*JUMMALA DILLALIYA* Written Sa'adatu Ta Batulu Group 👇 https://chat.whatsapp.com/C9Gc6WqmpCMEMIMFY5gSpy?s=cl&p=a&ilr=1&amv=3 *MABUDI* Masu iya magana suna cewa Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Tabbas wannan kalmar Hajiya Jummala ta kinkimo ta afa wa kanta domin biyan buƙatun rayuwar ta. Dillaliya ce wacce akewa take da komai da ruwanki (Gayu kuma na kiranta da "Ta fita kunya) Zamu iya kiran ta da uwar harƙalla, mace ce mai kamar maza ta ɓangaren neman na kanta ta hanyar ƴaki halak ƴaki haram. Babu abun da bata saya kuma bata saidawa, babu irin rikicin da bata shiga kuma bata shigarwa. Labari ne mai cike da chakwakiya da kuma jajircewa akan cikar mafarki da kuma neman na kai, gami da rashin tsoro wanda ya jawo mata suna da kuma baƙin jini a gurin al'umma, domin duk inda kake neman mara mutunci akan kayanta, to idan ka samu Jummala ka gama. Gefe guda kuma ga Iro hatsabibin yaro wanda ya gagari kowa da rashin ji. Hamm ba sai na cika ku da surutu ba, ku biyu Ta Batulu domin ganin Wacece Jummala da kuma Iro. *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDUNA MUHAMMAD WASSALIM* Chapter 1️⃣ "Tsamiya uwar ƙwanƙwamai ai karo dake gwara ai da treda Allah ya taimaki uwar fita kunya, namu maganin a kwaɓemu." Abba ya faɗa fuska cike da fara'a. Dillaliya tana zaune a kujera fuska kamar bata taɓa dariya ba. Ta ɗaga masa hannu ta ce. "Faɗa mun abin da ya kawoka tun ban sauke maka jidalina ba." "A huce haka ta fita kunya, daman madam ce bata nan" Abba ya faɗa yana ajiye mata makulli ya fita. Dillaliya ta kira masu yi mata aiki ta basu key ta faɗa musu aikin da za suyi. Motar kwashe kaya suka ɗauka zuwa gidan Abba, suna zuwa suka nufi bedroom suka kwashe akati guda biyar, labulaye carper duk suka cire, har da mashin ɗin Abba suka bar unguwar. Dillaliya ta buɗe kayan akwati ɗaya bayan ɗaya ta ƙirga, babu leshi guda biyu ta fara salati tana tsinewa Abba, ɗaya daga cikin ma'aikantata ya ce. "Ta fita kunya harda mashin ɗinsa muka ɗauko saboda tsaro." Dillaliya ta rangaɗa buɗa ta kwance hannun zanni ta sallamesu. Gidan Abba. A tare suka shigo da matarsa gudun zargi, suna shigowa ta fara salati tana hawaye bedroom ta nufa, babu akwati babu carpet labulaye, ta kira mijinta cikin kuka ta nuna masa ɗakin Abba ya rasa tunanin da zai yi, domin babu mashin ɗinsa kuma yana da tabbacin aikin dillaliya ne amarya tana kuka ango yana yi, gaba ɗaya sun cika gidan da ihu shi babban damuwarsa mashin ɗinsa, kuma yana da tabbacin ko zai mutu ya dawo dilalliya ba zata bashi mashin ɗinsa ba, amarya kukan lefe take yi maƙota suka ji ihun ya yi yawa suka leƙo domin ganin abin dake faruwa, suka janye Abba matan suka rarrashi amarya har tayi shiru. Bayan kwana biyu Abba ya shirya ya nufi gidan, dillaliya, tana ganinsa ta ɗaure fuska ta turo ɗankwali gaban goshi. Abba ya fara mata kirari. "Allah ya taimaki hankaka mai da ɗan wani naka, gatan samari da ƴan mata sai dake Hajiyan Allah gaba salamun baya salamun." Dillaliya ta ɗaga masa hannu ta ce. "Yi sauri kayi maganarka fita zanyi." "Dan Allah ki taimaka ki bani mashin ɗina." Abba ya faɗa yana marairaice fuska. Dillaliya ta ce. "Acikin kayan dana baka babu leshi guda biyu, kuɗinsa dubu ɗari da ashirin idan kana san mashin ɗinka, kaje ka kawo mun kuɗin kayana ka ɗauki mashin ɗinka." Tana gama faɗa masa haka ta saɓa jaka ta fita. Jiki a sanyaye ya miƙe ya tafi kasuwa, Dillaliya gurin masu furniture's ta nufa suka gaisa ta nemi guri ta zauna. Bata jima da zama ba matashiyar budurwa ta ƙaraso shagon tasha lalli ƙafa da hannu tana ɗaukar ido kamar amarya, suka gaisa da mai shagon ta nufi gurin dillaliya tana cewa. "Allah ya taimaki ta fita kunya namu maganin kukan mu." Dillaliya tayi dariya, suka zaɓi kaya masu kyau aka zuba a mota tare da ma'aikata suka tafi. Sun ajiye komai a inda ya dace daga nan suka yi sallama suka tafi. Dillaliya suka nufi gidan su yarinyar suna shiga aka fara buɗa yara suna ta waƙar Amina amarya, dillaliya ta keɓe da Maman Amina sun jima suna tattaunawa kafin suyi sallama ta fita zuwa gidan Atine, sun taɓa hira kafin Dillaliya ta miƙe Atine ta bata kudin adashi daman abin da ya kawota kenan, haka ta rinƙa bin gida gida tana karɓan kuɗin adashi, gab da yamma ta kira yaranta suka nufi gidan Saude, a ƙofar gida suka tsaya ta yi sallama ta shiga ciki, Saude da amaryanta suna dambe kamar zasu kashe juna. Dillaliya ta raɓa ta shiga ɗakin Saude bata jima ba yaranta suka shigo gidan bisa umarninta, basu kalli kowa ba suka fara fitowa da kujerun Saude. Amarya ta rangaɗa buɗa ta ce. "Daman kujerun na bashi ne, ake mana iyayi da yanga. Allah nagode maka da ganin wannan ranar mai daɗi kamar daren lailatul ƙadri." Saude ta nufi gurin dillaliya tana cewa. "Allah ya taimaki ta fita kunya, dan Allah mu shiga ɗaki muyi magana." Dillaliya bata saurareta ba suka kwashe kujerun suka tafi, amaryan Saude ta rinƙa zabga dariya harda hawaye, daman duk ta isheta da faɗin iyayenta basu yi mata kayan arziki ba, kullum sai tayi mata gori ashe kujerun haya ne , dillaliya gida suka nufa da kayan ta sallamesu ta zauna tana kiran Mashiɗa, kamar daga sama taga an faɗo gidan babu sallama, ta miƙe da sauri tana ƙare musu kallo. Mata guda biyu kowacce da ɗammara dillaliya ta fashe da dariya tana cewa. "Maraba da gayyar soɗi." Zaginta suka farayi suna nuna mata yatsa, dillaliya ta damƙi hannun ɗaya daga ciki ta karya dambe ya kaure tsakaninsu, har ƙofar gida suna dambe dillaliya duk ta yaga musu kayan jikinsu, dambe suke yi kamar za su kashe junansu, dillaliya ta haye cikin ɗaya ta rinƙa zabga mata nushi a fuska, ta sumar da guda ɗaya ta koma kan ɗayan gaba ɗaya ta sanja musu kamanni. Ganin suna neman kashe junansu aka kira ƴan sanda suka tafi dasu, bayan awa ɗaya mazajensu suka zo beli aka fara mayar da magana. Dillaliya ce ta yiwa mijinsu hanyar bazawara ya aura, shi ne suka zo ɗaukar fansa, sai kuma akayi rashin saa dillaliya tayi musu dukan tsiya. Mijin dillaliya yana gefe yana bayar da haƙuri, da ƙyar aka bayar da belin dillaliya shima mijin wancan matan ya biya, domin ta rantse mijinta ba zai biya ko sisi ba. Har sun fito ta koma aka yi musu iyaka da gidanta, suna tafe mijinta yana mata ƙorafi akan neman rigimarta "Aunty wallahi Baba ya siyawa Maman mu atamfa da takalmi ya ce kar ta bari ki gani." Iro ya faɗa yana cin gyada. Yana sanye da zabgegen riga da wando rigar har gwiwa, wandon kuma yanda kasan doguwar riga, kayan dai dai tsawonsa idan ya miƙe yana tafiya, kamar zai tashi sama idanu sun sha kwalli, ga wani ƙaton glass mai ido ɗaya ya kusa cinye rabin fuskarsa, yana ta walƙiyya kamar ya shafa man gyaɗa. Aunty ta ce. "Iro bana san ƙarya ka sani koh.?" Iro ya fara rantsuwa yana zaro ido Aunty ta bashi naira ashirin ya fita da gudu yana dariya, ɗakin Mamansa ya shiga yana mannewa a bango. "Iro kaje gurin Talatu ka amso mun kaya.". Mama ta faɗa tana hararan sa. Iro yaje ya amso kayan kamar abin arziki ya faki idanun mutane ya shiga ɗakin Aunty ya nuna mata kayan, ya kaiwa Mamansa ya zauna kusa da Inna dake girka abincin rana. Bai motsa ba har aka gama abincin aka raba ya ɗauki nasa ya cinye ya sha ruwa sannan ya nufi ɗakinta. Inna tana zaune ta miƙe ƙafa tana cin abinci ya yi dariya yana cewa. "Lahira bakya cika." "Dan ubanka ni sa'ar wasanka ne.?" Inna ta faɗa a hassale. Iro ya kwantar da murya ya ce. "Haba Innata mai share mun hawayena, Innata tafi uwata ƙaunata Allah yaja zamanin uwar gida a gidan