai ƙarshen maganar a mugun wahalce. Ɗan shiru yayi na wani lokaci kafin ya miƙe yace "Bara na dauko mukullin mota muje hospital, ai zama da jinya babu daɗi...." Yay maganar yana fita, babu ɓata lokaci kuma se gashi ya dawo hannunsa riƙe da car key, da kansa ya taimaka mata ta saka kaya ya tallafota suka fice zuwa compound na gidan, da ko ina hasken solar da bata jima ba aka gyara, suna gaf da isa gaban motar se ga Raƙabiya kamar wacce aka cillo daga sama, kallo ɗaya ya mata don haukarta tayi yawan da ko tanka ta baya son yi, gaba ɗaya yanzun kaff gidan itace me basa ciwon kai. Be kula ta ba sema kwantar da Meenal da yayi akan kujerar motar, kana ya zaga ɓangaren me zaman banza yaja motar suka fita, kai tsaye wani private Hospital ɗin dake nan kusa da su ya kaita, sai da ya buɗe mata file sannan suka shiga gurin doctor ɗin. Ƴan tambayoyi tai mata dake Dr ɗin macece kafin ta kira nurse tace suje ayi mata test, nan suka je aka mata shi dai Alƙali Yahaya yana ta adda'ar ALLAH yasa ciki ne da ita, sedai saɓanin hakan ya samu don cewa sukai maleria ne ya mata yawa. Magunguna aka basu suka koma gida, anan ɓangaren nata ya kwana yana kulawa da ita, washe gari bayan ya dawo daga sallar subhi ya dawo se ya ɗan janwota jikinsa bayan ta gaida shi yace.... "Wai yaushe zaki bani baby?, ina son inga kin haifa min baby kyakkyawa me kama dake..." Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsun hannunta tace "ALLAH ne be kawo ba amma nima ina so ai..." "ALLAH ya kawo mana masu albarka" yace yana fita kai tsaye don shiryawa ya tafi wurin aikinsa. Sannu a hankali ababuwa suka fara cakuɗema ma Meenal a gidan, ga yara da kamar ma turo su ake takanas su mata rashin kunya, in abu ya sayo irin duk gidan nan se an ga dama za'a raba da ita, gashi yanzun kamar sun haɗe mata kai ne, bata da wata kyakkyawar sukuni a gidan, tin bata kai masa kara har ta fara don ababuwan sun fara fin ƙarfin, ga wata shegiyar rama da tayi ita ba wacce tasan jinyar laulayi take ba, tin a wasu ababuwan yana bin bayanta yana bata kariya harta kai ta kawo yanzun se dai ma ya hauta da faɗa da masifar cewa da shi duk be san wasu ababuwan nan ba se da auro ta, shifa yanzun wani bin har dana sanin aurenta yake, gaba ɗaya ta gama ficewa a hayyacinta gashi tin da aka yi auren zuwanta gida befi uku ba, don matsin lamba ce dashi wajen fita, kuma baya taɓa barin ta wuni sedai taje da magribar fadi isha'a yaje ya ɗauko ta, wai a hakan ma ada ɗin kenan yanzun wani bin ma girkinta yakan shiga har ya fita bata saka Alƙali a idon taba, kafin taje ya rufe ɓangarensa wanda tin abun baya mata ciwo har shi ma ya shiga sahun daya sake figar da ita, idan kaga yadda ta tsige ta rame zaka ɗauka DEEPIKA PUDAKUNE ce farkon shigarta BOLLYWWOD dan rama, ko ina se ƙasusuwa da ƴan hakwara likely dai tamkar deepika ɗin ga duk wanda ya mata farin sani farkon fara film nata lolz🤩. A lokacin da Shareefah ta mata zuwan ƙarshe da kuka suka rabu ita kuka itama kuka, amma tace karta faɗama Baffansu ko yaya Sadeeq su tashi hankalinsu, gashi shirye shiryen bikin Shareefah ɗin da Bilkisu ake lokacin, dan dama kusan fikon turakane tsakaninsu. Ko da ta koma gida adda'a ta dukufa