BABBAR SAKAYYAH *BOOK*2 *SADAUKARWA AL,UMMAR MUSULMAI* Godiya Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai tsira da aminci Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya. De * inagodiya da gudummawar da kuka bani har nakawo wannan kan matsayin danake kai ayanzu,ina godiya ga uncle usama,Allah ya bar zumunci,ina godiya musa baffa,Allah ya baka abinda kakeso duniya da lahira,ina godiya ga mahaifiyata abarkaunata,Allah ya sanya ki a aljanna madaukakiya, daduk wanda bansamu damar ambaton sunan shi/ke ba suma ina matukar godiya Allah ya bar zumunci. NOTE Wanan littafin mai suna babbar sakayyah narubutashine badan komai ba saidan gera ga al,ummar musulmai,domin fadakarwa , nishadanvtarwa,ilimantarwa,duk acikin wanan littafin mai suna babbar sakayyah kamar yadda rayuwa,da duniya , ta juyamata Baya ,duniya ta ko mamata tamkar ma kabarta a zuciyarta,duk asanadin so' jama'a kada ku bari abaku labari'' kutsaya ku karanta domin sanin me ya aykata mata. KIRKIRA Wannan littafin kirkirarran labarine,ban rubutashi dan na muzan ta wani ba kodan na bayyana sirrin wataba, no ba hakabane, littafina kirkirarsa nai kuma nasan hakan tana faruwa, amma duk wadda taga yayi shige da labarin rayuwarta, arashin sanine. GARGADI Ban yarda wata tajuyamin littafinaba, kokuma adinga siyarmin da littafi batare da saninaba, banaso, banyarda wani ko wata sukarantamin book ba batare da iziniba muddum kinsan basaya kikayi ba ,wannan littafin paid book ne. Ban amince wani ko wata akaranta min littafi ,ayi adio dinsa batare da izinina ba sannan ban yarda a sauyamin littafi ko adau wani bangare na jikin littafina ajuyashi ta kowace sigaba馃槨ngd BABBAR SAKAYYAH Ep 2 *DORAYI* Gabakidaya zaratan Mazan haduwa sukayi a Gidan alhaji ABDULHAMID ME NASARA susu biyar ne akawai abdul kanin mus,af saï muhsin shima kanin mus,af ne sai mus,af baisamu damar zuwaba Yana asbiti ba a sallameshi ba jukin nasa yayi tsanani, saï "yayan uncle ABDULHAMID su uku nafarko shine Fahat sai me bimasa zaidu, sai na ukunsu autansu me suna faruq Gaba daya Haka suka rankaya G.G.S.S dorayi domin Kai ziyara mota 15 ne suka tafi dasu motoci biyu suna tsakaiya sune wadda suke ciki. __________________________________________________________ Tun da akaji jiniya tana tashi aka shiga bude musu get din makarantar nafisa kuwa tun da taji ance ga alhaji ABDULHAMID ME NASARA ya iso ta Kama kanta tashiga kallon inda motocin za su shigo ,kaitsaye parking space sukayi parking .sai da aka yi kusan minti 5 kafin abude motar sufito wayyo Allah jama,a kuzo kuga kallo a gurin dalibai da malaman makarantar mata abin sai wan da yagani wata marainiyar kwallace me cike da so da kauna ta soma fitowa daga idon nafisa tsabar so da kaunar alhaji ABDULHAMID da take Masa tabbas yau Allah ya cika mata burinta taga jaruminta wan da ta Dade tana son gani , fateema kuwa kallon ta ta tsaya tana yi Tace" nashiga uku nafisa wanan wane irin so kikewa wanan mutumin tun kan kisan zaki ganshi zuciyarki takamu da sonshi acikin sakonni kawai sabi da jin labarinsa da kikayi Anya kuwa nafisa wanan so haka?" "Uhm! Bazaki gane ba fateema son sa ajinina yake Dan allah fateema inason na tsaya kusa dashi na tabashi ko zuciyata zata Sami sassauci " "ke baki da hankali tafada tare da zaro ido kinsan saye shi kuwa,nafisa kodai son shi kike kikeson aurensa ?" Aurensa Kuma Baki Gandhi ba me a haihuwar kaji ya haifeni Dan Allah ki bar maganar Nan bakiga yaransa ba ne" au toenene aciki Dan kin soshii da aure " a,a ba Haka nake nufi ba kawai dai BURINA na rungumeshi "suna cikin wanan maganar