Alhaji Baban mu, sai kinyi ministan uwar gida in sha Allah." Inna ta washe baki ta miƙa masa abincin gaba ɗaya, daman abin da yake jira kenan ya zauna ya cinye tas ya lashe kwano, Inna ta zuba masa ruwan randa mai sanyi yasha sannan ya nufi bakin ƙofa yana cewa. "Inna abinci ya yi daɗi sosai da sosai, amman dan Allah kar aƙara irin girkin nan girki kamar za bawa ƴaƴan aljannu. Gaskiya Baban mu yana da haƙuri wallahi tsawon lokacin nan yana kwasan wannan abincin aljannun." Yana gama faɗa ya zura da gudu, Inna tabi sa a baya, sai dai ko kafin ta ƙarasa tsakar gida ya fice da gudu yana dariya, Inna tayi ƙwafa ta koma ɗakinta. Bayan sallar la'asar ya shigo gidan ƙafa a karkace yana tafiya irin na guragu, dai dai ƙofar ɗakin Kaka ya tsaya idan yakai ƙarshe sai ya dawo, tun bata lura da abin da yake yi ba har idanunta ya dawo kansa, ita ɗin bata tafiya komai a ɗaki take yi idan zata fita sai a ɗaurata a keken guragu, suna haɗa ido ya ƙara shanye ƙafa da hannu ɗaya ya ce. "Kunga kiɗan guragu, ga shokin guragu. Ga tafiyar guragu, kunga rawar guragu, kunga zaman guragu, kunga gudun guragu." Duk abin da ya faɗa sai ya kwatanta Kaka ta fashe da kuka tana jan jiki, Iro ya yi waje da gudu yana cewa. "Allah ya ƙarawa gurgus lafiya." Kaka ta fasa ihu tana cewa a kira mata Salisu yazo ya yi mata iyaka da Iro, sai dai babu wanda ya fahimci abin da take nufi domin sun san Iro ya jima da fita, ganin ta fara surutai suka watse suka barta. Bayan magrib Inna ta gama abinci tuwon dawa miyar kuka, Iro ya leƙa ɗakin mahaifinsu ya gansa zaune yana cin nama da lemu. "Allah ya ƙarawa Baban mu lafiya da nisan kwana da albarka ubangiji ya jiƙanka da rahama." Baba ya daka masa tsawa ya ce. "Kaga shegen yaro mai baƙin hali, dan uwarka a ina na mutu.?" Iro ya sosa ƙeya ya ce. "Yanzu dai kawo ladan addu'a zanci taya." Baba ya ɗauko yanka biyu ya basa cike da kashedin kar ya kira masa kowa. Iro yana amsa ya zura da gudu, ɗakin Aunty ya fara shiga ya nuna mata naman yana cewa. "Baba ya ce kizo da plate ya zuba miki nama." Sauran ɗakunan matan duk haka ya faɗa musu kafin ya fice yana dariya. Baba yana shan lemu yaga matan kowannen su ta shigo da plate, suka fara kallon juna. "Lafiya kuka tsaya mun a kai da plate kamar masu karɓan sadaka.?" Baba ya faɗa yana janyo raguwar namansa, Aunty ta janye ledar ta buɗe ta raba musu naman ta ɗauke raguwar lemun tayi gaba tana cewa. "Ko banza na rage zafi." Baba ya saki baki da hanci yana kallon su. Mama tayi waje tana faɗin. "Allah ya kyauta." Baba ya kalli Inna dake tsaye tana hararansa ya ce. "Tashi mun a kai dallah karki cinye ni ɗanye." Inna tayi tsaki ta ce. "Allah ya raba rai da wahala." ta fito ɗakin cike da takaici. Iro yana cikin zagaye unguwarsu wani saurayi ya kirasa zai aikesa ya kira masa budurwarsa, kafin saurayin ya fara magana Iro ya ce. "Kiran bazawara ɗari biyar, budurwa dubu ɗaya." Saurayin ya saki baki da hanci yana kallonsa. ganin kayan jikinsa da wata kafceciyar hula da ya saka a kai, yasa ya kwashe da dariya ga ido yasha kwalli, ya lallaɓasa akan ya yi haƙuri Iro ya yi banza dashi kuma yaƙi tafiya, duk yaron da ya kira zai aika yana ganin Iro a gurin yake zurawa da gudu, ganin babu mafita ya biya kuɗin ya kira masa budurwansa ya yi gaba, duk wanda ya kirasa haka yake faɗa masa babu laifi ya samu kuɗi, ƙarfe goma ya nufo gida, a gurin mai tsire ya samu takarda ya naɗe a leda ya shigo gidan, a ƙofar ɗakin Kaka ya zauna yana cewa. "Gaskiya tsire duniya ne, musamman idan kana da kuɗi zuciyarka bata mace ba." Ya rinƙa ya mutsa ledar kamar yana cin wani abu, sai da ya tabbatar ya gama aikinsa ya miƙe ya nufi ɗakin Mama. Tana zaune tana karatu babu sallama ya nemi guri ya kwanta ya rufe fuskarsa da hula, Mama bata hanasa ba ta cigaba da karatunta, bayan ta gama ta yayyafa masa ruwa da ƙyar ya farka, ta riƙe hannunsa suka nufi tsakar gida ta ce ya yi alwala, da ƙyar ya yi suka nufi ɗaki ta shimfiɗa darduma ta ce ya yi sallolin da bai yi ba. "Tab wallahi sallolin suna da yawa zan dai rage ko babu yawa." Iro ya faɗa yana tura baki, Mama tayi banza dashi ta kwanta Iro ya fara salloli yana idarwa yake tayar da wani sai da ya kai ƙarfe ɗaya, sannan ya tashi Mama da baccinta ya yi nisa, cike da takaici ta ce. "Lafiya zaka tasheni ina bacci.?" Ganin yaƙi cewa komai ta koma ta kwanta sai da ya bari ta fara bacci sannan ya ƙara tashinta yana cewa. "Mama tashi muyi dariya dan Allah." Mama tayi banza dashi, shi kuma ya dage sai ta tashi sunyi dariya. Ganin ba zata tashi ba ya miƙe ya lallaɓa ya ɗau tuwo kwano ɗaya ya fita, ƙofar ɗakin Baba ya nufa ya raba tuwon biyu ya yi masa kwalliya, duk ya ɓata ƙofar ɗakin sai da ya shafe ko ina da tuwo ya nufi ƙofar ɗakin Inna yana cewa. "Wanda tayi girki dole ta samu ladanta." Kamar yanda ya yi a ƙofar ɗakin Baba itama haka ya yi mata, ya dawo ɗaki ya ɓoye kwanon ya kwanta bacci ya ɗaukesa. Likes and sharing Ta Batulu ce ✍️*JUMMALA DILLALIYA* Written Sa'adatu Ta Batulu Godiya ta tabbata ga Ubangiji talikai sarkin da baya bacci ballantana gyangyaɗi, yanda na fara rubuta labarin na lafiya ubangiji kasa in gama lafiya, dubun godiya ga ƙawayena mallamai na ƴan uwana masoyana, Ta Batulu na alfahari daku. Gargadi ban yarda a sauya mun labari ko wani abu dana rubuta ba. Group https://chat.whatsapp.com/C9Gc6WqmpCMEMIMFY5gSpy?s=cl&p=a&ilr=1&amv=3 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* Chapter 2️⃣ Washegari Baba ya buɗe ƙofa zai tafi massalaci yaji ƙafarsa ya taka wani abu, ya haska fitilar wayarsa tuwo ya gani an shafe ƙofar ɗakin, ya samu ruwa ya wanke ƙafarsa ya nufi massalaci ko da aka idar da sallah bai fito ba, sai da gari ya yi haske ya miƙe ya nufi gurin mai shayi. Itama Inna kamar yanda Baba ya yi haka ya kasance da ita, har sai da takusa faɗuwa ba ta ce komai ba tayi sallah, sannan ta fara masifa matan gidan suka shigo suna tambayar abin da ya faru, duk wanda yazo sai  ta nuna masa ƙofar ɗakinta Mama ta ce. Allah ya kyauta ta bar gurin Inna ta rinƙa masifa tana zagin Iro domin tayi rantsuwa wannan aikin sa ne, ƙarfe goma Baba ya shigo gida ya tsaya gurin Kaka suka gaisa ya miƙe zai tafi ta kirasa ta ce. "Jiya ina bacci naji motsin Iro yana cin nama a ƙofar ɗakina, kuma nasan baya sana'ar komai." Cike da mamaki Baba ya ce. "Nama kuma.?" "Ƙwarai da gaske nama, domin sai dana gani da idona, Maganar gaskiya ba zan zama gantalalliya in zuba ido ina ganin ɓarna a gidana ɗana ban tsawatar ba, dan haka kaje ka bincike sa." Baba ya miƙe ya nufi ɗakinsa. Da rana Iro ya shigo gida ɗauke da babban littafi ya zauna a tsakar gida ya kira Samira ya aiketa ta kira masa Bashir da Nasir. Ba a jima sosai ba suka shigo suna tafiya a karkace Iro ya yi fito suka amsa shima ya miƙe ya fara tafiya a karkace, har zuwa ƙofar ɗakin Kaka suka lanƙwashe ƙafa Iro ya karkata murya bakinsa ya karkace ya maƙale ido ɗaya, sannan suka haɗa baki suka gaisheda. Kaka ita kam tana zaune ta zabga tagumi tana kallansu, Iro ya fara miƙewa yana tafiyar guragu ɗaya bayan ɗaya suka fice, Iro ya ɗauko tabarmar Aunty ya shimfiɗa suka zauna. "Wani sabon sana'a na samo mana, wanda zamu rinƙa samun kuɗi." Iro ya faɗa yana miƙa musu littafin, koda suka buɗe basu ga komai ba sai rubutu guda ɗaya an rubuta. Register suka kallesa cike da mamaki, Iro ya cire glass ya karkace hula ya ce. "Daga yau duk wanda zai yi kiwon kaji sai yazo ya yi register na saka hannu na bashi iznin. Idan kuma ba haka ba zamu ɗauke kajin zan