yima Sister ɗin nata kan ALLAH ya yaye mata dukkan abinda ke damunta, in kuma rabuwar su ce alkhairi Ubangiji ya bama kowa hakuri don idan wata ukubar tayi yawa rabuwan shi yafi alkhairi... Ita kuma Meenal a nata ɓangaren ba taji zata sare ba, za taci gaba da juriya da hakuri In Sha ALLAH, don bata son aurenta ya sama matsala se adda'ar itama data riƙe da nafilfilu kuma har lokacin ko ɓatan wata bata taɓa yi ba a gidan. Komai take cikin ƙarfin hali da ƙarfin zuciya take, wanda hakan har bama Shareefah mamaki take, don ta sha tambayarta ita kuwa wanne kalan ƙarfin hali ke gare ta, takan yi murmushi a lokacin tace mata. _Wani lokacin muna murmushi ne domin kar duniya tasan ciwon dake cikin zukatanmu.._ Akwai mutanen dake kewaye dani amma babu wanda ke fahimtar irin kaɗaicin dake cikin zuciyata, ina murmushi ne kawai don kar a tambayeni amma har cikin zuciya hawayene ke kwarara ba tare da tsayawa ba. Na koyi zama ni kaɗai na kuma sake yarda da wasu ke cewa, wasu mutanen daga nesa suke burgeka saika haɗa hulɗa dasu zaka yi nadama. Wasa wasa se gashi har gashi har mun shiga wata na huɗu cikin wannan matsalar, wanda ya kama watanmu tara da aure kenan, tuni kuwa har wasu ƙananun maganganu sun fara fita waje har zuwa can cikin anguwarmu, wai Miji da kishiyoyi nacin ubana suna soya min aya a hannu, duk lokacin da zanji makamantan zantukan kalan hakan nakan yi murmushi ne kawai kamar yadda na saba, murmushin na lulluɓe duk wani miƙin dake cikin zuciyar tawa... Yau dake girkin tane da wuri ta kammala shirinta, don yau itama ta tanaji kalaman fara dawo dashi kan daidai ɗinsa, da huri ta isa lokacin ɓangaren nasa tin kafin ya shigo, amma se da ta tabbatar me girkin ta fita kuma Maman Abeed ce wato Raƙabiya. Ɗakinsa ta fara gyara masa tsaf kana ta fito parlour ta kunna kallo, tana zaune sega Maman Abeed ɗin ta shigo kamar wacce tayi mantuwa, bata ko kalla inda take ba har ta gama juye juye da aune aunenta ta kama hanya ta fice bayan ta mata tsaki, amma in ta tankatama ai ta sama arziƙi... Babu jimawa kuwa se gashi ya shigo ɓangaren nasa, sedai turus yaja ya tsaya yana kallarta da take cikin shigar kayan bacci masu kyau. Zaune ta tashi fuskarta ba yabo ba fallasa, sannu da zuwa ta masa lokacin da yake kaiwa zaune saman kujera. Gaidasa tayi a natse ya amsa yana jin duk babu daɗi da abinda yake mata, Se dai babu yacce ya iya ne dole ne saboda ya na son bata kariya.... Se dai be san da wanne bakin ze mata magana ba, be kuma san da wanne idon ze dube taba, wata ajiyar zuciya ya sauƙe yana kamo tafin hannunta cikin nasa, lumshe idonsa yayi yana jin kamar zuciyarsa zata fashe da tsananin ƙaunarta da tausayinta. Ahankali ta zame hannunta daga cikin nashi tana kaiwa ƙasa cikin rawan murya tace... "Daddy'n Nusaimah don ALLAH ka yi hakuri idan na baka wani abu ne ba tare da sani naba,kasan duk inda ɗan Adam yake azijine wllh ban san kome na maka ba, na kuma duk iyaka yi na amma ban gano daga inda matsalar take ba... Daddy'n Nusaimah Me ya sa kake ƙoƙarin sanjawa daga yadda na sanka?, Me ya sa kake ƙoƙarin daina bani kulawanka?, Me ya sa ka daina jin tausayina?, Me ya sa a yanzu bana gabanka?, ka dena lallashina. Me ya sa