*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ _ƊAN ƊANO daga alƙalamin AMMEY LAYLERH ✍️✍🏼_ *FOR YOU HAFSAT MUHAMMAD ALIYU, AMMIN SA'EED.... UBANGIJI YA ƘARA MIKI LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI... * _YOTAWANMU GABA ƊAYA WANNAN LITTAN TUN DAGA FARKONSA HAR ƘARSHENSA NAKU NE KYAUTA...._ *✯ 🌠YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION {YOTA}💫* The Writer's of *KAREN BANA* *JALAAL AREEF* *ƘAUNA BIYU* *MIKIYA* *TA DABAN* *SO DAN RAYUWA* *DUNIYARMU* *RAMIN KURA* *ƘARSHEN ƘADDARA* *AND ONGOING DUHU na dukan DUHU* Page 1 _Trailer out now_ ꨄYa musulunta ata sanadiyyar soyayyarta, ya yarda ya ɗauki kasadar rabuwa da ahalinsa dama duk wani makusanci nashi duk ata dalilin zazzafar soyayyar da yake ganin zata kaishi ga wata mafita ce ta daban. Sai da tafiya tai tafiya tafiyan da yay nisan da babu komawa baya a cikinta, bayan da ya riga ya mata wani kalan nisan zango na ninƙaya a cikin duniyar sonta, Ya fuskanci ashe ita ɗin fanko ce na ashanar aci bal bal. Wacce bata da amfani a cikin tashi Rayuwar dama DUNIYARSA baki ɗaya, tunda shi ɗin ya kasance DUHU ne, yayin da yake ganin itace tsananin da zata kai shi ga hasken da yake kwadayin samu, sedai ashe ita ce hasalin DUHUN na DUKAN duhu ɗin ma gaba daya. Se dai kuma wannan ƙwadaitakar daya riga da yay a addinin da ba nasa ba, saboda ya romon addinin Musulincin daya riga da ya gama kwankwaɗa ya sanya shi jin yanzu ne ma wasan se soma, don kuwa Ya gama fuskantar *YASMINE DUHU ce na DUKAN DUHU* A cikin rayuwarsa dama Duniyarsa baki ɗaya. Wannan wacce iriyar kaɗdarace me zafi data haɗa tafiyar da kuma take maban banta a gare su? Shin kai me karatu ya zaka tsammaci wannan karin magana ta DUHU na DUKAN duhu?..... ꨄ_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦° ♡ "Papaah!!!" Ya faɗi cikin muryan shogoɓa da sakalci yana karyar da wuyansa gefe har farar fuskarsan na dakunewa. "Johseph?" Mr jef deefer daya kasance mahaifi ga Joseph ɗin shima ya furta, Yana kallon yaron nashi cike da tsantsar son da yake jin kaff duniyar babu mai masa kalansa. tsaiwarsa ya gyare tare da ɗan karkatan da hulan daya kasance me zubi da irin malafar nan yay, cikin harshen English ya furta. "Yeah Johseph har yanzu kai ƙaramin yaro ne, ba ko ina ya kamata ace naka barinka kana shiga ba, dole driver ne zai kaika" wani kalan sake ɓata ransa yay yana komawa da baya tare da faɗawa ɗaya daga cikin saman 1str ɗin da suka zagaye parlour'n, yana kaiwa zaune tare da jingina da jikin kujeran. Zama papan yay daga gefensa yana shafa sumarsa like woni baby'n goye nan. "To shikenan na yarda zaka fita ba guard's Amma nima fa ina da sharaɗi akan hakan" ba tare dayay tunanin wanda sharaɗi bane ya furta."Ohh papa problem" daƙuwa papan ya masa da dariya a fuskanshi "Na barka jeka dawo zamuyi magana akan Deepika" cike da zumuɗi ya miƙe harda ƴar rawansa na farin cikin zayyi driving da kansa yau, ze kuma fita ba tare da guard's ko ɗaya ba, Wani tsallen farin ciki ya buga daidai da papan na cilla mishi trow pillows ɗin dake zagaye da lafayayyar kujeran da suka zagaya parlour'n. Da ɗan gudunsa ya bar parlour'n yana riƙe kunnuwansa alamun ya tuba. Tunda ya fito kuma ya maida fuskan nan me ɗauke da kyakykyawan murmushin nan yana medata tamkar maɗaukar zunubi. Cikin yanayi na kamewa yake takunsa cikin ƙarfin jiki da kuma izza, don kuwa duk wanda yasan Joseph yake kuma rayuwa dashi to kuwa tabbas yasan irin izzar da yake da. ♡ Hannunsa dake ɗauke da tsadaddar wayansa ƙirar iPhone x ce riƙe a hannunsa yana kamar duba woni abu ne me muhimmanci, haka ya ringa ratsa wuraren gidan daya kasance wani irin tsararre haɗaɗɗe kuma. Tun kamin ya ƙara sa isowa Micheal yay hanzarin isa Parking car na gidan,kai tsaye wata shahararriyar mota ƙirar zamani ash color da ta gaji da haɗuwa yay hanzarin fiddota compound na gidan. wacce kallo ɗaya zaka mata kai da kanka ka fidda ƙiyasin maƙudan kuɗaɗen data lasa kafin a mallaketa. Dan The car ɗin is so majestic, so elegant, so classy, so luxurious. ♡ Yana ƙoƙarin shiga mazaunin driver sit cikin wannan daƙilallar muryan ya cira masa hannunsa ɗaya tare da furta. "Uhmmm... uhmmmm" yana kuma bashi hannu alamun ya bashi car key na motarn. Cikin ɗari ɗari da tsoro da kuma rawan jiki Micheal ɗin ya furta "Amma Bo..... A dake muryarsa har na ɗan tashi kaɗan ya furta "Ba buƙata" daga haka ya sanya kansa cikin haɗaɗɗar car ɗin, tare da yin reverse nata yana barin haraban gidan wanda hakan yay daidai da zazzaro idanu wojen da Micheal yay cike da ruɗin fitan da yay shi kaɗai. Don yasan wannan ɗin dokar paah ne baya taɓa barin Joseph ɗin fita shi kaɗai ɗin sa ba tare da guard's ko driver nashi ba. Kasancewarsa pilot kuma dama hakan doka ce a kansu duk wani pilot baya taɓa driving da kansa sedai a ja shi... Paah dake tsaye daga samar benen dake kallon fitan Shalelen yaron nashi yay ƴar dariya cikin sautin da zaifita sosai yay ma Micheal ɗin magana kan cewan karya damu yasan da fitan. Woni kyakykyawan numfashi ya kawo yana kuma shan zuciya irin alamar na tsira ɗin nan da ƙyar. ꨄ Shi kuwa Johseph cike da nishaɗin daya gaza ɓoyuwa har saman kyakykyawar fuskanshi kai tsaye kana iya kallar hakan. Tunda ya hau saman kwaltan yake driving motan nashi very slowly, cikin ɗan tafiya tinanin papah'nshi kan rashin barinsa fita shi ɗaya ko yay driving Kamar haka shi kaɗai. Ɗan ɓata fuska yay tamkar yana gaban mahaifin nashi ya furta "Ahh dad I'm anger so what about me which condition I'm in I have a difficulties something that happened to me papahh, everything happen to me like a young age, ahh seriously me I'm a big like any serious good human being I'm proud for my self for that hmm may be I will show him do to really understand, but I love you Papa so much I LOVE YOU paah!!" Yay maganan yana wani lumshe kyawawan fararen idanunsa da kwayar cikin su ta kasance gold colour. Wani kalan jan birki yay ƙoƙarin yi amma ina hakan na neman gagaransa kasancewar an daɗe ba'a haɗu ba, don ba a barinsa yin driving da kansa koda kuwa zuwa ƙofar gida ne. A wani irin zuciye yajuya kan motar yana tsaida ita, amma duk da hakan seda car ɗin ta bugi matashiyar buduryar dake sanye cikin shijab kalan ash colour har ƙass.Farar ƙafarsa dake cikin baƙin takalminsa me shegen ƙyau ce ta fara bayyana, kafin blue dogon wandon outpit ɗin dake jikinsa. A kuma zafafe ya fito don baiga hurimin ubanda ya kawo ta saman kwaltan haka ba. Ita kuwa wacce aka bige ɗin kamar ba zata juyo ba, sai kuma zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncin ne haka .da ya nemi kaɗe ta. Idasa fitowar yay yana ƙarasowa har inda take duƙe da jikin motor ɗin. A gabanta ya tsaya yana hucin ɓacin rai shegen tsayinsa harna ƙaruwa yana ganin tsayin kansa da nata ba ɗaya ba, duk da kasancewar a duƙen take har yanzun kuwa. ♡ Soft fararen hannuwansa masu aji ya sanya kai tsaye yana kai hannun da nufin wurgar da ita daga jikin motar nashi. Se kuma aka sami akasi hannunsa kawai ya sauka saman shimar nata yana cilli dashi. Wani kalan waro manyan idanunta tay ganin an fusge dogon shimar ɗin dake jikin ta, saur̃in sáke ƙanƙame Alqur'anin dake rungume a hannunta tay, Zuciyarta na wani kalan tafasan ɓacin rai har tana jin yadda bugun ta ke fita fatt² haka da mugun ƙarfin gaske. Se kuma gaba ɗayanta ta juyo a fusace kai tsaye tana ɗauke wannan kyakykyawar fuskan nashi da wani lafiyayyen mari ta ɓangaren dama kana again ta sake juyowa ta kuma wanke shi da woni ta ɓangaren hagu.... ♡ "Shin kai babu zuciyn a ƙirjinka ne hala!? kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?.Amma kaikam duk ahalunka babu masu imani kuma bakusan menene daraja da muhimmancin ƴa mace ba?" Matashiyar budurwarn ta faɗi fuskanta ɗauke da mugun ɓacin rai, Kana ta bishi da kallo tun daga sama har ƙasa, wasu shegun riga da wando ne a jikinsa outpit kalan koɗaɗɗun nan masu ya ga² Se kuma sarƙan Cross na diamond ɗin dake saƙale a wuyansa, se bariman warin diamond ɗayan dake manne a kunnensa, se wani shegen kalan ɗan iskan askin dake kansa irin me kibiyar nan, ta ƙasa kuma ya tari gashin kan nasa ya tufke shi. iyaka su kaɗai sun isa tabbatar maka da cewan Ehhh lallai wannan ɗin ba musulmi bane Christian ne. Da wani kalan wulaƙantaccen kallo ta bishi kana taci gaba da furta. "Koda yake alamu sun gama nuna cewar musulumcinma kai baka da!, don da dukkan alamu arziƙinsa ma baka samu ba bare kuma har aje ga sanin daraja ɗan Adam. Amma duk da haka Kai mutum ne wadda ko acikin Christian ɗin ma kai baka da daraja daga kallonka na tabbata haka, duk iskancin da irinku masu addininku suke dashi basa taɓa wulaƙanta ɗan Adam irin haka" A nutse ya janye idanuwansa daga kallonta yana rasa ma ta inda wanna ƴar filic ɗin yarinyarn ta sama kwarin gwiwan yi may maganganu har haka? Duk da kasancewar motsin da bakinta kaɗai keyi ne ya tabbatar may da cewan masifa take may bawai don yasan abinda take cewan ba kuwa. Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin eye glasess ɗin dake sanye a idonsa, ba tare da yama nuna alamar ya fahimta yaren da take maganar da shiba, ko nuna yama ji zafin marin data may ba ya raɓata zai wuce abinsa, saurin sake shan gabansa tay ganin kamar duk bayajin hausarn da tay maganan dashi, hakan ne ya sanya kai tsaye ta juye harshe zuwa English ta furta "To dan ma kaji Wllh² baka buge banza ba!, tun da kai baka da cikakken imani da kuma tausayi to kuwa wllh se na nuna maka hasalin yadda ake mutum ta mace da kuma darajantata!" Wani kalan ɗan ware mata manyan idanunsa yay tare da ambatar "what? Hhhhh this girl is very stubborn and stopid shutter. stopid girl wannan wani kalan shashancine kodai ke baki da class ne? ko da yake naga ke mahaukaciyane ok you are deaf" Yay maganan yana zare eye glasses ɗin dake sanye a cikin idonsa, Daidai da loƙacin da niƙab ɗin dake sakaye da fuskanta iska me ƙarfin dake kaɗawa ta yayeshi sama, daga saman kyakykyawan farar fuskarta, wani irin bugawa dummmm gabansa yay. Don haɗewan da idanuwasu sukai wuri guda,Wanda wani kalan launinsu da hasken kwalliyar halittar da idanuwanta suka yi may tozali. Haka yaga gilmawar fararen idanuwan ta tamkar hasken farar zinariya mai ɗauke da tambarin Alkuki acikin ragayar fitilar kwai. Wani kalan ɗan dukan kansa yay yana tsurama kyawawan laɓɓanta da kai tsaye yake iya tantace kalan laushinsu. A mugun fusace ta sake fidda zara zaran yatsun ta biyar da ALLAH ya halatta mata ta sake ɗauke kyakykyawar fuskan shi da wani kalan arnen bahagon mari me gigita duniyar wanda aka yima shi. A kuma daidai loƙacin ne bodyguard nashi da madame Victoria Osteen ta balbalesu da masifan barin shi fitan da yay shi kaɗai. Domin ba ƙaramin Mahaukacin S0 take ma Johseph ɗin ba, Ba tare da yasan da wanzuwar su wurin ba kattin arnan majiya ƙarfin kawai suka ma matashiyar budurwarn ƙawanya aka tamkar zasu cinye ta ɗan ya, Da wani irin mugun kallon baku da hankali ya shiga binsu dashi ɗaya bayan ɗayan. Se kuma ko wannensu ya shiga yin baya da baya a mugun tsorace don sune kawai suka san ainihin ko wanene Johseph ɗin. Ita kuwa wani irin nauyi ƙahon zuciyarta ya mata tamkar za ta faso ƙirjina ta fito haka taji ƙirjinta ya danne.A karo na biyu a kuma kausashe ta sake furta. "Kar ka yadda ko a rashin sani ne wannan ƙazamin hannun naka ya sake yinƙurin taɓa koda hijjabin jiki nane balle hannuwana Malam" tai maganar tana ƙara sa fusgo numfashinta da ƙyar da suke kokawa da juna wajen barazanar barin jikinta da yake shirin yi wajen fita baki ɗaya. Wani kalan taɓune fuska yayi yana tsurama kyawawan laɓɓanta ido. Wanda suka yi matuƙar burgeshi sosai wajen yadda take balbala bala'in masifan, hakan ya sanya ba tare da tunanin komai ba ko dede ze aikata ko akasin hakan babu zata babu tsammani kawai taji sauƙar lisp nashi saman nata. A wani irin daskare ta tsaya chak da shirin tafiyan da take ƙoƙarin yi tamkar wacce akayi freezing nata. dan ko iya juyowa ba tayi ba balle tay tunanin meke faruwa da ita, Wani kalan rumtse idanunta tayi for the moment tana sauraran bugun zuciyarta, sharrr kuma hawayen tashin hankali suka wanke samar kyakkyawar fuskarta na tsantsan tashin hankali. Shi kuwa John samm be san abinda ya aikata a gareta me girma bane duk da kasancewar dama samm can shiba Mutum bane ma'abocin irin hakan ko da kuwa da yake ba Musulmi ba. Amma samm hakan tsentseni yake bashi kuma da ƙazantane yake danganta hakan. Amma se gashi yau da kansa shi Johseph Mr jef deefer ya aikata hakan ga wata? Watan ma Hausa gurl, shi ne ma sanadiyyar da har su Micheal suka janye shi daga gare ta be farga da hakan fa. Don ji yay Duniyar na juya masa yana jin tamkar shi kansa ba shi bane haka yake binsu, suna daɗa janshi ganinsa na ƙare nesa da ita har zuwa gaban Manyan motocin da suka zo dasu wajen guda biyar. Chark ya ja ya tsaya da shirin shiga car ɗin da yake yi, sakamakon sauƙar wani abu me nauyi da yaji a tsakiyar gadon bayansa. Su kuwa kattin arnan nan a 370 sukayi kanta da niyar su dagargaza ko wanne ƙashi da tsoka na jikinta. A wannan karon ma dakatar dasu yay ta hanyar ɗaga musu hannu. Cikin mugun azabar daya dirar masa lokaci guda ya juyo ga kallonta daidai tana shigewa cikin jibgegiyar car ɗin da ta taho ɗaukanta, Ba don ya soba don dole ya faɗa cikin car ɗin, yaransu najan motocin da shegen gudu na tsiya don sosai sukaji haushin hana musu raga raga da naman yarinyan da yay. Hakan yasa cikin mugun fushi ɗaya daga cikin yaran suka kira Madam Victoria Osteen tun kamin su Isa ga gidan suka sanar mata cewan wata Hausa girl ta jima John rauni. A silo tarin motocin nasu suka lula zuwa haɗaɗɗiyar unguwar Banana Island, a katon get ɗin makeken gidansu sukayi Parking car nasu. Wani kalan mahaukacin hong suka shiga do ƙawa. Kai tsaye kutsa kansu cikin wargajejen katon get ɗin gidan sukai loƙacin da aka gama wangale musu shi. Baki ɗaya jama'ar gidan tun daga kan yaransu har manya suna kammale a ƙofar parlour'n shigowa, kasancewar Micheal yayi woya dasu kan cewar ai Johseph ɗin yayi faɗa da wata Hausa gurl ne, harma ta jimay ciwo, jin ambatar iyaka ciwon ne ya tashi duka hankalin madame itama tana tasar hankalin duk jama'ar gidan. Jin jirin tsaiwar motocin sune ya sanya su yowa Parking car ɗin dukansu barin ma jikin Madam Victoria osteen da har wani rawa² yake yi. Tun kamin ya ida fitowa ta shiga motar tana fitowa dashi kusan rungume a jikinta dukansa, duk ta cewan girman jikin da yake da amma samm ita bata gani idanunta sun rufe akan ƙaunar Shalelen ɗan nata. A hankali a kuma nutse suke tafiya yana jingine da jikinta suke takowa zuwa cikin parlour'n. Dab da inda Papan shi yake zaune Madam Victoria ta zaunar da Johseph ɗin, itama tana zama gefensa suka sanya shi tsaƙiyansu. Sake tsumewayi yayi wuri guda jin yadda duk iyayen nashi suka bi suka ruɗe da ɗan bugun da besan ko miye ba yarin yan ta buga masa. A wani irin hankali yaji zuciyarsa tana narkewa tuno da waɗan nan mayun idon da bai taɓa ganin irin suba. A bayyane ya shiga furta. "Meri har saash me tu ♥️_ _meri har Khushi me tu tere bina jindg_ _meri nhi kyu ki Meri jindagi hai tu ♥️😘 I love you, my sweet dreams baby_ As much ASI love you _ _I've finally accepted that it's time to let you go_ _you will always hold a place in my heart ♥️ _ _but you no longer belong in my gurl _ more thant I accepted Mee_" Baki ɗaya suka saki baki suna kallonshi cikin yanayi na ɗan tsoro. Papa ne ya sake sipping hannuwansa ya ɗago kan Johseph ɗin tare da furta. "John what the problems?" Kansa ya girgiza se kuma ya kamo hannun papa'n yana ɗorawa saitin Heart nashi tare da furta. "Nan ciwo kawai papah nan" yay maganan yana sake tura hannun paah cikin buɗaɗɗiyar rigarsa data buɗe kusan rabinta. Tashi tsaye madame Victoria Osteen tay tare da tafa hannuwanta tana furta "Ohhhh Lord I pray for.. Jesus jesu hoooooh John hooooh john, darling don me zakabar ƙanƙanin yaro kamar John fita shi kaɗai? Amma dai ai kasan bana barin shi koda yin driving ne ko? Bare fita shi dayan sa! Oh Jesus...... Mr jef deefer da madame Victoria Osteen ta ƙira da darling ne ya ɗago kanshi yana dubanta cikin faɗa ² da yarensu ya furta. "Amma dai ai kinsan baki fini son john ba ko?" Ihu tamay a ka ta dibilbele may baki take zuba masifanta. Domin kowa yasan madame Victoria Osteen bala'ice ita kanta, shi yasa kowa na gidan ke tsoronta fiye da kowa. Gata ƙaƙƙarfa mace tsananin riƙo da addinin ta ya sanya addininta na christian bata wani babban muƙami gareta a church, da di da ƙari gasu masu shegun kuɗi ne su gaba da baya wannan shi ne ya sake kankarota da sake babban matsayi. ♡ *YASMINE* Tun da suka ɗauki hanya ta nutse a cikin kujerar motan tare da lafewa luff tana jin yadda bugun zuciyarta ke ta faman kai kawo har zuwa yanzun kuwa, hakan ya sanya bama tasan sun kawo katafaren dogon ginin gidan masu ba har saida driver ɗin ta ya mata magana tare da ɗan bubbuga gilashin motar kana ta firgigit ta dawo daga duniyar data lula. Fitowa tay ta fara tafiya cikin nutsuwar da tafi kama da jin kai da taƙama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankalin me kallonta. Da wata maid service ta haɗu a gaban ƙofar parlour'n shiga gidan tana shanyar kayan data wanke na masu gidan. Shijab ɗin jikinta ta wurga mata saman fuska tare da dogon wandon uniforms ɗin Islamiyyar jikin nata. Kasancewar rigar irin duguwar nan ce har kusan gwiwar ta, Duk inda ta wuce sannu da dawowa ma'aikatan gidan ke mata amma bata kula kowa. Da mahaifinta Ambassador Kabeer Usman ta fara cin karo. Hakan ya sanya a guje tayi kansa tana faɗawa jikinsa tare da fashewa da kuka. "Ohh god waye kuma daga dawowan Ambasa baby zai taɓa min ita?" Fitowan Mahaifiyarta lowyer Khadijah Haroon ne ya sanyata haɗiye maganarta makut tana takurewa jikin mahaifin nata. Cikin muryan No nonsense ba tare data kalli ko inda take ba ta furta. "Oya get out of the here" sum sum ta miƙe tana yin sama se wani tattaro rigan jikinta take. Kai tsaye toilet ta shige tana sakar ma kanta shower, Bata fi 20 minute da shiga ba se gata ta fito ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta. Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin, sannan tashiga shafe shafen lotion masu sanya fata tayi laushi. Kafin ta feshe jikinta da tarin turarikanta, bayan ta mulke jikinta da Shu'umar humrarta. Cikin clothes na kayanta ta shige, wasu haɗaɗɗun simple ciffon riga da wando taciro tasaka nude, there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka daga kanta ba don wani masifar ƙyaun da kayan suka mata ko nace ta musu. Don kuwa tabbas YASMINE me ƙyau ce, idan nace ƙyau ina nufin maƙura ƙarshe. Sake fitowa cikin parlour'n tay loƙacin an jima da idar da sallar maghriba. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour'n, ciki kuwa harda Omer da babu jimawa ya zo gidan ɗa ga yayan Hajiya Khadijah Haroon Mahaifiyar yasmine. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance jininta ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya, tana jan fruits table ɗin dake gaban daddy'nta. Tsawa Mafaiyarta da take ƙiranta da Maama t.a buga mata kan cewar bata iya gaida mutane bane? Kana maza tayi hanzarin maida fruits table ɗin data janye daga mahaifin nata. Hannun Ambassador Kabeer ya ɗagama Maama tare da girgiza mata kai alaman ta kyale mishi yarinya haka nan tayi abinda ranta yake so. "Amma daddy'nta sau nawa zamuyi ta maimaita magana ɗaya kan Ambasajo eheeee? Yasmine fa har yanzu ba yarinyar goye bace gidan wani zata je. Don me ina kallon kusa kurai a cikin rayuwanta tana aikatawa amma da nayi yunƙurin gyarawa kace na dena kona bari? Haba Impossible wllh wannan bame yiyuwa bane bama dole na gyara rayuwar yarinyana da kaina wllh, don duk wata uwa data kasance ta gari ga ƴaƴanta dole zataso ganin ɗan ta cikin kyakykyawar nasaba ba wai a bauɗe irin Ambasajo ba!!!" Daga haka fuuuuu ta bar wurin bayan ta cillama yasmine wani mugun kallon zamu haɗe ne..... *John* A.......... _Washhh Hannuna ciwoooo!_ _To ya kuke ganin ko kuke tunanin wasan ze fara?, Nasan wasu zasu fara tunanin...... Ehhhhh ya neeeeee to koma dai miye mu haɗe a page na gaba lol 😄😍🥰 don jin yacce zata kaya_ _Anan ina son mu sani cewar komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurar ubangiji, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddararsa yake, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan, Se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas, nan take takan iya sanjawa. Ita kuma yarda da ƙaddarar kanta me kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin cikakken Imanin ko wanne bawa!.... A cikin Rayuwar ko wanne bawa kuma bai zama lallai ace saika amfana da wanda yake tare dakai ba, saboda wasu loƙutan ma ban banta akan sha wannan fama na kusa da kai da kake ma kallon Inuwar ka, ko Allon jinginarka, Tashin farko kwatsam se kaga kaine zaka kyautatawa na kusa da kai, Se kuma kaga sama ta ka wani shi ne zai shigo cikin rayuwarkan daga nesa ya zamo shi ne Haskenka ba wannan wanda kake ma kallon shi ne hasken naka na, bayan ka daɗe da linƙaya a cikin DUHU na DUKAN duhu'n. Duk da kasancewar tunaninsu iri ɗaya ne haka zalika Ma'amalar su iri ɗaya ce, duk da hakan bazai hana su saɓama junan suba wata rana, Amma da sun yi Haƙuri da juriya a cikin zaman takewarsun ta yau da kullum su duka se su tashi a ƙarƙashin Inuwar ita wannan Hasken Farin watan_ _Se dai kash..... _Shin shin shinnm...... Kowa yaje yayi tunani ya ƙaraci tunaninsa don duk yacce kuke zata ko tunani to wasan ba haka yake ba lol 😄💃, don nayi ma kaina alƙawarin tabbas sena gindayar daku a wannan karon ma fiye da MIKIYA, koko TA DABAN, ko kuwa dai DUNIYARMU. koma nace fiye da komai ɗin ma hhhhhhhh, ciki kuwa harda RAMIN KURA......_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐍𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐀𝐍𝐃 𝐒𝐇𝐀𝐑𝐈𝐍𝐆 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 2 Paid book *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION {YOTA}* _NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA_ *NIMCY LUV* har abada ƙaunarki ɗaya ce a gareni Marh, domin duk inda akaje aka zo ke ce AMMEY LAYLERH 💐. _Special Thanks to Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke Love you all 💞💖💘💗_ ꨄ_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦°♡ *John* Yana shiga bedroom nashi sarƙar cross ɗin dake wuyansa ya zare, yana ratayeta jikin wani ɗan hanger ƙarami mai kyau dake cike da sarƙoƙi kala-kala a ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban mirror'n yanata faman yamutse fuska. kana a natse ya mike kansa tsaye yana nufar bathroom. Yana shiga babu jimawa aka fara knocking kofar bedroom nashi, amma sai ya sha re yana ci gaba da abinda yake da uzirinsa. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin farar ƙafarsa dake nan fara tass ta bayyana, yana ƙarasa fitowa jikinsa sanye da bathrobe sky blue, Hannunsa ɗaya kuma na rike da karamin towel yana tsane gashin kansa da kallo ɗaya zakai ma gashin ka fahimci yana masifar lasar manyan kudade bana wasa ba, kodan kyau da kyallin da gashin keyi domin yafi karfin a kirashi da suma. Duk abinda yake yi tana nan maƙale a ruhinsa da tunaninsa, Sam beyi tunanin ganin Madame Victoria a bedroom ɗin ba. Ɓata face nashi yayi tamkar wani yaron goye yana nufar inda take zaune daga bakin bed nashi. Zama yayi gefe da ita tare da jingina kansa da jikinta. Bayansa ta shafa a hankali inda ya waro manyan fararen idanuwansa cike da tsoro, jin ta tabo masa inda waccen babyn robar ta jefeshi. "Ouch Mah!!!" ya sake furtawa da ɗan ƙarfi jin ta sake taɓa masa wurin. Kansa ta dungure masa tana tashi ta ɗebo masa ƙananan kaya black da black ɗin speck. Closet nashi ya shige don baya taba shiryawa gaban Mommah ɗin nashi, duk lokacin data masa kutse irin haka duk kuwa da yanda take sashi gaba. Bai wani jima sosai ba se gashi ya fito cikin black ɗin shigar, inda yamay wani kalan kyau bana wasa ba wanda ya sake fito da ainihin hasken farar fatarsa me kyau da mirjewa. A gaba ta sashi suka fita zuwa entrance dinner na gidan baki ɗaya. Wanda kowa ke hallare a wurin, Mr jef deefer ne ya fara taryan yaron nashi da kayataccen murmushinsa me kyau, kafin X Eeshika itama ta sakar masa nata murmushin wacce take Ƴa ga kanwar Mommah nashi, daga nan se jelly wacce take kanwa a gareshi. Yana zama kujerar kusa da paah ɗin sa X Eeshika ta tsalloka tsilik zuwa kujerar dake kusa dashi, wacce ke pacing nashi. Kwanciya yayi jikin papanshi Mommah ce ta miƙe tana me furta. "Stand up and eat your food" Ta faɗa tana mantawa da gadon bayansa tana ɗagoshi, wata uwar ƙara ya sanya yana riƙo gadon bayan, Se wani haɗa uban zufa yake yana matse kyakykyawar fuskar nan tamkar wani yaron goye, saurin sanya hannunta tayi tana dafe bayan nasa tana furta. "Ohhhh Jesus Sorry boy sorry!" Madame Victoria ta faɗi tana tada shi zaune daidai da tallafin papah'nsa, Sannu mutanen parlourn suka shiga masa x Eashika harda guntuwar kwallarta. Jelly ce tayi saurin ƙara gudun fanka tsabar ɗaurewa karya ƙugu, "Ma'am What wrong with this john?" X Eashika ta tambaya Mommah kai tsaye. Nan madame Victoria ta sanar dasu abinda ya faru, haba nan fa suka shiga babin tsinema Hausa girl dukansu, cikin su kuwa harda masu cin alwashin duk ranar da suka haɗu da yarinyar se sun fasa mata baya itama kamar yanda ta fasama John ɗin su. Jin yanda suke zagin masa pretty ne ya sanya John miƙewa yana me furta. "Momma I can't eat anything now, i want to sleep, because am feeling sleeping". Ya bata amsa can ƙasan maƙoshinsa kuma ya faɗi hakan ne bawai don hakan yake ba, A ahh kawai dai ze basu wuri ne bazai iya zama ana zagar masa love tashi ba. Duk da kallo suka bishi suna son masa magana suna kuma tsoron masan ya sauƙe musu ruwan Bala'insa da ya iya buhu², don shi tamkar fire and Ice haka yake, yanzu za'a kalleshi cikin nishaɗi yanzun kuma za'a kalleshi cikin mugun tsare gida da ɓacin ran da idan ka ganshi a lokacin zama kayi tunanin cewar be taɓa sanin wata aba wai dariya bane. Don haka kowa yayi gim da bakinsa yana tsoron masa magana. _Great place a wonderful mension_ Mension ne babba da ko a cikin Cristian suke ji dashi, domin kuwa shi ne lamba ɗaya wanda sunansa ya zage baki ɗaya katafanin garin Lagos ɗin harma da kewayenta, sunan POWER kun san me ma'anar sunan yake nufi, kalmar POWER kalmace dake tattarene da karfin iko, Isa, Izza, taƙama. ★ *Mr jef deefer* shi ne ƙatoton arne lamba ɗaya da suke ji dashi. Baya da Imani ko kaɗan, haka Kuma baya da tausayi ko rangwame bare yafiya. Idan kanason ganin murmushi ko dariyarsa to ka tabbatar yana tare da zuciyarsa ne gaba ɗaya wato John. Wani irin mahaukacin So uwa da ubansa suke masa, Wanda samm samm hankali baze Iya ɗauka ba. Mahaifinsa Mr jef deefer Wani irin shimfideden iko yake gudanarwa, sedai samm baya taɓa yarda da maci Amana ko kaɗan. Idan kuwa har ya kama mutum da cin amanarsa yana gindile masa yan yatsu biyu ne, ma'ana babbar yatsar mutum da kuma yar ƙurinsa wannan shi ne hukuncin wanda ya kama da laifin cin amanarsa. A tsarin mension ɗin nasu kuwa. Wani irin katafaren mension ne mai matuƙar kyau da tsaruwa, Wanda ya gama gajiya da haɗuwa iyaka haɗuwa kam gidan nan ya haɗu, kai da ganin ginin gidan kasan masu rayuwa a cikin sa sedai wani babban ƙusa daga gomnati ko dai wani babban ɗan kasuwa ne, gate ɗin gidan kawai abin a tsaya a kalla ne, bangaren uku ne a cikin gidan ga wani dan ma dai dai cin pool a tsakar harabar gidan, daga gefen hagu katafaren parking space ne mai dauke da ƙaton rumfa gefe guda kuma ga wasu fittatun manyan motonci nan babu kalan da babu, tin daga kan su *Mercedes-Benz* *McLaren solus GT.* *Roll-Royce boat Tail* *land cruiser * Kai ganan dai su motocin babu kalan da babu, su kansu kawai abun kallo ne. daga gefen dama kuma shuke shuken plowers ne in different colors awajen masu matuƙar kyau da ban sha'awa. daga ɗan gefen parking space ɗin kuwa, wani Katafaren wajen hutawa ne dake zagaye da glass. wajen ɗauke yake da wasu ƙayatattun sofa set ɗaya launin sky blue, a tsaƙiyar kujerun kuma wani haɗaɗɗen sofa table ne mai ɗan girma a wajen, daga gefe guda kuma ga wani irin deep fridge ƙawace da wajen, Wanda suke ɗauke da lemukan sha da barasa, haɗuwa kam gidan ya gama tsaruwa tabbas..... John kuwa kai tsaye balcony na gidan yayi shigewansa phone náshi tare dashi, Akan wata doguwar Royal Caribbean chier yakai zaune, yana taune gefen lips náshi da tsarin halittarsu yake pink. gaba ɗaya tunaninta ne yake neman fasa kansa,kodan be taɓa jin hakan dangane da kowacce mace bene oho. Amma dai abinda kawai ya sani seya mallaketa kota yayane. Gaba ɗaya lissafinsa cikin lokaci ƙanƙani ya nemi daya kwance, dukkan wani motsi da zayyi ƙamshin turarenta kawai yakeji daya shaƙa yana sake hargitsa tunaninsa, ya sani tabbas shi masoyin ƙamshi ne but a rayuwarsa bai taɓa jin asalin ƙamshin daya taɓa masa ba bayan nashi ƙamshin se yau daya shaƙa nata. Tsaye ya miƙe yana riƙe da ƙugunsa ya fara aikin safa da marwa, yana ma rasa ta ina tunanin wannan Baby'n robar ke kutso masa kai?. Da misalin ƙarfe 9:44 ya lallaɓa ya fito zuwa compound na gidan. Kai tsaye bayan ya baro ɓangaren sa parking space ɗin dake gidan ya nufa, dake daidai lokacin babu kowa shi ya bashi damar shigewa cikin motar nashi, yana tada ta ya fice a gidan bayan ya ba get man umarnin buɗe gidan. ko lamps ɗin motar bai kunna ba gudun kada a ganshi tamkar wani ɓarowa haka ya saɗaɗa yana ficewa a gidan baki ɗaya. Yana ɗan nesa da gidan nasu ya kunna lamps na motar ya harbata saman titin. Wanda daidai lokacin garin ke haɗe wani irin hadarin da yama sama ado ta hanyar ƙawanyar daya masa da gajimare. *Ambassadors kabeer house* Gaba ɗaya mutanen gidan zaune suke cikin wani katafaren parlour na alfarma, Me ɗauke da wasu manya manyan sofa set guda masu numfashi wanda suka kasance masu launin blue da milk, Wanda kalan sukayi wani irin ƙawata parlour'n sosai suka sake fito da asalin kyaun sa, inda yaji komai da ake buƙata na rayuwa, wanda idan nace zan tsaya zayyana muku kyan parlour'n kaɗai ɓata ma juna time,A natse matashiyar yarinyar wacce take fara tas yanayin jikinta kuma kai tsaye na bayyana tsantsar hutu da jin daɗin da suke ciki ta ɗan saci kallar mamy'n nata tare da furta. "Aunty yasmine tana lafiya kuwa Mummy?, Har yanzun bata fito ɗinner ba. Ita da mahaifiyar nata suna sanye cikin shiga iri ɗaya na lace doguwan riga inda ita yarinyar nata a kasance fitet gown ne, ita kuma uwar normal doguwan rigawa esharp. Cakkk kuwa Abbin nasu ya dakata daga sipping coffee ɗin da yake yi, tare da dubar matashiyar yarinyar yana me furta. "Maza Husna je dubomin ko lafiyarta" yay maganan yana dire bowl ɗin dake hannunsa ya zubawa upsairs nata idanu tare da buga wani uban tagumi. Takun takarmin ta da kuma ƙamshin turarenta da baya taɓa ɓuya kawai mahaifin nata ya shaƙa ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya. Har zuwa lokacin data ƙara so cikin tsaƙiyar parlour'n ba a sake ba. "ALLAH sarki Ambasa Baby'n daddy'nta ƙaraso mana",cewar mahaifin nata, wanda ya sata ƙarowa sum sum domin bata mata kashedin mahaifiyar nata ba da tace da ita zasu haɗe. Don duk iskancinta tana tsoron mamy'n nasu. Sum sum take tafiyar har ta kai gaban daddy'n, zaunar da ita yayi gefensa yana tura mata duka kayayyakin dake jere a gabansa. "Eat it ambasajo na" Murmushi ta masa tana gyaɗa kanta wanda babu ko band. "Ina ɗankwalin ki Hau'wa?" Haka ta tsinkayi muryan Mummy nata wacce tayi maganar da ɗan ƙarfi, tura ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi, domin idan da sunan da yasmine ta tsani taji an ƙirata dashi to shi ne Hau'wa. Har ƙara ƙara yasmine ɗin ma amma ita a son samunta kowa ma ya dinga ƙiranta da ambasajo ɗin da mahaifinta ke ƙiranta dashi. "Ba magana na ke miki bane yasmine?" Ta sake wulla mata tambayar a karo na biyu. "Ambasajo ɗin Daddy'n ta maza tashi kije ki samo ko hula ne, Mummy naki bata son a zauna lafiya kinji". Kanta ta ɗaga mishi tana tashi tana tashi,"yawwa that's my girl" babu jimawa kuwa se gata ta dawod da Baby shijjab jikinta. _*HAUWA KABEER USMAN MAINA*_ kenan da akafi sani da suna _YASMINE HUTU_ ƙyaƙyƙyawar budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin da biyu a duniya. Wacce ta kasance ɗiya da farko a wurin mahaifinta Ambassador kabeer Usman Maina, Mahaifinta sananne ne da kowa kusan duka duniyar ta sanshi kasancewar matakin ambassador ɗin daya riƙe.Bayan haka babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin duk wani company'n dake tashe a zagayen Lagos da ketarenta. Yasmine yarinya ce da batajin magana sammm, amma ga wanda be santa ba kai tsaye ze mata kallon nutsatstsiyar yarinya ne, Se dai sammm ba haka take ba. Wanda badan mahaifiyarta dake tsaye a kanta ba da tuni rayuwarta ta jima da taɓarɓarewa, domin kuwa mahaifin shike wuce mata gaba a duk wani rashin ji da kirki nata, Idan mahaifiyarta ta tilasta mata zuwa islamiyya setayi tafiyarta manyan club's ko park. Se ta dedeci loƙacin tashi yayi kana ta nufo gida. kullum zaka kalleta idan zata tafi cikin shigar kayan islamiyya, wanda hakan yasa wasu ke mata kallon kamila kuma natsassiyar mace. gata masifaffiyar gaske ce lamba ɗaya ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu, Musamman ma ga mahaifinta ambasador kabeer maina. Gatan data samu da rayuwar da take a cikin ta seta tashi tamkar renon turai,Inda ta samu zurfafa kanta harta samu wadataccen ilimin boko, sedai na addinin kuwa ko oho amma fa idan ka taɓa ta akan addinin ta bata barin ko ta kwana, wacce zaka ɗauka cewar ita ɗin irin wannan shahararrun yaran nan ce masu haddar Alqur'ani izu sittin a kansu, sedai ko rabin izu bata da. Karatunta kuwa gaba ɗaya a ƙasar ƙetare ta yisa, idan ka cire Nursery school datai a Nigeria kawai. Sam bata son harkar talauci ko haɗa hulɗa da mutanen da suka kasance talakawa, wannan dalilin nema yasa sammm ta tsani islamiyyar da Mahaifiyata ta saka ta. A cewar ta haɗa wurin zama tare da su harma da shaƙar numfashin juna kan iya taɓa ta itama, wai wataran ta zama irinsu kodai ta auri talakan, Wannan dabi'a tata yana taɓa mahaifiyarta kwarai da gaske. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shi ne kasancewa da namiji. Sedai takanyi irin su sking love haka don tace wannan kamm babu laifi, amma fa ba Inji AMMEY LAYLERH ba 🤗 🤣 ato. Inji yasmine lol 😄😍........ "Ambasajo ku matso mu fara dinner, kamar Omer yana nan ma ko?" Yayi maganar da alaman tambaya. Husna ce ta ɗaga kanta ita kuwa yasmine ko motsi batayi ba, duk kuwa da cewar Omer ɗin dan ita yazo.tana ƙoƙarin buɗe kyakykyawan foodplask ɗin dake gabanta, sega Omer ɗin nan ma yana sauƙowa daga saman bene mai ɗan jiki kaɗan haka fari tas da shi. Wanda fuskarsa ke ƙawace da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo, yana da manyan maganai kamar bull ga dogon hanci, wanda kallo ɗaya zaka masa ka kalla irin tsantsar kamar dake tsakanin sa da matar da suke kira da Mummy. A natse ya ƙara sa saukowa daga zuwa downstairs ɗin yana zama. Tare da furta. "Good evening Daddy", "Good evening Omer how was your night?" Cewar Daddy ɗin Mummy na tura masa plate ɗin dake ɗauke da abinci. Husna ce ta fara gaida shi, yayin da yasmine ta sha kunu, domin ita yanzu tunda Mummy nata ta fara sako zancen aure tsakaninta da Yaya Omer ɗin ta dena sakar masa fuska. "Hala yasmine da dukkan alamu bata ga Omer ba ko?" Mummy ta faɗi cikin gatse. Fuskarta ta ɓata ita fa wllh shi yasa sammmm bata son zama kusa da Mummy'n, duk wasu hanyar kusheta seta fito mata dasu, da kuma diagata gaban ko su waye. Ranta a ɓace ba tare data kalle shi ba ta ce dashi. "Ya Omer good evening da "how was your night?" Ya amsata yana ɗan sakar mata murmushin sa me kyau. _I don't like her_ ta faɗi a zuciyarta tana murguɗa masa baki, wanda hakan da tayi ya sanya Omer ɗin kallonta yana waro idanunsa sosai yana kallonta speechless. "Baby yadai? Nafa kina murguɗa min baki" Ya faɗi yana sake waro idanunsa akanta. "Malam wai ina ruwanka da nine ka fiye takura min fa Aha! Kana takura rayuwana." "Ya takura rahuwar taki yasmine!, Me ya sa ke samm baki da kirki ne idiot kawai" Mummy'n ta ta faɗi a fusace tana miƙewa tayo kanta. Wanda ya sa ta kwasa a mugun guju tana ce dashi zasu haɗu ne. Ta haye samanta tana sauƙe ijiyan zuciya, a gaban mirror taja ta tsaya tare da zare band tare da ribbon ɗin kanta, tana tsurama kanta Ido slowly ta tura hannayen ta cikin gashin kanta, ko me ta tuna kuma se ta wani daki kan nata kaɗan. Tana me furta "Ohhhh ALLAH!!!" A bayyane sakamakon gilmawar kyakykyawar face nashi data gani a cikin zuciyarta. Daidai kuma lokacin ne aka fara yayyafi, kafin a tsuge da ruwan saman sosai, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadacciyar da ta ga gauraye ko ina dake cikin garin. A daidai kuma wannan lokacin John ke zaune cikin motarsa yayi Parking nata a wani bakin masjid. Tin yana saka ran za'a dauke ruwan har ya cire. Don kuwa yaga abin bana ƙare bane, se yaji duk zaman motar ya gama gundirarsa. Don haka a natse a kuma wani irin Hankali ya fito daga cikin motar. Wata brander ya hango babu kowa a wurin, se yaji kamar hankalinsa ya ɗan nutsu da daya zauna a wurin. Umbrella ɗin dake bayan motar ya miƙa hannunsa yana ɗauka, kai tsaye yana yin wajen.... *Around 5:00pm* ♡ Ahankali slowly ya shiga buɗe blue eyes nashi wanda suke ɗauke da barci, kai da ganin idon nasa zaka san cewar idon nasa barcin be gama ishar shi ba, yanayin seya sanya idon nasa ya ƙara kyau dan yanayin se yayi yanayi na daba, wani kalan saurin miƙewa a zabure yayi tuno da wani kalan hargitsetstsen mafarkin da yayi akanta. Wani kalan duka yaji ƙirjin sa ya masa lokaci guda, wadda yasa yaji barcin ya watstsake masa, miƙewa yayi zaune a tsakiyar makeken gadon nasa yana dafe da saitin faffaɗar kirjin sa, "What happiens?, Meke shirin faruwa da rayuwana? " dan bai taɓa jin makaman cin wannan bugun zuciya ba a tattare da shi, shiru ya ɗan yi na ɗan lokacin kafin ya yaye bargon jikin sa a hankali ya zuro zara zaran kyawawan fararen kafafunsa zuwa ƙasan bed ɗin kana ya miƙe yana nufar toilet. Wanka yayo yana fitowa jikin sa na ɗigar ruwa ya shirya kansa cikin wani haɗaɗen jeans mai kyau da tsada launin baki da high neck sleeve shirt launin ash, hakan ya bayyanar da kakkafar suran ƙirjin sa, faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe take sosai cikan damatsan hannun sa yasa faffaɗar kirjin nasa ta kara buɗe wa sosai, ba karamin kyau kayan suka masa ba, kamar dan shi akayi su se hular pcap ɗin daya sanya, bayan ya ɗaure dark black curly hair nashi inda gashin ya sakko harta ƙasar ƙeyarsa. Kai tsaye yana fitowa zuwa garden na shi, yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai, fuskar nan a ɗaure take tamau don mafarkin da yayi sosai ya sake taɓa zuciyar sa, don haka na yau ma tafi na kullun matse wa, jikin sa sai tashin fitinannen kamshi yake, hannunsa na ɗaure da diamond watch me shegen kyau, kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $56000, kasan cewar takalmin launin baƙi ne sai yayiwa farar ƙafar sa bala'in kyau bana wasa ba, a natse yake takunsa irin na manyan jaruman na, ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkarfa ke tinkaro ka. Zaune ya kai kan wata Linder exclusive chair fara. Tare da janyo laptop nashi yana fara wasu ayyuka ta cikin ta. Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop amma fa da an jima kaɗan zaka kalla yana famar cizan lallausan laɓɓansa, ga lips nashi har ya ƙara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza sun da yake famar yi a kai a kai, duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar tunanin me wannan mafarkin da yayi yake nufi?, dan shi har yanzu yaƙi bama ko wacce ƙofa kome mafarkin nasa yake nufi, duk lokacin kuma daya tuna mafarkin sai yaji zuciyar sa ta buga, Tamkar walƙiya haka yaga gilmawar fararen mayun idanunta, zaro nashi idon waje yayi yana tunanin wai meke shirin faruwa da shi ne haka?, "Oh Jesus help" ya furta a bayyane yana kaima iska naushi tare da furzar da abin da ya to kare ƙirjinsa. Tsaye ya miƙe ya shiga kaiwa da komawa zuciyar sa na daɗa ɗaukar ɗumi.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐍𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐀𝐍𝐃 𝐒𝐇𝐀𝐑𝐈𝐍𝐆 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 3 Paid book Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ ```Mommah Narh!, Oum narh, Masoyiya ta Ashanty love, tare da ƙaunata Nainerh kd, tare da Ta Ƙarfen (Rabi'atu Fulani),Aysher Na Lado, Aunty Sayyada narh,ku sani haƙiƙa bana da baƙin da zan iya buɗewa wajen furta kalmomin tarin ƙaunar da kuke min, kawai abinda zance Rabb yabar ƙauna ta har gaban abada abadan abada....``` ꨄ Shigowar ƙira ta hanyar vebratin Vibrating ring doorbell sound ɗin da wayan shi ya soma ne ya sanya shi dakatawa cak, ɗakin ya ɗau wani shiru… se ƙaram vibrating na wayar kawai, amma zuciyar John na bugawa, numfashinsa kuma na fita da sauri da sauri idanunsa jajir, jikinsa na rawa kamar wanda aka zubar da shi cikin sanyi. “Problematic Girl” ya furta a hankali murya cike da rauni, sakamakon hotonta daya sake gitta fuskansa. Wani kalan rumtse idonsa yayi kafin da ƙarfi ya ɗaga hannunsa ya bugi madubin da ke gabansa... Take madubin ya tarwatse ya zama gutsuttsura, jini ya fara fita daga hannunsa… amma bai ji zafi ba. Abinda yake ji kawai…. Idanunsa sunyi jaaa sosai gefe guda kuma ga gutsattsarin madubin daya fashe nan suna walƙiya a ƙasa, suna nuna fuskar John.... fuskar da duniya ta sani a matsayin kwararren matukin jirgin sama, amma yau ita ce a rikice haka. Numfashinsa na fita a hankali, amma zuciyarsa kamar zata fashe. “A dream? No… this isn’t a dream.?” ya furta murya ƙasa ƙasa sosai, wannan ba mafarki bane kawa, wani abu ne da yake neman karya shi daga ciki. Yana tsaka da wannan tunanin har besan lokacin aka sake kiran shi ba a karo na biyu ba, shigowar ƙira na ukun ne ya katse masa tunaninsa, yana sake lumshe ido ya nufa wayar nashi ya ɗauka a hankali, ahankali raunin daya jima hannunsa ke zubar da jini, Screen ɗin ya haska.. _CAPTAIN JOHN – PRIORITY LINE_ Idanunsa ne suka ɗan sauya colour,wannan ba kawai ƙira bane na kowa da kowa ba, ƙira ne me muhimmancin da duk abinda yake yi da zarar ƙiran ya shigo se iya katse ko uban maye kuwa.. kai tsaye answering call in yayi... “Captain John speaking.” Muryar da ta amsa masa cike take da girmamawa. “Sir… we need you!. Urgent deployment. International flight. No one else can handle this route like you.” Wani kalan shiru yayi sai numfashinsa kawai dake ɗan fita kamar a wahalce, yana kuma furzar da wata iska me zafi daga cikin bakinsa, ya jima da sanin cewa shi ne mafi kyau. Shi ne kuma wanda ake nema idan komai ya tsananta, shi ne… wanda sama ta yarda da shi. Se dai tunanin da yake a yanzun shi ne cewar anya ze iya?, domin zuciyarsa tana can a wajen yasmine. “Sir?” Aka sake ƙiran sunansa wanda ya saka shi lumshe ido, yana jin kalmar mafarkin tana dawo masa amma yana danne hakan. Se ma buɗe rinannun idonsa a hankali da yayi. “Prepare the aircraft…” ya faɗa da murya mai sanyi. “Captain John is coming.” Ya katse wayar amma bai motsa ba, A karon farko yana jin wani tsoron tuƙa jirgin cikin rayuwarsa, ba wai tsoron jirgi yake ji ba, A ahhh se tsoron zuciyarsa kawai da yake ji dangane da lamarin da take nemar jefa shi, cikin danne duk wani abinda ke taso masa ya miƙe a natse da ƙyar ya faɗa toilet, bayan yayi dressing ya tsaya gaban madubi. A hankali ya gyara farar rigarsa mai tsabta, ya ja hannun rigar ya daidaita cuff nata sannan ya ɗora epaulets ɗin zinariya a kafaɗunsa masu ɗauke da layuka huɗu masu walƙiya. Alamar dake nuni da iriyar kwarewar da yake da da kuma babban matsayin da yake takawa a sararin samaniya duk da kasancewarsa ba musulmi ba. A natse ya ɗauki tea shima baƙi ya ɗaura shi da nutsuwa. Idanunsa suna kallon kansa cikin madubin amma zuciyarsa kamar tana wani wuri daban, sanin cewar tuƙin dare ne zeyi gashi kuma ƙasar daya nufa me sanyi ce ya saka shi ɗaura jaket ɗinsa dark blue akan shigar ma'aikatan dake jikinsa, yana sake daidaita komai ya yi fitting kamar an ƙera shi ne domin shi kaɗai dama, p-carp nashi ya ɗora a kans. sannan ya ɗan sunkuyar da kansa kaɗan yana kallar yadda cikakken kamanninsa na iko, na izza na wanda duniya ke girmamawa... A natse ya soma takowa zuwa entrance ɗin fita daga parlourn nasa zuwa na gidan gaba ɗaya, yana tafiyan ne kuma takalman sa baƙi masu sheƙi suna bada umarnin saƙƙowarsa. “John…” Haka yaji murya Mahaifiyarsa da wasu lokutan yakan ƙirata da Mother ko Marh ta daki kunnuwansa, don haka cak ya tsaya a hankali tare da juyowa, A nan ya hango Madame Victoria tsaye daga jikin ƙafar benenta cikin kayan alfarma, idonta cike da wani abu mai wuyar a fassara shi kai tsaye… wanda yafi kama da tsantsar ƙauna kai tsaye ta sake jefa masa kalmar... “Where are you going tonight?” ta jefa masa tambayar a hankali amma muryarta na ɗauke da nauyi, wani daƙune farar fuskansa yayi yay kaɗan… “I was brought to Florida by an urgent job” Wani yanka zuciyarta tayi tana faɗuwa tare da takawa kusa da shi idanunta na sauka kan epaulets ɗin sa... “Captain…” ta faɗa a hankali kamar tana ƙoƙarin gwada kalmar ne, tare da ɗago da kanta ta kalle shi kai tsaye bayan ta iso har inda yake tsayen. “Amma wasu hanyoyin ba kowanne ne ya kamaci ace ka bi ba, John!, saboda ban gama yarda dasu ba...” Kai tsaye kalmar Mother ta tsaya masa a zuciya, domin kusan ya gama haddar waɗan nan kalmomin kamar tana nufin wani abu ne daban. Amma koma dai miye shi yanzun baya da lokacin ɓatama lokaci lokacinsa, peack ta bashi a goshi tare da sake nanata masa kalmarta irin ta ɗazun sakk dai, wanda ya saka John matse hannunsa a hankali. “Me kike nufi, Mother?” Wani kalan shiru Madame Victoria tayi kafin ta juya baya, ba tare da ta ba shi amsa ba ta furta... “Ka yi hattara da abin da nake yawan maka tuni Love bye....” ta faɗa tana barin entrance ɗin da yake gaba ɗaya kamar wata walƙiya. Tsaiwa kawai a wurin John yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Kalmar “Ba kowanne hanya ba…” na sake dawowa cikin kansa, lumshe idanunsa na ɗan lokaci yayi numfashinsa na fita a hankali. wayarsa ta sake ƙara wanda ya yanke masa tunaninsa... Yana answering call in aka sake furta... “Captain John… we need you NOW. Emergency flight to Florida No delays pls.” take komai nashi ya dawo yaji kamar ana ingiza jinin jikinsa duk wata damuwarsa na ɓacewa zuwa ƙwarewar da duniya ta gama sanin shi da ita. “Copy that,” ya faɗa a natse yana juyawa ya nufi hanyar ficewa kawai tare da ƙoƙarin saka ƙiran Paah nashi. Wayar na fara ring Papa nashi ya amsa da.... “Hello, John?” A hankali yace, “Paah!, I’ve been called in… it’s urgent.” kafin ya ɗan ja numfashi ya sake furta. “I’m leaving for Florida… right now.” daga inda paah nashi yake ya wani karkatan da kansa tare da furta, “Florida? Right now?” tamkar John na a gabansa ya gyaɗa masa kai yana kuma ci gaba da tafiyan ya ce... “Yes… there’s no delay. I’m the only one they can assign to this route.” wani ɗan numfashi Papa'n nashi ya fesar tare da furta. “Take care of yourself, Joseph….Remember not every journey is like the others.” “I know, Papa…” John ɗin ya faɗi wani ɗan worried smile na kufcewa daga kyakkyawar fuskar san tare da furta. “I’ll be back.” “You better come back safe. Jesus protect you.” Daga suka yanke wayar daidai lokacin da ya isa compound na gidan, tun kan ya ƙarasa ƙarasowa Mecheal yay hanzarin buɗe masa lafiyayyar wata mota ƙirar Black Rolls-Royce Phantom. Kai tsaye ya shiga bayan ya bashi umarnin Airport ze kashi, cikin tafiyan da basu 10 minutes ba suka isa airport na _Murtala Muhammed International Airport_ (MMIA) kasancewar tsakaninsu babu wani nisa. Motar na gama daidai parking nata Mecheal yay hanzarin fitowa yana zagayowa cikin ladabi ya buɗe masa ƙofar baya. Ƙafafunsa dake sanye cikin classic shoe se famar walƙiya suke ya fara zirowa, kafin ya fito gaba ɗayansa cikin kayan pilot ɗinsa masu tsafta, hularsa na riƙe a hannunsa ɗaya mara bandage, fuskar nan tasa mai ɗauke da wani ɓoyayyen damuwa amma idanuwansa cike da wani irin iko. Ahankali wata sassanyan iska ta daki fuskarsa kaɗan wanda ya saka shi ɗaga kansa ya kalli sararin samaniya, tamkar me karantar yanayin samaniya. Gefe guda kuma mutane nata zirga-zirgansu… amma mafi hankalinsu tun farkon bayyanuwar lafiyayyar motar suka dakata hankulansu yana fara karkata wuri guda sakamakon fara takun da yake yi cikin nauyin zuciya dana ƙirji, Cak wata Matashiyar budurwa ta tsaya a inda take, har jakar dake riƙe a hannunta na ƙoƙarin zubewa, gefe guda ma ga wasu maza dake magana amma suka daina maganan suma idanunsu akan John ɗin, domin kuwa wani irin baiwar kyau da zubi da tsarin halitta UBANGIJI ya masa. Wani yaro ne ya kamo hannun mahaifiyarsa tare da furta. “Mom…who is he?” sake riƙe hannun yaron nata da kyau tayi tana cewa “I don't know him...” daga haka suka wuce.... Gaba ɗaya mutane naci gaba da kallon yadda yake tafiya, ba gaggawa, ba jinkiri haka ba garaje. Wasu daga cikin ma’aikatan airport ɗin ne suka kalli juna kafin cikin wata irin girmamawa ɗaya daga cikinsu cikin muryan raɗa ya ce “That’s him… the one they called.” Sarai ya jisu amma bai ko tsaya ba bare kallan inda suke, zuciyarsa naci gaba da bugu yana jin kamar wata inuwa na bin bayansa. Kai tsaye John ya shige cikin hall ɗin da ake fara son ganinsa, Sanyin AC mai sanyi da ƙamshi na tashi wanda suka haɗe suka sake fidda ainihin tsafta da tsarin hall ɗin, kafin cikin muryan kururuwar ƙarar announcements ya fara tashi a sama sama na isowar _JOSEPH Mr JEF DEEFER PATRIARCH _ “Attention please… final boarding call“ nan bayan yayi wasu ƴan ƙananun rubuce rubuce ya sake fitowa wani guy na bin bayansa, ma’aikata naci gaba da gaishe shi cikin girmamawa. Su kuma dama already sauran crew ɗin jirgin sun riga sun gama daidai komai kawai jiran isowansa suke. “Captain… we’ve been expecting you.” Ya ɗaga kai kaɗan, kafin cikin nutsuwa ya furta. “Let’s move.” Daga nan suka fara takawa zuwa ainihin inda jirgin ke fake, hanya suka bashi bayan sun buɗe masa ƙofar zuwa runway, Jirgin yana tsaye babba suna isa matakala ta sauko… a wani kalan hankali ya fara takawa zuwa matakalan ɗaya bayan ɗaya. Har zuwa lokacin zuciyarsa na ɗan bugawa kaɗan da kaɗan, dan kawai mafarkin da yayi ne ke dawo masa yana yawo a ransa… a tausashe sautin takun sawunsa ke amsawa a cikin dogon corridor na airport ɗin cikin nutsuwa… ga wani kalan ɗan banzan kyawun da uniform ɗinsa na pilot suka ƙara masa,me tafe da wani irin ƙima da kwarjini wanda da ace a musulmi aka yi shi to kuwa da tabbas anyi jajirtaccen akan addininsa, se dai fuskar nan a wani irin ɗaure take sakamakon abu mai nauyin da yake jin kamar ya tokare masa ƙirji da zuciyarsa. A ƙofar shiga restricted area ya tsaya ƙofar ta buɗe a hankali da kanta John ya shige ciki, hasken waje ya bar bayansa, ya shiga wani yanayi mai sanyi da tsari inda komai ke nan bisa ƙa’ida da kuma tsari, sauran crew ɗin jirgin suna tsaitsayekowa cikin uniform nashi mai tsabta.fuskokinsu ɗauke da girmamawa suna daidaita tsayuwarsu lokaci gudan da suka hangowa tahiwarsa, Chief Flight Attendant ɗin data kasance mace ta ɗan matsa gaba, zuciyarta na bugawa da sauri amma kuma tana riƙe kanta ta furta. “Captain Joseph… ur welcome, sir.” Muryanta ta faɗi da ladabi me wani irin nauyi,suma sauran crew suka mara masa baya suna furta. “Good evening, Captain!.” Daidai lokacin da yake kawowa inda suke, ja yayi ya ɗan tsaya Lafiyayyun Idanunsa na bin kan kowa ɗaya bayan ɗaya, tamkar yana nazarin su ko kuma yana neman wani abu a cikin su. kafin ya wani ɗan ɗage kai sama kaɗan kawai tare da furta “eveninig.” Kalma guda ce amma kuma ta wadatar dasu, wani co-pilot ne ya matsa kusa matashi ne amma ana ganin kwarewa a tare da shi tare da ambatar. “Sir… mun shirya komai. Flight plan ya riga ya kammala, amma weather… stable for now.” “...for now?” John ya maimaita a hankali, yana kallon sa kai tsaye. Co-pilot ɗin ya haɗiye wani yawu kaɗan tare da gyada kansa yana me furta. “Eh sir… akwai ɗan turbulence a hanyar Atlantic… amma under control.” Ɗan lumshe ido kawai John yayi. _Atlantic…_ Tabbas kalmar ta daki zuciyarsa kamar ƙarar ƙaho, har besan lokacin da ya faɗa wani tunanin daban ba. “Are U okay Captain?” muryar Chief Attendant ɗin ta dawo da shi daga ɗan tunanin daya cilla, kafin ya buɗe idonsa a hankali. Juyawa kawai yayi ya fara tafiya zuwa cockpit ɗin bayan ya furta. “Let’s move.” Kowa ya bi umarni ba tare da ɓata lokaci ba, wata flight attendant ce ta raɗa ma abokiyarta. "There’s something about him today…" Wani murmushi kawai ɗayar tayi cikin sanyi tare da amsa mata da. "Yeah… like he’s not alone." A ƙofar cockpit ɗin John ya tsaya. kai tsaye lokacin da yake bayyana a gaban cockpit ɗin. Wani haske mai laushi ya cika cockpit tare da fuskansa…...Komai a tsari yake buttons, screens, komai na aiki kamar yadda aka saba. Gaba ɗaya baya jin zuciyarsa a daidai bata cikin tsari kawai dannewa yake, Kafin ya zauna a kujerarsa tare da daura bel ɗinsa a hankali. Idanunsa suna kallon gaban jirgin amma ba ganin runway yake ba, mafarkinsa kawai yake haskowa.... “Captain, all systems ready.” Maganar da co-pilot ɗin ya faɗa cikin girmamawa ya dawo dashi cikin nutsuwansa, ɗan jinjina kai kawai John ɗin yayi tare da furta.. “Proceed.” Muryansa a dake rin wacce ke bayyana No nonsense ɗin nan. A ciki kuwa... mataimakinsa (First Officer) ya riga ya zauna yana duba na’urori. “Captain John,” ya faɗa cikin girmamawa. “Komai ya shirya. Weather ya ɗan canza kaɗan… amma babu matsala sosai, ba kamar baya ba....” Ahankali John ya zauna a kujerarsa yana ɗaura belt. Idanunsa suka bi dukkan panel ɗin na’urori... “Copy that…” ya amsa a hankali kafin wani shiru ya ratsa cockpit na ɗan lokaci, wanda hakan ya saka John ɗan lumshe ido hoton Yasmine na faɗo masa… “Captain?” mataimakin ya sake ƙirar sunan shi da dolen dole ya saka John buɗe idonsa da sauri. “I'm fine. Let’s proceed.” Daga nan Engine suka fara ƙara, Cockpit ya cika da hasken buttons masu walƙiya. “Ready for pushback.” “Pushback approved.” Jirgin ya fara motsi a hankali, kafin cikin wucewar wasu ƴan mintuna, John ya ɗaga hannunsa ya kunna PA system nashi, Muryarsa ta cika cikin jirgin cikin sautun nutsuwa,iko da bada kamar umarnin kai tsaye ya ce... “Ladies and gentlemen, this is your Captain speaking…Welcome onboard. We’ll be departing shortly. Please fasten your seatbelts.” Tuni fasinjoji suka fara nutsuwa da jin muryarsa. wasu suna waya, wasu suna kallon waje, Crew kuma suna motsi cikin kwarewa… amma wasu daga cikinsu suna jin wani sanyi da ba su iya bayyana ba... Cockpit… “tashi checklist complete, sir.” John ya ɗan gyara hularsa ya kalli runway ta gaba, yana kallar dogon layi mai haske da ke kaiwa cikin sararin sama shawagi. “Let’s go.” ƙafafun jirgi suka fara motsi hasken runway yana walƙiya a gefunan Co-pilot. “Speed building…” Runway… “Cleared for takeoff.” John ya matsa lever ɗin gaba wacce ta saka Injin jirgin ya yi ƙara mai ƙarfi, da haka Jirgin ya shiga runway… “Speed?” “Checked.” “Rotate.” John ya ɗaga hancin jirgin a hankali zuwa sama ya fara ƙoƙarin landing na tashi, gajimare suna karɓar jirgin cikin sanyi. Co-pilot ya kalli screens... “Sir… slight turbulence unexpected.” wata nutsuwa John yayi yana kallar yadda gajimare masu duhu ke taruwa a nesa kamar suna jiransa, a hankali ya furta. “Something is wrong…” Daga jirgin ya fara keta sararin samaniya, mutanen dake ƙasa suna kallon yadda yake ratsa sararin sama… daidai setin zuciyarsa ya danne a bayyane ya furta.... “So I miss you… more than you will ever know, Yes, I am still struggling to let go. This is a process I need to go through… so for now, I’m ok with missing you.. I WILL Really miss you too my Trouble....” _Hummmmm!!! Tirƙashi. Masu karatu wai ya take ne???.😲. Mi kuke tunani dangane da littafin DUHU na DUKAN duhu ne?, shin ma wanene Wannan Joseph ɗin kansa? Sannan wacece yasmine daya laƙa ba mata sunan Trouble?, shin ku a ganinku yaya zata kasance mana ne kamm? Minene zai faru kuma?..._ *Amsar waɗanan tambayoyin duk suna a Littafin DUHU na DUKAN duhu!! da ke cikin ɗaya daga cikin lates Amazon stories na wannan year's ɗin IN SHA ALLAHU....* _Nie dai AMMEY LAYLERH nace Wllh karku bari ayi tafiyar nan babuku, dan wannan littafin fa da zafinsa yake tafe uyhmmmm, wanda ya rasa shi yaso domin na tabbatar muku tafiyar wannan littafin ko???, to ta dabance MASOYAN AMANAR AMMEY LAYLERH😋🤗🤗😀😀......_ _ku sani cewar Wasu duhun... suna farawa da kuskure ne... Yayin da wasu duhun ke farawa da rashin sani...._ _Wanda suke farawa da kuskuren ku sani daga ƙarshe... rayuwar tana lalace musu ne, to shin akwai bukatar ci gaba da bin littafin DUHU na DUKAN duhu kenan ko???...._ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 4 Paid book Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ *Tabbas maganan hausawa dai dai ne da suke cewa Shimfiɗar fuska tafi Shimfiɗar tabarma, da haka nake so na mika tarin godiyana ga mutane na musamman zuwa ga Yotawanmu, ALLAH ya ƙara mana tarin basira, ɗaukaka,tarin nasarori... Tarin godiya na sosai ga Ayshacool.....* ꨄ Idanunsa yaja yana lumshe su, tare da crossing hannuwansa ta bayan kansa yayi shiru na wani ɗan lokaci, a hankali fuskarta ya sake bayyana a zuciyarsa, yadda ta dalla masa marin nan, har besan lokacin da ya wani buɗe idanunta masu cike da wani irin ɓoyayyen abu. “Captain John? Are you there?!” Muryan co-pilot nashi ta katse shi yana buɗe idonsa tare da furta. “I’m on my way.” Ya furta yana ɗora hannunsa kan controls, amma haka kawai yake jin wani sanyi na ratsa jinin jikinsa, Co-pilot ɗin sa ne ya kalle shi tare da sake jefa masa tambayar. “Sir, everything okay?” Ɗan Lumshe masa idanunsa yayi da wani ƙaramin murmushin da bai gama fitowa gaba ɗaya ba. “Yeah… let’s fly.” _Shin kai babu zuciya a ƙirjinka ne hala!?...._ yaji kalmomin sun wani daki cikin kansa, _kokuwa kana tunani da zuciyar naka ne bada ƙwaƙwalwa ba?...._ ya sake rumtse idonsa yana kuma toshe kunnuwan nasa, amma duk da haka hakan be saka kalmar ta na gaba sake bugar cikin kwakwalwarsa. _Amma kaikam duk ahalunka babu masu imani !, kuma bakusan menene daraja da muhimmancin ƴa mace ba?