gina babban keji in zuba a ciki." Suka nuna masa cewar aikin yana buƙatar kuɗi, Iro ya yi dariya ya ce. "Karku damu in sha Allah zan samo kuɗi, amman dole sai kun tayani." Duk sun amince da hakan kowa ya watse Iro ya shiga ɗakin Mama ya ɓoye littafin ya fito zuwa gurin Inna. Kamar abin arziki ya zauna ya zuba mata ido. "Wallahi Iro bana san munafurci ya zaka zuba mun ido saboda baƙin hali irin na uwarka." Inna ta faɗa tana jefa masa takalmi. Iro ya ce. "Allah sarki Innata abin ƙaunar Iro, baki san abin da yake shirin faruwa dake ba shi yasa nayi tagumi ina tayaki jimami." Tana jin ya faɗi haka ta matso kusa dashi, Iro ya yi ƙasa da murya ya ce. "Amman lokacin da Baban mu zai aureki bai ganki da rana ba, dan wallahi da ya ganki da rana ba zai aureki ba." Yana faɗa ya yi waje da gudu yana dariya, Inna ta miƙe a fusace ta nufi gurin Mama tana zuwa ta fara zaginta tana tsine mata gida ya fara rikicewa da hayaniyya Mama tun tana kawar da kai har sai data fara bayar da amsa. Kaka tana zaune daga cikin ɗaki tana ganin duk abin da yake faruwa hasalima ko kallansu ba tayi ba, kamar za suyi dambe Aunty ta shiga tsakani tana bayar da haƙuri, Inna sai da tayi hawaye saboda ɓacin rai Iro yana maƙale a bayan mutane yana kallan abin da yake faruwa, da daddare Baba ya tarasu gaba ɗaya a ƙofar ɗakin Kaka ya fara faɗa cike da gargaɗi, sai da ya gama masifar sannan ya tambayi abin da ya faru, babu wanda yasan ai nihin abin da ya haɗa kawai dai sunga Inna ta fito tana masifa, amman saboda rashin tsoron Allah Kaka tayi karaf ta ce. "Sadiya ce ta tura Iro ya yiwa Hadiza rashin kunya." Gaba ɗaya mutanen gurin sai da suka riƙe baki hatta Inna sai da abin ya bata mamaki, Mama zata yi magana Baba ya daka mata tsawa, mutanen gidan babu wanda ya yi magana Iro ya miƙe ya shiga ɗaki, ya ɗauko ghana mazgo ya fito ya ce. "Tun da bakwa ƙaunata gwara in tafi yawon duniya ko na huta da masifar gidan nan." Ya yi hanyar waje Kaka ta fashe da kuka tana cewa. "Dan Allah ku taimaka mun kar ku barsa ya tafi na san Legos zai nufa tun da ya faɗi hakan." Iro ya yi karaf ya ce. "Kuma wallahi ƙasan gada zan nufa." Kaka tana jin hakan ta fara salati tana share fuska da gefen zani, Baba ya riƙo Iro ya wurgar dashi gefe, Mama hawaye kawai take sharewa cike da baƙin ciki da takaici. Iro ya kalli mahaifiyarsa yaji tashin hankali ya shigesa. Ya tsani yaga hawaye a idanun mahaifiyarsa, ya faɗi ƙasa yana birgima. Da farko sun yi tunanin wasa ne, sai da suka ga kumfa yana fitowa a bakinsa, yana ta fari da ido duk ya ɓata kayansa ya miƙe yana tafiyar guragu ya nufi ɗakin Kaka baki yana tsiyayar da kumfa. "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un jama'a ku taimaka mun ku bani zawo dan Allah ku bani zawo." Abin da Kaka take faɗa kenan, sauran matan duk sun gudu ban da Mama dake zaune ta kasa ɗago fuska, Baba ya yi ƙarfin halin matsawa zai riƙosa. Iro ya daka tsalle ya faɗa ɗakin Kaka, domin ya yi alƙawarin sai ya koya mata hankali tun da ta saka mahaifiyarsa kuka. Kaka ta fara jan jiki tana matsawa Iro ya zaro harshe yana lashe baki, Baba ya riƙosa ya fito dashi Iro yaƙi tsayawa guri ɗaya burinsa kawai yaje gurin Kaka. Da ƙyar Baba ya kullesa a bedroom ɗinsa. Kaka tana baje a tsakar ɗaki tana mayar da numfashi Mama ta miƙe ta nufi ɗakinta, Baba sai da ya samu natsuwa ya matsa gurin Kaka ya ɗibo ruwa ya bata. "Dole a kai yaron nan gurin mai magani, domin bashi ɗaya bane wallahi." Kaka ta faɗa bayan tasha ruwa. Baba ya yi mata sallama ya nufi ɗakinsa ta window ya leƙa ya hango Iro maƙale a bango kamar ƙadangare, da sauri ya nufi ɗakin Inna. Washegari da safe kowa ya manta da Iro, Baba tun da yaje sallahr asuba bai dawo ba, sha ɗaya na safe Mama ta buɗe ɗakin Baba. Iro yana kwance a katifa ya bubbuɗe ƙafa yana bacci ga fanka yana gudu, cike da takaici Mama ta zabga masa duka ya miƙe a firgice yana cewa. "Yana ina ɓarawon." Ganin Mama tsaye a kansa ya duƙar da kai yana zare ido, ta riƙo hannunsa suka fito zuwa ɗaki sallahr, asuba ya yi zai fice Mama ta riƙosa ta fara magana cike da rarrashi. "Dan Allah Ibrahim ka natsu ka dawo mutum kamar kowa, bana jin daɗin yanda ake hantarar ka a cikin gidan nan kowa ya taso kaine, da laifinka da wanda ba naka ba duk kaine, ka girma amman har yanzu kana aikin yara mai kake so ka zama dan Allah.? Ko kana so zuciyata ta buga ne in mutu kowa ya huta kaima ka huta da takura maka da nake y? Duba kayan jikinka kamar wani sabon mahaukaci, ga wata kafceciyar hula ka saka kamar wanda ya dawo daga dawanau. Duk gidan nan babu mai wannan shigan sai kai haba Iro, ina kake so in saka raina dan Allah.?" Iro ya turo baki yana cewa. "Ni fa yaro ne Mama dan haka dole in ci lokacina." "Dan gidanku kaine yaron.? Ɗan shekara goma sha biyar za a kira yaro.?" Mama ta faɗa a hassale. "Hajiya Maman Iroro Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana." Ya faɗa cike da rarrashi Mama tayi banza dashi, ya fita zuwa ɗakin Kaka. Yau bai sameta a bakin ƙofa ba ya faki idanun mutane ya faɗa ɗakin, Kaka tana kwance tana bacci Iro ya yi sallama da ƙarfi ta amsa tana tambayar wanene, Iro ya ce. "Mutuwa ce tazo tafiya dake gurguwa." Kaka garin sauri har tana tintsirowa daga katifa, suka haɗa ido da Iro ta hararesa ta ce. "Bana san iskanci da iya shege." Iro ya zauna kusa da ita ya ciro ƙaramar wuƙa a cikin aljihunsa ya ajiye ya kalli Kaka data zaro ido ta manne a jikin bango ya ce. "Na farko zan faɗa miki zan fara zuƙe zuƙe da kore kore, sannan zan zama ɗan kidnaping zan kwashe kayana in koma Legos can ƙasan gada, domin na gaji da wannan rayuwar ta rashin ƴanci." Kaka ta zaro ido tana kaɗa kai Iro ya ɗaura wuƙa a saman baki ya ce. "Ban baki damar magana ba mallama mai haɗa husuma daga zaune." Kaka ta gyaɗa kai cike da bin umarni. "Ina so ki saka ɗanki ya gina mun ɗakina wanda zan rinƙa kwana a ciki, domin ba zai yiwu ina kwana ɗaki ɗaya da mahaifiyata ba. Idan kuma bai gina ba wallahi a ɗakin nan zan rinƙa kwana ina saman katifa kina ƙasa." Kaka ta share zufa murya yana rawa ta ce. "To to zan faɗa masa." Iro ya daka mata tsawa ya ce. "Ba faɗa masa za kiyi ba umarni zaki basa, idan kuma ba haka ba zan zama yanda na faɗa miki. Kuma wallahi ku zan fara addaba kafin mutanen gari." Ya miƙe zai tafi ya ce ta bashi kuɗin shan ruwa a hanya, ta ɗaga ƙasan pillow ta damƙo kuɗaɗe masu yawa, ta miƙa masa ya amsa ya fita yana mata gargaɗin kar ta faɗawa kowa, Kaka sai data tabbatar ya bar gidan ta fashe da kuka tana kiran jama'a. Dillaliya kwananta biyu a gida ta shirya fita, bayan sallahr azahar tana ɗaura ɗankwali taji sallamar mace, ta amsa tana cigaba da aikinta babbar mace tana sanye da shiga na alfarma kana ganinta kasan Hajiya ce, suka gaisa daga nan ta gabatar da kanta. "Sunana Hajiya Turai." Dillaliya ta dakatar da ita ta hanyar cewa. "Bana buƙatar hakan, kawai ki faɗi abin da ya kawoki sauri nakeyi zan fita." Hajiya Turai tayi murmushi ta ce. "Aiki na kawo miki da fatan ba zaki watsa mun ƙasa a ido ba." Dilialliya ta miƙe tana faɗin. "Zan wuce idan kin shirya faɗar abin da ya kawoki kya dawo watarana." "Wani taro nake so ku watsa mun keda tawagarki, idan ya kama a zane duk wanda yaje taron bana da matsala da hakan." Hajiya Turai ta faɗa tana ajiye mata ɗaurin dubu ɗaya guda ɗaya, ta nufi hanyar waje tana faɗin. "Ki kasance a shirye." Kafin Dillaliya tayi magana ta fice daga gidan. "Oh ni Jummala naga ta kaina, daga dillanci kuma na koma ƴar jagaliya." Ta ɗauki