ka sanja min cikin ƙanƙanin lokaci haka?, Me ya sa?, Me na maka?....." Tayi maganar muryanta na rawa sosai... Hannunta ya kamo tare da ɗago ga yana share mata hawayen fuskarta cikin taushin murya yace. "Baki min komai ba Ameenatou!,babu abinda kika min wllh, kawai ina jin kamar ba daidai nake ba, ina kuma jin kamar ban chanchanta inci gaba da zama dake irin haka ba, sedai na rasa akan me akan kuma wane ne..... Wani kuka ta fashe dashi tana me furta. "Tabbas na fara zargin kaina da cewar ko ababuwan dana aikata ne ALLAH be gama yafe min, amma nima a cikin raina inajin kamar cewa tabbas wata rana zaka rasani, sannan zakai kewata ba don nafi kowa ba, ba kuma don na zarta sauran matan kaba, A ahhh se dan kawai na san ranar zata zo maka wata rana, kuma idan wannan ranar tazo, kada ka kira shi da ƙaddara, ka ƙira shi da sakamakon abinda ka aikata!!!, tun da na tambayeka laifi na kace ban maka komai ba, haka kawai zuciyarka ta tsara maka fara tsanata sabo da binciko tsoffin laifukana na baya shi ne ka fara ɗora alamar tambaya akai na ka kuma dena SO da TAUSAYINA, wanda dama nasan su suka huce maka gaba wajen auren na...." Daga nan ta kwace jikinta a nashi ta fice daga ɗakin a guje tana riƙe bakinta da kuka ke son kwace mata...Ahankali kuma taɗan buɗe idanunta wanda cikinsu ya cika da ruwan hawaye, ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, tare da ƙoƙarin shanye ruwan hawayen nata, dan batajin zata iya barinsu sukai ga sauƙa akan fuskar _MAJEED DAWOUD_ zaune yake saman sofar dake gaban gadonsa, system na shi ajiye saman desk se wasu ƙananun glass cup yana opreting wasu files na asibitin daya ziyarta na Young pharmacy and private clinic...tshirt ce mai gajeran hannu a jikinsa sai dogon wandon ta masu taushi. Idanunshi a sakaye cikin farin glass ya zuba su akan system ɗin da yake ta famar aikinshi akai. Daga gefen sa kuwa Ayla ce kwance ta dora kanta saman jikinsa,kanta babu scaf anyi saima space buns ɗin da aka mata irin na Babyn nan, wanda suka mata kyau sosai gwanin birgewa... Duk da kasancewar aikinsa yake gudanarwa amma kuma ƙasan zuciyarsa mamakin abinda ya gani yake, amma duk da haka cikin ƙarfin halin danne abu a zuciya da kuma yanayin sa na rashin bama abu mahimmanci da basarwa ya ture tunaninta a ransa, se kuma yayi saurin istighfari a ƙasan zuciyarsa yana sakin wata ajiyan zuciya, abinda ya danne ƙirjin nasa na ɗan lafa masa yana jin ɗan sassaucin ba kamar ɗazun ba. Shiru kawai yay yana lumshe idonsa tare da jingina bayansa da jikin gadon, kafin ya sauƙe idonsa ahankali akan Ayla dake lafe a jikinsa tana bacci hankalinta kwance, sake lumshe lumsassun fararen idanuwansa yayi yana ɗan tafiya wata duniya... Wani gauron numfashi ya kawo kuma jin numfashinsa na shirin fiffizgewa , alaman tunanin daya tafi me ɗan zurfi ne. Da Ayla ya tashi a jikinsa kai tsaye Part na Ummiensa ya nufa, kai tsaye ya kwantar da ita a gadon ummie bata ɗakin, peck ya bata a goshi kana ya fice yana komawa room nashi. Zaune yake dafe da kansa ya ɗan jima a hakan kafin yayi kundin balar miƙewa adda'a ɗauke a bakinsa, zare kayan dake jikinsa ya shiga yi wannan asalin lafiyayyar chocolote skin ɗin nashi na bayyana