_ Haka muryarta ta sake shiga kunnensa, wanda hakan har yasa be san lokacin daya saka hannunsa da ƙarfi yana danne controls na jirgin ba, “Sir?” co-pilot yay gaggawar masa magana wanda yasa John haɗiye yawu wani abu yana me furta. “I’m fine.” Wanda a baɗini kuma ba hakan bane, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya tare da shi, mafarkinsa ne ya sake kutsowa cikin tunaninsa, tuni idonsa suka wani irin rine suka yi jaaa sosai, sai ya ji kamar yana sake shiga cikin wani duhu ne da bai taɓa fuskanta ba. gefe guda kuma ga Jirgin dake shawagi a sararin sama cikin nutsuwa, komai na tafiya yadda ya kamata. A can cikin cockpit ɗin kuwa hasken na’urori naci gaba da walƙiya a hankali green, amber, da ɗan ja duk suna nuna cikakken aikin da suke kai bisa tsarin da aka gana seta su, shi kuma yana zaune a kujerarsa, hannayensa a kan controls cikin ƙwarewarsa wacce har ta saka duniya ta sanshi a matsayin shahararren pilot number ɗayan da suke ji dashi a duk faɗin Nigeria bama iyaka Lagos ba... “Altitude steady.” Ya faɗa a hankali idanunsa na kan dashboard. Co-pilot ya amsa da girmamawa shima yana me furta. “Confirmed, sir.” ɗan baya John yaja tare da ɗan matsa wani lever… ya gyara heading… ya duba instruments ɗaya bayan ɗaya, komai dai naci gaba da tafiya daidai. Haka jirgin yaci gaba da keta sararin samaniya cikin daren daya fara rufe sararin samaniyar… a cikin idonsa yake hango wani kalan duhu, duhu mai ɗauke da kauri tamkar ana zuba shi da hannu, amma hakan besa ya girgiza ko jin komai ba Jirgin yaci gaba da shawaginsa a cikin gajimare masu nauyi, shi kuwa Captain John ya zauna cikin nutsuwarsa, idanuwansa suna manne da instrument panel, wani haske mai launin kore da ja yana haskaka fuskarsa yana ƙara masa wani irin kwarjini mai ban tsoro. “Altitude stable… speed normal…” in ji First Officer ɗin cikin ɗan sanyi murya, wanda tun kan ya kai ga rufe bakinsa ƙarar ƙararrawa ta cika cockpit na Jirgin yana girgiza da ƙarfi, kamar wanda jirgin ya bugi wani abu ya daga waje. “Captain! Turbulence is increasing!” tabbas wannan ba gizon fuskanta yake gani ba, jirginsu ne ke ƙoƙarin shiga cikin matsala, wanda hakan ya saka John matse handle ɗin da ƙarfi. Idanunsa na canzawa zuwa wani mataki na daban, “Stay with me…” ya faɗa a hankali kamar yana magana da jirgin kansa. Autopilot ya kashe da kansa, jirgin ya shiga sanar musu da WARNIN warning system failure. Take hankalin First Officer ya fara tashi cikin tsananin ruɗewa yake furta... “Sir… we’re losing control fa...!” Wani kalan fusga jirgin yayi ya fara ƙoƙarin karkata kansa gefen da ba nan suka nufa fa, ganin wannan babban hadarin dake nemar ruskar mutanen dake cikin jirgin suka fara kururuwan ihu, gaba ɗaya tsoro ya gama mamaye kowannensu masu ƙarfin imanin cikin sune kawai ke adda'a daga cikin musulmanmu kenan. Amma shi kam John ko kaɗan bai firgita ba, sai wani numfashi da yaja a hankali, yana saka hannunsa ya kama throttle, ɗayan kuma yana sarrafa yoke. Jin har lokacin ihun passinger's bai dena ratsa tsakiyan kan sa bane ya sake shi furta.... “Listen to me,” ya faɗa da murya mai ƙarfi a kuma tsawacen daya sakasu dole haɗiye komai. “we are not going down.” se kuma wata walƙiya ta sake bugawa jirgin ya nutse ƙasa kaɗan... “PULL UP! PULL UP!” Ƙarar system na ƙara tsananta, John ya ɗaga jirgin da ƙarfi har wasu daga cikin jijiyoyin jikinsa suna fitowa waje, idanunsa sun ƙone da determination. “Come on… come on…” ya sake furtawa a dake yana juya jirgin cikin dabara, ya fice daga tsakiyar gajimaren daya shigar masa hanya, A hankali ahankali kuma girgizan da jirgin yake ya fara raguwa. Wanda ya saka First Officer nashi zaro ido woje, duk da kasancewar ba yau bane karon farkon daya saba ceto rayuka daga cikin hadarin jirgin, kai tsaye tare da furta... “Sir… you did it.” John dai bai ce komai ba, se ɗan murmusawan da yayi kaɗan tare da furta. “Not yet. Keep watching.” ci gaba da kula da daidai na'urorin yayi zuciyarsa na masa wani irin bugun daya gaza kane ko na miye. A cikin cockpit, ƙarar alarm ta dawo fiye da farko ma.Wannan karon kuma _ENGINE FAILURE_ ne, a ɗan rikice First Officer duba inda John yake kai tsaye tare da furta. “Captain… engine one is down!” nan take Jirgin ya sake karkata har kamar wannan karon ma ya fi muni akan ɗazun, tuni passinger's suka sake ɗaukan wani sabon ihun wasu suna kuka, wasu suna kiran sunayen ALLAH kamar ɗazun. Ahankali John ya sake ɗaga kansa kaɗan yana me furta musu. “Declare emergency,” ya faɗa cikin taushi amma da iko. “Mayday, Mayday, this is Flight 271… we have engine failure, requesting immediate landing clearance…” Sai wata murya daga control tower ta amsa mai cike da damuwa ta hanyar furta. “Flight 271… nearest runway is unstable due to storm. Visibility almost zero…” a tsorace First Officer ya kalli John yace. “Sir… we might not make it…” kafin shiru na ɗan lokaci ya gitta kawai se John ya ɗan yi wani murmushi kaɗan irin murmushin da ke ɓoye wani abu mai girma, ahankali ya furta. “Then we create our own way.” daga haka ya kama controls ɗin da ƙarfi. Sedai Jirgin yana saukowa da sauri, iska na dukan shi kamar za ta tarwatsa shi..._ALTITUDE LOW TERRAIN! TERRAIN!...._ “Pull up, Captain!!” “A’ahh No!…” John ya faɗa a hankali. “not yet…”Wata walƙiya ce ta haskaka filin samaniya tana bayyana na ɗan lokaci, sannan ya ɓace.. “NOW!” Da ƙarfi ya daidaita jirgin ya juya shi cikin dabara da zallar kwarewansa wajen iya sarrafa jirgin. *Florida...... Miami International Airport...* A can cikin babban control tower na Miami International Airport kuwa, hasken fitilu ne kawai suke kyalli, allunan radar suna ta haskawa da motsi ba kakkautawa, sai kuma ƙarar ƙararrawa mai tsanani ta katse nutsuwar daƙin.... “Sir! Mun rasa daidaiton altitude na Flight JX-27...” wani daga cikin jami’an ya faɗa cikin tashin hankali. Shugaban kula da zirga-zirgar jiragen sama ya mike tsaye da gaggawa. “Wane jirgi ne?” kai tsaye tambayar daya cilla musu kenan. “Na Captain John, sir… daga Murtala Muhammed International Airport zuwa Florida!” Wani irin shiru mai nauyi ne ya ratsa ɗakin na ƴan dakiku, Kafin shugaban ya ɗaga wayar gaggawa yana magana da cikin muryan kamar bada umarni yake ta nanata kalaman.... “Emergency protocol activated! Notify all units! We have a critical situation in the air!” take kuma a lokaci guda aka aika da saƙon gaggawa zuwa sauran hukumomi ciki har da Federal Aviation Administration. “Flight JX-271 is experiencing severe instability… possible system failure!” daga inda suke Allon radarsu yake nuna jirginsu John dake sake karkata daga hanyarsa, yana kuma gudu sama da kima. “Try to reach Captain John NOW!” wannan shugaban ya sake faɗi da dan karfi. “Sir, mun kasa samun cikakken response… siginar na yankewa ne...!” Hannun wasu ma’aikata na rawa yayin da suke ƙoƙarin daidaita sadarwa. “Mayday signal detected!” wani ya yi ihu, ɗakin ya cika da tashin hankali. Shugaban ya runtse ido na ɗan lokaci da ƙarfin bala'i sannan ya buɗe da ƙarfin. “Prepare emergency landing clearance. Ko da menene… dole ne mu sauƙar da wannan jirgi lafiya!..... A can cikin sararin samaniya kuwa tuni wasu daga cikin rayukan mutane sun gama saduda da saddakarwar se dai wasu basu ba, Kowa a cikinsu zaman jiran tsammanin warabbuka suke, kowa na jiran abin da zai biyo baya ko ganin abinda hali zayyi. Idan muka shiga cikin cockpit ɗin kuwa, inda komai ke tafiya da tashin hankali a cikin cockpit na jirgin, hasken gaggawa (emergency lights) ne kawai ke kyalli. A wannan karon kam gaba ɗaya gumi ya gama jiƙe goshin Captain John yayin da hannunsa ke rike da controls da ƙarfi. “Control… this is Flight JX-271… we are losing control!” muryarsa na rawa, amma yana ƙoƙarin daurewa, sai karar ƙararrawa ta sake tashi Allon gabansa na sake nuna masa matsala mai tsanani, engine ɗaya yana rasa ƙarfi. “Damn it… not now!” ya furta a hankali, kafin ya danna wani maɓalli yana ƙoƙarin daidaita jirgin.“Come on… come on…”Jirgin ya fara karkata gefe guda da ƙarfi.Co-pilot ɗinsa ya kalle shi cikin firgici.“Captain, we’re dropping altitude too fast!” John ya matse steering (yoke) da ƙarfi, jijiyoyin hannunsa suka fito. “Stabilize it! Reduce thrust on engine two… NOW!” “Engine two reduced—but sir, engine one is failing completely!” Wata ƙarar girgiza ta sake ratsa jirgin. A wajen jirgin kuwa gajimare masu duhu ne suke sake kewaye jirgin nasu sakamakon ƙasar Florida ɗin da take daf da shirin fara zubar da ruwa ba tare da sun san hakan zata iya kasancewa, duk da cewan seda suka aika da komai na tashin nasu zuwa ga Florida ɗin tace su taho babu Matsala, su a nasu ganin har jirgin ya iso ruwan be fara sauka ba, iska mai ƙarfin data sake dukan jirgin kamar zata fasa shi gida biyu ya sake saka zuciyoyin kowa sake rugujewa, John ya haɗiye wani abu daga cikin maƙoshinsa yana cewa. “Okay… listen to me,” ya ce da ƙarfi, yana ƙoƙarin kwantar da hankali. “We’re not going down. Not today.” Ya kunna sadarwa da control tower na Miami International Airport. “Mayday, Mayday, Mayday! This is Captain John of Flight JX-271… we have an engine failure and unstable controls. Requesting immediate landing clearance!” A can ƙasa aka amsa da sauri. “Flight JX-271, this is Miami Tower. Runway is clear. You are authorized for emergency landing!” John ya numfasa da ƙarfi. “Alright… this is it.” Jirgin na rawar jiki yayin da yake saukowa a hankali. “Flaps… now!” “Flaps deployed!” “Landing gear!” “Landing gear… not responding!” Idanunsa suka buɗe sosai. “WHAT?! Try again!” “Still not working, sir!” Shiru na ɗan lokaci ya ratsa cockpit ɗin… sai ƙarar iska kawai, John ya lumshe ido na daƙiƙa ɗaya, sannan ya buɗe su da sabon ƙarfi. “Then we land it… manually.” Co-pilot ya kalle shi cikin tsoro, yace “Sir… that’s risky…” John ya ɗan juya kansa kaɗan, idanunsa cike da natsuwa mai zurfi irin wacce ake samu ne kawai a lokacin da mutum ya yanke hukunci na ƙarshe. “Risky… amma dole,” ya faɗa a hankali. “Ka yarda da ni.” Jirgin ya sake girgiza da ƙarfi, sai ƙarar iska mai razanarwa ta cika cockpit. “All instruments unstable, sir!” “Forget instruments… feel the aircraft!” John ya faɗa da ƙarfi, yana ɗan sassauta hannunsa a kan starring yana jin yadda jirgin ke amsawa. “Altitude?” “2,500 feet… dropping!” “Okay… muna da kaɗan lokaci.” Ya kunna mic cikin gaggawa. “Cabin crew brace passengers immediately!” A can cikin jirgin, ana jin muryoyin firgici… ihu… addu’o’i. Amma a cockpit shiru ne mai nauyi da ruguza zuciya, John ya kalli gaba… runway ɗin Miami International Airport yana bayyana cikin ruwan sama da gajimaren dake kamar soma basu hanya, “Speed is too high!” co-pilot ya faɗa. “Na sani,” John ya amsa, yana rage thrust a hankali. “Kar mu yi overcorrection… ko mu stall.” Jirgin ya ɗan yi ƙasa da ƙarfi.... “Careful!” “I’ve got it!” Ya daidaita shi da sauri, yana gyara nose ɗin jirgin, “Listen,” John ya ce cikin ƙarfi, “Za mu yi belly landing. No landing gear… no mistakes.” Co-pilot ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya gyada kai.“…I’m with you, sir.” John ya ɗan numfasa. “Good.” “500 feet!” Runway ya kusa sosai yanzu. Iskar waje na ƙara ƙarfi, ruwan sama na bugun gilashin cockpit. “Hold it steady…” “300 feet!” Zuciyar su na bugawa da sauri.“200 feet…” John ya matse Starring da ƙarfi yana ɗan ɗaga nose kaɗan. “100 feet…!”Shiri na ɗan lokaci ya yi kamar ya tsaya.“NOW…” Jirgin ya bugi ƙasa da ƙarfi ba tare da ƙafafun sun sauka ba.Wuta da walƙiya suka tashi daga ƙarƙashin jirgin yayin da yake gogayya da runway. “Keep it straight!!” John ya yi ihu. Jirgin na son karkata amma ya ja shi ya dawo daidai. “Don’t lose it… don’t lose it…” ahankali gudun jirgin ke raguwa, amma har yanzu yana da ƙarfi. “Brakes not available!” “I know!”Ya ci gaba da riƙe shi da ƙarfin hali, A kuma ahankali ahankali gudun ke raguwa, kafin Jirgin ya tsaya cak.Ba motsin komai, ba ƙara sai numfashi mai nauyi a cikin cockpit. Co-pilot ya dubi John da idanu masu cike da hawaye. “We survived.” John ya jingina baya, ya rufe ido na ɗan lokaci. “Everyone did,” ya faɗa a hankali.... ★ Cikin ƙasar Florida kuwa, tuni labari ya gama karede ƙasar cewar jirgin daya taso daga Lagos zuwa Florida ɗin is bad….. kan kace me ne labarin har ya fara gama fita, irin su hidan talabijin na Florida sun katse shirye-shiryensu... “BREAKING NEWS!” “An emergency situation involving an international flight approaching Florida…” Hoton jirgi a cikin hadari ya bayyana a screen, mutane a gidajensu tare da su aka kalla komai cikin tashin hankali.... A filin jirgin sama na Miami International Airport motocin gaggawa sun fara jera ambulance, fire service, police duk sun shirya. Wani jami’i ya faɗa da ƙarfi, “Prepare for emergency landing!” gaba ɗaya ƙasar na kallon jirgin ko sai sauƙa lafiya… ko kuwa zai zama labarin ƙarshene?. A lokacin da jirgin yayi kamar wata fisga daidai zai sauka ƙasa cikin sauri Fasinjoji wasu suka riƙe kujerunsu da tsoro, wasu na runtse ido cike da tashin hankalin da basu taɓa shiga, saurin ya fara raguwa har seda jirgin ya sauƙa akan diga digansa yana tsayawa da kansa, wani shiru na mamaye ilahirin jirgin. Fuskan First Officer cike da fara'a ya zube a kujera yana me furta “we survived Finally....” John ya kalli gaban jirgin yadda ruwan saman ke zuba a gilashin cockpit ɗin, Ya wani lumshe ido na ɗan lokaci, yana sakin wata ijiyar zuciya me kyau tare da furta.... “Welcome back to earth.” Yana ci gaba da kallon ruwan saman yanda yake zuba a hankali… ga hasken motoci na walƙiya a ko’ina a filin jirgi. Har dama tarin Ambulance… ƴan jarida… jami’an tsaro duk sun cika wajen. Kafin da a aka buɗe ƙofar jirgin fasinjoji suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya… wasu suna kuka, wasu suna godiya. “Thank you! Thank you!” wasu na cewa “God bless the pilot!” Suna kiran suna guda ɗaya… JOHN shi ne ƙarshen fitowa haka ya fito sanye da uniform ɗinsa mai tsabta duk da abin da ya faru, amma kayan na nan fesss, Ruwan sama naci gaba da sauƙa a kansa, amma bai damu ba, gefe guda ka ƙaran ƙaran cameras suka juya gare,wani irin numfashi John ya fesar me ɗan zafi, lokacin da wata ƴar jarida ke cilla masa tambayoyi. Cikin wani irin zallar izzar da yake da yaci gaba da takawansa, A hankali yana janye idanunsa da ga kallon su cike da basarwa alamar ƴan izzar na kusa kenan. Wata daga cikin yar jaridar ce ta sake matsa kusa dashi, tare da furta... “Captain John! How did you manage to land under such conditions?!” ko kallo bata isheshi ba ya drectly yana nufar wata mayyar Black jeeb ɗin da aka buɗe masa ya shige, aka jata da mugun gudu suna barin airport ɗin baki ɗaya.... *Hhhhhhh mun sha da kyar,don ALLAH zuciyoyin su waye suka girgiza suma bayan ta AMMEY LAYLERH,da kuma passinger's namu?.......* *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 5 Paid book Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ ꨄ Drectly babban Hilton Blue Lagoon motar ta nufa, ga shirun daren daya sake nisanta yanayin se hasken streetline ɗin daken kyalli, A natse aka faka motar a gaban Hilton Miami Airport Blue Lagoon ɗin dake ɗauke da hayaniya tamkar ba dare ba, Ahankali ya fito daga motar fuskar sa babu wani abu me kama da annuri, se kawai gajiya da wani abinda ke damunsa a zuciya, kai tsaye a reception har an riga an tanajar musu komai. Ɗaya daga cikin ma'aikatan reception ɗin ya furta... “Good evening, Captain John… your room is ready.” Kansa kawai ya ɗan jinjina ba tare da ko tsaya amsa gaisuwan daya kawo masa ba, key card na room ɗin kawai ya amsa yana nufar room nashi, yana shiga ɗakin ƙofar ta koma ta rufe da ƙaramar ƙara, shiru babu motsin komai a room ɗin se A/Cn dake kaɗawa a hankali kaɗai. A tsaƙiyan ɗakin John ya tsaya na ɗan lokaci, tamkar wanda bai san me zai yi ba, p-carp nashi kawai ya zare daga kansa yana jefa ta saman gado yana jan wani numfashi mai nauyi… kafin ya kai zauna gefen gadon hannunsa riƙe kansa da yake jin na sara masa sosai,Wata iska me zafi ya fesar yana me ambatar kalmar. “Ohh Jesus..” saboda yadda abinda ya faru a jirgin ne kawai ke dawowa a kansa, tun daga kan muryoyi, gargaɗi, firgicin da mutane suka shiga dama sauran crew ɗin su. Tsaye ya miƙe ahankali ya isa bakin window, yana kallar ainihin tsakiyan birnin Florida ta hasken fitilun Miami suna kyalli kamar komai yana tafiya lafiya… ya jima tsaye a wurin kafin ya dawo gefen gadon ya zauna, se da ya ɗan sake diban lokaci kana ya faɗa bathroom yayo wanka ya fito, kayansa ya sanja kawai zuwa na bacci ya rufe ido, amma baccin ya ƙi zuwa, don daya rufe idon yaje jin kamar har yanzu yana cikin cockpit ɗin ne, ga zuciyarsa dake bugawa da sauri ba sassauci ko sauƙin hakan dangane da lamarin, a ɗan wahalce ya juya gefe ɗaya, nan ɗin ma babu sauki ,don haka ya sake juyawa ɗayan gefen shima hakan babu afuwa. Daga ƙarshe ma sai buɗen idonsa yayi cikin duhun ɗakin, ga gajiyan dake ci gaba da ratsa ilahirin jikinsa, zuciyarsa babu nutsuwar komai, haka dare ya ci gaba da tafiya ba tare da John ya sama runtsawa ba, daga ƙarshe ma yadda yaga daren ranar haka safiyar ta iske shi amma idanunsa a lumshe kuma se dab da farkon fara ƙiraye ƙirayen sallan subhi ya rufe idonsa da ƙarfin daya saka komai nashi mutuwa. 8:00 Hasken ranar da ya shiga ɗakin na Hilton Miami Airport Blue Lagoon ne ya saka John buɗe idonsa a ɗan firgice, numfashinsa ya ɗan yi nauyi. Kafin ya tashi zaune da sauri yana jin haushin kansa daya farka yanzun,saboda baccin da bai sama ba a daren jiyan, wani yamutse fuska yayi tare da furta kalmar… “Damn it…” A bayyane yana saukowa daga gadon da ƙarfi kai tsaye ya nufi window… direcly hasken rana ya kutso ta cikin labulen glass na ɗakin yana sauka a fuskar John. Sai ya buɗe idonsa da kyau yana amsar iskar dake kaɗawo daga sama tana sauƙa a kyakkyawar fuskarsa, tafin hannunsa ya ware yana cusa su cikin gashin kansa ya soma yamutsawa, tare da dafe glass door ɗin da hannunsa ɗaya ya matse shi sosai har jijiyoyin hannunsa suka fito. Yana daga tsayen da yake ya ji kamar yanzun ne komai ke ƙoƙarin shirin sake faruwa, Muryar “Mayday” da kuma lokacin da hannunsa ya sauƙa kan control yana matse shi da ƙarfu, da kalmar... “Control… we are losing” Wani toshe ƙofofin kunnuwansa yayi yana me furta... “STOP IT!” Ya wani faɗi a tsawace yana janyewa daga jikin window'n ɗin kamar wanda ake ja da shocking ,tafiya ya fara cikin ɗakin gaba da baya kamar zakin da aka kulle a cikin keji ya kasa fita, hannunsa yakai ya ɗauki wayarsa ya kulketa yana yin jifa da ita saman gado da ɗan ƙarfi. Domin baya son magana da kowa, haka baya son jin komai!, Kafin ya taka ya nufi bathroom. Shower kawai ya buɗe ya sakar ma kansa, take kuwa ruwan ya soma zuba da sauti mai ƙarfi yana dukan fuskansa da jikinsa,hannuwansa duka biyun ya saka yana jingina da sink, yana kallon kansa a mirror da Idanunsa da suka ɗan yi ja. Fuskar sa ta canza ba ba kamar John ɗin farkon da muka fara gani bane, wannan ɗin ya rikiɗe zuwa wani John ɗin na daban, haƙoransa ya matse da ƙarfi yana taune gefen lips nashi, kafin cikin wani ƙaƙƙarfan sautu ya ce.... “You need to get a grip, John…” Ya faɗama kansa da kansa da ƙarfi, yana wanke fuskansa da ruwa mai sanyi. Sanyin ruwan daya gama ratsa shi ne ya saka ji jan wata ajiyar zuciya na ɗan lokaci, sake nutsuwa yayi yana jin sanyin yana ci gaba da ratsa fatar sa da zuciyarsa. Bayan wasu mintuna ya fito daga bathroom ɗin, ya shirya cikin sauri kamar wanda yake gudu daga wani abu, lafiyayyar jacket ɗinsa ya ɗauka yana ɗorawa saman shigar jikinsa, kai tsaye ya nufa bakin ƙofar. Se da yaja ya ɗan tsaya kafin ya kai hannunsa kan Handledoor amma be kai ga budewa ba, se shirun da kawai yayi kafin yaja wani numfashi mai nauyi…ya buɗe ƙofar inda Corridor ɗin hotel ɗin ya bayyana inda yake nan shiru, a hankali ƙafafunsa suka soma taka carpet mai laushi sanyin safiyar ranar da kuma na na'urorin dake bayar da sanyin suma, tafiya yake ba tare da ya waiwaya ba. Kuma jin duk wani taku yake a wani mataki me nauyi, yana jin ba wai kawai yana tafiya ba ne, har ababuwan dake ransa yake son yaga yayi ƙoƙarin kawarwa, a haka har ya kawo inda lift take, da kanta Lift ɗin ta buɗe ya shiga, ƙofar ta rufe a hankali… Reflection ɗinsa ya bayyana a cikin glass ɗin lift. Kafin ya wani kalla kansa a hankali ya wani kawar da kansa daidai lokacin da Lift ɗin ke kawo shi Ground floor. Ƙofar lift ta buɗe tana bayyana Reception ɗin Hilton Miami Airport Blue Lagoon ɗin dake cike da hasken safiyan ranar da motsin mutane masu kai da komo, ahankali ya fito yaci gaba da tafi daidai wata Receptionist na ƙarasowa har inda yake da murmushi a fuskarta take furta. “Good morning, Captain” Bai tsaya ba, bai kuma amsa mata ba yayi wucewarsa kai tsaye, Iskar safiyar na sake bugar fuskar sa wanda ya saka shi ɗan lumshe ido, ya furzar da wani numfashi mai zurfi… yana ƙarasa fita daga ainihin hotel ɗin hannuwansa zube cikin aljihunsa, haka yaja ya tsaya a bakin hanya na ɗan lokaci yana kallar yadda motoci ke wucewa…wayar sace tayi vibrating ɗin da dole ya saka shi fito da wayar ya kalli screen nata ahankali, _Airline Operations_ Fuskarsa ta ɗan canza duk da yasan hakan ba wani abun mamaki ba ne, wayar ya ɗaga inda yana kai ta kunne aka furta. “Good morning Captain,” muryan da aka kira shi ɗin ya faɗa cikin tsari. “We hope you got some rest.” Sai ya ɗan yi shiru Idonsa ya lumshe kaɗan kafin ya wani furta kalmar. “Not really.” aka sake yin shiru na ɗan lokaci, kafin muryar ta sake dawowa... “We need you ready. Your next flight is scheduled…” John ya ɗan matse haƙoransa. “Next flight?” “Yes, Captain. You’ll be departing soon.” aka sake bashi tabbacin hakan, Zuciyarsa ce ta ɗan buga da ƙarfi. “Where to?” se kuma yayi shiru kawai yana jiran amsar da za'a bashi, tamkar wanda yake tantance yadda zasu faɗa masa aka furta... “…Back to Lagos.” Wani irin shiru ne ya ratsa tsakanin wayoyin nasu, kafin John ya juya ya kalli hotel ɗin dake bayansa. Sai kuma ya sake kallon hanyar, tare da matse wayar da ƙarfi. Komawa Lagos?… Wannan tafiya da ta kusa zama bala’i…sake komawa cikin jirgi?, duk da dai bawai yana a tsorace bane, se dan kawai buƙatan balance ɗin da yake ko ya samu ƙwaƙwalwansa ta huta. “Captain, are you there?” Wannan kalmar ta dawo dashi cikin tunaninsa, kafin a dake ya furta. “yeah.” Ya amsa yana jan numfashi mai nauyi, “When is departure?” “In a few hours. Transportation will pick you up.” daga nan call ɗin ya katse, duk da haka John be motsa ba, bai kuma yi komai ba,sai iskan dake ci gaba da kaɗawa, kafin ya samu ahankali ya juya a hankali, ya sake shiga cikin Hilton Miami Airport Blue Lagoon…Matakansa sun fi na da ɗan nauyi yanzu, ba kamar wanda zai huta ba… Amma kamar wanda ake tura shi zuwa wani abu da bai gama fahimta ba, haka Lift ta ɗauke shi zuwa sama… Reflection ɗinsa ya sake bayyana amma yanzu, ya bambanta yana jin ba kawai gajiya ba ce…Dole akwai wani abu mai zuwa koda ya isa masaukin nasa tsayawa kawai yayi a tsakiyar ɗakin. Ya kalli gadon da bai iya bacci a kai ba daren jiya, box nashi kawai ya ɗauka ya fara shiryawa cikin nutsuwa amma cikin fushin da fuskansa bata bayyana shi ka tsaye ba, don baya son tafiyar amma amma ya sani dole ce, a haka da wannan tunane tunanen ya samu ya rufe box nashin bayan ya shirya cikin shigarsa ta pilot. key card na room ɗin ya dauke yana nufar ƙofan fitan, amma se da ya ɗan tsaya a bakin ƙofa na ɗan lokacu, kafin ya lumshe idonsa da sauƙe wani numfashi mara sautu ko kaɗan kana ya buɗe ƙofar. Ya fara tafiya Jacket ɗinsa na'a hannunsa. Yana dap da isa compound na hotel ɗin wani sabon kiran ya sake shigo masa, kamar ba zai daga ba amma kuma dole ya amsa, kai tsaye shi da kansa ya furta ... “Captain John. Is calling” Muryarsa a takaice ta faɗa hakan, “Captain…” muryar airline ɗin ta dawo, amma wannan karon akwai ɗan canji. “We have a situation.” wanda ya saka John ɗan faɗa fuska kaɗan ba da yawa ba, “Go on.” Sai wani ɗan shiru ya bayyana, “Your return flight has been delayed till tomorrow morning.” aka faɗi kai tsaye daga cikin wayan da ya saka John yin shiru ganin ana son sake caja masa kai ya ce. “Delayed?” “Yes, Captain. Technical inspection and clearance issues. We cannot proceed today.” Hannunsa ya saka yana matse wayar da ƙarfi, Idonsa na ɗan rufewa har na ɗan lokaci, kawai yana jin kamar son ruga shi kawai suke, tamkar wanda aka tilasta masa yin maganar yace. “fine.” a takaice call in na katsewa daga nan, kai tsaye ya koma room nashi, yana yasar da box nashi saman kujera da ɗan ƙarfi, Yana kai hannunsa ya rufe fuskarsa tare da furta kalmar.... “Damn it…” A bayyane kai tsaye kayan jikinsa ya sanja bana aikin ba wannan karon ya saka simple shirt da jeans… Kamar wanda yake ƙoƙarin zama mutum na al’ada ba wannan pilot ɗin ba ya sake ɗaukar key card nashi ya fita daga ɗakin. Yanayin ya ɗan sake sanjawa ba kamar ɗazun ba har zuwa lokacin kuma zuciyarsa ba ta gama warwarewa ba. A bakin hanya ya tsaya sai ga wani taxi nan, ya ɗaga hannu masa hannu Motar ta tsaya a gabansa. “Where to, sir?” me motar ya tambaye shi, ɗan shiru John ya yi na alamar tunani don bai ma san inda ya nufa ba, sai kawai yace... “Just… drive.” Driver ya kalle shi a mirror ɗin gaba, amma bai tambaya ba motar ta fara tafiya bayan ya shiga, ahankali motar ta fara ratsa titunan Miami… Garin yana da kyau sosai musamman bishiyoyin da suke kusan kewa da garin, gashi sun fara hango ruwan teku daga nesa, ga dogwayen gine-gine masu kyau da tsari, shiru kawai yayi kallon komai ne tamkar be taɓa zuwan ƙasar ba, A ahhh sedan wannan ɗin jin sa yakai daban da sauran, ahankali motar nasu ke ci gaba da tafiya har suka wuce kusa da South Beach… Ga teku nan nata famar walƙiya, Mutane na yawo a wurin, wasu na dariya, wasu na hutawa ne kawai, shi ma se yaji yana son kasancewa ɗaya daga cikin mutanen don haka bar besan lokacin da bakinsa ya furta... “Stop ita....” Dan waiwayowa driver ɗin yayi alamar gaskata wa tare da sake tambayar. “You wanna stop here, sir?” Sake kallar wajen John ya yi ahankali tare da sake furta “…Yeah.” Daga nan ya sauƙa a motan kai tsaye ƙafafunsa na nitsewa cikin yashi me laushi, Iskar tekun kuma ta taho da ƙarfi ta bugi fuskar sa. Nan ya fara takawa zuwa gaba a hankali, ya tsaya yana kallon ruwan. Ruwan yana motsi a hankali, amma yana da ƙarfi a ƙasa kamar yanda yake jin zuciyarsa, hannuwansa duka biyun na cikin aljihunsa ya lumshe idonsa ahankali yana shaƙar ƙamshin ruwan, baka jin komai a wurin se iska da ƙarar tekun. Sai ya buɗe idonsa a hankali, wanda yaji sun ɗan yi masa sanyi kaɗan, amma kuma ba cikakkiyar nutsuwa ba ce, yana jin kamar yayi missing wani abu me muhimmanci a cikin rayuwarsa tun daga lokacin da ya haɗu da ita... tamkar kuma dama wanda tunanin ke jiran ya fado masa kalmarta ta. _Koda yake alamu sun gama nuna cewar Musulunci ma kai baka da!...._ Ɗan runtse idonsa yayi, amma har yanzun be dena jiyo ci gaban kalmar nata ba. _Don da dukkan alamu arziƙinsa ma baka samu ba, bare kuma har aje ga sanin daraja ɗan Adam..._ Se yaji kansa kuma na ɗan fara jujjuya yawa, kalmar musuluncin kawai nemar tarwatsa kansa yake, _Amma duk da haka Kai mutum ne wadda ko acikin Christian ɗin ma kai baka da daraja daga kallonka na tabbata haka, duk iskancin da irinku masu addininku suke dashi basa taɓa wulaƙanta ɗan Adam irin haka...._ Hannunsa ya zare daka toshewar da yama kunnuwan yana fara jujjuya a wurin, kafin ya fara tafiya a bakin rairayin… kamar wanda ke nemar wani abu amma bai san ko menene shi ba, kafin a hankali ya cira kansa ya kalli sararin sama, yana jin wani abu me zafi na kama zuciyarsa, _To dan ma kaji Wllh² baka buge banza ba!, tun da kai baka da cikakken imani da kuma tausayi, to kuwa wllh se na nuna maka hasalin yadda ake mutum ta mace da kuma darajantata!...._ Kalmarta ta gaba ta sake dakar kansa, jikinsa ya ɗan fara masa rawa nan take, ga hasken ranar daya soma dakarsa a hankali, wata kara yayi yana me furta. “Ohhh jesus” Ya furta yana samar wata ƙarƙashin bishiya ya kwanta a ƙarƙashin lemar wurin, kusa da wani ɗan farin dattijon dake zaune saman darduma da Alqur'ani a wurin yana karatu cike da wata irin natsuwa, kuma dattijon da ganinsa ɗan 9j ne ma, wata irin nutsuwa John yaji yana sama da jiyo sautun karatun Alqur'anin, take wani daddaɗan bacci yayi awon gaba dashi, baccin daya jima be sama irin saba da jimawa, shi kuwa wannan Dattijon a natse ya sauƙe idonsa kan John ɗin da tun farkon bayyanuwarsa akan idon sane, da ihun da yayi da kuma jujjuya kan daya ringa yi duk a kan idon sane, haka kawai yaji ƙaunar son yaron, da kuma son rabauta shi daga cikin wannan ƙazamin addinin nasa, don kallo ɗaya ya masa yasan cewar ba musulmi bane, kuma ba yau bane karonsa na farkon daya taɓa haduwa da John ɗin ba, a natse ya ƙarasa har inda yake ya kama kan John tare da soma furta.... “Allahumma ihdi JOHN waftah ƙalbahu lil-Islam. Allahumma ihdihina siratal mustaƙim....Allahumma a’iz al-Islam bihi....” _Ma’ana yana nufin ALLAH ka shiryar da John ka bude zuciyarsa zuwa ga Musulunci... Ya ALLAH ka shiryar da shi hanya madaidaiciya.... Ya Allah ka karfafa Musulunci ta wurinsa...._ Kafin ya rufe da... “Allahumma a‘izzal-Islāma bi-aḥabbi hādhaynir-rajulayni ilayka... Ya ALLAH!, ka shiryar da wannan bawan naka, ka kuma buɗe zuciyarsa ga hasken ka, ka faɗaɗa kirjinsa ga imaninka, ka fitar da shi daga duhu zuwa haske, Ya Ubangijin talikai.... Ya ALLAH!, shi bawanka ne, Kai ka fi sanin halinsa, ka ji tausayinsa, ka gafarta masa, ka sanya shi cikin bayinka na ƙwarai. Ya ALLAH!, kada ka bar zuciyarsa ta ƙaƙƙarfu, kada ka bar shi ga kansa ko da kiftawar ido ne, ka shiryar da shi zuwa hanya madaidaiciya....” ya masa adda'an cikin nutsuwa mai girma da murya mai sanyi. Daga nan iska ta tsaya,duk wani sautin dake tashi a wurin ya rauraya, kamar duniya ta saurari addu’ar, Shi kuwa John tamkar wanda aka farkar a cikin baccin haka yaji sautin kalaman wannan dattijon da ke riƙe da saman kansa har zuwa lokacin. Ga wani kalan abu da ya fara ji daban, shi ba tsoro ba haka shi ba fushi ba, saima wani irin natsuwan da bai taɓa ji ba ne a caf rayuwarsa na kamasa, ahankali cike da nutsuwa mutum ya yunƙura da nufin miƙewa amma kuma John ya riƙo hannunsa, har lokacin kalmomin adda'ar nan da ya masa na ci gaba da ratsa zuciyarsa. Don haka mutumin yaja da baya kaɗan yana kallon John ɗin da shima shi yake kalla cike da nutsuwa, yana jin kamar wannan ba shi ne karon farko daya taɓa ganin fuskar ba.... “Me… ka yi min…?” Muryan John ya ratsa cikin kunnuwan dattijon, ahankali ya kalla John ɗin cike da wata kalan nutsuwa da haiba ya ce. “Ban yi maka komai ba…sai kawai roƙon Ubangijin mu da nai kan ya seta ka akan hanya madaidaiciya, wacce zata tseratar da kai ranar gobe kiyama... Ina son wannan rana ta zama ranar farkon haske a gare ka…..a cikin DUHU na DUKAN duhu!!!......” John ya saki hannun mutumin ya koma ya sake kwanciya baccin ya sake tafiya da shi me cike da wata kalan salama da nutsuwa, se wajajen uku ya farka, hakan ma iska me ƙarfin da aka fara kaɗawa ne, da kuma ruwan da aka soma yi sama sama, yana tashi yaga gorar ruwa har biyu a gabansa ya bude ya shanye na farkon, na biyun kuma ya ɗauke yana tafiya da ita cikin ruwan dake ƙara ɗan ƙarfi, fesss yaji zuciyarsa tayi akan zuwansa wurin da yazo cikin wani irin ƙuncin da duhun zuciya, kai tsaye masaukinsa ya wuce, yana shiga ya zare Jiƙaƙkun kayan jikinsa da suka jiƙe sosai kana ya fito yaci abinci ya sake kwanciya, Washegari gari... Misalin goman safe ya shiga buɗe idonsa a hankali, ba' a firgice kamar jiya ba, bayan haka ga wata cikakkiyar nutsuwa yana jin tana bin ilahirin gangar jikinsa, zaune kawai yayi yana kallar Pop na room ɗin, yanajin kamar yayi loosing wani muhimmin abun da be gudanar ba a cikin safiyar, da yake jin kamar nauyin hakan na neman dannar zuciyarsa, wayar aka kira ake sanar dashi Flight nasu is ready... “Let’s get this over with…” kawai ya faɗi ƙasa ƙasa yana shigewa bathroom, fuskansa kawai ya wanke da ruwan sanyi ya tsaya yana kallar kansa a cikin mirrorn dakin, sai yaga Fuskar sa ta fi jiya nutsuwa kaɗan, a natse ya shirya kansa cikakken uniform ɗinsa. White shirt mai tsabta sai Epaulets a kafaɗansa, Jacket ɗinsa riƙe a hannunsa ɗaya ahankali ya fara taka ƙafafunsa har zuwa Corridor ɗin da ya yi shiru kamar jiya, Ya shiga lift ƙofar ta rufe, Reflection ɗinsa ya bayyana. collar ɗinsa kaɗan ya gyara Kamar yana ƙoƙarin saka mask, har ya sauƙa a Ground floor. Reception ɗin Hilton Miami Airport Blue Lagoon ya fara cika da mutane sosai, mutane nata zirga zirga da dangoginsu. “Good morning, Captain.” Wannan ma'aikaciyar ta jiya ta sake gaida shi, wannan karon kam kai tsaye ya amsa mata da “Morning.” yana ɗan jinjina kansa. Kai tsaye Motar da aka tanadar masa tana jiransa, don haka yana fita compound na hotel ɗin driver ya buɗe masa motar, yana me furta... “Airport, sir.” John ya shiga ba tare da magana ba, kana shima ya shige ya soma driving John suka bar harabar hotel ɗin a baya. Titunan Miami suna cike da motsin safiyar ranar. cikin ƙanƙanin lokaci se ga gine-ginen airport suka fara bayyana a nesa kaɗan dasu, haka har suka iso dab jirage suna ta sauka da tashi abinsu, Motar ne ta tsaya driver ɗin ya ɗan saci kallonsa don ba ƙaramin cika ido bane da John ɗin, kafin ya iya furta.... “We’re here, Captain.” yayi maganar yana buɗe ma John ƙofar motar ya fito, wata sassanyan iska ta bugi fuskar sa ya ɗaga kai a hankali ya kalla samaniya kafin ya dawo da kallonsa ga filin jirgin, Miami International Airport na wani ɗan lokaci…kafin ya soma tafiya yana jin kamar ƙafafunsa sun yi masa nauyi. Direcly cikin Miami International Airport ya wuce, inda wurin ke cike da motsin crew lounge ɗin su, wasu na shan coffee. Wasu na duba schedules, wasu kuma na dariya a hankali,yayin da wasu ke sabgoginsu, kai da ganinsu komai na tafiya musu yacce suke so, ahankali ya shigo cikin wurin, nan take idanu da dama suka ɗan karkata zuwa gare shi. Ba wai don saboda sabon abu ba ne a gare shi, A ahhh sai don saboda yadda ya shigo ɗin,tafiyarsa a hankali amma cike da nauyi, Fuskarsa a tsaye babu walwala sosai kuma ba a ɗaure take can ba.... “Captain John!” Ɗaya daga cikin cabin crew Mary ta taso da murmushinta tana me furta. “Good morning, sir!” Ta zo kusa da shi cikin girmamawa shi kuwa John kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa itama yana amsa mata da. “Morning.” ɗin kawai cikin murya mai sanyi, ba tsauri amma ba kamar yadda ya saba ba. Ganin hakan suma sauran crew ɗin suka zo kusa suna miƙa tasu gaisuwar. “Morning, Captain!” “Glad you made it, sir.” Kowa na ƙoƙarin nuna girmamawa da annuri ɗauke saman fuskokinsu, ɗaya daga cikin crew ɗin da ba nasu bane radawa na kusa dashi... “he looks different.” ƙasa ƙasa shima ɗayan ya furta... “Yeah… like he didn’t sleep.” daga haka yayi gum da bakinsa kamar an ɗinke da zare, shi kuwa John ajje jakarsa a gefe ɗaya yayi, tare da cire safar hannunsa a hankali, Idonsa yana sake zagaya wajen sosai tamkar me nemar wani abu, First Officer (mataimakinsa) ya matso kusa tare da ambatar “Captain.” cikin muryan nutsuwa ya sake cewa. “Everything okay?” Idonsa kawai John ya ɗan lumshe kana ya ce “we fly today.” ɗan kallonshi first Officer nashi yayi yana jinjina kai yace. “Yeah… we do.” shi kansa ya fahimci cewan wannan Captain ɗin na yau ba na jiya bane, Mary ce ta sake magana cike da ladab ta sake cewa, “Sir, briefing in 10 minutes.” kansa kawai ya jinjina mata yana cewa. “I’ll be there.” tare da ɗaukar box nashi ya fara tafiya zuwa briefing room. Crew ɗin da suke tsaye suka biyo shi da idanu kawai, duk cikinsu kuma babu wanda ya sake furta uffan har zuwa lokacin, sai zuwa can ahankali yace. “Something’s off.” yaci gaba da tafiya sauran crew naci gaba da mara masa baya kowannensu shirye cikin uniform ɗinsa a tsaf… lokacin da suke isa ƙofar briefing room ɗin,suka tsaya yakai hannunsa a natse kan handle, A hankali ya buɗe ƙofar cockpit na jirgin, kai tsaye switchet, screens… controls komai na a shirye, Kafin ahankali John ya zauna a kujerarsa yana daidaita belt ɗinsa…hannunsa ya taɓa controls na ɗan lokaci, First Officer ya zauna a gefensa yana ambatar. “Pre-flight checklist, Captain?” A hankali John ke kallon gabansa, yana kallar yadda screens ke nuna masa komai normal daidai, A tausashe ya ce. “Go ahead.” Ya faɗa a hankali Checklist ta fara. “Battery?” “On.” “Fuel?” “Checked.” “Instruments?” Sai…John ya tsaya Idonsa na maƙale akan screen, cike da kwarewa yake gudanar da komai, gefensa, co-pilot yana shirye. “Let’s make this a smooth one… Lagos awaits.” “Copy that, Captain. All systems checked. We’re good to go.” “Tower, this is Flight JX-217, ready for departure Lagos.” “Flight JX-217, cleared for takeoff. Runway 27. Safe flight to Lagos.”John ya ɗan murmusa yana kama controls da ƙarfi amma cikin Jirgin ya tare da furta “Thrust set.” Engines suka fara karar tashi suna cika iska. Ahankali jirgin ya fara landing na tashi a sannu a sannu John ya ɗaga hancin jirgin a hankali… ya tashi daga ƙasa zuwa sama, “Positive climb.” co-pilot ya fadi. “Gear up.” John ya amsa, Jirgin na hawa sama cikin nutsuwa, yana barin ƙasar United States a baya. A hankali John ya daidaita jirgin akan hanyarsa na zuwa Nigeria, John naci gaba da kallon gabansa, “Long journey ahead… but we’ll get them there safe.” Fasinjoji kuwa baki ɗayansu suna cikin kwanciyar hankali, wasu suna barci, wasu suna kallon sama ta taga wasu na ɗan zarya zuwa cin abincin ne toilet ne,sauran ma'aikata naci gaba da kula dasu har suka kawo Ƙasar NIGERIA... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 6 Paid book Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ ꨄ Bayan doguwar tafiya a cikin sararin samaniya, jirgin JX-217 yana ci gaba da sauka a hankali yana kusantar Lagos. A cikin cockpit, Captain John yana zaune cikin cikakken nutsuwa, hannunsa a kan controls, Ahankali Co-pilot nashi yace. “Captain, we’re approaching Lagos airspace.” a tsanake John ya furta. “Alright… let’s bring her down nice and smooth.” ga sadarwa ta ƙasar Lagos ɗin na kururuwar furta... “Lagos Tower, this is Flight JX-217, requesting permission to land.” Lagos Tower....“Flight JX-217, you are cleared to land. Runway 18L. Wind calm. Welcome.”Ƙaramin murmushi John yayi wanda ya bayyana har a kan fuskarsa. “Copy that… cleared to land.” a hankali Jirgin ya soma sauƙa a hankali, yana ratsa gajimare masu laushi, hasken birnin Lagos yana kyalli a ƙasa. Co-pilot ne ya furta, “Speed stable… glide path good.” Ahankali John ya furta “Perfect… keep it steady.” ahankali jirgin ya taɓa runway. “Touchdown!”A natse John ya naɗa tare da amsawa da “Reverse thrust.” Engines suka rage ƙarfi, jirgin yana rage gudu cikin kwanciyar hankali. Jirgin ya juya daga runway zuwa parking bay. “Flight JX-217, welcome to Nigeria.” John ya naɗa tare da amsawa da “Thank you. Safe landing confirmed.” A bayan jirgin kuwa tuni fasinjoji suka fara tafa hannuwansu cike da farin ciki, wasu suna murmushi, wasu suna jin daɗin saukar lafiya. John ya ɗan jingina bayansa da jikin kujerarsa, yana sauƙe wani numfashi cike da nutsuwa, a bayyane yana me furta “Thanks Jesus....domin sauƙarsu lafiya cikin tsari da farin cikin da shi kansa yake a cikinsa. Bayan jirgin JX-217 ya tsaya a parking bay, ƙofar jirgi ta buɗe a hankali… Iskar Lagos mai ɗumi ta fara kaɗawa zuwa cikin jirgin. Hasken rana yana bugawa jikin jirgin, yana ba komai wani irin kyalli mai kyau. A waje ma’aikatan filin jirgi suna tsaye cikin tsari, wasu cikin uniform mai tsafta wasu da murmushi a fuskokinsu. Ahankali Captain John da shi ne kusan fitowar karshe ya fito daga cockpit, yana tafiya cikin kwanciyar hankali, yana kallon yadda komai ke tafiya cikin tsari, wani kyakkyawan murmushi ne ya bayyana samar fuskansa me kyau, tare da ambatar. “This… this is a good landing.” haka passinger's suka ci gaba da fita, wasu na ɗaukar kaya, wasu na yin hotuna, yayinda wasu ke furta Alhamdulillah, cikin yaruka maban banta, Ingilishi, Hausa, Yoruba… duk suna haɗuwa cikin farin ciki... Ga wasu ƙananun ma'aikata masu kula da Airport nata furta musu kalmar... “Welcome! Welcome to Nigeria!” tsaiwa kawai John yayi yana kallon yadda mutane ke cikin farin ciki… yana nan tsaye se ga motar airport ɗin ta ƙaraso har inda yake don kaishi gida, Kai tsaye ya shige motar cikin nutsuwa motar ta fara tafiya, ga hasken titi yana shigowa ta cikin gilashin motan yana ɗan haskaka fuskarsa, yana jingine da jikin kujerar motar, idanunsa lumshe amma gaba ɗaya ita ke wayo a cikin zuciya da ruhinsa gaba ɗaya, be taɓa jin ya ƙaunaci wani abu duk girmansa karon farko irin yasmine ba, sunanta kaɗai idan ya tuna yakan sa yaji zuciyarsa ta ɗan buga, daga lafen da yake a jikin kujerar yake tuno yadda ta tsaya gabansa… yadda idanunta suka kalle shi cikin yanayi na ɓacin ran da bai taɓa mantawa ba, maganganun da ƙaramin bakinta ya dinga yanko masa masu zafi, ƙirjinsa yaji ya sake bugawa shin ta ina ma ya kamaci ace ya fara nemar trouble ɗin nashi nema?, wani munafikin numfashinsa ya fesar, tuno yadda ya kusanto ta, yadda lokaci guda ya tsaya gabanta, kafin bakinta da take masa masifan ya ɗauki hankalinsa har zuwa lokacin da karon farko yaji sha'awan yin kissing wata mace a karonsa na farko, tuno yanayin data shiga yayi na tsoro me girman daya bayyana akan fuskarta, yadda shi kuma a nashi ɓangaren yaji kamar duniyar ce baki ɗaya ta tsaya mishi, da kyau ya wani matse hannunsa a jikin kujeran, yana jin wani abu na ƙoƙarin ɓallo masa, Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarsa ba dariya ba ce, amma wani abu ne mai cike da nisa da ƙauna ga zuciyar data faɗa tarkonsu, sai kuma nauyin hakan ya biyo baya,domin ya san komai bai gama bayyana ba, yana cikin wannan tunanin har besan lokacin da motar ta tsaya gaban mension nasu ba, se da yaji maganar driver na faɗin “Sir, we’re here.” kana ya iya buɗe lumsassun idanunsa a hankali, yana dawowa daga duniyar tunani zuwa ta gaskiya. Direcly ya fita a motan yana nufar katon get na gidansu, dake anan gida lokacin yammaci ne kuma weekend ce don haka gaba ɗaya ahalin suna zazzaune basu jimawa daga dawowa daga couch ba, don haka da katafanin family ɗin nasu ya fara cin karo, ciki kuwa harda kakansa PATRIARCH, Madam Victoria Osteen ce ta fara ganin tsaiwar yaron nata a kansu... “My Love…” Madam Victoria Osteen ta ƙira sunanshi cike da wani irin zumudin da aduk lokacin da zata ganshi take shiga, ko kafin kowa yayi wani motsi tuni har ta isa gabansa ta rungume shi da ƙarfi, irin rungumar da ke tabbatar da cewa tabbas mahaifiyar nashi tayi kewar yaron nata kwarai da gaske, Nan sauran family ɗin ma suka taso, fuskokinsu cike da annuri da farin cikin ganinsa lafiya, don duk hankalinsu a tashe yake, duk da cewan sun ga komai lafiya, amma hankali da nutsuwansu baya tare dasu, yana ga John ɗin ne kawai, shi kuwa John cike da ƙaunar family ɗin ya tsaya a tsakiyarsu, yana jin ɗumin tarɓar daya samu daga su duk da kasancewar har lokacin tunaninta na nan maƙale a ƙasan zuciyarsa daram, har yanzun kuma yana jin dumin rungumar mahaifiyarsa a jikinsa. Kafin ya ɗan ja baya kaɗan yana kallar yadda har yanzun hannunsa ke riƙe cikin nata, tana kallon fuskarsa da kulawa, kafin cikin muryan nuna ƙauna ga yaron nata take tambayar... “Are you okay, John?” tayi tambayar cikin damuwa, kansa kawai ya gyaɗa mata ahankali yana bata amsa da. “I’m okay, Mother… I’m fine.” Deepika ce ta iso da gudunta ta faɗa jikinsa tana basa kyakkyawar rumgumar da haka kawai ya bata ran John, don shi sam ba ma'abocin son ire iren waɗan nan tarin tarkacen nasu yake ba, wata kafuwar hararan gefen ido Madame Victoria Osteen ta mata a fakaice, X-Eashika ma a fakaice ta harara Deepikan wacce mahaifinsa Mr JEF DEEFER PATRIARCH ke son John ɗin ya aura, itama yar ƙanin Papa'n ce yayainda Deepika ta kasance yar gidan ƙanwarsa Oueen Ara, da murmushi me kyau mahaifinsa ya matsa kusa dashi, fuskar sa cike da tsananin ƙaunar yaron nasa shima yake tambayar... “ Joseph we heard something about the flight… they said there was a problem. What really happened?” se gaba ɗaya parlourn nasu yayi ɗan yi shiru na wani lokaci, kafin a natse John ya sauƙe wani numfashi a hankali, yana kau da idonsa kaɗan yana kuma ja baya ga kowa. “It was serious… but we handled it.” “Serious?” X-Eashika tayi saurin taryan numfashinsa. “We’ve been worried sick!” Mahaifiyarsa tayi maganar tana sake riƙe hannunsa. “We couldn’t even sleep… we kept thinking about you.” ta sake faɗi tana kallar John ɗin kai tsaye. Wani laushi na ratsa zuciyarta da ALLAH ya kuɓutar mata da yaron nata mafi soyuwa a cikin duniyarta gaba ɗaya, “I’m here now,” ya faɗa a hankali. “I’m safe.” daga haka suka zauna tare da shi a parlourn suka ci gaba da jero masa tambayoyi ɗaya bayan ɗaya... “What exactly went wrong?” “Were you scared?” “What about the crew?” “How did you manage it?” Gaba ɗaya sun fara cika kansa amma haka yake amsa su dole cikin nutsuwa, sedai yana rage wasu wasu bayanan yayin da suke maganar, yana jikin kakansa Patriarch daya gudu can saboda da Mommah nashi da take wani maƙale masa, daga nan yaci gaba da jinsu yayi shiru yana tafiya ma tunanin Babyn Robar shi, jin shirunsa yayi yawa ne, gashi yana ga masa magana ya saka Mommah nashi ɗan jan ƙafarsa tana me furta... “Joseph … you seem distant. Is something bothering you?” ɗan murmushi kawai yayi, amma murmushin ba cikakke ba ne. Se kawai ya amsa mata da “I’m just tired, Mom… it’s been a long trip.” kallonsa kawai na ɗan lokaci tayi kamar wacce keson son fahimtar wani abu… amma ta barshi. Wanda ahankali John ya miƙe yana riƙe da p-carp nashi a hannu ya ce. “I think I need some rest,” ya faɗa cikin taushin murya wanda Mother tayi saurin gyaɗa masa kanta tana me furta. “Of course… you need it.” daga haka ya juya ya nufi hanyar ɗakinsa, takunsa a hankali kamar wanda jikinsa yake jin nauyin gajiya da tunani a lokaci guda. Koda ya isa ƙofar ɗakin ahankali ya buɗe ya shige, komai nashi na nan a killace, room ɗin yayi shiru, jacket ɗinsa ya cire kai tsaye ya jefa a kan kujera. Ya zauna a gefen gadonsa, ya ɗan sunkuyar da kansa idanunta na masa gezau, A hankali ya ɗaga kansa ya jingina da bango… idanunsa suna ɗan rufen har lokacin, maganar ta _Ta duk kan alamu ma kai arzikin muslunci ma baka da...._ nan take bugun zuciyarsa ya sake tsananta tuna yadda ta kalle shi… yadda idanuwanta suka cika da wani abu da ya kasa fassara, _Kar ka yadda ko a rashin sani ne, wannan ƙazamin hannun naka ya sake yinƙurin taɓa koda hijjabin jiki nane balle hannuwana Malam..._ Gaba ɗaya neman birkicewa ƙwaƙwalwan kansa ke yi, Hannunsa biyu yakai yana riƙe kansa ya ɗan motsasu a hankali...yana jin yadda kan ke nemar dirar masa da ciwon kan nan take, sannu a hankali ya buɗe idanunsa yana kallon samar Pop… Ahankali ya kama sarƙan Cross ɗin dake maƙale a wuyansa yana ɗan jujjuyawa cike da nauyi, yana jin yadda ciwo ciwon kan nan ke ta kokarin ganin ya taso mishi. Abinci da babu jimawa aka shigo mishi da shi ya kalla, sedai baya jin ci, don shi abknci bai dameshi ba sam sam, rabon dayaci abinci tun kafin ya shiga jirgi, shima kuma coffee. kawai ne yasha. Sake lafewa a kan gadon daya gama amsar amanarsa yayi yana lumshe rinannun idanuwanshi da suka kaɗa sosai a tashin farko. Wani abu me kama da tsananin SO ko ƘAUNA yake ji lokaci ɗaya akan gal ɗin, yanayin dake nemar sake sashi birkicewa nan take, wasu surutai ya fara yana wani lullumshe idonsa har barcin yayi nasarar daukansa na dab da magriba. Ba sosai can yayi baccin ba, don haka lokacin daya farka ahankali ya shiga buɗe sleeping eyes nashi da sukayi masa nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da yake gani acikin su ne ya sashi maida idanun nasa ya rufe ruf, sosai yaji kansa na wani irin bala'in sara masa, dan haka yakejin gaba ɗaya jikinsa yayi weak.... Hannu yasa yana ɗan dafe kansa dake yi masa ciwo kaman zai rabe biyu,still rinannun idanunsa dake a lumshe ya buɗe tare da sauƙe ganinsa akan gadonsa. Kafin kuma ahankali ya ɗan motsa jikinsa tare da soma ƙoƙarin ɗaga kansa da yakejin yayi masa nauyi sosai, wanda kuma yasan hakan bai rasa na saba da tarin tunaninkanta daya ringa yi ba, jingina bayansa kawai da jikin fuskar gadon yayi, tare da sakin ajiyar zuciya yana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin ɗakinsa. Shower ya sakamar kansa tare da tokare hannuwansa da jikin sink, haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma kansa. jin kamar numfashinsa na ƙoƙarin ɗaukewa ne ya sanya shi janye jikinsa da ƙyar. idanunsa jajur alamar har yanzun komai na nan daram a cikin kansa, da bathrube ya fito a jikinsa walking slowly kuma yake tafiya fuskar nan babu alamar annuri ko guda. Kai tsaye kayan shan iska ya saka ya yi waya aka kawo masa dinner nashi, wanda Mother ce ta kawo masa da kanta, amma itama ganin yadda yanayinsa yake ya sakata ficewa salin alin. A natse yayi peeding kansa, bayan ya kammala yaja ɗan madaidaicin plask tare da tsiyanyar coffee a mug , Ahankali yake ɗan sipping coffee ɗin dake left hand nashi, ɗayan kuma yana yana latsa wayarsa daya gaba ɗaya ya gama maida hankali da tunaninsa kanta, yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen wayar kaɗai ya isa baka tabbacin abu mai matukar muhimmanci ne yake yi. Dan sai loƙaci bayan loƙaci ya kan ɗan ɗauka mug na Coffee ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajje mug ɗin, hankalinsa kacokam na kan abinda yake yin ɗin da wayan. Cikin deep down ɗin da yake amsa daga cikin zuciyarsa ya ɗan lumshe idonsa, bayan ya kammala shan coffeen ɗin kuma ahankali ya miƙe tsaye yana nufar hanyar fita, duka ahalin nasu na Zazzaune a parlourn gidan ya musu gaisuwan jam'i a takaice yana nufar hanyar fita, kafin muryan Mommah nashi ya dakatar dashi cak daga fitan da yake kokarin yi wajen fara nemar yasmine....... _Hhhh nace to ya kukaji salon rubutun littafin DUHU na DUKAN duhu ne?, Salon na musamman ne, kamar yadda tafiyar ma take ta daban ce, haka ma littafin DUHU na DUKAN duhu na mai rabo ne, domin bamu sa hannu bama a komai, wasan dai yanzun ne zai fara🤸🤸🤸🤸......_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 7 Paid book Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ ꨄ “Joseph!!!....“ ta ƙirayi sunan shi kai tsaye tana tashi daga inda take zaune ta iso har inda yake tsaye can, kafin ya juyo a hankali cike da ɓoyayyiyar damuwar dake lulluɓe da fuskarsa, ɗan kallonsa ta shiga da idanunta masu cike da alamar tambaya, ta sake matsowa kusa da shi kaɗan cikin harshen Ingilishi take sake jefa masa tambayar... “Ina zaka je a wannan lokacin? bayan ko gama hutawa ba kayi ba, bare kuma mu zauna dakai?” ta tambaya cikin ɗan nuna damuwa a muryarta. “Ka san lokaci yayi… dare yayi sosai John.” ta sake faɗi tana ƙoƙarin kamo hannunsa,kansa ya ɗan kau da yana ƙoƙarin ɓoye abin da ke ransa, cikin silent voice nashi ya ce... “Zan ɗan fita ne kawai Mother, Ina da buƙatan nasha iska kaɗan.” ya mayar mata shi ma cikin harshen nasara. Bata yarda ma sema sake tsayawa da tayi tana kallonsa na wasu daƙiƙu… kamar tana jin akwai wani abu fiye da hakan ne kawai dai ya ɓoye mata ne, kafinnta sake maimaita kalmar “Iska?” ta sake ɗorawa da cewa. “A irin wannan lokacin kuma?” wani ɗan shiru ne kawai ya ratsa tsakaninsu, tana sake matsawa kusa da shi sosai, ta ɗora hannu a kafaɗarsa ta ce... “Love!, me ke damunka?” ɗan lumshe ido kawai John yayi, zuciyarsa na masa nauyi sosai, shi bai san yadda zai bayyana mata ba domin shi bai san kome zai ce mata ba… ba ta san Yasmine ba… ba ta san dalilin da yasa zuciyarsa ke neman fita cikin daren ma ba, “Babu komai, Mom…” ya faɗa a hankali amma muryarsa ta nuna akwai ɓoyayyen abu. Madame Victoria ta ɗan girgiza kanta kaɗan, kafin ta ce “Ni na haife ka John… na san lokacin da kake ɓoye abu, don gaka meke faruwa da kai?....” Wani ɗan murmushin ƙarfin hali kawai yayi idanunsa na sake bayyana damuwar da yake a ciki, kafin a takaice ya ce. “Please… kawai ki barni na fita Mommah zan dawo da wuri I promise!.” duk da haka bata yarda ta sake tare masa hanya, kallonta kawai yayi yana rasa me kuma zai ce mata, shi fa wannan takura da rashin son fitan da ba'a son aga yana yi akai akai kan takura rayuwansa suke, wani numfashi ya fesar Zuciyarsa na faɗa masa kawai yace mata... _Wajen Hausa gal ɗin sa zai je, saboda yana son ya sake kissing nata irin na ranar?...._ ko kuma cewa ze mata _Ya sama wacce yake so?..._ yana tsaka da wannan tunanin kuma yaga ta bashi hanya tamkar ta karanto zuciyarsa bata son ya furta mata kalaman ne don haka ta bashi hanyar, da murmushin yaƙen dolen data ƙaƙalo a fuskanta ta ce... “Before you go, let’s pray“ ɗan sunkuyar da kansa kawai John yayi cikin yanayin girmamawa, Ita kuma ta wani rufe idanuwanta a hankali, tana fara masa adda’a cikin nutsuwa “Heavenly Father, I commit my son into Your hands as he goes out today. Please guide his steps and order his path. Protect him from every danger and evil. Surround him with Your grace and bring him back home safely. In Jesus’ name, Amen.” Bayan ta gama ta gama masa adda'an ta buɗe idanuwanta tana murmushi mai cike da ƙauna ta sake ce dashi. “Go, my son… God is with you.” John ya kalli mahaifiyarsa da girmamawa zuciyarsa cike da kwanciyar hankali dajin daɗin adda'an data masa ya ce “Thank you, Mom.” ya juya, har ze fita ta sace dashi. “Go in peace, God is with you.” “I will, Mommh…” daga haka ya buɗe ƙofar a hankali ya fita, Mecheal na ganin fitowarsa wanda shi ne dawwamammen driver nashi in yana gari yayi hanzarin nufar wata Black Bentley ya buɗe masa. A tsanake John ya shiga motan a hankali, driver ɗinsa ya kunna motar tare da tambayar.... “Where to, Boss?” ɗan shiru John yayi don shi kansa be san inda suka nufa ɗin ba takamaimai, sema shiru kawai da yayi yana kallon titi ta cikin gilashin motar, zuciyarsa cike da rashin tabbas ya ce da Mecheal ɗin kawai.. “Just… drive,” hakan kuwa akayi Mecheal tafiya kawai yake yi, shi kuma idonsa na waje yana kallar hasken streetline, da mutanen dake tai da komo wasu a ƙafa, wasu abin hawa motace ,keke ne, mashin ne, wasu shaguna suke rufewa bayan dogon yini. duk daga inda John ke zaune lafe a bayan motar yake kallar komai, hannunsa riƙe da wayansa amma kuma babu abinda yake da ita, har lokacin kansa na waje yana kallon kowanne fuska da suke wucewa, kamar yana fatan ganin wacce yake nema ne, haka motarsu ta dinga yawo daga titi zuwa titi, daga unguwa zuwa wata unguwar amma babu Yasmine babu alamarta, lokacin har takwas na dare ya gota, don haka driver ɗin ya ɗan leƙa ta madubi yana cewa... “Boss… mun riga mun zagaya kusan ko’ina a wannan yankin fa…” ɗan risinar da idonsa kawai John yayi, yana jin wani irin gajiya a cikin zuciyarsa, yana jin kamar ya sare amma kuma cikin yaƙini ya sake ce dashi “Keep driving…” haka har suka isa wani titi mai ɗan shiru da hasken fitila ɗaya kawai ke kyalli. Se wasu zirarin mutane kaɗan kawai dake wucewa. Ahankali motar ta ratsa titin, John ya sake jingina da kujeran motar yayi shiru idanunsa har sun fara nuna gajiya… har yana jin kamar ya yardan ma zuciyarsa cewa watakila ba zai same ta ba a daren nan. Amma wani ɓangaren na daga cikin zuciyar ma sake ƙarfafashi akan kada ya sare, domin dama shi can ba mai sarewan bane. Shi kuwa Mecheal da hannunsa suna soma gajiya da driving ɗin ne ya ɗan sake kallarsa a ɗan tsorace yace... “Sir… should we head back home?” Yayi maganar yana ɗan rage gudun motar, amma shiru John bai bashi amsa ba sai ma sake maida kansa woje da yayi amma ba sosai yake duba yanayin wajen ba, don shi kansa ya fara gajiyan, se kawai taurin zuciya irin nashi, motar nasu har ta ɗan gitta wani gefen titi… inda wata yarinya ke tsaye da dogon hijjaba har ƙasa a jijinta,inda tun da ya fito se yanzun yaga me kalan wannan abin, kuma sak irin na Trouble nashi Ash.. don haka ya dakatar da Mecheal yana buɗe motar ya fita hanzarce amma yana fitan abin mamaki ya nema yarinyar ya rasa ta ɓace masa, daga can inda yasmine ta ke kuwa ta ɗago kanta a hankali tana waiwayar bayanta, Idanunta cike da wani irin yanayin da ita kanta taji kamar ita ma tana jin cewa wani abu ya wuce kusa da ita me muhimmancin da bata san ko miye shi ba, don haka yar tsuka kawai taja tana faɗawa motar ƙawarta dake jiranta... Shi kuwa John wani kalan lumshe idonsa yayi yana jin kamar tabbas ita ne ya gani, gangar jikinsa na bashi cikakken tabbaci akan hakan,amma hanya ta raba su, duk da cewa sun yi kusa da juna fiye da yadda suka taɓa tunani ba tare da sanin junan su ba. Haka motar John ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, tamkar wanda aka zabura ya furta... “Stop the car…” wanda ya saka driver ɗin ya taka birki yana ambatar “Boss What happen?” Riƙe kansa kawai John yayi yana jin kamar ze rabe masa guda biyu, da ƙyar ya iya ce dashi. “I don’t know… just—wait.” Shiru ne kawai ya mamaye motar, kafin John ya buɗe ƙofar motar ya fito. Kai tsaye sassanyar iskan daren ta bugi fuskarsa, tsai kawai yayi a gefen titin yana kallon hanyoyi daban daban. Zuciyarsa naci gaba dan bugawa kamar tana ƙoƙarin gaya masa wani abu amma bai gane ba, ya juya bayansa kenan motar data fito daga wancan titin ta wuce a guje tamkar walƙiya, motar kawai ya dawo ya zaune tare da furta “Let’s go…” kawai motar taci gaba da tafiya. Sake kwanciya John yayi a jikin kujeran motar ya lumshe idonsa, yana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba. Haka suka koma gida bayan sun jima a wurin da hasalin haɗuwarsu na farko ya fara, hakan ma don ƙiran da Papa'nsa ya dinga masa ne tare da Madame Victoria dole suka dawo gidan ba don yaso ba, daren ranar nan haka John ya gansa be runtsa ba, saboda zuciyarsa ita kawai take muradi, idanunsa cike suke da ɗaukin sake ganinta,haka zuciyar John taƙi hutawa a daren ranar, a cikin ransa yana ayyana ko da bai san sunanta ba yana son sake ganin wannan kyakkyawar fuskar, Saboda fuskar ta ƙi barin zuciyarsa.... ★... A washe garin ranar se wajajen sha ɗaya ya fito daga ɓangarensa, yana fitowa Mommah nashi kallo ɗaya ta amsa tasan bai yi bacci ba daren jiya, don haka ta ƙira ye shi kai tsaye ta zaunar dashi a gefenta, tana shafa fuskarsa da se faman kawar da ita yake. “My love what happens???, me ya sa baka yi bacci ba jiya gaya nan ina kallon hakan a idanunka!” hannunta ya ɗauke daga fuskan yana matsawa jikin Grandfather nashi Patriarch. A tare yaci abinci da kakan nasa wanda kusan shi yake bashi da kan sa ma, X-Eashika ta matsa kusa dashi tana ɗora kanta saman kafaɗar John ɗin, Madame Victoria ta daka tsawa tana cewa ta ƙyale shi, ko bata ga baya da lafiya bane, Deepika ce ta faɗa fuska tana isa ga John tana ƙoƙarin kama hannunsa ya mata tsawa yana miƙewa a fusace fuuuu ya fita daga parlourn, inda gaba ɗaya suka bishi da kallo cike da zullumin ko me ke damunsa tsakanin jiya da yau ɗin?, amma babu wanda ya tanka sema kowa miƙewa da suka fara ɗaya bayan ɗaya suna barin wurin, ya rage daga Papa se Patriarch.. John kuwa yana fita Mecheal ya taso ya buɗe masa mota, zuciyarsa cike da tsantsar munafincin ko me ke damun Boss ɗin haka?, yau ma zaga garin suka yi, inda sake komawarsu wurin kai tsaye ya bama Mecheal ɗin hasken kodai Hausa gal ɗin nan John ɗin ke nema yasa su cinye ta ɗanya?, kai tsaye ya labe a bayan mota ya ƙira Madame Victoria yake sanar da ita duk abinda ya faru, tin daga fitarsu na jiya har zuwa yanzun har dama ƙarin gishiri a zancen nasa, kai tsaye hankalin Madame Victoria ya tashi amma kuma sanin halin Joseph ɗin ya sa bata yi yunƙurin komai a lokacin ba, har suka sake dawowa gida. Kai tsaye ya haye sama cike da zafin zuciyar rashin nasarar samunta da yau ma basu yi ba, tun da ya shige kuma babu wanda yayi gigin zuwa inda yake har ita kanta Victoria ɗin, se can ta shiga kai miahi dinner da yaki saƙƙowa yayi, don bata taɓa barin su Deepika ko X-Eashika wani shigar masa ɗaki,gudun ma kar wata ta rinjayi ra'ayinsa a cikinsu. Ahankali ta zauna a gefen gadonsa da yake kwance da kayan shan iska ta ɗora hannunta saman goshinsa, tare da masa adda'a irin tasu kana cikin tausasa murya tace dashi, in dai akan maganar wannan Hausa gal ɗin ce ya bar maganar a hannunta, duk inda take a faɗin lagos se ta saka an nemo mata ita, ita da kanta ta saka an hukun tata ba sai ya wahal da kansa ba, wanda ita tayi hakan ne da biyu don bata son taga kowacce mace ta rabe shi bayan ita, kamar yadda bata son taga shi ma ya raɓa ko wacce macece. Wani duba ya mata jin wai zata sa a hukuntata, hukuncin me to?, yayi maganar da zuciyar yana kawar da zancen hakan, duk da yayi mamakin yadda bata manta zancen ba, kuma ma har tasan itan yake nema kai tsaye, da kyar ya yarda yaci abinda ƙarfe biyar na cika ya sake fita a gidan, zuciyarsa babu daɗi daga shi se wani kakkauran wando na jeans iya gwiwwarsa, se guntuwar shirt mara hannu, se ƙatotuwar sarƙar Cross ɗin sa daya sanja me hoton kwandalar dake jikinsa da me hoton tauraro, ko gashin kan yau sama sama ya gyara sa fuskar nan a turɓune murtik kamar hadarin daya ƙunshi ruwa yaki ya fashe, directly wani lafiyayyen mall ya nufa saboda duk kayan kwalam nasa ya karar dasu,kuma Mommah me bi bata kula ba, don haka zuciyarsa kawai ta bashi shawaran ƙara ya saya kawai, don yadda kwana biyun nan ba wani cin abincin kirki yaje ba se dangin su biscuit chocolote ɗin yasa shi bin umarnin zuciyar, suka yada zango a shagon suka fara siyayyar Mecheal na tura masa basket na kayansa da yaje jida kamar wanda ke shirin buɗe ɗan ƙaramin shago, daga ƙarshe ma Mecheal ya bari yaci gaba da zaɓa masa manyan biscuit ɗin masu lafiya da tsada, samun kansa yayi da fara zaga mall ɗin kamar me neman wani abu, har idonsa ya sauƙa akan best chocolate nashi ta Ferrero Rocher, wacce tun da suka shigo ita yake ta nema, ya miƙa hannunsa kenan da niyar ɗauka,wani hannun ma daban ya kawo da niyar ɗauka,hakan yasa kusan lokaci guda hannunsa ya ɗoru akan chocolate ɗin har yatsun hannun nasu na ɗan haɗuwa, ɗagowa yayi da nufin ganin waye kai tsaye idanunsu suka sarƙe cikin na juna, Cak numfashin John ya tsaya, yana tunanin anya kuwa ita ce?, ba gizo idonsa ke masa ba, anya kuwa ita ce yarinyar da akan ya dinga yawo cikin dare yana zaga anguwannin da suka yi kusa da inda suka haɗu?... Ita kuwa yasmine da kai tsaye bata gane shi ba ne ta ɗan kallesa kawai tare da cewa... “Ohhh… I’m sorry,” ta faɗa a hankali tana janye hannunta daga kan chocolote in, shi kuwa John gaza ko wanne irin motsi yayi jin daddaɗar muryanta ta ratsa har tsakar kansa, ko yanzun ma tana sanye da niƙab nata,wanda ta dage shi ne don ganin wanda ya rigata ɗaukar cutie chocolate nata, John da yake kallonta kamar wanda ya samu abin da ya rasa wani faffaɗan murmushin da kai tsaye baka isa gani daga fuskarsa cikin sauƙi ba na kufce masa a bazatan ganintan da yayi, godiya yama Mommah a cikin ransa don yasan ƙarfin adda'an data mishi ce yasa har ya haɗu da ita cikin sauƙi haka... “My Trouble…” ya faɗa a hankali yana ci gaba da kallon ta wanda hakan ya saka yasmine ɗan ɗage gira ɗaya “Excuse me zan iya ɗauka?” tayi maganar dana sake kai hannunta kan chocolote ɗin da yayi hanzarin ɗaukewa, idanunsa naci gaba da kallonta kai tsaye. “Babyn roba…” ya sake faɗa da murya mai laushi kamar yana gwada yadda kalmar ke fita ne a bakinsa. Cak ta dagata domin wannan karon kai tsaye tasan da ita yake kenan, don haka da alamar mamaki tana haɗe ranta ta ce... “Do I know you?” ta tambaya, wanda ya saka John saurin zagawa yana girgiza mata kai kaɗan, murmushinsa har lokacin bai gushe ba yace “Not yet…” ya faɗa tare da sake matsota ya sake furta. “Amma na jima ina nemanki, har daren jiya ma” Kai tsaye kalmarsa ta tsaya mata a zuciyarta ta wai ya jima yana nemanta, kafin ta kalleshi kamar tana ƙoƙarin tuna wani abu tace... “Nie kuma?, nemana fa really?” ta yi maganar mamakinsa har lokacin bai bar ran ta ba. Taku biyu ya sake yi gabanta har yana ƙoƙarin haɗe tazarar dake tsakaninsu tayi hanzarin yin baya, ne damu ba sema kai tsaye da yace mata. “Last night… I was out there,” ya nuna kansa kaɗan. “Trying to find you… I didn’t even know your name.” wani kalan shiru ne ya ratsa wurin kwakwalwarta na son tuno mata ko shi ɗin waye, zuciyarta ce ta ɗan buga kai tsaye ta gane shi kam yanzun, musamman da se a lokacin da masa kallon tsaf, ga wannan shegiyar sarƙar Cross ɗin nasa nan se rito take a jikinsa. “Strange…” ta furta da ɗan ƙarfi tana ja baya fuskarta sanjawa zuwa tsuketa da tayi, tana haɗa duk abubuwan da suka faru a ranar a cikin ranta. “Wait…” ta faɗa a hankali tana sake matsawa da kyau tana kallonsa, kafin a wani kalan fusace tace... “Don’t tell me…” se kuma ta ɗan yi dariya kaɗan amma dariyar ba ta da sauƙi a gare shi, “You’re that guy from last day…?” ɗan murmushi kawai yayi yana harɗe hannuwansa a ƙirji ya ce da ita. “Maybe…” ya faɗa a hankali wanda ya saka yasmine ɗan girgiza kanta, kafin kuma ta warto Ferrero Rocher ɗin daga shelf ɗin da take da ƙarfi kaɗan. “Unbelievable…” ta furta tare da sake kallonsa amma wannan karon idanunta cike suke da ɗan rashin kunya da ƙarfin hali irin na farko. “Toh yanzun ma ka biyo ni har nan ɗin kenan don ka maimaita irin na ranar ko?, tayi maganar da hausa wanda gaba ɗaya be gane me take nufi ba, don ba directly ya iya hausa a cukurkude irin haka ba, kaɗan kaɗan ya iya kawai, amma ta sake ɗaga masa hannu ta dakatar da shi da cewa. “No, no… don’t even start.” kafin ta sake matsawa kusa da dashi ta nuna shi da yatsa tace. “Listen, mister… ban san ko kai waye ba, kuma honestly ban damu ba.” tayi maganar da ihu, wanda ya jayo hankalin mutanen har wasu na ɗan juya suna kallon su kaɗan, amma ita ko kaɗan bata damu ba seka ci gaba da nuna shi da tayi tana ci gaba da faɗin. “Ka dena bin bayana,” ta faɗa kai tsaye. “Because if I catch you doing that again” ta ɗan karkata kai tana kallonsa da ƙanƙanin murmushi mai haɗe da gargadi “ ka sani zan iya sake marin ka a karo na biyu And trust me… I don’t miss.” tun da ta fara maganar John ya tsaya yana kallonta… mamaki da ɗan dariya na haɗuwa a fuskarsa duk lokaci guda. Ta juya zata tafi amma ta sake juyowa da sauri tace “Seriously. Stay away.” Ta fara tafiya cikin ƙarfin hali kamar yadda ta saba daga hakan ta ɓace cikin mutane.