Basu rufe bakiba suka jiyo karar bindigu suna tashi tako Ina ga jiniya ta motocin sojoji abin dai gwanin Sha,awa gaba daya student din Ido suka zuba domin ganin me su zuwa shiko alhaji ABDULHAMID farinciki ne ya kaashe Sabi da ganin abin kaunarsa ya tashi har ya hallacci taron, parking motocin sukayi tukunna aka bude murfin motar Nan take ya fito da kekkewar kafarsa wadda taji gyra da tsafta kamar madar Dan haske da Kelli batare da ya sake jiraba ya dakko farin glass dinsa ya saka tare da fitowa wow Masha Allah yau Kuma sanye yake da blue din shadda wadda taji dinki babbar riga ta haujikinsa tayi Masa kyau kwarai shi Daman gashi fari ga kyau dan ma ya dan rame jin yar da yayi a asbiti, tin da yafito ake cewa wow wasu ko har da dilalaln yawu wasu kuwa sai neman faduwa suke tsabar kallo kamar sa cinyeshi ,cikin takun kasaita yashiga takowa sojoji n'a biye a bayansa har suka Isa inda alhaji ABDULHAMID yake atsaye Yana kallon abin kwaunar nashi cike da so da kauna, Daga Nan Kuma aka shiga gabatar da abin da ya kawosu bayan angama ne alhaji ABDULHAMID ya musu kyauta ta daban daban tun daga kan malamansu har dalibai . Daga Haka Kuma suka nufi parking space tare da sauran malaman ,nafisa ce kusa da fateema take cewa" Dan Allah kizo muje kina gani zasu tafi fa kizo ki rakani " ke walalhi bazani ba " ay juyowar da fateema zatai ta hango nafisa har ta Isa gaban alhaji ABDULHAMID ta fada jikinsa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un shikkenan tqjama bala,I cewar fateema " hannu Mus,af ya saka cikin zafin nama ya funciko ta tare da hada ido da ita yace" kina da hankali kuwa ?" Harara nafisa ta watsa masa ta fincike hannunta ta Kara makale wa ajikin alhaji ABDULHAMID Haushin hararar da tamasa ne yasa mus,af ya sake funciko ta tare da tsinka mata Mari jikike Tau luuu, wani gigitaccen Kara ta saka tare da cikukuyo gaban rigar mus'af ta saki kuka ,batare da mus,af yace komai ba sojojin suka karaso suka janye nafisa daga jikinsa tare da yin gefe da ita , afusace mus,af yacire blue din shaddar jikinsa tasama ya fada cikin mota cikin fishi sanan ragowar suma suka Shiga suka ja motar Banda alhaji ABDULHAMID da ya ruko hannun nafisa cike da taisayinta yadda fuskarta tayi kunburi tayi Shari" cikin voice dinsa me dadi yace" yarinya meyasa kikayi Haka kidaina kinji ko Babu kyau kiyi hakuri da Marin da yamiki" kuka nafisa tasaka Tace" Wallahi ni kaunarka nake jinayi bazan iya jurewa ba shiyasa nazo na rungumeka nadade Ina kaunarka tun da naji ance Kai mutumin kirkine" tana Gama fadar Haka tasake fashewa da kuka, shiko alhaji ABDULHAMID rukota ya sakeyi tare da mannata akirjinsa cikin rarrashi yace" to ya Isa Haka kiyi hakuri kinji yarinya ta " Yana Gama fadar Haka da ya tabbatar ta Yi shiru sai ya saketa tare da Bata kudade masu yawa da harta ki karba taga ya hade Rai sai ta amsa tare da yimasa godiya. *DOGUWA* Tun da mahaifiyar amra tayi addu,ar Allah ya tashi kafadun amra ,daga lokacin ta Mike tare da dagata suka cigaba da tafiya har suka hadu da me kura ta riban ruwa ya taimaka aka saka umman su amra aciki ya kaisu bakin titi ,suna ta tsaye a bakin titi sunfi awa 5 suna faman neman n'a allah wqn da zai daukesu ya ragemusu hanya ay ko saiga wani tsoho Nan da Yar kurkurarsu ya daukesu suka tafi sai da sukayi tafiya menisa suka iso cikin jejin falgore tukunna ya ajiyesu yace su samu wani ya sake taimaka musu. Alokacin da ya ajiyesu ya tafi amra tashiga tashin hankali sabi da yadda taga jejin Babu kowa tsit ga duhun gaske cikin tsoro da furgici amra tashiga yin addu,a Nan take tsoro ya