tana ɗaukan ido, saboda samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau da yake amfani dasu. Kai tsaye bathroom ya faɗa tare da sa karma kansa shower yana lumshe idanuwansa ruwan na sauƙa akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna sanyaya jikinsa a hankali. Ya jima sosai sosai a ruwan yana wankan, kafin ya fito ɗaure da babban towel me ɗan kauri white har wani miski miskin blue yake, jikinsa na fidda ƙamshin shower Soap ɗinsa na Ocean seaweed. Hannun sa ɗaya na riƙe da wani mini clean blue towel ɗin daban yana tsane jikinsa a natse. Pyjamas farare ya zira yana kallar agogon bangon dake ɗakin nasa. Ganin se yanzu ne ma sha biyu ke bugawa ya sanya sake ɗaukan system nashi, akan wata arniyar ɗunƙulalliyar kujera ya zauna yana fesar da hucin numfashi, Ci gaba da ayyukansa yayi har zuwa wajen ɗaya, iska ya zuƙa ya kuma fesar yana jan idanunsa ya lumshe ganin ya kammala aikin nashi, Goran ruwan dake a Centre table ɗin dake gaban gadonsa ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin, yana ambatar ALHAMDULILLA a bayyane....... ★ Zaune takai akan gefen gadonta tana haɗe kanta da gwiwwarta ababuwa na nemar fasa kanta ,idanunta sunyi wani irin jajir ɗin kaiwa maƙura a ɓacin rai da tashin hankali, daga inda take cakuyen take me roƙon ALLAH inama ya bata damar fashewa da gursheshen kuka. Se dai tayi duk yacce za ta yi amma ina kukan nan yaƙi iyuwa ya, tabbas se a yau take sake yarda wani kukan ma rahama ne, lallai kuma ta sake yarda da zancen nan na mutane da suke cewa idan baƙin ciki yay baƙin ciki kukan ma baya taɓa yiwuwa, Shin me rayuwa take nufi da ita ne wai har haka?, hannunta na dafe da kanta ta buɗe idonta, se kuma ta ware duka hannuwanta guda biyun tana me furta..... "YA ALLAH!, kai ne ka ƙaddara min wannan daddaɗar jarabawar taka kuma na amsa da hannu bibbiyu, haka kuma kai ne ka ƙaddara min duk kan abinda zai faru dani a yau ɗina har dama gobena!. Haka kuma komai a cikin ikon ka da yardarka suke ci gaba da tafiya, Ya ALLAH kaci gaba da zama gatana!, YA ALLAH a koda yaushe cikin gode maka nake akan duk abinda ka jarabceni dashi a cikin duniyar, ka kuma bani juriya da hakurin ibadarka, domin kuwa UBANGIJINA ka fini sanin daidai, Komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurarka, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddarar sane, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas nan dake takan iya sanjawa. Ya ALLAH ka fini sanin daidai na, ka mini maganin dukkan matsalolin da suke kewaye da wannan rayuwar tawa!, ka Zama gatan Mara gata... Ya ALLAH na amshi wannan rayuwar data zo min a wani irin hagunce, Hakan da ka tsara min na gode Ya Rabb, Tabbas wata rayuwar ba tamu ba, kamar yadda wata wata ƙaddarar ba sakacinmu ba ne, domin kuwa ƙaddara ba canki in canka bace bare kace zaka zaɓarma kanka kalar rayuwar da kake so ba, Ya ALLAH bana da iko ko halin da hukuncin ka, amma ka yanke min duk abinda yake ba alkhairi na bane..... Mafita ALLAH!, mafita ya ALLAH...." Tayi maganar jikinta na wani kalan tsuma, ji tayi kamar ana fuskarta zuwa baya don haka idanunta suka fara ganin xbibbiyu numfashinta kuma na gwamewa.... Se dai be kai ga rabuwa