Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO:+2349030159301 *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers (p.m.l) Written By Nana Fa'ad In dedication to Fiddausi Sodangi {June,2017} _[>>Page 1-5<<]_ Da misalin karfe biyun dare a garin Maiduguri, b'arayi neh suka shigo cikin wani dank'ararren gida duk fuskokin su a rufe da masks, wani tsohon mai gadi neh a bakin gate suka harb'e da bindiga(silencer) wanda idan anyi harb'i ba lalle bane wanda yake gefe yaji sautin, shiga sukayi cikin main gidan kusan su goma. Suna shiga duk suka rabu kashi biyu sabida gidan babba neh sosai, d'aki d'aki suke bi suna dubawa duk suka fitar da mutanen gidan suka kawo su parlor na kasa. Da Allaji, sai Matar sa, sai yaransu mata guda biyu. Yaransa mata biyu da matar sa duk kuka suke sai Alhaji wanda duk jikin sa yana shocking ya rikice iya rikicewa. Wani husky voice neh yayi magana a cikin b'arayin yace "Alhaji ka had'umini duk kaddarorin ka koh na kashe ka da yaran ka gaba d'aya" Alhaji wanda already ya gama tsorata without hesitation yace "Bara naje na d'auko su please karku kashe mun yaranah they mean a lot to me they are my everything" Yaron yace ''Ama Man of my words, believe me idan ka d'auko kayi signing documents d'in I assure you, you will all be free muje" Tare da Alhajin suka d'au papers d'in a sama suka dawo downstairs yayi signing documents d'in gaba d'aya, ya basa takardun gidajen sa,filaye, company da kuma motoci...Yaron yace "Good Man ashe kana da wayo" juyawa yayi wajen wanda naji suke kiran sa da Oga yace "Oga I am done mu wuce" bushewa da dariya Ogan yayi yace "ISSAM idan kagama aikin ka ai ni ban gama ba" ya cire bindigansa ya harb'e Alhaji a zuciyan sa. Wanda ya kirada Issam was so shocked atake ya cire mask na fuskanshi with so much surprise on his face muryan sa yana rawa yace "Oga bamuyi haka da kaiba, bamuyi zaka kashe shi ba, I directed you to his house sabida inada wani unfinished business da shine I dnt say zamu kashe shi, this is out of our deal" Babban yarinyan Alhajin da taji abunda Issam yake cewa na _I directed you to his house_ a take ta d'aga idonta dan taga wanda ya musu jagora zuwa gidan su, bata san lokacin da taja baya ba, she was speechless and helpless, kuka ma ta kasayi, zuciyanta na bugawa kamar wanda zai fito...... *Few Hours Ago* Gudu yake sosai akan Bike nasa k'irar Dodge tomahawk V10 wanda bike d'in is one of the most expensive Superbike a duniya, dai dai yazo wajen hold up trafic light yakawo red alaman "Stop" kenan duk an tsaya ana jira yakawo green "Go" dan su wuce amma hakan bai hanasa ya wuce ta gefe gefen motoci ba, zai tsallaka ta hanyan daba nasa ba wata mota k'irar BMW hurricane bak'a tazo wucewa, bai ankara ba kawai ya buge motar, neman waje akayi parking na motar, wata yarinya ce wanda ak'alla baza ta haura ashirin da hud'u ba tafito a motar, tasha bak'in abaya tayi rolling kanta da maroon veil, shima guy d'in neman waje yayi ya parking Bike nasa, tafiyan ta mai d'aukan hankali takeyi har ta k'araso inda yake,shi kuma guy d'in baisan da isowar taba sai wani faman duba Bike nasa yake koh yasamu matsala kamar wanda shi aka bugawa bike, wayan sa neh yafara ringing take ya cire a aljihun sa tare da cire helmet nakan sa company BELL ya sa wayan sa a kunne yana waya baima lura da itaba. Da sauri taja baya a lokacin da yacire Helmet na kansa sabida ta matuk'ar razana, a rayuwan ta bata tab'a ganin namiji wanda ya amsa sunan namiji kamar saba, she was speechless tana kallon shi baki, ido hanci bud'e yana juyawa da sauri taja da baya da sauri tashiga motarta ta fisga shi kuma bayan ta kawai ya kalla ya d'auke kai ba tareda ya kawo komai a ransa ba Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad In dedication to Fido Sodangi {June,2017 } Page 6 Gudu sosai take kamar titin na ubanta tana sake sake a ranta, anya mutum tagani koh aljani, atake tace "No mutum neh" tare da bugan siterin motan ta, can tayi murmushi wanda ya bayyana dimple nata da fararen hak'oran ta tas tace "Ya Allah yanxu naga class d'ina, yanxu naga irin namijin da yakamata na aura, duk inda kake sai na nemo ka, sai ka soni, in my whole life ba namijin da ya d'aura ido akaina ba tare da yaji wani abu a HAYAAT nasa ba" haka ta cigaba da driving har ta iso cikin University Of Maiduguri, tana shiga ta wuce parking lot tayi parking motar ta, tafiya take kamar batason tab'a kasa har ta isa cikin faculty of science, direct Microbiology Lab tawuce tun kan tashiga take jin hayaniyan student, kas x3 k'aran high heel nata wanda yabawa students d'in shaidan lecturer su tashigo, tana shiga kaf lab d'in yayi tsit kamar basu suke hayaniya ba. Bayan ta nutsu ta ajiye jakar ta tace "Sorry I am late" tafara musu lecture akan Mycology, batayi minti biyar ba taji waya yana ringing among the students, take ta k'ara murtuke fuska tace "I guess this is the end of my lecture for the whole semester, I told you people time without number to switch off your goddamn freaking phone whenever ina cikin this this damn Lab, so you caused, till we met in my test and exams.... Bye" take ta d'au jakarta tafita a Lab d'in, zo kuga ihun students suna cewa we are sorry ma, wasu na dunduma wanda wayarsa yayi ringing ashar, wasu kuma suna zagin ta suna cewa 'yar k'arama da ita sai shegen fad'in rai kai k'ananan lectures akwai su da bak'in hali especially na Microbiology department. Tana fita ta wuce parking lot tashiga motar ta ta fisga da karfi tabar cikin makaranta, hankalin ta duk yana kan guy data had'u dashi Wannan kenan Back to lbr ""Issam"" ta furta a hankali hawaye kwance akan fuskan ta, Tab'ata da kanwar ta tayi ta dawo daga dogon tunanin da ta fad'a, kanwarta tana kuka tana cewa "Adda Fido sun kashe mana Daddy, Adda Fido ki duba Daddy fa baya breathing" wasu zafafen hawaye neh suka sauka kan kuncin ta atake ta rungume kanwar ta tana cewa "Easy habibti, cool down Shamcy Dad bai mutu ba he is alive In Shaa Allah" tana shafa bayan ta Ogan b'arayin neh ya bushe da dariya yace "Girl I never miss a target, ya jima da wulawa so sai kuyi hakuri" Issam ya cire bindigan sa ya saita akan Ogan su yace "This is not our deal, bamuyi haka dakai ba how dare you" Ogan shima ya saita bindigan sa kan Issam yace "Yeah naji bamuyi haka dakai ba, but munyi haka da Goner" Issam saka hannu yayi akai yace "Ohh My God, how could he, how dare him" Ogan yace "Duk d'aya kuke bird of the same feathers kaga tafiyar mu if you like ka zauna anan" take yayiwa sauran yaran sa hannu suka fita a gidan Issam ma yabi bayan su. Suna fita Fido da Kanwar ta suka fashe da sabon kuka, take su uku da mamar su suka d'aga Daddy'n suka sakashi a mota Fido ta fisga motar da karfi sai asibin NAKOWA Hosp,Suna shiga asibi nurses sukayo kansu, suna ganin bullet d'ayar Nurse d'in tace "Sorry we can't help without a police" Fido a tsawace tace "WTF! what do you mean that you can't help sai mun kira police, can't you see he is dying" ta fad'a tana kuka, Nurse d'in tace "Eh nagani but so sorry madam dole sai da sa hannun 'yan sanda" "Excuse me! My name is not Madam, My Name is Fiddausi so please take note" take ta cire wayan ta tayi dialing number, ana picking tace "Hello Yaya Ahmad its me Fido, kazo da police yanxu yanxu a nakowa hospital Daddy ba lafia" take tayi hanging call d'in tana zub da kwalla, ta rasa yazatayi sai safa da marwa takeyi a asibiti, tana ganin wani doctor yafito acikin operation room taje takamasa tana kuka mai ban tausayi tace "Please Please help my Dad, I can't live without him. I won't be able to bear my life without my Dad. Please help him!" Doctor ya juya ya tab'a Daddy yacewa Nurses su shigar dashi cikin Operation room, d'ayar Nurse d'in tace "but Doc" yace "shhh just shut up" haka suka shigar dashi cikin Operation room d'in suka kulle kofa. Wani saurayi neh yashigo wajen wanda ak'alla shekarun sa zasu kai talatin da biyu, dogo neh sosai bak'i broad chest yana da dara daran ido sai dogon hanci da lips nasa moderate amma bak'i, kallo d'aya zaka masa kasan shi kyakkyawa neh amma kana kallon bakin sa zaka ganeh yana shan abu, tana ganin shi taje ta zube a gabansa tana kuka mei cin rai tana cewa "Yaya Ahmad sun kashe mini Daddy, Yaya Ahmad I can't live without my Dad" Yaya Ahmad ya d'aga ta yace "Haba baby'n Dad nata ki daina kuka, ki daina fad'an haka bashida kyau a musulunci, haba sai kace ba musulma ba kiyi imani da kaddara khairihi wa sharrihi kuma kisani EVERY SOUL SHALL TASTE DEATH" da kyar yasamu ya lallashe ta tayi shuru, mum da Shamcy kam sun gama kariya sunyi shuru, Fido ce zuciyan ta yake bugawa ita ba zama ba ita ba tsayuwa ba tana ta zirga zirga a wajen, Yaya Ahmad ya daka mata tsawa yace "Will you stop moving around and gasping frantically like a lunatic" "I can't Yaya, I just cant ! He's my other half, I love my Dad" a tsawace yace "Just shut up gurl everybody loves his Dad so stop moving around like an insane lunatic" Daidai lokacin wutan room d'in yakawo green, take duk suka zubawa kofan ido, doctor na bud'e kofan Fido taje takamasa tace "Doc, tell me something" "I am sorry we lost him, he is dead" cewar Doctor Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad In dedication to Fido Sodangi {June,2017 } Page 7 Inna Lillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un duk suka furta, Fido kama rigan Doctor tayi tace "Karya kake Doctor, Dad d'ina bai mutu ba, yana nan da ransa, My Dad is alive" ta fashe da kuka, Shamcy da gudo tazo ta rungume Yayar ta suka fashe da wani irin kuka mai tsoma zuciyan duk wani mai sauraro, da kyar da kyar Yaya Ahmad ya lallashe su had'e da musu wa'azi mai shiga rai kan sukayi shuru. A ranar akayi jana'izan sa aka kaisa makwabcin sa. Bayan Wata Uku Zaune suke su uku a parlour duk sunyi shuru Mummy ce tafara magana tace "Tunda yanxu Alhaji ya rasu sai mu koma wajen dangin mu a Katsina dan gaskia Maiduguri nan ya fice mini a ka yanxu" Shamcy tayi caraf tace "Gaskia Mummy nima nafison mu koma wajen Inna a Katsina dan sam yanxu Maiduguri bai mini dad'i" Fido kuma tunani take, idan har ta kuskura tabar Maiduguri ina zata k'ara had'uwa da Issam, caraf tace "Toh Mum ni yanxu ya zanyi da aiki nah, you know I love my Job" Mum tayi jim tana tunani kan tace "Fiddausi ai baza mu barki ke kad'ai a Maiduguri" "Mum toh Yaya Ahmad yana nan ai" "Ahmad baya zama waje d'aya, yau shineh anan gobe shineh anan, koh da Ahmad baya tafiye tafiye bazan tab'a barinki keda shiba a gida d'aya, idan har kinason aikin ki dagaske toh ki nema transfer" "Mum wollah neman transfer da wahala, da kyar su mini transfer" "Zasuyi In Shaa Allah kedai ki rubuta transfer letter" Duk yadda Fido taso Mum tabarta akan ta zauna a Maiduguri amma Mum taki, can bayan tagaji da magiya tace "Toh shikenan Mum your wish is my command, yanxu yaushe zamu koma Katsina" Mum tayi murmushi tace "Koh kefa mamana zuwa next week In Shaa Allah" "Ohk Allah kaimu" Amma a zuciyan tana cewa duk inda Issam yake a fad'in duniyan nan sai ta nemo sa kuma sai ta wulakanta sa, shineh sanadin mutuwar mahaifin ta ita kuma zata zama sanadin shi na barin Dunya...... Yau sati d'aya cif da maganarsu na barin Maiduguri kuma a yau zasu bar garin, Fido duniyan ya gama mata zafi, cikin kwana bakwai da tayi bata zama a gida kullum tana yawo cikin gari koh Allah zaisa ta gansa har zuwa yau da zasu bar garin. Hawaye neh ya sauko akan fuskan ta na bak'in cikin rashin ganin Issam da batayi ba amma tayiwa kanta alkawari har Allah ya d'auka ranta bazata tab'a daina neman sa ba. Maiduguri International Airport Bak'in material da touches red neh a jikin ta d'inkin dogon riga gown tayi rolling da R$S veil Red, takalmin ta high heel bak'i da stones nashi red sai karamin jakan ta black $ red. Farin glass neh mai tsada ta toshe idon ta dashi, ta had'u iya had'uwa amma kallo d'aya zaka mata ka fahimce She was broken, and as she crumpled like a piece of crushed paper. Komai da sanyi sanyi take, Mum neh ta mata magana tace "Haba Habibty ya kike abu kamar mara jini a jiki, please kije ki duba mana sauran kayan mu" Toh kawai tace tare da juyawa, tana tafiyan ta a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki taga Icecream shop ta tsaya ta siya guda biyu, neman kujera tayi ta bud'e Icecream d'in tafara sha kamar wacce ba'a jiran ta, sha take hankali kwance ta manta da tabar su Mum suna jiran ta, K'aran wayan da taji yasa dasauri ta d'aga wayarta dan ganin wanda ke kira, '''Mum'' tagani baro baro kan screen take ta tashi tace "Hello Mum gani nan zuwa fa da kayan" d'ayan hannun ta waya a kunne d'ayan kuma Icecream, ji tayi an bugeta da karfi d'iris yarage ta fad'i kasa dan dogon takalmin dake kafarta, ji tayi a rik'e ta Idon ta gam ta rufe ita ta riga tayi loosing hope zata fad'i jira kawai take tajita a kasa taji an kamota, bud'e idon da zatayi tayi ido hud'u da yaron da tayi wata uku tana neman sa ruwa a jallo kallo kallo suke, fuskan sa a murtuke kamar wanda bai tab'a murmushi ba ya furta "Astagfirullah", da sauri ta d'aga tana gyara jikin ta dan duk ta b'atashi da Icecream, har yanxu bai tafi ba he was starring at her yana kallon ta fuskan sa a murtuk'e so furious, a hankali ta d'aga manya manyan idon ta tana kallon sa idon ta yakai kan Suit na jikinsa fari kal wanda a yanxu ya b'aci da icecream sai kuma wayansa wanda ya fad'i a kasa screen yayi kaca-kaca, a hankali ta furta "Sorry" tsoki yaja yace "Next time you should watch where you're going" ya tsunkuya ya d'auka wayan sa yayi gaba. Ranta idan yayi dubu ya b'aci dan shineh yake tafiya yana danne danne da wayansa, da gudu gudu tasha gabansa tace "Excuse me but you bumped into me" tareda rolling idonta "Yeah, so sai mei kina waya and wasn't looking forward, Just be glad I'm not making you pay for my Suit, da saina sakaki kin wanke" "Kaji Mallam ai nace kayi hakuri and you weren't even kind enough to say it back so I don't think you should be the one asking of reparations. And plus kana danne danne da waya while walking anyways" Kallon ta yake sosai, he was shocked irin maganganun da ta masa dan ba wata mace a duniya data tab'a fad'a masa haka, tabbas her face seems familiar to him, kamar yasan fuskan a wani waje but he can't recall where!!!!!! Wata matace wadda ak'alla bazata haura hamsin ba ta tab'a shi tace "Son what happen" Yayi murmushi yace "Nothing" tareda rik'e hannu ta yace "Let's go" suka fara tafiya suka barta a tsaye a wajen. Murmushi tayi tace "Issam kenan, this is just the beginning, zan shiga rayuwarka, Your HaYaat" Bayan minti talatin jirgin su ya d'aga Abuja dan babu direct flight zuwa Kt,a jirgin sai kallon sa take dan yana gefen su, shi baima san tana gefen suba, wayan ta taciro ta d'auke sa hoto. Bayan sun sauka a abuja taji yana magana da matar da tazo tasamei shi a airport na Maiduguri yana ce mata "Karki damu Umma idan naje UK zan kirata" zuciyan tane ya buga daya ambato UK, yanxu zaibar kasar kenan, Inaaa dole saina bisa duk inda zashi, dole sai nima nabar Nigeria zuwa UK Toh fa *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad In dedication to Fido Sodangi {June,2017 } Page 8 Bayan minti talatin jirgin su ya d'aga zuwa Kt, cikin minti goma sha biyar sai gasu a Umaru Musa Yar'aduwa airport, bayan sun kwashe kayan su suna jira azo a d'auke su zuwa gida, can sai ga wata mota perfection bak'a tazo tayi parking a gaban su, wani saurayi wankan tarwad'a dogo neh yafito a motar fuskan sa d'auke da murmushi ya durkusa har kasa ya gaishe da Mum "Mum sannu da zuwa ina yini" "Lafia k'alau Son mun samei ku lafia" "Lafia k'alau wlhy" mik'ewa yayi yaja gyalen Shamcy yace "Shamcy beb sai k'atuwa kike zama fa" tura masa baki tayi tace "Allah Yaya Khaleal kadaina ce ina zama k'atuwa banso" yayi murmushi yace "Tam naji baby last" juyawa yayi wajen Fido yace "Mss Beauty ina gaisuwa" murmushi Fido tayi wanda yake kashesa tace "Yauwa Mallam" tareda wartan key motar hannun sa ta bud'e motar tashiga driver seat tareda kicking motar ta juya ta d'aga musu gira tace "Sai kuzo mu tafi ai I really wanna go and rest" Goruba road tayi dasu straight cikin wani babban gida, cikin gidan flat neh guda biyar sai kuma upstairs wanda yake bakin gate Flat na gefen Upstairs d'in suka shiga, wata tsohuwace zaune kan kujera ta rik'e remote a hannu tana kallon Mbc Bollywood, yadda ta maida hankalin ta akan Tv sai ka rantse tana jin yaren. Shamcy da gudu tazo ta rungume ta tace "Ohhhhhh My Innas" Tsohuwar tsayawa tayi tana kallon ta tace "Wannan ba Fiddausi ba" Fido tazo gaban ta tace "Kai Inna just five months back fa mukazo Kt hutu ace bakya ganeh mu, a haka kike kallon Indian film koh mei kike kallo a ciki Oho, keba gani meh kyau ba keba jin yaren ba kinga asaran zama kenan" dunkule Inna ta mata tace "Toh ni ina zan ganeh ku, kullum sai k'ara girma kuke kuma uwarku taki ta aurar daku, da a kauye kike da yanxu keda Shamsiyya kunada jika" ta juya ta kalle Shamcy tace "Yanxu ke Shamsiyya shekarun ki nawa" Shamcy ta tura bakin ta tace "Innas I am just Sixteen" "Sittin na gidan ku, ki kiyaye ni 'yar rashin kunya yarinya daga tambayan shekarun ki zakice mini sittin, koh marigayi mahaifin ku baikai sittin ba" Shamcy ta fashe da dariya Fido ce tayi guntun tsaki tace "Inna toh mei tace, tace goma sha shida, a turance Sixteen" "Toh ni ina zan sani, turanci ai sai ku 'yan rashin kunya yaran zamani" Kefa Fedo "Ashirin da hud'u" ta fad'a a takaice, salati Inna tayi ta aza hannu a ka tace "Nashiga uku, yanxu shekarun ki har yaka ashirin da hud'u ba aure ba yaro, Inna Lillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un, ni lokacinda nakeda shekarun ki ai marigayi da wayon sa, gaskia hakan bazaiyu ba, bari Salisu yazo asan yadda za'ayi, a cikin yara samarin gidan sai a had'a ku da d'aya" Fedo tace "Tab, karki ma fara wlhy Inna ni sai nagama makaranta zanyi aure kuma kiji ...." bata k'arasa maganar ba Mum tamata mugun kallo, take tayi shuru "Ni nashiga uku, Makaranta fa kikace, toh wlhy ba a gidan nan ba, shekaru nawa kikayi kina makaranta har yanxu baki gama ba, wannan wace irin kwakwalwa gareki, gaskia wannan rashin illimin a wajen uwarki kika gada ba wajen marigayi Muhammadu ba, kuma keda makaranta yakare" Fedo shiga tayi cikin d'aki dan gani take a yadda takeji a ranta ba wanda ya isa ya hanata zuwa United Kingdom, ta kudirce a ranta zuwa two weeks zatabar kasar Nigeria..... Bayan Mum sun gama magana da Inna akan yaran duk za'a musu aure, Mum tashiga cikin d'aki ta sameh Fedo kwance kan gado da waya a hannun ta, shafa kan Fedo tayi tace "Mamata ya naji kina maganar sabon abu wai shi makaranta, kamata yayi kiyi aure idan yaso koh professor kizama amma da aure akanki dan aure shineh mutuncin 'ya mace" tashiwa Fedo tayi tace "Mum bazaki ganeh baneh, kinsan ni lecturer ce, bazan iya zama a position d'ina na Assistant Lecturer ba, I wanna be on my own, Masters kawai zanje nayi kuma shekara d'aya neh, pls Mum ku barni naje nayi nadawo" "Toh idan zakiyi saidai a garin nan" "Mum wlhy a garin nan sai nakai shekaru biyu ban gama ba, amma kinga kasar waje highest shekara d'aya zanyi na dawo pls Dan Allah Mum" "Shikenan toh, zan ma wan Dad naku magana" Tayi hugging mum nata tace ''Thank you so much Mum, please try your possible best naje nayi masters d'innan" "I will sweeryh yanxu kitashi ki shirye kuje ku gaisa da mutanen gidan" had'a rai tayi tareda turo bakin ta tace "Tab Mum gaskia a gaje nake, ni koh zani ma side nah Mami zan shiga gaskia bazan shiga wajen Umma da Hajja ba" "Kidai shiga kinji ai duk d'aya suke please" "Ohk Mum anything for you" tashiwa tayi akan gado tareda yafa gyalen ta tafesa turare suka fita itada Shamcy dan gaisar da mutanen gidan... B'angaren Mami suka fara shiga da fara'ar ta karb'e su, zama sukayi suna hira sosai da 'yar ta Ayeesha wacce take sa'an Shamcy, daga nan suka shiga side na Hajja, Hajja da kyar ta amsa sallaman su tacigaba da abunda takeyi, sai can Shamcy tace "Amm Hajja Zee bata gida neh" "Eh" kawai tace tareda shiga cikin d'akin ta.. *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad In dedication to Fido Sodangi {June,2017 } Page 9 Dogon tsoki Fedo taja tace "Aikin banza, ke Shamcy tashi mu tafi basai ta k'ara kallon kafar mu a Side nata ba, ni wollah tunda nashigo nakejin wari zuciya nah tashi ma yake ai da mun d'ebo mata turaren wutan da mukazo dashi daga Maid" rufe bakin ta Shamcy tayi tace "Shhhh dan Allah ki rufa mana asiri kiyi shuru please dan ni wollah tsoron matar nan nake" "Mtswww you are nothing but a coward, dallah tashi mu wuce" tashiwa sukayi suka shiga Side na Uwargida Umma. Sallama suke tun a bakin kofa amma shuru ba amsa ba, tusa kai sukayi suka shiga ciki to their very suprise sukaga Fatyma a parlour tana zaune kan kujera da pot na shisha agaban ta tana zuga, Shamcy was shocked, Fedo taja dogon tsoki dan tasan halinta har a snap take posting videos tana shan Shisha tace "Teema bakisan mahimmancin sallama ba koh" d'aga kai Teema tayi tareda jan tsoki tace "Sannu ke wacce kika sani" tacigada shan Shishan ta, wayan ta dayake gefen ta Shamcy ta d'auka tace "Adda Teema irin wayata" hararan ta Teema tayi tace ''Ni sa'ar kice,wannan ba iPhone 6 baneh iPhone 6+ ce" "Eh I know kin gan nawa same colour with yours" tareda ciro nata, karb'an wayan tayi Teema tana juyawa tace "Hmmm kicedai na Fedo" Shamcy tayi dariya tace "Ai Adda Fedo iPhone 7 yana fitowa koh wata d'aya baiyi ba tasiyo" tareda mika mata wayar Fedo dan duk yana hannun ta. Teema ji tayi zuciyar ta yayi bak'i k'irin, a yadda take jin kanta babbar yarinya ai da kunya, tun da takejin haushin Fedo because she's always ahead of her. Tsoki taja tace "And so what, nasan koh a yawon iskanci aka siyo mata" murmushi Fedo tayi tace "Ai Teema iskanci ma kala kala neh, kingani koh a cikin 'yan iskan ni daban ce" tashiwa tayi tareda jan tsoki tace "Shamcy tashi mubar nan it makes me puke" Teema ta zuga Shishaa ta busa mata iskan tace "It makes you Uwarki ba Puke ba hegiya" murmushi Fedo tayi had'e da girgiza kai takama hannun Shamcy suka bar side d'in. Da daddare Abba yadawo gida ya had'a meeting. Bayan sun bud'e da addu'a Alhaji Sanusee wanda suke kiransa da Abba yayi gyaran murya yace "Abunda yasa nace duk ku had'u anan shineh daga yau Fiddausi da Shamsiyya sun dawo gidan nan permanent, bazasu k'ara komawa Maiduguri and acikin samarin gidan idan Allah sa Fedo sun daidaita da d'aya daga cikin su sai a d'aura musu aure" "Cabd'i nidai bada tilon d'ana ba" cewar Hajia Khadija, Maryama tayi caraf tace "Nidai 'yayana maza biyu kuma duk sunada aure kuma bazasu k'ara ta biyu ba ehn" Abba ya daka musu tsawa yace "Kuyi shuru, shin mehsa bakuda kunya neh, toh zan tara samarin gidan acikin su idan akwai wanda yakeso shikenan khalas" Mum mahaifiyar Fiddausi ce tayi magana tace "Alhaji Dan Allah inada magana" "Inajin ki Zainab" "Ammm daman Fiddausi ce takeson yin Masters nata kan tayi aure shineh tace dan Allah na maka magana" Hajia Maryama tace "Cab, duk girman tan nan ai..." Bata k'arasa ba Abba ya tsaida ita da hannu yace "A inaa takeson yin Masters d'in" Mum tace "A UK" "That's very good, zan barta amma da sharad'i d'aya" ya juya yana kallon Fedo "Sharad'in shineh idan Allah sa kin gama kina zuwa gida koh sati biyu bazaki k'araba zan aurar dake, kin amince" d'aga kai Fedo tayi alamun Eh ta amince, yace "Yawwa Madallah" yacigaba "Daman Aliyu Haydar an turashi wani training a UK so inaga zaku tafi tare" duumm zuciyar Fedo ya buga, a rayuwar idan akwai wanda takejin shakkan sa toh bai wuce Yaya Aliyu ba, General Aliyu Sanusee Sodangi. Hajia Maryama ce ta buga wani uban salati tace "Wani Aliyu, Aliyun nawa, Haba Alhaji kana adalci mana, bayan kasan Aliyu da matarsa zaiyi tafiyar nan" "Nasani ai sabida haka kimun shuru, kuma ai zama ita kad'ai a wata uwa duniya ba dad'i" hmmm kawai Hajia Maryama tace had'e da kananan maganganu.... ASALIN SU Mallam Umaru Sodangi 'dan asalin Katsina neh da matar sa d'aya Hawwa'u, sana'arsa noma yanada yara maza gudu biyu. Sanusee shineh na fari sai Muhammad. Tun daga lokacin haihuwa ya tsayama Inna. Mallam Umaru yayi iya kokarin sa dan ganin yaransa biyu sunyi karatu. A lokacin da Sanusee yagama degree d'insa a political science Allah ya d'auka ran mahaifin su. Sunsha kuka sosai dan mutuwar mahaifi ba karamin abu baneh. Sanusi da kud'in bautan kasar sa yake biyawa Muhammadu kud'in secondary har Allah yasa bayan bautar kasan sa yasamu aiki a state government amma duk da haka yacigaba da karatu. A lokacin ya aure matarsa Maryama wacce take shuwa usul 'yar Maiduguri kyakkyawar mace fara Sol. Sun haifa d'ansu na fari yama k'anin sa takwara ya rad'a masa suna Muhammad. Daganan ya k'ara aure mata biyu wato Khadija da Jamila. Hajia Maryama tanada yara hud'u biyu maza biyu mata, Muhammad, Aliyu haydar, Husnah da Fatima. Sai Hajja Khadija wacce aka auro ta bayan haihuwar Muhammad yanxu tanada yara uku, Ahmad shineh d'anta nafarko, Amani da Zainab. Sai kuma matarsa na Uku Hajia Jamila ita tanada yara biyu, Ahmad da Ayeesha... Alhaji Sanusee shi karatu yaciga dashi har yakai matsayin professor, shiyasa da Mum tamasa maganan karatun Fedo ya amince da wuri.... Marigayi Alhaji Muhammad d'an kasuwa neh, yana business amma Allah kad'ai yasan business da yakeyi, idan wansa Sanusi ya tambaye sa sai yace duk kud'in sa na gidan mai da yake dashi a cikin Maiduguri neh amma kud'in sa ya zarce kud'in gidan mai kwalli d'aya. Matar sa wato Mum asalin 'yar Adamawa ce Fulani gaba da baya, Allah ya zuba mata kyau 'yayan ta biyu sun d'auke kyaunta dan shima Alhaji Muhammad kyakkyawa neh sosai. Saidai Fedo ta d'au complexion na mahaifin ta Ita chocolate colour Shamcy kuma farace sosai amma duk da haka mutaneh sunce Fedo tafi kyau. Wannan kenan Back to Asalin Lbr Zaune take a d'akin ta laptop agaban tayi applying University a UK har sun tura mata message a email nata akan tasamu admission... Wani Ihu tayi tace "yeeeehhhhhhhhhhyyy" d'aga kai da zatayi tayi ido hud'u da wani Saurayi wanda ak'alla bazai haura talatin ba. Dogo neh wankan tarwad'a, ga Sajen sa wanda ya kwanta a fuskan sa yayi luguf, sai dogon hancin sa da bakinsa wanda ya dace da fuskar sa, kallo d'aya zaka masa kasan namiji neh ajin farko, lumshe idonta tayi tace "uhmmmm My First love" a zuciyar ta, dogon tsoki yaja yace "Ke ina Inna tashiga" da sauri tace "Tashiga side na Mami" fita yayi ba tareda yace mata k'ala ba, lumshe idonta tayi tace "Ohhhh He is my HAYAAT, I thought shineh the most handsome guy on planet not until I met Issam, and Issammm my Dushmann (enemy da India)" Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } ```Page 10``` Laptop nata ta rufe tareda dialing number a wayar ta, da taji yafara ringing ta saka a loudspeaker tareda ajiye wayan akan laptop d'in, muryan macece tace "Hello Gimbiya Fedo ya akayi" "Hmm kedai Eesha akwai good news, yanxu na bud'e email d'ina sun turo mini na samu admission" Ihu Eesha tayi tareda cewa " I am so happy for you gurl" "Thank you!!!! Ya maganar mu" "Yeah nasa an binciko mini shi ashe friend nah Faruq neh yana Masters nasa a Cambridge" "Wow Good bari yanxu idan mun gama processing Visa zan miki magana koh, take care bye" tareda katse wayan. Kwantawa tayi zuciyar ta na k'ona, ba wanda takeso tayi Ido hud'u dashi kamar Issam, a yadda yayi sanadiyyar mutuwar mahaifin ta sai ta wulak'anta sa a doron kasa, sai duniyar ya daina masa dad'i kan ta shafeshi a doron kasa.. Wani dogon tsoki taji anja atake ta d'aga kanta dan ganin wanda yaja tsokin, to her very own surprise taga Meena matar Yaya Aliyu, yarinyan da bata wuce shekaru ashirin da biyu ba. "Are you alright? Are you freaking OK?" cewar Fido, kara jan tsokin tayi tareda cewa "Ba lafia ba, kuma wollah kifita a hanya ta da mijinah idan ba haka ba zan baki mamaki, kawai dan kinji labarin zamuje UK harda kirkiro karya wai zaki karatu, wlhy kibar ganin kin girme ni toh" dariya Fedo tayi ta tashi tana mata kallon uku saura kwabo, tace "Wow yarinya kin girma wlhy Allah ni mai taka banza ce and you know I hate when people disrespect me especially young girls like you" tareda jan tsoki tad'au laptop da phone nata tafita tabar mata d'akin gaba d'aya, Meena ta cika tayi fam amma ba yadda ta iya, kuma bata isa tayiwa General Aliyu magana ba....... Fido fitowa parlour tayi ta zauna ta kunna Laptop nata tana kallon American Film 'Suicide Squad' da earpiece mak'ale akan kunnen ta, Inna ce tazo ta zauna kusa da ita tace "Fiddausi ga Tv a falo mei kuma na kunna wannan abun kina kallo" "Inna ni wannan nakeson kalla dan Allah kibarni naji abunda suke fad'a" "Toh ai baki isaba kisa mana dukkan mu mugani idan ba son kaiba" Fedo cire earpiece tayi ta k'ura volume tace "Inna ai kinaji koh" d'aga kai Inna tayi tareda maida hankalin ta kan Laptop d'in kamar wanda takejin turancin. Meena ce tafito a d'aki tana wani harare harare ta kumbura fuska, Inna ta d'aga kai tana kallon ta tace "Ikon Allah, ke meh haka kin wani kumbura fuska kamar fanken da yeast yamasa yawa, dan Allah sake fuskan koh baki had'a rai ba bayamun kyaun gani balle kin had'o rai Meena tak'ara cika tayi fam, fita tay a parlour Inna ta kyalkye da dariya harda bawa Fedo hannu su tafa, tace " 'yar jakar uwa wai ita a dole tayi fushi, wani fuska kamar rub'ebb'en kosai fitsararriyan yarinya, ni banga abunda Aliyu yagani a jikinta ba daya nace dole sai ita gata kamar fatalwa" Fedo ta kara fashewa da dariya tace "Wollah Inna ai idan na had'u da irin ta da daddare sai nayi fitsari a wando Kut! ai abar tsoro ce" "Bar 'yar duniya kamar su d'aya da Aliyu gasu duk da bak'in hali kamar na uwarsu" Fedo takara kyalkyalewa da dariya tace "Kinsan Allah Inna, wlh koh muciya aka d'aura wa zani, aka masa kwalliya toh wollah zai fita...." Bata k'arasa ba gani sukayi mutum tsaye akansu ya had'o rai yace "Inna dawa kuke wai" ya dakawa Fedo tsawa yace "Da Ubanwa kike ni sa'ar kice" nan da nan jikin ta yafara b'ari da gudu tashiga d'aki ta kulle. Inna ta harare sa tace "Ja'irin yaro ka isa ka tab'ata a gabana" Murmushi yayi yace "Ban isa bakam a gaban ki amma idan ta bini kasar waje makaranta sai na lahira yafita jin dad'i" Inna tayi salati tace "Wani makaranta kuma" "Auu daman basu fad'a miki ba, wai k'arin karatu zatayi a kasar waje" Inna salati tayi tareda cewa "Sanusi baya kauna ta, maza maza kira mani shi a waya naji ta bakinsa" Aliyu ciro wayan sa yayi yana dariyar mugunta ya mata dialing number Abba, yana ringing yasaka mata a kunne. Da karfi Inna tace "Sanusi bakada mutunci, bayan mun gama magana dakai akan Fiddausi aure zatayi naji mummunan labari ka turata makaranta a wata uwa duniya Wata magana Abba ya fad'a mata naga ta washe hak'ora tace "Ohhh haba, ai toh shikenan. Da Aliyun zasu tafi koh? Allah kaisu lafia" ta katse wayan tana washe hak'ora Aliyu kawai tsayawa yayi yana kallon ta dan he was surprise koh meh Abba ya fad'a mata sai Allah... Shiga b'angaren Umma yayi, bayan sun gaisa takece masa "Wlhy Son karka yadda ka tafi da wannan yarinyan mei kama da mayu" "Umma toh ya zanyi ni kaina ba son tafiya nakeda itaba, kiyi hakuri kawai ai mun samu 'yar aiki koh ba komai" "Nidai tafiyar kuce gaba d'aya banso Aliyu" "Karki damu Umma ba komai, Ina Teema tashiga" "Tana cikin d'aki itada Amani, ni wlhy sam bana kaunar Amani tana shigowa wajenah" "Ohk lemme check on them" tareda tashiwa ya nufe d'akin ta, tun a bakin kofa yakejin Kamshin Shishaa (Shisha kamshi neh dashi ba wari ba) bud'e kofan kawai yayi ba tareda Sallama ba. Zaune suke a kasan carpet suna zugan Shishaa abunsa kawai sukaga General Aliyu a kansu, kame kame suka fara Amani tanaso ta gudu Aliyu ya capko ta, rufe kofan d'akin yayi ya cire belt na aljihun sa yafara d'irkan su. Umma buga kofan take tana cewa Aliyu mei suka maka dan Allah kabarsu, koh da zaka dake Amani ka daka amma please karka tab'a Teema. Shikam inaaa koh kulata baiyi ba ya cigaba da d'irkan su, sanda ya musu lik'is yagaji kan ya kyalesu. Bud'e kofan yayi take Umma tashigo tace "Meyafaru" ransa b'ace yace "Shisha suke sha Umma" Umma tayi salati tace "Wlhy Amani ce Teema sam bazata sha ba" girgiza kansa Aliyu yayi dan yasan halin uwarsa sosai akwai ta da d'aurawa yaranta baya......... Bayan Sati Biyu Duk sun taru a airport Shamcy tayi hugging Fedo tace "I'm gonna Miss you alot Sis, in fact more than a lot " Fedo tayi murmushi tayi hugging nata tight tace "Hug me like you mean it Baby last, emma gonna miss u more" General Aliyu Haydar da Uniform nasa na sojoji tsaye yayi yana kallon su, Meena kuma duk ranta a b'ace bataso hakan yafaru ba, taso ace yak'i tafiya da ita.............. Bayan minti talatin jirgin su ya d'aga Toh fa Sai mun had'u a UK readers 07034419520 *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } ```Page 11``` *Anglia Ruskin university, Cambridge* Wata mota Ferrari GTO bak'a ce tayi parking a gabar school d'in, kusan minti biyar shuru ba'a bud'e motar ba sai can General Aliyu Sanusi Sodangi ya bud'e motar yafita ya zagaye b'angare d'aya side na motar ya bud'e kofa. Kafarta d'aya d'auke da high heel bak'a tafara saukewa kan kusan seconds goma ta sauke d'ayar kafan. Straight skirt bak'i neh ajikin ta sai dogon top iya gwiwan ta shima bak'i tayi rolling gashinta da veil bak'i. Tsoki yaja yace "Dole nah gyara lock nah kofan nan bazaiyu ina bud'e miki kofa kullum ba sai kace driver ki kuma Wlhy nan gaba idan nakara kallon ki da irin wannan heel d'in saina tattaka ki" itadai batace masa komai ba ya shige motarsa yayi gaba. Ciro wayan ta tayi a cikin jakar ta tareda dialing number k'awar ta Eesha, ringing d'aya Eesha ta d'auka tace "Kibani just 10mins yanxu zaki ganni" Fedo jan tsoki tayi kawai ta katse wayan ta. Kalle kalle take a makarantan har idon ta yakai kan wani Shop an rubata '''COFFEEHOUSE''' a hankali ta taka har cikin coffeehouse d'in tayi ordering Coffee, bayan an kawo mata Seat data zauna sam baiyi mata ba wani yaro ya kura mata ido gashi wajen kusa da window tanajin sanyi. D'auka coffee cup nata tayi tareda tashiwa a seat d'in dan ta koma seat na baya. Tafiya take a hankali tayi missing step gashi dogon takalmin dake kafan ta zube luuu zata fad'i taji an kamota Bud'e idon ta tayi a hankali dan ganin wanda ya kamota, ido hud'u tayi da ISSAM. Fuskan sa a murtuke yake kallon ta "Astagfirullah" yayi mumbling, take ta gyara tsayuwan ta fad'a a hankali "As if baya committing sins more than tab'a mace" taja wani dogon tsoki. Tsayawa yayi yana kallon ta dan kamar yaganeh ta but wata zuciyar nace masa ba ita bace ai wancan kabarta a Nigeria. Juyawa tayi zatayi tafiyar ta yaje gyalen ta yace "Are you insane, next time you should watch where you're going plus you can't even open your filthy mouth and say thank you kina jan tsoki, I really hate that" ranta idan yayi duba ya b'aci wai 'filthy mouth' ranta b'ace tace "How dare you!!!! How dare you open your big mouth and insult me kuma kana wani magana bance thank you ba. Why should I even say thank you to a person who bumped into me last month and he can't even say sorry" Kallon ta ya tsaya yakeyi dan yanxu yakeda tabbacin itan ce, sai can yace "Just be glad I'm not making you pay for my Suit and ban buge bakin kiba" kallon jikin sa take taga ashe coffeen duk ya zube a maroon Suit nasa , kuma Coffee nada d'an karen zafi. Juyawa yayi yayi tafiyarsa ya barta tsaye..... Cizon yatsan ta tayi tace ISSSAM kenan muna nan da kai Wayarta neh yafara ringing ta d'auka da wuri tace "Wlhy Allah Eesha baki kyauta mun ba ina wani Coffeehouse opposite Whey Libry" nan da minti biyar sai ga Eesha tazo, yarinya ce sa'ar Fido chocolate colour siririyace sosai kuma tanada tsayi, ba laifi tanada kyau iya gwargodo. Hugging na Fedo tayi tace "Gurl been a while, tun time da muke service fa" had'a rai Fedo tayi tace "And so? Shineh zaki shanya ni for almost an hour yanxu" "Very sorry my love" "Don't call me that OK!" "Kiyi hakuri toah Fiddausi" " please next time karki k'ara, you know I am new here yaarrr" "Kefa banza ce Allah sa karki hakura" Haka sukaita yawo da Eesha tagama nuna mata makarantan tareda kaita department nasu, a yau tagama duk abunda yakamata ta gama ita bata dawo gida ba sai karfe taran dare. Tana shiga taci karo da Aliyu a parlour yana danne danne a laptop nasa. Gaishe sa tayi ba tareda ya amsa ba yace "Sai yanxu?" Eh kawai tace tareda kokarin shiga d'akin ta, daka mata tsawa yayi yace "Ain't done with you gurl da zaki wuce, tun d'azu nake kiranki mesa baki d'auka ba?" "Banji ba wollah wayar na Silent" "And you can't call back" "Sorry ba kud'i a wayar shiyasa" "And kinfi karfi ki kirani da wayan Eesha koh? Lemme tell you one thing nan gaba idan kika kai karfe shida a waje sai jikinki ya fad'a miki. Very stupid girl kawai" tura bakin ta tayi ace da girman ta shekaru ashirin da hud'u tana neman shiga na biyar nan da wata shida amma ace za zaneta, lallai ashe za'aga drama, kai baima isaba. Shiga tayi cikin d'akinta ta watsa ruwa dan tana fashin sallah, shafa cream tayi ajikin ta tareda saka dogon kaya da cardigan akai dan garin ana sanyi sosai. Kunna heater na d'akin tayi dan yayi warming d'akin cox yayi sanyi sosai amma warmer bayayi. Dogon tsoki taja tareda d'aukan laptop nata da wayanta tazo parlour ta zauna, a lokacin Meena tana manne ajikin Aliyu ita a dole tana masa shagwab'a. Tayi niyan ta koma ciki amma wata zuciyar tace zauna kiga ikon Allah. Zama tayi daram a gabansu tana facing nasu, mugun kallo Aliyu ya mata amma hakan bai hanata zama daram ba. Meena kuma ganin haka yasa ta k'ara zagewa tana kissing nashi shima yana biye mata, ganin abun nata yana son wuce gona da iri yace "Ummm Meeenah bari nagama aikin nan tukunna" Inaa ita kuma sai k'ara narke masa take, tsawa ya daka mata yace "Please just leave me alone". Ranta idan yayi dubu ya gama b'aci, Fedo sai dariya take a hankali wanda ya k'ara kular da Meena. Tashiwa tayi tashiga ciki a fusace, ran Fedo kuma yayi fari kal sai murmushi take tana danne danne da laptop nata. Aliyu neh ya daka mata tsawa yace " Dan Ubanki dariyan meh kike kuma what's the reason zakizo kisani a gaba kina kallo nah" "Warmer d'aki nah baya aiki kuma wollah akwai sanyi shiyasa" tsoki kawai yayi yacigaba da aikin gaban sa. Can yunwa yaci karfin ta tashiga kicin koh zata samu abun sakawa a baki amma shal ba komai tace "Kut!!! Yarinyan nan yar iskace bata ajiye mini abinci ba mtswww" kunna gas tayi ta dafa indomie wanda yaji atargu ta zuba a plate ta kawo parlour. Cigaba da aiki take a laptop nata duk hankalin ta yana kan binciken da take akan Issam tana d'an tab'a Indomie ta. Aliyu kamshin Indomie yariga yagama cika masa hanci yanata had'iye saliva yaga ina idan baici bafa akwai matsala. D'aga idonsa yayi yana kallon ta gaba d'aya hankalin ta na kan laptop d'in ga left hand nata wanda ta tusa shi a cikin dogo bak'in gashin ta. Zuwa yayi da hankali ya d'auka plate d'in indomie ba tareda da tasani ba danma Tv yana aiki ya kura volume balle taji karan tafiyan sa...... *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } ```Page 12``` D'aukan plate na Indomie yayi ahankali yawuce kitchen ya juye a plate ya b'oye a wardrobe yak'ara zuwa parlour ya ajiye mata plate d'in. Duk abunda yayi bai wuce secs talatin ba. Zama yayi a kujera ya had'a rai yana aikin sa, Fido kuma juyawan da zatayi ta d'eba Indomie taga wayam ba komai a plate d'in. Juye juye tafara tagafa su biyu neh a parlour kuma tanada tabbacin ba ita ta cinye ba dan Indomie da zafi kuma ga zafin pepper. Ihu tayi ta tashi a wajen tazo dab kusa da Aliyu tace "Wlhy Yaya akwai aljani a gidan nan, na ajiye indomie kan na juya sun cinye" wani tsawa ya daka mata yace "Kee kishiga hankalin ki bawani aljanu da suke gidan nan, tun d'azu naga kina cin Indomie kuma yanxu kice aljanu neh suka cinye, kinadai daci kamar gara" Itadai duk jikin ta yayi sanyi dan tasan ba ita ta cinye abincin ba tace "I swear Yaya Aliyu wlhy Allah ban cinye ba" "Just sharrrapp I don't wanna hear anything idan bake kika cinye ba toh ubanwa ya cinye Stupid gurl" "Ohk fine, nagode" Jiki a sanyaye ta kwashe laptop nata da wayarta tashiga d'akin ta. Duk da haka hankalin ta bai kwanta ba tsoro duk ya mamaye ta. Tana shiga d'akin ta Aliyu ya tashi da sauri ya nufe kitchen ya d'auko Indomie ya ajiye a dinning yafara ci. Da k'yar ya iya yaci dan yaji ahaka yana had'awa da Juice meh sanyi yana wayyoo Allah nah yaji yarinyan nan tana son kashe ni washhhh.... .....Washegari....... Tun kusan karfe takwas Aliyu ya shirya yana jiran Fido ta shirya ya sauke ta a school, duba agogon hannun sa yayi yaga past nine. K'ofan ta yafara bubbuga wa yana cewa "Idan kika k'ara minti goma wlhy tafiya zanyi na barki kusan awa d'aya kenan ina aikin jiranki" A lokacin Fido tafito a wanka da sauri ta shafa cream ta d'auko rigan ta Material bak'i da touches