kuɗin ba tare data irga ba ta ajiye a ɗaki ta fito. Mashiɗa data gama sauraron duk abin da ya faru ta ce. "Mama dan Allah." Dillaliya ta ɗaga mata hannu ta ce. "Karki wahalar da kanki yarinyar kirki, domin ba zan fahimceki ba rayuwa sai da kuɗi, kuma basa samuwa sai da gwagwarmaya da jarumta." Tana gama faɗa ta fita, gidan Aminu ta nufa ganin get ɗin a kulle ta kira yaranta suka iso da motar kwasan kaya, suka kwashe komai na gidan hatta spoon basu bari ba sun tattara komai, suna shirin tafiya maƙota suka firfito suna tambayar abin da ya faru. Dillaliya ta fashe da kuka tana cewa. "Aminu ya saki Safiyya, shi yasa muka zo kwashe kaya." Maƙocinsu bai yarda da abin da ta faɗa ba ya kira number Aminu wayar yaƙi shiga, suka watse dillaliya ta shiga mota suka bar unguwar, bayan la'asar Aminu da Safiyya suka dawo, suna shirin buɗe ƙofar gidan wannan maƙocin yake basu labarin abin da ya faru, Safiyya bata gama sauraron abin da yake faɗa ba ta shiga gidan da sauri, Aminu bai yi mamaki ba hasalima yasan hakan zai faru shi yasa ya ƙirƙiri zuwa unguwa shi da ita, ihun Safiyya ya jiyo daga cikin gidan yana shiga ya sameta a kwance bata numfashi. Ya ɗauketa zuwa hospital. Allah ya jarabci Aminu da ƙaunar Safiyya, lokacin da yaje neman aurenta akwai manyan masu kuɗi da suke ƙaunarta, iyayenta kuma kwaɗayayyune sun amince za su bashi aurenta da sharaɗin sai ya yi mata kayan ɗaki, lokacin baya da kuɗi sosai a hannunsa kuma yana tsoron ya rasata, shi ne akai masa hanyar dillaliya ta haɗa masa kaya masu kyau da tsada akwati da kayan furniture's, da sauran kayan. Safiyya tana ta yanga da iyayi zata auri mai kuɗi har ƙawaye ta sauya. Gida suka nufa da kayan suka shigar mata dashi store ɗin da take ajiye kayan furniture's, ta sallamesu ta miƙe ta nufi gidan Amina. Suna zaune da ƙawayenta dillaliya tayi sallama suka amsa suna ya tsina fuska, babu wanda ya ƙara bi ta kanta suka nufi bedroom cike da mamaki dillaliya ta kallesu ta kwashe da dariya, sanin cewar dariyarta babu alkhairi Amina ta ɗauko ruwa mai sanyi ta ajiye mata, sannan ta sunkuyar da kai cike da jin kunya ta gaisheta, dillaliya tayi dariya ta miƙe ta fita Amina ta bi bayanta tana bata haƙuri, amman dillaliya ko kallo bata isheta ba. Tana zuwa ƙofar gida ta samu Abba yana jiranta gida ta shige kamar bata gansa ba, yabi ta zuwa cikin gidan dillaliya ta miƙa masa hannu, ya kwaso kuɗaɗe masu yawa ya bata suka irga kuɗin da Mashiɗa, sannan ta bashi mashin ɗinsa ya tafi. Bayan sallar magrib ta kira yaranta, ta basu hular rufe fuska ta basu address ɗin Amina ta faɗa musu aikin da za suyi daga nan ta koma gida. Ƙarfe ɗaya suka shiga gida Amina ita kaɗai suka samu a gida, babu wanda ya kulata suka kwashe kayan furniture's gaba ɗaya, zasu fito Amina ta saka ihun ɓarayi suka fito da wuƙa cike da gargaɗi, sai da suka yi nisa Amina ta fashe da kuka ta kira mahaifiyarta a waya ta faɗa mata ƙarya da gaskiya, washegari da sassafe Maman Amina ta nufo gurin dillaliya anyi masifa kamar za a ƙona gidan, kuma dillaliya ta faɗa mata cewar ba ita bace ta kwashe kayan, kuma wallahi sai sun biyata kayanta baram baram aka rabu ana zagin juna. Paid book 700*JUMMALA DILLALIYA* Written Sa'adatu Ta Batulu Group https://chat.whatsapp.com/C9Gc6WqmpCMEMIMFY5gSpy?s=cl&p=a&ilr=1&amv=3 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* Chapter 3️⃣ Da ƙyar Auwalu ya rarrashi dillaliya ta bar maganar kayan, domin tayi rantsuwar sai ta saka an kullesu. Bayan kwana biyu dillaliya tana ƙirga kuɗi, samari guda biyu sukayi sallama ta amsa ba tare data kallesu ba, suka gaisheta bata amsa ba sai data gama ta ɗago ta ƙare musu kallo, tun daga dressing ɗin jikinsu ta fahimci akwai kuɗi ta amsa gaisuwar tana tsaresu da idanu, ɗaya daga cikin su ya ce. "Muna buƙatar motoci guda biyar masu kyau da tsada." Dillaliya ta ce. "Kunga nayi kama da me dillancin motocine? Kuje kasuwa." Ta miƙe zata shiga ɗaki ɗayan saurayin ya ce. "Haba ta fita kunya muna da tabbacin zamu samu duk wani abin da muke buƙata a gurinki." Jin sunan da ya ambata, dillaliya ta tsaya suka yi magana ta amince zata amso musu motoci da driver's kamar yanda suka buƙata, kudaɗe masu yawa suka fitar duk san kuɗin dillaliya sai data ji tsoro kuɗi ne ya kai dubu ɗari biyar, duk da cewar masu motocin ma sai ta basu wani abu amman ta firgita, kuma sun faɗa mata na kwana biyu suke buƙata za suyi biki ne, ta haɗa su da yaranta a matsayin driver's. Suka ajiye magana zasu zo da safe, wani number ta kira ta faɗa masa abin da take buƙata suka yi ciniki, ta tura musu kuɗi ta ware kuɗin yaranta sannan ta adana nata kason, tana zaune tana ƙarewa gidan kallo tayi murmushi cike da gamsuwa da abin da zuciyarta ya raya mata. Washegari motoci suka iso yaranta suka hau bisa umarninta suka nufi address ɗin data basu, harda sabon ɗinki tayi musu kala bibiyu kowani mutum ɗaya, ta shirya ta kwashi kuɗaɗe ta zuba a jaka ta fita. Ta kira mijinta Auwalu ta buƙaci ya rakata wani waje. Suka nufi ƙasan unguwarsu  ta samu fili babba ta siya miliyan biyu da rabi shaidu sun shaida itama ta gayyato mutanenta kowa ya shaida, aka bata takardun fili suka nufi gida cike da farin ciki da murna, Auwalu dai baya farin ciki da wannan siyan filin domin yasan babu alkhairi. Bayan kwana uku Hajiya Turai tayi sallama dillaliya tana zaune tana lissafin kaya, ta matsa ta bata guri, Hajiya Turai ta zauna dillaliya bata ce komai ba sai data gama sannan suka gaisa. Hajiya Turai ta ɗauko pass guda goma ta miƙawa dillaliya ta ce. "Akwai anko guda goma na tawo dashi zan biya kuɗin ɗinki." "Ban fahimta ba." Dillaliya ta faɗa cike da mamaki. "Wannan shine aikin dana ce za ki yi amman bake ɗaya nake buƙata ba, duk da nasan kina da mutane da yawa shi yasa na kawo miki pass da anko keda mutanenki." Hajiya Turai ta faɗa tana murmushi. Dillaliya zata yi magana Hajiya Turai ta ɗaga mata hannu ta ce. "Mijina ne zai ƙara aure, shi ne nake so keda mutanenki ku watsa gurin kowa ya samu rabonsa." Dillaliya ta fara tunani Hajiya Turai ta ciro kuɗi ƴan dubu ɗai ɗai rafa biyu ta ajiye ta ce. "Idan aiki ya kammala zan cika sauran kuɗin. Address da bayanin komai yana ciki." Dillaliya tabi bayanta da kallo. Ta janyo babbar ledar gabanta ta buɗe atamfofi ne Holand masu kyau da ɗaukar hankali, ta ɗauko waya ta kira ƙawayenta Atine Lanti Zulai wajen mutane takwas ta kira, ta faɗa musu abin da take buƙata sannan ta basu atamfa da kuɗin  ɗinki, kowannensu ya yi farin ciki duk da bata faɗa musu abin da zata biya su ba sun san za a samu da tsoka, bayan sun tafi ta aiki Mashiɗa ta kai musu ɗinki daman atamfa biyu ta cire. Bayan kwana uku da misalin karfe takwas gidan dillaliya cike da mutane kowanensu tayi kwalliya kamar zasu je gasar kyau, Mashiɗa ma tayi kwaliyya bisa umurnin mahaifiyarta, domin ta ce mata dole ne taje ta dangwali arziki ƙila ma ta samo saurayi. Sunyi kyau sosai atamfar tayi musu kyau, dillaliya ta fito sanye da gyale a kafada yanda kasan ba ita ta haifi Mashiɗa ba, ta dawo yarinya daman bata da jiki sosai,  tayi gaba tana taku ɗai ɗai suka take mata baya zuwa ƙofar gida motoci guda biyu masu kyau tayi order,  yaranta sune driver's. Daman sun gama tsara komai a gida G.R.A suka nufa kamar yanda suka gani a rubuce babu abin da yake tashi sai kiɗa, hall ɗin ya cika ana jiran shigowar ango da amarya dillaliya da tawagarta suka shiga ciki, Hajiya Turai tayi murmushi tana mata alama da ido, guri suka samu suka zauna Mashiɗa tana gefe