🥀 *BAYAN DUHU*🥀 🌑 GABATARWA 🌑 Bismillāhir-Raḥmānir-Raḥīm Godiya ta tabbata ga Allah (Subḥānahu Wa Ta'ālā), Ubangijin talikai, Mai rahama kuma Mai jin ƙai, Wanda Ya ba ni ikon fara wannan littafi tare da kammala shi cikin ikonsa da yardarsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (Ṣallallāhu Alaihi Wasallam), da iyalansa, sahabbansa da duk waɗanda suka bi tafarkinsa har zuwa ranar sakamako. Masoya karatu, ina yi muku barka da zuwa cikin wannan sabon labari mai suna BAYAN DUHU. Labari ne da ya ƙunshi darussa masu amfani, ƙalubalen rayuwa, haƙuri, soyayya, cin amana, juriya da kuma fata. A cikinsa za ku fahimci cewa duk tsananin duhun da rayuwa ta kawo, akwai ranar da haske zai bayyana da izinin Allah. Ina roƙonku da ku karanta wannan littafi da zuciya ɗaya, sannan idan kun ga wani kuskure na nahawu ko rubutu, ku gyara ni cikin ladabi, domin babu mai kamala sai Allah Maɗaukakin Sarki. A ƙarshe, ina godiya ga dukkan masoyana da masu karanta rubuce-rubucena bisa irin ƙauna, addu'a da goyon bayan da kuke ba ni. Allah Ya saka muku da alheri, Ya sanya wannan littafi ya zama sanadin alkhairi gare mu baki ɗaya. Barkanmu da sake haɗuwa a cikin... Book1️⃣ Page 0️⃣1️⃣ ___________🥀BAYAN DUHU🥀______________ *A'isha Muhammad Kabir* _Ma'eesher_✍️ Gida ne na masu matsaikacin ƙarfi wata kyakkyawar budurwa a tsakar gidan tana wanki, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yarinyar ta haɗa jini da larabawa saboda irin kyau da hasken fatarta, Wata mata ce ta fito daga ɗaki, kallon ta tayi cikin masifa tace " wai ke Ayrah wace irin jakar yarinyar ce kwata-kwata bakya aiki da sauri tun ɗazu baki gama wankin nan ba bayan kin san ɗiban ruwa yana jiran ki". Ayrah tace "kiyi hakuri mama abu na kusa gamawa". Matar tace "Hai dallah wawiyar banza jaka minti 10 na baki kigama wankin nan ki fita ki ɗebo mana ruwa idan ba haka ba jikinki ya gaya miki". Tana kaiwa nan matar ta juya abinta ta koma ɗakin ta tana ƙwafa, hawayen da Ayrah taƙe riƙewa ne suka fara fitowa, hannun ta tasaka ta share a ranta tanajin kewar ummin ta , saboda tasan halin mama abu, cikin minti goma sha biyar 15 ta gama wankin ta shanya, Sannan ta nufi kitchen ta ɗauko bocket ta fice daga gidan tanajin cikin ta na mata kukan yunwa dan rabon ta da abinci tun jiya da dare da taje gidan su ƙawarta Sa'adatu ta bata tuwo taci, har yanzu da yake ƙarfe 12:20 bataci komai ba, Tana fita ta nufi fanfon tuƙa-tuƙa wanda yake da ɗan nisa da gidan su, tana isa bakin fanfon zuciyarta tai mugun bugawa saboda wanda ta gano a bakin fanfon, jiki a sanyeye ta ƙarisa, Tun kafin ta ƙarisa yaron sa ya kallesa yace "hattara dai oga gacan cilar ka tana zuwa". Bakin ta ɗauke da sallama ta ƙarisa bakin fanfon, wanda yayi magana ɗazu ya kalleta yace "Sa'a dai amaryar ogan mu". Ɓata fuska tayi kamar zatai kuka sai kuma ta basar tasaka bocket in ta alayi , Ai kamar jira yake yi ya kalli yaron nasa yace "Dauda". Dauda yace "Sa'a dai oga Tanko". Tanko yace "matata bai kamata tabi layi ba a cire botikin uban kowa asaka mata nata". Ai kuwa haka Dauda ya saka mata botikin ta ya cika sannan ya cire mata,. Yana ƙoƙarin ɗauka tace " barshi zan ɗauki abuna".bai mata musu ba ya bar mata, ta ɗauka ta nufi hanyar gida babu abinda cikin ta yake mata banda ƙugin yunwa". Bakin ta ɗauke da sallama ta shiga gidan nasu, wata budurwa ce wacce bazata wuce shekarun Ayrahn ba, kallon tayi rai ɓace tace "to soloɓiyo sai yanzu kika ga damar kawo mana ruwan tun ɗazu inaso nayi wanka kin shanya mutane sai jiranki suke". Ayrah ta kalle ta tace "kiyi hakuri ma'u". Tsaki ma'u taja tace "dalla can mayya ki wuce ki kaimin wannan botikin bayi zanyi wanka sai ki ɗauki ɗayan botikin". Ayrah tace "ma'u mama abu fa ta hana wanka da botikin nan". Ma'u ta ƙule tace " shegiya ni kike faɗawa mama ta hana ke dai da kike jaka ke aka hana, ta ɗaura da cewa zakije ki kaimin ko sai na canza miki kamanni?". Ayrah batace da ita komai ba ta wuce ta kai mata ruwan bayi, Tana fitowa ko kallon inda ma'u take batayi ba ta ɗau ki wani bocket in ta fice daga gidan, Batayi wata doguwar tafiya ba, tazo dai-dai ƙofar wani gida taji ana neman almajiri, ƙarisawa inda yarinyar take, tace "dan Allah idan abinci zaki bashi ki bani zanci wallahi yunwa nakeji". Yarinyar ta tsaya tana kallon ta da kwanon abincin a hannun ta , hawaye na bin ƙuncinta tace "mallama Ayrah!". Mamaki ya cika Ayrah amma ta ɓoye tace "ki bani abinci naci". Yarinyar tace ki shigo ciki". Ta faɗi hakan yayinda take kama hannun Ayrah suka shiga ciki, Wata mata ce a zaune a tsakar gidan tana gyara shinkafa kallon su tayi, tace "Maryam wannan ba Ayrah ba?". Maryam tace "itace wallahi aunty itace malamar mu a islamiyya da". Ta faɗa yayinda take miƙawa Ayrah abincin hannun ta, ta ɗebo mata ruwa ta bata, Abinka da mejin yunwa haka ta zauna tana ta cin abincin hannu baka hannu ƙwarya, bayan ta gama ci tasha ruwa, ta Musu godiya ta fice dan bata so ta daɗe, Bata gama ɗiban ruwan nan ba sai kusan 1:30 ta ajjiye botikin, ta ɗauki buta tayi alwala ta shiga ɗakin su, ma'u ta samu tana kwance tana waya ko kallon inda Ayrah take batayi ba, har Ayrah ta shimfiɗa kwalin ta, ta gabatar da sallar ta, Ta daɗe tana addu'a tana kaiwa Allah kukan ta, tare da fatan duk inda mahaifiyyarta take ta kasance cikin ƙoshin lafiya, Tana idarwa ta jiyo muryar mama abu tana ƙwala mata ƙira, Da sauri ta fita ta nufi inda sautin kiran mama abu yake fitowa, Tana fitowa ta samu mama abu tsaye da tiren goro a hannun ta, tace "uban me kike tun ɗazu kinaji ina ƙiranki?". Tace "kiyi hakuri mama". Mama abu tace "to gashi maza ki tafi talle kuma karki dawo min gidan nan sai kin tabbatar da kin siyar da goron nan idan ba haka ba jikin ki ya faɗa miki". Ayrah ta karɓi goron hannun mama abu ta nufi ƙofar fita daga gidan,. Wunin ranar haka Ayrah taita zage gari amma batayi ko biyar ba, har 6pm bata koma gida ba saboda tana tsoron abinda zataje ta tarar, Tana tsaye a bakin titi daga ƙarshe ta yanke shawarar komawa gida, tsallaka kwalta ta take yi amma zuciyar ta cike da tunani kala-kala kamar da ga sama wata lafiyayyar mota ta bigeta, ta faɗi ƙasa sumammiya, Da sauri drivern ya fito, cikin tashin hankali shima wanda ake driving ɗin ya fito , kyakkyawane fari tas tabar kallah masha Allah, hasken sa irin na larabawa, Da sauri ya ƙariso kanta kallo ɗaya ya mata yaji zuciyarsa ta masa wani irin bugun da bai taɓa jin irin sa ba sai yau, Drivern yace" ranka ya daɗe bari na ɗakko ta muje asibiti". Kallon drivern yayi yace "zan ɗakko ta". yana faɗan haka yasaka hannu ya ɗauki Ayrah sai cikin mota, a back seat ya ajjiye ta shi kuma ya koma front seat, tare da umartar drivern akan ya ƙara gudu, Yanayi yana juyawa yana kallon fuskanta har suka ƙarisa hospital in, da wuri aka karɓeta aka shiga da ita, Ba'a daɗe da shiga da ita ba wayar sa ta fara wringing, picking yayi tare da sallama, Bayan an amsa masa sallamar, daga ɗaya bangaren yace "bro kana inane har yanzu baka ƙariso ba hankalin mu duk yabi ya tashi bayan ka sanar da mu 5 zaka ƙariso". Yace "karka faɗa a mami amma mun bige wata yarinya ne yanzu haka muna asibiti ". Yace"subhnallahi yanzu kuna wani asibitin?". Yace" muna asibitin ku". "Ok" kawai yace tare da kashe wayar, Basu daɗe da magana ba, sai gashi ya shigo asibitin, da saurin sa, Yayi kan su yana tambayar su "ya jikin yarinyar?". Yace" basu fito da ita ba tukunna dai tana ciki". Yace "bro ka taso muje office ɗina ka jira acan nima zan shiga na duba yanayin jikin yarinyar". Ya faɗa yayinda yayi gaba shi kuma ya bishi abaya har izuwa office in, inda aka rubuta Dr. Ahmad M Saraki,. Zama yayi akan kujera zuciyar sa cike da tunane-tunane , shi kuma Dr. Ahmad ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fice, Baifi minti 5 da fita ba sai gashi ya dawo ya kalle shi yace "alhamdulillah bro insha Allahu soon zata samu lafiya zaka iya zuwa ka ganta". Batare da yace komai ba ya fita ya nufi ɗakin da aka ajjiye ta, yana shiga ya samu tana bacci hannun ta ɗauke da da drip, Fuskarta ya tsaya yana ta kallo yana jin zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri, Turo ƙofar akayi aka shigo Dr. Ahmad ne da wata nurse, juyawa yayi yana kallon su, Dr. Ahmad yace "kazo mu tafi gida ga nurse zata kula da ita". Yace" no". Dr. Ahmad yace "Please kazo mu tafi za ta kai gobe 9am kafin ta farfaɗo kuma idan bakazo gida ba me zance a mami bayan kace kar na sanar da ita". Kallon ta yayi sai kuma ya juya ya nufi ƙofar fita, basu yi tafiya mai nisa sosai ba, suka shiga wani tamfatsetsen gida mai kyau, suna shiga sukayi parking, suka fito shida Dr Ahmad suka shiga ciki bakin sa ɗauke da sallama, Wata kyakkyawar budurwa dake ta faman kaiwa da komowa ta juyo fuskanta ɗauke da farincikin da ya kasa ɓoyuwa a zuciyarta, ta miƙa musu gaisuwa dukkan su suka amsa, Tace" sannu da zuwa yah Amjad". Yace "yawwa". Ba yabo ba fallasa, Ana cikin haka sai ga mami ta fito da sauri ya ƙarisa yayi hugging in ta, Itama cikin farin ciki ta riƙeshi tace "welcome my son". Yana matuƙar ƙaunar mami kamar itace ta haifesa ƙaunar da yake mata ne ma ya shafi 'yar ta maya, wacce tun haihuwar ta yake ƙaunar ta amma shi yana mata ƙaunar 'yan uwan taka ne, saɓanin ita da take masa ƙaunar aure, Wanda hakan yasa family suka yanke shawarar haɗasu aure, duk da baya mata so na aure bazai iya rejecting jinin mamin sa ba ko yaƙi yin biyayya a familyn su, Mami ce ta kalle shi tace "to yanzu kaje kayi wanka kayi sallah sai ka fito muyi dinner". Yace "ok". Tare da nufar ɗakin sa, Dr. Ahmad ne ya kalli maya da farincikin ta ya kasa ɓoyuwa, yace "maya ya maganar tafiyan mu Abuja goben?". Murmushi tayi tace "yah Ahmad kawai abar tafiyar nan sai upper week". Murmushi mami tayi ta juya ta nufi kitchen, shima Ahmad ɗin dariya ya fara mata ya juya ya nufi ɗakin sa saboda yasan duk saboda zuwan Amjad ne yasaka tace su bari sai upper week, Itama bin bayan mami tayi har yanzu farincikin fuskarta ya nan, tana zuwa tai kan wata budurwa da take haɗa kunun madara, Ta rungume ta, juyowa tayi tace "masha Allah maya wannan farincikin ya tabbatar min da cewa yah Amjad ya ƙariso". Sake ta tayi tace "Erh mana mubeenah bakiga yadda ya ƙara haske da kyau ba masha Allah ". Mami tace "Allah ko?". Sai a lokacin ta lura da mami dan ita wallahi tama manta mami tana gurin, Ai bashiri ta juya da gudu ta nufi upstairs ɗakinsu ta shiga ta faɗa kan gado tana rungume filo, bata daɗe da shigowa ba mubeenah ma ta shigo hannun ta ɗauke da glass cup da kunun madarar ta, zama tayi a bakin gado tana sha, Ta kalli maya tace "maya irin wannan farinciki haka sai kace wanda kika yi one year baki ganshi ba?". Maya tace "bazaki fahimta bane, 5 months fah nayi bangan shiba to kowani month jinsa nake kamar year". Mubeenah zatayi magana wayar ta, tafara wringing, picking tayi tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren aka amsa mata sallamar ta, Tace "Barka da dare". Yace " Barka dai mubeenah fatan kina lafiya". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Yace "masha Allah yasu mami?". Tace "duk suna lafiya wallahi alhamdulillah ". Yace "hope dai yah Amjad ɗin ya iso?". Tace"Erh ya iso tun ɗazu". Yace "ok ina maya?". Tace "tana nan". Yace "ok ina zuwa I will call you back". Tace" ok" tare da kashe wayar ta ajjiye, A saman bed side drower, maya ta kalleta tace "yah Aliyu ne ko?" Mubeenah tace "Erh shine". Maya tace "sis ko kinso ko kinƙi fa gaskiya ɗaya ce shine yah Aliyu yana sonki". Mubeenah batace da ita ƙala ba, ta shiga bathroom domin ɗauro alwala alwala tayi ta fito ta da Sallah, ..... A ɓangaren Amjad suma tare suka tafi masallaci shida Dr Ahmad sukayi sallah suna fitowa suka tsaya a dining,.. Mubeenah ma bayan ta idar da Sallah , tare suka fito da maya wacce tayi wanka ta canza kaya zuwa riga da wando masu laushi maras sa nauyi, sai ƙaramin half Sunnah black da ta saka, sai ƙamshi take, A dining suka tadda mami da kuma su Dr Ahmad zama sukayi tare da gaida kowa, bayan sun amsa Amjad ya kalli mami yace " mami kaddai daddy baya gari?". Mami tace " Erh yana Abuja amma may be gobe zai dawo". Yace "ok". Daga nan babu wanda ya ƙara cewa komai a ɗan uwansa mami ce da kanta tayi saving ɗin su, bayan sun gama suka dawo falo suka fara hira, maya ta kalle shi tace "yah Amjad wannan karan baka siyo mana abayas bane?". Yace " dukka suna mota". Mami tace "ohhh maya ke ko sha'awar atamfa bakyayi ne? Kullum rayuwar ki cikin abaya". Miƙewa Amjad yayi yace "mami na zanje wani guri amma ban daɗeba zan dawo". Tace "ok". Ahmad yace " bari muje tare". Tare suka fita basu tsaya a ko ina ba sai a M. SARKI hospital, ya daɗe a dakin yana kallon ta kafin daga baya ya miƙe ya jamata bedsheet ya rufe ta tare da karanto mata addu'oi sannan ya fice,... ****Washe gari misalin 9:20am ta farfaɗo a hankali ta sauƙe idonta akan Dr Ahmad sai kuma ta maida kallon ta kansa, hawaye ne suke bin ƙuncinta, Dr Ahmad yace "mata sannu". Kai kawai ta iya ɗaga masa, yace "akwai inda yake miki ciyo?". Tace "a'a ina ne nan ina mama abu da ma'u ina kuma talle na?". Yace "ki kwantar da hankalin ki, kin samu accident ne ". Tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un". Dr Ahmad yace "kiyi hakuri insha Allahu zuwa anjima zamu sallame ki amma kafin nan ki bamu numbern wani naki sai mu kira mu sanar da shi". Tace "no kabarshi kawai". Yace"Meyasa?". Tace "ina buƙatar nayi sallah ". Toilet ya nuna mata sannan dukkan su suka fita, ita kuma ta tashi ta shiga toilet in, bayan tayo alwala ta fito ta shimfiɗa kwalin ta tana gabatar da sallolin da ake binta, Bata daɗe da idarwa ba sai ga su sun dawo, da sallamar su ta amsa musu, sannan ta gaishe su, suka amsa, abincin da suka siyo mata ya miƙa mata, yace " ga abinci kici ". Tace " ok". Ta karɓa tare da yi masa godiya, ledar ta buɗe ta ciro abinci da ruwan sai kuma ta tsaya tana bin abincin da kallo, Dr. Ahmad yace "ki saki jiki kici abincin ki bari muje mu dawo". Bata ce da su komai ba har suka fice, bayan 'yan mintuna suka dawo suka samu tagama cin abincin tana ta hawaye, Dr Ahmad yace "ƙanwata lafiya kike kuka?". Tace " babu komai". Yace "akwai mana karkiji komai ki faɗa min meyake da munki ki ɗauke Ni matsayin yayan ki". Tace " dama idan na koma gida babu kuɗin goron mama abu ne to zata iya kasheni da duka". Ta faɗa tana mai share hawayen idonta yace "babu komai yanzu amshi maganin nan kisha insha Allahu zan baki kuɗin goron sai muje mu bata hakuri". Ta karɓi maganin tace" no ba sai kunje ba ai dan idan kukaje ma kuna tafiya zata dake ni". Yace "maman kice?". Tace "a'a matar mahaifina ne ni ummi na ta ɓata tun shekaru 3 baya". Amjad yace "ayya I'm sorry Allah ya bayyana ta ". Tace "Ameen ya Allah thank you ". Misalin ƙarfe 11:00 na safe suka ajjiye ta a unguwar su , babu yanda basu yi da ita akan sukai ta gidan su ba, amma sam ta ƙi, haka suka hakura suka ajjiye ta suka bata kuɗi suka wuce, gidan su ƙawarta Sa'adatu ta tsaya, Sa'adatu na kallon ta taso da gudu ta rungume ta tana hawaye, Tace "Ayrah lafiya ina kika shiga hankalin mu duk yabi ya tashi?". Maman Sa'adatu tace " ai saiki barta ta huta tukunna". Kama hannun ta Sa'adatu tayi suka zauna ta basu labarin duk abinda ya faru, ta ciro kuɗin da suka bata wanda ita kanta bata san adadin su ba, ta ciri dubu biyar , tabawa maman Sa'adatu sauran tace " mama ga wannan ki ajjiye agurin ki barinje gidan". Tana faɗan haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita, Bakin ta ɗauke da sallama ta shiga gidan ma'u ce zaune a tsakar gida tana kwalliya, kallon Ayrah tayi tace "sai yanzu kika ga damar dawowa daga yawon karuwancin naki kenan?". Ayrah bata kulata ba ta ƙarisa shigowa gidan, Ma'u ta ƙwala kiran mama jin shiru yasa ta ƙaracewa "mama ki fito ga karuwar gidan ki ta dawo".............✍️ DUHU 🥀 ________ *A'isha Muhammad Kabir* -Ma'eesher- Feature writers association N F.U.W.A 2... ***** Da sauri mama ta fito daga ɗakin tana bin Ayrah da wani mugun kallo, Ayrah tai ƙasa da murya tace "mama ina kwana". Mama tace "zo nan muna fuka". jiki babu ƙwari ta ƙarisa gun mama, mama tace "dan ubanki ina tiren tallen da kuma goron?". Take hawaye ya fara bin ƙuncinta cikin rawan murya tace "mama dan Allah kiyi hakuri wani ne ya kaɗeni a asibiti ma na kwana amma ya biyani kuɗin goron". Mama abu da jira take kawai Ayrah ta gama maganar ta, ta ɗauketa da mari jin maganar ta na ƙarshe na kuɗin ya sakata da katawa da marin da tayi niyyar mata tace "ina kuɗin?". Hannun zaninta ta kunce ta ciro 5k wanda ta cira acikin kuɗin can ta bawa mama, mama na washe baki ta irga, tace "Allah ya taimake ki munafuka yau da kinci uban ki". Ma'u tace " mama bafa wata mota da ta kaɗeta kawai karuwanci ta fara". Mama tace " Ni kam ina ruwana indai zata na kawo min kuɗi taje tayi abinda yafi karuwancin ma". Ma'u tace "to munafuka tunda kin dawo sai kizo ki ɗibo mana ruwa ki dafa mana abincin rana". Tace "to". Botiki ta ɗauka ta nufi famfo sai da ta cika ko ina da ruwa agidan kafin ta hura wuta ta ɗaura abinci, tana girkin tana shara bayan ta gama share gidan tas taje ta share ɗakin mama ta gyara sannan taje ta gyara nasu, lokacin ta gama dama shinkafa da wake ta girka musu, zuwa tayi ɗakin mama ta tsaya a bakin ƙofa tace " mama nagama girkin". Mama ta ɗebo mata barkono da su maggi tace taje ta daka yaji, Bayan ta gama da ka yajin ta tattara wanke-wanke ta fara, bayan ta gama tayi alwala ta shiga ɗaki domin lokacin sallah yayi, ɗan kwalin ta, ta shimfiɗa ta fara sallar ta, tana idarwa ta juya ta kalli ma'u tace "ma'u wai Meyasa bakya sallah ne, ma'u kiji tsoron Allah ki tsaida sallah wallahi idan kika gyara sallar ki Allah zai gyara miki dukkanin al'amuranki". Ma'u tace "wallahi idan baki rufe min baki ba na tashi sai nayi ƙasa -ƙasa dake a gurin nan shegiya karuwar banza". Shiru tayi bata ƙara cewa da ita komai ba, mama abune ta shigo ɗakin, hannun ta ɗauke da kwanon abinci, ta miƙawa ma'u tace "gashi kici idan kin ƙoshi ki rage mata". Ma'u tace "mama zan iya cinye abincin nan fah". Mama tace"shikkenan bari a tsakuro mata ka ɗan". Ma'u bata ƙara cewa komai ba, haka itama Ayrah mama ta nufi ƙofar fita, taje ta ɗibo mata abincin ka ɗan hakan ma ba'a saka mai ba ruwa kawai aka saka kaɗan aciki a madadin mai sai yaji, Ayrah ta karɓa tace "mama Nagode". Mama ta miƙa mata 5k in data bata ɗazu tace "gashi kina gamawa kije shagon lauwali ki haɗo mana kayan abincin siyar wa yau jollof in taliya zamuyi ta siyar wa". Tana kaiwa nan ta fice bata jira amsar da Ayrah zata bata ba, Ayrah tana gama cin abincin ta sharuwa ta fice, bayan ta siyo abubuwan tazo ta ɗaura girkin, ka fin ta ɗibi ruwa ta shiga wanka, har lokacin da fito, ma'u tana zaune tana faman danne- danne a wayar ta, kallon ta Ayrah tayi tace " aunty ma'u dan Allah ki bani vassiline mana na shafa idan kina da shi". Ko kallo bata isheta ba, ballantana ta amsa mata, jin shiru ya saka ta miƙe tasaka wata tsohuwar doguwar rigar material, da wani koɗaɗɗen half Sunnah black abinka da farar mace sai tayi kyau abinta, Fita tayi ta ɗauki roban tallen nata ta fice daga gidan, bata dawo ba sai 5:00pm, ta siyar duka, tabawa mama abu kuɗin, sannan tayi shara tayi wanke-wanke ta ɗaura abincin dare..... **** Tunda suka rabu da yarinyar nan idan ya rufe idonshi ita yake kallo ya kasa goge photon yarinyar nan a idanuwansa, yauma kamar kullum yana zaune ita ɗin dai yake tunani, knocking akayi yace "shigo". Maya ta shigo tasha abaya mai kyau da tsada black, abinka da farar fata tayi kyau sosai, sai ƙamshi take yi hannun ta riƙe da babban plate wanda yake ɗauke da jug da kuma 2 cups, "good evening yah Amjad". Yace "evening a daƙile". Ta ajjiye masa plate in tace "mami tace na kawo maka". Yace "ok thank you". Ta gyara tsawuwar ta tace "kamar akwai abinda yake da munka?". Yace "nothing and you can go". Jiki babu ƙwari ta nufi ƙofa ta fita, A main falo ta tadda mubeenah tana zaune tana chatting, zama tayi a gefen ta, dagowa mubeenah tayi ta kalle ta tace" sis lafiya?" Tace "ina kuwa lafiya mubeenah a tunani na da yah Amjad yana sona ne kamar yadda nake son shi so na aure amma yanzu na fahimci son da yake min so ne kawai na 'yan uwan taka". Mubeenah tace "why you said that?". Tace"mubeenah you know everything tun lokacin da aka fara maganar auren mu ya canza min baya da lokaci na kwata-kwata ". Ta ƙarisa maganar tana share hawayen da suka zubo mata, mubeenah ta ajjiye wayar ta tace"kiyi hakuri Maya ki dage da addu'a insha Allahu everything will be alright ". Maya tace "Allah yasa amma wallahi har na fara tsoron rayuwar da zamuyi bayan aure". Mubeenah tace "karki damu ke dai ki dage da addu'a insha Allahu nima zan tayaki ". Tace "thank you "............ Ayra ta samu mama ta sanar mata zataje gidan su Sa'adatu, bata hanata ba dan haka ta fice ta nufi gidan su Sa'adatu bakin ta ɗauke da sallama, a tsakar gida ta samesu sun shinfiɗa taburma suna zaune itama zaman tayi tana miƙawa mama gaisuwa, mama ta amsa tace "Sa'adatu jeki ɗebo mata tuwo" Sa'adatu ta tashi ta ɗebo mata tuwo ta kawo mata taci, ta sha ruwa tana miƙawa mama godiya, mama tace "karki damu Ayrah Allah ya muku albarka" . Tace "Ameen mama". Shiru ya biyo baya sai kuma tace " mama da ma nazone akan maganar kuɗin nan dan Allah ki bawa Sa'adatu ko dubu 5 ne taje ta ɗinko mana hijabai ni da ita". Mama tace "to shikkenan badamuwa". Tace "mama dan Allah kema ki ɗauki wani abu acikin kuɗin kinji". Sa'adatu tace "gaskiya mama zata taɓa ko biyar a kuɗinki ba bestie kiyi hakuri gobe zamu koma makaranta kuma insha Allahu zanje na miki registration na Neco". Ayrah ta kalli Sa'adatu tace "kema kin san muddin mama abu tana raye ta sha alwashin babu ni babu karatun boko ko na addini sai dai talle saboda haka kawai ki bar wannan maganar nasan bazata taɓa bari na nayi ba". Sa'adatu tace " insha Allahu zakiyi karki damu akwai yadda zamuyi".... Sai da tayi sallar Isha ta fito ta nufi gida, tunda ga bakin ƙofa ta fahimci abban ta ya dawo, da sauri ta ƙarisa fuskar ta ɗauke da farinciki, Amma sai dai farincikin ya tsaya saka makon sauƙar marin da taji a fuskar ta, bata ankara ba taji an ƙara sauƙe mata wani, sai da ta zauna,............... ________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______ *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Ma'eesher*✍️ Feature writers association F.U.W.A 3. ... Ta dafe ƙuncin ta da duka hannayen ta biyu, tana jin kanta na mugun sara mata, ta ɗaga kai ta kalleshi hawaye na gangarowa daga idanun ta, tace "Abba". Yace "daga ina kike?". Tace "Abba naje gidan su Sa'adatu ne". Yace " ƙarya kike munafuka ai Abu ta sanar min kwanan ki huɗu rabonki da gida ko kin tashi dawowa ma cikin dare kike dawowa". Hawayen idanun ta ne suka ƙara gudu tace "Abba kayi hakuri". Bai ƙara cewa da ita komai ba ya juya ya nufi ɗakinsa da yake jikin ɗakin mama abu, a hankali ta miƙe tana hawaye ta nufi ɗakin su, tana zuwa kwanciya kawai tayi tanajin zazzaɓi yana sauƙa mata, ba ta daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ta, lokacin ana kiran sallar asuba Abba yazo ya ƙwanƙwasa musu ƙofa, Ma'u ce ta tashi ta buɗe kofar yace "su tashi suyi sallah". Yana faɗan haka ya juya, Ma'u ta dawo tayi kwanciyar ta taci gaba da baccin ta, duk abinda yake faruwa tanaji amma ta gagara tashi saboda zazzaɓin daya gama sauƙa mata, Tafi minti goma a kwance kafin daga bisani ta tattara jarumtar ta, ta miƙe , ta fita ta ɗauro alwala ta dawo ta shimfiɗa kwalin ta, ta tada sallah, bayan ta idar ta ƙara kwanciya wasu hawaye masu zafi suna bin ƙuncin ta, tana tuna da idan bata da lafiya yadda ummin ta take tattalin ta, amma yanzu gata a jefe akan ta burma, tunda aka nemi ummi aka rasa mama abu ta kwashe kayan ummi duka ta siyar bata bar komai ba sai taburmar da ta barmata wani abun mamaki Abba bai taɓa tambayar ummi ba har yau, Tana cikin wannan tunanin hawaye na bin ƙuncin ta sai rawar sanyi jikin ta yake yi, har gari ya waye 8am ma'u ta farka ta kalle ta sai rawan sanyi take yi, fuskarta ta kumbura abinka da farin fata shatin hannun Abba ya fito a fuskar ta, duk rashin imanin ma'u sai da taji jikin ta yayi sanyi, tace "sannu Ayrah ki tashi ki dawo kati fa ta, ai ƙasan da sanyi". Ko maganar bata gama ba mama ta banko ƙofar ta shigo tana masifa, wai Ayrah bata fito ta ɗaura musu ɗumame ba, ma'u ta kalleta tace" mama Ayrah fa bata da lafiya ne". Mama abu tace "to ni ina ruwana a wannan zamanin dama waye yake da lafiya ?,Ai kowa ma bashi da lafiya a wannan zamanin?". Ma'u tace " mama kawai ki ɗaura ɗumamen". Mama tace "ban ɗaura ba kuma ko zata mutu sai ta min aiki waya sani ma ko cikin shege taje tayo a yawon karuwancin nata". Wasu zafafan hawaye ne, suka gangaro a fuskar Ayrah, ta buɗe hajabin da ta lulluɓun ta miƙe da kyar kanta na sara mata, ta fice ɗumamen kawai tayi ta dawo ta kwanta , kanta na mugun sara mata , ko minti 30 batayi ba, da kwanciya sai ga inna ta shigo da tiren goro wai ta tashi ta tafi talle, wani baƙin ciki taji ya tsaya mata a zuciyarta, yanzu kam hawayen ma yaƙi zuwa abubuwa da yawa duk akanta ita ka ɗai, ga wahalar da take sha agidan nan, ga baƙin cikin rashin ummin ta, ga jinya, ga kuma babban tashin hankalin ta yanzu Abban ta ma ya juya mata baya yana zargin ta da karuwanci,. Haka ta miƙe jiki babu ƙwari ta karɓi tiren ta fice kowani taku ɗaya ji take kamar ana kwaɗa mata guduma akan ta saboda ciyon da yake mata, gidan su ƙawarta Sa'adatu ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, Sa'adatu bata nan ta tafi makaranta, mamace kawai a zaune tana ƙulla kayan miyan da take siyarwa, kallo ɗaya mama ta mata taji zuciyar ta, ta karye, kwanciya tayi akan taburmar da mama take, da sauri mama ta kai hannun ta kan fuskar Ayrah tace "Ayrah ai baki da lafiya kuma meya samu fuskar ki ta kumbura haka?". Ayrah tana hawaye tabawa mama labarin duk abinda ya faru, ta share hawayen ta tace "yanzu barin baki paracetamol kisha". Tana faɗan haka ta tashi ta nufi ɗaki ta kawo mata maganin da ruwa, sai da mama tayi da gaske kafin Ayrah tasha maganin saboda bata son shan magani, bayan tasha tace "mama ki juye goron nan tunda kina ci, kawai ki bani dubu biyu acikin kuɗin nan ". Yadda tace haka maman tayi, sai kuma ta ƙara kallon mama tace "mamaki ara min wayar ki idan da kati nayi kira". Mama tace "to". Ta miƙa mata wayar, wayare ƙwalin kanta tayi , ta bincika cikin gashin kanta ta ciro wata paper, numbern jiki ta ɗauka tare da dailing, har kiran ya katse ba'ayi picking ba, ta ƙara kira a karo na biyu, har ta cire rai sai kuma taga anyi picking, karawa tayi a kunnen ta, sai kuma ta fara kuka mai tsuma zuciya, "stop carrying ". Shine abinda yace, yana jin zuciyar sa tana bugawa da sauri, amma kamar ba da ita yake ba, taci gaba da kukan ta, ya kashe wayar, ta tsaya tana kallon wayar kamar zata ƙara kira sai kuma ta fasa, tana kwance ko 2 minutes bata ƙara ba, sai gashi ya kira, Picking tayi tare da sallama, ya amsa sai kuma yace "why are you carrying?". Murya ƙasa-ƙasa tace "bana da lafiya ne ji nake kamar zan mu......". Ai bai bari ta ƙarisa ba, yace " zanzo inda muka ajjiye ki ranar, zan ƙariso nan da 15 minutes, yana faɗa ya kashe wayar, ajjiye wayar tayi tana bin wayar da kallo, mama da yanzu fitowar ta daga ɗaki hannun ta riƙe da kofi, ta kalli Ayrah tace "tashi ki sha kunun nan kinji". Ayrah ta tashi ta karɓi kunun ta sha, duk ƙarfin hali take, Allah ne kaɗai yasan yadda takeji, haka ta daure ta karɓi tiren goron nata agun mama bayan mama ta juye, ta tashi ta fita, gidan su ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, mama abu dake zaune a tsakar gida ba abinda take yi,... Ta ɗaga kai ta kalleta, Ayrah ta miƙa mata kuɗi da tiren, mama abu tace "yawwa gacan wanke-wanke na haɗa miki kiji kiyi yanzu nan, ai Ayrah ko kallon inda take fa, batayi ba ta fice daga gidan tana dafe kanta saboda yadda yake mata ciyo, ga wani hajijiya da take ji ƙarfin hali kawai takeyi tana tafiya tana dafe jikin gini hawaye na bin ƙuncinta, yana zaune acikin matarsa ya hango ta, da sauri ya tada motar ya ƙariso inda take, ya buɗe mata front seat yace " shigo". Shiga tayi ya tada motar ya juya, tunda ta shiga ta lumshe idonta ƙamshin turaren sa wanda ya haɗu da sanyin AC take shaƙa, a hankali ta buɗe idanun ta da su kai ja saboda wahala ta sauƙe su akan shi, tace "good morning". Yace "morning ya jikin?". Tace "alhamdulillah". Yace " meyake da munki ?". Tace "ban sani ba kawai dai kaina ne nakejin kamar ana bugamin guduma sai kuma zazzaɓi da nakeji ka ɗan". Yace "ok dama tuntuni kinayi ne lokaci zuwa lokaci ko kuma?". Tace "sometimes inaji amma ba sosai ba kawai sai na danne bana faɗawa kowa sai ƙawata Sa'adatu saboda babu wanda zai saurereni ita kuma sai ta siya min magani na sha shikkenan ". Yace "ok". Daga nan kuma shiru ya biyo baya ta ƙara lumshe idonta, shi kuma ya ci gaba da driven da yakeyi zuciyar sa cike da tunani kala-kala akan ta, har suka ƙarisa asibitin aka fara duba ta........ ________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______ *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Ma'eesher*✍️ Feature writers association F.U.W.A ...4 Tana kwance a ɗakin su ba bacci take amma zuciyar ta cike da tunane-tunane kala-kala wayar ta ce tafara wringing, hannun ta ta miƙa ta ɗakko wayar asaman bedside drower, kallon wanda ke kiran take, numbern anyi saving da "LOML* tare da emoji na love, picking tayi tare da sallama, bayan ya amsa yace "kina ina". Tace "gida". Yace "ok ki haɗa min breakfast mai kyau ki kawo min hospital office in Dr Ahmad ". Tace"ok". Tare da kashe wayar, ta miƙe ta nufi kitchen bata daɗeba ta gama ta dawo tayi wanka, ta saka baƙar abaya mai kyau da tsada, tai rolling kanta da farin veil, sai hand bag da plate shoe in ta shima white, simple make-up tayi, ta fito wani dadɗan ƙamshi yana tashi daga jikinta, ɓangaren mami ta nufa ta sanar mata, kafin ta koma kitchen ta ɗauki haɗaɗɗen basket in da haɗa masa komai aciki, ta nufi ƙofar fita, ......... AYRAH...... An duba ta sosai, an ɗaura mata drip an mata allurai, ta samu bacci, ta daɗe tana baccin, kafin a hankali ta fara buɗe idonta ta ɗaura su akan shi, murmushi ya sakar mata, yace "ya jikin". "Alhamdulillah " tace, sai kuma ta fara ƙoƙarin tashi amma ta gagara, yace "sannu ki koma ki kwanta jikin ki babu ƙarfi". Komawa tayi ta kwanta tana kallon sa, yana zaune akan kujera yana danne-danne a wayar sa, wayar ce tafara wringing, picking yayi tare da sallama, Maya dake zaune a mota cikin sanyin murya tace "ina parking space ko in ƙariso?". Yace "no kijirani anan ina zuwa". Tare da kashe wayar, ya maida kallon sa kan Ayrah da ta zubawa saman room in ido, yace "I will be back soon". Kai kawai ta ɗaga masa ya fice, yana zuwa ya buɗe front seat ya shiga, tana zaune tana chatting da mubeenah tana tambayar ta ina ta shiga ne tazo ɗakin su bata ganta ba, yana shigowa ta ajjiye wayar tana kallon sa, yace " ina kika sani inda ake sai da jallabiya da abaya na mata masu kyau?". Bata kawo komai a ranta ba, ta sakar masa murmushi, tace "algazaru ventures". Yace "ok I'm coming barinje in dawo ki raka ni". Tace "ok". Yana fita ta turawa mubeenah recording hiran da sukayi, shi kuwa da ya fita sai da ya buɗe back seat ya ɗauki basket in kafin ya koma ciki, a yanda ya barta haka ya sameta ya ajjiye basket in, yace barina ƙira nurse ta taimaka miki kici abinci make sure kin sha magani bayan kin gama ci, sannan ta taimaka miki kiyi wanka kafin na dawo zanje wani guri yanzu ". Tace "insha Allahu " . Juyawa yayi ya fice, ya tura mata nurse ya koma inda Maya take, suka tafi, shi yake driving ita kuma tana zaune a back seat, time to time tana kallon shi, ba tare da ya kalle ta ba yace "tunda na dawo banga kunje islamiyya ba, haka banga kunje aiki ba". Tace" islamiyya dai muna hutu, aiki kuma insha Allahu gobe zamu fara fita". Yace"ok" suna tafiya tana directing ɗinsa har suka ƙarisa tare suka fito suka shiga yace"taje ta zaɓi duk abinda take so sannan ta zaɓawa mubeenah ma". Tace"ok". Sanda ta gama zaɓa suka je gurin biya yace "taje mota ta jirashi yana zuwa". Bata kawo komai a ranta ba ta fita, zuciyar ta cike da farinciki ko ba komai yau wanda take so ya bata lokacin shi har ya fitar da ita shopping, shi kuwa tana fita shima yaje ya jido abayas guda 10 masu kyau ya zo ya bada ATM ɗin sa, bayan yayi making payment, ya fito ya buɗe boot ya saka mata nasu ya saka nasa a back seat , ya fita suka wuce, A bakin asibitin yayi parking ya ɗauki ledan nasa, itama fitowa tayi ta kalle shi, tace "thank you". Murmushi kawai ya sakar mata, ya nufi hospital in, Yana shiga ya sameta tana kwance tayi duk abinda yace, sallama yayi ta amsa masa tace"sannu da dawowa". Yace "Yawwa Fulani". "Fulani". Ta maimaita sunan a zuciyarta, ajjiye mata kayan yayi yace " ka kaya ki canza ni zan wuce Company idan na dawo zan biyo na dubaki Ahmad zai kawo miki lunch ". Tace "Nagode sosai Allah yasaka maka da alkhairi". Yace "Ameen" har zai fice ya juyo ya kalle ta , yace " make sure kina shan magani akan lokaci". Tace "insha Allahu". Yace "idan na dawo zamuyi magana mai muhimmanci". Tace "Allah ya dawo da kai lafiya". Ya amsa da Ameen yayinda yake fita". Tunda ya fita bai dawo ba har bayan la'asar kamar yadda ya faɗa Dr Ahmad ne ya kawo mata lunch taci suna ta hira da yake bashi da wuyar sabo har sun saba sosai jinshi take kamar ɗan uwanta na jini, sai 5pm ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, tace "wa alaikassalam". Ya ƙariso ya zauna a kan kujeran yana kallon ta, yace "ya jikin?". Tace " da sauƙi alhamdulillah". Yace "Allah ya ƙara sauƙi". Tace" Ameen, sannu da dawowa". Yace "kin sha magani?". Tace "Erh". Yace " sallah fah". Tace "nayi". Yace "yawwa masha Allah". Hannun sa ya saka a aljihun sa ya ciro waya techno spark 50 ya miƙa mata, yace ki riƙe wannan akwai layi aciki sanna akwai number ta duk lokacin da kike buƙatar wani abu sai ki kirani, sannan akwai data a layin ko kallo kinayi saboda yana ɗebe miki kewa idan babu kowa a gurin ki". Tace "a'a ka barshi wallahi Nagode ". Ya haɗe rai ya shiga yanayin da bata taɓa kallon sa aciki ba fuskar nan babu annuri yace"karɓa". Jikin ta na rawa ta karɓa dan har ga Allah ya bata tsoro, dai-dai nan Dr Ahmad ya shigo bakinsa ɗauke da sallama suka amsa masa, ta shi yayi ya koma bakin gadon ya zauna Dr Ahmad kuma ya zauna akan kujerar , ya mata ya jiki ta amsa, . Amjad ya kalle ta yace " dama na faɗa miki akwai maganar da nake so muyi da ke mai muhimmanci". Tace "Erh". Yace "ina so ki bamu labarin ki and please karki ɓoye min komai na miki alƙawarin zamu taimake ki". Sunkuyar da kanta tayi hawaye na bin ƙuncinta gurin yayi shiru babu abinda kakeji sai sautin kukan ta.......... Sai da tai kukan ta mai isarta kafin a hankali ta fara magana, sunana "A'ishatul Humaira na taso ban san kowa ba a dangin ummina haka na abbana muna zaman lafiya da Abbana da ummina wani lokaci abba yace zai ƙara aure ummi bataji daɗin hakan ba amma babu yanda muka iya haka baba ya aura mama abu tazo da 'yarta ma'u wacce take Sa'a ta sai kuma ɗan ta Tanko ɗan shaye-shaye babu irin abinda mama abu bata mana ba , na wulaƙanci Abba yana goya mata baya sai da muka zama tamkar bayi a gidan nan, wata rana aka nemi umma na aka rasa lokacin muna jss3 tun daga lokacin babin wahala ta ya buɗe, Ni nake komai a gidan nan, idan nayi kuskure ka ɗan mama abu takama ni tamin duka, shi Tanko bai cika kwana a gidan ba sai yayi sati biyu ma bai shigo gidan ba, yace a mama abu yana sona, tun daga lokacin ta yanke babu wanda zan aura sai shi kuma wallahi bana son shi, bana son auran ɗan shaye-shaye, daga baya idan mama Abu tamin abu Abba na baya iya magana amma yana bani hakuri, ya kan bani kuɗi a ɓoye na siya duk abinda da nake so, amma yanzu Abba shima ya canza ta kwashe labarin duk abinda ya faru jiya da dare ta basu,........ ________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______ *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Ma'eesher*✍️ Feature writers association F.U.W.A 5 Ba Amjad ka ɗai ba shima kansa Dr Ahmad ya tausaya mata, Amjad yace" kiyi hakuri Allah yana jarabtan bayin sa da yake ƙauna ta kowace irin hanya fatan mu dai Allah ya baki ikon cinye wannan jarrabawar insha Allahu bazan bari a aura miki wannan ɗan shaye-shayen ba, kuma insha Allahu zan inganta miki rayuwar ki, sai kin zama abin alfahari a idon duniya, kuma insha Allahu, Allah zai bayyana mana ummin ki". Tace "Allah yasa yayinda take goge hawayen idon ta". Ta ƙirkiro murmushi tace " yah Ahmad menene sunan brothern ka?". yace "gashi nan ki tambaye sa mana ". Sai ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsar ta, Amjad yace "Ahmad yaushe zaku sallame ta?". Ahmad yace"gaskiya akwai buƙatar ta kwana a nan saboda akwai sauran drip in da za'a ƙara saka mata da allurai". Yace "to shikkenan". Ya kalle ta yace "zaki iya kwana ke kaɗai ko mu samo miki me tayaki kwana?". Tace "zan iya kwana ni ka ɗai". Yace " kin tabbata?". Tace" Erh insha Allahu". Basu bar asibitin nan ba sai da sukayi Isha, sannan yazo ya mata sallama, ta kalle shi tana da fe cikin ta dake mata ciyo sama-sama tace" sai da safe". Yace " ki yi addu'a kafin ki kwanta, masu night duty zasu na zuwa suna du baki". Tace "insha Allahu Nagode ". Bai ce mata komai ba ya fice, wayar da ya bata ta ɗakko ta kunna data, tayi downloading TikTok da Whatsapp, TikTok ta sai ta tana ta kallo, abinta sai kusan 11:30 bacci sace ta,.......... Shi kuma bayan sun koma gida yayi wanka ya fito dinning lokacin da ya ƙariso kowa hallaru, yau kam hadda daddy, bayan ya zauna ya gaida daddy sannan ya gaida mami, shima su Maya suka gaishe shi, mubeenah tace "yah Amjad mun gode da shopping Allah ya saka da alkhairi Allah ya ƙara arziki". Dukkan su suka amsa da "Ameen ". Daddy ya kalle shi yace " Amjad ya maganar komawar ka Madina?". Yace daddy nan da 2 weeks insha Allahu zan koma". Mami tace" sai a musu Engagement kafin ya koma yana dawowa Sai a musu aure". kunya ce ta kama Maya kamar ta nutse ƙasa a hankali ta tashi zata bar gurin?". Mami ta kalle ta, tace "where are you going?". Tace "I'm okay". Mami tace "to ai bakici komai ba, dawo kici abincin ki". Ba dan taso ba ta koma gurin tanajin kunya kamar ta nitse ƙasa, bayan sun gama dinner Mami ta kira ammi ta sanar da ita shawarar da suka yanke ita da daddy Ammi tayi farinciki ta sanar da ita insha Allahu suma suna hanya cikin satin nan zasu zo kawai sai a tsaida ranar Engagement in, shi kam tunda ya kwanta duk juyin sa labarin Ayrah ne yake masa yawo a kunne tunda aka yanke shawarar haɗa shi aure da Maya bai taɓaji baya son auren ba kamar yadda bai taɓaji yana son auren ba, sai da Ayrah ta shigo rayuwar sa, ya rasa gane me yake ji game da yarinyar nan, Washe gari misalin 7:00am duk sun hallaru a dining suna breakfast saboda duk zasu fita aiki yau, daddy yayi gyaran murya yace "Yayana ya ƙirani jiya yace sun tsaida auren Ahmad da kuma 'yar gurin sa fadila nan da zati ɗaya wato this Saturday". Wani farinciki ne ya mamaye Dukkanin su domin dama sun riga da sun shirya gidan su amaryar kawai suke jira, daddy ya ɗaura da cewa na yanke za'a haɗa auren da Engagement ɗin su Amjad kawai". Mami ce kawai tayi magana tace "ai kuwa hakan yayi Allah ya tabbatar mana da alkhairi ". Suka amsa da "Ameen ". Bayan sun gama breakfast Amjad da Ahmad suka wuce asibiti sai da ya tsaya ya mata take away a hanya kafin ya suka wuce, baƙin su ɗauke da sallama suka shiga ɗakin ta amsa murya ƙasa-ƙasa ta gaishe su, suka amsa , Ahmad yace "ya jikin ?". Tace " da sauƙi alhamdulillah ". Yace "Allah ya sawwaƙe". Ta amsa da "Ameen ". Yace barin wuce akwai Patience da zan duba". Tace "ok sai anjima". Zama Amjad yayi a bakin gadon yana bin fuskar ta da kallo". Yace "are you okay?". Tace "I'm okay kawai cikina kemin ciyo sai kuma jikina da banajin ƙarfinsa". Yace "karki damu you will be okay soon insha Allahu ". Tace "insha allahu ". Amma dai yau za'a sallameni ko?". Yace " I don't know". Ya ajjiye mata ledan yace kici abinci anjima nurse zata zo ta miki allura ta saka miki sauran drip ɗinki". Tace "insha Allahu Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ". Yace " ni zan wuce office". Tace "to Allah ya tsare". Yace "Ameen ".... Ai kamar jira cikin ta yake ya fita ya fara mata mugun ciyo, juyi take a kan gadon tun tana daurewa har ta fara hawaye tana addu'a". Wayar da ya bata ta ɗauka da kyar numbern da ta gani tai dailing picking yayi , ko sallama batayi ba tace "yah mufaddhal cikina zan mutu". Yace "sorry barin turo nurse ta dubaki". Yana faɗan haka ya kashe wayar ya tura mata nurse,..... MAYA...... Bayan sun gama breakfast suka shirya suka fito suka nufi Company, basu da ɗe da isa ba wata ta shiga office ɗin Maya tace "Madam C.E.O yana ƙiranki". Tace "okay". Ta ajjiye files in da take dubawa ta miƙe ta nufi ƙofa, fitowar ta tayi dai-dai da fitowar mubeenah daga nata office ɗin da yake facing na Maya, tare suka ranka ya zuwa office ɗin nasa , nocking sukayi ya ɗau kusan 5 minutes kafin ya basu izinin shiga, tare suka shiga ko waccen su ta tsaya, sukace "good morning sir". Da wani irin kallo ya bisu kafin yace " before mu ɗauke ku aiki bakuce mana sai kun ga dama zaku na zuwa Company ba". Kallon sa Maya tayi tace "yah Amjad dama". Tsawa ya daka mata yace "who is yah Amjad". Jin ƙarar tayi har cikin kanta, take ta faɗi ƙasa sumammiya.......... ________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______ *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Ma'eesher*✍️ FEATURE WRITERS ASSOCIATION. F.U.W.A .....6 Da sauri mubeenah tayo kanta, ta ɗebo ruwa a pridge ɗin office ɗin ta watsa mata, a hankali ta fara numfashi ta buɗe idonta, ta ɗaura akan mubeenah sai ta maida shi kansa dan shima tuni ya taso yayo kan ta, yace "mubeenah tai mata ki Kaita office ɗin ta". Mubeenah ta kamata suna zuwa office ɗin ta, ta tun tuntsire da dariya, tai ta dariya sai da tayi mai isarta, ta kalli mubeenah tace "ya kika ga kafcen nawa?". Mubeenah ta tsaya kallon ta, tace "Allah ya kyauta amma wallahi nayi tunanin da gaske ki ke". Tace " da banyi hakan ba Allah kai ɗai yasan abinda zai mana kamar ba yayan mu ba". Mubeenah tace "hakane kam barin wuce office akwai ayyuka da yawa a kaina". Tana faɗan haka ta fice.... Yau ma bai dawo hospital in ba sai 5pm zaune yake a bakin gadon yana kallon ta, itama a zaune take a can dungun gadon tana wasa da yatsar ta, kallon ta yayi yace" Fulani". Tace "na'am". Yace " idan kin amince min inason naje na samu abbanki na nemi aurenki". Jin abun tayi tamkar a mafarki, ta kama bakin gyalen abayan ta, ta rufe fuskarta, tana dariya, yace "bakice komai ba". Tace "kar mu yaudari kan mu yah mufaddhal tausayi na kake ba sona kake ba". Yace " waya faɗa miki ko kin manta ana cewa daga tausayi soyayya take farawa, Fulani tabbas akwai wani abu a tsakanin mu wanda Allah ne kawai ya sanshi, amma tun lokacin da muka bigeki da mota, na fara jin wani abu game da ke". Tace " to Allah ya tabbatar da alkhairi ". Yace "Ameen yaushe zanje na samu Abban?". Tace " ba yanzu ba tukunna saboda yanzu ko kaje ma bazai amince da kai ba, saboda nima yanzu kallon karuwa yake min". Ta ƙarisa maganar hawaye na bin ƙuncinta, yace "haba Fulani ke fa musulma ce kuma ya kamata ki yadda da ƙaddara kyakkyawa ko mummuna , ki daina kukan nan haka kinji". Tace "to insha Allahu ". Sun daɗe suna hira, sai da yaji an kira sallah kafin ya miƙe ya mata sallama ya nufi masallaci, bayan ya dawo a inda ya barta ya sameta, da har zai mata maganar sallah sai kuma ya fasa, yace" mata kishirya zamu mai da ke gida, wannan karan insha Allahu zanje na yiwa baban ki bayani kuma zamu tafi da ta kaddun ki na asibiti as evidence ". Tace" Thom shikkenan ". Ta miƙe ta fara shirya wa, shi kuma ya fita zuwa office ɗin Dr Ahmad bayan ɗan lokaci, suka dawo tare har tagama shirya wa, ta tattara kayan ta, acikin ledan da ya siyo mata abayas, shida kansa ya karɓi ledan suka fita, Ahmad ke driving sai shi a front seat ita kuma a back seat, kallon Ahmad yayi yace "ku fara shirye-shirye dan na samu mata". Dr Ahmad yace " ai ka daɗe da samun mata dama". Yace "ina magana ne akan Fulani". Dr Ahmad yace "wacece kuma Fulani?". Yace "bayan ni da kai sai waye a motar nan". Dr Ahmad yace " ƙanwata". Sai kuma yayi shiru da ɗan wani lokaci kafin yace "to kafara min biyayya idan ba haka ba, bazan baka ƙanwata ba". Kallon sa kawai yayi ba tare da ya ƙara cewa komai ba, har suka iso unguwar tana directing ɗinsu ai kuwa sunyi Sa'a lokacin da suka ƙariso lokacin Abban ta yana zaune akan taburma a ƙofar gida sauƙa sukayi daga motar suka ƙarisa inda yake, cikin ladabi suka gaisheshi, ita kuma ta shige gida, bayan sun gaisa cikin ladabi suka masa bayanin cewa sun kaɗe ta ne, shine suka Kaita asibiti tare da gabatar masa da ta kaddun asibitin, sannan sukace sunyi ƙoƙarin kiran wani nata amma tace " bata haddace numbern kowa ba, tunda suke magana yake ta kallon su kamar wanda yake son tuna wani abu amma ya kasa, bayan sun gama masa bayani ya musu godiya sosai , suka masa sallama tare da ajjiye masa kuɗi a gefen sa, suka wuce,.. Ita kuma bakin ta ɗauke da sallama ta shiga, gidan a zuciyarta tana ta addu'ar Allah yasa Abba ya yadda da su, ai kuwa tana shiga ta samu mama abu tana girki, tace "mama ina wuni". Mama tace "riƙe gaisuwar ki munafuka, kawai sai yanzu kika ga damar dawowa daga yawon karuwancin naki ". " 'yata ba karuwa bace". Cewar Abba da yanzu shigowar sa, da sauri Ayrah ta juya ta rungume shi tana hawaye, yau dai Abban ta ya dawo bayan ta, ya kalli mama abu yace "kar na ƙara ji ko ganin kince wa 'yata karuwa". Mama abu tace "kayi hakuri ". Jiki na rawa ta shige ɗaki, a zuciyarta tana cewa na shiga uku ni abu yau asirin jikin Mallam ya karye, Abba ya kama hannun Ayrah yana bata hakuri suka shiga ɗakin sa, suka zauna, ya kalleta a hankali yace "mamana ina ummin ki?". Kuka ta fashe masa da shi mai tsuma zuciya tace "Abba ummi ta barmu Abba ummi ta daɗe da barin gidan nan ban san inda ummi na take ba". Shima kansa duk yanda ya kai ga jurewa sai da yayi hawaye, yace ". Mamana ki kwanta ki huta, zan je na sanar da jami'an tsaro". Tace "to Abba". har zai fita ta kalle shi tace "Abba". Ya juyo ya kalle ta, tace "wanda ya kawo ni ɗazu farinne ya siya min wannan wayar". Yace "bari sai na dawo zamuyi magana". Tace "to". Yana fita bai daɗe ba sai ga, Sa'adatu ta shigo har suna karo da mama abu a hanya, tana sauri zata fita, ita kuma Sa'adatu tana shigowa, ko ta kan Sa'adatu da ta bige bata biba, ta fice, babban tashin hankalin da mama abu ta shiga shine bokan da ya mata aiki akan Abba ya mutu, gawar sa har ta fara wari acikin daji, dan haka dole ta koma gun wanda ya mata aiki akan ummi, da sauri ta fice daga jejin ta nufi inda ɗayan bokan nata yake..... A ɓangaren Ayrah kuwa tana kwance ta jiyo muryar Sa'adatu tana ƙwala mata ƙira, ta leƙo tace "kishigo ƙawata ina ɗakin Abba na". Sa'adatu ta ƙarisa ta zauna tana kallon Ayrah, tace "Ayrah na yadda dake bazan taɓa zargin ki da aika ta abinda ba shine ba, amma ya kamata ki sani abinda kika aikata ba dai-dai bane taya zamu nemeki murasa har kwana ɗaya da yini ɗaya, kinyi tunanin mu da muka damu da ke wani irin hali zamu shiga?". Tace "kiyi hakuri ƙawata". Nan ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta bawa Sa'adatu kuma ta nuna mata wayar da Amjad ya siya mata, Farinciki a fuskar Sa'adatu ba'a cewa komai tace "alhamdulillah Allah Nagode maka Finally dai ƙawata zata huta da wahala". .. AMJAD..... Shi kuwa suna juyawa ya kalli Ahmad yace "yawwa na tambaye ka mana?". Yace "ina jinka". Yace "dan Allah yarinyar nan bata maka kama da mubeenah?". Yace "wallahi nima naga kamar su, kawai dai hasken ta ya banbanta da na mubeenah ne hasken ta ya zama kalan naku, shiyasa tafi mubeenah kyau". Amjad yayi dariya yace" wato mu hasken namu daban yake".yace "Erh mana ai hasken naku ya banbanta da namu"........ AYRAH...... Sa'adatu bata bar gidan nan ba sai bayan Isha, mama abu ma bata dawo ba sai 9 Abba kam neman ummi yayi ta yi har 9:30 kafin ya dawo, lokacin har ta koma ɗakin su tayi bacci, Washe Gari..... Misalin ƙarfe 9:00am na safe tana zaune tana wanke-wanke kamar yadda ta saba, Tanko ya shigo gidan ko sallama babu, bata kula shi ba, ya fara ƙwala kiran mama! Mama!! Da sauri mama abu ta fito tana tambayar sa ko lafiya, yace " mama yanzu saboda bakya ƙaunata Erh shine kawai zaki bar yarinyar nan ta fara karuwanci da manya manyan mutane?". Ayrah tace " Ni ba karuwa bace kuma insha Allahu bazan aure ka ba". Ai bata ankara ba taji ya ɗauke ta da mari, ta dafe ƙuncinta yace "ko zaki mutu sai kin aureni". Mama tace "ƙara mata marar kunyar banza". Ya kall unii mama yace " mama kawai a aura min yarinyar nan kowa ma ya huta". Mama tace" ka kwantar da hankalin ka akwai abinda na shirya nan da wata ɗaya zata zama matar ka". Yace " Sa'a dai mama Allah ya biya wallahi Allah". Dai-dai nan Ma'u ta shigo ko sallama babu, ko Tanko ne ya kalle ta yace " Sa'a dai ƙanwata, ɗan yarfa min wani abu mana". Hannu ta sake a jakar ta taciro 5k ta bashi tai wucewar ta ciki, Ayrah dai cigaba da wanke-wanken ta tayi, kamar bata gurin bayan ta gama tayi shara ta ɗaura abincin rana, shi kuwa Tanko tuni ya fice daga gidan, bayan tagama abincin rana ta shiga ɗakin su ta ɗauki wayar ta, Ma'u sai bin wayar take da kallo, tana fitowa ta ɗauki bocket in ɗiban ruwan ta, ta fice, gidan su Sa'adatu ta nufa, mama tayi farincikin ganin ta samu lafiya taita sakawa su, Amjad albarka, tana fita daga gidan ta wuce ɗiban ruwa bayan ta gama ɗiban ruwan ta shiga wanka, bayan ta fito, ta saka ɗaya daga cikin abayan da Amjad ya siya mata, Mama tace"ke kije ku fara shirye-shirye zamu bar unguwar nan saboda munafukai sunyi yawa"...... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ *A'isha Muhammad Kabir* -Mer'eesher-✍️ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... 7.... Mamice zaune a falo ita da mubeenah sun shirya sai ƙamshi suke yi, Maya da Ahmad tare suka shigo falon suma sun shirya abinsu, sanye maya take da abaya blue tayi kyau sosai, suna ƙarisowa Mami ta kalle su, tace "sai yanzu kuka ga damar fitowa for how long kuka barmu muna jira anan". Ahmad yace" ayi hakuri Mami". Mami zatai magana kenan, ƙamshin sa ya cika falon, Maya ce ta juya tana kallon sa, a hankali ta sauƙo da idon ta kan kayan jikin ta, sai kuma ta juya ta kalli mubeenah, Mami tace" dan Allah kuyo sauri mu tafi". Mubeenah ta kalli Mami yayinda suke fita daga falon tace "Mami amma a motar mu zamu tafi ko?". Tace "a'a wallahi ni fa har yanzu Ban gama yadda da driving ɗin ku ba". Maya ce ke driving sai mubeenah a front seat, sai motar can kuma Dr Ahmad ke driving Amjad a front seat sai , Mami a back seat, motar su Amjad ce ta fara fita, sai Maya ta bi bayan su, a wani makeken gida suka kutsa hancin motan nasu, suna parking suka fito, gidan baban gidane mai ɗauke da part-part, Part na biyu suka shiga dukkanin su, bayan sun saka masu aiki su shigo musu da kayan da suka tafo da su, suna shiga falon suka Zazzau na wata, babbar mata ce ta fito fuskar ta ɗauke da glass, tana shigowa Maya tace "tsohuwa mai ran ƙarfe barka da dawowa Nigeria". Tace "ai kyabari na zauna dai ko". Zama tayi dukkan nin su, suka shiga gaishe ta hadda Mami tana amsawa ɗaya bayan ɗaya, masu aiki suka fara shigo mata da abubuwan da suka zo mata da su, ta kalli Mami tace "A'isha ke kam bakya gajiya da hidima". Mami tace"babu komai hajjah ai yiwa kaine". Hajjah tace " to Allah ya muku albarka". Mami ta amsa da "Ameen". Sun daɗe a ɓangaren Hajjah kafin daga baya suka wuce ɗaya ɓangare bakin su ɗauke da sallama, momy dake zaune a falo tana waya da 'yan uwanta akan fadila ta juyo ta kalli Mami ta amsa musu sallamar cikin fara'a tare da kashe wayar, bayan sun zo sun zazzauna sun gama gaisawa, Maya da mubeenah suka wuce upstairs wani daki suka shiga, tana zaune a gaban dressing mirror, jin antura ƙofar ya saka ta juyawa da sauri tana kallon mai shigowa, Maya kam direct kan gado ta faɗa, tana cewa "wallahi na gaji". Mubeenah ta zauna a bakin gadon tana kallon fadila, tace "amaryar mu mai capacity". Fadila tace "point of correction aunty fadila". Maya ta ɗago da sauri tace "aunty? who is aunty?" Wallahi fadila kina ruwa indai Maya zatace Miki aunty ". Mubeenah tayi murmushi tace "that's my Maya ". Fadila ta, taɓe baki tace "kwaji da shi". Mubeenah tace "yawwa sister fadila ni kam nace ya jikin wannan matar?". Fadila tace "da sauƙi dai zai ace amma fa shiru har yanzu bata farfaɗo ba". Mubeenah tace "ayya Allah ya bata lafiya". Dukkan su suka amsa da "Ameen". Suna zaune a gurin suna ta hirar su, har sai da lokacin lunch yayi mommy tazo ta kirasu, dukkanin suka tashi suka bi bayanta, a dining suka Zazzau na tare, da gaishe da kowa, kowa ya amsa, Hajjah ce ta kalli Maya tace "kishiyar ya naga sai kyau kike ƙara wane". Murmushi maya tayi tace "Hajjah kawai dai jikin yarinta ne". Hajjah tace "to ai nima nawa jikin na yarinta ne". Mubeenah tayi dariya tace "tabbb Lallai kam ragajab suna ya kama wani abu". Itama mayan murmushi kawai tayi, ba wanda ya ƙara magana har suka gama lunch ɗin, sannan suka koma ɗakin fadila dan gabatar da Sallah, bayan sun idar suka koma gun Hajjah inda suka kafa sabon hira Hajjah tana tsokalar su suna bata amsa, basu bar gidan ba sai da sukayi Isha...... AYRAH..... zuwa yanzu soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin AYRAH da Amjad wanda suke jin baza su iya rayuwa ba sai da juna, yau ma kamar kullum tana zaune, a tsakar gida tana, wanke-wanke, bayan tagama ta tattare yau tun, da tai sallar asuba bata koma bacci ba, take ta aiki, bayan ta kammala tayi wanka tana ta sauri tana yi tana duba a gogon wayar ta, a gaggauce ta shirya, cikin wata doguwar rigar material ta saka half Sunnah fari wanda duk ya koɗe, ta fito mama abu da yanzu fitowar ta, ta tsaya tana kallon ta, tace "ke gidan uban wa zakije ne kike ta sauri haka". Dammm zuciyar ta buga ta tsaya cak a inda take, ta juyo ta kalli mama tace "mama ina kwana ". Mama tace "nace gidan ubanwa zakije". Ayrah tace "zanje gidan su Sa'adatu ne" mama tace "ƙarya kike munafuka zaki fita yawon karuwancin naki dai da kika fara ballagaza kawai". Ayra batace mata komai ba ta wuce abinta gidan su Sa'adatu suka je daga nan suka ranka ya zuwa makaranta domin yin registration ɗin Neco a Ayrah ..... Rana bata ƙarya kamar yadda aka tsara haka ranar sartuday aka gabatar da ɗaurin auren Ahmad M Sarki tare da amaryar sa fadila A sarki, Farinciki a gurin su Maya Ba'a magana ƙawayen amarya kuma ƙannan ango, gashi suma ranar akayi Engagement ɗin ta da farincikin rayuwar ta, Bayan angama biki ranar talata dangin Mami wato Ammi wacce take mahaifiya a gurin Amjad da kuma Abbie wato mahaifin Amjad sai kuma, ƙannan sa Aliyu da kuma farhan, da kuma shi kansa Amjad ɗin suka kama hanyar gida Abuja, A ranar yini Maya tayi jikin ta babu ƙwari kamar wata me jinya saboda rashin ganin, Amjad ɗin, .. Tana zaune a office ɗin ta, hankalin ta yana kan system ɗinta tana typing, akayi nocking ƙofar office ɗin, batare da ta ɗaga kanta ba, ta bada izinin shigowa, Mubeenah ce ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi, ta ƙariso ta zauna, tace" sis dama wannan