blue, ta d'auka veil blue da takalmin ta bak'i da d'an colour blue high heel as always. D'aukan kayan makeup nata tayi ta zubasu a babban designer jakarta. Da gudu gudu tafita a cikin gidan tasamei sa a mota ta zauna tana sauke numfashi. "Gerrrouttt". Yece mata a tsawace, kallon sa take with so much surprise on her face tace " what!!! Why???" "Are you asking me why? Bakisan kiyi sallama ba kan kishigo dallah fita malama" ajiyan zuciya tayi tana kokarin ajiye jakarta a motar yace "Kifita da duk wani abunda kika shigo dashi" d'aukan jakarta tayi sai tura baki take dan ya matukar bata haushi tafita a motar. Da sallama ta bud'e motar tashiga ta rufe kofan nan take yaja motarsa yana wani shan k'amshi. Ciro kayan Makeup tayi a jakarta, watsa mata kallo yayi yace "What the heck are you trying to do" "Yaya wlhy fuskata idan ba kwalliya akwai matsala" "Tambayar ki nake bance kimun dogon bayani ba gurl" "Make-up" ta furta a hankali, yan buriki yayi da karfi yace "Not in my car, kifita mun a mota ki zauna a can kiyi" tareda nuna mata wani slaps "Idan kin gama painting fuskan ki sai ki d'au taxi yakaiki sch" fuskan tausayi ta masa tace "Please General Aliyu" "Just shutup and do as I command" "Ohk fine, nafasa kwalliyar" jan motarsa yayi tareda cewa "Good" Bayan yayi dropping nata a sch ta wuce wajen lecture, ita bata gamaba har kusan karfe biyu dan tayi practical. Cafeteria ta wuce direct dan already sunyi waya da Eesha tana wajen. Tana zuwa wajen ta kira Eesha a waya Eesha tazo tasamei ta suka shiga cikin wajen. Kujeran zaman mutum hud'u neh. Tun a nesa Fido hango Faruq wanda yake saurayin Eesha sai d'ayan kuma wanda ya juya mata baya batasan koh wanene ba. Fido ta tab'a Eesha tace "Ummm Hajia keda your Boo neh" dariya Eesha tayi tace "Don't call him that again" "Idan na k'ara fa, me zakimun" "Ahswear I'll cut off your head, mijin da zan aura neh ba saurayi nah ba. He is my fiancée" "Ohk naji" tareda jan kumatun ta. Suna isowa wajen Fido taja kujera ta zauna tace "Washhh m so very tired wlhy, Eesha please kimini ordering noodles be fast please" Eesha tace "Ohk" tareda yima masu abincin magana Fido ta juya ta gaishe da Faruq tace "Su Faruq manya ba'a kallon ka a Nigeria sai a kasar waje, the last time da muka had'u a Dubai koh" murmushi wanda aka kira da Faruq yayi yace "Ba haka baneh fa kawai haka Allah ya kaddara bamu tab'a had'uwa a Nigeria ba, ga abokinah ku gaisa" Juyawan da zatayi suka had'a ido da Issam, HAR A ZUCIYA tana yaba da irin kyaun da Allah yamasa. Issam dogo neh sosai meh broad chest, irin mazan da sukasha gym yana da ten packs. Fari neh sol irin farin nan neh meh kyau, yanada manya manyan Ido da dogayan eye lashes kamar mace, gashin giransa har wani had'ewa yake, yanada dogon hanci tsit da karamin bakinsa d'an pinkish, gashin kansa kuma bak'i neh wuluk dogo kamar na Roman Reings nidai nace Mashaa Allah.. Ajiye abincin da yakeci yayi yana kallon ta, yace "Are u a spy, or you are among those gurls who beg for attention" Kallon sa Fido take tama rasa meh zatace masa baki bud'e take kallon sa, yacigaba "Shin mesa kike bibiyata, tun a Nigeria and you followed me har nan why?" Fido was speechless wai tana bibiyarsa koh dayake baiyi karya ba, tayi karfin halin cewa "I beg your pardon! I really don't get you, ban ganeh what you are trying to say ba, ban ganeh meh kake nufi ba" karamin tsoki yaja yace "WTF! Are you deaf, hausan neh bakiji koh turancin" "Both" ta basa amsa a takaice, Eesha da Faruq shuru sukayi suna kallon ikon Allah Tashiwa yayi akan kujeran ya kwashe jakan laptop nasa da wayoyin sa, yace "Muddin na cigaba da cin abinci ina kallon yarinyan nan wlhy amai zanyi, bye Faruq" d'aukan Pepsi na gaban tebur tayi ta watsa masa a kayan sa, da mamaki ya juya yake kallon ta, tace masa tana meh nuna masa yatsa "Next time you should watch your big mouth kan kayi magana" kama hannun ta yayi ya murd'a. Turesa tayi tace "How dare you!!! don't you ever and never again touch me with your filthy phalanxes" murmushi yayi yayi tafiyar sa. Faruq yana kwala masa kira amma shuru koh ya juya. Hawaye tafara zubda wa tareda d'aukan jakarta. Eesha tana bata hakuri ta d'aga mata hannu tace "Please just leave me alone" tafiyar ta itama tayi tana meh mugun tsanar Issam, tunda take a rayuwar ta bawanda ya tab'a wulakanta ta kamar Issam. Shi laifin sa ma sunfi duba. Tayiwa kanta alkawari sai tayi maganin Issam, sai ta masa abunda bazai tab'a mantawa dashi a rayuwar sa ba murmushi tayi tace ''zaka shiga hannu nah ISSAM" Taxi ta d'auka yakai ta gida, tana zuwa bakin kofan gidan daidai lokacin Aliyu shima ya dawo gida. Da gudu Meena tafito ta rungume sa tace "Welcome the moon of my life" tareda kissing na bakin sa, Murmushi ya mata yace "Thank you dear" wannan abun duk a gaban Fido abun ma dariya ya bata tayi shigewar ta ciki. Bayan tayi wanka ta canza kayan dake jikin ta tafito dan ta wuce kitchen. Tana fita a d'akin ta zata kicin Meena tace "Yawwa the moon of my life kasan banjin dad'i babyn ka yana damuna sosai so ban samu na girka maka abinci ba tunda Allah yasa Fido tazo saita dafa mana kaji" Fido kallon ikon Allah take tana jiran abunda Aliyu zaice, sanda yamata peck a kumatu yace *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {June,2017 } ```Page 13``` Pecking na Meena yak'arayi for the second time ya kalla Fido yace "Ummm kinsan meh Dear" Meena ta girgiza kanta tace "Tell me the Moon of my life" lips nata yayi kissing kan yace "Last time da Inna tabani abincin ta naci rashin lafia nayi, da naje asibiti Docter yake cewa typhoid neh yake damuna kingani yanxu idan naci abincin ta bansan kuma wata cutar zata kamani ba bana ma sai Cholera takama ni" "Ohhh the Moon of My life ai bansan abun haka yake ba" itadai Fido bataji haushin maganar sa ba dan koh ba komai daman bason girka musu abinci take ba. Wucewar ta zatayi zuwa kitchen taji Meena tacewa "Ai the Moon of My life tun ba yau ba nasan yarinyan nan muguwar k'azama ce" Aliyu dai shuru yayi baice komai ba, ran Fido idan yayi dubu ya b'aci, idan bata tanka mataba nan gaba ma zata k'ara mata fiye da haka wata zuciyar kuma na ce mata tabarta kawai Silent Is The Best Answer Giving To A Fool. Dogon tsoki Fido taja tace "Psychotic Bitch kawai" tayi wucewar ta kicin. Meena tace "Swt kaji abunda tace mun kuwa kayi shuru?" "Toh meh kike so nace afterall you started it" "We started it or I started it koh kuma she started it?" "I don't know kibarni please inada abunyi idan nagama zan samei ki a d'aki" "Are you serious" tana kallon sa da mamaki irin an zage ta bai rama mata ba. Yace a tsawace "Ki barni please dan Allah" Tashiwa tayi tana k'ananan maganganu ta shige d'aki. Fido Flour ta d'eba ta had'a tayi d'anwaken ta. Kad'an tayi dai dan cikinta ta zuba a kwanu ta masa had'i, gidan duk ya d'auka da kamshin man g'yadan data soya wanda yaji albasa sai ka rantse wani delicious ta girka. Zuwa parlour tayi ta ajiye kwanun ta wuce d'akin ta ta d'auko wayarta da laptop nata ta zauna tafara operating na laptop d'in. Kamshin duk yabi yacika hancin Aliyu ya rasa yazaiyi kuma harga Allah yashiga ransa sosai ga wani uban yunwan da yakeji Yau kuma d'anwaken na gaban ta ba yadda zaiyi ya d'auka dole sai ta kamasa. Dogon tsoki yaja yace "Niwai meh dalilin da kikeson sakani a gaba kina kallo" "Allah sarki Yaya I told you yesterday akan warmer na bayayi kuma d'akin d'an karen sanyi neh dashi" Tsoki yaja yacigaba da aikinsa yana had'eye miyau. Tashiwa yayi zuwa balcony inda Switch na wutan su yake ya kashe. Ganin wuta ya d'auke take ta tashi duk da laptop nata ya d'an haskaka wajen. Aliyu kwala mata kira yayi da karfi yace "Kee Fiddausi zoki haska mini na duba Switch d'in nan koh da matsala" tashiwa tayi ta kunna touch light na wayar ta taje tana haska masa, sai wani kame kame yake yace "Jirani na duba koh fault d'in daga cikin gida neh" "Ohk" kawai tace dashi tana mamakin meh yahad'a Soja da Engineering. Aliyu da sauri yashiga kitchen ya d'auka plate yazo parlour ya juya d'anwaken ya ajiye mata empty kwanu ya k'ara komawa kitchen ya b'oye a wardrobe Zuwa yayi ya sameta ya d'anyi tab'e tab'e ya kunna Switch d'in sai kawai wuta yaxo. Fido tayi ajiyan zuciya tace "Alhamdulillah" tayi shigewar ta cikin gida. Zama tayi gaban laptop nata duba kwanun da zatayi taga empty ba komai. Take ta tashi tareda wani irin Ihu "Wayyoo Allah nah" da sauri Aliyu yashigo parlour yace "Lafia kuwa ke" , zuwa wajen sa tayi da guda tana hawaye tace "Wlhy Yaya Aliyu akwai aljanu a gidan nan" Wani dogon tsoki yaja yace "Dallah Mallama ba aljanu a gidan nan saidai idan kece Aljanan" "Wlhy Allah Yaya Aliyu dagaske nake, kaga kwanun nan nafara cin d'anwake na kenan wutar nan ta d'auke kace nazo na haska maka yanxu kuma babu komai a ciki" "Mtswww kice dai kin cinye mana 'yar ranin sense" "Wlh Yaya ban...." Bata k'arasa ba yace "Just shutup please kinsan na tsana yawan magana kuma karki k'ara cewa akwai aljanu a gidan nan" Kwashe kayan ta tayi na parlour tayi shigewar ta d'aki ga wani uban yunwan da takeji, Corn Flakes ta had'a da madara tasha ta kwanta bacciiii cike da tsoro. Aliyu kuma bayan yaji shuru ya wuce kitchen da sauri ya d'auko d'anwaken yafara ci yana "washhhhh wayyo Allah yaji" nidai nace kai kasa kanka General Aliyu Washegari Saturday ita bata tashi a bacci ba sai kusan karfe goma, tana tashiwa ta shiga toilet tayi wanka. Bayan tafito ta shafa cream nata meh kamshin gaske tareda d'auka wando jeans bak'a tasaka, ta cire wata dogon riga Milk colour wanda tsagun sa har cinye tasaka. Zama tayi gaban dressing mirror tana tsara kwalliya, sanda tacika fuskan ta da makeup kan ta tashi ta nema d'ankwali bak'i ta d'aura tareda saka takalmin ta milk heel. Fesa turaren kan dressing mirror ta tayi wanda yakai kusan kala goma. Aliyu zaune a parlor yana kallon Tv yaji kamshi ya buge hancin sa, a hankali ya d'aga idonsa yaga Fido tana gyara agogon hannun ta. "Kee ina zakije yau ba Saturday baneh" "Wlhy wajen Eesha kuma inada lecture kamar karfe uku". Kallon ta yayi sama da kasa shi kansa yasan ba karamin kyau tayi ba, ji yayi zuciyan sa yana bugawa kamar zai fita, a hankali yace "Kije ki cire kayan nan kuma karki fesa perfumes haka" "Haba Yaya wlh nayi......" Bata k'arasa ba ya daka mata tsawa yace "zaki canza koh sai na tattakaki" Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } ```Page 14``` Turo bakin ta tayi tace "Zan canza but i don't see any thing wrong with what I'm wearing" Mugun kallo ya watsa ma take ta juya ta koma d'akin ta. Zama tayi akan gado tana meh mugun jin haushin Aliyu, can koma sai ta tashi taje gaban mirror tana kallo kanta. Tsoki taja tace " Wlhy Allah bazan canza kayan nan ba" Jakarta ta d'auko ta lek'a parlour taga wayam ya tashi a wajen, da hankali tafita a gidan ba tareda wani ya sani ba. Tana fita taxi ta tsaida bai gama tsayawaba ta bud'e tashiga ciki tana sauke numfashi tana dariya kamar wata zararriya. Kofan gidan su Eesha aka sauke ta tashiga ciki. Da sallama tashiga parlour ta tarar da Antyn Halima wacce take yayar Eesha, Faruq kuma Cousin na Eesha neh so dukkan su a gida d'aya suke da zama. Murmushi Anty Halima tayi tace "Su Fido manya yakike" zama tayi tareda cewa "Washhh!!! Wlh agaje nake. Lafia kalau Anty Halima" bayan sun gama gaisawa Fido tace "Inaa yar air nan tashiga neh" "Suna can garden" take ta tashi tace "Anty Halima ga jakata idan na tashi tafiya zan shigo na d'auka" "Ohk toh" fita tayi a parlour ta wuce bayan gidan wajen garden. Da sallama ta iso wajen su duk suka amsa mata da fara'ar su. Tace "Kudai kullum kuna tare dan Allah kuyi aure kowa ya huta" dariya Faruq yayi yace "Karki damu Matar abokinah zamuyi Soon amma maybe ku rigamu" Fido kallon sa take dan bata ganeh meh yake nufi ba tace "I dnt just get you, what do you mean by matar abokin ka?" Eesha ta kashe mata Ido tace "Issam mana. You know people flocked around him, it wasn't just his perfect looks; it was his charisma and genuineness that made you wanted to be around him" Fido kallon ta take da mamaki, she can't believe abunda kawar ta Eesha take fad'a wai tana son Issam. Eesha taciga "And you know what my friend? Inaji ajikinah Issam na kaunar ki fiyeda yadda kike tunani" Kan ta bud'e baki tayi magana sai Faruq yace "Gashi nan ma yana zuwa" d'aga kai Fido tayi tana kallon sa, tafiya yake kamar zaki, idan ba fad'a makaba sai ka rantse ba d'an Nigeria baneh. A farko data gansa taji tana masifan sonsa, amma yanxu kam tsantsan tsana take masa,she can't even explain how much she hate him. Take ta tashi a kujerar ta tace "Inada lecture sai mun had'u next time" tareda barin wajen. Eesha tabi bayanta tace "Yake haba karki bani kunya mana" had'a rai Fido tayi tace "Dan Allah kibarni bana son magana" sunzo dai dai da Issam Eesha ta gaishe shi, da kyar ya iya bud'e baki ya amsa. Fido tace "baga irinta ba, kina gaishe shi yana wani jin kanshi Wlhy kin bani haushi" Eesha tace "Haka nature shi yake miskili neh na gaske" tsoki taja tace "Nature buru uba, naga Yaya Aliyu uban miskilanci". Dariya Eesha tayi tace "Toh Issam ya ninka sa a miskilanci" "I don't have time for this" tayi shigewar ta wajen Anty Halima ta d'au jakarta tayi mata sallama ta tafi Har a ranshi Issam baiji dad'in barin wajen da tayiba data gansa, baya kaunar yarinyan koh kad'an amma each time da sukayi fad'a yana samun nishad'i koh ba komai ya b'ata mata rai...... Fido bata dawo gida ba sai da yamma likis kusan karfe shida, Aliyu tagani a waje tareda wani saurayi wanda shekarun sa bazasu haura talatin ba. Taji dad'i data gansa da abokin sa koh ba komai bazai mata fad'a agaban sa ba. Gaishe su tayi zata wuce ba tareda jiran amsan su ba dan bata bukata, Aliyu yace "Yau Saturday ma sai yanxu" "Eh" kawai tace a takaice, wanda suke taren neh yace "Wow wannan itace sister ka d'in" "Eh" Aliyu kawai yace dashi, abokinsa zai kara magana Aliyu yace "Maza kishiga ciki" tawani b'ata rai tashiga abun ta... Ji tayi abokin sa yana cewa "gaskia zaka bani wannan kanwar ka d'in ta mun" Aliyu yabasa amsa yace "Ba yanxu zatayi aure ba" Fido tace gwara daka fad'a masa haka a zuciyar ta bata k'arajin zancen su bakuma. Fido shiga tayi d'akin ta tayi wankan sallah, tana cikin shafa mai ajikin ta taji Aliyu yana kwala mata kira, da sauri ta saka kaya zuciyan name bugawa tana cewa "wayyo Allah yau na banu" "Kifito koh idan nashiga cikin d'akin nan zan karkaryaki" jikin ta yana shaking ta bud'e kofan, janta yayi kamar tsumma zuwa parlour yace "Dan Ubanki banace ki canza kaya kan ki fita ba" Tura bakin ta tayi tace "Haba Yaya kana treating d'ina kamar wata 'yar 18 years na girme matar ka fa". Cire belt na jikin sa yafara yana cewa " maimaita abunda kikace" tana ganin zai cire belt nasa ta haura a goje yabita amma inaa yakasa kamota tashiga d'akin ta tasa lock. Yayi bugun duniya amma inaa taki ta bud'e. Duk da yunwan dake addabar ta Corn Flakes kawai tasha tabi lafiar gado..Tace "wai Allah ya d'au beli nah" _Bayan Wata D'aya......_ Tun ranar da Fido ta had'uda Issam gidan su Eesha bata k'ara kallon sa ba. Tanason tambayar Eesha amma kar Eesha ta d'auka dagasken sonsa take, tsoki taja tace "basai ta d'auka inason sa ba d'in" D'aukar wayan ta tayi ta latsa number Eesha, bayan Eesha ta d'auka sun gaisa tarasa ta yadda zata tambaye ta, sai can tace "Kina gida neh?" "A'a ina cikin school yanxu muka fita cin abinci" "Ohk nima ina School lemme come and meet you guys but hope baku tareda da yaron nan" "Wani yaro kuma?" "Ummm mei ma sunan sa, kinsan ba kowa nake rik'e sunan saba, abokin Yaya Faruq dai" Eesha taganeh tsaf amma sai ta muge tace "Wa kenan? Kinsan abokan sa suna nan dayawa" "Ummm koh Issam neh koh meh yakeda suna" "Are you freaking serious Fido, kefa kika kirani time da kike Nigeria akan kina neman details na yaron akan akwai wani unfinished business tsakanin ki da yaron yanxu kuma kice bakisan sunan sa ba?" Ajiyan zuciya Fido tayi tace "Yanxu yana ina? It been long ban gansa ba" "Ya koma gida" atake Fido tace "Wani gida?" Dogon tsoki Eesha taja tace "Yanada gida da yawuce Nigeria neh?" "NIGERIA?" ta fad'a da karfi "Eh Fido, wani abu neh?" Take tace "No ba komai thank you bye" ta katse wayan. Salati tafara a hankali, yanxu ya zatayi, danshi tazo UK gashi baza barta ta koma Nigeria ba sai bayan ta gama d'an iskan Masters d'in nan... Toh fa masu karatu, shin zatabar Issam???? Wa zata aura??????? Aliyu, Issam koh abokin Aliyu... Nima dai dunno *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } GAISUWA NA MUSAMMAN MUNAYSHA, words can't explain how much I missed yhu.. ```Page 15``` D'aukan jakarta tayi hankalin ta duk a tashe, batasan ina zata k'ara had'uwa da Issam ba, batasan ina neh asalin gidan su yake ba. Jin k'aran horn yadawo da ita daga dogon tunanin data fad'a. Abokin Aliyu neh ya fito a motar yana mata murmushi yace "Sister nah ina zuwa haka" "Hmm gida" "Shigo toh na kaiki" shiga kawai tayi dan ita hankalin ta sam ma baya jikin ta, surutu yake mata a hanya wanda batasan ma yanayi ba. Ya tambaye number wayar ta ta mik'a masa wayar kawai ya latsa number shi yakira wayan shi yayi saving. Ya kaita har kofan gidan su ta sauka ba tareda tace masa tagode ba. Lokacin daidai Aliyu shima ya dawo gida kenan. Wani mugun kallo Aliyu ya watsa mata take tashiga cikin gida. D'akin ta direct tashiga tayi wanka tayi alwala tayi sallah. Fashewa da kuka tayi tana meh tuna mahaifin ta, mahaifin su yana sonsu kamar ransa. Baya barin Mum tamusu fad'a koh kad'an. Duk da sangantar dasu da yakeyi haka baisa sun lalace ba. Bazata tab'a mantawa da last maganan da sukayi da mahaifinta ba a daren dasu Issam suka shigo gidan _idan kin samu namiji meh hankali wanda kike sonsa yake sonki toh ki gabatardashi koh da bashi da koh sisi, bazan miki auren dole ba tunda bakison yaron marigayi abokinah duk da nayi alkawarin zan had'a ku aure nayi watsi da alkawarin nan sabida farin cikin ki shineh nawa_ Kuka ta fashe dashi tana dana sanin kin auren yaron abokin mahaifinta wanda batasanshi ba bai santa ba. Ringing na wayan tane ya dawo da ita dogon thinking data fad'a, rejecting tayi dan a halin yanxu she ain't in the mood of receiving any call. Same number neh yake sake kiranta, dogon tsaki taja ta d'auka wayar ta danna loudspeaker ba tareda tace komai ba sabida new number ce "Assalamu Alaykum Beauty" muryan namiji but it seems familiar to her. "Wa'alaykum Salaam" ta amsa k'asa k'asa "Queen of beauty har kin fara bacci neh" "Who is on the line?" "General Suleiman Abubakar" sai yanxu ta ganeh abokin Yaya Aliyu neh "Ohh sorry ina yini" "Lafia kalau Beauty, daman I just call to say hi" "Thank you" "Ba komai, kiyi saving number nah" "In Shaa Allah" "Bye" ya katse wayan. Tashiwa tayi akan gado dan yunwa sosai takeji, zata wuce kitchen Aliyu yakira ta yana zaune a parlour kuma sai ta wuce parlor kan tashiga kitchen. Yace "Ke zonan" kallon sa take ba tareda tayi motsi daga inda take ba, tsawa ya daka mata yace "Ba dake nake magana baneh" Tafiyan ta ahankali take har ta iso cikin parlour ta nema kujera ta zauna tayi crossing leg. Duk kallon ta suke daga Aliyun har Meena. Yace "Sauke kafan nan" sanda tayi kusan secs goma kan ta sauke kafan. Aliyu yace "Uban mei yahad'aki da S.A? Ina kuka had'u?" "S.A kuma ni ban sanshi ba" dunkule ya mata yace "Kinci gidan ku, aboki nah da yayi dropping naki d'azu" "Ohhh you mean Suleiman?" "Shi" "Nima dai ganin shi a school namu nayi, yana tamun magana naki na kulashi, shineh ya durkusa har kasa wai nayi hakuri koh bazan kulasa ba nashiga motar sa yakaini gida, shineh ni kuma na tausaya masa nashiga" Meena ce tayi magana tace "Kut!!!!!!!!! S.A d'in ya durkusa miki har kasa, ahhh lalle ke muguwar mak'aryaciya ce, kinsan S.A kuwa, kinsan mahaifin sa waye neh a Nigeria?" "Ban sani ba kuma ban damu na saniba, kuma yanxu yakirani a waya yana rok'o nah akan na so shi idan baniba bazai iya ruyuwa ba, yana cewa nice HAYAAT nasa" Aliyu dai kallon ta kawai yakeyi dan yasan Fido terrible liar ce, wata zuciyar kuma na gaya masa S.A zai iya aikata haka akan abunda yakeso Gyaran murya yayi yace "Don't even dare fall him, sabida an miki miji" "Yaya Aliyu kasan mutum bai sanin lokacin da zai fad'a cikin so, we don't get to choose who to love, love just happen" "Sannu Mrs Love kinji maza ki tashi kibani waje kuma karki kuskura ki sake masa fuska" "Dan S.A yafi karfin ki wlhy kije can ki nema class naki" cewar Meena Fido tashiwa tayi tana mamakin abunda Meena tace wai S.A yafi karfin ta, ita bataga wani abun fin karfin ta dayayi ba. Duk da yahad'u sosai amma wollah baifi karfinah ba. Juyawa tayi ta watsa wa Meena kallo tace "Wlhy Allah watarana sai mu bibbiyu zan miki dukan gaske naga meh kwatar ki, sai kin raina kanki yarinya" Bud'e baki duk sukayi suna kallon ta, Aliyu mamaki yake irin karfin halin Fido, yace "Ki mata duka kema jikin ki ya fad'a miki, wato kin raina matata koh? Ita ba aunty ki bace ehhhh? Very stupid girl kawai b'ace mini anan bana kaunar ganin wannan fuskan meh kama dana mayu" Ficewa Fido tayi tana cewa a hankali "wlhy koh kai baka isa ka tab'a lafia ta ba" Meena tayi hugging Aliyu tace "Moon of my life Fido ta manta da MATAR SOJA take zance, zan karkarya tane idan tamun iskanci" Aliyu kallon ta kawai yayi yasan dai Fido zata iya aikata abunda ta fad'a. Girgiza kansa yayi yana wani shu'umin murmushi.... Nigeria Abuja Issam neh awani mansion parlour, Mahaifyar sa ce take sauka akan stairs har tazo dab inda yake amma baima san tazo ba hankalin sa yana wani wajen. Tab'a sa tayi tace "lafiya Son". Take yayi firgit, saka hannun sa yayi cikin dogon bak'in gashin sa yayi ajiyan zuciya yace " I didn't know what to think of or maybe I did and I just refused to think about it. Mum all I know is that I liked this gurl" rik'e Mum nasa yayi gam yace "Ina tsoro Mummy, nafara jin ajikinah idan ban samei taba rayuwata tana cikin hatsari, inajin wani abu gamei da ita, Mummy karshen tama inajin kamar SHE'S MY HAYAAT, kamar ITACE RAYUWATA!!!!!!!!" Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } Na sadaukar da wannan page ma Shamcy, I heart you dear.... ```Page 16``` Mummy shafa gashin d'anta tayi tace "Karka damu Son, idan har Allah yayi matar kace toh tabbas sai ka aure ta, kasani mutum baya auran matar wani, matar mutum kabarinsa kaidai kata addu'a nima kullum ina cikin maka" Murmushi yayi yace "Mother you won't just understand, inaji ajiki kamar ta tsane ni, I see nothing in her eyes but hatred, she hated me Mother, ta tsane ni" "Shhh karna k'arajin ka fad'a haka, mesa zata tsane ka, bata tsane kaba Son kaji" Murmushi yayi yace "Yanxu naji relief" "Yanxu yaushe zata dawo Nigeria?" "In next 10 months In Shaa Allah" "Wow Allah kaimu" "Ameen" yace tareda rik'e hannun mahaifiyar sa gam kamar wanda idan yasake zata b'ace..... UK Washegari Fido tun da sassafe ta shirya zuwa school, bayan Aliyu yayi dropping nata yace "Wlhy Allah kar kishiga motan kowa idan kin tashi zuwa" "Koh da Motar Suleiman" "Shi d'in kanin Ubanki neh koh na Uwarki" fita tayi kawai a motar ba tareda da ta kara cewa komai ba, tace "Gosh!!!! Ban kaunar maza masu ashar wlhy, basu san aji down baneh" Bayan ta gama lecture da practical nata taje wajen Eesha, acikin hiran neh Eesha take fad'an Issam dole yabar Abuja yazo KT auran su, anan tasan Issam yanxu yana Abj. Tunani tafara idan Allah yasa ta koma gida wani irin k'arya zatayi da za'abarta taje Abuja. Eesha ce ta tab'o ta tace "Lafia kuwa Fido?" Firgit Fido tayi ta kwakulo murmushi tace "Lafia" Wayar tane yafara ringing d'aukawan da zatayi taga Gen. Suleiman, bata d'auka ba a first call sanda ya k'ara kira na biyu, Eesha tace "Ki d'aga mana ba kiranki ake yi ba?" "Mtswww kedai bari wlhy wani abokin Yaya Aliyu neh shima an turo shi wani assignment but shi tun last year yana nan, next month ma zai koma gida" "Wow kice kin samu Soja" "Kinsan duk rashin kunya nah ina shakkan su ai, tun lokacin da wani tsinannen Soja yamini rashin mutunci a Maiduguri, tun lokacin nake shakkan su" Dariya Eesha tayi tace "Ba ke kince you are very stubborn ba, ai kin had'u da daidan ki" "Kinsan wani abun takaici, Sojan fa recruit neh, kurkutun banza, a yau idan na had'u dashi sai na saka Yaya Aliyu da S.A sun masa rashin mutunci, zance su zaneh sa a gaba nah kuma su sakashi frog jump" dariya Eesha tayi tace "Ahh lalle bakida dama, please kiyi receiving call d'in mana" "Ohk bara na saka a loudspeaker kiji" Picking call d'in tayi ta danna loudspeaker "Haba Queen of beauty inata kiran ki bakya d'auka wa" "So sorry wlhy wayar ce a silent ina lab" "Ohh ayyah, yanxu kina ina?" "Na fita shan coffee" "Wani coffeehouse?" "Rio" "Ohk yanxu zaki ganni In Shaa Allah" ya katse wayan Eesha tace "wow kice kinyi sabo, toh ina zakikai Issam namu" Murmushi Fido tayi tace "The truth is that I feel nothing for Issam, believe it or not Eesha. Idan ma ina feeling wani abu akanshi bai wuce hatred ba" "Sub'hanallah!!!! Tsana kuma Fido, meya miki da kika tsaneh shi" "Forget it" "Hmm Allah shi kyauta, but kinsan tsana yana iya komawa SO" "Never!!!! Allah sawwaka" Sallama S.A ya musu tareda neman waje ya zauna "Good afternoon" cewar Eesha. S.A yayi murmushi yace "Afternoon durlin" dariya duk sukayi Fido tace "Kar Faruq yakama ka kana kiran ta durlin" S.A yace "Wait are you jealous" Dariya Eesha tayi tace "Inaga she's jealous, Mrs J!!! Bari natafi ana jirana bye" tareda d'aukan jakarta ta. S.A yace "Toh baki fad'a mun sunan ki ba?" "Eesha" tareda musu bye bye tabar wajen.. S.A tasowa yayi a kujeran sa ya koma kujeran da Eesha ta tashi wanda yake opposite na Fido. Kallon ta yake with so much tenderness on his eyes. Yace "Your eyes, they're so mesmerizing, so beautiful" Murmushi Fido tayi tace "Thank Yhu!!!!!" Hira sukayi sosai dan S.A mutum neh mai barkwanci, akwai shi da wasa da dariya daga nan suka wuce gida. Yau ma kamar jiya yayi dropping nata Aliyu yana waje kan kujera yana karanta magazine. B'ata rai yayi kamar wanda bai tab'a dariya ba, wucesa Fido tayi ba tareda ta gaishe shi ba. S.A mik'a masa hannun yayi suka gaisa ya nema waje ya zauna yace "Mutumina ya akayi neh" "Kalau" yabasa amsa a takaice yacigaba da karanta magazine na hannun sa "Aliyu kana son Fido neh?" Tambayan yazo masa banbarakwai atake ya d'aga ido ya kallesa yace "What The Fuck!" Yaja dogon tsaki yacigaba da karanta magazine nashi. S.A yace "Man be serious, idan kana sonta wlhy shikenan zan hakura da ita duk da ina matuk'ar sonta, duk da yanxu ina jinta a jikinah, duk da a yanxu ta zama wani b'angare na jikinah bari na kad'aita maka lbr, d'an zaman da mukayi da ita inajin itace RAYUWATA, Like she's my HAYAAT" Hankalin Aliyu yayi mugun tashi wanda baisan na menene ba, shi sam baya sonta, baima yarda wa zuciyan shi yana sonta ba, yace "Allah sawwaka meh zanyi da ita, ai da ina sonta da an mana aure tun kan muzu nan. Ni sam ba class d'ina bace ni sam bata mun ba, abunda yasa nace maka tanada miji cox Abba yace tana dawowa za had'ata aure a cikin brothers d'ina" "Kai baka sonta?" "Bana sonta, ban tab'a sonta ba kuma bazan tab'a son taba, i'm just been protective of her cox she's my sister, so just chill!!! Banaso irin ka gama falling mata kuma sai a hanaka auren ta" murmushi S.A yayi yace "Idan tana so nah inaga baza'a mata auren dole ba" Mik'a masa hannu Aliyu yayi yace "All the best my Man" hugging nasa S.A yayi yace "Nagode, Nagode" Bayan Sallah isha'i suka fita zasuje wajen assignment nasu su dawo, already shi S.A nan da wata d'aya zai koma dan yagama training nashi Aliyu kuma yanxu yafara. Bayan sun fita Fido taje kitchen ta dafa Indomie ta zuba a plate ta kawo parlour, kan yayi sanyi tace bara tayi sallah. Tana cikin sallah Meena ta fito ta d'au Indomie ta zauna akan dinning tafara ci abunta hankali kwance. Fido bayan ta idar da Sallah taga Meena tana cin Indomie data dafa, Fido k'arasowa tayi wajen dinning d'in tace "Uban wa yace kid'au mini Indomie kici" "Ubanki neh yasa na d'auka kuma baki isa kiyi komai ba" Tasssss!!!! Fido ta wanka mata mari mai rai da lafia wanda sanda Meena taga stars. Tashiwa Meena tayi suka shiga dambe, yi suke gashi ba kowa a gidan, nima dai ba karfi baneh gare ni dana raba. Suna cikin yi Fido tana ruwan cikin ta tana d'irkan ta Meena sai ihu take "wayyoooo Allah zata kashe ni" Aliyu neh yashigo gidan da gudu, ganin Fido a ruwan cikin Meena yasa yayi gudu zuwa wajen yayi wurgi da Fido kamar kayan wanki, cire belt na jikinsa yayi yafara zaneta baji ba gani, da karfi hali irin na Fido koh kuka batayi shineh yake kara kular dashi yacigaba da dukan ta. S.A yashigo da sauri ya rik'e Aliyu yace "Haba lafian ka" Aliyu ransa yayi mugun b'aciwa ya nuna ta da yatsa yace "Idan har wani abu ya samei yaro nah wlhy saina illataki banza mara hankali kawai" Fido karfin hali tayi dukda taji jiki tace "Wlhy Allah toh kayi warning na matarka idan ta kuma mun iskanci sai na mata abunda yafi haka Wlhy Allah zan manta juna biyu neh da ita na mata dukan gaske, kuma idan nadake ta na daka banza" Duk rik'on da S.A ya masa hakan baisa yayi kanta yafara zuba mata belt ba. S.A da duk karfin sa ya rik'e Aliyu, yace "Maza ke Fido ki shiga d'aki" tana kumbure kumbure had'e da kananan maganganu tashiga d'akin ta. Ajiyan zuciya S.A yayi yana mamaki irin halin Fido, ji yayi ya k'ara sonta haka yakeson matarsa tazama ba tsoro kuma baza iya danne mata hakkin ta tayi shuru ba..... Da k'yar S.A ya lallashe Aliyu kan ya hakura. Zuwa yayi wajen Meena yashafa cikin ta yace "My dear baby nah lafia koh". Dogon tsoki taja tace "Wato babyn ka kadamu baka damu da lafiata ba koh?" "No ba haka baneh" zai rungume ta, dakatar dashi tayi tace "Haka neh mana, baka mata fad'an tab'a lafia ta da tayiba kana mata maganar babyn ka, zanyi maganin dukkan ku biyu Wlhy billahillazi, sai tasan ta tab'a lafiata" taja dogon tsoki tashiga d'akin ta... Aliyu ransa yayi mugun b'aci, yara kanana duk sun raina sa, yana mamaki irin raina shin da sukayi, ahakan baya musu wasa, da ina musu wasa da dariya ai da sai abun yafi haka ya fad'a a zuciyar shi... Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } Na sadaukar da wannan page d'in ma Amnaj and Aisha(jalingo) bisa k'aunar da kuke nunawa Hayaateey! Nagode😊 ```Page 18``` Wani jibgegen gida neh meh d'an karan kyau, daga funitures har cotton nah gidan foreign neh, tsaya baku labarin tsaruwan gidan b'ata lokaci neh dan ya had'u the end. S.A zaune a k'asa kan carpet sai wata mata wanda ak'alla zatakai shekaru hamsin ba take zaune akan designer cushion. Tun daga kan fingers nata, hannun ta, wuyanta da kunnen ta gold neh masu tsadan gaske k'irar Saudi. Tace "Haba Suleiman, bayan mun gama dakai akan idan ka dawo zaka aura yarinya His Excellency, yarinyan shugaban k'asa yanxu kazo mini da maganar banza akan wai wata daban kakeso, wanda mahaifin ta ya rasu ba'asan shi a Nigeria ba, haba Suleiman!!! Idan ka aura Safiyya fa status naka da namu zai k'aru, mahaifin ka da yakeso yayi contesting for president for the next election kanaso ka kawo mana cikas, gaskia bazamu lamunta ba" S.A kansa a k'asa yace "Mummy gaskia ni ita nakeso sai dai kuyi hakuri, ina ruwan politics da aure nah kuma, kudai kuce kuna so ku aura mini Supy for your own selfish interest" Taassss ta wanke sa da mari. "S.A ni kake fad'awa sabida Selfish interest namu akan wata banzan yarinya, toh kasani ba kai ba auren ta" "Toh Wlh Mummy idan ban aure taba bazan aura wata Supy ba, Mummy do you really know how much I love her? Mummy inason Fiddausi sosai, inason ta kamar raina, Mummy Fiddausi itace Rayuwa ta, SHE'S MY HAYAAT!!!!!" Mum ba karamin girgiza tayi da kalamun tilon d'an nata ba, tana son d'anta sosai kuma batason abunda zai b'ata masa rai, a kullum tana kokarin son abunda yakeso amma a halin yanxu tafi kaunar tajita a matsayin Matar shugaban k'asa duk da a yanxu Minister ce Mijin ta kuma Abubakar Babangida Senator. Kwantar da murya tayi tace "Haba Son, kayi hakuri idan yaso bayan ka aura Safiyya sai ka aura ita wanda kakeso kaji" "Mum nifa koh da a yau bazan aura Fiddausi ba toh wlhy bazan aura Jamila ba koh da ita kad'ai ce mace a duniya bazan aure taba, she ain't the type of woman I wanna spent my life with" Hajiya Lubabatu ranta yayi mugun b'aci, duk wani hope nata yana neman rugujewa akan Fido, murmushin dole tayi tace "Shikenan na amince but on one condition" Take ya d'aga kansa yana murmushi yace "Ina jinki Hajia" "Sai naje naganta first, idan har na yaba da tarbiyan ta shikenan sai ayi auren but daga baya zaka aura Safiyya" A take ya d'aga kai ya kalle mahaifiyar sa, ganin ba wasa a fuskan ta a sanyaye yace "Na amince" "Good! Yanzu sai naganta farkon tukun" "Mum Allah sa hakan neh har zuciyan ki" "Meh kake nufi?" "Nothing" Address nasu Fido ya bata akan gobe zataje KT dan ganin Fido da iyayen ta. Suna rabuwa da mahaifiyar sa ya kira Fido ya sanar da ita akan gobe Hajiya zata KT wani business and tayi insisting tanaso taga iyayen ta. Fido bata kawo komai aranta ba murmushi kawai tayi tace Allah kaimu zan sanar da Mami sai ta fad'a wa Abba. Da daddare Fido taje b'angaren Abba, da sallama tashiga taci sa'a yana parlour yana kallon News. Amsa mata sallama yayi yana murmushi yace "Mutanen UK ya gajiyan hanya?" Murmushi tayi ta zauna a kasan carpet tace "Abba Alhamdulillah" "That's Good, toh ya karatu?" "Alhamdulillah" "Good, d'azu Mami take fad'a mun akan Mahaifiyar S.A zatazo gobe, but a ganina ai Maza suke zuwa tambayan aure ba Mata ba" "Eh Abba business tazo KT shineh takeson ganina" "Ohk,Kinsan already mun gama da Inna akan kina zuwa zamu d'aura miki aure da Aliyu, sai d'azu Aliyu yake fad'a mini kun daidai ta da S.A, haki'ka S.A mutumin kirki neh dan tun da nasanshi tareda Aliyu yanada hankali sosai he's very respectful and responsible person. Tunda shi kike so ba komai idan tazo zan mata magana ta turo Maza dan wannan ba maganar mace baneh " "Toh Abba Nagode" "Ba komai" Hajja ce tashigo cikin parlour, tana ganin Fido ta watsa mata harara tareda jan dogon tsoki, Abba yace "You can go Allah miki albarka" "Ameen Abba" Tana fita Hajja tace "Kai Alhaji duniyan nan an tara wanda basa tsoron Allah" Alhaji yace "Kwarai kuwa, but mekika gani?" "Alhaji tun yaushe S.A yakeson Ramlah? (Amani na canza zuwa Ramla) amma rana d'aya wasu suka juye masa hankalin sa lalle boko yana aiki" "Fal yaqul khaira aw liyas mut, kifad'a alkhairi koh kiyi shuru. Banson maganan banza kinji". Tashiwa tayi tana kananan maganganu Abba dai girgiza kansa yayi yace MATA kenan! Akan hanya suka had'u da Teema, wani harara take wa Fido tace "Yanxu wai S.A kike so naji labari?" "Shi yake so nah kuma shi zan aura" Fido ta bata amsa tareda barin wajen, da karfi Teema tace "Ai wollah S.A yafi karfin ki karamar 'yar iska kawai" Fido ko kulata batayi ba tacigaba da tafiyan ta, tace wollah 'yan bakin ciki saidai su mutu _Washegari_ Eesha da Fido zaune cikin motar Eesha wata mota Benz bak'a tashigo cikin haraban gidan, Eesha tace "Anya wannan ba Mahaifiyar S.A baneh" "Ke ja motar dan Allah banso mu had'u inajin kunya" Wani dogon tsaki Eesha taja tace "Kunyan banza kuji yarinya wai kinajin Kunya" Wayan Fido neh yafara ringing ganin New number ta d'auka tace "Assalamu Alaykum" Can muryan wata mata ce tace "Ina cikin gida ku kifito" "Ohk" Fido tace a hankali tareda katse wayan. Juyawa tayi ta kalla Eesha tace "Eesha wannan wace irin matace, mesa S.A yabata number nah?" "Awww kina nufin ita ta kiraki?" "Mtswww wai tana waje nafito, dan Allah rakani" "Ohk muje" Tare suka fita acikin motan, Fido atampa Holland neh ajikin ta d'inkin dogon riga sai gyale data yafa R$S da dogon high heel dake kafan ta, Eesha kuma Abaya Purple neh tayi rolling kanta da veil nashi. Zuwa wajen motar sukayi suka tsaya dan basu kallon wanda ke cikin motar dan glass d'in Super tint ce, haka suke tsaya kusan minti goma kan wani yafito a motar da sauri har sanda suka firgita ya bud'e ownest corner. Mahaifiyar S.A ce tafito tasha kwalliya jikin ta yasha gold, wani kallon sama da kasa take musu kan tace "Wacece Fido a cikin ku?" Ina meh baku hakuri kwana biyu kun jini shuru wlhy banajin dad'i shiyasa By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } ```Page 17``` S.A yace "Haba Aliyu meh haka? Kai da yakamata ka tsaya kaji meh yafaru before taking any action amma kawai sai ka fara zaneta, gaskia banji d'adin wannan abun ba, idan badan kai yayanta baneh Allah da sai mun b'ata" Aliyu hararan sa yayi yaja dogon tsaki yace "Kaga please let me rest bana son wani headache" "Ohk tunda haka kace, but please karka kuma dukan mun mata" Aliyu a ransa yaji maganar amma ya dake yayi shigewar sa d'akin, S.A girgiza kai yayi shima yafita a gidan..... Fido zaune take akan gado tana shafa Robb ajikin ta dan ba karamin jin jiki tayi ba, wani farin ciki takeji koh ba komai tayima Meena duka, gani take daga yau sun raba raini. Wayar ta neh ya dawo da ita daga dogon tunanin data fad'a, S.A tagani baro baro kan screen. "Yaa Salaaam" ta furta a hankali, zatayi receiving call d'in sai kuma ta fasa "Mtswww yaga Aliyu yana duka nah ai da kunya, kai wlhy Yaya Aliyu yakawo mini cikas, ai wannan aji down neh" haka tabari wayan yata ringing bata d'aga ba... Can bayan ta kwanta taji message yashigo mata waya, ita duk a tunanin ta zataga number S.A, sai dai kuma code na Nigeria da tagani, bud'e wa tayi taga message: _Mesa kike zuwa cikin mafarki nah and my thoughts every blessing day, WHY???????_ Tsaki taja ta kunna data na wayar ta tana ganin trailer wani sabon film Haseena, sai can tak'ara jin message yashigo wayar ta. Bud'ewa tayi taga same number: _Kina saka ni cikin damuwa and dilemma, why HAYAATEE?