jikinta duk ya yi sanyi tana tsoron abin da zai faru. Ango da amarya suka shigo maƙale da hannun juna dillaliya ta ƙare musu kallo gaba ɗaya, angon ba yaro bane amman yana da kuɗi amaryan kuma yarinya ce. "Ikon Allah, yanzu wannan ne amaryan kamar a karya a jefar." Dillaliya ta faɗa tana kwashewa da dariya, mc ya gabatar da shigowarsu aka fara raba abinci dillaliya da tawagarta suka cika cikinsu sannan suka miƙe ta kalli Mashiɗa ta ce. "Ki zauna a mota ki jiramu." Mashiɗa zata yi magana dillaliya tayi gaba ta bata guri, ta share hawayen fuskarta ta fita cike da takaicin halin mahaifiyarta. Hajiya Turai ta gyara zama tana murmushi dillaliya suka nufi filin gurin da mutane suke rawa,  wata budurwa tana ta rawa ƙirji a waje kayan duk sun matseta, dillaliya ta faki idanun mutane ta daki tsakiyar kanta yarinya ta ƙwalla ihu ta faɗi, hankali mutane ya koma gurinta dilalliya da mutanenta suka fara wargaza gurin, kamar ƙiftawar ido sunyi kaca kaca da gurin mc ma ya samu rabonsa, ta janyo kunnen amarya ta ce. "Mijin wata shine zaɓin ku." Hall ya ruɗe mutane suka fara guduwa ango tun da yaje karɓan amarya a hannun dillaliya Atine data zo da gudu zata janye decorations ɗin gurin ta bangajesa ya faɗi da ƙyar ya miƙe ya nufi hanyar waje. Ƙawayen amarya sun sha zana. "Dan ubanku ba kunce mijin wata shine zaɓin ku ba, zaku gane shayi ruwa ne." Dillaliya ta faɗa tana tsula musu bulala. Dambe ya kaure da dangin amarya. Mutanen gida sun cika ɗakin Kaka amman taƙi cewa komai, Baba ya yi sallama ya shigo suka watse, suna ƙananun surutai. "Saboda gantalewa irin naka, ta yaya Sadiya zata rinƙa kwana ɗaki ɗaya da saurayi." Kaka ta faɗa tana share hawaye. Baba ya ce. "In sha Allah za su rinƙa kwana a ɗakin matasa." Da sauri Kaka ta ce. "Kul kayi wannan gangancin, ta yaya zaka ɗauki Iro ka kaisa cikin masu zuƙe zuƙe da kore kore. Ban amince ba domin sanin kanka ne duk cikin yaran gidan nan Iro ne kawai baya shaye shaye, dan haka wancan filin ka gina masa ɗaki." Baba zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce. "Umarni nake baka." Baba ya nufi ɗakin Aunty kamar abin arziki ta faɗa masa ƙarya da gaskiya, ya nufi ɗakin Mama ya zageta tas ya fita kuma duk abin da ya faru a kunnen Iro, domin yana da ma'aikata a gidan. Baba ya fara tunanin yanda zai yi domin aure yake son yi, kuma idan ya kwashe kuɗin ya yi gini babu kuɗin aure kansa ya kulle ya rasa yanda zai yi, har bayan magrib bai samu mafita ba ya nufi gurin abokinsa Talba, sun jima suna tattaunawa kafin su tsayar da magana. A daren Iro ya nufi gurin bazawaran Baba ya karɓi dubu goma ya ce mata idan yazo zai ninka mata, bata tsaya dogon tunani ba ta ɗau kuɗin ta bayar jin cewar Baba ya aiko. Iro ya ɓoye kuɗin ya nufi hanyar gida gab da zai ƙarasa gida ya hango yayyinsa zaune suna shaye shaye, Abdul Nazifi Lado yaran Inna Umar yaron Aunty. "Allah ya raba rai da wahala." Iro ya faɗa yana zurawa da gudu, Nazifi ya zaro adda yabi bayansa da gudu suka take masa baya kowanne da makami, Iro har zai yi kwana ya tuna da fitinar da ya kunna da sauri ya nufi gida, duk suna zaune harda Baba ana shan iska Mama tana ɗaki Kaka tana zaune a cikin ɗaki labule a ɗage, ƙananun yaran gidan suna cin abinci Mansura ƴar shekara 18 Samira 10 Yaseer 5 yaran Inna Isma'il Ahmad twins ne yaran Aunty, Iro ya shigo gidan da gudu yana cewa kowa ya yi takansa, ɗakin Kaka ya shige kafin su miƙe Lado sun shigo da gudu, ganinsu kamar zasu je yaƙi kowa ya yi takansa Baba ma ɗaki ya gudu, Kaka ta rarrafa ta kulle ƙofa suka fara kewaye gidan suna ihu. "Iro tun da kazo duniya nake shan wahala har yanzu." Kaka ta faɗa tana fashewa da kuka. Iro ya fito daga bayan drower ya ce. "Ai idan kika ga kin huta wallahi mutuwa nayi." "Dan ubanka zoka bar mun ɗaki shege mai kama da uwarsa." Kaka ta faɗa tana jefa masa kwano. Iro ya shafa kansa ya fashe da dariya ya ce. "Kaka kiji tsoron Allah, wannan ƙaton kan nawa ai na kine ga wani sharɓeɓen baki nawa kamar na zomo kuma duka a gurinki na gada. Amman shi ɗayan Kakan namu yafiki kyau da haske. daga gani auren dole akai muku dashi sadakarki aka basa aka cucesa." Kaka ta fashe da kuka tana cewa. "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un Iro ni kake zagi saboda taɓewa da rashin albarka, wallahi Sadiya ta cuce ni." "Wallahi kina ƙara ambatar sunan uwata sai na buɗe ƙofar nan." Iro ya faɗa yana ɗaure fuska. Kaka ta rufe baki tana hararansa ƙofar suka ji ana bugawa da ƙarfi kamar za a karya. Kaka ta rarrafa ta shige toilet ta rufe Iro ya shiga drower, ranar kam sunga hauka iya hauka wajen ƙarfe ɗaya su Lado suka kwanta a tsakar gida bacci ya ɗaukesu, Iro ya bubbuga ƙofar toilet ya cewa Kaka ta fito. "In fito ka kasheni koh.? Wallahi ba zan fito ba." Iro da ƙyar ya lallaɓa ta fito, ya taimaka mata ta hau katifa ya kwanta a saman kujera asuba ta gari. Sha biyu dai dai dillaliya taji wayarta tayi ring da sauri ta fice mutanenta suka take mata baya, mota suka shiga suka bar gurin da gudu, gaba ɗaya sun lalata hall ɗin sun sha dambe da dangin amarya kasancewar dangin amarya fitinannu da ƙyar suka ƙwaci kansu. Amarya da ƙawayenta sun sha zana a gurin dillaliya, domin harda bulala taje taro ya watse kowa ya yi takansa, sai da aka sauke kowa a gida dillaliya ta tashi Mashiɗa dake bacci suka shiga gida, Auwalu yana zaune a tsakar gida yana gyangyaɗi dillaliya, tayi sallama ta shiga ɗaki Mashiɗa ta nufi ɗakinta, ya miƙe ya kulle gidan ya dawo bai ganta a parlour ba ya nufi bedroom nan ma bata nan har zai fito yaji ƙaran ruwa a toilet ya zauna a bakin gado yana jiranta, dillaliya ta fito wanka ta shirya ta kwanta Auwalu ya ce. "Dan Allah ki tashi muyi magana." Ta miƙe tana kallonsa. "Dan Allah mene ne amfanin wannan rayuwar da kike yi.?" Auwalu ya faɗa cike da rarrashi. "An taɓa kawo maka ƙarata an kamani da wani.? Ko kuma anganni ina cin amanar aurenka.?" Dillaliya ta faɗa tana hararansa. Auwalu ya girgiza kai, ta cigaba da magana. "Neman kuɗi kawai nakeyi bana sata bana shirka bana bin maza bana maita, ka godewa Allah." Tana gama faɗa tayi kwanciyarta. Bayan kwana biyu babu inda ta fita tana gida tana lissafin ta yanda zata fara gini, gashi bata da kuɗi masu adashi sun kwasa ta rasa yanda zata yi. Hajiya Turai ta aiko mata da kuɗi dubu ɗari uku, dillaliya tayi murna kamar zata yi rawa ta kira Mashiɗa ta bata dubu goma ta siyo kayan kwalliya, sauran abokan aikin ta ware musu nasu hatta yaranta sai da suka samu da tsoka, idan ku kayi mata aiki tana biyan su da tsoka shi ya sa duk wanda ta kira yazo ya yi mata aiki yake zuwa, babu laifi ta wannan fanin tana da kirki da mutunci tana ƙaunar mijinta da ƴarta guda ɗaya da Allah ya bata. Dillaliya ta samu mijinta da maganar gini, ya bata shawaran tabi komai a sannu kar tayi gaggawa, ta nuna masa tana buƙatar gidan da yafi wanda suke ciki girma, domin tana so ta ƙara faɗaɗa kasuwancinta. Ta Batulu ce ✍️ Ta Batulu ce ✍️*JUMMALA DILLALIYA* Written Sa'adatu Ta Batulu Group https://chat.whatsapp.com/C9Gc6WqmpCMEMIMFY5gSpy?s=cl&p=a&ilr=1&amv=3 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* Chapter 4️⃣ A ƙarshe ta yanke shawarar yin abin da take ganin shine mafita, ta cigaba da harkokinta kamar yanda ta saba ta fara gini a hankali idan ta samu kuɗi ta zuba, Auwalu ya ce zai taimaka mata amman ta nuna bata buƙatar hakan, tana zaune tana lissafin adashin da za a zuba taji sallama ta yi hamdala tana faɗin. "Ga kuɗaɗen nan sun zo Allah yasa masu