fita daga cikin zuciyarta ta daga mahaifiyar su suka shiga cikin jejin sai da suka Yi nisa aciki daidai wajan wata bishiyar tsamiya suka tsaya amra ta tsinko ciyayi ta hadasu dayawa akasa yayi tudu sosai kamar gado sanan ta kwantar da mahaifiyar su akai. 10 .. Bayan sun kwantar da itane amra tashiga cikin jejin domin neman abin da zasuci dakuma sassakar itacen da zata hada bukka, tare da sauran "yan uwanta maza su uku da Jafar da Jamal da Abed ,saï da sukayi tafiya medan nisa sannan suka samu bishiyar Mango Nan take suka shiga murna da farinciki Daman rabonsu da cin abinci tun jiya hakanne yasa Abed da yake shine babba ya haukan bishiyar yashiga karkadiwa nunannu masu jaki su amra suna kwasa ,sai da suka dibi me yawa sannan ya sakko suka cigaba da tafiya har suka tadda bishiyar inibi manya manya sunyi marun har wani Baki Baki suke tsabar nuna, wannan lokacin ma abed ne ya au ya debo musu sannan ya sakko suka shiga sassakar ciyayi da itace ,sosai suka loda da yawa sannan suka koma inda suka bar sauran "yan uwansu da mahaifiyar su lokacin da suka koma mahaifiyar su tatashi daga bacci hakanne yasa su jaber suka tsallaka bakin kogin dayake gurin suka wanke abin da suka tsinko sannan suka dawo suka tarar har amra ta fara dasa bukkar agurin Dan Haka suma suka Kai kayan Mango da inibin gaban mahaifiyar su sannan suma suka shiga Taya Amra hada bukka , Masha Allah sai da suka hada bukka uku manya sannan suka sassake ciyayin gurin yayi sarari tukunna suka zauna suka Shiga shan Kayan da suka tsinko, bayan sungama amra suka raka bakin rafin tayi wanka sannan suma sukayi ,suka Sami wata babbar Leda suka zubo ruwan aciki amra ta wankewa mahaifiyar su jikinta daganan kuma Gaba dayansu baccci me dadi yayi awan gaba dasu sabi da dadin iskar da takada tako ina. *ADAMAWA* Tun da NINEE ta fito daga gida ta nufi titi take ta neman n'a allah ya taimaka mata yakaita doguwa Amma Ina haryanzu shiru Bata samuba gashi Bata da kudi balle ta biya tatafi ,tana tsaye agurin sai ga Allah ya kawo wani me mota da alama haya yake ,Yana zuwa yayi Parking a gabanta tare da sauke gilass din motar yace " hajiya tafiya ne ina zaki Doguwa ko Abuja?" Yallabai doguwa zani saï dai bana da ko sisi wan da zanbiya natafi Dan Allah kataimaka min kamar yadda Allah ya taimakeka kakaini doguwa Dan Allah ,idan kamin wanan taimakon bakasan adadin ladan da zaka samuba Dan Allah kada kace bazaka taimakeni ba" kallonta yayi sosai Yana son ya gano wani abu acikin idonta sai da yagama karemata kallo Sanan yace shigo mutafi " murna da farinciki kamar sa kashe NINEE indakasan zata hadiyesa sabi da godiya ,Shiga tayi suka soma tafiya . ________________________________________________________ Gudu suke kwararawa a hanyar doguwa har suka Isa tashar doguwa anan me motar ya sauke NINEE bakaramar godiya tamasa ba daga Haka ta juya takama hanyar gidansu tun da take tafiya kanta yashiga juyawa sakamakon ganin canje canje da anguwar tasu tayi ,tun da take tafiya samarin anguwar da "yanmata kowa kallonta yake cikin mamaki da rashin sanin meya dawo da ita gida bayan tsawan shekaru da Bata nan. Itako NINEE tafiya kawai take kanta tshaye Bata bi takan kowaba har ta karasa kofar gidansu , rass gabanta ya Fadi abin da yaganine ya sa ka kanta juyawa zuciyarta tashiga bugu dum dum hannu tasaka ta ruko kwadon dayake jikin kofar a datse tare da cewa" innalillahi wa'inna ilaihirraju un umma amrah duk ina suke kannena kenan ina NABEHA nashiga uku ta sulale agurin tare da fashewa da kuka Tace" idan danasan wanan bakincikin zanzo na tarar wallahi gwara nazauna