file ɗin na kawo Miki ki duba". Ta faɗa tare da ajjiye file ɗin akan desk ɗin, ɗagowa Maya tayi ta kalle ta, tace" zan duba amma ba yau ba gaskiya i have alot to do let's keep it till tomorrow". Mubeenah tace "ok Thom shikkenan badamuwa uwar gidan mai girma C.E.O".". Da sauri Maya ta haɗe rai tana watsa mata harara tace "uwar gida kuma amarya ba". Mubeenah tace "mu fa yayan mu bazai zauna da mace ɗaya ba, gara ma kisaka wannan a ranki". Maya tace"wallahi kima daina faɗan haka kar Mala'iku suce Ameen, domin wallahi bazan iya zama da kishiya ba". Mubeenah tace "Hmmm kar dai ki sake jiki dan wallahi namiji bashi da tabbas". Tace "lallai kam kina ruwa". Mubeenah tace "Allah fah mata huɗu yace su aura". Tace"Ni fah zan iya haɗiyar zuciya na mutu saboda kishi". Mubeenah tace "Allah ya yaye Miki". Ta ɗaura da cewa "let me go back to my office "...... AYRAH...... Yau tunda ta tashi takejin zuciyar ta na mugun bugawa, sai addu'a takeyi haka mama ta, tattaro mata kayan ta da na Ma'u da kuma na Tanko duka tace mata ta wanke, tun 9 take wanki har yanzu 3 bata gama wankin ba sallah ne kawai yake ɗagata akan wankin, ko abinci ba taci ba, mama abu da tun ɗazu ta fita, ta shigo ko sallama babu, tana ganin Ayrah, Tace "kan uba lallai yarinyar nan kin cika muguwa har yanzu baki ɗaura mana abincin rana ba so kike ki kashe ni, ni da 'ya'ya na da yunwa ko?". Ayrah tace"mama dama so nake na ƙarisa wankin sai na ɗaura abincin". Mama tace "ƙarya kike munafuka kawai so kike ki kashe mu ni da yara na saboda mugun ta da munafurci irin wanda uwarki ta koya Miki". Tace " mama ni bazan iya kashe mutum....". Ai ko ƙarisawa batayi ba taji sauƙar mari a fuskar ta, "Subhnallahi" tace tare a dafe gurin tace "mama dan Allah koyi hakuri". Mama tace "hakurin ubanki shegiya kawai karuwar banza ni zan faɗi magana ki mayar min". Tace "mama dan Allah kiyi hakuri". Mama abu tace" wallahi ki ma riƙe hakurin ki domin yau zakici ubanki". Tana kaiwa nan ta fara ƙwala kiran Ma'u, Ma'u tana fitowa ta kalle ta, tace " wai mama dan Allah menene kike ta faman ƙwala min kira sai kace mai cutar makanta". Tace " miƙo min muciyar can naci uban yarinyar nan tukunna". Ma'u ta juya zuwa kitchen tana ƙunƙuni tace"yanzu dan Allah baki fini kusa da kitchen ɗin nan ba amma kawai saboda a tashi mutum daga abinda yake yi shine zaki ƙirani". Tana ta gunguni haka taje ta ɗakko ta miƙawa mama Ayrah tana ta bata hakuri amma haka ta riƙe ta da hannu ɗaya ta mata duka, gashi ita kuma bata iya ana dukan ta, ta gudu ba, Bayan mama ta gama dukan ta, ta wuce ɗakin ta tabarta agurin, sosai ayrah take kuka ganin kukan bazai kaita ba, ya saka ta, tashi tana jin jikin ta duk babu daɗi, taje ta hura wuta, ruwan zafi ta juye ta shiga wanka da shi ta ƙara ɗaura wani, Bayan ta fito tana wankin tana girkin, bata gama ba sai 4:30 tana gamawa ta faɗawa mama ta gama tare da wucewa tayi alwala taje ta gabatar da sallar la'asar, Bayan ta idar tagama addu'o inta, ta ɗan kwanta domin tanajin kanta yana mugun sara mata dan haka ta ɗan kwanta, Mamace ta shigo da kwano a hannun ta, ta kalli Ma'u dake faman danne-danne a waya tace "'yar albarka ga abincin naki". Ma'u ta ya mutse fuska tace" shigo ki ajjiye min idan na tashi zanci". Ta shigo ta ajjiye tana kallon Ayrah tace" munafuka ke kam wallahi yau sai dai ki kwana da yunwa dan ubanki". Ayrah tace" mama dan Allah kiyi hakuri ki daure ki bani ko kaɗanne naci wallahi yanzu ma kaina ciyo yake min". Mama tace "wallahi da zaki mutu ma dan kin taimake ni, na huta da maitar ki". Ayrah batace komai ba ta share hawayen da suke bin ƙuncinta, wayar tace tafara wringing, picking tayi tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren yace "Ameen wa alaikissalam Fulani na". Tace "ina yini". Maimakon ya amsa mata sai taji yace "what is wrong with you?". Murmushi ta ƙaƙalo tace" babu komai wallahi yah mufaddhal ". Yace "ok bazaki faɗa min ba kenan sai nazo?". Tace"a'a kaima kasan da akwai da na faɗa maka". Yace"yaushe ƙarya tafara shiga tsakanin mu?" . Tace"I'm serious babu komai". Yace" on my way". Yana faɗan haka ya kashe wayar, Mamaki ne ya rufe ta shi da yake Abuja kuma yace "sai gobe zai zo ya mata sallama saboda jibi zai wuce Madina, kallon agogon wayar tayi taga 4:45 ta ajjiye wayar a gefen ta, ta koma ta kwanta, Nan kuwa bacci ya ɗauke ta sai 5:30 dan haka kawai ta shiga wanka bata daɗeba ta fito ta shirya cikin Abaya blue tayi kyau sosai abinta, kwalli kawai ta saka , ta ɗakko wani half Sunnah fari da Sa'adatu ta siya musu tare, ta saka ta ɗauki wayar ta ta fice daga gidan, ta wuce gidan su Sa'adatu, ..... A ɓangaren Amjad kuwa yana kashe wayar sa, ya kira Aliyu bayan yayi picking yace kamin booking flights yanzu zuwa Kano, Bai jira abinda Aliyu zai faɗa ba ya kashe wayar ya ajjiye, ya tashi ya fara haɗa kayan sa, infew minutes ya gama ya shiryawa, Aliyu ya kirasa ya sanar da shi an samu flight ɗin 5:30 ok yace tare da kashe wayar, Fitowa yayi ya wuce ɓangaren Ammi bakin sa ɗauke da sallama ya tura ƙofar ɗakin ta ya shiga, tana zaune abakin gado tana waya, kallon sa ya saka ta kashe wayar tare da amsa masa sallamar sa cikin fara'a....... ________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______ *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Ma'eesher*✍️ FEATURE WRITERS ASSOCIATION. F.U.W.A 8. ..... Ƙarisa wa yayi, ya zauna a ƙasan carpet tare da gaishe ta, ta amsa, yace "Ammi ni kam zan wuce Kano yanzu inshaa Allah". Tace " ikon Allah bazaka jira Abbie ya dawo ba, ko kuma zaka dawo". Yace "Erh ammie ba daga can zan wuce ba, inshaa Allah gobe zan dawo". Tace" Thom shikkenan Allah ya tsare". Yace "Ameen ya hayyu ya qayyum ammie na" . Ya faɗa yayinda yake fita, Yana fitowa falo ya tadda Aliyu daga alamu shi yake jira, "ka ɗakko min akwatina mu wuce". Ya faɗa yayinda yake ƙarisowa cikin falon, Aliyu baice komai ba ya wuce ya nufi ɓangaren Amjad , Yana tsaye yaji an turo ƙofar falon an shigo bakin ta ɗauke da sallama, zuciyar ta tayi mugun bugawa tana kallon shi, sai kuma ta sunne kai tace" good evening yaaya". Maimakon ya amsa sai kawai yace " from where are you?". Ta sunne kai ƙasa tace"from school". Bai ƙara ce mata komai ba, dan haka ta fara shigowa falon, ɗaga kanta tayi tana kallon Aliyu dake shigowa yana jan akwatin hello king a hannun sa, Murmishi ta sakar masa tace" favorite ina zakaje naganka da akwati?". Yace "banawa bane na yah Amjad ne zai tafi Kano". Tace "favorite dan Allah nima zan raka ku airport ɗin". Yace "ok ki same mu a mota". Shi kam Amjad tuni ya fice ya nufi parking space, ita kuwa farhan autar ammie, school bag ɗin ta kawai ta ajjiye ta ƙara feso turare, ta ɗakko hand bag ɗin ta tana sauri, ta fito ta samesu a parking space tana shiga suka wuce airport........ P.O.V .... AYRAH.. Suna tsaye suna hira ita da Sa'adatu a ƙofar gidan su, sai ga Tanko yazo wucewa ya ƙariso inda suke yace" ke uban mekikeyi a nan gurin?". Banza sukayi da shi kamar basu sanda mutum a gurin ba, ƙarisa yayi gurin cikin masifa yace "ke dan ubanki ba da ke nake magana ba". Ayrah kuwa ganin ya nufo ta yasa ta juya da gudu ta shige gidan su Sa'adatu, Sa'adatu kuwa ta juya ciki tare da rufe ƙofar gidan, Ayrah bata fito daga gidan su Sa'adatu ba sai 6:30 suka fito tare da Sa'adatu suka nufi inda yayi parking ɗin motar sa, yana tsaye jikin motar hannun sa ɗaya na cikin aljihu ɗaya kuma ya kara waya a kunnen sa daga alama waya yakeyi, yana ganin su ya kashe wayar , bakin su ɗauke da sallama suka ƙarisa, ya amsa cikin fara'a , Sa'adatu tace" ina wuni". Yace "lafiya klw alhamdulillah Sa'adatu mun samo ku lafiya". Tace"alhamdulillah" yace "masha Allah yasu mama". Tace "suna lafiya mama tama ce a gaishe ka". Yace"ina amsawa". Tace"to ni zan koma dama na fito ne kawai mu gaisa". Yace "ayya Nagode sosai Sa'adatu". Tare da ciro kuɗi a aljihun sa ya miƙa mata, amma tace" kabarshi wallahi Nagode". Tare da juyawa tabar gurin, a ranta tana ayyana irin kyawun da bawan Allahn nan yake da shi, bayan Sa'adatu ta tafi, Ayrah ta sunkuyar da kanta, tace "ina yini". Yace"ai ni bazan amsa gaisuwar ki ba". Tace"subhnallahi me nayi kuma?". Yace "ɓoyemin damuwar ki mana". Tace"nifa babu abinda yake damuna kawai abbane ya tafi garin da yake aiki kuma kwana biyu yake ya dawo amma yau kwanan sa 4 shiru". Yace" Fulani addu'a kawai zaki dinga masa tare da fatan Allah yasa yana lafiya". Tace"insha Allahu". Yace "amma kin ƙira wayar sa?". Tace"Erh kullum sai na kira amma baya tafiya". Yace" Tom shikkenan ki dage da addu'a mu jira nan da 2 days idan bai dawo ba kije garin ki ɗibo shi". Tace"Thom shikkenan yasu ammie?". Yace"ammie tana nan lafiya". Sun daɗe suna hira kafin daga bisani ya mata sallama tare da bata kuɗi yace "ta kaiwa Sa'adatu". Godiya ta masa ta juya ta tafi, sai da yaga ta shiga gida kafin shima ya juya ya wuce... MAYA...... Tana zaune a falo tana kallo, aka murɗa handle ɗin ƙofar falon aka shigo, jin Muryar dake sallamar ya saka ta saurin ɗago kanta, tana kallon sa babu ko ƙiftawa, sai da ya ƙariso har inda take ya haɗe rai yace" ke baki iya gaisuwa bane?". Ta sunkuyar da kanta tace " ina wuni". Bai kula ta ba ya wuce part ɗin sa, ta shi tayi da sauri ta nufi part ɗin fadila, tana shiga falon taga fadila da mubeenah suna hira da sauri ta ƙarisa ta faɗa jikin mubeenah tana farinciki, kamar kuma wacce ta tuna wani abu nan farincikin ya koma baƙin ciki, fadila ta kalle ta tace"sis lafiya?". Maya kamar zatai kuka tace " lafiya fadila kawai dai yah Amjad ne ya dawo". Mubeenah tace "ai kin banza to shine na baƙinciki da farincikin?". Maya tace "u will never uderstand ". Mubeenah tace" how will I not understand?". Maya tace "jibi zai koma Madina". Fadila tace "hakuri zakiyi ki saki ranki abinda yana dawowa zaku zama husband and his bride daga nan ko ina zai tafi saiki bishi tayi murmushi sai kuma ta miƙe tace "Allah yasa dai kun rage min kunun madara?". Fadila tace "ki duba fridge". Maya bata ƙara cewa komai ba ta tashi ta nufi kitchen,....... Shi kuwa Amjad bai fito ba sai lokacin Isha, ya fito yaje ya gaida Mami daga nan ya wuce part ɗin daddy ya gaishe sa tare suka fita sallar Isha, bayan sun dawo kuwa kamar yadda suka saba suka tsaya a dining, Mami da fadila ne suke fitowa da warmers daga kitchen, bayan sun gama suka zauna can sai ga su mubeenah suka saƙƙo daga upstairs, suma ƙarisowa sukayi suka zauna, fadila ce ta fara gaida Amjad sai kuma su Maya ya amsa batare da ya ɗago ya kalle su ba, bayan sun kammala dinner su mubeenah suka wuce ɗakin su, suna shiga Maya ta ɗauki wayar ta akan bedside drower ta buɗe data,tare da kwanciya akan gadon, ta fara chatting da wata ƙawar su, status ta gani Amjad yayi updating da sauri tayi viewing sai taga addu'a ne, duk da ba chatting suke ba, amma ta masa reply da "Ameen ya hayyu ya qayyum yah Amjad". Tana turawa taga yana online, ta cigaba da chatting ɗin ta, after some mutes taga yayi viewing amma bai mata reply ba, bata ji daɗi ba haka ta, tashi ta shiga bathroom wanka ta ƙarayi tayi brush tare da ɗauro alwala, bayan ta fito ta saka kayan baccin tana ƙoƙarin saka hularta ta kalli mubeenah da take ta waya tun shigowar su, sai kuma ta saka hular ta, ta faɗa kan gado taja duvet ta rufe jikin ta tare da ɗakko wayar ta, ta buɗe data, sai ga massage ɗinsa ya shigo da sauri ta buɗe, ta karanta abinda yace mata bata sanda hawaye suka fara binƙuncin ta ba saboda farinciki, ta share hawayen ta kalli mubeenah dake ƙoƙarin shiga bathroom tace" ya Amjad yace bayan ya tafi da sati ɗaya akwai taron kasuwanci da za'a yi, zamuje Madina mu sameshi". Da sauri mubeenah ta juyo tana kallon ta, tace " Masha Allah, Allah yasa a Dubai za'ayi taron". Tana faɗan haka bata jira me Maya zatace ba ta wuce bathroom, Maya kuwa reply ta masa da Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya, sai kuma ta kashe da datar ta takwanta dan tasan ba lallai ya mata reply ba,..... AYRAH...... Ayrah bayan takaiwa Sa'adatu kuɗin nan mama take sanar mata brothern Sa'adatu Allah ya azurta shi ya siya musu gida a Abuja insha Allahu acikin satin nan zasu koma sosai Ayrah taji babu daɗi sai kuma ta kalli mama tace "to mama Allah sanya alkhairi kice ƙawata za'a zama mutanen Abuja". Sa'adatu tace "wallahi da abbanki zai yadda da mun tafi da ke". Ayrah tace "kema kin san wannan ba abu ne me yiwuwa ba". Sa'adatu tace "kwata-kwata bana farincikin tafiyar nan saboda ke ƙawata". Ayrah tace "amma meyasa yah Adam ɗin bazai bari sai kin rubata Neco ba?". Mama tace "yace acan zai nema mata makaranta ta rubuta daga nan kuma sai ta shiga makarantar gaba da secondary ". Haka nan dai suka sha hira duk suna jin babu daɗi saboda har mama bason yin nisa Ayrah take ba kawai dai babu yanda ta iya ne, sai da suka yi sallar Isha sukaci abinci, sannan Ayrah ta musu sallama tare da fita, ta shigo gida jikin ta babu ƙwari, tana shiga ta samu mama abu zaune a tsakar gida ita da Ma'u suna cin balangu ga 5alive da coke a gefen su, Ma'u ta kalli mama tace" wallahi, kinfiye loma da yawa kawai raba naman nan zamu yi". Mama tace" haba 'yar albarka". Ayrah tayi sallama amma basu kulata ba hakan ya sa ta wuce cikin ɗakin su tai kwanciyar ta, ƙarfe 3 na dare ta tashi tafara gabatar da Sallah ta daɗe akan kwalin ta, tana miƙawa Allah buƙatun ta, Allah yasa duk inda umman ta, take tana cikin hali nagari, Allah yasa Abban ta ma yana cikin ƙoshin lafiya....Washe gari tun da wuri ta tashi ta fara aikin ta saboda Amjad yace mata zai zo, tagama tayi wanka ta shirya , bayan yazo lokacin da zai tafi tasha kuka sosai ya bata kuɗi dayawa sai da ya shiga ya gaida mama kafin ya mata sallama ya fita, bayan ya koma su Maya suka masa rakiya har airport itama tana ta kuka, ji take kamar ta bishi abujan wallahi, amma bazai yiwu ba saboda aikin Company, tunda baya nan tasan yanzu itace on his behalf, ........ Bayan kwana biyu da tafiyar Amjad, ayrah ta shiga damuwa Saboda rabon ta da shi, tun lokacin da ya kira ta yace mata ya ƙariso airport basu ƙara magana ba, bayan yace mata idan ya isa zai kirata amma shiru har yanzu, yau ma kamar kullum tana cikin gida tana shara taji ana sallama daga waje, har zataje sai ga wani yaro ya shigo, haka kawai taji zuciyar ta na tsinkewa, yaron yace wai abokan me gidan ne suna so abasu izinin shigowa tare da me gidan suke, Ayrah tace" kace su shigo". Tana faɗan haka mama ta fito hannun ta da taburma tace jeki shimfiɗa musu, a ƙofar ɗakin Abban ta, ta shimfiɗa musu suka shigo da sallama tunda ta ɗago kai ta kalli Abban su, sai kuma ta tsaya kamar andasa ta agurin with shock, hawaye ne suka fara binƙuncin ta, mama tace"bissimillah ku ƙariso ". Ƙariso wa sukayi suka kwantar da Abban nata da babu abinda yake motsi a jikinsa sai ido, ita kuwa Ayrah banda hawaye ba abinda take , sai kuma ta kalle su tace "ina wunin ku". Sukace" lafiya". Bayan sun gaisa da mama suka sanar mata cewa faɗuwa yayi suna cikin aiki, su ba 'yan garin nan bane kwanan su biyu suna neman garin su kafin aka samu wanda ya sanshi, mama ta musu godiya suka masa fatan Allah ya bashi lafiya tare da ajjiye musu kuɗi dubu 20 akan taburmar suka fice, Ayrah kam ji tayi duniyar ta mata duhu yanzu Abban tane ya dawo haka "innalillahi wa inna alaihi raji'un". Ta furta a bayyane, ta kalli mama tace" mama dan Allah mu kai Abba asibiti". Mama tace "mayya wato kinga kuɗin nan ko to wallahi ko biyar daga ke har ubannaki babu wanda zaici a kuɗin nan". Ayrah ta tsaya tana kallon mama hawaye na bin ƙuncinta........ *🥀BAYAN DUHU🥀* *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Mer'eesher*✍️ FEATURE WRITERS ASSOCIATION... 9...... Mama bayan tagama magana ta kai hannu ta kwashe kuɗin, Ayrah tana zaune a gurin can dai ta miƙe, ta ɗau hijabin ta ta fice, ta nemo maza suka zo suka saka mata Abban a ɗakin sa, ranar haka ta wuni damuwa ta mata waya duniyar gaba ɗaya ta mata zafi, da dare ta fita taje gidan su, Sa'adatu ta sanar mata halin da ake ciki tare suka dawo, tana kallon Abban nata, Sa'adatu tace "sannu Abba Allah ya baka lafiya". Basu sa ran zai basu amsa ba kuma hakan ne tafaru, Sa'adatu ta kalli Ayrah tana jin tausayin ta a zuciyar ta, saboda tasan duk wahalar da take sha yanzun mai sauƙine saboda mahaifin ta yana raye, amma ranar da akace babu ran Abba batasan yadda rayuwar Ayrah zata kasance ba, kamar bazata yi magana ba sai kuma tace "ƙawata gaskiya bai kamata abar Abba haka ba,gobe a kai shi asibiti". Ayrah tace "Nima nayi tunanin nan Sa'adatu Allah ya kaimu goben sai muje". Sa'adatu tace "Ameen Allah ya bashi lafiya". Ayrah ta amsa da "Ameen". Daga haka su ka fice daga ɗakin ta raka Sa'adatu bakin ƙofa sannan ta dawo, ranar a ɗakin Abban nata ta kwana, da asuba ya tashi ya zura mata ido yana kallon ta, tana kwance akan taburma a ƙasan yana ta kallon ta, can ta miƙe tana kallon sa, tace "Abba na maka alwala ne". Ya rufe ido ya buɗe , ta tashi ta fita bata daɗe ba sai gata da buta da baho, haka dai ta lallaɓa ta masa alwalan, sannan ta taimaka masa ta saka pillow a bayan sa ta jinginar da shi, sannan ta fita itama tayo alwala ta dawo ta tada sallah, bayan ta idar ta gyara masa kwanciyar sa , sannan itama ta kwanta, ba'a jima ba bacci ya sace ta, ƙarfe 7:30am ta tashi ta fita, ɗaura abinci bayan ta gama, tayi wanke-wanke tana cikin shara Sa'adatu ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, Ayrah ta amsa mata sallamar tana kallon ta, Sa'adatu tace "sannu da aiki ya jikin Abban?". Ta faɗa yayinda take shiga ɗakin da Abban yake, Ayrah tace "da sauƙi ". Sai kuma ta ajjiye shawarar ta bi bayan Sa'adatu, Sa'adatu ta shiga bakin ta ɗauke da sallama tana ganin Abban tace "Allah ya baka lafiya Abba". Da ido kawai yake kallon ta, amma bazai iya magana ba, Sa'adatu tace" Ayrah kishirya barinje na nemo mana me napep ya kaimu asibitin, Ayrah tace"to ƙawata nagode ". Sa'adatu ta fita daga gidan, bayan wani lokaci ta dawo da me napep, Ayrah taje ƙofar ɗakin mama, tace "mama ga me napep yazo ki fito mu kai Abba asibiti". Mama daga cikin ɗakin tace "kuje kawai zan samo ku". Ayrah bata ƙara ce mata komai ba ta wuce suka tafi ita da Sa'adatu da kuma mama, Basu daɗe ba aka karɓe su a asibitin aka shiga da shi, aka fara dubashi, sukawa suna tsaye suna jira, can likitan ya fito ya kalli mama, yace " ya kuke da marar lafiyan". Mama tace "ƙanwar sace ni wannan kuma 'yar sace". Yace "ku biyun ku sameni a office". Yana faɗan haka yayi wucewar sa, jiki babu ƙwari mama da ayrah suka nufi office ɗin nasa, Ayrah babu abinda da take idan ba addu'a da fatan Allah ya bawa baban ta lafiya ba, Da sallamar su suka shiga office ɗin likita ya amsa musu yana kallon su, da ido yace "mama bissimillah ki zauna". Ya faɗa yana nuna mata kujeran gaban table ɗin, zama tayi ita kuma Ayrah ta tsaya, likita ya nuna mata ɗayar kujeran yace "bissimillah ƙanwata". Zama tayi zuciyar ta cike da fargaba, tace " likita dan Allah meyake damun Abba na?". Yace "sunana Kamal". , Ayrah dai batace komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin hana wayen da suka taru a idon ta zubowa, mama tace "Kamal meyake da munsa". Dr. Kamal yace "abinda nake so da ku, ku kwantar da hankalin ku" Mama tace "likita Meyasa baya magana baya iya motsa jikin sa?". Kamal yace " Ya samu mummunan bugun jini da ya shafi wani muhimmin sashe na ƙwaƙwalwa da ake kira brainstem. Wannan sashen ne ke isar da saƙonni daga ƙwaƙwalwa zuwa sauran sassan jiki ". Mama tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un ,Shin yana jin mu ne ko baya jin mu idan mukayi magana a inda yake?" Kamal Yace "Eh. Yana jin duk abin da kuke faɗa. Yana ganin ku. Yana gane ku. Yana tunani kamar kowane mutum. Amma lalacewar da ta samu ta hana jikinsa amsa umarnin ƙwaƙwalwarsa." Mama tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un ". Ayrah dai tayi shiru takasa magana hawayen da take riƙewa ne suka fara zubowa, ta saka hannun ta, ta share, Mama tace " likita to menene mafita". Likita"Hajiya, a wannan lokaci babu wata mafita guda ɗaya da zan ce idan mun yi ta komai zai daidaita. Amma akwai abin da za mu yi domin mu ba shi damar samun sauƙi. Na farko, za mu ci gaba da ba shi duk magungunan da suka dace. Na biyu, za mu fara masa physiotherapy tun da wuri, domin kada tsokokinsa su daskare. Na uku, za mu tabbatar yana samun abinci mai gina jiki, kuma idan ba zai iya haɗiye ba, za mu riƙa ciyar da shi ta bututun da aka tanadar. Na huɗu, za mu riƙa bibiyar yanayinsa kullum. Idan Allah Ya sa ya fara samun ko da ɗan motsi ko damar magana, za mu ƙara masa wasu nau'ikan jinya". Mama tace "Likita... shin kana nufin haka zai iya kasancewa har ƙarshen rayuwarsa?". Dr. Kamal ya sauke numfashi Yace "Hajiya, akwai yiwuwar hakan. Amma akwai kuma marasa lafiya da suka fara samun sauƙi bayan watanni ko ma shekaru. Ba za mu yanke ƙauna ba, amma ba zan yi miki alkawarin abin da ba na da tabbaci a kanshi ba." Maman tace: "To me za mu yi yanzu?" Dr. Kamal yace"Ku kasance tare da shi. Ku riƙa yi masa magana. Ku yi masa addu'a. Ku ƙarfafa masa gwiwa. Mu kuma a matsayinmu na likitoci za mu yi duk abin da ilimin likitanci ya ba mu damar yi. Sauran kuma muna roƙon Allah, domin Shi ne Mai ba da lafiya." Mama tace" mun gode likita amma kana ga aikin zai ci kamar nawa?". Kamal Yace" banace ba mama amma dai ku ta nadi kamar million 3 zuwa 5 haka". Mama tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un likita wallahi bamu da wannan kuɗaɗen". Likita Yace "aikuwa ya kamata Ku ƙuƙuta ku samu dan yanzu ma zaku fara biyan 100k kuɗin CT scan (computed tomography). Da muka masa sai kuma kuɗin gado 30k ". Mama tace "shikkenan likita mun gode insha Allahu zamuje mu biya a inda ake biya". Ayrah kam tana zaune a gurin ta kasa motsi mamace ta kama hannun ta, suka fita tana janta, hawaye kawai Ayrah takeyi tana bin duk inda mama take janta, a haka har suka ƙariso inda Sa'adatu take zaune ta tafka tagumi, Tana kallo su, ta taso da sauri tayo kansu tana tambayar su, me likitan yace?, Mama ce ta kalle ta, tace " ku zauna da Ayrah barin je na biya kuɗin". Tana faɗan haka ta sake hannun Ayrah, Ayrah ta zauna a gurin hawaye na bin ƙuncinta magan-ga nun likita suna dawo mata kanta, Sa'adatu ta dafata tace "Ayrah kiyi hakuri kinji Abba addu'a yake buƙata ba kuka ba". Ayrah ta ɗago kanta ta kalli Sa'adatu sai kuma ta maida kanta ta haɗa kai da gwuiwa taci gaba da kukanta, Bayan wani wani lokaci likitan yazo ya musu rakiya zuwa ɗakin da Abba yake yanzu, Suka shiga suna kallon su, shima yana ta binsu da kallo, mama tace "sannu Mallam Allah ya baka lafiya ". Su Ayrah suka amsa da "Ameen " Ayrah dai tana zaune a bakin gadon tana ta bin Abba da kallo, shima ɗin ita yake kallo, Suna zaune a haka babu wanda yake yiwa ɗan uwansa magana, sai shiru, sukaji an murɗa handle ɗin ƙofar an shigo, mama abu ce ta shigo ita da Ma'u, Ko kallon inda mama take mama Abu batayi ba, ta wuce ta tsaya akan Abba, saboda wani haushin mama takeji da take taimakon Ayrah, Mama tace "abu har kun ƙariso kenan". Mama Abu tace" Erh" . A ɗaƙile, Mama ta tashi tace " to ni zan wuce Allah ya bashi lafiya". Su Ayrah suka amsa da "Ameen". Mama ta fice tabar Ma'u da mama Abu da kuma su Ayrah da Sa'adatu a ɗakin, Babu wanda ya cewa ɗan uwansa wani abu, suna ta zaune, Ma'u sai kallon banza takeyi wa Sa'adatu, Sa'adatu kuwa ko ajikin ta, dan bata ma san tanayi ba, Nurse ce ta shigo ta kalli Ayrah tace "kije Dr kamal nason ganin ki". Ayrah ta miƙe ta kama hannun Sa'adatu suka fita daga room ɗin, Bayan sun ƙarisa Dr. Kamal ya kalle su yace " lokacin da jinyar nan ta sameshi yana iya cin abinci ne?". Ayrah tace " jiya aka dawo mana da shi a halin da yake ciki, nayi ƙoƙarin bashi kunu ma amma ya gagara sha". Likita Yace " Gara da baki bashi ba, idan da kin bashi saka makon larurar da yake ɗauke da ita, abincin zai iya bin huhun sa ya haifar da wata cutar, saboda haka zamu saka masa NG tube, saboda abinci da magun-guna". Ayrah tace " to shikkenan likita asaka masa kawai". Sa'adatu tace "kuma nawa ne NG tube ɗin?". Yace "15k ne ". Sa'adatu tace" amma gashi ina tunanin mama ta tafi da kuɗin sai dai anjima idan ta dawo". Dr. Kamal yace "karku damu zan je nayi making payment ɗin tunda naga kamar ba wani kuɗine da ku sosai ba". Sa'adatu tace" mun gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ". Yace "Ameen ". Ayrah dai sai kallon sunan da ke kan table ɗin nasa take, tana son tuna a ina ta taɓajin kalan sunan amma ta manta, Dr. KAMAL A SARAKI, cikin sanyin murya tace " mungode". Sai kuma ta, tashi tabi bayan Sa'adatu da ta fara fita..... MAYA....... Cikin ta shin hankali take driving ɗin kana kallon ta zaka san da damuwa kwance a zuciyar ta, a gidan su fadilah ta kutsa hancin motar ta, ko gama gyara parking batayi ba ta fice, ta nufi ɓangaren Hajjah da sauri, tana shiga ta sameta , falo taga Dr. Ahmad yana zaune, tace "yah Ahmad ina Hajjahn kuma ya jikin nata?". Dr. Ahmad yace " ki kwantar da hankalin ki jikin ta da sauƙi tana ciki". Da sauri Maya ta shige bedroom ɗin, ta samu Jaddah tana kwance, fadilah da Mami suna zaune a gefen ta, Maya ta ƙarisa da sallamar ta, ta zauna abakin gadon, tana kallon Mami tace " Mami ya jikin nata?". Mami tace "jiki alhamdulillah". Maya ta kalli Hajjah da tasamu bacci, ta sauƙe ajiyar zuciya tace "Ya hayyu ya ƙayyum kaga halin da Hajjahn mu take ciki Ya Allah ka bayyana mata ɗanta, Ya Allah ka kawo mata ƙarshen wannan jarrabawar da tai shekara da shekaru tana fama da ita". Dukkan su, suka amsa da "Ameen ". Suna zaune a inda take har azahar kafin suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya suna zuwa suyi sallah su dawo, bayan sun idar suka fita zuwa dining domin cin abinci nan ma sai da Mami tayi da gaske kafin fadilah da Maya suka fita zuwa dining ɗin, suka bar Mami agun Hajjah tea kawai Dr. Ahmad ya kawo mata kamar yadda ta buƙata, suna cikin cin abincin, Dr. Kamal da shima da bai daɗe da shigowa gidan ba, ya fita sanye da riga da wando masu taushi da laushi daga alama bayan ya dawo sai da yayi wanka ya fito, yaja kujera kusa da mommy ya zauna , yace "mommy wallahi yau naga wata mai kama da mubeenah a asibiti". Mommy tace "kasan kowa yana da mai kamar sa guda bakwai". Yace " Mami suna kama sosai fah kawai dai ita hasken ta yafi na mubeenah kyau ne kuma ita yarinya ce bata kai mubeenah Shekaru ba". Mommy tace "bata da lafiya ne?". Yace " lafiyar ta ƙalau jinyar baban ta takeyi". Mommy tace "ayya Allah ya bashi lafiya". Yace "Ameen, yawwa ya jikin Hajjah?". Mami tace " da sauƙi har yanzu dai bata farka ba". Yace "Allah sarki Hajjah Allah Ubangiji dai ya bayyana mata ɗan ta nan kusa". Dukkan su suka amsa da "Ameen". Dai dai lokacin Dr. Ahmad ya fito daga ɓangaren Hajjah yana kallon Kamal yace "likita bokan turai har ka dawo kenan". Kamal yace" wallahi fah bro, ya labarin Amjad ne?". Dr. Ahmad yace" up to now he's not picking call". Kamal yace " Allah yasa dai lafiya". Ahmad yace "Ameen".......... AYRAH....... bayan sun idar da sallar la'asar tana zaune akan sallayar da mama takawo musu, tayi nisa cikin tunanin da take, Sa'adatu ta kalle ta, tace " ƙawata ya kamata fa kici abincin nan ko kaɗan ne, tunda cinki ko rashin cinki bashi zai bawa Abba lafiya ba". Ayrah ba tace komai ba ta ɗago ta kalle ta, Sa'adatu ta janyo food flask ɗin da mama ta kawo musu abinci aciki, ta ɗeba a plate ta miƙa mata, tace "dan Allah ki daure kici insha Allahu, Allah zai bawa Abba lafiya ". Ayrah ta amsa abincin tana kallon abincin amma ta gagara ci, Sa'adatu tace "Please ƙawata ki daure kici abincin nan mana". Ayrah ta fara cin abincin badan tana jin daɗin abincin ba kawai ta na turawa ne, kaɗan taci ta miƙawa Sa'adatu plate ɗin, Sa'adatu ta karɓa, ta miƙa pure water guda ɗaya, tasha , Ma'u ta kalli mama Abu tace " nifa nagaji gaskiya mama zan tafi gida". Mama Abu tace "ai Nima nagajin kinsan ba son zaman asibitin nakeyi ba ". Ma'u tace "to ki tashi mu tafi kawai". Mama Abu ta tashi suka tafiyar su, Ayrah ta ɗaga kanta ta kalli Abban ta da har an saka masa NG tube ɗin hawaye na bin ƙuncinta............. ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ *AISHA MUHAMMAD KABIR* *Mer'eesher*✍️ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... 10.......... Sa'adatu ta kalle ta, tace "wai ƙawata Meyasa kuka baya Miki wahala ne?". Ta juya ta kalli Sa'adatu sai kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayen ta, a ranta tace " lallai Sa'adatu bata san abinda take ji ba, Sa'adatu tace "gaskiya baxan zo muna jinya kina sakani a gaba kina min kuka ba da wanne zanji?". Ayrah dai batace da ita komai ba, Sa'adatu ta miƙe tace "barinje gida na ɗebo mana kaya kafin ki gama kukan banzan naki ". Ayrah batace mata komai ba ta sunkuyar da kanta saboda wani nauyi da take ji zuciyar ta, tana mata, Sa'adatu ta kalle ta tace "bayan kaya babu abinda kike buƙata na ɗaukko Miki". A hankali tace " wayata a ɗakin Abban mu akan gado". Sa'adatu tace "to". Tare da ficewa daga room ɗin, tana fita Ayrah ta, tafka uban tagumi a ranta tana addu'ar Allah yasa ya kirata, Sa'adatu bayan me napep ya ajjiye ta, a ƙofar gidan su, ta shiga taga mama tana ta haɗa musu kayan sakawar su a Ghana most go, ta kalli mama tace "mama ba dai yah Adam yaƙi yadda da ɗaga tafiyar nan ba". Mama tace "kwana biyu kawai yace mu ƙara". Sa'adatu tace " mama gaskiya baxan iya tafiya nabar Ayrah a halin da take ciki ba".Mama tace "zan masa magana ya barmu tukunna sai munga jikin Abban ayrahn yayi sauƙi sosai". Tace "yawwa mama Allah yasa ya yadda". Mama tace "amma fa sai dai ki rubuta jarrabawar taki a makarantar ku, dan shi saboda kije ki samu damar rubutawa ne kafin lokaci ya ƙure ya damu mu koma da wuri". Tace " shikkenan mama zan rubuta a makarantar tamu insha Allahu". Mama tace "Tom shikkenan"., Tashi Sa'adatu tayi tace "mama barin yi wanka". Bayan tayi wanka ta fito, vassiline kawai ta shafa ta canza kayan ta zuwa doguwar rigar abayan da Ayrah ta bata, acikin wanda Amjad ya siya mata, batayi wani kwalliya ba, tayi rolling kanta da jersey vail tayi kyau abinta, tace "mama barinje gidan su Ayrah zan ɗakko mata wayar ta". Mama tace "shikkenan kiyi sauri" har zata fita sai ta dawo ta zauna tace "yawwa mama na manta ban faɗa miki ba, kinsan mama Abu da Ma'u tun ɗazu suka baro asibitin wai baza su iya zaman hospital ba". Mama tace "ikon Allah, Allah ya kyauta". Daga haka bata ƙara cewa komai ba, Sanin halin maman ya saka Sa'adatu tashi ta nufi kofar fita daga ɗakin, Da sallamar ta, ta shiga gidan su, Ayrah mama Abu ce ta amsa mata sama-sama, ta ƙarisa ciki, ta samesu, sun baje kaza suna ci, ita da Ma'u ga goru nan, fanta a gefen su, Sa'adatu tace "Barka da hutawa mama". Mama Abu bata kulata ba, dan haka tace "zan ɗaukawa Ayrah wayar ta a ɗaki". Mama tace "gaki ga ɗaku nan ai". Miƙewa Sa'adatu tayi ta nufi ɗakin Abba tagama dubanta amma bata ga waya ba, ta dawo tana kallon Ma'u tace "Ma'u dan Allah kinga wayar Ayrah?". Ma'u tace "halan kin bani ajiya ne". Sa'adatu taja tsaki ta shiga ɗakin su Ayrah amma bata ga waya ba fa duk dubanta, ta fito ko kallon inda suke ba tayi ba, zata fice hatta kai bakin ƙofa, taji Muryar mama tana cewa" ki sanar da ƙawarki gobe dan gin baban Tanko zasu zo neman aurenta, kuma insha allahu ƙanina kawu Audi shi zai bada ita, Wani mummunan faɗuwa gaban Sa'adatu yayi amma ta danne tai wucewar ta, sai da ta fita hawaye suka fara bin idonta, a ranta tana cewa shikkenan za'a ƙarisa rusa rayuwar ƙawarta , Yanzu arasa wanda za'a aura mata Sai Tanko ɗan iska ɓarawo kuma ɗan shaye-shaye, sosai hankalin ta ya tashi, ta shiga gida tana bawa mama labarin abinda ya faru, mama ta kalle ta with shock tace "Innalillahi wa inna alaihi raji'un Allah sarki Ayrah ita kuma ta, ta irin ƙaddarar kenan". Sa'adatu tace " Ya Allah ka dubi rayuwar ƙawata Ya Allah ka cire ta a cikin duhun da take ciki, Ya Allah ka kawo mata haske BAYAN DUHU, hasken da zai canza rayuwar ta daga mummuna izuwa kyakkyawa daga baƙin ciki zuwa farinciki ". Mama tace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, kin ɗakko mata wayar ta, ta ne?". Sa'adatu tace "wallahi mama banga wayar ba, kawai zan je na bata kuɗin napep ta zo ta duba da kanta, mama tace "to shikkenan". Sa'adatu ta miƙe tare da yiwa mama sallama ta fita,.... Zaune yake a ƙasan lallausan carpet ɗin dake falon, ya tattara duk nu nutsuwar sa , Yana yiwa Daddyn nasa bayani tare da fatan Daddyn zai gamsu, sanda ya kai aya, Alhaji Abdullahi saraki, ya kalle shi, yace "Karka damu Kamal insha Allahu zan taimaka musu, amma sai dai daga kai sai shine zaku tafi kaci gaba da kula da rayuwar shi, tunda kace daga shi sai 'yar sa ne, amma bazan bari ka tafi da kai da ita jinyar sa ba, duk da na yadda da kai Kamal amma zuciya bata da ƙashi, kuma shaiɗan yana ko ina". Kamal yace "Nagode sosai daddy Allah ya ƙara arziki da nisan kwana kuma insha Allahu zan musu bayani idan na koma asibitin". Alhaji Abdullahi yace "Ameen Ya Allah, amma wace ƙasa zaku je". Kamal yace "Egypt saboda suna da kwararrun likitoci". Alhaji Abdullahi saraki yace "babu damuwa ka fara shirya muku tafiyar , Allah ya bashi lafiya". Kamal yace "Ameen". Tare da ƙarayiwa Alhaji Abdullahi saraki godiya sannan ya masa sallama ya fito daga ɓangaren nasa saboda komawa asibitin, Tunda ta fito take tafiya tana tunane-tunane zuciyar ta, ta kasa nutsuwa da bada auren Ayrah da za'a bada a wannan ɗan iskan, gashi ta kasa samun abun hawa, wata baƙar mota ce tayi parking dai-dai inda take tsaye, ya sauƙe glass ɗin motar yana kallon ta, yace " mallama ina zuwa haka?". Tayi murmishi tace "zan koma hosital ne". Yace "bissimillah ki shigo mutafi nima can na nufa amma zaki biyani". Tace "badamuwa ". Tare da zagaya wa ta buɗe front seat ta zauna, Ya tada motar, ya juya ya kalleta yace "I'm sorry na manta ban tambayi sunan mallamar ba". Tace "sunana Sa'adatu". Yace "Masha Allah, Ni kuma sunana .......,". Tace "Dr kamal ". Murmishi ya sakar mata ya na maida hankalinsa kan driving ɗin da yake yi, yace "how do you know?". Tace "a office ɗin ka mana nagani". Yace "ohhh haka fa, Mahaifin kune ba lafiya". Tace "Erh kusan mahaifi yake a gareni". Yace "ok ". Daga nan babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana har suka isa hospital ɗin, ta fita tare da masa godiya ta wuce, bayan ya sanar da ita yana buƙatar kallon mama, ........ Da sallamar ta, ta shiga ɗakin da Ayrah suke, ta samu Ayrah zaune a inda take, kallon ta, tayi tace "kaddai tunda na tafi baki tashi ba, Ayrah tace "na tashi nayi sallah, ina wayar tawa?". Nan da Sa'adatu take sanar mata wallahi bata ga wayar ta, ta ba, tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un ". Sa'adatu tace "amma ga kuɗin mashin kije ki duba, daga nan sai ku tafo da mama likita yana buƙatar ganin ta". Ayrah tace "to" tare da miƙewa ta amshi kuɗin ta fita, *MADINA* Wata datijuwar mata ce, ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama, ya ɗaga kai ya kalle ta, tare da amsa mata sallamar, sai kuma Yace " Jaddah ya jikin Amjad ɗin, tace "alhamdulillah da sauƙi, inajin anjima ma za'a sallamo shi". Yace "Allah ya ƙara lafiya". Tace "Ameen " Yace "Jaddah baki ga yadda hankalina ya tashi ba lokacin da kika kirani, irin wannan jinya lokaci daya haka kamar mutum zai mutu". Jaddah tace "wallahi Nima na tsoruta shiyasa na kiraka ban kira 'yan Nigeria ba, saboda kar hankalin su, ya tashi gara kai tunda soja ne, kana da taurin zuciya". Dariya maganar ta , ta bashi ya tsaya yana kallon ta yana dariya sai kuma Yace " Lallai Jaddah wato ance Miki mu sojoji bama da imani da tausayi ko?". Tace "ban sani ba". Yayinda take wucewa ɗakin ta, Yace "haba Masoyiyar Yanzu fushi kikayi da ni?". Tace "Masoyiyar ka tana can Nigeria wato hajjah". Daga nan bai ƙara ce mata komai ba ya maida hankalin sa kan kallon da yake yi, bai fi minti biyu ba, agurin ya miƙe, ya ɗau wayar sa, ya fice, ya ɗauki mota, A hankali yake driving ɗin sa cikin nutsuwa, har ya isa wani makeken hospital dake garin Madina, fita yayi ya shiga asibitin, direct ɗakin da Amjad yake ya shiga, ya sameshi a zaune a bakin gado, sai faman dailing number yake amma baya shiga, bayan yayi sallama ya amsa,kallon sa yayi Yace "good morning bro". Yace "morning ya jikin naka". Yace "alhamdulillah". Yace "to Allah ya baka lafiya". Yace "Ameen". Shiru ya biyo baya, can Amjad Yace "yaushe zaka koma Nigeria?". Yace "may be next week". Amjad yace "amma zaka je gida ko?". Yace "dama a jeji nake?". No ba Abuja ba, i mean Kano, kasan fa Hajjah bata da lafiya ". Yace "ok zanje insha allahu, daga nan shiru ya biyo baya, babu wanda ya ƙarayiwa ɗan uwansa magana kowa hankalin sa nakan wayar sa, har likita ya zo ya salllamesu suka kama hanyar gida,....... *AYRAH*..... Ko da taje gida ta gama duba, duben ta amma bata ga wayar ba, haka ta hakura ta fito ta sanar wa da Mama Abu likita yana buƙatar ganin su ita da mama, mama Abu tace suyi gaba tana zuwa, bayan ta fita, Mama Abu ta kalli Ma'u tace " nifa bazan jeba dan wallahi bazan iya jinyar kashi da fitsarin ƙato ba". Ma'u tace "ki daure kije mama may be zai ce muku ya kusa mutuwa ne". Mama Abu tace"ai kuwa da na huta wallahi ". Daga haka ta shige ɗaki ta ɗakko gyalen ta, ta nufi, ƙofar fita,...... Da mama da mama Abu zaune suke akan kujera, bayan ya gama musu bayani, mama Abu tace "babu komai likita sai a fitar da shi ɗin, mungode sosai Allah ya saka muku da alkhairi". Dukkan su suka amsa da "Ameen". Mama dai bata so a kai gaggawar amsa wa ba duk da hankalin ta ya kwanta da tafiyar bayan sun fito sai da ta kira ɗan ta Adam take faɗa masa Yace "badamuwa Mama babban yayan likitan abokina ne, dama su da mahaifinsu suna haka, kawai kubar shi ya tafi da shi". Tace "to shikkenan". Taje tayiwa su Ayrah bayani duk Ayrah taji daɗin tafiyar but in one side tanajin zatai kewar Abban ta sosai, .... Bayan an gama komai jirgin su Abba ya daga zuwa Egypt, mama da Sa'adatu da Ayrah suka dawo gida, sosai Ayrah take kuka suna rarrashin ta ranar a gidan su, Sa'adatu ta kwana , washe gari Yah Adam ya turo mota , bayan sun fito da kayan su, Ayrah dai tana tsaye jikin motar sai kuka takeyi, Mama ta kalle ta bayan driver ya gama saka kayan a mota, tace "kiyi hakuri Ayrah ai tafiya ba mutuwa bace insha Allahu wataran Allah zai haɗa fuskokin mu fatan mu dai Allah ya bawa Abban ki lafiya". Sa'adatu da yanzu ta fito, bayan ta , rufe gidan ta ƙariso jikin motar, itama idanuwanta sun kumbura kana kallon ta zaka san tayi kuka sosai, kallon Ayrah tayi tace "bestie wai ke Meyasa kuka baya Miki wahala ne ?". Tayi maganar tana sunkuyar da kanta, saboda hawayen da suka cika mata ido, Ayrah a hankali cikin kuka tace "bestie nagode, nagode sosai da kulawar ki agareni Nagode da duk abubuwan alkhairi ki a gareni bazan taɓa mantawa da ku ba, ke da mama a rayuwa ta, saboda kuka zamemin bangon da zan jingina , kuma inuwar da zan shiga bayan na rasa mahaifiya ta, Allah ya saka muku da alkhairi kuma ya kaiku lafiya". Sa'adatu da ta rasa abin faɗa kawai ta rungume Ayrah ta fashe da kuka, Mama ma hawayen takeyi hakan ya saka ta saurin buɗe motar ta shiga, a hankali Ayrah ta zame jikin ta daga na Sa'adatu hannun su riƙe da na, juna tace "bestie ku tafi kar na ɓata muku lokaci". Ta faɗa tana share hawayen da yake gangaro mata, ta zame hannun ta daga na Sa'adatu ta juya ta fara tafiya, da sauri Sa'adatu ta ƙarisa ta janyo ta, tare da rungume ta, tana kuka mai sauti, itama Ayrah kuka takeyi sosai, ka fin ta zame jikin ta a hankali tace "Allah ya tsare". Sai kuma ta juya, tana share hawayen idonta, ita ma sa'adatu juyawa tayi tana kuka har ta ƙarisa ta shiga cikin motar ta sauƙe glass tana kallon Ayrah, jin tashin motar ya saka Ayrah juyowa da sauri tana kallon su, Sa'adatu tana hawaye tana ɗaga mata hannu, agurin Ayrah ta zube tana kuka, har motar su, ta ɓacewa ganin ta, ta fi minti 3 agurin tana kuka kafin daga bisani ta miƙe, ta nufi gida hannun ta riƙe da jakar da mama ta bata jiya, ta shiga bakin ta ɗauke da sallama babu kowa a tsakar gidan sai uban datti gidan kamar wanda yayi shekara ba ayi shara, ta wuce tana kallon uban tarin wanke-wanke shima, tana zuwa ta zube a ɗakin tana sake sabon kuka, ta buɗe jakar da mama ta bata, taga kayan Sa'adatu ne kala 5 aciki da hijabai, sai kuma kuɗi dubu 20, da ido take kallon kayan hawaye na bin ƙuncinta, kafin daga baya tasaka jakar acikin Ghana most go ɗin ta, ta kwanta agurin tana kuka har bacci ya ɗauke ta......... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* 11........ Bayan kwana biyu da tafiyar su, Sa'adatu ta, Ayrah ta rame, saboda ayyukan gidan nan da tunanin halin da Abban ta yake ciki, kullum cikin addu'a take da fatan Allah ya bashi lafiya, kullum cikin kewar Sa'adatu da mama take sometimes takan sha kuka idan ta tuna su, gashi yanzu bata da waya ballantana taji daga garesu,...... MAYA.... Tunda yah Ammar ya kira yace" su je Madina su sameshi ita da mubeenah, jikin ta yayi sanyi, babu abinda bata kawo a ranta ba, mubeenah kam babu abinda ta kawo a ranta sai murna take ji, tana fatan Allah yasa a Dubai zasu yi taron kasuwancin nasu, haka suka fito suna jan akwati nan su, a falo suka ajjiye akwati nan suka wuce ɓangaren Mami suna shiga, suka sameta a falo tana kallo, ƙarisa wa sukayi suka gaisheta, ta amsa da fara'a tace "har kun shirya kenan". Mubeenah tace "erh Mami". Mami tace "Masha Allah, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya". Dukkan su, suka amsa da "Ameen". Mami tace "ai munyi waya da Amjad ɗin ma Yace taron na ku, sai after 5 days, amma dai ku tafi yanzu saboda wasu dalilai,". Sosai Maya taji hankalin ta ya kwanta, jin anyi waya da Amjad, bata san sau nawa ta kira shi ba, amma baya picking, mubeenah tace"Mami Allah yasa a Dubai za'ayi taron". Mami tayi dariya tace "Ni kam mubeenah wani yaji kina maganar nan ai sai yayi tunanin baki taɓa zuwa, Dubai ɗin ba". Tace " Mami Allah ina son ƙasar ne sosai". Mami tace "to Allah ya baki mijin da zaku zauna da shi a Dubai ɗin". Tace "Ameen Mami nah". Maya tayi sauri tace "Mami ai ɗan kine ma, mijin baki sani ba". Da sauri mubeenah ta juyo tana kallon ta, Mami tace "to ɗana kuma ko dai Aliyu?". Mubeenah ta tashi ta fice daga falon tana hararan Maya, Mami tayi farinciki sosai da jin wannan labarin 'yar mijin nata, da ɗan yayan ta take soyayya, Mubeenah na fitowa taga Aliyu zaune a falo yana danna wayarsa, da sauri ta ƙarisa ta zauna tana kallon sa tace " Meyasa baka faɗa min zaka zo ba, bayan ɗazu ma sai da mukayi waya?". Ya ɗaga kai ya kalle ta sai kuma ya maida wayar aljihun sa, yace "The happiness I saw on your face is exactly why I decided to surprise you." Har zata yi magana sai ga Ahmad da fadila sun shigo falon sai baza ƙamshi suke yi, Aliyu yace "good morning bro". Ahmad yace "morning Aliyu yanzu nake tunanin kiranka ashe ma ka ƙariso". Mami ce ta fito tare da Maya, da sauri mubeenah ta, tashi daga gefen Aliyu da take zaune tana sunne kai, Mami tayi murmishi tace "Aliyu ashe ka ƙariso?". Yace "Erh Mami ". Tace "ya ka baro su ammien da farhan?". Yace " suna lafiya". Ahmad yace "Mami zamu tafi saboda saura 30 minutes flights ɗin su ya tashi, Mami ta kalle su tace "to Allah ya tsare a gaishe min da Jiddah da Ammar da sauran mutanen gidan". Aliyu Yace" insha Allahu zan suji". Mami taita musu addu'a tare da musu sallama suka wuce, Ahmad ne ke driving sai Aliyu a front seat, su kuma matan suna baya, suka nufi airport,..... AYRAH..... Yauma kamar kullum tana wanki tsakar gida, Tanko ya shigo ko sallama babu kallon ta yayi yana wani irin murmishi ɗago kanta, tayi ta kalle shi, sai kuma ta sunkuya taci gaba da wankin ta, Yace "ke dan ubanki baki iya gaisuwa bane?". Tace "ina wuni". A taƙaice, Yace" lafiya an faɗa maki, an bani auren ki?". Dammm zuciyar ta, tai mugun bugawa da sauri ta ɗago ta kalle shi, idon ta na tara ƙwallah, tace "wa ya baka aure na?". Yace "kaji 'yar rainin hankali ni kike tambaya?". Sosai taji hankalin ta ya tashi, ta kasa magana, tasa hannu ta share hawayen da yake zubo mata, ta ci gaba da wankin ta, Tanko ya kalle ta ya kwashe da dariyar mugun ta, yace "au kuka ma kike?, ai baki ma yi kuka ba yarinya sai an daura mana aure nan da wata ɗaya". Wai nan da wata ɗaya, Mafi ce ta fito daga ɗaki, ta kalle su tace "kaga angon wata ɗaya da amaryar wata ɗaya ". Tanko yace "sa'adai ƙanwata". Ma'u tace " Ni dai idan ka amince da abubuwan da na faɗa maka, komai kake so zan maka a auren nan". Yace "darrr ƙanwata ai ko mutum kika saka na kashe Miki sai na miƙa miki shi lahira indai bukata ta zata biya akan wannan yarinyar". Ma'u ta kalle shi tace" sai da kai ɗan uwana". Daga haka ta koma ɗakin su". "Aure nan da wata ɗaya kuma da Tanko, kuma menene Ma'u ta shirya masa danna san abin dole yana da nasaba da ni". Da Ayrah tayiwa kanta tambayar da bata da also shinsu, a ranta tana fatan Allah ya kar ya bawa su mama Abu iko akan ta, domin wallahi bazata iya zama da Tanko ba, ......... MAYA....... Bayan sun sauƙa a garin Madina Ammar da kansa ya zo ya ɗauke su, a airport, zuwa gidan jaddah, da sallamar su suka shiga, wata kyakkyawar budurwa tana zaune a falon ta ɗaura ƙafar ta ɗaya akan ɗaya sai faman jijjiga ƙafar take, hannun ta ɗaya ɗauke da remote tana kallo, sosai Maya taji jikin ta yayi sanyin saka makon kallon budurwar da tayi, har suka ƙarisa falon budurwar ko ɗagowa kanta batayi ba, ballan tana tasan da mutane a falon, Mubeenah tace "ikon Allah Nailah wai bakiji sallamar mu bane?". Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalli Mubeenah, tace "wa alaikissalam". Daga nan ta maida kallon ta kan TV, su kam wucewa sukayi ɗakin da suke sauƙa idan sun zo Madina wanda itama Nailah a nan ta sauƙa, bayan sunyi wanka sun gabatar da sallolin su, suka fito suka nufi ɓangaren Jaddah, a falo suka samu nailah tana kwance akan cinyar Jaddah, tana kallon su ta haɗe rai, Jaddah tace"Masha Allah Maya har kun ƙariso kenan?". Maya tana murmushi tace "erh Jaddah tun ɗazu ma". Jaddah tace "to sannu ku da zuwa". Mubeenah tace"sannu Jaddah". yayinda take zama agefen Jaddah, Maya ta kalli Jaddah tace "yanzu ke baiwar Allah haka ake tarban baƙi?". Mubeenah tace "ƙyaleta dai tabarmu ko ruwa bata bamu ba". Jaddah tace"lallai yaran nan, yaushe dama kuka zama baƙi a gidan nan ban sani ba?". Maya tace "to ni dai yunwa nake ji". Jaddah tace "kuje ku kira Ammar da Amjad su fito muyi dinner". Maya tace "to". Ta miƙe ta fita, Mubeenah tabi bayan ta, suna fita, ta kalli Mubeenah tace "dan Allah kije ki kira yah Ammar kinga ni ba shiri nake da shi ba". Mubeenah tace "Madam faɗi gaskiya dai, ke dai kawai kina so ki kira masoyin ki". Maya tace "idan nayi hakan ma ai banyi laifi ba". Mubeenah taje ɗakin Ammar ta kai 3 minutes tana knocking kafin ya buɗe, yana kallon ta yace "what's up?". Tace "dinner is ready". Bai ce mata komai ba ya rufe ƙofar, ta juya tana tafiya, tana dana sanin biyewa Maya da tayi tazo kiran wannan bawan Allahn, a haka suka ƙarisa dining bayan sun, gama dinner, kowa ya tashi ya rage daga Maya sai Mubeenah, Mubeenah ta kalli Maya tace "wallahi yah Ammar ɗin nan haushi yake bani sai shegen miskilan ci da iyayi". Maya tace"meya faru?". Mubeenah tace "wai fah da naje sai da nayi jiran 3 minutes kafin ya buɗe, yana buɗewa wai what's up". Maya bata san lokacin da ta fara dariya ba tace " ikon Allah". Mubeenah tace "wannan cankalkalar Kuma a hakan wai Yah Amjad take so, shiyasa take mana wannan iyayin". Maya dai bata ƙara ce mata komai ba, haka har suka gama suka wuce bedroom ɗin su, haka a kai su kai zaman 5 days ɗin su, suka wuce Dubai ɗin su, one week sukayi a Dubai daga nan suka wuce Nigeria, amma banda Amjad shi kam, Madina ya koma, Su Maya a Abuja suka sauƙa gidan ammie, zo kaga farinciki agun farhan kamar ta mai da su ciki, Maya tana zaune a falo tana kallo ita da farhan, Mubeenah da ammie kuma suna kitchen suna girki, Maya ta kalli farhan tace "kunyi waya da yah Amjad ɗin ne?". Farhan tace "erh munyi waya yace next week insha Allahu zai dawo ko upper week ". Maya tace "Allah ya dawo da shi lafiya". Dai-dai lokacin Ammar ya shigo falon hannun sa riƙe da laptop ya zauna with out looking at them, Maya tace "good evening bro". "Evening". Yace a ta ƙaice, still bai ɗago kansa ba yana danna system ɗin sa, yace " farhan make coffee for me". Farhan ta miƙe ta nufi kitchen, aka bar shi daga shi sai Maya hankalin ta yana kan TV, hannu ya saka ya ɗauki remote tare da canza channel ɗin ya mai dashi zuwa channel ɗin kwallo, ta daga kai ta kalle shi kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta miƙe ta nufi kitchen itama, Tana shiga farhan ta kalle ta, tace " ya canza channel ko?". Maya tace "how do you know?". Farhan tace "to ai kullum haka yake, idan yana gidan nan kwata-kwata bana da sukuni har gara yah Amjad sau dubu ɗari, shifa ko magana ba yayi sai dai make coffee for me,". Ammie tace "nifa ku daina gulmar ɗana". Maya dai bata ce komai ba ta fice ta koma ɗakin farhan, ....... AYRAH....... Babu ƙiftawa take kallon Sa'adatu da mugun mamaki, ta sa hannu ta share hawayen ta, tace "Sa'adatu ba gaskiya kikaji ba wallahi Abbana bai rasu ba, Sa'adatu ta saka hannu ta kama Ayrah cikin kuka tace "Ayrah kiyi hakuri amma ko da zasu shigo jirgin sai da ya sanar min, wallahi Ayrah jirgin su abbane ne ya ƙone kuma babu wanda yayi rai acikin jirgin, da sauri Ayrah ta janye jikin ta, daga na Sa'adatu ta kama hanyar fita, da sauri Sa'adatu tabi bayan ta, tana tsaida napep Sa'adatu tai sauri ta shige, a asibiti aka ajjiye su, Sa'adatu ce tabiya me napep ɗin, sannan ta shige ciki ta shige, a reception ta tsaya tana kallon nurse ɗin da taga sunfi kusa da DR Kamal tace "dan Allah sis ki faɗa min gaskiya da gaske, Abbana da Dr kamal sun rasu, nurse Zainab ta ɗago idanuwan ta da duk sun kumbura saboda kuka, tace "kiyi hakuri Ayrah addu'a suke buƙata ba komai ba". Ayrah ji tayi jin ta ya ɗauke ganin ta ma ya fara ɗauke wa, su Sa'adatu basu ankara ba, suka ga ta faɗi a gurin......... Idan kun gama karantawa ku kasance BAYAN DUHU DISCUSSION FORUM 📚, domin comments, ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 12...... ***** A hankali ta buɗe idonta ta sauƙe shi akan Sa'adatu sai kuma ta mai da kallon ta kan drip ɗin da aka saka mata, ta maida kallon ta kan Sa'adatu dake zaune a bakin gadon tace "dan Allah Sa'adatu kice min Abbana bai rasu ba kinji, kice min Abbana yana da ransa kinji". Sa'adatu bata ce mata komai ba ta, tashi ta fice daga ɗakin, saboda bata so Ayrah ta kalli hawayen da take ɓoyewa, tana fita mama tana shigowa, mama ta zauna a agefen gadon tana kallon Ayrah, tace"sannu Ayrah Ya jikin naki". Tace "mama kema kin yadda Abbana ya rasu kenan?". Mama tace "kiyi hakuri Ayrah yanzu Abban ki babu abinda yake buƙata sama da addu'ar ki". Kallon mama take babu ko ƙiftawa tana jin zuciyar ta, tana ta wani irin nauyi, she wish zata iya kuka ko zataji sauƙin abinda take ji aranta, mama tace "kiyi hakuri, ke musulmace ya kamata ki yadda da ƙaddara kyakkyawa ko mummuna, wannan ba komai bane sai jarrabawa kuma muna Miki fatan ki cinye ta ɗari nisa ɗari". Ayrah ta rufe idon ta kawai ta juya, tanajin maganga nun mama yana mata yawo a kanta, ganin ta rufe idonta mama bata ƙara ce mata komai ba tayi shiru, a rufe idon da tayi har bacci ya ɗauke ta,..... *MAYA* Tana zaune a falo, kana ganin ta zaka gane baƙara min kuka tayi ba, fadilah na zaune a gefen ta itama ta zuba uban ta gumi, Dr. Ahmad ne ya shigo ya kallesu, yace "Ni kam ban san sau nawa zan muku magana ba a gidan nan, kullum cikin kuka da tagumi kuke, kuma ana muku magana sai kuce kaunar Kamal kuke, wannan ba ƙauna bace, babu ƙaunar da zaku nunawa Kamal da ya wuce ku masa addu'a, anjima zamu wuce inda jirgin ya kone ni da su daddy". Maya ta ɗaga kai ta kalleshi tace " kayi hakuri yah Ahmad Insha Allahu, bazamu ƙara kuka ba,". Yace "Yawwa Allah ya Muku albarka". Fadilah dai ta kasa cewa komai, dan maganar da suke yi ma yanzu Allah ka ɗai yasan koƙarin da take gurin hana hawayen ta zubowa, A ɓangaren mommy kuwa, ammie da Mami ba ƙaramin ƙoƙari sosai suke yi ba,wajen ganin sun rarrashe ta, duka a hali biyun baƙara min tashin hankali suka shiga ba, wato alhalin QURAISH da ahalin SARAKI,......... *AYRAH*...... Kwanan ta biyu a asibiti aka sallame ta, har yanzu Allah bai bata ikon yin kuka ba, Yau ma tana zaune a tsakar gida ita da mama da Sa'adatu Mama Abu kuma suna ɗaki ita da Ma'u, Sa'adatu ta kalle ta tace" ƙawata Insha Allahu gobe zamu koma". Ayrah ta ɗago kanta tana kallon Sa'adatu sai a lokacin ta samu damar yin kuka, tace "wai yanzu shikkenan Abbana ya rasu ya barni kamar yadda ummi ta tafi ta barni?". Mama ta janyo ta jikin ta, tace"kiyi hakuri Ayrah Insha Allahu ummin ki tana raye kuma Insha Allahu wataran Allah zai haɗa fuskokin ku". Sosai Ayrah ta fashe da kuka, tace "rayuwa ta bata da amfani idan babu Ummi kuma babu Abba, ina ma Allah ya ɗauki raina na huta da wannan mummunar ƙaddarar". Tana kaiwa nan ta fashe da kuka sosai, mama ta rungume ta amma ita ma ta kasa ce mata komai Saboda bata son hawayen da take ɓoyewa ya zubo, Sa'adatu ce tai ƙarfin halin cewa Ayrah ki daina faɗan haka dan Allah, bai dace dan Allah ya jarabce ki, ki dinga faɗan haka ba". Bata cewa Sa'adatu komai ba haka taci gaba da kukan ta, suma basu hanata ba, domin idan tayi zata rage jin wani abun da takeji...... *BAYAN WANI LOKACI*...... **** Ayrah duk da ta ɗan warware amma har yanzu kana kallon ta zaka san tana cikin damuwa, mutanen sabuwar unguwar da suka dawo kowa ya shigo gidan mama kawai, ma'u da Tanko take cewa 'ya'yan ta, ita kuma Ayrah tace mai aikin ta ne, Yauma kamar kullum tana zaune a tsakar gida tayi nisa cikin tunanin da take ciki, Tanko ya banko ƙofa ya shigo ko sallama babu yana kallon ta, sau ɗaya ta kalle shi ta ɗage kai, tace "ina wuni". Yace "lafiya amarya". Sai kuma ya maida kallon sa kan mama da Ma'u da suke zaune a gefe suna hirar su, Yace "mama wai ya labarin aurena da yarinyar nan ne, Erh naji batu yayi shiru, wallahi Allah". Mama tace "Karka damu Tanko yaushe kake so a Daura muku auren?". Yace " ko gobe ma ni banƙi a ɗaura ba mama ". Mama tace "zan samu kawun ku da dangin baban ka, na musu magana tunda wanda ya mutu ba dawowa zai yi ba, gara kawai ranar juma'a a ɗaura muku aure". Hawaye ne ya zubo a idon ayrah ta saka hannu ta share a ranta tana fatan Allah kar ya tabbatar mata da auren nan, Ma'u tace "ga munafuka kuka take". Mama tace "to ai ko zata haɗiyi rai ta mutu babu abinda zai hana auren nan". Ma'u tace "Yanzu sai tace ita bata son ɗan uwana ko ? Bayan rufa mata asiri zai yi ya aure ta, tunda ta gama wayon karuwancin ta ba mashinshi ni ". Ayrah dai batace musu komai ba ta, tashi ta shige ɗaki, tana ta tunani ta ina zata fara dan wallahi ko zata mutu bazata auri Tanko ba, ....... *MAYA*....... Suma izuwa yanzu sun hakura sun barwa Allah komai sai dai ba dare ba rana suna addu'a a Kamal da marar lafiyar da ya tafi da shi, kamar yadda Ayrah itama take yi, Tana tsaye a jikin wardrobe tana jera kayan ta, Mubeenah ta shigo da saurin ta, tana kallon Maya tace "sis can you guess what?". Maya ta juyo tana kallon ta, tace "i can't". Sai kuma ta juya taci gaba da abinda take, Mubeenah tace "Yah Amjad ya dawo". Da sauri Maya ta juyo tana kallon Mubeenah tace "are you serious?". Mubeenah tace" You can go and see for yourself ". da sauri Maya ta fice daga ɗakin tana fatan Allah yasa ba tsokanar ta Mubeenah takeyi ba, tana fita ta sameshi a zaune a falo yana kallon ball duk da hankalin shi, baya kan TVn kawai idanuwansa ne suke kai shi bai ma san abinda suke cewa ba, ta daɗe tana kallon sa kafin ta ƙarisa tace "ina wuni yah Amjad". Yace "lafiya". A taƙaice, kitchen ta wuce ta fara haɗa masa kunun madara saboda tasan ya naso, kafin ta fito har ya tashi ya tafi ɓangaren sa,..... Suna zaune a farlo shi da Dr. Ahmad, Dr. Ahmad ya kalle shi, Yace" wai dama da gaske kake kana son yarinyar nan wallahi i thought wasa kake yi". Amjad dai ya kalle shi, baice masa komai ba, yaci gaba da danna system ɗin da yake yi, Dr Ahmad yace "dan Allah ka cirewa kanka damuwa, dan mun rasa inda yarinyar nan take ba yana nufin mun rasa ta har abada bane". Amjad ya ɗago kai ya kalle shi, yace "amma ai ban san halin da take ciki ba". Dr. Ahmad yace " nifa ina mamaki yadda ka damu da rashin samun yarinyar nan". Amjad bai ce masa komai ba, Dr. Ahmad yace " mubarshi a kasamu yarinyar nan ta ina zaka fara gabatar da ita a matsayin kana so ka aure ta bayan kasan Maya tana sonka, kuma da baikonka a kanta". Amjad Yace " I don't know". ......... Bayan ta haɗa kunun madaran ta, ta saka a jug mai kyau ta ɗaura akan plate mai ɗan girma ta haɗa da cups guda biyu, ta ɗauka ta nufi hanyar ɓangaren sa, tana tafiya zuciyar ta, cike da tunane-tunane sai tayi karo da mutum, kunun duka ya zube a jikin sa da mugun mamaki da haushi lokaci guda ya ɗago yana kallon ta, zuciyar ta tayi mugun bugawa bayan ta ɗaga kai ta kalle shi, a zuciyar tace "na shiga uku, Yah Ammar". *AYRAH* Ayrah bata tashi shiga damuwa ba sai ranar Alhamis da taga mama abu na ta, shirin auren su, sosai hankalin ta ya tashi tarasa abin yi, wai Ma'u ce da babu abinda da ta iya zata mata lalle a matsayin ta, na wacce za'a aurar gobe, tace ita kam ba sai an mata lalle ba haka suka barta, tana kwance a ɗaki da dare tana tunani, hawaye na bin ƙuncinta tace "ummi ina kika shiga kika barni za'a lalata min rayuwata a saka ni acikin duhun da ban san ranar fitowa ba". A ranta tace "Allah sarki ni Ayrah yanzu daga gobe rayuwa ta, ta ƙare, duk wani mafarki na da yah mufaddhal ya yazo ƙarshe,". Cikin kuka taci gaba da cewa " Yah mufaddhal bazan iya rayuwa da wanin ka ba, duk tsanani duk wahala sonka bazai bar zuciya ta ba, ko ƙaddara ta ƙaddara aurena da Tanko to gangar jikina kawai zai aura amma zuciyata tana tare da kai,ina fatan watarana Allah ya haɗa fuskokin mu, ina fatan mu rayu cikin inuwa ɗaya a matsayin ma'aurata,". Ita ka ɗai take magana kamar mahaukaciya, ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 13...... Cikin ɓacin rai yace "baki da hankali ko?, ina tunanin ki ya tafi da zaki ɓata min jiki". Ita dai tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana hawaye, Yace "ba da ke nake magana ba?". Tace "I'm sorry Yah Ammar". Kallon ta yayi daga sama har ƙasa sai kuma yayi ƙwafa ya juya, i tama ta juya ta koma ɗakin su, Mubeenah ta ɗago kai tana kallon ta, tace "sister lafiya". Maya ta kalle ta, tace" wannan Yah Ammar ɗinne mana". Mubeenah tace "me ya Miki?". Maya tace "wai ban sani ba, zan kaiwa Yah Amjad kunun madara kawai ya bige ni abun ya zube a jikin sa, kuma ya tsaya yana min faɗa". Mubeenah tace "ikon Allah shiyasa nifa banason zaman mutumin nan a gidan nan yabi ya taƙura rayuwar Mutane kaman uban mu ne shi". Maya tace "Ni wallahi sai yanzu ma nakejin haushin hakurin da na basa, idan ni tunanina ya tafi wani guri shi ina nasa tunanin ya tafi?". Mubeenah tace "Allah ya kyauta amma sam Yah Ammar bai kyauta ba". Maya bata ƙara cewa komai ba, kawai ta kwanta akan gadon, tare da rufe idon ta, she wish bacci ma ya ɗauke ta, ko zata rage jin baƙin cikin da take ji idan ta farka,........ *AYRAH* Wani tunani ne yazo mata lokaci guda ta miƙe ta nufi ƙofar fita, ai kuwa tayi sa'a Mama Abu tana zaune a tsakar gida ita da ƙanwar ta aunty Maryam da kuma Ma'u, ƙarisawa tayi gun Ma'u tace "ƙanwar mijina dan Allah ɗan ƙiramin mijina mana, a wayar ki inaso na faɗa masa wani abu". Ba Ma'u kaɗai ba hatta mama Abu da aunty Maryam sai da suka shiga shock, ka ɗan ya rage Ayrah ta fara dariya saboda yadda mama Abu ta sake baki da hanci tana kallon ta, ganin Ma'u bata da niyyar bata wayar yasaka ta sa hannun ta akan wayar, ai kuwa Ma'u ta sake mata , kallon Ma'u tayi tace " me kikayi saving numbern mijin nawa?". Ma'u tace "ɗan uwa". Searching Ayrah tayi tare da dailing bugu biyu, yayi picking babu ko sallama, Yace " sa'a dai ƙanwata". Ayrah tace " ba ita bace masoyi amaryar ka ce Ayrah". Tanko wani abu yaji ya daki zuciyar sa, yayi shiru na wani lokaci, Ayrah tace "baby kana jina". Yace "sa'a dai amaryar Tanko inajin ki wallahi Allah". Tace "dama kaga tun safe banci komai ba, kuma wallahi yunwa nakeji nace barin sanar maka nasan baxaka so amaryar ka ta kwana da yunwa ba". Yace " yanzu mekike son ci". Tace "kaza". Yace "angama yanzu za'a kawo miki ". Cikin shagwaɓa tace "Nagode sosai masoyi". Ta kashe wayar ta miƙawa Ma'u, kawai ta wuce ta barsu da sakakken baki, zama tayi a ɗakin tana hawaye tare da addu'ar Allah yasa plan ɗin ta yayi aiki, tana zaune after 30 minutes taji Muryar Tanko yana ƙwala mata ƙira da sauri ta fita, tana ƙaƙalo murmushi, tana fita ta ƙarisa inda yake tace" Barka da shigowa masoyi". Yace"sa'a dai amaryar Tanko ga kazarki hadda lemon gora aka haɗa miki, ta karɓa tare da godiya tace"Allah ya kare min kai mijina". Ya daka tsalle yace "wiyihuhu aradu sai ni Tanko angon Ayrah ". Ta juya tana murmushi ta shige ciki, sai a lokacin ya lura da su Mama Abu da suke kallon ikon Allah baki sake, Yace" ya dai kun antayo min ido ne?". Bai jira me zasu ce ba, yayi ficewar sa daga gidan, ita kuwa tana shiga ta laɓe a bakin ƙofa tana jira taji result ɗinta, Aunty Maryam ce ta kalli Mama Abu, tace "yanzu haka zaki bari wannan makirar yarinyar tana juya Miki ɗa?". Ma'u tace "ina wallahi da sake, ki duba kiga wannan kafin ayi auren fah kenan, inaga anyi auren kuma?". Mama Abu tace "Ni kam wallahi nama rasa abinyi". Aunty Maryam tace " ai kuwa ya kamata ki san abun yi, dan haka in kika bari ɗan ki ya auri wannan yarinyar to wallahi baƙin ciki ne zai kashe ki dan sai yadda tayi da shi ". Ma'u tace" tun wuri ki dakatar da auren nan idan ba haka ba, duk azabtar War da kikeyiwa yarinyar nan, agidan nan sai ta rama bayan ta auri Tanko ". Mama tace " kira min kawun ku yanzu a waya Ma'u". Ma'u tai dailing numbern kawunsu tabawa mama Abu, bayan sun gama magana, Mama Abu ta miƙa mata wayar ta, Ma'u tace "wani hanzari ba gudu ba, Mama ya kamata ki kori yarinyar nan a gidan nan, dan idan Tanko ya samu labarin fasa auren nan, kuma yazo yaga yarinyar nan a gidan nan akwai matsala, ". Ayrah sosai zuciyar ta, ta buga taja da baya ta zauna tana addu'ar Allah yasa kar mama ta amince ta koreta daga gidan, dan ita a plan ɗin ta fasa auren ne kawai amma babu batun korar ta a gidan, tana zaune suka shigo Ma'u ta wafce ledar hannun ta tace"munafuka wallahi bazaki ci kazar nan ba,wato kina so ki mallake min ɗan uwana ko?". Mama tace"Ma'u ɗago mata jakar kayan ta dan Allah mu korata waje". Ayrah tace "mama dan Allah kiyi hakuri ki rufamin asiri karki koreni cikin daren nan, wallahi ban san ina zan shiga ba". Mama Abu tace " wallahi sai kinbar gidan nan yau tunda ba na ubanki bane". Aunty Maryam ne taja hannun ta Ma'u kuma ta ɗauki jakarta suka wullata waje tare da wulla mata jakar ta, suka rufe gidan su, sosai Ayrah take kuka dan batasan ina zataje ba gashi dare yayi dan an daɗe da yin Isha, ganin kukan bazai kaita ba, ya saka ta ɗauki jakarta kawai tafara tafiya ba tare da sanin zata je ba......... *MAYA*.... Bayan ta gama baccin ta, ta farka bathroom ta shiga tayi wanka ta fito , ta zauna a gaban dressing mirror, ta shafe jikin ta da tsadadden lotion ɗin ta, Sannan ta saka riga da wando masu taushi da laushi na bacci, ta feshe jikin ta da turaruka masu daɗin ƙamshi, sannan ta ta juyo ta ɗauki wayar ta akan bedside drower taga 9:30, ajjiye wayar tayi ta fice daga, a main falo ta samu Mubeenah da Yah Ahmad da fadilah suna hira ƙarisawa tayi jikin ta a sanyaye, ta zauna tare da sallamar ta, fadilah tace " Maya kin tashi kenan?". Tace "Erh wallahi". Mubeenah tace " Yawwa Yah Ahmad dan Allah yaushe Yah Ammar zai koma ne?". Dr. Ahmad yace" i don't know, wani abu ne?". Mubeenah tace "shi yasaka Maya baccin dole". Ta ƙarisa maganar tana ƙumshe dariyar ta, kallon ta Maya tayi tace"kiyi dariyar ki". Mubeenah zatai magana wayar ta, ta fara wringing tashi tayi tare da musu sallama ta wuce ɗakin su, Maya ta kalli fadilah tace"sister fadilah kunyi dinner be?". Fadilah tace " Erh fah munyi dinner tun ɗazu". Maya tace barinje nayi nima, tana faɗan haka ta miƙe, suma su Yah Ahmad tana tashi suka mata sallama suka wuce ɓangaren su, tana shiga kitchen ɗin kawai ta ɗaura tea, bayan tagama tea ɗin, ta juye a cup ta rufe, ta fice ɓangaren Yah Ahmad ta nufa, knocking tayi fadilah ta buɗe tace "Bissimillah Maya ki shigo mana, tace" no sister fadilah dama zuwa nai na tambaye ki, idan kina da snacks ki ɗeba min zan je naci ". Fadilah tace"ok barin kawo Miki". Daga haka ta juya ta koma ciki, bata daɗe ba sai ga ta, ta fito da bowl mai kyau ɗauke da snacks aciki, miƙawa Maya, Maya ta amsa ta mata godiya tare da sallama kawai ta wuce, tana shigowa falon ta kalle shi, hannun sa riƙe da kalan cup ɗin da ta juye tea ɗinta yana danne-danne a wayar sa yanayi yana sha, bata kawo komai a ranta ba ta wuce kitchen, tana shiga ta duba inda ta ajjiye tea ɗin ta, taga wayam, a ranta tace "kenan Yah Ammar tea ɗina ya ɗauke yake shanye wa". Har zata ƙara ɗaura wani sai kawai ta fasa, ta buɗe fridge ta ɗauki, nutri-milk ta juya ta fice daga kitchen ɗin,...... *Kuyi hakuri da wannan yau banajin daɗi wallahi so ban samu damar typing da yawa ba*. ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 14...... Bayan ta fito daga kitchen wani kallo ta watsa masa kafin ta wuce ɗakin su, ko da ta shiga bata tadda Mubeenah ba, amma taji ƙarar ruwa alamun, Mubeenah tana wanka, zama tayi a ƙasan carpet ɗin ɗakin ta ajjiye snacks ɗin hannun ta tare da nutri-milk ɗin, tunawa tayi bata ɗakko cup ba, dan haka ta juya ta koma kitchen, wannan karan bata ganshi a falon ba, sai ƙamshin turaren sa da yake tashi a falon , ƙarisa wa tayi kitchen ɗin, ta sameshi yana wanke cup ɗin da yayi using, bata ko kalli inda yake ba, ta ɗauki cup ta ficewar ta, shima haka ko inda take bai kalla ya ci gaba da abinda yake yi....... *AYRAH* Ta fiya kawai takeyi ba tare da tasan ina zataje ba, tayi tafiya mai nisa kafin ta zauna abakin wani titi, Kasan cewar tarasa gurin zuwa , ta daɗe tana yawo for almost 2hours tun 9 gashi yanzu har 11, tana zaune tana ta kallon motoci suna wucewa, wata farar mota ce tazo har ta wuce ta, tayi reverse ta dawo dai-dai inda Ayrah ke zaune, ta buɗe motar ta fito, ta ƙarisa har inda Ayrah take, ta kalle ta, sai kuma ta maida kallon ta kan jakar kayan Ayrah, tace "ƙanwata lafiya kike zaune a bakin titi da daren nan bakya tsoron 'yan isakan unguwa su zo, su sameki a nan?". Ayrah ta ɗaga kai ta kalle ta sai kawai ta fashe da kuka, matar ta kalle ta tace "ba kuka zakiyi ba ƙanwata kiyi magana kinji". Ayrah ta kai hannu ta share hawayen idonta tace "bansan ina zanje ba". Matar tace "subhnallahi kinga ki tashi muje gidana kiyi wanka kici abinci zuwa gobe da safe sai na maida ke gidan ku". Ayrah dai tai shiru bata ce mata komai ba, matar ta tsugunna ta dafa Ayrah tace "ki yadda da ni sunana Jiddah zaki iya kirana da aunty Jiddah wallahi ban tsaya a nan gurin ba sai da niyyar na taimake ki, saboda duk mai hankali bai kamata ya ga mace budurwa a bakin titi acikin halin damuwa kuma ya tafi ya barta ba". Ayrah ta daga ido ta lalle ta, Jiddah tace "Please tashi muje kinji". Ayrah ta miƙe Jiddah ta ɗauki kayan ta, ta saka mata a back seat, ta buɗe mata front seat ta shiga, ita ma ta zagaya ta shiga tare da yiwa motar key, tunda suka shiga motar babu wanda ya ƙara cewa ɗan uwansa wani abu, sunyi tafiya mai nisa kafin suka isa wani makeken gida, hon ɗaya tayi gate man ya buɗe mata suka shiga, bayan tayi parking ta kalli Ayrah tace " fita muje kinji ƙanwata". Ayrah ta fita jiki a sanyaye, Jiddah ta zagayo ta buɗe Black seat ta ciro kayan Ayrah, ta kama hannun ta suka shiga ciki, Masha Allah Ayrah ta furta a zuciyar ta lokacin da suka shiga falon saboda kyau da tsarin da falon yake da shi, yara guda uku ne biyu mata da na miji ɗaya kwance a falon suna bacci, Jiddah ta ajjiye jakar ayrah ta ɗauki na mijin ta shiga da shi ciki, Ayrah dai tana tsaye a inda ta barta har ta dawo ta ɗauki ɗaya macen, Ayrah ta ƙarisa itama ta ɗauki ɗayar ta bi bayanta, sai da suka kwantar da yaran kafin ta kalli Ayrah tace "muje na nuna Miki inda zaki kwana". Ta fita Ayrah ta bi bayan ta, sai da ta ɗauki kayan Ayrah a falo kafin suka wuce, wani ɗaki ta kai Ayrah wanda yake kusa da na yaran nata, ta kalle ta, tace kishiga kiyi wanka kafin nan barin je, na da fa Miki ko indomie ne dan babu da faffen abinci a gidan". Ayrah dai tana tsaye bata ce komai ba, Jiddah tace "muje na nuna miki yadda zakiyi using da bathroom ɗin, Ayrah tabi bayan ta, sai da ta gwada mata komai kafin ta fita, tana fita Ayrah ta buɗe jakar kayan ta, wani photo ta ciro na maza yara guda uku sai da mace ɗaya babban cikin su yana ɗauke da macen, kallon ƙaramin ciki tayi kafin tace "Abba na, nayi kewarka, Abbana duk inda kake Allah yasa kana cikin ƙoshin lafiya, Abba sunce ka rasu, amma ni ban yadda ba, Abba na dan Allah ka dawo gareni". Ta ƙarisa maganar hawaye na bin ƙuncinta, sai da tayi kuka sosai ganin kukan ba zai kai ta ba, ya saka ta, ta shi , ta shiga bathroom ɗin, wanka tayi tare da ɗauro alwala, ta fito, ta ɗauki doguwar rigar material acikin kayan ta, ta saka, ta saka half Sunnah black, tana zaune sai ga, Jiddah ta dawo hannun ta ɗauke da babban plate, tace "ƙanwata har kin fito?". Ayrah tace "Erh aunty" . Jiddah ta ajjiye mata babban plate ɗin wanda yake ɗauke da, da plate ɗin da ta juye mata indomien ta rufe sa da wani plate sai kuma, ruwa gora 1 da cup, bayan ta ajjiye ta kalli Ayrah tace " ki sake jikinki kamar kina gidan ku, kinji?". Ayrah ta gyaɗa mata kai tana wasa da yatsun ta, tace "Yawwa na manta ban tambaye ki sunanki ba". Ayrah tace "sunana Ayrah ". Jiddah tace"Masha Allah, to kici abinci Ayrah barinje nayi wanka nima ". Ayrah tace "Nagode ". Jiddah ta sakar mata murmushi ta juya ta fice daga ɗakin, Ayrah ta jima a zaune tana tunani kafin daga baya ta buɗe plate ɗin abincin ta fara ci, ka ɗan taci, ta rufe sauran ta buɗe goran ruwan ta raga a cup ɗin ta sha, ta tashi ta ɗauki plate ɗin ta fice, tunda ta fara tafiya takejin kaman ido na yawo akan ta, ita dai bata ɗaga kai ba har ta ƙarisa falon, kafin ta ɗaga kanta, da wani irin mugun kallo Yake binta, haka kawai taji ta tsargu a ranta tace "subhnallahi wannan wane irin kallo ne". Tana ɗaga kai taga yana kallon ta har wani lashe lips yake, cikin sanyin murya tace " ina wuni". Yace "lafiya 'yan mata". Tace "dan Allah ina ne kitchen?". Hanayar kitchen ɗin ya nuna mata, yana bin ƙirjin ta da kallo, ita dai kan ta a ƙasa ta wuce kitchen ɗin, bata fito ba sai da ta wanke, duk abubuwan da taga anyi amfani da su ba a wanke ba, ta wanke ta tsaftace gurin ka fin ta fito, lokacin da ta fito, bata kalle shi ba, a ranta tana hamdala ga Ubangiji ta wuce ɗakin da aka ajjiye ta, tana shiga tai kwanciyar ta akan bed in tana kartanto addu'oi, bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta, Jiddah ce ta shigo ta bakin ta ɗauke da sallama amma da taga tayi bacci kawai ta ja mata duvet, ta mayar mata da wutan ɗakin, dim light sannan ta fice, tare da rufo mata ƙofar, .......... *WASHE GARI* ****** Ma'u tana zaune a bakin ƙofa tana kallon uban tilin wanke-wanken da mama tace tayi, a ranta tace "Ni zanyi wanke-wanken nan to ashe ma ni jaka ce". Da mugun ƙarfi aka banko ƙofar aka shigo, ta tsaya tana kallon sa tace "ɗan uwa lafiya ?". Tanko yace "ban sani ba dan ubanki". Har Ma'u zatai magana Mama Abu ta fito daga ɗaki, tace "lafiya kake buga min ƙofa kamar zaka karya min ƙofar gida".Ma'u tace "tambaye shi dai Mama".' Tanko yayo kan Ma'u yace "zanci ubanki na ƙarajin maganar ki a gurin nan". Ma'u ta juyar da kanta, tana murguɗa masa baki, Yace " tukunna ma wai ina Ayrah?". Mama tace "ba ta nan ta, tattara kayan ta, tabar gidan nan saboda bata so ta aure ka". Yace " wallahi ƙarya ne, sai dai kun haɗa baki da 'yar ki kun koreta". Ma'u tace "to idan an koretan sai me?, gidan ubanta ne da......". Ai bata ƙarisa maganar ba taji sauƙar mari a fuskar ta, ta dafe ƙuncinta tace " kutumar uba ni ka mara?, lallai yau zaka gane baka da hankali". Tana rufe baƙin ta, ta ƙara jin sauƙar wani zazzafan marin, da sai da yasa ta bugu da bango, da sauri ta, tashi ta nufi gurin wanke-wanken da aka tara, ta ɗakko murfin tukunya Tanko bai ankara ba, sai ji yayi ta buga masa da iya ƙarfin ta, sai da yaje ƙasa, tace "na fika iskanci da tashanci wallahi". Hankalin mama yayi mugun tashi, ganin jinin da yake zuba daga goshin Tanko, hankali tashe ta kama hannun sa tace "tashi muje chemist". Gyalen ta, taja akan igiya suka fice, Ma'u tabi bayan su da kallo, tace "ka ɗan ma ka gani ƙaramin ɗan iska". Tana faɗan haka , ta juya ta ɗauki bocket ta ɗibi ruwa ta shiga, wanka bayan ta fito ta shirya, abinta taci kwalliya ta fice tabar gidan babu kowa, ...... *AYRAH* Misalin karfe 8:00am ta, tashi ta fito da mugun mamaki ta fito, tana bin falon da kallo yanda ya fita fes-fes ko ina sai ƙamshi ya keyi, kitchen ta nufa domin ɗaura musu ko da indomie ne, da mugun mamaki take kallon Ayrah da take tsaye tana soya Irish, Ayrah jin kamar ana kallon ta, ya saka ta saurin juyowa, murmushi ta sakarwa Jiddah tace "good morning Aunty". Jiddah tace "morning Ayrah". Still tana tsaye tana kallon Ayrah, Ayrah ta juyo bayan ta tsame Irish ɗin a kosko ta saka wani, ta kalli Jiddah tace "aunty kina buƙatar wani abu ne?". Jiddah tace "no Ayrah, thank you". Ta wuce ta juya ɓangaren ta domin ta tayi wanka ta shirya, Ayrah bayan ta gama haɗa musu break past, ta kai dining ta jere, ta koma ta gyara kitchen ɗin da duk abubuwan da ta tayi amfani da su, sannan ta fita, ta nufi ɗakin da suka kai yara jiya, bakin ta ɗauke da sallama ta buɗe ƙofar ta shiga, mace ce, wacce bazata wuce 7 years ba tana ƙoƙarin sakawa ƙanin ta kaya wanda shima bazai wuce 4 years ba, juyowa sukayi suna kallon ta, ta ƙarisa inda suke tana murmushi, macen ta kalle ta, tace"good morning". Tace" morning". Shiru ya biyo baya, Ayrah ta kalle ta, tace kawo shi , na shirya sa, ta karɓi rigar yaron ta saka masa tana, murmushi ta kalli macen tace "sunana Ayrah ke fah?". Itama murmushin tayiwa Ayrah tace "sunana liyana". Ayrah tace "nice name". Bayan ta gama sakama yaron kaya tace "what about you" yace Khalil ". Tace "Masha Allah nice to meet you ". Dai-dai nan aka murɗa handle ɗin bathroom aka fito, dukkan su juyawa sukayi suna kallon ta, Ayrah ba ƙaramin shock ta shiga ba, ta kalle ta, ta juya ta kalli liyana tace "twins?". Liyana ta gyaɗa mata kai tana murmushi, tace "sunan ta leenah ". Leenah ta ƙariso tana kallon Liyana tace " sis please help me dry my hair". Liyana tace "ba zan iya ba gaskiya". Leenah ta kalli Ayrah tace "aunty help me please ". Ayrah taje ta busar mata kanta da hand Drayer, bayan ta gama leenah ta shirya Ayrah ta kalle su tana murmushi tace "to muje kuyi break fast". Khalil da yake riƙe da hannun Ayrah yace "aunty Ni bana son taliya ko indomie kullum momy taliya take mana ko indomie". Ayrah ta daga shi sama tace "Tom yau aunty bata maka taliya ba kuma bata maka indomie ba". Yace "aunty me kika mana". Tace "abun daɗi". A haka suka ƙariso dining ɗin suna ta hira da Ayrah suna dariya, Ayrah taja kujera da zaunar da Khalil suma twins suka zauna, sai lokacin suka lura da momyn su da take zaune take break fast hankali kwance, dukkan su, suka gaishe ta, ta amsa, Abubakar shima da yanzu ƙariso warsa yaja kujera ya zauna, Jiddah tace "good morning darling". Ayrah tace ", morning". Ayrah da sauran yaran duk sukece "good morning ".Yace " morning". Yana kallon Jiddah yace "baƙuwa mukayi ne?". Jiddah tace "itace wacce jiya nace maka zamuyi magana akan ta".Yace "ok". Da ga nan shiru ya biyo baya ita dai Ayrah ta kasa sakewa saboda yanda take jin idonsa akan ta, ........... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 15...... ***** Ayrah dai bata wani sake taci abincin kirki ba, kasancewar yau ranar Lahadi ce, babu aiki, bayan sun gama breakfast suka dawo falo suka zauna, Jiddah ta kalli su Liyana tace "kuje kuyi wasa amma banda faɗa kunji, zamuyi magana da aunty". Leenah ta kama hannun Khalil suka fice daga falon, Jiddah ta kalli Ayrah, tace "ai da baki wahalan tar da kanki ba, na fito ne fa zan haɗa mana break fast na ganki a kitchen ɗin". Ayrah tace "babu komai ai da yake na saba da aiki ne sosai, to idan bana aiki sai naji bana jindaɗi". Jiddah tace "ayya Nagode sosai fah". Ayrah tace "nice da godiya ai,". Sai kuma tace " lokacin da muka zo jiya ko dan dare ne, ban lura da kaman nin su Liyana ba, ashe twins ne". Jiddah tace "ayya wallahi twins ne". Sai kuma shiru ya biyo baya babu wanda ya ƙara cewa komai shidai Abubakar yana zaune,kaman yana danna waya amma hankalin sa yana kan Ayrah da take zaune a ƙasan carpet, after some minutes Jiddah tai breaking silent ɗin nasu da cewa "Ayrah". Ayrah ta ɗago kai tace "na'am". Jiddah tace "dan Allah inaso ki faɗa min tsakanin dan Allah mekike jiya cikin dare a bakin titi". Ayrah kamar baza tai magana ba, sai kuma tace "ban san inda zanje bane wallahi". Abubakar yace "to ina gidan ku yake?". Tace " sanin gidan mu bashi da amfani domin yanzu gidan yafi ƙarfina". Abubakar yace "ban fahimta ba". Ayrah ta share hawayen idonta tace " da ni da matar babana muke rayuwa kuma ta kore ni". Jiddah tace "amma Meyasa?". Ayrah tace"saboda tana so ta aura min ɗan ta, ɗan shaye-shaye kuma ɓarawo ". Nan ta kwashe labarin duk abinda ya faru jiya ta faɗa musu, Jiddah ta kalli mijin ta, tace "dan Allah darling idan babu damuwa ta zauna damu mana". Abubakar yace "babu damuwa Allah ya mana jagora, Allah ya shirya masu hali irin na kishiyar maman ta". Dukkan su, sukace "Ameen". Ayrah a zuciyar ta tace " dan ma ban faɗa muku abubuwan da ta min da kuma gidan mu da tasiyar ta siya wani ba". Jiddah ta kalle ta, tace "Ayrah ina zaki zauna damu". Ayrah tace "Nagode sosai Allah ya saka Miki da alkhairi aunty". Jiddah tace "Ameen ya Allah". Ayrah ta kalli Abubakar sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta tace ", Nagode uncle". Yace "karki damu Ayrah ai yiwa kaine". Daga nan ta tashi ta fita gurin su leenah ta biye musu suka fara wasa kamar wata yarinya,..... *AMJAD* I zuwa yanzu har ya gaji da neman da yake yiwa Ayrah ya tattara komai ya sallama wa , Ubangiji addu'a yake babu dare babu rana, akan Allah ya haɗa fuskokin su, a lokacin da baiyi tsammani ba, tunda yaga ba samun ta zai yi ba ya tattara kayan sa ya koma Madina, saboda yana tunanin idan ya zauna ma auren sa da Maya za'ayi kwana kusa,....... *MAYA* Kasancewar yau Lahadi ne, babu aiki, Mubeenah ta shirya musu fita ita da fadeelah , duk dama ba'a sanar mata gurin da za suje ɗin ba,tana gaban mirror tana feshe jikin ta da turaruka masu daɗin ƙamshi, wayar ta, ta fara wringing picking tayi tare da sallama daga ɗaya ɓangaren yace "wa alaikissalam Maryam Yakike?". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah Abie ya su ammie?". Yace "suna lafiya ya gidan naku?". Tace "lafiya ƙalau Abie na". Yace "Maryam akwai wata matsala ne?". Tace "babu matsalar komai Abie". Yace "bakya buƙatar wani abu?". Tace "alhamdulillah bana buƙatar komai Abie". Yace "to shikkenan alhamdulillah amma duk da haka zan tura miki kuɗi kiyi wani abun da shi". Tace "Abie wanda ka turamin ma fah bai ƙare ba". Yace " badamuwa Maryam zan ƙara Miki saboda nasan koya ƙare ɗin ma ba magana zakiyi ba". Tace "Nagode sosai Abie Allah ya saka da alkhairi Allah ya ƙara arziki". Yace"Ameen Maryam Allah ya miki albarka". Tace "Ameen Abie nah". Bai ƙara cewa komai ba, ya kashe wayar, bayan ya kashe ya tura mata kuɗin, kafin ya kalli ammie da take zaune a gefen sa tun ɗazun yace "yarinyar nan akwai hankali". Ammie tace "Maryam kam babu laifi, Amjad yayi sa'ar mata, sai dai mu, musu fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, Allah ya nuna mana lokacin". Abie yace "Ameen Fatima". Sai kuma ya ɗaura da cewa "bana fatan Allah ya nuna min lokacin da yarinyar nan zata ɗanɗani ɗacin maraici, Allah kar ya nuna min lokacin da yarinyar nan zatai kewar mahaifin ta, lokacin da yarinyar nan zata ji ina ma mahaifin ta yana raye, saka makon wani baƙin ciki, Allah yasa ta tun daga tuna shi tana masa addu'a a lokacin da a take farin ciki, amma ba a lokacin da muka nuna gazawar mu akan ta ba". Ammie tace "Ameen Allah ma kar ya nuna mana lokacin da zamu nuna gazawar mu akan Maya". Yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum"........... Maya bayan ya kashe wayar, ta ajjiye ta akan mirrow tanajin ƙarar shigowan massage tasan abie ne, ya tura mata kuɗin, a fili ta furta, ina ƙaunar ka sosai Abie na, the best father of the world, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, Allah ya bamu ikon maka biyayya tare da faranta maka a kowani hali muka tsinci kan mu". Mubeenah ce ta turo ƙofar ta shigo sanye da riga da scate na Atamfah ya mugun mata kyau sosai, kallon Maya ta rinƙayi kamar bazatai magana ba, sai kuma tace "dan Allah ina kayan da na baki, yanzu bazaki saka muyi ankon ba kike nufi ko me?". Maya tace "kema kin sani ba zan iya saka Atamfah ba, idan kina so muyi anko kawai kisaka Abaya". Mubeenah tace "wallahi bazan saka ba, amma ai kinsan saboda ke nayi ɗin kin nan guda biyu iri ɗaya". Maya tace"it's okay tunda bazaki saka Abaya ba". Mubeenah taja tsaki ta shigo ɗakin, ta ɗauki kayan a kan bed, ta buɗe wardrobe ta saka, ta ɗauki wayar ta, da hand bag ɗin ta, akan mirrow ta fice, sosai Maya taji babu daɗi akan abinda tayiwa Mubeenah amma ya kamata Mubeenah ta fahimce ta, ba laifin ta bane, kawai ita tafi gane tasaka Abaya bane, itama wayar ta da hand bag ɗin ta, ta ɗauka da kuma key ɗin motar ta, ta fice, ɓangaren Mami ta nufa taje har ta mata sallama bata ga, Mubeenah ba, saboda haka ta fito, ta nufi ɓangaren fadilah, knocking tayi fadilah ta buɗe mata, itama ta shirya cikin Atamfah irin na Mubeenah, tana kallon Maya tace "kuttttt Maya wai kina nufin baki saka kayan nan ba". Maya tace" kuma kun san bazan iya sakawa ba, to miye na damuwa da dole sai na saka". Mubeenah tace "Please ki daure ki saka dan Allah ". Maya tace "gaskiya bazan iya ba". Yayinda take shiga falon, Mubeenah ce ta fito, batare da ta kalli inda Maya take ba, tai wucewar ta, suka bi bayanta sai da fadeelah ta shiga tayiwa Mami sallama kafin ta fita, ta samu Maya a tsaye a compound ita kuma Mubeenah ta shige motar ta tana zaune, a driver seat, Fadeelah ta ƙarisa ta shiga front seat, kafin Maya ta shiga back seat, Maya bayan sun fara tafiya ta ciro wayar ta, a hand bag ɗin ta, ta shiga gallery ta ƙurawa photon Amjad ido, tana kallo tana jin wani sanyi a zuciyar ta, ........ *AYRAH*........ Misalin ƙarfe 2:30 na rana suna zaune a ɗakin su Liyana suna ta hira abinsu kamar sun daɗe da sanin juna, Jiddah ta shigo tana kallon Ayrah tace "Ayrah ki tashi kije kishirya kizo mu tafi unguwa". Khalil yayi sauri yace "momy Nima zan biku". Jiddah tace "bazaka kaje ba ka zauna kuyi wasa da 'yan uwanka". Liyana tace "dan Allah momy kiyi hakuri kije damu". Jiddah tace "babu inda zakuje". Ayrah tace "dan Allah aunty kiyi hakuri mu tafi da su". Jiddah tace "shikkenan ku shirya sai mu tafi". Ayrah tace "mun gode aunty". Ta kama hannun Khalil suka shiga bathroom sai da ta shirya Khalil, ta bar su Liyana su shirya ta wuce ɗakin ta, basu daɗe ba suka shirya suka, fice sosai Jiddah tayiwa Ayrah shopping hadda akwati ta siya mata, da abayoyi shower gels da turaruka da sauran su, su Liyana da leenah da Khalil ma an ɗan musu shopping ɗin, kafin suka dawo gida sosai Ayrah taita yiwa Jiddah godiya hadda kukan ta, .......... *MAYA*........... Tana zaune a hall ɗin sai bin Mutane take da kallo ko wacce da shigar ta irin ta su Mubeenah, masu cin snacks suna ci, masu photo sunayi, fadeelah ce ta ƙariso inda Maya take ta zauna, tace "Wai ke Meyasa bakya son zama cikin mutane ki duba curse mate ɗin mu suna ta farinciki, shekaru nawa rabon da mu haɗu, amma ke kin ware kanki, kin zo nan kin zauna". Maimakon ta bawa fadeelah amsa, sai kawai tace " dama get to gether za muzo shine, baku faɗa min ba". Fadeelah tace "naga wadda akwai maza ne, bakya son zuwa, wannan kuma na mata zallah ne". Maya ta ɗaga idanun ta, ta kalli Mubeenah sai rawa takeyi an saka musu waƙa, su da wasu curse mate ɗin su, fadeelah tace"ina zuwa " tana faɗan haka ta miƙe, ta shin ta ke da wuya Maya ma, ta tashi ta fita compound ɗin, ta zauna tana danna wayar ta, da ido take bin motar, bayan kusan minti 4 , ta tashi ta miƙe, ta buɗe front seat ta shiga, tana zaune tana ta danne-danne a wayar ta, Ya nufo motar, bai kula da mutum a motar ba, har sai da ya shiga yaji ƙamshin turaren ta, da mugun mamaki ya juyo yana kallon ta yace " ke.... From where?". Ta sunkuyar da kanta, tace "munzo get together ne, kuma wallahi I'm very tired and da mota ɗaya muka zo kuma su ba yanzu zasu tafi ba". Yace "ki hau taxi mana". Tace "Please yah Ammar I'm begging you ka kaini gida dan Allah". Ya kalle ta sai kuma Yace "ina da gurin zuwa". Tace "dan Allah ". Bai ƙara ce mata komai ba yaja motar ya fice......... *AYRAH* A iya yinin yau da tayi baƙara min jindaɗin zama da ita Jiddah tayi, taja yaran ta ajiki, kuma ita take duk wasu aikace-aikacen cikin gidan, tana kwance cikin dare, taji an janye duvet ɗin da ta lulluɓu da shi, sosai zuciyar ta, ta tsinke, ta tashi , jikin ta yana rawa, ta nufi gurin kunna haske, taji an ruƙo hannun ta, cikin firgita da tashin hankali, ta janye hannun ta, ta kunna hasken ɗakin, da mugun mamaki take, kallon sa , hawaye na bin ƙuncinta tace"uncle me yakawo ka ɗakina me kake buƙata da ni?". Yace"Ayrah haɗin kanki nake buƙata Ayrah dan Allah ki taimaka ki amince da ni, na miki alƙawarin zan Miki duk abinda kike buƙata a duniyar nan idan dai kuɗi zai iyayin sa". Ayrah har yanzu hawaye bai daina zirya a idonta ba, tana kallon sa da mugun mamaki da kuma tashin hankali............ ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 16...... ***** "A'uzubillahi minash, shaɗanirrajim, dan Allah kayi hakuri uncle, ka fita min a ɗaki". Ta faɗa idon ta na zubda hawaye, ga nin yana ƙoƙarin yowa kanta, ya saka ta bige shi, ta fice da gudu, ɗakin su Liyana ta shiga ta rufe jikin ta yana ta rawa, bayan ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar, ta fashe da kuka, tuna su Liyana suna ɗakin kuma ya saka ta rufe bakin ta tana kuka, sosai ta zame ta zauna a gurin zuciyar ta na mata wani irin zafi a ranta tana fatan Allah ya fitar da ita daga cikin wannan mummunar ƙaddarar da take bibiyar ta, agurin bacci ɓarawo ya ɗauke ta, sai guraren sallar asuba, ta tashi, ta koma ɗakin jikin ta na rawa har lokacin bata fita daga cikin ta shin hankali da take ba, ko da ta shiga sai da ta, tabbatar baya ɗakin kafin ta rufe ɗakin ta ciki, tana shiga bathroom ta wuce ta ɗauro alwala, ta fara sallolin nafila tana roƙon Allah ya bata ikon cinye wannan jarrabawar ɗari bisa ɗari, Allah ya kawo mata mafita da ɗauki, bata tashi akan sallayar ba har sai da ta gabatar da sallar asuba, bayan ta idar ta fara karanto azkhar ɗin ta, bayan ta gama ta shiga bathroom tayi wanka, ta fito ɗaya daga cikin doguwar rigar da Jiddah ta siyo mata, ta saka, bayan ta gama shafe-shafe, da har zata fesa turare ta fasa, ta ɗakko dogon hijab ɗin ta blue ta saka, ta fice ta nufi kitchen jikin ta a sanyaye, saboda har yanzu memoring abinda ya faru jiya yana mata yawo a ƙwaƙwalwar ta,.... *MAYA* Ita dai tunda suka fito ta lura ba hanyar gida ya nufa ba, amma bata da 'yan cin yin magana saboda Yah Ammar bashi da sanyin hali, a ƙofar wani gida yayi horn gateman ya huɗe musu gate suka shiga, ita dai tana son ta, tambaye shi amma takasa, saboda bai bata fuskar yin tambayar ba, bayan ya gama parking ya kalle ta, Yace "fita muje". Cikin sanyin murya tace "ina ne, nan ?". Ya wani kalle ta ya haɗe rai Yace "ban sani ba". Tace "dan Allah ni kam Ya Ammar ka kaini gida". Ya juyo ya kalle ta, kamar bazaice komai ba, sai kuma ya haɗe rai Yace "zaki fita ko sai na bigeki". Ta tura baki ta buɗe motar ta fice, shi dariya ma ta bashi yadda ta tura bakin, shima fita yayi, ya wuce tabishi a baya, knocking yayi basu da daɗe ba, wata mata ta buɗe ƙofar tana kallon su, fuskar ta, ɗauke da fara'a tace "Yah Ammar bissimillah ku shigo mana". Ta faɗa yayinda ta juya ciki, suka shiga suka zauna akan kujera, ta juya da fara'a tana kallon Maya tace "sannu sis Yakike?". Maya tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ta maida kallon ta kan Ammar tace "Yah Ammar ai da kasanar da mu da baƙuwa zaku zo, sai mu shirya mata abubuwa". Yah Ammar yace "karki damu hafsat". Hafsat ta kalli Maya tace "Maya ko?". Maya tace "Erh nice". Hafsat tana murmushi tace "ina zuwa ". Bata daɗe da tafiya ba, sai ga mijin ta ya shigo hannun sa riƙe da na, 'yar su Amal, suna shigowa ya yarinyar ta sake hannun Daddyn ta tafi da gudu ta rungume, Yah Ammar tace "i miss You uncle". Ya ɗago fuskantar ta Yana dariya Yace "miss You too Amal". Fahad ya zauna yana kallon, ta sunkuyar da kanta ƙasa tace "ina yini" Yace "lafiya Madam ya gida". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ya kalli Yah Ammar Yace "itace Maya ko?". Yah Ammar yace gata nan ka tambaye ta mana". Maya tace "nice" tana miƙa hannu a Amal, Amal ta je ta gunta, can wayar Maya tayi ƙara alamar shigowar massage, ta duba bayan ta karanta massage ɗin, ta ɗaga kai ta kalleshi, ita wallahi bata taɓa tunanin ma yana da numbern ta ba, ta tashi ta kama hannun Amal tace "muje mu ɗakko saƙo a mota". Suka fita basu daɗe ba suka shigo da ledoji har guda biyu, suka zauna Amal tana kallon ta, tace "aunty wannan duka nawa ne?". Maya ta ɗaga mata kai tana mata murmushi, hafsat ta kawo musu abinci da drinks hadda snacks sosai, Amal ta sake da Maya har tana tambayar ta yaushe zata dawo, lokacin da Maya zasu tafi, hafsat ta bawa Maya turaruka masu ƙamshi da tsada, ta mata godiya, sannan suka wuce gida......... *AYRAH*........ Tana zaune akan sallaya tunda ta idar da sallar azahar bata, tashi a gurin ba, sai tunane-tunane take, ta rasa meyake mata daɗi a zuciyar ta, taji an buɗe ƙofar ɗakin ta, an shigo da sauri ta tashi tana kallon ƙofar gaban ta na faɗuwa, ƙarisowa yayi ya zauna a bakin gadon yana kallon ta, ita kuwa sai ja da baya take kamar wacce ta kalli mutuwa, tajinginu da bangon ɗakin, tana kallon sa, hawaye ya fara zirya a idanun ta, ya gyara zama yace "bazan Miki dole ba Ayrah amma inaso ki amince da kanki, ki mallaka min kanki, zan iya fitar da ke daga gidan nan, na mallaka Miki gida naki na kanki, na siya Miki mota da duk wasu abubuwan more rayuwa amma idan kin amince zakina biya min buƙata ta ko wani lokaci ". Ayrah tace "dan Allah uncle kayi hakuri ka fice min daga ɗaki, uncle wallahi ko duniyar nan zaka bani bazan iya aikata zina ba". Ta faɗa tana share hawayen da yake bin ƙuncinta, Ya kalle ta kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya fice daga ɗakin, Yana fita, ta shiga bathroom ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar tana kuka, cikin kuka tace "wannan wace irin rayuwa ce ƙaddara ta jefo ni ciki, Yanzu haka zan cigaba da zama ana farautar mutunci na?". Ta ma kanta tambayoyin da bata da amsoshin su, sai da tayi kukan ta mai isar ta, kafin tayi wanka, ta fito, ta shirya cikin doguwar rigar material, ta saka hijabin ta, Yanzu kam babu abinda ta shafa a fuskar ta, ta fita, tana fita ta sameshi a main falo, shi da wani saurayi, kallon sa tayi, ta kauda kai kamar bata ga mutane a gurin ba, ta wuce, kitchen ta shiga ta fito da warmers ɗin da ta zuba abincin da ta girka na rana, ta fito da su ɗaya bayan ɗaya ta jere a dining, ta juya zata wuce, tana zuwa dai-dai inda suke saurayin ya ɗago ya kalle ta, ya yatsine fuska, Yace "ke baki iya gaisuwa bane? Ko gidan ku babu manya?". Maganar gidan su babu manyan ne ya tsaya mata a ranta, ta juyo ta kalle shi, kamar zatai magana sai kuma ta juya ta wuce, ya juya ya kalli Abubakar Yace "wacece ita?". Abubukar Yace "zamuyi magana akan ta daga baya, amma yanzu ka ɗauka sistern Jiddah ce". Baice masa komai ba ya tashi yana kallon Abubakar ɗin, Yace "barin shiga inyi wanka". Abubakar Yace "ok". Daga nan ya wuce. Ayrah tana shiga ɗakin ta, ta rufe ƙofar a ranta tana addu'ar Allah ya dawo da Jiddah yanzu, kwanciya tayi a kan gadon zuciyarta cike da tunane-tunane kala-kala har Bacci ya ɗauke ta, bata farka ba sai ƙarfe 5 na Yamma a mugun zabure ta tashi ta diro daga kan gadon, ta wuce bathroom wanka tayo ta ɗauro alwala bayan ta fito, ta shirya cikin riga da scate na Atamfah na Sa'adatu wanda mama ta bata, bayan ta shirya tana kallon kanta, a mirrow tace "Allah sarki mama Allah sarki Sa'adatu na Wallahi nayi kewarku sosai, ina ma nasan inda kuke yanzu da ban kasance cikin gidan nan ina fuskantar wannan mummunar barazanar ba". Ta ƙarisa maganar hawaye na bin ƙuncinta, tunawa da tayi batayi sallah ba, ya sakata saka hijabin ta brown, ta shimfiɗa sallaya ta fara gabatar da Sallah, bayan ta idar ta fice ta nufi kitchen, tana tsaye a kitchen ɗin tana girki, taji motsin shigowar mutum a mugun tsorace ta juya sai kuma taga wannan saurayin ɗazun, cup ya ɗauka ya fice, with out looking at her, sai 6:30 tagama girkin, lokacin Abubakar ya tafi ɗakko su, Liyana a school, har zuwa lokacin basu dawo ba, sai da tattare komai ta kai dining ta jera, ta kwaso na ɗazun, ta dawo da su, ciki, ta wanke ko ina, ta gyare kitchen ɗin kafin ta fice, taje tayi sallah,......... ***** Mama abu tana zaune a cikin gida ta zuba uban tagumi sai bin gidan take da kallo, tun lokacin da ma'u sukayi faɗa da Tanko har yau bata dawo gidan ba, tunanin ta duk ya tafi kan ma'u saboda kayan abincin ta ya kusa ƙarewa kuma dama Ma'un ce me siya mata kayan abincin, tunda suka dawo gidan nan, tana cikin wannan tunanin Ma'u ta shigo ko sallama babu, Mama Abu ta kalle ta, tace "ina kika shige ne 'yar albarka kwana biyu shiru?". Ma'u ba tare da ta kalli Mama Abu ba, tana cire gyalen kan ta, tace "tunda dai na dawo lafiya ai shikkenan, ni ba yarinya bace da za'a tsareni ana tambaya ta, ko ina naje". Mama Abu tace " Allah ya baki hakuri 'yar nan". Ma'u tace "Ameen"........ *AYRAH* misalin ƙarfe 9 na dare tana zaune a falo tana kallo, ita da Liyana dan sauran yaran duk sunyi bacci, Ya shigo falon yana kallon Liyana yace "ke tashi kije ki kwanta dare yayi". Zuciyar Ayrah tai mugun bugawa saboda ita wallahi ba fahimtar kallon take ba, kawai dai tana yi ne, saboda bata son tafiya ɗakin ta, Abubakar ya bita, Liyana ta miƙe ta lalle shi tace "uncle Jabeer sai da safe". Bai kalle ta ballantana ya amsa, ita dai Ayrah still tana zaune akan kujera tana kallon da bata fahimta, Jabeer ya zauna a falon da system ɗin sa yana ta danne-danne, after some minutes ya ɗago ya kalle ta, yaga still idon ta yana kan TV suna zaune a gurin, har 11 ya kalle ta Yace"Madam marar gaisuwa ba zakije ki kwanta ba ne". Ta kalle shi, tace " sunana Ayrah kuma banjin bacci ne shiyasa". Yace "ok". Daga nan bai ƙara ce mata komai ba, har 12:00 wayar sa ce ta fara wringing yayi picking tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren yace "mutanen US Yakake". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ɗayan yace " ɗazu Abdul yake faɗa min aika dawo Nigeria shine nace barin kira mu gaisa, Jabeer yace"ok thank you good night ". Tare da kashe wayar, bayan ya kashe wayar ya tashi ya ɗauki system ɗin sa, batare da ya kalli Ayrah ba ya kashe TVn yace"maza kije ki kwanta". Ba musu Ayrah ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin ta, jikin ta a sanyaye, ya bita da kallo, sai kuma shima ya wuce nasa bangaren..... Abubakar kuwa da sallamar sa ya shiga ɗakin Jiddah ya sameta, a kwance a kan gado, ya kalle ta, ya zauna a bakin gadon yace "baby inaso muyi magana ne". Ta buɗe ido ta kalle shi sai kuma ta rufe idon tace " kayi hakuri dan Allah, kabar maganar nan, sai gobe da safe, ni agajiye nake kuma bacci nake ji". Yace " amma Jiddah kinsan a matsayina na mijinki ina da haƙƙi a kan ki ko?". Tace " nasani but dan Allah kayi hakuri ka tafi ɗakin ka, ka kwanta darling, bacci nake ji". Tana faɗan haka ta ja duvet ta juya masa baya, jiki a sanyaye ya tashi ya fice daga ɗakin,..... Ayrah kasancewar yau ta rufe ɗakin ta da key kafin ta kwanta, tanaji yana knocking tayi shiru, kamar tana bacci, Yace "Ayrah kizo ki buɗe ƙofar nan ko na ɗakko nawa key ɗin na buɗe, babu ɗakin da bani da key ɗin sa a gidan nan, duk da tasan hakan zata iya yiwuwa amma bata ɗauki maganar serious ba, jin ya daina knocking na wani lokaci ya sakata, ta saƙƙowa daga kan gadon, sanye take da riga da wandon bacci masu taushi da laushi sai kuma hula a kanta, tana tsaye a gurin, yazo ya buɗe ƙofar tafara ja da baya tana girgiza masa kai, ta nufi ƙofa zata fita, ya riƙo hannun ta, Yace"dan Allah Ayrah ki taimaka min, na Miki alƙawarin idan kika taimaka min yanzu bazan ƙara zuwa ɗakin ki ba". Ta daga kai ta kalle shi, hawaye na zirya a idanuwan ta, tace " kasake ni wallahi ko na maka ihu". Yace "Please Ayrah ". A tunanin sa bazata iya ihun ba, ai kuwa bai rufe baki ba, ta ƙawala ihun da ko ina a gidan sai da ya amsa, ta ƙara saka wani ihun, kowa a gidan ya fifto daga ɗakin sa, hadda su Liyana Khalil ne kawai bai tashi ba, Jabeer ma ya fito haka Jiddah, dukkan su suka nufi dakin Ayrah cikin tashin hankali........ ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 17....... Kallon Ayrah yayi Yace "Yanzu da abinda zaki sakawa Jiddah kenan?". Ta ɗaga kai ta kalle shi tace "ban fahimta ba". Yace "bakya tunanin halin da zata shiga idan ta gano mijin ta ne, yazo ɗakin ki yana neman ki". Tace "kai bakayi tunanin halin da zata shiga ba, idan tai find out kake ne mana". Yace "nasan idan Jiddah tasan gaskiya bazata taɓa cigaba da zama da ni ba, kina so kizama sanadiyyar raba uwa da yaran ta kenan?". Zatai magana ta ji ƙarar tafiyar su, da sauri ta fice daga ɗakin, tana kallon Jiddah ta tafi da gudu ta rungume ta, tana kuka". Dukkan su, suka tsaya suna kallon ta, Jiddah tace "Ayrah lafiya?". Tace "Aunty kyankyaso ne ya hau ƙafata". Dariya sosai leenah tayi tace "aunty wallahi nayi tunanin aljani kika gani". Ta ɗago kanta tana kallon leenah tace "to kinga wahalar da na sha ne, kafin na kashe shi?". Jabeer yaja tsaki , Yace "baki san yadda ake addu'a ba sai ihu ko?, duk lokacin da na ƙara jin ihunki da dare a gidan nan akan kyankyaso sai na ɓata miki rai". Yana faɗan haka ya wuce ya barsu a gurin, ta kalli Jiddah tace "aunty dan Allah nikam zan tafi ɗakin su leenah na kwana". Liyana tace "akan kyankyaso?". Jiddah tace "a'a ina kin kashe kyankyason muje na cire miki shi, sai ki kwana a ɗakin ki, kinga ɗakin su leenah babu guri". Tace "Tom shikkenan aunty kawai ku tafi ku kwanta zan koma ɗakin nawa". Jiddah tace "no muje na cire miki kyankyason ". Ayrah tace "Allah aunty kije ki kwanta kawai ". Jiddah tace "to shikkenan". Ta kalli su, leenah tace " ku wuce kuje ku kwanta". Basu ce komai ba suka juya suka nufi ɗakin su, itama ta nufi ɗakin ta, Ayrah ta koma ɗakin ta jikin ta a sanyaye ta kalle shi, tace " uncle dan Allah ka fice daga ɗakin nan". Ya kalle ta baice mata komai ba, ya fice, yana fita ta zube a inda take ta fara kuka, sosai tayi kuka har bacci ya ɗauke ta a gurin, ......... *AMJAD* Kwana biyu duk yabi ya rame saboda tunanin da ya saka a ransa, Yana kwance a falo akan 3 seater, Nailah ta shigo hannun ta ɗauke da cup ta ajjiye masa tace "Yaya ga coffee". Yace" thanks batare da ya ɗago ya kalle ta ba, Jaddah ce ta shigo, ta zauna akan kujera tana kallon sa, tace "Muhammad ". Amjad ya tashi ya zauna ya jinginu da kujerar Yace" na'am Jaddah". Tace "Muhammad na gaji da ɓoyeyen da kake min, ka duba kaga yadda ka dawo, kabi ka rame yau lafiya gobe jinya, ka faɗa min gaskiyar abinda yake damunka ". Nailah tana jin anfaɗi haka tasamu guri ta zauna domin itama tana sonjin ai nihin abinda yake damun sa, Amjad ya rufe idonsa ya buɗe, ya kalli Jaddah yace" zan faɗa miki gaskiya amma kimin alƙawarin babu wanda zaki faɗawa a gidan mu, it should be secret between us". Dammm zuciyar Nailah ta buga a ranta tana addu'ar Allah yasa kar Jaddah ta Kore ta, Jaddah tace" ina jinka". Yace " na haɗu da wata yarinya ne, kuma mun fara soyayya, and kuma ina sonta sosai, daga baya kuma naje gidan su, sun tashi kuma a unguwar babu wanda yasan inda suka koma shine hankali na ya tashi sosai". Jaddah tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un, yanzu yaron nan dama akan mace ne, kake neman kashe kanka". Ya ɗage idon sa daga kanta ya lumshe idonsa, sosai Nailah taji gaban ta ya faɗi, a ranta tana jin babu daɗi sosai, Jaddah tace " maimakon ka miƙawa ubangiji komai ka dage da addu'a, sai Allah ya dubi lamarin ka". Ba tare da ya buɗe idanun sa ba, Yace " wallahi Jaddah ina addu'a ba dare ba rana". Tace "to Allah ya maka mafita, amma ita Maryam ɗin ya za kayi da ita?". Yace "zan aure ta Jaddah". Jaddah tace "to Allah ya zaɓa maka abinda yafi zama alkhairi". Yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum Nagode sosai Jaddah". Jaddah tace "Allah ya maka albarka". Jiki babu ƙawari Nailah tace "Ameen". Sai kuma ta miƙe ta shige ciki, itama Jaddah tashi tayi, ta shige ciki,...... *MAYA* Suna isowa gida bayan yayi parking ta juya, ta kalle shi, tace "thank you". Baice mata komai ba ya buɗe motar ya fice, itama ta buɗe ta fita ta shige ciki, tana shiga ta wuce ɓangaren su, tayi wanka bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando na bacci masu taushi da tsada, sallar la'asar ta gabatar tare da kwanciya akan bed, bata jima ba, bacci ya ɗauke ta, bata farka ba sai wuraren, 7 tana tashi, ta janyo wayar ta, taga missed calls in fadilah har 8 missed calls sai na Mubeenah 5, sai a lokacin ta tuna ma da ta baro su, a can, tana shirin dailing numbern Mubeenah sai ga ta, ta shigo, tana kallon Maya, kamar za tai magana sai kuma ta fasa ta fara rage kayan jikin ta, ta shige bathroom tana fitowa Maya ta kalle ta, tace "kun dawo ashe?". Mubeenah tace "Erh". A taƙaice, Maya tace "gobe su Abie zasu zo neman auren ki". Mubeenah bata san lokacin da ta fara dariya ba, ta faɗa jikin Maya tana tambayar ta "dan Allah da gaske?". Maya tace "wallahi I'm serious na manta tun jiya Abie ya Kirani ya ke faɗa min, and ɗazu ya saka min kuɗi a account ɗina". Mubeenah tace "Masha Allah kinga gobe sai ki ɗauke mu, muje musha ice cream". Maya tace "insha Allahu". Mubeenah ta, tashi ta buɗe wardrobe tana duba kayan da zata saka, tace" Ya akayi kika dawo gida ke ka ɗai?". Ta mata tambayar dan ita har ga Allah har ta manta ma fushi takeyi da Mayan, Maya ta bata labarin yadda akayi ta dawo, Mubeenah bayan ta gama saka doguwar rigar ta, ta juyi ta kalli Maya tace "to amma ya akayi suka san sunan ki?". Maya tace "Nima wallahi ban sani ba". Mubeenah tace "amma abin ya bani mamaki ". Maya tace"Nima haka". Mubeenah tace "ikon Allah ". Daga nan babu wanda ya ƙara cewa ɗan uwansa komai Mubeenah ta fice daga ɗakin,....... *MAMA ABU* Tana kitchen tana girki, ta leƙo taga uban tarin wanke-wanken da suka tara, ta juya ta kalli Ma'u da take danne-danne a waya tace "Ma'u yanzu bazaki tashi kiyi wanke-wanken nan ba?". Ma'u hankalin ta akan waya batare da ta ɗago ba, tace "kiyi hakuri kiyi na yau kawai mama dan gaskiya bazan iya ba, gobe zan ne momiki me aiki kafin na tafi". Mama tace "shikkenan amma ina zakije Ma'u?". Ma'u tace "Abuja mana ai dama na faɗa miki". Mama tace "to Allah ya kaimu". Tana faɗan haka ta fito ta ɗebo ruwa ta fara wanke-wanken, Ma'u kuwa tana zaune tana danne-danne a waya, idan taga abin dariya takwashe da dariya, ita kuwa mama tana rana tana wanke-wanken ta, shi kuwa Tanko tunda aka fasa auren sa da Ayrah da suka samu matsala da Ma'u har yau bai ƙara dawowa gidan ba,...... *MAYA* Bayan fitar Mubeenah ita ma ta, tashi ta shiga bathroom tayi brush ta fice, kitchen ta nufa, amma taga Mami da su Mubeenah har sun gama komai sun jere a dining, ɓangaren fadilah ta nufa inda ta sameta ita da Mubeenah suna ta labarin abinda ya faru, a gurin get together da sukayi, zama itama tayi a falon, tana kallon TV idon tane kawai yake kan TVn amma hankalin ta ya tafi Madina, to ita rabonta da Amjad tun yana Nigeria ta kirasa, kusan 4 bayan tafiyarsa in several times amma baya picking, tana zaune can wani tunani yazo mata, ta buɗe datar ta, ta shiga Whatsapp tayi searching numbern Jaddah, ai kuwa tayi sa'a Jaddah tana online batayi wata-wata ba, ta kirata vedio call, bayan Jaddah tayi picking tace "Assalamu alaikum". Maya tace "wa alaikissalam kyakkyawar tsohuwa". Jaddah tace "to idan ma gatse kike min kin tadda gaskiya Maryam dan kema a kyawun nawa ne kika samu ka ɗan". Maya tayi murmishi tace "ai kuwa kam". Jaddah tace "yakike to?". Maya tace "lafiya alhamdulillah". Jaddah tace " ya su Mamin naku da su Mubeenah?". Tace " suna lafiya". Jaddah tace "ina kishiya ta da mijin ta?". Ai kamar jira fadilah take, ta taso ta wafce wayar a hannun Maya tace "mijina yafi ƙarfin ki Jaddah gara ma ki daina cemin kishiya dan babu abinda mijina zaiyi dake". Jaddah tayi dariya tace" to ai shi kuma yana sona". Mubeenah ta leƙo tace " faɗa mata dai Jaddah amaryar yah Ahmad". Jaddah tace "turamin account numbern ki, Mubeenah dole na saka Miki wani abu". Fadilah tayi dariya tace " Jaddah amma dan Allah ga Yah Amjad a gurin ki, ga Yah Ammar ki rasa wa zaki ce kina so sai mijina". Jaddah tace "to ai mijin naki duk yafi su nutsuwa da hankali, shi Ammar magana ma wani lokacin wahala take masa, kuma ba'a kallon dariyar sa kullum fuskarsa a murtuƙe". Fadilah tace "to ai shikkenan sai ki auri Yah Amjad". Jaddah tace "gaskiya bazan iya auren sa, ba saboda wannan bai min ba kwata-kwata shima ai banbancin sa da Ammar ɗin kaɗanne". Har fadeelah zatayi magana, Mubeenah tayi saurin cewa " Jaddah dan Allah ki nuna min Yah Amjad". Jaddah tace "baya nan ya fita gurin aikin da yakeyi ku dai kuci gaba da kula masa da Company yana aiki tuƙuru a nan saboda cigaban Company". Mubeenah tace "insha Allahu Jaddah". Jaddah tace "karku cika ni da surutu sai anjima ". Tana faɗan haka ta kashe wayar ta, suka miƙawa Maya da take zaune tana sauraron duk hirar tasu da Jaddah, wayar ta, Maya ta karɓi wayar ta, ta ajjiye ta akan kujerar, ta tashi ta nufi bathroom ɗin falon alwala ta ɗauro ta fito, ta shiga ɗakin fadeelah ta gabatar da Sallah bayan ta fito bata ga Mubeenah ba, itama wayar ta, ta ɗauka ta fice, ta nufi ɗakin su....... *AYRAH* Washe gari da safe da wuri ta, tashi ta shiga kitchen ta haɗa musu breakfast ta jere a dining, ta koma kitchen ta wanke duk wasu abubuwan da tayi amfani da su, ta gyare kitchen ɗin, kamar ba ayi amfani da shi ba, ta wuce ɗakin su Liyana ta taimaka musu suka shirya, tana zaune tana sakawa Khalil riga, tace "zanyi kewar ka Khalil". Khalil yace "aunty ai zamu dawo da wuri". Tace " to Allah ya dawo min da ku lafiya". Daga nan bata ƙara cewa komai ba, tace " ku fito kuje dining kuci abinci". Suka ce to, suka fito suka nufi dining, ita kuma ta koma ɗakin ta, tayi wanka ta shirya cikin ɗaya daga cikin bluen abaya wacce Amjad ya siya mata, tunda ta ciro kayan acikin kayanta, take hawaye, a bayyane tace "nayi kewarka Yah mufaddhal ɗina, ina fatan duk inda kake kana lafiya ta share hawayen da yake bin fuskar ta, tace " Ni kuma kalan tawa ƙaddarar kenan, rasa wa 'yanda nake so a rayuwa ta". Hijabi ta ɗakko maroon babba ta saka, ta nufi ƙofar fita, a dinning ta samesu kusan kowa ya hallara, tana zuwa ta ɗebi nata abincin ta faraci, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tayi kuka sosai saboda yadda idon ta, ya kumbura, ba tare da ta kalli Abubakar ba, tace "good morning uncle ". Yace "morning ". A taƙaice, tanajin idanunsa suna yawo akan ta, tace " good morning aunty ". Jiddah tace"good morning Ayrah ". Ta maida kallon ta kan Jabeer tace "good morning uncle Jabeer ". Yace "morning " shima a taƙaice, abincin ta, tafaraci, bayan sun gama Abubakar ya fice shi da su Liyana zai ajjiye su a school sai ya wuce gurin aiki, basu daɗe da fita ba, shima Jabeer ya fita hannun sa riƙe da lab coat ɗayan Kuma riƙe da bakar jaka, shima ya fice, Ayrah bayan ta tattare komai ta kai kitchen ta, Jiddah ta fito itama zata wuce gurin aiki, Ayrah ta kalle ta, tace " aunty akwai wani surprising ɗin da zan miki, idan kin dawo ki shiga ɗaki na kan mirror zan ajjiye Miki abu ko menene kika gani, ki buɗe ke ka ɗai kuma ina fatan kiyi amfani da shi, Jiddah bata kawo komai a ranta ba, tace "tom shikkenan na Miki alƙawari". Ayrah tace "Nagode". Jiddah bata ce komai ba ta fice, misalin ƙarfe 2 na rana tana gurin aiki, Abubakar ya kirata, Yace " mata ya dawo ya duba ko ina bai ga Ayrah ba, cikin tashin hankali ta nufo gida ko da ta, ta iso sun duba ko ina agidan nan basu ga Ayrah ba, tuna abinda Ayrah ta faɗa mata kafin ta fita da safe, ya saka ta, nufar ɗakin Ayrah da sauri, tana shiga ta rufe ƙofar ɗakin, ta nifi gaban mirrorn Ayrah taga wata farar fefar Please cap ɗauke da rubutu, ta buɗe ta fara karantawa kamar haka:-......... *Dan Allah ku daure mutanena ku shiga BAYAN DUHU DISCUSSION FORUM 📚 kuna comments domin karfamin guiwa, sannan dan Allah kuna liking da reacting, Love You all, thank you*......... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 18.......... _______ Jiddah ta fara karantawa kamar haka:- *Assalamu alaikum aunty nasan lokacin da zaki riski lattern nan nayi nisa da gidan ki, da farko ina so na fara da gode Miki, saboda taimaka min da kikayi kema ina Miki addu'ar Allah ya taimaka miki, kamar yadda kika taimake ni, aunty akwai abubuwan da na gani a gidan ki, kuma nakeso na taimaka miki kamar yadda kika taimaka min, kin banzatar da rayuwar yaranki da na mijinki bayan Manzon Allah da kansa yace duk kan ku ma kiwata ne kuma za'a tambaye ku akan abinda kuke kiyo, yanzu idan kika mutu Ubangiji ya tambaye ki ya kikayi da kiyon da ya baki, na yaranki da mijinki wace amsa zaki bashi? Aunty karki nemi duniya fiye da lahirar ki, idan har uncle ya miki rantsuwar bazai Miki kishiya ba, bakya tunanin zai iya neman matan banza saboda banzatar da shi da kikayi, aunty mijinki yana ƙaunarki shiyasa har ya miki rantsuwar bazai miki kishiya ba, amma ke da kanki kina neman kai mijinki wuta bayan kinkai kanki, aunty yaranki suna buƙatar ki, sosai basu san daɗin uwaba ko kaɗan, dan Allah aunty ki zauna ki gyara auranki kibar fifita neman duniya akan lahirar ki, and ni babu abinda yasaka na bar gidan ki sai alkhairi saboda inaso naga kin gyara rayuwar ki da ta mijinki da kuma ta yaranki, kuma ina fatan zakiyi hakan, daga ƙarshe ina mai ƙara gode miki da taimaka min da kikayi, kina cikin mutanen da bazan taɓa manta alherin su ba, a gareni Nagode sosai ki gaishe min da su Khalil zanyi kewarku sosai kuma ina fatan Allah ya ƙara haɗa fuskokin mu watarana* Jiddah tasaka hannu ta share hawayen ta bayan ta gama karantawa, a fili ta furta "Nagode Ayrah Nagode sosai da taimakawa rayuwa ta sa kikayi ina fatan Allah ya tsare ki a duk inda kike Allah yasa ki faɗa hannu na gari". Tana gama faɗan haka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya a ranta, tace"lallai na yadda da duk wanda ka taimaka indai kayi da zuciya ɗaya, shima watarana zai taimake ka". Sai da ta gama kukan ta kafin ta tashi ta fito, ta samu Abubakar da Jabeer a zaune a falo, fuskokin su ɗauke da damuwa, suna kallon ta suka fara tambayar ta "Lafiya?". Ta yi murmishin ƙarfin hali tace "Ayrah ta barmin saƙo tace ta tafi bazata dawo ba tana fatan Allah ya haɗa fuskokin mu watarana". Take Abubakar ya fara gumi, Yace "bayan nan babu abinda ta faɗa miki?". Jiddah tace "shikkenan ko dai dama akwai wani abu ne?". Yace "babu komai ina nufin ko ta faɗa miki gurin da taje ne?". Jiddah tace "bata faɗa min ba". Tana faɗan haka ta wuce ɗakin ta, wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigar Atamfah ta fito ta nufi kitchen zata ɗaura musu abinci kamar wacce akace ta juya tana juyawa ta kalli dinning sai taga warmers a jere, batasan lokacin da fara hawaye ba, kawai ta juya ta nufi ɗakin ta, a ranar haka ta yini jikin ta babu ƙarfi, misalin ƙarfe 5 na yamma tana kitchen tana girki Liyana ta shigo da gudun ta, turus tayi ta tsaya tana kallon Jiddah tace "momy yau kuma kece me mana girki mommy ina aunty?". Jiddah ta juyo tana murmishi tace "nice me muku girki yau, aunty kuma yau maman ta, ta kirata ta tafi gidan su amma zata dawo". Liyana tace "to Allah ya dawo da ita lafiya". Jiddah tace "Ameen". Ta juyo tana kallon ta, tace "muje na taimaka muku kushirya sai kuzo muyi dinner daga nan mu muje mu sha ice cream". Leenah da basu da daɗe da ƙarisowa ba, suka rungume Jiddah suna farinciki, ta rungume su tayi tana hana hawayen idonta zubowa saboda kar su gani, bayan sun shirya sun fito Sunyi dinner, Jiddah tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda light blue, sai ƙamshi take yi da veil ɗin ta white, tayi kyau sosai, ta fito daga ɗakin ta, ta wuce ɗakin Abubakar, ta sameshi yana zaune a bakin gado yana danna system ɗin sa, da mugun mamaki ya ɗago yana kallon ta har ta ƙariso ta zauna a gefen sa tace "Barka da aiki Darling". Yace "Barka dai sweetheart". Tace "dama magana nake so muyi". Ya ɗago kansa yana kallon ta yace "ina jinki sweetheart ". Hawayen da take riƙewa ne suka fara zubowa, ta zame ƙasa tace " nasani na cutar da kai sosai na cutar da yaran mu, ban kasance uwata tagari ba kuma ban kasance mata gari a gareku ba, wallahi nayi da nasani kuma ina roƙon ka dan Allah kayie hakuri ka yafe min , nayi maka alƙawarin zan kasance muka mata tagari kuma uwa tagari, zan kula da kai kuma zan kula da yarana". Ya saka hannun sa ya ɗago ta ya dawo da ita kan gadon ta zauna a gefen sa, ya juyo yana facing ɗin ta, ya saka hannu ya share mata hawayen fuskar ta, yace "na yafe miki sweetheart dan Allah ki daina kuka kinji, Allah ya miki albarka". Tace"Ameen Nagode ". Sai kuma ta fara murmushi tace "zamuje shan ice cream da yarana kaima kabar aikin nan sai mun dawo". Yace " da dare nan". Tace "wani dare shiyasa ma mukayi dinner nan mu da wuri yanzun fa duka-duka 8 ne". Yace "ok barin shirya ". Tace " barin taimaka maka ka shirya da wuri mu tafi". Ta faɗa tana tashi ta nufi wardrobe tana duba masa kaya, ya bita da ido yana jin wani sanyi da nutsuwa suna ratsa zuciyar sa, a ransa ya na yiwa Allah godiya da baibarsa ya aikata zina da Ayrah ba, kuma yana ƙarayiwa Allah godiya da ya canzawa matar sa ra'ayi, ta juyo ta kalle shi, tace "gobe zan ajjiye aiki ". Yace" Meyasa ". Tace "saboda kula da ku yafi min aikin muhimmanci, kuma ai dama babu abinda na nema na rasa agidan nan, gara na fara business ". Yace"Tom shikkenan Allah ya taimaka kuma Allah ya Miki albarka". Tace "Ameen mijina farinciki na".......... *MAYA* Suna zaune a dining suna dinner ta kalli daddy tace "daddy gobe insha Allahu idan su Abbie suka zo zan bisu mu tafi Abuja". Daddy yace "Allah ya kaimu amma yaushe zaki dawo". Tace "bazan daɗe ba daddy ". Mubeenah tace" sisy yanzu tafiya zakiyi ki barni". Maya tace "to kishirya mu tafi mana". Mubeenah tace "ki bar waye a Company?". Maya tai shiru bata ce da ita komai ba, ai kuwa haka akayi, bayan su Abbie sun zo anyi Engagement ɗin Mubeenah da Aliyu, ta shirya kayan ta tabisu Abbie zuwa Abuja,........... Maya tana zaune a falo ta zubawa photon Amjad da Aliyu ido wanda tun suna yara akayi photon, farhan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ta ƙariso ta zauna a gefen Maya, Maya ta juya ta kalle ta, tace " Meyasa babu photon yah Amjad ko guda ɗaya a palon nan sai wanda suke yaran can". Farhan tace "shiya ɗebe su kaf gidan nan babu palo ko ɗakin da yake ɗauke da photon sa idan ba nasa ba, sai ɗakin Abbie, Maya tace "ok". Daga nan bata ƙara cewa komai ba......... *AYRAH* bayan ta bar gidan direct tashar mota, ta nufa, duk da batasan inda zataje ba, hannun ta ɗaya riƙe da akwatin ta tanaja ɗaya kuma ɗauke da jakar kayan ta, wacce ta baro gidan Mama Abu da ita, tana zuwa taji ana Abuja saura mutum ɗaya, mutumin ya tambaye ta yace"Madam Abuja ko Kaduna?". Tace "Abuja ". Yace "shiga mota ta cika". Ta shiga, ya saka mata akwatin ta a Boot jakar ta kuma ta shiga da abunta, motar su ta tashi sai Abuja.......... Ranar da suka isa dai a tasha ta kwana, anan ma aka sace mata, akwatin ta, ya zama daga ita sai jakar kayan ta, yanzu ma da yake misalin ƙarfe 9:00 na dare tafiya kawai take yi ba tare da tasan inda zataje ba, ta biyo ta wani layi inda maza suke zazzaune kana kallon su kaga 'yan iska 'yan shaye-shaye, sai da ta ƙariso sai tin su, ɗaya daga cikin su, yace "kunga wata cika" wani yace" gata kuwa kamar ita tai kanta, lallai kuwa yau zamu more". Tana jin haka ta fara sauri, ɗayan yace "ku tashi mu bita kar ta gudu". Ayrah najin haka ta fara gudu sosai kamar ƙafarta zata cire, su kuwa tuni sun tashi sun fara Binta da gudu, sosai take gudu amma basu kamota ba, ta juya tana kallon su, tana gudu ai kuwa ta gwaru da wani gini ta faɗi a gurin, sukuwa suna kallon haka suka ƙara gudu........ ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 19......... Ga nin sun ƙara gudu suna ƙoƙarin cin mata, ya saka ta saurin miƙewa, ta dafe goshin ta da yake zubda jini, ta cigaba da gudu, batayi gudu mai yawa ba ta ƙarisa bakin titi, ganin suna tun karota yasaka ta gyara goyon jakar da take bayan ta, motar da take tafowa ta fara tsayarwa, a ranta tana addu'ar Allah yasa motar ta tsaya, amma motar bata tsaya ba, ta wuce ta, take ta fara tsaida ta bayan ta, tanayi tana juyawa tana kallon su, hannun ta ɗaya dafe da goshin ta, ai kuwa taci sa'a ta tsaya, da sauri ta tsallako tana nufowa Maya tana cewa "dan Allah ki taimake ni Marainiya ce bani da kowa bansan kowa ba, wasu ne suka biyoni zasu min........". Bata ƙarisa wata mota da fito a da mugun gudu ta ɗeba ta, faɗi, sosai gaban Maya ya faɗi ta fito tana kuka, kafin kace me mutane sun taru agurin tuni me motar da ya bigeta kuma ya gudu, ganin Maya tana ta kuka suka tambaye ko ta san tane, tace "sistern ta ce". Tuni aka saka mata ita a mota suka wuce asibiti wani na miji guda ɗaya kuma ya wuce police station, ai kuwa sai da police suka shiga kafin aka fara aiki a Ayrah, Maya tana tsaye a bakin room ɗin da aka shiga da Ayrah, tana ta kaiwa da komawa, wayar hannun ta ce tafara wringing picking tayi tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren Abbie Yace "Maryam kina ina ne, har yanzu dare yayi baki dawo gida ba?". Tace" Abbie na ina asibiti ne". Yace "subhnallahi Maryam lafiya dai ina?". Tace "lafiya ƙalau Abbie wata yarinya ce ta samu accident a hanya shine na kawo ta hospital". Yace "ayya Allah ya bata lafiya barin zo nima sai naga jikin na ta". Tace "to Abbie barin tura maka address ɗin". Yace "ok". Tare da kashe wayar, ita kuma ta tura masa address ɗin,bayan wani lokaci sai ga Abbie da farhan sun ƙariso, farhan ta ƙarisa ta rungume Maya tace "aunty Maya ya jikin nata?". Maya tace "alhamdulillah sun fito da ita ma sun kai ta wani room". Farhan tace "ayya Allah ya bata lafiya". Likita ne ya ƙariso ya gaida Abbie tare da sanar musu yana buƙatar ganin su, a office ɗinsa, yana tafiya dukkanin su suka bishi a baya zuwa office ɗin nasa, Abbie ya zauna akan kujera , Maya ma ta zauna farhan kuma ta tsaya, Likitan yana zaune a gabansu, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya fara magana. “Alhamdulillah, yanayin lafiyarta ya fara daidaituwa. Amma akwai wani abu da ya kamata ku sani".dukkanin su suka maida hankali gareshi, Yace" Raunin da ta samu a kanta ya shafi ƙwaƙwalwarta,a yanzu tana fama da abin da ake kira partial amnesia, wato wani ɓangare na ƙwaƙwalwarta ya samu matsala, Ba wai ta manta komai ba ne, Za ta iya tuna wasu abubuwa, amma akwai wasu abubuwan da ba za ta iya tunawa ba". Abbie Yace "Shin za ta iya dawo da tunaninta?". Likitan ya ɗan yi shiru, sannan Yace"zai iya dawowa,Amma ba za mu iya cewa ga lokacin da zai dawo ba, Wasu abubuwa na iya dawowa a hankali, musamman idan ta samu natsuwa, Wani lokaci ko wani wuri, suna, magana ko wani abu da ya shafi abubuwan da ta taɓa fuskanta a baya zai iya tayar mata da wani ɓangare na tunaninta".Abbie Yace"Kenan ta manta da mutanen da ta sani?". Likita Yace" Erh Hakan na iya faruwa, Amma ba lallai ne ta manta da kowa ba, Tana iya tuna wasu mutane sosai, ta kasa tuna wasu, ko kuma ta tuna wani abu amma takasa tuna lokacin da abun ya faru". Likita ya ɗaura da cewa "Abu mafi muhimmanci yanzu shi ne kada ku matsa mata da tambayoyi, Kada ku tilasta mata ta tuna abin da ba ta iya tunawa,Ku ba ta lokaci, da kulawa da kwanciyar hankali, Idan tunaninta zai dawo, ya fi kyau ya dawo a hankali, saboda haka, idan tace ba ta san wani abu ba, ku yadda da ita kada ku ɗauka cewa tana yi ne don ta ɓoye wani abu. Ƙwaƙwalwarta ce ke buƙatar lokaci". Abbie Yace "insha Allahu zamu kula kuma zamu kiyaye da dukkanin abubuwan da ka faɗa, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ". Dukkanin su suka amsa da "Ameen ". Daga nan suka masa godiya tare da sallama suka fice, Abbie ne ya wuce zaije yayi making payment, bayan yayi, Ya dawo ya wuce room ɗin da likitan Yace suje Ayrah tana can, Abbie ya shiga bakinsa ɗauke da sallama ko da ya shiga, ya samu Maya tana zaune abakin gadon, ita kuma farhan tana zaune akan kujera, ko da ya ƙarisa ya tsaya yana ta kallon Ayrah can kuma ya kalli Maya yace " Yanzu ni zan wuce gida ɗaya daga cikin ku tazo muje, ta tafo muku da abubuwan da zaku buƙata sai Aliyu ya dawo da ita, dan ya kamata Ku kwana a gurin ta, bai kamata a barta ita kaɗai ba". Maya tace "Abbie ku tafi da farhan". Yace "Tom shikkenan farhan ɗin Abbie tashi mu tafi". Farhan tace "Tom shikkenan aunty Maya sai na dawo". Maya tace "Tom Abbie sai da safe". Yace "sai da safe, Maryam Allah ya bata lafiya". Tace "Ameen" daga nan suka fice suka nufi gida shi da Farhan, Maya kuwa ta zubawa Ayrah ido tana ta bin ta da kallo, a ranta tana jin ƙaunar yarinyar sosai kamar wacce ta daɗe da sani,................. Kwanan su biyu aka salla mesu suka koma gida, a kwana biyun da sukayi kaf gidan babu wanda bai zo ya zauna da Ayrah ba, duk da bata tambayar su, wacece ita da kuma matsayin ta agurin su ba, amma ta sake da su sosai, ......ta na kitchen tana girki ita da Farhan da yake Farhan itace age mate ɗin ta, amma Maya ta girme su, Maya zata kai 26 su kuma baza su wuce 21 ba, Farhan ta kalle ta, tace "sis kinsan menene?". Ayrah tace "no sai kin faɗa". Farhan tace "anjima zamuje mu miki registration na Neco, mu dawo nasan kafin a fara zaki warware sosai". Ayrah ta juya ta kalli farhan bayan ta rufe towan da take girkin, tace "Masha Allah sis gaskiya Nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairi ". Farhan tace"Ameen ya Allah, amma na tambaye ki mana?". Ayrah tace "ok Allah yasa dai nasani ". Farhan tace "kiyi hakuri idan kinji tambayar tawa wata iri". Ayrah tace "karki damu ki tambayeni kawai". Farhan tace "zaki iya tuna gidan ku da kuma iyayenki?". Ayrah tace "bana da iyaye bansan inda suke ba". Farhan tace "amma kin taɓa makaranta?". Maya da yanzu shigowar ta tace "Farhan kin taƙurawa ƙanwata da tambayoyi fah". Ayrah tace "ƙyale ta dai aunty ". Maya ta ɗauki cup ta buɗe pridge ta ɗauki goran ruwa, tace "dan Allah Farhan ki daina taƙurawa ƙanwata da tambayoyi ". Farhan tace "insha Allahu bazan ƙara ba aunty Maya". Maya tace"better". yayinda take ficewa". A ranar suka je suka yiwa Ayrah registration ɗin Neco, bayan sun dawo Maya tana zaune a ɗakin ta, tana vedio call da mubeenah, Maya tayi murmushi tace "Ni na manta ma ban tambaye ki ba ina Yah Ammar fah?". Mubeenah tace "ai shima ya tafi tun ranar ya koma gun aiki pass ɗin sa ya ƙare". Maya tace "ayya Allah sarki". Dai-dai nan Ayrah ta tura ƙofar ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, Maya ta amsa mata, tana murmushi, Mubeenah tace "ƙanwar taki ce ta shigo?". Maya tace "Erh mana". Mubeenah tace "bazaki nuna min ita ba". Maya tace "barin nuna Miki ita wallahi kuwa kuna kama". Tana faɗan haka ta kalli Ayrah tace " kizo ku gaisa". Ayrah ta, taso ta zauna a gefen Maya tana kallon Mubeenah, Mubeenah tana kallon Ayrah ta miƙe da sauri ta fara cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Maya tana tambayar ta Lafiya amma, ko tsayawa amsa mata, ba tayi ba ta fashe da kuka, Maya tace "why are crying Mubeenah what happened ?". Sosai Mubeenah take kuka ko sauraron Maya bata yi ba, ta kashe wayar............... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 19........... ______ Mubeenah na kashe wayar Ayrah ta tsaya tana kallon Maya, tace " meyasa take kuka?, ko dai ta Sanni ne?". Maya tace " kawai taga yadda kuke kama ne may be ya saka ta tsoruta". Ayrah tayi murmushi tace "aunty to ai ance kowa ma yana da masu kamar sa guda 7 a duniya". Maya tace "hakane kam". Haka Maya ta zauna a Abuja ta gagara komawa Kano, saboda Ayrah da kuma yadda suka shaƙu kwana biyun nan, babu abinda bata siyawa Ayrah ba tunda ga kan kayan sakawa, shower gels masu kyau da tsada , turaruka da dai sauransu, idan ka kalli Ayrah yanzu bazaka ce Ayrahn mama Abu bace, saboda yadda tasamu nutsuwa da kwanciyar hankali kuma daula da arziki suka zauna a jikin ta, tayi wani fresh kyaun ta ya ƙara fitowa hasken ta ya ƙara gyaruwa,....... Tana tsaye a gaban mirrow tana rolling gyale a kanta Farhan ta tura ƙofar ɗakin ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, Ayrah ta amsa mata sallamar, ta juya ta kalle ta, bayan gama rolling gyalen a kanta, sanye take da abaya blue tayi kyau sosai, kallo ɗaya zaka mata ka gane ta haɗa jini da larabawa, kallon Farhan tayi, tace "sis sannu da dawowa". Farhan tace "Yawwa sannu". Yayinda take ajjiye school bag ɗin ta a gefen mirrorn, bayan ta ajjiye ta kalli Ayrah tace "yana ga kina ta shiri ne, kuma sai fara'a kike tayi sosai". Ayrah ta kalli Farhan da take ƙoƙarin cire abayar jikin ta daga saman school uniform ɗin ta, tace "kin manta aunty tamin alƙawarin idan na maida hankali nayi exam ɗina, nagama lafiya zata siya min waya". Farhan tace "ban manta ba". Bayan ta cire abayar riga da wandon uniform ɗin ta, suka bayyana, wando ne ash colour sai kuma farar riga, Ayrah yayinda take fesa turare a jikin ta tace " to shine fah yanzun zamu fita a cika min alƙawarina". Farhan tace "ai kuwa Nima dani za'aje barin yi wanka na fito dan Allah ku jirani". Ayrah tace "Tom shikkenan amma dan Allah karki daɗe". Farhan tace "insha Allahu". Daga nan ta fara rage kayan jikin ta, ta shiga bathroom, ita kuma Ayrah ta fice daga ɗakin ta nufi ɓangaren ammie, bakin ta ɗauke da sallama ta shiga palon, ta samu ammie da ya Aliyu ta samu a falon, ta ƙarisa ta zauna a gefen Ammie tana kallon Yah Aliyu tace "ina yini". Yace"lafiya ƙalau Ayrah". Tunda ta shigo take ta kallon sa tace "Ammie ina wuni". Tace "lafiya ƙalau Ayrah na, har kun shirya?". Tace" Erh Ammie ". Ammie tace "ina twins sistern naki". Tace" yanzu ta dawo daga school tana wanka". Aliyu ya daga kai a karo na babu a daɗi suka haɗa ido da Ayrah, Yace "Ayrah yaya dai?". Tace "babu komai kawai dai inaji kamar na sanka ne". Yayi murmushi Yace "anya kuwa to amma a ina kika Sanni?". Tace"wallahi na kasa tunawa". Yace"ikon Allah zata iya yiwuwa amma ni dai bansan ki ba". Tace "to tayiwu wani me kama da kai ne". Yace "it will be". Ammie tace"Ayrah na ina auntyn naki?". Ko rufe bakin ta batayi ba, sai ga Maya ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ta zaune gefen Aliyu ta gaida Ammie, sannan ta juya ta gaida ya Aliyu, Yah Aliyu yace " wai ina zakuje ne haka?". Maya tace "sisy na tagama exam ɗinta kuma na tabbata tayi ƙoƙari sosai shiyasa tun kafin result ɗin ya fito, za muje yawo sannan muje na siya mata phone, kaima ka kawo contribution ɗinka". Yace "Masha Allah ai kuwa dole na kawo contribution ɗina". Ya juya ya kalli Ayrah sannan Yace "congratulation sister ". Tace "thank you Yah Aliyu ". Yayi murmushi Yace" ki faɗa min abinda kike so insha Allahu I will buy it for you". Tace "Nagode sosai Yah Aliyu insha Allahu zan faɗa maka amma sai nayi tunani". Yace " Tom shikkenan ina jiranki amma sai naga result ɗin ki yayi kyau sosai". Tace "Tom shikkenan Yah Aliyu thank you". Maya tace "kinga Ayrah tashi mu tafi naga maganar ki da Yah Aliyu ba ƙarewa zatayi ba". Ayrah tace "Aunty bari naje na kira farhan ". Tana faɗan haka ta miƙe, bata daɗe da fita ba sai ga ta ita da Farhan sukayi yiwa su Ammie sallama sannan suka fice, gurin sai da waya suka fara zuwa, suka aka siya mata wayar ta iphone 15pro. tayi registern sim sannan suka wuce, Hans&René, domin shan ice cream, gurine mai kyau da tsafta, suna zuwa suka zauna, sukayi ordern ice cream da cookies, bayan an kawo musu Farhan ta kalli Maya tace "Aunty Maya ni yaushe Yah Amjad zai dawo ne?". Ayrah tace "wallahi nima na ƙosa naga farincikin rayuwar Aunty na". Farhan tace "Yawwa Ayrah ke baki da saurayi ne?". Tace "ina da shi, akwai wanda zuciya ta, take mutuwar so, kamar yadda aunty take son uncle Amjad" Farhan tace "Masha Allah to meye sunan sa?". Ayrah tace "ban sani ba wallahi, Ni dai kawai inajin zuciya ta tana ƙaunar sa ne". Farhan tace " Masha Allah, Allah ya bar ƙauna". Maya tace "Ameen". Ayrah tace "to ke fa baki taɓa bani labarin wanda zuciyar ki take so, ba Aunty na kam kullum sai ta bani labarin uncle Amjad". Farhan tace "wallahi Ayrah ni bana soyayya ban taɓa kula wani ɗa na miji da sunan soyayya ba". Ayrah tace "Ayya Allah sarki na fahimta". Haka dai suka sha hirar su, bayan sun gama suka tashi Maya tayi making payment suka fita, suna zuwa jikin mota, sukaji ance "Assalamu alaikum". Dukkanin su, suka juya suna kallon sa, Ya kalli Ayrah , Yace "kamar Ayrah". Tace "nice ina yini?". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah Ayrah ya kwana da yawa". Tace "alhamdulillah sai dai bangane ka ba". Yace" haba dai amma wasa kikeyi ko?, uncle Jabeer ne fa, na gidan aunty Jiddah". Tace "Aunty Jiddah kamar dai nasan ta, amma wallahi na kasa tunawa". Jabeer yace" ban fahimci kin manta aunty Jiddah ba". Maya tace "uncle Jabeer ina yini". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Tace "idan babu damuwa zamu iya magana". Yace " why not?". Maya taja gefe ya bita, Maya tana kallon sa tace "kasan ta ne?". Yace " Erh mun zauna da ita a gidan yayana a Kano rana ɗaya muka ne Meta muka rasa, amma meyasa kika tambaya?". Tace "she had an accidental, ta samu bugawa a brain ɗin ta, ba komai take tunawa ba, amma kai ɗan uwanta ne?". Yace "kina nufin yanzu tana fama da partial amnesia kenan?". Maya tace "Erh ". Yace "ikon Allah, sai kuma ya juya yana kallon ta, Yace "amma wannan yarinyar tana fama da jarrabawar rayuwa kala-kala, Allah Ubangiji ya kawo mata ɗauki". Maya tace "Ameen". Yace "idan babu damuwa zan isa samun nimbern ta ko na ɗaya daga cikin ku, akwai maganar da nake so muyi". Maya tace "babu damuwa barina baka numbern ta, yanzu muka yi registern sim ɗin amma anjiman insha Allahu zamu ɗaura akan waya". Yace "ok inajinki". Maya ta buɗe hand bag ɗin ta, ta ciro sim ɗin, ta faɗa masa numbern tare da mayar wa hand bag ɗin ta, ya kalle ta, Yace " Nagode". Tace "nevermind". Daga haka suka koma inda Ayrah take, tana ta kallon sa har ya ƙariso, yayi murmushi yana kallon ta, Yace "Madam marar gaisuwa kin kasa tunani ko?". Tayi murmushin ƙarfin tace"Erh". Yace "Tom shikkenan nagode ni zan wuce, insha Allahu zanzo har gida muyi magana". Tace "thank you ka gaida mutanen gidan". Yace "zasuji". Ya wuce abinsa suma suka shiga mota suka koma gida, tun da suka shiga motar Ayrah bata ce ƙala ba, ta jinginu da seat ɗin, ta lumshe idanun ta, suna ƙarisawa gida ta fita, ta wuce ɗaki ko ta kansu bata biba, tana shiga ta faɗa kan gado ta fashe da kuka.............. Mubeenah tana kashe wayar ta share hawayen ta, ta tashi ta buɗe wardrobe ta ciro hijabi ta saka , ta fice ta nufi ɓangaren Daddyn su, bakin ta ɗauke da sallama, ta samu daddy yana zaune akan kujera fuskar sa ɗauke da glass ya riƙe Alqur'ani a hannun sa yana karatu, ta ƙarisa falon ta zauna a ƙasan carpet ɗin, sai da ya kai ƙarshen a yar ya ɗago yana kallon ta, yace "Wa alaikissalam mubeenah". Tace " Daddy Barka da karatu". Yace"Barka dai mamana lafiya?". Tace" Daddy dama magana nake so muyi". Yace"inajinki". Ya faɗa yayinda yake rufe Alqur'anin ya ajjiye, tace" Daddy dama akan baiwar Allahn da Maya ta tsintane, ɗazu muna vedio call nagan ta, wallahi Daddy muna kama sosai kuma a jikina naji ita ɗin jinina ce wallahi Daddy". Ta ƙarisa maganar tana hawaye, Yace " Abbie ma ya Kirani munyi magana akan yarinyar yace zai bincike ta kuma Insha Allahu duk halin da ake ciki zai sanar da ni, mubeenah tace"Tom shikkenan daddy Allah yasa muji alkhairi". Yace "Ameen ". Mubeenah tace"kuma Daddy ina zargin mahaifin ta shine wanda suka rasu tare da Yah Kamal". Daddy yace"idan ma shi ɗinne ke ya akayi kika sani". Tace"Daddy lokacin munje duba jikin hajjah muna dinner Dr kamal yake cewa yaga wata me kamata ta kawo mahaifin ta asibitin su, har yake cewa mommy kamannin da muke ya ɓaci kawai dai ta fini haske mai kyau ne". Daddy yace "ok yanzu dai mujira miji abinda Alhaji Abdullahi zaice". Mubeenah tace "Tom shikkenan ". Daga nan suka canza wata hirar......... Kuka tayi me isarta, sai yau take jin ciyon kasa tuna wani abu a rayuwar ta, bayan ta gama kukan ta, tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito tasaka doguwar riga marar nauyi, Farhan ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama bata jira Ayrah ta amsa mata ba, tace "kizo Abbie na kiranki, a main falo". Ayrah taji zuciyar ta tayi wani mummunan bugu, ta buɗe wardrobe ta ɗauki hijabin ta, tasaka ta fice, a main falo ta samu, Abbie, ammie, yah Aliyu Maya da kuma Farhan, ta zauna a ƙasan carpet tana gaida Abbie ya amsa , sannan Yace "duk kan mu nan mun hallara ne dalilin ki, inaso na Miki wata tambaya kuma ina so ki faɗa min gaskiya tsakanin da Allah kinji mamana". Tace"insha Allahu Abbie zaka sameni da faɗan gaskiya". Yace"Masha Allah, kin san mahaifin ki?". Tace"Erh nasan shi, sun cemin ya ƙone a jirgi da shi da wani likita Dr kamal wanda ya taimake ni ya fitar da shi waje, domin sama masa lafiya". Dukkanin su suka ɗago kai suna kallon ta with shock kenan mahaifin ta ne ya rasu tare da Yah Kamal?, Abbie Yace "kin san 'yan uwansa tace"ban sani ba ". Yace "ko kina da photon sa ?". Tace "Erh ". Yace "jeki ɗakko min". Ta tashi ta fita bata daɗe ba sai gata da photo ta durƙusa ta miƙawa Abbie, ya karɓa yayi snapping ya turawa Daddy,........ Daddy suna zaune shi da mubeenah yaji ƙarar shigowan saƙo, dubawa yayi yaga Abbie ne ya turo masa photo ta Whatsapp, a mugun zabure Abba ya miƙe yana kallon Mubeenah bayan ya buɗe photon yace "hasashen ki ya zama gaskiya wannan photon Ibrahim ne tare da ni da kuma A saraki da autar mu". Yayi sauri yayi dailing numbern Abbie, Abbie yayi picking tare da sallama ya saka a speaker, Daddy yace photon nan na mune lokacin muna yara ni da A saraki da kuma ƙanin mu da ya ɓata wanda har yau hajjah take, jinya saboda rashin sa, ta tabbata wannan yarinyar jinin ɗan uwan mune". Sosai Ayrah ta fashe da kuka mai sauti bayan taji abinda Daddy yace............... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 21.......... _______ sosai familyn saraki suka cika da farincikin ganin jinin ɗan uwansu, hatta Hajiya autar su Alhaji Abdullahi saraki wato Hajiya sai da aka kirata aka sanar mata, farinciki agun Hajjah kuwa ba'a cewa komai, a ranar ta fara shirin baro ƙasar da take zuwa Nigeria, washe gari gidan Alhaji Abdullahi saraki da gidan Alhaji Mustapha saraki wato mijin Mami, jirgin su yayi landing a Abuja, farinciki agidan Abbie ba'a cewa komai, sai nan suke yi da Ayrah musamman mubeenah ta yadda take janta ajiki ba'a magana, Ayrah da mubeenah suna zaune a falon Ammie suna ludo, a wayar mubeenah Dr Ahmad ya shigo , shida fadilah Ayrah ta ɗaga kai tana kallon sa, tace "ina yini". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Ta kalli Mubeenah tace "shima a gidan ku, yake ko agidan Daddy saraki?". Mubeenah tace "yayana ne maman mu ɗaya amma Allah yayiwa mamar mu rasu, amma sai dai bamu san maraici ba, saboda matar daddayn mu Mami ta riƙe mu da amana sosai". Ayrah tace "ayya Allah sarki". Shi dai Dr Ahmad tun da ya zauna yake mamaki, can ya miƙe yace "ina zuwa". Daga haka ya fice, ya buɗe datan sa, ai kuwa sai ga saƙon Amjad ya shigo, yana tambayar su ko sun isa Abuja lafiya, Dr Ahmad ya ƙirasa voice call, bayan yayi picking sun gaisa, Yace " bro ya kun isa Abujan ne?". Dr Ahmad yace "mun iso lafiya wallahi alhamdulillah". Amjad yace "Masha Allah". Dr.Ahmad Yace " yanzu wani albishir zan maka amma You will pay idan albishir ɗin ya maka daɗi". Amjad yace "ok ina jinka". Ahmad yace "wannan dai cousin sistern nawa da muka zo gani, kasan wacece?". Amjad bai kawo komai a ransa ba, yace "ya za'ayi na santa? Kaji ka da wani banzar tambaya". Dr. Ahmad Yace " she's your girlfriend A'ishatul Humaira ". Amjad yace "wannan ba gaskiya bane". Dr. Ahmad yace "switch this call to vedio call zan shiga na nuna maka ita". Amjad yace "ok". Tare da yin switch ɗin call in zuwa Vedio call, Dr Ahmad ya shiga falon bakin sa ɗauke da sallama, lokacin Ayrah ta maida mubeenah gida a game ɗin da suke yi ta fara dariya tana yiwa mubeenah gwalo, dai-dai lokacin Dr Ahmad ya hasko ta, sosai zuciyar Amjad ta buga, saka makon kallon ta da yayi, Dr Ahmad ya samu guri ya zauna, yace "Yane Mallam send me, my money in my opay". Yana faɗan haka ya kashe kiran, a ɓangaren Amjad kuwa, fita yayi ya sanar da Jaddah abinda yake faruwa, Jaddah tace "Masha Allah ai dama muma gobe muke shirin tafiya ni da Nailah kawai sai mu tafi tare". Yace "Allah ya kai mu Jaddah". Yana faɗan haka ya fice, daga falon, Jaddah ta bishi da kallon tausayi a ranta tana matuƙar tausaya masa, saboda bata ga ta yadda auren sa da yarinyar da yake faɗa zai yiwu ba, bayan Maya tana rayuwar sa , abinda zata iya masa shine, ta taya sa da addu'ar Allah ya zaɓa masa wacce tafi zama alkhairi a rayuwar sa, ....... A ɓangaren Ayrah kuwa sosai taji adaɗin Kasan cewar ta da dangin mahaifin nata, duk da sometimes ta kan keɓe kanta gefe tayi kuka, tana jin ina shima mahaifin nata yana raye suga wannan ranar farincikin tare, wallahi tayi kewar mahaifin ta sosai kullum tana musu addu'a shi da ummin ta, ba dare ba rana, kwana ɗaya mutanen Kano sukayi suka tattara suka koma amma banda Hajiya autar su daddy da kuma Mubeenah, washe gari jirgin su Jaddah ya sauƙa a Nigeria, farinciki a gun Maya ba'a cewa komai, sosai tayi wannan tayi wancan, har lalle suka je aka musu ita da Ayrah, Black and red yayi kyau sosai abinka da fararen fata, Ayrah tana ɗaki tana danne-danne a wayar ta, sai yau wayar ma ta samu lokacin ta, wayar ta fara wringing da ido tabi numbern da ake kiran na ta, to ita waye me numbern ta, bayan duk 'yan familyn su tayi saving numbern su, kamar bazata yi picking ba, can dai tayi picking tare da sallama, bayan ya amsa, Yace "Madam marar gaisuwa fatan dai kun koma gida lafiya". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Yace "nasan baki gane me magana ba ko?". Tace "Erh wallahi ban gane ba". Yace " uncle Jabeer ne". Tace "ohhhh wanda muka haɗu da shi wancan ranar". Yace "Erh". Tace "ayya fatan kana lafiya". Yace " alhamdulillah". Tace "Masha Allah". Yace"dama kawai na kirane naji lafiyar ki, sai anjima". Tace"thank you". Yace "bye". Tare da kashe wayar, bayan ya kashe tabi wayar da kallo, Farhan da ke zaune akan bedside drower tana duba hand-out ɗin ta, tace "wanene wannan kuma sis?". Ayrah tace" wancan mutumin da muka haɗu dashi wancan ranar uncle Jabeer". Farhan tace "ayya Allah sarki". Mubeenah ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama tana kallon, Ayrah tace "sisy na kina nan ashe ina ta neman ki". Ayrah tace "wallahi kuwa aunty mubeenah". Mubeenah tace "to su Jaddah ne suka ƙariso tun ɗazu yanzu suna falon Ammie ki fito ku gaisa". Ai ko rufe baki, mubeenah ba tayi ba Farhan ta tashi ta fice da saurin ta, Ayrah ta miƙe ta ɗauki hijabin ta, ta saka suka fita tare da mubeenah, Maya da Amjad da Jaddah da kuma Ammie sai kuma Farhan da yanzu shigowar ta suna falon, suna zaune, Ayrah ta shigo bakin ta ɗauke da sallama ita da mubeenah, Jaddah ta ɗago kai tana kallon ta Ayrah ta ƙarisa ta zauna a ƙasan carpet tana miƙawa Jaddah gaisuwa, Jaddah tace"lafiya ƙalau alhamdulillah". Tana ta kallon Ayrah kamar me nazarin wani abu, Ayrah ta mai da kallon ta kan Amjad tace "uncle Amjad ina yini". Yace"lafiya Fulani". "Fulani ta maimaita abun a ranta, wasu memories suka fara dawo mata, "yaushe ƙarya zata fara shiga tsakanin mu Fulani?". Maganar da ya mata ranar da yazo Kano suka gaisa da ƙawarta Sa'adatu ya fara mata yawo, a hankali maganganu suka fara mata yawo a ƙwaƙwalwar ta.............. ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 22........... End of Book 1 _______ Jaddah dai tana ta kallon ta, can tace "ƙawata menene sunanki?". Ayrah tace "sunana A'isha amma ana cemin Ayrah ". Jaddah tace"Masha Allah suna mai daɗi". Ammie tace "ayya Allah sarki". Hajiya ce ta shigo hannun ta ɗauke da akwati, ammie tana kallon ta tace "Hajiya lafiya naganki da akwati haka?". Hajiya tace "wallahi zan tafi Kano ne amma insha Allahu kafin na wuce gidana zan dawo nan ɗin". Ammie tace "ayya Allah sarki to Allah ya tsare". Hajiya ta kalli Amjad tace "my son kazo ku ajjiye ni a airport kai da 'yar tawa". Amjad yace "to Hajiya". tare da miƙewa Har zai fita, mubeenah ta kalle shi, tace "Yawwa Yah Amjad ɗazu naji kace a sister na Fulani ita fa sunan ta Ayrah ba Fulani ba". Ya kalli mubeenah kamar ba zaice komai ba sai kuma Yace "ok". Hajiya ta kalli Ayrah tace "daughter zo ku rakani airport". Ayrah tace "to Hajiya" tare da miƙewa ta tabi bayan su, ko da suka isa har Amjad ya saka akwatin Hajiya a Boot Hajiya ta shiga back seat Ayrah Kuma ta shiga front seat, tun da suka fara tafiya ta jinginar da kanta ajikin seat ɗin ta lumshe idanun ta tana shaƙar ƙamshin turaren sa da ya haɗu da sanyin AC da yake ta shi acikin motar, tana ƙoƙwarin tuna wani abu a ranta tana ji kamar wannan ranar ta taɓa faruwa, Muryarsa taji ta dake dodon kunnen ta da wani sautin sa mai daɗin sauraro, Yace "Fulani naga kin rufe idonki ko dai bakyajin daɗi ne?". Ta buɗe ido ta kalle shi, cikin sanyin murya tace "lafiya na ƙalau". Yace "ok". Daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba har suka isa airport ɗin, suka sauƙa hannun Hajiya riƙe da na Ayrah shi kuma ya ja mata akwatin ta, Hajiya ta tambayi Ayrah ko tana da account ne, tace"a'a ita fah bata da account ". Hajiya ta kalli Ayrah tace "amma ai kina da national ID card". Tace "erh ina da shi". Hajiya ta mai da kallon ta kan Amjad tace "my son dan Allah ko zuwa gobe ma if you have time ka ɗauke ta ka rakata ko bank ɗin Abbie ne ta buɗe account". Yace "badamuwa Hajiya insha Allahu zan kai kaita ". Hajiya tace "Yawwa Nagode". Tare da musu sallama ta wuce, su kuma suka juya, suna cikin mota suna tafiya ya kalle ta, Yace "Fulani sai kuma naji labarin ke ahalin SARAKI ce". Tace "Erh fah". Yace "Fulani nasan yanzu kinsan komai game da Engagement ɗin da yake kaina ko?". Tace "nasani mana ko ba Engagement ɗin ka da Aunty na ba?". Yace "shi". Yace "amma yanzu menene matsayina a zuciyar ki?". Tace "uncle Amjad nifa ban fahimci akan me kake magana ba". Yace "amma ya akayi kika haɗu da Maya". Tace "wallahi Nima ban sani ba, nakasa tunawa". Yace "ban fahimta ba". Tace "bakomai nake iya tunawa saka makon bugun da na samu a brain ɗin na". Da mugun sauri ya taka burki, sai da ta ɗan bugu da seat ɗin motar, ta maida kallon ta kanshi tace "lafiya". Yace "kina nufin kina fama da partial amnesia kenan?". Tace "Erh haka likita Yace ". Yace "yanzu kina nufin Nima baki tunani ba". Tace "inajin kamar nasan ka tun ba yau ba, kuma ina iya tuna wasu maganganu da suka faru tsakanin mu, amma ban yadda irin maganar da nakeji ta taɓa shiga tsakanin mu ba kawai ƙwaƙwalwata tana yaudara ta ne". Yace "ikon Allah to Allah ya baki lafiya". Tace "amma fa inajin wani abu game da kai wanda shima ban yadda da shi ba". Yace "Allah ya baki lafiya". Tace "Ameen thank you". Da ganan babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana har suka isa gida, ........... *MA'U* ta tsaya tana binsa da kallo, kamar mai son ɓoye wani abu can kuma tace"aure fah kace sagir". Yace "Erh wallahi auren ki zanyi Ma'u idan har kin amince zaki aure ni, to ni bana da wata matsala ". Tace "sagir amma kasan fa rayuwar da muka yi a baya taya zakace zaka aureni kuma na amince da kai". Yace "wallahi Ma'u ko yau kikace min kin amince insha Allahu acikin satin nan zan turo magabata na, sai ayi maganar auren mu". Tace "amma........". Yace "amma me? Ko dai bakya sona ne Ma'u?". Tace "ina sonka mana amma inajin tsoron kar 'yan uwanka su zo bincike su binciko abinda na aika ta". Yace "karki damu babu wani bincike da zasu yi insha Allahu nasan yadda zanyi da su fatana kawai dai ki amince da aurena". Tace "babu komai sagir na amince Allah ya shige mana gaba ". Yace "Ameen Nagode ". Da ga nan sukai sallama ta fita daga motar ta shige gida". Tana shiga ta samu Mama Abu a zaune lantana sabuwar mai aikin su, tana shara, tana zuwa ta shige ɗakin Mama Abu tace "ki shigo zamuyi magana". Da sauri mama Abu ta tashi ta bi bayan Ma'u, ta sameta a zaune a bakin gado, itama ta zauna tana kallon ta tace " 'yar albarka lafiya". Ma'u ta kalle ta tace "sagir ne wani tsohon saurayi na ya zo wai aurena zaiyi". Mama Abu tace "aure kuma?". Ma'u tace "Erh shifa auren ko haramunne?". Mama Abu tace "a'a ba haramun bane". Ma'u tace "to ki sanar da 'yan uwanki, acikin satin nan dangin sagir zasu zo neman aurena, ko dan ma ashe dangin babana zasu je bana ki ba". Mama Abu tace "yanzu Ma'u aure zakiyi ki barni bayan da ke na dogara". Ma'u tace" aure fa babu fashi mama gara ma kisani ". Mama Abu tace " Ni kuwa wallahi banason kiyi auren nan". Tace "mama kawai ki fito fili kice baƙin ciki kike min da hassada kuma wallahi aure babu fashi ". Tana faɗan haka ta miƙe tai ficewar ta bata ƙara bi ta kan Mama Abu ba, Mama Abu da kallon mamaki haɗi da baƙin ciki da ta kaici tabi Ma'u, sai da Ma'u ta fice daga ɗakin Mama Abu ta tafka uban tagumi maganar auren tana mata yawo a zuciyar ta, yanzu idan Ma'u tayi aure ya zatayi ga shi dai sagir ɗin nan ba wani shegen mai kuɗi bane, ballantana ta saka a ranta, zata na samun wani abu agurin Ma'un bayan tayi auren, .............. *AYRAH*......... Washegari ita da Amjad da Farhan suka fita aka mata bvn aka buɗe mata account suka dawo, basu wani jima ba kasancewar su, masu bankin,.... Tana tsaye a kitchen tana wanke-wanken Farhan ta shigo kitchen ɗin tana kallon ta, tace "sis kije Jaddah tana kiranki". Ayrah tace "tana ina?". Farhan tace "tana ɓangaren ta". Ayrah tace "ok barinje". Tana faɗan haka ta fice daga kitchen ɗin ta nufi ɓangaren Jiddah a falo ta samu, Nailah tana kwance tana ta danne-danne a wayar ta, ta kalli, Ayrah tayi sallama Nailah ta amsa mata cikin fara'a ba tare da sanin itace wacce Amjad yake so ba, Ayrah ta ƙariso ta zauna tana kallon Nailah tace "sis Jaddah fah". Nailah tace "tana ciki". Ayrah tace "ok Nagode".tare da nufar ɗakin Jaddah, knocking tayi Jaddah dake zaune a bakin gado, ta bata izinin shiga, kafin ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, tana shiga ta zauna a ƙasan carpet tana gaida Jaddah, Jaddah ta amsa cikin fara'a kafin, ta kalle ta, tace "magana nake so muyi ƙawata". Ayrah ta sunkuyar da kanta tana wasa da carpet, dai-dai nan ya turo ƙofar ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, dukkanin su suka amsa masa, ya shigo shima ya zauna yana gaida Jaddah, ta amsa masa, itama Ayrah ta ɗago kai ta kalleshi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin fara'a, jaddah ta kalle ta, tace "ƙawata kin san Wannan?". Tayi maganar tare da nuna Amjad, Ayrah tace "Erh nasan shi". Ba tare da ta ɗago kai ta kalle shi ba". Jaddah tace "a ina kika sanshi kafin ki ganshi a gidan nan ". Tace "bansani ba, na kasa tunawa ni dai kawai abinda nakeji na sanshi tun kafin yanzu ". Jaddah tace " ya sanar min kun nemi mahaifiyar ki kun rasa tun shekarun baya". Hawaye ya fara bin ƙuncinta ta, ta saka hannu ta share tace "tabbas hakane". Jaddah tace" so nake ki bani labarin asalin mahaifiyar ki saboda mu taimaka Miki wajen nemo ta". Tace "jaddah wallahi bansani ba, bazan iya tunawa ba". Jaddah tace "shikkenan tashi kije". Ayrah ta, tashi ta fice tana share hawayen idanun ta, Nailah har yanzu tana zaune a inda take, bayan Ayrah ta fito, ta takalle ta tace "sis har kin fito?". Ayrah tace "Erh na fito". Daga haka babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana har Ayrah ta fice, yau girke-girke suke kala-kala saboda yau jirgin su Hajjah zaiyi landing a Nigeria.......... Misalin ƙarfe 4 na yamma motar su Hajjah ta shigo cikin gidan Aliyu ne, ya ɗakko su daga airport, ko da suka iso ɓangaren Jaddah suka nufa, ta kalli ɗayar ta ta, tace "ki taho mana ". Matar tana kallon Hajjah tace "wallahi Hajjah ji nake gabana yana faɗuwa". Tace "to kiyi addu'a mana, idan ma tunanin gidan ki, kike 2 days kawai zamuyi a nan gidan na maida ke gidan ki". Ita dai bata ƙara cewa komai ba, ta bi bayan Hajjah suka shiga ɓangaren Jaddah bakin su ɗauke da sallama, Nailah da yanzu fitowar ta daga kitchen, ta ƙariso ta rungume Hajjah tana tace “ƙawata". Hannun Hajjah riƙe da na Nailah suka ƙariso falon suka zauna, Aliyu ya shigo busu da akwatunan su, Nailah ta kalli matar da tunda suka shigo ta ke kallon ta, tace "ina yini ". Matar tace "lafiya". Dai-dai nan aka tura ƙofar aka fito Ammie ne da Maya da Farhan da kuma Jaddah tun ɗazu su Ammie suke ɓangaren Jaddah suna jiran ƙarisowar Hajjah ko fitowar su tayi dai-dai da ɗagowar kan matar nan, a mugun zabure matar ta, tashi tana kallon su, Jaddah tace "Fatima". Matar hawaye na bin ƙuncinta ta tafi da sauri ta rungume Jaddah tace "Ammie!". Jaddah ma hawaye take sosai, itama Ammie hawaye take, tace "Fatima ashe kece wacce Hajjah suka jinya?". Matar ta sake Jaddah ta rungume Ammie tana kuka sosai tace "Aunty". Suma kuka suke sosai , Ayrah tayi sallama ta shigo hannun ta riƙe da plate da jug da cups, ƙarar faduwar plate ɗin yasa dukkan su, juyowa suna kallon ta, da ko kula da plate ɗin da ta fasa batayi ba, ta wuce har tana taka wani, ta tafi da gudu ta rungume matar tana cewa"ummie". Itama sosai take kuka, Jaddah tace "Allah sarki ashe jikata muke riƙewa agidan nan batare da mun sani ba". Sosai Fatima take kuka tana rungume da Ayrah itama ayrahn haka,take Ayrah taji wasu abubuwa suna mata yawo a ƙwaƙwalwar ta, memoring ta ya dawo ta tuna komai, sosai take kuka, sai a lokacin Maya ta ƙarisa ta kama hannun tace " sisy na kinfa taka glass ɗin da kika fasa gashi ƙafar ki tana ta jini". Maya ta kalli Farhan da ita ma hawaye take tace "jeki kira Yah Aliyu yazo da first aid box ya bata taimakon gaggawa"...................... ___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________ FEATURE WRITERS ASSOCIATION.... *AISHA MUHAMMAD KABIR* *MER'EESHER ✍️* Book 1 Page 23........... ***** Bayan an bawa Ayrah taimakon gaggawa tana kwance akan kujera tana kallon ummin ta, ummin ta kuma tana zaune akan kujera tana cin abinci, ummi ta kalli Jaddah tace "Jaddah yaushe kuka dawo Nigeria". Jaddah tace "tunda muka ga kinyi shekara muka jiki shiru, shine muka tattaro muka dawo Nigeria". Ummi tace "ayya Allah sarki a ina kuka samu Ayrah kuma?". Jaddah tace "Maya ce ta kawo ta gidan nan ta haɗu da ita tayi accident shine ta taimaka mata". Ummi ta kalli Maya tace "ayya Allah sarki amfanin taimako kenan ga shi kin taimake ta, batare da sanin ita 'yar uwarki bace". Maya tace"wallahi fah ummi". Ummi tace "ayya Allah ya muku albarka". Dukkanin su, suka amsa da "Ameen ". Ummi ta kalli Nailah tace "jaddah kaddai wannan itace Nailah?". Jaddah tace "itace Nailah ". Ummi ta rufe plate ɗin abincin gabanta tace "alhamdulillah I'm okay". Maya ta tashi ta zuba mata lemon kwakwar da ta haɗa mata, a cup, ta miƙa mata ummi ta karɓa tace "thank you". Sai kuma tace "Maya kira min Mamin na ku mana". Maya tace "ok". Tare da dailing numbern Mami, Mami tayi picking tare da sallama, Maya ta miƙawa Ummi, Ummi ta karɓa, tace "wa alaikissalam". Daga ɗaya ɓangaren Mami ta miƙe daga zaunen da take hawaye yana bin ƙuncinta cikin muryar kuka tace "ukty". Ummi ta goge hawayen idonta, tace "ashe zaki gane muryata". Mami tace "to jini wasa ne?". Ummi tace "a'a ba wasa bane". Daga haka suka canza wata hirar, bayan wani lokaci sukayi sallama tare da kashe wayar, ta miƙawa Maya wayar ta, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo , dukkanin su, suka amsa masa, Maya ta tsaya tana kallon sa tana jin wani sanyi mai daɗi yana ratsa zuciyar ta, idonsa ya sauƙa akan ummi yana kallon ta, cikin rawar murya tare da shock lokaci guda, Yace "Ummi". Ummi ta miƙe tana kallon sa tace "Muhammad". Ya ƙarisa da sauri ya rungume ta, Yace "Ummi ina kika tafi kika barmu kiki barmu da kewar ki?". Tace "Nima nayi kewarku Muhammad". Kukan da Ayrah take riƙe wa ne ya fito fili, kuka take sosai abun ta bata damu da mutanen da suke falon ba , tasan baza su fahimci akan me take kukan ba, ta kalli Amjad sai kuma ta kalli Maya da take zaune a gefen ummin ta shima Amjad ɗin ya zauna a gefen ummin na ta, Ayrah ta ƙara fashewa da kuka tanajin zuciyar ta, tana mata wani irin ciyo, kamar zata fasa ƙirjin ta, ta fito, tashi tayi tana taka ƙafar a hankali, ta nufi ɗakin jaddah, tana zuwa ta faɗa kan gadon Jaddah tana kuka mai tsuma zuciya, Allah ya gani tana son Amjad sosai fiye da yadda zata iya misaltawa, amma Amjad ya cuceta meyasa bai taɓa faɗa mata yana da Engagement ɗin wata akansa ba, sai da ya bari zuciyar ta ta saba da sonsa sosai tanajin bazata iya rayuwa ba tare da shi ba,......... A ranar Mami tazo Abuja ita da ummi kamar zasu cinye junan su, kwanan ta biyu ta koma Kano, ita kuwa Ayrah a duk kwana biyun nan ta zama kamar marar lafiya duk abinda zai haɗa ta da Amjad bata son shi, bata son haɗuwa da shi, ko ɓangaren ammie ma sau biyu take zuwa a rana, taje ta gaida Ammie da safe sai kuma da Yamma, lokacin da Abbie ya dawo kusan yafi kowa farincikin ganin Ummi,...... Ayrah tana zaune a falon Jaddah tana danne-danne a wayar ta, Farhan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama ta zauna a gefen Ayrah tana kallon ta, tace "sis ki shirya mana anjima ki raka ni unguwa". Ayrah tace "dan Allah mu tafi yanzu ba sai anjima ba". Farhan tace "ikon Allah yanzu kuma?". Ayrah tace "Erh yanzu wallahi zaman guri ɗayan ya isheni". Farhan tace "ok barinje na shirya kema ki shirya sai mu tafi". Ayrah tace "ok". Yayinda ta tashi ta nufi ɗakin ta, dan tuni ta tattaro kayan ta ta dawo ɓangaren Jiddah , tana shiga bathroom ta wuce tayi wanka, ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar azahar, sannan ta shirya cikin doguwar rigar Atamfah mai kyau, veil, hand bag plate shoe, duka farare ta saka tayi kyau sosai, ta fito ta wuce ɗakin Jaddah, ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, ta zauna a ƙasan carpet ta gaida Jaddah, jaddah ta amsa cikin fara'a, kafin ta maida gaisuwar tata kan Hajjah, Hajjah ta amsa mata itama da fara'a Jaddah tace "mamana ina zuwa naga kin yi kwalliya haka". Ayrah tace "unguwa zan raka Farhan". Hajjah tace "Masha Allah to Allah ya tsare". Ayrah tace "Ameen Hajjahn mu ". Ta faɗa yayinda take tashi ta fice, ta shiga ɗakin ummin ta, bakin ta ɗauke da sallama, Ummi tana zaune a bakin gado Ammar kuma yana zaune akan dressing mirrow, dukkan su suka amsa, ta ƙarisa ta zauna a gefen ummin ta, tace "Ummi ina yini?". Ummi tace "lafiya ƙalau Ayrah na". Ayrah ta ɗaga kanta ta kalli Ammar da yake kallon wani direction da ban, tace "ina yini". Yace "lafiya". Lokacin Farhan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama itama ta shirya cikin Abaya blue tayi kyau sosai, ta gaida Ummi , Ummi ta amsa mata cikin farin ciki kafin ta gaida Yah Ammar, ya amsa kamar yadda ya amsa wa Ayrah, Ayrah tace "Farhan ta shi mutafi". Ina zakuje ya tambaya a tsare, Farhan tace "Yah Ammar zamuje shopping ne". Kamar ba zai yi magana ba sai kuma Yace "duk abinda zakuyi karku kai 2 hours a waje". Farhan tace "insha Allahu". Sai kuma ta juya ta kalli Ummi tace" Ummi mun tafi". Ummi tace "sai kun dawo Allah ya tsare". Suna fitowa suka samu Mubeenah da Nailah da kuma Maya suna zaune a falo suna Game ɗin ludo master, kamar ba Nailah ce mai gaba da su adaba, Maya ta Kalle su tace "lallai bayin Allahn nan wato fita ma zaku yi shine ko neman 'yan rakiya bakwayi?". Farhan tai sauri tace "ikon Allah wai dama Ayrah bata faɗa muku ba?". Nailah tace "karfa ki mata sharri Farhan inajin ki, lokacin ina kitchen kikace ta shirya ta rakaki wani guri". Mubeenah tayi dariya tace" Indai Farhan ce zata aikata abinda yafi haka ". Ayrah tace "aunty na an sake result fah". Maya tace "Erh zan duba miki ɗazu Yah Amjad ya tambaye ni wai wace makaranta kike son zuwa?, zai ne maki admission". Ayrah da taji wani abu ya bigi zuciyar ta, tai murmushin da iya kacinsa fuskar ta, tace "idan mun dawo za muyi shawara da sisy na". Tana faɗan haka suka nufi hanyar fita driver ne ya kai su saboda Ammie ta hana ta driving, restaurant suka fara tsayawa, suna zaune bayan an kawo musu abinci suna ci, kamar da ga sama Ayrah taji ance "Ayrah". Ta ɗaga kai zuciyar ta tayi mugun bugawa sakamakon kallon sa da tayi amma ta danne saboda kar Farhan ta fahimta, tace "uncle Bissimillah ka zauna mana". Abubakar ya zauna yana murmushi, tace "uncle ina yini, ya gida ya su aunty Jiddah?". Yace "suna nan lafiya ". Tace "Masha Allah". Yace "Ayrah yanzu a ina kike da zama?". Tace "na samu familyn Abba na da na ummie na, wannan ma cousin sister na ce". Ta ƙarisa maganar tana nuna Farhan, Farhan tace "ina yini". Yace "Lafiya fatan kuna lafiya". Tace "alhamdulillah". Sai kuma ya maida kallon sa kan Ayrah Yace " na daɗe ina neman ki Ayrah tare da addu'ar Allah ya ƙara haɗa fuskokin mu, na nemi yafiyar ki akan abinda ya faru". Tace "babu komai wallahi uncle karka ji komai ni na yafe maka, kuma tun a lokacin ni ban riƙeka a zuciya ta ba". Yace "Yawwa Nagode sosai Ayrah ". Tace"badamuwa ". Yace " sannan ina so na gode miki domin kin zama sanadiyyar dawowar farincikin gidana, yanzu Jiddah ta canza ta ajjiye aiki bata da aikin da ya wuce kula da mu, ni da kuma yaran mu". Ayrah tace "alhamdulillah amma wallahi naji daɗi uncle kuma nayi farincikin jin haka". Sai da ya musu marking payment ya karɓi numbern Ayrah, kafin ya musu sallama ya wuce, suma daga nan suka shiga mota suka wuce shopping, tana cikin mota taji wayar ta, tayi ƙara alamar shigowar massage, buɗe wayar ta duba, taga credit alert na 1M da mugun mamaki, ta ke kallon sunan wanda ya tura mata, Muhammad Ahmad QURAISH, ta kalli Farhan kamar zatai magana sai kuma ta fasa, bayan sun ƙarisa sun gama shopping ɗin su, suna ƙoƙarin fitowa , Ayrah hankalin ta yana kan wayar ta, taci karo da wata, da sauri ta ɗago da niyyar bawa wacce ta bige ɗin hakuri, da mugun mamaki ta tsaya tana kallon ta, ita ɗin ma ita take kallo, sai kuma ta daka tsalle ta rungume Ayrahn tana hawayen farin ciki tace "bestie". Ayrah tace " ƙawata nayi kewarki sosai ". Itama tana hawaye, Ayrah ta sake ta tana share hawayen idon ta, da bakin veil ɗin ta, tace " ina mama?". Sa'adatu tace "mama tana gida mun ne meki sosai har mun fidda rai kullum muna Miki addu'ar Allah yasa kina hannu nagari kuma cikin farinciki". Ayrah tace "ai nasamu familyn Abba da na Ummi, yanzu haka ma muna tare da Ummi na a gidan elder brothern ta". Cikin farinciki Sa'adatu tace "Masha Allah na ma fasa shopping ɗin kawai zan biku naje naga Ummi ". Ayrah tace "a'a kije kiyi shopping ɗin ki, kawai ki bani numbern wayar ki, insha Allahu gobe zamu zo har gida ni da ummi". Sa'adatu tace "shikkenan". Ta karɓi wayar Ayrah ta saka mata numbern ta, har zata tafi sai kuma ta tsaya tana kallon Ayrah tace "bestie amma akwai abinda yake da munki". Ayrah tace "zamuyi magana zuwa goben ko anjima ". Sa'adatu tace "Tom shikkenan amma ina Yah mufaddhal yake ?". Ayrah tayi murmushin da iya kacinsa fuskar ta, ne tace "yana nan". Sa'adatu tace "to bazaki gabatar min da ƙawar taki bane?". Ayrah tace "ohhhh I'm sorry she's my cousin sister me sunan Ummi ce, amma ana ce mata Farhan ". Sa'adatu tace "Masha Allah Farhan nice to meet you ". Farhan tace "nice to meet you too". Daga haka sukayi sallama suka wuce, ko da suka dawo gida, ɗakin ta ta nufa ta ajjiye shopping ɗin nasu, tayi wanka ta ɗaura alwala bayan ta fito, ta canza kaya zuwa doguwar riga marar nauyi, ta gabatar da sallar la'asar, tana kan sallaya wayar ta, ta fara wringing, kallon screen ɗin wayar tayi taga, baƙuwar number, picking tayi tare da sallama, yaji Muryar ta, ta daki dogon kunnen sa, ya amsa mata sallamar, sai shiru ya biyo baya, Yace "Fulani". Har cikin zuciyar ta taji kiran da ya mata, maimakon ta amsa sai tace "naga alert ɗazu Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Allah ya ƙara arziki". Yace "Ameen Fulani na, Allah ya Miki albarka". Tace "Ameen". Yace "kun dawo ne?". Tace "Erh mun dawo". Yace "kinyi Sallah?". Tace "Erh". Yace "Masha Allah, to abinci fah?". Tace "munci abinci dasu yanzu kuma banajin yunwa". Yace "shikkenan Fulani na Allah ya Miki albarka". Tace "Ameen". Daga haka ya kashe wayar, yana ƙara jin ƙaunar ta yana ratsa dukkan wani sassan jikinsa, ita kam yana kashewa tabi wayar da kallo kawai ta fashe da kuka tanajin wani abu mai nauyi ya tsaya mata a zuciyarta, ganin kukan bazai kaita ba, kawai ta miƙe ta nufi, bathroom ta wanke fuskar ta, ta fice ta nufi ɗakin ummin ta, bata samu Ummi a ɗakin ba, sai ta wuce ɓangaren ɓangare hajjah ta sameta a falon Hajjah tana zaune suna magana da Jaddah kallo ɗaya zaka yiwa Ummi ka gane tana cikin damuwa, sosai Ayrah tace "na ƙariso ko na koma maganar da kukeyi mai muhimmanci ce". Jaddah tace "shigo ƙawata". Ummi tana kallon Ayrah ta fashe da kuka, jaddah tace "to miye na kukan kuma, addu'a mijinki yake buƙata ba kukan ki ba". Ayrah da idon ta ya ciko da hawaye ta danne tace " haba Ummi miye amfanin kukan kuma? Kawai ki tashi ki shiga ɗakin kin Hajjah, kiyi alwala kiyi sallah ki roƙa masa gafara a gurin Ubangiji ". Ayrah tana faɗan haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita, domin hawayen ta take ɓoyewa yana ƙoƙarin tona mata asiri........... Misalin ƙarfe 9 na dare dukkanin mutane gidan sun hallaru a falon Abie Abie ya buɗe taron da sallama kafin ya fara magana Yace "da farko dai zamu fara da nuna farinciki da gidiyar mu ga Allah da ya bayyana mana jinin mu kuma 'yar uwar mu Fatima tare da 'yar ta A'isha, sai kuma magana ta biyu akan auren Aliyu da mubeenah da kuma auren Muhammad da Maryam, sai kuma batu akan Auren Ammar". Dammm zuciyar Ammar, Ayrah, Amjad , da kuma Maya a tare zuciyoyin su suka buga da mugun ƙarfi, Abie Ya kalli Muhammad Yace" fatan dai ka gama aikin da kakeyi a Madina domin bazaka koma ba sai da matar ka". Amjad mai makon ya bada amsa sai ya juya ya kalli Maya ya Kalli Ayrah sai kuma ya kalli Jaddah ya sunkuyar da kansa, jaddah tace "Ahmad Yanzu a saka ranar auren Mubeenah da Aliyun amma ina so amin alfarma abamu lokaci ni da Muhammad akwai abin da muke shirya tukunna". Abie yace Tom shikkenan Jaddah mun baki lokaci, Amma bazamu fasa saka ranar auren ba, mun saka nan da 2 months za'ayi auren Maryam da Muhammad, Aliyu da mubeenah, kafin 2 months ɗin sai ku gama shirin na ku, idan kuma lokacin bai muku ba sai ki faɗi lokacin da kike so Jaddah ". Jaddah tace "babu komai lokacin yayi min, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya". Abbie Yace "sai kuma kai Ammar kaima na gaji da kallon ka haka, na baka 2 months ɗin ka fito da mata, idan ba haka ba, na haɗaka aure da koma wacece ". Shi dai Yah Ammar ya sunkuyar da kansa baice komai ba, Abie Yace" sai kuma Nailah tunda kin kammala karatun ki, bazaki ƙara bin Jaddah ku koma Madina ba, a nan zaki zauna kuma kema ki fito da mijin aure". Tace "insha Allahu Abie". Yace "akwai me ƙorafi ko kuma ƙarin bayani ". Jaddah tace "babu Ahmad hukuncin da yanke yayi Allah ya maka albarka". Yace "Ameen Jaddah". Daga haka dukkanin su, suka watse a gurin, babu wanda yake cikin farinciki, Nailah da Ayrah suka nufi ɗakin su, dukkanin su jiki babu ƙwari duk zuciyoyin su babu daɗi musamman Ayrah ji take zuciyar ta kamar zata fasa ƙirjin ta, ta fito............ GODIYA Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jinƙai. Alhamdulillaah, godiya ta tabbata ga Allah (SWT), wanda Ya bani ikon farawa, Ya bani ƙarfin ci gaba, kuma Ya bani damar kammala wannan littafi book 1. Ba dan ikonsa ba, da wannan rubutu bai zama komai ba. Ina mika godiya ta musamman ga duk wanda ya karanta BAYAN DUHU, ya bi labarin tun daga farko, ya fahimci saƙonninsa, ya yi dariya, ya yi mamaki, ko ma ya yi tambayar, “Me zai faru a gaba?” Ga masu karantawa shafi bayan shafi, ga waɗanda suka yi min magana a lokacin posting, da waɗanda suka ƙarfafa ni da kalamansu—na gode sosai. Ƙaunar da kuke nuna wa rubutuna ita ce ɗaya daga cikin abubuwan da suke ƙara min ƙwarin gwiwa. Allah Ya saka muku da alheri, Ya kuma sanya wannan littafi ya zama abin tunani da darasi ga duk wanda ya karanta shi. RUFEWA A nan ne muka kawo ƙarshen Book 1 na BAYAN DUHU. Amma ƙarshen wannan littafin ba yana nufin ƙarshen komai ba ne. Abubuwan da suka faru sun bar tambayoyi da dama, wasu abubuwa kuma har yanzu suna ɓoye a bayan labarin. Wasu amsoshi ba su zo ba tukuna, domin akwai abubuwan da sai lokaci ya bayyana su. Ku huta da wannan labarin na ɗan lokaci… domin idan lokaci ya yi, za mu sake komawa inda muka tsaya. Book 1 ya ƙare… amma labarin BAYAN DUHU bai ƙare ba, Yanzu ma labarin ya fara — MA’EESHER ✍️