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 8 Paid book Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ ♡♡♡♡ ꨄ John tun da ta ɓace a cikin mutanen ya tsaya a wurin kamar wanda aka dasa, idanunsa na bin bayanta har ta ɓace cikin cunkoson mutanen mall ɗin. Wani irin shiru ne ya mamaye shi na wasu daƙiƙu.ya saki wani ɗan ƙaramin dariya mai sanyi. “Still the same…” ya furta a hankali yana girgiza kai. Mecheal da ke tsaye daga nesa yana kallon duk abinda ke faruwa ya matso kusa da shi yana ɗan ɗaga gira. “Boss…?” ya kira shi da yanayin tambaya. Amma John ko kallonsa bai yi ba… har yanzu idanunsa suna kallon inda ta bi kamar yana tsammanin zata sake bayyanane. “Did you see her?” ya tambaya a hankali. Mecheal ya ɗan rikice tare da furta. “Which one, sir?” A hankali John ya juya ya kalleshi… idanunsa cike da wani irin haske da Mecheal bai taɓa gani a cikinsu ba. “My trouble…” ya faɗa kamar wanda yake magana da kansa. Kafin ya ja wani gauran numfashi ya ce… “Find her.” Cak Mecheal ya ƙame tare da buɗe baki kafin yayi kunɗunbalar cewa. “Sir…? Find who exactly?” John ya ɗan yi murmushi, amma murmushin nan na nufin abu ɗaya ne ba zai bar wannan ba. “The girl in hijab!… the one that almost killed me yesterday…” ya faɗa da ɗan sarcasm. Mecheal ya ɗan yi dariya kaɗan. “Sir, Lagos ba ƙaramin gari bane fa…” “Then search it.” John ya katse shi kai tsaye ta hanyar fadin hakan. Kafin wani ɗan shiru ya gitta tsakaninsu, sai kuma ya juya ya fara tafiya zuwa exit ɗin mall ɗin yana cewa… “I want her name… where she lives… everything.” ♡ A ɓangaren Yasmine kuwa… Tana fita daga mall ɗin zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri fiye da yadda ta saba. “What happen…?” ta faɗa a hankali tana dafa ƙirjinta. Ƙawarta Aysher da ke jiranta a mota ta kalleta da mamaki kafin tace. “Yasmine lafiya? Kina ta faman numfashi kamar wacce kika yi gudu.” Motar kawai ta shige tana gyara niƙab ɗinta. “Wani ne kawai…” ta faɗa a takaice. Ƙawarta Aysher ta ɗan yi murmushi mai ɗan raini. “Wani ne… ko wani NE?” ta jaddada kalmar a bayyane. Ɗan hararanta Yasmine ɗin tayi tare da furta. “Please, ki ja mota kawai muje.” Don har zuwa yanzun hoton fuskar John kawai take gani ranar da yayi kissing lips nata a tausashe gaba daya hakan ya ƙi barin zuciyarta. Barin ma wannan munafikin murmushi nasa, Idanunsa, da yadda a yau ɗin kuma ya wani kira ta... “My Trouble…” Se kawai ta tsinta kanta da wani lumshe ido a hankali, kafin ta furta. “Ya Allah…” a bayyane daidai lokacin da suke parkin car nasu a babban get ɗin gidan su... Aysher ɗin bata shiga ba kasancewar magrib ta kawo kai. Don haka ta buɗe motar ta fita tare da ledanta a hannun. Zuciyarta cike da wani irin tunani da bata saba ji ba, ta jefa jakarta a kan kujerar babban parlourn gidan su, ta zauna tana kallon bango kamar wacce aka ɗaure da tunani. “Me wannan mutumin yake nufi da ni ne wai?” Ta faɗa a hankali a kuma bayyane, tana tuna yadda ya tsaya yana kallonta… yadda ya kira ta da suna “Babyn roba” duk da cewa ita kanta ta gargade shi. Wani mugun tsakin da yaja hankalin ƙanwarta Husna ƙanwarta da tun farkon shigowar Yayar tata take kallonta kawai. Ba tare da sanin kalmar zata kwace mata ba ta sake furta... “Wannan mutumin matsala ne… amma me yasa nake tunaninsa haka?” Husna gaza yin shiru tayi har seda ta. “Ambasajon Daddy lafiyanki kuwa tun da kika shigo se surutai kike?” Yi tayi kamar ta fasa ɗan ƙaramin ihu amma tana mazewa tama mike tana barma Husna ɗin dogon hijjaba nata da ledan sayayyar, ta haura sama daga ita se riga da wando Three quiter din dake jikinta pink. Da kallon tausayawa kawai Husna ɗin tabi Yayar nata dashi, don sau da dama irin haka tausayin Yayar nata kamata yake. Tana daf da hawa saman kuma ta dakata cak dan jin muryan mahaifiyarta da tayi na tambayarta yau ma yawon ta sake fita ko?... “Maamah ni ban fita yawo ba Aysher kawai na raka mall...” tayi maganar bakinta a sama tana kara sa hayewarta saman. Kanta kawai Hajiya Khadija ta jijjiga tana ci gaba da ma Yasmine ɗin fatan kintsuwa anan gaba. Tun da kuma ta shige ɓangaren nata babu wanda ya sake ganinta har dare, koda aka fito dinner Ambassador Kabeer ke tambayan Ina Baby?, Husna take sanar dashi ai tun yamma data kulle kanta a ɗaki bata sake fitowa ba, nan ya rufe Maamah da azababben faɗan duk ranar data kashe masa Ambasaja wllh daga ranar zamansu ya ƙare. Wani irin shiru kawai Hajiya Khadija tayi, takaici da dana sanin auren mijin nata take yi. Ya yake son tayi a matsayinta uwa jigo ga rayuwar ƴaƴanta?, shi kenan ita bata da ƴancin yima yaranta faɗa musamman ma dai Yasmine ɗin da take kamar ransa. Tashi kawai a wurin tayi cike da ɓacin ran da yake kokarin kai ta kasa ba tun yau ba. Kai tsaye ɓangaren Yasmine ɗin ya isa da kansa. A lokacin tana zaune da wasu guntayen kaya a jikinta. Tayi zurfi sosai cikin tunanin wancan ƙaton arnen taji anyi wani irin knocking a ƙofar. Wata after dress brown ta janyo TA ɗora saman guntayen kayan taje gaban ƙofar taki buɗewa tana tambayar waye?. Gyaran muryan mahaifin nata da taji ne ya saka ta saurin budewa ta faɗa jikinsa tana sakar masa kukan data jima tana riƙewa se yazo, ɗan bubbuga bayanta ya shiga yana bata baki. “Kiyi hakuri Ambasajo in dai akan fita ne zan sa miki 1 billion a account naki kije shopping ki sai duk abinda kike so...” da haka ya samu fushi da kukan nata ya sauƙa suka fito zuwa dining ɗin, kanta a dage a sama ta zauna duk a tunaninta Maamah ɗin nata na wurin, har se da ta lura bata nan kana ta ɗan saki ranta. Husna da taga take takenta se ta kyale ta ƙarshe ma ta bar musu wurin, bayan sun kammala dinner ɗin har ɓangaren nata ya sake raka ta. Har ze fice ta kirayi sunan shi daya saka shi tsayawa cak. Ahankali ta dawo ta setin da yake tsayen tace. “Mukullin motar ka zaka bani, dan na fara gajiya da tawa, kamar ma ina son a sanja min ita ta gama isa na...” Murmushi yayi dama car key ɗin jikinsa ya bata fita bayan ya kashe mata hasken ɗakin ya bar mata ƙadan irin dum ɗin nan. Be jima da fita ba sega alert ɗin One billion ɗin daya mata alkawari. Wani uban ihu ta buga tana direwa a saman gado don ita kaf duniya tana son ganin Daddyn ya mata kyautar kuɗi irin haka, duk da kasancewar itama tana da wasu irin kuɗin masu nauyi cikin account nata. ꨄ Tsaye yake a balcony ɗinsa, iska na ɗan ɗaga rigar jikinsa da kuma sumarsa. Hannunsa riƙe da ƙaramar chocolate ɗin ta Ferrero Rocher ɗin da seda ya saka Mecheal ya nemo masa a daren, Ahankali ya juya yana zama kan doguwar kujerar hutawar dake wurin, ajje ledan chocolate ɗin yayi yana lumshe idon sa maganganunta na ɗan dawo masa ka. Sake gyaran murya a kusan karo na uku kenan Madame Victoria Osteen tayi ma yaron nata, amma duk be ji taba har seda yaji hannunta cikin gashin kansa kana ya ɗan dago a firgice. Ganin Mommah nashi ce ya saka shi wani bata fuska idonsa da suka yi wani haske sosai, ga kuma alamar ruwan daya tarun masa a ciki ya zuba mata yana kamo hannunta daga sumarsa da taci gaba da shafa masa, sake kwaɓe fuskan shi yayi a saman laɓɓansa ya furta. “Mommah” a wani irin shagwaɓen da za kayi tunanin irin befi 3 year's ɗin nan bane. Kansa ta sake shafawa tana sake jefa masa tambayar lafiyansa kuwa?, tunanin meke damunsa haka? ɗauke hannun nata ya sake yi kansa yana miƙewa tare da gyara maɓalan gaban riharsa da suka buɗe kuma kai tsaye Mommah'n nashi na shirin kai hannunta saman jikinsa, gyara maɓalan rigan yake yana soma tafiya ba tare daya ɗauka sauran chocolote in nashi ba, yake ce mata babu komai kawai yana buƙatan spece ne. Ɗan zama daga inda ya tashin tayi ta lumshe idonta kafin ta buɗe su suka sauƙa kan sauran chocolote ɗin nashi. Kai tsaye ta ɗauke chocolote ɗin tana miƙewa da ita tabar balcony ɗin. Kai tsaye saman lafiyayyen gadonsa ya faɗa hoton kyakkyawar fuskarta ta ɗazun na dawo masa, ƙiran waya ce ta shigo masa yana kallon daga inda ƙirar yake yayi sweetching wayar nashi ma baki ɗaya. Ya jima beyi barci ba se can zuwa dare kana barcin ya iya nasarar sace shi. ★… Washegari da niya yaƙi tashi da wuri se wajajen sha daya saura, kafin ya gama shirinsa ya fito kuma har sha biyu ma ta ɗan gota,kamar jiya yau ma duk yadda family nashi suka so yin dinner tare dashi basu sama wannan damar ba, gashi kakansa Patriarch na shirin tafiya da,amma se ya ce ya fasa se John ya sama lafiya. Don su a nasu ganin wai baya da lafiya ne, yana ficewa suma kaf suka fice suka nufi couch don yi masa adda'a. Ga Papa'nsa shi kuma baya ƙasar yana India kwanansa biyu da tafiya, kuma tare da Deepika ya tafi tana son ganin gida in yaso daga baya ta dawo, kai tsaye shi kuwa John wannan Mall ɗin ya koma, amma duk iyaka bincikensa da yayi be ganta ba, don haka ya rin ga bin manyan wurare ko ALLAH ze sa ya ganta amma be ganta ba har rana ta take masa, ƙin hakura ya koma gida yayi haka yau ma ya haɗa Mecheal da gantalin zaga manyan wurare a garin Lagos, ƙarfe biyar cif na yamma zuciyarsa ta sake bashi shawarin ya sake komawa wannan shagon. Aikuwa akayi haka sedai kuma bata nan ɗin. Take yaji kamar ana tafasa ƙwaƙwalwar kansa ne da rashin ganin nata, ga Madame Victoria ta ishesu da da kashe ɗin lallai duk inda suke su dawo a wayar Mecheal don shi ƙin amsata yayi,yana tsaka da wannan zafin kan yaga tamkar gimlawar wani abu, haka yaga gimlawar kyakkyawar fuskar ta, wacce ke frowning na zallar kyau yau ma sanye da brouwn dogon hijjaba har ƙasa. Don haka da sauri ya fara zagayen ta inda yaga gimlawar nata sedai be ga kome kama da ita ba, kai tsaye ya bama masu mall ɗin umarnin a tattaro gaba ɗaya jama'ar dake cikin mall ɗin yara da manya. Kafin ƙiftawar ido kuwa se gashi an tattaro kan jama'ar wurin suna ta fitowa. Yana tsaye hannuwansa ɗaya saman kansa yana shafa sumar kanshi, ɗayan kuma rike da ledar chocolote ta raspberry yana taunawa. Kansa a sama tallefe da ƙeyarsa fuskar nan tayi wani irin ɗinkewa ɗif alamar No nonses kenan. Haka ya fara zagaye tarin jama'ar dake Mall ɗin ƙatuwar sarkar Cross nashi na faman rito tsaƙiyan ƙirjinsa da tsaban iskanci ya ɓalle mata maɓallai wajen uku zuwa huɗu, kansa a sama amma yana fahimtar kowa se wani faman huhhura hanci sama yake, yau gashi tsohun shege. Haka ya shiga zagaye matasa mata da mazan dake wurin, yara da tsofaffi amma kuma babu ta babu alamarta, kamar wacce aka ce kalla ɓangaren damar ka yaga wata na sanye da brouwn dogon hijjaba har ƙasa tana ci gaba da ɗibar duk abinda ya mata, sosai wani irin mamaki ya kama shi, ganin ita babu abinda ya dameta ko bata san anyi taron bane, don haka a ɗan fusace ya isa gare ta amma tun kafin ya ƙarasa kuma ya tsaya cak. Sabo da bugun da yaji ƙirjinsa ya masa, wanda kai tsaye hakan kamar yana alamta masa cewar ita ne tsayen, cikin ƙarfin hali ya isa gare ta yayi amfani da ledar chocolate ɗin dake hannunsa wajen karkaɗa mata saman fuskarta, amma ko wanne motsi bata yi ba. Shi kuwa Idanuwansa ne suka fara yawo ko ina a jikinta tun daga sama har ƙasa, kamar zakin daya fito domin farauta. Cikin ransa yake furta _Wannan alamar ta wuce wasa a gare ni..._ Sak idanun John su kayi akanta,duk da baya ne ta bashi tsaye ɓangare guda na mall ɗin tana ci gaba da duba wasu kaya. sanye da niƙab ɗinta kamar kullum kamar ko da yaushe. “It’s her…” ya faɗa a hankali, kuma bai jira komai ba ya fara takawa zuwa dab da ita kai tsaye. Ita kuwa daga ɓangarenta duk abinda ke faruwa tana sane kuma tun lokacin data shigo ta lura dashi,har zuwa kan sanda yake zagayen kamo tattaro masa mutanen da akayi ɗin. Ahankali ta zame nikab nata zuwa sama, kai tsaye idanunsu suka sarƙe ana juna amma nata suna cike da ɓacin ran kaiwa maƙura a ƙoƙarin fara takura rayuwarta da wannan ƙaton arnen yayi. “Not again…” Ta furta a hankali kafin ta juya zata ci gaba da sayayyarta. Ganin tana ƙoƙarin sake ɓace masa ne ya saka shi furta kalmar. “Hey!” Haka muryarsa ta dakatar da ita ta tsaya cak. Kafin ahankali ta juyo idanunta cik da haushi... “Ban gaya maka ka dena bina haka nan ba?” ta faɗa kai tsaye. Wanda ya saka John tsayawa a gabanta, ba tare da tsoro ko nadama ba ya furta. “I told you… I was looking for you.” ya mayar mata cikin natsuwa, wata ƴar dariya kaɗan tayi mai cike da raini tace. “Looking for me? For what exactly?” “To finish what you started…” Shi ma katse ta yana sake matsowa daf da ita a hankali. Take fuskanta ya sauya ta ce. “Excuse me?” Ta faɗa da ƙarfin daya saka Mutane suka fara kallonsu. “Ka na nufin me?” ta sake faɗa da tsawa, bai ja baya ba sema sake tallafe kansa da yayi, kafin ya zuba mata maraitattun mayun idonsa murya a wani kalan hankali yace... “Ina nufin… you slapped me… and left.” yace da wata irin murya so calmly wani ɗan murmushi na bayyana a gefen bakinsa. “That’s not how it ends.” Wannan karon kam da ihu Yasmine tace... “YOU MUST BE CRAZY!” ta faɗa da ƙarfi kafin ya dawo daga duniyar ihun data masa ya sake jin sauƙar mari me ƙarfin gaske saman fuskarsa, wanda ya saka Mecheal saurin rintse idonsa tare da jama'ar Mall ɗin da har yanzun suke tsaitsaye. Komai bai ji ba dangane da marin data masa sema kawai ɗan karkata kansa gefe da yayi yana sake bata fuskan,yana sake mai da kallonsa ga kyakkyawar fuskarta ba tare da fushi ko wani abu ba. Sai ma wani irin murmushin daya zagaye fara tas ɗin fuskar shi, nuna shi ta shiga yi da yatsa tana huci tace... “I warned you!” Ta sake faɗa a tsawace, taci gaba da nuna shi. “Na gaya maka ka dena bina!” Wannan karon murmushin daya mata harb sai daya ɗara laɓɓansa,ya sauka kaɗan zuwa saman fuskarsa. Bai kuma ce komai da ita ba yaci gaba da bin ta da idonsa, yana ci gaba da bin ta da irin wannan tausassan murmushin, wanda ya saka Yasmine taji wani abu ya tsaya cak a kwanyarta. Kafin ahankali ya ce. “Next time…” Se kuma ya ɗan dakata alamar yana son samun hutu daga bugun da zuciyarsa ke masa kafin ya sake cewa. “I won’t let you go.” Sai kuma idanunsa suka rage kaifin hasken da suke ɗauke dashi a da, suna ɗan yi duhu kaɗan. “This time… you’re mine....” Wani shegen kallo ta masa kafin ta juya zata bar wurin, ya riƙo hannunta yana binta da wani kallo ƙasa ƙasa, sake watsa masa manyan fararen idonta tayi ta kalla hannunta ta kalla nashi daya riƙe natan, ta buɗe baki kenan zata yi wata maganar ya rigata ta hanyar furta... “ Da nayi sakacin barin ki tafi ba tare da sanin ainihin suna ko inda kike zaune ba!, Amma wannan karon ba zan bari ki gudu ba...” wani kalan fusge hannunta a nashin tayi ta juya cikin ɓacin rai ta bar wurin yana take mata baya. Mecheal ne yayi saurin take masa baya yana cewa. “ Easy Boss… are you okay?” Ya tambaya cikin damuwa, da hannu kawai John ya dakatar dashi Idanunsa har yanzu suna kallon inda ta bi yana zame hannunsa cikin na Mecheal daya riƙo bayan ya ce. “I like her more now.” Wanda ya saka Mecheal ya tsaya cak a bayyane yana me furta.. “Lallai Boss ya shiga uku…” ★... Saurin zaro wayarsa yayi ya dokama Madame Victoria ƙira, cikin ring farko ana biyun ta ɗauka. Tun kafin yayi magana tace “Mecheal ina yarona?...” “Madam…” ya faɗa cikin girmamawa kafin ya dora da faɗin. “Na ƙira ne in sanar dake… Akwai wata yarinya!, Ohh wannan Hausa gal ɗin Boss yana ci gaba da bibiyarta sosai.” wani ihu daga ɓangaren Madame Victoria ta yi tana cewa. “Wa...ce...ce...wacce yarinya?” tana ma mancewa da batun Hausa gal ɗin John ɗin.. wani yawu Mecheal ya haɗiye da ƙarfi wanda ya kusan kwarar da shi yace... “Ban san sunanta ba… amma tana sanye da hijab… Hausa girl narh.” Cak numfashin Madame Victoria ya kusa yanke wa tuno da yarinyar... “Hausa… girl?” ta maimaita sunan da taji ya mata wani irin nauyi a cikin zuciyarta, take ta fara ganin kamar duhu duhu daga cikin idanunta. Kafin kamar a zabure ta ce.. “Keep watching him, duk inda zai je… duk wanda zai gani… ina son sanin komai.” “Y-Yes, Madam…” Mecheal ya amsa kamar a ɗan rarrabe yana kashe wayar. Daga can ɓangaren Madame Victoria kuwa tana sauƙe wayar taji kamar wani abu me zafi aka zuba mata a cikin idanu da kirjinta. Wata kafuwar zabura tayi fuskarta cike da wani irin yanayi me matuƙar haɗari tayi wani ɓangare daban a cikin ɓangaren nata zuciyarta na wani irin mahaukacin tafasa. “Ba zan bari wata mace ta karɓe min ɗana ba…” Ta sake faɗa da karfi Idanunta naci gaba da rikiɗewa ta sake ce “Not this time.” John kuwa ko kafin ya isa har ta sake ɓacema ganinsa, duk kuwa da yacce yayi ta zaga harabar wurin, wani ƙaramin ihu yayi ya daki ginin dake gabansa wanda ya saka take hannunsa fashewa jini ya fara zuba, goshinsa ya sake bugawa ya sake daga hannu da niyar fasa glass na motarsu Mecheal yayi hanzarin kamo hannun yana furta... “Easy...Easy Boss, Relax Pls...” Rinannun idonsa ya ɗago yana watsawa Mecheal ɗin daya saka shi ja baya da sauri, daidai da lokacin da kakansa Patriarch da Madame Victoria taje ta sanarmawa suka iso wurin suka kamashi yana ihu yana komai suka zira cikin mota suka tafi dashi gida.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 9 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Tun da shige ɓangarensa yau ɗin ma kamar jiya babu wanda ya sake jin koda motsin sane, ga likita sun riga da sun kirawo da zai duba goshi da hannunsa. Haka daren ranar yazo ya riskesu tamkar masu zaman makoki sun jere a gaban bedroom nashi. Shi kuwa a nashi ɓangaren koda ya shige saman sofa ya zube a ruf da ciki, sam be damu da jinin da hannunsa ke zubarwa ba, duk kuma uban bugun da suke yana jin su yayi kunnen uwar shegu dasu, daga ƙarshe ma parlourn ya bari ya shigewansa bedroom nashi... Ko nutsatsestsiyar dinner babu wanda ya samu yayi a cikinsu kowa hankalinsa a tashe da ciwon da John ɗin yaji, a daren ranar haka Papa da ko rabin abinda ya kaishi India be biya biyo jirgi, don sun gama rikita shi da cewan John ba shi da lafiya sosai. Shi kuma a duniya baya taɓa iya haɗa kowa da ƙaunar yaron nasa, don jinsa yake kamar shi ne ransa gaba ɗaya. Take wani mayataccen mayen zazzaɓi ya kama Madame Victoria don kaf duniyar ita har Papa ɗin ma gani take ta fishi ƙaunar John ɗin. Duk kin ta da Deepika haka tana ji tana gani dole se ita ce ta ringa kula da ita don jelly bata nan tana wurin wani birthday ɗin freind nata Solomon. Har zuwa dare can sosai gaza runtsawa tayi har se da Deepika ta taimaka mata da adda'a bayan ta ɗauko bibble nasu. Abincin kuwa da ita ma bata ci ba kenan,don cewa tayi idan taci ai kamar taci amanar John ne, tun da shi yana can rai a hannun ALLAH. Yana tsaye gaban mirrornsa fitowansa a wanka kenan ɗaure da fari tas ɗin towel a ƙugunsa, ahankali ya kalla kansa ta cikin mirror ɗin,kafin ya sake dawo da kallon masa kan hannunsa dake naɗe da bandage ɗin da shine ya saka gashi a disheveled, amma idonsa kamar yana neman abu ne da ya ɓace tun da daɗewa hannunsa yakai saman goshinsa yana me furta... “Crazy…” Amma baga yasmine yake nufi ba wa shi kansa yake nufi. Ƙirar wayar daya shigo masa ne ya saka shi kallar inda wayar yake,sunan Mecheal daya gani kawai ya bashi tabbacin Mommah nashi ce. Kamar ba zai ɗau wayar ba se kuma ya ɗauka. Jin a daga wayar kai tsaye ya saka Mecheal saurin cewa. “Boss!, please don’t move Madam said” Kai tsaye John ya katse shi da furta. “I don’t take orders when I’m like this.” Ya kashe wayar gaba ɗaya yana jifa da ita saman lafiyayyen gadonsa. Ko a washe garin ranar ma se wajajen sha biyu ya fito sanye da black wando irin na shaƙatawa dake da madauri da blue t-shirt, wacce tayi matuƙar kama jikinsa ta bayyana siffar faffaɗan kirjinsa. Gashin kansa dake so coily kuwa ya sake naɗe kansa ya kwanta luf abinsa, goshinsa da hannunsa naɗe cikin bandage. A hankali yake saƙƙowa ƙafafunsa sanye cikin slipper's masu taushi, hannun sa riƙe da wayoyinsa guda biyu IPhone da Samsung latest. Tunda ya fito yake cin karo da mutane dake kwasar gaisuwa amma ko kallo basu ishe shi ba, se ma fuskar daya sake matsewa sosai babu ɗigon fara'a bare ma ayi tunanin kawo masa wargi ko titsiyesa akan maganganun da yasan sune danƙare a bakunan kowa, da haka iso babban parlourn gidan. Zaune yakai cike da wani irin izza saman kujerar mai kaman cushin. Su kuwa ɓangaren mutanen gidan yau ɗin ma kusan kowa a birkicen yake har zuwa loƙacin.... Wani uban ihun farin ciki jelly da wajen ƙarfe uku itama ta dawo gidan, don jikin Madame Victoria ne ya matsa don haka bata tsaya an kammala birthday ɗin da ita ba ta yo gida, don gaba ɗaya kaf family nasu basu taɓa haɗa ƙaunar Joseph data kowa. Uban ihun data kwarara tana yin kansa a mugun guje ne ya saka hankalin kowa yowa inda tayi ɗin, don tun ƙarfe bakwai ɗin safe suka runguɗa suka yi cauch adda'a ma John da jikin Madame Victoria. Tana isa ta ɗane jikinsa don daga shi se ita iyayensu suka haifa,don haka suke wani irin ƙaunar junansu bana wasa ba. Goshinsa dake ɗauke da bandage take taɓawa idonta na cikowa da ruwan hawayen tausayinsa, don ko tuntuɓe basu ƙaunar ganin John ɗin yayi bare kuma rauni irin hakan. Sake ƙamƙame shi tayi bayan taga yadda na hannunsa har ya so fin na goshin yawa. Take gaba ɗaya duk sauran family ɗin suka isa gare shi suma suna rungumeshi... Kafin da ƙyar Madame Victoria ta samu suka sake sa, itama ta matsa tana rungumoshi jikinta tana jin a se lokacin bugun tata zuciyarta ke dedetuwa, wani hawayen farin ciki na gangaro mata saman fuska. Hannunsa me ciwon yasa ka ɗan yana ɗan buga bayanta tare da ɗagota yana mamakin hawayen na miye?. Batare da yace komai ba ya zaro wani fari tass ɗin handkherchief a aljihunsa ya share mata hawayen. Ƙarason kakansa Patriarch dasu Papa ne ya saka dole Mommah matsawa ta basu wuri suma duk suka rungumesa, hakama X-Eashika ta zo tana rungume sa tare da kissing peck nashi ta janye baya. Kakansa ya sake shigar da shi jikinsa yana kwanto wani jibgegen dutse a wuyarsa da nufin rataya ma John, karon farko kaf rayuwarsa yaji bai son wannan shirmen, su hakan ma daya fito musu basu san ɗaurewa kawai ya yi bane, bai son ya tada hankulansu sosai ne, amma ba don haka ba shi da su sake saka shi a cikin Idanuwansu se nan da kamar 4to 5 days. Kuma kowa kamar yasan bai son a masa wata ta daban se kowa me magantun ba kamar yacce yayi fatan kuwa. Madame Victoria ce ta kama hannunsa mara ciwon ta jingina da jikinta suka nufa dining ɗin dake shirye da ƙayatattun abinci babu wanda aka taɓa saboda zuciyarsu baya cikin mood me daɗi... har gaban kujarar da Papa ne kawai ke zama ta kaishi ta zaunar, wanda shi kuma Papa ɗin ya komanta John ɗin da shi ma in ba shi ɗin ba babu me hawar masa koda baya nan ne. Ruwa me sanyi sosai ta kawo masa don ta san kyakkyawar alaƙa ce me ƙarfi tsakaninsa da ruwan sanyi, bare kuma uwa uba ƙanƙara, so da tari idan zai yi wanka ma seya jefa kankara a ciki ruwan wankansa tun iyayen na masa faɗa har suka ƙyale shi don basu son takura masa ko kaɗan ne kuwa. Bai musaba kuwa ya amsa yasha kusan fin rabi, signing Madame Victoria tama Papa da ido akan ya tambaya John ɗin abinda ke faruwa dashi, wanda ya zaman kamar wayo ta masa ne don ko ransa ya ɓaci ita banda ita kenan, zata sake yin shiru ne taki magantuwa akan lamarin. Take kuwa Papa'n nasa ya jeho masa tambayar abinda ke faruwa dashi tun last week?. Wanda hakan ya saka John wani irin dafe kansa da yaji kai tsaye ya sara masa, ɗan lumshe idonsa kawai yayi ba tare da yace komaiba. Sanin bazai ce ɗin bane tun da yayi gum ɗin yaƙi ya tanka ya saka Papa jan nasa bakin ya rufe ruf shima. Gaba ɗaya ma yaji zaman wurin da abincin da dama don dole yake ci yaci sun isheshi, amma dole haka ya daure bayan sun kammala aka koma babban parlour.... Shi dai kin zama yayi ya sake hayewa sama abinsa duk da yacce yake son fita amma dole haka ya danne ya koma saman. Be rufe ba wannan karon ya bar ƙofar parlourn a buɗe yayi kwanciyarsa saman kujerar daya gyara mata zama ta koma ɗan ƙaramin gadon shan iska. A haka Madame Victoria tazo ta same shi. Zama tayi daga gefensa tana ɗago kansa ta ɗora kan ƙafafunta ta dafe saman goshin a hankali ta fara masa adda'a. Ta jima tana masa adda'an kafin yakai hannunsa ahankali ya zame daga goshin, ya buɗe baki kenan da nufin mata magana ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kai alamar shiiiii yayi shiru kawai... Amma duk da haka se da ya sake riƙe hannuntan yana cilla mata tambayar. “Mommah what are you praying for me, why are you waiting so long?” Saman kansa ta shiga shafawa kafin ta bashi amsa da... “Oh my love, I pray to Jesus to cleanse us.... I carry you in my prayers every single day. I lift your name before God with tears in my eyes and faith in my heart. May the Lord Jesus Christ surround you with His divine presence, guide every step you take, and fill your life with His light....May He protect your heart from every hidden danger, every temptation, and every voice that is not from Him. May no evil come near you, and may every plan of the enemy against your life be destroyed in Jesus’ name.... I pray that God shapes your destiny according to His perfect will, grants you wisdom beyond your years, and keeps you standing firm in righteousness. Wherever you go, may His grace speak for you, His mercy cover you, and His Spirit lead you... You are covered, my child… now and always.” “Thank you for your prayers, Mom, but I am not in any danger.” Ya wani faɗi a shagwaɓen daya saba dashi dama. Ɗan Rungumesa da kyau Madame Victoria tayi cikin Jin daɗin ganin ya sake lokaci guda tace... “Yes, I know, but I have to pray for you, Jesus, to continue to care for you” “I love you Mother” Ya wani faɗi a narke wanda ya saka Madame Victoria cike da zallar son da take masa ita ma tace... “I love you too Sweetie....” Ɗan lumshe fararen idanuwansa yayi saboda da fuskar yasmine data fado masa. Ganin ya fara yamutse fuska ne ya saka Madame Victoria miƙewa tsamm don barinsa ya huta bayan ta sake masa peck ta fita, anan parlourn ya wuni family'n nata faman sintirin leƙo shi, kowa se wani sabon nan nan yake dashi ko ina babu wanda yay yunƙurin fita a duk yau ɗin. Da rana beyi dinnerh ba se dare yana yi kuma ya wuce room nashi. Ko da ya kwanta kasa bacci yayi saboda wani irin azaba da tiririn son ganinta da zuciyarsa kawai keson yi, wanda hakan ke azabtar da zuciyar nasa, don haka luff ya sake lafewa cikin lallausan farin duvet nashi, tare da lumshe ido ahankali cikin sanyin murya yace... “I love this feeling,,,and I love you my unknown beloved....” Da ƙyar bacci ya ɗan fusgesa can tsaƙiyan dare. Sassafe ya kuwa farka da wani tsimammen ciwon kai bana wasa ba, wanda ya saka har jijiyoyin kansa suka tashi. Daga saman gadon ya saƙƙo yana zama ƙasan gadon hannunsa na saƙale da gefe da gefen gadon. Don haka koda Madame Victoria ta shigo hannunta riƙe da bibble nan bedroom ɗin nashi da niyar masa adda'a se ta tsaya cak. Sakamakon ganinsa da yayi zaunen da kuma yadda gaba ɗaya yanayin jikinsa ya sanja, saurin isowa gare shi tayi tana ajje bibble nata gefensa tana tambayarsa me ya faru. Shiru kawai ya mata yana sake dafe kansa da ke fitar da wani hucin ɗumin zazzafan zazzaɓin daya kawo masa farmaki. “Ohhh Jesus Bring my child and take him. Help him and give him health, Jesus.” Haka take ta faɗa tana shiga bathroom nashi ta jiko towel tazo tana shafa masa daga goshi zuwa ƙirjinsa idonta na cikowa da ruwan hawaye. Da wayar John ɗin tayi amfani wajen kiran Papa tana masa ihun yayi maza yazo John babu lafiya sosai, kafin kace se gasu gaba ɗayansu. Kuka kawai jelly da X-Eashika suka saka ganin yadda jikinsa ke rawan zazzafan zazzaɓin daya rufe sa, Papa ne ya ƙira Mecheal yace yayi maza ya shirya mota John babu lafiya zasu asibiti, amma ƙememe John duk da halin masifar da yake ciki yace babu inda ya zashi, duk yacce suka so lallaɓa shi yaƙi yarda dole suka meda akalar fitan da kitan family Dactor nasu emmanuel. Cikin abinda be gaza 30 minutes ba se gashi ya iso, ruwa ya fara ɗaura masa first kafin komai, daga nan yace su bashi wuri seka koma second ploor yayi gwaje gwajensa ya masa alluran zazzaɓin kana ya fito.. “Emmanuel, what's wrong with my son?” Mademe Victoria tare da Papa suka kusan haɗe baki suna tambayar lafiyansa... “Be at peace, it is only a small burden troubling his heart.” Daga nan ya shiga kwantar musu da hankali yana cewa da zarar ruwan ya kare ya sake shan maganin daya ajje masa shikenan, godiya suka masa ya tafi yana masa fatan samun sauƙi. Mecheal duka family ɗin suka tirke akan dole ya faɗa musu gaskiyar komai, duk yanda gabansa ke faduwa game da irin hukuncin da zai amsa daga uban gidan nasa amma dole ya sanarma da su Papa'n komai, inda gabansu kusan a tare suka buga. Damma sa'ar sa ɗaya be ce ta sake marin saba a haduwa ta biyun da suka yi... Hausa girl kuma?, to Miye kuma haɗin John ɗin su da girl aikuwa ko yar uban waye se sun saka an binciko musu ita. Daga nan zaman meeting aka shirya akan John ɗin suka yi iya ka su manyan.... Wajen kwanaki biyu kenan da John ke fama da jikinsa,ga tunanin maƙale cikin ransa da yake jin kamar ma shi ya hana sa warkewan... ★... A kwanaki biyun nan da suka sake rufama wancan biyun baya sosai abubuwa suka sake ma John tsauri. Ba tare da kowa na gidan ya sani ba ko baccin kirki baya iya yi, ita kawai yake son gani, sosai zuciyarsa ke azalzalansa akan dolen dole ita kawai ido da gangar jikinsa zasu gani ya samu sauƙin jikin nasa, in ba haka ba kuwa to lallai ba zai taɓa warkewa. gaba ɗaya neman birkicewa yake, kansa neman juyewa yake saboda tsananin azabar da yake amsa daga zuciyarsa. Gashi duk yacce yaso da son fita iyayen sun bi sun tare masa hanyarsa, wayar sama sun sace masa don kar yayi amfani da ita. Don haka tun a daren jiya zuwa yau ɗin yaƙi yin magana da kowa a gidan,ya kuma ƙi cin abinci, kai daga ƙarshe ma kulle kansa a ɗaki yayi ya hana uban kowa ganinsa. Tun suna ganin abin kamar wasa har abin ya dawo basu tsoro. Haka Madame Victoria tayi ta bugun ƙofar bedroom nashi amma yayi kunnen uwar shegu dasu, ga tabbacin abinda ke sake basu tsoro shi ne babu komai ko ruwa a bedroom ɗin nasu, don gaya nan ya fito musu da komai ya zubar a parlourn da yake a buɗe.Tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa, haka ma kakansa Patriarch da Papa duk sunyi sun gaji, Daga ƙarshe ma har babban amininsa Joshua aka ƙira amma yaƙi buɗewa.... ★... Kusan ƙarfe biyar na yamma sai gashi ya saƙƙo ƙasan dan kansa cikin shigar riga da wando designers masu shegiyan tsada da kyau kalan sky normal, wacce suka wani kalan haska farar fatarsa me kyau. Se dai tashin farko kana iya hango shegiyar ramar da yayi,Kuma kallo ɗayan zaka masa ka hango tsananin damuwa tattare da shi. Mademe Victoria ce kawai zaune a parlourn sai jelly duk kowa ya kama gabansa ganin zaman makokin da suke ba ƙarewa zai yi ba don haka kowa ya fita safgar gabansa, saɓanin ita data kasa dara ko ina. Jelly na ganinsa cike da girmamawa a garesa ta shiga gaida shi babu wannan rawan kan nata ganin yadda ya koma. Hannunsa ɗaya kawai ya ɗaga mata yana ida ƙarasowa inda suke ba tare da yayi magana ba. Kafin Ahankali ya kai dubansa kan Mommah nashi da idanuwansa da suka yi zurfi sosai... “John...” ta ambaci sunan shi ganin ba tare daya sake kallar inda take ba ya nufi ƙofan fita, cikin harshen turanci take tambayarsa ina zayaje da wannan ƙurararren lokacin haka, tayi masa tambayar ne kuma tana wani tsatstsaresa da idanunta manya,da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da... “I like to breathe fresh air.” Ita ma sake mayar masa da tambayar da sake yi da... “All the air in this house is not enough to make you go out ne?.” “I need them...” Ya sake bata amsa shi ma, wanda ya sakata yunƙurowa ta miƙe ta ce. “There is nowhere to go.” Kansa kawai ya ɗan girgiza mata ba tare daya bata wani ƙarin bayani ba yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa. Saurin take masa baya tayi tana kiran sunansa amma ko waywayota be ba, kamo hannunsa tayi da ihu tana cewa babu inda zai je wllh.Yanzun ma bai juyoba har sai da yaja wasu sakanni. Dole ita ce ta sake zagayawa ta gabansa ta tsaya, muryarnta cike da damuwa tun kan ta buɗe baki ta masa wata maganan, yakai yatsunsa kan bakinta yay mata alaman tayi shiru kawai yana sumbatar goshinta ya juya ya bar wurin, bayan ya mata murmushi tare da lumshe idonsa alamar zai kula da kansa... Haka tana ji tana gani ya fice Mechealna buɗe masa mota suka fita. Wani ɓoyayyen numfashi john ɗin ya sauƙe mara sauti numfashin sa na cunkushewa da bugun zuciyarsa... Be san inda suka nufa ba, kawai dai yace yau ɗin ma yayi yawo dashi sosai, ganin uban hadarin daya gangamone ya saka shi cewa Mecheal ɗin su koma gida. Har sun wuce wata hijjab girl yace Mecheal ya koma baya, domin shi yanzun duk inda yaga hijjab bashi girma yake. Kamar a mafarki yaga yasmine tsaye kamar a ɗan firgice. Da sauri ya isa gare ta yana zube mata duka idanuwansa akanta cike da wata irin kewa... Da kyar ta iya buɗe idonta ta kallesa, wanda kallon data masa ya sake take jin wata muguwar zazzafar soyayyarta na sake shigarsa da ƙarfi, Ƙafafunsa na kamar rawar sanyi ya ƙarasa dap da ita sukaima juna kallon ido cikin ido, kafin ita ta wani rintse idanuwanta saboda ba zata iya ci gaba da kallon cikin kwayar idonsa. Ahankali ya bude baki cikin ƙaramin sauti laɓɓansa na rawa yace. “I love you My unknown beloved...” Ɗan bubbuga jikin kujerar da yake jingine a jikinta ɗan baccin da bai da tsawo ya ɗebe sa ya shiga faɗin. “Boss wek up wek up Pls an fara yayyafi kar ruwa ya ritsaka baka isa ba....” _Hhhhh ashe mafarki yake jama'a 😮‍💨🤩🤐🏃🏃🏃🤸🤩 _ _To ai shikenan a gimtse kawai anan..._ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 _Dont forget to vote, follow and comments_ *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 10 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Sake ɗan jujjuya kansa ya shiga yi yana son tantance a zahirinsa yake ko baɗini. “Boss… wake up… it’s raining…” Haka John ya sake tsinkayar muryan Mecheal ahankali, cikin mafarkin nasa daidai yana tsaye gaban Yasmine hannunsa na riƙe da nata, zuciyarsa cike da nutsuwa amma muryan Mecheal ɗin ta yanke masa komai. Kamar a ɗan burkice ya buɗe idanunsa da suke a rufe yana ambatar sunan yasmine ɗin da a yanzun a kuma cikin mafarkin nasa ta sanar da shi sunanta. “YASMINE!!” ya furta a hankali cikin ruɗani, numfashinsa na hargitsewa. Kafin ya kalli gefen da yake da sauri babu ita,sai duhu sai motar kawai se kuma Mecheal.Wani irin haushi ne yaji ya taso masa nan take, na yanke masa mafarkin da Mecheal ɗin yayi. Wata Zazzafar numfashi ya fesar me ɗumi kafin idanunsa suka koma kan Mecheal ɗin da ya durƙusa a wajen motar yana ƙoƙarin sa shi fita. “Boss please… rain is heavy, we need to go inside” “SHUT UP!!” JOHN ya katse shi cikin tsawa mai ƙarfi, wacce ya saka Mecheal ja baya babu shiri, wani dafe kansa John yayi yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar zata fashe. “Why… why now?!” ya faɗa a hankali cikin laushin da muryansa yayi nan take, buɗe ƙofar motar yayi da ƙarfi, amma bai fita ba. Ya tsaya a bakin kofar kawai yana kallon ruwan sama da ke sauka ahankali da aka fara yanzun, se yake ganin saukar ruwan kamar shima yana da alaƙa wajen katse masa mafi muhimmanci abu cikin rayuwarsa. “YASMINE…” ya sake faɗa ƙasa-ƙasa, kamar yana kiran ruhinta. Mecheal ne ya sake matsowa ruwan shi na sauƙa a jikinsa ya sake furta. “Boss, please… let’s go inside.” wani kallo John watsa masa da idonsa mai cike da jin zafin katse shin da yayi. “Because of you… I lost her face.” ya faɗa da wani zafin a hankali amma kuma cikin muryan nasa wani irin nauyi ne a cikin ta. Shiru kawai Mecheal ya yi, don kamar bai fahimci me yake nufi ba. Kawai iyaka abinda ya sani shi ne cewar JOHN ɗin ba'a cikin nutsuwa da hayyacinsa yake ba. ★... A can cikin gidan kuwa jin yadda ƙarar iska da ruwan saman dake ƙara ƙarfi ne ya sake tada hankalin iyayen nasa, gana ɗaya cikin gidan babu nutsuwa ko kaɗan kamar dai yadda suka saba ruɗewa akan John ɗin da duk abinda ya dangance shi. Shigowar Mecheal ya saka su sakin ajiyar zuciya sedai ganinsa ba tare da John ba ya sake tashin hankalinsu. “Where is John?!” Papa da a wannan karon hankalinsa yafi na uban kowa tashi ya faɗa cikin tsawa yana tashi tsaye. Ganin hakan ya saka itama Madame Victoria ta miƙe da saurin ita ma, hannunta na rawa. “Mecheal!!” ta kira shi da ƙarfin daya saka Mecheal ƙarasa shigowa parlourn gidan cikin sauri, jikinsa a jike da ruwan sama. Tun kafin ya ƙarasa isa tsaƙiyan parlourn Papa ya isko shi fuskar nan babu alamun rahama ko kaɗan, ya sake dakawa Mecheal ɗin tsawa yana sake jefa masa tambayar. “I said WHERE IS MY SON?!” Ya faɗa da muryarsa da ta sake cika parlourn. Madame Victoria ma ta matso, idanunta cike da tsoro take ɗan fara jijjiga Mecheal ɗin tana sake faɗin... “Oya Tell me! John yana ina?!” wani yawun azabar da be shirya haɗiyar saba Mecheal ɗin ya haɗiye. Se da ya ɗan dedeta numfashinsa da yawun ya sarƙe kana ya ce.. “ Relax Ma’am… Sir… he is outside… in the car… but he refused to come in.” Wani shiru ne ya rufe parlourn na second. Kafin Papa ya wargaza wurin da uwar tsawar daya daka yace. “Are you mad Mecheal?! Rain like this and he is outside?!” ya faɗi yana jin zuciyarsa kamar zata faso ƙirjinsa ta fito, domin sun fi kowa sanin irin illar da ruwan saman ke ma John idan har ya dake shi. Wani ja baya Madame Victoria tayi irin alamar ta mutu ɗin nan, kafin ta rufe bakinta da hannunta ɗaya ɗayan kuma na kanta tace “Oh my God…” kafin kuma kamar wacce aka zabura ta fara tafiya cikin gaggawa zuwa wajen. Take Papa ma ya mara mata baya cikin tashin hankali. “Bring him inside NOW!!” ya umarci Mecheal......A can waje kuwa zuwa lokacin ruwan har ya fara ƙarfi sosai. Shi kuwa John har yanzu a zaune yake cikin motar, idanunsa a rufe tsayin lokacin da Mecheal ɗin ya fice, yana jin muryar Yasmine a zuciyarsa fiye da komai data faɗa masa sunanta _YASMINE_ Wani dukan gaban motar yayi tare da furta kalmar. “Don’t leave…” ya faɗa da ƙarfin kamar yana magana da ita. “Don’t disappear again…” “JOHN!!” Muryar Papansa kai tsaye ta katse shi daga ɗan ƙarin haukar daya kusa kama shi a cikin motar. A hankali ya buɗe rinannun idon nasa da suka sanja sosai zuwa tsananin fushi da ɓacin rai, kai tsaye ya kalla ta inda muryarn Papa'n nasa ke fitowa. Kai tsaye idanunsa suka sauƙa akan Papa'n nasa da Madame Victoria tsaye cikin ruwan, Fuskar Papa cike da fushi yayin da fuskar Madame Victoria ke cike da tsoro da alamun kuka. “Get out of that car NOW!” Papa ya sake katse tunaninsa cikin tsawa. Amma John ko motsi be yi ba, sema kallarsu da yayi da Idanunsa da suka yi zurfi sosai. Kawar da kansa yayi daga kallonsu ya furta. “I’m not coming in.” Take wurin ya ɗauki shiru tamkar wacce mutuwa ta gimla wurin se ƙarar ruwan saman da ke sauƙa kawai in banda shi kuwa tamkar wacce duniya ta tsaya haka suka sanƙame yawa kuma ka. Ita kuwa Madame Victoria wani dafe ƙirji tayi tana jin kamar numfashinta ze rabe. “John… my son… please…” muryarta na rawa ta soma ƙoƙarin lallashinsa. Amma John ya girgiza mata kai a hankali, kafin cikin muryan da yayi ƙasa sosai yace da ita. “Not now…” Papa ne ya matso jikin motar motar sosai ya riƙe murfin dake a buɗe ya ce. “Are you losing your mind?! What is wrong with you?!” kallonshi a hankali John ɗin yayi yana jin inda abinda yafi losing to yayi karon farko cikin wannan lokacin, ga Idanunsa da suka yi ɗan yi laushi suna ɗan zurbawa ciki. “I saw her…” ya faɗa a hankali. Papa ya tsaya cak. “Who?!” ya jefa masa tambayar daya saka John ƙarasa jan idanunsa ya kulle kayansa na ɗan wasu daƙiƙu, kamar ba zai yi magana ba don har sun fitar da rai kana yace. “Someone I don’t even know… but my heart does.” Shiru ya sake game wajen ga ruuwan saman dake sauƙa a kansu suna tsayen amma basu damu ba. Sai ma Madame Victoria data sake matsowa a hankali tace. “John… come inside first… we will talk later…” Amma ɗan bawan ALLAH 'n nan ya sake ɗan girgiza musu kai. Kafin ma gaba daya ya danna window ɗin motar yana rufe ta a hankali. “Take me home…” ya faɗa ga Mecheal. Mecheal ya yi saurin kallon Papa da Madame Victoria. Papa ya yi ƙwafa cikin fushi. “Let him go… but this is not finished.” Madame Victoria kuwa ta tsaya kawai tana kallon motar tana tafiya. Idanunta cike da hawaye ta ce. “Jesus… please guide my son…” Wata nannauyar ajiyar zuciya duk su ukun suka saki lokacin da suka ga ya kashe motar daidai wata rumfar da dama shi shi kaɗai ne ke parking ma car nashi idan yaso, ko yana cikin rigima irin haka yace dole se yayi driving da kansa... Yafi ƙarfin sama da minutes kana ya fito da umbrella a hannunsa ya shige ya bar iayayen nasa tsaye. Saurin rufa masa baya suka yi bayan sun ɗan sake yin wata magana da Mecheal, suna shiga suka tarar da bai ma tsaya a parlourn ma, Madame Victoria cikin tashin hankalin da har yanzun take a ciki take cewa Mr jef deefer kawai ya tura John ɗin wata ƙasar ko ma kawai ya koma bakin aikinsa wannan tashin hankali da bala'in sun gama isarsu haka. Sosai ya gamsu da shawarin nata don haka kai tsaye yayi magana da wurin aikinsa suka tabbatar masa da lallai zuwa dare John ze samu ƙiran gaggawa, da wannan suka sami nutsuwar ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin salama, Hakan kuwa aka yi ƙiran ya same shi wajajen sha biyun dare kan cewar lallai umarni ana son ganinsa 6:pm a airport. Duk da yanda zuciyarsa take cike da ƙunci da kuma damuwa haka dole ya amsa ƙirar, koda ya isa kai tsaye ƙasar Ethiopia ma suka tura shi akan cewar ze sake woras da wasu yara yadda ake control na jirgi idan ya shiga wani haɗari har tsayin 3 months. A lokacin da suke isar masa da wannan sakon ji yayi kamar ya fasa ihun tashin hankali, yana jin kamar ba zai iya tafiya ya barta har na tsayin wannan months ɗin ba, sedai baya da yacce zeyi yana gani aka fara masa duk wasu cike cike da shirye shiryen tafiyan, kasancewar ba shi ma yau a matsayin passinger's ze fito. 7:00 jirginsu yayi landing zuwa kasar Ethiopia. 2:50 na yamma jirgin daya ɗauka John yayi dirar angulu a ƙasar Ethiopia. A wannan babban airport nasu na Addis Ababa Bole International Airport cikin nutsuwa, amma har lokacin John be gama jin ya dawo daidai ba, ya jingina bayansa da kujerarsa idanunsa lumshe zuciyarsa na bugawa da ƙarfi kamar tana son fito wa waje. _Mun iso Ethiopia…_ ya faɗa a ransa a hankali. Lokacin da ƙafafunsa suka taɓa ƙasar, sai ya ji kamar duniya ta sauya masa gaba ɗaya. Wani yanayi daban, iska daban… komai sabo ne a gare shi. Ya bi sahun mutane cikin nutsuwa, amma a zahiri zuciyarsa cike take da tambayoyi. Me zai tarar a gaba? wa zai same shi?, da ya fito ɓangaren “Arrival”, sai ya tsaya cak. Idanunsa suka fara zagaye ko’ina. Mutane da yawa ne wasu suna dariya, wasu na rungumar juna cike da farin cikin kewar juna, wasu kuma na ɗauke da allo mai rubutu. A cikin wannan hayaniyar, sai idonsa ya sauƙa a kan wani mutum tsaye cikin nutsuwa, yana riƙe da takarda. A jikin takardar an rubuta sunansa da manyan haruffa, zuciyarsa ta ɗan tsaya na ɗan lokaci kafin ya ɗan ja numfashi, sannan ya nufi mutumin a hankali. “Are you…?” mutumin ya tambaya da murmushi. tsayuwarsa kawai ya gyara yana shaƙar iska ya fesar kana ya jinjina kansa tare da fadin... “Yes… I am.” cikin girmamawa mutumin ya amsa jakarsa yana me furta.“Welcome to Ethiopia Sir” Kalmar ta sauka a kunnensa kamar wani sabon babi na rayuwa. Gaba mutumin yayi yana mara masa baya zuwa mota mai kyau a waje. Yayin da yake shiga, ya juya ya kalli airport ɗin da yake jin kamar ita ce ƙasar da zata iya canza rayuwarsa ko shiga tsakannsa da farin cikinsa. A natse ya shiga motar kana driver ɗin yaja motar ta fara tafiya cikin titunan Addis Ababa, lumshe luhu-luhun idanunshi kawai yayi yana ƙara buɗe su, daidai kuma lokacin ƙira ke shigo wayarshi amma bai buɗe idon ba bai kuma ɗauka ba. Har motar nasu ta tsaya gaban babban hotel mai ƙayatarwa nn Ethiopian Skylight Hotel. Wani kayatacce fitaccen hotel ne dake kusa sosai da airport ɗin, wanda yake da wani mahaukacin tsaruwa da kyau tamkar wata duniya ta daban ce. A hankali ya fara ziro fararen sawayensa yana kallon ginin wajen dake fidda wani sanyi mai daɗi, kafin waya daddadar iska ta bugi fuskarsa, ƙamshi mai kyau ya cika hancinsa. Lafiyayyen hotel ne me rai da lafiya suka sauƙe shi, tun da ya isa a ranar be yi komai ba haka ma washe gari, se a ranar sa ta uku kana zai fita koya musu training ɗin. Washe garin ranar daya kasance ranar sa ta uku a garin zai fita, su kuwa matasan suma kaf sun gama shirinsu suna nan a filin jirgin saman suna tsaye cikin tsari suna jiran isowan malamin nasu. Babu jimawa se gashi ya iso cikin nutsuwa, sanye da kayan pilot masu kyau. Idanunsa sunyi matukar nuna ƙwarewa da ƙwarewar shekarun da ya shafe yana tukin jirgin. JOHN ahankali yake koyar da su yadda ake sarrafa jirgi a cikin haɗari a wani ɗakin horo na musamman nan cikin airport ɗin na Ethiopia, inda ɗaliban suke zaune cikin nutsuwa, kowannensu da littafi a gabansa. A gaban su kuwa akwai wani magzine ɗin dake haska musu komai. A natse ya sake isa ya tsaya a gaban magzine ɗin, ba tare da ɓata lokaci ba ya zana siffar jirgi a cikin iska, sai ya zana girgizar iska mai ƙarfi a kusa da shi. A wani irin natse cikin harshen English ya ce. “Wannan…” ya fara da murya mai natsuwa, “Shi ake kira turbulence.” kafin ya juya yana kallon su yace. “Idan jirgi ya shiga irin wannan yanayi, abu na farko daya kamata ka fara sani shi ne kada ka firgita.” Ya ɗan dakata yana kallon idanunsu ɗaya bayan ɗaya, kamar yana auna ƙarfin zuciyarsu. “Duk inda kalmar Pilot take to ku sani ba kalma ce ta tsoro ba… a ahhh kalma ce ta wanda yake iya sarrafa tsoron sa ne.” Sai ya danna wani maɓalli, allon ya canza zuwa hoton girgizar jirgi a cikin gajimare. “Ku lura,” ya ci gaba, “kar ku yi ƙoƙarin yin fighting da jirgi. Ku bari ya bi iska kaɗan… ku riƙe control a hankali.” Ya nuna musu da hannunsa yadda ake riƙe control yoke ɗin kana yaci gaba da cewa.“Kar ku ja da ƙarfi, haka kar ku turawa ƙasa da sauri, small movements steady control.” se ɗan fesar da wata iska kana yaci gaba da faɗin. “Ku saurara da kyau sosai,” John yaci gaba da murya mai ƙarfi amma cike da kwarin gwiwa. “Control na jirgi ba ƙarfi bane, hankali ne.” ya sake nuna musu cikin jirgin, yana bayyana yadda ake rike control yoke a hankali, ba tare da firgita ba. “Idan kuka ja sama da ƙarfi, jirgi zai iya rasa daidaito. Amma idan kuka sarrafa shi a hankali… zai bi umarninku kamar yadda kuke so.” Ɗaya daga cikin ɗaliban ne ya ɗaga hannu alamar yana da tambaya da ka John ɗin ya bashi izinin tambayar. “Sir, idan jirgi ya fara sauka da sauri fa?” John ya ɗan murmusa duk da cewa murmushin a wurinsa ba abu bane me sauƙi amma ya murmusa ɗin. Kana ya kalla matashin yana sake juya zuwansa ga allo, wani layi ya sake zana musu mai gangara kana yaci gaba da cewa. “Ku gyara daidaito a hankali. Kada ku yi overcorrection. Idan kuka yi sauri… zaku iya jefa jirgi cikin haɗari mafi muni.” Sai ya nufi wani simulator da ke gefen ɗakin. “Ku zo.” yace kawai dasu suna binsa ɗaya bayan ɗaya. Ya zauna, ya kunna wata na’ura. Nan take aka nuna musu kamar suna cikin jirgi a saman iska tana girgiza shi. “Ku kalla yanzu.” Hannunsa ya riƙe control cikin nutsuwa, yana motsawa kaɗan-kaɗan. Jirgin yana girgiza… amma bai fita daga daidaito ba. “Kun ga?” ya ce cikin nutsuwa kamar musulmi ba Christian ba. “Ba ƙarfi bane… balance ne.” Sai ya miƙa wa ɗaya daga cikin ɗaliban control ɗin yace. “Gwada.” Yaron ya fara da ɗan tsoro… hannunsa na rawa. John ya dafa kafadarsa a hankali cikin lallausan sautu yace. “Breathe… ka ji jirgin… kar ka yi masa faɗa.” A hankali yaron ya rage firgita ya fara sarrafa jirgin. Girgizar ta ragu kaɗan. Inda gaba ɗaya sauran ɗaliban suka fara jin wani sabon ƙarfi a zuciyarsu na kamasu. Domin dukansu sabbin matukan jirgi ne amma tsoro ya sa suka janye.John ya ɗan ja baya yana kallon su da wani murmushi mai zurfi a wannan karon ma yace. “A yau,” se kuma ya ɗan dakata kafin ya numfasa ya ce, “Ba wai kawai kun koyi yadda ake sarrafa jirgi ba ne…” Ya ɗan ɗaga hannu yana nuna ƙirjinsa yaci gaba da cewa. “Kun fara koyon yadda ake sarrafa kanku ne daga tsoron tuki.” daga nan darasin nasu ya ranar ya ƙare se washe gari kuma. Kai tsaye daga nan garin ya ɗan zagaya sosai sai can dare ya koma logedge ɗinsa. Seda yafi ƙarfin 1 months yana koya musu kana ya shirya fita dasu outing wanda shi yake son suyi tuƙin da kansu. Sha biyu daidai ya sake fitowa wannan karon kam cikin shigar cikakken pilot nashi, kai tsaye cikin ɗakin simulator ya isa, duk suna suna shirye cikin uniform ɗin su na cikakkun pilot. Gaba ɗaya manyan wajen su wajen goma sha biyar ne suka fito tare da John kowa fuskarsa washe da kyakkyawan murmushi. Har gaban katon jirgin suna isa suka zazzauna. Shi da kansa ya shiga ya ja jirgin, tafiyar tsayin kilomita biyar suka yi suna nufar wani yanke daban iskar sararin samaniya ta sanja ta soma bugun jirgin, gajimare masu duhu suna mamaye komai. Take jirgin ya soma girgiza sosai, ƙarar iska na cika kunnuwan su gaba ɗaya, inda nan take hankalin gaba ɗayansu ya tashi, a natse John ya kai dubansa gare su tare da cewa. “Wannan ba wasa bane,” ya faɗa cikin nutsuwa kafin yaci gaba da faɗin. “Ku nuna min abinda kuka koya.” yayi maganar tare da miƙa control ga wani ɗalibi mai suna Daniel. Da fari Daniel ya riƙe control ɗin da ƙarfi, yana ƙoƙarin nuna jarumta. Amma take jirgin ya ƙara girgiza hannunsa ya fara rawa cikin muryan tashin hankali ya kai dubansa ga John numfashinsa na rikicewa yace. “Sir… I… I can’t…” ya fara faɗa cikin tsoro. Jirgin a cikin simulator ya fara karkata gefe. “Daniel, ka kwantar da hankalinka,” John ya faɗa cikin murya mai sanyi, amma tsoron ya riga ya kama shi. “Zai faɗi! zai faɗi!” Shi ne kawai abinda Daniel ɗin ke fadi yana ƙara rikicewa, yana jan control ɗin da ƙarfi. Jirgin ya ƙara fita daga daidaito. Sauran ɗaliban suka fara kallon juna cikin firgici. Sai John ya matsa kusa da shi cikin sauri amma ba da hayaniya ba. Ya dafa kafadarsa a hankali yace.... “Daniel… kalle ni.” Daniel bai so ba amma a hankali ya ɗago idanunsa. “Numfashi,” John ya ce masa a hankali. “In… out…” Ya nuna masa da hannunsa yadda zai yi. A hankali… Daniel ya fara bi. Numfashinsa ya fara dawowa daidai. “Good,” John ya ce cikin kwarin gwiwa. “Yanzu… ka ji jirgin. Ba zai yaƙe ka ba… kai ne za ka jagorance shi.” Ya riƙe hannun Daniel a kan control ɗin ba don ya kwace ba, sai don ya taimaka masa. “Ka rage ƙarfi… small movement…” A hankali Daniel ya sassauta riƙon sa, Jirgin ya daina karkata sosai. Girgizar tana nan… amma yanzu akwai control. “Ka gani?” John ya ce da murmushi kaɗan. “Ba hadarin bane matsala… tsoro ne.” A ƙarshe, jirgin ya dawo cikin daidaito, shiru ya mamaye jirgin. Daniel ya jingina bayansa da kujerar jirgin, jikinsa cike da gajiya… amma idanunsa sun cika da wani sabon ƙarfi. “I… I did it…” ya faɗa a hankali wanda hakan ya saka John ɗan jinjina kai. “Eh. Ka yi.” Sai ya juya ya kalli sauran ɗaliban yace. “Ku ji wannan da kyau” ya ɗan ɗaga murya kaɗan. “Idan kuka bari tsoro ya jagorance ku!… To kuwa tabbas zaku rasa komai.” Ya ɗora hannu a ƙirjinsa kana ya sake cewa. “Amma idan kuka sarrafa shi, ko hadari mafi muni ba zai karya ku ba.” daga nan suka dawo zuwa ainihin inda suke cike da alfahari da jarumta, suna sake yabama John da sake bashi wani irin girman da idan ka gani zai baka mamaki, don wannan ɗin duk cikin shirin sane shi ya shirya hakan. Nan yaci gaba da basu horo me kyau inda tun daga wannan rana, ba kawai Daniel ba… dukkan su sun canza... ♡ Haka al'amurra suka ci gaba da wakana tare da shuɗewa tuni suka sake samun wata sabuwar kwarewar da babu dar ko shakkar tuƙin cikin kowanne irin muni ko haɗarin wuri. Sun san duk wasu matakan kariyar da zasu bama jiragensu cikin aminci, misali kamar irin suna cikin tuƙin nan wani yaki ya tashi irin na ƙasa da ƙasar nan to zasu iya kuɓutar da jirginsu ba tare da an ɓaro shi daga sama ba kamar yadda ake ɓaro wasu ba. Alhamdulillah kafin ka ce sega ƙasar Ethiopia ta sake bama John wani irin girma da ƙarin matsayin da ba iyaka piloting bane, zai iya zama special pilot ga ko wacce ƙasa idan yaso, wanda dama kuma akwai ƙasa shen da suke harinsa ba kaɗan ba.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 _Dont forget to vote, follow and comments_ *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 11 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Duk yammacin duniya tun da yazo ƙasar a cikin Hawassa yake ƙarasa darensa, Hawassa shima duk a cikin hotel ɗin ne se dai ɓangaren ruwa ne kawai, amma irin pool pool ɗin nan kashi yafi ɗari. Ga shi kaɗai zaka ruwan na walƙiya kamar madubi tana haskaka kasan ƙarƙashin ruwan, ga gaba ɗaya wurin cike yake da wata irin natsuwa da ƙamshi irin na wuraren hutawa haka. Inda ko wanne pool yake kewaye da kujerun shakatawa da bishiyoyi masu mugun kyau da tsaruwa. Kamar kullum yau ma ahankali John ya fito sanye da light short da t-shirt mai laushi, yana tafiya a natse amma cikin ransa fal yake da tunani da kuma kewan tsiwan ta, masifanta da yadda take sarrafa cikul ɗin bakinta tana wani motsa shi idan tana masa jaraban, wanda hakan shi ne abu na farkon daya fara motsa duk wani abu a kanta, shi ne wannan yanayin da fuskanta ke shiga, idonunta kuma su wani janye irin mutum yana tsaka da masifan nan. Wanda duk yau ɗin haka ya tashi gaba ɗaya da so da ƙaunar ganin nata in yaso ko marin ne ta sake bashi, ko masifan ne ta masa yana son ganin ta da kuma ɗaukar duk wani hukuncin da zata ci gaba da bashi indai zai ci gaba da ganin koda fuskan tane. Haka zuciyarsa ke cike da tunanin da har ma bai lura da cewan ya isa bakin pool ɗin ba. Wanda se a sannan ya ankare yana jan wata kyakkyawar blue nd white chiar ya zauna yana fuskantar ruwan. A hankali ya sauke ƙafafunsa cikin ruwan inda kai tsaye wani sanyi mai daɗi ya ratsa jikinsa. Wanda dole ya saka shi lumshe ido na ɗan lokaci. Iskar da ke tashi daga bakin Hawassa Lake ɗin na kaɗawa a hankali, tana motsa gashin kansa. Ana jin ƙarar tsuntsaye daga nesa, da kuma dariyar wasu mutanen daga ta gefen pool ɗin alaman suna cikin nishaɗi. Amma shi… ya kasance cikin duniyarsa. “Why am I even here…?” ya furta a hankali cikin turanci kamar yana magana da kansa. Tunanin duk abin da ya faru ya fara dawo masa kai, yadda aka tilasta masa tafiya zuwa Ethiopia, yadda ya so ya ƙi amma aka matsa masa. Ba shi ne ma zai tuƙa jirgin ba, amma aka ce dole sai saboda zai bada horo ne, shi yasa yayi zuciya da ƴan gidan nasu baki ɗaya, yaƙi yin waya da kowa tun da yazo, wanda se suna suka yi tattaki suna zuwar masa har karo biyu, ganinsa cikin nutsuwa kamar babu alamar komai tattare dashi ya saka su farin cikin da har suke jin kamar zasu iya sallamawa ƙasar shi yaci gaba da mata aikin kawai. Ahankali yaja wani numfashi Kafin ya buɗe ido, ya kalli ruwan pool ɗin da ke motsi a hankali saboda ƙafafunsa dake ciki. Ta cikin ruwan ya ga hoton kansa yana motsi amma ba irin John ɗin da ya sani ba ne, A ahhh wannan John ɗin ya gaji, wannan John ɗin ya rikice komai na nemar kwace masa kafin daren jiya zuwa wayewar yau. A hankali ya ɗago da kansa ya kalli sararin sama mai shuɗi. Yana tsaka da wannan tunanin wata murya ta katse masa tunanin nasa ta hanyar furta.... “Nice view, right?” Wanda dole ya saka shi juyawa a hankali ya na kallar kyakkyawar matashiyar budurwan dake tsaye a bayan sa, sanye da farin riga mai sauƙi, gashinta gaba ɗaya zube a kafaɗunta da iska ke kada shi. Idanunta suna cika da natsuwa sosai. Ahankali John ɗin ya ɗan gyara zamansa sedai fuskar nan babu alamun rahama ko annuri ya ce. “Yeah… it is.” a natse ta zo ta zauna a kusa da shi, amma ba kusa sosai ba. Ta sauke nata ƙafafun cikin ruwan itama wani shiru ya ratsa wurin, kafin ta katse shirin ta hanyar ce wa. “Sometimes… people come here to forget things.” John ya ɗan motsa kaɗan cikin sautin da bai fita da kowacce kalan sauti ko hayaniya yace. “And sometimes… they come here because they have no choice.” sai ta juya ta kalle shi sosai, kamar tana son fahimtar abin da ke zuciyarsa. “Which one are you?” Ya yi shiru na ɗan lokaci komai be ce da ita ba. Kafin ya kalla ruwan a hankali ya ce... “I don’t even know anymore…” Ahankali iskar dake kaɗawa taci gaba da kaɗawan da ya saka ruwan pool ɗin ya motsa shima, ga uwa uba hasken ranar dake haskawa yana faɗuwa a kan Hawassa Lake ɗin, yana ƙara masa kyau kamar wani zane. Ahankali zuciyar John ta fara jin kamar wani sabon labari ne yake shirin farawa shima, labarin da bai san inda zai kai shi ba.Iskar mara ƙarfi ta sake kadawa a gefen swimming pool ɗin, tana motsa ruwan a hankali. John ya ɗan sunkuyar da kai, kamar yana tattara kalmomin da zai faɗa. Wanda ya saka budurwar ta kalle shi da nutsuwa, sannan ta yi murmushi kaɗan ba tare da damuwar komai ba tace. “Sunana Almaz,” ta faɗa a hankali. John ya ɗaga kai ya kalle ta kafin a wani irin hankali ya ce da ita “John.” se shiru ya sake ɗaukan wurin amma wannan karon ba irin na farko ba ne ya ɗan fi sauƙi. Almaz ta ɗan karkata kai kai tsaye ta jefa masa tambayar, “Kana da wanda kake tunani ko kewa ko?”don tashin farko a kallonsa ta karanci hakan, wanda ya saka John ɗan motsa bakinsa kaɗan, se ya sama kansa da murmusawa don yau ɗaya ze fara firan yasmine da wata. Ahankali ya yaci gaba da motsa ƙafafunsa cikin ruwan kamar komai ba zai ce mata ba don ita har ta fidda rai ma kana kamar daga sama taji yace... “Eh… akwai wata. Sunanta Yasmine.” Da jin sunan, Almaz ta ɗan yi shiru, amma ba da wani irin kishi ko damuwa ba. Sai dai wani irin fahimta da ta bayyana a fuskar ta. “Ka na sonta sosai?” John ya kalli ruwan pool ɗin, ƙafafunsa suna motsa shi a hankali kafin yace. “Fiye da yadda zan iya bayyanama duniya…” wani kallo me tattare da zallar fahimta ta masa, kana ta sake cilla masa tambayar. “Are a Muslim yasmine ba?” Cak ya dakata domin kuwa kalmar Muslim ɗin wani irin duka tama ƙirjinsa. Wanda dole ya saka shi yin wani irin shiru kamar ruwa ya cinye.Almaz ta ja numfashi a hankali tana kallon nesa inda Hawassa Lake ke haskawa. Kafin cikin nutsuwan da muryanta ke da yaji tashin maganarta tana cewa. “Wani lokacin rayuwa tana kawo mana mutane biyu ne cikin duniyarmu, ɗaya da zuciyarmu ke so… ɗaya kuma da rayuwa ke ba mu don ta koya mana wani abu.” se ta dakata cak wanda ya saka john ɗaga kai ya kalle ta sosai kafin shi ma ya jefa mata tambayar...