tsokane." Matasa uku ɗaya yana da jiki suna sanye da kaya masu kyau, dillaliya ta amsa sallamar ta basu gurin zama, sanin cewa gidan na jama'a ne yasa bata zama babu mayafi. Suka gaisa ta zuba musu ido tana jiran abin da zasu ce, babbar cikinsu ya gyara zama ya ciro ɗaurin dubu ɗaya guda biyu ya ajiye mata ya ce. "Muna buƙatar iyayen ƙarya waɗanda zasu je nemo mana aure." Dillaliya ta ƙare musu kallo ta ce. "Ku faɗa mun dalilin da yasa kuke neman hayan iyaye, domin ba zan saka kaina a masifa ba." Ɗaya daga cikin su ya ce. "Sunana Aliyu akwai yarinyar da muke soyayya da ita, ƙanin mahaifina ya ce ba zan aureta ba sai dai in auri ƴarsa ni kuma ba zan iya aurenta ba shi yasa nazo ki yi mun jagora dan Allah." "Kana nufin kai ɗin marayane.?" Dillaliya ta faɗa cike da tuhuma. Sun tattauna sannan suka faɗa mata kuɗin da za su biya dillaliya ta cika da farin ciki, ta karɓi address ɗinsu ta ce sai tayi bincike ta gano gaskiya sannan zata shiga maganar, sun amince da abin da ta faɗa suka yi sallama ta basu kwana biyu akan su dawo suji result. Baba ya kira ma'aikata suka ginawa Iro ɗaki ciki ɗaya, harda toilet lamarin da ya janyo cece kuce a gidan kasancewar akwai part ɗin ƙannen Baba guda biyu da suke zaune a gidan Hudu Yusuf kowanne da iyalinsa, sai ya zamana babu zancen da suke yi sai maganar Iro Mama ta zubawa kowa ido tana bin yaronta da addu'a. Iro ya haɗa kuɗaɗensa aka gina masa babban keji mai hawa uku, ya ajiye a ƙofar ɗakinsa bai cewa kowa komai ba ya cigaba da rayuwarsa, bayan kwana biyu Kaka tana sallar walha ya faɗo ɗakin yana cewa. "Kaka yanke sallar nan kiji wata lukutar masifa." Tayi banza dashi ta cigaba da sallah, ya fashe da kuka yana cewa. "Yanzu shike nan duk mutuwa zamuyi, inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Kafin ya rufe baki yaga Kaka a kusa dashi tana cewa. "Ban fahimci abin da kake nufi ba.?" "Tashin ƙiyama za a yi gobe, gayi can jama'a sunata shiryawa nace bari in zo in faɗa miki." Iro ya faɗa yana fashewa da kuka. Kaka ta ce. "Da gaske kake yi ko wasa Iroro na Hajiya Kaka ikon Allah."  Iro yana kuka ita ma ta nayi a zahiri idan ka kalli Iro kasan ba kuka yake yi ba, buɗe baki kawai yake yana ƙyafta ido. Iro ya ce. "Kaka bai dace ki yi kuka ba domin ke Allah ya sallameki." Tayi banza dashi tana cigaba da kuka Iro ya janyo kwanon dambun nama, ya cika baki yana fashewa da kuka. Bata ce masa komai ba hasalima ido ta zuba masa Iro ya rinƙa dannawa a bakinsa yana cigaba da kuka, sai da yaci da yawa sannan ya miƙe yana cewa. "Ni kam zanje in yi shirye shirye." "Tsaya muyi magana." Kaka ta faɗa cikin kuka. Kiran sallah suka ji a massalacin ƙofar gida lamarin da ya ƙara ruɗa Kaka ta shige toilet, speaker massalaci ne ya samu matsala ake gyarawa, duk wani abinci da yake ɗakin sai da suka fitar dashi wasu har sun lalace, kuɗaɗe wasu duk sun manne da juna tsabar ajiya, Iro ya samu kuɗi da yawa Kaka ta rinƙa sadaka har da matan gida kowa ta bashi kuɗi da nama, Baba da ƴan uwansa duk sun samu nasu harda matan gida, lamarin ya ɗaurewa kowa kai tana kuka tana bayarwa kamar anyi mata dole, sai data rabar da komai na ɗakinta wayarta kawai ta tsira dashi. Kuma taƙi cin komai tana zaune da charbi wayar ma ta ce ta baiwa Iro kyauta. Washegari Kaka tayi zuru zuru tana zaune da charbi a hannu, idan taji motsin tafiya sai ta fara faɗin kalmar shahada. Iro ya shigo ɗakin yana cewa Kaka ya dace muci abincin ƙarshe a tare. Da ƙyar ya lallaɓa ta amince ya karɓo mata abinci ya faki idanunta ya zuba maganin bacci, domin ya tabbatar jiya ba tayi bacci ba Iro harda lemun kwalba ya siyo mata Kaka ta cinye abincin tas lemun ma ta shanye tana lashe baki, ta matsa kusa da katifa tana jan charbi Iro ya gyara gurin ya yi waje, suka haɗu da abokansa suka tafi tsokanar mutane. Har bayan kwana ɗaya Kaka shiru ta samu Baba ta faɗa masa abin da ya faru, sai da ya yi dariya a ɓoye Kaka saboda jimamin kuɗinta sai da aka ƙara mata ruwa, a lokacin Aunty da Inna suka ƙullawa Mama sharri wanda ya yi sanadiyar da Baba ya saketa saki ɗaya, abin da ya faru shi ne bayan ta gama girki ta zubawa kowa nasa Iro ya ɗau na Kaka ya kai mata ashe Inna ta zuba kalanzir a cikin abincin, Kaka ta kira Baba da sauran mutanen gida ta faɗa musu Mama tana so ta kasheta, babu bincike Baba ya danƙara mata saki a daren ta bar gidan, kuma duk abin da ya faru akan idanun Iro yaji komai yaga komai, tun daga lokacin ya ƙullaci Inna da Kaka. Baba yaje biko Mama ta ce ta haƙura da aurensa ya tura Iro yaje ya rarrasheta ya kitsa masa abin da zai faɗa mata, shi kuma yana zuwa ya ce mata kar ta dawo gwara ta zauna a gidansu, Mama ta buƙaci Iro ya zauna a gurinta Baba yaƙi amincewa, Iro yana sane da motsin kowa har lokacin da Mama tayi sati ɗaya da barin gida a ranar ya kwashe kajin gidan gaba ɗaya, ya zuba su a keji ya ce duk mai san kiwon kaji sai ya yi register ya saka hannu, tun suna ganin lamarin wasa suka fahimci da gaske yake yi, kowa ya shiga zaginsa yana aibatasa, ya yi banza dasu babu ruwansa da kowa idan yana jin yunwa ɗakin Kaka yake zuwa ya ɗau abinci, domin yanzu basa zuba masa abinci a gidan anyi ƙaramin yaƙi da Iro akan ya saki kajin da ya kwashe, amman ya yi rantsuwa ya ce sai sunyi register ya basu iznin kiwo. Lamarin da ya fusata Inna ta ka maganar police station, domin kajinta sunfi yawa a gidan babu wanda ya nuna mata hakan kuskure ne, Kaka bata san abin da yake faruwa ba tana bacci a ɗakinta ko hayaniya bata jiba. Ƴan sandan abin ya basu dariya Iro da littafinsa da biro a cikin aljihu, sunyi sunyi ya sakin musu kaji ya ce babu makulli a hannunsa, an duba jikinsa babu suka je har ɗakinsa suka duba nan ma babu, Inna ta ce a kullesa har sai ya fito mata da kajinta ɗaya daga cikin ƴan sandan ya bata shawarar suje gida su rarrashesa, domin idan aka kullesa kajin za su iya mutuwa babu abinci, Inna tayi banza dashi ta saka masa ido tana tunanin ba zai iya ciyar dasu ba, Iro ya kwaso kajin maƙotansu ya kulle har kwana ɗaya bai sake su ba a ranar me kajin tazo Iro ya faɗa mata sai tayi register, sannan ta biya kuɗin abincin da suka ci da ruwa ta fara dariya tana ganin lamarin kamar wasa. Ganin da gaske yake yi ta rinƙa lallaɓasa amman yaƙi haka nan ta biya ta kwashi kajinta tayi gaba, Inna data gaji tazo ta ce ya faɗa mata nawa zata biya ya bata kajin ya lissafa mata abincin da sukaci da ruwa da makwancin da suka kwanta da kuɗin register, Inna ta kama baki tana kallonsa tayi ƙwafa ta ce. "Bari Abdul yazo ya karɓan mun kajina." Iro ya yi banza da ita ya miƙe ya bar gidan ya nufi gurin Mama. Dillaliya tayi bincike bayan ta fahimci gaskiya Aliyu ya faɗa mata, babu ɓata lokaci tayo hayan mutane suka nemo aure, kamar da wasa lamarim ya tabbata an saka lokaci sati ɗaya kamar yanda ango ya buƙata, dillaliya ta haɗa kayan akwati masu kyau da tsada gidan ma ita ce ta shirya musu aiko ta samu kuɗaɗe sosai, bayan an ɗaura aure da kwana ɗaya ƴan sanda suka zo zasu tafi da ita diilalliya ta ce musu wallahi babu inda zata je domin ba tayi laifin komai ba, ganin zata ɓata musu lokaci suka ce matan su kamata. Dillaliya ta shige gida ta kulle suka rinƙa dukan gidan kamar zasu karya, ganin taƙi buɗe ƙofa suka tafi akan zasu dawo anjima. Bayan la'asar Auwalu ya dawo gida ya ɗauki dillaliya suka nufi police station, ba wani babban case bane ƙanin Baban Aliyu ne ya kawo ƙaranta akan abin da tayi, dillaliya zata yi magana Auwalu ya hanata ƴan sanda suka kira Aliyu, aka mayar da