da gangar jikin nata ba wannan dai hayaniyar data gudonmawa na sake iskota har zuwa nan sashen nata, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un take ambata tana jin inama a yanzun ba sai anjima ta mutu tabar duniyar, wannan wanne kalan ƙalubale da jarabawa ce haka, me ta tare ma Hajiya Ana surukuwarta kuma Uwar Mijinta?, me ta mata da zafi haka, don kawai ta auri ɗan ne?, ko kuwa kawai don akan wannan ƙaddarar ta taɓa faɗa mata ne? Ta na tsaka da wannan tunanin ne kuma burum taji an bugo mata ƙofar bedroom ɗin nata.... "Kina ina shegiya baƙar munafuka!, to wllh na gaji da zama dake a haka, gaba ɗaya tun da kika auri Yahaya na dena gane mishi, gashi zama yayi zama ace zama har shekara na ƙoƙarin wucewa amma ace ko ɓatan wata baki taɓa yi ba, to wllh da sake, A yau ba sai yanzun ba indai ni uwace ga Alƙali Yahaya Shehu Usmanu seya sake ki Aminan...." Jikintane ya tsananta rawa sosai fiye da farko, amma babu ɗigon hawaye ko ɗaya a ƙwayar Idonta, shigowar Alƙalin kamar wanda aka kifo ne ya saka Meenerl ɗin saurin miƙewa tana nufarsa, don gani take a cikin wannan yanayin shi kaɗai ne Garkuwa da madogararta, hannunsa ta koma cikin kamar ta fice a hayyacinta tana jan shi gaban Hajiyar tasa suka zube, "Don ALLAH Hajiya kiji tausayina, ki tausayama maraicina kiyi hakuri ki janye kalamanki akan mu, wllh ba laifi na bane, Daddy'nsu kace wa Hajiyarmu nima zan haihu, kai nake ta jira wllh a shirye nake indai zaka bani cikin!!!, Nima ina son yaran Hajiya...." Cafe zancen yayi shima ta hanyar sake furta. "Hajiya dan girman ALLAH, don Annabin Rahama Annabi Sallallahu alaihi Wasallam kiyi hakuri Hajiya, don wanda akai duniya dominsa lahira dominsa, aka yi wuta don maƙiyansa, aljannah kuma don masoyansa ki gafartamana ki mana sassauci wllh ina son Jaririyata, ina jin tsananin tausayinta, wllh ban san wanda ya haɗani dake ba cikinsu, amma kamar yanda kika shariɗanta min wllh tin daga wannan ranar ban sake kusantar ƴar shila ba gata nan ki tambayeta koba haka ma Meenal?..." Wanda ita kuwa Meenal ɗin jin kalamansa na ƙarshe ne suka sake nemar gigita ƙwanyarta, me hakan ke nufi?, Hajiyar ce ta hana masa dena kusa tarta kenan da yayi tsayin watanni kusan har ukku kenan?, wanne laifin tama ALLAH ita kam da yake jarrabarta da ƙaddarori masu kwamanceceniya da juna?, ita kuwa Hajiyar se wani sake huhhura hanci sama take tana wani karkada ƙafafunta. "Ta yaya kake son inci gaba da yarda dakai Yahaya?, A gabana fa yanzun gashi nan kake ƙiranta da sunaye na fitsara da rashin mutumci har da wata ƴar shilarka, dan ubanka yau she ka fara farauta ban sani ba da har kake da wata ƴar shila?, kuma ni dai iyaka sani na baka taɓa sunkuyawa da kanka ka haihu ba bare na sake tabbar da cewar kana da jaririyar, ka sani idan har kaji bakina ya sake buɗuwa da nufin kowacce kalan magana to ka sani ta tsinuwace gare ka Yahaya....." "Hajiya don alfarmarki da Sayyiduna Muhammadun Sallallahu alaihi Wasallama kuyi.....h......." _ALHAMDULILLAH!,ALHAMDULILLAH!!, ALHAMDULILLAH ala kulli halin🙏 🙏!!!, Anan na kawo ƙarshen book One na KARSHEN ƘADDARA, sai kuma ALLAH ya haɗa mu da masu rabo a BOOK TWO nashi_ _Tofa masu karatu yaya take ne?, mike