“Ke wa ce ce?” gyara zamanta Almaz da wata ƴar siririyan dariya kaɗan mai cike da natsuwa ta ce. “Ni? Ba zan zama matsala a rayuwarka ba, John.” se kuma ta sake yin shiru kana tace. “Zan iya zama ƙawa kawai.” Wani shiru yayi kamar me tunani ko nazarin wani abu kana ya miƙa mata hannu kawai. Almaz ta kalli hannun da John ya mika mata na ɗan lokaci, kana ta girgiza masa kai tana murmushi alaman ba zata kama ba tare da furta. “A friend sounds good kawai.” A wannan lokacin, wani abu ya sauya. Ba soyayya ba, haka ba rikici ba, sai dai wani irin sabuwar fahimta ta abota mai tsaftar data shiga tsakaninsu. Daga nan suka zama good friend ita da John, wanda mafi akasari anan suke yawan haɗuwa, abu na farko daya fara jan hankalin John ga yasmine yadda take kunna wani abu a cikin wayarta me kama da waka, amma kuma yasan ba waƙar ba ce duk da kasancewar ba da Yaren da yake ji bane, amma yasan ba waƙar bane. Haka zai ga ta lumshe idonta tana bin sautin abin cike da wata irin nutsuwa da bin harrufan ɗaya bayan ɗaya, se dai be taɓa gigin tanka mata ko mata shishshigi ba duk da abin na birgesa, don har so yake tazo don yanzun ta kai ta kawo idan bata zo ba tsintar kansa yake cikin ƙuncin daya rasa gane masa, kamar yanzun daya da yake a zaunen da tsammanin ko zai ganta, ga wayarta baya shiga kwata kwata yau tsayin 3 day's kenan rabon daya saka ta cikin idonsa... Ahankali ya ɗago kansa yana fesar da wani numfashi me zafi, ya kwashe sama da 50 minutes zaunen da yake, fararen zaratan sawayensa zube cikin swimming pool ɗin. Amma babu ita babu dalilinta. Ahankali yaci gaba da karkaɗa ƙafafunsa cikin ruwan, bayan 40 minutes ɗin aƙalla ya sake kwashe sama da 30 minutes ɗin data rufama 40 ɗin baya awurin yana jiran yaga ta inda zata ɓullo amma babu ta babu alamar nata. Wani irin shiru kawai yayi yana sake jingina bayansa da kujerarn hutawan dake wurin. Ahankali iskar dake kaɗawa take sake shiga cikin jikinsa da shafar fuskarsa kamar tana son kwantar masa da hankali.... Hannunsa ɗaya na riƙe da glass na juice ɗin da be jima da ɗauka ba, ɗayan kuma ya jingina a gefen kujerar. Ahankali yake ta ƙoƙarin ya danni kansa a kan wani irin fushin da yake jin na taso masa,amma duk da yana ƙoƙarin dannewar hakan be hana har fuskarsa fidda yanayin ba. Gaba ɗaya yaji wurin ya haɗa masa wani irin shegen yanayi be cike da cunkushewar zuciya, duk kuwa da yanayin dake bayyana tsantsarn nutsuwar da ƙaton beach ɗin ke bashi amma banda yau ɗin nan kam, buɗe idonsa yayi yana ɗan taune jajayen lips nashi tare da dafe saman goshinsa.Yanda ya dafe goshin nasa kaɗai ya isa baka tabbacin ka fahimci cewar kanne ke masa ciwon, musamman idan kai duba da yadda ya dafe kan da tafin hannunsa. sake lumshe tsumammun idanunsa yayi yayin kamar wani abu na nemar hanyar kassara rayuwarsa ne gaba ɗaya, ahankali cikin daure ciwon da kan ke masa ya sake taune lips nashi da ɗan ƙarfi tare da nutsa hannuwansa cikin tulin sumar dake kwance luff luff saman kan.ya shiga chakudawa da duka hannuwansa kafin a wahalce ya miƙe yana tangaɗi tamkar ɗan maye yana nufar hanyar komawa lodge nashi. Cikin sassarfa ya kutsa kansa cikin lafiyayyar lodge ɗin yana kama hanyar bedroom nashi. Cikin bala'in zafin zuciya ya nufi part 0122 yana haɗe baki ɗaya abubuwansa wuri guda yana jin dole a yau se ya bar ƙasar Ethiopia ɗin tun da bata ubansa bace. A irin wannan masifaffan yanayin da yake ciki ya ci gaba da shirya kayansa kamar ma a hargitse. Kafin kace me cikin ƙankanin loƙaci har ya buƙaci barin ƙasar duk kuwa da cewar sai nan da 10 days zai tafi, amma baki ɗaya yaji gida kawai yake da buƙatar komawa domin sammm zuciyarsa ba zata ci gaba da ƙuntata irin haka ba, wanda a zahiri da za'a iya buɗe zuciyarsa da kuwa tabbas kun girgiza da ganin abubuwan dake ɗan ƙare a cikin ta. A loƙacin 4:00pm na yamma ne, amma haka yasa dole aka barshi yabi jirgin da zai tashi aka keta hazo dashi yau ma a matsayin passinger's yana barin kasar baki ɗaya.... 6:15pm na magrib jirginsu ya sauka a airport ɗin Nigeria dake lagos. Inda filin jirgin yake cike da hayaniyar mutanen da wasu sun zo ɗaukar iyaye ne wasu yayye wasu mataye wasu ya'ya. Haka mutane keta famar shiga da fita wasu na runguma da ƴan uwansu, wasu kuma na hawaye na farin ciki. John ya sauko daga jirgin, gajiya na bayyane a fuskarsa bayan duguwar tafiya daga Ethiopia. Hannunsa riƙe da jakarsa, amma zuciyarsa ba ta kan tafiyar ba… tana kan abu guda...Yasmine....Almaz. lokacin da sunan yasmine ɗin ke ratsa zuciyarsa ji yayi kamar wutar da ba ta taɓa mutuwa ba ce take ƙoƙarin ruruwa. Kansa ya ɗan girgiza jin kamar bugun zuciyar ba daga iyaka ambatar sunan nata kawai ba ne, kamar dole tana cikin airport ɗin ne, don duk lokacin da zai ganta irin wannan bugun zuciyarsa ke masa.... Tamkar wanda aka ce waywaya gajiyayyun Idanunsa suka sauka kanta tana tsaye ta bada baya kaɗan amma kuma ana ganin fuskarta, tana sanye da hijabi fari mai tsafta, idanunta zube tana kallon masu fitowa tamkar tana jiran wani. Da wani irin ƙarfi zuciyar John ta buga har besan lokacin da bakinsa ya ambata sunar. “Yasmine…” ya furta a hankali kamar yana tsoron aikata wani mugun kuskure ne..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 _Dont forget to vote, follow and comments_ *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 12 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Cak ta dakata da alama taji sadda ya haɗa sautukan fitan sunayen nata, don haka ta ɗago kanta a hankali ta masa wani ɗan kallon fishaa da slowly eyes nata kafin ta janye, batare da tayi ko irin alamun nuna ta san shin nan ba tayi gaba abinta daidai Daddy'nta ke ƙarasowa ta rumgumoshi cike da missing na kewar shin da tayi wajen One months. Ko da ta sake ɗagowa Idanuwansu ne suka sake sarƙewa wanda yanayin fuskarta ya sauya nan take daga farin cikin da take a ciki zuwa tsauri. Shi kuwa kai tsaye ya tuna mari na farko, mari na biyu, kamo muggwan kalaman da take faɗa masa duk lokacin da zasu haɗu da suka fi masa mari zafi. Ahankali ya taka ƙafafunsa da nufin isa inda take, amma kafin ya isa ta sake rungume Daddy'n nata cike da tsananin farin ciki ta ce. “Daddy!, I miss you so much” ɗan bubbuga bayanta ya shiga yi cikin kulawa da SO me ƙarfi sosai ya ke cewa. “I miss you more than I thought ambasaja shalalen Daddy'nta I miss you...” daga nan ta kama hannunsa suka nufi motar da ita kawai tazo ɗaukarsa, don ma babu wanda ya san da zuwan nashi se ita kaɗai, John da bai motsa ba na ɗan lokaci ne zuciyarsa tayi saurin ankarar dashi akan cewa kada ta sake ɓace maka. Ai kuwa da wani kalan sauri ya ɗauki jakarsa ya bi su a hankali daga nesa. Ba ya son su gane amma ba zai sake barinta ta ɓace masa haka kamar kullum ba, suna fita daga filin jirgi suka shiga mota. John ya tsaya cak... “Damn…” ya furta kamar a ɗan fusace sai ya hango taxi, ya ɗaga hannu da sauri. “Follow that car,” ya faɗa da gaggawa bayan ya shiga, driver ya kalleshi da mamaki, amma ya tada motar John ma nuna masa alamun yabi motar, take kuwa taxi ɗin ta rufa musu baya Idanun John na manne a gaban motar nasu don karta ɓace musu, ga zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. “Wannan karon… ba zan sake rasa ki ba My Unknown beloved,” ya faɗa a ransa. Bayan wasu mintuna motar su Yasmine ta shiga wani hadaddiyar anguwa mai me shegen kyau da natsuwa, in da ma she basa da wata tazara ta a zo a gani tsakaninsu. Ahankali yaga motar ta tsaya a gaban wani gida mai kyau. John ya umarci direban ya tsaya daga nesa shi ma, ahankali ya fito daga motar yana kallon yadda Yasmine ta fito, tana taimakawa mahaifinta. Tana wata irin dariya…irin dariyar da bai taɓa ganinta tana yi masa ba. Wani abu me kama da kwanciyar hankali yaji yana kamasa na ganin gidan nasu kawai, daga nan ya saka mai taxi ɗin fita a anguwan ya faɗa masa anguwansu ya kai shi, duk da kasancewar su estate ɗin nasu taxi baya taɓa shiga, amma kuma ganin John ne ya saka su barinsa har bakin mension nasu. Kuɗin da ba ma canjin naija bane Ya bashi, wanda idan ya sanja yana iya zame masa 100k, don haka ya tafi da murnan sa yana binsa da fatan alkhairi a cikin rayuwarsa. Tun kafin ya isa ga ƙofar gidan nasu ya soma jin sautin kiɗa mai ƙarfi da ihu na tashi daga cikin gidan. Nan take yanayin fuskarsa ta sauya zuwa na ɓacin rai, idanuwansa kuwa har wani ƙanƙancewa suke cikin tsananin ɓacin rai. Wato gidan bayan baya nan ma kura ta mutu ai wasa suka mayar dashi, bayan sun san babu abinda yafi tsana fiye da wannan sokon kiɗe kiɗen da rawo rawo zuwa party birthday wanda ko jelly sedai ta saci hanya, ji yayi gaba ɗaya suna nemar ɓata masa ɗan sauran farin cikin daya samu. Kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba ya taka zuwa ƙofar ya buɗe da ƙarfi. Har da wata kalan sassarfa yake haɗawa, duk ma'aikacin daya gansa se kuga ya riƙe baki alamar yau da bala'i kenan. A lokacin da yake isa ainihin babban parlourn gidan abin da ya gani ne ya saka shi tsaya cak. Jelly ce tsakiyar maza da mata freind nata, tana rawa da juyi hannunta riƙe da kwalbar wine tana kwankwada wanda kallo ɗaya zaka mata kasan cewar tana cikin farin ciki sosai, tun daga yanayin yadda take tikar rawar ta cikin manyan yara maza da matan da suka cika ko’ina, wasu na rawa, wasu na dariya, wasu ma har suna riƙe da drinks. Kiɗa na tashi kamar gidan ba na iyali ba ne. Kowannensu cikin shigar shegun kaya irin nasu na Christian. Take yaji wani irin zafi na taso masa tun daga zuciyarsa. “JELLY!!!” ya daka mata tsawa a wani irin haukacen daya saka jelly yin wata irin katantanwa ta kusa hantsilawa, kafin cak ƙiɗan ya tsaya dariya ta mutu. Kowa ya juya yana kallonsa cike da tsoro don duk wasu sun san dokar John ɗin musamman ma wanda suke da kusanci sosai da Jelly ɗin,ita kuwa jelly da jikinta ke se a lokacin ta ɗago kanta tana satar kallonsa don ba ta yi tsammanin zuwansa ko kaɗan ba bare ganinsa. Numfashinta ne taji yana ƙoƙarin tsayawa ahankali kuma jikinta ya fara rawa, kafin cikin rawar muryan ta ɗan soma ja baya tana me ambatar sunan shi cikin ƙinƙinar da bata taɓa sanin cewar tana da ita ba. “J… John…” ta furta tana sake ja da baya har tana lafewa a jikin ƙawayenta, inda suma kowa ya lura da canjin yanayin nata, ga John ɗin da ko sake motsawa bai yi ba. Sai ma wani irin mugun kallon da yake jefa musu na tsananin gargaɗi. “What is going on here?” ya faɗa a ɗan tsawace cikin turanci mai nauyi. Ba wanda ya iya amsawa sai wani farin guy ɗin matashi daya motsa kaɗan kai da ganinsu kaga irin marasa jin nan kangararru kuma, wani ɗan munafikin murmushi ya saki yana cewa. “Hey bro, it’s just a” ai tun kafin ya ƙarasa abinda yayi niyar faɗin John ɗin yayi wani irin katse shi cikin tsawa kawai yace.. “Get. Out Everybody .” Makut kuwa ya haɗiye maganar nashi don ganin yadda John ɗin ya dawo lokaci guda kamar wani fusataccen zaki. Nan take tashin hankalin ganinsa hakan ya mamaye wajen. Kafin ɗaya bayan ɗaya suka fara zarar jiki suna ficewa ba tare da jayayyar komai ba. Wasu ma kuwa harda haɗawa da tuntuɓe saboda gaggawa. Jelly ta rage tsaye ita kaɗai… jikinta na rawa sosai. Ta kasa kallon idonsa cikin muryan tashin hankali ta ce. “I’m… I’m..sorry…” ta faɗa da ƙyar. Kafin a hankali ya fara takawa zuwa gare ta cikin kaushin murya ya sake ce da ita. “You disobeyed me.” ya faɗa da tsawar daya saka jelly ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa kawai wasu ruwan hawaye na sake cika mata Ido. “I said no parties.” ya ƙara faɗi. “I know…” muryarta na rawa ta faɗi tana sake cewa. “I’m sorry Joseph…” Wani shiru ne ya ɗan ratsa parlourn yama gaza cewa da ita komai kuma, daidai nan sega saƙƙowar takun sawaye nan daga saman benen, wanda jin shiru babu kida da iface ifacen ihun sune ya saka su fitowar suma kowa da nashi kwalbar giyar a hannu, haka suka fito Madame Victoria na tambayar. “Baby, what's going on? I heard your music stop.” aikuwa itama cak maganar nata ya tsaya cak ɗin lokacin da idonta suka sauƙa kan John. Tsit gaba ɗaya parlourn ya ɗauka wani irin yanayi na sauya gidan bama iyaka parlourn ba, kafin cikin muryan mamaki da kuma tsoro Papa ya furta. “John…?” ya ambata a hankali cike da mamakin ganinsa daya haɗe da wani irin tsoro. Domin kuwa babu wanda ya san zai dawo hasalin zuwar bazata ne kawai ya musu. Madame Victoria dake tsaye a gefe ce ta ɗan haɗiye wani yawu, kana ta yi kundunbalar furta. “You’re back…” ta faɗa a hankali. Amma babu wanda ya kuskura ya matsa kusa da shi. John ya juya ya kallesu a hankali. “Yes.” ya amsa gajere. Sautin muryarsa kaɗai ya isa ya sa nutsuwa ta koma tsoro. Idanuwansa suka sake komawa kan Jelly ya ce. “Clean this mess.” ya faɗa kai tsaye. Ta sani baya da buƙatar maimaita magana don haka Jelly ta gyaɗa masa kai da sauri, jikinta har yanzu na rawa. Mommah ce ta yi ƙoƙarin danne tsoronta tace “John, maybe we should” tun kafin tace komai ɗin ya ɗaga mata hannu kaɗan alamar tayi shiru kawai, don a dai yanayin da yake a ciki baya buƙatan kowa yace masa komai. Papa ne ya sauke wata numfashi a hankali me ɗumi yana sake ɓoye kwalban giyarsa a bayansa ba tare daya sake yunƙurin magana ba. Haka kowa ya ƙame su ka kuma yi shiru, ganin shirun yayi yawa ne ya saka Papa ɗan gyara tsayuwarsa tare da cewa. “No… I mean, we didn’t expect you” Da wani kallo kawai John ya bishi bai ce komai ba, amma kallon kawai da yake binsu dashi ya isa sanar musu komai, Mademe Victoria ta kau da idonta da sauri a kan sa, ta ɗan matsa kusa da Papa'n kamar tana ɓoye wani tashin hankali. Jelly ta ɗan ɗago kai… tana kallon iyayensu, ta lura da suma yadda tsoron John ya bayyana saman fuskarsu suma, Kuma ba wai kawai tsoro ba ne ta sani harda giyar daya kamasu suna sha, musamman ma Madame Victoria ta ita kwata kwata ya hanata sha. Ahankali John yaci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya. Idanuwansa har sun ɗan yi zurfi. “Is there something I should know?” ya tambaya a hankali. Babu wanda ya amsa, sai ɗan wani murmushin dolen da Papa yayi yana samu ya ɓoye kwalbar nashi cikin wani ɗan dub daya samu yana furta. “No. Nothing.” ya faɗa da sauri fiye da kima wanda ya saka Madame Victoria saurin gyaɗa masa kai tana cewa “Yes… nothing at all.” Amma kuma muryarta ta ci amanarta wajen bayyana ƙin bata damar bayyana gaskiyar. John ya ɗan matsa gaba kaɗan ya musu wani kallon daya saka dukansu zuciyarsu bugawa da sauri... “You’re lying.” ya faɗa kai tsaye, nan take Madame Victoria ta haɗiye wani yawu. Komai be sake ce musu ba ya juya ya nufi sama, ƙafafunsa na takawa a hankali… amma kowanne taku na ɗauke da wani irin nauyin da iayayensa suka haifar masa. Suna tabbatarwa da cewar ya gama hayewa sama Madame Victoria ta saki wani numfashi da ƙarfi. “Oh jesus…” ta faɗa a hankali Papa kam rufe ido yayi na ɗan lokaci.“John he’s back…” ya fadi a bayyanen daya saka jelly sake kallon iyayen nasu kamar a ɗan firgice tace “Me kuke ɓoye masa ne bayan party…?” ta tambaya a hankali. Amma babu wanda ya amsata. John dake tsaye saman bene yana kallon su daga sama bayan ya ji kamar shirunsu ya yi yawa ya saka shi dawowa. Saurin riƙo hannun Papa Victoria tayi tana sauƙe wata ijiyan zuciya tace.... “We can’t hide it anymore…” ta faɗa cike da kamar tsoro amma Papa ya girgiza mata yace “Not now… not like this.” Jelly ta sake kallarsu da mamaki tace. “Hide what?” Madame Victoria ta kalli ƙofar sama ta rage murya sosai tace. “His marriage…” wanda ya saka jelly buɗe ido sosai da sauri ta sake maimaita kalmar “Marriage for what?!” “To Deepika…” Papa ya faɗi wanda kai tsaye se cikin kunnuwan John dake tsaye har zuwa lokacin daga sama... Take Idanuwansa suka canza a bayyane ya maimaita “Deepika…?” Wani irin shegen murmushi na kwace masa. “So… this is what you’ve been hiding from me na yheeee.” *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 13 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Gaba ɗaya kusan a tare suka ɗaga kansu zuwa ga inda suka jiyo sautin maganar John ɗin. Kafin a hankali cikin nutsuwa ya ke sauƙowa daga benen, but at the same time cikin kuzari da taku irin na cikakkun mazaje, that confident masculine stride of a man da ya san worth ɗinsa. ƙarasa saukowansa cikin parlourn ba ƙaramin rikita iyayen nasa yayi ba, sai dai a nashi ɓangaren ba tare da ya ko kalli sashen da suke tsaye cirko cirko ba yayi wucewar sa ya buɗe ƙofar babban palourn ya sake ficewa kamar bai gansu ba ko bai san da su a palourn ba, da idanu duk suka bisa kowa da irin abinda ya ke saƙawa a zuciyarsa ga baki ɗayansu sun girgiza da irin kwantaccen ɓacin ran da suka hango daga fuskar John ɗin. Kai tsaye Mecheal na ganinsa yay hanzarin nufar wata rantsatstsiyar mota ya buɗe masa don dama zaman jiran hakan yake yasan doke se ya dawo,direct motar tasa ya nufa mai matuƙar kyau da tsada ya buɗe masa ya shiga sannan ya maida murfin ya rufe tare da sauƙe wata gajeriyar ajiyar zuciya, tun da dai be tanka kowa ba. John kuwa a nashi ɓangaren ƙatoton mikin da yazo ya dannesa masa ƙirji ne ya sa ko buɗe bakin bai son yi bare har yayi magana, wanda kai tsaye har zuwa lokacin wata irin kwantacciyar ɓacin rai ne zagaye da fuskar nashi. Sa'ar sa ma ɗaya p-carp ɗin da ke kansa ya rufe rabin fuskar nasa da kuma shade ɗin idanunsa, sannan ga nose mask ɗin da ya sa ya toshe hancinsa da bakinsa, wanda ko samun damar cire su bai yi ba bayan ɓacin ran da suka shaƙa masa shi ne suka sake guma masa wani ta hanyar tsomo da auren ifritin wannan yarinyar cikin rayuwarsa. A hankali Mecheal ɗin yama motar key kasancewar ya san Boss ɗin nasa idan yana a irin wannan yanayin baya son gudu sosai can a mota, kafin su ƙaraso harabar har mai gadi ya wangale masa gate ɗin, take ya cilla motar titi nasu saman titi suka fara tafiyar da baifi ta 30 minutes ba suka isa wani kayataccen gida. Hong ɗaya kawai yayi get man ɗin dake kula da gidan yay hanzarin zuwa ya buɗe masa ƙofar, kana ya cinna hancin motar nasa ciki. Parking yayi koda yayi ya jima kafin ya fito har lokacin da fushin sosai a cikin fuskarsa... Direcly ya wuce zuwa ainihin babban cikin gidan dake a gyare sosai tamkar macece a ciki, kai tsaye wani lafiyayyen bedroom ya nufa har zuwa lokacin ji yake kamar zuciyarsa zata iya faso ƙirjinsa ta fito fili kowa ya ganta. Dama haka yake duk lokacin da yake cikin tension irin haka dawowa yake nan ɗin yayi zamansa har se zuwa lokacin daya sauƙa dan kansa. Ko ta kan abincin da Mecheal ya kawo masa be yi ba bare ma tunanin zai ci. Zuwa lokacin kuma tuni har 8:00 na dare ya gota ma, don haka ƙarƙashin shower kawai ya wuce da kayan jikinsa yana son samun sassauci daga zafin dake neman illata rayuwarsa gaba ɗaya. Ya jima sosai ƙarƙashin shower ɗin kafin ya zubar da Jiƙaƙkun kayan jikinsan anan cikin bayin ya fito, dake yana da uban kaya anan ɗin don yana yawan zama sosai a gidan,wanda nasa ne idan yaso har kamar kusan ma dawowa yake da zama gaba ɗaya. Sanin ainihin halinsa da baƙar zuciyarsa idan ta motsa ya saka Mecheal zama ya kwana a gadroom. Washe gari har sha biyu be fito ba zuwa ƙarfe biyu sega su Madame Victoria nan sun biyo sahunsa ita da Papa, don suna ta ƙirar wayarsa amma baya ɗauka daga ƙarshe ma seya kashe gaba ɗaya duka wayoyin nasa. Kuma har lokacin bai fito ba, har kusan karɓe huɗu na yamma suka zauna zaman gadin fitowar nasa bayan ya sha magiyar ya buɗe musu amma in ginin wurin yayi motsi to kuwa shima John ɗin yayi. Huɗu da rabi suka tattara nasu ya nasu suka mension nasu abin mamaki kuma suna tafiya da kamar 30 minutes ya fito shirye tsaf cikin shigar wasu riga da wando Calvin Klein underwear. Kansa da p-carp ya fito kai tsaye wurin parking car na gidan ya nufa, Mecheal na ganinsa ya miƙe da sauri ya buɗe masa ya shiga suka fita. Duk da dai yau yaso zuwa gidan su yasmine amma baya mood ɗin da zai iya fuskantarta don haka kawai wani store market yace ya sauƙe shi, yana son yayi sayayya don gaba ɗaya babu ababuwa da yawa na ci. Tsaf suka kammala sayayyar duk abinda yake so don ya rantse a wannan karon ze musu yajin da yake jin be taɓa musu irin saba kaf rayuwarsa. Mecheal ne ya wuce da kayayyakin zuwa cikin mota shi kuma yana tsaye yana duba wayarsa da wani saƙo ya faɗo masa. Kamar ance daga kanka ya ganta cikin hijjaba dogo har ƙasa fuskanta ƙawace da murmushi me kyau tana tafe tana ɗago hannu alamar sallama sune yi da wata ko wani, har ta isa inda tayi parking car nata bata dena daga hannunba, ɗayan kuma riƙe da keda bame girma ba. Tana ƙoƙarin buɗe motar ta ta shiga taji kamar tsaiwan mutum a bayanta, a hankali ta ɗan juyo ido biyun da suka yi ne ya saka ta haɗe kyakkyawar flluskarta nan take cike da fushi. John kuwa kallonta kawai yake Idanunsa a kanta ko kyaftawa ba yayi. “I like you, nd I Miss U My unknown beloved…” ya faɗa a hankali wanda ya saka bakinta rufewa ruf daga Ƴar ƙaramar haukar da taso manna masa. Domin kuwa ba ƙara mun duka kalmar ta mata ba a cikin zuciyarta. Amma kuma se ta dake saima wata ƴar dariyar rainin hankalin da ta yi ta nuna shi da yatsanta manuniya ta ce. “You made a mistake…” ta faɗa a hankali kafin ta sake nuna shi da yatsan taci gaba da cewa “Kayi kuskuren fahimta.” Kaɗan ya matsa gabanta hannuwansa duka biyun zube cikin aljihunsa yace. “I’m serious.” Ɗaga hannu tayi ta dakatar da shi ta hanyar furta. “Don’t.” Sai kuma ta ɗan matsa kusa da shi kaɗan… idanunta har sun sauya zuwa na fushin kai tsaye tace. “Who Are you?, kai ɗin wanene? How dare you talk about my life?, menene haɗin ka da rayuwana?.What do you want?,why did you bring me here?, leave me I can't... ka fice daga cikin rayuwana idan ma kwai wani lalataccen buri kake dashi a kaina to ina son ka sani Nie *HAUWA KABEER USMAN MAINA* nafi ƙarfin ka!, domin kuwa ba kanwar lasarka bace, idan ba dan wani tunani daban kazo to ka sani cewar wannan yasmine ɗin dake tsaye gabanka ba irin sauran marasa ɗa'ar nan bace irin ta Addininku na christian. Domin Addinina da naka… sun yi nisa da tazarar dake tsakaninsu tamkar tazarar dake tsakanin ƙasa da sama ne, don haka ka fita a cikin rayuwana gaba ɗaya, in ba haka ba wllh³ zaka yi nadamar sanina a cikin rayuwarka ok?....” daga nan ta shige cikin motar ta fuuuu ta jata da mugun gudu tana barin wurin. Wani huci me zafi ya fesar kana ya kaima iska naushi ya shige tasu motar suma suka tafi. Lokacin da suka koma gida goma saura don haka anan parlourn ya zube yana sauƙe wata ijiyan zuciya me ƙarfi. Babu jimawa ya miƙe ya shige bedroom nashi, da sauri Mecheal ya rufa masa baya ya bishi ya jere masa dangin su cake ɗin da suka shigo dasu. Kana ya ware masa wasu a dinning da coffee ɗin da ya saka aka haɗa masa tun kan su iso anan parlourn. Sanye ya fito da wata irin singlet ɗin da se a Indian film ake ganinta fara tas. Ahankali yakai zaune saman wata kujera mai tsananin laushi kaman gado. Gefensa laptop nashi ce saman cinyarsa ya buɗe zai yi wani aiki ne a cikinta, yanda ya maida hankali kan laptop ɗin kaɗai ya isa sanar maka da cewar kowanne aiki yake yi to kuwa me muhimmanci ne. Gefen sa ga wani ƙaramin glass table ɗin da aka ɗora masa coffee nashi cikin mug mai kyau sai zuba uban tururi yake, se wayoyinsa da suke zube gefe guda. Yana aikin nasa sama sama yana kai hannunsa ya tura cikin coily hair nashi, wacce gaba ɗaya ya gama wargaje ta saboda da yawan kai hannun da yake ya hargitseta. Jin kansa na shirin fara ɗaukar chaji ne ya saka shi kai hannunsa ya dauka mug ɗin ya fara sipping a hankali. Tsaye ya miƙe daidai da kammaluwar aikin nasa ya nufa sama. Se dai ko taku ɗaya be yi ba ƙiran waya ya shigo masa wanda ya sashi wani daƙune farar kyakkyawar fuskarsa me kyau, wacce dole ta saka shi komawa zaunen da yake yananyin fuskarsa dake ɗauke da ƴar guntuwar damuwar na sake riƙedewa lokaci guda zuwa wani irin deadly expression ɗin ka ganshi a lokacin babu abinda zai hana ka tsorata. Tsaye kawai ya miƙe hannunsa yana barin ma laptop ɗin anan hannunsa cikin aljihunsa ya nufi carridor wayar manne a kunnensa. Kafin se a lokacin yake bama wanda suke wayar da furta. “And what?....” yayi maganar da wata irin deadly voice nashi. Daga ta can ɓangaren me ƙirar kuwa aka ci gaba da kwantar masa da hankali akan amren Deepika ɗin da indai bai so babu me ɗaura masa. Se a lokacin yake sakin wata bahaguwar ajiyan zuciyar daya saka me wayar ɗan lumshe idon jin ya dawo cikin haytacinsa. Kana aka sake ce dashi. Shiru kawai John yayi yana ci gaba da sakin ijiyan zuciya. Cike da son sake bashi tabbacin babu me masa auren dolen mahaifin daya kasance na Deepikan ne wato Goush David ke kwantar ma da John ɗin hankali. “OK. finally My boy ina son ka cire damuwan komai a ranka, kaje yanzu ka kwanta ka hutu dan nasan ka sam baka iya ɗaukan abu da zafi ba, I will call you tomorrow Alright?, I love you PAPA'S BOY” Kai kawai John ɗin ya gyaɗa masa kamar yana a gabansa ne ko yana kallonsa yace. “Alright Dad ,I love you more " daga haka ya yanke wayar yana jin kamar an yaye masa wata gimgimemiyar dutse ne a tsakiyan ƙirjinsa.... ꨄ Ɗan jujjuya kanta take yi cikin baccin nata, gaba ɗaya gumi ta gama jiƙe gaban goshinta tsaf. Cikin baccin take sake ɗan jujjuya kanta kafin tayi saurin ware masa manyan idonta masu ƙarfi a kansa, tare da buge hannunsa dake kan fuskanta yana shafawa a hankali kafin a ɗan fusace tace. “What are you doing?” Tace ranta a wani irin mugun ɓace ta fesar da numfashi tana kallonsa, Wani lumshe mata lumsassun idanunsa yayi da wani irin emotion kan fuskar sa yace mata. “I'm sorry Babe na kawo miki abincin ne naga kin yi aiki kin gaji ne. Gashi kuma bakici komai ba tun ɗazun se famar kaiwa da komowa kike kar yunwa ya cin yi min cikin Baby...” A fusace ta miƙe tsaye tana kallonsa kallo irin na fusatara nan tace. “To ina ruwan ka da ciki na?, cikin ka ko nawa?.... ehhhh nace cikinka kane ko nawa?....” Komai daga nan bai sake ce mata ba saima miƙewa tsayen da yayi hannuwansa zube cikin aljihun bakin wandonsa. Bata lokacin da idonta ya fada kan faffaɗan ƙirjinsa da bai ƙarasa ɓalle botiran rigar jikinsa ba sai wani munafikin ƙwara ɗaya daya saƙala daga tsakiya. Wanda hakan shi ya bama gaba ɗaya surar jikinsa bayyanuwa gaba ɗaya... Ga wani irin ƙamshi me daɗin daya bar mata shi just like heaven. Don haka bata san lokacin data shagala a kallon nasa ba, musamman ma daya juya baya bayan nan, se dai kuma ko yaya aka yi se tsintar idonsa karaf tayi a cikin nasa ya kamata tana kallonsa, amma mutuniyar se tayi saurin composing ɗin kanta ta hanyar tamke fuskarta. Wani lalataccen Murmushin daya kusa kwarar da ita yayi kawai ya juya ya fice bayan ya mata wata shegiyan alaman da bata san ko me take nufi ba, ita kuma ta bishi da kallo tana jin haushin kanta da kanta, but don't blame me. Ita tasan dan bakuga abinda ta gani bane, he's perfection out of perfection. A wani kalan haukace ta farka daga nannauyar barcin daya ɗauke ta babu jimawa tana furta noooooo.....“Wllh ƙarya ne sharri ne!, sharri kawai yake son min ko kullu min wani sharrin, wllh bana son ka me zan yi da kafiri arne wanda baya Sallah....” gaba ɗaya ta gama haɗa zuba wanda ya saka Mamynta da Daddy'nta dake tsaye a kanta mata sannu, wanda ita sema a lokacin take dawowa kamar hayyacinta ne. Don haka ta sake matse fuska ta shiga muzuran gaske tana daga hanci sama. “Ambasaja lafiya kuwa?, me ke damunki?, wa ye kafirin?, waye arnen?, wani ne yake bibiyar min rayuwarki ne da bana da labari?...” gaba ɗaya a rikice Daddy'nta ke jefa mata tambayoyin yana zama gefenta yana mata sannu da share mata zufa. “ALLAH yasa ba aljannu kike je garin kwashe kwashenki kika kwaso mana ba Yasmine. Ubangiji ya ALLAH ya ƙarasa shirya ki.....” Mahaifiyarta ta faɗa wanda ya saka Daddy'n saurin kallanta yana cewa. “Ke wai Khadijah me yasa har abada bakinki baya faɗar alkhairi ne akan ambasajo?, wllh da ba'a gabana kika haife Yasmine ba da nace sanja ta akai ba kece asalin mahaifiyarta ba....” wani jimmm tayi kawai tayi kana ta saka kanta tana ficewa barin parlourn zuwa bedroom nata, don dama a parlourn take har baccin bayan la'asar ɗin ya kwashe ta. Wayoyinta kawai ta kwasa tana yin sama tana jin wata fusata da son ganinsa ta buga masa mugun gargaɗi me ƙarfi a kanta, tun da har abin nasa ya fara wuce bibiyarta iyaka a zahiri har cikin barcin nata ma ba zai ƙyale taba... 7:10pm ta fita da motar ta ta ringa zaga garin nemar inda zata gansa. Amma ALLAH be sa sun gamu ba haka ta koma gida. Washe gari da wuri ta fita zuwa Islamiyyar da take zuwa. Wacce se ta kwashe sama da One Months ba'a leka taba, ko ta leka ɗin kuma babu malamin da take kalla da rahama bare zaman aji, idan kuwa kaga taje to wata tijarar ta shirya ma wani daga cikin malaman makarantar, wanda su kansu duk lokacin da suka ganta a cikin tashin hankali suke tsintar kansu. Domin kuwa sun san ba alkhairi bane ya kawo ta se wata tsiyar ko lokacin sanja wani malamin ce tayi. Suna daidaita shiga islamiyya ɗin ta gan shi tsaye jingine da jikin mota, wannan bita zai zai ɗin nasa na gaban motar da alamar gyara musu yake tsayawa ne tayi. Wani uban birki taja tana takawa har zuwa inda suke dama akwai ruwan roba me sanyin dake hannunta tana zuwa kawai ba tare da tunanin komai ba ta juye masa a fuska. Babu zato ko tsammani se jin sauƙar ruwan sanyi jikinsa yayi, wanda ya saka shi wani irin zabura sedai haɗuwar idonsu a kan junane ya saka shi wani irin ƙamewar ban mamaki, domin kuwa exactly jinginen nan da yake irin mafarkin sak yake yi. Mamakin be sake kashe shi ba har se da yaji ta fara magana cikin zallar fusata. “Me na ma ka????...., Malam na ce me na ma ka? haka da zafi da har kake bibiyan rayuwana irin haka?. Bayan hakan ma duk ba zaka ƙyale ni se ka bini har cikin bacci na kana min hauka Where are doin?, wa ne ne kai?... Idan ma wani abu ne a cikin ranka game da yasmine to ina son kayi gaggawar cire komai ye, domin kuwa akwai wani irin banbanci me girman tazarar da ba zaka iya kamo ni ba...Kai bama kawai bambanci bane…wani layi ne da ba kowa ke iya tsallakawa ba.” Cak John ya tsaya yana kallon bakin dake rufe shi da bala'i da masifan da cikin kwanakin da basu wuce 5to6 days ba yaje ya koyi Hausa a sabo da ita kawai. Sedai komai a maganar nata be fahimta ba sakamakon guma guman Hausa ne wannan take yi masa. “What if I can?” ya tambaya a hankali wanda ya saka yasmine jan wani numfashi ta fesar ta ce. “Saboda ni ba abokiyar wasar ka bace...” Sai kuma ta wani ɗan karkatan da kanta gefe taci gaba da faɗin. “I’m not playing. Again Mr No Name Ni ina rayuwa ne da abin da na yi imani da shi.” Sai ta ɗora hannunta saman ƙirjinta tace. “Kuma shi wannan abun daya faru bisa kuskure ina son ka manta dashi a cikin memory naka in ma shi ke sake taɓa kan ka shaidan kuma ya buga maka ganga, to ka sani niba irin sauran Christian watsatstsun ƴan matayenku bane, ina da addini!, ina da daraja daga yau karka kuma kuskuren leƙa cikin rayuwata ba.” Cak John ya tsaya a karo na farko ya kasa magana. “ Bayan wannan abin kuma idan har a cikin zuciyarka da abinda kake shirin aikata min...” Se kuma ta dakata cak kana ta nuna shi da yatsarta manuniya ta ce... “…Toh kuwa ka shirya rasa abubuwa da yawa daga cikin rayuwarka.” wanda ya saka John wani jan idonsa su tafi luuuu kamar zasu lumshe amma be lumshe ba. Wani kalan bugawa tsakiyar ƙirjinta yayi da ya saka ta ja baya kaɗan ta sake nuna shi da hannunta ta ce. “Na...tsa....ni....duk me takura rayuwa na ka san wannan....” wani buɗe idonsa a kanta yayi "And I love marh?....” wani rumtse idonta tayi ta toshe kunnuwanta tace. “Kada ma kace zaka fara....ka da ma ka ce kana sona mr No Name…” Wanda ya saka John fesar da wani abu me nauyi daga cikin ƙirjinsa tun kafin yayi shirin furta wata kalmar ta riga shi ta hanyar furta.. “Because loving me…is not easy.” fuuuuuuu daga haka ta juya ta barshi a daskare.... *JOHN* Tin da abun nan ya faru gaba ɗaya jikinsa ya rikice wanda da kyar Mecheal ya lallaɓashi suka koma gidan daya koma, ko da dare kasa bacci yayi duk inda ya juya ita kawai yake kalla tana masa masifa da bala'inta. Don haka ya tashi zaune daram ya zabga uban tagumi shi kaɗai a cikin zuciyarsa yake tambayar kansa. _Menene matsalan?, da ga kuma ita take?, shin to kodai shi ne matsalan?.... Wani numfashi zazzafa ya fesar kai tsaye tare da ɗaukan wayarsa ya doka ƙiran Mecheal. Yana jin anyi answering call ɗin kai tsaye yace. “Mecheal.” daga ta can ɓangaren Mecheal ɗin kamar wanda yake gabansa ya wani sara masa da faɗin.. “Yes, Boss.” “Find me a place…” ya faɗa yana ɗan dakatawa kana ya sake ce. “…where I can learn.” wani jimmm Mecheal yayi tare da tafiya duniyar tunani har seda gyaran muryan John ya tayar dashi kana ya ce. “Learn what, sir?” Mecheal ɗin ya tambaya, wanda ya saka John rufe idanuwansa na ɗan lokaci kawai ya ce... “Her world.” ƙit daga haka ya datse ƙirar yana jifa da wayar da take ta fashe tayi rugu rugu.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 14 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄWayar da yay jifa da ita ta watse ba ƙaramin razana Mecheal tayi ba, duk da cewa bai ji ƙarar ba amma ya san halin Boss ɗinsa. A hankali ya sauke numfashi yana kallon wayar hannunsa kamar yana kallon matsalar da zai warware. “Her world…” ya maimaita a hankali. A wannan daren kuwa, John bai sake kwanciya ba. Ya zauna a gefen gadonsa, idanunsa buɗe, amma zuciyarsa a wani wuri daban. Kalaman Yasmine na ta yawo a kansa kamar ana sake kunnawa. "Because loving me… is not easy." Wani lumshe idonsa yayi a bayyane yana me furta. “Then I’ll make it easy…” kawai ya furta a hankali.ꨄ Ko washegari da safe da yasmine ta tashi ta John ta tashi cikin ranta,wani irin abu me kama da farat ɗaya take ji a kansa sosai. Wani irin motsi take jin kamar ana motsa wani abu daga cikin zuciyarta.uwa uba kuma kwana mafarkin John da tayi, se dai mafarkin nata me cike da sarƙaƙiya da rikita ƙwanya. Gaba ɗaya basirarta ta toshe ta rasa ma ta yacce zata ma mafarkin nata dalla dalla ta wargaje bare kuma in ta wargaje ɗin ma ta sama damar sake haɗe shi cif wuri guda. Mafarkin ba ƙaramin girgiza tunaninta yayi ba, gaba ɗaya ji tayi kanta ya cunkushe ya cushe mata da wasu hargitsatstsun ababuwan da bata san ko su miye su ba ɗin ba. Wani lumshe idonta tayi daga kwancen da take gaba ɗaya rabin jikinta na saman gadon yayinda ƙafafunta suke a zube a ƙasa tana jijjigasu cike da zafi da rashin sanin mafita. Wani saurin zabura tayi sakamakon fuskar John data wulga mata tana buɗe idonta duka. “Na shiga uku” ta furta tana ɗora hannu a ƙirjinta. “Me ke shirin faruwa dani ne haka?” ta sake tambayar kanta cike da tashin hankalin abinda ke shirin kamata akan wannan arnen. Mutumin da a koda yaushe take cike da jin haushinsa, amma yau ace zuciyarta zata mata haka?, Shin me yasa zuciyarta zata ci amanarta irin haka ta ƙaunaci mutumin da bai dace ba.? Husna data kwashe sama da 15 minutes a kanta tana mata magana ne ta ɗan girgiza ta da kyau tana tambayar... “Yaya Yasmine lafiya kuwa? Tun ɗazun inata ta miki magana Daddy ya na son ganinki amma kamar kin tafi wata duniyar tunani ce ta daban…” wannan maganar ta Husna da girgiza tan da tayi shi ya dawo da ita hayyacinta. “Ba komai…” Ta furta da ƙyar tana ƙoƙarin boye halin da take ciki don bata san Husna ɗin ta fuskanta komai ɗin. Ɗan matsowa kusa da ita Husna tayi idonta cike da damuwa tace. “Aunty Yasmine, wannan ba kamar ba komai bane. Nifa wani lokacin kina bani tsoro wllh…” kanta ta juyar gefe tana gujema kallon Husna ɗin tace. “Na ce miki ba komai Husna enough mana kije zan zo yanzun” ta faɗa da ƙarfin da sai dai Husna ta ɗan tsaya tana kallonta kamar zata sake wata maganar amma daga ƙarshe ta juya ta fita kawai... Tana fita Yasmine ta saki wani numfashi mai nauyi, hannunta har yanzu manne a ƙirjinta. _Duk abinda ke faruwa dani… ba na fahimtarsa._ ita kaɗai ta faɗi cikin zuciyarta tana miƙewa tsaye a hankali, amma ƙafafunta na ɗan soma mata rawa kamar ba nata ba. jingina ta ɗan yi da jikin gadon na ɗan lokaci kafin ta nufi madubi. Idonta kai tsaye ya sauka akan madubin ya sauka a kan fuskar kanta…Amma ba fuskar da ta saba gani ba ce jiki, cikin abinda be wuce seconds ta hangi fuskar John a cikin madubin daya saka ta fasa ihu tana me furta. “Ahh!” Ta ja baya da sauri, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar zata fasa rufin fata bakwai ɗin dake ƙirjinta ta fito. “Me hakan ke nufi…?” ta furta da muryar da ke rawa. Jin motsin kamar za'a shigo ne ya sakata saurin faɗawa toilet ta rufe kawai tana fasa kuka bayan ta saki shower yanda ko waye ta shigo ba zai ji sautin tashin kukan nata ba. “Baby ambasa ki na ina ne haka?” Daddy'nta daya shigo da kansa don jin shirun yayi yawa shi ne ya biyo bayanta, daidai kuma lokacin da take fitowa jikinta gaba ɗaya da laimar ruwa tana murmushin yaƙe tace. “Daddy ina zuwa fa wanka ne nayi...” fita yayi don bata damar shiryawa, kayan jikinta ta zare ta saka wasu marasa nauyi ta fesa tura. Daga haka ta nufo ƙasa ta sauƙo sedai ganin Mamynta a dining ɗin be mata daɗi Ba. Su kuwa a nasu ɓangaren tun kamin ta iso wannan shegen ƙamshin nata tuni harya gama sanar musu cewar zuciyar Daddy'n ce tafe, daga gefen Daddynta ta zauna tana wani bata fuska da kumbure kumburen ba kawai. plate ɗin dake ɗauke da donut,pizza taja zuwa gabanta ta ɗauka tana ɗora shi kan cinyarta gefenta ga kwalin picanto ɗin data fito dashi zata ci... Kai tsaye metres sarvice ɗin dake aikin shirya kitchen ta kwalama ƙira tana bata umarnin kawo mata fruits masu kyau daga fridge. Babu jimawa kuwa se gata hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits ɗin a ciki masu sanyin kuma kamar yacce ta buƙata, gashi ta mata yanka ƙananu². Yadda bata nuna tasan anyi ruwan Mamyn ba itama seta ɗauke nata kan. Fira suke da Daddy'n da idan tana fira dashi babu me saka mata baki, cikin firar har ta saƙƙo kan shirin fina finan hausa, don haka cike da zakuwa ta dubi Daddy'n da shi ne dama ya fara kawo mata batu akan Nafisa Abdullahi ga sabon Film ɗin da take kan yi a yanzun me suna *ƘADDARA*tace.... “Ywwh Daddy I'm seriously ina son fara Film ne fa wllh harkan na mugun burgeni tuni....” wani wawan tsaki Mahaifiyarta taja tana miƙewa tsaye a fusace. “ALLAH wadaran naka ya lallace, ke yanzun in banda hauka da jahilcin dake taɓa ki uban me za kiyi da Hausa Film?. Wannan ai sana'ar marasa tarbiyya ce da suka fi ƙarfin iyayensu, mutanen da babu aikin da suka iya seta tallace tallacen tsiraicinsu suna zubarma da mata mutumcinsu ke kuma shi ne abinda ke rinjayarki?....” Daddy ne ya mike a fisacen shi ma yace. “Kinga enough Khadijah!!!. Wai har se zuwa yaushe zan dena miki kashedin dena takuramin Baby?, ko ita Husna ba ya bace da har abada baki da abar kushewa da musguna wa sama da Baby ambasajo uyhmmmm?. To wllh ki sani Inma baƙin ciki kike mata sena nemo mata hanyar shiga Film, ke Inma a cikin shirin ƘADDARAR take son a saka ta se an saka ta, dama ABDUL-AMARD ɗin ma ai mutuminane zanyi magana dashi, ke ba kannywood ba ko da PRABHAS ko SHAH-RUKH_KHAN tace tana son yin film dasu se tayi...” daga haka fuuuuu yabar wurin yasmine ta mara basa baya don tasan tsaf Mamyn zata kai mata bugu. Wani hawayen baƙin ciki zallane ya ɓalloma Mamyn da cikin tashin hankali Husna ta rumgumeta tana saka kuka tare da bata bakin ta dena zubarma yasmine hawaye kawai taci gaba da mata adda'a a matsayin ta na uwa mahaifiya.. ꨄ Yau ma tun wuri ya shirya ya fita bakin Islamiyyar nan, sedai ko me kama da ita be sake gani ba tsayin 1 week, inda gaba ɗaya abin har ya so bashi mamaki, anguwarsu ma koda yaje be sama ganin taba duka, gaba ɗaya se jinyarsa ta dawo sabuwa ga takurar da su Papa suka masa akan lallai se ya dawo mension don tsilli tsilliaganar auren nasa da Deepika kan faɗo masa. Wacce Mecheal ke tsegun ta masa cewar cikin satin ma wai Deepikan zata dawo daga ƙasar India. Tsaye yake jingine da jikin motar shi daga can nesa da get na gidansu yasmine. Yana sanye da farar shert me gajeren hannu da wando three quieter se p-carp daya saka a kansa ya karkatan da ita gefe guda, se shade ɗin daya rufe fuskarsa dashi hannuwansa zube cikin aljihunsa yana kallon ƙofar get ta gidan, wanda yau tsayin 3 day's kenan kullum se sun zo wurin. Mecheal dake tsaye a gefensa ne ya dubesa don ya kasa ɓoye mamakinsa ga sabbin ababuwan da Boss ɗin nasa ke fito masa dashi, don haka ya kallesa yace. “Boss… are you serious about this?” John ɗin be kalleshi ba ya amsa da “Yes.” wani numfashi me kama dana tsoro Mecheal ɗin ya fesar yace kana cikin harshen turanci yace. “Amma… wannan ba irin rayuwarka bane Boss” “Exactly.” ya katse shi cikin kafin ya juyo gaba ɗayansa ga Mecheal ɗin kai tsaye ya ɗora da fadin... “If I want her… I must understand her.” Wani shiru ne ya baƙunci wurin sakamakon hangota daga nesa da yayi, daidai da lokacin da take ɗago kanta Idonsu suka haɗe wuri gudan daya sakata tsayawa cak. Shi kuma a nashi ɓangaren yana gaza motsawa sema wani irin bugun zuciyar dake ci gaba da ziyartan sa a duk lokacin da zai ganta. Daga nesan da suke ya wani ɗage mata gira kaɗan alamar ya dai?, ko dai kina mamaki ne?. Wanda shi kuma a ɓangaren Mecheal ya saka shi ƙamewa ganin hijjab girl ɗin nan ce ashe har yanzun Boss ɗin nasa ke ci gaba da bibiya. Ita kuwa a nata ɓangaren a hankali ta fara taku zuwa gare shi… Idanunta cike da tambaya. “Me kake yi anan…?” Ita ce tambayar data fara jefa masa kamar cikin sanyi amma kuma akwai wuta a ciki. Kansa ya ɗan rausayar kaɗan kafin cike da nutsuwar da yake da ya buɗe baki tamkar me tausayin yin maganar ya ce.... “I came to learn.” Ta ɗan ja baya kaɗan cike da kamar mamaki ma tace. “Learn what?” wacce jin abinda ta furta ya saka John kallanta kai tsaye idanunsa har sun ɗan sanja yace. “Your world.” wanda ya saka shiru ratsawa daya saka numfashinta kusan ɗan rikicewa. Sai ta juyar da kanta gefe tana girgiza kafin ta juyo ta ce masa. “Too late…” wani karkatan da kansa gefe yayi yana bin ta da wani shegen kallon da indai zai ganta seya mata shi yace. “I’m not leaving.” Cak ta tsaya bata juya ba amma kalamansa sun daki zuciyarta amma kuma dake gwanace a fannin komai ta juya ɗin tana me ce dashi. “You completely disappeared from my life.” Wani kallo ya mata tare da bata amsa da. “This is not a time like this” Tsayuwa tayi cak kamar an dasa ta a ƙasa numfashinta ya ɗan rikice, zuciyarta na bugawa da wani irin saurin da ita kanta bata fahimta ko na menene ba. Kafin ahankali ta juya Idanunta suka sauƙa a kansa… Yana nan tsayen har yanzun cikin kuma nutsuwar nasa, kamar ba shine mutumin da yake haddasa mata tashin hankali ba. Fuskarta ta sake ɗaukar zafi don haka cike da zafin tace. “You said you wouldn't go out at a time like this?” Ta tambaya cikin kaushin muryan daya saka John ɗan matsaws kusa da ita kaɗan, amma ya kiyaye tazarar dake tsakaninsu ya furta. “Not until I understand you.” Hancinta ta hura sama cikin muryan tsawa tace. “Ba ka buƙatar fahimtana.” “Amma ina so.” ya amsa da sauri. Sai ta ɗan ɗage girarta ɗaya tana kallonsa da wani irin kallo mai haɗa raini da takaici. “Ka san me kake shiga kuwa…?” John bai janye idanunsa daga kanta ba ya ce. “I don’t care.” Nan take ta juya gaba ɗaya tana fuskantarsa da fusata sosai tace. “Toh ni na damu!” ta faɗa da ƙarfi kaɗan. Wani shiru ya ratsa tsakaninsu. Iska kaɗai ke motsa gefen hijabinta. “Ka sani…” ta fara magana a hankali. “Rayuwata ba wasa bace, addinina ba wasa bane, iyakokina kuma ba wanda yake tsallakawa.” John ya ɗan lumshe idanunsa na ɗan lokaci kafin ya buɗe su a kanta yace. “Then teach me your limits.” Wani irin abu ne ya motsa a zuciyarta amma kuma tana dannewa. Ta tilasta kanta tsayawa da ƙarfi gabansa ta nuna kanta tace. “Ni ba malamar ka bace.” ta faɗa tana ɗan ɗaga kanta sama. Sai ya ɗan murmusa kaɗan ba dariya ba, murmushi na nutsuwa yace. “Zan zama ɗalibi mai kyau.” Wani abu kamar dariya ya taso mata…Amma ta haɗiye shi da sauri. “Ka raina ni…” ta furta cikin sanyi. “No.” Sai ya ɗan matsa kusa kaɗan. “I respect you.” Kalmar ta tsaya mata a zuciya. Respect. Ba like ba ba kuma love ba. Respect. Nan take ta juya tana kallonsa ta ce “Ka koma duniyarka…” ta faɗa tana fara tafiya. “Wannan ba naka bane.” Sai ya biyo da murya mai sanyin daya rasa kome ya sanyayata yace “Then let me earn a place in it.” Ta tsaya cak ƙafafunta su ƙi motsi amma bata yarda ta juya ba taci gaba da tafiya har ta shiga koma get na gidansu ta rofu da ƙarfi..ꨄ John ya tsaya yana kallon ƙofar get ɗin data bugo da ƙarfin. Sai ya sauke numfashi a hankali. “Boss…” Mecheal ya ƙira shi amma bai juya ya kalleshi ba ya nufa motar shi don haka dole da gudu Mecheal ɗin ya mara masa baya. Yasmine na zaune saman gadonta gaba ɗaya ta tafi cikin duniyar tunani. Zuciyarta cike take da tunaninsa fal barin ma wannan kalmar ta "I respect you." Ta fi komai bata zafin kai don haka tayi saurin dafe kan ita kaɗai kamar wata mahaukaciya tace. “Me yasa yake damuna haka…?” ta furta a hankali kafin ta miƙe tsaye da sauri. “A’ah! Wannan ba daidai bane.” Ta sake faɗa tana fara kai kawo a cikin ɗakin. “Ni da shi? Impossible.” Amma wani ɓangare na zuciyarta na cewa _Amma ya zo gareki…_ Ta tsaya cak tare da rufe idanunta. “Ya ALLAH…” ta furta a hankali. “Ka tsare ni…” ta fadi ta na zubewa a wajan tana fashewa da wani irin kuka kamar zata haɗiye zuciya “Daddy na shiga uku ina son arne!!!....” inda karaf maganar ya faɗa kunnen mahaifiyarta da kalmar arnen ta wani irin bugar zuciyarta ta tsaya cak ƙafafunta na kamar gaza ɗaukarta.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 15 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta yanj zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ "Arne?" Mahaifiyarta ta sake nanata kalmar. Sedai bata kai ga ɗarawar ba ta sake jin muryanta kamar cikin sautin kuka ma tana me sake furta. "Wllh Ina son shi!, ina son shi har inajin zuciyata zata iya samun matsala idan ban same shi ba, Ina jinsa a can ƙasan zuciyata Daddy" Wani kalan daskarewa ta sake yi domin zata iya rantsewa duk rashin kunya da rashin ji irin na yasmine ɗin bata taɓa jin ko me kama da ire iren waɗan nan kalmomin ba daga gare ta. Har ta ɗora hannunta kan Handledoor na ƙofar bedroom nata amma ta koma da baya tana hana kanta shiga. Wani numfashin dake fita kamar a sace Mamyn ta saki kamar wadda aka kama da wani laifin. Ahankali ta juya a hankali ta koma parlour, ta zauna kamar wadda babu abinda ke damunta, ta ɗauki remote ta kunna TV amma idanuwanta ba su kan screen ɗin ba. Maganar yasmine ce kawai ke dawo mata tana mata yawo a kunnenta… "Ina son shi… zuciyata zata iya samun matsala idan ban same shi ba…" Wani irin abu ne taji kamar ya ratsa zuciyarta. Fuskar nan tata ta zama kamar dutse amma ba damuwa, ba mamaki, ba wani abu. Babu jimawa sega fitowarta kuwa fuskar nan a ɗinke tsaf, amma ganin Mamy zaune a parlourn ya saka ta tsaywa a tsakiyar parlourn bata kai ga ƙarasowa, amma haka kawai taji idanunta sun cika da hawayen da babu mai share mata. Don haka seta sama kanta da kallon mahaifiyar nata idonta yayi zurfi sosai ta zauna tana kama hannun mahaifiyar nata ta ƙira sunanta kamar da siga ta tambaya tace. “Mamy…?” Shiru tayi kamar bata jita ba, don haka ta sake matsowa kusa sosai muryarnta na rawa ta sake cewa. “Mamy kina ji na sani Pls kiyi hakuri ki gafarceni…” Sai ta ɗan juya kai kaɗan, kamar wadda aka katse daga wani tunani mai nisa, ta ɗan kalle ta amma kallon babu taushi a ciki kai tsaye tace. “Na ji ki.” Ta faɗa a taƙaicen daya saka Yasmine sake shiga hankalinta, tana tariyo rayuwarta ta taba, ita kaɗai ta shiga ma kanta da kanta tambayar shin ina wannan Mamyn nata ta baya?, wanne kakar zunubai ne son zuciyarta yasa ta aikatawa mahaifiyar da tayi dalilin kawota cikin duniyar?. Idanunta ta rumtse da ƙarfi ganin Mamyn ta sake meda hankalinta kan tv, harma tana ɗaga ƙarar sa kaɗan. Don haka Yasmine ta tsaya cak, domin wannan shiru ɗin ya fi mata duka kalamai nauyi, take taji numfashinta ya fara nauyi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, tana jin kamar ana matsa mata kirji. “Mamy… don ALLAH ki ce wani abu…” ta sake furtawa da muryar da ta kusa karyewa. Sai Mamyn ta sauƙe remote ɗin a hankali, ta jingina bayanta da jikin kujerar ta rufe idanunta na ɗan lokaci, kamar wadda ke yaƙi da wani abu a cikin zuciyarta, kafin ta dubeta cikin nutsuwa amma da ɗan sanyi a muryan tace... “Ki tafi ki huta, Yasmine.” Kalmar ta fito da sauƙi… amma nauyinta ya fi duka abin da zata faɗa, sai ta tsinci kanta da girgiza mata kai a hankali, hawaye na sauka ba tare da izini ba. “Mamy… wannan ba hutu nake buƙata ba mafita ce.…” Tana ambatar mafitar cilak Mamynta miƙe tsaye a hankali, tare da gyara mayafinta, ta wuce kusa da ita ba tare da ta ƙara kallonta ba amma ta ɗan dafa kafaɗarta tace. “Wani lokaci,” Daga haka ta saka kai tana tafiya tana barin mata parlourn har taje bakin ƙofar bedroom nata ta waywayo tare da sake furta. “shiru shi ne mafi alkhairi fiye da maganar da zata ɓata komai wani lokacin.”ta wuce bedroom nata tabar Yasmine tsaye ita kaɗai da zuciya mai cike da soyayya… da kuma tsoron abin da zai biyo bayan hakan. Don haka gaba ɗaya daren ranar nan yasmine gaza bacci tayi na kirki, se dab da subhi ta samu baccin ya dauke ta. Washe gari sassafe uban kidan data saka kusan shi ya fito da kowa daga makwancinsa, duk da ba sabon abu bane wannan sedai ta kwana biyu bata saka shaiɗancin nata ba, duk da kiɗane mai taushi da nutsuwa da _HARSHVARDHAN RANE_ da _SONAM BOJWA_ A cikin Film ɗin _EK DEEWANI KE DEEWANIYAT_ amma abin mamakin koda suka leƙa ta baccinta take rai fess don ta kasa baccin bayan kiran wayan wani friend nata da shi ne ya tashe ta, shi ne ta kasa komawa baccin ta kunna kidan. Mamy ta yunƙura da niyar nufar ɗakin amma Daddy ya hana ta ga yaya Omer dake tsaye wanda yazo tun jiyan shima ya bayyana a wurin. Husnace ta kama hannunta suka wuce ɓangaren Mamyn kowa ya koma inda ya fito, se masu aiki da suka ci gaba da hidimarsu ta ƙoƙarin haɗa dinner. 8:00am kaf ɗinsu suka gama hallara a dining, sai dai fuskar kowannensu a turɓune da takaicin ƙiɗan da yasmine bata kashe ba har yanzun. Ɗan kallon Husna Daddy yayi yace "Maza je duba min Baby ta tashi ne?" Cike da girmamawa ga mahaifin nata ta ɗan rissinar da kanta tace Daddy har yanzun bacci take amma ai limit nata ya kusa ƙarewa ma tun da yau zata fara fita aiki...." Kansa ya gyaɗa yana cewa "Okay shikenan ƙyaleta ta huta sosai to tun da haka ne, in yaso ko gobe ne ma seta fara fita aikin..." Yay maganar yana kallon Mamy da tayi kicin kicin da fuska, tun kafin ya kai ga furta komai Omer ya dube shi ya ce. “Yanzun Daddy ba zaka ce komai ba kenan?”. “Game da?” yay maganar da alamun ya bashi haske kenan. “Yasmine mana Daddy, ya yarinya zata dinga nemar ta koma kamar wata wacce bata san addini ba uyhmmmm?, ai ko kafiri a wannan zamanin dai ba kowa ke iya saka kiɗa ya kwanta da shi ba, kuma ina da tabbacin ko sallar asuba yanzun haka batayi ba.....” da wani irin sauri Daddy'n ya katsehi ransa ɓace yace. "Shi yasa sam bana maraba da zuwanka gidan nan Omer, domin kana ɗaya daga cikin masu takura min rayuwar Baby. Kuma da kake cewa kana da tabbacin batayi sallar ba uban wa kai yace ma batayi sallar ba?...” Mamy ce ta dube shi tare da furta. “Ai ba sai wani ya faɗa masa ba abinda kowa ya riga da ya sani ne ambassador. Ni wllh gaba ɗaya kai na kullewa ma yake ban san wanne irin makahon so kakema yasmine ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kawai kakeyi matsayinta na ya mace. Da ace haka kowacce yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka har ka aura ba matsayin iyayensu. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan yasmine?” Se kuma wani ruwan hawaye me zafi ya zube mata ta rintse idanuwanta tana jin nauyin maganar da zata fadi amma ranta yakai ƙoluluwa wurin ɓaci don haka ta miƙe tsaye tana cewa. "Wllh da ace Husna kake nuna ma wannan irin mahaukacin so ɗin da na ce ko son ta ka kamu dashi, amma yasmine ce yasmine dai...." Takai ƙarshen maganar tana toshe bakinta da duka hannuwanta biyun. Husna ɗin ce ta miƙe itama jikinta na rawa sosai take kallon Mamyn banda Omer da kawai kansa ya rissinar ƙasa wani irin hucin bala'i na fita daga bakinsa, Maganar gaskiya wannan Mijin ba irin uban daya dace ka zaɓa ma yaranka bane a matsayin uba na gari. Gaba ɗaya duk yacce Mamyn nasa taso tattara shirginsa ta zuba a kwandon shara seda ya saka ta faɗin maganar da bata dace ba. Cike da borin kunya Daddy'n ya miƙe tsaye yana jefa ma Mamyn wani banzan kallo haɗi da galla mata hahara. "Na gode ai ko babu komai kin nuna min iyaka na akan cewar ba nine na haifi Husna ba Nagode kwarai Khadijah..." Duk da yacce jikin Husna ɗin ke rawa hakan be hanata kamo hannun Mamyn ba ta riƙe gam cikin nata, ta fara janta zuwa ɓangarenta sanin yanzu ne zasuyi sama da Daddy'n, zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi take kallonsa, ta rasa mike damun mijin nata akan yasmine ɗin har haka?, da yake nuna mata ƙazamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin ƙoƙarinta tayi koma tace tana kanyi akan yasmine amma abubuwa sake taɓarɓarewa sukeyi. A hankali wasu hawayen masu raɗaɗi suka silalo mata saman kumatu, ta saka bayan hannunta tana kwace wa tace. "Kai ba uba na gari ba ne Khabeer!, kai ba irin uban daya dace tun farko a zaɓa bane domin maimakon ka tayani tarbiyan da yaran sema tufkar da nake ta ƙoƙarin tufkewace kai kuma kake min warwara daga baya ngd kwarai da gaske, amma ka sani na gama zaman aure dakai wllh, maza kayi gaggawar biyoni da takardar sak.... Ai tun kafin ta ƙarasa suka ji an fasa wata uwar ƙara da kururuwar daya saka su kallon inda ihun da ƙarar suka fito ban da Mamy kawai, a guje Husna, Daddy, Omer ɗin suka yi kan yasmine ɗin dake gangarowa daga saman bene, wacce fitowarta kenan gaba ɗaya kunnuwanta suke jiye mata waɗan nan muggwan kalaman. Idan tace hankalinta be tashi ba toma tama uwar data haife ta ƙarya, duk yadda takai da rashin kirkinta tabbas tana ƙaunar mahaifiyar nata, kawai abinda ta ɗauka abinda take mata wata ƴar takurawace da rashin son ganin rayuwarta taci gaba. Amma kuma yau taji abinda ya girgiza duniyarta, Husna ba ƴar gidan Daddy'n ta bace?, to yar gidan waye?, ita dai tana da wayon da tasan lokacin da Mamyn ke ɗauke da cikin Husna ɗin, kuma tana da wayon da Mamyn nata ta haihu to ta yaya Husna ɗin ta zama ba yar gidan Daddy'n nasu ba, kai ina wannan ma bame iyuwa bane makaran kunnuwanta ne suka jiyo mata ba daidai ba, amma kuma kalmar takardar sakin da Mamyn tayi niyar faɗin ne ya kusan tashin kiyamarta. Da Wannan tunanin taci gaba da gangarowa har Husna data riga kowa isa ta tare ta ta faɗo saman jikinta, daidai da lokacin da Mamyn ke isowa a fusace ta janye Husna daga jikin yasmine kafin ta juya ta kalli Daddy'n tace. "Alhamdulillah ko yanzu naga irin tarbiyar da ka ba Yasmine tayi rana, tun gashi nan ta kamu ta ƙaunar ARNE!!!....." Cak Daddy yaji zuciyarsa ta tsaya na ɗan wani lokaci numfashin sa ya kusan sarƙe maƙoshinsa. Itama a ɓangaren Yasmine ɗin Cak ta dakata ɗin, why Mamynta tasan da maganar?, tuno shashncin da tayi a daren jiyan ya saka ƙirjinta bugawa, fuskarta daga gefen idonta ya fashe, da gefen bakinta amma duk da se da ta yunƙura ta mike amma babu shiri ta koma zaune, sakamakon azabar da taji daga ƙafafunta alamar taji rauni sosai, da rarrafe ta isa ga Mahaifiyar nata cikin muryan kuka tace. "Mamy don ALLAH ki gafarceni ki yafe min..." A fusace ta janye ƙafarta tana ɗauke fuskarta da wani irin marin da kowa seda ya rumtse ido yana kuma riƙe fuska. Fuuuu taja hannun Yasmine zuwa sama don ɗaukar hijjabarta, tana nufar saman Daddy'n da jikinsa ke wani shegen rawa yayi saurin mara mata baya tana shigewa ya kulleta ta baya. Yin duniya tayi ƙofar ta buɗe taki a fusace ta nufi ɗaukar wayarta sedai tana tunowa da ashe ta barta a parlourn, zama tayi gefen gadonta tana jin kamar ta fasa ihu. Gaba ɗaya daga can ɓangaren Daddy ya haɗa uwar zufa se famar kaiwa da komo yake hannunsa goye a bayansa, gaba ɗaya yana jin be taɓa shiga tashin hankali makamancin haka ba tun da uwarsa ta haife sa. Shi kuma Yaya Omer shi ne ya tafi da yasmine asibiti. Gaba ɗaya se gidan ya koma wani irin shiru hatta masu aikin gidan duk sun shiga taytayinsu saboda halin da gidan ke a ciki. Da haka Daddy'n ya lallaɓa ya ma fi ce a gidan zuciyarsa na sake ɗaukar ɗumi. Koda suka dawo daga asibitin sashen Mamyn duk suka nufa dama kuma sun san a rufen yake, cikin tausasa murya Omer yayi ta bata baki akan ta ƙara hakuri akan wanda take kan yi, sai Ubangiji ya bata ladan ibada, kuma ta dena ma Yasmine ɗin kuka ko zuciya ta ɗebe ta ta mata bakin da ba iyaka ita kaɗai ba suma se sun shiga uku. Cikin fusata daga bedroom ɗin da take tace. "Na jima ban yi mata bakin ba dan ubanka kai ma Omer mara zuciyar nan, kuma wllh ka sani daga yau na haramta maka maganar aure tsakaninka da wannan mara tarbiyyar, tun da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kansa yace muwa ƴaƴan mu zaɓen uwaye na gari,to ni kai na da nake matsayin mahaifiyar yasmine na shaida cewar bata gari bace..." Kanta take jujjuyawa daga inda take zube fuska manne da bandage Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un take son ganin ta kama tayi ta maimaitawa amma kuma harshenta ya mata nauyi.... Gaba ɗaya dai yau yinin gidan babu daɗi. Cikinsu kuwa har da yasmine dake dake zaune daga bakin bedroom ɗin mahaifiyar nata itama anan ta wuni, Daddy se yamma ya dawo gidan ko abinci se da Ya Omer yayi da gaske ta samu taci. Ta jikin window'n ɗakin ya leƙa shima ya dinga bata baki yana sake bata hakuri da Husna wacce tayi ta ma Mamyn roƙon ta faɗa mata wacece ita amma ta daka mata tsawa tace ta sake mata wannan tambayar seta ɗauke shashar fuskarta da mari, jikin window'n ta matso tace "DADDY don girman ALLAH ka gaya min wacece ni Mamy taƙi min magana har yanzun..." Shima tsawar ya daka mata yace ta masa shiru haka nan. Sema wayarsa daya miƙa mata yace ta miƙawa Mamyn, kin amsa tayi dake a handsfree yasa wayar ya saka na cikin wayar daka tsawa yana cewa. "Khadijah way me yasa wani sa'in kike da baƙar zuciyane?,akan ɗan abin da be taka kara ya karya ba har ki buɗi baki kice mijinki ya sake ki ashe baki da hankali?, to wllh ko da wasa na sake jin zance irin haka zaki ga hukuncin da zan miki kuma ki jirayeni ina nan shigowa Lagos ɗin ma ɗan ubanki, tun ni kaina nasan idan wannan baƙar zuciyar taki irin ta kafiran farko akan riƙe ra'ayi idan ta motsa kowa baya ganin da kyau..." Cikin muryan kuka ta katse ƙanwar mahaifiyar da a yanzun ita ce matsayin mahaifiya a gare ta ce... "Addaya kimin uzuri amma Wllh ba laifi na bane, Khabeer ya gama ƙure iyaka hakuri nane akan Yasmine,kin kuwa san girman saɓon daya saka na aikata?, mugun son kansa ne ya sa yau baki na harya suɓuta gaban yara na furta ce masa Husna ba ƴar sa bace..." Daga can cikin wayar aka kwafe da cewa. "Kuma se me dama ai ba yar tashi bace, dan tun farko ƙin kine, shi yasa nace kina da baƙar zuciya wllh Khadijah da tun farkon kin bayyana ma Husna ɗin ba kune iyayenta ba ai da duk hakan bata faru ba, kuma ke da a wannan zamanin ma uban wa yace miki ana irin wannan karar da zaki riƙe ɗa har ya koma ga ALLAH ba zai san ba ku kaka haife shi ba ai zamanin ya sanja, dama nasan dole ranar hakan zata zo, wacce ke da bakinki ba sai wani ya matsa ki ba za ki bama FATEMEERH amsarta...." Ƙit ta datse wayar daga haka wacce ta jima ta faɗuwa saman gado sabo da subcewar da tayi daga hannun Husna ɗin, amma tsananin ƙarfin hali dana zuciyar da Husna ɗin ke da be sa yarda ta sume ba amma ta sake shiga mugun shock ɗin jin Mamyn ma ba tata bace, to ita wace?, wa ce ce ita?.... A sace Daddy ya buɗe ɗakin ya shigo ya buɗe baki ze mata magana ya saka ta daga masa hannu alamar bata buƙata don haka salin alin ya ɗauka wayarsa ya fice tun da yana da tabbacin babu inda ta isa ta fita yanzun.... Aka ce wai me hali baya taɓa fasawa kai tsaye bedroom na Yasmine ya wuce yaje ya sake lallashinta kana ya wuce samansa don watsa ruwa. Kwana uku gidan ya kwashe baya cikin yanayi me daɗi ana huɗun kuma se ga zuwan Addaya gidan, wacce tun usili Mamyn ce ta saka mata sunan Addayar, dake haka kowa yake ƙiranta Adda a lokacin harda mahaifiyarta kafin ALLAH ya mata rasuwa, to shi ne itama kuma se ta daddage tace mata Addaya, wai tana nufin Addata. Shi ne Addaya ɗin. Zuwan nan nata kuwa shi ya kawo ƙarshen komai, ta zaunar dasu gaba ɗaya har da Omer ɗin da tace ya tattara kayansa yau ɗin nan in sha ALLAHU zasu wuce Kano. Kasancewar hasalinsu yan can ne har Daddy'n,wanda shi kasuwanci da yawon siyasa ne ya dawo dashi nan Lagos ɗin zaman gaba ɗaya..... Hannun Husna dana Mamyn na cikin nata bayan ta huta dake zuwan wuri tayi, kuma ƙarfe biyar In sha ALLAHU zasu ɗauki hanya. Duk da Mamyn ta so ta tsaya tayi ko kwanaki uku ne amma tace lalalala bada ita ba. Cikin taushi da kwantar da murya take tausar zuciyar Mamyn da Husna har dama Omer bayan ta kawo bayanan ban hakuri dana kamar sake ta'aziya gare su ta fara da cewa.... "UBANGIJI yaji kan Fatimatul zahra, yasa halinta nagari ya bita, ya kuma sa aljannatul firdausi ita ce makomarta." Da Ameen duk suka amsa harda Husna da duk take jinta ba daidai ba. Cikin sanyi shiga basu labarin Fatima babbar ƴar ta da kusan tare suka taso ita da Khadijan (Mamy). Komai nasu a rayuwa iri ɗaya ne har ALLAH ya karbi ran yayarta Haj Fatima da itama Addaya ɗin tata fatimar sunan yayar nata ne ta saka mata, tashin hankali matuƙa sun shiga a wancan lokacin koma dai tace ta shiga akan mutuwar yayar nata, daga nan se riƙon Khadijan (Mamy) ya dawo hannunta da ƙarfin tsiya, don da dangin mahaifin Khadijah ɗin sun ce su ba zasu bayar da ƴar ɗan uwansu itama ta dage har dai suka haƙura suka bar mata. Don haka Fatimah da Khadijah suka taso a taro kamar yan biyu, dama kuma kusan komai nasu iri ɗaya ne ko lokacin da mahaifiyarta take raye, don haka komansu seya sake zama ɗaya. Har ta aurar dasu rana ɗaya. Sedai da wuri Fatima ta sama ciki saɓanin Khadijah, sedai har Fatima ta haifi ɗan ta namiji Omar Khadijah babu labarin ciki, wacce ita sam bata ma wani damu a ganinta tun da ƴar uwarta ta haifa musu ai shinenan. Seda Omer yayi 7 year's itama ALLAH be sake bata wata haihuwar ba, kwatsam kuma sega Khadijah da ciki wacce suka koma Lagos last year's. Faɗin irin zallar murnar ma da suke ciki a wancan lokacin to kamar ɓata baki ne ma su a wurinsu, a ɓangaren mijin ta kuwa cab babban hauka ne kawai be buga ba, amma yayi ɗan ƙaramin kam, don wannan cikin jin sa yake fiye da duk wani hasashen me tunani, wani abun mamaki kuma kuma shi da Fatima ba'a san wanda yafi wani ƙaunar cikin nan ba, don kusan kullum tana hanyar Lagos dake itama sun koma Abuja da mijinta. Haka har ALLAH ya sauki Khadijah lafiya wanda ta haihu gaban ƴar uwarta Fatima dake nurses ce itane ta amshi haihuwarta, se dai abu na farko ko nace saɓanin farko daya fara ratsa farin cikin haihuwar Khadijah shi ne Mijinta, don tazo masa da tsohuwar maganar da kusan suka yi alkawari tun kafin aure cewar duk randa ALLAH ya bata haihuwa indai macece yarta ta farko Fatima ce, a lokacin seya amsa ya kuma yi na'am da zancen har bayan aure takan tuna masa, amma kuma bayan haihuwar tazo masa da waccen maganar yace be san zance ba shi sunan uwarsa da bata jima da rasuwa ba ze saka wato Hauwa'u. Wannan abu shi ne matsala ta farkon da ta saka seda ni da kaina nayi tattaki tun daga garin kano har nan Lagos kamar rana irin haka bana mancewa. Na zo na rarrashi Khadijah tare da ƴar uwarta data nuna mata ba komai gaba seta saka ta In ALLAH yaso, yarinya ta amsa sunan Hauwa'u da ake ƙiranta Yasmine, tun daga haihuwar Yasmine gaba ɗaya hankalin Khabeer ya koma kan Yasmine. Sedai wata sabuwa tun Yasmine na yarinya idan tayi ba daidai ba irin na yara uwarta bata isa tsawatar mata se uban yahau sababi, itama data gane idan tayi abu ko baya nan daya shi go seta harhada cikin gwarancinsu na yara ta faɗa masa. Haka dai har ta girma kusan da shekaru sega Fatima da Khadijah na ɗauke da ciki. faɗin irin sabuwar murnan da muka tsinci kanmu gaba ɗaya bata baki ne, zuwa lokacin kuma Omer nada Shekaru sha biyu. Yayin da yasmine keda huɗu kawai a duniya, wannan karon kam dole Fatima ta matsawa mijinta Aminu suka dawo Lagos da zama sabo da samun damar ganin ƴar uwarta a koda yaushe, kusan a anguwa ɗaya. Rana ɗaya ciwon naƙuda ya kamasu sedai Khadijah tafi Fatima jin jiki, don haka Khadijah cikin mawuyacin hali take barma Fatima sallahun idan ta mutu ta sakama yar da zata haifa suna Fatima, ma'ana sunanta kenan, inda ashe ba haka abin yake kowa na nashi ne shi kuma ALLAH na nashi. Khadijah se ta riga Fatima haihuwa sedai dama abinda ta haifa be zo da rai ba, tsiransu babu nisa Fatima ta haihu sedai tana haihuwar kuma jikinta ya rikice jini ya ɓalle mata, babu jimawa tace ga garinku nan.... Innalillahi wa'inna ilaihir ³ mutuwar Fatima ba ƙarami tashin hankalinmu tayi ba, inda shi kuma mijin nata dake dama shi almajiranci ne ya kawo shi Kano ɗan asalin Jigawa ne ya tafi ɗauko ɗaya daga cikin danginsu Ubangiji shi ma ya amshi ransa, wanda shi ne ƙarasa rikicewar jikin Fatima jin ALLAH ya ɗauki ran mijinta, a lokacin da ake isa da Babyn da Fatima ta haifa tana canyara kuka irin nasu na jarirai wurin Khadijah. Kifeta kawai a ƙirjinki tayi tana fasa wani kukan da itama ya kusan wucewa da ita, se da tayi 3 day's bata san inda kanta yake ba. Mu kuma can muna can cike da tashin hankalin rashin sanin takamaiman dangin mijin Fatima, gashi kaf cikinmu babu wanda yasan inda taka maiman dangin nasa yake a Jigawa,inda a lokacin mijina yayi ta fafutar bi gari gari a Jigawa sedai be gano dangin mijin Fatima ba, a dawowarsa shi ma yayi accident ALLAH ya ɗauke nawa mijin nima tashin hankali iyaka tashin hankali mun tsinci kanmu a wannan lokacin. Farfaɗowar Khadijah take jin mutuwar Abbansu Abdullahi ta sake komawa doguwar sunar da saida ta sake ninka one week. Itama har mun gana fidda rai da ita, a lokacin Omer shi yayi ta aikin kula da jaririyar da ko takamaiman suna bata da, duk da dai uwarta Khadijah ta ƙirata da sunan ƴar uwarta Fatima, se bamu gama yanke sunan ba kuma kuma sake tsintar kanmu cikin wata sabuwar duniyar da mutuwar ta sake kawo mu. Dan haka kaf cikin dangina dana mijina babu wanda yasan hasalin waye mahaifiyar jaririyar dake raye, don haka muma dake a lokacin muna tsaka da tashin hankali na rashi yasa babu wanda na tara da wannan zancen, har Khadijah ta farfaɗo tace ita yar ta bata mutu ba dama can ALLAH yayi Fatima itace yarta. Banda mijinta se ni se kuma Omer babu wanda yasan ba Khadijah bace hasalin Mahaifiyar Fatima ba, wacce take kiranta da Husna, bayan lafawar komai har an ɗan ɗebi shekaru ma samu Khadijah da maganar ya kamata ko yaya ne Husna tasan labarinta amma Khadijah tayi kicin kicin harda kukan wai kawai so nake na nuna mata iyakarta akan Husna ni kuwa jin wannan magana yasa naja baki na nayi kitsim amma ni dama a raina nasan a wannan zamanin dai dole ko shi mijin wata ran se ya saka ka faɗi ɗan dake hannunka ba naka bane da bakinka gashi kuma yau ALLAH ya kawo mu ranan, bayan tazarar shekaru ɗai ɗai har shekaru goma sha takwas... Da wani irin kuka da rarrafe Husna ta rarrafa gafan Mamyn tana sake rungumeta ta shige jikinta tana fasa wani kukan daya saka kowa kwallar tsananin tausayinta zubo masa harda Yasmine duk kuwa irin yacce take da ƙarfi zuciya. Cikin kukan take faɗin. "Wllh har zuwa gaban abada kene mahaifiyana Mamy ki gafarceni ki gafarceni idan na taɓa miki wani abu ba daidai ba, wllah tun da na taso ko daga ɓangaren Daddy'n Addaya ban taɓa fahimtar wani abu da ba daidai ba, na rantse da ALLAH duk iya kwakwkwafin mutum be isa gano waɗan nan bayin ALLAH ba sune hasalin iyayen da suka yi sanadiyar kawo ni duniyar ba, domin sune suka bani rayuwar, suka kuma bani tarbiyya me kyau, kuma ni ko abinda Daddy kema Aunty Yasmine wllh wani bin tausayi ne suke bani, wanda nasan hakan shi ne jarabawarsa, kuma nasan da yawa daga jikin family iren waɗan nan ababuwan kan faruwa don me zan fitar da wani tunani na daban a cikin rai na, wllh kunyi min komai Mamy Daddy kuma In sha ALLAHU kune zakuci gaba da amsa sunan iyayena,kuma kamar yadda maganar nan babu inda ta fita In sha ALLAHU ta zaunu kenan kawai abu ɗaya ne nasan naji daɗin sa ko babu komai zan yima mahaifiya na da mahaifina harma da Abba Abdallah adda'a...." Se kuma kukan da take yi yaci ƙarfin ta Ya Omer karonsa na farko yaja ƴar uwarsa jiki ya rungume sosai a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta yana ɗauke kwalla. Daga nan Addaya ta sake musu nasiha harda Daddy'n da gaba ɗaya jikinsa ya gama sanyi da yasmine wacce take jin In sha ALLAHU itama zata ƙaunaci ƴar uwarta kwatankwacin yadda iyayensu suke ƙaunar junansu, wanda dama tana masifar ƙaunarta kawai dai wani sanin kamar suna mata shishshigi a cikin rayuwarta ne ya saka take nesantasu cikin rayuwarta... Da haka Addaya ta fara shirin tafiya wacce dai taki yarda ta kwana ɗin har da Omer ɗin kuma suka tafi...... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 16 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta yanj zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Tun da suka tafi ɗin gidan ya sake komawa so silent. Amma sannu a hankali ya fara dawowa da ƙarsashin da kusan suka rasa daga farko, ga Daddy ya shiga taytayinsa don babu ƙarya yana ƙaunar Mamyn fiye da tunanin duk me tunani, don haka bayan ɗan fushi da shashshare junan da suka yi suka dawo normal. Yayin da a ɓoye Mamy tay mugun sakama Yasmine ƴan leƙen asiri duk inda zata iya kasancewa. Wacce ta warke ras sedai babu wasu ababuwan rashin ɗa'ar da takan yi tun daga kama daga kyarar masu aiki da wannan ciccin maganin da take ma Mamyn. Zuwa lokacin ma har ta fara fita wurin aikin nata an jingine Islamiyyar bogin a gefe, amma fa har yanzun duk inda ta zata da himar se taje cikin office nata take cirewa. Don haka baccin asarar da take yayi sauƙi, don bata taya Mamyn komai kamar Husna da take tsayawa kan jiki kan ƙarfi suyi komai tare. Sam ita to ko tsinke bata taɓa ɗaukewa Mamyn bare kuma maganar girki, ga manyan ƙawayenta biyu na hannun damarta sun dawo daga England karatu. Safiya da Nafisa don haka kusan kullum suna tare a wurin aikinta, idan kuma suka taso se su tafi yawo wuraren ciye ciyen kayan kwalam, don haka Mamyn tayi mugun saka mata ido don ƙawayen nan nata se a hankali kawai. Kuma bayan haka sun sha haɗuwa da John amma bata bama zuciyarta damar aminta da haɗuwarsu, don haka bata yarda ta tsaya dashi, sedai sannu a hankali wani abu me kama da deep emotional love ke ke sake tsaga jini da jijiyar kowannensu ya shiga ba tare da sun farga ba, su Fiyya da Nufy ma tuni sun san da zaman John harma sun san shi a zahiri amma bata taɓa yarda sun bayyana kansu gare shi ba. Har nan wurin aikin nata ma ya sani don yakan biyota har nan ko nace ya mata rakiya, bayan nan ma seda tafiyar kwana biyar ta kama shi zuwa kasar Ethiopia amma se da yayi One weeks. Inda ya sake haɗuwa da Almaz har take tambayarsa Unknown beloved nashi, kuma ta bashi hakuri na wancan lokacin da basu sake haɗuwa ba da kashe wayar da tayi jikin Abbansu sune ya matsa dama shi suka kawo asibitin ƙasar. shi yasa wancan ranar hankalinta ya tashi ta bashi tabbacin duk lokacin da yake neman wata shawara daga gare ta hanyarta a buɗe yake. Dirarsa kenan daga airport yasa Mecheal yowa nan dashi, domin fara tozali da bugun zuciyarsa Yasmine. Ita kuma yau gaba ɗaya ranta a ɓace don haka lokacin tashin nata koma yi be yiba ta fito don tafiya gida, sedai driver nata be zo kasancewar yasan se ƙarfe biyar yake zuwa ɗaukarta,gashi kuma se yanzun ma huɗu take ƙarasa cika, don haka tayo tattaki daga cikin Company ɗin da ƙafarta tana ta sake saka ƙiran wayarsa se faman buga tsaki take, se dai kuma Cak ta dakata sakamakon tozalin da tayi da kamar dama rashin ganinsan da bata yi cikin satin ne ke tunzura zuciyanta, komai aka mata se faɗa se fushi koda a gida ne, rashin ganin nan nasa da bata yi ba tsayin week ɗin gaba ɗaya jin kanta take tamkar wata Marainiya. Sabo da wata irin nutsatsestsiyar SOYAYYA'r da zuciya da ruhinta suka kamu dashi na John, sedai ita da kanta kunyar kanta take ji shi yasa ta zaɓi ƙin bashi dama da kuma bayyana maganar, barin ma wancan ranar da Mamyn tayi maganar ta kamu da ƙaunar ARNE. Wannan abu idan ta tuna wani shegen faɗar mata da gaba take, gashi ta lura da saka idon da Mamyn nata ta mata, don haka take kulle duk wata kafar da zata sama hujja a kanta, don ma ALLAH ya taimake ta duk sauran friends nata maza kamar wanda ALLAH ya kaɗar musu da hankali daga kanta, ta dena yawon gidan party tun farkon da John ya fara bibiyarta, se kwanan ma da suke ɗan charting dasu sama sama. Yana zaune cikin nutsuwa saman motar, kansa da p-carp se wannan sarƙar Cross ɗin wacce yau kuma taga ya sanja kamar yadda a saba yau me tambarin tauraro ce rataye a wuyansa, gaban rigarsa a buɗe yayi stocking rigar ta cikin wandon yanayin iskar da ake kaɗawa kan ɗan dage rigar sama se iyaka singlet ɗin kawai, wanda kai tsaye bai san cewa kasancewarsa hakan kawai a wurin kan rikita tsarin rayuwar da lissafinta yake ba. Kallo ɗaya ta masa tasan baya cikin kowanne mood me daɗi, haka shi ɗin ma a yau kallo ɗayan yayi mata ya tabbar akwai abinda ya mata kutse cikin farin ciki da kwanciyar hankali da kuma walwalarta,sosai fuska da jikinta baki ɗaya suka nuna gazawa da kasawarta, ji yayi zuciyarsa ta motsa da koma menene ya rabata da farin cikin nata, don haka ya ringa jin ahankali ƙirjinsa na bugawa da koma menene ya haddasa mata sauyin yanayin. A nata ɓangaren kuwa ganin yadda ya wani kafe ta ido ne taji wani irin haushi ya taso mata, kai tsaye ta nufi inda yake zaunen saman motar, cikin takunta me kama dana wahainiya idanunta cike da tsantsar wutar SO ɗin data gama cinye zuciyar dama me zuciyar duka. Ja tayi ta tsaya gabansa kuma tayi shiru, shi kuma ahankali ya ɗago kansa ya kalleta cike da kewar rashin ganintan da be yi duk satin, kai tsaye Idonsu suka haɗu wuri guda. Bakinta ne taji ya soma rawa ta na son faɗin abinda yake ba shike nan ba, ba kuma tasan iyaka abinda maganar ka iya janyo mata ba, don haka kai tsaye ta wani nuna shi da yatsarta manuniya tace. “Why don’t you leave me alone?” Ta faɗa ƙasa da murya, amma zafinta ya cika sararin da ke tsakaninsu, kafin ta sake furta. “Or you think this is a game?” Wanda hakan ya bama John damar sake jingina bayansa kaɗan da jikin motar daya saƙƙo, ba tare da alamar alamar komai, sake dubansa da kyau tayi tace. “Do I look like I’m playing?” Ta ɗan rausayar da kanta gefe wanda ke ɗauke da wani murmushi mai ɗaci daya tsaya iyaka saman leɓɓanta. “Toh bari ka ji.” Ta sake matsawa har kusan babu tazara a tsakaninsu me yawa.Har numfashinsu na gaurayawa da juna ta ce. “If you cross my path again like this…” Ta ɗan tsaya, idonta cikin nasa. “To zan karya maka zuciya.” Wani ɗan murmushi ne ya zame masa wanda be shiryama zuwan saba, tare da wata irin tsaiwa gabanta da seda ya saka gaban Yasmine faɗuwa, kana ya wani motsa zama lips nashi ba da yawa ba kaɗan ya ce. “Try me.” Wannan kalmar daya furta mata ita ce kalmar data saka nan take idonta ya canza, nuna shi tayi da yatsarta tace. “Are you looking for a fight?…” “I’m already in” Ya amsata yana sake matsota. Baka jin komai sai sautun buguwar zuciyarta. “Yasmine!!!.” Dum haka taji zuciyanta ya buga, sakamakon wannan shi ne karon farkon daya soma ƙiran ainihin sunanta kai tsaye. Ahankali ta ɗago idanunta da suke kamar a ɗan lumshe ta ce. “Don’t call my name.” ta faɗa cikin wata long tong voice. “Why?” “Because you don’t deserve it.“ Ya ɗan taka kusa kaɗan dap. “Then tell me what I deserve.” Zuciyarta ta motsa amma ta danne. “Distance.” Ya tsaya cak… amma bai ja baya ba. “Too late for that.” Wani shiru ne mai nauyi ya sake kame wurin, kafin ya taka kaɗan ahankali ya matsa kusa sosai har sai da ta ji bugun zuciyarta a kunnenta. “Ka sani…” ta fara da ƙyar. “Ni ba irin waɗanda kake wasa da su bane.” Ɗan rage tsayinsa yayi ta hanyar rankwafowa kaɗan, wanda ya saka Yasmine rumtse idonta da ƙarfi. “I know.” Nan take ta ja baya, idonta cike da mamaki da fushi. “Toh me kake nema a wurina?!” Ya kalleta kai tsaye ba tare da wata kwana kwanar komai ba, se tsantsar gaskiya a idanunsa ya nuna ta da hannunsa yace. “YOU.” Kalmar ta sauka a zuciyarta da bugar mata ƙirji. Cak tayi ta kasa magana, se yanzu wani shegen tsoron ma ya furta yana son nata ya kamata, riƙe kanta tayi da ƙarfi ta shiga girgiza shi kafin ta shiga ja baya da baya tace. “A’ah… wannan ma kamar hauka ne…” Taci gaba da ja baya,haka kuma tana ci gaba da cewa. “A’ah!” Kafin ta juya da sauri amma bai bari ta tsere daga kalamansa ba ya tare ta ta hanyar tare mata hanya da jikinsa ya ce. “Then don’t hide it… please, Yasmine. Tell me the truth.” Ta rumtse ido da ƙarfi, kamar tana yaƙi da zuciyarta… sannan ta buɗe su, wasu ruwan hawaye na taruwa a cikin su. “Ina son ka sani… dabi’ata ta sha bamban da taka. Haka za addinina da naka ba ɗaya bane, John… kuma wannan ba ƙaramin abu bane.” Shiru ya sake kama wurin me nauyi, “But feelings… they don’t care about religion, do they?” ya faɗa cikin rauni daya saka ta sake watsa mata idonsa cike da tuhuma ta tsaresa dasu. “Su feelings ɗin ne matsala?! Ni Musulma ce… kai kuma Christian ne. Babu yadda za’ayi na taɓa haɗa SOYAYYA'r da nasan ba gaskiya bace bare aurenka.” Cak haka ya tsaya… amma bai juyo baya ba. “So… all this… means nothing to you?” Ta matso kusa ba tare da ta sani ba. “Means everything… shi yasa nake jin tsoro.” Ta ɗaga hannu tana son ta taɓa shi… amma ta dakata. “Idan na bari zuciyata ta ci gaba… zan rasa kaina. Zan rasa addinina… kuma ba zan iya hakan ba.” “And what about losing me… can you handle that?” Hawayen da take ta ƙoƙarin tarewa suka zubo mata masu ɗumi. “Zan iya jure komai… amma ba zan iya jure na saɓawa Ubangijina ba. Ni da kai… muna da banbanci...” “Banbanci ba ya hana mutane zama tare” kai tsaye ya faɗi cikin Ingilishi. “Addinina da naka suna da banbanci!” ta katse shi. John ya kalleta kai tsaye, idanunsa cike da tambaya da rashin yarda shima. “Amma soyayya ai ba ta tambayar addini, Yasmine…” Shi ma ya faɗa da murya mai sanyi. “Zuciyata ta zaɓe ki ne, ba ta zaɓi addininki ba.” Ta girgiza kai a hankali, murmushi mai ɗaci na bayyana a gefen leɓenta. “Kai zaka iya ganin hakan a sauƙaƙe… amma ni ba zan iya ba.” Ya matsa kusa da ita kaɗan. “To ki koya min. Ki nuna min yadda zan zama wanda zai dace da ke.” ya faɗa a ƙage cike da dokantuwa da jirayin tsammanin wa rabbuka. Sai ta ɗaga kai, idanunta sun cika da wani irin zafi mai nutsuwa. “Ba game da ka canza bane, John…” ta ɗan dakata, “…game da ni ne. Ni ba zan iya rayuwa ina kallon mutumin da nake so yana tafiya a hanyar da addinina ya hana ni bi ba.” Shiru ya ratsa tsakaninsu na ɗan lokaci. John ya lumshe ido, sannan ya sake buɗewa, muryarsa na rawa kaɗan yace. “Don haka… kina cewa ko da ina son ki, ba zan taba isa gare ki ba?” Ta sauke numfashi mai nauyi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi itama tace. “Ina cewa… ko da na so ka fiye da yadda ya kamata… akwai wani iyaka da ba zan taɓa tsallakewa ba.” “Kamar?.” Ya tambaya da wani irin yanayi mai rikitarwa. Ta ɗan jinjina kai, hawaye na fara taruwa a idanunta cike da raunin da mayen SO ya gama cinye wa. “Saboda abin da nake tsoron na rasa idan na bi zuciyata kawai.” Ahankali ya kalleta da raunatattun idanunsa da suke shiken ruwan da suka cika kwarminsu. “To ni kuma fa? Ba zan iya zama wani abu mai muhimmanci a gare ki ba?” Ta kalli fuskar sa da kyau, kamar tana ƙoƙarin haddace shi. “Kana da muhimmanci… sosai har ya zama dole in tsaya. Sedai ina son ka nesanta kanka gareni domin zan iya rasa kaina gaba ɗaya idan har zanci gaba da tsaiwa dakai irin haka.” Wani lumshe idonsa yayi yana jin kamar ya yago zuciyarsa ya jefar a ƙasa. “To ki bar ni na zama wanda zai tsaya tare da ke… ko da kuwa hanya ce mai wahala.” Ta girgiza kai da ƙarfi wannan karon. “Ba kowa ne zai iya shiga wannan yaƙin ba John… kuma ba zan ja ka cikin abin da ba ka fahimta ba.” Iskar da ake kaɗawa naci gaba da kada himar nata tana sake tattaro shi jikintan. “Ka nisance ni… ka daina bibiyana.” “So that’s it?” Ya faɗa da ɗan dariya mai ciwo. “Ba ka zama nothing ba… shi yasa nake ce maka ka tafi.” Ya matsa kusa sosai har kamar babu wani space daya saura a gare su yace. “Then why does it sound like you’re breaking while saying it?” “Saboda gaskiya ba ta da sauƙi…” “And what if I don’t stop? What if I keep choosing you?” Saurin space ɗin dake tsakaninsu yake kokarin haɗewa ta tura shi da ƙarfi kaɗan baya, cikin wani abu me kama da rashin iya kame kai tace. “Kar ka sa ni na tsani kaina! Ka dena bibiyana… don ALLAH.” “You’re the only place I’ve ever wanted to stay.” ya faɗa a hankali. Ita kuma hawayenta suka zubo. Tana jin kamar ba zata iya jurewa ma yanayin ba bayan ta juya baya tace. “Then learn to leave… kafin mu hallaka juna.” fuuuuu ta bar wurin daidai motar da tazo ɗaukarta ta shige aka ja da mugun gudu..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 17 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* _Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta yanj zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci? To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials duka fa akan farashi mai kama dana kyauta ♡♡♡♡ ꨄ Ji yayi kamar da rayuwarsa ne motar ta tafi, ya jima ya tsayen da yake kamar wanda aka dasa shi a wurin,Mecheal har ya saka ran yau kuma kwanan bakin titi zasuyi kenan, tun da sun saba zaga garin Lagos ɗin sassafe da cikin dare, don haka yake ganin meya rage musu kuma?, seda ya bashi umarnin tafiyar ne kuma ya yarda da ba kwanan bakin titin za su yi ba ashe. A natse yaja motar suka nufi gida, a sace ya ɗan kalla side ɗin Boss ɗin nasa yake don ganin ko hankalinsa yana kan hanyar ne, ganin kamar gaba ɗaya hankalin nasa ma ba'a kansa yake bane ya saka shi ɗaukar hanyar mension nasu, duk da zuciyarsa ɗar ɗar da dukan uku uku take, aikuwa kamar daga sama yaji sauƙar maganarsa. “Where are we going with this?” Jikinsa ne ya ɗan ɗauki rawa, ya fara ƙoƙarin magana cikin kama kama da inda inda yace. “Sorry Boss, I thought we were talking about Mension.“ komai be sake ce masa ba daga haka ya meda idanunsa ya lumshe. Hanyar Ikoyi dole ya sake ɗauka inda ya koma tun last months, ko gama daidai tsayuwar motar be yi ba ya fice hatta phone's nashi a wurin ya barta se shi ne ya bi bayansa da duka kayansa. A tsakiyan parlourn ya tsaya yana jin yadda zuciyarsa ke masa kamar zatayi aman wuta. Maganarta ne ya shiga dawo masa kansa. “Then learn to leave…” Ya yi wata ƴar dariya mai raɗaɗi, tare da girgiza kai. “Leave?” ya maimaita a hankali. Hannuwansa duka biyun ya nutsa a cikin gashinsa yana jan sa kaɗan kamar yana son ya dawo da nutsuwar sa. “Na makara da wannan…” Ya juya a hankali, ya fara tafiya ba tare da ya san ina yake nufa ba. Amma abu ɗaya ya tabbata a zuciyarsa ba zai taɓa barinta ba har ƙarshen abada idan be mallaketa ba. Ɓangaren yasmine kuwa motar ce ke gudun amma jin take kamar zuciyarta ce ke bugawa fiye da gudun motar. Hannunta na rawa da jikinta, tana matse hannuwanta duka biyun kamar tana son hana zuciyarta fashewa ko dannarta daga gudun aikata wata ɓarna ko ba daidai ba. Driver nata akai akai na ɗan satar kallonta ta cikin madubin motar, ya lura da yadda take hawayen ke zubo mata amma bai ce komai ba. A hankali ta ɗaga hannunta ta goge hawayen, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta. “Na yi daidai… na yi daidai…” ta furta a hankali, amma zuciyarta kamar a ƙaraye take. Fuskarta na kallon window'n motar, tana kallon cunkoson mutanen dake ta fafutuka da warkajabe kajabensu, wasu a ababen hawa wasu kuma a ƙafa,wasu a kekuna,wasu mashina, gasu nan duk kowannensu na kai da komonsa,amma ita gata cikin lafiyayyar motar data gama haɗuwa da gajiya wajen kyau, amma babu irin fa'arar dake sauran fuskokin da take kalla. Ta cikin motar ta zubama sararin sama idanunta da suka kumbura, amma zuciyarta ta fi haka rauni. A hankali ta sake rufe idonta, sakamakon gimlawar muryarnta da tazo ta doki ƙofofin kunnuwanta. “You’re the only place I’ve ever wanted to stay.” Hawaye ya sake zubo mata. “Me yasa…?” ta furta. Daidai lokacin da driver nata ya gama daidai tsaiwar motarsa a parking car na gidan. Kowa babu a parlourn don haka drectly ta wuce ɓangarenta kai tsaye, anan parlourn ta zube tana cilli da takalmanta ta jefa jakanta saman kujera tare da riƙe kanta "Damm it" ta faɗa tana miƙewa tsaye ta ƙarasa bedroom nata, himar dake jikinta ta fara zarewa. Tana ƙarasawa jikin mirror tana kallar kanta da fuskarta, gaba ɗaya se taga kamar ba ita bace a jikin hoton madubin. Wata iska ta fesar tana faɗawa toilet, bata wani dauki lokaci me tsayi ba ta fito tana jikinta da towel. Sauri sauri ta shirya kanta cikin farar shirt da wandon Jeans ɗin da be gama kai ƙwaurin ta ba tana ɗaukar wata oversized hoodie ta ɗaura saboda sanyin da aka soma kaɗawa na bajewar hadarin da yay, tana shirin tayar da sallah aka yi knocking doorhandle nata ne ya sa ta juya ta kalli ƙofan, izinin shigowa ta bada Baba azumi ce me aikin da ita kaɗai ta yarda ta shigar mata se kuwa jikarta jimmala, wacce ita kuma taje kauye ne. sai da ta gaishe ta kafin ta tambayeta ko za'a kawo mata abinci nan sama ne?, murmushin daya bama Baba azumi mamaki ta kakalo. " No Baba azumi zan fito yanzun, Dada yana nan ne?" dake in taso tana ƙiransa Dada ɗin. " Ah ah sun fita tare da Mamyn ma amma basu ma dade da fitan ba" Kanta kawai ta gyaɗa mata tana cewa. "Okay kije ina zuwa, a sama min hot chocolote pls kafin na fito" Ɗan risinar da kai tayi tace. "Toh sai kin Fito" ta faɗa tana fita a ɗakin tare da rufo mata ƙofan, ita kuma ta koma jingine da jikin gado ta rufe hannuwanta da fuskarta. Ta jima sosai kafin ta saƙƙo zuwa parlourn, babu kowa a parlourn lokacin da take saƙƙowar, ita Baba azumi na kitchen tana haɗa mata hot chocolote ɗin data buƙata, ita kuma Husna yau wata exams ce da ita me zafi shi yasa bata dawo zata kwana a school. kujera ta ja a dining ta zauna tana daura ƙafafunta duka biyun a kan kujeran ta tanƙwashe, tana ɗaukan sandwich ɗaya ta kai baki tana maida hankalinta gaba ɗaya kan abinda ake haskawa, kan wani ɗan ta'addan da yake nemar gagarar duniyar koma ace ya gagara. "*CODE BLACK⁉️*" ta sake maimaita sunan da taji ya wani irin yankar mata da gaba, Waye shi?, ko kuwa wacce kalar ƙungiyace da take nemar gagarar duniyar baki ɗaya?. Kamar idan zata iya tunawa wannan shi ne karo na biyu data ga ƙasar _Nerovia_ ƙarƙashin jagorancin *Noctra city*, gaba ɗaya ko media ka shiga a wannan lokacin labarin dake trending kenan, *EMPEROR RAEL (TARIQ)* A duk lokacin ma'aunan mizanin kimiyya zasu kwalkwala abinda yake basu kenan, wato *EMPEROR RAEL (TARIQ)*. Daga ƙasan zuciyarta take jin kamar zata taɓa sanin mahin hinin labarin, kodai haɗa alaƙar wani abu ko wani nata wanda ya ze danganceta a cikin labarin ɗin. Maganar da Baba azumi ke mata ne ya saka ta ɗan nisawa tana dawo da nutsuwarta gare ta, "NAGODE" ta furta lokacin da take amsar hot chocolote ɗin, ba kawai Baba azumin kalmar Nagode ɗin da yasmine ɗin ta furta mata ta daka ba, harda iyayenta dake daf da shigowa amma basu kai ga shigowanba. Domin kuwa wannan kalma ba kalma bace me sauƙi wajen furtawa a wurin Yasmine. A natse cikin ƙaunarta me zurfi Daddy ɗaya riga Mamy isowa parlourn ya ɗan shafa saman kanta, fuskarsa ƙawace da kyakkyawan murmushi. “Ma sha ALLAH haka nake son ganin farin cikin Baby narh kuma Shalelena fiye da komi dake cikin wannan duniyar, ɗan rausayar dakanta tayi tana wani langoɓewa tace. “Thanks u Daah! nd I love U so much...Mamy barkanku da dawowa...” ta rufe zancen nata da da musu sannu da zuwa ɗin. Da kallo kawai Mamyn ta bisu a ranta tana ayyana me hali dai baya taɓa denawa, amma tunda dai yanzun tana iya lankwasata shi yasa abin yazo mata da sauki, kuma baya magana ko wannan faɗan nasa. Ƙiran daya shigo mata wayar tane ya sakata miƙewa tana nufar sama da hot chocolote nata. Ba me yawa ba tayi wayan ta kashe tana ɗaukan headphone ta saka a kunnenta tayi connecting da laptop nata, taci gaba da kallon Film ɗin da take na Kaddara 4. Bayan ta gama kallon kwanciya tayi cikin yanayi na kwanciyar hankali tana jin wani abu me daɗi na ratsata ilahirin jikinta idanunta a lumshe. Santala santalan ƙafafunta saman doguwar kujerar da take kwance ta yi hugging na matashin Kujerar irin tightly ɗin nan. Ɗan jujjuyawa take yi tana jin ƙaunar John na ci gaba da ratsa ko ina na jikinta Ta juya hagu haka kuma ta juya dama. Amma kalmarsa guda ɗayar nan ce kawai ke bibiyarta. “YOU.” Ta rufe idanunta da ƙarfi tana ambatar. “Ya ALLAH!…” Kafin ta sake wani juyin a kusan karo na babu adadi. “Ka fitar da shi daga raina…” Amma zuciyarta ta ƙi yarda.... ♡ _IKOYI high-brow area..._ Anguwar tayi wani irin shirun dake bama duk wani mazaunin dake cikin anguwar ko nace mension ɗin tsaro,da sanya nutsuwa najin cewar ehhh lallai yana cikin kwanciyar hankali, komai anguwar ta haɗa tun daga kan daraja, Tsaro. Abin dai gwanin birgewa musamman ma manyan gidajen dake tsaye kamar manyan ganuwar mulki, gaba ɗaya kuɗi,hutu,jin daɗi na rayuwa,wadata, kwanciyar hankali sune suka haɗa ƙarfi da ƙarfe suna ma mutanen dake cikin estate ɗin taron dangi tsabar gata. *JOHN* Drectly bedroom nashi ya wuce bayan awannin daya ɗiba zaune a parlourn. Yana mayar da ƙofan ya rufe harda saka key ya jingina da jikin ƙofar yana sauƙe wata zazzafar ajiyan zuciya, Ahankali ya ɗaura hannunshi kan heart ɗin sa da duk wani motsi na bugun da zuciyar zatayi tana bugawa ne tare da yasmine, hannun daya dage zuciyar ya kafe da ido jikinshi namai wani iri tuno wannan kalmar ta *Then learn to leave* ɗin da ta furta masa. Sosai kalmar ke wani kalan dukansa ba da wasa ba. Idanunsa ya Lumshe dafe da Heart nashibya kai kwance saman bed ɗin daya gama jin komai da komai. Hannunsa duka biyun ya saka yana taro ƙeyarsa dasu, ya zaman komai nasa na kallon sama ƙafafuwan sa kuma na a ƙasa yana zubawa Pop tarts lafiyayyun fararen Idanuwansa da yake jin kamar an sauya musu ƙarfin ganinsu.... A haka wani ɗan bacci yazo yay gaba dashi, daga nan be saka farkawaba har seda hasken ranar daya dallare idonsa kana ya motsa, sakamakon raba curtains da yayi biyu wanda hakan shi ya bama ranar damar haskesa son ranta ita ma, har kuma lokacin hannun na dafe da heart nashi. Ahankali ya zubo ƙafafunsa ƙasa yana saka hannuwansa biyu ya ɓangare yana yin baya kaɗan idanunsa su ɗan tafi suma luuuu wanda baccin be gama sakin su ba. A natse ya faɗa bathroom yayi taking shower ya fito yana nufar gaban makeken glass na window'nsa yana kallon waje. Hannunsa ɗaya cikin dark Gucci jogger pants dake jikinsa, Wanda yabi dogon figure nashi me tambarin Gucci dake jikin dogon wandon nasa, ya ƙara wani modern flair to the look not as casual as he wanted to look, fitted balanciaga hoodie ne a jikinsa charcoal grey colour, taushin cotton ɗin making him feel comfortable yet sophisticated. Ƙafafunsa zube cikin slipper's masu taushi na Versace's. Knocking doorhandle ɗin da akayi a bakin ƙofa sau biyu ne ya sa shi juyowa yana barin jikin glass ɗin, ya zauna a gefen gado yana bada izinin shigowa, da sallama Mecheal ya shigo Room ɗin yana sanye da kaya na shan iska tamkar dai me gidan nasa. Zama yay Kan kujerar dake facing data Boss ɗin nashi, kafin ya shiga wasu ƴan latse latse yay tare da tura may Ipad ɗin gabansa yana me furta... "Good morning Boss" Da ka ya amsa shi yana sake yin relax saman gadon daya daddafe gefe da gefensa kamar wanda ciwon naƙuda ya kama. Ganin ba zai tanka shi ba ne ya saka miƙewa. Breakfast ɗin da ya ajje masa don ya damu da yaga be fito ba shi ne ya biyo shi har nan ɗin dashi, idonsa a lumshen da suke be buɗe ba har ya kammala jera masa a kan table glass ɗin dake dap da gadon ya fita, ya jima a hakan kafin ya buɗe idon ya kalla break ɗin idan da yiyuwar ya iya ci se ya ga. A natse yayi break ɗin kana ya miƙe yana goge bakinsa da tishu ya fita suka bar gidan. Tun daga nesa ta hango shi tsaye yau ɗin ma jingine da jikin motarsa, waya ƙare a kunnensa alamar he is making a phone call, 3 quarter ne baƙi a jikinsa with gray polo idonsa lumshe yana ci gaba da amsar wayar. Yasmine ta sake ɗago idanunta a hankali tana ci gaba da kallonsa kai tsaye cikin idanu… kallon da ya haɗa kauna, tsoro, da kuma rashin tabbaci akan abinda zuciya ta riga data kamu da son sa babu zata ko tsammaninta. Ahankali ya fara jin bugun zuciyarsa na sanjawa zuwa na matakin kai da kai ɗin da yake ji duk lokacin data bayyana a wuri, don haka ya zare wayar daga kunnensa yana katse ƙiran idonsa a kanta daga tsayen da take. “My unknown beloved!” ya furta a saman laɓɓansa da motsawarsu kawai ta gani amma ta fahimci sunan daya ambata ɗin.Yasmine ta wani kallesa kafin ta fara taku ta iso har inda yake idanunta na taruwa da wani abun da bata san ko me ye shi ba tace. “John… ka san me? duk yadda nake ƙoƙarin ɓoye komai amma se gashi zuciyata tana ƙoƙarin yaudarata akan hakan.” Jin wannan kalmar ya saka John matsawa kusa kaɗan, idonsa cike da tambaya da tsananin ƙaunar da yake hangowa tashi cikin idanunta. “Then don’t hide it… please, Yasmine. Tell me the truth.” Ta lumshe ido na ɗan lokaci tana amsar bugun da zuciyarta take.m kamar tana yaƙi da wani abu a ranta… sannan ta buɗe su, hawaye na taruwa a gefen idonta. “Ina son ka fita a rayuwana!, ka barni haka nan na rayu cikin salama da aminci ba da azabtar wa irin haka ba.” Shiru ne ya ratsa wurin kafin ya kalleta zuciyarsa naci gaba da bugawa, ahankali murya cike da raunin da ake son tallafa zuwa kwarin gwiwa yace. “Ina son ki Yasmine!, zan kuma ci gaba da SO da ƘAUNARKI har ƙarshen abada.. ba zan taɓa rabuwan da kika ce inyi dake My world....” A hankali ta ɗago idanunta tana zuba masa manyan fararen idanunta tas a kan shi, kaɗan ya yi saurin ɗauke nasa idanun saboda abin da ya kalla daga cikinsu ba masu sauki bane. Don haka shi ma ya zuba mata nasa idanun har na kusan second goma ya ɗauka yana kallonta, yana kuma hukuntata da idanunshi kafin daga baya ya buɗe bakinsa kamar baya son yin magana yace. “You know I love you too.” kanta take ɗan girgiza masa. “Ka taɓa jin cewa zuciya na iya canza mutum…?” Kai tsaye itace kalmar data ratsa cikin kunnuwansa, wani ɗan murmushi yayi mara ƙarfi. “Ban taɓa yarda da hakan ba… sai da na haɗu dake.” Yasmine ta lumshe idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri. “Idan haka ne… ka shirya ka bi gaskiya… ko da zata raba ka da kowa da komai?” John ya ɗan yi shiru… kamar yana yaƙi da kansa, kamar kuma ya tafi nazari da fashin baki akan maganar nata ne. “Gaskiya…? Wacce gaskiya…?” Ta kalle shi da idanu masu cike da wani haske na daban. “Musuluncin da kake gudu daga gare shi… shi ne kawai zai baka salama.” Wani irin shiru yayi maganar ta bugi zuciyarsa kai tsaye. “Musulunci…?” Ya sake furta kalmar a hankalin daya saka Yasmine gyaɗa masa kai. “Ba don ni ba… ba don kowa ba… sai don kai da zuciyarka.” JOHN ya juya baya…yana kallon sararin sama. A karo na farko… zuciyarsa ta girgiza. Ba don saboda soyayya ba… amma saboda son gano gaskiyar dake cikin zancen nata... “Ina son ka fahimta, John ba zan aure ka ba!” Kalmar data saka John tsayawa cak kenan kamar an watsa masa ruwan sanyi, ko wanne akayi freezing nashi. “Saboda me? Saboda addini? wannan ne kawai?” Ta ɗaga murya kaɗan cike da mamakin maganarsa ta wai Addinin ce kawai?. “Wannan ne kawai ɗin ka ce? Ka kuwa san me kake magana kuwa?” Ya matso kusa da ita yana daidaita tsaiwarsa. “Eh! Ina magana ne akan mu! Akan soyayyar da kike ƙoƙarin guduwa daga gare ta!” Ta yi wata ƴar dariya mai ɗaci. “Soyayya?” Ta faɗa kafin ta nuna shi da yatsa, “Ka kira wannan soyayya amma baka gane komai akanta ba!” “To ki gaya min!” ya faɗa da ƙarfi, “Me nake rashin fahimta?!”. Ta taka zuwa gabansa, zuciyarta na tafarfasa. “Ina ce maka addinina ba wasa bane! Ba abu bane da zan ajje gefe saboda zuciyata ta motsa ba!” “Ni kuma ina ce miki zuciya ba abin da za a kashe bane saboda tsoro!” Wani ɗan cizar laɓɓanta tayi “Ba tsoro bane imani ne!” “To me ya sa kike ji kamar idan kika zaɓe ni, kin aikata laifi?” Ta ɗaga murya sosai yanzun kam tace. “Saboda a wurina haka yake tamkar laifin domin kuwa ƙatoton zunubi ne nake shirin aikatawa idan har na yarda zuciyana ta rinjayi ra'ayina!” Wani shiru ne ya ratsa wurin kowannensu cike da fargaban rashin tabbaci, amma fushin su bai ragu ba. Sai ya kalleta da wani irin zafi a idanunsa. “Don haka… duk wannan da muka gina, kina iya jefar da shi saboda abin da kika riga kika yanke?” Ta matsa kusa da shi, murya na rawa amma cike da tsauri. “Ba abin da na yanke bane hanyar rayuwata ce!” “Kuma ni fa? Ni ba na cikin wannan rayuwar taki?” ya jefa mata da tambayar kai tsaye. Ta ɗan ja baya kamar kalmar ta motsa mata zuciya, amma ta ƙi sassautawa. “Saboda tawa rayuwar tana da iyaka, ba ko ina ake shiga aji daɗin da ake nufin samu ba!” Ya yi dariya mai ciwo. “Ko kuma kawai baki son in shiga ɗin ne ba?” Ta kalleshi kai tsaye, idonta cike da hawaye amma murya nata ta tsaya daram. “Ko da ina son ka… to ka sani ba zan taɓa karya abin da nake yi wa ALLAH ba saboda kai.” Kalmar ta bugi zuciyarsa. “Toh kenan kina zaɓar addininki a kaina?” Ta amsa ba tare da jinkiri ba. “Eh haka ne.” Hannuwansa ya zuba jikin Quiter ɗin dake jikinsa yana jinjina kai a hankali, zuciyarsa na kamar zata karye. “Na gane… to ni kuma ba zan daina son ki ba Yesmine.” Ta juya da sauri, hawaye na zuba. “Ka daina bi na JOHN… don ALLAH!... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 18 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Tsayuwar da JOHN yayi a wajen kamar wanda aka dasa shi a ƙasa ce, har motar Yasmine ta ɓace daga idanunsa bai motsa ba. Iskar sanyin da ke kaɗawa ce kawai ke bugun fuskarsa amma shi ko kaɗan bai ji komai ba. A hankali ya sauke numfashi mai nauyi yana lumshe idanunsa. “Why does it hurt this much…?” Ya furta cikin muryar da ko shi kansa bai gane ta ba. Mecheal dake jingine jikin motar daga ɗan nesa ya jima yana kallonsa. Tun shekaru yana tare da JOHN amma bai taɓa ganin sa a irin wannan yanayin ba. Boss ɗin nasa wanda ko hatsarin da yake shiga a cikin jirgi bai sa shi firgita ba, amma yau se gashi mace guda ɗaya ce ta sauya komai nasa, gaba ɗaya neman birkita masa Boss ɗin nasa take yarinyar, wata zazzafan ijiyan zuciya ya fesar yana dan matsowa kadan a hankali yace. “Boss…” Amma JOHN bai amsa ba sai ma kawai juyawar da yayi ya nufi motarsa cikin tafiyar kasala irin ta mutumin da zuciyarsa ta gaji da yaƙi. Bai jira Mecheal ya buɗe masa ƙofar motar ba ya buɗe shi da kansa ya shiga. Tun da suka dauki hanyar dawowa gidan babu wanda ya sake magana cikinsu. Sai ma ƙarar music mai laushin dake fita a cikin motar da Mecheal ɗin ya saka musu dan ɗebe kewa ga ogan nasa… Amma duk da haka kalamanta ne kawai ke ci gaba da dawo masa. “Eh haka ne… na zaɓi addinina akanka.” Wani irin ɗaci ne ya zo ya masa tsai a ƙahon zuciyarsa. Yana saka gaskata a karo na farkon da ya ji an taɓa girman kansa. Ba don ta ƙi sonsa ba sai don ta fi son wani abu a kansa. ♡ IKOYI... Kai tsaye Mecheal ya danna hancin motar a katafaren gidan da John ɗin ya dawo da zama, kai tsaye a fito daga cikin motar ba tare da jira ba. Ya fara tafiya cikin nutsuwa amma daga yadda ya matse jaw ɗinsa zaka fahimci cewa lallai akwai abinda ya ɓoye cikin kirjinsa. Tun kafin ya ƙara sa shiga parlourn nasa yaji kamar muryan Mammoh nashi, wacce sam tsabar yadda yake a ruɗe besa ya kula da katuwar motar ta dake harabar gidan ba. Ahankali yaja ya tsaya cak a hankali ya ɗaga idanunsa yana kallon MOTHER ɗinsa dake zaune cikin parlour ɗin, sanye da wata doguwar riga wine colour, hannunta riƙe da glass cup na tea. Duk da shekarunta… har yanzu akwai wata irin haɗuwa da kwarjini tattare da ita. Idonta ƙanƙance a kansa da furta. “Come here.” Numfashi ya sauke a hankali ya ƙarasa cikin parlour ɗin. “Good evening Mother.” giranta ɗaya ta dage. “Really? Good evening?” Ta ajje cup ɗin hannunta tana kallonsa sama da ƙasa. “Tun safe nake trying to reach you.” “Busy ne” “Busy?” Ta katse shi da wata ƴar dariya mai saukin nauyi. “Busy doing what exactly?” Shiru ya mata yaki magana, wanda hakan ya bata damar mikewa tsaye tana gyara zaman silk wrapper ɗinta. “Deepika called me today.” jin sunan ne ya sa JOHN lumshe idanunsa a hankali kamar wanda kansa ya fara sara. “Mother not tonight…” “Oh yes tonight!” Ta faɗa da ƙarfi wanda ya saka John toshe kunnuwa sa ya juya yana son barin wajen amma muryarta ta sake tsaida shi. “Look at me when I’m talking to you!” Fuskarsa babu walwala ko kaɗan ya juyo, wanda ya saka Mother ɗin matsowa kusa da shi sosai. “Me yake faruwa da kai ne?” Ta tambaya tana kallon idanunsa kai tsaye. “Tun da ka dawo daga Ethiopian ka sauya gaba ɗaya.” ta sake fadi da harshen turanci. Komai be ce mata ba taci gaba da fadin. “Deepika is the perfect woman for you.” ta faɗi duk da tana dannar zuciyar ta, don gani take da John din nata yayi aure mace zata mallake mata shi gaba ɗaya, shi yasa take tsoron yayi auren tun farko. Wata ƴar dariya mara sauti yayi, a ransa yake ayyana da ace Mother ɗinsa ta san yadda sunan Yasmine kawai ke iya rikita duk wani tunani nasa. To da ba zata sake cewa Deepika perfect ba. Kai tsaye kuma maganar ta ta sake sauƙa tsakiyan kansa. “An tsara komai game da aurenku already.” Ta ci gaba da magana. “Families, companies, future… komai!” Sai yanzu ya ɗan ɗaga idanunsa ya kalleta. “And what if I don’t want it?” Wani irin shiru ne ya ratsa parlour ɗin. Mother ɗinsa ta ɗan zaro ido. “What?” Ya ƙarasa kusa da ita, tare da gyara tsaiwansa gabanta yana wani karkata kai irin na rikakkkun shegun nan yace. “I said… what if I don’t want to marry her?” Fuskar Mother ɗinsa ta sauya gaba ɗaya. “Is there another woman?” Tambayar ta fito kai tsaye, wanda ya saka JOHN ɗauke kansa gefe guda alamar ko a jikinsa. Wannan kaɗai ya isa ya bata cikakkiyar amsar ta akan shi akan auren. A hankali Mother ɗinsa ta ja baya tana kallonsa cikin rashin yarda. “Oh Jesus…” Ta furta a hankali tana ɗan riƙe kanta kafin ta furta. “Who is she?” Se da ya sauke wani numfashi. “It’s complicated.” wata dariya tayi cikin takaici. “No. Don’t give me that nonsense.” Ta nuna shi da yatsa. “You are going to marry Deepika and that is final!” Wanda nan take fuskarsa ta ɗan ɗauki zafi. “For once in my life can I choose something for myself?!” wani irin kafe shi da ido Madame Victoria din tayi cike da mugun mamakinsa. “You sound insane.” “Maybe I am.” Ya furta ba tare da tunanin komai ba Saboda gaskiyar ita ce…Tun haɗuwarsa da Yasmine komai nasa ya daina tafiya yadda ya saba. Madame Victoria ta ɗan girgiza kai cikin takaici. “This is why love is dangerous.” Wani murmushi mai ciwo yayi. “No Mother…” Ya faɗi yana ɗan lumshe idanunsa. “It’s dangerous when it’s real.” Kai tsaye daga haka ya juya ya hau upstairs ya bar ta tsaye wurin tana binsa da kallon mamaki da tashin hankali. Domin a karon farko ta ga ɗanta yana yaƙar abin da ko kuɗi ko iko ba zasu iya kashewa ba. Da wannan tashin hankalin ta nufi hanyar fita, kai tsaye da niyya tace Mecheal ya kai ta gida dake da kanta tayo driving ɗin. Fuskarta cike da tsantsar tashin hankali take kallon Mecheal din dake mata bayanin yadda Boss din ke gwagwarmaya a tituna a sabo da yarinyar kawai. “Ka tabbatar min…” ta faɗa cikin murya mai dauke da tsantsar ɓacin rai. “Who is the girl?” “Muslim Hijjab…” Wani irin tsalle zuciyarta tayi Idanunta suka buɗe sosai, shekaru wasu shekaru da suka jima da shudewa na ɗan gitta kanta “WHAT?!” Ta faɗi da ƙarfi tare da furta. “Impossible…” Ta faɗa tana ɗan girgiza kanta. Muslim!?, Ita John ze jayoma abin kunya da tozarci kuma?, dama yan uwanta da dangin ubansa na cewa tsoron sa take ji, to kuwa lallai idan ta bari maganar nan ta fita cikin dangi ba tare da tayi maganin matsalar ba akwai damuwa babba ma kuwa. “No ba ma zan taɓa barin hakan ya faru ba…” Tayi maganar da kallon Mecheal sosai tace. “Idan har wannan maganar ya fita cikin dangi, zan muzanta, Ina son yin wani abu…” Sai ta lumshe idanunta da har sun yi ja.... “Zan kawar da ita.” Ta faɗi tana fidda wani sautin huci, kafin cikin sake hangulowa tace. "Lallai duka bayanan yarinyar nake da ɓukata, tun daga Ranar haihuwarta har zuwa matakin da take a yanzun, And ƴar gidan uban waye ita? " ɗan zaro ido Mecheal yayi tare da furta. "Madame itama wannan girl ɗin Family nata nada wani irin power sosai a cikin garin nan...” wani kallon sa tayi cikin mugun ɓacin rai tace. “Waye ubanta a kaf garin Lagos shi ma nasa aci nashi uban harda uwarsa zan saka a haɗa min...” “Ɗiyar Ambassador Kabeer Usman Maina ce” Wani shegen lalataccen murmushi mara ɗan sautu Madame Victoria ɗin tayi, kafin ta dube shi da wani irin kallo da Idanuwanta da har na fidda wani kalan bala'i balain jin mugun zafin maganar da Mecheal ɗin ya kawo mata. Wani shegen munafikin numfashi a wahale ta fesar tare da furta... "Kana manta cewar gaba ɗaya Lagos din a hannunmu take ne?, mune nan masu juya al'amuran ciki da wajen Lagos din, dan haka ka ringa gyara wasu kalaman naka Mecheal right and understanding?" Daga haka tace ya fice mata a mota don ta fasa yayi driving din nata ma, tana kuma sake jaddamasa cewan lallai a goben take da buƙatar sabbin bayanai dan ga ne da yarinyar. ♡ *Yasmine* Tun da taja motar kusan hankalinta ke a rabe, ɗaya naga tukin ɗaya kuma naga John data gama kashewa da muggwan maganganun ta masu zafi. Don haka hankalinta yake kamar ba'a jikinta ba, wanda har bata san wata motar na bayan nata ba da suke kamar kusan a tare ma, hannunta ɗaya na saman sitiyarin motar ɗayan kuma ta ɗan riƙe kanta a hankali tare da ɗan lumshe fararen idanunta masu kaifi bayan tayi parking car nata. Har bata san lokacin da dayar motar ta faka ba har na cikinta na fitowa se jin saukar maganarsa tayi a kanta. "YASMINE" Ya kira sunanta a hankali cikin muryarsa mai cike da nutsuwa, wanda jin saukar muryan nata yasa ta buɗe idanunta din da take jin sun mata nauyi ta kalle shi. Yana tsaye daga wajen wurin iska na kada gashinsa me kyau da sheki Ya Omer ne, Ya Omer ɗin da yake mata wani irin mahaukacin So bana hankalin da zai iya dauka ba. Amma tun tuni ta rasa abinda yasa taji kawai be mata a mijin da zata iya aura ba, ga kuma yanzu data kamu da tsananin ƙaunar ARNE. Wani abu me kama da abinda aka rasa ta furta tana buɗe motar ta fito, hannunta rike da wayar ta m gaba ɗaya duk tayi laushi. "Barka da zuwa Ya Omer!, I'm sorry ban jika ba, and yau wata gajiyar da ban san taba nake jin na kwaso..." kansa ya gyada mata yana rufa mata baya don tuni har ta wuce zuwa cikin gidan. Mamynta tana kitchen Dad nata kuma be dawo ba, se iyaka Husna dake watching channel zaune a parlourn. Hannu kawai ta iya cirama Husna ɗin bayan ta bata side hug ta haye sama, ita kuma Husna na murnan taran Yayan nata da girmama kamar koda yaushe. Tana isa bedroom nata ta zube a gefen ƙofar kamar wata yarinyar da aka watsar. Wani kuka ta fashe dashi mara sauti sabo da ji tayi in ba kukan ta fasa ba hankalinta bazai taɓa kwanciya ba. Kukan take da nufin duk abinda ke sukar zuciyarta zai janye, amma maimakon sauƙi da afwar da take nema sema jin da take kamar ana ƙara zafin zuciyarta ne. "Na shi ga uku Ƙaunar ARNE nake da gaske jama'a...." Ta faɗi tana sake cusa kanta tsakanin cinyoyinta, wanda ya saka jikin Husna data shigo ɗakin a hankali soma dan rawa. Don ganin Yasmine ɗin haka…Da sauri ta rufe bakinta da hannunta. “Aunty Yasmine…” Se kuma ta karoso da gudu ta zauna kusa da ita. “Me ya faru? Me ya faru haka da zafi?” Da kyar ta iya ɗago kanta idanunta sunyi ja har fuskartama abinka da fara. Kwantowa jikin Husna ɗin tayi, don tanajin hakan shi ne kadai abinda zai iya bata salama a dai halin da take a ciki. "Son ARNE CHRISTIAN na kamu dashi Husna, Wllh da gaske ji nake kamar in ba aure shi mutuwa ma zan yi I love her³" Tayi ta nanata kalmar lover her ɗin. Dan bubbuga bayan ta Husnan ta shiga, don ba ta san abin da za ta ce mata ba saboda ta san akwai irin raunin da baya buƙatar magani. Haka kuma tasan awai irin SOYAYYAR da idan ka bari… tana kashe ka. Tunda ya shige bedroom nashi yayi rub da ciki saman gadon sa ya lumshe ido, kalmar. “Ka tafi John…Ka tafi ka nemo kanka… kafin ka nemo ni. Domin idan ka nemo ni yanzu… za ka rasa kanka.” kalmar ce kawai ke masa amsa kuwwa, kamar kuma wanda aka zabura ya mike zaune, tare da fiddo wayarsa ya buɗe search engine. Hannuwansa na rawa yayin da ya rubuta. *“What is Islam?”* Kowanne layi da ya karanta… yana buga zuciyarsa kamar gudumar ne. _Submission to the will of God._ _Peace through obedience._ _There is no god but God._ Wani rufe idanunsa yayi karo na farko cikin rayuwarsa… ya ji kamar yana tsirara. Kamar dukiyar da yake da ita, iko da yake da shi, suna… komai ya zama kamar ƙura a idonsa. “Submission…” ya sake maimaita kalmar. A duk rayuwarsa bai taɓa miƙa wuya ga kowa ba shi ne wanda ake miƙa wa wuya. Amma yanzu… wani ya ce masa akwai wanda ya fi shi ƙarfi. Wanda ba a gani… amma komai yana ƙarƙashinsa. Take zuciyarsa ta shiga rarrabewa cike da rudewa... *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 19 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Shiru kawai John yayi a tsakiyar gadonsa, idonsa na kan wayar amma zuciyarsa ba ta nan. Kalmar “Submission to the will of God” na ta juyawa a kansa kamar ana maimaita masa ta daga sama. “Submit…” ya sake furta kalmar a hankali. Wani irin murmushi mai cike da ruɗani ne yaso kwace masa. In banda abu ma ta ya za'a ce wani abu guda ɗaya ne za'a ware shi za'a bautama a masa biyayya ?, shi da ake masa biyayyar, shi da kowa ke tsoron kuskura ya ce masa a’a… yanzu shi ake cewa akwai wani da dole a masa biyayya?. Ahankali kuma ya sauke wayar daga hannunsa tare da dan lumshe idonsa ya koma yana jingina da jikin gadon. “Who exactly are you… Yasmine?” ya furta kamar tana gabansa. Amma a lokaci guda, hoton Yasmine din ya sake bayyana a zuciyarsa, kukan ta, yadda muryarta ke rawa idan ta kira sunan ARNE CHRISTIAN, da kuma yadda ta kalli tsakiyar cikin idonsa tace. “Na zaɓi addinina akanka.” Wani zafi yaji kamar ze tsaga masa kirji, ya tashi tsaye da sauri kamar wanda ake tunzurawa tunani mai nauyi. Ya fara yawo a cikin ɗakin, hannunsa sarke a kirjjnsa. “No… this is not normal.” ya faɗa da ƙarfi. Amma duk yadda yake ƙoƙarin karyata abinda yake ji… zuciyarsa na ƙara tabbatar masa da akasin haka. Haka jonh ya kusan raba daren yana searching dangane da kalmar Islam, da kyar ya iya barin kansa runtsawa wajen uku da rabi na daren ranar. Basu sake haduwa ba da YASMINE har tsawon 5 day's, ga Dad ɗin India yazo mahaifin Deepika wacce yau kwananta biyu a gidan John din amma ko kallo bata ishe shi ba. ♡ Madame Victoria tana zaune a ɗakinta da yake kamar na sirrin ta wanda yake ɗauke da duhu kaɗan, labarin Mecheal ya jefa mata tashin hankali fiye da yadda ta zata. “Muslim… Hijab…” ta sake maimaita sunan cikin ƙiyayya, waɗan su ababuwa da suka shude na kokarin faso brain nata su fito, Ta mike tsaye ta soma zagaye dakin a hankali kamar mai lissafin wani abu. Ta jima tana juya abinda zuciyarta ke kudirta mata kafin t ɗauki wayarta a hankali ta fara kira. Ana amsa kiran abinda ta fara bada umarni dashi shine. “Get me everything about Ambassador Kabeer Usman Maina’s daughter. Everything.” Daga haka ta katse kiran tana fitar da numfashi mai nauyi. “Idan aka bari har John ya yi kuskuren nan…” ta yi shiru na ɗan lokaci. “Ba zai zama John nawa ba kuma.” ♡ A gidansu Yasmine kuwa… Ta kwanta a kan gadon ta, idonta a buɗe amma zuciyarta a rufe da nauyi. Husna ta bar ɗakin bayan ta tabbatar Yasmine ta yi bacci ko da kuwa na karya ne tayi. Wayarta na gefenta, amma ba ta da ƙarfin ɗauke wa. “Ya Omer…” ta furta a hankali. Amma sai hoton John ya shiga tsakanin tunaninta ba tare da izini ba, ta rufe idonta da sauri tana me furta. “No… no no no…” ta fara girgiza kai. “Ya isa.” ta sake faɗa tana ta shi zaune cikin sauri tana riƙe kanta dake mata barazana da fashewa. “Why am I thinking about him?” Sai ga hawaye sharrr suka zubo mata. Domin gaskiya ita ma ta sani da wannan ɗin kamar wani gagarumin yaki ne tsakanin karya da kuma gaskiya. Karfe biyar saura John ya sake buɗe laptop ɗin sa. Ya fara karanta game da Islam fiye da da. Kowanne layi yana ƙara masa tambayoyi, ba amsoshi ba. Sai ya tsaya a wani abu: “A Muslim, God is closer to you than your jugular vein.” Ya ɗaga kai a hankali. “Closer than my life?” ya maimaita. Wani abu ya tsinke a cikin zuciyarsa, a wannan lokacin kamar ya ji muryar Yasmine a nesa. “Ba zan iya sauya addini ba…” Sai ya tashi tsaye da sauri. “Then why do I feel like I’m the one about to change?” ya furta cikin tashin hankali. Wani bugun ƙofa ya katse shi. “Boss…” Haka ya tsinkayi muryar Mecheal daga waje. John ya tsaya cak, kafin ya bashi izinin shigowa ta hanyar furta. “Come in.” Mecheal ya shiga cikin girmamawa, amma fuskarsa cike da damuwa. “Madame Victoria… ta fara bincike sosai.” John ya kalle shi cike da madaukakin mamaki. “Bincike akan me?” Mecheal ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce. “On Yasmine.” Idanunsa da yake dauke da bacci ya dan ja yana lumshe wa kamin ya ce. “Tell her…” ya fara magana a hankali. Sai ya dakata. Wani irin zafi ya hau masa zuciya. “Tell her… not to touch her.” Mecheal ya ɗaga kai cikin mamaki. “Boss… you sound like you’re falling.” John ya kalle shi da idonsa da suke cike da nauyin bacci yace. “No.” kafin yaja numfashi yana mikewa tare da furta. “I’m already in it.” Ya faɗa toilet Mecheal ya fita. Kwana biyu bayan haka…Karfe shida cif da cif Yasmine ta fito daga wurin aikinta da se yau ɗin take dawowa ma, ta fito ke nan tana gyara likab nata ta nufi wurin motar ta taji an furta kalmar.... “Ke…” Da wata murya mai kaushi mai ɗauke da iko haka taji an kira daga bayanta. Cak! Kuwa ta tsaya zuciyarta na bugawa. Kafin ta juya a hankali tayi tozali da wata mata tsaye a gabanta… Cikin kaya masu tsada da kamshi mai ƙarfi. Idanunta cike da wani irin ƙarfi da iko me tafe da girman kai. Kafin ta tako a hankali bodyguard biyu na take mata, kallo ɗaya ta mata ta tabbatar da cewar ba musulma bace, tun daga yanayin kananun shigar dake jikinta dan wata rigace a jikinta wacce da ƙadan ta wuce gwiwwarta. Cikin izza ta isa ga Yasmine ɗin tana tsayawa a gabanta cikin kaushin murya tace. “Ni ce nake nemanki…” matar ta faɗa a nutse amma kuma cike da cikakken iko mai kama da Umarni, Yasmine ta ɗan haɗe gira dan in jiji da kai da girman kai ne ai gidansa tazo. “Ni kuma ban san ki ba.” Matar ta ɗan yi murmushi me kama dana mugunta ko dai wani abu tace. “Amma kin san ɗana.” ta faɗi tana ƙare mata kallon sama da ƙasa don taga me yaja hankalin Yaron ta da har akanta ya gaya mata maganganun daya ga dama irin na daren jiya?. Cak! Yasmine ta dakata kalmar ɗana ta daki zuciyarta da gaske. “Ɗanki…?” ta maimaita kalmar, Matar ta ɗan matsa kusa da ita. “Joseph.” Nan take Yasmine ta gane har fuskarta na sanja yanayinta tace. “Toh?” ta faɗa da ɗan tsauri. Matar ta sauƙe tabarau ɗinta a hankali faffadar fuskarta na bayyana ta nuna kanta da yatsa tace. “I am his mother.” Matar faɗi tana sake kallar Yasmine daga sama har ƙasa, daidai da lokacin da wata iska me ƙarfi ta dage nikab ɗin Yasmine. Wanda matar taga kamar walkiya ce ta gimla mata, amma dake gwanace wajen shanye ko wanne irin tracks bata karaya ba sema matsawa data sake yi ta nuna ta da yatsa tace. “Ki nisance shi.” Ta faɗi kai tsaye ba tare da ɓoye ɓoyen komai ba. Wanda hakan ya ɗan ba Yasmine dariya har ta dan dara din mai sanyi, ta dan kada hannunta a fuskar matar babu tsoron komai tace. “Hi excuse me?” sedai kafin tace komai Matar ta rigata ta hanyar cewa. “Ki ji ni da kyau… duk abin da kike tunanin kina yi da ɗana…ki dakata haka nan.” wanda ya saka Yasmine gimtse fuskarta tana haɗe rai sosai tace. “Ni ban neman ɗanki ba.” Matar ta ɗan ɗaga gira. “Amma shi yana nemanki.” Shiru ne ya ɗan ratsa wurin, wannan karon kalmar ta shiga zuciyar Yasmine. Amma ta ƙi nuna hakan sema kallarta da tayi tace. “Toh ki gaya masa ya dena bibiyana dama wanda zan ba saƙon nake nema, amma fine tun da na hadu da gyatumarsa, nasan ke zaki fi kowa bashi gargadi me kyau!,.” ta mayar mata da maganar cikin tsauri. Wanda jin wannan maganganun ya saka Madame Victoria ta ɗan yi murmushi mai haɗari. “Zan iya… amma ba haka nake so ba.” Ta ɗan karkata kai tare ka kafe ta da ido tace. “Ina so ne… ke da kanki ki ɓace daga rayuwarsa.” Wani shegen haushi ne ya tuke Yasmine “So?” ta ɗan fesar da numfashi tace. “Ko me zai iya faruwa idan ban fita a rayuwan nasa ba?” Madame Victoria ta kalleta kai tsaye tace. “Everything.” Madame Victoria din ta faɗi tana medai eye glasses nata. Ta juya daga haka zata shiga motar ta. “HEY!” Haka ta tsinkayi muryan John mai ƙarfi ta katse mata shiga motar. Kusan a tare Madame din da Yasmine suka juya suna kallon John dake tsaye idanunsa cike da wani abu me kama da wuta. Zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi ya kalla mahaifiyarsa, kana ya kalla Yasmine. “Mom… what are you doing here?” ya tambaya cike da fusata. Madame Victoria ta ɗan yi murmushi kamar ba komai me cike da munafunci tace. “I should be asking you that.”Amma bai bi ta kanta ba kai tsaye ya matsa kusa da Yasmine yana me tambayan.... “Are you okay kuwa?” ya tambaya cikin damuwa. Amma Yasmine ta gaza kowacce irin maganama, domin wannan shine karo na farko da ta ga wani irin damuwa a idanunsa saboda Ita. Amma duk da haka bata nuna komai ba se ma cikin fusatar da tayi cikin ɗan ihu tace. “I don’t need your help.” Ta juya zata tafi John ya ɗan riko tsintsiyar hannunta wanda ya saka Yasmine tsaiwa cak. Ta juyo cikin ɓacin rai. “Let go of me!” Amma bai sake ta ba. “Not until you tell me what she said to you.” Madame Victoria dake tsaye tana kallon wannan scene ɗin tuni idanunta har sun fara canza wa. Wannan ba abin wasa bane kuma, Ahankali Yasmine ta kalli hannunsa da ke riƙe da nata… sai kuma ta ɗago ta kalleshi cike da tsauri tace. “Your mother is crazy.” Cak kusan gaba ɗayansu suka tsaya don da turanci ne tayi maganar, don haka baka jin komai sai bugun zuciyoyinsu da suke bugawa a kirjinsu. John ya ɗan matse hannunta bada yawa ba kafin ya zube mata mayun idanunsa a kanta ya furta. “Don’t talk about her like that.” Wannan karon muryarsa ta sauya. Yasmine ta ƙara fusata sosai fiye da baya “Then tell her to stay away from me!” daga haka ta fizge hannunta da ƙarfi ƙaran saukar mari ya biyo baya ji kake tasss³, mari har uku a jere. Cikin fusata tace. “Ba na ce ma kada ka sake yarda ko hijjabana hannunka ya sake yunkurin taɓawa ba?, to ina son ka sani cewar indai a haka kake tunanin zaka gina SOYAYYARKA gareni Ina son ka sani ƙa ra sa ruguza komai hakan keyi Right and understanding?.....” Wani irin shiru ne ya kame wurin na ɗan lokaci, John dake kame tamkar gunkin da aka sassaka haka yake kallonta ya kasa kowanne irin motsi. Sema ci gaban da yayi da kallonta tana fidda wani huci kamar wata za kanya. “Ka fita daga rayuwata.” ta sake faɗa da ƙarfi kafin ta juya ta tafi ba tare da waiwaya ba. Madame Victoria ta ɗan yi murmushi a hankali…amma a zuciyarta wuta ce na marin da aka ma dan nata me kama da tozarci. Amma kuma a wani bangaren dadi take ji ta san ko babu komai dole ya hakura da Hausa gul din nan dolen dole, a cikin zuciyarta tace. “Toh… haka ne kenan…” ta furta a hankali tana jin wani abu me kama da samun sassauci. John kuwa…ya ɗaga kai a hankali yana kallon sama idanunsa sun canza gaba daya. “I won’t stop…” ya faɗa a hankali. “Not now.” ya faɗi yana kaima iska naushi kafin ya nufa motarsa Mecheal na bata wuta wanda dama ganin Madame Victoria din ne ya sa bai fito ba, don shi ya nuna mata Yasmine ɗin ya kawo ta har wurin aikin nata a jiya. ★ Daddyn India ne da kansa yaje ya dawo John din gida, inda Madame Victoria tayi gum da bakinta taki sanarma kowa labarin abinda idanunta suka gane mata, amma Papa’nsa yasan da maganar Muslim girl ɗin da John din ke so, sedai baya da labarin abinda ke faruwa daga iyaka haka nan. Ga mugun sanya idon da aka masa kamar wani ragon da ake son tirkewa, Ba a daɗe ba gidan ya fara sauyawa gaba daya, bada hayaniya ba, ba da faɗa kai tsaye ba. Don Daddyn India ma da dawo ba sosai ya fiye fitowa babban parlor ba sun fi gane kowa yana nasa bangaren. Gefe guda uwar Amarya Deepika wato Lady Rebecca, ita kanta wata macece da kamar ma taso tafi Madame Victoria jiji da kai, sedai tasu tazo ɗaya sosai amma kowa na hassada tsakaninsu da ci gaban da wani ya samu. Ahankali ya sauko jin gidan babu hayaniyar komai yau