magana daga nan suka sallami dillaliya suka bata haƙuri domin sun gano bata da laifi, aiko ta ƙi tafiya ta ce wallahi sai anbi mata haƙƙinta na ɓata mata suna a cikin gari, da ƙyar Auwalu ya janyeta suka tafi gida suna tafe yana mata faɗa, shi yana tsoron ranar da zata ɗauko masifar da yafi ƙarfinta domin bai san yanda zai yi ba, gashi bata jin magana. Dilalliya tun daga lokacin ta sanja tsari idan kazo tayi maka aiki sai an buga takarda ka saka hannu. Bayan sati biyu tana shirin fita tayi baƙuwa suka gaisa ta gabatar da kanta sannan ta ce. "Sunana A'isha, ina tafe da kayan furniture's masu kyau idan zaki siya." Dillaliya ta buƙaci ganin kayan A'isha ta faɗa mata second ne kayan ba sababbi ba, dillaliya ta kira yaranta suka tafi gidan A'isha. Mai gadi ya buɗe musu ƙofa suka shiga dillaliya taga kamar kayan sojojine a jikinsa, ta kalli A'isha murya yana rawa ta ce. "Yana ga kayan sojoji a jikin me gadi." "Mijina babban soja ne, ya auroni a kudu shi ne muka samu saɓani ya sakeni kuma bani da kuɗin motar komawa gida, shi ya sa nazo gurinki ki sai kayan ɗakina in koma garin mu." A'isha ta faɗa hawaye yana wanke mata fuska. "Haba dan Allah ya zaki yi mun hakan, me yasa tun farko baki faɗa mun ba sai yanzu. Gaskiya kin cuceni ni." Dillaliya ta faɗa a hassale. "Dan Allah ki taimaka mun wallahi mijin nawa mahaukaci ne, kullum sai ya zaneni idan kuma na gudu ya zane ƴan aikina, saboda yana da lalura in har yazo wucewa ya ganka a tsaye kawai sai ya ciro belt ya fara dukanka." A'isha ta faɗa da iyakar gaskiyarta. Dillaliya ta zura da gudu tana cewa. "Kice gidan mahaukaci kika kawo mu." Tana zuwa akin get me gadi ya ce. "Oga yana hanya ya ce kar a bar kowa ya fita daga cikin gidan nan." A'isha jin abin ya faɗa ta fashe da kuka tana faɗin. "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Dillaliya da yaranta sunyi cirko cirko a tsaye, ta kira yaranta suka matsa gefe magana suke yi a hankali, suka nufo gurin mai gadi gaba ɗayansu juyin duniya yaƙi basu hanya gashi ƙaƙƙarfa ne ba halin su tura shi gefe, suna cikin jimami oga ya dawo. Me gadi ya buɗe masa ƙofa ya shigo dillaliya ta buɗe murya ta ce kowa ya kwanta, harda A'isha duk su kayi plat a ƙasa mai gadi ya matsa ya buɗe masa ƙofa, dillaliya ganin get a buɗe ta zura da gudu ta fice, yaran ma suka gudu A'isha tabi su a baya, oga ya bayar da umarnin a sakin musu karnuka, dillaliya taga wanda yafi ta bala'i gudu suke yi karnuka suna binsu, ta jefar da gyallenta takalmin ma ta cire ta haɗa da jaka ta riƙe, ganin sun kusa cin musu ɗaya daga cikin yaranta ya shige wani babban kwata, ɗaya yaron ya ɗibo ƙasa ya watsa musu ya ɓuya a zauren wani gida, yaran duk sun nemi mafaka saura dillaliya da A'isha gashi tsakanin unguwar zuwa gidanta akwai tazara, haka nan ta dage tana zabga gudu tana yi tana kuka tana tsinewa A'isha, domin duk ita ce ta ja musu wannan bala'in A'isha ganin dillaliya zata samu mafaka ta barta, yasa ta riƙo rigarta suna gudu a tare, dillaliya data fahimci abin da tayi ta fashe da kuka tana cewa. "Dan uwarki da ubanki ki sakeni, ko nice na haife ki ai kya ƙyaleni in huta kin manne mun kamar zaki koma ciki. To ko a lahira kowa ta kansa yake yi." Hhhhhhh dillaliya tamu ta amana Ta Batulu ce ✍️*JUMMALA DILLALIYA* Written Sa'adatu Ta Batulu Group https://chat.whatsapp.com/C9Gc6WqmpCMEMIMFY5gSpy?s=cl&p=a&ilr=1&amv=3 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* Last free Chapter 5️⃣ A'isha ta ƙara riƙe dillaliya da kyau, ganin babu mafita suka faɗa wani gida suka mayar da ƙofa, duk da haka karnukan suna bakin ƙofa suna haushi kamar zasu karya ƙofar, dillaliya ta shige cikin gidan a guje A'isha tana bayanta, mutanen gida suna zaune a tsakar gida suka ga mata sun shigo da gudu, suna waigen baya. Gaba ɗayansu suka watse kowa ta nufi ɗakinta ta rufe ƙofa, dillaliya ta kama ƙaramin katanga ta dira A'isha tabi bayanta, bata tsaya a ko ina ba sai a bakin titi, napep ta tsayar zata shiga taji an bangajeta an shige, dillaliya ta faɗa da sauri tana cewa mai napep ya yi sauri su bar gurin. Mai napep ya tuƙa da gudu suka bar gurin karnukan suka ƙaraso a guje suna haushi, a cikin napep bayan sun yi nisa dillaliya ta fara masifa tana zagin A'isha. Baiwar Allah tayi shiru tana zare ido lamarin da ya ƙara fusata dillaliya, ta rinƙa tsine mata tana tijjara me napep yana ta bata haƙuri dillaliya hospital ta ce ya kai ta, suna zuwa ta sauka A'isha ta sauka diilalliya ta sallamesa ta shiga gurin Doctor, kamar yanda tayi tunani targaɗe ta samu a ƙafa taimakon gaggawa suka bata aka saka mata drip da alluran bacci, A'isha ta buɗe jakanta ta duba gurin kira my daughter, taga ni last bata tsaya tunanin komai ba ta kira. Mashiɗa ta amsa haɗe da sallama, A'isha ta faɗa mata suna hospital mai wayar bata da lafiya. Bayan kwana ɗaya dillaliya ta farka suna haɗa ido da A'isha ta ce. "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un wannan wani irin masifa ne, wai ke baki da dangine da zaki manne min kamar kaska.?" A'isha ta kawar da kai, domin har ta fara sabawa da masifar dillaliya. Tana ta masifa tana zaginta kuma duk da hakan bai hana ta miƙa mata hannu akan ta taimaka mata ba, kwananta biyu aka sallameta suka tafi gida tare da A'isha, gidan kullum cike da mutane masu zuwa dubiya wasu mutanen ma dillaliya bata san su ba, harda Hajiya Turai Atine da sauran tawagar kullum sai sun zo dubata, bayan sati ɗaya Auwalu ya kira su gaba ɗaya ya kalli dillaliya ya ce. "Na zuba miki ido har yanzu baki ce mun komai game da wannan baƙuwar ba, ko kin fara dillancin mutane ne bani da labari." Dillaliya ta kalli A'isha ta zabga mata harara, duk abin da ya faru sai data faɗa masa, tun daga faɗar da suka yi da mijin da zuwan da suka yi gidan, Mashiɗa har tana hawaye saboda dariya dillaliya ta kai mata duka Auwalu ya riƙe hannun yana ƙunshe dariyarsa. Ya karɓi address ɗin A'isha daga nan ya fita, ranar data cika sati biyu da daddare suna zaune a tsakar gida suna shan iska, Auwalu ya yi sallama mijin A'isha yana bayansa dillaliya tana ganinsa ta miƙe zata shige ɗaki, Auwalu daya kasa riƙe dariyarsa ya riƙota yana dariya, kowa sai da ya yi dariya a gurin A'isha ma gurin ɓuya take nema, Mashiɗa tana zaune tana dariya idan ta kalli mahaifiyarta ta kalli mijin A'isha sai ta fashe da dariya. Da ƙyar aka samu dillaliya ta zauna suka gaisa Auwalu ya ce. "Naje na samu mijin A'isha munyi magana ta fahimta dashi, kuma in sha Allah ba zai ƙara dukanta ba sannan yana baki haƙurin abin da ya faru." Dillaliya tana zaune bata ce komai ba A'isha ta miƙe suka yi sallama da Mashiɗa, mijin A'isha ya yi godiya ya ajiyewa dillaliya kuɗi masu kauri suka fita, basu jima da fita ba yara suka shigo da kayan abinci masu yawa, dillaliya ta sallami yaran ta duba kuɗin da ya bayar, dubu saba'in ta ce. "Ladan jinya da abincin da matarka ta cinye mana." Auwalu da Mashiɗa suka rinƙa dariya suna tsokanarta. Bayan kwana biyu A'isha ta aikowa da Mashiɗa kaya masu kyau da tsada, harda kayan makeup. (zaman da tayi a gidan kayanta ta ke amfani dashi) Dillaliya tayi farin ciki sosai ɗan saƙon ya karɓi numberta ya tafi. Gini ya fara nisa kuɗi ya tsaya dillaliya ta kwashe kuɗaɗen adashin mutane ta zuba a gini. Inna ta samu mazan gidan ta faɗa musu ƙarya da gaskiya, suka tsare Iro zai shigo gida suka zazzabga masa mari amman ya dage ba zai bayar da kajin ba, juyin duniya yaƙi bayarwa ganin za su yi masa taron dangi ya faɗa gida da gudu ya shiga ɗakin