shirin faruwa?..._ _Shin ya kuke ganin za a kare tsakanin Alƙali Yahaya Shehu Ɗan Batta da kuma mata da mahaifiyarsa?...._ _Ku a naku gani da tunanin wannan sakin ze iyu kuwa?, Me kuma kalaman Hajiyar suke nufi da gasken kenan itace da kanta ta dakatar dashi ci gaba da mu'amulantar matarsa?, kai wannan cajin kai dai da yawa yake...._ ~A tunaninku shike nan wasan zezo ƙarshe ne?, La la la..... Yanzu ne ma zamu ɗauki wani salon shima me zafi, kuma shima kakan nashi ƙalubalen daban shima~ _Domin kuwa a gobe ma da wani labarin, Kwarai kuwa haka Nie AMMEY LAYLERH'NKU ɗin ku naceeee...._ _Wai hausawa suka ce ɓukatar maji hajji Sallah, karfa ku manta da hasashen Ahmad kar dai ya zame mana gaskiya jama'a, domin fa ance sunan littafin ƘARSHEN ƘADDARA karku manta, me bi kuwa akwai yiyuwar wasu aure auren bayan na Alƙalin dake kanta, wanda yake daf da rugujewa shima....🤸🤸🤸🤸_ _Amma fa kar FAN'S su ce na fiye zaƙewa nima a zaƙen nake da jin yadda zata kaya ɗin ne ai🤩_ _Tofa wata daban kuma wata sabuwa, wai ma waye wannan MAJEED DAWOUD ISHAQ ɗin ne?, Baban AYLA kuma lawyer ɗin daya tsaye ma AMEENERH SHEHU USMAN, har se da Shari'a ta bata gaskiya....?_ _Wai kuwa 👍 🙂 duk kun shirya bin AMMEY LAYLERH'NKU, don warwarar wannan ƙaddarar da daku?, kun shirya ayi tafiyar daku cikin labarin littafinta me SUNA KARSHEN ƘADDARA???_ _Hhhhh Hajiya ke dai nace bara nai shiru kar na cika masu karatu da tarin jawabai, domin kuwa tafe labarin yake da tarin gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon da ban taɓa yin irin saba na sani_ _HUMMM Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakuɗe cikin wannan littafin_ _Duk zamu samu amsoshin waɗannan tarin tambayoyi namu ne idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo ƙarshen BOOK 1 NA ƘARSHEN ƘADDARA Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin ƘARSHEN ƘADDARA 500 Hundred ne kacal babu yawa..._ _Ga duk mai son biya kai tsaye zai tuntuɓeni a wannan number_ 👇 08104493215 Wanda suke sun biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin 👇 8104493215 Maryam Nasiru Opay Or 3206656358 Maryam Nasiru First Bank A turo shedar biya ta wannan number 08104493215 _Masoya na amana a nuna min kauna sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na KARSHEN ƘADDARA, daga AMMEY LAYLERH'NKU me ƘAUNARKU FAKA FAKA_🤸🤸🤸_ _Byee my FAN'S sai mun sake HAƊUWA a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuɗin ka saida rabonka littafin ƘARSHEN ƘADDARA ba hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo?...... To ai shikenan kawai A gimtse ɗinnn🤸🔏 🫰✊_ _MASU TAMBAYANA JERIN SUNAYEN LITTATTAFAINA TO GASU KAMAR YACCE NA MUKU ALƘAWARI ZAN LISSAFO MUKU...._ *KAREN BANA FREE* *JALAAL AREEF FREE* *ƘAUNA BIYU FREE* *MIKIYA PAID ONLY 500 HUNDRED* *TA DABAN ONLY 500 HUNDRED* *DUNIYARMU ME CIKE DA TARIN ƘALUBALE ONLY 1K* *SO DAN RAYUWA ONLY 500 HUNDRED* *RAMIN KURA ONLY 1K* *DUHU na DUKAN duhu ONLY 1K* *SE KUMA SHI WANNAN ƘARSHEN ƘADDARAR shima 500 HUNDRED yazo muku* Ku sani waɗan nan litattafan suna jerin sunayen littattafan nawa ngd👏👏👏.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* ᴬᴹᴹᴱʸ ᴸᴬʸᴸᴱᴿᴴ🤫😶🤐😥😢😩👌✍️🙏👩👁️🤦🙅‍♂️🙋‍♂️🙆‍♀️....... 08104493215