din, a dining ya tarar da iyayen nasa, a natse ya zauna a dining table ɗin, iyaka papansa ne se kuma Madame Victoria se Jelly me bi mishi kenan. Suna dinner nasu a natse babu wanda ke magana cikinsu saboda ganin yau din su kadai ne ya saka Madame ba Papan labarin abinda ya faru ranar. Madame Victoria ce fara ɗaga kai a hankali ta kalleshi “Joseph…” Ta kira sunansa cikin nutsuwa. Ya ɗago ba tare daya kalla inda take ba ya furta. “Yes, Mom.” Ta ɗan yi shiru na daƙiƙa ɗaya kamar tana nazarin fuskarsa, cikin son danne komai dake son taso mata tace. “Ka canza.” Kai tsaye wani shirun ya sake ratsa wurin kafin ya saki murmushin da yaba kowa mamaki yace. “People change.” Tare da ɗan ɗaga gira ɗaya yana ɗaukar glas cup yakai bakinsa. “Not like this.” Papa’nsa ya ɗan kalleshi daga gefe. “Your mother is right.” Cak John ya tsaye tare da ɗan daure fuska. “Me kuke nufi?” Madame Victoria ta ɗora hannu a tebur a hankali cike da muryan bada umarni tace. “Muna son ka daina fita kamar da!, ka daina mu’amala da mutanenka kaf koma waye, ka daina duk ababuwan da ka saba.” Se ta dan dakata tare da motsawa ƙadan taci gaba da fadin. “Saboda muna son killace daga annobar dake kokarin riskoka kamar shekarun baya.” “Stop bringing up things nobody asked you about.” Papa ya dan faɗa cikin tsawa don bai son kowa nasu ma yasan da wannan shudadden labarin, kafin Papa’n ya ɗan haɗe gira ya kalli John din yace. “Don’t what?” “Don’t bring her into this.” Madame Victoria ta ɗan yi murmushi… amma ba na farin ciki ba tana kallon Papa din daya furta. “Toh kenan gaskiya ne.” ya faɗa yana tsaida idonsa akan John. “Wace ce ita?” Papa’n ya sake jefa masa tambayar kai tsaye. Shiru John yayi yaki ya musu magana ba don bai san abin da zai ce ba, sai don saboda kawai ba zai faɗa din ba, in yaso wacce ta kawo zancen inta matsu ta faɗa, kamar kuwa Madame Victoria tasan abinda ke ransa kenan ta riga shi yin maganar ta hanyar furta. “Hausa girl ce.” Cak Papa’n ya ɗan ja da baya kadan akan kujerar da yake. “Hausa…?” Ya fada cike da tashin hankali domin shi duk labarin da take bashi ai bata taba ce masa ga yaren gul ɗin ba. “Joseph…” Ya faɗa cikin mugun bacin ran da baya John mamaki. “Ka san abin da kake shirin aikatawa kuwa?” wani dage girarnsa John din yayi tare da dage kafadunsa yace. “I do.” “Then stop it.” Papa’nsa ya faɗa yana mikewa tsaye “Ba za ka sake jawo mana irin wancan matsalar ba.” John dake kallon Papan da mugun mamaki yace. “What problem?” ya tambaya cikin son sanin ko ma mi suke shirin ɓoye masa din daya danganta rayuwarsa ta bayan. Papa’nsa ya ɗan buga tebur da hannu. “Everything! Difference in culture… religion… background!” John ya miƙe tsaye a hankali har kujarar daya tashi a kai na ɗan ƙara kaɗan, cike da son ya fusata iyayen ya musu wani kallo ya dage kafada daya... “This is my life.” Ya faɗa cike da isar daya saka Madame Victoria miƙewa ita ma tace. “Mu kuma ai mu muka haife ka. Wanda ya saka John kallonta kai tsaye yace. “And that means I don’t get to choose?” Yayi maganar da alamar tambayar daya saka su yin shiru. Iyaka wannan tambayar ta tsaya a iska. Madame Victoria ta matso kusa da shi ta taɓa kirjinsa tace. “Zaka zaɓa…” ta faɗa. “Amma ka zaɓa da hankali.” Ta ɗan tsaya kaɗan sai taci gaba da cewa. “Domin wasu zaɓukan… ba sa dawowa baya.” Hanyar samansa ya dauka yana sake ce wa dasu. “This is my life.” _Hhhhhhhh tabbas nie AMMEY LAYLERH ✍️ nace wllh duk wanda ya bari akayi tafiyar nan ba tare dashi ba, to kuwa tabbas anci da rabon sa ne. _Saboda a labarin kansa bamu fara komai ba, duk wata sauran kulla kulla da cakwakiya tana can a gaba, inda muka kusa kammala free pages.... _ _Kana na baku wata ƴar satar..... Amma dai bari nayi gummm da baki na masu hasashe da zurfin tunani tuni zasu fara hango gaskiyar cewar Yasmine ba ita ce hasalin S tamu ba🤸😎😍🤣😂😜 Hhhhhh ALLAH dai yasa masu karatun na ganewa _ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 20 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Gaba ɗaya da kallon tashin hankali suka bishi harda jelly. Lady Rebecca ita kuma da sawo kanta kenan ta tsaya cak ɗin tana daskare da mutuwar tsaye, wani shegen baƙin cikin bata san kome ne farkon labarin ba na kamata, da Kyar ta iya danne abinda take ji ta kara so parlor din tana shimfida murmushin yaudara ta maza kamar bata ji komai ba, suma sai suka yi saurin gyara yanayin nasu tana zaman daya bama Papa damar barin wurin kai tsaye, hannu lady Rebecca sukayi da Madema Victoria kana suka zauna, Lady Rebecca din tana faɗa mata dinner tazo yau Chicken wings and BBQ ribs Emo ya musu se juice na Cranberry juice. Ita kuma wannan duk bata fiye son su ba, saboda bata son tayi jiki sosai, shi kuma naman alade jiki da kitsen jiki yake sawa ya saukarwa da mutum tumbi da teɓa. Ta kuwa ci sa'a su nan mutanenta aka yi, Beef steak, Roast chicken, se lemu na Lemonade, Eggs (omelette, boiled, scrambled) Bread, pastries da cakes duka su sukayi. Kaɗan kaɗan suke taɓa ƴar fira har rana ta gota, kana ta koma nata bangaren cike da tunanin san sanin abinda ke faruwa. Tun da Lady Rebecca ta bar sashen itama Madame Victoria ta wuce nata bangaren, ita kuma jelly ta wuce school gidan ya koma wani irin shiru, Yayi tsit tamkar ba a cikin sa ake rayuwa ba. Kowa yana nasa ɓangaren, amma duk da haka wani irin nauyin da ba a gani yana yawo cikin ko ina na gidan. John yana tsaye jikin glass window na ɗakinsa, hannunsa cikin aljihu, idanunsa akan hasken birnin da ke kyalli daga sama. Amma ba komai yake gani ba face fuskar Yasmine lokacin da ta mare shi. Tasss³… Har sau uku tamkar yanzu abin ke sake sauka a kunnensa. Ya ɗan runtse idanunsa tare da sauke numfashi a hankali. “She hates me…” Ya furta da wata murya mai cike da ruɗani. Amma zuciyarsa ta ƙi yarda. “No…” Ya fada yana girgiza kansa kaɗan “She’s fighting me.” Wani ƙaramin murmushi marar daɗi ya suɓuce masa. Bai taɓa tunanin akwai ranar da wata mace za ta mare shi ba… har kusan karo na uku kenan… sannan shi kuma ya tsaya ba tare da ya fusata ba. Yadda take riƙe da shi kamar numfashinta, wani irin bugun zuciya ya doki kirjinsa lokacin da ya tuna yadda ta ce: “Na zaɓi addinina akanka.” Ya juya da sauri kamar wanda wani abu ya tokare masa ƙirji. Hannunsa ya dafe kansa. “Why is this getting into my head?!” Ya furta da ƙarfi sai kuma ya tsaya cak… Domin a karon farko a rayuwarsa… ya ji tsoron kansa. Tsoron cewa wata rana zai iya rasa komai saboda yarinyar nan. A can ɓangaren Madame Victoria kuwa…Tana zaune cikin duhu tana kallon video ɗin CCTV da aka turo mata. Video ɗin marin Yasmine. Sau ɗaya. Sau biyu. Sau uku, shiru ta yi tana kallo har video ɗin ya ƙare. Sai kuma ta ɗan murmusa. “Interesting…” Ta furta tana ɗaga wine glass ɗinta. “Yarinyar tana da zuciya.” Ahankali kuma murmushin nata ya ɗauke. Idanunta suka canza launi zuwa wani irin baƙin duhu. “But she touched what belongs to me.” Ta ajiye glass ɗin a hankali. “John…” Ta furta sunansa kamar mai mallaka. “Ka fara manta ko kai ɗin waye.” Sai ta ɗauki waya ta kira wani number. Ana ɗagawa ta ce cikin muryan bada umarni tace. “I want the girl watched everywhere she goes.” Ta ɗan dakata. “And if she tries getting close to my son again…” Kafin a hankali murmushinta ya dawo. “Break her completely.” ♡ Yasmine kuwa… Tun da ta dawo gida take jin kamar zuciyarta na cin kanta. Ta cire nikab ɗinta a hankali ta zauna gefen gado. Hannunta har yanzu na rawa. Domin duk da tsanar da take ƙoƙarin nunawa… Lokacin da John ya riƙe hannunta taji wani abu. Wani abun ɗin da ya tsorata ta, saurin dafe kanta tayi tana furta. “Astaghfirullah…” Hawayen da take ƙoƙarin dannewa suka silalo mata. “Ya Allah…” Ta sake furtawa cikin rauni. “Kada ka jarabceni da abin da zuciyata ba za ta iya ɗauka ba…” Sai kuma ta tuna yadda ya kalle ta bayan marin. Ba fushi bane cikin idanunsa, ba kuma ƙiyayya bace, wani irin ciwo ne mai zurfi, mai kuma karya zuciya. Nan take ta mike tsaye cikin tashin hankali tare da furta. “No!” Ta faɗa tana girgiza kanta da ɗan ƙarfi. “Ba zan tausaya masa ba.” Amma kuma zuciyarta ta kasa bin umarninta ta karfi. Domin duk sanda ta rufe ido shi kawai take gani, yadda ya tsaya yana kallonta kamar wanda aka cire masa rai. ♡ Washegari…Tun karfe tara na safe. Dining hall ɗin gidan ya cika da manyan mutane cikin nutsuwa mai nauyi. Lady Rebecca na gefen Daddy'n India data fito dashi zuwa babban parlourn, tana sanye cikin shiga ta alfarma. Sai Madame Victoria dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana sipping coffee ɗinta cikin Isa. Sai John da sakkowarsa kenan daga saman stairs. Yaja ya tsaya ba tare daya kalla kowa ba, domin yau ne karo na farkon da ya sauko breakfast ba tare da ya gaishe da kowa ɗin ba. Ya ja kujera ya zauna shiru kawai. Daddy'n India ne ya ɗan kalle shi tare da ƙiran sunanshi. “John.” Bai ɗago kan ba see kawai amsawa da yayi da. “Hmm.” Madame Victoria ta aje cup ɗinta a hankali. “Where were you last night?” shiru yayi ya kiyin magana. “John, I’m talking to you.” Sai ya ɗago idanunsa a kanta. Cold. Heavy. Tired. “Don’t start.” Tsit kowa a wurin ya yi kamar wanda ruwa ya cinye. Lady Rebecca ta ɗan ɗaga gira ɗaya cikin mamaki. Madame Victoria kuwa ta ƙanƙance idanunta. “Excuse me?” Sai John ya ɗan matsa gaba. “For the first time in my life, Mom…” Ya haɗe idanunsa da nata. “I need you to stay out of my business.” Wani irin shiru ne ya sauka akan dining hall ɗin. Saboda babu wanda ya taɓa yi wa Madame Victoria magana haka. Koda Daddy'n India sai da ya ɗago kai. Amma John bai tsaya ba. “Don’t go near her again.” Ya furta a hankali amma da nauyin da ya girgiza zuciya.Madame Victoria ta yi wani murmushi mai cike, Murmushin da baya nuna farin ciki ko kaɗan. “Oh…” Ta furta tana gyara dan gyara zaman ta cike da isa. “So the Muslim girl has finally destroyed your senses.” John ya matse face nashi sosai fiye da farko fitowarsa. “She didn’t destroy anything.” Daga haka ya miƙe tsaye tsam ahankali. “She made me realize how empty this life is.” Kusan sarkewa numfashin Madame Victoria yayi a karon farko na ganin cewa tabbas da gasken gaske ɗanta yana fara kubuce mata da kwarai. ꨄ Tun bayan maganar da John yayi a dining hall gidan ya sake sauyawa ba wai an fara faɗa kai tsaye bane ba… a’a. Amma komai ya sauya hatta da iskar gidan ma ta koma mai nauyi. Kowa na kallon John kamar wani baƙo da ba su taɓa gani ba, duk da dai dama in ya tashi cin mutuncinsa ya kan shuka musu tafi haka ma, So amma abinda yasa wannan ɗin yafi musu ciwo shi ne akan Hausa girl ne. Shi kansa Daddy India ya fara lura da yanda JOHN din ke canzawa a hankali. Canjin da ba kuɗi bane ya jawo hakan ba. Ba kuma mace kawai ba. Wani abu ne mai zurfi… wanda yake fara shiga ransa. John ya daina yawan zama da mutane. Hatta fav piloting nashi ya jima da jingine shi a gefe, se dai a waje babu wanda yasan ainihin abinda ke faruwa. Saboda duk dare… idan duniya ta yi bacci… John na cikin duhun ɗakinsa shi kaɗai da laptop. Islamic lectures. Qur’an recitations. Videos akan rayuwar Annabi ﷺ. Tambayoyi akan Allah. Tambayoyi akan rayuwa. Kuma duk sanda ya gama sauraro…Sai yaji kamar zuciyarsa na narkewa. Sannu a hankali wani abu ya fara rushewa a cikinsa. A ɓangaren Madame Victoria kuwa… Ranar da aka kawo mata rahoton cewa John ya soke babban dinner meeting saboda yana cikin ɗaki yana kallon Islamic documentary… Ɗan ƙaramin babban hauka ne kawai bata buga ba a gidan, amma dai kam tayi ƙarami tare da dukan glass tana furta. “What nonsense!!” Ta faɗa cikin tsananin fusata tana kallon Mecheal dake tsaye gabanta ya sunkuyar da kansa, wanda shi ne ya kawo mata rahoton. “Madame… he’s changing.” “SHUT UP!” Ta daka masa tsawa har ya yi shiru. Numfashinta ke fita da ƙarfi. “Wata yarinyar musulma zata tarwatsa min rayuwar ɗana?!” Ta fizgi wayarta da sauri. “Get Deepika here. NOW.” Cikin ƙasa da awa ɗaya sai ga isowar Deepika dake can wani babban clubhouse. Sanye cikin wani dogon red gown mai matuƙar kyau. Amma yau ko makeup ɗinta bai iya ɓoye irin tashin hankalin dake cikin idanunta ba, sabo da tun kan ta iso har mutane sun tsegunta mata abinda ya faru. Domin ita ma ta fara noticing canjin John. Yana guje mata ba kamar baya da sukan zauna har da dariya ba, ko kiranshi tayi da zarar yaga number ɗinta ne baya ɗagawa. Lokacin da ta shiga ɗakin Madame Victoria… tsaye ta tarar da ita jikin window. “Mom…” Deepika ta kira cikin sanyin murya. Madame Victoria ta juya a hankali. “Your fiancé is slipping away.” Kalmar ta sauka kai tsaye cikin zuciyar Deepika. “What do you mean?” Ta tambaya, Madame Victoria ta matso kusa da ita. “That Muslim girl.” Nan take fuskar Deepika ta canza. “Yasmine?” Madame Victoria ta ɗaga kanta da take jin kamar ze rabe. “He’s changing because of her.” Kafin Deepika ta yi magana… Sai ƙofar ɗakin ta buɗe suna ɗaga kai sukayi tozali da John dake tsaye sanye cikin black shirt. Fuskarsa cike da gajiya. Amma idanunsa sun sauya. Idonsa ya sauka akan Deepika. Sai ya ɗauke kai. “John…” Deepika ta kira sunansa tana murmushin forced smile. Amma bai amsa murmushin ba. Madame Victoria ta ɗan haɗe hannu. “Good. You’re here.” John ya kalleta ba tare da motsi ba. “I’m busy.” yayi maganar yana kokarin barin wurin tayi saurin fisgoshi tana me furta. “Busy doing what?” ta faɗa da tsauri. “Watching Muslim sermons?” Ya faɗi don shi be wani iya ɓoye ɓoye ba Wani irin shiru ne ya sauka a wurin, Deepika ta zuba masa ido cikin tashin hankali. Sai John ya ɗan lumshe mata idanunsa kafin ya furta a hankali. “Yes.” Cak!!! Deepika ta tsaya tamkar mutum-mutumi. Madame Victoria kuwa ta matse baki sosai. “What did you just say?” John ya kalleta kai tsaye yace. “I said yes.”Ya ɗan ja wani numfashi. “And I’m tired of pretending.” Daddy'n India dake shigowa parlour ɗin ya tsaya cak shima, “What is going on here?” Sai John ya juya a hankali yana kallon Daddyn tare da mahaifinsa yace. “For the first time in my life…” Ya furta cikin wata murya mai nauyin gaske. “I finally feel like I’m searching for something real.”Madame Victoria ta girgiza kai cikin rashin yarda ta shiga furta. “No… no… this is insanity.” Sai John ya ɗan yi murmushi marar Sautu yace. “Maybe.” Ya ɗan dafe ƙirjinsa. “But every time I hear about Islam…” Ya haɗiye wani abu mai nauyi. “My heart becomes quiet.” Kukan Deepika ne ya katse komai. “STOP IT!!” Ta fashe da kuka sosai. “If this is about that girl then I can change! I can do anything you want John!” Amma John ko kallo bata ishe shi ba. “No…” Ta girgiza kai hawaye na zuba. “No no no… don’t look at me like that…” Sai ta ƙarasa gabansa ta riƙe shirt ɗinsa da ƙarfi. “You’re mine!” Ta faɗa tana kuka da dukan kirjinsa. “We were supposed to get married!” John ya runtse idanunsa cikin ciwo. “I’m sorry Deepika…” Kalmar ta kashe wani abu a zuciyar ta, ta sake shi a hankali kamar wacce aka cire wa rai. Madame Victoria kuwa a wannan lokacin ji tayi kamar ta fasa ihun da kowa se yaji a cikin duniyar. Sai dai ihun ma ta gane cewar wuri yake samu, tun da gata yau nema take ko haukan ne ta taɓa, amma ta gaza sema jirin daya fara dibarta ahankali numfashinta na rawa. “No…” Ta furta kamar mai roƙo. “Not my son…” Amma John ya juya ya nufi stairs nashi ba tare da ya sake kallon kowa ba, kafin ya hau ya tsaya ba tare da ya juya ba ya furta. “And cancel the wedding.” Kamar walkiya kamar saukar aradu haka kowa yaji saukar kalmar John din, wanda ya saka Deepika fasa wani irin kuka mai karya zuciya. Lady Rebecca da ta tsaya bakin ƙofa kuwa sai da ta riƙe bango saboda tashin hankali. Madame Victoria kuma Idanunta suka canza gaba ɗaya. A hankali ta furta. “That girl…” Sai ta ɗago kanta tana bama kanta karfi da kwarin gwiwwa ta ce. “She started a war.” Tunda Madame Victoria ta haye samanta babu abinda take se safa da marwa cike da tashin hankali. Kafin ta fito bata yi duba da cewar dare bane ta kalla ɗaya daga cikin guards tace. “Prepare the car.” Ta faɗa da murya mai cike da iko da kuma izza. “Tonight… I want to see that girl.” Wani daga cikin guards ya girgiza kai. “Yes ma’am.” da sauri ta juya “Nobody… nobody takes my son away from me…” *AMBASSADOR KABEER HOUSE* Tun kan sha ɗaya kowa ya wuce makwancinsa kowa ya yayi bacci amma banda ita, tana zaune saman gadon ta gaba daya abinda ya faru ne keta famar dawo mata ka ɗazu a wurin dinner meeting ɗin nan, ko tace dinner party, ita ta ganshi lokacin daya shigo da mugun ɓacin rai amma shi bai ganta ba, tayi saurin buya domin haka kawai taji bata son ya ganta a wurin. Tana tsaka da wannan tunanin ne taji anyi wani mahaukacin hong me ƙarfi, wanda ya saka ta saurin mikewa gabanta na wani irin mugun bugawa tace. "Innalillah wa'inna ilaihi raji'un ³ me ke faruwa kuma yanzun?" tayi maganar ne kuma tana mufar window na ɗakinta, abinda ta gani ba ƙaramin taɓa ta yayi ba. Wasu lafiyayyun manyan motoci ne har guda uku duka black masu ɗauke da glass tinted, Kuma gaba daya sun tsaya ne a harabar gidan nasu. Zuciyarta ta buga da ƙarfi don ita duk a tunaninta ko yan fashi ne ma. “Ya ALLAH…” TA faɗi tana dafe zuciyarta tana kuma ja baya a mugun tsorace, domin dama yau wuni suka yi labarin manyan barayin da har da rana tsaka ma shige duk inda suke so suke suyi fashinsu kuna su fito lafiya, saboda tsabar karancin tsaron dake tattare da kasar tamu. A kuma daidai lokacin ne ƙofar ɗakinta ta buɗe da ƙarfi, wanda ya sakata wani irin mugun firgitan daya sakata fasa ƙara a tunaninta barayin ne suka iso. Amma ganin mahaifiyarta ce ya ɗan sanyaya mata rai sedai ita ma Mamyn fuskarta cike take da tsoro me tsanani. "Momy me ke faruwa a gidan nan ne wai?" Hannunta Mamyn ta kama tana ce mata ba lokacin taja hannunta zuwa bangarenta data ɓoye Husna. A can waje kuwa cike da isa aka budewa Madame Victoria mota ta fito tana wani huhhura hanci sama, daga inda take tsayen ta ɗaga kanta idonta ya sauka kan gidan. Sai tayi murmushi mai mara ma'ana tare da furta. “So… this is where she lives…” Gaba ɗaya gidan ya cika da ruɗani Servants na gudu…guards na fita waje… Ambassador Kabeer ya fito cikin gaggawa yana tambayar “Wane ne a wannan lokacin?!” ya faɗa cikin murya mai cike da iko daidai lokacin da da kofar ke buɗewa. Madame Victoria Osteen ta bayyana cikin takunta ɗaya bayan ɗaya mai cike da izza da kuma iko…kamar wacce ta mallaki duniya. Taja ta tsaya a tsakiyar parlour tana ƙare masa kallo kafin idonta kai tsaye ya sauƙa akan Yasmine da fitowar su kenan da Mamy. Wani irin shiru mai nauyi ne ya dan ratsa parlourn kafin ta ɗan karkata kai ta murmusa tana me furta. “So… you are the girl.” YASMINE kuwa ganin da wacce idon ta suka mata tozali ne ya saka zuciyarta bugawa… amma kuma hakan be nuna ta tsorata ko a fuska ba, sema dubanta da tayi ba tare da tsoro ko shakkun komai ba tace. "Me ya kawo ki gidanmu? ko a tunaninki nan ɗin ma kin zo ne kiyi baraza wa ahalina tunda kin kasa ja da ɗan da kike ikirarin cewar naki ne?..." “Kin san ko wace ni ce, Kana ina son ki sani nazo gida gaban iyayen ki ne domin su farga da wuri, ba sai sun rasa ki suzo suna kukan rashi ba?” Ɗan gyara hannunta data nade a kirjinta Yasmine tayi, ta re da ɗan murmusa kaɗan mai ɗauke da raini tace. “Wacce take tunanin duniya mallakarta ce… wacce girman kai da izza suke hana mata gane gaskiya.... Sai kuma ta ɗan dakata. “Sai dai kuma ki sani kin makaro!, domin wannan zuciyar a yanzun ma ta sama kwarin gwiwwarta na ci gaba da ƙaunar abinda take so, ina son ki sa a ranki cewar nie Yasmine diya ga ambassador so na shayar dake mamallakin da zata ko tsammaninki bai taba baki ba right?..." Wani irin shegen shiru ne ya hade wurin Servants ɗin dake tsaitsaye suka kalli juna. Ambassador ya ɗan motsa amma ya tsaya be ce komai ba, don yaga yarsa tana tsaye da ƙarfinta. Ahankali Madame Victoria ta matsa kusa sosai da Yasmine har numfashinsu na haɗuwa tace. “Ki saurara sosai…” Ta faɗa cike da ikon dake dauke da mugun gargadi tace. “Ki nisance ɗana.” Wani kallo Yasmine ta mata tare da cewa, “Ko idan aka ki nisantar nashi me zai faru?” ta jefa mata tambayar kai tsaye, wanda ya saka Madame Victoria ta ɗan yi dariya irin ta shegun da suka jima a duniya tace. “Zaki lalace tabbas.” ta dan dakata tare da sake kallonta da idanunta masu kama dana mashaya tace. “Zan lalata rayuwarki… zan sa ki nemi mutuwa… amma ki rasa wannan kadan kenan idan har baki nisanci dana ba.” Husna ta dafe bakinta da duka hannuwanta, Mummy ta matsa kusa da Yasmine amma Yasmine din ta ɗaga mata hannu, alamar kowa ya tsaya. Sai ta matsa gaba kaɗan idanunta da su kayi ja ta ta zubama Madame Victoria tace. “Ki zo ki lalata nin na ga ni.” ta faɗa a hankali tana fesar da wani abu me kama da bacin rai taci gaba da cewa. “Se dai ki sani… ni ba irin yaran da kuke tsoratarwa bane.” Wani irin shiru ya sake sauka a wurin. Madame Victoria kuwa mutuwar tsaye a wurin tayi tana kallonta kamar me na zartar halaye ko dabi'unta. Kafin a hankali ta janye tana dan sakin murmushi tare da tafa hannayenta tace. “Good…” ta faɗa tana sake tafa hannayen nata. “Ina son ƙalubale.” Daga haka ta juya ta fara tafiya, seda takai har baƙin kofar fita ta ta dan dakata. Ba tare data juyowa ba se dan kada hannunta da tayi suka bada wani sautun ɓass kana tace. “Let the game begin.” Ta saka kai tana ficewa zuwa inda Motocinta ke fake ta shige suka bar gidan cike da wani irin mugun kudiri a cikin rai da ruhinta. Suna barin wurin Mamy ta isa ga YASMINE cike da wani irin tashin hankali tace. "YASMINE me kike yi haka?, faɗa faɗanma kuma da Christian, ina kika san wannan matar wacce da gani bata san ko miye imani ba, and Waye dan nata da take ta ikirari a kansa?" "JOSEPH" furta a fisge tace. "Kwarai da gaske matuka na kamu da mayen SO da KAUNARSA Mamy...." Numfashin Mamy ne ya kusa fita da ƙarfi amma tayi hanzarin tare shi, tana bin Yasmine ɗin da kallon baki da hankali?, ba kuma kisan abinda kike shirin aikatawa ba, ta bude baki kenan za tayi magana Daddy ya daga mata hannu yana dubar Yasmine ɗin da Husna yace kowa yaje ɗakinsa... ♡ JOHN dake zaune cikin motar daya dakko ya fito bayan yaga fitar mahaifiyar nasa ne ya sauƙe wani nannauyan numfashi, domin tun daga lokacin da yaga mahaifiyar nasa a wurin aikin Yasmine ɗin ya saka mata bi diddigi. Yaji komai Yes… yana saurare, wani ɗan rufe idonsa yayi amma kuma daya tuna da irin maganganun Yasmine ɗin da yaji ta faɗi har besan lokacin da kyakkyawan murmushi ya bayyana a fuskarsa. Ya wani dafe kirjinsa yana me furta. "Just because you love someone, doesn't mean they feel loved by you. You know love is an action. Love is a verb. It's not enough to just say it. If you really love someone. You'll do the work to make. Sure that they feel it from you too...." Ya kai ƙarshen maganar yana wani lafewa jikin kujerar motar.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 21 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Cikin one week kawai sega Yasmine da John sun fara sabawa, duk da ba wata magana me zurfi ce ke haɗa su ba, gashi kuma yana shirye shiryen komawa bakin aikin sane, kuma har tsayin wannan lokacin be nuna mahaifiyarsa komai dange da gidan su Yasmine ɗin da taje ba. Yau tun farar safiya aka tashi da hadari amma ALLAH be kadarta ruwan ba se yanzun da yamma take list, har kamar ma ana gaf da kiran Sallah, se dai a zahiri kuma lokacin bai kara soba, dan da ƴar sauran tafiya ma. Ruwa ake kamar da bakin ƙwarya wanda ruwan yau shi ya hana John fita ko ina, yana bedroom nashi bai yana tunanin ta yadda ya kamata ace ma ya ɓulloma lamarin. Ƙarar da wayarsa ta dauka ne ta dakatar dashi dole daga duniyar tunanin daya lula, wani kasaitaccen murmushi ne ya kubce masa ganin ko waye me kiran, yau shi ne karo na biyun data taɓa kiransa ita da kanta, tun bayan da sukayi exchange number. “Yas-mine!?…” ya ƙira sunanta cikin murya mai laushi. Daga can bangaren Yasmine kuwa, seda ta ɗan fesar da wani numfashi me dumi tace. “John… ina kan titi. Motana ta tsaya driver ya tafi zai nemo mai gyara amma ya daɗe bai dawo ba. Ga ruwa, ga uban duhu… I'm scared,” ta faɗa cikin murya shagwaɓa mai ɗauke da tsoro. Ahankali ya tashi zaune daga kishingidar da yayi cikin taushin murya yace. “Wani titi kike?” ya tambayata kai tsaye yana mikewa, kwatancen inda take ta masa ya fita dake ruwa ake yasa kowa yana ɗaka a lafe babu wanda yaga fitan John ɗin. Cikin mintuna talatin da biyar, ya iso wajen duk da iska mai ƙarfi da ruwan da ke hana gani sosai. Wanda garin ya fi farko duhu mai nauyi tsabar ruwan da ake tsalawa. Da ƙyar ya hango motar nata, Ta buɗe masa ƙofa ya shiga. “Sorry, Yas-mine!… ruwan ya tsananta sosai. Are you okay ma?” ya tambaya da damuwa a fuskarsa wacce so ya gama cinyewa, “I’m fine… yanzu da ka zo,” ta amsa tana kallonsa da wata nutsuwar da haka kawai taji tana jin ya kamata. Ɗan murmushi kawai yayi yace. “Mu tafi na sauke ki gida” Ta gyada kai suka fito ya cire jacket ɗinsa ya rufe mata kai da shi saboda ruwan ga kuma sanyin sa garin ya dauka, Suka nufi motarsa.Duhun wurin da ruwan da ke sauka ya sa Yasmine ta matso kusa da shi sosai saboda tsoro. John ya fahimci hakan, sai ya ɗan tsaya ya ɗauke ta a hankali ya kai ta cikin mota duk da bata so ba. Suna shiga suka rufe ƙofar dukansu sun jike, amma John bai damu da hakan ba hankalinsa gaba ɗaya yana kan yadda zata ji lafiya. Ya kunna motar amma gani ya yi ba zai iya tuƙi da kyau ba saboda tsananin ruwan. “Zan tsaya nan kaɗan… sai ruwan ya lafa,” ya faɗa yana ajiye motar a gefe duba da cewar shi pilot ne, kuma a dokance duk pilot baya taɓa tuka mota, Idan kuma aka kama shi da laifin hakan hukunci ne me tsanani a kansa. A hankali ruwan dake jikinsu ya fara ratsa su yana haifar musu da wani mugun sanyi, “Yasmine…” ya kira a hankali yana sake miƙa mata jaket ɗinsa dake gaban motar ajje. Ta sake amsa ta rungume jikinta da shi, shiru ya ratsa tsakaninsu. Duhun wajen, sautin ruwan, da ƙarar iska duk sun haɗu sun ba yanayin wani irin nauyi. “I’m scared,” ta faɗa ahankali kuma ƙasa ƙasa, “Ba komai… ina nan,” ya bata amsa da nutsuwa. Ta jingina kaɗan kusa da shi not ba dan saboda wani abu ba, sai don ta samu kwanciyar hankali. John ya kame kansa sosai, yana ƙoƙarin ya kiyaye nisan da ya dace, bai so ya wuce iyaka ba domin ita ce da kanta ta dokan ta masa iyakokin. Yanayin wurin ya sake ɗaukar shiru duk da cinkoso irin na garin Lagos, sun jima sosai a wurin kafin ya tada motar su tafi, har cikin gidan ya shigar da motarsa ya sauke ta ya rakata har kofar shiga kana ta ɗaga masa hannu tana masa bye bye ta shige shi kuma ya juya ya tafi. Washegari Joseph ya tashi da mummunan zazzafan zazzabin da iyayen suka san tabbas ya bari ruwan sama ya dake shi kenan?, hankali tashe suka yi asibiti dashi don ko wanne irin kuzari baya da, shi kansa yasan illar da dukan ruwan ke masa amma kuma ya fita din cikin ruwan. Kwanansa biyu a asibiti kana suka dawo gida, yaki ma kowa magana duk kuwa da uban tambayar da ake masa. Wani ne daga cikin guads din gidan ke sanar ma da Mademe Victoria ai ranar fita yayi a mota, shi kuma ya bi bayansa ba tare daya bari ya gan shi ba, don ba motar gidan ma ya bi bayansa ba a napep ne. Daga nan ya bata wayarsa ta fara kallon hotunan da aka ɗauke su cikin motar, da lokacin da yake cire jacket na jikin sa ya rufa mata, da lokacin daya dauketa din nan tayi saurin dago ido a tsorace tana kallonsa. Wani yawu Madame Victoria ta hadiye da taji ya mata wani shegen daci a makoshi. Bangaren Yasmine kuwa… lokacin da yake suke isa gidansu ta ce banda kiranta, banda kuma tura message ko mata magana WhatsApp. Amma kuma kwana biyun da bata gan shi ba duk se taji ta jigata, tana zaune a babban parlourn gidansu wayarta na hannunta. A kai akai take kallon screen na wayar, Ba saƙon, ba kiran. Sai ta lumshe ido a hankali. A hankali kwanaki suka fara wucewa… John ya kiyaye duk wasu kalmanta a kansa na cewar ba ƙira, ba kuma zai nemeta ba... A gidan su Joseph kuwa wani irin tsaro Papa da Madame Victoria suka sake ninkawa a gidan nasu saboda kawai kada John ya sake fita ko ina, wanda shi kuma dama tun da ya dawo daga asibiti be taɓa koda tunanin fitar bane, amma kuma yau yaji duk duniya babu ubanda ya isa hana mishi fitar nan, don haka ya sakko cikin wasu kananun kaya amma dogon wando har kasa da t-shirt me yalwa ba ire iren irin wacce ya saba sakawaba. Se dai me yana isa security ɗin suka nemi dakatar dashi, wani shegen kallo ya jefa ma securities ɗin yana gyara rikon da yama Pcarp nashi yace. "Duk wanda ya yarda darty hands nashi ya taɓa jikina, ni kuwa sai na kwantar dashi a gadon asibiti kuma ya bar aikin sa kenan har gaban abada a gidan nan, bama a cikin gidan nan ba harma kasar baki daya saina lalata duk wani offer nashi na samun aiki" yay maganar cikin yarensu, wanda ya saka securities ɗin ja baya. Ko kallon inda Mecheal yake bai yi ba ya fita da kafansa, a ƙafa ya dinga yawata duk wurin daya masa. yana tafiya shi kaɗai a wani titi mai natsuwa, ba tare da Mecheal ba. Ahankali yaji wani sauti me sanyi ana furta. “…ALLAH ya ce…” muryar wani malami ce ke fita daga wani ƙaramin speaker. John ya tsaya cak ba tare da shiri ba, daga gefen titin kuma wani tsoho ne zaune a kujera wayarsa a hannunsa yana sauraron wa’azi. Washe gari daya sake fita yana zaune a café shi kaɗai sai Cup ɗin coffee a gabansa, Wanda bai kai ga sha ba, daga gefe dashi kuma wani matashi ke zaune. Wanda shi bai lura da John ba din ba, ya fitar da wayar sa ya kunna audio na karatun Al-Qur'ani. Sautin ya cika wurin a hankali bada ƙarfi ba, amma irin mai shiga zuciyar nan ne, wanda ya saka John ya ɗago kai kaɗan. Duk da bai fahimci harshen ba amma ya ji wata nutsuwa ta musamman. Wani irin nutsuwar da bai saba da ita ba. Ya lumshe ido na ɗan lokaci kafin ya buɗe su a hankali. “Why does it feel like this…” ya furta a hankali. Haka dai John ya cinye satin yana saurarar ma ban banta ababuwa. Ranar wata Juma’a da misalin sha biyu ya shirya suka fito shi da Mecheal, garin yi shiru sai motsin mutanen dake wucewa zuwa masallaci. “Stop here.” Ya faɗa a hankali wanda ya hakan yasa Mecheal ya ɗan kalleshi da mamaki… amma bai ce komai ba ya tsaya har zuwa sanda John ya buɗe ƙofar motar ya fito. Idanunsa suka sauka kan masallacin da ke gabansa, Mutane nata shiga a hankali, wasu cikin natsuwa wasu cikin gaggawa. Daga ɗan nesa da wurin ya tsaya ba tare daya motsi ba. Zuciyarsa na bugawa kaɗan ahankali. “Just watch…” ya faɗa wa kansa. Sai ya tsaya a gefe yana kallon su suna shiga. Wani tsoho ya wuce kusa da shi. Ya tsaya kaɗan yana kallon John. Sai ya yi murmushi. “Dan samari ya ba ka shiga ba?” ya tambaya cikin sauƙi. John ya ɗan rikice tare da cewa “No… I’m just” Tsohon ya ɗaga hannu yace. “Ka tsaya ka kalli yadda ake bautar UBANGIJI ma ibada ce idan zuciya na neman gaskiya.” gaban John ne ya sake faɗuwa amma bai ce komai ba, sema gefe da ƙofar masallacin daya samu ya zauna. Daga can cikin masallacin kuwa Muryar liman “Bismillah Rahmanir Rahim! Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu,Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillaha, famanyuddul fala hadiyala waasshadu'alla'ila'ha'illalahu wahdahu lasheri kalah, wa asshahadu anna muhammadan abduhu warasulu! ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum. Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa'ah wattaƙullah lazitasa'aluna bihi, wal'arhama innallaha kana alaikum raƙiba,ya haiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna'asdaƙal hadisi kitabullah wa'ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi'a wa kulla bidi'atin balala wa kulla balaltun finnar." Tun da aka dakko doguwar adda'ar ko mace hudubar zuciyar John tayi wani irin tsalle. Kafin ya dawo daga wannan tunanin ya sake tsinkayo muryan Malam liman yana ci gaba da faɗin. “Ya ALLAH duk wanda zuciyarsa ke neman gaskiya!… ya ALLAH ka nuna masa hanya bisa tafarkin gaskiya da gaskiyarka...” Aka ci gaba da huduba akan masu neman hanyar gaskiya da gaskiya domin ranar gobe kiyama su rabauta. Kana aka ƙira sallar juma'a duk John na zaune daga gefe, sedai mutanen se sake karuwa suke wanda har seda ya sake komawa ta can baya sosai amma yanajin karatun sallar limamim, daga inda yake zaunen kansa a kasa yana sauraron komai amma bai fahimci komai ba sosai…Se dai kalmar “gaskiya” ta tsaya masa a rai ga kyakkyawan karatun dake fitowa cikin suratul _An nisa_ Har aka gabatar da sallar juma'a ɗin raka'a biyu. Aka sake wasu adda'oin masu ratsa zuciya. Bayan an idar da sallar ne mutane suka fara fita. Har kuma lokacin John bai motsa ba, sema sake matso wa inda yake zaunen ɗazun da yayi, ganin mutanen da suka shimfida abin sallar su sun nade, wasu ma buhu ne suka shimfida. Wannan tsohon na ɗazun ya sake fitowa ganin John zaune har lokacin ya isa gabansa, “Sunanka?” ya tambaya John din cike da hikima da kamala. John ya ɗan ɗago kai ya kallesa. “…Joseph.” Tsohon ya ɗan yi murmushi me faɗi da kayatarwa yace. “ALLAH ya shiryar dakai John.” Cak John din kuya ya dakata daga shirin mimewar da yake shirin yi, bawai don ya saba jin irin wannan kalma ba. Cikin zuciyarsa ya tambayi. “Me yasa kowa ke ce haka…?” Tsohon ya kalleshi cikin nutsuwa, saboda yaga sauka da hawar mukwallatonsa, kai tsaye ya bashi amsa da. “Saboda idan mutum ya tsaya a ƙofar gaskiya…toh yana dab da shiga ne.” Daga haka dattijon ya tafi yabar John da tunani mai nauyi. Ko da ya koma motarma wani shiru yayi daya saka Mecheal kallonsa ta madubi yace. “Boss… are you okay?” kamar ba zai tanka masa ba, dan kansa ma ya fitar ta woje kafin yana idanunsa ya lumshe yace. “…I don’t think I’m the same anymore.” Lokacin da John ke shigowa babban parlourn nasu babu kowa, sai iyaka Madame Victoria dake tsaye tana kallon shi daga sama har kasa, tana kallon yadda yake tafiya, yadda yay wani shiru, yadda ya shigo kamar mara laka, Kai tsaye wayarta ta fidda ta saka ƙiran Mecheal. “Where did he go today?” Mecheal ya yi shiru kaɗan yaƙi cewa komai, don yana tsoron uban gidan nasa sosai. “Answer me.” ta sake faɗa a ɗan tsawace. “…Masjid.” Ya faɗa cikin tsinkewar zuciya. Wani irin mugun bugawa kirjin Madame Victoria yayi har tana kusan kwarewa tace. “What Masjid…?” ta maimaita masjid din Idanunta nayin ɗan duhu. Wayar ce ta zame daga hannunta ta faɗi ta fashe, ta nufi bangaren Papa da gudu tana ihu. John yana isa bedroom nashi ya isa gaban madubi yana hargitse tulin sumar kansa da tayi tozon rakumi ta gaba, keyar kuma tayi shuwal shuwal haka ya tsaya a gaban madubin yana kallon kansa, sai dai abinda yake gani yanzu a fuskarsa ba wannan fuskar John din bace ta pilot, wannan din fuskar wani mutum yake gani daban, fuskar mutumin da yake shirin karya duniya domin soyayya. Ƙarfin Iko na Family, Family ɗin da suke kamar ba mutane bane na yau da kullum. Saboda su ne Cristina Dynasty. Iyaye masu iko, masu kuɗi, masu tasiri a duniya. Wanda suke da tarin mallakin ababuwa tun daga kan kamfanoni… jiragen sama… siyasa… Kuma abu ɗaya ne dokar su. Ba a taɓa auren wanda bai dace da sunan family nasu ba. Da baya ya koma ya zauna, kamar kuma wanda aka zabura ya mike ya soma hada kayansa domin tafiya Ethiopia. Yana son ganin Almaz. Yana son su sake tattaunawa game da YASMINE da feeling Islam da yake ji... A lokacin da Madame Victoria ta isa bangaren Papa jikin sa kawai ta faɗa tana sake fasa wani sabon kukan, "Mun shiga uku sweetheart wllh in ba muyi wani abu akan Joseph ba muna da da rasa shi.” tallafarta yayi seda ta gama kukan ta ya share mata kana yake tambayar ta abinda ke faruwa?, nan ta shiga sanar masa da komai, wanda tace a gobe take son a tada maganar aurensa da Deepika bayan ta nuna masa har pictures din nan data tura a wayar wannan security din, take a lokacin Papa ya kira Patriarch mahaifinsa kenan shi kakan John din kuma ya sanar dashi halin da ake ciki, cikin gaggawa yace shi ma yana tafe zuwa gobe. Daga nan ya kira Daddyn India wato Daddyn Deepika ya sanar dashi ya gayyato friends nashi za'a yi baikon John da Deepika, wanda ya saka deepika dake tare da mahaifinta da mahaifiyarka buga ihu tayo bangaren nasu a guje. Kai tsaye bangaren John ta nufa daya mance be rufe kofar bedroom nashi ba, isarta yayi daidai da fitowarsa daga wanka bathrobe sanye a jikinsa Iya gwiwwa fara tas me naski naskin da yake ɗan sirka blue, tana isa babu tsammani yaji ta rungume shi tayi saman gado dashi suka fara juyi, ya bude baki zai yi magana ta kuwa hade bakin nasu ma ta fara bashi wani irin deep kissing ɗin da zai yi wahala in kai cikakken lafiyayye ne ka gaza ke tare tarkon, bare kuma shi da hakan ba komai bane gare su, se dai duk da haka ALLAH ya saka masa wani irin tsentsenin abun har se lokacin da gama tabbatarma da kansa cewar ya gama mallakar mace, Se gashi Yasmine a karon farko itace ta soma fara karya wannan alkadarin nashi. Ita da kanta take kissing nashi tana sake juyi dashi a saman faffadan gadonsa da duk ta gama yamusewa. Jin hannunta na yin inda ba'a aike ta bane ya saka dan sauran hankalin John dawowa ya figeta daga jikinsa yana tsaida kan diga diganta ya ɗauke ta da zafafan maruka a jere har uku kyawawa. Ya jata kiiiiii Kamar wata kayan wanki ya zubar a bakin kofar ya mayar ya rufe. Washegari ƙarfe duk yanda John yaso barin gidan be sama ba, don sun ce masa ya tsaya masu baikon jelly ne zasu zo, kuma yasan dole ze dashi tun da kamar al'adan sune hakan. Ƙarfe goma na dare kowa ya gama hallara a babban hall na gidan nasu, gashi an huhhura huta wa abin bautar su ya sakawa wannan aure albarka, duk wasu friends na kusa dana nesa sun gama hallara. Saboda an san baya son kide kide yasa ka babu kidan da yawa, abu na farkon daya fara bashi mamaki ne shi ne ganin manyan friends nashi a wurin, musamman ma dai babban amininsa Joshua. Amma se ya maze suma duk sukayi fuska. Bayan an zaune wurin ya dauki shiru sega shigowar wasu manyan mata biyu sun sako deepika tsakiyansu wacce fuskar ta ke rufe, don har yanzu bata sabe ba daga uban marukan data amsa daga John ɗin. Sedai taki fadin ma kowa abinda ya faru tace zamewa tayi a bayi. Ana shigo da ita cikin babban hall din aka saki wasu haske…Mahaifin John ya zauna cikin girma da iko, Daddyn India ma ya zaune deepika na daga kafafun John, Kafin Mahaifiyarsa Madame Victoria dake sanye cikin wata irin shiga ta mike, ta amshi zobe daga hannun Patriarch dare da wani abu nade ta isa ga Papan ta mika masa. Wanda yayi gyaran murya ya amsa ya ce. “An gama shirya komai.” Yay maganar yana mikawa John zoben yace ya saka ma deepika ita ma daidai nan Lady Rebecca ke mika mata natan. “Me ake nufi?” Mahaifiyarsa ta yi murmushi mai sanyi. “Za ka auri Deepika ne baiko za kuyi.” Ai a wani irin tsiyace ya mike yana fatali da wutar dake gabansa me hasken da suka sa mata launi yace. “Ƙarya ne!!!....” Kalmar ta fito daga bakin John cikin ihu da tsananin fusatar daya saka duka hall din ɗauka. Papa ne ya mike tsayen shi ma a fusace yace. “Me ka ce?” “Ba zan aure ta ba.” Ya bashi amsa kai tsaye ba tare da shakkun komai ba. “A kan wanne dalili ?” Papan da Mom suka furta kusan tare. John ya kalli cikin idanuwansu su duka biyun kafin kai tsaye. “Saboda Yas-mine.” Gaba daya jin saukar kalmar sukayi kamar gashewar bam. Kowa a wurin babu wanda be girgiza ko ya gigice ba. Da ƙarfi mahaifinsa ya buga masa wata uwar tsawar da tin da yazo duniyar ko me kama da irinta be taɓa masa ba yace. “HE DISGRACED US!” Mahaifinsa yay Maganar yana buga tebur din da yake zaune da ƙarfi. Mahaifiyarsa kuka kai tsaye kuka ta sanya tana fadin. “Mun rasa ɗa… ba shi bane wannan!” Amma shi John bai damu ba kuma ko a jikinsa sema kuwa da yayi ya soma tafiya yana me sake ce dasu. “Zan aure ta.” _Hhhhhhhh shi yasa nake ce muku duk wanda ya bari aka yi wannan zazzafar tafiyar ba tare dashi ba to ya bar dadi wllh. _ # JANNERH +IBRAHIMUL KHALEEL # YASMINE +JOHN # DEEPIKA JOSEPH # X_ESHIKA JOSEPH # AKA AMMEY LAYLERH ✍️ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 22 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Gaba ɗaya a wannan daren mutane da yawa basu runtsa ba, daren da suka ga ya ƙara musu zurfi ba. Madame Victoria kuwa ko rufe ido kasawa tayi saboda tsananin tashin hankalin da take a ciki wanda tunaninta ya kasa samun nutsuwa wuri guda. “Not my son…” ta faɗa da ƙarfi tana ɗaukar wayar ta ta saka kira, “Arrange emergency meeting with the families. Tonight or tomorrow morning. I don’t care.” Ta katse kiran da tsananin fushi. “Wannan aure se ya daru.” A wannan lokaci shi kuwa JOHN ya na zaune a gefen gadonsa wayarsa riƙe a hannunsa yana dan jujjuyata sega ƙiran Mecheal ya shigo masa. Muryar Mecheal na rawa kaɗan yace. “Boss… akwai sabon update.” John ya ɗan lumshe ido yana furzar da wani huci yace. “What now?” “Family meeting has been called. Your mother… and Yasmine’s family.” Da kamar alamar tambaya JOHN ɗin yace. “Meeting?” “Yes Boss. It’s about… marriage arrangement.” Mecheal ya sake bashi cikakken tabbaci daga cikin wayar, wanda ya saka take idanun John suka yi duhu nan take tare da yanke kiran. A tsakiyar ɗakin ya mike ya ɗan fara zagawa yana fitar da hucin wani numfashi mai nauyi. “Marriage…” ya sake maimaita kalmar, Kafin wata irin dariya mai ɗaci ya biyo baya. “Without my permission?” A can gidan su Yasmine kuwa babu wanda yasan abinda ke faruwa, ko nuna musu cewar kawunnan John sun zo masa da wata magana tun a daren, don haka yau ko shirin fita aiki be yiba, kwata kwata ma ko parlourn kasan be sakko ba se yanzun da yake fitowar. A natse Ambassador Kabeer Usman Maina ya zauna a kujerar parlourn cike da nutsuwa amma fuskarsa cike da damuwa. A natse ya ke sanarma da Mamy komai wacce tayi zuru abar tausayi, don abar a tausaya mata ce mana. Cikin sanyin murya amma a zahirin gaskiya cike take da tashin hankali tace. “Wannan magana ba karama ba ce…” Tayi maganar tana sauke ajiyar zuciya me nauyi sosai mara nutsuwa, Gyara zamansa Ambassador yayi ya ɗaga hannu yace. “I know.” Sai ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce, “Family of that boy… they are powerful. Too powerful.” Cikin kwantar da murya Mamy tace. “Amma ka duba labarin kawai ace Yasmine tana son wani…” Sai da ya sauƙe numfashi. “Love is not enough when politics enters.” daga haka suka ci gaba da tattaunawa akan maganar. Mecheal na zaune tare da sauran Guards na gidan suka ga fitowan John, yayi saurin mikewa da nufin binsa amma kan ya karasa har ya figi motar da wani irin gudun tashin hankali bana wasa ba. Don haka Mecheal cike da tashin hankali ya mara masa baya a mota ta biyu. “Boss! Where are you going?!” Mecheal ɗaya ƙira shi a waya yake tambayar John ɗin, “To the source of this madness.” Suna zaune harkokin a parlourn suka jiyo karar mahaukacin Hong ɗin daya saka dukkan su mikewa tsaye babu shiri. Ko kafin suyi wani yunkuri ma sega security ɗaya ya fado parlourn yana cewa. “Sir… wani mutum ne a waje duk da mun hana shi shigowa amma seda ya shigo.” tun kafin ya sake cewa komai sega shigowar John ya bayyana a parlourn gidan, directly kuma idonsa akan Ambassador Kabeer suka fara sauƙa. Wani ɗan shiru ne ya ratsa wurin na ɗan lokaci kafin cikin ƙarfin hali da dauriya Ambassador ya yi magana a hankali. “Mr. John… this is unexpected.” John ya tsaya kai tsaye tare da bashi amsa da. “I came for one thing.” Sai ya ɗan juyo kaɗan, kamar yana jin duk duniya na kallonsa. “I heard there is a marriage being arranged.” kafin ya fesar da wani dan numfashi ya ɗaga kansa ya kalla sama inda yake jin Yasmine na nan. “Between me…” ya ce a hankali. Ya kuma nuna kansa “and her.” Daidai lokacin da Yasmine ke sakkowa amma bata karasa sakkowarba ta tsaya a bakin stairs tana kallonsa . Idanunsu suka sake haɗewa wuri guda, John ya sake kallonta ba tare da yayi ƙoƙarin ɓoye abin da ke zuciyarsa ba yace. “Tell me…” ya ce da idonsa a kanta. “Is it true?” Yasmine ta kasa magana saboda ta riga da ta san gaskiya ɗaya ce. Idan ta ce eh zuciyarta za ta iya fashewa, haka kuma idan tace a’a ɗin ma hakan take duk. Ga kuma iyayenta dake ƙasa suna kallon juna cikin tashin hankali…suna fahimtar cewa wannan ba kawai magana ta aure ba ce, yaƙi ne amma na soyayya, addini, iko… da kuma makoma. Ita kuwa Yasmine ta makale ne a stairs din saboda gajeren wandon dake jikinsa babu riga se iyaka vest army green me ruwan wandon. Wanda shi shaf yama mance da cewan sune a jikinsa ɗin kuma har yanzun bema farganba, Kafin Kowa ya sake yunkurin cewa komai sega shigowar Deepika kamar wacce aka jefo. Kai tsaye ta isa ga John din tana riko hannunsa ta fara dan jijjiga jikinsa tana faɗin. “John!, Joseph… tell me this is a lie.” ta furta cikin rawar murya. Amma idan kujerun dake parlourn sun motsa shima ya motsa, sema Idonsa dake kan Yasmine, wacce haka kawai taji wani abu ya tsaya mata game da yadda Deepika ta shige jikinsa, duk da yanda take ƙoƙarin ganin ta riƙe hawayenta amma seda suka ciko idon ta, wacce tayi saurin kawar da kanta, daidai da lokacin da JOHN ke janye deepika daga jikinsa yana kallonta da ɓacin rai yace. “It’s not a lie.” Wanda ya saka Deepika ta yi wata yar dariya mai ɗaci. “So it’s true…” ta ce tana girgiza kai.“After everything, after our families… after the agreement…” Ta sake matsowa kusa da shi sosai. “You chose her?” Wani irin juyi John yayi tare da kamo kafadunta ya jijjiga tare yace. “I didn’t choose you either.” Kalmar da Deepika taji ciwon ta fiye da duk abin da ya faɗa a daren jiya. Taja baya kamar wacce aka mara. “What…?” Ambassador Kabeer ya ɗaga hannu. “This is getting out of control.” Madame Victoria tare da her family nasu da suka jima tsaye duk sun yi shiru suna kallon komai kamar mai film, Wannan ba rikici ba ne a gare ta tsari ne da zai iya rushewar da take da cikakken tabbacin babu gyara. A hankali Yasmine ta ɗago kai ta kalle shi tare da furta. “John… please stop.” ta ce cikin hikima “I don’t want anyone hurt because of me.” John ya fara taka wa zuwa inda take. “You think you are the problem?” ya tambaya ta girgiza masa kai. “I am.” Shima ya girgiza mata kan nan yace. “No.” Sai ya ɗaga hannunsa a hankali kamar yana nuna mata gaskiya. “You are the only honest thing in all this mess.” Da sauri Mecheal ya matsa baya kaɗan, yana jin kamar yana kallon wani abu ne da ya fi karfin sa. Deepika ta share hawayenta tana kallonsa. “This is humiliation.” ta ce cikin fushi. “I will not be part of this circus.” daga haka ta juya zata tafi amma Madame Victoria ta katse ta ta hanyar furta “Stop.” Kowa dake parlourn ya juya se a sannan suke sanin da tsaiwar su a wurin...kafin a natse Madame Victoria ta ƙara so cikin parlourn tana me furta. “No one is leaving until this is settled.” Ambassador Kabeer ya kalle ta. “Settled? Our children are breaking apart in front of us.” wani duba ta masa tare da girgiza kanta tace. “This is not about emotions.”Ta nuna John. “It is about structure. Power. Future.” sai ta kalli Yasmine tace. “And unfortunately… she does not fit that future.” Yasmine ta ji kalmar kamar wuka aka caka mata a kirji. John ya matso kusa da ita a natse kafin ya furta. “Don’t talk about her like that.” Ya faɗa da ƙarfin da wannan shi ne karo na farko da muryarsa ta nuna fushi sosai a wurin. Madame Victoria ta kalle shi cike da zafi tace. “Then what do you suggest?”John ya yi shiru na ɗan lokaci kafin kamar wacce aka fusgi maganar daga bakin sa yace. “I cancel everything.” Kowa yaja ya tsaya cak, Deepika ta ɗago kanta cike da tsoro. Ambassador ya ce cikin mamaki. “You can’t just cancel arranged marriage like it’s a meeting.” John ya juya masa kai alamar tabbaci kafin yace. “I just did.” saurin katse shi Yasmine tayi tana girgiza kanta tace. “No… John… don’t.” Amma John ya riga ya yanke hukuncin da babu wanda ya isa tilasta shi. “Enough.” ya ce. “Enough control. Enough arrangements. Enough forcing lives.” Sai ya matso kusa da Yasmine ya wani kalle ta yace. “I choose my life now.” Ya furta kalmar ne amma muryarsa na ɗauke da wani irin ciwo da ya kasa ɓoyewa. Wani shiru mai nauyi ya sake kame ilahirin wurin. Deepika ta fashe da kuka ta fita a guje daga falon. Ambassador Kabeer ya koma ya zauna a kujera cikin gajiyawa. Madame Victoria kuwa wani murmushi tayi me ɗaci tare da furta. “You think this is freedom?” ta tambaya John din daya kalle ta yana me bata amsa da “Yes.” Idonta har ya fara ganin biyu biyu ta isa gabansa ta jijjigasa da kyau tace. “Then you will learn the price of it.” TA ɗan juya. “Because I will not allow this disgrace to continue.” Yasmine ta ɗaga kai cikin halin ko in kula tace... “What are you going to do?” ta tambaya. Madame Victoria ta kalleta kai tsaye tace. “Protect my son.” Wanda kalmar ta ma Yasmine nauyi sosai kamar wacce tafi kama da barazana ce. A waje kuwa tuni ƙofofin sada zumunta sun riga sun cika da labari, kowa na ta fira da hotuna da kalaman da ke yawo kamar wutar daji. Wanda bama a san wanda ya fitar da maganar ba, kuma maganar nasu ɗaya ce kawai ke yawo shi ne. “Engagement officially broken!Ambassador’s daughter na cikin wani babban scandal da ya girgiza zukata!. Uwar John ta yi barazanar daukar mataki mai tsauri!” Gaba ɗaya tun daga kan shafukan Instagram zuwa X (Twitter), mutane na ta jefa ra’ayoyi, wasu na tausayi, wasu na zargi, wasu kuma na ƙara tayar da kura. Kofar gidan kuwa ta cika da motoci, ‘yan jarida, da masu son ganin abin da zai biyo baya. Daga can cikin gidan kuwa wani irin tashin hankali ne ya mamaye parlourn bayan fitan Deepika. Kowa na wurin ji yake kamar iska ma ta sauya masa yanayin shakar da yake da. Kowa a cikinsu maganganun da JOHN ya furta ɗazu sun tsaya a zuciyar kowa kamar ƙarar fashewar wani abu mai girma. Madame Victoria dake tsaye cak tun ɗazu awurin, idanunta akan ƙofar da Deepika ta fita, duk da nutsuwar da take ƙoƙarin nunawa amma ta gagara saboda zuciyarta a dagule take fiye da yadda kowa zai iya zato. Hannunta ta matse sosai har farcen yatsunta suka kusa soke tafin hannunta. Ambassador Kabeer dake zaune murza goshinsa kawai yake yi cikin gajiyawa. Domin ko a shekarunsa a siyasa bai taɓa tunanin wata magana ta soyayya za ta kai wannan matakin ba. Mamy ma gaba ɗaya ta rasa abin cewa, idanun ta ne kawai akan Yasmine wacce ke tsaye kamar mutum-mutumi, zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Sai JOHN ya ɗan ja numfashi a hankali. Ya kalli kowa ɗaya bayan ɗaya ba tare da ya sake cewa komai ba. Fuskar nan tasa babu alamun wasa ko sassauci ko kaɗan. Kafin daga bisani ya juya ya fara tafiya zuwa ƙofar fita. “John…” Madame Victoria ta kira sunansa cikin murya mai nauyi. Amma ko juyowa bai yi ba sema ta kun san da yaci gaba da yi ba. Yasmine ta ɗan matsa gaba kamar zata bi bayansa amma ƙafafunta suka kasa motsi. Tana jin kamar wani abu a zuciyarta ya hana ta kiransa, ko kafin kowannensu a cikinsu ƙarar hayaniyar mutane daga waje ta fara shiga cikin gidan. Tun kafin security su samu damar tarwatsa su, reporters suka cika harabar gidan gaba ɗaya da cameras da microphones. JOHN na fitowa flashes suka fara haskawa tamkar walkiyar aradu. “Mr. John! Is the engagement truly cancelled?!. Are you in love with Ambassador’s daughter?!. Did you reject Deepika officially?!, Is there crisis in your family?!” Wani ɗan tsayawa yayi a saman stairs ɗin entrance ɗin gidan. Idanunsa cike da wani irin baƙin yanayi mai firgitarwa. Gaba ɗaya wajen yayi tsit na ɗan lokaci saboda yadda kallonsa kaɗai ya isa ya saka tsoro a zukatan mutane. Sai ɗaya daga cikin reporters ɗin ya sake ɗan matsowa kusa da microphone ɗinsa. “Sir, people are saying you disgraced your family tonight” Cikin wani irin sauri JOHN ya fizgi microphone ɗin daga hannunsa ya jefar gefe da ƙarfi har ya buga ƙasa ya tarwatse. Kafin ya matsa kusa da mutumin sosai cikin sanyin murya mai ɗauke da fushi yace. “Next person that blocks my path…” Yay maganar na daƙiƙa biyu kafin ya tsaya yana kallon kowannensu ɗaya bayan ɗaya. “…will regret it.” Babu wanda ya sake motsi a cikinsu se numfashin mutanen dake fita kamar suna tsoron yi. Daga haka JOHN ya wuce kai tsaye zuwa motarsa ya shiga. Da ƙarfi ya fisgi motar daga harabar gidan ya bar wajen cikin wani irin tashin hankali da hayaniyar cameras. Wani lumshe ido Yasmine tayi a hankali bayan jin ƙarar tafiyar motarsa. Wani irin faɗuwar gaba taji wanda ita kanta ta kasa gane dalilin sa. Madame Victoria ta juya cikin fushi tana kallon sauran family ɗin ta. “This is exactly what I warned all of you about.” Ta furta maganar cikin matsanancin ɓacin rai kafin ta ɗauki jakarta ta fita ita ma ba tare da ta sake kallon kowa ba. Gaba ɗaya sauran sauran wuni da daren ranar babu wanda ya yi su cikin kwanciyar hankali. Washegari tun da sassafe gidan nasu JOHN ya shiga cikin wani sabon tashin hankalin. Servants na zirga-zirga cikin tsoro yayin da Madame Victoria ke saukowa parlour da sauri cikin doguwar rigarta ta alfarma. “Where is John?” Ta sake tambayarsu cikin tsananin fushi, domin gaba ɗaya an rasa shi har gidansa da yake yawan zuwa idan ransa na a bace amma baya can. Shugaban securities na gidan ne ya haɗiye wani yawu da kyar kafin yace. “Ma’am… he didn’t come home last night.” Sake tsuke Madame Victoria tayi tana me ambatar. “What?” Cikin rawar murya ɗaya daga cikin guards yace. “His cars are gone too.” Wani irin shiru ne ya ratsa parlourn. A karo na farko wani mummunan tsoron ya sake shiga zuciyar Madame Victoria na gaske. Da sauri ta juya tana ɗaukar wayarta ta saka ƙiran number na John amma switched off, Haka ta ringa jera masa kira amma har zuwa lokacin amsar daya suke bata wato switched off. Ta ɗaga wayar kenan za tayi jifa da ita sai wayar ta ɗan yi vibration. _Unknown number_ ta gani alamar boyayyar numba ce da ba'a son a santa, kamar ba zata daga din ma amma se wata zuciyar ta bata kwarin gwiwwar dagawar. “Mr. John left Nigeria early this morning.” Numfashinta ne ya tsaya cak tana kokarin silalewa kasa aka sake furta. “Destination to Ethiopia.” Wani irin ɗif taji ƙofofin kunnuwanta sun mata, kafin wayar ta sulale daga hannunta tana fadowa ƙasa ta tarwatse amma jelly da isowarta kenan tayi saurin cafe ta. *Ethiopia*. Ƙaton private jet ne ya sauka a cikin nutsuwar sanyin safiyar ta Addis Ababa. Bayan mintuna kaɗan saiga fitowar JOHN daga cikin jet ɗin sanye cikin baƙar jacket da glasses, fuskarsa ɗauke da wani irin yanayi mai wahalar karantawa. Iskar Ethiopia mai sanyi ta bugi fuskarsa a hankali yayin da ya tsaya cak na ɗan lokaci yana kallon sararin garin. Kafin ya furzar da wata iska me zafi ya yi oder Cap. A can wani luxury penthouse dake tsakiyar birnin JOHN ya kama, kai tsaye bayan sun isa ya bashi credit irin na kasar kana ya wuce daga shi kayan jikinsa, don babu abinda ya dauka nashi a gidan. Bacci me rai da lafiya ya yi har bayan sallan zuhr kana ya fito sanye da kayan shan iska, Ya nufi bakin glass window yana kallon yadda garin ke kayace ta ko ta ina, hannayensa zube cikin aljihun wandonsa, amma zuciyarsa cike take da wani irin tunaninta. *Yasmine* A hankali ta sauke wayarta daga hannunta bayan ta gama kallon hotonta tare da na JOHN sun mamaye social media gaba ɗaya. Wani irin nauyin abu ne ya tsaya mata a ƙirji, musamman ganin yadda mutane ke ta magana akanta kamar ita ce silar rugujewar komai. Gashi dama abinda ya fara farkan da ita tun safe take receiving calls daga manyan mutane, investors, relatives…Friends kowa na neman jin gaskiyar abinda ke faruwa, wani dafe kanta tayi tare da furta. “This is becoming a disaster…” Ta furta cikin fushi tana jefa ipad ɗinta saman table Husna tayi saurin taro ta. *BY AMMEY LAYLERH ✍️ * 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 23 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ *Ethiopia* ꨄ Bayan John ya gama warwarewa abu na farko daya fara shi ne neman ƙawarsa Almaz, ita ke zuwa ta debe masa kewa suyi yawonsu tare tana sake nuna masa wuraren daban daban , shi kuma yana faɗa mata abubuwan da ke damun sa. Amma duk da dariyar da yake yi… zuciyarsa tana tare da Yasmine har zuwa lokacin. Wata rana da yamma suna zaune a cikin beach na hotel ɗin bayan sun dawo daga wuraren da suna ziyarta Almaz ta dube shi ƙadan, tana kallon yanda ya sake haske yayi fawai akan ranar daya zo. Cike da hikima tace “Kana son komawa wurinta, ko?” John bai ɓoye mata komai ba a wannan karon kai tsaye ya ce mata. “Eh.” se kuma ya ɗan furzar da iska daga bakinsa tare da shafo keyarsa yace. “Ta ce ba za ta aure ni ba sai na musulunta.” Almaz ta kalle shi, amma ba tare da mamaki ba tace. “Shi ya sa kake a rikice?” John ya gyada mata kyai kawai yace. “Ba kawai hakan bane amma ina jin kamar zan rasa kaina ne idan na yi wani abu da ba daga zuciyata yake ba.” Almaz ta ɗan yi murmushi me kyau cike da wannan hikimar nata tace. “To kada ka yi komai saboda wani.” Ta ɗan tsaya kaɗan sannan ta ƙara da cewa. “Idan zaka canza… ka canza saboda ka yarda. Ba saboda soyayya ba, se dan saboda kai da kuma ALLAH.” Kalmomin da suka shiga zuciyar John kenan, ya ɗan ware hannayensa yana kuma jan idonsa kamar zai lumshe amma bai lumshe ɗin ba. Sema kamar a karon farkon da bai ji kamar yana gudu daga wannan gaskiyar ba. Komai be sake ce mata daga haka ba ya mike, itama ta mike suka jera suka fara tafiya ya kama hanyar bedroom nashi ita kuma ta kama barin fita daga hotel ɗin, don wanna karon ya canza Hotel ne. Yana shigewa ɗakina ya kwanta akan doguwar sofa tare da zaro tsadaddar wayarsa ya shiga chat, number Yasmine ya shiga tare da ɗan tsayawa na wani lokaci kamar me na zartar wani abu. Kafin yayi kundunbalar rubuta mata, _I miss you… but I need to find myself first._ Ya danna send yana sake lafewa luf cikin sofa ɗin hadi da lumshe ido. Yana a kwancen har zuwa lokacin da daren ya dan fara nisa, amma hasken fitilun hotel dake haskawa ba zai sa ka gane cewar ma daren bane, idanunsa lumshe yana amsar bugun da zuciyarsa ke masa cike da nauyi. Kamar kuma daga sama yaji wayarsa ta yi ƙara. Zuciyarsa ta bugo da ƙarfin daya saka shi saurin buɗe ido, hannunsa na ɗan rawa ya buɗe saƙon. _I miss you too… but you know what I said._ Ɗan lumshe ido John yayi a hankali yana jin yadda kalmomin ke shigar sa suna ratsa zuciyarsa kai tsaye. Saboda wannan shi ne karo na farkon data taɓa furta masa kalma matankwacin wannan, wayar ya sake kalla yana sake bin saƙon ya karanta. Sai ya ajjiye wayar a hankali, ya tashi ya nufi taga. Iskar dake kadawa daga wajen ta bugi fuskarsa har tana motsa bishiyoyi cikin hasken fitilun da suke nan kamar rana. “Ohh Jes…” se kuma yaji harshensa ya sarke numfashinsa na rikewa, saboda kalmar Jesus ɗin kawai da yayi niyar ambata baya. Wani shiru ne ya biyo bayan hakan, yana komawa ya jingina da bangon windows ɗin zuciyarsa na bugawa sosai. Shin soyayya ce kawai ke jan shi? Ko kuwa akwai wani abu mafi girman da yake kiransa?... Hannuwansa duka biyun ya saka yana rufe fuskarsa ya koma da baya da baya yana komawa inda ya baro. A fisge yana me furta kalmar. “YA ALLAH!!!?... " Kalmar data taho masa da wani irin kwanciyar hankalin da yaji tun da yake be taɓa samun kalar saba. “YA ALLAH?!!” Ya sake ambata nan take wani nannauyar baccin da yaji a da kamar ba zai iya ba ya ɗauke sa, ko washegari da yake tashi se yaji komai kamar a mafarki ne suka faru. Kuma ba komai ne ma ya tashe saba illa ƙiran sallar subhi da masallacin Hotel ɗin ya ƙira. Ahankali yaji wani nauyi na taho masa, nauyin da yake jin ya hausa kuma kamar yana da danganta da kiran sallar da aka ƙira, duk yadda yaso daya koma ya kwanta abin faskara yayi, ƙiran sallar ne kawai ke masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa. A hankali ya ziro fararen kafafunsa yana mikewa ya shige bayi yayo wanko ya fito, koda fito din ma kasa zama yay, haka kawai zuciyarsa ke jan sa zuwa ga kiran Sallah ɗin, don haka ya fito harabar Hotel ɗin har wurin masallacin ya zaune daga gefe. A kan idonsa mutane suka fara shiga masallacin aka tayar da Sallah aka idar duk yana zaune. Wafi yawan duk wanda zai wuce se ya kalla John kan yayi gaba, daga nan ya wuce zuwa inda suke zama tare da Almaz. A nan kuwa ya sami Almaz din na zaune tana kallon ruwan beach din kamar yadda ta saba. “Kin riga ni yau,” John ya faɗa yana zama tare da zube kafafunsa cikin ruwan. Ta yi murmushi kawai tace “good morning” da morning kawai ya amsa ta kafin cikin kamar alamar gan ɗoki yace “Ta yi min reply.” Almaz ta juya kai kaɗan tana dan waro ido tace “Me ta ce?” John ya ɗan yi shiru kafin ya amsa da. “Ta ce tana sona… amma dole na musulunta.” Almaz ta sauke wani numfashi a hankali kafin cikin nutsuwa tace. “Tambayar ba ita ce me take so ba…” Ta ɗan karkata kai, tana kallon shi sosai. “Tambayar ita ce kai me kake so?” John ya yi shiru domin ji yayi wannan tambayar… ta fi komai wahala a gare shi. “Ban sani ba…” Ya furta a hankali, Ahankali Almaz ta ɗan yi murmushi tare da dubansa tace. “To mu fara daga nan.” Tare da miƙewa