Kaka har yana tureta. Ganin shigowarsa a guje ita ma ta fara neman gurin ɓuya domin tasan duk lokacin da ya yi irin wannan shigowar babu alkhairi, suka faɗo ɗakin kowanne da bulala a hannunsa Kaka ta fara zare ido kamar mara gaskiya, sun dudduba basu gansa ba Abdul ya daka mata tsawa yana tambayarta gurin da ya ɓuya, Kaka ta ce. "Wallahi Audu ka zama gantalalle, yanzu idan ba gantalewa ba Iro ne zaku yiwa taron dangi saboda kunga shi kaɗai uwarsa ta haifa. Koda yake ai ba kune gantalallu ba Sadiya ma ai ta gantale data kasa tsayawa ta riƙe yaronta guda ɗaya da Allah ya bata, ni kam gidan Salisu ya zama gidan rashin tsoron Allah, kowa ya zama munafuki Allah ka yafe mun wannan zunubin dana aikata maka, daka jarabceni da jikoki irin su lado." "Hattara dai tsohuwa ko yanzu in yi miki ɓalli ɓalli a baya ki kasa tafiya." Lado ya faɗa yana zaburowa. "Yauwa yaya Lado ko daddatsata ne kayi dan Allah, duk ta addabi mutane da shegen surutu mara kan gado da ma'ana." Iro ya leƙo da kai ta cikin toilet ya faɗa, Kaka ta fashe da Kuka tana tsine masa, suka rinƙa bugun ƙofar kamar za su karya, Baba ya shigo ɗakin sakamakon kiran da Mansura tayi masa, ya kore su ya fara rarrashin Kaka. "Yanzu ace a gidan nan babu wanda yake ganin girma da mutunci na.?" Ta faɗa cikin kuka. Iro ya ce. "Ai girma da mutuncinki kin jima da tuntsirarwa, da kanki dan haka dole ki girbi abin da kika shuka wallahi." Baba ya daka masa tsawa yana umartansa ya fito ya bar ɗakin. "Wallahi babu inda zanje, har sai naji abin da zaku tattauna." Kaka ta ce. "Yanzu idan ba gantalewa da rashin albarka ba, ina ka taɓa jin wannan ɗibar albarkan." Iro ya yi karaf ya ce. "Sai a gidan Salisu." "Wallahi idan ka bari na karya ƙofar nan na shigo sai na kusa sumar da kai shasha kawai." Baba ya faɗa a fusace. "Ka bari sai ka tabbatar da zaka iya sumar dani ɗin." Iro ya faɗa yana dariya. Baba ya miƙe zai nufi toilet. Kaka ta ce. "Wallahi kar ka fara wannan gangancin, nufinka ɓalle ƙofar zakayi ka jamun asara wallahi ban yarda ba, kuma ni banga abin tayar da hankali ba Iro yaro ne baya da cikakken hankali." Ganin ta fara masifa da sababi ya fita ɗakin yana tunanin irin dukan da zai yiwa Iro idan ya kamasa. Har bayan sallar azahar yana ɗakin Kaka abincin da aka zuba mata ya ɗauke ya cinye yasha ruwa ya fita, Iro bai dawo unguwar ba sai bayan isha'i kai tsaye police station ya nufa ya samu dpo ya ce. "Ƴan zuƙe zuƙe da kore kore suna nan a wani lungu suna korawa." Dpo ya yi dariya yana ƙare masa kallo. Babu abin da yafi bashi dariya irin shigar jikin Iro, ga wata kafceciyar hula ya saka ido yasha kwalli ga wata glasa mai ido ɗaya. Ganin kamar bai yarda dashi ba Iro ya fara rantsuwa, dpo ya gargaɗesa idan ƙarya ya yi masa sai ya kullesa a cell. Iro ya amince gabansa yana faɗuwa dpo ya haɗasa da yaransa guda huɗu suka tafi a mota, ta baya suka ajiye motar suka taka da ƙafa Lado Abdul gaba ɗaya suna zane har da abokansu kowa yana zuƙawa, kafin su farga sunga ƴan sanda sun zagaye su Iro ganin buƙata ya biya ya silale ya gudu. Kwanansu uku aka yi belinsu, kowannensu mahaifiyarsa tayi belinsa. Inna dole ta yi belin kajinta a gurin Iro, kuma tun daga lokacin duk wanda ya sai kaji a cikin unguwar sai ya yi register, abokansu duk sun gudu a gefe ɗaya kuma ya taso matan babansa a gaba, Baba sai da ya biya kuɗin da yaje ya amso a gurin bazawaransa, duk lokacin da Iro ya yi laifi ɗakin Kaka yake guduwa ya ɓuya duk da cewar itama ba ɗaga mata ƙafa yake yi ba, amman tana karesa bata ƙaunar laifinsa, ƙannen Baba sunyi gini sun tashi a gidan yanzu daga Baba sai matansa da ƴaƴa. Kaka ta koma part ɗin da suka tashi Iro yana biye da ita, shima ya samu ɗaki guda ɗaya daman ɗakuna ukune da toilet. Gaba ɗaya yaran gidan ya kaisu makaranta amman banda Iro a cewarsa baya da amfani, Kaka tayi faɗan har ta gaji matansa sun hana ya saka shi a makaranta sun ce asaran kuɗinsa zai yi, daga ƙarshe ma suka bashi shawarar ya kaisa almajiranci zai fi samun ilimi mai kyau, ya samu Kaka da maganar lokacin Iro yana kwance a bedroom ɗinta, duk yanda Baba yaso taƙi amincewa daga ƙarshe ta rufesa da faɗa kamar zata dakesa, bayan kwana ɗaya Iro ya samu Inna zaune a ɗaki tana ƙulla gyaɗa. "Allah ya tsareni da sharrinka da makircinka, yaro ɗan ƙarami sai haɗa husuma kamar shaiɗan." Inna ta faɗa tana hararansa. "Za ki ga aikin shaiɗani." Iro ya faɗa yana kawar da kai. "Dan uwarka me ne kake cewa." Inna ta faɗa tana jefa masa kwano ya kauce. Yana zama kusa da ita ya ce. "Ko lokacin da Mama take nan kece uwar Iro, kuma har yanzu matsayinki na nan bai sauya ba." Inna tayi banza dashi ta cigaba da aikinta. "Ni ba wani abu ya kawoni ba, daman nazo in faɗa miki abin da yake faruwa a gidan nan ne, amman tun da bakya buƙata bari inyi tafiyata kawai, daman ance wanda ajali ya yi kira dole sai ya tafi." Iro ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri ta riƙo rigarsa tana faɗin. "Haba Iroron Inna, zauna ka faɗa min abin da yake faruwa mana ɗan albarka, ɗan da aka haifa tsiya yana bacci." Ya ɗau gyaɗa gwangwani ɗaya sannan ya zauna ya ce. "Kullum sai naga Aunty tana barbaɗa wani abu a cikin abincin Baba, ranar zan wuce naga tana haƙa murhun da kuke girki tana binne wani abu. Tana kiran sunanki dana Baba." Inna tayi shiru tana nazarin maganar da ya faɗa, ganin ta fara yarda da maganar da ya faɗa ya miƙe yana baza riga ya ƙara ɗaukan gyaɗa gwangwani ya yi waje. Ɗakin Aunty ya shiga kamar yanda ya faɗawa Inna, haka ita ma ya faɗa mata cewar Inna tana barbaɗawa Baba magani a cikin abinci. Dare ya yi nisa Inna ta miƙe ta nufi kitchen Aunty dake laɓe tana kallonta ta fito a hankali tabi bayanta, Inna ta samu icce ta tona tsakiyar murhu ta ciro ƙaton laya an soka masa allurai, Aunty ta dafe ƙirji tana zaro ido har zata tafi ta ƙara duba gurin taga ƴar tsana, duk anyi wani rubuce rubuce a jikinta babbar magana Aunty ta zaro ido. Inna jikinta har rawa yake yi ta mayar da gurin ta gyara Aunty ta shige ɗaki da sauri . Asuba ta gari muga wainar da za a soya Iro ya kunna bom. Gini ya kammala saura rufi dillaliya ta kwashe kuɗaɗen jama'a ta zuba a gini, daga ƙarshe ta yanke shawarar ta siyar da gidan da suke zaune daman gidanta ne, Auwalu ya bata shawarar tabi komai a hankali, dillaliya ta yi kamar bata ji abin da ya faɗa ba, duk wani kuɗin da yake hannunta ta kwashe ta zuba a gini, har da kuɗin masu haɗa lefe komai ta zuba a gini. Lamarin da ya ƙara zaburar da ita akan neman kuɗi bayan sallar magrib yaro ya shigo ya ce ana sallama da ita, dillaliya ta cewa yaron ya shigo da wanda yake sallama. Wani matashi ya shigo yana duƙar da kai Mashiɗa tana zaune tana gyara ƙumba, wayoyi guda biyu da mashin ya kawo suka yi ciniki, duk da cewar bata da kuɗi a hannunta amman sai da taje maƙota ta aro kuɗi ta biya kuɗin, yana karɓa ya fita da sauri. bayan kwana biyu sojoji suka zo tafiya da ita game da kayan data siya, kayan babban soja ne da wayoyinsu an shiga gidansa anyi masa fashi da makami, sannan sun illata masa yarinya guda ɗaya. Masu adashi suma sun zo karɓan kuɗin su sunyi zuga sun tawo ga sojoji sun zo tafiya da ita. Danqari da sauran tafiya a gaba wannan sharan fage ne. Menene makomar rayuwar Iro? Ya labarin makomar Dillaliya? Duk mai buƙatar cigaba 500 in saka shi a paid group. Iro ga dillaliya citta iya citta 8138098887 Opay Sa'adatu Ibrahim Marubuciyar RAYUWARMU MA'EESHAT WANI SHARRIN YAUDARA ZALLAH KULUWA ƳAR BALA'I MATAR YAYANMU Ta Batulu ce ✍️