na mutu a hannun sir muhsin wayyo Allah na " saki Kara tare da Dora hannunta duk biyun aka . "Ikon Allah wanake gani haka kamar NINEE ?" Jajayen idanuwanta ta dago ta watsa masa su Tace " nice zubairu Ina su umman mu" zama rubairu yayi yace "duk da bananan abin da yafaru dasu yafaru Amma naji labari anan ne ta kwashe duk abin da yasani ya fadamata tun daga kan korar Karen da baba yayi musu da barin angusarna da sukayi ba asan inda sukeba sanan yakara dacewa " NINEE shawara zanbaki ki koma inda kika fito domin Babu me taimakon ki anan "Kinga tafiyata nabarki lafiya "daga Haka ya Mike ya cigaba da tafiya. NINEE kuwa mikewa tayi cike da tashin hankali ta Mike daker tashiga Jan kafa tana waige waige tamarasa inda zata nufa. 11.. *Abangaren NABEHA kuwa tun da take tafiya tana hutawa anamata kallon mahaukaciya har tagaji tayi likiss har dare tana faman tafe, yanzuma misalin karfe 8pm tana Tace bataji Bata gani sabida wahala da yunwa ga kishiruwa hakan yasa wata mota tataho hucewa ta layin tana tayi mata hown Amma ko gigau NABEHA batai ba gashi metuka motar soyake ya tsayar da motar take tsayawa har sai da yakaraso gurin motar tayi awan gaba da NABEHA Nan take tasulale akasa. *Dagudu yayi parking din motar ya fito aguje ,tashin hankali sai da nacikin motar yafito nakula ma Ashe macece ba namijiba da sauri ta karasa inda taga NABEHA a kwance fuskar Nan jagejage da jini ga kafratamq kamar ansake ballo wani sabon jinin sai numfashi takeja samasama kamar zata mutu ,cikin sauri wanan baiwar Allah da ta kadeta wadda akalla shekarun ta zasuyi 26 ta aduniya, durir kusawa tayi ta dauketa kamar wata jaririya tasakata acikin motarta gidan baya,motane kuwa ancika agurin kowa saï kallo yake manya da samari wasu Kuma sai tsurku suke faman yi, Shiga cikin motar tayi tafara tuki da hanzarinta tahau kan titi har ta Isa wani Dan karamin asbiti nakudi tana dosar get din Aka wangaleshi ta shiga cikin mintina kalilan bayan ta Yi Parking likitoci suka fito aka shiga da NABEHA ciki. Tun da aka shiga da NABEHA ciki wanan baiwar Allah tashiga zarya zuciyarta na bugu sai faman zufa take domin abin da tagani game da yarinyar ya dagamata hankali sosai kada dai ace tamutu innalillahi wa'inna ilaihirraju"ta fada tare da jingina kanta a jikin bangon asbitin ,tana haka doctor ya fito tare da cewa "kishigo Ina son ganinki a office "Babu um Babu um um tabishi abaya batare da Tace comai ba har suka Isa office din, bayan sun shigane doctor ya Bata guri tazauna sannan ya zauna yadan kalleta nawasu Dan lokacin kafin yace" wacece ke a gurin wannan yarinyar da kika kawo" "ni yayarta ce " tafada a takaice "oky kushirya zamuyi shari,a da ku domin kun cutar da RAYUWAR wannan yarinyar meyasa zaku lalata mata rayuwa eh ku mutanene kuwa yanzu da tutu fa BAYAN an mata ciki sannan cikin ya soma tasawa kuka mata duka takarfi har sai da cikin yazube wannan rashin imanin har Ina karamar yarinya cefa me ta tsare muku inda da Baku sonta ba Haka yakamata kuyi ba sai ku kasheta kawai ku huta da wannan azabar da kukai mata gashinan yarinyar tazama abin tausayi Ina tunanin ma kade ta akayi Dan gashi tasamu targade guda biyu da gocewar Kashi kafa da hannu kuko meta aykata kuka mata wannan hukunci wane irin zunubi tamuku to kutabbatar sai munyi Shari,a daku "hawayen dake kwance a idon tane ya karasa zubowa Tace "doctor wallahi nayi rantsuwa da Allah bansan wannan yarinyar ba tabbas Nina kadeta Sabi da ban kula da mutum ba saï da n'a karaso in da take sai Kuma motar Taki tsayawa har sai Dana karasa na bigeta Amma wallahi bayan Haka bansan