tsaye tace “Zo mu je wani wuri.” TA fadi suna mikewa ya rufa mata baya babu musu suka ɗauki hanya zuwa wani wuri kusa da gefen beach din. wani ƙaramin wuri ne mai natsuwa ba hayaniyar kowa hasali ma wurin ba mutane da yawa. Wani tsohon mutum suka gani zaune kan buzu na farar fata. Almaz ta gaishe shi da girmamawa, shima John da ya lura da yadda take girmama shi. Se ɗan kalle ta da ido alamar “Waye shi?” da idon ta masa alama da. “Mutum ne da yake da hikima,” ta mayar masa da amsar cikin sauƙi kana suka zauna kusa da shi. Tsohon ya kalli John, idanunsa cike da natsuwa da kuma wani kyakkyawan murmushi idonsa tsabar fari har na fitar da wani haske haske. “Ka zo neman amsar ka ne? Ko kuwa kazo akan kaddarorin da zasu bibiyi rayuwarkane akan, DUHU na DUKAN duhu din da kake gaf da afkawa… ?” Ya furta kai tsaye. Shi kuwa John kallon wannan dattijon mutumin yake, yana son ya tuna ina da ina yasan fuskar nan?, a kuma ina ne ƙarshen ganinsa da fuskar?, amma se yaji kamar an mantar dashi komai kamar an toshe basirar da yake da da wani abu me nauyi, duk da a ɗan firgicen daya tsinci kansa na sanin ko mai zai ce masa ba se ya tsinta kansa da furta. “Wataƙila… duka biyun.” Tsohon ya yi wani murmushi kaɗan irin na tsoffi masu cike da hikima yace. “Idan kana neman gaskiya… to ka saurari zuciyarka. Amma ka tabbata ba tsoro bane ke magana.” Kalmomin suka dirarma John a zuciya. ★.. Washe gari da yamma bayan rabuwarsa da Almaz ya koma masaukinsa amma ya ringa jin zuciyarsa kamar ana masa kida ne akan yana son samun abu me nutsuwa fiye da wannan. Ga wani irin shiru mai zurfin daya ratsa ɗakin nasa, irin shirun nan da ke cike da tunani fiye da hayaniya. Ahankali ya shiga cikin chart nashi da Yasmine suna nan. Kalmar _You know what I said_ na yawo a kansa kamar ƙarar da ba ta daina ba, jin hakan ma ba nutsuwar da yake son samu zai yi ba seya shiga contact nashi yana lalubar No na almaz cewa yay mata su hadu inda suka saba haduwa, daga haka ya datse kiran yana fitowa, sedai ganin almaz din zaune yaso ya bashi ɗan mamaki matuka, wanda har ya gaza ɓoye wa yake tambayarta wai ta ya ta riga shi bayan yasan irin tazarar dake tsakaninsu?, murmushi me kyau tayi tana ce dashi ai dama tana gab da wurin ne. Kawar da hakan yayi ta hanyar kiran sunanta da yayi. “Almaz,” Ya kira sunan kai tsayen daya saka Almaz din dubansa tana me furta. “Me ya faru?” “Ina so… ki kai ni wani wuri.” Ya fada yana ɗan lumshe idonsa. “Wani wuri?” Ta sake maimaitawa da alamar tambaya. Kansa ya gyada mata alamar tabbaci yana me furta. “Inda zan samu nutsuwa… inda zan fahimci abubuwa sosai.” Almaz ta ɗan kalle shi na ɗan lokaci kamar tana tantance gaskiyar sa ne, kafin ta miƙe tsaye. “To mu je.” Ba wani wurin shakatawa suka nufa ba wannan karon. Gari suka shiga sosai suka wuce hayaniya, suka shiga wani wuri mai sauƙi… mai tsarki bakin wani Masallaci. John ya tsaya daga bakin ƙofar ya yi shiru. Yana kallon mutanen dake shiga suna fita, wasu suna sallah, wasu suna zaune cikin nutsuwa. Bai taɓa shiga irin wannan wuri da irin wannan yanayi ba. Idonsa ya ɗan sauya yanayi jikin sa ya fara kamar alamar rawa saboda wata irin muryan dake tashi wacce da alama kuma wani recording ne na karatu aka kunna, wacce take fita da wata irin murya me sanyi da nutsuwa kuma ta mace. “Ba dole bane ka shiga,” Almaz ta faɗa a hankali ganin yadda yanayinsa ya koma. Kansa ya girgiza yana jin wani irin abu na ratsa ilahirin jikinsa gaba ɗayan da bai san ko menene ba. “A’a… ina so.” Ya fada a hankali ya taka ƙafa ɗaya… sai na biyu ya shiga. Tun daga harabar masallacin komai ya bambanta da irin kowanne wuri, ba hayaniya ba sautin kida ba komai, se iyaka muryan dake sake karade ilahirin harabar masjid ɗin. Sai ma wata irin natsuwar da ko a hasashe ba zai taɓa iya bayyana ta ba yaji na shigar sa. Ahankali ya kai zaune saman tattausan carpet ɗin dake malale daga ƙofar masallacin, Wani abu yaji kamar ya tsaya cak a kwanyar kansa,daidai sanda aka dakatar da wannan karatun me cike da nutsuwa cak. yayin da kiran salla ya mamaye gurin gaba daya. Yadda yayi shiru haka duniyar ke kamar tayi shirun tare da JAMA'AR dake cikinta, kowa yana sauraren kiran sallar dake tashi cikin wata kwantaciyyar muryar dake saukar da wani irin nutsuwar da haske ya mamayi musulmin gurin, Ko shi da yake ba musulmin ba wani irin nutsuwa yaji na shigar sa. Yana sauraren yadda wani da babu jimawa ya zauna gefen sa ƙasa ƙasa yana karanta addu'ar bayan kammala sauraren kiran sallah,baka jin abinda yake fadi tar amma kadan kadan muryarsa tana motsawar da ahankali yake maimaita kalmar. “Allahumma rabba hadhihid-da‘watit-tammah, was-salatil-qa’imah, ati Muhammadan al-wasilata wal-fadilah, wab‘athhu maqaman mahmudan alladhi wa‘adtah, innaka la tukhliful mi‘ad.” Tun da ya fara karanto adda'ar John ya lumshe idanuwansa a hankali. Haka kawai ba tare da yasan ma'anar kalaman ba amma haka yaji zuciyarsa ta karɓesu kafin kunnuwansa su gama jin su. Ga wani irin sanyin da yaji ya ratsa jikin sa. Hatta da bugun numfashinsa sai da ya ɗan tsaya na wasu sakanni, sai yaji kamar hayaniyar cikin zuciyarsa tana raguwa a hankali… kamar ana cire masa wani dutse mai nauyi daga ƙirji. Bai san dalilin da yasa idanunsa suka cika da ruwa ba, shi kansa bai san yadda akayi zuciyarsa ke amsar sautin ba, domin rayuwarsa bai taɓa jin wani abu da ya shiga masa rai irin haka ba, shi ba waƙa ba, ba kuma kalaman soyayya ba, haka zalika ba sermon ɗin cocinsu ba. Wannan daban ɗin daban ne, wani abu ne mai nauyi amma kuma mai salama. Ya juya a hankali yana kallon mutumin dake zaune gefensa da tasbaha a hannunsa, yana ci gaba da ambaton addu’ar cikin ƙasƙantar da kai . John ya haɗiye wani yawu a karon farko cikin rayuwarsa ya ji zuciyarsa tana tambayarsa tambayar da bai taɓa bari ya fito fili ba. “Me yasa wannan addinin yake taɓa zuciyata haka…?” Kuma abin da ya fi tsoratar da shi shi ne… Ya ji kamar yana son sake jin addu’ar. Yana nan zauna a gefe har aka shiga sallar, yana kallon yadda mutane ke yin Sallah gwiwoyinsu na taɓa ƙasa cike da nutsuwa, fuskokinsu kuma cike da tawali’u, ahankali yaji zuciyarsa ta fara sauya wa ba saboda Yasmine ba, ba saboda wani ya tilasta masa ba, sai don saboda abin da yake gani da abin da yake ji a zuciyarsa. “Me yasa nake jin haka…?” Ya sake tambayar kansa, Idanunsa naci gaba da cika da ruwa. Har aka idar da salla kana ya fito suka sake nemar guri kusa da masallacin suka zauna. John ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya kalli Almaz. “Idan na yanke shawara…” Tayi saurin katse shi cikin nutsuwa kamar ta san abinda ke ransa dama can. “Kada ka yi saboda Yasmine.” Ya yi ɗan murmushi kaɗan tare da gyada mata kai. “Na sani.” Sai ya ɗan tsaya yana jin kamar yana shirin taryar wani gungumemen yaki ne irin na ƙasa da ƙasar nan, kafin ya ɗora da cewa. “Zan yi saboda ni.” Almaz ta yi murmushi irin wanda ke nuna farin ciki na gaskiya tace. “To yanzu ka fara fahimta.” Suka tashi suka soma tafiya domin komawa masauki. Yaso taka mata kamar koda yaushe amma tace ta gode. Yana komawa ya zauna saman sofa tare da ɗaukan wayar sa ya buɗe chat ɗin Yasmine. Amma wannan karon ba tare da shakka ba ya rubuta mata. “I’m not there yet… but I’m searching. Not for you… for me.” Ya danna send yana jingina bayansa zuciyarsa na mata beating. Ahankali ya Mike ya na nufar gaban doorwindow ya jingina kansa da gilashin na windows din, idanunsa a buɗe amma zuciyarsa ta nutse cikin zurfin tunani. “Thinking about thinking…” Ya furta a hankali kafin ya yi dariya kaɗan ba dariyar farin ciki ba, amma ta fahimtar kansa. “Na shiga wani irin zagayen tunani ne…” Ya ƙara faɗa a ransa yana tunanin Yasmine amma ba kamar da ba, ba da zafi kawai ba, sai da tambaya, yana tunanin Almaz amma ba da ruɗani ba sai da godiya. Yana tunanin kansa amma wannan shi ne mafi nauyi. “Me nake so da gaske?” ya tambayi kansa. Yana komawa gefen gado da tarin tunaninnika wata zuciyar na ce masa. “Ka tafi wurinta.” Wani ɓangaren kuma na ce masa. “Ka tsaya ka gane kanka.” Idonsa ga rufe da ƙarfi. “Why is my mind like this?” ya furta yana sake komawa duniyar tuninin, ba wai tunani ne matsala ba sai yadda yake gudu daga tunanin. Ahankali ya sake tashi tsaye a wurin yana sake komawa bakin window. Ya ɗora hannu a kirji. “Thinking about thinking…” ya maimaita a hankali, wannan karon cikin nutsuwa, sai ya ƙara da cewa. “Maybe I don’t need all the answers tonight.” Ya jingina kansa da taga, idonsa a buɗe, zuciyarsa a hankali tana samun wata natsuwar yanke shawarin da yake kokarin yi. A kuma karon farko cikin kwanaki da damar da tunaninsa bai yi masa nauyi ba, cike da jin kwarin zuciya ya kwanta a ransa. ★.. Washegari bayan wannan daren mai cike da tunani, John ya tashi da wani sabon yanke shawara a zuciyarsa. Ba gudu ba haka za bada rikicewa ba sai dai tafiya don fahimta. Ya shirya jakarsa cikin nutsuwa, ya kalli ɗakin da ya zauna tsawon kwanaki a Hotel ɗin, sannan ya fitar da wani numfashi mai zurfi. “Time to move…” ya furta a hankali.... A filin jirgin sama kuwa baka jin kai sai sautin tashi da saukar jirage na cika iska. John yana tsaye yana jiran jirgin sa idonsa cike da tunani amma zuciyarsa tana da wani sabon natsuwa. Yasmine bai sake rubuta sake rubuta mata komai ba tun saƙon ƙarshe. Almaz kuwa ta masa saƙon ban kwana me tattare da fatan alkhairi, wacce ita ce ma ta saka shi a hanyar ita da mahaifinta suka bashi address na inda ya nufa a kasar Saudia. “Ka je ka gano kanka. Kada ka ji tsoro.” Bakuna biyun suka hade baki zuciyoyi da idaniyarsu cike da fata da kuma burin da bai san ko na minene ba... Ahankali ya sake jingina kansa da kujerar jirgin da babu jimawa ya tashi idonsa a rufe, Yana jin yadda jirgin ke ci gaba da ratsa sararin samaniya. Bayan wasu sa’o’i jirgin daya taso daga kasar Ethiopia ya sauka a kasar Saudi Arabia. Ƙasar dake ɗauke da natsuwa da kuma tsari. A natse ya biyo sawun passenger's na jirgin zuwa filin jirgin, wata iIska mai dadi ta masa maraba a filin jirgi, Kamala Ilmaha da natsuwa suka bambanta da abin da ya saba gani. John ya tsaya na ɗan lokaci a ƙofar fita yana kallon mutane suna tafiya cikin natsuwa, wasu cikin sutura masu alamar addinin Musulunci, wasu cikin girmamawa da shiru. Zuciyarsa ta ɗan yi nauyi amma ba tsoro mafaka ba. Sai dai nuna jajircewa da bada kwarin Gwiwwar da yake jin cewa yana shiga wani sabon babi ne na rayuwa. A birnin Riyadh John ya fara wata sabuwar rayuwa, ba tare da hanzari ko garage ba. Sai dai kallo, sauraro, da koyo. Yana ganin yadda mutane ke rayuwa cikin tsari da ibada. Yana ganin masallatai masu haske da nutsuwa. Yana jin wani abu a zuciyarsa yana ci gana da motsawa ba tilas ba, sai dai tambaya. “Is this what I’ve been missing… or just what I’m learning?” Tun da yazo babu da wanda yayi waya ko chart, don haka yau da yake karasa cika kwanki uku cif ya ɗauki wayarsa ba tare daya buɗe chat ɗin Yasmine ba. Bai kuma nemi Almaz ba ya buɗe sabon note ya rubuta. “I'm not becoming someone else. I'm trying to meet myself.” Daga haka ya rufe wayar yana kallon gajimaren da sukama sama ƙawanya ta hanyar ado. Iskar yammacin ranar naci gaba da kadawa me ɗauke da wani irin shiru mai nauyi amma mai kyau. Washe gari ya shirya kansa cikin wasu yard masu taushi milk ya dauki cap zuwa inda zuciyarsa keta azalzalarsa akan yayi yaje. Rana ce mai haske ga iska mai ɗan sanyi tana ratsawa a cikin harabar wajen, tana motsa ganyaye a hankali suka nufi babban masjid dake ƙasar. Ahankali ya fito daga cikin motar Idanunsa na kallon wajen da bai saba da shi ba. Duk da baya son hayaniya, ba kuma ya son ya fiye ganin taron mutane, shi yasa ko da can ma ya tsani zuwa club ko party haka. Amma yau ya zo ne saboda wani abu da bai san dalilinsa ba. Kamar wani abu na tura shi haka yaja ya ɗan tsaye tare da shakar wani ni'imantaccen numfashi ya soma tafiya ahankali, kafin ya ɗaga kansa a natse yana kallon Babban Masallacin dake tsaye a gabansa.... _To fa jama'a AMMEY LAYLERH me john ke shirin yi ne?_ _Ikon ALLAH me yadda yaso to bari mu taro page na gaba kuma jama'a...._ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 #MUSLIMS #JANNEERH AMMEYLAYLERH #JOHN +IBRAHIMUL KHALEEL *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 23 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Ahankali John ya sake ɗaga kansa yana kallon Babban Masallacin dake gabansa. Wani irin haske ne ya mamaye harabar gurin, fararen ƙoyaye na kyalli ƙarƙashin hasken rana yayin da iska mai ɗan sanyi ke ratsawa tana ɗauke da sassanyar ƙamshin turare da tsabtar wajen. Wasu mutanen na ta shiga suna fita cikin nutsuwa bada hayaniya, ba kuma ture-ture ba, komai na gurin na ɗauke da wani irin salama da zuciyarsa ke kasa fahimta. Ya haɗiye wani yawu a hankali kafin ya taka mataki na farko zuwa cikin harabar masallacin, wanda duk taku ɗaya da zai yi yana jin kamar yana taka wa ne da bugun zuciyarsa. “Why do I feel like I’ve been here before…?” Ya furta ƙasa-ƙasa ahankali ya ƙarasa shiga. Kai tsaye da sautin karatun Al-Qur’ani ya fara cin karo wanda ya karade kunnuwansa, wannan karon ba recording ba. Murya ce ta gaske, murya mai sanyi, mai zurfi mai ratsawa kai tsaye har cikin zuciya. John ya tsaya cak jikinsa na ɗan ɗaukar wani irin rawa. Da Idonsa ya bi inda yake jin sautin na tashi har ya hango wani Dattijo zaune daga can gefe cikin fararen kaya masu sauƙi. Al-Qur’ani ne a gabansa yana karantawa cikin nutsuwa kamar wanda babu komai a duniya face shi da kalaman ALLAH. Kusa da Dattijon wasu mutane ne zaune suna sauraro, John bai san dalilin da yasa ƙafafunsa suka soma kai shi wajen mutumin ba, duk da rawan da ƙafafu sa keyi amma haka yake jin kamar ana jansa ne zuwa ga Dattijon. Cikin kamar tafiyan sassarfa ya ƙarasa kusa da dattijon, kamar yasan da zuwan John ɗin Dattijon ya ɗago kansa a hankali, inda kai tsaye Idanunsu suka hadu da juna. Wani irin faduwa john yaji gabansa yayi saboda haduwar idanun mutumin da nasa. Cike da wata irin nutsuwar cike da wani irin haske, wannan Dattijon ya yi murmushi kaɗan. “Lokacin har ya ƙara so kenan?.” Wanda wannan tambayar da yayi ya saka John tsayawa cak yana kallonsa. “Ka… ka san ni?” Mutumin bai amsa kai tsaye ba sai ma rufe Al-Qur’anin da yayi a hankali yana nuna masa wajen zama kusa da shi. “Zauna, ya Jikina.” Bai san dalilin da yasa ya bi umarnin mutumin ba ya kuwa zauna din, sun jima a zaunen har na wasu daƙiƙu babu wanda ya yi magana. Sai sautin iska da kuma sassanyar karatun wani yaro daga can gefe dake tashi, kafin daga bisani Dattijon ya dubi JOHN. “Ka daɗe kana ta gudu.” Yayi maganar daya saka John ya ɗan haɗe gira yana furta. “Daga me?” “Daga kanka.” Kalmomin suka bugi zuciyarsa kai tsaye. Ya sauke numfashi yana shafa fuskarsa tare da furta. “I don’t understand what’s happening to me…”Ya furta cikin raunanniyar muryan daya saka Dattijon ɗan sakin murmushi kaɗan. “Ba dole ka gane komai yanzu ba.” Yayi maganar tare da ɗan matsa kusa da John ya cilla masa tambayar data saka John saurin dagowa yana kallonsa. “Ka faɗamin… Lokacin da ka ambaci ‘YA ALLAH’ a karon farko… Me ka ji?” Nan take jikin John ya ɗan yi sanyi take yana tuna daren nan, yadda zuciyarsa ta sami nutsuwa ya kuma yi bacci cikin salama da kwanciyar hankali. Idonsa ya sauƙe ƙasa tare da bashi amsa da. “…Peace.” Ya amsa da ƙyar, Dattijon ya gyada kai a hankali yana amsawa da. “Domin zuciya idan ta fara gane Mahaliccinta… Komai yana canzawa fara canzawane daga yadda aka san shi.” Wani shiru John yayi kafin ya jefa masa tambaya cikin rawar murya ya ce. “But what if I’m wrong?” Wani ɗan murmushi Dattijon ya yi yana sake bashi amsa da. “Saboda da duk mutumin da yake neman gaskiya da zuciya mai tsabta… ALLAH baya taɓa barinsa cikin duhu.” “DUHU?…” John ya maimaita kalmar a hankali kamar wanda wani abu ya tsaya masa a rai. Kansa ya gyada masa alamar kwarai kuwa yana ci gaba da faɗin. “Wasu duhun tsoro ne. Wasu kuma duhun zuciya ne, sai dai mafi haɗarin shi ne duhun da mutum yake rayuwa a ciki alhali yana tunanin yana cikin haske ne.” Wani irin sanyi John yaji kamar yana ratsashi, Kamar kalaman suna warware wani abu ne a ransa. Ya ɗago idanunsa a hankali bayan ya kalla mutumin yace. “If I choose this path…” Ya haɗiye wani yawu tare da sake furta. “…everything in my life will change.” Dattijon ya sake gyada masa da bashi amsa da “Eh.” Wani shiru ya biyo bayan hakan, kafin mutumin ɗora da maganarsa cikin murya mai cike da nutsuwa. “Amma ba zaka rasa kanka ba…” Ya ɗora hannunsa a ƙirjin John yace. “Zaka same shi.” Idanun John suka cika da ruwan hawayen da bai san ko na miye ba nan take, numfashinsa kuma ya nemi ɗan rikicewa. Duk kalaman da yake ta gudu daga gare amma gasu yau suna shiga zuciyarsa kai tsaye cikin sauƙi ba tare da yaƙi ba. Idanunsa ya rufe da ɗan ƙarfi yana dafe zuciyarsa cikin raunin murya yace. “Why am I crying…” Dattijon ya yi murmushi idonsa zube akan John din yace. “Saboda zuciyarka tana farkawa ne.” Kalaman da suka sake karya wani abu a tare da John kenan gaba ɗaya. Ya buɗe idanunsa da sauri yana kallon dattijon. “What do I do…?” Dattijon ya ɗan yi shiru kafin ya ce. “Ka furta abin da zuciyarka ta riga ta gaskata.” Bugun zuciyar John ya ƙaru Lips ɗinsa suka soma rawa, Idanunsa cike da hawaye. Dattijon ya ɗan janyo shi jikinsa a hankali tare da soma furta kalmar shahada... “ASHHADU AN LA ILAHA ILLALLAH !.WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH …” Wani saurin dafe ƙirjinsa John yayi kamar zuciyarsa zata fito woje. Ga masallacin da ya yi wani irin shiru… amma ba shiru na yau da kullum ba, A Ahh shiru ne irin mai cike da tsarki mai kuma sama zuciya nutsuwa, amma a lokaci guda yana tare da tsoro. Ya haɗe hannayensa wuri guda kamar wanda ya zo neman wani abu da ya wuce duniya. Yana zaune gaban babban malami dake zaune yana fuskantarsa. Fuskar sa cike da natsuwa idanunsa na ɗauke da hikima wanda ya sa John sake kallonsa da zurfi. “Ka shirya?” Malamin ya sake tambayarsa a hankali. Numfashin John ya ɗan rikice yana sake kallon ƙasa zuciyarsa na hasko masa hotunan rayuwarsa na baya, duk abinda ya taɓa sani, duk abinda ya taɓa yi. Sai ya ɗaga kansa Idanunsa har sun canza launinsu suna cike da tsoro amma suna ɗauke da haske a cikinsu. “Na shirya…” Malamin ya ɗan gyada kai yana me furta. “Ka sani wannan hanya ba wasa bace,” ya faɗa a hankali, “amma ita ce hanya ta gaskiya.” Zuciyar naci gaba da bugawa da ƙarfi kamar zata fito waje. Kamar wani abu na jan shi baya, kamar tsoron rasa komai tsoron canji da tsoron sabuwar rayuwar da bai sani ba. Hannunsa dake rawa ya matse ƙasa sosai wanda ya saka malamin ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa. “Kar ka ji tsoro ALLAH yana tare da wanda ya zo gare shi.” ya faɗa a natse cikin sanyi kuma. Kalmar ta shiga zuciyarsa wani irin sanyi ya ratsa shi. Hawaye suka sake taruwa a idanunsa yana buɗe bakin sa a karon farkon da yaji ya masa nauyi ya kama kalmar da yaji ya Malamin ya faɗi cikin kusan sarkewar murya yace. “ASHHADU… AN LA ILAHA ILLALLAH …” Se ɗan dakata sakamakon muryan daya kusa sarkewa. Wanda Malamin ya tallafoshi yana sake nanata masa kalmar gaban. “WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH …” Da wani irin kwarin gwiwa me cike da tabbaci da kuma zuciya ɗaya john ya sake kama kalmar gaban yana maimaita kamar haka. “WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH!!!.” Wani kalan shiru ne ya mamaye wurin, irin shirun nan ne mai cike da rahama. Wasu hawaye suka zubo daga idanun John, ba na baƙin ciki ba, na samun wani abu da bai taɓa tunanin samu ba. Malamin ya kalle shi cike da murmushi mai cike da alfahari yace. “Daga yau…” Sai ya ɗan dakata zuciyarsa na sake bashi kwarin gwiwwar aiwatar da cewan tabbas wannan suna shine mafi dacewa ga JOHN ɗin, domin da shi yafi chanchanta. “Kai ba JOHN bane!…” Wanda ya saka zuciyar John ɗin wani irin bugawa kamar duniya ta tsaya. Malamin ya sake kallar Idanun John din yaci gaba da fadin. “Kai IBRAHIMUL- KHALILU NEEEE... Sunanka… IBRAHEEM…KHALEEL!” Kalmar data sauƙa a cikin zuciyar John da wani irin zafi da kuma sanyin samun salama da nutsuwa, ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana jin kamar an cire masa wani nauyi ne da ya daɗe yana ɗauke da shi. Kafin a hankali ya shiga maimaita sunan a cikin zuciyarsa. _IBRAHEEM? IBRAHIMUL KHALEEL…_ Ahankali sunan ya sake amsawa cikin zuciyarsa kamar wani abu da ya daɗe yana nema amma bai taɓa sani ba. Wani irin sanyi mai gauraye da nauyin hawaye ya mamaye shi, yayin da yake jin kamar rayuwarsa gaba ɗaya tana sauyawa a wannan lokaci guda. Malamin ya zuba masa ido cikin nutsuwa kafin ya furta a hankali. “Ka san me yasa zuciyarka take jin tsoro yanzu?” IBRAHEEM ya ɗan girgiza kai alamar a’a. “Saboda rai idan zai bar duhu zuwa haske… sai ya ji kamar yana rasa wani ɓangare na kansa ne.” Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin malamin ya miƙe a hankali yana nuna masa wata ƙofa daga can gefe. “Zo tare da ni.” Ba tare da gardama ba IBRAHEEM ya miƙe yana binsa. Ahankali suke tafiya cikin harabar masallacin yayin da sassanyar iska ke bugun fuskarsa, duk mutanen da suke wucewa suna kallonsa da murmushi irin na ƴan’uwa, alhali babu wanda ya san shi, wannan kaɗai ya sake karya wani abu a zuciyarsa. “Why are they smiling at me like that…?” Ya tambaya cikin raunanniyar murya, Malamin ya ɗan yi murmushi. “Saboda daga yau kai ɗan’uwansu ne musulmi” Kalaman suka sake ratsashi kai tsaye har suka ƙarasa wajen alwala. IBRAHEEM ya tsaya yana kallon ruwan dake gudana daga famfon kamar wanda bai taɓa ganin ruwa ba a rayuwarsa. Wani irin nutsuwa ce kawai yake ji tana sake kama sa yake kallon malamin daya buɗe famfon a hankali sannan ya ce. “Mutane da yawa suna tsammanin musulunci kalmomi ne kawai…” Ya ɗan ɗebo ruwan hannunsa. “Amma musulunci dawowa ne zuwa ga ALLAH.” Sai ya zuba ruwan a tafin hannun IBRAHEEM. Nan take wani irin sanyi ya ratsa jikinsa har cikin zuciya. “Ka wanke hannunka…” Malamin ya faɗa cikin tausasawa. “…domin akwai abubuwan da suka taɓa rayuwarka da bazaka sake komawa gare su ba.” IBRAHEEM ya bi umarnin cikin nutsuwa, idanunsa na kallon yadda ruwan ke zuba daga hannunsa zuwa ƙasa. “Ka kurkure bakinka domin daga yau zaka fara furta kalaman da suka fi dukiyar da abinda ke cikinta daraja.” Hawayen dake idanun IBRAHEEM suka sake taruwa sosai. “Ka wanke fuskarka…” Sai ya ɗan dakata kafin ya ƙarasa da cewa. “Domin akwai hasken da ALLAH yake sanyawa a fuskar bayinsa idan suka neme shi da gaskiya.” A hankali ruwa ya soma gangaro a fuskar IBRAHEEM yayin da yaji kamar numfashinsa ke rawa. Sake kama John yayi suka nufi wani ƙebantaccen wuri, wani matashin balarabe ya nuna ma John yana faɗa masa ya musulumta ne, yaje da shi yayi wankan shiga addinin Musulunci. Shi kuma ya koma inda ya baro, sun jima sosai kafin wannan matashin ya dawo tare da John. “Alhamdulillah daga yau duk zunuban baya ALLAH ya kankare maka su, ka zama kamar jariri sabon haihuwa Alhamdulillah ya rabb.” Ahankali aka soma kiran sallah me shiga zuciya. “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! …” Wani lumshe idonsa IBRAHEEM yayi yana jin wani kwanciyar hankali, nan Masallacin da mutanen cikinsa suka sake tarbar sa… Wani dattijo ya yi masa murmushi dake kusa da Babban Malamin nan ya mika masa hannu tare da furta. “Assalamu alaikum.” IBRAHIMUL KHALEEL ya ɗan tsaya kalmar ta tsaya masa a rai don jin yacce kalmar ta so masa kamar sabuwa… “Wa alaikumus salam,” Ya amsa a hankali da muryar da ba ta da ƙarfi sosai Ahankali muryan wani yaro dake karanta “Ayatul Kursiyyu…” da murya me nutsuwa yaja hankalin IBRAHEEM. Kalmar ta ratsa shi ga wani irin sanyin da yaji ya shiga jikin sa, Sai ya lumshe idanunsa a ransa yana furta kalmar. _Shin zan iya zama kamar su…?_ ya tambayi kansa, yana tsaka da wannan tunanin wannan Babban malamin ya katse shi, ya kalle shi yace “Ka na kallon duk yacce nayi daga yau haka zaka yi” Ibraheem ya gyada masa kai yana kallon yadda yake motsi… Shi ma ya shiga ƙoƙarin kwaikwayon duk yacce yayi din. Tun daga kan Ruku'u... Sujjada… tare da duk wani motsi kamar sabon abu ne a gare shi. A lokacin da goshinsa ya taɓa ƙasa yaji zuciyarsa na samun nutsuwa tare da wani irin sanyi, wanda bai taɓa ji ba a rayuwarsa. Bayan sun idar suka zauna a ƙasa numfashin Ibraheem na tafiya a hankali. “Yaya ka ji?” Malamin ya tambaya. Ibraheem ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce. “Kamar… na sauke wani abu mai nauyi.” Malamin ya jinjina kai yana kallon sa cike da nutsuwa da ƙauna. Ibraheem ya buɗe idanunsa a hankali yana jin yadda duniyarsa ta yanzu ta bambanta data baya. Yana jin kamar an wanke duk wani duhun da ya tara cikin zuciyarsa shekara da shekaru. Dattijon ya ɗora hannu a kafaɗarsa da murya mai sanyi yace. “Ka zo da sunan John… Ka tafi da sunan IBRAHEEMUL KHALEEL sunan da ALLAH ke son yaji an ambata .” *To fa jama’a, Yasmine za ta iya karɓar wannan gaskiyar ne? Ko kuwa wannan shine ƙarshen soyayyarsu?* *BY AMMEY LAYLERH ✍️ 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 25 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ Two Months later. ꨄ Ƙaton jirgin private jet ɗin daya taso daga kasar Saudi Arabia yayi dirar mikiya a garin Lagos da misalin goma da rabi na dare. A wani irin natse fuskar mutumin da ya fito daga cikin jirgin ɗauke da farin jalabiya mai sauƙi da ɗan hularsa a kansa, ta fi komai ɗaukar hankali. John kenan wanda yake amsa sunan _IBRAHEEMUL KHALEEL_ Cike da wata irin nutsuwa yake takunsa irin wacce ba’a taɓa gani tattare da shi ba. Babu hayaniyar bodyguards ɗinsa kamar da, babu ɗaga murya, babu girman kai irin na tsohon JOHN. Sai dai wani irin kwarjini mai cike da salama me ɗauke da wata irin kamewar kai. Wani ɗan ƙaramin tasbaha ne riƙe a hannunsa yayin da lips ɗinsa ke motsi a hankali kamar mai ambaton ALLAH. Cab ya tara zuwa gida don babu wanda yasan da zuwan sa bare azo tarbansa, tun da taxi ɗin ta fara tafiya Ibrahimul khaleel ya koma ya jingina da kujerar motar yana tasbihi a cikin zuciyarsa, yana kuma hasaso garin daya baro ba don ya so ba sai dan saboda cilastawan Dattijon Arziki Sheik IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL WAXER. Bayan motar ta tsaya a bakin mension nasu John yaja ajiyar zuciyar da bai san ko ta menene ita ba. A hankali driver ɗin ya zagayo ya buɗe masa ƙofar motar. Fararen kyawawan ƙafafunsa ne suka fara bayyana, wanda suke sanye cikin wasu luxury leather sandals masu taushi. Kafin daga bisani shi kansa ya fito gaba dayansa, tsaye kawai yayi a wurin idanunsa a lumshe kamar mai jin daɗin wani abu da duniya bata fahimta ba. Ahankali ahankali kuma yana jan wani ɗan ƙaramin tasbaha dake rike a hannunsa. Lips ɗinsa kuma na motsi a hankali suna me ambatar. “Subhanallah!…” ƙasa-ƙasa Mecheal ne ya fara lura da tsaiwar uban gidan nasa, don da da farko ma be gane shi bane kwata kwata, se daga baya aikuwa yayo wurinsa cike da wani irin murna da farin ciki yana ambatar. _Boss!,Voss!!._ Sai dai ya ƙame ƙam a inda yake ne sakamakon dago kan da John ɗin yayi, inda Mecheal ke kallon zallar tsananin nutsuwar dake tattare da John ɗin kaɗai ta isa razana mutum. A hankali ya ɗaga kansa yana ci gaba da kallon katafaren gidan daya taɓa ɗauka a matsayin duniya baki ɗaya, wanda sai yanzu yake jin duk wannan rayuwar bata taɓa cika masa zuciya ba can dama. Cikin nutsuwa yaci gaba da takawa zuwa cikin ainihin gidan bayan ya ɗaga ma Mecheal tare ma da saurin security na gidan hannu. Wanda duk suma suka yi mutuwar tsayen irin ta Mecheal, a ransu suna ayyana me ya haɗa uban gida da kalan wannan sutura ɗin?. Sanya kansa tsakiyar parlournsu yayi daidai lokacin da Madame Victoria ke sakkowa daga samanta zuwa parlourn. Se dai itama ta kame kam ne gabanta na wani irin yankewa ya faɗi rass. “JOHN!,JOSEPH!! MY LOVE!!!” Ta kira sunan nashi cikin tsananin tashin hankali tana ƙarasawa gabansa tana binsa da wani irin kallonsa. Tun daga kan fararen kayan dake jikinsa, tasbahar dake hannunsa, sai kuma idanunsa.. Idanun nan da suka rasa hayaniyar JOHN ɗin data sani ta baya da ihu idan an ɓata masa ransa. “Mom!…” Ya furta cikin taushin muryan daya saka Madame Victoria haɗiye wani yawu. “Me… meke faruwa da kai…?” “I’m asking you a question, give me John’s answer.” Ta sake faɗa a tsawace tana sake matsowa kusa dashi sosai. Wani ɓata fuska Ibraheem yayi kafin a hankali ya furta. “Not JOHN!, IBRAHEEM!! IBRAHIMUL KHALEEL!!!...” Wani irin ƙara Madame Victoria ta saki tana ja da baya, tare da sakin glass cup ɗin dake hannunta ya faɗi ƙasa ya tarwatse a wurin ya baje. A dai-dai kuma lokacin Mr. Jeff Deefer ya fito daga saman stairs ɗin gidan cikin sauri shima, don yaji karar madame Victoria ɗin, don haka ya sakko cikin sassarfa yana me tambayar. “Victoria meke far... Se dai shima kalaman nasa sun makale masa ne sakamakon ido biyun da yayi da John ɗin. Wani irin canzawa shima tashi fuskar tayi kamar wanda yaga fatalwa. Idanunsa sauƙa kan hannun IBRAHEEM dake rike da tasbaha. “JO... JOSEPH!!!....” Ya furta sunan cikin wata irin murya mai cike da ruɗani da tsoro. Da nutsuwa John ya ɗago idanunsa gare shi, bai ma fahimci dalilin wannan firgicin ba, sai dai duk da hakan cikin ƙarfi da kwanciyar hankali ya gyara tsayuwarsa sannan ya furta. “IBRAHEEMUL KHALEEL... not Joseph, Papa....” Kamar an danna ma Papa wani maɓallin tashin hankali haka yaji, ya ɗan shiga jan Jikinsa baya kamar wanda ƙafafunsa suka kasa ɗaukar nauyin jikinsa. Idanunsa suka ƙara buɗewa cikin tsantsar firgici, leɓɓansa na rawa tamkar wanda aka zarewa rai yake sake nanata kalmar _IBRAHIMUL KHALEEL?... _ Saurin damƙe railing ɗin staircase ɗin yayi da ƙarfi saboda firgicin daya ratsashi. “IBRAHEEMUL... KHALEEL...?” Wannan karon kam ya maimaita sunan a bayyanen daya saka ƙafarsa zamewa gaba ɗaya yayi baya kamar zai faɗi saboda gigicewa, domin jin sunan nan kadai yay jinsa yay kamar daidai yake da rabuwar numfashinsa. Da sauri Jelly dake sakkowa daga staircase ɗin benen ta hangi yadda yake tangal-tangal kamar zai zube ƙasa. “Papa!!” Ta faɗa cikin firgici tana saurin ƙarasa isowa da gudu ta tare shi kafin ya faɗi, hannayenta na riƙe da shi sosai take tambayar. “Papa lafiya? Me yake faruwa?” Take tambayarsa cikin tashin hankali, amma Papa ko kallonta bai yi ba sai idanunsa daya kafe akan John tamkar wanda yake kallon wani abu daya gagare shi tun da jimawa. Numfashinsa ya fara fita da ƙarfi wani gumi na keto masa a goshinsa na tsantsan tashin hankali da rudun daya shiga. Shi kuwa John tsayawa yay cak cike da mamaki, idanunsa na yawo tsakanin Madame Victoria da Papan nasu. Saboda shi kansa bai fahimci dalilin da yasa sunan “IBRAHEEMUL KHALEEL” ɗin ya firgita su har haka ba. “Wa ya baka wannan sunan?! And ama ina uban ya ka hadu dashi da yaja mana ra'ayinka akan wani can addininsu na karya?....” Ya tambaya cikin tsananin firici da wani sabon tashin hankalin da yake jin kamar yana dirar masa. IBRAHEEM ya ɗan haɗe girarsa jin suna nemar taɓa addininsa, addinin da yake da cikakken tabbaci da kuma yakinin cewa shi ne addinin gaskiya. “Wani babban malami ne a Saudi Arabia…” Ai tun kan ya ƙarasa furta wa Mr. Jeef Deefer dake jingina da jikin jelly yay wata bahaguwar mikewa da ƙarfi yana sake jefa masa tambayar. “Ka ce a wacce ƙasa ka musulunta?” “Saudi Arabia .” Kamar walƙiya haka Papa yaga shudewar wani abun daya jima mantawa dashi ya gitta masa. Madame Victoria kuwa cike da wani irin rudewa ta dafe baki cikin tsoro tana ambatar. “…Shikenan.” Cikin rawar muryan daya saka IBRAHEEM ya sake kallonsu. “Me... ya... sa dukanku kuka firgita haka?” Sai dai babu wanda ya amsa masa sabofada a wannan lokacin… Saboda duk gani suke wani sirri ne na shekaru da shekaru ke neman farkawa daga cikin duhun da suka jima bisnewa. “Saudi Arabia…?” Kusan a tare suka hade baki wajen nanata wannan kalmar. Wacce jin sunan kasar kawai jinsa suke tamkar sauƙar mashi a cikin zuciyoyinsu. Madame Victoria ta matsa kusa da Papa cikin rawar murya da tashin hankali ta riko hannunsa cike da tsoro tace. “Jeff…” Stop ya mata da hannunsa yana me furta. “Kar ki cemin komai... shiru!” Ya katseta da sauri idanunsa cike da tashin hankali. IBRAHEEM ya tsaya kallonsu zuciyarsa na bugawa yana jin kamar akwai wani abu da ake ɓoyewa game da rayuwarsa. Game da sunan nan da kawai ya dawo dashi game da Saudi Arabia. Game da dalilin da yasa zuciyarsa ta amsa musulunci kamar wanda ya daɗe yana jiransa dama. Mr. Jeff Deefer ya sake kallonsa kamar a tsorace yace. “Ka ce min…” amma duk da haka seda ya gaza mai kalmar duka har se da ya haɗiye wani yawu kana ya ɗora da. “…wa ya saka maka sunan na IBRAHEEMUL KHALEEL ɗin?” “Babban malamin masallacin kasar da na musulunta.” Madame Victoria ta dafe baki ta sake furta kalmar. “…Shikenan.” Ta furta cikin rauni kamar wacce ke tsoron a kwace mata wani abunda yake kamar ba nata ba. IBRAHEEM ya ɗago yana kallonta cike da Tuhuma yace. “Meyasa kuke tsoro ne…?” “AM AMM KA GA SOON BA KOMAI BA FA NE DA MA.... DA MA......” “DAMA BAMASON KA RINKA ZUWA IRE IREN ƘASASHEN NAN NE SABODA YAKIN DAKE FARUWA DASU HAKA.....” Madame Victoria ta yi saurin fanshe mijin nata, wanda wani kallon ban yarda daku ba kawai John ya jefesu dashi yana shigewarsa stairs nashi... *INDIA* Cikin katafaren gidan Lady Rebecca dake India kuwa. Tun da suka dawo ake ta shirye shirye bikin auren Deepika da JOHN. Don sun ce aure ne babu fashi tabbas duk inda ya tafi ma zai dawo ya tarar da an daura masa aure da Deepika ɗin, yanzu haka sun kammala duk sauran shirye shiryensu dake India suna jiran visa nasu ya fito su taho Nigeria don dama alkawari su kayi duk sanda auren Deepika ya tashi da John sun gama zaman India kenan. Wayar Deepika dake gefe da ita ne ta soma ringing. Da murmushi Deepika ta ɗauka don ganin wanda ke kiranta, sai dai murmushin nata ya ɓace ne nan take sakamakon abinda aka faɗa mata daga cikin wayar daya saka ta mikewa tsaye a firgice tana furta kalmar. “WHAT?!” Cikin tsananin firgici Lady Rebecca ta juyo da sauri ga Deepika din tana jefa mata tambayar. “Deepika meke faruwa?!” Deepika ta kalli mahaifiyar nata da idanunta da suke cike da tsoro ta furta. “JOHN ne! …” Ta haɗiye wani yawu ta ɗora da fadin. “…YA MUSULUNTA .” Wani irin shiru ne ya mamaye Wajen “MUSULUMCI?…” Lady Rebecca ta sake furtawa a hankali don ji tayi kamar bata ji daidai ba. Deepika ta girgiza kai hawaye na taruwa a idanun ta tana me sake furta. “Not John…” Ta furta cikin rawar murya. “Yana kiran kansa IBRAHEEMUL KHALEEL.” Nan take fuskar Lady Rebecca ta sauya cike da tsananin tashin hankali ta matsa kusa da Deepika tana rike kafaɗarta ta girgizata tace. “Me... Ki.... ka... ce?!” A dai-dai lokacin da Daddyn Deepika ke shigowa parlour ɗin. “Rebecca me ke faruwa ne?” Shi din ma kalmar IBRAHEEMUL KHALEEL ɗin kawai data ambata masa ne ya saka wani irin firgici ya bayyana akan fuskarsa yana ja da baya tare da furta. “No…” Ya ci gaba da furta kalmar No din yana girgiza kai. “This can’t be happening…” Lady Rebecca ta kalli mijinta cikin rawar murya. “Ka tuna abinda Sheikh ɗin nan yace shekarun baya da suka wuce…?”Nan take ya juya yana mata kallon tsoro. “Kar ki sake ambaton wannan maganar!” Deepika ta zaro ido tana kallon su da furta. “Wait… what’s going on?!” Sai dai babu wanda ya bata amsa saboda dukkaninsu sun san wannan sunan ba ƙaramin suna bane me haɗari tattare da sake fasuwarsa cikin ahalinsu.... *YASMINE * A gefe guda kuma gaba daya yinin yau YASMINE ta yi sane cikin faduwar gaban haka kawai, Ko yanzun ma tsaye take bakin window ɗinta tana kallon ruwan dake sauka kaɗan ƙadan. Zuciyarta cike take da rashin nutsuwa tun kwanakin nan bama iyaka yau ɗin ba. Wani irin faɗuwar gaba take ji kamar akwai wani abu da yake shirin canza rayuwarta gaba ɗaya, wayarta data soma ringing ne ya saka ta saurin kallo, tana ganin sunan wanda ke kiran taji numfashinta ya kusa tsayawa. Hannunta na rawa ta daga wayar tare da mannata da kunnenta. Wani shiru ne ya ratsa tsakanin wayar, kafin daga bisani ta ji muryarsa mai cime da nutsuwa ya furta mata kalmar. “Assalamu alaikum, Yas_mine…” Wani irin bugun zuciyar YASMINE tayi saboda wannan…ba muryar JOHN ɗin data sani bane. _Hhhhhhh to ai shikenan jama'a a gimtse haka nan._ _Shin kuna ganin cewar YASMINE kuwa ko za ta iya karɓar sabon IBRAHEEM din daya dawo mata a madadin JOHN?_ _Ko mene ne sirrin dake tattare da sunan IBRAHEEMUL_ KHALEEL?.. Kome yasa kowa ke firgita da jin sunan Saudi Arabia kawai bayan sunan kuma sunan IBRAHIMUL_KHALEEL ɗin…?_ _Ko kuwa sirrin da ke tattare da sunan IBRAHEEMUL KHALEEL ɗin shi zai fara rusa komai?_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 26 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ Wani irin sake yankewa ya fadi gaban YASMINE yayi lokacin da muryarsa ta sake ratsata ta cikin wayar a karo na biyu. “Assalamu alaikum, Yas_mine…” Numfashinta ne ya ɗan tsaya na wasu sakanni kafin daga bisani cikin rawar murya ta amsa. “Wa… alaikumus salam…” Sai dai zuciyarta gaba ɗaya ta shiga wani irin ruɗani saboda wannan ba JOHN ɗin data sani bane. Wannan muryar cike take da wata irin nutsuwa da sanyin da take ji har cikin ranta. A hankali ta lumshe idanunta tana riƙe wayar sosai a kunnen ta furta “John…?” Shiru ya ɗan ratsa tsakanin wayar kafin daga bisani ta sake jin muryarsa cikin taushin da ya taba zuciyarta ya ce. “Not John…” Ya furta a hankali. “IBRAHEEMUL KHALEEL.” Wani irin faɗuwar gaba YASMINE ta ji sai dai ba tsoron sunan tayi ba kamar sauran mutane… zuciyarta ce kawai ta shiga bugawa da sauri saboda yadda take jin canjin dake cikin muryarsa. “Ka… ka dawo Nigeria…?” “Na dawo.” Ya amsa cikin nutsuwa wani shiru ne ya sake ratsa tsakaninsu kafin daga bisani ya furta. “Ina son ganinki.” Nan take zuciyar YASMINE ta sake bugawa da ƙarfi. Tun kafin ta samu damar magana ya sake cewa. “Please…” Wannan kalmar tasa ce ta karya mata zuciya gaba ɗaya saboda bata taɓa jin JOHN yana roƙon kowa ba. A hankali ta haɗiye wani yawu kafin daga bisani ta furta, “Ina… ina gida.” “Zan zo.” Daga haka ya kashe wayar. YASMINE ta sauke wayar daga kunnenta a hankali zuciyarta na wani irin bugawa, don har yanzu bata gama yarda cewa JOHN ya musulunta ba. “To wai… me yake faruwa ne…?” Ta furta a hankali tana dafe ƙirjinta. ★.. Tun bayan shigewar IBRAHEEM ɗakinsa Mr. Jeff Deefer ya kasa zaune ya kasa tsaye ko na minti guda. Sai faman kai kawo cikin parlourn yake tamkar wanda aka ce masa hankalinsa zai bar jikinsa, Madame Victoria kuwa gaba ɗaya idanunta sun yi wani irin zurfin sanya ɓacin rai, tana maƙale wurin mijin nata. “Jeff…” ta kira cikin rawar murya, sai dai ya dakatar da ita da hannu cikin tsananin fushi. “Na ce kar ki sake min wannan maganar!” ya furta a tsawace. “Wannan yaron bai san abinda yake kunnawa kansa ba!” Jelly dake zaune gefe tana kallonsu cikin ruɗani ta kasa jurewa tace. “Papa… me yasa kuke tsoron sunan nan haka ne?” Nan take parlour ɗin yayi tsit. Mr. Jeff Deefer ya tsaya cak har numfashinsa ya ɗan tsaya shima kafin daga bisani ya juya ya kalli Jelly da idanunsa da suka kaɗa suka yi ja. “Saboda wannan sunan…” Ya fara cikin murya mai nauyi.“…yana da alaƙa da mutumin daya taɓa rusa rayuwar mutane da yawa.” Wani irin faɗuwar gaba Madame Victoria ta ji. “Jeff stop please…” Ta furta cikin tsoro sai dai ya girgiza kai. “A’a Victoria! Lokaci yayi da zamu fara fuskantar gaskiya.” don haka ya juya yana kallon staircase ɗin da yake jin kamar motsin wani abu. “Na rantse bazan bari ya sake komawa kusa da waɗannan mutanen ba.” A dai-dai lokacin kuma wayar Papa ta soma ringing wanda yake masa maganar da yake yi yana daukar wayar da sauri, sai dai abinda aka faɗa masa ne ya saka idanunsa buɗewa sosai cikin firgici. “What?!” Madame Victoria ta miƙe da sauri. “Me ya faru?” take tambayarsa cike da wani sabon tsoro da rikicin. Sauƙe wayar a hankali yayi yana kallonta. “…John ya cire sunan DEEFER daga duk wani social account nasa.” “What?!” “He changed everything to IBRAHEEMUL KHALEEL.” Wani irin shiru ne ya mamaye parlour ɗin. Jelly ta zaro ido, Madame Victoria kuwa ta dafe baki. Shi kuwa Mr. Jeff Deefer cikin wani irin fushi ya sake ɗaukar wayarsa yana saka ƙiran wata No. “Freeze every single account belonging to him.” “Sir?” Aka so katse shi daga cikin wayar. “I said EVERYTHING!” Ya daka musu tsawa yana ci gaba da bada umarnin. “Credit cards, company access, shares, properties… komai!” Madame Victoria ta kalleshi cike da mamaki da tsoro ta ce. “Jeff no!” Sai dai ko kallonta bai yi ba ya ce. “Daga yau ba JOHN DEEFER bane shi.” A kuma dai-dai lokacin Wayar IBRAHEEM dake gefensa ta soma vibrating babu ƙaƙƙautawa. ACCOUNT BLOCKED,ACCESS DENIED OWNERSHIP REMOVED. Haka Saƙonnin suka cigaba da shigowa, amma sam sam a fuskarsa bai nuna ko ɗigon tashin hankali ba. Sai ma ahankalin da yaja idanunsa ya lumshe kawai yana ci gaba da jan tasbahar dake hannunsa yana jan numfashi. “ALHAMDULILLAH…” Ya furta cikin nutsuwa kamar wanda dama tun farko ya shirya rasa komai saboda addininsa. Wayarsa ce ta sake haskawa da wani sabon saƙon. _YOU HAVE BEEN REMOVED AS CEO OF DEEFER EMPIRE._ Wani ɗan murmushi ne kawai ya bayyana akan lips ɗinsa. Daidai kuma lokacin ƙofar ɗakin nasa ta buɗe da ƙarfi, Mr. Jeff Deefer ne ya shigo cikin tsananin fushi. “Ka rasa komai!” Ya furta yana nuna shi da yatsa ta da sake ɗorawa da “Everything all!” Cikin nutsuwa IBRAHEEM ya ɗaga kansa yana kallon sa ba tare da shakka ko tunanin komai ba yace. “ALLAH yana tare da ni” Wannan kalmar tasa ce ta ƙara fusata PAPA har besan Lokacin da sake furta. “Ka haukace ne?!” ya daka masa tsawa. A hankali IBRAHEEM ya miƙe tsaye yana kallon mahaifin nasa. “Ina son yin aure.” Nan take Papa ya tsaya cak yana binsa da wani irin kallon mamaki. “Da wa?” Cikin kwanciyar hankali IBRAHEEM ya furta. “YAS-MINE.” Wata irin zabura Papa yayi tamkar wanda aka caka wa wuƙa cikin ihu ya furta. “NEVER!!” “Na fi son ganin mutuwarka akan ka aureta, akan sabuwar masifa da bala'in da kake kokarin sake kunno mana bayan shekaru!” Wani irin shiru ne ya mamaye ɗakin kafin amma duk da zafin kalaman be saka fuskar IBRAHEEM nuna tsoro ba. Sai ma sake sauke idanunsa da yay cikin nutsuwa kafin daga bisani ya furta. “Ina sonta saboda ALLAH.” Wani irin tsit ne ya mamaye ɗakin bayan furucin IBRAHEEM, Ko motsin numfashi ba’a jin sa sosai saboda yadda kalamansa suka tsaya cak cikin zuciyar kowa. “Ina sonta saboda ALLAH.” Kalmar ta sake masa amsa kuwwa cikin kunnuwan MR. JEFF DEEFER tamkar ana maimaita masa ita sau dubu. Idanunsa kuwa tuni sun sake yin ja saboda tsananin fushi da kuma wani irin tsoro da yake ƙoƙarin ɓoyewa. “Ka haukace Ibrahim!” ya sake faɗa cikin tsawa. “Ka rasa komai amma har yanzu baka gane abinda ka janyo mana ba?!”Duk wannan abin kuwa da yake tunanin yanayi ne don ya razana IBRAHEEM ɗin amma bai motsa ba. Sai ma tsayen da yayi cikin nutsuwa kamar dutse, hannunsa riƙe da tasbaharsa yana kallon mahaifin nasa cikin idanuwan da suka rasa girman kai na duniya amma suna dauke da wani kalan kamewa da kwarjin da girma irin na musulunci daya bashi. “A duk rayuwata…” ya faɗa cikin nutsuwan murya. “…ban taɓa jin nutsuwa kamar lokacin da na san ALLAH ba.” Papa ya girgiza kai cikin takaici. “Saboda wata yarinya zaka jefar da rayuwarka?” A hankali IBRAHEEM ya ɗan girgiza kansa, “Ba saboda ita kaɗai ba…” ya furta. “…saboda gaskiyar da na gani.” Madame Victoria dake bakin ƙofa ta kasa jurewa ta fara kuka a hankali. “John please…” ta furta cikin rawar murya. “Ka dawo mana yadda kake…” Wani irin rauni ne ya ratsa fuskar IBRAHEEM kafin daga bisani ya sauke idanunsa ƙasa. “Sunana ba John bane kuma, Mom.”Wata irin faɗuwar gaba Madame Victoria taji har sai da ta dafe bango. “Ni IBRAHEEMUL KHALEEL ne.....” Da wata irin tsawa Mahaifin nasa ya dube se cikin kallon tsana ya nuna masa hanya yana furta.... “OUT” A wani irin tsawacen daya sake rudar da Madame Victoria tayi wurin Mijin nata tana riko hannun sa tana bashi hakuri akan kada ya kori JOHN daga gidan. Madame Victoria ta fashe da kuka mai ciwo tana bin bayan IBRAHEEM yayin da yake fita daga ɗakin cikin nutsuwar sa. “IBRAHEEM please… don’t leave…” ta faɗa cikin rawar murya tana riƙo hannunsa. Sai dai a hankali ya sauke idanunsa yana kallon hannun mahaifiyarsa dake rawa saboda kuka. Wani irin tausayinta ne ya cika zuciyarsa amma duk da haka ya san bazai iya komawa baya ba. “Mom…” ya furta cikin sanyin murya. “Idan na zauna zan rasa kaina ne, amma idan na tafi ALLAH bazai taɓa bari na tozar ta ba.” Wata irin kuka Madame Victoria ta sake fashewa dashi tana girgiza kai. “A’a… a’a John Ohhh Jesus! Ohh Jesus Help me with your John…” Wani ɗan rumtse idonsa yayi yana zame hannun sa a nata. A dai-dai lokacin kuma JELLY ke sakkowa daga upstairs cikin tashin hankali bayan jin ihu da hayaniya. “Mum… What happened?” ta tambaya tambaya cikin firgici tana kallon akwatunan da already wasu guards suka fara saukowa da su daga ɗakin IBRAHEEM. Papa kuwa tsaye yake a wurin ƙamm kamar dutse fuskarsa cike da wani irin baƙin ciki da fushi da ya kasa ɓoyewa. “Ya fice daga gidan nan.” Ya ya furta a taƙaice.“What?!” jelly ta faɗa tana zaro ido tana kallon ɗan uwan nata. “Joseph … kana nufin zaka bar komai ne saboda ita?, Saboda addininta, and Ai zaka iya aurota ka kawo ta gidan nan kowa yayi rayuwarsa yacce yaso right?” A hankali IBRAHEEM ya ɗan taka gabanta kafin ya kalli sama ya ce. “Wasu abubuwan na duniya idan ka barsu saboda ALLAH… ALLAH yakan baka mafi alkhairi wasu, ki dauka haka Jelly.” Wani irin tsit ne ya sake ratsa parlourn yayin da ya juya ya nufi ƙofa. Madame Victoria kuwa ta bishi da gudu har outside cikin kuka. “IBRAHEEM!” Ya tsaya cak tana isa gabansa ta riƙe fuskarsa da hannayenta masu rawa. “Ka kula da kanka…” ta furta cikin kuka, wani irin rauni ne ya bayyana a saman fuskarsa kafin daga bisani ya sunkuyar da kansa ya sumbaci hannunta cikin girmamawa. “Ki yafe min Mom amma nayi abinda ya dace ne…” Daga haka ya juya ya shiga motar da se da kyar Madame Victoria ta zaro masa key nata. A hankali motar tasa ta fara barin katafaren gidan DEEFER mansion yayin da Madame Victoria ke tsaye tana kuka kamar zuciyarta zata tarwatse. ★ Wasu sa’o’i bayan haka... Tsaye yake gaban wani ƙaramin modern flat house dake wani unguwa mai nutsuwa a Lagos. Ba wani katafaren gida bane irin wanda ya saba rayuwa a ciki, amma wajen cike yake da salama. Agent ɗin gidan na miƙa masa key yana murmushi. “Congratulations sir.” A hankali IBRAHEEM ya karɓa yana kallon gidan. Bedroom biyu ne kawai, sai ƙaramin parlour da kitchen… amma a karon farko cikin rayuwarsa ya ji kamar yana gida na gaskiya. Ya shiga ciki a hankali yana kallon ko’ina kafin daga bisani ya shimfiɗa prayer mat ɗinsa a ƙasa. Sujjada yayi mai tsawo. “ALHAMDULILLAH…” Hawaye ne suka zubo masa karo na farko tun bayan fitowarsa daga gidan mahaifinsa. *Washegari…* Wajajen Sha biyu IBRAHEEM ya isa gidan su yasmine tare da wani babban malamin da SHEIKH IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL WAXER ne ya hada shi dashi, get man ya musu iso bayan ya leko sun bashi sakon, har babban parlourn gidan suka isa. Ambassador yana ganin John ya gane shi, kuma Yasmine ta faɗa masa labarin musulumtar da yayi. “Assalamu alaikum.” Ibraheem ya fara sallama kafin ta malamin ta biyo baya, “Wa alaikumus salam…” mahaifin YASMINE ya amsa yana binsa da kallo kafin ya ce. “Ku karaso mana.”A parlourn gidan ya zauna cikin nutsuwa. Bayan an kawo musu ruwa ne ya ɗago kansa yana kallon su Ibraheem din. Tun kafin yayi magana wannan malamin ya taryi numfashinsa ta hanyar. “Mun zo ne da magana mai muhimmanci” Ambassador Khabeer ya sake gyara zamansa yana amsawa da. “Ina jinka.” A hankali SHEIKH AUWAL ALBANI ya sauke numfashin. Kana a natse ya faro da basu tun daga farkon komai… yadda ya musulunta… yadda ya rasa komai saboda addininsa… yadda aka cire shi daga wurin aikinsa na pilot… da yadda ya bar gidansu gaba ɗaya. Cike da wata irin nutsuwa Malamin yake magana amma kowace kalma tasa na sauka da nauyi cikin zuciyar kowa. Domin duka har yasmine ɗin da malamin ya bukaci gani tana zaune tare da Mamy da Husner. Mahaifin YASMINE ya daɗe yana kallon John kafin daga bisani ya ce. “Saboda yarinyata ka jure duk wannan abun?”A hankali IBRAHEEM ya girgiza kai. “Saboda ALLAH ne farko… sannan saboda ina sonta da gaskiya.” Ambassador ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya juya ya kalli YASMINE. “Yasmine…” “Na’am Daddy…” “Kin tabbata kina sonsa?” Nan take idanun YASMINE suka cika da hawaye. Cikin rawar murya tace. “Fiye da komai ma …” Mahaifinta ya daɗe yana kallonta kafin daga bisani murmushi mai cike da tausayi ya bayyana a fuskarsa. “To…” ya faɗa cikin nutsuwa yana kallon IBRAHEEM. “Idan haka ne… gara a daura auren nan tun wuri.” ALLAH Sarki Mamy komai bata ce domin tashin farko taji John din ya kwanta mata a rai, tun daga kamo yadda komai nashi a natse da kuma taka tsantsan. Malamin ne ya jinjina kai ya buɗe baki kenan da niyar magana, amma amma wata irin ƙarar tsayuwar motoci ta cika harabar gidan. Kowa ya juya da sauri cikin firgici…!Wata irin ƙarar tsayuwar motocin ce ta sake cika harabar gidan gaba ɗaya tamkar an zo kama wani ɗan ta’adda. Kafin wani ya samu damar magana aka turo ƙofar parlourn da ƙarfin, Jelly ce ta fara shigowa numfashinta na fita da sauri kamar wacce tayi gudu, bayanta kuma wasu security guards ne tare da… MR. JEFF DEEFER. Nan take gaba ɗaya yanayin wajen ya canza. Ambassador Khabeer ne ya miƙe tsaye cikin mamaki. “Mr… Deefer?” Sai dai ko kallonsa PAPA bai yi ba sai ma Idanunsa daya mayar kan Ibraheem gaba ɗaya. “Ka raina ni har haka ne?” Ya furta cikin wata irin murya mai nauyi. Shiru IBRAHEEM yayi yana kallon mahaifinsa cikin nutsuwa. JELLY dake tsaye tana kallon Yayan nata idanunta duk sun kumbura saboda kuka ta girgiza kai tana ce. “Joseph … Mommy fa tana asibiti…” “What happened?” Ya tambaya da alamar damuwa a fuskarsa. Papa ya ɗan busa iska cikin takaici yana kallon Mahaifin Yasmine dake basu wurin zama. Wani kallon ƙasƙasci PAPA yama duka parlourn cikin tsananin fushi ya ce. “Bani da abin zama a nan!” Sai ya nuna IBRAHEEM da yatsa. “Na zo daukarsa ne.” A hankali IBRAHEEM ya sauke numfashi tare da furta. “Bazan koma ba.” Nan take idanun PAPA suka sake yin ja. “Saboda ita?!” Ya fada yana nuna YASMINE cikin tsawa. “Saboda rayuwata.” Ibraheem ya furta yana jin wani abu na taso masa game da wannan kutsen da suka masa. Sheik Auwal ne ke kallon su gaba ɗaya cikin nutsuwa irin ta manyan malamai kafin daga bisani ya ce. “Mr. Deefer…” PAPA ya juya yana kallon sa, shi kuma ya dan fesar da wani numfashi kana ya ɗora da faɗin. “Ɗanku mutum ne babba. Kuma idan ya zaɓi addininsa da rayuwarsa… bai kamata ku tsane shi ba.” “You know nothing!” Papa ya katse shi cikin tsawa tare da juyawa yana kallon IBRAHEEM yace. “Zan ga kuma inda addinin da kake ikarin gaskiya ne zai kaika....”. “Wasu sirrukan ba a ɓoye su don a kare duniya... Amma ana iya ɓoye su ne don a kare zuciya guda ɗaya daga rushewa.” Dum gaban Papa ya faɗi, saboda jin wannan kalmar data taɓa kamanceceniyar da aka taɓa faɗa masa shekarun baya, “Zan kawo ƙarshen komai dole...” ya fadi daga haka ya juya yana barin wurin bodyguard nashi na rufa masa baya suka fice. Ambassador Khabeer ne ya sauƙe ajiyar zuciya tare da kallon Sheik Auwal Albani yace. “Ni dai magana ɗaya zan yi. Idan wannan yaron har ya iya barin dukiya saboda addini… toh ina tabbatar muku bazai cutar da yarinya ta ba.” YASMINE ta runtse idanunta hawaye na cika mata su .Sai dattijon ya juya yana kallon Ambassador tare da masa godiya. Ba komai yace yana sake nanata masa kalmar. “Aure kam za’a daura shi In sha ALLAHU.” “NEVER!” Gaba ɗaya haka suka jiyo muryan PAPA daya dawo ɗaukan jar sandarsa daya manta. IBRAHEEM ne ya ɗan taka gaba yana kallon mahaifinsa ido cikin ido ya ce. “Ko duniya zata ƙi ni…” ya furta cikin kwanciyar hankali. “…bazan sake barin YASMINE ba.” *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 27 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Wani irin shiru mai nauyi ne ya ratsa parlourn bayan kalmar “NEVER!” ɗin da Papa ya furta. Ga Idanunsa dake cike da fushi sosai, hannunsa riƙe da sandar da ke rawa saboda tsananin tashin ɓacin rai. “Ba zai faru ba!” ya sake maimaitawa cikin ƙarfi. “Wannan auren ba zai taɓa faruwa ba matuƙar ina raye!” Ibraheem ya tsaya a wuri ɗaya, fuskarsa a nutse kamar komai baya damunsa a zahiri. Sheikh Auwal ne ya matso gaba a hankali cikin natsuwa yace. “Mr. Jeef Deefer…” ya faɗa cikin sanyin murya kafin ya ɗora da faɗin “Fushi ba zai magance komai ba. Wannan lamari na zuciya ne da kuma addini…” da hannu Papa ya katse shi cikin tsawa.“Ni ban tambaye ka ba!” Ibraheem ya ɗan ɗaga ido, ya kalli mahaifinsa cikin nutsuwa ya furta. “Papa…” Kalmar ta sa Papa ya tsaya cak na ɗan lokaci amma sai ya ƙara fusata. “Kar ka sake kirana Papa!” ya faɗa a mugun tsawacen daya saka wani irin shiru ɗin ke wurin tsaf. Ibraheem ya sauke kai a hankali, sannan ya ce cikin murya mai nutsuwa. “Ko ka yarda ko ba ka yarda ba… ni na riga na zaɓa.” Ya ɗaga kai ya kalli Yasmine ahankali tare da fara taka wa zuwa gabanta yace. “Ina son ta. Kuma zan aure ta.” Daidai lokaci da Jelly ta fashe da kuka wacce shigowar ta kenan a karo na biyu tana furta. “Joseph No! John A ahhh…Mommah tana asibiti saboda wannan abun!” Tun kafin ya sama zarafin magana cikin fushi Papa ya sake ce. “Idan ka auri yarinyar nan… ka sani ka riga ka raba kanka da ni har gaban abada.” Fuuuu yaja hannun jelly suka bar wurin a mugun fusace yana dafe ƙirjinsa dake kamar zai ɓalle masa ko zuciyarsa ta fashe ƙirjin ya fito. Bayan wucewar sune Ambassador Khabeer ya kalla Sheik Albani yace ya ya kawo shaidu bayan an fito daga sallan zuhr kawai a daura auren. Hakan kuwa akayi yazo da wasu abokansa uku shima nan da shaidunsa aka hadu bayan idar da Sallah ga masallacin a cike yake taf liman yace kar kowa ya watse akwai ƊAURIN AUREN da za'a gudanar. Waliyyin da ambassador Khabeer ya tsayar ne a matsayin na YASMINE ya kalla Ibraheem yace. “Shin ka yarda?, ka kuma yi imanin amsar wannan auren, da zuciya ɗaya bada wata manufa ba?...” “Idan hakan ne zai sa na tsaya kan gaskiya… to na yarda.”Wani irin shiru mai nauyi Masallacin ya yi tsit… Sai ƙarar iska kaɗan da ke ratsawa a tsakanin mutane da kuma numfashin juna. Sheikh Auwal ya kalla Ibraheem cikin nutsuwa yana me ambatar. “ALHAMDULILLAH!…” Nam kowa ya sake nutsuwa Ibraheem ya sauke kai, hannunsa na rawa kaɗan amma zuciyarsa cike da imani. Sheikh ɗin ya kalli Wiliyyin Yasmine. “Waliyyi ya ba da izini?” Waliyyin Yasmine ya yi shiru na ɗan lokaci… sannan ya sauke wani numfashi yana mai furta. “To ALHAMDULILLAH a fara…” Sauƙe wani nutsatstsen numfashi Ibraheem yayi yana jin samun nutsuwan abinda ya jima da toƙare ƙirjinsa na komawa ya kwanta. A wani irin natse Sheik albani dake matsayin waliyyin ANGO ya Isa gaban Waliyyin Yasmine cikin kamala da dattaku da kuma jin nutsuwar aikata abinda zuciyan sa ke umar tansa daya aikata ya furta. "NI SHIEKH MUHD AUWAL a matsayina na waliyyin ango ina mai nemawa Yaro na *IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL * Auren ƴarka _*HAUWA KABEER USMAN MAINA*_ a bisa sadaki Naira dubu Hamsin" Wata irin Ajiyan zuciya da numfashi me ɗumi Ibraheem ya sake sauƙewa. Shi kansa Daddy'n Yasmine ɗin wani daɗi yaji yana rufe shi har cikin ranshi da zuciyan sa, faɗar irin farin ciki da nutsuwar daya tsinta kam kamar wani ɓata baki ne ma. Wani irin kwantaccen farin cikin gaske ne ke zagaye da kyakkyawar fuskar Ibraheem yana amsa addua tare da godiya ga ALLAH da shi ne kawai ya shirya wannan Auren. Ɗaurin auren aka fara gabatarwa cikin nutsuwa da haiba. Haka aka ɗaura Auren HAUWA KHABEEER USMAN MAINA tare da IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL akan sadaki dubu Hamsin. Zuciyarsa ce yaji kamar ana narka masa ita da tsananin farin ciki. “ALHAMDULILLAH…” ya faɗa a zuciyarsa dake cike da fata da kuma burin zuwan wannan rana. Washe gari kuma aka tashi da walima,na maza daban na mata ma haka, wacce tuni Mamy ta sanar ma da yan uwa da dangi se gashi har sun cika gidan, ALLAH Sarki Ya Omer lokacin da zancen auren ke isa gareshi seda wata hajijiya ta kusa zubar dashi, amma yayi ta maza ya maze. Haka Mahaifiyar Mamy ta iso itama tun a ranar kusan komai a gaggauce aka ma Yasmine ɗin, bayan ta ƙare mata tasss din taki auren jikan ta ta auri sabon tubar da bata da cikakken tabbaci akansa. Toshe kunnuwanta kawai tayi sema kokarin maida hankalinta kan party ɗin da suka hada ita da friend nata da tayi. Kwana uku ran na huɗun aka karasa kimtsata da yamma aka mikata hadadden tsararren gidanta dake cikin anguwar Kabuga Jan bulo,kada kuso ganin yadda yan uwa suke zuba santin gidan Yasmine ɗin, duk da kasancewarsa ba wani tsararre ma amma kuma komai bisa tsari yake shi yasa ma gidan ya musu kyau sosai, wanda tuni komai na ciki an sauya an zuba mata nata sabo gwanin burgewa,bayan ƴan rakiyar amarya sun fara tafiya duka da yake dama ba wasu mutane ne na daban ba yan uwane kawai se makwabtansu. Manyan kawayenta biyu aka bar mata suka zaune tare da ita har dare, tara da rabi dadi IBRAHEEM ya shigo gidan shi da ɗan gidan Sheik Albani me suna Usman. Bayan ya sake musu nasiha ya debi ƙawayen Amarya ya wuce dasu, aka bar iyaka ango da amaryarsa kawai masu fata da burin suga sun mallaki juna. *AUJARA JIGAWA STATE* A wani irin mugun firgice matar dake bacci ta farka bakinta yana jeranta duk adda'ar da yazo bakinta. "A'uzhubillahi minashshaiɗanir rajiiym.. Laa ilaaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn Allahumma inni as’aluka sakinah fil qalb, wa rahat fid-dunya wal-akhirah!! Allahumma inni a’udhu bika minal-hammi wal-hazan!!!....” Yanayin yadda ta farka da ɗin ne ya saka gumi keto mata duk uban sanyin dake cikin ƙayataccen bedroom nata. Da sauri Magidanciciyar matar da shigowarta kenan bedroom ɗin ta nufo inda take fuskarsa cike da damuwa tana tambayarta "JANNEERH LAFIYANKI?...” Kirjinta ta dafe tana dago manyan idanun ta da yanayin su suke kamar na mai jin bacci ta kalla Mahaifiyar nata data zauna daf da ita rike da kafadunta. Kanta take ɗan girgiza mata idanunta kamar an soye mata su se wani irin uban zugin da suke mata ta girgiza kai, tana haɗiye wayun da take da tabbacin babu su da kyar ta makoshinta tana kallon Mahaifiyar nata tana ƙirƙirar wani murmushi saboda ta ganin yadda hankalin Ummien nata ya tashi ta sake girgiza mata kai alamar babu komai. Ahankali Mahaifiyar nata tayj ajiyar zuciya tana kallon yarinyar nata cike da ƙauna tana riko hannunta ta sake jefa mata tambayar "What happened Dear?" Ɗan jim wacce aka ƙira da jannerh tayi tana tunanin abunda za ta faɗa ma Ummien nata, ce mata za tayi mafarkin namiji tayi?, ko kuwa zata ce mata na mafarkinta ta gani tare da wata macen a daren yau cike da Duhu da kuma Haske duk a cakuɗe dasu. A hankali ta lumshe idanunta kawai tace "mafarki nayi" Wacce aka ƙira da ummein ce ta sake yin ajiyar zuciya kafin tace "Ok! Ai kinyi adda'ah ko?, IN SHA ALLAHU nothing will happen" JANNEERH ɗin tace "IN SHA ALLAH" Mahaifiyar nata na kamo kanta tana ɗorawa kan Kirjinta wani irin tausayin ƴar nata na cika ta tana karanta mata. “Hasbiyallahu la ilaha illa huwa, ‘alaihi tawakkaltu, wa huwa rabbul arshil Azeeem.” cike da tsananin tausayi irin na uwa akan ƴaƴanta, bayan ƙaddarar aure, cikin year's ɗin nan kuma gaba ɗaya mafarkai take yawan yi marasa kan gado, wacce har zuwa yau ta gaza basu takamammiyar amsa akan irin mafarkin da take yawan yi ɗin. Mahaifinta MALAM MUHAMMAD ALIYU BAITA babu irin adda'an da bai mata ba, ita kanta tsaye take akan diga diganta amma ALLAH be kawo makarin abun ba. Duk da kasancewarta babbar malamar musuluncin da gaba ɗaya jihar ta ke ji da ita, kasancewarta gwana wajan lashe musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa da ƙasa, ita kuma ta ƙara jawo kima da martabar jiharsu ta gasar duk shekarar da akeyi ta kasar Madina. Malamar dake sake nutsur da matan aure akan darajar da kuma martabar dake cikin aure duk da kasancewarta budurwa bame auren ba. Wacce kaddarar auren kuma ta hau kan tane sakamakon addinin da mazajen auren ke ganin kamar ya mata yawa, suna ganin ta yaya ne zasu iya fara fuskantar MALAMA HAFSAT da maganar aure?, wannan dalili yasa kowa ke gudun aurenta don gani suke kamar ta jima da wuce a jinsu, su kansu manyan makamai da Ustazan da zuciyoyinsu suke cike da ƙaunarta tsoron fuskantarta suke, saboda tsananin kwarjininta,Addini da haiba da kamalar da ubangiji ya mata, tana son AURE, tana son ta budi ido wata ran ta ganta a dakin MIJINTA koda na kara ne, sai dai mutane na ganin kamar wasa ne. Sake shafo kanta ummey tayi cike da kwantar mata da hankali kamar kullum cike da hikima ta shiga faɗin. “Ƙaddara ba ta tambayar ra’ayinka… tana aiwatar da hukuncinta ne kawai, duk kuwa gudun da za kayi ta yi to kuwa ƙaddara tana nan tana jiranka ne a inda zaka tsaya. Wani laifin ba naka bane ƙaddara ce ta shirya komai tun kafin a haife ka!, domin ita ƙaddara tana da hanyoyi masu ban tsoro… amma a ƙarshe, tana kai ka mutum inda ya dace ne. Ina son ki dauka cewar ba duk wanda ya zo rayuwarka ne ya zo da gangan ba… wasu ƙaddara ce ta turo su domin su sauya ka har abada, abu guda nake son ki saka a ranki shi ne *WANNAN MA ZAI WUCE!