_ Wani dogon tsaki taja tace koma waye saidai ka cinye kanka tayi blocking number......... Tun daga lokacin Meena tana mugun shakkan Fido sabida tasan ba meh kwatar ta amma ta rantse da Allah duk ranar da suka koma gida Nigeria she must regret tab'a mata skin da tayi, ta ayyana a ranta har Aliyu bazata barshi ba tunda ya nuna mata a fili ba ita yakeso ba abunda yake cikin ta yakeso. Fido karatu take ba kama hannun yaro, takan bincike akan Issam wanda taji labari gidan su yanxu yana abuja. S.A kam ya koma Nigeria amma kullum suna cikin waya da Fido, yake ce mata tana dawowa za'ayi maganar auren su.. Itadai saidai tayi murmushi dan har ga Allah S.A yakai namijin dazata So shi!!!!!!! _Bayan Shekara d'aya_ Nigeria Umaru Musu 'Yar aduwa Airport General Aliyu neh rik'e da kyakkyawan baby girl a hannun sa, gefen sa na dama Fido ce tasha bak'in sunshade, da doguwar riga ready made purple da flowers yellow tayi rolling da black veil da takalmi da jakanta shima black, ba karamin kyau tayi ba, sai nace weather UK ya karb'eta sosai, by his left kuma Meena ce tayi jiki sosai, sai wani shan k'amshi take tana hura hanci a dole ita meh miji da baby itama ba laifi ta k'ara haske duk da ma tun da fara ce, sai idon ta k'anana da yak'ara shiga ciki dan jikin da tayi.. Shamcy da gudu tazo ta rungume Fido tace "Wow sis kinyi kyau, gaskia UK ta karb'e ki sai kace ba karatu kikaje ba" Fido taja hancin ta tace "You can at least say Welcome first!?" "Sorry Sis! Welcome " "Thanks" Shamcy ta gaishe da Meena wanda dakyar da amsa, ta gaishe da Yaya Aliyu ta karb'a babyn hannun sa tace "Wow Mashaa Allah Yaya kuna kama da Basma amma hasken Anty Meena tabiyo" "Ke ke ke ban daughter nah bana son jagwalgolo" cewar Meena. Shamcy jiki a sanyaye ta mik'a mata Basmah ta wuce wajen Fido da Yaya Khaleal. Fido tayi dariya tace "Maganin ki nan gaba ki k'ara kinji, da maitan ki na son yara d'in". Shamcy dai shuru tayi batace k'ala ba sai wani tura bakin da take. Fido da Shamcy shiga motan Yaya Khaleal sukayi, su Aliyu kuma suka shiga motan Teema. Fido tana shiga parlour taga Inna da remote a hannu tana kallon B4U Movies, da gudu taje ta rungume ta tace "Inna keda India sai kace kina jin yaren" "Ja'iran yarinya ai kin tsorata ni ya kasar waje ya karatu?" "Alhamdulillah Inna" "Kai Mashaa Allah kin ganki kuwa, kin k'ara kyau lalle Aliyu yana kula dake sosai, tunda Allah yasa kin dawo sai maganar auren ku" "Aure nah da waye kuma?" "Kuji 'yar iskar yarinya, tambayata ma kike?" "Kinga Inna I don't have time for this, let me freshen up" Barin ta tayi tashiga d'aki tayi wanka, bayan ta fito tayi sallah. Shamcy ta zauna kusa da ita tace "Adda Fido ina tsarabar mu?" "Mtswww ke kyale ni ba yau ba, ina SIM card da nace kimun register?" Tashiwa Shamcy tayi ta d'auko mata, bayan ta saka a wayar ta takira number Eesha, Eesha tana d'agawa tace " 'Yar duniya ai na d'auka zakiyi missing aure nah" "Hmm na isa nayi missing auren ki, yanxu saura sati nawa?" "Three weeks" "Da sauran lokaci ma ashe, umm Issam zaiyi attending kuwa?" Dariya Eesha tayi tace "Ai dolen sa yana best friend na Faruq" Fido wani sanyi taji a ranta, tunani take wani irin mataki zata d'auka a kansa. Eesha tace "Ya naji kinyi shuru? Wani abu neh? "A'a wlhy ba komai" "Zanzo gobe ki ajiye mini tsaraba ta" "Mtsww bakida damuwa sai kinzo bye" Fido shuru tayi tana tunani, hankalin ta gaba d'aya yana kan Issam, tunani take wani irin mataki yakamata ta d'auka akan sa. Wani yace ta shafe shi a doron kasa, take ta girgiza kanta tace "NOOOO" wani zuciyan yace ki masa abunda bazai tab'a mantawa dake ba har karshen rayuwar sa. Ya Allah toh meh kenan zan masa?!!!! Ringing na wayan tane yasa tayi firgit ta dawo a dogon tunanin data fad'a, receiving na call d'in tayi tana murmushi tace "My Man Shamcy ce ta tura maka number na koh?". Tayi dariya sai can tace "ohk toh ba matsala idan kayiwa Hajiya magana duk yadda kukayi sai ka fad'a mini". "Ohk bye" tareda katse wayan. Abuja Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } ```Page 19``` Duk suka durkusa har kasa suka gaishe ta, d'auke kanta tayi tace "Ba gaisuwan ku nake buk'ata ba, koh kunji nace ku gaishe ni? I just asked you people a simple question kunje kuna abu daban, na tabbata da exams neh da kunyi failing. For the last time nace wacece Fiddausi a cikin ku?" Da hankali Fido ta furta "Nice Mummy" Dogon tsaki Hajiya Lubabatu taja tace "Toh kaini wajen Ubanki" A sanyaye Fido ta tashi tace "Muje" B'angaren Abba takai ta, a bakin kofa tace "Bara na mishi magana idan yabada permission sai ki shigo" Kallon Uku saura tara ta mata ta bud'e kofan da karfi da shiga, Allah yasa yana parlour yana rubuce rubucen sa Mami da Inna na gefen sa. Gani kawai sukayi an bangaje kofa an shiga ba koh sallama, da mamaki suke kallon ta Abba yace "Ya ke lafia kike kuwa?" "Aw so kake kace ni mahaukaciya ce koh?" "Toh idan ke ba mahaukaciya bace toh tabbas bakida cikekken hankali" "Mei kake nufi kenan?" Fido da gudu taje wajen Abba tace "Abba Mahaifiyar S.A ce fa" A tsawace Abba yace "And so bloody what? Who gave her the audacity ta shigo mini parlour na haka?" Dariya tayi Hajiya Lubabatu tace "You called this a parlour, mei ma kake da suna? Professor Sanusi Umaru Sodangi kake koh? Ai wannan da kake kira da parlour koh driver nah parlour sa yafi wannan. Nawa kake karb'a a wata salary ka. Dubu d'ari hud'u, dubu d'ari biyar koh dubu d'ari shida?" Abba shuru yayi ya rasa meh zai ce mata dan yafi karfi ace yana sa'insa da mace, a tsawace Hajiya Lubabatu tace "Answer me mana" Fido ranta idan yayi dubu ya b'aci, tazo gaban Hajiya Lubabatu tace "Hajiya Lubabatu ke d'in da kanki salary ki nawa yake? Ai bai wuce irin na mahaifina ba, saidai shi d'in halak malak nasa yake ci, ke kuma hakkin talakoki kuke sata kuke ci" "Ni kike fad'a wa haka?" "Ke d'in, highest abunda zakice shine bazan aura d'anki ba koh? Toh ai nima haukan da kika zo kikayi shi kad'ai ya isa yasa bazan aure shi" "Better da kika furta da kanki baza ki aure shiba, dan Wlhy d'ana yafi karfin gidan nan" ta fice a parlor. Inna tayi salati tace "Yau naga tsinanniyar uwa. Kai Allah shirye mu, Ameen" Abba yace "Fiddausi zo nan" Gaban sa taje ta durkusa, yace "Fiddausi no matter what learn to respect your elders you shouldn't have talked to her that way" Fido jikinta yayi sanyi tasan tayi kuskure koh ba komai akwai mutunci tsakanin ta da S.A tace "In Shaa Allah Abba bazan k'ara ba" "Maza toh tashi ki tafi" jiki a sanyaye ta fita. Inna ta fashe da kuka, tace "Alhaji baga irinta ba, ni tun farko ba son auren nan nake ba, nace ka d'aura auren da Aliyu amma kayi kunnen shigo wato ni ban isa da kai ba koh? " Haba Inna kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan nan" "Sai ka mini alkawarin zaka had'a ta da Aliyu" "Na miki alkawari" Inna atake ta share hawayen ta tace "Amma kasan duk mei karya alkawari alaman munafiki ni koh, tam" "Kai Inna mei yakawo maganan munafiki kuma haba, na tambaye ki mana Inna" "Ina jinka" "Of all mazan gidan mesa kika nace sai Aliyu bayan shi yanada matar sa, ga Khaleal, ga Ahmad duk basu da aure" "Toh ai Aliyun neh yace yana son ta" "Kin tabbata?" "Aww toh karya zan maka?" "Ohk bari zan mishi waya yazo naji ta bakin sa" ********************** Mahaifiyar Issam ce zaune tana kallon News a Al-jazeera. Issam yashigo yana murmushi yace "Mum come with me please" Murmushi Mum tayi tace "Ina kuma Isssaaam?" "Kedai kizo ki gani" Tasowa Mum tayi tace "D'an rikici, muje koh" Wani d'aki yakai ta a cikin gidan wanda batasan dashi ba tunda take a gidan, bud'e kofa yayi yace "Mum She's the one!" Mum bud'e baki tayi tana kallon cikin d'akin, zuciyan ta yana mei bugawa, tunda tasan d'anta bai tab'a son mace ba. Drawing na pictures na Fido neh kaf cikin d'akin, a kowani zanen hoto ya rubuta *Hayaateey*, wasu ya rubata *She's My Hayat* Zuwa yayi koh wani zanen hoton yana shafa fuskan yana murmushi yace "Mother ban tab'a tsanmanin i'm good architect sanda nafara sonta. Mother can you see how beautiful she is?" Mum take ta goge hawayen da yake sauko wa kan fuskan ta kar yagani, tayi murmushi tace "She's Beautiful!" "Yeah she is, I so much love her Mother. Cant wait auren Faruq na fad'a mata that I've falling for her, na fad'a mata ina Sonta, ina kaunar ta, itace ruhina, jinin jikinah, itace RAYUWATA. HAYATEEY FIDDAUSI" ****************************** Aliyu kwance yake akan gado zuciyan sa yana bugawa, a yanxu ya tabbatar wa kansa lalle dagaske yana son Fido more than tunanin sa, So na hak'ik'a, bud'e wayan sa yayi, folder daban nagani wanda pictures na Fido neh zalla a ciki, wasu tana tafiya, wasu tana bacci, wasu tana cin abinci, wasu tana chat a waya. Murmushi yayi yana shafa kan screen na wayan yace "Fido words can't explain how much I love you, ina sonki ina matuk'ar sonki, zuciyata ta gama kamuwa da sonki, kece numfashi nah, kece jinin jikinah, kece Qalbee nah, kece RAYUWA TA!!!!!!" K'aran wayan sa neh yasa yayi firgit, atake yayi picking call d'in dan ganin Abba "Assalamu Alaykum" sai can yace "Ohk Abba In Shaa Allah anjima zanzo bayan Isha'i" ya katse wayan zuciyan sa na mei bugawa. Fido zaune a kan gado laptop a gaban ta tana kallon wani series Game Of Thrones, k'arar message taji ya shigo wayarta a take ta d'au wayan duk a tunanin ta S.A neh dan yata kiranta bata kusa bata samu tayi recieving call d'in ba, ganin wani message new number yasa ta bud'e, message kamar haka _Believe me, you are the one, whom my heart finds, whom my heart reminds me of, whom my destiny wants, whom I love the most! Believe me, idan nace miki Kece farin ciki nah, jin dad'i nah. Believe You are my HAYAT!!!_ Sau uku take karanta message d'in dan har aranta taji dad'in sa. Murmushi tayi sai can kuma taja dogon tsaki tace Maybe ma k'ananan 'yan iskan nan neh.. Batayi deleting ba dan ba karamin dad'i ya mata ba, wani message neh ya k'ara shigowa take ta bud'e tafara karantawa _Kar kiyi kuskuren blocking d'in number ta kamar yadda kikayi a lokacin da kike UK dan kece zaki sha wahala, bazanyi k'asa a gwiwa ba dan ganin na miki messages kullum koh da zakina blocking every Sim card da zan na tura miki message dashi and plus don't think of changing your number sabida a ranar da kika canza zan samu!!! Stay Safe Hayateeyy_ Tunani tafara shin wanna waye neh? Duk yadda akayi ya santa or yasan someone very close to her. Jin k'aran wani message yasa tayi sauri ta bud'e _And please Dan Allah kar kizo mini a mafarki nah kinji koh Hayaateey ? And my thoughts please!!!!!_ Murmushi tayi tace Lalle baka da aiki tareda jan dogon tsaki. Shamcy ce tashigo cikin d'akin tace "Adda Fido Abba yana kira" "Shammcyy you can't you say Assalamu Alaykum first! Wannan wace irin halin neh" "Adda Fido nayi bakiji ba" "Banson karya dallah b'ace mini a gaba" Hijabinta ta d'auko wanda yake har kasa ta saka ta d'au wayarta da yake kan gado. Direct side na Abba ta wuce tayi sallama tashiga. Zuciyan tane ya tsinke dan ganin Matan sa uku da tayi, mahaifiyar ta da kuma Aliyu wanda yake zaune a kasan carpet kamar wani mutumin kirki. Waje ta nema ta zauna ta gaishe su. Abba yace "Fiddausi abunda yasa muka kiraki shineh kinga dai abunda mahaifiyar S.A tazo tayi a gidan nan, kuma daga baya Mijin ta Alhaji Abubakar Babangida ya kirani wai zai bani any amount dan mubar maganan auren, shine nace yabar kud'in sa nima na fasa. So yanxu munyi deciding zamu d'aura muku aure da Aliyu dan tun daman can dashi za'ayi kikace S.A kike so. Kin amince?" Ji tayi abun yazo mata banbarakwai, ita a da taso Aliyu kamar ranta, shuru tayi, Abba yace "Me kikace Fiddausi, idan bakison sa bazamu miki auren dole ba" Fiddausi a hankali ta furta "Na amince Abba, zab'in ku shine nawa" "Yawwa Madallah, In Shaa Allah nan da wata d'aya za d'aura auren, ki tashi ki tafi Allah miki albarka" A sanyaye ta tashi tabar parlor, ta rasa meh take feeling, farin ciki koh bakin ciki? Fashewa da kuka tayi tace "Allah gani gareka!" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life (p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } *Words can't explain how much I love you babes😘. My kanwa Meenarh Parrot and my dear Teemerhlurv❤. Heart yhu gurls plus i dedicated this page to yhu both* ```Page 21``` A hankali tashiga cikin motan ta zauna, d'aga kai tayi suka k'ara four eyes dashi ya kashe mata ido d'aya a take ta sauke kanta dan ya mata bala'in kwarjini. Farar shadda neh a jikin sa mei kyaun gaske yasha zuben hannu bak'i, hulan kansa ma bak'i wanda ya dace da kalar fatan sa fari. Ga sajen sa bak'i wanda ya kwanta luguf a kyakkyawan fuskan sa, ya had'u more than farkon data fara kallon sa saidai yanxu ya d'an rame. "Kyaun maciji" tayi mumbling tareda jan dogon tsaki wanda yasa duk suka juya suka kalleta. A take Issam yaja wawan biriki wanda ya tsoratar dasu Eesha tace "Lafiyan ku kuwa?" Issam yace "Ask her, kinsan I hate tsaki and I hate anybody da yakeyi" Wani dogon tsaki ta k'ara ja tace "We are running late Mallam dan Allah muje haba" "Kayi hakuri Issam haba yau ina cikin farin ciki abokinah bai kamata ka mini haka ba, please don't ruin it" cewar Faruq Issam ya tada motar yace "I swearit if she dare hiss again zan zubar daku a mota nah idan yaso kwayi waya a zo a d'auke ku" Faruq yayi dariya yace "Naji abokinah hakuri zakayi" Fido dai shuru tayi bata k'ara cewa komai ba gani take ta kuma yin wani maganan aji down neh. A Katsina Motel Hotel suka sauka, Cameras neh sukayi caaaa akansu suna d'aukan su hoto lokacin da suke fitowa a mota. Bayan Issam da Fido sun sauka a motar suka bud'e wa amarya da ango kofa suma suka fito. Eesha da Faruq suka shiga gaba, Issam d Fido suna binsu a baya suma kamar couples. Issam matsowa yayi daf kusa da kunnen ta ya mata magana wanda ni kaina bansan mei ya fad'a mata ba. Wani irin kallo ta watsa masa tareda jan tsaki, murmushi yayi tareda shafa sajen sa. Hall d'in yasha decorations Mashaa Allah yayi kyau sosai, high table sukaje suka zauna. An bud'e taru da addu'a, aka kira best friend na ango wato Issam ya hau kan stage ya bada history ango. Zo kuga yadda all eyes on him, Ramla da Teema wanda sunyi attending dinner suna gefen Fido suka ce "Mashaa Allah" Teema tace "Ramlah kina ganin guy, wayyooo Allah nah yayi karshe" Ramla tace "Da a hanya na gansa sai na rantse da Allah ba mutum baneh, Kut! Hmm nama rasa mei zance" Fido dai shuru tayi tana jinsu, Bayan ya gama aka kira Fido itama tazo ta bada history amarya. A hankali take cat walking wanda a yanxu ya riga ya zame mata jiki, mazan nan duk ido a kanta dan ta had'u iya had'uwa. Tafiyan ta ma kad'ai abun kallo neh bare azo ga kayan jikin ta da kuma kyawunta. Tana cikin tafiyan ta mistakenly ta taka dogon rigan ta wanda yake jan kasa sai gata zata fad'i kasa. Rufe idon ta tayi gam jira kawai take ta fad'i tashiga kunya. Ji tayi an taro ta, a hankali ta bud'e idon ta tayi ido hud'u da Issam wanda ya zuba ido yana kallon ta. "Astagfirullah" ya furta a hankali tareda tsayar da ita dam. Zo kuga Hall kowa na kallon su kamar sun samu T.V. A hankali Issam yace "Try to watch your steps next time gurl and plus if you can't walk with a shoe like this karki k'ara sakawa. Village gurl" A ranta taji zagin amma ba yadda ta iya and yayi saving nata da yau taji kunya. A sanyaye taje kan stage d'in ta bada history amarya cikin harcin turanci sai ka rantse bata iya hausa ba... Bayan nan aka ci aka sha, ganin 'yan pure moment nayi sunata warwaso kan abinci duk da abincin serve yourself neh amma ko wacce da k'aton tare da Leda a hannu, a cika tray a cika leda na tambaye su ledan na menene wai zasu kai gida. Basu gama dinner ba sai kusan 11:40 na dare. Kamar yadda suka zo haka suka koma a cikin mota. Eesha da Faruq da suke baya sai magana kasa kasa suke suna dariya. Issam kuma minti minti yakan juyawa ya kalle ta. Idan sun had'a ido sai tace "What??? Banson kallo dayawa, inaga kaf zuri'an ku babu iri nah koh?" Murmushi yayi yace "Gaskia kam babu irin ki, a zuriyan mu banga meh irin your complexion ba, blacky!! Yuck!" Tareda girgiza kansa Ranta idan yayi dubu ya b'aci wai ita blacky, ba sau d'aya ba million times mutaneh sukan ce skin colour nata yana da kyau, ita ba bak'a ba kuma ba fara ba, za d'an iya ce mata tanada haske sosai and many times mutaneh kance tana kama da Christiana Milan "Ya kamata kaje doctor ya duba ka cause ni ba blacky bace , and kuma meh acikin bak'in fata? Afterall bak'in fata tsada neh dashi unlike fari wanda shi a kasuwa anybody can buy it" Murmushi yayi bai k'ara magana ba har yayi dropping nasu a gida. By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {July,2017 } *Godiya na musamman to all members of Pure Moment Of Life Writers. I ❤ y'all... #oneluv* ```Page 20``` Umma ce zaune a d'aki itada Aliyu, ranta duk a b'ace tace "Haba Aliyu ka kyauta kenan? Dududu yaushe auren ka da Meena har zaka mata kishiya, Haba Meena fa 'yar uwarka ce ta jini, sanin kanka neh mu biyu iyayen mu suka haifa, nida Uwani" "Umma Fido ma ai 'yar uwa tace, d'aya suke a waje nah" "Wlhy sam ba d'aya ba, akwai mugaye irin dangin uba neh. Ai a duniyan nan 'yan uba da dangin uba sune enemies naka first!" "Hmmm Umma kenan, kiyi hakuri sabida ina kaunar Fido sosai, fiye da tunanin ki, more than anything" "Ohhh tun ba'aje koh inaba har sunkai sunan ka wajen boka, har ta mallake ka" "Umma ki daina fad'an haka, ni ba abunda Fido ta mini, as you can see d'azu kawai umarni tabi ba wai dan tanaso ba" "Shikenan! Nidai zanta maka addu'a har ranar da zaka dawo cikin haiyacin ka. Wannan masifan da me yayi kama Ya Allah" "Yawwa Umma addu'an ki nake bukata, nagode" "Allah maka albark d'ana, Allah rabaka da kuma wannan bala'in" "Umma ni na wuce". " ka gaida gida, and kuma da daddare kazo mini da Meena akwai maganan da zamuyi da ita" "Toh shikenan ba matsala" Fido tana shiga d'aki ta kwanta akan gado ta fashe da wani irin kuka meh tsuma duk wani zuciyan mei sauraro. Mum ce tashigo d'akin ta shafa kanta tace "Fido you always told me that Aliyu neh first love na ki, shin mesa baki farin ciki da faruwan haka ba?" "Mum I wish, I wish that inason shi har yanxu da yanxu ina farin cikin TAWA TA SAMENI. But Mum, a yanxu I ain't feeling anything for him, a yanxu ina jinsa kawai a matsayin brother and nothing else" "Fiddausi kina son S.A sosai?" "Mum inason S.A, inason shi sosai Mum. I can't hide my feelings for him but ya zanyi Mum? Iyayen sa basu son auren mu tare" ta fashe da kuka. Mum ta rungume tace "Kita addu'a Allah sa shine mafi alkhairi, Aliyu is the perfect match for you gurl In Shaa Allah" Murmushi Fido tayi tace "Kai Mum, Allah sa toh" "Ameen" tareda rungumo 'yar nata sosai.. .... ********** "Wlhy Allah baka isa ba, tun ba yau ba nasan takeken ka, wato duk iskancin da kuka gama yi a UK bai ishe ku ba yanxu ku dawo kuce aure zakuyi, Wlhy Allah bazan yarda ba" cewar Meena wanda ta gama cika tayi fam. Aliyu ransa yayi mugun b'aci, duk da yadda yabita a sannu a lallashe amma take gaya masa bak'ar magana(nidai nace Aliyu baisan kishin mu na mata ba) ransa a b'ace yace "Ba yardan ki nake nema ba ai, sabida haka da ki yarda da karki yarda duk uwar uban su d'aya" "Hmmm, lalle Aliyu!!! Uwata ta zauna ba kishiya dan haka nima wlhy bazan zauna da kishiya ba wlhy. Idan har ka kuskura ka kawo Fido cikin gidan nan it will be the greatest mistake da kayi a rayuwar ka. I swear, I sweaerit!! Dan wlhy sai kayi dana sani" "Kar kiyi kuskuren aikata wani abu Meena, dan wlhy Allah idan har naga kin aikata wani abunda bashi ba toh ki sani a ranar zaki tattara kayan ki kibar mini gida nah. Ai tun farko ni bance ina sonki ba, ke kika ganni kika lik'e mini, kika ce sam ni kike so ni zaki aura(hmm readers maza kenan). Zubewa Meena tayi a kasa ta d'aura hannu a ka, yau Aliyu ya mata rashin mutunci akan Fido. Wani irin kuka ta fashe dashi tace "Abban Basma gori kake mini?" Aliyu jikin shi yayi sanyi yace "I am sorry" Tana goge hawayen ta tace "Ba komai, ka kaini wajen Umma kace tana son gani nah ai koh?" Zuwa yayi daf kusa da ita ya kama hannun ta yace "Kiyi hakuri dan Allah, nasan ban kyauta ba but you pushed me! Ina sonki Meena plus inason Fido. Hakuri zakiyi bazan iya rayuwa ba Fiddausi ba, She's My HAYAT!!!" Meena ji take kamar ta had'iye zuciyanta ta mutu, tunda take a rayuwa bata tab'a jin bak'in ciki irin na yau ba. Murmushi tayi amma Allah kad'ai yasan what's on her mind tace "Ka kaini kar dare yayi" "Thanks alot Swthrt!" Tareda hugging nata "Muje" S.A tunda yaji labarin auren Fiddausi da Aliyu yabi ya birkice, a kullum yana hanyan zuwa gidan su shi sam a fasa auren tunda Fido ba son Aliyu take ba. Shi koh iyayen sa basu amince ba a musu auren haka tunda yanada kud'in sa and he doesn't need help from anyone. Kamar kullum Fido ta shirya zata gidan su Eesha kawai taga S.A a gaban ta. Zuwa daf yayi kusa da ita yace "Beauty dan Allah karki yadda su rabani da ke kinji. Please dan Allah beauty zuciya na zata iya bugawa idan baki aure ni ba, ki taimaka mini dan Allah beauty, kece Rayuwa ta!" Hawaye neh daf suka cika a idon ta, da sauri ta shiga motarta tabasa wuta. Duk da yayi kokarin shiga gaban ta amma hakan baisa ta gauje tabar haraban gidan ba. Gudu take sosai akan titi, waje ta samu tayi parking motarta ta rushe da kuka. Can taji message ya shigo mata waya take ta d'au wayarta tana goge hawayen da yake sauka kan kuncin ta. Bud'e message d'in tayi tafara reading: _I've been thinking about you a lot Hayaateey!_ Wani irin fashewa da kuka tayi tace "Ya Allah you know what's best for me" *Bayan Sati Uku* Tun daga lokacin Fido bata k'ara yin ido hud'u da Aliyu ba. Tana jin muryan sa take b'uya, shima dai banza yayi da ita dan duk gudun ta in some few days zata shigo hannun sa. Shirye shiryen biki suke ba kama hannun yaro dan saura sati d'aya ayi biki. A yau neh dinner Eesha gobe d'aurin auren ta. Duk wani gyaran jiki tare sukeyi dukda ma Fido bata so amma Eesha takan sata dole. Eesha ce kwance a kan gado Fido kuma a kan tiles, Eesha tace "Fido ki hau kan gado mana" "Ke barni tiles sanyi neh dashi" "Hmm kedai dason sanyi sai kace a Russia aka haife ki" Fido tayi dariya tace "Ai wlhy wataran sai naje Moscow nan naji" "Umm yawwa Fido please ki cigaba da gyaran jikin nan sabida nasan halin ki" "Mtswww kedai barni dan Allah, gyaran jiki ma uban waye zanyi, mijin da baya raina" "Don't tell me you still have feelings for S.A?" "Mtswww, ke ni na manta da S.A ma, yana ta kirana lokacin akan karna yarda aure nah da Yaya Aliyu zaiyi convincing parents nashi, kawai na canza sim na" "Toh koh ISSAAM kike so?" Atake Fido ta tashi ta zauna tace "Yazo?" "Tun ana one week to aure" Tusa hannun ta tayi cikin dogon gashinta ta furta a hankali "Ya Salaam!" "Lafiya Fido?" Anty Halima ce tashigo cikin d'akin tace "Kufa 'yan air neh, maza ku tashi kuyi wanka ku shirya. Event d'in fa 8:00pm neh yanxu 6:50 koh wanka bakuyi ba kun tsaya kuna hiran ku da baya karewa gashi make up artist ku take jira tun d'azu" A sanyaye duk suka tashi suna "washhh wlhy Anty Halima mun gaji baza ki ganeh ba" Tsaki taja tace "Banso ma na ganeh maza ku tashi kuyi wanka" _Bayan awa d'aya_ Eesha tasha doguwar riga gown golden colour, da doguwar designer heel nata da jakan ta k'arami wanda ya dace da shigan ta, fuskan nan yasha make-up tayi kyau Mashaa Allah. Gefen ta kuma Fido ce wanda tasha ubansu material maroon colour mei kyaun gaske, sai head na kanta, high heel na kafanta, pouse na hannun ta duk black daman black is her favourite. Tasha su bangles masu kyaun gaske da necklace nata shima had'ad'd'e. Fuskan nan tasha kwalliya wanda yayi mata kyau sosai, tsaya baku labarin irin kyaun da tayi b'ata time neh. Anty Halima tace "Mu tafi koh suna ta jiran ku tun d'azu" "Eh muje" cewar Eesha Har bakin kofan motan Anty Halima ta rakasu, ta bud'e wa Eesha bayan motan wanda already Faruq shima yana baya, bayan Eesha tashiga sai ta rufe ta bud'e kofan gaba tace "Fido bismillah ki shiga". A hankali Fido ta d'aga kanta dan ganin wanda zaiyi driving nasu. Ido hud'u sukayi ISSAM By Nana Fa'ad *HAYAATEEY* Pure Moment Of Life Writers (p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] {July,2017} _In dedication to Fido Sodangi_ ```Page 22``` *Dedicated this page to Real Amani.😘* D'aki direct suka wuce bayan su Issam sunyi dropping nasu. Eesha kwanciya tayi flat akan gado Fido kuma tana kokarin cire kayan jikin ta, har yanxu incidence na d'azu itada Issam yake yawo a brain nata. Bayan ta cire kayan jikinta ta d'aura towel tace "Eesha d'azu idan badan Issam ya taimaka mini ba da nasha kunya, ai wlhy idan na zube kasa bani ba dinner nan gida kawai zan dawo". Eesha tayi dariya tace "Mutumin ki ai yayi saving naki yakamata ki kirasa ki masa godiya" Zaro eyes nata tayi tace "Wa! Ni? Allah sawwaka nakirasa" Eesha ta tashi daga kwancen da take tace "Yawwa ni Fido d'azu da zamu shiga cikin hotel d'in naga yana miki magana a kunne meh yake fad'a miki and kuma tunda kika shiga cikin motar yana ta kallon ki" Dogon tsaki Fido taja tace "THAT SON OF A GUN! He shamelessly stared at me tun shigowa ta motan! And then he had the audacity to wink at me! HE WINKED AT ME! How dare he? And you know what, kinsan maganan da yazo kusa dani yake fad'a mini? Wai I had too much contour on and that I shouldn't cover up my inner beauty!!!! Ina ruwan shi dani da make-up d'ina. He's very stupid" Eesha tayi dariya kamar cikin ta zai fashe tace "Kedai da mutumin ki" "Wlhy idan kika k'ara fad'an haka zamu b'ata. Mene kin baje a kan gado dallah tashi kiyi wanka" "Idan naki fa?" "Na fad'a wa Faruq K'azamiyar amarya ce ke" "Kut!!! Ai Wlhy dana tsane ki". "Akan Faruq zaki tsane ni? "Sosai ma kuwa" "Good nagode, kin nuna mini Faruq yafini" "Banza ina ma zaki had'a, mtsww ki shiga wankan idan kin gama nashiga bacci nake ji" "Hmmm" kawai Fido tace tashiga bathroom. _Washegari_ Da misalin karfe tara na safe aka d'aura auren Faruq da Eesha. Tunda gari ya waye Fido bata samu zama ba sabida itace best friend kuma tana make suring duk k'awayen su sun samu abinci da take away. Ita bata samu zama ba sai kusan karfe bakwai na dare. A kan gado tazo ta kauna tace "Wayyo Anty Halima wlhy Allah nagaji" Anty Halima tayi dariya tace "Ai dole ki gaji kina zaman best friend" "Wai ni ina amaryan neh kum what time za'a kaita gidan ta?" "Yanxu tashiga wajen Abba already ma abokan ango sunzo tafiya da amaryan" A take Fido ta taso daga kwancen da take tace "Dan Allah? Bara nayi wanka sharp sharp" "Gwara kam, Yawwa Fido ga wayar ki tun d'azu ake kiran ki fa" Karb'an wayan Fido tayi tareda mata godiya. 50 missed calls ta gani da kuma 6 messages. Wajen messages ta shiga taga Yaya Aliyu, S.A da kuma number da yake tura mata text kusan kullum. Number ta fara bud'e wa taga: _Hayaateey!!!!! You are so beautiful, sometimes I just can't take my eyes off your pictures. And you know what? You looked gorgeous yesterday night_ A k'asan still message na number neh: _How do i love you? i really cannot tell, for it is a pain like no known ache, a pain with which i would not part, for i treasure HAYAAT and life is my QALB, and my QALB is yhu!_ Murmushi tayi bayan ta gama reading text message d'in tace "lalle baka da aiki" Bud'e text messages na S.A tayi wanda duk akan tayi hakuri tasa afasa auren ayi dashi, Wanda har messages uku duk nasa. Guda d'aya message na Yaya Aliyu neh, zuciyan ta neh ya buga bayan ta gama reading message d'in. A hankali take k'ara karantawa: _Ashe haka kike bakida kamun kai? A cikin jama'a wani yake rik'e ki ba kunya ba tsoron Allah. Wannan ba dinner kukayi ba sunan shi Talla. And be ready zanzo na d'auke ki_ A hankali ta furta "Wayyoo Allah nah". Wayar tane yafara ringing, da sauri ta duba dan ganin wanda yake kira, Yaya Aliyu tagani baro baro kan screen. D'aga wa tayi, tun kan tayi magana yace "Inata kiranki ina kika shiga baki d'aga wayata ba ehh?" "Wlhy bana kusa neh" "Mtswww, kinban kunya Fido. Pictures naki kaca kaca nake gani a social media keda wani ya rik'e ki kuna kallon juna, shi d'in uban waye neh, bai san auren ki saura kwanaki baneh, Afterall kece jahilan da kika barsa" A take ta katse wayan hawaye yana sauka akan kuncin ta. Mutaneh kenan duk abunda yake faruwa sai sun d'au hoton sun buga a social media kai Allah sawwaka. Jiki a sanyaye tashiga bathroom tayi wanka, koh lipstick bata shafa ba bare powder. Dogon riga Swiss lace ta saka wanda ya amshe jikin ta sosai tayi spreading perfumes a jikin ta. Anty Halima ce tashigo d'akin tace "Fido duk friends na amarya fa an kaisu yanxu keda amarya ake jira hope kin shirya" A hankali tace "Eh muje" ta d'auko gyalen ta tayafa Eesha da babarta ta neh a bayan mota sai gaban kuma Fido da Issam shi yake driving. A hankali ya d'an kawo kansa kusa da ita yace "You look beautiful without make-up, Thank Allah yau bakiyi contouring fuskan ki ba. Gosh! yesterday you looked like a masquerade dana ganki har zan gudu na d'auka aljana ce" Fido juyawa tayi dan ta gasa masa d'acin magana to her very own surprise kuma fuskan sa a d'aure yayi squeezing yana driving kamar bashi yayi maganar ba. Dogon tsaki taja tace "Mahaukaci" a hankali. Bayan sun kaita gidan ta, abokan ango sukace baso son kowa ya kwana a gidan. Fido tace "Kaii Eesha haka Faruq yake jarababbe" "Dan Allah Fido ke ki masa magana ki kwana gobe sai ki tafi" "Tab lalle yadda ake koran mun nan ai dole na tafi, and kuma Yaya Aliyu yace yana hanya bara na fita na tsaya a bakin gate dan baisan gidan ba" Da kyar Eesha tabar Fido ta tafi. A bakin gate tana jiran Aliyu Issam yayi parking a gaban ta. D'aga kanta tayi kamar bata gansa ba. Sauka yayi a cikin motar yace "Shigo na kaiki gida Mss Contour" "Mtswww kaga nayi kama da kalar wacce zaka kaita gida neh" "Ke kin fiye tsaki sai kace 'yar tasha" A ranta taji maganar wai 'yar tasha. A zuciyan ta tace yau kuwa zan nuna maka ni 'yar tasha ce. Coke na hannunta ta bud'e ta watsa masa a farar shaddan sa tareda tufa masa miyau na bakin ta tace "Yau na nuna maka ni cikekkiyar 'yar tasha ce" Murmushi yayi tareda d'aukan ta cak ya bud'e bayan mota ya wurga ta aciki da sauri ya zagaya ya shiga gaba yayi locking doors d'in tareda ba motar wuta..... By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] In Dedication To Fido Sodangi {July,2016} *Gaisuwa na musamman Yaya Faty K. Batagarawa And Ayshah K. Batagarawa*. ILYSM😘 ```Page 23``` K'okarin bud'e motan take amma ina ya riga ya danna masa lock. Ihu tafara yi tana cewa "Wayyoo Allah ku ceceni Issam yayi kidnapping d'ina." Murmushi yayi yace "Wow! Ashe fa kinsan suna nah". A tsawace tace "Ka bud'e motar nan koh na shak'e ka ta baya dukkanmu mu mutu" A take yajuya yana kallon ta yace "Don't even dare! I am warning you! Maza ki saka seat belt kinga ni already da seat belt" Ina Fido ko kulasa batayi ba ta cire gyalenta ta kama masa wuya ta baya, kan yasani yaje ya buga wani kanti. Buga kanta tayi a jikin motar, shi Allah neh ya soshi baiji ciwo ba dan yasaka seat belt. Juya baya yayi da sauri yaga Fido kwance bata motsi. "Fido! Fido please ki tashi" Amma inaaa koh motsi batayi. Da sauri ya d'au wayar sa yayi dialling number "Hello Dr Naeemah please kina ina? Dan Allah kizo ina neman taimakon gaggawa" ya katse wayan. Zuciyan shi neh yake bugawa ya rasa mei yake masa dad'i. Can bayan minti ashirin sai ga wata wanda ak'alla bazata haura shekaru ashirin da takwas ba tafito a mota. Da sauri Issam yazo kusa da ita yace "Please help me Naeemah" Murmushi Naeemah tayi tace "Ba komai ka sakata a mota" Istigfari Issam yayi tareda d'aga ta cak ya sakata cikin motar Naeemah Bayan sun shiga cikin motar Dr Naeemah tace "Hospital koh gidan ka?" "No gida nah" "Wacece haka Issam?" "Sister nah! And please don't ask me any more questions" "Ohk fine! Ina gidan ka yake?" Kwatance ya mata har zuwa gidan sa, bayan tayi parking a parking lot ya d'auke ta cak tareda furta "Astagfirullah" har zuwa cikin wani d'aki meh kyaun gaske. Da ganin d'akin na macece dan komai na d'akin tun daga bedsheet,curtains, kujeru duk purple and black neh. A kan gado ya dirata, yace "Dr please duba ta" Bayan Dr Naeemah tayi gwaje gwajen ta tace "Ka kwantar da hankalin ka ba wani abu baneh suma kawai tayi dan ta firgita sosai kuma ta d'an buge kanta" "Yanxu what's the solution?" "Zan mata allura tareda bata magani but sai kaje ka siyo dan ba yawo nake da su ba" A birkice yace "Ba wani abu ki rubuta mun naje na siyo yanxu" "Ohk toh" Takarda ta ciro da biro a jakarta ta rubuta masa magani da alluran da zai siyo. A take ya karb'a ya fice a gidan. Cikin minti goma sha biyar sai gashi da ledan maganin. Murmushi Naeemah tayi tace "Gaskia kana ji da kanwar mu" Murmushi yayi yace "Ai dole nah" Fita yayi a d'akin a lokacin da zata mata allura. Bayan ta gama ta kira shi ta masa bayanin idan ta tashi ga maganin da zai bata. Yace "Words ain't enough to thank you Naeemah" Murmushi tayi tace "I can do anything for you" Bayan ta tafi kujera ya d'auka ya zauna yana kallon ta har bacci ya d'auke sa. Bud'e idon ta take a hankali, bin d'akin take da kallo cike da mamaki. Ganin mutum zaune a kan kujera yana bacci wanda gashin kansa bai bari ta kalla fuskan meh kyau ba dan ya d'an rufe masa ido hanci da baki kawai ake hangowa. A razaneh tayi wani irin ihu. Issam atake ya tashi yazo daf kusa da ita yace "Fido lafiya?" A hankali incidence d'in ya dawo mata, a tsawace tace "Where the hell is this place?" "Don't shout Fido, bakida lafia. Easy gurl calm down" "WTF! Bansan inda nake ba and kana ce I should calm down???? Anki ayi calm down d'in" ta fad'a a tsawace. Fita yayi a cikin d'akin, bayan minti biyar ya shigo da tray. Zuwa yayi kusa da ita yace "Kici abinci kisha magani gobe da safe In Shaa Allah sai na kaiki gida" "Allah wlhy bazan ci ba" kokarin tashi take amma ta kasa, da kyar dai ta iya ta tashi tacigaba "Wlhy Allah bazan ci ba, Allah ya isa tsakani nah da kai kuma wlhy yanxu zan tafi gida" "Kiyi hakuri kici please" ya ajiye mata tray d'in a stool na gaban gadon. Wulli da tray d'in tayi sai gashi su Tea da potatoes duk sun zube plate da cups duk sun fashe. A tsawace tace "Wlhy Allah yanxu zan bar gidan nan kuma baka isa ka hanani ba kayi kad'an" Shuru yayi yana kallon ta, da kyar ta iya ta tashi akan gadon, a hankali take iya takawa duk da ciwon kan dake addaban ta, Issam yace "Haba Fido please kibari sai gobe as you can see ana lightening akwai hadari sosai" "Ba hadari wlhy koh ruwa ake sai na bar gidan nan" "Toh ni kuma bazan bud'e miki kofa ba kingani nan" tareda nuna mata keys "Ga keys na gidan nan a hannu na sai naga ta yadda zaki fita" Kuka take sosai tana ihu amma duk da haka yaki ya kulata, sai can koh mei ta tuna tace "But gobe da sassafe zaka kaini gida koh?" "Eh In Shaa Allah gobe da sassafe bayan kin wanke mini kayan da kika b'ata" "Zan wanke, yanxu bacci nake ji" "Yawwa toh kwanta" Kan gadon ta koma ta hau ta kwanta, tace "Kai baza kayi bacci baneh koh zaka sakani a gaba kana kallo na neh?" "Ohk bara naje d'aki na na kwanta, good night" Murmushi ta masa tace "Night" Fita yayi a d'akin yana murmushi a zuciyan shi yana cewa "Lalle wai yarinyan nan wayo zata mun" Kujera ya d'auko ya ajiye a gefen kofan d'akin ya zauna yana gadin ta. Ita kuma Fido ta rantse da Allah a daren nan zata bar gidan. Tana jin motsin sa a kofan d'akin wanda ya tabbatar mata Issam bai shiga d'akin sa ba. Sai can kamar karfe d'aya bayan taji shuru ta tashi a hankali, a wajen kofan d'akin taga Issam yana bacci akan kujera, hannu ta saka a cikin aljihun rigan sa ta d'auki key holder. A sanda ta fita a gidan har takai bakin gate, wani tsoro taji dan garin ana wani irin iska tareda lightening hadari ya had'u sosai. Duk keys d'in take gwada wa har Allah yasa ta bud'e. Tana fita ruwa mei karfin gaske yafara saukowa. Wani sound na thunder akayi da karfi wanda ya tsorata ta, sound na thunder shi ya tada Issam daga baccin da yake, a take yashiga cikin d'akin to his very own surprise yaga wayam ba kowa a ciki. Fido gudu sosai take cikin ruwan, ga wani uban tsoron da takeji, wani irin haske tagani kan ta ankara taji an buge ta, Issam dake baya yayi Ihu yace "HAYAATEEY" Kan ya iso wajen motar daya bugeta yayi ribas da gudu yabar wajen.. Issam a guje yazo wajen yana jijjigata, dukda karfin ruwan da yake sauka bai hana ganin jinin da yake fitowa a goshin taba, Hawaye yake kamar ba Issam namiji mei ji da kansa ba yana cewa "Hayaateey dan Allah ki tashi kece RAYUWA TA, dake nake kwana dake nake tashi. Believe me, you are the one,Whom my heart finds,Whom my mind reminds me of,Whom my destiny wants,Whom I love the most! KECE MY HAYAT!!!Dan Allah ki tashi" Ganin bata koh numfashi ya d'auke ta cak ya kaita gidan sa ya kwantar da ita a kan gado. Gashi da mota d'aya yazo dashi Katsina kuma motar d'azu sunyi accident dashi. Saka hannun sa yayi cikin dogon gashin kansa ya furta "Ya Salaam". Nan take kuma ya tashi ya d'au First aid box yafara mata treating inda ta buga goshinta. Take yayi traating ya manna mata bandage. D'aukan wayar sa yayi yayi dialing number Dr Naeemah ya ji number a kashe. Duba time yayi yaga karfe ukun dare. D'auko kujera yayi ya zauna yana kallon ta koh Allah zaisa ta tashi a haka har karfe biyar yayi bai runtsa ba. Ganin ana kiran Sallah a take ya k'ara dialing number Dr Naeemah Allah yasa yashiga. Ringing d'aya ta d'auka tace "Issam lafia kuwa?" Muryan sa yana shaking yace "Naeemah ba lafia ba, jiya da daddare ta fita mota ya bugeta and she lost alot of blood, nayi treating nata gashi har yanxu bata farka ba" "Ohk ka jirani yanxu zanzo" "Ohk sai kinzo nagode sosai" "No thanks anything for you dear" "Ohk" yace kawai tareda katse wayan... Nan da minti goma sha biyar sai gashi Naeemah tashigo idan, data shigo a lokacin ya idar da sallah subh. Bayan sun gaisa ta d'auka jinin Fido tace "Zanje Lab nayi PCV ta, idan har jinin ta low sai mu gwada naka a saka mata but for now zan saka mata drip" "Ohk toh ba matsala" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] In Dedication To Fido Sodangi {July,2016} ```Page 24``` Aliyu a daren yaje yata kiran number ta baya shiga, daga baya yayi deciding ya buga musu kofa. Bayan ya buga kofa Faruq ya bud'e mishi kofan, bayan sun gaisa Aliyu yace "Ummm sunana Aliyu, brother Fido" "Ohh Allah sarki, ya gida?" "Alhamdulillah lafiya kalau, Fido nake nema kuma I tried calling her but her number was switch off kuma munyi da ita akan zanzo na d'auke ta" "Ohhh ayyah kasan daman ba wanda zai kwana a gidan and d'azu naji kamar Eesha tana cewa zaka zo ka d'auke ta. Lemme talk to her" "Ohk Nagode" Faruq ya shiga ciki sai kusan bayan minti biyu ya fito tareda Eesha, Eesha tana ganin sa tayi murmushi tace "Ango kasha k'amshi, baka had'u da amaryar kaba?" Aliyu ya d'an sosa kansa yace "Wallahi kuma munyi zanzo na d'auke ta" "Kuma wallahi haka ta fad'a mini har tace bara ta fita da wuri dan bakasan actual gidan nan ba, ka kirata?" "Yeah na kirata but her number a kashe" "Ya Salaam! Ohk give me some seconds let me call my sis koh ta koma gidan mu, mushiga daga ciki" "Aiit nagode" Bayan sun shiga ciki suka zauna a parlour. Shiga d'aki tayi ta d'au wayarta tafito parlor, number Anty Halima tayi dialing, bayan ya shiga ta saka a loudspeaker "Hello amarya lafiya kuwa?" "Anty Halima ina Fido? Tana gida neh?" "A'a Fido fa bata nan, tace mun Yayan ta zaizo ya d'auke ta a gidan ki, mesa kika tambaya?" "Wlhy Yayan tane yazo kuma batanan and number ta akashe" "Ikon Allah, toh ina tashiga? Allah sa lafiya" "Ameen Anty Halima" "Ki kira wasu koh Allah zaisa kiji labari" "Ohk toh nagode, bye" ta katse wayan. Eesha ta kalla Aliyu tace "Kaji bata wajen, but bara nakira Anty Rif" A take tayi dialing number Anty Rif itama yayar Eesha ce, tana d'aga wa tace "Amarya lafiya kika kirani hope baki manta komai a gida ba?" "Lafiya kalau wallahi, amm daman Fido nakeson na tambaye ki koh kin ganta da zaki bar gida nah" "Ohh Fido, da zan wuce na ganta tsaye da Issam abokin Faruq. Har naji yana maganan zai kaita gida" "Ohk toh Nagode" ta katse wayan. Zuciyan Aliyu neh yake bugawa, tabbas ya ganeh Issam dan da akayi posting pictures nasu a Facebook yaga an saka sunan sa. Take yace ki kiramun number Issam d'in. Take Eesha tayi dailing amma shima switch off. Tace "Yaya Aliyu number sa akashe, inaga ya kaita gida neh. Tabbas ba inda Fido zata wuce gida ya kaita" Faruq yace "I trust my friend ba inda zai kaita sai gida, kaje gida In Shaa Allah tana gida" Aliyu duk yadda yaso ya b'oye b'acin ransa amma sanda suka gane. Yayi murmushin dole yace "Ba komai nagode" Tafiya yake a cikin motar sa amma zuciyan sa yana me bugawa, tsananin kishi ya rufe masa Ido, buga siterin motan yayi yace "Auren mu saura one week amma tana kula wani, wallahi Allah sai ta ganeh kurenta" A haka har ya isa gida, yana shiga cikin gidan wani irin parking yayi ya fito a motar da sauri, direct b'angaren Inna ya wuce. Yana shiga ya ganta da Shamcy suna kallo a parlour. Inna tace "Aliyu lafiyan ka kuwa? Har yanxu baka wuce gidan ka ba?" Bai bata amsa ba yace "Inna ina Fido?" "Kaji ja'irin yaro, toh Fido bata gidan nan gidan auren k'awarta zata kwana" "Inna kina nufin Fido bata dawo gidan nan ba?" "Toh karya zan maka neh?" "Kee Shamcy ina Yayar ki?" "Yaya Aliyu bata dawo gida bafa, ka manta yau ana auren k'awar ta Eesha? Sai gobe zata dawo" "Bata dawo gida bafa kukace?" Inna ta harare sa tace "Ka fara zautuwa neh? Sau nawa zamu fad'a maka bata gidan nan tana gidan aure" "Inna bata wajen auren dan daga can nake, ance wai an ganta tareda wani" "Kaga Aliyu bana son shirme, toh Fiddausi d'in binshi zatayi gidan sa sabida an gansu tare? Maza ka tashi ka tafi gidan ka dare yayi" "Inna baki yadda dani ba kenan?" "Ban yadda ba, kuma idan ka k'ara cewa Fido ta fita da wani toh ban yafe ba duniya da lahira, kai Allah ya isa ma" Tsantsan mamaki neh ya cika Aliyu, yace "Shikenan Inna sai da safe" Tura d'ankwalin ta gaban goshi tayi ta nuna masa kofa tace "Otttt" Fita yayi yana mamakin Inna, yana fita Shamcy ta kwashe da dariya tace Inna "Out ake fad'a ba Ottt ba" "Ke barni duk d'aya ai nayi k'okari d'an rainin hankali kawai" ******************* Dr Naeemah tayi PCV Fido taga is very low, tayi screening jinin Issam Allah yaso yazo daidai. Take Issam ya bada jinin sa aka saka mata Yace "Yanxu Naeemah yaushe jinin zai k'are?" Duba agogon hannun ta tayi tace "Amm yanxu 7:00am In Shaa Allah zuwa 6:00pm zai k'are da ruwa da jinin gaba d'aya or even before then" "Ohk nagode sosai" "Anything for you dear" Da sassafe kamar karfe shida da rabi Aliyu yadawo gidan, direct side na Inna yashiga, a lokacin Inna tana zaune akan sallaya. Bayan sun gaisa yace "Inna Fido ta dawo gida kuwa?" "Kai yaron nan da takura kake yaushe gari ya waye da Fido zata dawo, sai da yamma zata dawo gida dan haka mukayi da ita lokacin da zata bikin" "Inna kina nufi har yanxu bata dawo ba?" Dunkule ta masa tace "Kaci gidan ku, toh karya zan maka neh? Maza tashi kabar mini gida" Tasowa yayi yace "Inna ya miki kyau, koma wallahi zan baku mamaki" "Kaji dashi ja'irin yaro kawai". Tunani yake koh zai fad'awa Abba neh, wani zuciyan yace no karka fad'a. "Or should I call Eesha?" "No bazan k'irata ba kar su d'auka na damu da ita" duk shi kad'ai yake maganan zuci, sai can yace "zanga gudun ruwan ta, idan har yau bata kwana a gida ba zan sanar da Abba". At the end yayi deciding ya kira Eesha, bayan sun gaisa yace " Eesha har yanxu fa Fido bata dawo gida ba, bakuyi magana da Issam ba?" "Umm munyi magana da ita ashe tana gidan Anty Halima basu had'u baneh lokacin da muka kira but anjima da yamma zata dawo gida In Shaa Allah" "Ohk Nagode". Ya katse wayan, har cikin zuciyan sa bai yadda da abunda Eesha ta fad'a masa ba. 8:00pm A hankali take bud'e idon ta, ganin kanta tayi a sabon waje, gefe guda kuma Issam neh zaune kan kujera yana bacci, a sannu memories abunda yafaru da ita jiya da daddare yadawo brain nata. A hankali ta furta "Issam, Issam" Kamar wanda yake jira takira sunan sa nan take ya farka, ganin tana kallon sa take yazo daf kusa da ita yace "Ya jikin ki? ina yake miki ciwo? kina jin yunwa?" "Gida zan tafi please" "Ohk let me call the Dr tazo ta duba ki" D'aga masa kai tayi da sauri yafita yabar d'akin, cikin seconds talatin yazo da Dr Naeemah, murmushi Dr Naeemah tamata tace "Sis yajiki?" "Da sauki, please gida nakeson natafi" "Ohk karki damu zakije gida kinji, dan tun around karfe uku jinin da muka saka miki yak'are hope ba inda yake miki ciwo?" "Babu" Bayan Dr Naeemah tagama dubata ta bata tea me kauri da Potatoes, ba karamin ci Fido tayi ba dan tana jin yunwa sosai. Daga nan tace "Bawai dan kinji karfin jikin ki baneh zan rubuta miki sallama sabida naga you insisted" "Nagode" Bayan an basu sallama Naeemah ta taimaka mata tashiga cikin mota. Har kofan gida Issam yayi dropping nata, tana mamakin yadda akayi yasan gidan su. Bud'e bakin sa yace "Eesha ce ta tura mini address na gidan ku so don't be surprise" A daidai lokacin Aliyu yasha corner layin gidan yaga mota a bakin gate, parking motar sa yayi zuciyan sa yana bugawa, addu'a yake Allah sa ba Fidon sa bace tareda wani gardi. Ganin Issam yayi yafita a motar ya bud'e kofa, to his surprise yaga Fido tafito a motar. Innalillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un shineh abunda yake maimata wa. "Fido bara na rakaki cikin gida na musu bayani" "Ka barshi ba komai but karkayi tunanin na barka abunda kamun, wallahi Allah bazan barka ba kuma bazan yafe ba" Murmushi Issam yayi yace "Get well soon Baby" "Don't call me Baby" ta had'a rai. Issam yace "Toh wani suna zan kiraki?" Shuru tayi bata basa amsa ba, yacigaba "But if akwai matsala call me zanzo na musu bayani" ya mik'a mata compliment card nasa, karb'a tayi tace "Good da kabani number ka" "Bye" "I hate you Issam" Murmushi yayi yace "And I Issam, I.....". Bai k'arasa ba aka bud'e gate d'in. Shamcy ce tafito da gudu tayi hugging na Yayar ta. Issam kuma yashiga cikin motar sa yayi basa wuta. Duk wannan abun a idon Aliyu Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] In Dedication To Fido Sodangi {July,2016} ```Page 25``` Shamcy ta taimaka mata tayi har suka shiga ciki, bayan sun zauna Inna tafito a d'akin ta tace "Fiddausi naji wai kinyi hatsari, Allah kiyaye gaba" "Ameen" Fido ta bata amsa a takaice. Inna tace "Ya hakan ta faru neh?" "Kinga Inna I'm so damn tired kibarni please" "Shamcy me tace wai?" Shamcy tayi dariya tace "Cewa tayi tagaji dan Allah kibarta ta huta" "Ohhh ayyah, shegen Aliyun nan yazo mini da maganan banza wai an ganki da wani kin bisa gidan sa" Nan take zuciyan ta ya tsinke, tace "Inna haka Yaya Aliyu ya fad'a?" "Kibar ja'irin yaro ai na wanke shi tas da soso da sabulu" Fido hankalin ta yayi mugun tashi, take ta tashi tashiga d'akin ta tace "Inna bara nayi wanka nayi sallah" "Toh 'yar albarka, kiyi baccin ki kawai ba sai kin k'ara fitowa ba kinsha hidiman biki ai" Tana shiga d'aki ta zube kan gado tace "Ya Salaam Yaya Aliyu kar yamun mummunar fassara". Hawaye neh taf cike a idon ta, zuciyan ta yana tsinkewa ta rasa abunda yake mata dad'i. Shamcy tana shiga d'akin tace "Adda Fido wannan guy da kukazo tare ai shineh bestfriend na Faruq a wajen auren koh?" Nan take Fido ta goge kwallan idon ta tace "Eh shine, wani abu neh?" "No just that he's so damn beautiful, ba handsome ba. Any gurl will love to have him" "Are you crazy! bakya jin kunya na koh?" "Toh ai na girma kina magana kamar ni yarinya k'arama" "Just shut up, ni banga ma wani kyaun shi ba mutum kamar aljani" "Kai Adda Fido" Tsaki taja tace "Dan Allah kibarni naji da abunda yake damu nah please bana son surutu" "Ohk bara na kawo miki abincin ki kan ki fito a wanka" "Better" ta amsa mata a takaice. _Bayan kwana shida_ Ranar asabar da misalin karfe goma na safe aka d'aura auren General Aliyu Sanusi Sodangi da Fiddausi Muhammad Sodangi a sadaki dubu d'ari. Anyi shagalin biki sosai ango yasha manyan kaya farare kal masu uban kyau. Wajen amarya kuma in banda kuka ba abunda take. Rabuwan ta da Aliyu har ta manta tun kan auren Eesha, bai kuma kirata a waya koh ya neme taba tunda tadawo gida. Eesha ta rungume ta tace "Haba Fido kukan ya isa haka mana, kin manta before da bakin ki kike fad'an Yaya Aliyu crush naki neh, mesa yanzu kike kuka bacin kina sonsa?" "That was then Eesha, but a yanxu I don't have feelings for him, kuma Yaya Aliyu yana shirya mini wulankanci neh, nasani Eesha! Tunda nadawo gida Yaya Aliyu baibi ta kaina ba" "Karki damu Fido ai na fad'a masa a gidan mu kika kwana" "Daga baya kenan fa, kinsan he's a military guy baza ki masa k'arya ace bazai ganeh ba. You should have told him the truth lokacin daya kiraki. But yanxu yasan muna b'oye masa abu neh" Eesha ta goge mata hawayen ta tace "Don't worry habibty, everything will be fine In Shaa Allah. And zaki kashe sa a first night ai, bakin sa zai mutu" ta kashe mata ido. Fido hararan ta tayi tace "I don't like jokes, kin sani" "Sorry habibty" Text message neh ya shigo wayar ta nan take ta bud'e, gani tayi: _I know you can’t see it, but I love you with all my HAYAT. If that means watching you with him, then I will gladly endure the pain so that you might have the chance at a happy life. Just know that if you fall, I will always be there to catch you cox You are My HAYAAT, My Qalb and My Everything. And I promise you daga yau bazaki k'ara ganin text message d'ina ba but now I must tell you that I'm in a state of dilemma please do pray for me. I wish you happy marriage life. Goodbye!