*....” Idanunta taf da ruwan hawaye take gyadama Ummien nata kanta tana sake yarda da duk maganganunta, tabbas ta sani cewar. _Kullum kowanne ɗan Adam yana rayuwa ne a yadda ƙaddara ta zaɓa masa, domin duk nunfashinka guda ɗaya yana sake kusantar dakai ne ga tarin ƙaddarorin dake nan suna jiranka. Shi yasa a koda yaushe ake son ɗan adam ya kasance cikin bautawa ALLAH, ya kuma yi masa biyayya ya yawaita aiyukan alkhairi a rayuwarsa, adda'a da kusanta kai ga ALLAH ne kawai kan sassauta kaifin ƙaddara amma ba iya gudunka ko saurin kane ze fansheka daga cikin kaddarar data zabi rayuwa da kai irin haka ba._ Wata ajiyar zuciya me nauyi ta sauƙe bayan fitar Ummien nata ta sake to feta da adda'a. Zaune ta tashi a tsakiyar gadon tana dafe setin zuciyarta ita kadai ta shiga tambayar kanta da kanta cewar. 'Me yasa nake jin wani abu mai kama da ƙaguwa a raina! amma kuma ban san abin da nake nema ba?, Zuciyata na kuka da sunan da ban iya tuna shi ba… amma na san yana da muhimmanci a cikin rayuwata tun da har ya kasance ina mafarkin sa babu dare babu rana. Na rayu cikin kunci da zamewa abar zargi ga wasu zukatan, yayin da a koda yaushe murmushi na kawai suke gani wanda nake ara na yafama kai na na ƙarfin hali da kuma tawakkali da mika lamura ga ALLAH… amma gashi ayau a cikin jikina ina jin kewar abin da ban ma san ko me ye shi ba' Tsaye ta Mike tana a bayyane tana mai furta. “Mai yasa nake jin wani abu na cin raina kamar akwai wani ɓangare na rayuwata da aka cire?, me yasa nake jin kamar akwai wani wuri da ya kamata in koma amma ban san inda yake ba?.. Ban san me yasa zuciyata ke kiran koma waye ba, amma duk lokacin da nayi mafarkinsa ina jin ƙaguwata na ƙaruwa, me yasa kuma yau nake jin kamar wani abu me kama da rauni na kokarin kama ni a kan ka? Why duk da ban san ka ba. Amma zuciyata tana jin kamar ta daɗe tana jiranka why? A Ina ka makale daka gaza isowa gareni tsayin shekarun nan?....” Sai kuma ta saka tafukan hannayenta biyu tana rufe fuskar ta, saboda ita kanta ji tayi tana jin nauyin kanta, wasu hawayen da suka zubo mata ta sharce tana cewa. “Na tsorata da irin yadda nake buƙatar ka alhali ban san dalilin hakan ba. Akwai wani abu a cikin raina da ke motsi…kamar sirrin da ke neman fita.” Ta sake matse jikinta wuri guda taci gaba da faɗin. “Na fara jin tsoron kaina…saboda zuciyata tana tunanin abin da kwakwalwata ta manta. Me yasa wasu lokutan nake jin kaina kamar akwai wata rayuwar dana taɓa fuskanta a baya?, Nasan kuma hakan shima duk yana cikin jerin Ƙaddarorin dake kirana…amma ban san sunan da take kirana da shi ba...” Ta dafe ƙirjinta da hannuwanta duka biyun…zuciyarta na bugawa da wani irin raɗaɗi mai zafin gaske, ba ta san abin da take nema ba amma sai take jin kamar ta rasa wani abu mai girma ne cikin rayuwarta. Ahankali ta mike ta faɗa toilet babu jimawa ta fito fuskarta ɗauke da damshin ruwa alamar alwala ta dauro, nan ta shiga jera nafilfulun da suka ƙarasa janta tsawon daren. Bayan ta idar ta lumshe Idanunta cikin wani irin ƙira'ar da indai kaji duk rashin imaninka sai zuciyarka ta rusuna ko bata girgiza ba, wani irin sautin laffuzane ke tashi cikin ɗakin wanda ya saka komai nutsuwa a lokacin, wasu zirarayen hawaye na biyo shatin gefen idonta dake rufen. Tana zan zaune har aka ƙira sallar subhi, bayan an idar da sallar ta faɗa toilet a gurguje ta watso ruwa ta sanja kaya ta fito cikin ƙaton himar nata, hannunta ɗauke da jakarta da tarin litattafanta ke ciki. Ɗakin mahaifiyar ta ta fara nufa ta gaida ta kamar babu abinda ya faru, ta san Baffa baya gida don ba lokacin shigowar sa bane, kamar zata wuce sauran matan Baban nata amma kuma zuciyar ba zata iya ba taje ƙofar ɗakin tsakiyarun ta ɗan ɗurkusa daga bakin ƙofar ɗakin tace. “Mama barka da asuba, mun tashi lafiya..” kamar babu kowa a dakin haka aka banzatar da ita kafin kuma daga ƙarshe kamar wacce a fusace aka amsa. “Lafiya...” kawai da wani guntun tsaki. Haɗiye abinda ke taso mata tayi tana nufar ƙofar ɗakin Anty Amarya. Ita din ma dai a fusgen ta amsa da lafiya ɗin yaronta me Halifa daga can uwar ɗakan uwar yana cewa. “Anty Hafsa Don ALLAH gani nan” amma uwar ta katse shi a tsawace tana cewa zata fashe masa baki in bai dena shiga sabgar wannan guzumar da taki auruwa ba. Makut haka taji wucewar wani abu cikin ranta ta mike tsam tana cewa ya sameta Islamiyyar. *IBRAHEEM * Washe gari yana zaune daga gefen gadon yana kallon Yasmine, zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi amma ya hana kansa yin ta. Saboda yana tsoron amsar ƙadan yaja idanunsa a hankali ya rufe yana gaya wa kansa “Komai zai daidaita…” Yana kallon hakan a matsayin hawalar da tasha a daren jiya ne ya saka ta kasa tashi har zuwa yanzun, juz'i amma ɗin dake hannunsa ya koma yana ci gaba da karantawa. Fita yayi babu jimawa ya dawo musu da takeaway ɗin da yayo musu as breakfast. Da kyar ya iya tashinta ya lallamata su kayi, kana ya saka tayi wanka ta sake kwanciya har wajajen sallar zuhr, da zai fita masjid ya data yace tayi Sallah ya fita a gurguje ya barta gudun kada yayi let. Koda ya dawo abinda ya bashi mamaki shi ne yadda ya barta kwancen haka ya dawo ya sameta, don haka ya sake tashinta amma ta farka cike da jin haushin katse mata baccin nata take cewa ita ya kyale ta ba zata yi sallar ba. Duk yadda yaso tashi da fahimtar da ita sallah akan lokacinta kin tashin tayi, haka ya fita ya kyale ta. Yana fita babu jimawa kawayenta na Amana Sofy da Aysha suka shigo, nan suka barar da guntun lokacinsu zaune har bayan sallar asari amma kaf cikinsu abin mamaki babu wanda yayi motsi sema topic da suka sanja zuwa ta tambayarta ya daren ta na jiya ya kasance. Wani murmushi me kyau tayi tana basu labarin yadda ya wahal da ita tana dariya tana komai dake basu labarin duk abinda ya faru tun daga farko har ƙarshe. Wani irin faduwa Ibraheem dake sanyo kansa kenan yayi yana jan burki kuwa babu shiri. Har bayan magrib suna gidan se daf da Isha'a kana suka tafi, bayan sun jidi abinda ransu ke so a gidan. Washe gari ma hakan ce ta sake kasancewa bayan yasha fama da ita kan Isha'a da se da kyar tayi ta da magrib a gabansa, wanda tashin farko a sallar nata ya fahimci akwai manya manyan gyararraki. Amma se ya sake bama hakan uziri da may be ciwon jikinta ne.... Ɗan kallonta yayi lokacin da take fitowa daga bedroom zuwa parlourn da yake zaune yana karatu, ya ɗago idanu kawai ya kalleta tare da furta. “Kin yi latti against.” Ya faɗa cikin nutsuwa yana ci gaba da karatunsa, babu jimawa ya matso zuwa gabanta yace ta masa dori, gaban Yasmine yayi wani irin faɗuwa a ranta tana mai furta. 'Na shiga uku ni Hauwa wanne irin miji na aura haka?' don haka seta shiga matse fuska ta nemi wuri taba kwanciya kamar bata ji shi ba saman sofa, Ahankali ya ajje alqur'ani ɗin yana komawa inda take kwancen ya dago kanta yana ɗorawa saman cinyarsa daya koma sofar ya zauna, cike da murmushi saman fuskarsa yace. “Ohhh na fahimta dake ku manya ne shi yasa ba sai da alqur'ani ba?” 'Innalillah wai me nake shirin fuskanta haka ni Yasmine, nida ko sabbi seda kyar nake rutsa ta ya taso ni gaba da wani maganar dori, Sallah, Wanka akan lokaci ba kyau kwana da najasa na shiga uku na bar duniya!, ni da nake murna nayi auren yanci babu takura babu komai tun da sabon tu ba na aura amma sai gashi tafiyar tun bata kai ko ina ba na fara da fuskantar ƙalubale da barazana..... ' “Babe ka barni nayi bacci kaina ke min ciwo pls” kan ya taɓa yana fara ɗan tofa adda'ar da yake a bayyane data bama Yasmine ɗin mamaki, don ita tana jin a cikin adda'oi dai, basu fi kala biyar ba wanda ta iya, daga Innalillah wa'inna ilaihi raji'un, sai kuwa irin su Subhanallahi Hasbinallahu wani'imal wakeen, Duk dai irin wanda ake tsinta a bakunan jama'a ne suma ɗin ta tsinta, yo ina take zuwa Islamiyyar?, Islamiyyar da idan anga taje wani malamin taso cima mutumci. Ahankali ta sauƙe boyayyar ajiyar zuciyar amsar uzirin nata da yayi, amma kuma wata zuciyar na ce mata, idan yau kin tsere gobe fa, ko zuwa anjima. Ƙululu haka taji cikinta ya bada sautin da har shi seda yaji har yana dafe cikin nata. Wani gumin tashin hankali ya shigo keto mata, don haka wata zuciyar kai tsaye ta bata bad idea akan cewar, fuska zata dena bashi, bare har yayi tunanin kawo mata wargi kuma, da hakan kuwa ta yi na'am tana bama kanta kwarin gwiwwa akan hakan. Sannu a hankali sabbin halayen data fara masa suka fara fitowa fili. Kamar su magana mai ɗauke da rashin ladabi idan ya mata gyaran wani kuskure haka. Daga ya mata zata ta be baki tace. “Ka daina min wannan preaching ɗin, don ni ba irin matan da za ka canza ba ce, in ma banda haka kai yaushe ma ka shiga cikin muslumcin?” Shi kuma kai tsaye yake bata amsa da. “Ba zan canza ki ta karfi ba yas-mine kawai Ina nuna miki hanyar da na ga itace me ɓillewa a gareki.” ita kuma sai tace. “Ka ga dai! Wannan ne matsalar ka! Kana ganin kai ka fi kowa!” Ahankali ya kawo numfashi yana ayyana tabbas anbar tarbiyya da rashin tsarin rayuwar da aka bari a baya. ★ Washegari da safe ma kin Sallah tayi, da yayi mata magana sai ta juya masa baya kafin cike da raini ɗauke a fuskar ta ce. “Again yau ma dai lecture ɗin?” A natse IBRAHEEM ya girgiza mata kansa yana nuna mata kusa da inda yake zaune shima yace. “Zauna.” Ta zauna din kuwa tana huhhura hanci tana kuma harararsa, cike da nutsuwa sosai yace. “Yasmine… ba zan dinga faɗa miki kina dauka ba? And kina ganin wannan rayuwar a hakan zamu ɗore kuwa? Ki sani ita fa rayuwar kanta ba an gina mata ita bane don muyi yadda muka so kawai, ubangiji yana da nashi nufin na bauta masa da cike dokokin da duk ya gindayamana”. Amma maimakon Yasmine ta rusuna sema wani murmushi da tayi tare da cewa. “Ni haka na taso ban san takura ba, shi yasa na taso bama wani cikakken shiri da Mamy saboda exactly yacce ka fara nuna takurarka a kaina haka take min, So ina ganin indai kana son mu zauna lafiya ka dakatar da duk ababuwan da ka fara a kaina na nuna takurawa, Sallah kuma time to time idan naga nayi balance free na kan daure koda biyu zuwa uku ce nayi a rana, ita dai asba inayi dama, na kan yi magrib sabo da sauƙinta, so wani bin ma na kan daure nayi zuhr, Isha'a da la'asari ce ban fiye son yi ba gaskiya....” Ai tun da ta fara maganar Ibraheem yayi wani irin ƙamewa cike da wani shegen tashin hankali yake kallonta, shi da yake tunanin ya sama hasken da zata ci gaba da haskaka rayuwarsa ashe ba tare daya sani ba ita ɗin.... *DUHU NA DUKAN DUHU* Ce a cikin rayuwarsa gaba ɗaya?. A wannan lokacin ne IBRAHEEM ya fara fahimtar abu guda shi ne cewar, ba rayuwar aure mai sauƙi ya shiga ba… kawai ya shiga aikin gyara zuciya ne da kuma rayuwa wanda ba karfi hakan ke buƙata ba illa hakuri, addu’a, da kuma hikima. A wani irin hankali yaja idanunsa yana lumshe su, tare da furta kalmar. “Ya ALLAH!… ka bani hikima kafin in rasa komai a cikin wannan tafiyar ta. *DUHU NA DUKAN DUHU* TSAKANIN NIDA YAS-MINE....” *AMMEY LAYLERH ✍️ * 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 28 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Washegari tun da safe IBRAHEEM ya shiga wani irin yanayi na tunani. Maganganun YASMINE ne kawai ke ta yawo cikin kansa kamar ana maimaita masa su. “Ni haka na taso…ba zan iya wannan takurar ba…” daya tuna maganganun se yaji wani abu me kama da rauni na wani irin kama zuciyarsa sosai. Don haka gaba ɗaya yake a wani irin so silent gaba ɗaya yinin ranar. Koda yaje masallaci shiru kawai yayi bayan idar da salla, hannunsa riƙe da Alƙur’ani amma zuciyarsa cike da wani irin nauyi. Sheikh Albani ne ya shigo ya zauna kusa da shi cikin nutsuwa yana me ambatar sunan shi. “IBRAHEEM…” A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli Sheikh ɗin. “Na lura da gaba ɗaya kwanakin da suka rufa ma na bikin nan naku baya gaba ɗaya hankalinka ba'a kwance yake ba.” Shiru kawai yayi kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya. “Na shiga tsoron abinda ke gaban ne Sheikh…” Cikin hikima Sheikh Albani ya ɗan murmusa yana mai furta “Ka san me yasa ALLAH ya haɗa ka da ita?” Kai ya girgiza alamar a’a. “Shekaru da yawa wata ƙaddara ta jingine maka wani keɓantaccen kadarar da kowa ya gaza mallaka... IBRAHEEM ya gyada kai a hankali don bai da abin cewar daya wuce gyada kai din. “To wataƙila… ita ce jarabawarka ta farkon da zata sadaka da ainihin Hasken da nake hangowa tattare da kai, wani irin sirrin haske ne da ba kowa ne zai iya hangosa ba, amma kaci gaba da godiya ga ALLAH nesanka ce ke shirin matsowa kusa nan ba da jimawa ba..” Sosai maganganun suka ratsa Ibraheem kasamcewar da turanci ne yayi maganar. Kai tsaye daga nan bayan ya dauki karatun ya dawo gida, sedai tun kafin ya gama isowa compound ya soma jin karar kiɗa!, kiɗan da yafi komai tsanarsa kaf duniyar. YASMINE kuwa dake tare da ƙawayenta da kusan kullum suna hanyar gidan ne suke ci gaba da shan music nasu suna dariya har Aysha na ɗan motsawa daga zaunen da take, domin dama can yafi Sofy rashin ji don ita babu inda bata fantamawa. Sai dai a badinin hakan a cikin zuciyar Yasmine wani irin tsoro da rashin nutsuwar dawowar gidan a koda yaushe take, domin a karo na farko a rayuwarta ta haɗu da namijin da baya tsoronta, baya bin son zuciyarta, kuma baya gajiya da jan ta zuwa ga ALLAH. *JIGAWA* A can JIGAWA kuwa JANNEERH ce zaune bayan gama gabatar da tafsir na matan data gama, wanda suke cakuɗe da yara da kuma manyan matasan yan mata da masu aure da take gabatarwa duk Alhamis kasancewar Alhamis ɗin babu karatu. Wata ƙaramar yarinya ce ta matso kusa da ita tana murmushi tace. “Malama… kin taɓa yin waiting ɗin mutum da baki taɓa gani ba?”Tambayar data saka JANNEERH tsayawa cak, zuciyarta tayi wani irin bugawa. Kafin ahankali ta kalli yarinyar cikin muryan da bata gama fita ba tace. “Eh…” Sai ta nunama yarinyar setin ƙirjinta a hankali tace. “Saboda wani lokacin… zuciya tana gane wanda ƙaddara ta rubuta mata tun kafin idanu su taɓa ganinsa…” ★... Wata irin nutsuwa ce ta mamaye harabar gidan MALAM MUHAMMAD ALIYU BAITA bayan dawowar JANNEERH daga tafsirin mata. Kamar kullum cikin kamala da nutsuwa take tafiya, hannunta riƙe da littattafanta yayin da babban hijabinta ke jan ƙasa kaɗan. Duk wanda ya ganta sai ya tsaya ya bita da kallo, ba wai saboda kyau kaɗai ba… A’a. Saboda akwai wani irin natsuwa da kwarjinin dake tattare da ita da ke saka mutum jin kamar yana kallon mutumiyar da ba ta cika shiga cikin hayaniyar duniya ba. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan. “Assalamu alaikum…” Sai dai kamar kullum…shiru ne ya amsa mata daga ɓangaren matan mahaifinta. Mama Rukayya ce ta fara kallonta da wani irin rainin wayo kafin ta ja tsaki ƙasa ƙasa ta amsa da. “Wa alaikis salam…” ta karasa amsawa a yatsine. Mama Bilkisu kuma ta ɗan kalli hijabin JANNEERH tana murmushin gefen baki tare da furta. “ALLAH ya ƙara mana malamai…” ta faɗa tana kallon yar ƴar uwar cin mushenta suka saka dariyar dake cike da ma'ana. JANNEERH ta sunkuyar da kanta kawai kamar bata ji komai ba, amma duk da haka basu kyale taba musamman ma ganin babu wilgin ummieh a wurin, inda tana kokarin wucewa ne Mama Bilkisu ta sake cewa. “To wai ni Rukayya… har yanzu kamar babu wani motsi fa da nake ji haka ne?” Sai suka sake saka dariyar dai kusan tare, kafin Mama Rukayya ta cafe da. “Ko dai aljanune ke tsoratar da mazajen?” cewar Mama Rukayya. Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar JANNEERH, duka kalaman sukan zuciyarta kai tsaye cikin tsakiyar kirjinta, amma duk da haka… ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba. Domin ta saba tun tana yarinya take rayuwa cikin irin wadannan ire iren kalaman. 'Yarinyar nan ta cika tsarki da yawa…' 'Kamar ba mace ba…' 'Wa zai aure ta?' 'Kowa tsoronta yake…' Wadannan kalaman sun zama kamar iska a rayuwarta. Sai dai duk lokacin da aka furta su… zuciyarta na zubar da jini ne a ɓoye. Adda'a tayi A hankali tana ci gaba da tafiya zuwa ɗakin Ummien ta. Tana isa ga mahaifiyar nata taji kamar wanda aka cirewa nauyi a kirjinsa haka ta sauƙe ajiyar zuciya. Ummie na zaune kan sallaya tana Jan carbi. Tun daga kallon farko ta fahimci wani abu ya sake faruwa ke nan, duk da dai da ababuwan matan uban nata yayi sauƙi yanzu ne suka dawo dashi sabo tsakankanin ƴan satikan nan. “Hafsat…” Mahaifiyar nata ta kira sunanta cikin taushin murya. JANNEERH ta zauna kusa da ita tana kokarin ɓoye damuwarta ta amsa da. “Na’am Ummie…” Sai dai tun daga yanayin yadda maganar ke rawa ummien ta fahimci wani abu. Murmushi Ummien tayi tana shafa gefen fuskar ta tare da cewa. “Sun sake magana ko?” Idanun JANNEERH ne suka cika da hawaye nan take, kafin ta girgiza kai da sauri tana mai bata amsa da. “A’a Ummie…” Sai dai muryarta ta tona ta a wannan karon ɗin ma, don haka Ummien ta ja ta jikinta a hankali kamar ƙaramar yarinya ba ƴar shekaru ɗai ɗai har ashirin da bakwai bace gabanta. “Ki dena ɓoye wa zuciyarki ciwo Hafsat…” Ta faɗi wanda ya saka hawayen JANNEERH suka zubo da take ta kokarin makalewa. “Ummie… shin ni akwai wata matsala a tare dani ne ban sani ba?” Tambayar ta fito da wata irin rawar murya. Kafin cikin rawar murya ta ɗora da cewa. “Me yasa duk inda na shiga sai a dinga kallona kamar ni ba cikakkiyar mace ba ce saboda ban yi aure ba, ko ina da wani nakasu ko tawayar halittar da ni bana iya ganewa kai na Umm?” Wani irin runtse ido na ɗan lokaci ummien tayi saboda tausayin yar tata. Cikin nutsuwa tace. “Ki saurare ni da kyau Hafsat…” Ta ɗago fuskarta ta share mata hawaye. “Ba kowanne jinkiri bane rashin dacewa.” tayi maganar tana kamo hannuwanta cikin nata taci gaba da fadin. “Wani lokacin ALLAH yana ɓoye maka alkhairi ne har sai lokacin da zuciyarka zata iya ɗaukarsa.” se ta ɗan fesar da wani numfashin azaba bawai don bata jin ciwon hakan ba, amma haka ta ci gaba da mata magana cikin hikima. “Kin san me yasa mutane suke magana?” Kanta jannerh ta girgiza mata alamar A ahhh. “Saboda basu san me ALLAH ya tanadar miki gaba ba.” Sai ta ɗan murmusa kaɗan kafin ta ɗora da cewa. “Mutane suna ganin wanda yayi saurin aure shine mai dace…” ta sake fesar da wani numfashin me cike da bacin rai. “To wa yace haka?” Kafin a wani irin hankali ta ɗaga haɓarta jannerh ɗin kaɗan tana kallon cikin idanuwanta da suke cike da rauni tace. “Wasu auren nasu jarabawa ne. Wasu kuma jinkirin nasu rahama ne.” Kalmar ta shiga zuciyar JANNEERH sosai, sai dai har yanzu tana jin wani irin ciwo a kasan ranta. Cikin sanyin murya tace. “Amma Ummie… ni ma ina son a SONI !, INA SON naji wani yace yana SONA ...” Murya ta karye amma haka taci ga da faɗin “Ina son na kasance a ɗakin MIJINA nima…Ina son wani ya kalle ni nima kamar sauran mata ya ce ni ce natsuwarsa…” Wani irin tausayinta ne ya sake kame zuciyar Mahaifiyar nata. Ta rungumeta sosai tana shafa bayan ta cike da bata kwarin gwiwa tace. “Kuma zai zo IN SHA ALLAHU HAFSAT…” ta lumshe idon ta tana ɗauke kwallar data cika idon ta tace. “Na rantse miki da ALLAH zai zo. Saboda mutumin da zai zo cikin rayuwarki ba zai zo saboda kyanki ba ne, ba kuma zai zo saboda sunanki ba ne… Zai zo ne saboda ƙaddara ta gama rubuta sunanki cikin zuciyarsa tun kafin ku haɗu…” A lokaci guda wani irin bugawar zuciya JANNEERH taji. Kamar akwai wani abu da ke kokarin tasowa daga cikin kirjinta, wani suna, wata fuska… amma duk ta kasa gani. Sai kawai ta dafe ƙirjinta da sauri har Ummie ta kalleta da damuwa. “Hafsat?” A hankali JANNEERH ta lumshe idanunta. Sannan ta furta cikin muryar da bata gama fita sosai ba tace. “Ummie…Kullum zuciyata na jin kamar akwai wani mutum da yake kirana…” Ta ɗago idanunta masu cike da ruɗani ta ɗora ta faɗi “Amma ban san ko waye shi ba…” *AMMEY LAYLERH ✍️ * 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 29 Paid book 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Wani irin kallo Ummie ta tsaya yiwa JANNEERH ɗin…Kallo mai cike da zurfin tunani da kuma wani irin tsoro na uwa. Domin ba wannan ne karo na farko da Hafsat ke furta irin waɗannan kalaman ba.Tun shekarunta na ƙuruciya akwai wasu mafarkai da take yawan yin su. Mafarkai masu cike da duhu… hawaye… da wani mutumin da bata iya ganin fuskarsa gaba ɗaya, sabo da yana a cikin tsakiyar wani irin DUHU ne da ko tafin hannu ba'a iya gani. Sai dai duk lokacin da zata farka zuciyarta cike take da wani irin raɗaɗin kewa. Kewar da take jin kamar ta rasa wani ɓangare na rayuwarta ne. Ummie ta ɗan shafa kanta cikin lallashi kafin tace. “Ki dena tsoratar da zuciyarki da tunanin da baki da tabbacin sa Hafsat…” ta sake janyo ta jikinta kamar yar shekara biyu. “Wasu lokutan zuciya tana jin abubuwan da basu faru ba tukuna…” JANNEERH ta sauke ajiyar zuciya. “To amma Ummie…” Ta ɗago idanunta masu cike da ruɗani. “Me yasa duk lokacin da nake yin addu’a…sai naji kamar ina roƙon ALLAH ya kare min wani mutum ne daban?” Nan take Ummien ta tsaya cak, ƙirjinta yayi wani irin bugawa sai dai ta ɓoye komai a fuskar ta, sai ma cikin natsuwar data bata amsa. “Saboda wataƙila ƙaddararki tana gabatowa ne....” Kalmar ta sake jefa JANNEERH cikin wani irin yanayin daya sakata lumshe idanunta tana jin wani sanyi da zafi a lokaci guda. A Can waje kuwa… Mama Rukayya da Mama Bilkisu dake zaune suna ci gaba da gyaran zogalensu ne Mama Bilkisu wato Anty Amarya ce ta taɓe baki tace. “Ni wallahi yarinyar nan tana bani tsoro ma.” Mama Rukayya data kalle ta tare da gyara zamanta tana sake tattare bakin zaninta tace. “Tsoro kuma?” Ta matso kusa da ita tana rage murya sosai tace. “Kinga yadda MALAM yake ɗaukakarta kamar wata waliyyiya?” Tsaki ɗayar tayi tana furta, “To ba dole ya ji da ita ba, kar fa ki manta itace mikullin arzikinsa” cike da isgilanci suka saka dariya Mama Bilkisu tace. “Ni dai har yanzu ban yarda babu wani abu a tattare da ita ba. In banda haka wacce irin budurwa ce shekaru suna tafiya amma babu namijin da ya isa ya tsaya a gabanta?” “Kin manta da ɗan Alhaji Bashir ne?” Mama Bilkisu ce ta ɗan rage murya sosai tace. “Ehhhh fa to shi ma daga karshe ai cewa yayi ba ita Hafsa ɗin yake nufi ba, Hafsan gidan Uba tela yake nufi” “Yo in ma dai ita ɗin ce ai gashinan maganar gaba ɗaya ta mutu, tun da har yau babu wanda yace yasan abinda ya faru bayan hakan...” Wani irin shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Kafin Mama Rukayya ta ce. “Ni dai bana son yarinyar nan. Saboda yadda take kallon mutum da idanunta kamar tana karanta zuciyarsa… nifa wani sa'in wallahi haka kawai sai naji jikina yayi sanyi ma...” A dai-dai lokacin ne kuma JANNEERH ke fitowa daga ɗakin Ummie ɗauke da hijabinta da littafi a hannunta zata nufi bedroom guda da Baffanta ya ware mata ita ka dai. Da sallama cike da girmamawa ta sake wuce su amma kamar kullum… ba wanda ya amsa mata da kyau. Har ta kai bakin ƙofar bedroom nata kamar abin kirki Aunty Amarya ta kira sunanta. “Hafsat…” Ta tsaya cikin nutsuwa tana amsawa da. “Na’am Anty…” Mama Bilkisu ta kalleta sama da ƙasa kafin ta mele baki tace. “Yaushe zaki daina fakewa da karatu da wa’azi ne wai don ALLAH ki nemi mijin aure ne?” Wani irin shiru tayi tamkar wanda ruwan sama ya cinye kafin ta sauke idanunta ƙasa cikin ladabi tace. “ALLAH ne mafi sanin lokacin komai Mama…” Mama Rukayya ce ta bushe da dariya tare da amshewa da cewa. “To ai idan kika ci gaba da jiran irin haka kina fakewa da ALLAH ne bai kawo ba zakici gama da zama haka har tsufa.” Kalmar ta shiga zuciyar JANNEERH kamar an caka mata allura sai dai ta haɗiye komai. Domin tasan idan ta tsaya kare kanta…Rashin kunya ne don a hankali tace. “ALLAH ya kyauta…” har ta juya zata wuce amma muryan Mama Rukayya ta sake katse mata lissafi. “Ko kuma dai akwai wanda zuciyarki take jira ne?” Cak haka jannerh ta tsaya ba tare da ta shirya ba… zuciyarta tayi wani irin bugawa don ji tayi kamar an ambaci wani abu da take ɓoyewa daga kanta ita kanta. Sai dai kafin ta iya magana… Ummie ta fito daga ɗaki. Idanunta cike da izza da hikima ta kalli matan gidan nan take suka yi tif tace. “Ku dena ɗora wa yarinya nauyin da ALLAH bai ɗora mata ba.” Mama Bilkisu da take Amarya ce ta taɓe baki tana cewa “Mun dai faɗi gaskiya ne kawai.” Ummie ta gyara tsayuwarta tana jefa mata wani kallo tace. “Gaskiya? Shin wai yaushe rashin aure ya zama aibi ga mace a ƙasar Nigeria ne?” aikuwa suka yi tif kamar ruwa ya cinye kana cikin nutsuwa ta ɗora da fadin. “Idan aure ne ma’aunin darajar mace…to da matan Annabawa basu fi sauran mata daraja ba.” Wani shirun suka sake yi don kaf cikinsu kowa shakkarta yake, Ummie ta kamo hannun JANNEERH tace. “Ku bar Hafsat da ƙaddararta.” Sai ta kalli yar tata cike da nutsuwa da jin kwarin gwiwwar tabbas MIJINTA seya kasance na daban ɗin da sai duniya tayi alfari da wannan auren bama iyaka matan gidan ba, don haka cike da jin cikakken yakini tace. “Domin duk ranar da ALLAH zai buɗe mata ƙofa tabbas kowa sai ya san cewa jinkiri ba yana nufin rashin dacewa bane.” fuuuuu haka taja hannun ƴar suka wuce. ★KABUGA JAN BULO★ Wani irin shiru ne ya mamaye parlourn gidan gaba ɗaya, sai ƙarar pages ɗin Alƙur’anin dake hannun IBRAHEEM da yake juyawa a hankali. YASMINE kuwa kwance take saman kujera tana scrolling wayarta hankali kwance kamar babu wata damuwa a rayuwarta. Tun bayan maganar jiya… IBRAHEEM ya shiga wani irin yanayi na zurfin tunani, bawai saboda ya tsani YASMINE ba…A’ahhh har yanzu yana sonta sai dai a karon farko ya fara fahimtar cewar soyayya ita kaɗai ba ta wadatar da aure. Mutum biyu na iya son junansu amma zuciyoyinsu su kasance a duniyoyi daban kamar yadda ya kasance a gare su. A hankali ya ɗago idanunsa daga karatun da yake yi ya kalleta. “YAS-MINE…” Ta amsa ba tare da ta ɗago ba da. “Hmmm?” wani ɗan murmushi kawai yayi kafin yace “Zan iya tambayarki abu ɗaya?” guntun tsuki tayi tace. “Kamar ya ya?” “Kin taɓa jin tsoron ALLAH kuwa bare kuma kiyi tunanin haduwarsa dake?” Cike da fusata ta mike tsaye tana me furta. “Wai me yasa duk wata magana taka sai ta koma addini ne?” Cikin natsuwa yace “Saboda rayuwata gaba ɗaya addini ne.” Kallonsa take tana wani jijjiga kai kamar ƙadan garuwa kafin tace. “To ni kuma rayuwata ba haka take ba.” Kalmar ta tsaya masa a zuciya sai dai bai fusata ba. Sai ma a hankali ya rufe Alƙur’anin hannunsa yana kallonta sosai yace. “Kin san me yake bani tsoro dan gane dake Yasmine?” gira ɗaya ta da ge masa alamar really?. Kansa ya jinjina mata yana me furta. “Ba rashin sallarki ba ne, ba kuma halayenki ba…Abin da yake bani tsoro shi ne yadda baki jin akwai matsala a cikin abin da kike aikatawar.”YASMINE ta ɗan ƙame karo na farko maganar tasa ta shiga zuciyarta kaɗan. Amma son zuciya ya hana ta nuna hakan, cikin rashin damuwa tace. “Ni dai don ALLAH ka barni na huta haka nan…” ta juya zata shiga bedroom nata, amma muryarsa ta sake dakatar da ita. “YASMINE.” ya sake ƙiran sunanta, ta tsaya ba tare da ta juyo ba. A hankali yace. “Na rantse da ALLAH idan har baki gyara tsakaninki da UBANGIJINKI BA, wata rana zaki shiga cikin duhun da babu fitarsa.” Kalmar ta sata jin wani irin faɗuwa a zuciya ta danne komai ta shige ɗaki tana buga ƙofar. IBRAHEEM ya lumshe idanunsa yana sauƙe wata irin ajiyar zuciya mai zafi tare da ambatar “Ya ALLAH…” cikin sanyin murya da kuma tausasa kalamai ya ce. “Ka taimakeni akan abin da zuciyata ta kasa gyarawa…” ★ *AUJARA JIGAWA* Ahankali guntun yayyafin da aka gama tsala ruwa ke sauƙa saman kwanukan gidajen bayan ALLAH. JANNEERH zaune take kan sallayarta bayan idar da nafila Idanunta a rufe hannunta kuma riƙe da carbi. Gaba daya yau ɗin jin zuciyarta take ba cikin nutsuwar data saba samu ba ce. A kuma karo na farkon data kasa fahimtar dalilin bugawar zuciyar nata, Wanda take jin kamar akwai wani muhimmin abun dake kokarin gabatowa cikin tata rayuwar ne. Wani abu mai nauyi, wani abu da zai sauya mata komai. A hankali ta buɗe idanunta wanda taji hawaye sun gangaro mata, kirjinta ta dafe tana mai furta. “Ya ALLAH!!!...Meye wannan da zuciyata ke ji ne?…ji nake kamar akwai wani baƙin ciki da yake nemar hanya zuwa gareni…” Sai kuma tayi saurin girgiza kanta kamar wata karamar yarinya tace. “Ko kuma…wani mutumin da ban san shi ba?” Nan take ta tuna da mafarkin da ta yi jiya. Wani namiji cikin duhu fuskarsa bata fito sosai ba amma zuciyarta na kuka saboda shi. Da sauri ta mike tsaye kamar mai gudun tunani. Ta ɗauki Alƙur’aninta tana son ta karanta domin ta samu nutsuwa, ta buɗe idanu a hankali ta kalli rubutun Alƙur’anin, ta fara karantawa amma ba ta kai ko aya uku ba sai ta dakata. Ta sauke Alƙur’anin a gefe ta dafe kanta ta sauƙe numfashi mai nauyi, tana mikewa ta fara zagaya ɗakin. Daga yanda take zagaye dakin ko bata budi baki tace maka komai ba zaka fahimci cewa akwai abinda ke damunta, amma ita kanta ba ta iya fassara abinda take ji ɗin ba. A natse ta kalli window ɗin ɗakinta da iska ke motsa labule. Hannayenta ta zira ta cikin window ɗin ta ɗora kanta saman ƙarfen windown, ta jima jingine a haka kafin ta juya ta koma ta zauna a kan gadon. Alƙur’aninta ta sake buɗewa ta fara karantawa cikin nutsuwa, wannan karon kam ta yi ƙoƙari sosai ta ci gaba, har ta kai wani lokaci tana karantawa ba tare da tsayawa ba. Amma duk da haka zuciyarta bata mata sanyin da take son mata ba, maganganun su Mama Bilkisu ne kawai ke famar mata amsa kuwwa. Alqur'anin ta ajje a gefen gado. Ta zauna shiru na ɗan lokaci, kawai tayi shirun dake dauke da wata damuwa boyayya a fuskarta. A natse ta miƙe ta isa gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta na ɗan lokaci. Tana son ganin ta inda take da wata tawaya ko aibu, saidai kuma babu wani abu da ya bambanta a fuskarta, amma ita tana jin kamar wani abu ya canza a cikin zuciyarta. Ahankali ta janye idanu daga kan madubin ta koma gefen gadon tana sake zama tana tunanin rayuwar gidansu. Rayuwar gidansu data kasance wata irin rayuwa ce mai cike da san zuciya, sabanin shekarun baya da gidan yake cike da wata irin tsafta da girmama juna. Saboda tsarin zaman gidan abun burgewa ne ga kowa,har dama mutanen anguwa lokacin da Unmeinta ke tare da Uwar gidan Baffan nasu Mama Sakina. Mace me hakuri, kara kawaici, a lokacin tana babbar yarta mace Sadiya, se kuma namijin dake bi mata Salisu. Sedai zaman nasu be wani ci nisan wuta ba ALLAH ya amshi ran Mama sakina, Bayan rasuwarta ne Baffan ya sake auro Mama Rukayya kafin Aunty Amarya. Amma banda yanzun da zaman gidan yake kusan a hargitse, wanda ɗan wannan wancan be isa hukunta wa ba, ga shegiyar hassada da munafuncin tsiya komai na tsegumine. Su kuwa a da tun daga kan yanayin soyayya kulawar da suke gwadawa juna idan ka shiga gidan baka isa cewa kishiya da kishiya bane, ga yaran nasu suma kowa na kaunar kowa babu kawo munafuncin uwar wane ta dake ni,duk lokacin bata da wani cikakken wayo sai Yayarta Aunty Binta. Su kuma matan gidan nasu na yanzu abinda ya sake sakasu tsana da jin haushin ummien saboda kawai Mijin nasu karara yafi son ta akan akansu, kodan kasancewarta gwana wajen tsaftar jiki da kuma ta gida da yaranta, bata yarda da daukar kowanne irin wargi daga sauran matan. Amma kuma tana hakuri sosai akan yaranta, bata fiye magana akan su ba, dama kuma yaran nata uku ne kawai, daga Aunty Binta sai Yaya Jafar, sai kuma ita da take auta, duk da bayan ita tayi haihu amma dan ma be zo da rai ba. Wannan abu shi ya saka bakar kiyayya a tsakanin matan nasu har suka hade mata kai se dai bata damu babu ruwanta rayuwarta kawai take yi, tun tana da tabbacin Mijinta na so da ƙaunarta. Ahankali ta kawo gauruwar ajiyan zuciya tana saukewa lokacin da karar wayarta ke katse mata lissafi, ganin sunan Aunty Binta ne ya saka fuskarta faɗaɗa da murmushi me kyau, mayar da kiran da har ya riga ya katse tayi, kai tsaye Aunty Binta ɗin ta taryeta da cewan... "Me kike yi ne haka da tun dazun nake ta kiranki ina son ki hada ni da ummieh amma baki amsa ba?...” Bata iya karya ba, ba kuma ta iya launa zance don kare kai ba, don haka kai tsaye tace. “Na ɗan tafi wani tunani ne Aunty narh ta kai na....” “Hmmmm!, wato dai ba zaki dena cusama ranki tunanin ban za ba ko HAFSAT?” Ɗan murmushi kawai tayi tana katse maganar da bara in mika mata wayar, daga haka ta yanke don ta san korafin yayar nata ba karewa zai ba inta fara zubo shi. A tsakar gida ta ganta tana ɗurin humrorin da take hadawa da kanta har dasu turaren wuta ne, Kabbasa ce, madarar turaren zalla duk dai wani abu daya danganci kayan ƙamshi babu abinda bata sayarwa. Tana amsar wayar Aunty Binta din ta ɗora da fadin. “Haba Ummie wai me yasa wani lokacin Hafsa ta fiye taurin kai ne uymmm?, ba zaki saka ta dena banza yen tunannika akan wasu can mutanen da ba gama sanin kansu su kayi ba bare kuma ubangijinsu” “To Sarkin korafin kin gama ko kuma da saura?, dama shi ne maganar da kika kira ki gaya min?” Ɗan rusunar da murya tayi tana kuma gaida ta cike da girmamawa tana cewa tayi hakuri dama wata makwafciyar tace Maman Meemah take son hadin humra na dubu talatin. Ɗakinta ta shige da wayar ita kuma Hafsa ta zauna tana ci gaba da duddura humra ɗin, ummien na gama shige wa ɗakin nata Su mama Rukayya suka wani ja tsaki ƙasa ƙasa suna furta aikin banza. Kallo basu ishi Hafsa ba taci gaba da zuba Humrarta, babu jimawa ma sai ga ummien ta fito ta amshi zuba humra ɗin don lokacin zuwan ta Islamiyya yana daf. *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 *AMMEY LAYLERH ✍️ * 08104493215 *◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐* _Royalty versus love_ ~Maryam Naseer Mirrah~ *AMMEY LAYLERH ✍️* Page 30 Last free page's 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. ♡ Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215 *Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ* ♡♡♡♡ ꨄ Wani irin shiru ne ya mamaye parlourn gidan gaba ɗaya… Shirun da idan mutum ya zauna a ciki na ɗan lokaci zai fara jin kamar zuciyarsa na nutsewa cikin wani irin duhu ne. IBRAHEEM zaune yake saman dardumar parlourn. Alƙur’ani a buɗe gabansa… amma yau karatun ma baya shiga zuciyarsa kamar da, tun bayan maganar da yayi da Yasmine, wani irin tsoro ne ya shiga ratsa shi, tsoron makomar rayuwarsa, tsoron auren da yake rushewa a hankali… alhalin har yanzu zuciyarsa na son matar nan. A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli bedroom ɗinta babu motsinta. Babu dariyarta, babu sautin wayarta. Sai dai duk da hakan jin zuciyarsa yake bata samun nutsuwa. A hankali ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya mai zafi.“Ya ALLAH…” “Ka nuna min gaskiya ko da zata karya zuciyata ne…” ya furta a bayyane yana kwantar da kansa jikin kujerar. ★ A Can cikin bedroom kuwa Yasmine ce zaune gaban mirror tana share tears ɗin mascara ɗin data ɓata. Fuskar nan tata cike take taf da takaici da wani irin ɓacin rai. “Wai duk saboda addini…” Saboda addini mutum zai dinga takura rayuwarsa haka?” Ta furta tana ɗan cije lips ɗinta sai kuma ta tuna yadda ya kalleta ɗazun. Wani irin kallo mai cike da tausayi amma kuma mai karya zuciya ne, kallo irin wanda mutum yake yiwa wanda yake son cetowa daga hallaka. Da sauri ta girgiza kanta tana mai furta. “No! I can’t live this kind of life…” Ta furta da turanci cikin rawar murya. Sai dai duk yadda take son ƙaryata zuciyar ta amma maganar IBRAHEEM taƙi fita a ranta. “Wata rana zaki shiga cikin duhun da babu fitarsa…” Ibraheem har lokacin yana zaune saman sofa yaji ƙarar horn ta tsaya a harabar gidan. Don haka ya ɗago kansa a hankali tare da yunkurawa ya leka, gabansa ne ya faɗi saboda ganin motar PAPA ɗinsa. Da sauri ya mike tsaye daidai da lokacin da ƙofar parlourn ɗin ke buɗe.Papa ne sai Mom daga bayansa wacce duk ta fice hayyacinta. Wacce kai tsaye Idanunta suka sauka akan IBRAHEEM. Nan take hawaye wasu ruwan hawaye suka cika cikin idanun nata tana mai ambatar. “Oh my Jesus help… John…” Kalmar ta fito daga bakinta kai tsaye wanda take fuskar Ibraheem ta sauya sai dai bai ce komai ba. PAPA ne ya ƙaraso kusa da shi yana kallonsa sama da ƙasa. “You look tired…” Ibraheem ya sauke idanunsa ƙasa cike da wata irin girmamawa irin ta iyaye yace. “I’m fine Papa.” “Fine?” Papa ya ɗan bushe da dariya mai ciwo yana nanata kalmar. “You abandoned everything for this life… and now look at you.” Shiru kawai Ibraheem yayi Mommah kuma na matsowa kusa da shi tana riƙe hannunsa, cikin rawar murya take furta kalmar. “John… please come back home.” Da sauri ya ɗago idanunsa da suka surka da wani abu me karfi ya ɗan ja baya yana dan girgiza kansa, kafin ya ce. “Mother.... My name is Ibraheem! Ibrahimul khaleel” Wani shiru ne ya ratsa wajen Mommah ta wani lumshe idanunta cikin rauni tana mai furta. “I know…But you’re still my son.” Nan take zuciyarsa tayi wani irin bugawa. PAPA kuwa juyawa yayi yana kallon parlourn ɗin gaba ɗaya. Simple, ba wata rayuwar alfarma, ba wata rayuwar da ya taso a cikinta ba ta asalin jin dadi da hutu, babu aikinsa da ada din yafi ƙauna sama da komai. Ahankali ya dawo da kallon sa kan ɗan nasa cikin son ya kure shi yace. “Is this really the life you want?” A hankali Ibraheem gyada kansa yana amsawa da. “Yes Papa! Even with the pain?” Shiru Papan yayi kafin ya matso kusa da shi sosai yace cikin sanyi kuma wannan karonm “Come back to the mansion Ibrahim.” Numfashin Ibraheem ya tsaya. PAPA ya ɗora da magana cikin nutsuwa. “You can still be a Muslim. You can pray!, You can worship your God.” Sai ya ɗan dakata kafin yaci da maganar.“But stop destroying yourself over people who don’t even understand you.” kalaman da Ibraheem kamar suna shiga zuciyarsa sai dai bai ji zai amince musu. Mommah ce ta matso tana riƙe fuskarsa cikin tausayi ta ce. “We miss you… The house is empty without you.” Wani irin zafi ne yaji ya taso masa daga ƙasan zuciyarsa, saboda duk yadda yake ƙoƙarin mantawa har yanzu akwai wani ɓangare nasa da ke kewar rayuwarsa ta baya. Rayuwar JOHN…Rayuwar ɗan gata… ɗan mension… ɗan da duniya ke kallon sa da tarin arziki da iko. Sai dai yanzu shi ne IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL... Wanda a yanzun shi ne wani mutum na daban ɗin da yake neman nutsuwar addini… amma rayuwarsa na ƙara shiga cikin wani irin duhu. PAPA ne ya ɗan katse sa daga ƴar doguwar tunanin daya faɗa. “Think about it son…” Sai ya juya zai fita daga haka Madame Victoria na take masa baya cike da wani irin rashin kwarin zuciya dana jiki. Har ya taka zai fita sai kuma ya dakata ba tare da ya juyo ba yace. “And one more thing…” Wanda ya saka Ibraheem ɗago kansa, Papan ya kallesa kafin yace cikin murya mai nauyi. “Never destroy your soul trying to save someone who doesn’t want to be saved.” Kalmar… wannan kalmar ta bugi zuciyar Ibraheem kai tsaye.Saboda Abu na farkon da zuciyarsa ta fara hasko masa shi ne fuskar Yasmine. Idon sa a kansu har suka ɓacema ganin sa gaba ɗaya. ★ JANNEERH Zaune take a Islamiyya bayan an tashi karatu amma ita ta kasa tashi, Alƙur’ani ne riƙe a hannunta amma yau ko haruffan ma basa shiga cikin zuciyar ta yadda ya kamata. Tun jiya zuciyarta take wani irin bugawa wanda take jin kamar akwai wani abu mai nauyin dake tinkaro rayuwarta, sai dai bata san ko menene ba, ta kuma rasa miye ainihin abinda take ji ɗin. A hankali wasu matan aure biyun dake gefenta daga ɗan nesa kaɗan suka fara magana ƙasa-ƙasa suna kallonta, ba yadda zata gane ko ta ji ba wata daga cikinsu tace. “Waccan ce ko?” Da sauri ta gefen nata ta gyada kai tana cewa. “Eh ita ce mana…” Ɗan tsaki ɗayar tayi tana cewa. “To ni wallahi bana ganin akwai namijin da zai iya zaman aure da ita indai waccan guzumar matar ce.” “Why?” Ɗayar ta tambaye, wani dan mele baki wacce da ganin ta dama bata sauki tayi, tana cewa. “To ke Halimah in banda abunki dubi yacce kullum take cikin hijabi da karatu da wa’azi, alhalin mazan yanzun sam ba haka suke bukata daga mace ba, a wannan rayuwar da muke ciki mazanmu na aure sun fi bukata da son mace mai ɗan budaddan ido, ba wacce zata zame musu sumbum buƙumin ba....” wata uwar dariya suka saka wanda take duk kalaman nasu suka shiga kunnen JANNEERH. Sai dai ta sunkuyar da kanta kawai ne kafin ta sake jin sun kuma bushewa da dariya. “To ni ma dai hakan na gani Naja don naji ance har yanzu babu wanda ya taɓa cewa yana son ta koda kare ne.” “Hmmm Maybe akwai wata matsala a tare da ita ne Halimah…” Zuciyar Jannerh ce taji ta sake kamuwa da wani irin rauni sosai, da tsananin tausayin kanta da kanta, amma duk da haka taƙi ɗago kai, saboda tasan wasu kalaman idan mutum ya tsaya kare kansa a kansu… zai rasa darajarsa ne kawai. To don me zata wani damu kanta ma akan kamalan da kullum suke zame mata kamar tuni ne a cikin rayuwarta, amma kuma duk sanda zata ji ɗin tana jin suna mata wani irin ciwo ne kamar bata taɓa jin nauyin kalaman ba sai yau ɗin. Sai dai yau a karo na farko yasa ta fara jin kamar ita ɗin daban ce da sauran mata, kamar akwai wani abu tare da ita da duniya bata fahimta ba. A hankali ta mike tsaye zata wuce amma wata ta sake faɗar wata maganar da ya saka ƙafafunta suka tsaya cak kafin su soma wata irin rawar dari, wasu ruwan hawaye na kokarin ɓallo mata amma tana hana hakan ta komar da abinta tana shanyewa kamar kullum, kamar ko da yaushe. Sabo da maganar Ummienta data tuna. “Jinkiri ba yana nufin rashin dacewa bane…haka zalika a duk inda kika tsinta kanki to kuwa ki kasance mai toshe kunnuwanki, daga kalaman da zasu ringa shiga marasa tsarki da ma'anar ji” A hankali ta lumshe idanunta kafin ta buɗe ta sauƙe a kansu, karon farko cikin rauninta zata taɓa mayar da martani akan ƙaddara da mutane ke kushe mata. Ga wani irin hasken da ya bayyana cikin idanunta. Haske mai cike da ƙaddara ta dasu. “Wasu zukatan…ALLAH baya haɗasu da kowa ne sai wanda zai gane darajarsu…” Daga haka ta juya ta fice zuciyarta na wani irin kuka mai zafi amma ta ciki wanda ido basa iya ganinsa. Kuka irin wanda ke gab da buɗe ƙofar wata ƙaddara mai girgiza rayuwa… Ibrahimul khaleel.... Jingine yake daga jikin gadon su daga kasa, fitilar wajen kaɗai ce ke bada haske mai rauni na dum light. Gaba ɗaya tun bayan tafiyar PAPA da MOMMAH zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa. Maganganunsu ne kawai ke masa yawo cikin kansa kamar ana maimaita masa su ne. 'Come back home…The house is empty without you…!, Never destroy your soul trying to save someone who doesn’t want to be saved…” Da sauri ya dafe kansa yana runtse idanunsa a bayyane yana mai furta Kalmar. “Ya ALLAH…” Ya furta cikin murya mai rauni kafin ya ɗora da faɗin. “Kada ka mayar dani baya bayan ka nuna min haske…” Sai yaji wasu hawaye masu zafi sun cika idanunsa, saboda a yau ya fara fahimtar cewa shiriya tana da tsada. Inda wani lokacin sai mutum ya rasa mutane ya rasa farin cikin sa ya kuma rasa komai ciki harda rayuwar da ya saba kafin ya samu ALLAH. A hankali ya ɗago idanunsa zuwa sama tare da hannayensa ya furta. “Ko duniya gaba ɗaya zata guje ni… ba zan koma rayuwar JOHN dana bari ba.” Kalmar ta fito daga bakinsa cikin yakini muryarsa na rawa. Duk wannan abin da yake Yasmine na kwance ruf da ciki tana kallon hotunanta a waya. Tun daga kama kan Party… club… da duk inda taga damar zuwa. Sai ta tuna yadda Ibraheem yake kallonta idan tana aikata wani abu mara kyau. Wani irin kallo mai cike da ciwo ba tsana ba…sai dai kamar mutum ne da yake ganin wanda yake so yana nutsewa a hankali. Ɗan tsaki tayi ta ajiye wayar kasa kasa take cewa. “Why is he making me feel guilty for being myself?” *AUJARA JIGAWA* Ƙofar Fada Babban Masallacin juma'a. Mama Rukayya ce ke ta faman mita saboda ruwan famfo ya ɗauke, ita kuma Aunty Amarya na nata surutun ne akan tsadar kayan miya. JANNEERH tun bayan maganganun nan na jiya ta kasa samun sukuni, suna kawai ke mata yawo a rai. 'Maybe akwai matsala a tare da ita Idan mace ta kai shekarunta babu aure akwai magana…' Ta runtse idanunta da ƙarfi karo na farkon da taji kalaman mutane sun fara karya wani ɓangare nata. A hankali ta fito tsakar gidan ɗauke da bokitin ruwa zata wanke manyan hijjabanta a tsakar gidan. Ammma muryan mahaifinta ta katse mata tunani ta hanyar ambatar sunanta da yayi. “HAFSAT…” Da sauri ta juyo haka nan gabanta YA ɗan faɗi. mai cike da nutsuwa da kwarjini fuskarsa cike da hasken ibada… amma idanunsa ɗauke da wani irin zurfin tunani saurin sunkuyar da kanta tayi tana furta. “Ina kwana Baffa…” A hankali ya amsa yana kallonta sosai. “Lafiya kalau… Ina son ganinki idan kin gama abinda kike... " A take Mama Rukayya da Aunty Amarya suka kalli juna. Saboda BAFFA ba kasafai yake kiran Hafsat shi kaɗai ba. A bayan gidan ƙarƙashin bishiyar mangwaro ta same shi, Iskar safiyar ranar na ɗan kaɗa hijabinta kaɗan. Ita kuwa kanta a ƙasa cikin girmamawa ta zauna tana saɓunta gaisuwar nasu, amsata yayi kafin ya ɗan dubeta na wani lokaci yana kallonta, yana karanto irin damuwar dake shimfide saman fuskarta. Kallo yake mata, kallo irin na uba mai cike da fahimta. Kafin daga ƙarshe ya sauke numfashi a ɓoye kana yace. “Kin san me yasa nake yawan kallonki da tausayawa Hafsat?” A hankali ta girgiza masa kai alamar A Ahh, kafin a bayyanen tace. “A’ah Baffa…” Ɗan murmushi yayi mai ciwo yace. “Saboda kina ɗauke da ƙaddarar da mutane basa fahimta.” zuciyarta taji ta mata wani irin bugu, a hankali ta ɗago idanunta tana kallar Mahaifin nata. “Wasu mutanen idan ALLAH yana son su…baya barsu su samu komai da wuri.” Wani shiru kawai JANNEERH tayi tana sauraron mahaifin nata kana ya ɗora da. “Kinga zinare? ba’a samunsa a saman ƙasa, sai an tona da wahala kafin a same shi.” Hawaye suka fara cika idanunta sai BAFFA ya ɗora da magana cikin nutsuwa. “Mutane zasu miki dariya saboda baki yi aure ba…Wasu zasu ce akwai matsala tare dake… wasu kuma zasu raina ƙaddararki saboda basu ga hikimar ALLAH ba.” Nan take hawayen da take ta kokarin ɓoyewa suka zubo mata duk da wannan ɗin ba sabamun abu bane a wurinta. BAFFA ya kalleta sosai kafin ya sake ce “Hafsat…” TA amsa da “Na’am Baffa…” “Ki saurare ni da kyau ina son ki sani wata rana…ALLAH zai haɗaki da mutumin da zai sa ki manta dukkan hawayen da kika yi.” A hankali maganganunsa ke ratsa ko ina na jikinta kafin ya ɗora da fadin. “Amma kafin ranar ta zo…Dole sai ƙaddararki ta bi ta cikin DUHU.”Kalmar data bugi zuciyarta kenan kai tsaye sai taji wani irin sanyi da tsoro a lokaci guda. “Baffa…” Ya ɗaga hannu ya katseta ahankali ya ɗora da faɗin. “Kada ki taɓa jin kin makara a rayuwa saboda baki yi aure ba, babban bala’i ba rashin aure bane Hafsat…Babban bala’i shi ne mace ta rasa mutuncinta saboda tana gudun kada ace ta makara.” Hawayenta da take tarewa suka zubo mata. BAFFA ya miƙa hannu ya share mata hawaye kamar tana yarinya ƙarama. “Kuma ki sani…” Ya ɗan yi shiru kafin yace cikin murya mai nauyi. “Duk macen da duniya ta kasa fahimta…sau da yawa tana ɗauke da ƙaddara mai girgiza rayuwa ne.” Nan take zuciyar Jannerh tayi wani irin bugawa mai ƙarfi. Har taji kamar bata jin iskar bishiyar mangwaron da suke ƙarƙashinta. Daga can tsakar gida kuwa Mama Rukayya ce ke ta faman mita. “To wallahi ni ban fahimci wannan yarinyar ba!, na fara kai wa bango, ya Ƴa kwaya ɗaya saboda san zuciya yasa taki fidda miji tayi aure saboda duniyanci ana mana wariyar launin fata uymmm?.” Tana wanke kayan miyar tana famar mitar nata. Aunty Amarya ta ɗan taɓe baki tana mai ɗorawa da faɗin. “Yo taya ni gani dai Kullum cikin hijabi kamar wata ta gari ko zaɓaɓɓiyar da aka ce an zaɓa daga sama ba, Shegiya kana kallonta kasan babu namijin da zai iya jure irin wannan rayuwar.” Sadiya wacce take ƴa ta uku ga Aunty Amarya dake zaune gefe tana latsa waya ta bushe da dariya tana mai furta. “To ai yanzu Mama maza basa son mace irinsu Aunty Hafsa shi yasa baa son mace ta fiye zurfi a karatun addini sosai, shi yasa Baffa yayi ta fadansa amma yabi ta bayan kunnena wllh.” Mama Rukayya ta gyada kai da sauri tana amshewa da fadin. “Wallahi kuwa! haka ne, Namiji ai yana son mai wayewa sosai ba irin su sukumbiya ba…” dariya suka fashe da ita gaba ɗaya daidai nan jannerh ke karasa shigowa tsakar gidan ɗin, cike da wani irin kwarin gwiwar fara maida martanin ga duk mutumin daya faɗa mata ba daidai ba, ko da ba da rashin kunya bane, ko da cike da hikima ne tama kanta alkawarin zata fara wannan yakin maganar koda bata iya ba zata koya. Saboda ta gama gajiya da jinyar ciwon dake a ɓoye. A hankali ta karasa shigowa cikin gidan ɗin daya saka su yin tsit, dadi da kari kuma yau ɗin sunga idanunta cike da wani irin ciwo mai zurfi. Ta kalli Mama Rukayya kai tsaye ta kira sunanta. “Mama…” Muryarta tayi magana mai cike da nutsuwa da kuma kamun kai. “Shin mace bata da wani amfani a rayuwa ne sai aure?” Duk shiru su kayi kafin Mama Rukayya ta taɓe baki tace. “To ai idan ba aure ba me kuma?” Wani irin murmushi JANNEERH tayi… Murmushi mai ciwo. “Kenan idan mace bata yi aure ba ta zama marar amfani kenan ku a wurinmu?” kaf ɗin su babu wanda ya bata amsa. Sai ta sake ɗago idanunta masu cike da wani kalan ɓoyayyan rauni kafin tace. “Shin kun taɓa tunanin yadda kalamanku ke karya zuciyata ne?” A karo na farko kenan da Mama Rukayya ta rasa bakin magana saboda yau muryar Jannerh bata asalin jannarh'r da suka saba ji bane. “Wallahi wani lokacin…ni kaina bana fahimtar me yasa wasu aurarrakin ke jinkiri…” Hawaye suka ciko idonta Amma basu subo ba tace. “Amma hakan ba shi ke nufin ALLAH ya tsaneni ba?” Aunty Amarya ta ɗan saki baki saboda bata taɓa ganin JANNEERH tana magana daga zuciya haka ba. “Kullum kuna kallona kamar ina da wani aibu…” Sai ta girgiza kai da ƙarfi tace. “Alhalin ni ma mace ce…ni ma ina jin ciwo…ina jin kaɗaici…” Kalmar ƙarshe ta fito daga bakinta da wani irin raunin da yasa ko zuciyar dutse sai ta tausaya mata. Sai kuma ta sharce hawayenta da sauri, ta dago Idanunta da suka canza wani irin haske ne mai cike da ƙarfi ya bayyana cikinsu. “Amma duk da haka…Ba zan taɓa neman soyayya ta hanyar saɓawa ALLAH ba.” Wani irin shiru ya rufe tsakar gidan gaba daya kafin ta ci gaba da magana. “Idan ƙaddarata tana zuwa a hankali…to zan jirata cikin aminci da mutunci.” Har ta juya zata shige ta dakata tace. “Amma wata rana zaku gane cewa ba kowanne jinkiri bane rashin dacewa…” TA wuce ta barsu cikin wani irin shiru mai nauyi. Gaba ɗaya jannerh a daren wannan ranar gaza runtsawa tayi, daga bangaren Ibrahim khalil ma hakan ce ke faruwa a wurinsa, Dukansu suna kallon sama kowannensu cikin wani irin duhu. Cikin irin shigen ƙaddara ɗaya gare su wacce ke jan rayuwarsu zuwa hanya ɗaya a hankali. Hanyar da zata haɗa Royalty… da kuma Love…wanda idan suka hade zai zama kamar Love Mystery kenan. Sai dai kafin wannan ranar ta zo dole sai zukata sun sake takura da jin cewar kamar sun gaza ne. _LAGOS_ *IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL * IBRAHEEM tsaye yake bakin balcony ɗin gidan yana kallon yadda ruwa ke sauƙa ahankali. Rigar jikinsa ta jike kaɗan saboda feshin ruwan dake ɗan fesowa amma ko motsi bai yi ba, hasali ma tunanin rayuwarsa kawai yake. Tun daga JOHN… har zuwa IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL. Wani irin murmushin ciwo yayi ahankali yana furta. “Rayuwa kenan…” “Mutum zai iya mallakar komai amma kuma ya rasa nutsuwar zuciya.” Ya tuna mansion ɗinsu, ya tuna Papansa, ya tuna Mother Ya tuna rayuwar da yake ciki kafin ya musulunta. Rayuwar party… mata… kuɗi… shaye-shaye… rayuwar da mutane ke kallo suce perfect life. Sai ya lumshe idanunsa yana sake maimaita kalmar Perfect?… kansa ya dafe domin duk waɗan nan ababuwan babu abinda yake aikatawa. Domin duk cikin hayaniyar rayuwar… zuciyarsa ta kasance babu komai a ciki sai Duhu kawai. Sai bayan kuma da ya gano ALLAH…kana ya fara jin kamar yana numfashi, amma yanzu kuma shin me yasa zuciyarsa ke sake jin wani irin duhu?. Yasmine kawai idan ya tuna sunan wani irin ciwo ne ke ratsa shi. Sakamakon da da idan ya tuna sunan yake jin zuciyarsa kamar ana wanke masa ita da alkausara ne. Tun baya jin gajiya har yanzun yake jin ya fara gajiya. Gajiyar yaƙar zuciyar mutum da baya son canza wa a hankali ya ɗaga kansa sama. “Ya ALLAH…” ya furta muryarsa tayi rauni sosai. “Idan akwai alkhairi a rayuwa ta kawo min shi cikin sauƙi…” Sai kuma ya ɗan yi shiru karon farko ba tare da ya shirya ba wani suna ya fito daga cikin tsakiyar zuciyarsa..... “Who is Hafsat…?” Ya furta gabansa na faduwa cike kuma da mamaki saboda bai taɓa sanin wata Hafsat ba bai kuma taɓa haɗuwa da ita ba, amma me yasa zuciyarsa ta ambaci sunan?... Cikin sati biyun da su Ibrahim suka sake yi da Yasmine ya ganoma kansa guma guman ababuwan da bai masan da mai zai musaltasu ba. Duk lokacin da zai yi mata wata magana akan gyara game da rayuwarta, sai tace ita ya bari yana takura rayuwarta ne. Ga kuma wani mayen zazzafan zazzabin dake takura rayuwarta, wanda bayan ya kira wani likita gwajin farko yace tana dauke da cikin One Months ne. Wanda gaba daya ta bi ta ɗaga hankalinta akan cewar ita ba zata taɓa haife wannan cikin ba sai dai a zubar. Idanunsa ya dan lumshe ahankali muryan sa ba ta fita sosai yake tambayar kansa mai yasa matsalolin ke neman fin kafin sane?, mai yasa ababuwan ke nemar masa yawa ne?, mai ya saka ya fara jin kokonto akan kansa addinin Musuluncin ma?, mai yasa haka addinin su nasu su yake kamar baya da alfarma baya da wani sauki ko ramgwame?. Mannuwar da yaji tayi da jikin sane ya saka shi sakin wani wawan ajiyar zuciya yayi, a ransa yana yin addu'ar ALLAH yasa komai ne ya kusan zuwa ƙarshe. A hankali ya juyo da ita yana zuba mata janyayyun idanunsa da su kayi laushi sosai, fuskanta ya dago yana furta "Why Yas-mine mai yasa kike ƙoƙarin karya kwarin zuciyana?". Kwacewa tayi daga jikin nasa tana bin sa da wani irin kallon kai mai yasa gaba daya a rayuwa baka da komai sai magana akan addini addini addini dai?, wani irin rauni ne ya ziyarci zuciyarsa mai tafe da fara sarewa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yayin da al'amura ke sake zuwa suna wucewa,wasu masu dadi wasun kuma kishiyar haka,yayin da a ɓangaren family na John sosai rayuwarsu ta sake kunci musamman dai Madame Victoria, inda zuwa yanzun an samu kimanin watanni uku da auren Ibraheem da kuma Yasmine sai dai komai na karasa lalacewa ne. Ga shi kusan kullum seya amsa waya daga family nashi kan cewar sun bashi go ahead ɗin dawowa, in yaso kowa yayi addininsa, yayi rayuwarsa amma ya dawo kusa dasu ɗin zai fi, in da ganan sun dawo masa da duk komai daya rasa nashi, Ga Yasmine najin maganar komawar tayi tsallen ala tsine uwar mai ƙarya tace sai sun koma. *TO ALHAMDULILLAH DUKA DUKA NAN ZAMU DAKATA A BOOK ONE NA WANNAN LITTAFIN KUMA FREE PAGE'S... * _Shin kuna tunanin cewar John (IBRAHIMUL KHALEEL) zai koma mension nasu?_ _Shin kuna tunanin cewa haka rayuwarsu zata ji gaba da tafiya da YASMINE ba tare da wani sauyi ba? _ _ababuwan dai suna da yawan da ni kaina ba zan iya furta su cikin sauri ko gaggawa haka ba, dole dai sai an bini a sannu cikin tafiyar DUHU NA DUKAN DUHU kashi na biyu_ _And Ana ina son mu sani cewar wasu ƙaddarorin basa zuwa da wuri… saboda ALLAH yana fara gyara zuciyar wanda zai ɗaukesu ne kafin su iso gare shi_ _Kuma ina son mu sani cewar ba duk jinkiri bane rashin dacewa… wani lokacin ALLAH yana ɓoye maka alkhairi ne har sai lokacin da zuciyarka zata iya riƙe shi ba tare da ta lalace ba kana yake bayyana a gare ka. Kuma mu sani wasu Mutane suna ganin shiru a rayuwar ka ne kawai… alhalin a sama ana rubuta maka labarin da zai girgiza zukata ne_ *Wani lokacin ƙaddara tana zuwa maka ne ta cikin DUHU… saboda idan haske ya bayyana zaka gane cewa duk hawayenka ba a banza suka zubo ba* _Domin anan ina mu sani ne cewar Akwai mutane da duniya ke rainawa yau… amma gobe su ne darasin da duniya zata koya cewa jinkiri baya hana daraja. Ta inda wasu zuciyoyin sai bayan sun karye ne suke iya gane hanyar ALLAH._ *Masu kaddarar jinkirin aure ku sani ba kowanne ciwo bane azaba… wasu ciwon gyaran ƙaddara ne. Domin Mutum baya rasa abin da ALLAH ya rubuta masa… ko da duniya ta rufe masa ƙofofi, ƙaddara tana da hanyar da zata riskeshi* _Wani lokacin ALLAH yana hana ka abin da kake so ne saboda akwai abin da zai girgiza rayuwarka da yafi shi alkhairi wanda ya tanajar maka.Duk wanda ya koya jira saboda ALLAH… wata rana zai ga dalilin da yasa aka hana masa abubuwansa da wuri_ _Akwai hawayen da mutane ke gani suce rauni ne… alhalin a wajen ALLAH su ne matakan ɗaukaka. Ba kowa bane zai fahimci ƙaddararka saboda wasu labaran sai bayan sun cika ake gane hikimar su. Don haka ku tausaya wa zuciyar da take jira cikin halal… domin akwai yaƙin da take yi da kanta wanda mutane basa gani. Wacce wata rana zaka waiwayi rayuwarka ka gane cewa abubuwan da suka karya ka su ne suka kai ka inda addu’arka take_ _Ku daina kallon rashin aure tamkar rashin daraja ne domin ba kowacce mace bace take makara, ku sani cewar wasu ƙaddarorin ne kawai basu iso lokacinsu ba. Ku daina tambayar mace dalilin da yasa bata yi aure ba… wataƙila tana cikin yaƙin da ita kanta bata iya furta wa ba_ *A dai wannan zamanin ba duk wanda yayi aure bane ya dace… kuma ba duk wanda bai yi ba ne ya rasa dacewa, ku tuna cewa ƙaddara bata bin agogon mutane. Wata macen zata iya zama ita kaɗai shekaru… amma tana tare da ALLAH fiye da matar da take cikin aure babu nutsuwa! * _Ku daina ɗora wa mata nauyin aure kamar shi ne ma’aunin kimarsu… domin darajar mace tana cikin mutuncinta ba cikin sunan matar wani ba_ *Ku tuna cewa abin da ALLAH ya rubuta baya wucewa. Ba kawai Auren da yazo da wuri ba ne alkhairi ba… wani lokacin jinkiri shine ceton rayuwa. Ku daina kallon mace marar aure da idanun tausayi… wataƙila ita ce mafi nutsuwar zuciya a cikin ku, domin ba laifinta bane idan ƙaddararta bata zo da wuri ba… kuma ba laifinta bane idan ta zaɓi mutunci akan saurin aure* _Don ALLAH ku dena karya zukatan mata da maganganunku, domin wasu murmushin da kuke gani yana ɓoye hawaye ne masu nauyi a cikinsa, akwai matan da suka zaɓi jiran halal duk da zafin kaɗaici… saboda sun fi son hawaye na duniya akan nadamar lahira tamkar dai *HAFSAT MUHAMMAD ALIYU (JANNEERH)*_ ︎⠀ _HUMMM Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakuɗe cikin wannan littafin_ _Duk zamu samu amsoshin waɗannan tarin tambayoyi namu ne idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo ƙarshen BOOK 1 DUHU NA DUKAN DUHU Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin DUHU NA DUKAN DUHU 1K NE, Amma ga mutanen farko zu biya 700 Hundred kacal babu yawa..._ _Ga duk mai son biya kai tsaye zai tuntuɓeni a wannan number_ 👇 08104493215 Wanda suke sun biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin 👇 8104493215 Maryam Nasiru Opay Or 3206656358 Maryam Nasiru First Bank A turo shedar biya ta wannan number 08104493215 _Masoya na amana a nuna min kauna sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na DUHU NA DUKAN DUHU babu ku, domin anan ne hasalin kaddara da labarin yake, na haduwar John ko nace IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL da kuma JANNEERH wacce itace zata kawo haske cikin rayuwarsa. Shin ya kuke tunanin wasa zata fara ne ma wai?, Manyan Malamai manyan mutane kowa na shakkar furta mata kalmar SO ɗin da take ta mafarkin samu, to don ALLAH ta ya kuke ganin John zai iya shiga cikin rayuwarta, shin mutane sun fara gane zauren cen mu na DUHU NA DUKAN DUHU KUWA?, Su waye suka gane cewar YASMINE itace hasalin duhu na dukan duhu din data shiga rayuwar John kamar da ƙarfi da yaji, da kuma yaudara da cin amana?_ _MASU TAMBAYANA JERIN SUNAYEN LITTATTAFAINA TO GASU KAMAR YACCE NA MUKU ALƘAWARI ZAN LISSAFO MUKU...._ *KAREN BANA FREE* *JALAAL AREEF FREE* *ƘAUNA BIYU FREE* *MIKIYA PAID ONLY 500 HUNDRED* *TA DABAN ONLY 500 HUNDRED* *DUNIYARMU ME CIKE DA TARIN ƘALUBALE ONLY 1K* *SO DAN RAYUWA ONLY 500 HUNDRED* *RAMIN KURA ONLY 1K* *DUHU na DUKAN duhu ONLY 1K* *ƘARSHEN ƘADDARAR 500 HUNDRED ONLY * *SAI KUMA DUHU NA DUKAN DUHU WANDA YAZO A KAN 1K AMMA GA NA FARKO FARKON 700 HUNDRED * Ku sani waɗan nan litattafan suna jerin sunayen littattafan nawa ngd👏👏👏.... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* ᴬᴹᴹᴱʸ ᴸᴬʸᴸᴱᴿᴴ🤫😶🤐😥😢😩✍️🙏 BAKINA DA GORO AMMA NAYI SHIRU HAKA NAN. AMMA DUK DA NACE NACE TA INA WANNAN ZAZZAFAR KADDARAR ZATA FARA HAƊA IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL DA KUMA HAFSAT MUHAMMAD ALIYU?... 08104493215