_ Tausayin bawan Allah nan neh ya kamata. Tabbas tasan masoyin ta neh na gaskia, masoyi na hak'ika, she wish zata gansa, she wish da an fasa auren, but a yanxu bakin alkalami ya bushe. Fashewa da wani irin kuka tayi ta rungume Eesha tace "Please tell me that everything will gonna be alright" Eesha ta rungume ta sosai tace "In Shaa Allah Fido everything will be OK" ********************** Da misalin karfe sha d'ayan dare an kai Fido gidan ta har an watse. Fido zaune take akan gado fuskan ta a rufe tana kuka. Aliyu neh ya shigo d'akin yasha binjimansa, sai baza k'amshi yake, da an gansa anga ango. Dogon tsaki yaja yace "Keee nifa banson kukan munafurci plus kar kiyi tunanin zamu na had'a kwanciya dani dake, bazanyi taraiyan aure dake ba sai nan da wata uku idan na kira Doctor ya duba mini ke ya tabbatar mini bakida cika sai na taimaka miki" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] _In Dedication To Fido Sodangi_ {July,2016} Wannan shafin nakune 'yan Pure moment Of Life Writers: Mummy Sultan, Maryam S Bello, Sadnaf, Ummu yahya, Zee Yabour, Kausar Lurv, Maryam Abdoul, Anty Khadee, Aysha Garkuwa, Seemalurv, Biebie dee, Husna, Hafsat Musa, Ummi Hambali, Mum Ihsan, Ummyn Yusrah, Aisha Yabo, F k Ahmad, FaShuNa. Washh nagaji wanda basuji ba next page In Shaa Allah! ```Page 26``` Fashewa da kuka tayi tace "Yaya Aliyu please karka mini mummunar fassara, don't think otherwise, na yarda na kwana a gidan Issam but please ka yarda dani ba abunda ya shiga tsakanin mu" Tsawa ya daka mata yace "Don't dare try to explain anything to me, sabida ba k'aryan da zaki fad'a mini na yarda. And kuma me har zaikai ki gidan namijin da ba muharramin ki baneh? Nayi dana sanin amincewa na aure ki. I so much regret it Fido" "Please hear me out!" "Shhhhhh wallahi a halin yanxu koh voice naki bana k'aunar ji" Fita yayi a d'akin, yana fita ta rushe da kuka, sanda tayi mei isarta ta share hawayen ta tayi alwala tayi sallah tana rok'an Allah yasa Aliyu ya fahimce ta. Daga nan ta kwanta bacci b'arawo yayi gaba da ita. Aliyu yana fita a d'akin yaga Meenah tana lek'e. Tsawa ya daka mata yace "Uban mei kikeyi anan" "Amm daman nazo zan wuce kitchen neh" "Kitchen tanan, zaki b'ace mini a gaba koh sai jikin ki ya fad'a miki?" Da sauri tabar wajen, maganganun Fido yana yawo a brain nata, wato Fido har gidan wani take zuwa ta kwana. Tafi tayi tace "Ikon mai sama wonders shall never end ohhh" Zuwa d'akin ta tayi lokacin Basma tana rusa kuka, dogon tsaki taja tace "Gaskia sai na nema me raino dan ni gaskia bazan iya wahala ba". Aliyu yana shiga d'akin sa flat ya kwanta a kasa, ya rasa me yake masa dad'i, he always dreamed of this night, gashi yazo amma bazai iya kusantar taba. Yace "Why Fiddausi, kinsan yadda nake sonki kuwa? Kinsan yadda nake bala'in kishin ki? Koh fuskan ki banso maza su gani balle murmushin ki har yakai ga siffan ki. Na soki Fido, amma a yanxu I don't think ina miki son da nake miki a baya" haka ya ringa maganan zuci daga baya can bacci ya kwashe sa. Washegari da safe Fido tana kwance tana bacci, tunda ta idar da sallah subh ta k'ara komawa bacci dan har yanxu gajiyan jiya bai bar jikin taba. Tana cikin bacci taji an watsa mata ruwa a fuska, nan take ta farka. Yaya Aliyu neh tsaye yana watsa mata mugun kallo yace "Ba hutu baneh ya kawo ki gidan nan maza ki tashi ki dafa mini abinci kinsan breakfast early nake ci koh" Da kyar ta iya mik'ewa tace "Toah Yaya Aliyu" Dogon tsaki yaja yace "You can't fool me so please stop acting innocent" Shuru tayi bata basa amsa ba tafita a d'akin. Da k'yar ta samo kitchen, tunanin irin abincin da zata musu take daga baya tayi deciding tayi potatoes da liver sauce, d'anwake da fish roll. Cikin awa biyu ta gama girkin, d'auko su tayi zuwa dinning taga already dinning a cike da food flakes na abinci. Ajiye nata flasks d'in tayi tashiga ciki dan wanka. Super wax d'inkin riga da skirt wanda ya amshe jikin ta tasaka, yayi mata mugun kyau kamar a jikin ta aka d'inka. D'aura d'ankwali tayi ta shafa powder da lip gloss. Simple make-up tayi amma ba k'aramin kyau tayi ba. Fesa jikin ta tayi da designers turare kusan kala bakwai wani k'amshi mei dad'i neh yake tashiwa a jikin ta. A hankali take tafiyar ta mei d'aukan hankali har tazo kan dinning d'in. A lokacin Aliyu da Meena already suna wajen, tsananin kishi Meena taji a lokacin da ta d'aga ido ta kalle Fido, ita kanta tasan Fido ta had'u gaba da baya. Kujera Fido ta nema ta zauna a can nesa dasu, Aliyu daya kalle ta take ya sunkuyar da kansa, ta masa masifan kyau but kyaun d'in banza ta gama raba jikin ta a waje ya fad'a a zuciyan sa. Yace "Inna ta aiko da abinci tun da sassafe naga bazan iya ci baneh shiyasa nasaki ki girka wani, but sam k'arnin abincin ki yana tada mini da zuciya so I decided naci na Inna kawai" Meena tace "Moon of my life nima gaskia abincin Inna zanci wannan will make me puke idan naci" Fido dai shuru tayi tana kallon ikon Allah, haka suka d'eba abincin Inna su Peper soup na kayan ciki, rusted chicken, alale da kunun madara. Abincin ta koh tab'awa basuyi ba. Potatoes ta d'iba ta had'a shayi, da kyar ma take iya ci. Ganin Aliyu tayi da Meena suna bawa junan su abinci, ita kam koh ajikin ta koh irin kishin nan bata jiba, ta d'anci abunda zata iya ci zata tashi kenan Meena tace "Moon of my life ya maganar samo mini mai rainon da zakayi" Murmushi ya mata tareda yi mata Peck yace "Don't worry, ai yanxu kin samu mai raino, ga Fido me amfanin ta? Kinsan ai daman bana son bawa 'yata ma wata bare tana rik'e mini ita tunda Allah yasa Fido tana gidan nan kuma 'yar gida ce ai sai tana miki rainon, shin me ma amfanin ta? Daga yau ita zatana dafa mana breakfast, lunch da kuma dinner. And plus ta zama nanny Basma as from yanxu, Kinji koh?" "Eh naji" "Good yanzu ki karb'a Basma " D'aukan Basma tayi ta wuce da ita d'akin ta. Fido tana zaune rik'e da Basma tana mata wasa Meena ta shigo d'akin ba koh sallama ta mik'a mata kayaki tace "Ga kayan Basma anan, and kuma abincin ta yana store a kitchen ki kwaso wanda zakina amfani dashi d'akin ki kinji koh" Fido shuru tayi batace komai ba, a zuciyan ta cewa take idan ba k'addara ba har Meena ta isa ta fad'a mata magana tayi shuru ai ba'ayi taba. "Keee dake fa nake magana kin mini shuru" "Ohk naji" Dogon tsaki Meena taja ta fice a d'akin. A hankali Fido yaje kitchen ta had'o ma Basma abinci ta bata, ita mamaki ma take yarinyan da koh shekara d'aya bata cikaba bar an yaye ta Ikon God! Da daddare bayan ta had'o musu dinner suna zaune suna ci, Aliyu sai wani zazzare ido yake yace ma Meena "Dearie nikam bakijin zafin atargon abincin nan neh?" Meena ta kashe murya tace "Moon of my life wallahi nima dakyar nake iya cin abincin nan, banda pepper ma ai oil yayi yawa wai a haka ake dafa fried rice" Duk maganganun da suke Fido jinsu kawai take dan tasan yanxu tafara cin karo da wulakanci. "Keee" Aliyu ya fad'a a tsawace "Maza tashi kije ki dafa mana Indomie wannan abincin naki ba iya ci zamuyi ba" Fido ta maraice murya tace "Yaya Aliyu ka tausaya mini wallahi a gaje nake please" "Zaki tashi koh sai na kakkarya ki?" Kan ta tashi Basma ta fashe da kuka, Aliyu yace "Amma ke yarinyan nan kin bata abinci kuwa" "Ina kuwa zata bata muguwa so take yunwa ya kashe mini d'iya" "Ki bata abincin ta idan kin gama ki kawo mana Indomie mu nan" "Toah" ta amsa masa ta d'auke Basma suka bar wajen. Meena tace "Wallahi Moon of my life Fido...." Bata karasa maganan taba ya daka mata tsawa yace "Will you shut up" Nan take tayi shuru, ita ta lura a gaban Fido neh kawai yake mata wulakanci amma baya yadda a bayan idon ta ayi maganar ta. Tunani take wani irin tarko zata had'a da zaisa Aliyu ya rabu da Fido. Cikin minti goma sha biyar sai gata tazo da Indomie a plate, dira musu tayi a gaban su zata juya ta koma Aliyu yace "Ina zuwa?" "D'aki, nabar Basma ita kad'ai" "D'auko ta" Juyawa tayi ta wuce d'akin ta ta d'auko Basma, karb'an Basma yayi yace "Kwashe abincin ki kikai kitchen na koshi" Bak'in ciki neh ya cikata amma ba yadda ta iya, kwace su food flakes d'in tayi. Meena tace "Ki wanke su karki barsu haka nasan halin ki muguwar k'azama ce keh" Wani kallo Fido ta watsa mata nan take tayi shuru, ganin abun ya b'ata mata rai Aliyu yayi caraf yace "Toh karya tayi neh? Kije ki wanke su idan kin gama kizo ki amsa Basma" Ficewa tayi zuciyan ta na k'ona, hak'ika sunci mata mutunci, wani zazzafan hawaye neh suke sauko wa kan kuncin ta tace "Issam you make things worst for me and I won't forgive for that. I swear to Allah I won't spare you, the moment na bar gidan nan kaine target na! By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers(p.m.l) [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] In Dedication To Fido Sodangi {August,2017} I dedicated this page to members of Pure Moment Of Life Writers: Sad-nas, Mushkurat Othman, Mrs Fawwaz, Ayshat Asym, 'Yar gatan Sadnaf, Jannart Lameed'o, Sumyn bash, Leemcykhan, Mhis B hal, Aisha salihu, Faridat Musa, Minash bawa, 'yar adami, Raks Ruky, Aisha hanwa kai all & wanda sukaga a previous page d'ina. I heart❤ you all. ```Page 27``` Kwance yake a gadon asibiti ya rame yayi duhu, kamar ba Issam wanda mata suke hauka akan sa ba, gefen sa Mummy ce zaune kan kujera ta rik'e hannun sa damuwa fal a fuskar ta. A tsaye kuma wani mutum neh rik'e da Cup yana addu'a yana tofawa cikin ruwan, bayan ya gama ya mik'a wa Mum yace "Karb'i ki basa yasha, In Shaa Allah idan ana yawaita addu'a zai samu sauki, zan na zuwa ina masa addu'a and kuma yana tashiwan dare yana nafila, addu'oin da na basa yana karanta wa, zan wuce ana jirana, dan Allah ki tabbata yasha" Karb'a Mum tayi tace "Nagode sosai Mallam, In Shaa Allah zamu dage da addu'a" "Ba komai Hajiya, ni zan wuce" "Ka gaida gida'' " Gida zai ji" tareda da fita a d'akin. Mum mik'a masa tayi tace "Ungo karb'a kasha Issam" Juya kansa d'ayan gefen yayi yace "Mum ki yarda dani yanxu sam bata raina na jima da fidda ita a cikin zuciya ta" "Naji na yarda but dan Allah ka karb'a kasha" Mum ta taso zuwa inda ya juya tace "My Son dan Allah ka karb'a kasha, shin bakayi Imani da qaddara ba?" Shuru yayi bai amsa ba, tacigaba *"What is meant for you, will reach you even if it is beneath two mountains. And what isn't meant for you, won't reach you even if it is between your two lips. Allah chose for you a spouse before you were even born"* Jikin sa yana kakkarwa ya kamo hannun Mum nasa ya rik'e gam yace "Mother inason Fido, duk da tayi aure na d'auka sonta zai ragu amma kullum son ta yana multiplying acikin Zuciya nah, I don't really know how to explain this to you. Infacts words aiint enough to express how much I love her but ki yarda dani idan nace miki She's My HAYAAT, ITACE RAYUWA TA!" "Shhhh My Son, a yanxu matar mutum kake magana, kayi istigfari karka yi sab'o, so ba hauka baneh, kata addu'a don shine maganin komai. Kasani matar mutum kabarinsa, ba wanda ya isa ya aura matar wani. Babu wanda ya isa!" A sannu da lallashi ta basa ruwan yasha. _Bayan Wata Biyar_ Fido girki take a kitchen ta rame tayi baki sai ka rantse ba ita bace, gefen ta kuma Basma ce zaune akan keken ta, tayi girma sosai kamar wata 'yar shekara biyu. Basma ce tafara kuka gashi tana girki ta rasa yadda zata yi. D'aukan Basma tayi zuwa d'akin ta tahad'a mata Nan tabata tasha, da k'yar ta samu ta lallashi ta tayi shuru. Komawar ta kitchen taga an k'ara mata wutar girkin ta gas d'in naci sosai ga warin k'onan miya. Bud'e miyar da zatayi taga miyar ya k'one kurmus. Zuciyan tane yayi bala'in b'aciwa tasan kan tabar kitchen ta rage wutar. Fita tayi a kitchen d'in ta wuce d'akin Meena direct. Meena, Teema da Ramlah neh zaune suna shewa. A tsawace Fido tace "Uban waye ya k'ara mini wuta bayan na rage kan nabar kitchen d'in?" "Uban ki" cewar Teema, kan tagama fad'a taji saukan mari mai kyau da lafiya a fuskar ta, Fido ta nuna mata yatsa tace "Next time zan miki marin da yafi haka, ni sa'ar kice? Ni sa'ar kuce? Duk wanda ya k'ara tab'o ni a gidan nan wlh zan koya masa hankali 'yan iska kawai" Ramla tace "Kece babbar 'yar iska ai, wanda saura one week da auren ki kika kasa hak'uri kika kwana a gidan wani gardi" "Shiyasa Miji nah har yau ya kasa had'a kwanciya da ita, me zaiyi da left over, second hand ai wlh.." Cewar Meena, bata k'arasa ba itama taji saukan mari mai rai da lafiya a fuskan ta. Fido tace "Daga ke har mijin naki wallahi bana tsoron ku, shima daga yau na daina barin sa wallahi balle kannen sa, ku d'in banza" taja dogon tsaki tabar d'akin. Baki bud'e suke kallon ta, Ramla tace "Wallahi bata isaba, zamu mata dukan gaske kan mubar gidan nan, wallahi baza taci bulus ba" Meena tace "Wallahi bata isa ta tab'a fata na nabar taba, tayi kad'an, sai ta raina kanta wallahi a yau d'in nan" Fitan Fido kenan taci karo da Eesha, nan take tayi gudu ta rungumeta ta fashe da kuka tace "Eesha dan Allah ki taimaka mini, bazan iya zama a gidan nan ba, gidan nan idan banda bala'i da masifa ba abunda yake cikin gidan nan" Eesha tayi hugging nata sosai tace "Shhhh ki daina fad'an haka, duk abunda yayi farko toh hak'ika yanada karshe, muje d'akin ki" "A'a ki kije ga can d'aki nah" tareda nuna mata "Zan shiga kitchen na d'aura girki zanzo na sameki" "Ohk toh" Kitchen ta shiga ta d'aura sabon girki, amma bana na ita da Eesha ta dafa koh ajiye wa Aliyu batayi ba. Bayan ta gama ta kai musu suka zauna suka ci. Fido tace "Ya Faruq?" Eesha tayi murmushi tace "Lafiya sa kalau yana ma gaishe ki" "Allah sarki, nimafa ina son zuwa miki Allah baiyi ba" "Ayyah ba komai, shin yaushe zaki fara fita aiki Fido? "Wallahi kedai bari, Aliyu ya hanani kuma yace idan na fad'awa Abba a bakin aure nah. Yaya Aliyu mugu neh Eesha" ta fashe da wani irin kuka "Tunda nayi aure koh gate ban lek'a ba, kullum ina cikin gidan nan, bai damu dani ba, na zama musu mai aiki kawai" Eesha tace "Shhhh ki daina fad'an haka akan mijin ki, ki zama mai rufe sirrin mijin ki, duk abunda yayi farko yana da karshe, kita addu'a In Shaa Allah komai mai wuce wa neh" Haka suka ta hira har karfe biyar, daga nan Eesha tace zata wuce gida. Rakata tayi zuwa kasa Basma na hannun ta, a parlour k'asa Meena suna zaune da Teema da Ramla. Meena ta mik'a hannu akan Basma taje wajen ta, Basma ta rushe da kuka ta girgiza kanta ta kankame Fido. Bayan sun fita Teema tace "Meena tun ba'aje koh inaba har 'yarki ta fara gudun ki?" Ramla tace "A'a lalle kinada aiki a gaba" "Kan gaba zan shafe ta a dorar k'asa" cewar Meena. Duk suka kwashe da dariya sukace "I trust you girl" "Yanzu abunda zamuyi idan tashigo mu karb'a Basma koh bataso mu kaita d'aki sai muci uban 'yar iska" cewar Meena. Duk suka amsa da "Yes kin kawo shawara" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} ```Page 28``` Har bakin gate Fido ta rakata tace "Nagode sosai Eesha da advice da kika bani, In Shaa Allah zanyi amfani dasu" "Karki mini godiya, what are friends for?" Fido tayi murmushi tace "You're more than a friend to me" Eesha tayi murmushi tace "Really, wow! Thank you. Bye" "Bye" Tana shiga cikin gida Meena ta karb'a Basma dukda irin kukan da take tsalawa, Fido tace "Ki barta mana tunda bata so" "Nida 'yata kuma, kya jiki fa" Bayan Meena ta amsa Basma ta mik'a wa Ramlah ita, Ramla da gudu ta shigar da Basma d'aki ta rufe kofa. Ganin su uku tayi suna zuwa kanta, tace "Ya haka dai? Wani abu neh?" Meena tace "Taruwan dangi zamu miki ba komai ba" Kan ta iya k'ara magana suka hau kanta dukkan su uku, duk yadda tayi ta kare kanta amma karfin mutane uku ya wuce wasa. Jibgan ta suke kamar ba gobe, Meena tana ta sama, Ramla tana kan ciki, Teema tana kafa. Da ikon Allah Fido koh ihu batayi duk da yadda suke jibgan ta saima k'okarin ramawan da takeyi. Sun kusan minti goma suna abu d'aya, sai can dabara ya fad'o mata ta kama fatan Meena ta ciza kamar ta samu nama har sanda jini ya fara fitowa. Ihu Meena take sosai nan take ta tashi akan ta, Ramla da take ruwan cikin ta takama gashin kanta wanda yasha attachment ta ringa ja kamar zata raba kanta da gashin. Ba shiri Ramla ta taso akanta. Teema wacce ta rik'e kafa ta samu ta mata wani irin naushi a baki har sanda jini ya fito. Tashiwa tayi gashin kanta duk a barbazo ga kayan jikin ta sun yage duk ana kallon surar jikin ta. A tsawace tace "Dan Allah kuzo idan kun isa, idan ku mahaukata neh ni kuma babbar mahaukaciya ce" Zuwa kanta suka fara, ganin zasu k'ara hawwa kanta da gudu ta shiga kitchen ta d'auka tab'arya ta fito. Tace "Kuzo dan Uban ku" Meena itama shiga kitchen d'in tayi tafito da nata tab'aryan. Suna zuwa kusa da ita tafara kwad'a ma Teema da Ramla a jiki wanda yasa suka kwanta flat a kasa. Saura ita da Meena suna kalle kallen juna. Meena zata buga mata tab'arya ta tare da nata kawai sai ga tab'aryan duka biyu a k'asa. Shigan ta Fido tayi ta hau ruwan cikin ta tana d'irka. Zo kuga yadda Meena take ihu take fad'an "Wayyyooo Allah nah kuzo ku taimaka zata kashe ni!" Ganin Aliyu nayi ya shigo parlour da gudu ga S.A a bayan sa. Wurgar da Fido yayi kamar kayan wanki ya fara jibgan ta. Sai cewa yake "Zaki kashe mini mata koh?" Da k'yar S.A ya kwace ta a hannun sa, ganin irin kayan da yake jikin Fido yasa ya fita a parlour da sauri. Aliyu bak'in ciki neh ya rufeshi gashi S.A ya gan masa mata a haka. Jan ta yayi har zuwa d'akinta ya cire belt nasa yafara zane ta yana fad'in "Uban mei yakai ki parlour har kije kiyi fad'a da su ehh, abunda kike so yafaru tunda S.A ya gama ganin surar ki" Fido kuka sosai take tace "Yaya Aliyu wallahi she started it, itada Teema da Ramla" Yana jin haka ya fita a d'akin ya rufe kofa ya sauk'o k'asa daidai lokacin su Teema da Ramla sun kwasa kayan su zasu gudu gashi da k'yar suke iya tafiya Aliyu ya cafko su ya rufe kofa ya fara jibgan su da belt, dukan su yake har sanda belt nasa ya tsinke. Bai hak'ura ba yacigaba da dukan su da hannu da duk karfin da Allah ya basa. Yace "Ku fad'a mini gaskia ku kuka fara neman fad'an ta koh?" Da sauri Teema tana kuka tace "Mune Yaya dan Allah kayi hak'uri bazamu k'ara ba dan Allah Yaya karka kashe mu" Sanda ya gaji dan kansa ya barsu tareda jansu ya fitar dasu a cikin parlour ya wurga musu jakan su yace "Kubar gida nah idan na k'ara kallon kafar ku cikin gidan nan sai jikin ku ya fad'a muku, 'yan iskan yara kawai" Shiga yayi cikin d'akin sa ya watsa ruwa ya wuce masallaci lokacin su Teema da Ramla har sun bar gidan. Shi bai dawo gidan ba sai kusan karfe tara na dare. Fido ce kwance kan gado duk jikin ta yayi tsami, ga zafin duka ga ciwon kai dake addabar ta. Hawaye neh fal a kuncin ta tarasa abunda yake mata dad'i da k'yar tasamu tayi sallah. Kwanciya tayi sai can da k'yar a daddafe ta shiga tayi wanka ta fito daga ita sai towel, fesa body spray tayi a jikinta ta kwanta flat akan gado. Jin k'aran bud'e kofa yasa ta d'aga kanta dan ganin waye. Aliyu neh tsaye da bowel a hannun sa da kuma k'aramin towel. Zuwa yayi daf kusa da ita yace "Ki tashi na matse miki jikin ki" Ta had'o rai kamar hadari tace "Banaso, ban bukatar taimakon ka" Tsawa ya daka mata yace "Ina wasa dake neh? Maza ki tashi" Ba yadda ta iya taga ya b'ata rai kuma abu da Aliyu sai a hankali. Tasowa tayi ta zauna, k'okarin cire towel na jikin ta yake ta rik'e hannun sa tace ''What are you trying to do?" "Chill gurl, I aiint interested in your body" Da k'yar ta barsa ya zare towel d'in, rikicewa yayi a lokacin da yaga fulanin ta, a cike a tsattsaye. A hankali ya fara matse mata jikin ta, rufe idon ta tayi gam dan tana bala'in kunyan Aliyu. Ganin bazai iya hak'ura ba ya tusa kansa kirjin ta, hankalin ta yayi mugun tashi tace "Dan Allah Yaya Aliyu meh kake shirin yi dan Allah ka barni" Numfashin sa yana me tsayawa hankalin sa yayi mugun tashi yace "Dan Allah ki barni please" Zatayi magana ya had'a bakinsa da nata kamar wani mayunwaci yana kissing nata, duk iya k'okarin ta dan taga ta turesa amma ina jikin ta ba k'arfi tasha duka. Haka ya ringa shafata ta ko'ina yana kissing duk wani part na jikin ta. A hankali ya rabata da towel d'in gaba d'aya. Kuka sosai take tana dukan sa amma inaa hankalin sa baya jikin sa yariga yayi nisa. Ji tayi yana addu'a kan tace meh taji abu yashige ta, ihu sosai take tana dukan sa amma sai yi yake. Aliyu bai barta ba har sanda ya samu nutsuwa. Wani irin hugging nata yayi sosai yana cewa "Forgive me Fido, dan Allah ki yafe mini please" Idonta ta rufe gam tak'i ta bud'e su, jin tsanar Aliyu tace har cikin ranta, Aliyu mugu neh, duk da rashin lafiyan da nake fama dashi bai kyale ni ba! Fashewa tayi da wani irin kuka, Aliyu ya birkice iya birkicewa sai hak'uri yake bata. Daga baya ya tashi ya had'a ruwan zafi ya d'auke ta cak ya dirata a ciki. Tun tana jin zafi har tasamu taji daidai, bayan ya gama mata wanka ya shafa mata magani a jikin ta kuma ya bata magani tasha. Kwantar da ita yayi a kan gado yana shafa fuskan ta yace "Nagode Fido, Allah miki albarka, Allah barmu tare, wallahi ina masifan sonki ki yarda dani" Bud'an bakin ta tace "Aliyu na tsane ka, I hate you! Ka manta irin zagin da kamini? Ka manta kana cewa ina bin maza? Ka manta irin dukan da kamini, ka manta.. " bata k'arasa ba ya had'a bakin sa da nata, duk yadda taso kwatan kanta ta kasa dan Aliyu yanada karfi, sanda ya tsosa bakin ta son ransa kan yace "I know nayi babban kuskure and In Shaa Allah I'll rectify my mistakes. Everybody deserves a second chance, ina rok'an ki kibani dama na nuna miki irin son da nake miki please" Tufa masa miyau bakin ta tayi tace "Allah sawwaka, karka ma wahalar da kanka sabida bazan tab'a sonka ba, na tsane ka, na tsane ka Aliyu" Murmushi yayi yace "Ana ahubbiki Fido, kin riga kin zama jinin jikin nah a yanxu, ki kwanta kiyi bacci karki wahalar mini da kanki" Kiss ya mata a forehead ya fita ya bar mata d'akin. Kuka ta fashe dashi zuciyan ta yana k'ona, ga rad'ad'in da takeji a k'asan ta, ga zafin duka, ga ciwon kai. Kan tasani bacci yayi awon gaba da ita. Aliyu ya koma d'akin sa yayi wanka yayi alwala yayi nafila. Addu'a yayi sosai kan shima yabi lafiyar gado yana mai tsansan farin ciki. Da misalin karfe biyar da rabi Fido na kwance tana bacci Aliyu yashigo d'akin, pecking nata yayi yace "Fido! Fido" A hankali ta bud'e idon ta taga Aliyu yana mata murmushi yace "Tashi kiyi sallah Subh yayi" Da k'yar ya taimaka mata tayi sallah yana zaune a d'akin, bayan ta idar ta fashe da kuka, da sauri yazo ya samei ta yace "What happen Fido" "Yunwa nake ji" "Ohk jirani ina zuwa" Fita yayi a d'akin cikin minti goma sha biyar sai gashi da Indomie da kwai da bread. Dire mata yayi a gaban ta ya k'ara fita zuwan shi yazo da flasks ya had'a mata Tea mei k'auri ya mik'a mata. Ci tayi sosai har sanda taji ta koshi, magani ya bata tasha tabi lafian gado, kan kace kwabo bacci ya d'auke ta. Da misalin karfe sha biyu da rabi Aliyu yashigo d'akin Fido da Basma a hannun sa wanda take tsala kuka. Nan take Fido ta farka, Aliyu yace "Dan Allah Fido tun safe Basma take kuka tana neman ki" Fido tana karb'an ta tayi shuru tafara dariya, Aliyu yayi murmushi yace "Basma tana sonki Fido, nima ina k'aunar ki" Watsa masa kallo tayi tace "Wallahi duk da kai miji nane bazan tab'a son kaba, yadda ka haddasa mini bak'in ciki jiya nima sai na haddasa maka" Murmushi yayi yace "Ni zan fita sai na dawo" Koh amsawa batayi ba shima ya fita abunsa. D'aukan Basma tayi tana mata wasa tace "Muje kitchen na had'o miki NAN koh" Fita tayi d'auke da Basma a hannu ta zuwa kitchen, bayan ta had'o mata zata shiga d'akin ta taci karo da Meena. Fido tace "Lafiya kuwa?" "Basma nazo duba wa, tunda tayi shuru shikenan" ta wuce tabar wajen. Fido shiga d'akin ta kawai tayi bata kawo komai a ranta ba afterall 'yarta ce. Ganin Basma taki shan Nan d'in ta tab'a feeding bottle d'in tace "Bara na k'aro miki ruwan sanyi Basma kamar yayi miki zafi koh?" Goran faro dake kan gadonta ta d'auko ta d'an zuba ruwa kad'an acikin feeding bottle ta girgiza tace "Yawwa ungo kisha yanxu ba zafi" Basma tana dariya ta karb'a tafara sha. Cikin minti biyu kawai taga jini yana fitowa ta hanci da idon Basma ga wani irin kukan da takeyi... By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} ```Page 29``` Saka hannu tayi cikin jinin da yake fitowa a bakin Basma batasan lokacin da tayi wani irin ihu ba. Nan take Basma ta daina numfashi, girgiza ta Fido take tama kasa kuka sai jikinta da yake rawa takasa furta komai. Sai can tayi wani irin ihu wanda yafi na farkon wanda yasa kaf gidan ya d'auka. Cewa take "Basma dan Allah ki tashi, Basma meya sameki, Basma please ki tashi" ganin Basma bata koh motsi yasa ta fita a d'akin ta da gudu. Meena ce a d'akin ta zaune akan gado tayi crossing leg da kafarta, wani irin dad'i takeji koh ba komai jin ihun Fido tasan burin ta yacika. Wayarta ta d'auka tayi dailing number Umma ta saka a loudspeaker. Umma tana d'auka wa tace "Ya akayi 'yata?" Meena ta k'yalk'yale da dariya tace "Umma shawaran ki yayi, ai na cika aiki. Jiya da daddare bakisan yadda raina yayi bak'i k'irin ba. Yanxu Doctor Umar yana zuwa zaice maganin hana ciki tasha, batason d'aukan ciki tasha magani kuma ya mata destroying womb nata wato mahaifarta bazata iya d'aukan ciki" "Yawwa nagode 'yata har ta mutu bazata tab'a haihuwa ba". Meena tayi dariya tace "Itada haihuwa ai sai a lahira wallahi" Ji take an banko kofan ta wanda yasa tayi disconnecting call d'in da sauri. Ganin Fido tayi ba d'ankwali akan ta a birkice, Fido taje da gudu ta kamo hannun Meena da k'yar ta iya furta "BASMA!" Hankalin Meena yayi mugun tashi tace "What happen" Fido wanda har yanxu koh kwalla batayi ba dan tayi mugun tsorata tace "BASMA, a d'aki nah" muryan ta yana shacking, da gudu Meena ta fita a d'akin Fido tana biye da ita har d'akin Fido. Meena d'aukan 'yarta tayi tana girgiza ta amma ina rai yayi halinsa. Wani irin kuka ta fashe dashi ta ajiye 'yarta akan gado ta cukume Fido tace "Me kika bata? Kin kashe mini d'iya" Fido tana girgiza kanta tama kasa magana, feeding bottle da faro water ta nuna mata da hannu. Meena tayi wani irin kuka tace "Kin KASHE TA, kin kashe mini daughter!" Fido sai girgiza kanta take idon ta yayi jazur amma har yanxu ba hawaye. Meena d'aukar 'yarta tayi ta fita da gudu. Driver takira da saka 'yarta a mota nan yajasu zuwa asibiti. Da zuwan su aka duba Basma likita suka shaida mata tariga tacika. Wani irin kuka ta fashe har k'asa ta kwanta tana kuka mai tsoma rai duk wani mai sauraro. Nan take Driver ya k'ira Aliyu ya shaida masa suna asibiti ba lafia Koh minti goma ba'ayi ba sai ga Aliyu a cikin asibitin. Meena tana ganin sa nan take ta tashi ta rungume sa tana wani irin kuka sai cewa take "Basma! Moon of my life BASMA!" Nan take ya janye ta daga jikinsa ya samu Doctor Umar dake tsaye a gefe "Doctor what happen to my daughter? Ina take?" Doctor Umar yace "I am so sorry, we lost her!" "Inna Lillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un" shineh abunda yake maimaitawa. Idonsa yayi jazur kamar wuta, hankalin sa yayi mugun tashi, saka hannu sa yayi cikin suman kansa yace "Tana ina? Ya akayi haka I left her she was doing fine. Ohhh sorry! So stupid of me to ask you such question, haka Allah yayi lokacin tane yayi" Doctor Umar yace "Haka neh General but she was poisoned" Da sauri ya d'aga kansa ya kalla Dr Umar yace "What!!!!?" "Yes! she was poisoned" Hankalin sa neh yayi mugun tashi yace a nuna masa gawan 'yarsa. Bayan sun gama preparation na komai ya fita a asibitin Meena ta kama sa tana wani irin kuka "Ta kashe mini 'yata, she killed my only child. Wallahi bazan barta ba!" Hugging na matar sa yayi shi kanshi yana zub da hawaye. Yana son 'yarsa sosai, nan take maganar Fido yazo masa kansa *Aliyu na tsane ka, I hate you! Ka manta irin zagin da kamini? Ka manta kana cewa ina bin maza? Ka manta irin dukan da kamini?* *Allah sawwaka, karka ma wahalar da kanka sabida bazan tab'a sonka ba, na tsane ka, na tsane ka Aliyu* *Wallahi dukda kai miji nane bazan tab'a son kaba, yadda ka haddasa mini bak'in ciki jiya nima sai na haddasa maka* Wani irin k'ara yayi daya tuna maganganun ta, shiga motar sa yayi ya fisga da k'arfi, gudu yake sosai akan hanya, koh horn baiyi ba ya sauka akan motar sa yashiga ciki. Fido ce a parlour tama rasa me zatayi, ta kasa kuka ta k'asa zama ta k'asa tsayuwa. Zuciyanta neh yake wani irin tsinkewa, bugawa. Ji tayi an banko kofa nan take ta juya dan ganin waye neh. Aliyu tagani yana tsaya idon sa yayi jazur sai kakkarwa yake. Zuwa yayi ya shak'e ta yana wani irin nishi yace "Me Basma tamiki? Mei 'yata tayi miki? She's a child for goodness sake she don't deserve this. Mesa bazaki rama akaina ba? Daman kin fad'a kamar yadda na haddasa miki bak'in ciki nima sai kin haddasa mini koh? Gashi kin haddasa mini congrat!" Wurgar da ita yayi kan kujera ta fad'i ras! Ya rasa mei zaiyi kawai ya k'ara janyo ta yana janta. Sai janta yake masu gadi suna "Yallabai lafia?" Wani irin tsawa ya daka musu yace "Kar kowa yazo kusa dani" Har waje ya kaita yayi wulli da ita bai damu da kanta ba kalbi koh yanayin kayan jikin taba. Nunata yayi da yatsa yace "Fido Allah ya isa tsakani na dake! Bazan tab'a yafe miki ba kuma BAZAN BARKI BA! Kuma sai kinga sakamako tun a duniya wallahi tallahi! Na tsane ki! I hate you! KIJE NA SAKE KI SAKI BIYU!!!!!" Screen na wayana ya samu matsala just In case! By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain, we touch the ❤ heart of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} ```Page 30``` Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to VOTE! Kifa kanta tayi cikin cinyoyin ta tana mei wani irin nishi, har yanxu ta kasa yarda Basma ta mutu a hannun ta. Cikin wannan yanayin Shamcy da Yaya Khaleal sukazo suka same ta. Da farko basu d'auka ma ita bace sun d'auka wata mahaukaciya ce, sabida ba'a iya hango fuskan ta dalilin tusa kanta da tayi cikin cinyoyin ta sai gashi kawai wanda ya sauk'o cinyoyin ta. Shamcy hankalin ta yayi mugun tashi ganin 'yayarta cikin irin wannan yanayin. Zuwa tayi daf kusa da ita tana girgiza tana cewa "Adda Fido meyayi zafi haka? Nasan bake kika kashe Basma ba, nasan kinason Basma kuma kin d'auke ta kamar 'yarda kika haifa, Dan Allah ki d'aga kanki please" Shuru taji sai ajiyan zuciyan da takeyi "Adda Fido bakya jina neh? Dan Allah ki tashi mutafi gida" still ba respond. Shamcy ta juya wajen Yaya Khaleal tana kuka tace "Yaya Khaleal ya zamuyi? Koh zaka d'auke ta neh? Yaya Khaleal ya girgiza kansa yace "Hakan bai kamata ba, d'aga ta tashiga mota" "Na d'aga ta kuma? " Eh bance ki d'auke taba kija ta" Nan take Shamcy ta tsuguna kusa daf da ita tana kuka da k'yar ta iya d'agata ta tsaya, janta take har tashigar da ita cikin mota. Fido kamar wata zararriya, idan banda kallon su ba abunda take, yadda take kallon su kamar bata sansu ba kamar shine ranar farkon data fara kallon su. Bayan Shamcy ta tusata a motar seat na baya itama tashiga ta danna lock a kofan. Nan take Yaya Khaleal ya danna wa motar key ya fusga. Gudu yake sosai akan hanya, Shamcy ta rungume Fido tace "Yaya Adda kiyi kuka, rashin kukan ki zai janyo miki babban matsala, please try kiyi kuka" Amma ina Fido har yanxu ko kwalla d'aya bai fito a idon taba, sai wani kallon Shamcy take kamar bata santa ba. A haka har suka iso gida Shamcy ta taimaka mata ta sauka a motar. Suna shiga b'angaren Inna a parlour Fido ta yanke jiki ta fad'i kasa. Wani irin k'ara Shamcy ta sake tareda fita a parlour da gudu zuwa wajen Yaya Khaleal da har yanxu yake harabar gidan "Yaya Khaleal Adda Fido!" Nan take ya shigo cikin parlour da gudu, ganin ta kwance a k'asa yayi saurin shiga kitchen ya d'ebo ruwa ya yayyafa mata a fuska. Nan ta sauke wani irin numfashi, a hankali take bud'e idon ta. Ganin Shamcy da Yaya Khaleal tayi akanta suna kallon ta, k'okarin tashi take Shamcy ta taimaka mata. Nan take abunda yafaro yazo kanta, wani irin kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciyan duk wani mai saurari Tace "Wallahi Allah ban kashe taba, bani na kashe ta ba, ku yarda dani" Inna ce tashigo parlour ta zauna daf kusa da ita tace "Shhh Fiddausi mun san bake kika kashe taba, mun san halinki baza ki kashe koh ran mak'iyin kiba, ki daina kuka". Rungume Inna tayi tana wani irin kuka, Inna tana lallashin ta. Daga baya aka tayi da ita taci abinci amma tak'i ci sai kuka take. Sai can daga baya da lallashi tasha kunu kad'an. Da daddare tana nan tare dasu Inna, Shamcy, Mummy da sauran abokan arziki wanda sukazo mata ta'aziya. Umma ce tashigo parlour tana "Ina munafukar take?" Ganin Fido tana zaune kan sallaya tana addu'a tazo ta cukume ta tace "Munafukar banza munafukar ofi, addu'a mei kike bayan kin kashe mini jiki, Allah bazamu yafe ba kuma karki ga kinyi nasara kin kashe ta toh wallahi ba wani namijin da zai aure ki, duk wanda yazo da sunan aure yana jin kinyi k'isan kai zai gudu" Da k'yar aka raba Umma da Fido, suka samu suka fitar da Umma a d'aki. Wani irin kuka ta fashe dashi tana Allah gani gareka! Allah ka ganar dasu gaskian al-amarin!!! (boring page banson typing abun tausayi zan tsaya anan) _Bayan Wata Hud'u_ Gudu take sosai akan titi sabida tana da class by 8:00am gashi yanxu har 8:30 sam bataso hakan ba. Bataso tana lecture student suzo zasu shiga and she don't wanna keep them waiting. Wani dogon tsoki taja ganin wayan ta yana ringing tace "Who so ever is calling bazan d'aga ba". Ganin Shamcy baro baro kan screen na wayar ta yasa tayi saurin receiving tace "Shamcy ya akayi ba yanxu nabar gida ba?" "Adda Fido kin manta da Laptop da key office naki" Wani wawar buriki taja wanda yasa ta buge motar dake daf gaban ta. "Yaa Salaaam" ta furta ganin mai motan yayi parking itama take tayi parking motar ta tafito a ciki. Sai yanxu na kare mata kallo doguwar riga rug neh a jikin ta material purple da black tayi rolling da veil black, sai wani uban heel dake kafanta. Kallo d'aya zaka mata kagane tayi mugun ramewa tayi duhu. Wanda ta buge masa mota ya juya mata baya yana mai duba motar sa. Zuwa wajen tayi tana mai duba motan ba tareda ta d'aga kai ta kalla fuskan me motar ba. Gani tayi motar ba k'aramin jin jiki yayi ba. Batasan lokacin data furta "I am so so sorry dan Allah kayi hak'uri" tareda d'aga manya manyan idonta. Nan take taja da baya baki bud'e tace "YOU!!! ISSAM?" Shi kanshi Issam was surprised yama kasa magana Nan take tajuya tashiga motarta ta fisga da gudu By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate,we also touch the ❤ hearts of the readers.] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} *Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!!* ```Page 31``` Gudu take har ta isa cikin University of Katsina, cikin makarantan ma gudu take har sanda ta iso destination nata tayi parking motar ta a parking slot, ita duk budget nata yau zata kai har la'asar a makarantan sabida tana da lecture da zatayi by 2:00pm. Wani dogon tsaki taja tace "wannan yaron yayi ruining komai nah". D'aukar jakarta tayi ta fita a motar, direct venue da zatayi lecture d'in ta wuce. Ganin students tayi duk sun fita a hall d'in, duba agogon hannun ta tayi taga 9:01 tace " Yaa Salaam I'm so freaking late" Ganin lecturer su dasu kayi yasa duk suke gudun komawa cikin ajin. Tana shiga cikin ajin tace "CLOSS THE DAMN DOOR" Da sauri class-rep d'in yaja kofar ya rufe. Nan tafara musu lecture akan Parasitology, awa d'aya da rabi tayi mai kyau tana explaining, bayan ta gama ta d'au jakarta tace "Attendance please! And yes don't mistake to write it for your friends. Don't dare it! Ama warning!!!!" Haka koh wani student yana zuwa gaban ta ya rubata ID number sa ya koma seat. Bayan kowa ya rubata tace "The class-rep should meet me tomorrow morning in my office for today's handout. See you in my next class bye!" Ta fita a cikin ajin, direct parking space ta wuce tashiga motarta ta fisga. Har yanxu she can't stop thinking of Issam, bawai shid'in ba, yadda ya canza mata gaba d'aya. Gidan Eesha ta wuce direct, a d'aki ta same Eesha tana gyara kan gado. Tab'a ta tayi nan ta firgita harda d'an "wayyoo Allah". Fido ta k'yalk'ale da dariya tace " Amma ke muguwar tsoraciya ce" Eesha ta b'ata rai tace "Kinsan abunda kikayi bai dace ba koh?" "But atleast da kin rufe kofa ai, Allah ya kiyaye idan b'arawo yashigo fa?" Wani kallo Eesha ta watsa mata, Fido tace "So sorry Swthrt! Wai tun safe me kikeyi baki gyara kan gadon ki ba? Kinsan first thing abunda mace yakamata tayi idan ta tashi a bacci shineh gyaran gado" "Toh sannu uwata" "I am just saying neh" "Toh Ban gode ba I don't need your advice" "Ba godiyar ki nake buk'ata ba, break fast zaki had'o mini" "Ki shiga kitchen ki had'a". "Wallahi baki isa ba, daga class fa nake, idan baza kiyi ba sai na tafi gidan mu Allah" Ganin she is serious Eesha tace "Ohk bara na dafa miki Indomie zaifi dahuwa da wuri" "Be fast!" Bayan minti biyar sai ga Eesha da Indomie wanda yaji kayan had'i, Fido karb'a tayi tace "Thanks love" tafara ci. Tana cikin ci ta kalla k'awarta tace "Guess wa na had'u dashi yau? " I ain't good at guessing, so tell me who?" "Mts! ISSAM" Nan Eesha ta gyara zaman ta tace "Ohh haba" tayi mata wink. Fido taja dogon tsaki tace "Kina da damuwa wallahi. Tell me something? " What?" Fido ta ajiye plate na hannun ta tace "He aiin't himself anymore" Eesha tace "Ban ganeh ba? Kamar ya?" "He ain't the Issam I used to know, ya canza mini gaba d'aya, his looks and everything. Tell me, meke damun sa?" Gyara zama Eesha tayi tace "Its a long story" "Bani labari k'awata" "Hmmm akwai wata yarinyan da yake so neh" Dogon tsaki taja tace "Dama duk wannan abun akan mace ce? Gaskia har naji kunya. Duk irin wannan girman kansa har mace zatasa ya shiga cikin wani yanayi? Bata son sane? Koh da yake macen da zata so Issam sai wanda batasan halin sa ba, a yau koh da tana son shi wallahi zanyi iya k'okarina dan ganin na raba su sabida Issam doesn't desearve to be love" "Hmm yarinyan da yake hauka akanta bata ma san yana yiba. Kinsan me ake kira da UNREQUITED LOVE? Koh da a yau ya furta yana sonta toh a tunanin sa baza ta tab'a sonshi ba" "Why?" A zuciyan ta kuma tunani take koh yarinyan tasan asalin sa wato d'an fashi, idan har ta sani toh dole ta nema yarinyan. Eesha tace "Tayi aure, but luckily for him mijin ta ya sake ta" "Awww haba?" "Eh sun rabu, but zan bashi shawara yanxu shine dai-dai lokacin da zaiyi approaching nata ya fad'a mata sirrin dake ransa" "Ina yarinyan take, I desperately wanna met her" Fido ta tambaya "You so stupid!!!! KECE ISSAM KESO, KECE ISSAM YAKE BURIN SPENDING REST OF HIS LIFE WITH! KECE RAYUWAR SA!" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! *HBD in advance my small sis Meenarh Parrot and Sadnaf wish you age with grace with Allah's khair now and always* ```Page 32``` Fido kallon ta take with so much surprise on her face, sai can ta fashe da dariya tace "You must be kidding me right?" Eesha ta b'ata rai tace "I'm freaking serious Fiddausi, wallahi Issam yana mutuwar sonki. Mu bamu sani bama, Mum nasa ce tak'ira Faruk tace Issam ba lafiya, so har Abj yaje dan duba lafiyan sa. A time d'in Mum nasa take tambayar sa wacece Fido. Faruq ma was shocked lokacin data tambaye sa, shine ya mata bayani akan k'awata ce ke. So a time d'in mukasan dalilin ki Issam bashida lafiya, dalilin ki yashiga wani irin yanayi" Fido zuciyan tane ya buga, zuwa kusa tayi da Eesha tace "Tell me this is not true, tell me you're kidding me" "Wallahi Allah da gaske nake" "Tun yaushe yake so nah?" "I don't know so I can't tell" Ji tayi ta rikice gaba d'aya, tama kasa tunani. Jin sallaman da ake a k'ofa yasa Eesha ta d'au hijabin ta tace "Bara na duba wake sallama" D'aga kai Fido tayi ba tareda da ta amsa mata ba. She was so confused ta rasa me zatayi. Cusa hannu tayi cikin sumar kanta tace "Ya Allah help me" Da sauri Eesha ta shigo cikin d'akin tace"Guess wanda yake sallama" "Banson dogon surutu just tell me who?" "Masoyin ki" "What!" "Issam neh, yazo neman Faruq nace masa baya nan kinsan abunda yace?" "I don't wanna know please kibar zancen yaron nan" "Cewa yayi yaga motar ki na miki magana ku gaisa" "What? Kice bazan fito ba" "Haba dan Allah sai kace k'aramar yarinya, please" Da k'yar Eesha tayi convincing nata akan ta fita su gaisa. Hijabi dogo ta saka na Eesha ta fita. Zaune yake a parlour yana karanta Magazine, jin motsin ta ya ajiye magazine d'in. Sallama tayi da hankali wanda bata tab'a tsammanin zaiji ba balle ya amsa "Wa'alaykis Salaam" Neman waje tayi ta zauna tana facing nasa tareda crossing leg. Kusan minti goma ba wanda yace k'ala a zuciyan ta cewa take anya wannan yana so na kamar yadda Eesha ta fad'a mini kuwa? Koh dai wani abun daman yake nema? Tana cikin tunanin nan Issam yace "Naji labarin abunda yafaru, so sorry for your lost ya hak'uri" A hankali ta furta "Mun gode Allah" Daga nan kuma shuru ba wanda yace wani abu, wani dogon tsaki taja tace "Please if you don't have anything to say can you please excuse me" Kallon ta yake with so much tenderness in his eyes, kallon ba k'aramin kashe mata jiki yayi ba ya d'an yi murmushi ta gefe wanda ya k'ara fidda asalin kyawun sa duk da ya rame, yayi duhu yace "Were you expecting me to say something? Akwai maganar da kike so kiji koh kin d'auka zan fad'a miki wani abu neh bayan wannan?" Ranta neh yayi mugun b'aci tace "No! Yaro irin ka ma what will I expect ka fad'a mini? N-o-t-h-i-n-g" tayi emphasizing word d'in. Shuru yayi yana kallon k'aramin bakin ta, bai san ta yadda zai fara furta mata sirrin dake ransa ba. Wucewa tayi ta koma ciki ranta a b'ace, ta rasa yadda akayi Issam yake looking down on her. Shigan ta d'akin ta cire hijabin tayi wulle dashi, Eesha ta kashe mata ido tace " 'Yan mata ya akayi?" Dogon tsaki taja tace "Ki mantar da d'an iskan nan" "Shhh dan Allah kiyi shuru karki bari yajiki" "Allah sa ya jini, tsoran sa nake?" "Shikenan magana ya wuce" Fitan ta a d'akin yayi murmushi tareda tab'a k'irjin sa, ji yake yadda zuciyan sa ke bugawa fast "Ina sonki ki Fido bansan ta yadda zan b'ullo miki ba, kece komai nah, kece rayuwata" Washegari Fido tasha hijabin ta har k'asa sai faman karkad'a key motar take "Shamcy! Shamcy wallahi idan baki fito mun tafi ba zan fasa kaiki shopping d'in" Nan Shamcy ta fito a d'akin tasha kwalliyar ta tayi kyau tace "Adda Fido ya bakiyi make-up ba" "Muje banson dogon surutu". Tun lokacin da Basma ta rasu da mutuwar auren ta har yau bata k'ara kwalliya ba, koh kajal bata sakawa a idonta. Daga lipgloose shikenan. Tun lokacin tana cikin wani irin damuwa, tasan mutuwa da mutuwar aure duk daga Allah neh. Duk da bata son Aliyu amma zuciyan ta taji ba dad'i a lokacin da ya sake ta( duk yadda mace suke da mijin ta idan ya sake ta dole sai taji ranta yayi bak'i k'irin koh da bata sonsa) Tafiya suke cikin motar ta har suka iso babban super market. Parking motar ta tayi suka shiga cikin shopping mall d'in. Shamcy sai d'iban abu take tana sakawa cikin basket Fido tace "Wallahi idan kud'in ya wuce 20k bazan biya ba" Lan k'wasar da kanta tayi tace "Ayyah Adda Fido ba haka mukayi dake bafa" "Kee nidai na fad'a miki" Juyawan da zatayi kawai tayi kicibus da wani, cikin b'acin rai zatayi masifa kawai tayi ido hud'u da Issam, a hankali taja da baya. Shamcy tace "Ahh Yaya Issam koh" Murmushi yayi yace "Ashe kin ganeh ni Baby" Wani farin ciki taji daya kirata da Baby "Eh mana ai dole, naje auren Yaya Faruq ai kuma kai ka kawo Adda Fido gida lokacin" Cusa hannun sa yayi cikin sumar kansa yace "Eh haka, I thought baki wayeni ba ai" Kan Shamcy ta bada amsa tace "Kee zo mu tafi inada meeting yanzu" "Ohk Bye" Shamcy ta d'aga masa hannu tayi gaba, Fido zatabi bayanta ya rik'e hijabin ta ya kashe mata ido d'aya yace "Ban ganeh bafa?" "Baka ganeh me ba?" B'ata rai yayi ya had'e giran sa yace "You keep on following me duk inda naje, tell me why" Kallon mamaki take masa wai tacika binsa Yace "You are wasting my time my gurl" Deadly look ta masa tace "Don't call me that again, mesa ma zan bika?" D'aga kafad'a yayi yace "Nima shineh ban sani ba, but I don't like it ki daina kinji?" Yayi wucewar sa ya barta, ranta neh yayi mugun b'aci nan taje ta biyan kud'in aka ce mata an riga an biya, hararan Shamcy tayi tace "Mesa kika barsa ya biya? "He insisted and there is nothing I can do" Dogon tsaki taja tace "Muje" _Bayan sati d'aya_ Shamcy zaune take da Inna suna shan fruit salat sukaji sallama, hijabin gefenta ta d'auka tace shigo bismillah. Musa mai gadi neh yayi sallama ya shiga parlour yace "Inna ana sallama da Shamcy" Shamcy cikin mamaki tace "Waye?" "Issam wai" Shamcy bud'e baki tayi she can't believe Issam yazo wajen ta, nan take tace "kace yashigo" Cikin d'akin su tashiga lokacin Fido tana marking scripts na students nata, ganin Shamcy tayi tana fesa perfumes tace " 'Yar yawo ina kuma zuwa da yamman nan" Tana murmushi tace "Anzo waje nane". Fido ajiye Pen na hannun ta tayi tace " Ikon Allah, waye haka" "Idan kin fita zaki gansa" Fita tayi ba tareda ta jira meh yararta zata kuma fad'a ba. Cikin zumud'i taje parlour tayi sallama, amsawa yayi yana murmushi yace "Sister nah yakike" Inna sai kallon ikon Allah take tace "Ni Shamsiyya ai farko na d'auka baya jin hausa ashe har fultanci yanaji, d'auka wa nayi balarabe neh koh d'an India" Dariya Issam yayi yace "Inna mahaifina fulani neh mahaifiya ta 'yar Yemen" Inna tace "Yawwa shiyasa" "Shiyasa meh Inna?" Ya tambaye ta "Kana da kyau sosai" A dai-dai lokacin Fido tafito a d'aki, to her very own surprise taga Issam a parlour suna hira da Inna. Issam yace "Inna toh ai kamannin mahaifina na biyo sai dai hasken Mum nah" Inna ta washe baki tace "Mashaa Allah, Yaro wajen Shamcy kazo, idan sonta kake da aure sai nayiwa Abban ta magana" Murmushi yayi yace "Inna ai Shamcy k'anwa tace" Inna ta b'ata rai tace "Me kake nufi? Toh me yakawo ka gidan nan" "Neman aure" tareda d'aga idon sa ya kalla Fido Inna tace "Neman auren wa? " Yayar Shamcy" Shamcy mamaki da kunya neh yacikata, Fido kuma nan take ta shige d'akin ta. Inna tayi murmushi tace "Kai amma gaskia nayi murna, ai kullum ina mata addu'a Allah bata mijin da yafi shegen Aliyun nan, yanxu zamuga idon mutanen gidan nan" Issam murmushi yayi yace "Inna zan wuce" "Toh Shamcy shiga ki kira Fido ta rakasa". Issam ya tsaida Shamcy yace "No ki barta ba komai" Cire kud'i yayi a aljihun sa ya mik'awa Shamcy yace "Sister na gashi kisaya kayan makeup sauran ki sayawa Inna goro" Duk yadda Shamcy tayi dan ganin bata karb'a ba yasata dole ta karb'a. Inna sai saka masa albarka take. Tun daga ranar kusan kullum sai Issam yazo gidan, duk zuwan shi ba abunda ya tab'a had'a shi da Fido dan tana ganin sa zata b'ata rai. Inna har yakai ta gane kullum take masa nasiha akan In Shaa Allah Fido watarana zata soshi. A ranar ba kowa a gidan Fido tana zaune tana karanta hisnul muslim Issam yayi sallama, nan take ta gyara gyalen ta tabashi izinin shigowa. Neman waje yayi ya zauna, koh d'aga kanta batayi ba balle tasan yana yi. Kusan minti talatin ba wanda yace wa wani k'ala. Zuwa yayi ya zauna a k'asan carpet daf kusa da kafarta yace "Fiddausi" Mamaki abun ya bata dan a rayuwa zata iya k'irga sau nawa ya k'irata da Fido balle Fiddausi "Lafiya?" Tana meh d'aga masa gira Ya rasa ta yadda zai fara b'ullo mata zuciyan shi yana tsinke wa yace " Inasu Inna?" "Mtswww sai kazo gabana zaka tambaye su? Toh baso nan sun fita" tareda tashiwa ta barsa a wajen. Zama yayi ya rasa abunyi kuma ya kasa tafiya, sai can kusan minti goma tafito da cup da coffee a kitchin. Zaro idonta tayi tace "Aww har yanxu baka tafi ba?" Shuru yayi ya rasa amsar da zai bata, neman waje tayi can nesa da inda take zama na farkon ta zauna. "Please mik'a mini laptop d'ina" ta fad'a masa dayake yana kusa dashi. Ganin bashida niyar mik'a mata yasa ta taso da coffee a hannunta ta tsuguna zata d'auka kawai Cup d'in ya kife coffee ya zube mata a hannu, wani irin ihu tayi tace "Wayyoo Allah" Nan take Issam ya rikice yana mata sannu yana mai hura mata hannun ta da bakin sa, sai cewa yake "Does it pain, yana miki zafi koh?" Tsawa ta daka masa tace "Ina ruwan ka da if I am in pain, and what stupid question is that? Kallon ta yake ido cikin Ido yace " It will break my heart if you're in pain" "What!?" Ta tambaye sa dan abun ya bata mamaki, cikin idon ta yake kallo with much tenderness yace "If you were in pain, it will break my heart!" Matsowa yayi sosai kusa da ita yacigaba "And I will die if you ever In pain" K'ara matsowa yayi sosai wanda suke jin numfashin juna yacigaba Opppps be3 low Ana complain ina pages kad'an kuyi hak'uri rashin time neh but In Shaa Allah cikin two weeks zan gama or even less than that! #oneLove Comment 07034419520 *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! *You yell at times and you lose your mind. You get wild and you throw a fit too. But all that is excused because today is dedicated especially to you! Happy birthday Meenarh Parrot and Sadnaf* ```Page 33``` K'ara matsowa yayi sosai wanda suke jin numfashin juna yacigaba "Because there could be nothing left in me without you. Because if you were in pain, then my heart will would explode into a million pieces of broken glass. I wouldn't be able to breathe without you, I wouldn't be able to live without you. Because you are my HAYAT. Because i-i ----- Issam, I L-O-V-E yhu!!!" Ya fad'a yana mai kallon cikin idon ta, Fido kuma ta kasa komai and she's speechless baki bud'e take kallon sa, lokaci guda mutuwar mahaifin ta yayi bouncing brain nata batasan lokacin data d'aga hannunta ta wanke sa da mari mai rai da lafiya ji kake "Tassssss" Ba k'aramin girgiza yayi ba, a rayuwar sa bai tab'a furta wa mace yana sonta ba sai Fido, a rayuwar sa ba macen data tab'a d'aga hannu ta maresa harta mahaifiyar sa. Fido ta nuna sa da yatsa tace "Har kai ka isa kace kana so nah? How dare you open your filthy mouth kana ganin kwayar ido nah kace kana so nah? Wallahi koh da maza sun k'are a duniya bazan tab'a sonka ba, na tsane ka, I hate you more than anything" Muryan sa yana shacking yace "Mesa bazaki soni ba, mesa bazaki tab'a so nah ba, mena miki a rayuwa Fiddausi, if I ever wronged you unknowingly please ki fad'a mini wallahi zan baki hak'uri! Tell me why" Murmushi tayi tace "Do you really wanna know abunda ka mini" Da sauri yace "Eh" So take ta fad'a mishi gaskian kawai sai ta tuna idan har ta kuskura ta fad'a masa bazata iya d'aukan fansa akansa ba. Tace "Nothing kawai bana sonka, jina nah sam bai had'u dakai ba" A dai-dai lokacin wayarta tayi ringing, nan take tayi receiving tace "Ka shigo ina ciki ba kowa a gidan" ta katse wayan. Kallon Issam tayi tace "Yanxu zaka san mesa bana sonka" Sallama akayi sai ga S.A yashigo parlour, Murmushi Fido tayi tace "Bismillah have a seat" tareda nuna masa kujera. S.A yace "Thanks my love" Issam wani irin kishi yaji, Fido tace "Ammm Issam kaga mijin da zan aura koh? Sunan shi Suleiman" Issam murmushin k'arfin hali yayi yace "Happy for you". Ya mik'a masa hannu suka gaisa, S.A sai wani shan k'amshi yake yana b'ata rai. Fido ta juya wajen Issam tace "Can you excuse us please idan ba matsala" Murmushi yayi yace "Sure why not? Bye take care" Yana fita S.A ya b'ata ransa yace "Waye kuma wannan?" Fido zama tayi tace "Karka damu wai sona yake" "What?" Dariya tayi tace "Karka damu bana sonsa" Idan har bakya sonsa toh ki fad'awa Abba zan turo "Hajiya zata barka neh?" "Tun yaushe ta hak'ura" "Matar ka fa?" Murmushi S.A yayi yace "Tana gaishe ki ma" Dariya Fido tayi tace "Hmm Allah sa dagaske neh, Kasan mata da kishi" "Kibar maganan nan, yaushe zan turo?" Fido gyara zaman ta tayi tace "A gaskia bazan maka k'arya ba bazanyi aure yanxu ba, mutune zasuce koh shekara da mutuwar aure nah baiyi ba zanyi wani aure" "Fido baki sona, idan har kina so nah toh ki mantar da maganan mutaneh" "Ka turo toh" Kallon ta yake da mamaki yace "Are you serious?" Murmushi tayi tace "Yeah" Manage this🙈 By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ *Gaisuwa na musamman Shamcy Dahiru, Mum Ikram, Mum barista da My Shamcy❤ ina kaunar ku sosai sosai and muna mugun tare* {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 34``` Murmushi S.A yayi yace "Beauty nagode, yanzu sunyi tafiya nan da three weeks zasu dawo gari, suna zuwa gari washegari zasu zo nan In Shaa Allah" "Allah kaimu S.A" "Ameen beauty" Issam yana zuwa gida ya tattara kayan sa ya saka su a mota ya d'au wayar shi yayi dailing number, ana picking yace "Akwai jirgin da zai tashi yau?" Sai can kuma yace "Ohk gobe by 6:00am ba, aiit thank you" ya katse wayan. Wani irin zugi yakeji acikin zuciyar sa, ya rasa abunda ke masa dad'i, maganganun data fad'a masa ne suke yawo cikin brain nasa _Har kai ka isa kace kana so nah? How dare you open your filthy mouth kana ganin kwayar ido nah kace kana so nah? Wallahi koh da maza sun k'are a duniya bazan tab'a sonka ba, na tsane ka, I hate you more than anything_ Wani zazzafan hawaye neh suke sauk'a a kan kuncin sa, he just can't believe wai shine yake kuka akan mace yace "Ashe haka mata sukeji idan nace musu bana sonsu? Ashe haka abun yake so painful? Ashe haka sukeji idan na fad'a musu bak'ar magana? Ashe haka so yake?" Wani irin kuka yakeyi mai tsuma zuciyan duk wani mai sauraro, ya rasa dalilin da yasa yake sonta, idan kyau neh dubu son fita amma zuciyar shi ita kad'ai keso. Share hawayen sa yayi dajin k'irar sallar magrib ya tashi yayi alwala yaje masallaci. Da daddare ma same thing ya kasa bacci idan banda tunanin Fido ba abunda yake, daga k'arshe yayi nafila ya rok'e Allah daya cire masa sonta a ransa. Fido da daddare ta kasa bacci sai tunanin Issam take, ta rasa solution da zatayi tayi avenging abunda yayiwa mahaifin ta. Tasan kuma idan ta aura S.A Lagos zasuje dan acan yanxu yake. Cusa hannun ta tayi cikin sumar kanta tace "Ya salaam me zanyi dan na rama abunda Issam ya mini, nayi rantsuwa bazan barshi ba koma wallahi bazan tab'a barin sa ba, sai yayi dana sani wallahi" Da sassafe Issam ya wuce airport dan koh bacci bai samu yayi ba a daran jiya Koh minti talatin ba'ayi ba jirgin ya d'aga zuwa Abj. Yana shiga gida Mum nasa tayi welcoming nashi tace "Son ya Katsina ya hanya?" Murmushin dole yayi yace "Kalau Mother Alhamdulillah" Mum tayi murmushi dan tasan d'anta ba mai yawan son surutu dayawa baneh, kusan secs talatin yace "Mum har yanxu kina son kallon Zee world?". Murmushi tayi tace " Eh wallahi" can kuma yace "Ina Salala bata dawo ba?" Murmushi Mum tayi tace "Eh bata dawo ba" "Anty Sajida fa? Mum kama hannun sa tayi tana kallon cikin idon sa da yayi jazur, tasan Issam bashida yawan tambaya haka, tasan halin shi yana k'okarin b'oye mata halin da yake ciki neh. Tace "What's up anhh? Chatter is a fool's pursuit. Your eyes can't hide what your words conceal. Mesa bazaka bar tears d'in su sauk'o ba? Don't imprison them, let them free." Sai ga hawaye shar shar yana sauk'o wa kan kuncin sa, Mum abun har tsoro yake bata. Issam koh a k'arami bai kuka, last kukan sa mutuwar mahaifin shi neh wanda bazasu tab'a mantawa ba, sai kuma soyayyar da yakewa Fido. Issam ya rik'e Mum nasa gam yace "I really love her Mother, I so much love her. My Qalb only beats for her! She's my HAYAT Mother!" Rungume tilon d'anta tayi tana lallashin sa kamar yaro, tunani take meh yakamata tayi ta cece d'an ta. Sai can dabara yazo kanta tace "Son karka damu In Shaa Allah Fido matar kace" "Inaa Mother Fido tariga tamun nisa" "In Shaa Allah, katashi kashiga d'akin ka kayi freashing up" "Ohk" Da k'yar ya iya tashi, yana cikin tafiya sai kawai taji daf mutum ya fad'i. Ba k'aramin girgiza tayi ba dataga ya fad'i kasa. Da gudu taje wajen tana girgiza shi tana cewa "Issam habeebi dan Allah ka tashi, na maka alkawarin zaka aure ta, ka tashi Fido is yours I promise" Amma inaa koh numfashi bayayi, a guje ta fita tayiwa masu gadi da aiki magana nan sukazo suka d'auke shi suka saka shi cikin mota sai asibiti. Ana kaishi likita suka rik'e shi emergency, ganin likita ya fito a operation room d'in Mum a guje ta samu likitan tace "How was he Dr? "Karki damu In Shaa Allah he'll be OK, but inaso idan mun gama ki same ni a office" "Ohk ba matsala, but yanxu zanyi tafiya katsina In Shaa Allah idan nadawo a yau d'in nan zan same ka" Dr mamaki neh yacika shi ace d'anta rai hannun Allah tana maganan zatayi tafiya yace "Zakiyi tafiya kuma? Kinsan irin halin da d'anki yake ciki kuwa? Koh ba d'anki baneh?" "He is my son nasan me nakeyi, bye" Ta juya a guje ta samu driver ta Bala, tace "Bala k'arfe nawa yanzu?" "Tara cif Hajiya" "Kaimu Katsina banson wani magana kashiga muje" Take suka shiga motar sai Katsina, cikin awa d'aya sai gasu a KT sabida yayi gudu sosai, k'iran number Eesha tayi ta bata address na gidan tace idan taje anguwan tace tana neman gidan Professor Sanusi Umara Sodangi, zuciyan Mum neh ya buga jin sunan Prof. Sanusi Umara Sodangi, tunani take koh dai 'yarsa ce? Tana sake2 a ranta har suka iso anguwan. Gidan su Fido direct ta tsaya sabida gidan sananne neh sosai, tana shiga ta had'u da Aysha suka gaisa, Mum tace " 'Yan mata inane side nasu Fido " Aysha tayi murmushi tace "Muje na kaiki" Fido zaune take a parlour itada Inna suna cin biski da miyan kuka, Inna sai santi take tace "Ai idan bakwanan ba wanda zaiyi biskin nan" Fido tayi dariya tace "Kai Inna biski ma har abun so neh?" Aysha tashigo parlour tayi sallama, ganin bak'uwa a bayan ta Fido ta tashi tana sannu da zuwa ta nuna mata kujera ta zauna. Aysha tace "Adda Fido kinyi bak'uwa" Inna tace "Toh ikon Allah" Fido har kasa ta durk'usa ta gaishe ta, Mum tace "Lafia kalau 'yata" Daga nan Aysha tafita ta basu waje, Inna tace "Baiwar Allah daga ina?" Mum tayi murmushi tajuya tana kallon Fido tace "Kin ganeh ni kuwa Fiddausi?" Fido shuru tayi tana tunanin inda ta santa dan tabbas her face looks familiar, tunani take tayi taga ta kasa tunowa ta girgiza kanta tace "A'a wallahi ban ganeh ki ba" Mum tayi murmushi tace "Mun tab'a had'uwa sau d'aya a Maiduguri international airport, time d'in kuna tareda Issam, ni mahaifiyar sa ce" Wani mugun mamaki neh yacika ta, tunani take toh meya kawo Mum nasa kuma gidan su?. Inna tace "Ohhh sannu da zuwa 'yata, ashe ke mahaifiyar Issam ce, yaron kirki d'an albarka, ke Fiddausi maza tashi ki kawo mata abun motsa baki" Fido zata tashi Mum tace "Karki damu Inna, a yanxu da nake muku magana Issam yana asibiti rai a hannun Allah, na tabbata ciwon zuciya ke damun sa, kuma a dalilin Fiddausi" Inna ta kama baki tayi salati tace "Na shiga uku, Issam neh kwance a asibiti rai a hannun Allah akan wannan mummunar yarinyan, shi gashi kyakkyawa d'an balarabe yasa ma kansa damuwa? Inna lillahi wa inna Ilayhir Raji'un, akan wannan banza? 'Yata kije kizo da magabatan sa gobe za d'aura musu aure" Mum tace "a'a baza ayi haka ba, Fido sai ta yarda" Mum ta kama hannun Fido hawaye na sauka akan kuncin ta tace "Daughter nah duk abunda kikayi deciding dai-dai neh, I can't force you and nobody can force you, You've your own right to decide what's best for you. But ina rok'on ki da Allah ki cece d'ana, ina sonshi, ina matuk'ar sonshi, You're his HAYAT! Kinsan irin condition da yake yanxu kuwa? Dan Allah ki taimaka mini." Fido ba k'aramin mamaki tayiba ganin babbar mace tana mata kuka tana rok'an ta, amma zuciyan Fido koh karaya baiyi ba. Fido tana mai zubda kwalla ta share hawayen Mum tace "Don't cry please Mother, na amince, wallahi zan aure sa" Mum wani rungume ta tayi tana kuka tace "Nagode, Nagode" Fido wani irin murmushi tayi tace "Ba komai kar kimini godiya Mum" A zuciyan ta kuma cewa take "Kun kawo kanku gidan mutuwa! I'm gonna use this opportunity nayi shattering life na Issam" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 35``` Inna itama da guntun hawayen ta tace "Alhamdulillah Allah mungode maka! Fiddausi Allah miki albarka, Hajiya kinyi sa'a dan da yamma Sanusi zaibar k'asa yanxu muje a masa magana" Da Inna da Mum suka wuce part na Abba, a lokacin yana zaune yana kallon channel saudi suka yi sallama ya amsa musu. Mamaki neh ya cikasa da yayi ido hud'u da mahaifiyar Issam itama haka, yace "Hajiya Rumah? Ikon Allah kece wannan?" Zuciyanta ya buga da ganin sa, daman tun lokacin da aka bata address na gidan take sake-sake a ranta, last time dai tasan yana zama a Kd, murmushin dole tayi tace "Alhaji Sanusi rai kanga rai" "Bismillah" yace dasu duk suka zauna, Inna tace "Sanusi ina kasan Mahaifiyar Issam?" "Inna baki ganeh taba koh? Ai wannan matar Babangida ce, kin manta lokacin har kina zolayan sa akan yaje ya auro balarabiya mesa bai aura 'yar k'asar shiba?" Inna tayi salati tace "Ikon Allah, wannan matar marigayi ce? Ashe Issam d'an mu neh? Ahh shikenan abu yayi kyau" Nan dai aka samu akayi hira irin long time no see d'innan, sai can Inna tace "Sanusi kaji Ikon Allah wai d'an marigayi Babangida shi yakeson Fiddausi" Abba ya bud'e baki yana mamaki yace "Lalle kam abu yayi kyau nayi farin ciki da haka, ai lokacin anso a had'a Fiddausi da Issam sai duk suka nuna basaso, gashi yanxu Allah ya k'ara had'a su" Mum zuciyan tane yayi mugun tsinkewa addu'a takeyi Allah sa Fido ba 'yar marigayi Muhammad baneh, tayi k'arfin hali tace "Alhaji shin Fiddausi 'yar wajen marigayi Muhammad neh? "Eh wallahi 'yarsa ce" Bugun zuciyan tane ya tsanan ta, nan take wasu zazzafan gumi suke sauk'o wa akan fuskan ta dukda sanyin AC split, ji take kamar tace afasa maganar, da zata iya cire son Fiddausi aran Issam data cire dan sam Issam bai dace da Fiddausi ba, but lafian d'anta yafiye mata komai a rayuwa. Nan Inna ta zayyanawa Abba halin da Issam yake ciki, Abba yace "Ikon Allah haka abun yayi tsanani, Hajiya Rumah gobe ki turo da magabatan sa a gobe za'a d'aura masu aure a tafi da matarsa, daman da yamma zanyi tafiya but zanyi postponeding tafiyan " Hajiya rasa abun fad'a tayi, da k'yar ta kirkiro murmushin k'arya tace "Nagode Alhaji Allah bar zumunci" "Ahhh haba ba komai wallahi, gobe suzo" "Toh shikenan Alhaji, nizan wuce" "Toh shikenan Hajiya, Allah basa lafiya" Daga nan tafita tama Bala magana, nan suka kama hanyan Abuja hankalin ta duk a tashe, ta rasa abunda yake mata dad'i, a haka har suka iso cikin Abuja, asibitin direct suka wuce har zuwa lokacin Issam bai farka ba. Komawa gida tayi tayi wanka tayi sallah ta dafa abinci ta k'ara komawa asibitin. Daga nan Doctor ya nema ganin ta tahau office nashi, bayan ya nuna mata kujera ta zauna Dr Samaila yace "Amm Hajiya yaron ki is on very critical condition, but karki tada hankalin ki In Shaa Allah he'll be ok. Ammm abunda yasa nake neman ki shineh zuciyan yaron nan dab yake da bugawa, ina meh rok'an ki da ku taimaka ku masa abunda yake so" Mum ji tayi kanta yana juyawa da k'yar ta iya bud'e baki tace "In Shaa Allah Dr zanyi iya k'okarina" Komawa tayi ta zauna a wajen Issam wanda bacci yakeyi amma tana mai jin numfashin sa, rik'e hannun sa tayi gam tace "Habeebi ya zanyi? If only inada choice da bazan tab'a bari ka aura 'yar gidan mak'iyin muba, I don't know koh idan ka farka kaji labarin wacce kake so 'ya a wajen mutumin daka tab'a tsana neh, Ya Salaam!" tana meh zubda kwallah tacigaba "but ya zanyi? Tunda kana sonta dole na sota kuma laifin iyaye baya shafan yara" Washegari A garin Katsina da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren ISSAM BABANGIDA BADAMASI DA FIDDAUSI MUHAMMAD SODANGI a sadaki dubu hamsin!!! Wanda ango still unconscious bai farka ba! Fido ji tayi duniyan ya mata zafi, su Eesha, Shamcy Inna duk sai murna suke banda ita. 'Yan gidan kuma bak'in ciki kamar ya kashe su. Wani zazzafan hawaye neh suka sauk'a akan kyakkyawan fuskan ta tace "In Shaa Allah koh wata biyu bazan wuce a gidan shiba! Na rantse da Allah wallahi bazan barshi ba! Na rantse da Allah sai na masa abunda har ya mutu bazai manta ba!" Toh fa masu karatu Fido rantsuwan da tayin nan yana tsoratani, shin me zata masa???????? Ku biyo ni!!!!! By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 36``` Shamcy ce ta tab'a ta tace "Lafiya kike kuka Adda Fido? Share hawayen ta tayi tace "Kukan farin ciki nake Shamcy" "You sure?" D'aga mata kai kawai, Shamcy tace "By the way Yaya Aliyu yana miki magana yace ki same shi a d'akin Yaya Khaleal" Zuciyan tane ya buga tace "Yaya Aliyu kuma?" Shamcy ta maraice fuska tace "Eh shi, Dan Allah Adda Fido kije idan bakije ba bakisan me zai mini ba zaice ban fad'a miki baneh ya rankwashe ni" "Karki damu zanje" Mayafinta ta d'auka ta wuce boys quarters, d'akin Yaya Khaleal ta bud'e tareda sallama zuciyan ta yana mai tsinkewa, ganin sa tayi yana zaune akan kujera yayi crossing leg. Yana ganin ta take ya tashi yana wani irin shu'umin murmushi yace "Bismillah zauna amarya" tareda nuna mata kujera, zama tayi zuciyan ta name bugawa kamar zai b'ullo. Bayan ta zauna ya d'auko kujera ya zauna daf kusa da ita yace "Amarya kinsha k'amshi, wani irin gaggawa kukeyi da za'a d'aura aure haka? Koh dukkan ku a matse kuke? But kan a kaiki zan d'an sosa miki inda yake miki k'aikayi" Jawo ta yayi ta fad'a jikin sa yana mai son had'a bakin sa da nata, damke bakin ta tayi gam, yayi iya k'okarin sa amma ya kasa a karshe wurgi yayi da ita sai gata ta fad'i akan kujera, wani irin kuka ta fashe dashi tace "Mena maka a rayuwa neh Yaya Aliyu" Rik'e hannun ta yayi gama kamar zai raba k'ashin ta yana huci yace "Wato ma bakisan abunda kika mini ba koh? Kin amince zaki aure ni kawai dan ki tarwasa mini rayuwa koh? Kin amince zake aure ni bayan kinada wanda kike so, kin amince zaki aure ni sabida ki raba ni da abunda nafi so a rayuwata? Tuncan daman ina zargin dake da Issam, da kika kwana a gidan sa na tabbata ba irin jagolgolon da beyi dake ba. Da kika shigo gida nah kina saving jikin masa sai dai kash nariga na wanke rabo nah yanxu nabar masa fanko. Yaushe nema da rasuwar Basmah har zakiyi wani auren? Yaushe ma kika gama idda? Na tsane ki Fido! I hate you. Daman Meena tace zata kai k'ara court ina dakatar da ita but yanzu zance ta d'aura daga inda ta tsaya har sai kema kin rasa naki ran, Ki saurare sammaci very soon" Ya fita yabar mata d'akin, wani irin kuka ta fashe dashi, nan tayi mai isarta ta tattara tafita a d'akin. Aliyu direct part na Umma ya wuce, yaga basa parlour ya wuce d'akin Umma, tun a bakin kofa yake jin muryan Meena na cewa "Mtswww nayi a banza wallahi, ai nice da asara gashi yanxu zatayi auren ta wanda yafi Aliyun ma kud'i. Ni wai nakai mata magani yayi destroying mahaifan ta gashi 'yata ta mutu, asara bibbiyu" Nan yaji zuciyan sa ya buga, take yaja da baya a hankali yabar wajen. Fita yayi ya shiga motar sa amma ya kasa kicking, wani irin bak'in ciki yakeji, kifa kansa yayi akan siteri ya fashe da wani irin kuka. A ranar aka d'auka Fido aka kaita Abuja, gida neh had'add'e yasha kayan alatu amma koh burge ta baiyi ba. D'akin da aka ce mata nata babban gaske neh, komai na d'akin foreign tun daga kan gado har carpet. Zama tayi tana k'arewa d'akin kallo, Mum ce tashigo d'akin tayi sallama, Murmushi Mum tayi ta zauna a gefen ta tace "Daughter nah hope d'akin ki ya miki?" D'aga kanta tayi tace "Eh Mum yayi" "Ohk, ki huta yau sai gobe na kaiki wajen mijin ki dan yanzu its late k'arfe takwas ma ya wuce" "Mum zan iya zuwa yau" "A'a kibar shi gobe da sassafe sai a kaiki" "Your wish Mum ba komai" Shafa fuskan ta tayi tace "Saida safe, na saka a kawo miki abincin ki yanxu, ni zan wuce asibiti" "Nagode" "Ba komai, do take care! Goodnight" "Night" Mum fita tayi a d'akin, wani ajiyan zuciya tayi tace "Ina tausaya miki Mum, da kinsan abunda zanma d'anki da baki had'a auren nan ba" Cire kayan jikinta tayi tashiga toilet tayi wanka, bayan ta fito ta saka night wear ta, knocking na kofan akayi tace "Bismillah" Wata yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sha bakwai tashigo da tray na abinci, bayan sun gaisa tace "Sunana Dije, ni mai aikin gidan ce amarya" Fido murmushi tayi tace "Ki kirani da sunana Fiddausi" "Haba amarya" "Yeah nafison hakan" "Toh shikenan amarya" Bayan Dije tafita ta bud'e abincin, su fried rice, chips, chicken sauce, da pepper soup na kifi. Zama tayi tana cika cikin ta da abinci taji an bankad'o kofa, d'aga kan da zatayi taga S.A, wani irin mak'ure wuyan ta yayi fuskan sa ya canza kala yace "Wato ni zaki munafurta koh? Wato kin maida ni wawa mara hankali koh? Harda cewa wai na turo iyaye nah dan kin maidani dak'ik'i koh" Hawaye neh shar suke sauk'a akan kuncin ta tace "You are hurting me" Ta iya fad'a da k'yar, kare mak'ure wuyan ta yayi yace "I'll hurt you even more" Jin ana k'okarin bud'e kofan ya sake mata wuya da sauri ya lab'e a jikin kofa, Dije ce tashigo, Fido rik'e wuyan ta tayi tana wani irin tari, nan Dije ta zuba mata ruwa a cup tana mata sannu tace "Amarya sannu, meya same ki haka" Da k'yar Fido ta iya bud'e baki tace "Kwarewa nayi" "Ayyah sannu koh?" D'aga kai kawai Fido tayi, Dije tace "Amarya ga kunun madara na manta ban had'u miki d'azu gaba d'aya na kawo miki ba" "Ayyah ba komai nagode" Dije tana fita a d'akin S.A ya fito daga inda yake leb'e. Zuwa yayi daf da ita yace "Tun lokacin auren k'awar ki naga pictures naku kaca-kaca dake da mijinki a social media, but sabida kin raina mini hankali shekaran jiya harda cewa na turo kuma a lokacin na ganku tare tsaban kin raina miki hankali zaki ce mini baki sonsa? A bakya sonsa neh kika aure sa? Me yake dashi dani bani dashi? Me Aliyu yake dashi dani bani dashi? Idan ma kud'i neh sanin kanki neh duk nafisu, wani irin so da kulawa neh ban nuna miki ba Fido?" "Stop it Suleiman, bana son koh d'aya daga cikin su, ka yarda dani kaine zab'i nah" Wani tsawa ya daka mata yace "Just shut up!" Zuwa tayi daf kusa dashi hawaye yana sauk'a akan kuncin ta tace "Taya kake tunanin zanso mutumin da yake duka nah, mutumin da baya kula dani, mutumin da bai d'auke ni a matsayin komai ba, mutumin da bai yarda dani ba, mutumin da ya dake ni kuma yayi amfani dani ba tareda amincewa nah ba dukda yana miji nah?" Shuru S.A yayi yace "But kina son Issam, you can't lie to me, I can see that in your eyes that you love him" Murmushi Fido tayi tace "That's hatred you saw not love, do you really know how much I hate him? Na tsane shi, I hate him! A rayuwata ban tab'a tsanan wani ba kamar yadda na tsana Issam, do you know why?" "Don't fake any story Fido, karki mini k'arya nasan kina sonshi" "Idan kana fad'in ina sonsa wallahi wani bak'in ciki nakeji, tayaya kake tunanin zanso mutumin da shineh sanadin mutuwar mahaifi nah?" S.A kanshi neh ya d'aure yace "Ban ganeh abunda kike nufi ba?" Nan Fido ta bayyana masa abunda yafaru, har kuma shine dalin ta na zuwa UK tace "Bazan tab'a barin sa ba, just give me two months, wata biyu kacal zan rabu dashi, ZAN DAWO GAREKA I PROMISE!" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! *Wannan shafin naki neh Maman Nasiba!!! Allah ya raya mana yaran ki* ```Page 37``` Kwance yake akan kujera a parlour, ji yake zuciyan sa kamar an d'aura dutse mai nauyin gaske, duniyan ya masa zafi sai wasu zazzafan hawayen da suke sauk'a akan kuncin sa. Meena ce tayi sallama tashigo, dan tsaban bak'in ciki ya k'asa d'aga ido ya kalle ta, zama tayi a d'ayan kujeran da yake facing nasa tace "Moon of my life inata jira kazo ka d'auke ni shuru, nata kiranka a waya baka d'auka wa what happen?" Ji yake kamar ya tashe ya rufeta da duka dan bak'in ciki, ganin baida niyar amsa mata tace "Moon of my life dakai fa nake" Bud'e idanuwan sa yayi yana kallon ta, sai can da k'yar ya iya furta "Ki koma daga inda kika fito" "What! Me kake nufi?" Wani tsawa ya daka mata yace "Nace ki koma daga inda kike, kije na SAKE KI SAKI D'AYA" Hankalin ta tashe hawaye yana sauk'a kan kuncin ta tace "Yaya Aliyu mena maka? Mena maka da zaka d'auka wannan d'anyan hukunci?" Ta fashe da wani irin kuka. Tasowa yayi ya d'auke ta daga ita har jakarta ya fitar da ita a gidan sa, ya nuna ta da yatsa yace "Yanxu ba asara bibbiyu kikayi ba uku-uku kikayi. Na farkon shineh dalilin muguntarki 'yarki ta mutu, na biyu shineh mahaifanta kalau yake har koma tayi wani auren, na uku kuma shine mutuwar auren ki" Meena fashewa tayi da wani irin kuka ta durk'usa ta kama kafan sa tace "Dan Allah Yaya Aliyu ka taimaka mini, ka cece ni, kaine farin ciki nah, kaine jin dad'i nah, nasan na afka babban kuskure amma ka yafe mini wallahi zan gyara hali nah, wallahi ina k'aunar ka, ina masifan sonka, sonka neh sanadin abunda nayi, ka yafe mini dan Allah" "Bazan tab'a yafe miki ba Meena, bazan tab'a yafe miki ba. Kin kashe mini 'yata, kin rabani da masoyiyata, kin rabani da farin ciki nah, kin rabani da Fiddausi wanda a yanxu ta mini nisa sabida haka bazan tab'a yafe miki ba" Juyawa yayi ya shiga cikin gidan sa yaja door d'in. Kwanciya yayi a k'asan tiles yana mai wani irin nishi zuciyan sa kamar an zuba wuta. Tunanin irin wulakancin daya ringa mata yake, wasu zazzafan hawaye neh suke sauk'o wa yace "Ki yafe mini Fido, wallahi ina sonki, ina matuk'ar sonki, koda da rana d'aya ban tab'a tsanan ki ba kawai maganar baki neh, gashi yanxu kin mini nesa". S.A yace "Kin tabbata Fido, promise me you'll come back to me" Fido tace "I promise In Shaa Allah" Murmushi yayi yace "Nagode sosai Beauty, idan akwai abunda ya shige miki gaba just give me a call kinji? Ni bana k'auna ki zauna da wannan beast d'in" "Karka damu beast d'in bazai mini komai ba, bakaga koh a film d'in Beauty and the Beast ba?" "That's just a movie" Fido tayi murmushi tace "I know just kidding you, but karka damu In Shaa Allah bazai mini komai ba" "Ohk zan tafi, take care" "Aiit Thank you! Bye" Fita yayi a d'akin, yana fita tayi ajiyan zuciya ta zauna ta bud'e kunun madaran da Dije ta kawo mata ta fara sha tana lumshe ido. Bayan ta gama sha tayi brush da alwala tayi sallah daga nan tabi lafiyar gado.... Washegari da safe bayan tayi sallah ta shirya cikin riga da skirt atamfa super mai kyaun gaske ta yafa mayafin ta, ba k'aramin kyau tayi ba. Mum ce tayi sallama tashigo d'akin tana murmushi tace "Wow kinyi kyau" Fido rufe fuskan ta tayi da tafin hannun ta tana murmushin k'arya. Mum ta kama hannun ta suka zauna bakin gado Mum tace "Kinsan mai yafaru jiya?" Girgiza kanta tayi, Mum tace "Ina fad'a wa Issam an aura masa ke nan take ya farka, Fiddausi Issam yana sonki sosai dan haka ina rok'an ki dan Allah don't ever betray him cox it will break him into million piece of broken glass please" "In Shaa Allah Mum" Rungumeta Mum tayi tace "Nagode 'yata, Allah miki albarka" Daga nan driver ya kaita asibitin, tana shiga d'akin ta gansa kwance yayi uban rama kamar ba Issam ba, zuwa tayi kusa dashi tana mai k'are masa kallo "Tun jiya na k'asa samun nutsuwa, ina cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, I can't really tell you how happy I am" tareda bud'e idon shi k'yar a kanta wanda tayi mugun tsorata dan ta d'auka yana barci, yace "Don't move back Hayaateey! Come closer to me" Tsayawa tayi cak a inda take, da k'yar ta iya bud'e baki tace "How do you know nashiga d'akin kuma nice?" Kirjin sa ya nuna mata yace "Zuciyata, my heart! A duk ranar da zan had'u dake sai zuciyana ya fad'a mini, kinsan dalili?" Girgiza kanta tayi, murmushi yayi yace "Because you are my HAYAT! Kece RAYUWATA" Rasa abun cewa tayi, kujera ya nuna mata yace "Ki zauna please karki gaji da tsayuwa" Ba musu ta zauna, kallon ta yake baya koh kifta ido, ganin kallon bana k'arewa baneh tace "Ga breakfast na kawo maka" Murmushi yayi yace "Are you the one that cooked it?". Girgiza kanta tayi, yace " Naso naci abincin da kika girka da kanki but duk da haka bai b'aci ba you will feed me with your own hands" Had'a masa tea tayi mai k'auri da chips da kwai ta mik'a masa tace "Kaci" Murmushi ya mata yace "Feed me with your own hands" Had'a rai tayi tace "Idan baza kaci ba ka barshi, ance mini you're critically sick baka iya koh magana nazo naga sab'anin haka" Tasowa yayi ya zauna mai kyau yace "Duk wanda ya fad'a miki haka toh da gaske neh, banida lafiya sabida rashin ki, but tunda na sameki ai na warke, yanxu garau nakeji" Wani dogon tsoki taja tace "Sai katayi ai, ashe zaka kwana da yunwa idan har ni zan baka abincin" "Haka zakice?" Koh amsa masa batayi ba ta d'au wayarta a jakarta ta kunna data ta fara chating abunta tareda tusa chewgum bakin ta tana kas-kakas. Ido ya zuba mata yana kallon ta, baisan dalilin dayasa yake jin sonta har cikin ransa ba. A haka har zuhur yayi baici abincin sa ba, wata Nurse ce tashigo d'akin bayan ta gama dubasa tace "Kasha maganin ka yau kuwa?" "Eh nasha but yanxu ina jin dizziness sosai" "Kaci abinci?" "A'a" "What! Bakaci abinci tun safe ba? Why? Wannan datake zaune take danne dannen waya wacece da bazata baka abinci ba?" Murmushi yayi yace "She's my wife" "Matar ka? A'a dai wasa kake mini ai ba matar da zata bar mijin ta da yunwa koh lafiyan sa kalau balle kai da baka da lafiya" Wani mugun harara Fido take masa, Nurse d'in zama tayi ta d'eba abinci zata basa a baki ya girgiza mata kai yace "Mik'o mini kawai zan iyaci da kaina" "Zaka iya?" "Zan iya don't worry" "Ohk toh ba komai" Tasowa Nurse d'in tayi tace "Issam dear please next time kar a turo masu aiki haka wanda basuda aiki sai na chating bayan an biyasu dan suzo suna kula da mara lafiya" Wani uban tsaki Fido taje tama rasa mai zatace idan ba rainin hankali ba taga tayi kama da mai aiki neh, Nurse d'in bata kula Fido ba tace "Issam dear sai anjima" Murmushi yayi yace "Nagode sosai, bye" Tana fita ya fashe da dariya Fido kuma sai hararar sa take tace "Wallahi nan gaba idan ta kuma ce ni 'yar aiki sai ta raina kanta, after all gwara ma ta d'auke ni 'yar aiki akan ta yarda ni matar ka" Kallon ta ya tsaya yi yace "Sabida meh? Sabida kinfi k'arfin a k'iraki da matata?" "Eh" ta basa amsa a takaice, murmushi yayi yace "I am proud to call you my wife, so very proud. Ina alfahari dake, bazan tab'a gajiya da godewa Allah daya bani ke a matsayin matata ba, inaso ki sani ina sonki kuma zan jure duk wani wulak'ancin da zaki mini, ina ji a raina wata rana zaki soni, zaki soni fiye da yadda nake sonki!" Wani dogon tsaki taja tace "Wallahi bazan tab'a sonka ba, you have no idea irin abubuwan dana tanadar domin ka sabida haka kar kace zaka juri duk wulak'ancin da zan maka sabida bazaka iya ba" Kuyi hak'uri kunji ni shuru kwana biyu wallahi zirga zairgan asibiti nake Anty nah ba lafia #MunaMugunTare❤ By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 38``` Murmushi yayi yace "Wow! So much hatred! Why?" Koh basa amsa batayi ba ta tashi tashiga toilet tayi alwala, shima tashiwan yayi da k'yar ya shiga toilet dan alwala. Bayan duk kansu sun idar Dije ta kawo musu abinci ta gaishe su tace "Ni zan koma gida Allah k'ara sauki" "Ameen nagode Dije" Fido kuma koh k'ala bata ce ba, Dije tana fita a d'akin ta janyo tray na abincin ta d'eba iya wanda zata iyaci tafara ci abunta, Issam kam sai kallon ta yake yana murmushi, bayan ta gama ci yace "Nima ki zuba mini naci" D'auko wani plate zatayi ta zuba masa yace "Zuba mini a plate da kika ci" Ba musu ta zuba masa ta mik'a masa, yana ci yana kallon ta abun haushi yake bata, dogon tsaki taja tace "Wai cin abinci kake koh kallo na? Wallahi na tsana kallon nan kallo sai kace maye" "Kika sani koh mayen neh?" "Ahhh kam gaskia ba shakka dan kayi kama da su" Murmushi kawai yayi ya cigaba da cin abincin sa itama sai faman chating take da wayar ta. Da misalin k'arfe hud'u na yamma Dr yazo ya duba sa yaga yasamu improvement sosai yace zai rubuta masu takardan sallama, wani relief da dad'i taji sabida ta tsana zaman asibitin. Daga nan Issam ya kira driver dan ya maida su gida, cikin minti goma har Fido ta gama had'a kayan d'akin, sai kallon ta yake yace "Kin matsu ki koma gida koh bakison zaman asibiti?" "Na tsana zaman asibiti" Murmushi yayi kawai ya barta, can sai ga Bala driver yazo ya kwashe kayan su suka shiga mota sai gida. Mum ba k'aramin farin ciki tayi ba data ga d'an ta har ya warware, tace "kashiga d'aki kayi freashing up Fido jeki ki taimaka masa" "Toh" Mum tace "Inaga ma yau Fido zata koma side naka tunda ka dawo gida zansa a kawo miki kayan ki can" Wani bakin ciki neh ya rufe ta but ta rasa abunda zata ce, wuce part nasa sukayi, babban parlour neh da d'aki d'aya shima babban gaske, sai toilet da kitchen. B'ata rai tayi tace "Yanxu anan zamu zauna?" "A'a ana gyara mini gida nah na KT nan da sati d'aya zamu koma can" Wani relief taji dan tasan idan suna gida d'aya tareda mahaifiyar sa bazata iya aiwatar da abun da tazo domin shi ba, yace "Nasan kina aiki and you love your job, kuma baki karb'a leave ba sabida abun yazo a gaggawa. Nima inada aiki a company nah na KT idan yaso kan nagama zan nema miki lecturing a Nile In Shaa Allah zaki samu" "Karma ka wahalar da kanka dan ni sam zaman abuja baso nake ba" "Baso kike ba amma dole ki zauna sabida mijin ki a garin yake" Wani kallo ta watsa mishi tareda jan dogon tsaki ta shige ciki. Bayan yayi wanka ya canza itama haka yace "Zanje masallaci sai bayan isha zan dawo" "Uhum" kawai tace ya girgiza kansa yafita yana takawa da k'yar, itama fitan sa tayi alwala tayi sallah. Sai bayan Isha'i yadawo gidan lokacin tana kallon wani series a AMC Into the badlands, bayan ya zauna na minti biyar yace "Kizo muje wajen Mum muci dinner" Girgiza kanta tayi tace "Kace wa Dije ta kawo nan ni bazan je can naci ba" Bai musan ta taba ya d'au wayarsa ya kira Dije yace "Ki kawo mana abincin mu nan" ya katse wayan. Cikin mintuna biyu sai ga Dije tayi sallama ta shigo da abincin. Dira musu tayi a gaba tace "Yaya Issam ga abincin, ya jiki?" "Da sauki" "Toh Allah k'ara sauki" "Ameen Dije nagode" yana maganar kamar wanda akasa sa dole, wani uban tsaki taja nan take duk suka zuba mata ido suna kallon ta, Dije nan take ta tashi tabar musu fili, Issam ya b'ata rai yace "Ni wai ke 'yar tasha ce?" "Cikikkiya ma kuwa" "I seee" Da daddare tayi ta saka bump shot da wani d'an guntun riga, baza gashin ta tayi wanda tsawon sa har kafad'a. Sai wani shan k'amshi take taje ta dawo, Issam tunda ya d'aga kai ya kalle ta sau d'aya bai k'ara kallon taba. Kwanciya yayi akan gado yana karanta hisnul muslim, zuwa tayi ta tsaya masa a ka ta aza hannu a kwunkoso tace "Zan kwanta" Can gefen gadon ya matsa yace "Bismillah kwanta" Dogon tsaki taja tace "Tare zamu kwana a gado d'aya kake nufi?" "Eh" tareda bata amsa a takaice. "Nidai wallahi Allah bazan kwana gado d'aya dakai ba" Tasowa yayi yace "Ki kwanta" Kwanciya tayi akan gadon shi kuma yayi shimfid'a a k'asa ya kwanta yace "Don't forget to recite Suratul Mulk before sleeping" "Toh sannu Mallam toh ni ban iya ba" Shuru yayi bai k'ara cewa komai ba, kusan mintuna talatin da kwanciyar ta ya tashi ya d'au stool ya zauna kusa da gado ya karanta mata Suratul Mulk ya tufa mata duk tana jinsa shi a tunanin sa tayi bacci. Daga nan ya koma shimfid'an sa ya kwanta bacci. Da asuba a hankali yake buga gefen gadon, bud'e eyes nata tayi a hankali ganin sa datayi a tsaye akanta taja uban tsaki tace "Menene kuma?" "Subh Hayateey" "Toh sannu Sudeis" "Bud'e idonki da kyau shureim neh" Wani uban tsaki ta k'ara ja tareda tasowa akan gadon ta shige toilet tayi alwala, bayan ta fito ya mik'a mata hijabi ta karb'a ba musu yaja su sallah, bayan sun idar yaringa karato addu'a ita kanta ba k'aramin mamaki tayi ba, sai cewa take a zuciyan ta ashe haka yake da illimin addini? Sai can kuma tace ilimin addinin da baya amfani dashi toh meh amfanin sa?. Cire hijabin jikin ta tayi bayan ta shafa addu'an tana k'okarin kwanciya yace "Me kike shirin yi?" "Abunda idon ka yagani maka" "Karki kuskura kice zaki koma bacci ki bari rana ya fito" "Karna koma bacci na maka meh toh" "Ki karanta Qur'an" Zatayi magana ya daka mata tsawan daya firgita ta yace "Bana son musu" Haka ta taso akan gadon ya mik'a mata Al Qur'ani ta amsa, haka ta ringa recieting har sanda rana ta fito ta ajiye ta koma baccin ta, ita kanta taji zuciyan ta yayi sanyi. Da safe bayan tayi wanka ta tsara kwalliya sai zirga-zirga take daga parlour zuwa d'aki dan kawai ya ganta, shi kuma koh d'aga kai baiyi ba balle yasan ma tanayi. Can kusan k'arfe goma tana zaune tayi crossing leg a parlour tana kallon film a HBO channel Game of Thrones Issam yashigo yace "Hayateey tashi ki d'au mayafinki muje mu gaida Mum" Bud'e baki tayi tana kallon sa sai can tace "Tab! Wace Mum?" Shuru yayi yana kallon ta ya kasa cewa komai, wani dogon tsaki taja tace "Kaga Mallam ni yunwa nakeji a kawo mini abinci naci" Shuru yayi yana kallon ta sai can ya d'au wayarsa ya latsa number Dije, tana picking yace "Dije please ki kawo mana breakfast namu nan" ya katse wayan. Cikin two minutes sai ga Dije tashigo da tray na abinci, tace "Amarya kin tashi lafiya?" "Idan ba lafiya ba ai baza ki ganni haka ba" Shuru Dije tayi tace "Yaya Issam gashi nan na kawo" "Yawwa Dije nagode" Dije tana barin parlour Fido taja tray d'in gabanta ta zuba abinci tana ci tana kallon ta, shidai Issam girgiza kansa yayi tareda fita a parlour. Bayan Sati D'aya Fido ta gaji da zaman gidan, tabbas tasan idan har suna zaune a gidan su Issam bazata iya aiwatar da komai ba. Gashi yanxu lamarin Issam yana bata tsoro, takan tambaye kanta anya Issam namiji neh kuwa? Idan ma namijin neh toh tabbas bashida lafiya sabida kullum tana cikin saka k'ananan kaya masu bayyanar da tsadadden surar ta amma koh d'aga kai bayayi ya kalleta balle har ya tunkare ta da wani abu. Wani irin kuka ta fashe dashi tareda aza hannu a kanta, Issam dake parlour take yashigo cikin d'akin ya durk'usa zai tab'a ta tamasa wani irin tsawa "Don't touch me with your filthy phalanxes" Maida hannun sa yayi ya zauna kusa da ita hankalin sa duk a tashe yace "Meya faru Hayateey? Mesa kike kuka" "Gida" "Gida kuma Hayateey?" "Aiki nah" "Ohhh so sorry! Karki damu Hayateey gobe In Shaa Allah zamu koma KT kinji? Yanxu ma zan tattara miki kayan ki please don't cry! If you cry it will break my heart" "Promise?" "I promise" Fita yayi a d'akin yace bara na sanar da Mum, tun lokacin da tabar part na Mum koh da wasa bata k'ara shiga wajen ta da sunan zata gaishe taba, bata tab'a girki ba saidai a kawo mata. Wani shu'umin murmushi tayi tace "Had it been kasan abunda nake niyan aikatawa a kanka hmmmmmm" Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 39``` Mum tana zaune a d'akin ta laptop akan cinyarta Issam yashigo da sallama, duk'usawa yayi har kasa ya gaishe ta, amsawa tayi da fara'ar ta tace "Son ya akayi?" Sosa suman kansa yayi yace "Amm Mother daman Fiddausi ce takeso ta koma wajen aikin ta dan bata karb'a leave ba and kuma nima inaso naje na duba gidan mai na KT da company nah" Mum ajiyar zuciya tayi tace "Son zo ka hau kan gado" Tasowa yayi ya zauna a bakin gado kusa da ita yana facing nata, hannun sa ta kama tace "Son akwai abunda nakeso na fad'a maka, but farko lemme ask you something" Hankalin sa gaba d'aya ya tattaro zuwa gareta yace "Ohk Mother" "Shin kasan asalin Fiddausi? Kasan baban ta?" Girgiza kansa yayi yace "A'a Mother bansan shiba, but ai ya rasu" "Kasan sunan sa?" "Eh Muhammad" "Muhammad wa?" "Gaskia Mum ban sani ba" "Asalin sunan matar ka Fiddausi Muhammad Sodangi" A take ya taso tsaya yace "What!? Mum are you sure? No that's not true" "Bazan fad'a maka abunda i aiin't sure of ba, naje gidan su da kaina, mun had'u da wan baban ta Sanusi, nasan shi farin sani" Wani gumi neh yake sauk'o wa a goshin sa duk da sanyin AC split na d'akin, ya rikice iya rikicewa, Mum ta zaunar dashi tace "Son laifin uba baya shafan d'a, so inaso kayi hak'uri ka zauna da ita, ka mini alkawarin bazaka rabu da ita a wannan reason d'in ba" Kaman hannun Mum yayi gam yace "Mother I told you, She's my HAYAT! Bazan iya rabuwa da itaba, ina son ta, so na hakik'a" Murmushi Mum tayi tareda shafa fuskan d'anta tace "Allah maka albarka, Allah kawo zuri'a nagari" Da k'yar ya k'wak'ulo murmushi yace "Thank you Mum" "Gobe In Shaa Allah zanzo mu gaisa da amaryan kan ku tafi" "A'a Mum karki zo zatazo ma ta gaishe ki In Shaa Allah" "Ba komai Son zanzo" Murmushi yayi yafita a d'akin, koh da yazo tana parlour tana danne-danne da laptop nata ya shige d'aki hankalin sa duk a tashe, zama yayi dirshan a k'asa ya rasa abunyi, sak'e-sak'e yake a ransa, yace "Anya yarinyan nan bata ganeh niba?" Cusa kansa yayi cikin cinyoyin sa sai can atake yaciro kansa yace "Wallahi nacire mask nah that night, she saw me! She saw my face! Tasan ina cikin wanda muka shiga gidan su, Inna Lillahi Wa Inna Ilayhir Raji'un!" Safa da marwa yake a cikin d'akin, sai can yace "Tabbas tasan ni neh, Tabbas yaransa mata biyu neh lokacin da muka shiga gidan! Anya ba revenge tazo yi ba? Anya duk had'uwan da muke da ita ba shirin ta baneh? Anya bata aure ni da wata manufa ba?" Sai can yace "No! Duk accidentally muke had'uwa, and kuma bata aure ni sabida ta ganeh ni ba, da ta aure ni sabida wata manufa neh da tun tuni zata amince ta aure ni, ita zata kai kanta waje na ma, she'll beg for my attention but she never" Zama yayi dirshan a k'asa yace "Allah gani gareka! I really must have to keep eyes on her idan ma tasani, idan kuma bata saniba dole nah fad'a mata, I must tell her, I can't hide this to her, bazan b'oye mata ba, but ba yanxu zan fad'a mata ba har sai ta kamu da sona, har sai tanajin ajikin ta bazata tab'a iya rabuwa dani ba, dole tasan gaskiyar maganan, and kuma idan ta sani fa?" Nan take ya taso yace "Where on earth did I kept the CD plate?" Dube dube yafara a d'akin, tun daga kan wardrobe har k'ark'ashin gado, sai can yaja dogon tsaki yace "Yeah! Yana d'akin Mum" A guje yafita a part nasa zuwa main side d'in, d'akin Mum yashiga da gudu zuciyan sa yana bugawa addu'a yake Allah sa yasamu abunda ya b'oye, a lokacin Mum tana toilet, can k'asan wajen gadon ta ya buga da guduma sai ga wani safe, take ya d'au safe d'in ya latsa passport ya bud'e, wani CD plate neh a ciki, nan take yayi ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah Ya Allah" Cikin wardrobe na Mum ya bud'e ya ajiye akwatin yafita a d'akin, komawa b'angaren sa yayi har lokacin Fido tana zaune yadda ya barta, wani kallo tabishi dashi tace "Idan ba lafiya kake ba hope akwai psychiatric a Abuja?" Koh kallon ta baiyi ba yashige d'akin, a haka har dare yayi duk jikin sa a mace, Fido ma ta lura da hakan tana ganin kamar wani abu na damun sa, har dare yayi bataga yana shirya kaya ba, zuwa tayi ta same shi tace "Wai mun fasa tafiyan gobe neh?" "Why asking?" "Naga baka shiri" "Idan banyi shiri ba ke baza kiyi ba? Afterall ni akwai kayana a can kuma akwatin ki na aure gobe za'a kawo KT kinsan a Dubai Mum ta bada kud'i a had'u miki, so kibar kayan ki na nan kawai and please bana son surutu ki barni" Dogon tsaki taja tace "Kaika sani" ta bar wajen, haka bai kwanta ba yana ta sak'e-sak'e a ranshi, Fido kwanciya tayi ta rufe idonta amma ba baccin take ba. Can kusan k'arfe d'ayan dare ya tashi yaje daf kusa da ita dan ganin koh tana bacci, ganin tana bacci yasa yafita a d'akin a hankali, yana fita ta bud'e idonta itama ta taso daga kan gadon tabi bayan sa a hankali, gani tayi ya fita nan take ta lek'a window taga yashiga side na Mum, tunani take meh yake shirin aikatawa? What is he up to?, kusan minti biyar da shigan shi taga yafito da k'aramin akwati a hannun sa, nan take ta shige d'aki ta kwanta kamar tana bacci, shigowa d'akin yayi a hankali ya bud'e akwatin sa na kaya ya ajiye safe d'in aciki ya kulle ya koma shimfid'an sa duk tana kallon sa, tunani take toh meh a cikin safe d'in da yake b'oyewa bayaso kowa ya gani? Da tunanin haka a ranta har bacci ya d'auke ta. Washegari By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 40``` Tunda suka idar da sallah subh sukayi reciting Qur'an daga nan ba wanda ya k'ara komawa bacci, wardrobe ta bud'e tafara kwashe kayanta Issam yace "Bana fad'a miki akwai akwatinan ki a KT ba? Mesa baza kibar wa'yannan ba kuma kinsan nan zamu dawo permanent da zama komin daren dad'e wa" "Kaga Mallam wallahi koh towel na bazan bari a gidan nan ba kaji na rantse" tacigaba da kwasan kayan ta, shi kuma akwatin sa d'aya k'arami kawai ya d'auka wanda safe d'in yake ciki. 7:00am duk sun gama shiri, bayan sun saka kayan su a mota Mum tafito da fara'ar ta tace "Har kun shirya?" "Eh mun shirya Mother" Fido kunyan matan neh ya cikata dan kusan sati d'aya kenan bata shiga ta gaishe taba, koh ba komai d'anta neh ya mata laifi ba itaba, har k'asa ta durk'usa ta gaishe ta Mum ta amsa tana murmushi tace "Idan kinje gida kice ina gaishe su kinji Daughter?" "Zasuji In Shaa Allah Mother" Shiga motar sukayi Issam yajasu, Mum sai bye-bye take musu da hannu har suka b'acewa ganin ta. Tafiya suke ba wanda yacewa wani k'ala, Issam shurun ya masa yawa ya kunna wa'azin Sheik Ja'afar, wani uban dogon tsaki taja tayi mumbling "An kunna wa'azi sai kace wani mutumin kirki" "Me kika ce?" "Da kaina nake magana ban kira sunan kowa ba Mallam" Ku k'ara kulata baiyi ba har suka iso cikin KT misalin k'arfe d'aya, direct gidan shi ya wuce, gidan da bazata tab'a mantawa ba a rayuwar ta, mai gadi neh ya bud'e musu gate, bayan sun sauk'a suka gaisa da mai gadin ya bud'e masu gidan, gidan gaba d'aya an canza masa kamanni an tsara shi ya had'u iya had'uwa, a tsiwace tace "Mallam ina d'aki nah nifa nagaji da tsayuwa" "Zo muje" Ba musu ta bisa, wani kofa ya bud'e, wata had'ad'd'en parlour nagani wanda yaji foreign kujeru da komai na ciki, ita kanta parlour ya burge ta amma ba daman yabawa, bayan sun shiga akwai wani kofa by the right, bud'e mata yayi yace "Mss Contour ga d'akin ki" Hararan sa tayi tace "So can you please excuse me?" "Sure why not?" Ya juya ya bar mata b'angaren ta, shiga cikin d'akin tayi tana yaba kyawun sa, a rayuwar ta bata tab'a mallakan d'aki irin haka ba, a can gefe kuma ga akwati ashirin da had'u, zama tayi tana duba kayayyakin, tun tana dubawa tana yabawa a zuciyar ta har tagaji ta ajiye tace "Tab! Ai wallahi bazan bar gidan nan ba sai da kayana" Cire kayan jikin ta tayi ta fad'a toilet tayi wanka tayi alwala, bayan ta fito ta ciro doguwar riga material Red da black mai kyaun gaske tasaka ta zura hijabi tayi sallah. Bayan ta idar ta zauna a gaban mirror tasha powder da lip gloss ta d'au wayarta ta latsa number S.A, yana d'auka wa tace "Gani nan a KT fa kace mun kana nan koh zamu had'u neh?" Can yace mata "Kina ganin ba matsala?" "Kaidai kazo ba komai zan maka texting address na gidan" "Ohk gani nan" ta katse wayan ta tura masa address na gidan. Wani uban yunwa takeji amma ta dake ta zauna, minti talatin da wayar su sai ga S.A ya kirata a waya yace "Gani nan inda kika mini kwatance" "Ohk gani nan fitowa" Mayafi ta d'auka tafita a gidan ba koh tsoro ganin ba motan Issam ya tabbatar mata yafita, a waje ta same sa cikin motar sa ta masa nuni da hannu akan yafito, da murmushin sa yafito yace "Beauty har kin tsorata ni, irin wannan kyau d'in anya?" Dariya tayi tace "Ai dole tunda ina gab da aiwatar da abunda nayi alkawari, mushiga daga ciki" "Kinsan hakan bai dace ba koh? "Kuma tsayuwa ta anan a waje bai dace ba please mu shiga" Bin bayan ta yayi suka shiga cikin gidan, part nata suka shiga suka zauna a parlour, shi kanshi S.A gidan ya burge sa duk da yana shiga wanda suka fi haka, yace "Yanzu meh kike shirin aikatawa" Murmushi tayi tace "Kar ka damu, har ma ina ce maka nan da two months, ashe ma yayi yawa, nan da one week In Shaa Allah zan fito" "Why not mukai k'aran shi, why not we should sue him?" "I don't have any prove" "Hope you're not trying to kill him" Murmushi tayi tareda girgiza kanta tace "I won't even try to, but abunda zan masa sai mutuwan ta fiye masa" "Please if you need any help just give me a call" "Ohk I'll" Issam ya dawo kenan yaga mota a bakin gate nasa, horn yayi mai gadi ya bud'e masa kofa yace "Baba an shigo gidan neh?" "Eh kunyi bak'o" Issam bai k'ara cewa komai kawai yaga S.A yafito a gidan sa, Issam wani b'ata rai yayi S.A koh a kwalan sa yafita a harabar gidan. Mallam Iro yace "Alhaji wallahi na d'auka abokin kane shiyasa na barsa yashigo" "Ba komai Baba, d'an uwana ne kawai mun samu misunderstanding neh" Kwashe ledojin da yazo dasu yayi ya shige cikin gidan, d'akin ta direct yashiga yaga tana kwance akan gado ido ta a rufe, jin k'amshin turaren sa ya tabbatar da ita yashigo d'akin tace "Mallam yunwa nakeji fa" Wani tsawa ya daka mata yace "Me yakawo shi gida nah Fido" Wani dad'i taji dan da gayya ma ta gayyace S.A gidan, b'ata rai tayi tace "Abunda kake tunani" A tsawa yace "Idan ma bakya so nah ai at least kiyi respecting auren mu" d'ago ta yayi ya nuna ta da yatsa yace "Wallahi Allah nan gaba idan na gansa a gidan na sai na k'ark'arya ku" Kama yatsan tayi ta lankwasa tace "Wallahi nafi k'arfi ka nuna ni da yatsa, baka kai ka nuna ni da yatsa ba kaya kad'an" Zuwa yayi daf kusa da ita zai rik'e hannun ta a tsawace tace "Don't you dare touch me with your filthy hands useless being" Maganan a ransa ya tsaya masa, a duniya ba wanda ya tab'a gasa masa magana kamar ita, a duniya ba wanda yake sakasa yawan magana sai ita, wani kamota yayi ya had'ota da jikin sa gaba d'aya ya rungume ta da k'arfi wanda bazata iya kwatan kanta ba, yace "Yanzu not only my filthy hands ya tab'a ki har filthy body nah Hayateey" Duk k'okarin ta na ganin ta kwace kanta amma koh k'wakk'waran motsi bata iyayi, a haka yake tafiya da ita har suka zube akan gado yana nan matse da ita gam, lips nata ya nema ya had'a da nasa yana kissing nata roughly har wani cizon ta yake, damke idon ta tayi tana hawaye, wani irin bak'in ciki takeji mara misaltuwa, sanda yagaji dan kansa ya kyaleta yace "Nan gaba zan miki fiye da haka Mss Contour, ki kiyaye bakin ki" Wani irin kuka ta fashe dashi tace "I hate you! Na tsane ka, inglorious bastard kawai, stupid useless being, stray dog!" Duk da yaji zafin zagin yazo daf kusa da ita ya shafa fuskan ta yana murmushi yace "Hayateey ga abincin ki nan kinji and kuma idan bai miki ba akwai kitchen har biyu a gidan kishiga ki dafa" "Bazan ci ba! Mugu azzalumi kawai, castrated animal" "Oshhh Hayateey! Castrated animal? Lemme show you that I ain't castrated" Zuwa k'ofa yayi yayi locking, ba k'aramin tsorata tayi ba da taga ya rufe kofar, murmushi yake yana kallon ta yana zuwa kusa da ita, ita kuma tana komawa baya har takai jikin bango, kamota yayi ya damke ta da k'arfe ya had'u jikin sa da nata, wasu zazzafan hawaye neh suke sauk'a kan kuncin ta, bai tsaya cire kayan jikin taba kawai yasa hannu ya yaga rigan tun daga sama har k'asa, ya rage daga ita sai bra, rungumo ta yayi da k'arfi wanda har tana jin zafi sosai, a haka ya cire wandon jikin sa, ya kwantar da ita kan gado, wani irin damke idon ta tayi sai hawaye shar suke sauk'a kan kuncin ta gashi Issam d'an k'aran k'arfi neh dashi koh motsi bata iyayi, ganin hawayen fuskan ta yayi murmushi ya taso daga jikinta ya d'au wando sa yasa wanda har yanxu idonta a damke, shafo fuskan ta yayi yace "Hayateey bud'e idon ki mana" A hankali ta bud'e eyes nata ta sauk'e akan sa, murmushi yake mata yace "Hayateey banson raini, if you repeat that again zan miki abunda bakya so, dan haka ki kiyaye ni kinji?" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 41``` Tufa masa miyau'n bakin ta tayi tana hawaye tace "Bazan tab'a yafe maka ba k'azami kawai" Murmushi yayi yace "Mss Contour ai kece babbar k'azamiya tunda kika tufa mini miyau a jiki nah" Wani dogon tsaki taja tace "Aww daman so kake na had'iye wannan kayan k'azantan" Dole kuwa ki had'iya, zuwa yayi daf kusa da ita zata kurma ihu ya had'a bakin sa tareda nata had'e da damk'o hannun ta, sanda yayi kissing nata iya son ransa ya sake ta, wani irin bak'in ciki neh ya cikata nan take ta fashe da wani irin kuka, rungumo ta yayi sosai ya matso ta ajikin sa yace "Don't cry Hayateey, I really don't wanna see you cry" Da k'yar da iya furta "You're hurting me!" "Oshhh! Sorry" ya raba jikin sa da nata, har yanxu hawaye take, zuwa yayi daf kusa da ita tana ganin haka ta damke bakin ta tarufe shi gam ita duk a tunanin ta kissing nata zaiyi tareda rufo idonta, murmushi yayi yafara lashi hawayen da suke sauk'o wa a kuncin ta, nan take ta bud'e ido zatayi magana yace "Idan kika kuskura kika bud'e bakin ki kinsan mai zai biyo baya" Jin haka yasa tayi tsit bata k'ara cewa komai ba har sanda ya lashe hawayen tas yace "Karki k'ara kuka kinji Hayateey?" D'aga masa kai kawai tayi yayi murmushi yace "Yawwa ga abinci na kawo miki kinji, banson zaman ki da yunwa" nan ma d'aga masa kai kawai tayi yace "Ni zan fita anjima kad'an zan dawo" "Ohk" ta amsa masa da k'yar, yana fita a d'akin take tabi bayan sa tace "K'azamin namiji kawai, wallahi ban yafe maka ba!" Tana ganin ya juyo nan take ta rufe kofan tasaka lock, zama tayi dirshan a k'asa ta fashe da wani irin kuka, yi take har sanda tagaji dan kanta tashige toilet ta ringa goge jikinta da soso, bakin tama yafi sau hamsin tana saka toothpaste tana brush.... Bayan ta fito ta d'aga dogon kayan daya yaga, har aranta taji haushi dan kayan ya mata kyau sosai, zama tayi akan dressing mirror tashafa cream, bayan nan ta nema wani doguwar riga armless tasaka ta zuro hijabi tayi sallah Asr, bayan ta idar ta bud'e ledojin da Issam yashigo dasu, fried rice ne, sai chips da kwai, shawarma, icecream, da coke. Cin fried rice d'in take tana shan icecream da already yayi melting. Bayan ta cika cikinta ta bud'e data ta tashiga email ta turawa class-reps akan su shirya gobe zatayi lecture, tayi fixing na 'yan part two zatayi 9:00am, part four kuma zata shiga 11:00am. Daga nan ta kashe data ta dan batason damuwa, latsa number'n Shamcy tayi yana fara ringing tasaka wayar a loudspeaker, Shamcy tana picking call d'in tace "Adda Fido gaskia nayi fushi, ina kiranki baki picking kuma you dnt bother to call back" Ajiyar zuciya Fido tayi tace "So sorry Swthrt! Guess what?" "What?" "Ina KT!" Ihu Shamcy tayi tace "Are you serious?" "Mtssw kinga nayi kama da wacce zata miki k'arya" "Kai dad'i na dake Adda Fido yawan tsaki, please ki daina babu kyau" "Zakizo ne koh kuwa?" "Dole nazo Adda Fido" "Ohk toh bara na tura miki address d'in" "Karki damu nasan gidan" "Yaushe kika san gidan?" "Kedai nasani" "Ohk toh" ta katse wayan. Kwanciya tayi akan gado tana tuna irin wulak'ancin da Issam ya mata, wani shu'umin murmushi tayi tace "Wallahi Allah sai kayi dana sanin had'uwan ka dani" Laptop nata ta kunna tafara duba lectures da zatayi wa students nata gobe, cikin thirty minutes sai ga Shamcy tashigo d'akin, wani tsalle tayi ta rungume Fido tace "Gaskia Adda Fido nayi farin ciki da kikazo ki KT dan nayi missing naki sosai" "Mtswww sati d'aya shine har kinyi missing na? Kinga ni banson munafurci fad'a mini taya ki kasan gidan nan?" "Ai Adda Fido tunda kuka tafi muke zuwa gidan da Mami dubawa, kayan akwatinan kima mu muka kai miki" "Shineh dan wulak'anci kikayi pretending kamar bakisan da zuwa na ba?" "Ya wuce Adda Fido" "Karki k'ara kirana da Adda I told you times without number" "Sorry Yar! Yawwa me acikin ledojin nan?" "Duba ki gani" Bud'e su tayi tana ganin chips tace "Yawwa Alhamdulillah kamar kinsan abunda nake son ci kenan" Tana sakawa a baki ta yamutse fuska Fido tace "Ke lafia kuwa?" "Kinsan bana cin Chips da sanyi" "So? Akwai wanda yasaki dole ne?" "Nan ta ajiye Chips d'in ta d'au shawarma da coke, tace "Adda Fido ai da sai ki saka icecream d'in a fridge tunda yayi melting" "Tunda kinzo ba sai ki saka ba, ni tunda nazo gidan ma banga fridge ba" Dariya Shamcy tayi tace "Anyi 'yar kauye, bakiga fridge a parlour'n kiba?" "Ban lura ba toh Malama" "Bara na lek'a kitchen ina zuwa" D'aga mata kai kawai Fido tayi Shamcy tabar d'akin. Can kusan after twenty minutes taji gidan ya d'auka da k'amshi, nan ta tashi tace "Bara naje na duba mai yarinyan nan takeyi haka" Bata sha wahalan neman kitchen d'in ba dashike tana jin k'aran kwanuka, shiganta ta tsaya tana k'arewa kitchen d'in kallo, babban kitchen neh wanda yasha furnitures masu kyaun gaske tsaya describing na kitchen d'in b'ata lokaci neh, Shamcy tace "Adda Fido ya kin tsaya kina kallon kitchen d'in haka? Ya had'u koh?" Yamutse fuskan ta tayi tace "Ni banga had'uwar sa ba, what are you cooking haka inajin k'amshi?" Murmushi Shamcy tayi tace "Liver sauce, perper chicken, coconut rice" "Ohk idan kin gama kisame ni, already magrib tayi ma" "Ohk toh" Bayan sun idar da sallah Magrib suka ci abincin, Shamcy tace "Adda Fido kinji labarin Yaya Aliyu ya sake Meena?" "Haba! Wallahi banji ba, mesa ya sake ta?" "Wallahi ba wanda yasan dalilin" "Mtswww can ta matse musu" Haka suka ta hira har aka hira Isha, Shamcy tana cikin shirin komawa gida Issam yashigo da sallama, da fara'ar sa yace "Sis har zaki koma bazamu kwana ba?" Fido mamaki neh ya cikata tace "How do you know tazo?" Murmushi yayi yace "Ai munyi waya kan tazo" "Hmm ku kuka sani" Dariya Shamcy tayi tace "Toh ni zan wuce" Issam yace "Kin iya driving at night koh?" "Haba tun yaushe nake driving ai dole" "Gaskia kam kizo muje na raka ki" Shamcy rungume Fido tayi tace "Bye Sis" "Bye" Zama tayi akan gado tana ji inama Shamcy zata yarda su kwana, toilet ta fad'a tayi wanka, bayan ta fito ta shafa cream tasaka night gown tabi lafiyar gado dan already goma ma ya kusa Issam shima tunda ya raka Shamcy ya shige d'akin sa ya kwanta. Da misalin k'arfe biyun dare Fido tana cikin bacci kawai tafara jin kukan mage, a rayuwar ta tana bala'in tsoron mage tun bama kukan su da daddare ba, nan take ta farka tana karkarwa. A hankali ta d'au wayarta ta kunna touch light ta haska d'akin, duk da haka tana jin kukan, nan take ta tashi a guje ta fita a d'akin, dube-dube take har taga k'ofa a bud'e, lek'awan da zatayi taga wani k'aton d'aki ga Issam akan gado yana shakar baccin sa, rufe k'ofan tayi ta hau kan gado can nesa dashi ta kwanta, kanta sani har bacci ya d'auke ta. By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 42``` Farkawa Issam yayi da asuba yaga mutum a gefen sa, ba k'aramin mamaki yayi ba da yaga Fido, murmushi yayi yace "matsoraciya" a zuciyar sa. Toilet ya fad'a yayi alwala yafito, zuwa d'akin ta yayi ya d'au hijabinta ya k'ara dawowa d'akin sa. Tsugunawa yayi yana mai k'arewa fuskan ta kallo, suman kanta sai rufe mata fuska yake, murmushi yayi daya tuna tana yanga da gashin ta wanda tsawon sa bai wuce kafad'ar taba. Tattare suman kanta yayi yana shafa fuskan ta, a firgice ta tashi, ganin Issam yasata jan guntun tsaki tace "Lafiya Mallam?" "Ke yakamata na tambaye ki koh lafiya dan kece a d'aki na kwance akan gado na" Nan take ta taso ta cusa hannun ta cikin suman kanta tace "Ya Ilahu! Mtsw wai daman akwai mage a gidan nan" "Akwai su sosai ma, sunkai goma" "What! Har goma? Gaskia wallahi saidai a fitar dasu a gidan nan" "Yanzu dai tashi ki shiga kiyi alwala" "Zanyi a d'aki na" "Kin daina tsoron magen kenan?" Yamutse fuska tayi tace "Toh hijabi na fa?" "Gashi nan" ya nuna mata. Bayan sun idar da sallah sun karanata Al Qur'an tabi lafiya gado ta kwanta, yace "Ba zaki fita yau ba ya kika kwanta fa" "Dan Allah ka barni yanzu nefa 6:00am kuma na seta alarm k'arfe takwas" "Ohk toh" ita kuma tayi kwanciyar ta. Issam ne zaune ya saka Fido a gaba yana kallon ta yana murmushi, dan tun d'azu alarm d'in yake ta ringing bata farka ba, a hankali yake bubbuga ta a firgice ta tashi nan take ta duba wayarta taga k'arfe takwas da rabi, cusa hannun ta tayi cikin sumar kanta tace "Ya Salaam!". D'aga dara-daran eyes nata tayi ta sauke su akan Issam,murmushi ya mata ya rik'e hannun ta yace "Each time you awake and face a new day, remember that I’ll be beside you. I’ll hold your hand in mine and be the light that guides you. I’m not perfect, but if you ever lose your way, I’ll be your hero. I’ll be there to save the day. I’ll always try to make you happy,and make you feel loved, the way your heart desires, the way you’ve dreamed of. I know that life has brought you heartache and sorrow,but I’ll be there for you. I’ll make you smile tomorrow In Shaa Allah Hayateey" Kallon sa takeyi tama kasa furta komai, zuciyan ta name bugawa, duniyan ya tsaya mata cak, tab'a ta yayi nan ta dawo daga wani uwa duniyan data fad'a tace "Yuck! Please kabar ni" Ta taso akan gadon ta d'au hijabin ta tafita a d'akin zuciyan ta yana bugawa, tana shiga d'akinta ta fad'a toilet tayi wanka, fitowan ta kenan taga tray da foodflaskes, da flask na tea sai bread, kan gadon ta kuma kayan da zata saka. Can gefe taji yace "Umm you look sexy a towel Hayateey" "Mtswww dan Allah kafita mini a d'aki please" Tasowa yayi yazo daf kusa da ita, wani irin had'a rai tayi shi kuma murmushi yake yace "Ga breakfast na had'o miki, ga kuma kayan da zaki saka" "Naji so please get out" Fita yayi a d'akin, yana fita ta danna wa kofan lock, zama tayi ta shafa cream da sauri ta fesa body spray ta d'au kayan da Issam ya fitar mata dasu, Holland ne d'inkin riga da skirt, bataso sakasu ba but dan tayi latti batada lokacin duba wasu kayan kawai ta saka, shafa powder tayi da lipglose ta d'au jakarta da laptop nata, zata fita a d'akin kenan taga abincin da Issam yakawo mata. Wani guntun tsaki taja tace "Let me see abunda ya had'o" Bud'e flask d'in tayi taga fried yam da egg, "Wow!" ta furta, "Let me taste jagolgolon sa" Zama tayi ta had'a tea, gusura doyan tayi, to her very surprise taji yayi dad'i, nan ta zauna tafara ci, sanda taji ta koshi dam kanta bari, duba agogon hannun ta tayi taga tara da rabi, nan take tashiga toilet tayi brush tafito ta d'au su jakarta sai d'akin Issam. Zaune ta same sa yana danne-danne da laptop nasa tace "Zan fita" "Allah kiyaye hanya" "Key na mota nakeso kabani kan a kawo mini nawa" Mik'a mata key'n motan yayi yace "Karki damu za kawo miki sabuwar mota nan da sati d'aya, kibarwa Shamcy naki" "Ohk but zaka na yawo da tricycle kenan kan a kawo koh?" Murmushi yayi yace "Ba matsala, akan ki shiga a daidaita sahu gwara na shiga" "Good" ta fita tabar masa d'akin. Shiga motar tayi ta fisga sai cikin makaranta, tana zuwa tayi musu lecture, bayan ta gama dasu kamar 11:30 tafara yiwa 'yan part four, ita bata gama ba sai k'arfe d'aya. Bayan ta gama ta wuce parking lot ta shige motar ta, latsa number'n Eesha tayi, Eesha tana picking tace "Uwargida kina gida?", wani irin ihu Eesha tayi tace " Ina nan ina kuwa zanje? Zakizo ne?" "Yupp! Yanzu ma ina hanya" "Ohk toh sai kinzo" Tafiyan ten minutes tayi ya kaita gidan Eesha, sallama tayi tashige, da gudu Eesha ta rungume ta tace "Amarya bakya laifi, har kin fara fita? Mesa baki karb'a hutu ba?" "Ke barni na zauna a gida nayi me? I prefer ina fita aiki akan zaman gida" "Ohk ohh tunda mijin ki ya amince ni a nawa nake da zance baiyi ba" "Yawwa good gwara kiyi shuru" "Tab! Yau za'ayi ruwan sama da k'ankara" "Akan me kuwa?" "Ahyo ni ban tab'a ganin ki da gyale irin haka ba, gashi k'ato gashi thick yafi wasu hijaben ma thickness, na saba kallon ki a k'ananan veil kuma transparent" "Hmm kedai bari, a haka ma hibaji ya fitar mini na saka na saka wannan, ni duk ma yabi ya isheni sai uban nauyi ya sakani ciwon kai ma" Dariya Eesha tayi tace "Karki damu nan gaba zaki saba" A haka suka ta hira, a gidan tayi sallah'n zuhr da asr. Tana cikin shirin barin gidan Faruq da Issam suka shigo gidan, ba k'aramin mamaki yayi ba dayaga Fido a gidan. Faruq yace "Amarya bakya laifi, ashe kema kina nan? Yau ashe munyi manyan visitors" Dariya Eesha tayi tace "Ai kuwa" Bayan sun d'an gaisa Fido tace "Ni zan wuce" Tasowa Issam yayi yace "Muje nima gidan zani" Faruq da Eesha suka fashe da dariya Faruq yace "Lalle toh mungode bara na raka ku" Issam yace "Karka damu Allah kayi zaman ka" Bayan sun fita Fido tashige motar tareda saka lock a duk k'ofofin, Issam sai k'okarin bubbuga window yakeyi, sauk'e glass na motar tayi tace "Kaga Mallam nifa ba gida zani ba, zan tsaya a ATM na cire kud'i dan haka ka nema tricycle ya kaika gida" Murmushi ya mata yace "Ohk ba matsala" amma har a ransa yaji zafin abunda ta masa, a zuciyan sa yace "Bazan tsaya jani in jaka a waje ba but idan kinzo gida zaki fad'a gaskia" Haka ta fisga motar ta barsa a tsaye, shi kuma ya tsaida tricycle yashige. By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {August, 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 43``` ATM na Guarantee Trust bank ta tsaya tayi parking motar ta, sauk'an ta kenan taga Yaya Aliyu, wani had'a rai tayi tana tafiyan ta mai d'aukan hankali, Yaya Aliyu zuciyan sane ya buga lokacin daya ganta dan sati d'ayan da tayi ta k'ara haske da kyau. D'auke kai tayi zata wuce sa to her very own surprise taji yace "Fido sannun ki" Wani irin kallo ta watsa masa wanda yasa jikin sa ya mutu lik'is tace "Yawwa Sannu Aliyu" tacigaba da tafiyan ta, abun ba k'aramin mamaki yabasa ba, wato ma Aliyu ba Yaya Aliyu ba, shiga motar sa yayi ya fisga zuciyan sa na mai k'una full of dana sani. Bayan ta ta cire kud'in tashige motar ta sai gida, a lokacin daidai ake kiran sallar magrib. Toilet tashiga tayi alwala tayi sallah, bayan ta idar tana azkar Issam yashigo d'akin da sallama ta amsa masa da k'yar, ajiye ledojin hannun sa yayi yace "Mss Contour ga abinci" "Uhum" Juyawa yayi yayi ficewar sa, wani guntun tsaki taja tareda janyo ledojin, Shawarma, IceCream, roasted chicken da chips neh a ciki. Nan take ta bud'e icecream d'in tafara sha tana had'awa da roasted chicken d'in. Da misalin k'arfe goman dare Fido duk tsoro ya cikata gashi bataso taje d'akin Issam tace "Yanzu idan naje d'akin yaron nan sai ya raina ni ai, but ai na fad'a masa ya fitar da magen gidan nan nasan yanzu ya fitar dasu" Kwanciya tayi akan gado tayi addu'oin ta tashafa, koh minti goma batayi da kwanciya ba tafara jin kukan mage, magen ma ba d'aya ba. Nan take ta taso akan gadon ta kunna wutan d'akin, ganin kukan su ya k'aro atake ta d'au wayarta ta kunna touchlight a guje tafita a d'akin. A guje taje zata shiga d'akin Issam taji a rufe, wasu hawaye neh su sauk'a akan kuncin ta lokacin da taga wani bak'in mage, bugun kofan takeyi kamar zata b'alla. B'angaren Issam kuma dariya yake kamar cikin sa zai b'alle, sai can ya tashi yaje bakin kofan yace "Waye neh?" Nan take tace "Dan Allah dan annabi please open the door Issam" "Why should I? Wani abu neh?" "Cats!" "Toh sai na miki me? Kije ki d'akin ki mana" "Dan Allah Issam" A tsawace yace "Kefa bazan bud'e ba" Wani irin kuka ta fashe dashi dataga magen sun kai uku tsaye a gaban ta suna kuka, tana kuka tace "Dan Allah Yaya Issam ka bud'e mini" Wani irin dariya yayi data k'irasa da Yaya Issam, yace "Yaya Issam kuma?" Tace "Kayi hak'uri dan Allah, haba Yaya Issam! Haba Swthrt" Wani irin dariya yayi yace "Uhum" "Dan Allah Nurul Qalb, Nurul Hayat, Miji nah kaina bud'e mini mana" Ganin magen na neman hawwa kanta tayi wani irin ihu dayasa ya bud'e kofan atake, fad'awa jikinsa tayi tana wani irin kuka, ce mata yayi "Zaki k'ara mini abunda kikayi d'azu, wai nashiga tricycle koh" Nan take ta girgiza kanta tana hawaye tace "Kayi hak'uri wallahi Allah bazan k'ara ba" "Idan ma zaki k'ara repeating nasani na fitar dake a d'aki na su hau kanki daman sun jima basuci abinci ba kinga sun samu nama" Kama sa tayi tace "Ka yarda dani wallahi Allah bazan sake ba, na maka alkawari" "Shhhh toh shikenan yi shuru Hayateey". Yana mai bubbuga bayan ta ita kuma ta rungume sa sosai. A haka ya lallashe ta ya kwantar da ita akan gado sai kakkarwa takeyi, shima kwanciya yayi ya rungoma ta sosai yana cewa "Yi shuru Hayateey mijin kine" yayi wani shu'umin murmushi.. Da asuba ta farka tajita a jikin wani rungume da ita, wani irin ihu tayi dayasa ya farka yace "Ke lafiya" "Lafiya kake tambaya na? Who gave you the audacity ta touch me?" "And who the hell gave you the audacity to enter my room har ki kwanta akan gado na ehhh?" Ya fad'a mata a tsawace. Shuru tayi tana kallon sa dan bata tab'a tsammanin zai mata tsawa ba, sauk'a tayi akan gadon without uttering a word tafita a d'akin, wani tsoro tsoro takeji amma akan ta koma d'akin sa gwara magen su cinye ta, tana shiga d'akinta ta rufe kofan ta tana sauk'e numfashi. Duk da tana jin kukan magen haka ta dage tayi alwala tayi sallah, tana idarwa tabi lafiyar gado ta kwanta. Da misalin k'arfe tara na safe Issam yashigo d'akin ya ganta har yanzu shakar baccin ta takeyi, bubbuga ta yake da hankali nan take ta tashi a firgice, kallon ta yake yace "Wai ni ke baki iya tashiwa a bacci cikin kwanciyar hankali ba kullum a firgice kike tashiwa?" Guntun tsaki taja tace "Toh ina ruwan ka dani?" Duba agogon da zatayi taga k'arfe tara da rabi, nan take ta taso akan gadon ta cusa hannu cikin sumar kanta tace "Ya salaam! Muna da meeting k'arfe goma" "Sai ki tashi ki shirya ai" Fita yayi a d'akin ita kuma ta cire night gown nata ta fad'a toilet tayi wanka, fitan ta taga foodflakes da flakes na tea, kan gadon ta kuma ga kayan daya fito mata dasu. Murmushi tayi ta zauna ta shafo cream ta saka kayan daya ajiye mata akan gado, dogon habbaya neh bak'i da blue ,sai hijabi blue daya ajiye mata, zama tayi ta bud'e foodflakes d'in taga chips da kwai, had'a tea tayi taci da chips. Sanda taji ta k'oshi kan ta tashi tayi brush ta zura hijabin a jikin ta, wani dogon tsaki taja tace "Taya zan had'a abaya da hibaji kuma" gyale ta nema babba ta yafa ta fesa perfumes nata. Zuwa tayi ta same shi a d'aki ya shirya yayi kyau abunsa kamar a sace shi a gudu. Suman kansa sai yalk'i yake yasha gyara, ga sajen fuskan sa wanda ya kwanta yayi luguf luguf, ita kanta tasan ya had'u iya had'uwa, murmushi ya mata yace "Mss Contour kin shirya?" "Yeah nayi latti ma" Duba agogon hannun sa yayi rolex yace "Gaskia kam yanzu past ten, koh da yake akwai african time, please ki ajiye ni a gidan mai na mana" Kallon uku saura tara ta masa tace "Bakaji nace maka nayi latti ba?" "I know but tunda hanya d'aya neh ai ba matsala" Kamar tace baza tayi dropping nasa ba sai ta tuna da abunda ya mata jiya da daddare tace "Alright ka same ni a mota" tayi ficewar wa, abun ma dariya ya basa yadda take wani jin kai, girgiza kansa yayi ya d'au perfumes a wardrobe nasa ya fesa. Wani uban horn take danna wa sai gashi ya fito ya bud'e gaban mota yashiga, wani dogon tsaki taja tace "Shiri sai kace mace Allah sawwaka" "Dad'i na dake yawan tsaki kamar 'yar tasha" "Ba yau kafara fad'an haka ba balle ya dameni yaro" Wani dariya yayi yace "Aww nine yaro? Daga Yaya Issam, Swthrt, Nurul Qalb, Nural HAYAT, Miji nah yanzu kuma yaro?" Tsaki ta kuma ja tace "Whatever!" "Tsaki sai kace 'yar tasha" "Cikakkiyar 'yar tashan neh ai" Da hakan har ta sauk'e sa a gidan mai, kallon ta yake with so much tenderness in his eyes yace "Mss Contour hope zakizo ki d'auke ni?" "Akwai lectures da zanyi 4-6 so idan ka gama ka hau a daidai ta tsahu" "No ba damuwa zan jira ki Hayateey" "Mtss sai kata jira ai kaga koh zanzo ni" Murmushi yayi yace "I know definitely you'll come" "Mts kaga fita mini a mota nah nayi latti Mallam" Kallon gefen ta take ji tayi kawai yayi pecking nata yace "Take care Hayateey" "Mtsw fita please" Murmushi yayi ya fita a motar tareda d'aga mata hannu koh kulasa batayi ba ta fisga motar abun ta. Tun k'arfe biyu tagama duk abunda zatayi a makarantan, driving take zataje ta gida tace "Naje gida ma nayi me? Bara naje wajen Mummy kawai". Reverse tayi da motar ta direct gidan baffa Umar tawuce, wan Mummy wanda a yanxu take zama a gidan sa, da sallama tashiga gidan lokacin Mum tana parlour tana shan fura, hugging na Mum nata tayi tace "Mummy nayi missing naki" Murmushi Mummy tayi tace "I missed you too durling" "So ya mai gidan ki?" "Lafiyan sa kalau Mummy" "Mutumin kirki, jiya ma yazo ya gaishe ni kuma kullum sai ya kirani a waya, Allah masa albarka" "Hmmm Ameen" Haka sukata hira taci abinci sai da can yamma Mummy tace "Fiddausi yamma tayi ki tashi ki tafi gidan ki" Ji tayi kamar karta tafi amma ba yadda ta iya dole ta tashi ta shirya, bayan ta shirya tace "Toh Mummy ni zan wuce" "Toh Mamana Allah miki albarka, ki zauna da mijin ki lafiya kinji? Kuma ki zama mai rik'e sirrin mijin ki" "In Shaa Allah Mummy nagode" "Ba komai ki gaida shi" "Zaiji" Driving take ta duba agogon motar taga k'arfe biyar da rabi, ji take kamar ta wuce gida ba tareda ta tsayawa d'aukan saba, har ta wuce gidan mai d'in ta k'ara reverse, a can nesa da gidan mai d'in ta tsaya tana mai kallon sunan gidan mai d'in wanda aka rubuta *ISAL* , tunani take tasan sunan shi Issam toh AL d'in me yake nufi oho? Wayarta ta d'au ta danna masa kira, d'auka wansa yace "Mss Contour kinzo neh?" "Mts kafito idan ka k'ara minti biyu wallahi tafiya ta zanyi" "Yanzu zan fito please karki tafi kibarni Hayateey" "Mts sai kayi sauri ai Mallam" "Dad'i na dake yawan..." Bai k'arasaba ta tare numfashin sa tace "Tsaki kamar 'yar tasha koh? Sau nawa zan fad'a maka cikakkiyar 'yar tashan nema ba kamar 'yar tasha ba" "Ohk naji gani nan I'm on my way, banso kina masifa cox yawan masifa na tsufar da mutum and banso ki tsufa, dan idan kin tsufa zan auro wata neh ba ruwa na" "Ka auro uku mu zama mu had'u bazai dame ni ba, yanxu kaci minti biyar wallah natafi" ta katse wayan, tada engine na motar tayi kawai taga ya bud'e kofa ya shiga. Nan take ta fisga motar tana wani irin gudu, tace "Mesa zaka k'arar mun da credit na wayana bayan kana kan hanya" "Sabida ban gajiya dajin voice naki kuma da kike maganar k'arar miki da credit na waya naga jiya jiya kika cire kud'i a bank" Wani deadly look ta masa tace "And so bloody what idan jiya naje bank? It's your responsibility ka d'au nauyi nah" "Koh?" "Hell yeah" Cire wallet yayi a aljihun sa ya ciro ATM card kusan guda biyar, mik'a mata d'aya yayi yace "Duk time da kike needing kud'i ki cire" Karb'an ATM card d'in tayi a zuciyar tana cewa "Lallai yaro wallahi sai kayi dana sanin bani ATM card naka da kayi". Wani murmushi tayi tace "Are you sure about this?", d'aga mata kai yayi without uttering a word, tace "What's the password?" "1987" Murmushi tayi tace "Ohk" Bayan sunje gida kowa ya wuce side nasa, ita tayi sallah a gida shi kuma yaje masallaci bai dawo ba sai bayan isha'i. Zaune take a d'akin ta tana danne-danne da wayarta yayi sallama yashigo d'akin, guntun tsaki taja tace "Kai gaskia anyi asarar ilimi, wai mutum bazai iya jiran a amsa masa sallama kan yashigo ba?" "Ai naga gida na kuma d'akin matata nashiga" "Dan haka bazaka iya jiran a amsa maka sallama kan ka shigo ba?" "Yeah wifey" "Mtswww toh mai yakawo ka d'aki nah?" "Yunwa nakeji" "Sai kuma aka ce maka inada abincin da zan baka?" "Dafa mini zakiyi" Kallon uku saura kwabo ta masa tace "Nice zan dafa maka abinci? Allah sawwaka" "It's your responsibility ai as my wife" "Stop it, karka k'ara ce mini ni matar ka abun b'ata mini rai yake" "You have to accept that da kinki da kinso, ina ji a jiki nah watarana zaki soni fiye da yadda nake sonki, gwara ki fara nuna mini so tun yanzu before na mutu, kar yazama miki so late watarana kina dana sanin mesa baki nuna mini so da kauna ba" "Allah sawwaka, a yau idan ka mutu cewa akayi zai dame ni? Dan Allah fita mini a d'aki banson surutu dayawa" "Abincin fa Hayateey?" "Banda abinci kuma bazan iya girka wa ba" "Yunwa fa nakeji" "Sai kazo ka cinye ni ai nasan dagasken yunwa kakeji" "Na cinye ki?" Ya k'ara tambaya yana wani irin murmushi, nan take ta d'aga kanta tace "You really have a dirty mind, I beg you please don't think otherwise" Murmushi ya koma yi ya taso daga kan kujeran sa yaje daf kusa da ita, ita kuma tana ja da baya, yace "Na cinye ki koh?" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {Sept., 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 44``` *Wishing you all a happy sallah, May we witness many many more* Ja da baya take shi kuma yana matsowa kusa da ita yana wani irin murmushi yace "Kikace na cinye ki koh?" "Kayi misunderstanding d'ina please" "Kamar ya? Kikace na cinye ki ai kuwa zan cinye ki, koh ban samu na cinye kiba nasan koh latsan ki nayi zanji na k'oshi" "Kayi hak'uri please ka barni nayi maka alkawari zan dafa maka koh indomie ne" "No ai ke zakifi Indomie taste" Wani deadly look ta masa tace "Kamar ya?" "Oshh! I mean zakifi Indomie d'and'ano" "Ai ba turancin akace maka bana jiba, nidai please ka matsa banson kayan k'azanta" Matsowa yake ita kuma tana ja da baya har takai jikin bango, yace "No where to escape now Hayateey" "Please don't do anything stupid" "Ain't doing anything stupid I just wanna.." "You just wanna what???" ta fad'a tsawace, zai k'ara matsowa ta turesa da hannun ta, hannunta ya kama ya rik'e gam wanda bazata iya kwatar kanta ba, lips nata ya had'a da nasa yana kissing passionately, duk iya k'okarin ta na hanasa amma ina yafi k'arfin ta Sanda yagaji dan kanshi yabar ta yace "Yanzu na d'an ji dama-dama duk dama ban cinye ki d'in ba" "Allah ya isa na k'azami kawai" "Wallahi idan kika k'ara magana zan rufe d'akin na karb'a hakki nah inga mai kwatar ki" "Hakkin ka? Ai ni na d'auka baka da lafiya bazaka iyayin komai ba" Murmushi yayi yace "Zakisan banda lafiya kuwa watarana. Kinsan me Mss Contour? Basai kina saka k'ananan kaya or kina barin suman kanki ba zaiyi attracting d'ina, I know mesa kike haka, kina hakane sabida kija ra'ayina na tunk'are ki da wani abu ke kuma kik'i amincewa koh kisani a wani yanayi. Lemme tell you something Hayateey, So da Sha'awa akwai banbanci, sha'awa yana zuwa koh babu so amma So baya zuwa ba sha'awa. So da sha'awa suna tafiya ne tare, Son da nake miki ya wuce wasa, bazan tab'a miki dole ba Mss Contour, koh da zamu shekara dubu a haka idan har ina kallon ki kullum kuma ke tawa ce is ok by me" (nidai nana nace big lie) Abun ma mamaki yake bata, ta rasa wani irin so Issam yake mata, ta k'ara tabbatar da Issam na sonta so na hak'ika, amma bazata iya tab'a rayuwa da mutumin da shine sanadin mutuwar mahaifin taba. Wani zazzafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta, nan take ya rikice yace "Hayateey kuka kuma please ki daina kuka" matsowa yayi sosai kusa da ita yana lashe hawayen, nan ta ture sa tace "Kaga Mallam banson k'azanta". Tasowa yayi ya bud'e fridge ya d'auka icecream yace "Yanzu zakiga asalin k'azanta kuma wallahi idan kika kuskura kikayi mini rashin kunya zan karb'a hakki nah da kinki da kinso" "Ka manta yanzu ka gama fad'an baza ka tab'a mini dole ba" Murmushi yayi yace "Wasa nake yarinya amma duk ranar da kika kaini bango hmmm, nidai ina rabaki" Zama yayi kusa da ita ya bud'e icecream d'in yace " I am warning you idan kika kuskura kika hanani abunda nake shirin yi yanzu sunan ki sorry" Ita dai sai kallon ikon Allah take, Icecream d'in ya d'an d'iba da finger shi ya lakuta mata a wuya, nan take tace "Me haka so kake mura ya kamani" "Shhh" matsowa kusa yayi da ita wanda har suke shak'an numfashin juna, latsan icecream d'in yayi tas tana wani yamutse fuska, icecream ya k'ara lakuta ya shafa a bakin ta, nan ma ya lashe, haka ya tayi ya shafa icecream a fuskan ta da wuyan ta yana lashe wa, itama kuma sai yamutse fuska take gashi ya matseta gam ba daman guduwa, haka ya shanye icecream d'in tas kan ya bata waje yace "Now I feel better" "K'azami kawai, nidai ban yafe ba" "You should be grateful ina latsan wannan jikin naki da koh wanka mai kyau baya samu" "Na saka dole? Or you should be freaking lucky da na barka kana latsan jikin da koh a mafarki bazaka tab'a iya samu ba" "Nasan you enjoyed it you just beating around the bush" Wani dogon tsaki taja tace "Allah sawwaka wallahi" "Ameen toah mss Contour, idan kin gama ki sameni a d'aki nah kan na rufe kofa anjima ki dameni da knock" "Are you saying har yanzu baka saka an fitar dasu ba?" "Mesa zan saka a fitar dasu bayan nina kawo su?" "Please dan Allah a fitar dasu please badan halina ba" "On one condition" "What?" Ta fad'a a take, murmushi yayi yace "Idan zakina barina ina shan ice cream a jikin ki" Wani kallo ta watsa masa, kamar tace a'a wani zuciyan yace kawai ki yarda idan yafitar dasu kiyi maganin sa, yace "Ya kinyi shiru?" "Na amince" ta fad'a a sanyaye, murmushi yayi yace "Kizo da ice cream roba biyu d'aki nah and I promise you gobe da safe In Shaa Allah duk za'a fitar dasu but karki ce zaki mini wayo after an fitar dasu kiyi yunkurin hanani, a ranar da kika hanani zan kawo double wanda suke nan kin yarda?" She was speechless ta rasa abunda zatace, a zuciyar tace "Zanyi maganin ka once and for all na huta" "Na yarda" "Good gurl! Ki sameni a d'aki nah ina jiranki" ya fice a d'akin. Yana fita taja dogon tsaki tace "I swear you will pay for everything" Toilet ta fad'a tayi wanka, bayan ta fito ta saka night gown, zata fesa turare ta fasa tace "Gwara naje nata d'oyi koh zai kyale ni", d'aukan gyale tayi ta bud'e fridge ta d'au roban icecream guda biyu, har takai kofan d'akin zata fita tace " Gwara na fesa body spray karya raina ni kuma ba wani d'oyin da zanyi dan soap da nayi wanka dashi and yadda jikinah yake koh kwana biyar nayi ba wanka bazanyi wari ba" Shiga cikin d'akin tayi ta fesa body sprays da perfumes kanta fita a d'akin. Tun a hanya takejin kukan magen da d'an gudu-gudu tashige d'akin sa, a lokacin yana zaune kan gado yana waya. Bayan ya gama wayan yace "Mss Contour zoki zauna kusa dani" Ba musu taje ta zauna kusa dashi sabida tana jin kukan magen and karta masa rashin kunya ya k'oreta, kwantar da ita yayi akan gado yace "Relax Hayateey, ba abunda zan miki" Itadai shuru tayi tana tunanin nan da sati d'aya kawai zata gama dashi. Roban ice cream d'in ya bud'e ya d'an sha, sannan ya d'an shafa mata akan lips d'in ta, matsowa yayi kusa da ita ya lashe ice cream d'in tareda bakin ta, hakan nan ya ringa shafa ice cream asu wuyan ta, cikin ta yana lashewa har sanda icecream d'in roba biyu suka k'are a jikinta kan ya kyale ta. Daga nan ta shiga toilet nasa, wasu irin zazzafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta, ta kasa tantance me takeji gameda Issam a yanzu, haka da k'yar tayi wanka tafito. Bayan ta fito yace "Mss Contour kin wanke k'azantan neh?" Koh kulasa batayi ba tayi kwanciyar ta, yace "A sanyin nan zaki kwanta baki shafa mai ba? Maza tashi na shafa miki koh na fitar dake a d'aki na". Banza tayi dashi shi kuma ya d'au cream nasa ya janye blanket data rufu dashi yafara shafa mata cream d'in, yace " Miss Contour juya bayanki na shafa miki mai" Ba musu tayi ruf da ciki yana yaye night gown nata yana shafa mata mai, bayan ya gama ya rufe ta da kyau ya mata addu'a ya karanta mata suratul Mulk yace yana murmushi "Now you can sleep Hayateey" Rufe idon da tayi sai ga hawaye, girgiza kansa yayi yana lashewa da harcan sa "Please don't cry Hayateey, I really don't wanna see you crying" Haka ya lallashe ta har sanda bacci ya d'auke ta ya kwanta shima... Da daddare misalin k'arfe d'ayan dare wayan sa ya fara ringing, nan take ya farka ya saka wayar a silent, haska fuskan ta yayi yaga tana bacci, k'iran number'n ya k'arayi ana picking yace "Hello kazo CD plate d'in neh?" Sai can yace "OK yanzu zan fito na karb'a" ya katse wayan. Da sauri ya fita a d'akin nan Fido ta tashi ta bisa a hankali, fita waje yayi mai gadi ya bud'e masa gate, cikin five minutes sai gashi yashigo gidan nan take ta koma d'akin ta kwanta. Yana shiga d'akin ya bud'e wardrobe nasa ya bud'e ya d'au save ya latsa password yana bud'e wa ya saka abun hannun sa a cikin ya k'ara rufewa duk tana kallon sa, bayan ya saka ya rufe wardrobe d'in ya koma bacci.... Haka yata kasancewa kullum shi yake girka mata breakfast su fita tayi dropping nasa idan ta tashi ta d'auke sa. *Bayan Wata Biyu* Zaune take a gaban madubi da safe tana shirin fita aiki, Issam shigowa d'akin yayi da sallama yana mata murmushi yace "Mss Contour yau bana jin dad'i koh zaki mana breakfast neh?" Kallon uku saura tara ta masa tace "Bakaga ina sauri baneh nayi fixing zanma students d'ina test 9:00am gashi yanzu past nine" "Ohk ba damuwa idan na fita zan tsaya naci" "Thank God yau bazanyi dropping naka ba" "Da mota ta zan fita" Ajiye powder'n hannun ta tayi tace "Ni kuma sai na fita da uban me?" Makullin mota ya cire a aljihun sa yace "I promised you zan siya miki mota right? Here is your car key" ya mik'a mata" By Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {Sept., 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 45``` Karb'a'n key d'in tayi tana jujjuyawa tace "Wace iri?" "Idan kin fita zaki gani Hayateey!" Yayi pecking nata yace "Later Mss Contour" Murmushi ta masa tace "Later" Bayan ta gama shiri ta d'auka makullin motar ta fita haraban gida, wata mota Ferrari bak'a tagani k'irar M140i bud'e baki tayi tana kallon motar dan bata tab'a tsammanin Issam zai siya mata mota mai tsada haka ba. Addu'a tayi ta shiga motar, jin kanta take a sama tana shafa motar, daga nan ta fisga motar. Tafiya take amma ta kasa cire Issam a ranta, ita kanta tasan tayi missing nashi so badly, kwana biyun nan har ta saba tana driving yana zaune a gefen ta yana neman tsokanan ta. Batasan lokacin data d'aga wayarta ta latsa number shi ba, yana picking yace "Mss Contour hope lafiya? Motar ta tashi koh nadawo gida na d'auke ki?" Batasan lokacin da hawaye suka fara sauk'a kan kuncin taba, bud'e bakin ta tace "Ya tashi yanzu ma ina hanyan zuwa wajen aiki" Yayi ajiyar zuciya yace "Thank you Allah! So what's the problem anh?" "Bazan iya kiranka ba sai da matsala?" Murmushi yayi mai sauti yace "You don't have to say it Hayateey, I'm missing you more, in fact more than more" Tsaki taja tace "Allah sawwak'a" "Dad'i na dake yawan tsa...." Bai k'arasa ta tare numfashin sa tace "Tsaki kama 'yar tasha koh? Sau nawa zan fad'a maka muguwar cikakkiyar tasha neh ni" ta kuma jan dogon tsaki ta kashe wayar tace "koh da bana sonka Issam but I really care for you! And when I care I don't let go! I am really scared, yakamata nayi wani abu a yau d'in nan before it will be too late, Ya Allah I don't wanna fall for him" Reverse tayi da motarta ta latsa number'n Dr Kemi itama lecturer ce a department d'in, ringing d'aya Dr Kemi tayi picking tace "Hello Fiddausi" Fido tayi ajiyan zuciya tace "Hi Mrs Omolowo are you in your office?" "Yes any problem?" "Not at all, can you please help me inform part four students that the test has been cancelled" "Ohk I'll" "Thank You" ta katse wayan. Gida direct ta wuce, tana zuwa tayi parking motar ta tashiga, side na Issam ta bud'e wani k'amshi neh ya dosa hancin ta, shiga tayi tana kallon d'akin mai kyau, cire kayan jikin ta tayi ta d'aura towel ta shiga toilet nashi tafara wanke wa duk da ba datti, tunda tazo gidan bata tab'a d'aukan tsintsiya da sunan zatayi shara ba saidai tayi wanka ta fita idan ta dawo taga gidan a share fes kuma da ikon Allah bata tab'a tambayan wa yake share gidan ba, akwai ranar da Issam yace zai kawo mai aiki tace ita sam bata yarda ba dan kawai tana son ya gaji da halinta amma bai tab'a gajiya da itaba. Bayan ta wanke toilet ta fesa masa turare ta kunna turaren wuta, haka ta share d'aki da parlour'n sa tas ta saka masa turaren wuta. Daga nan tashiga kitchen nata wanda yake a share tas anyi moping, bud'e fridge d'in tayi taga akwai duk abunda take buk'ata. Had'a girki tafara yi cikin awa uku ta girka pounded yam with egusi soup, tayi pepper soup na kifi, tayi roasting na chicken, tayi blending na juice. Daga nan ta fad'a toilet tayi wanka, bayan ta fito ta saka doguwar riga armless bayan ta duk a bud'e wanda rabin k'irjin ta a bud'e ya baiyanar da fulanin ta, zama tayi tana kwalliya wanda rabuwar ta dayin kwalliya tun ranar auren Eesha. Murmushi tayi da tana contouring fuskan ta tace "Issam yau zakaga asalin Mss Contour". Ba k'aramin kyau tayi data gama kwalliyar ba, kallon kanta take a mirror tana murmushi, zuwa kitchen tayi ta kwashe abincin da already ta zuba a foodflakes takai kan dining. Bayan ta ajiye su tace "Bari na ma gidan kallon k'arshe" wasu zafafan hawayen neh suke sauk'a kan kuncin ta tana zagaya gidan tana hawaye. Jin horn ta motar sa nan take ta lek'a ta window taga Issam, duba agogon hannun ta tayi taga 2:30, d'akinta ta wuce da gudu ta k'ara shafa powder ta fito. Da sallama ya shigo gidan, ganin ta yayi a bakin kofa tana masa murmushi, ba k'aramin mamaki yayi ba shidai kawai ya tsaya yana kallon ta, matsowa kusa dashi tayi tace "Yau ka dawo da wuri fa" Sosa suman kansa yayi yace "Wallahi na tsince kaina da fad'uwar gaba, zuciya nah yana tsinkewa bansan dalili ba" "Oshh ayyah! Kata addu'a" Murmushi yayi yace "Ke kuma fa" Ba tsammani kawai yaji ta rungume sa sosai, shi abun ma mamaki yake basa da tsoro tace "Your food is ready kayi wanka ka fito" Bud'e baki yayi yana kallon ta he was surprise and at the same time zuciyan sa yana tsinkewa, yana doubting tun ba yau ba kamar Fido tasan shine d'in yashiga gidan su, yana tunanin anya ba trap ta had'a masa ba? Murmushi yayi yace "Ohk Hayateey" Yana shiga b'angaren sa ta ciro wayarta ta latsa wani number, ringing d'aya akayi picking, fita tayi ta bayan gidan tace "KBad kayi make sure bai mutu ba, karka kashe shi, inason duniyan ya masa zafi ya tsana kanshi gaba d'aya, bari na maka repeating aikin da zaka mini karka mini shirme, idan kuka shigo ku d'aure shi Ku rufe bakin sa, ku cire masa wando ku yanke gaban sa, kuna yanke wa ku d'aura wajen kar jini yayi flowing kaji ko?" Sai can kuma tace "Ohk good ashe S.A ya k'ara sanar muku sai kunzo" ta katse wayan. Zama tayi dirshan a k'asa ta rushe da wani irin kuka, daga nan ta tashi ta wanke fuskarta ta koma ciki, a daidai lokacin Issam ya fito a d'akin sa yana baza k'amshi, da ganin fuskan ta yasan tayi kuka shidai baice mata komai ba yace "Yau kin fito asalin Mss Contour'n ki, but I must confess kinyi kyau sosai sosai". Murmushi tayi tace "Thanks My Qalb". Murmushi yayi yace "Sometimes you really can act strange, but Allah sa ba sharri ake had'a mini ba". Had'a rai tayi tace "Kamar ya?" "Hayateey ki kwaso abincin muci a k'asa tare" Ba musu tace masa "Toh" ta kwaso abincin zuwa k'asa. Zama sukayi Fido tayi serving nashi, Issam yace "Ni zan baki da hannu nah Mss Contour" Murmushi tayi tace "Ba komai My Qalb" Haka ya ringa feeding nata itama tana basa abincin a baki, bayan sun gama ci yace "Zanje masallaci ki shirya zamu fita" "Fita kuma zuwa ina?" "Kedai ki shirya" Yayi pecking nata. Yana fita ta kwashe food flakes d'in takai kitchen ta wanke su tas, daga nan tayi alwala tayi sallah. Tana idarwa sai gashi yashigo d'akin da sallama yace "Mss Contour sai yanzu kikayi sallah? Maza tashi toh ki shirya" Ba musu ta tashi tace "Ohk excuse me zan canza kaya" Murmushi yayi ya matso kusa da ita yace "Ni nakeso na zan canza miki kaya yau" "Ohhh I will love that Dear ka canza". Take ya d'aga ido ya kalle ta cox that shocked him to his very core yace "You sure?" Tace "Very sure" Shi da kansa ya cire mata kaya a wardrobe superwax d'inkin riga da zani, tana ganin zani tace "Gaskia ka maida kayan nan bazan saka ba" "Mesa?" "Baka ganin zani neh? Nidai banso kuma ban iya d'aura wa ba" Murmushi yayi yace "Don't worry Hayateey zan d'aura miki" "Nidai ban yarda ba" "Shhh nace zan d'aura" "Ohk toh" Murmushi yayi yana sosa suman kansa yace "Yanzu zan cire kayan first koh?" Ita abun ma dariya ya bata tace "Eh koh akan kayan jiki na zaka d'aura?" Ya girgiza kansa yana mai sosa suman kansa, matsowa yayi kusa da ita yace "Ummm ta ina zan fara?" Tayi dariya tace "Ko ta ina ma" Da yake doguwar riga ce ya d'aga ta sama yace "D'aga hannun ki" Ta d'aga, haka ya cire rigan ta sama ya rage daga ita sai bra da pant ajikin ta. Komawa baya yayi yana mai k'are mata kallo, juya masa baya tayi tana murmushi tace "I hate that look" Matsowa yayi yayi hugging nata ta baya yace "Mss Contour I Love You So Much" Juyota yayi suna facing juna yana kallon cikin idon ta yace "My heart says that you like me, My eyes says that you feel something for me, My mind says that you think of me, But till now you are quiet why?" Ba shiri kawai yaga hawaye suna sauk'a akan kuncin ta nan take ya rikice yace "So sorry Hayateey, fad'a mini meke damun ki, koh maganar da nayi neh ya b'ata miki rai?" Girgiza kanta tayi tace "A'a" "Then please tell me the truth, meke damun ki?" "Babu" "Are you sure?". Ta d'aga kanta, hugging nata yayi yana panting na bayan ta yace " Banson na ganki kina kuka, yana breaking heart nawa idan baki sona neh ki fad'a mun" "Idan bana sonka zaka sake ni neh?" "Bazan iya ba, but if you'll be happy zan sake ki dan farin cikin ki shine nawa. Is rather na zauna cikin kunci kina farin ciki than ni ina cikin farin ciki ke kuma kina cikin kunci, I can't take that because your happiness means the world to me" Hugging nasa tayi sosai ta fashe da wani irin kuka wanda ya k'ara rikita shi, sai sannu yake mata har ya samu tayi shiru, bayan tayi shiru tace "Baza saka mini kayan ba koh mun fasa fitan?" "Bamu fasa ba" Rigan ya d'auko ya bud'e zip ya saka mata ya rufe zip d'in. Zanin ya d'auko sai faman ya d'aura mata yake amma ya kasa haka yata zagaye-zagaye sun kusan minti biyar yana abu d'aya ita kuma sai dariya take masa, haka suka kusan minti goma sha biyar suna abu d'aya ya kasa d'aura wa. Duk suka zube akan gado suna sauke numfashi take kuma suka fashe da dariya tace "Shine wai ka iya?" Sosa suman kansa yayi yace "Wallahi before na iya mantawa nayi" Dariya tayi tace "Lies ba wani, tsaya kaga na d'aura" Tasowa tayi itama haka tayi ta k'okarin d'aura wa da k'yar dai ta iya ta d'aura gaba dogu baya guntu. Tsaki taja tace "Nidai zan cire kayan nan" "A'a karki cire ya miki kyau ki d'aura d'an kwali mu tafi" Ba yadda ta iya haka ta d'aura d'an kwali ta shafa powder ta yafa gyale tace "Done" "Good to go?" "Yeah!" Kama hannun ta yayi suka fita haraban gidan yace "You drive or I drive?" Murmushi tayi tace "You drive" Bud'e mata gaban motar yayi ta shiga ta zauna ya rufo kofan yadawo driver seat ya zauna ya tada motar. Gidan su Aliyu first ya fara kaita, Inna ba k'aramin farin ciki tayi ba ganin Fido ta k'ara kyau tayi haske tayi jiki, haka suka shiga koh wani side suna gaisuwa. Mami ce ta karb'e su da fara'a su Umma da Hajja koh kulasu basuyi ba dan bak'in ciki. Sai bayan magrib kuma suka je gidan Eesha, Eesha tana ganinta ta rungume ta suka shiga ciki suka bar Faruq da Issam a parlour. Suna shiga cikin d'aki Eesha da k'aton cikin ta tace "K'awata naga kamar kema fa kun samu k'aruwa" Fido tayi dariya tace "Hmm ciki a ruwa ake sha neh?" "Kardai har yanzu bai tab'a kiba?" "Ba abunda ya shiga tsakanin mu ke har yanzu kuma bana fata wani abu ya shiga tsakanin mu" "But why Fido? Wallahi kina b'oyewa your eyes revelled that kina son Issam so stop pretending" "Mu bar maganan nan please". Haka dai suka ta hira har sallah'n isha'i su basu koma gida bai sai k'arfe tara na dare. Tun a mota Issam yake ta mata magana amma hankalin ta yana wani waje daban har suka iso gida. Kowa d'akin shi ya shige, Fido tana shiga d'akin ta wayarta ya soma ringing, hannun ta yana shaking tayi picking call d'in tace "Kunzo neh?" Can kuma muryan ta yana shaking tace "Ohk toh ku shigo". Tana katse wayan ta fashe da wani irin kuka, yi take kamar wanda za'a yanka kanta... _One hour Later_ Da hankali take takawa zuwa d'akin Issam dan kafarta ya mata nauyi da k'yar take iya d'aga wa. Ganin Issam tayi kwance akan gado an d'aure sa da kafa da hannu ga manya manyan 'yan daba akansa. Zuwa tayi tana kallon sa, murmushi ya mata yace " Hayateey nasan dama kina shirya mun something like this, koh mai na fad'a miki baza ki tab'a yarda ba amma inaso ki sani no matter what you did to me I'll always love you" "Ka fad'a mini waye neh ya cewa ogan ku a kashe Dad nah? " Komai yana cikin safe da nasan kinsan dashi" Juyawa tayi tana hawaye ta bud'e wardrobe nasa ta d'auka safe d'in tazo gaban sa tace "What's the password?" "Fiddausi" "Duk da yadda kake sona Issam bazan iya rayuwa da mutumin dayayi sanadiyar mutuwar Dad na ba, ni bazan kashe kaba but zan maka abunda har ka mutu baza ka tab'a mantawa ba. Kasan me zan maka? Za'a yanke gaban ka shikenan naka ta k'are, bakai ba k'ara aure, bakai ba jin dad'in rayuwa, bazaks tab'a ganin jinin ka ba" Ba k'aramin mamaki yayi ba, shi duk a tunanin sa kashesa zatace ayi but jin maganganun ta that shocked him to his very own core, Murmushi yayi yace "Nagode" Ta juya ta kallesu tace "Kuyi aikin ku". Tana fita a d'akin taji yayi wani irin k'ara mai firgitarwa Nana Fa'ad #MunaMugunTare *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {Sept., 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 46``` Da gudu tashigo parlour'n tana wani irin kuka a lokacin Inna tana parlour tana dama fura ta rungume Inna, Inna hankalin tane yayi masifan tashiwa ganin irin kukan da Fido takeyi, Inna tace "Fiddausi lafiya? Meya sameki kike kuka haka?" Girgiza kanta Fido tayi tacigaba da kukan, Inna tace "Koh Issam neh?" Nan take ta d'aga kanta, Inna hankalin ta ya k'ara tashiwa tace "Mutuwa yayi?" Nan ma ta girgiza kanta. "Bashida lafiya neh?" Still ta k'ara girgiza kanta, a tsawace Inna tace "Toh dan ubanki ki fad'a mini dalilin kukan ki bayan da magriba kukabar gidan nan" "Inna Issam yacuce ni, yaci amanata. Could you imagine bayan mun dawo gida naga wata arniya a gidan wai sunan ta Rita harda yaro a hannun ta, na tambaye sa wacece kinsan bud'an bakin sa abunda yace?" Inna tayi salati tace "Meya ce?" Tana wani irin kuka tace "Wai budurwarsa ce kuma yaron nasa ne, shine nace sam toh bazata zauna a gidan nan ba ya zab'a koh ni koh ita. Ya mini dukan gaske yace nafita nabar masa gidan sa" Inna tayi salati ta godewa Allah tace "Ikon Allah! Haka kukayi dashi? Ashe daman haka Issam d'in yake bashida mutunci? Gobe In Shaa Allah zan ma Sanusi magana ya kirasa yaji ta bakin sa" "Ku barsa kawai Inna ni na hak'ura dashi" "Sai muce ya aiko da takardan saki toh" Nan kuwa kukan ta ya tsaya cak, ita tama manta ashe bai saketa ba, a hankali ta furta "So stupid of me". Inna tace "Me kikace?" Cusa hannu tayi cikin sumar kanta wani irin jira na d'aukar ta, Inna tace "Idan bakiso ya sake ki toh zamu kirasa ayi sulhu karki damu kinji jikalle" Shiga d'akin ta tayi tana tunanin ashe fa Issam bai sake taba, rufe kofan d'akin tayi ta zauna dirshan a kasa ta rushe da wani irin kuka, a yanzu take dana sanin abunda ta masa. Nan take ta ciro wayarta ta latsa number'n Kbad Yana d'aukawa tace "Kun aikata aikin neh koh kuwa" "Tun yaushe Hajiya ai yanzu nashi ya k'are". Katse wayan tayi ta k'ara rushewa da kuka, Inna sai bubbuga k'ofa take akan ta bud'e kofa amma tak'i, Shamcy ma tayi bugun duniya taki ta bud'e. A k'arshe suka kira Mummy suka sanar da ita abun da ake ciki. Cikin fifteen minutes sai gashi tazo gida, buga kofan take tace "Habibty ki bud'e mini kofa Mummy ce, idan baki fad'a mini damuwar kiba mawa zaki fad'a?" A haka ta mata dad'in baki ta bud'e mata kofa. Tana bud'e wa ta fad'a jikin Mummy ta kuma rushewa da sabon kuka, Mummy kuma sai lallashin ta Tamshi, a haka har ta lallashe ta tayi shuru. Bayan duk sun zauna Inna tama Mummy bayanin abun sa Fido ta fad'a mata, Mummy tace "Habibty wannan k'arya kikayi, nasan halin Issam yana sonki sosai bazai miki haka ba ki fad'a mini gaskia meya had'a ki dashi?" Fido muryan ta yana shacking ta fara zano musu tun daga farko har binsa datayi UK har abunda yafaru a yau. Salati Mummy tayi ta wanke ta da wani irin mari wanda yasa taga stars tace "Kin bani kunya kin bani mamaki, sai kace niba uwarki ba. Nida nake zaman matar shi na barwa Allah komai ranar gobe zamuyi hisabi dasu balle ke yarinya k'arama, how are you even sure eh shi d'in neh? What prove do you have? Da dagaske kike ai da kin fad'a mini muyi sueing nasa a court. Wannan ba daidai baneh sam" Durk'usawa tayi gaban uwarta tayi tana kuka tace "Mummy ki yafe mini nasan banyi dai-dai ba, I made a very big mistake Mum. Mummy inason Issam fiyeda komai a yanzu, but nayi alkawarin zanga bayan shi and I can't live with mutum da shine sanadiyyar mutuwar mahaifina, Mummy I can't" ta kuma rushewa da wani kuka, Mum tace "Yanzu abunda zakiyi ki kawo mini evidence akan shiya kashe mahaifin ku idan ba haka ba bazan tab'a yadda dake ba" Tasowa tayi ta d'au safe d'in ta latsa password d'in kamar yadda ya fad'a Fiddausi sai gashi kuwa ya bud'e. CD plates biyu neh a ciki, d'auka d'aya tayi ta saka a DVD tayi playing **************** Six Years Back Alhaji Babangida Badamasi (Mahaifin Issam) zaune akan kujera a parlour'n sa yana duba wasu files, Yaya Ahmad neh yashigo cikin parlour'n suka gaisa, bayan sun gaisa Yaya Ahmad yace "Umm daman Uncle neh ya aiko ni wato ka amince da deal d'in?" D'aga kai Alhaji Babangida yayi yace "Haba dai ya Muhammadu zai mini haka? I told him several times wannan abunda sukeso na musu da governor bazai yuba, bazan iya bud'e musu wajen nan ba sabida budget na talakawa neh His Excellency ya bani a hannu na, nasan Muhammad bayin kansa baneh governor neh yake zuga sa" Cire bindiga yayi yace "Tunda baka yarda da deal d'in nan ba sukace na kashe ka na cire yatsan ka kaga easily zamu bud'e wajen" Tsaki yaja yace "You people ain't serious kun d'auka zaku iya tsoratar dani neh?" Dariya Yaya Ahmad ya fashe dashi yace "Mesa zamu tsoratar da kai ehhh? I am freaking warning you for the last time" Tsawa ya daka masa yace "Get out of my house now!" Murmushi Yaya Ahmad yayi yace "Say your last prayer" "I said getout!" Nan Ahmad ya harb'esa ya gutule yatsan shi ya fita a gidan da gudu... *************** Salati Mummy tayi tace "Ashe daman Issam yaron marigayi Babangida neh? Ikon Allah! Wallahi ban tab'a sanin matar shiba dan kullum tana garin su Yamen batason zama a nigeria" Fido kuma kanta neh ya d'aure ta rasa ganeh gaskiyar maganar, nan ta k'ara cire d'ayan CD plate d'in, ganin paper tayi nan take ta ajiye CD ta bud'e paper'n, bud'e paper tayi ta fara karantawa _Hayateey my heart is telling me kamar kin ganeh ni you just agreed to marry me so that you can avenge the death of your beloved Dad but believe me wallahi Allah banje gidan ku da niyyar kashe mahaifinki ba. Da farko na d'auka shiya turo yayan ki Ahmad akan yazo ya kashe Dad d'ina that's why nayi alkawari sai na rabasa da dukiyan sa tunda naga yana bala'in son kud'i not knowing that shima baisan da zancen ba. But I want you to know that I love you sooo much!!!!_ Wasu zafafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta, ashe shima haka aka kashe mahaifin sa?. A take ta taso tsaye tayi gudu tashige d'akin ta Mummy da Inna sai kiranta suke amma koh ta kulasu. Fitowar ta sai ga hijabi da key na mota a hannun ta, Mummy nan take ta bita itama tana cewa "Mamana ina zuwa karki yarda ki fita a gidan nan yanzu k'arfe sha biyun neh" Fido koh sauraron ta batayi ba ta shige motarta ta danna wani irin horn nan take mai gadi ya bud'e mata gate ta fisga motar. Wayarta ta d'auko ta latsa number Kbad tace "Kbad har yanzu kuna wajen?" "A'a fa bama wajen but kan mu aikata mishi ya bamu wasik'a mu kawo miki yanzu muna hanyan gidan ku ma" Ganin motar su Kbad tayi nan ta musu full light tareda danna musu horn suka tsaya. Parking motar ta tayi ta fito a motar ta tasame su, tace tana hawaye tace "Ina wasik'ar" Mik'a mata sukayi ta juya tashiga motar ta, kunna wutar motar ta tayi ta bud'e letter d'in wanda duk jini ya d'an b'ata taga *Ni Issam Babangida na sake matata Fiddausi Muhammad Sodangi saki d'aya* Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {Sept., 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to SHARE/VOTE!!! ```Page 47``` Mutuwar zaune tayi data karanta, zuciyanta na mai wani irin bugawa, ba wannan baneh mutuwar auren ta na farko amma wannan yafi mata tashin hankali fiyeda tashin hankalin daya sameta gidan Yaya Aliyu. Take ta fisga motar ta tana wani irin gudu akan titi har takai gidan ta, wani irin horn takeyi amma shuru, sauk'a tayi a cikin motar ta ringa buga gate nan ma shuru gate d'in ma a rufe da k'aton padlock. Zama tayi dirshan a bakin gate d'in ta rushe da sabon kuka, yi take har sanda muryan ta ya dashe hawayen ta suka tsaya. Ga wani irin ciwon kai da jirin dake d'eban ta. Ganin mota tayi anyi parking nashi dai-dai inda take, Mummy da Yaya Khaleal da Shamcy neh suka fito a cikin motar. Mummy ta sunkuya kusa da ita tace "Habibty baya cikin gidan neh?" Tana kuka tayi hugging nata tace "Mummy gidan rufe, bansan ina Issam yake ba, bansan a wani irin hali yake ciki ba, gashi ya sake ni Mummy na shiga uku" Bubbuga bayanta take a hankali tace "Shhhh! Baki shiga uku ba Habibty, In Shaa Allah everything will gonna be alright yanzu ki tashi mu tafi gida kusan k'arfe biyu fa" "Mummy ni bazanje ni gida ba sai naga Issam, Mummy wallah...." "Shhhh kiyi shuru Fido a daren nan ina zaki samu Issam? Kibari da asuba sai mufita neman sa kinji dan yanzu ba inda zaki same sa" Da k'yar ta lallashe ta suka sakata a mota sai gida, a gidan ma kuka take sosai koh wani minti biyu sai ta duba agogo taga koh k'arfe hud'u yayi. A haka batayi bacci ba anyi-anyi da ita ta kwanta amma sam taki kwanciya har k'arfe hud'u yayi. Tana ganin k'arfe hud'u ta tashi tace ita sam asuba yayi zata fita, haka Mummy da Inna sukaita bata hak'uri ta bari k'arfe biyar yayi, da k'yar ta iya jira zuwa k'arfe biyar, k'arfe biyar nayi tace zata tafi, Inna ta rufo k'ofa tace sam sai taci abinci, da k'yar ta yadda ta iya shan Tea kad'an tace ya isheta, had'ata da Yaya Khaleal akayi ya kaita duk inda takeso. Suna cikin mota Yaya Khaleal yace "Fido yanzu gidan ki zan kaiki koh ina? Fido da tayi zuru zuru daga jiya zuwa yau har ta wani rama idonta ya fito murya a dashe tace " Gidan Eesha zan fara zuwa" Direct gidan Eesha yayi da ita, da d'an gudu-gudu tashiga gidan tana kwad'a sallama, da sauri Eesha ta fito a d'akin ta tace "Fido lafiya? Ina kiranki jiya da daddare bakya picking calls nace da safe zanzo na duba ki" "Ina Issam?" Ajiyar zuciya Eesha tayi tace "Da asuba suka bar asibiti jirgin shi zai d'aga Abuja 7:00am" Take ta d'aga idonta dan ganin agogon dake mak'ale jikin bango taga 6:59 "Ohhh shit!" Ta furta a hankali tafita a gidan da gudu tashige motar tana haki tace "Yaya Khaleal muje airport and please drive fast idan bazaka iya gudu ba ka sauk'a kaban waje naja" Fisga motar yayi yana wani irin gudu akan titi, duk gudun da yakeyi gani take kamar baya tafiya, 7:12 dai-dai suka shigo cikin airport. Da gudu tashiga wajen ta tambaya akace mata yanzu yanzun nan jirgin ya d'aga. Fita tayi a guje ta same Yaya Ahmad tace "Can you drive me to Abuja?" "What! Abuja kuma? Bakida hankali neh?" "Dan Allah kayi hak'uri idan bazaka iyaba ka sauk'a kawai zan iya driving da kaina wallahi Allah" Tausaya mata yayi sosai yace "Toh shikenan barana kira gida" D'aukan wayar sa yayi ya kira Mami ya sanar da ita, ta musu Allah kiyaye hanya kuma yace ta fad'awa Mummy da Inna. Bayan sun gama wayan ya fisga motar sai hanyan Abuja, gudu yake sosai akan titi Fido gani take kamar ma baya tafiya taja dogon tsaki tace "Dan Allah ka sauk'a naja motar nan" Wani uban speed ya k'ara yana tafiya at 100, ni kaina sanda na tsorata a irin gudun da sukeyi, wata motace babbar Daf take zuwa ta gaban su kan su matsa gefe suka shige daji, yayi×2 ya danna brake amma ina is too late suka buga wata bishiya sai ga motar tayi kaca-kaca..... _After Eight Hours (Bayan awa takwas)_ A hankali take bud'e idonta ga wani irin ciwon kai dake addabar ta harta bud'e idonta gaba d'aya. Tunani take meya faru da ita har aka kawo ta asibiti dan da ganin cikin d'akin asibiti neh ga drip dake mak'ale a hannun ta. Sallamar da Doctor tayi shineh ya dawo da ita daga dogon tunanin data fad'a, Murmushi Doctor ta mata tace "Ya jiki k'awata" Da k'yar ta iya furta "Da sauki" "Meke damun ki yanzu, any pain?" "Kaina neh ke ciwo ga jiki nah ba k'arfi" "Karki damu zaki samu lafiya In Shaa Allah" "Dr please meya faru dani? Wannan wani asibiti neh?" "Don't stress yourself karki damu kinji" "I need to know neh, ina 'yan uwana?" "Gaskia kam you really need to know, accident kukayi a hanya shineh aka kawoku National Hospital, nan Abuja ne, had it been namijin da kuke tare dashi ya farka da ban fad'a miki ba, nida mijina a idon mu accident d'in yafaru shineh muka d'auke ku muka kawo ku asibiti Allah yaso ma ina aiki anan. But karki damu mun d'au wayar ku munga last dialed number suna Mami kuma munyi calling nasu yanzu suna hanya ma" Yanzu neh abun ya dawo mata kai, wani sabon tashin hankali ya taso mata "Dr ya jikin shi yake?" Murmushi tayi tace "Karki damu zai samu sauki In Shaa Allah don't worry. Yanzu nurse zata shigo da abinci idan kinci zata baki magani kisha" "Ohk Thank you" "Zan wuce sai da safe" "Yanzu k'arfe nawa neh?" "8:20pm, karki damu na kira mutanen gida kan nashigo d'akin nan ma sukace already suna cikin abuja so any moment from now zasuzo" "Ok nagode sosai Allah saka da alkhairi sai da safe" "Ameen! Goodnight" Dr tana fita a d'akin Fido ta damke idota tacire drip da aka mak'ala mata a hannu. Da k'yar ta iya tasowa dan ta bugu akanta sosai gashi goshin ta duk bandage, neman hijabin ta tayi dan ta rufe kanta amma bata gani ba, a k'arshe purse nata tagani a kan kujera ta d'auka tafita a d'akin ba d'ankwali duk suman kanta a waje. D'akin gefen ta tashiga tayi sallama taga wata yarinya mai kimamin shekaru goma sha bakwai a d'akin ga mata kuma kwance kan gado. Bayan sun gaisa Fido tacewa yarinyan "Sister dan Allah zan samu hijabi nayi sallah?" Murmushi yarinyan tayi tace "Mai zai hana na baki, gashi da gani kina jin jiki sannu Allah k'ara sauki". Hijabin gefenta ta d'auka ta mik'a mata, murmushi Fido tayi tace "Nagode sosai, d'aki nah shine next to you idan nagama zan aiko miki" "A'a karki sha wahala zanzo na karb'a da kaina" "Nagode" Fido saka hijabin tayi ta kama hanyan fita a asibitin, da k'yar ta samu k'ofan fita ta fice. Tana fita ta tsaida taxi tace masa Maitama. A daidai k'ofan gidan su Issam ta sauk'a ta biyasa kud'in. Danna bell na gate d'in tayi sai ga mai gadi ya bud'e mata k'ofa. Bayan sun gaisa yace "Ikon Allah Hajiya sai yau d'azu naji labarin mai gidan ki ya dawo gida amma bamu had'u ba sabida naje sadakan uku an mana rasuwa kanna dawo akace mini ya koma amma. Hajiya duk yadda akayi ba lafiya ba naganki haka duk ciwo a jikin ki" Murmushi tayi tace "Lafiya kalau wallahi, Hajiya tana ciki?" "A'a fa bata ciki, Issam yana dawowa gida tace a fad'a mini zasuyi tafiya amma zasu dawo kwanan nan" Zuciyan tane yayi mugun tsinkewa "yanzu kana nufin ba kowa a gidan?" "Wallahi ba kowa inaga suma ba lafiya ba dan tafiyar gaggawa sukayi" Wani jiri neh ke damun ta ji take kamar zata fad'i k'asa, kama kanta tayi ta rufe idonta dan Allah kad'ai yasan yadda takeji. Take mai gadi ya shiga gidan ya kira matarsa suka fito tare a lokacin har Fido ta fad'i k'asa Yace "Haule taimaka ki shigar da ita cikin gidan ba Hajiya tabaki mak'ulli kina shiga kina share gidan ba?" "Eh tabani". Da k'yar ta iya taso da ita suka shiga ciki ta bud'e mata cikin gidan tace " Duk d'akunan a rufe suke amma inaga d'akin mijin ki a bud'e yake" "Yana da d'aki neh anan side d'in?" Murmushi Haule tayi tace "Yana dashi, ai baison kwana acan sai anan sanda kukayi aure yake kwana a b'angaren sa" "Ina d'akin yake?" Nuna mata tayi tace "Gashi can" "Nagode" "Ba komai barana kawo miki abinci da maganin ciwon kai" Fita tayi a parlour'n Fido kuma ta kwanta flat akan dogon cushion, cikin ten minutes saiga Haule tashigo da kwanuka da maltina tace "Hajiya ki tashi kici abinci bakida lafiya ga kuma maganin ciwon kai" Da k'yar ta iya ta tashi, wainan kwai neh da d'anwaken fulawa tace "Hajiya Allah sa zaki iyacin irin abincin mu" Murmushi Fido tayi tace "Shine favourite d'ina ma" Nan tafara ci a hankali tana shan maltinan, Haule tace "Hajiya na tambaye ki mana dan Allah" "Ina jinki" "Meya sameki haka naga goshin ki duk bandagi" "Hatsari nayi a hanyan zuwa na nan" "Allah sarki Allah baki lafiya" "Ameen" "Ni zan wuce sai da safe" "Allah kaimu" Bayan ta d'an ci kad'an ta wanke hannun ta tasha maganin da Haule takawo mata ba tareda ta duba sunan maganin ba, da k'yar ta iya tashiwa ta shiga d'akin da aka nuna mata na Issam. A hankali ta bud'e k'ofan k'amshin turaren sane ya dake hancin ta, ji take kamar yana cikin d'akin. Mutuwar tsaye tayi dataga pictures nata a duk jikin bango. Wasu tana restaurant, wasu tana coffeehouse, wasu tana tafiya, wasu tana cikin class, a ko wani hoto ya rubuta HAYATEEY boldly.. Bin pictures d'in take d'aya bayan d'aya tana shafawa tana hawaye!!!!! Many suna tambayana ina labarin Issam???? Please don't panic zakuji labarin sa next page In Shaa Allah Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We just don't just entertain and educate, but we also touch the ❤hearts of the readers] Written By Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ ```Page 48``` A lokacin da Fido tabar d'akin Issam ta cewa su Kbad su aikatar da aikin data saka su d'aukan adda Kbad yayi yace "Alhaji kayi bye-bye da jin dad'in duniya" Wani yanka ya masa a hannun sa shineh dalilin dayasa yayi k'ara sosai dan yashige shi komai, Kbad ya b'arga boxers nasa ya d'aga gaban sa zai fara yankawa kenan Issam da k'yar ya iya furta "Zan muku doubling kud'in data baku" Kwashewa da dariya sukayi d'aya daga cikin su yace "Kasan nawa aka bamu kuwa? Naira na dukan naira har dubu d'ari" "Zan baku dubu d'ari biyu ku kunce ni" Kbad koh sauraron sa baiyi ba ya aza adda akai yaja sai ga jini yana malala, dariya sukayi sukace "Wanna soma tab'i neh, next kawai idan mun aza akai bazamu cire ba sai mun rabashi kashi biyu" Suka k'ara rushewa da dariya, 'yan sanda neh suka shigo d'akin suka nuna musu bindiga. Ba k'aramin tsorata sukayi ba dan a rayuwar su sun tsana 'yan sanda koh sojoji. Da sauri d'aya daga cikin police d'in ya d'aura wa Issam wajen yana masa sannu. Haka 'yan sandan sukayi arresting 'yan daban kusan su goma suka saka su a motar su, Issam da k'yar ya iya furta yace wa inspector d'in yace "Taya kuka san ina cikin wannan yanayin?" Inspector Tukur yace "Wannan baiwar Allah'n ita tazo ta sanar damu mu kuma mukazo cikin gaggawa" D'aga idon da Issam zaiyi yaga yarinya kyakkyawa ajin farko wanda ak'alla bazata haura shekaru ashirin da biyar ba, fara sol ce ga idon ta dara-dara, hancin ta tsit kamar pencil sai bakin ta madai daici. With so much surprise Issam yace "SALALA?" Murmushi tayi tace "Ya Issam don't stress yourself muje asibiti" "Tell me yakika sani?" Ajiyar zuciya tayi tace "Tun da rana nazo ni gidan na maka surprise visit naji tana waya, na kiraka a waya har na gaji baka d'aga ba a k'arshe nayiwa 'yan sanda waya bayan munzo gidan kuma mai gadi yace kun fita, haka muka ta neman ku a gari daga baya kuma muka dawo gidan" "Nagode Salala" "Anything for you broh" Suna haraban gidan gaba d'aya Fido ta kira Kbad a waya, har d'aya daga cikin police d'in zaiyi receiving Issam ya hana yace "Ku barshi yayi picking and kayi pretending baka tareda 'yan sanda kuma kace mata na baka letter ka bata" Haka Kbad yayi receiving call d'in Yace "tun yaushe Hajiya ai aiki ya k'are" zai cigaba Issam yayi masa nuni da hannu akan yayi shuru itama already ta katse wayan. Haka sukayi plan akan su Kbad su shiga motar su sukai mata takardan saki idan yaso sun bata sai su wuce dasu police station. Police d'in sunyi suyi arresting nata amma yahana. Tun a mota ya rubuta mata saki d'aya wanda koh kad'an bawai dan yaso ba sabida kawai bata sonshi and bazaiso ya zauna yana cutar da ita batason shi ba and duk da yana sonta bazai iya cigaba zama da ita ba. Suna hanyan gidan su Fido ta k'ara kiran Kbad a lokacin Kbad yake sanar da ita Issam ya bata sako. A idon su Issam Kbad ya bata letter harta shiga cikin motar ta.... Asibiti direct aka wuce dashi daga nan aka masa taimakon gaggawa aka d'inke wajen. Doctor daya d'inke ya kira Salala gefe lokacin kusan k'arfe biyu, bayan sun gaisa yace mata "A gaskia an samu matsala dan yanzu possibility da zai haihu is 40% but akwai Allah In Shaa Allah zai iya producing egg" Zuciyan Salala ba k'aramin bugawa yayi ba tace "Yanzu Doctor idan na d'auke sa na kaisa India fa? Akwai wani friend nah likita neh sosai he's good in this field" "Ohk ba komai zaki iya kaisa can" Tun a dare take waya take neman flight na India, akace mata sai jibi zai tashi a Lagos, haka ta nema na Abuja da k'yar wajen wata friend nata da take aiki a Umaru Musa airport. Da asuba ta kira abokin sa Faruq sukaje su airport k'arfe bakwai cif jirgin su ya d'aga zuwa Abuja kuma a k'arfe goma jirgin da zai kaisu Lagos zai tashi. Mum har zub da hawaye tayi dataji abunda Fido ta shiryawa d'anta, a gaggauce suka shirya kayan su zuwa airport. A k'arfe goma dai-dai jirgin da zai kaisu Lagos ya d'aga....... *************************** Fido haka ta ringa shafan pictures d'in tana kuka, a k'arshe zube kasa tayi bacci mai nauyi ya d'auke ta... _Washegari_ Ita bata tashi a bacci ba sai k'arfe goman safe, a yanzu ta d'an ji kanta yayi sauki kad'an amma jirin har yanzu yana nan. Duba agogon jikin bango tayi taga 10:05, da sauri ta taso daga kwance tace "Subhan' Allah". Wani relief taji data tuna tana fashin sallah, da k'yar ta iya ta cire kayan ta, bud'e wardrobe nashi tayi ta d'au towel ta d'aura. Kwasan kayan ta tayi ta wanke su tas ta shanya a toilet d'in tayi wanka. Haule ce tayi sallama tashigo d'akin da tray a hannunta ta dira a k'asa, bayan sun gaisa Haule tace "Hajiya kinsha bacci koh?" Murmushi Fido tayi tace "Wallahi nasha bacci har naji ciwon kaina da d'an sauki" "Ai dole, naga yanayin ki jiya shiyasa na had'o miki da maganin bacci" Zaro ido Fido tayi tace "Haba shineh baki fad'a mini ba?" "Na d'auka kin ganeh su neh ai kiyi hak'uri ashe sha kawai kikayi" "Karki damu ba komai" Jan tray d'in tayi zuwa gaban Fido tace "Ga abinci nan" Murmushi Fido tayi tace "Haba Haule nasa ki wahala haka?" "Ahhh haba dai wani wahala, ba wani wahala wallahi. Ni zan d'an fita sai na dawo" "Toh sai kin dawo" Bayan Haule ta fita ta bud'e abincin fried yam neh da kwai, wasu zazzafan hawaye neh suka fara sauk'a kan kuncin ta, Issam neh ya dawo mata akai dan bashida abincin da yakeyi da safe sai fried yam da kwai tace *" I miss you Issam"*. Haka tana cin abincin tana hawaye. Sallama taji da sauri ta d'aga kanta, ganin Mummy da Mami tayi, da gudu taje ta rungume Mummy tana wani irin kuka mai tsoma zuciyan duk wani mai sauraro tace "I had gotten so used to seeing him everyday, that now he was gone, the house was painfully and obviously quiet" "Shhh kiyi shuru Habibty In Shaa Allah zaki samu Issam ki daina damun kanki" Haka sukaita lallashin ta tayi shuru, daga baya sukace ta shirya zasu koma gida, duk yadda tayi akan su barta zata zauna suka k'i. Haka ta bisu zuwa asibiti aka rubuta mata magani aka sallame Yaya Khaleal suka d'au hanyan KT. Su basu isoba sai da yamma likis, suna sauk'a a motar 'yan gidan suka fara fitowa d'aya bayan d'aya suna lek'a su. Itadai bata kulasu ba tashiga cikin gida...... ********************** _Bayan Kwana Biyar_ India New Delhi Taj Mahal Hospital A wani babban d'akin cikin asibitin Issam neh kwance akan gado Mummy kuma zaune a gefen sa tana had'a masa shayi, bayan ta had'a ta mik'a masa ya karb'a yafara sha, Mummy murmushi tayi tace "Yanzu jikin da sauki koh?" "Sosai Mummy ai na warke saura mu koma gida" "Nikam mene kabi ka damu mu koma gida, daganan fa sai Yemen" Had'a rai yayi yace "Mummy Yemen kuma?" "Sosai kuwa kuma zamu kai kusan wata shida haka" Nan take ya ajiye cup d'in shayin hannun sa yace "Mummy har wata shida? Toh business namu fa?" "Akwai managers ai and suna alerting naka komai" "Mummy ni gask...." Bai k'arasa ba ta tare numfashin sa tace "Nasan dalilin dayasa kake son komawa Nigeria, toh wallahi bari kaji na rantse da Allah wallahi Allah idan ka maida Fiddausi bani babu kai, kai koh na mutu ban amince ka aure taba" Zuciyan sa ne yayi mugun bugawa, bai san lokacin da ya taso ya kama hannun Mummy ba yace "Dan Allah Mummy karki mini haka Mummy.." "Shhh idan ka k'ara mini zancen ta ban yafe ba, yarinyan da take neman halaka ka, yarinyan data tsaneka, yarinyan datake son ganin bayan ka, ka fad'a mini wani irin mutum neh zai maka haka idan ba babban mak'iyin kaba" Shuru yayi ya zuba rinannun idanuwan sa yana kallon ta "Fad'a mana! The truth is always bitter nasani but ni mahaifiyar kace kuma nace BAKAI BA ITA HAR ABADA, muna komawa Yemen za d'aura auren ka da Salala faqat!" Komawa gado yayi ya kwanta tareda rufe eyes nasa da k'yar ya iya furta "Allah sa hakan shine mafi alkhairi Mummy" Murmushi tayi tace "Ameen Son Allah maka albarka" _Bayan wata biyu_ Fiddausi ba k'aramin lalacewa tayi ba, ta daina fita aiki ta daina zuwa ko ina kullum tana aikin kuka. S.A yayi×2 da ita akan tunda ba idda akanta a d'aura musu aure amma tak'i. A koh wani bayan kwana biyu take zuwa Abuja koh sun dawo amma kullum amsar d'aya neh basu dawo ba.. Kamar koh wani bayan kwana biyu yau ma tana Abuja cikin gidan su Issam ta saka mai gadi a gaba tana masa kuka tace "Dan Allah ka taimaka ka bani number sa dan Allah" Wani irin tausayin ta Haule taji dan kowace rana idan tazo tana rok'on number'n su amma basu tab'a bataba dan Mummy tace kar a bawa kowa number'n. Haule tace "Fiddausi a gaskia bamuda number'n mai gidan ki amma munada number Hajiya" Da sauri Fido tace "Ku taimaka mini ku bani dan Allah" Haka suka bata number'n nan take ta latsa, ringing d'aya biyu Mummy tayi picking, nan Fido ta taso tsaye tana farin ciki tace "Mother ina yini, dan Allah Fiddausi ce, dan Allah karki katse wayan ki saurare ni" Kit Mummy ta katse wayan, haka ta ringa trying amma bata picking. Daga baya ta d'au jakarta ta musu godiya ta shige motar ta wanda yanzu ta d'au driver musamman wanda zaina kawo ta Abuja yana maidata gida KT..... Sai can dare ta isa gida KT tana zuwa bayan tayi wanka tayi sallah ta d'au wayarta ta k'ara latsa number'n Mummy. Ringing d'aya Mummy tayi picking tace "Mun yafe miki Fiddausi but karki k'ara kiran number na, yanzu bakida wani alak'a da Issam, Son bazai tab'a maida auren kuba sabida haka karki b'ata lokacin ki plus inaso ki sani yanzu watan shi biyu da aure" ta katse wayan.... Wasu zazzafan hawaye neh suke sauk'a akan kuncin ta, wani irin kishi takeji mara misaltuwa, ta rasa abunda yake mata dad'i a duniya, fashewa da wani irin kuka tayi mai tsoma zuciyan duk wani mai sauraro......... _Yemen_ Issam kwance akan gado ya rufe idonsa ya k'ara haske ga sajen sa wanda ya kwanta luguf a fuskar sa suman kansa na wani irin walk'iya da shek'e kallo d'aya zaka masa kasan ya rame sosai amma ya k'ara kyau, Salala ce tashigo d'akin wani dogon arabian gown bak'i neh ajikin ta tayi rolling kanta da veil bak'i ba k'aramin karb'an ta yayi ba dan fara ce sol kuma ya had'u da kaya bak'i, pecking nasa tayi tace "Habeebi guess what?" Bud'e sexy eyes nasa yayi ya mata kiss yace "You know i ain't good at guessing just kawai ki fad'a" Mik'a masa paper tayi ta rufe fuskanta da hannayen ta wanda yasha jan lalle yayi kyau sosai "What!" Ya furta tareda murza idonsa mai kyau yana mai k'arewa paper'n kallo "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah nagode maka" D'aga Salala yayi cak yana jujjuyata ita kuma tana dariya *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written by Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {Sept., 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to Vote,Share and Comment!!!!!! Many suna complain basu samu na a Wattpad here is my link: http://my.w.tt/UiNb/eSBnvlncmG ```Page 51``` *This page goes to all members of PML WRITERS TRUE FANS❤. I heart you guys to pieces😘😘* Tun lokacin da Issam suka rabu da Fido a Lagos basu k'ara had'uwa. Tunda suka kuma gida Abuja ya daina magana sai "eh" koh "a'a". Har yafi Issam nashi na da miskili yanzu yafi abunda ake kira da miskili, ba yadda Mummy batayi ba akan ya fad'a mata abunda ke damunsa amma yace ba komai. Wata d'aya da dawowan su Salala ta haife kyakkayawar 'yarta, Issam ba tareda yayi shawara da kowa ba ya rad'a wa yarinyan suna FIDDAUSI amma yana kiran ta da Jannah. Abun ba k'aramin sosa masu rai yayi ba Mummy tayi masifa tayi fushi amma duk a banza baima san tanayi ba. Salala kam kullum sai ta sha kuka dan tun daga ranar da ya rabu da Fido a Lagos ya daina shiga harkar ta. Idan tana kuka sai ya zauna yata kallon ta yace "Kiyi hak'uri bayin kaina baneh na k'asa cire Hayateey a raina neh". Idan zai kira sunan ta sai ya kirata da Fido, idan ta nema hakkin ta suna raya sunna ba sunan da yake fitowa a bakin sa sai Hayateey~Fido, abun sosai yake cin ranta, a kullum sai taje wajen Mummy tana kuka tace "MUMMY GANGAR JIKINSA NA AURA, Mummy kisa ya sake ni dan bazan iya zama dashi ba". Haka kullum Mummy ta ringa bata hak'uri, ta kira Issam ta masa fad'a amma sai abunda yayi nesa. A haka har akayi shekaru biyu, kullum yakan shiga d'akin sa na cikin part na Mummy wanda akwai pictures na Fido yata kallo yana nunawa 'yarsa Jannah wanda a yanzu ta girma tana magana, kullum suna shiga d'akin suta kallon ta suna hira. Idan yana zaune ma Jannah takan ce " Daddy bazamu je wajen Hayateey ba?" Toh fa nan duk abunda yake zai tashi su shiga d'akin suta kallon pictures nata suna hira, baida abokin hira a gidan sai 'yarsa Jannah... Rana d'aya sun shiga d'akin da Jannah kawai yaga wayam ba pictures, ransa yayi mugun b'aciwa ya same Mummy da Salala suna d'aki suna hira, zama yayi shima yace "Mummy waya cire pictures na Fido" A tsawace tace "Nice" "Mesa?". Ba k'aramin mamaki tayi ba da yake tambayan ta mesa, tace " Awww duk abunda ta maka baka gani ba" Salala ta fashe da kuka tace "Nidai Mummy ya sake ni wallahi nagaji da zama dashi idan bazaki sa ya sake ni ba zan tafi Yemen na kai k'ara wallahi nagaji" "Ki barni dashi nace bazai sake ki ba shida Fiddausi kuma sai a lahira duk abunda ta masa bai gani ba" Issam gathering confidence yayi yace "Mother ba abunda Fido ta mun, asalima ni na mata laifi. Kinsan me na mata kuwa? A ranar da b'arayi suka shiga gidan su Fido toh harda ni aciki" Mummy bud'e baki tayi tana kallon sa yacigaba "Tun ranar da naji labarin baban ta shi ya kashe mini Abba na d'au alkawarin sai naga bayan sa, banyi niyan kashe shi ba amma nayi alkawarin rabasa da duk properties nashi, na samu wasu gangs na b'arayi suka mini jagora na shiga gidan dan na karb'a duk k'addarorin sa nazo nasa a kashe yaron sa Ahmad wanda akafi sani da GONER, bayan mun shiga gidan na karb'a duk wasu takardun nasa yayi signing not knowing bakin su d'aya da Ahmad yasa su kashe ni, bayan mun fita naji tausayin su sosai nayi alkawarin zan maida musu da duk wani abunda na karb'a sai b'arayin da mukazo dasu suka harb'e ni a hannu suka karb'a takardun sukace Ahmad neh ya saka su, haka na sa ake mun bincike Ahmad shineh dalilin zuwa nah UK, tun acan na gano ba Dad nata baneh yasa a kashe Abba shineh suka had'a baki da governor akan zai biyasa, ita kuma ashe ranar dana shiga gidan su ta ganeh ni tayi alkawarin d'aukan fansa, shine dalilin da yasa tamun haka" Wasu kyawawan mari guda uku Mummy ta wanke sa dashi, ranta idan yayi dubu ya b'aci, hawaye take tace "Issam yaushe ka zama haka? Har zaka iya shiga cikin gidan su mutaneh da tsakar dare da suna sata? Ka bani mamaki, kaci amanar yadda dana makaa. Kaci amanar mahaifin ka, dukda munje court amma bamuyi nasaraba lokacin bai kamata ka d'au d'anyan hukunci ba, bai kamata sam kayi haka ba, ka bani mamaki, ka bani mamaki Issam. Sam ni yanzu banga laifin Fido ba dan hali d'aya kuke, duk kuka k'asa hak'ura Allah ya musu hisabi ranar gobe ku a dole sai kun d'au FANSA, yanzu suwaye suke shan wahala idan ba ku ba? kuma haka zaku dawwama cikin wahala dan bazan tab'a bari ka aure taba, tunba yau ba Salala take kawo mun k'ara akan gangar jikin ka ta aura ba ruhin kaba, yanzu inaso ka sake ta dan ba amfanin zama da mutum irin ka, baka dace da mace irin Salala ba sam" Zuwa gaban Mummy yayi yana hawaye yace "Mummy ki yafe mini, nasan nayi kuskure amma dan Allah ki yafe min, kuma bazan iya sakan Salala ba". "Bazaka iya sakan taba?" "Eh bazan iya ba" ya fad'a hankalin sa a tashe, Salala ce ta taso tazo gaban sa tace "Zaka iya min rabin son da kake yiwa Fido? Karka min k'arya Issam if you lie to me i'll never forgive you for that" Girgiza kansa yayi yace "Kiyi hak'uri Matata amma bazan iya miki rabin son da nake yiwa Fido ba, but I promise with time kina sakani addu'a Allah yasa na iya miki" Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace "Mummy kisa ya sake ni kawai" ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan duk wani mai sauraro. Mummy a tsawace tace "Ka sake ta nace koh nayi fushi da kai, fushi na har abada" Hankalin sa neh yayi bala'in d'agawa muryan sa yana shaking ba wai dan yaso ba yace "Ni Issam na sake matata Salala saki d'aya, idan kin samu miji kiyi aure" A take Salala ta fita a d'akin tana kuka sosai, Mummy ma tana hawaye ta nuna masa k'ofa tace "Ka fita mini a gida" Kallon ta yake da renannun idanuwan sa wanda sukayi jazur yace "Mothe..." Bai k'ara sa ba ta tare numfashin sa tace "I said OUT!!!!!!!" A sanyaye ya tashi ya bar wajen, side nasa direct ya wuce, ganin Salala tana kuka ya zauna kusa da ita yace "Me amfanin kukan da kikeyi bayan ke kika sa na sake ki" D'aga jajayun eyes nata tayi ta sauk'e su akan sa tace "Ka fad'a min good reason da zan zauna da wanda baya so nah?" "Koh sabida 'ya dake tsakanin mu" "Hakan na nufin sabida 'ya na zauna cikin kunci da bak'in ciki? Na tabbata 'yata baza tab'a so na zauna da wanda baya sona kuma bai d'auke ni a matsayin matar sa ba" "Shikenan Salala ya isa!". Ya tashi yabar wajen.... _A Bayan shekara d'aya_ (da shekara biyun dana fad'a muku shine ya kama shekaru uku kenan). Back To Asalin Labari Issam neh yashiga d'akin Mummy ya zauna ya gaishe ta, tun daga lokacin ba abun kirkin dake shiga tsakanin su sai gaisuwa, bayan sun gaisa zai tashi ya tafi tace " Son!" Nan ya tsaye cak dan rabon ta data kirasa da Son har ya manta "Zauna mana" Zama yayi kansa a k'asa, tace "Gobe Salala zatazo Nigeria" "Allah kaimu" "Ameen.... Zatazo ta gaishe ka, and kuma daga yanzu na baka izini kaje wajen Fiddausi ku dai-dai ta" Take ya d'aga eyes nasa yana kallon ta he just can't believe abunda tace, murmushi tayi tace "I am serious Son, go don't loose her". Murmushi yayi yama kasa magana he is speechless rungume ta yayi ya fita a d'akin....... Washegari..... Ranar Aure Fido tasha gyaran jiki tayi kyau sosai, zuciyan tane yake mugun bugawa idan ta kalla agogo, d'aga sexy eyes nata tayi cike fal da hawaye tace "Yanzu k'arfe tara saura minti goma(8:50am)" Murmushi Eesha tayi tace "Karki damu k'awata nan da awa d'aya da minti goma zaki zama matar General Aliyu ki daina zumud'i time yanzu zai gudu" "Mtsw Eesha zamud'i kuma? Auren nan fa ba yau neh na farko na ba, ina tausaya wa rayuwata zanyi spending rest of my life da mutumin da bana so. No! nafi tausayawa Yaya Aliyu da zai aura macen da bata sonsa" Eesha zama tayi kusa da ita tace "Karki damu with time zaki fara son sa kuma ai jinin ki neh" Murmushi tayi tace "I hope so" Shamcy ce tashigo da gudu cikin d'akin tace "Adda Shamcy na had'u da Yaya Issam a corner'n layin gidan nan, ya tambaye ni me ake a gidan yaga taron jama'a na fad'a masa auren ki yau ya juya da motar sa ya koma" Eesha taja tsaki tace "Yaushe muka rabu dake da har kika fita?" "Wallahi Allah da gaske nake na fita wajen tela karb'an kaya nah d'inki ai, idan k'arya nake miki ki tambaye Yaya Khaleal" Fido ta kama hannun ta tace "Karki min k'arya Shamcy ki fad'a min gaskia, idan har kika min k'arya zanyi fushi dake" "Wallahi fa nace miki Adda Fido Allah na gansa" Nana Fa'ad *HAYATEEY* Pure Moment Of Life Writers [We don't just entertain and educate, we also touch the ❤ hearts of the readers] Written by Nana Fa'ad _In dedication to Fido Sodangi_ {Sept., 2017} Follow me on Wattpad @Nana_Faad. Do read my write-ups and please don't forget to Vote,Share and Comment!!!!!! Many suna complain basu samu na a Wattpad here is my link: http://my.w.tt/UiNb/eSBnvlncmG ```Page 52``` The🔚 My last page goes to Eesha bae and Maryam Qaumi.. I ❤ yhu gurls to pieces😘 Nan take ta taso ta saka hijabin ta baibai tace "Shamcy bani key na motar ki" Eesha with confuse face tace "Kije ina?" "Ki barni Eesha ba ruwan ki". Ta juya wajen Shamcy a tsawace tace "I said give me the damn key gurl!" Shamcy ta tsorata da ita nan take ta mik'a mata makullin motar, take ta fita a d'akin. Zagaya haraban gidan take da gudu tana neman inda Shamcy tayi parking motar ta, kowa sai kallon ta yake da mamaki ana cewa "Fiddausi lafiya?" Amma ina babu wanda ta kula kuma bata damu da mazan da suka taru a wajen ba. Aliyu neh ya shiga cikin gidan ganin hankalin ta a tashe tana safa da marwa cikin gidan yace "Ke Fiddausi lafiya kike?". Koh kulasa batayi ba kawai sai ga Shamcy, a tsawace tace " Where the fuck kikayi parking motar" Shamcy muryan ta yana rawa tana regretting da bata fad'a mata ba tace "Outside" A guje Fido ta fita waje, ga maza sun taru an shimfid'a musu tabarma, danna key d'in motar tayi dan bazata iya bincikan motar ba dan irin yawan motocin wajen, tana jin k'arar motar take tabi direction d'in. Tana ganin motar ta shiga ta fisga da gudu, tafiya take da gudu akan titi kamar wacce zata tashi sama, Aliyu ma yana bin bayanta ita bata ma san yana yi ba har ta kai gidan Issam... Ganin sa tayi a cikin mota ya kifa kansa kan siteri, nan take ta fita a motar tazo wajen motar sa tayi knocking window'n motar, take ya d'aga eyes nasa wanda yake fal ciki da hawaye ya sauke su akanta. Ganin ta da yayi ba k'aramin mamaki yayi ba, jikin sa yana shaking ya bud'e k'ofa ya fita a motar. Fido durk'usa wa tayi a k'asa ta fashe da wani irin kuka mai tsoma ran duk wani mai sauraro tace "Issam ka wahalar da rayuwata, ka wahalar da ZUCIYA ta, shin bakasan irin son da nake maka baneh? Kaine Rayuwata, kaine jin dad'i nah. You mean the world to me without you the world is nothing to me. You are the other half of me, the most beautiful and best half of me I love you better than I love me, You are my HAYAT" Ta fashe da kuka tacigaba "Mesa zaka mun haka? Mesa ka kasa yafe min? Mesa ka gujeni?" Issam wanda idanuwan sa sunyi jazur yana kallon ta yace "You have no idea irin yadda nake rayuwa for all this years. My silence doesn't mean i forgot you, My disappearence doesn't mean i don't care about you cox you will always be in my deep heart. Kinsan when you love someone truly, you don't look for faults,you don't look for answers, you don't look for mistakes. Instead, you fight the mistakes, you accept the faults and overlook the excuses. Ban tab'a tsanan ki koh jin haushi ki akan abunda kika min ba sabida inason ki fiyeda tunanin duk wani mai tunani, ina sonki more than my own life". Fido wani dad'i taji tace "Just tell me KA DAWO GARENI" Juyawan da zatayi taga Aliyu zaune a cikin motar sa, ganin sun had'a ido Aliyu ya fisga motar sa da gudu yabar wajen, Issam ganin Aliyu yayi murmushi yace "Kije ki Hayateey, haka Allah ya k'addara mana" Girgiza kanta take tana kuka tace "Bazan iyaba" "Idan har kina sonah Fido do this to me, ki koma gida" Zatayi magana yace "Shh banson wata magana, kije ki kawai". Issam shiga motar sa yayi ya fisga ya barta nan tsaye tana wani irin kuka mai soma ran duk wani mai sauraro, sanda tayi mai isarta ta tashi tashiga motar ta, da kyar ta iya driving har takai gida a lokacin k'arfe 10:15am, zuciyan ta yana bugawa tashiga gidan taja hijabinta ta rufe fuskan ta har takai d'akin ta, tana shiga ta cire hijabinta ta kwanta kan gado tana kuka sosai, Eesha tazo ta zauna kusa da ita tace "Lafiya kike kuka Fido? Kin had'u da Issam d'in?" Tasowa tayi ta rungume Eesha tace "An d'aura koh?" "Ba'a d'aura ba har yanzu bansan me suke jira ba" "Eesha kije ki fad'a musu ISSAM YA DAWO GARENI kar a d'aura min aure da Yaya Aliyu" "Kiyi hak'uri Fido amma bazan iya ba" "Toh ina Shamcy?" "Ta fita" Kwanciya ta k'ara yi a kan gado ta fashi da kuka, yi take har sanda muryan ta ya dashe, Eesha tun tana bata hak'uri har itama tagaji tayi shuru. A haka har k'arfe sha biyu yayi ba d'aura auren ba, Eesha tace "Anya lafiya har yanzu ba d'aura auren ba" Shamcy ce tashigo d'akin da gudu ta rungume Fido tace "Adda Fido guess what?" Fido zuciyan ta yayi mugun bugawa tace "Ki barni, nazama matar Yaya Aliyu koh?" "A'a a yau kin zama matar Yaya Issam" Take ta taso daga kwanciyan da take tace "Banson wasa". Inna ma tashigo d'akin tana bud'a tace " Fiddausi matar Issam, ai yanzu kam mun huta da kukan ki" Da gudu taje gaban Inna tace "Inna dagaske kike?" "Kuji yarinya zan miki k'arya neh? Shegen yaron nan neh Aliyu yazo yace ya fasa auren a d'aura miki da wanda kike so Issam dan d'azu ma ya ganku tare, shineh aka nema shedu aka kira mamar sa aka d'aura aure" Wani irin tsalle Fido tayi tace "Allah nagode maka" Inna kallon ta take baki bud'e tace "Haka kika koma ba kunya?" Fido ta rungume Eesha tace "Kunyan wa zanji? Bazan iya b'oye farin cikin da nake ciki yanzu ba sabida nasha dreaming zama matar Issam" Haka ta ringa murna ba koh kunya and same time tana tausaya wa Yaya Aliyu Da daddare Abba ya kirata bayan taje ta zauna yace "Fiddausi nasan kina mamakin auren nan da aka miki, Aliyu neh yazo mini da maganar kun dai-dai ta da Issam idan kuma ya aure ki bai miki adalci ba sabida kowa yasan kina son Issam, shiyasa without wani tunani muka maida auren ki dashi, so ki shirya gobe da safe za'a kaiki Abuja dan shi already yau ya koma". Haka yata mata nasihohi bayan ya gama yace ta tashi taje ta Allah mata albarka. A yau Fido tayi baccin da ya jima bata yi irin sa ba, sai Allah Allah take gobe yayi ta ganta a kusa da Issam nata.... Washegari da safe Mummy tazo ta mata nasiha sai kuka takeyi ta rungume Mummy kamar wanda za'a rabasu, a haka har motoci suka zo dan tafiya Abuja, wannan time d'in kam mutaneh dayawa sun rakata, ciki harda Eesha, Shamcy, Mami, Yaya Khaleal da Yaya Aliyu... Cikin motar Yaya Aliyu akace ta shiga itada Mami, cikin motar sai hira yake musu kamar bashi ba, su basu iso Abuja ba sai da misalin k'arfe hud'u [9/16, 7:22 PM] Nana Fa'ad: Ba k'aramin tarban su akayi ba, Mummy da fara'ar ta tayi welcoming nasu mai kyau aka basu b'angare daban acikin gidan. Fido sai zuba ido take koh zataga Issam shuru babu alaman sa, can sai ga Salala tazo ta gaishe su da fara'ar ta, Fido ba k'aramin mamakin ta tayi ba, Salala tace "Amarya kinyi kyau kinsha k'amshi". Fido dai murmushi kawai tayi, bayan ta fita suka tambaye Fido koh wacece tace musu matar Issam ce, ba kad'an sukayi mamaki suka yaba da hankalin ta. Bayan fitan Salala daga wajen su Fido taci karo da Aliyu dalilin wayan da takeyi, murmushi tayi tace "So sorry wallahi ban ganka ba". Shima murmushi yayi yace "Ba komai" "Amma ke ba 'yar kasar nan ba koh? "Why do you say that?" "Naji hausar kice daban and kamannin ki" D'an dariya tayi tace "Babana d'an Yemen Mum na kuma 'yar a gadez that's Niger" "Wow! Mashaa Allah, a gaskia Allah ya zuba miki kyau" Murmushi tayi mai sauti tace "Duk kyawuna ina bayan k'anwar ka tunda ta iya kwace min miji" Zaro manyan eyes nasa yayi yace "Ohh sorry bansan kinada aure ba, koh kece Salala? "Eh, amma mun rabu for almost a year now. Kaine Aliyu right? Cox I saw you lokacin a Lagos but ni ina cikin mota shiyasa baka ganni ba" "Ohh ayyah so sorry" Dariya tayi tace "I am the one suppose to say sorry sabida ranar auren ka aka maka kwace". Duk suka fashe da dariya yace "You're funny! If you don't mind can I have your digits?" "Sure why not". Nan sukayi exchanging phone numbers Haka Fido tata zuba ido koh zataga Issam amma shuru, da can dare suna hira duk kansu Issam yashigo, bayan sun gaisa da duk kansu zai tashi ya tafi Mami tace "Fido ki d'an taka masa" Eesha tace "Haba nan da nan sai an taka masa" Fido tayi caraf tace "Ina ruwan ki?". Duk suka fashe da dariya, Fido d'aukan gyalen ta tayi tabi bayan Issam. Bayan sun fita Issam ya juya yana kallon ta with so much tenderness in his eyes yace "I miss you Hayateey". Rufe idanuwan ta tayi da hannayen ta wanda suka sha henna, dariya yayi yace "Wannan kunyan munafurci neh koh?". Itama ta fashe da dariya, yace " Kizo muje na nuna miki abu a d'aki nah" "Mene?" "Kedai muje" Haka tabisa har d'akin sa, bayan ta shiga ya rufe k'ofa, kallon sa take da mamaki tace "Yaka rufe k'ofa?" Zuwa yayi daf kusa da ita wanda suke iya shak'an numfashin juna yace "I just wanna be with you Hayateey" "D'auke kanta tayi daga kallon dayake mata dan bazata iya resisting kallon sa ba tace " Haba kar suga na jima" "Naga ai tareda mijin ki kike" "But still.." Bata k'ara sa ba ya had'a lips nashi da nata yana kissing passionately, haka har ya kaita kan gado ya kwantar da ita, nan ya fara kissing koh ina na jikin ta yana wani irin numfashi, sosai ta tsorata tace "Jaaan please ka bari". Ina shi baima san tana magana ba dan yariga yayi nesa, a tsawace tace "Issam ka barni please" Haka ma shuru sai aika mata sak'o yake wanda yake rikita ta, ganin yana k'okarin rabata da kayan jikin ta hankalin ta ya tashi nan ta samu ta cijesa wanda sanda yayi d'anyi k'ara tace "Please kabar ni ba yau ba". Tasowa yayi daga kan gadon ya had'a rai yace " Shikenan ba komai, zaki iya tafiya" Ganin ransa ya b'aci taji duk hankalin ta ya tashi ta taso ta same sa tace "Kayi fushi neh?" "Bazan b'oye miki ba nayi fushi" "Jaaan toh nabar mutaneh karsu ganeh ne ai" "Idan sun ganeh fa? Zina neh?" "A'a but please understand me akwai kunya ai" "Akan kiji kunya gwara ki b'ata wa mijin ki rai koh?" "A'a ba haka baneh" Matsowa yayi kusa da ita yana kallon cikin kwayar idonta yace "Idan da gaske kike Fido prove to me tonight that you love me idan kuma bazaki iya ba ba komai" Hankalinta ne ya tashi sosai dan a yanzu bataso ta b'ata wa Issam rai koh kad'an, batada wani option saidai ta masa proving eh dagaske tana sonsa. Ba tareda ta k'ara wani tunani ba tace "Bari nayi wanka toh, idan nafito sai kayi". Murmushi yayi yace "Why not muyi tare?" "Ba yau ba". Ba musu ya mik'a mata towel tashiga tayi wanka, kan ta fito har ya bata kayan da zata saka, shima shiga yayi yayi wanka, bayan sun saka kaya sukayi nafila biyu Issam ya ringa karanto musu addu'a daga nan suka shafa. Issam matsowa yayi kusa da ita yace "I am waiting Hayateey, prove to me that you love me" "You first have to off the light" Ba musu ya tashi ya kashe wutan, kan nan har ita ta koma kan gado, zuwa yayi kan gado ya cire wayarsa ya haska fuskan ta, murmushi tayi tace "Kashe wutan or bazanyi proving ba". Ba musu ya kashe wutar wayan yace " I am waiting Hayateey" Matsowa kusa dashi tayi ta had'a lips nata da nashi tana kissing passionately, shi koh ina ba hak'uri ya fara kissing nata roughly, daga nan yana kissing nata duk wasu part na jikin ta har ya rabata da kayan ta gaba d'aya. Ita kuma tsoro neh ya cikata da taji yana addu'an raya sunnan kar taji zafi irin yadda taji da Yaya Aliyu tace masa "Ka min a hankali please dan ina tsoro, this will be my second time" Take ya kalle ta yace "Second time?". D'aga masa kai tayi tana hawaye, shi kuma mamaki neh ya cikasa duk zaman da sukayi da Aliyu sau d'aya ya kusanceta. Latsan hawayen ta yake wanda suke sauk'o wa kan kuncin ta yace "Don't worry Hayateey" Ganin abun nashi azeeman neh yana son shiga wajen na tattara na fita a d'akin......Sai daga baya na lek'o Fido tasha wahala sosai dan itada budurwa ba bambanci idan akwai ma toh kad'an neh, haka ya d'auke ta cak ya kaita toilet ya had'a mata ruwan zafi ya saka ta aciki, duk irin ihun da take bai bare ta tashi a bath d'in ba, daga nan ya saka mata night gown ya kwantar da ita kan gado kan kace wani abu har bacci yayi gaba da ita. Issam tsintar kansa yayi cikin wani farin ciki mara misaltuwa kamar an masa albishir na aljannah..... Tunda ya tashe ta sallar asuba data kwanta bacci ita bata tashi ba sai kusan k'arfe sha d'aya. A hankali ta bud'e idon ta taga Issam yasha wanka sai baza k'amshi yake, ganin ta tashi ya matso wajen ta yayi pecking nata yace "Hayateey daman yanzu nakeso na tashe ki ku gaisa dasu Mami dan zasu wuce yanzu". Rufe fuskan ta tayi tana murmushi. Da k'yar ta iya tasowa zama ma da k'yar ta iya yinshi tace "Gaskia bazan iya fita ba kace musu ina bacci kawai" "Mesa?". Yana dariya k'asa-k'asa. Ta tura bakin ta tace "Toh idan sun tambaye ni daga rakaka sai na zauna me zance musu" Dariya yayi yace "Sai kice musu kin tsaya bawa mijin ki hakkin sa neh" tareda kashe mata ido. Bugin sa tayi a k'irji tace "Nidai kace ina bacci and kuma yunwa nakeji fa" "Bara na kawo miki abincin ki" Taimaka mata yayi tayi brush yayi serving nata abinci yace "Hayateey zanyi dropping nasu a airport" "Ohk toh Allah dawo da kai lafiya Miji nah" Pecking nata yayi yace "Ameen Hayateey, You know every time I look at you my heart skips a beat I wonder if you know, my love, that my heart is at your feet I leave it there for you to do whatever that you wish You could take my heart, and love me" Murmushi tayi tace "At night I'll love you In the morning I’ll still love you, A splendid day is what I wish you From the bottom of my heart this is what I pray for you Jaan, ka dawo lafiya." Kissing nata yayi yace "Take care Hayateey" Murmushi tayi tace "Tace care too" After Seven Months Bayan Wata Bakwai Jama'a neh sun taru a gidan Alhaji Sanusi Sodangi dan d'aurin Aliyu Sodangi da Salala Muhammad da kuma auren Khaleal Sodangi da Shamsiyya Sodangi.. Fido ce zaune ta mik'a kafa tana cin dambun kaza, Eesha dake gefen ta tace "Fido ke kam Mashaa Allah akwai ki da ci kamar gara" Hararan ta Fido tayi tace "Kema kinsan banda ci sai da nake da cikin nan". Wayarta tane ya fara ringing ganin JAAN baro-baro kan screen take tayi picking call d'in tace " Hello Jaan", sai can kuma tace "OK gani nan yanzu zan fito" Eesha dariya tayi tace "Ku dai anyi jarababbu, a ranar auren ku ma kuka kasa hak'ura da juna irin koh kunyan Mami bakiji ba daga ce ki taka masa kika kwana" Dariya Fido tayi tace "Wai har yanzu abun nan yana ranki?". " Ina kuwa zan manta, kika shanya mu kika kwana wajen mijin ki" "Eh naji na shanya ku d'in, ina zuwa yanzu zanzo yana nema na a waje" "Ahab, nida kallon ki ai sai kuma gobe" Dariya Fido tayi tace "Kedai yanzu ina zuwa" ta d'au gyalen ta tafita tana tura ciki. A cikin motar ta gansa ta bud'e k'ofa tashiga, murmushi tayi tace "Jaan lafiya kake nema na?" "Lafiya kalau Hayateey kawai nayi missing naki sosai neh" "Daga jiya zuwa yau d'in?" "Kema kinsan bazan iya jure rashin ki koh na awa biyar ba balle kwana, kinsan jiya na kasa bacci sabida rashin ki kusa dani?" Murmushi tayi tana mai k'ara jin son Issam a kowani sashin jikin ta tace "I miss you more Jaan,Ur precious love has turned my life completely around, I feel like I'm walking but my feet don't seem 2 touch the ground" Pecking nata yayi ta bud'e baki tace "Za'a kalle mu fa Jaan" "Toh a kalle mu mana". Fisgan motar yayi da gudu Fido tace " Jaan ya haka?" "Hayateey kedai kawai kiyi shuru". Haka taja bakin ta tayi shuru har ya kai gidan su, horn yayi mai gadi ya bud'e k'ofa yashiga gidan. Duk da k'aton cikin dake jikin ta haka ya d'auke ta cak sai d'akin sa ya dirata akan gado, Fido tura baki tayi tace " Haba Jaan yanzu haka Eesha ta gama teasing na wai idan natafi bazan dawo ba sai gobe" "Karki damu zaki bata kunya a yau d'in nan zaki koma" Had'a lips nashi da nata yayi yana tsosa yace "I miss you Hayateey" itama kissing nasa take passionately har suka lula duniyar ma'aurata Bayan Wata Biyu Fido ce zaune tasha kwalliya tayi kyau sosai, gefen ta kuma Issam neh rik'e da twins kyawawa gudu biyu maza duk shi kad'ai yana musu wasa, d'aya Hassan takwaran baban Issam wato Ibrahim Babangida, Hussain kuma takwaran baban Fido wato Muhammad, Fido tace "Jaan wallahi gajiyan sunan nan har yanzu bai fita a jiki nah ba, nida ka bari naje gida nayi fourty days amma ka hana" B'ata rai yayi yace "I told you karki k'ara mini maganan zuwa gida arba'in koh mu b'aci". Ranta neh ya b'aci ta tashi ta bar masa d'akin sa ta wuce d'akin ta. Zama tayi ranta duk a b'ace sabida ya hanata zuwa wanka gida, can sai ga Issam ya shigo d'akin yayi hugging nata sosai yana murmushi, kallon ta yake with so much tenderness in his eyes yace " Your eyes, they're so pure, so beautiful , so mesmerizing. Hayateey you're the most beautiful gurl on planet, I've never met any gurl so beautiful as you are, you're gorgeous, sexy" ya kashe mata ido, ji tayi gaba d'aya haushin ya tafi tayi murmushi tayi hugging nasa tace "You make me sound really hot, but i'm not" "Ki yarda dani Hayateey a duniya babu wacce takai ki da Jannah kyau" Dariya tayi tace "Awwww I miss Jannah, yanzu haka tana ma Yaya Aliyu da Salala rigima" Dariya Issam yayi yace "Zata aikata, yanzu kin daina fushi dani Hayateey?" "Bazan tab'a iya fushi da kaiba Jaan cox ina matuk'ar sonka, ina sonka, kuma bazan iya daina sonka ba har k'arshen rayuwata.You mean the world to me, Without you the world is nothing to me You are the other half of me. The most beautiful and best half of me I love you better than I love me" Hugging nata yayi sosai yace *"I love you more HAYATEEY "* 🔚 Ta kurun kus😃 TAMMAT BILLAH Anan na kawo k'arshen labarina abunda nayi kuskure Allah yafe min, nobody is above mistake. Though Eesha tace bai kamata Issam ya rabu da Salala. But koh kema baza kiso ki zauna da Wanda baya sonki ba. I hope all my Fans sunji dadin k'arshen and we all Leary that NEVER MAKE DECISION IDAN KANA CIKIN FUSHI AND BINCIKE YANA DA KYAU SOSAI. I can't thank anyone without Thanking You My *MUNAYSHA*, a duniya banida kamar ki. I want everybody to know that stupid English words can't explain how much I really love you.. I heart you gurl to pieces❤ Allah kawo miji musha biki naje Kebbi😃 *Godiya na musamman to all members of Pure Moment Of Life Writers I really don't know how to thank you people sai dai nace Allah ya biya muku bukatun ku masu alkhairi... I love you guys to pieces❤❤❤* Ina Kuke NANA FA'AD & EESHA NOVELLA, nagode sosai😘 I heart you all to pieces for your support and contribution. Hak'ika banda kamar ku Ina friend nah Jealous Eesha bae(Marubuciyar Hibbatullah da Zargi). I thank you for your support and contribution even thou u always jlos of me nafiki shape mai kyau🤣. Love you my childhood friend❤ My Dear Friend FATY AZLAND, I love you sosai sosai😘 K'awa da banda kamar ki *SHAMCY*. Thanks for your support and soyayyar da kike nunawa book d'ina. Allah ya barmu tare and I heart you more than words can't say Ina kuke Meenarh parrot Teemerhlurv and Memxiey❤ I love you gurls😘 Godiya na musamman Reine- My Ghanian friend Maman Nasiba Shamcy Dahiru Queen Supy Amani Aysha JJ Kuna nam dayawa can't list❤ Groups da banda kamar Ku, Nogede da irin son da kuke nunawa Hayateey *PLM writers true Fans* Shout out to you guys, I love you to pieces😘❤ Summyn Bash Taskar Munay Daga Taskar Mu My Group- Matan Mutunci Matan kwarai Kuna nan dayawa can't list them all *IN DEDICATION TO FIDDAUSI SODANGI* Nana Fa'ad ke muku fatan alkhairi, KU HUTA LAFIYA 07034419520 Nana Fa'ad Nana Fa'ad Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO: +2349030159301