taba Ni kawai na kawota asbiti domin aceto rayuwarta Dan Allah doctor kataimaka yarinyar Nan tarayu" "tom shikkenan yanzu dai min Gama mata ayki tasamu bacci insha Allah Nan da kwana biyar zamu sallame ku inason ki kula da ita Dan Naga yanzuma furgita take kamar dai Bata cikin hayyacinta "to doctor yanzu dai Bari da safe sai na koma gida na hado Mana abin ci da Kayan da zamusa tun da Naga yanzu dare yayi "okay badamuwa indai abinci ne zan sa akawo muku yanzu"thnkns doctor daga Haka yace Zaki iya shiga dakin yanzu domin nan da 3 n'a dare zata iya farkawa"Tom doctor daga Haka ta Mike jiki asanyaye Babu kwari ta fuce zuwa dakin da Aka kwantar da NABEHA,Tun da tatura kofar take kallon fuskarta cike da mamaki da Al,ajabi tabbas tasan fuskar Nan Amma Kuma takasa tuna Aina tasan wannan fuskar ' zama tayi ta karewa kekkewar fuskar NABEHA kallo can Kuma Tace "nagano" kanwar GENERAL MUS,AF, Kai Anya kuwa to kenan idan da gaske itace meya fito da ita Taya akai tazo Nan to waya aykatamata Haka Anya kuwa Bari dai mugani" ta dauki wayarta ta danna wata numbar bugu biyu aka daga tare da cewa" shegiyar gari lafiya kuwa Naga kiranki cikin Daren Nan karfa ki fadamin da hankali" "ke dallacan dakatamin tambayace zan Miki" oky inajinki wanann wace irin tambayace dabazaki iya jiran gari yawaye ba?" Ke tambayar ujilace "oky inaji" fateema shin kinsan wanan yarinyar "Yar ajinku kanwar GENERAL MUS,AF ?" Eh niko nasanta wata yarinya nan me kokari ay kaf ajinmu ana ji daita to Amma meyasa kikamin wanna tambayar bayan MUFIDA yau kusan shekara nawa da rasuwarta " zaro Ido tayi Tace bangane ba tarasu fa to inda ta tasu wanna ta kwancen ita Kuma wacece?' Kinga karfa ki rainamin hankali macecce baya taba dawowa duk wan da ya mutu yariga da yamutu ki daina wanan haukan Kinga sai anjima" takatse wayarta, itako tsayawa tayi takame guri daya tare da Kara kallon NABEHA dake kwance Tace me tamutu to idan tamutu wanan wacece?" Wazai ban wanan amsar GENERAL tun da ay shiya raineta yasan komai nata yasan ta farin sani tabbas dole na Nemo general namasa tambaya akan Haka idan ma itace zai fadamin idanma ba ita bace zai fadamin Amma fa Kuma komai nasu iri daya hatta hasken fatar su ikon Allah tafada tare da zabga tagumi. ________________________________________________________________ *Tun da su alhaji ABDULHAMID suka koma gida akaeta faman shawo hankalin mus,af amma ina ko takansu bayayi Sabi da ransa ya baci sosai agurin taron bakadan ba ,Wai Dan me kamar wanan yarinyar zatazo ta rungumi uncle dinsu acikin mutane kawai Don ta ja musu raini , alhaji ABDULHAMID a zaune kusa dashi Yana cewa" haba shalelena meyasa kake da irin wanan zuciyar ka rage kadaina irin sanan kaji my son kaman ta baka da lafiya shine zaka Kara dorawa kanka wata damuwar daban kadaina banaso kaji my son iDan baka daina ba Raina zai baci ko kanason bacin Raina"? Dan murmushi ya danyi wan da ya Kara Masa kyau da kwarjini yace " a,a uncle ni naisa naso ranka ya baci a,a kawai dai abinne ya batamin rai" to kayi hakuri kaji itamafa yarinyar soayyayr da takeminne yasa hakan tafaru shine kaikuma uban fishi ka sharara mata Marika Haka ko bakason wan da yake kaunata?" Tab Allah Ni uncle banasonta kana ganin yarinya kamar akanta Aka kare karshen muni ni banaso ay idan naganta ma wanan inda da daddarene tsorata Zan dingayi" hhh baka da dama' my son to Ni fa dama' inason na fadamaka wata magana " uhm inaji uncle?" Yauwa nagaji daganinka a Haka yakamata ka samu kayi aure ko Nima nasamu jika "yan dagwai dagwai kaga sai kasamamin farinciki tun da shi wancan abokin naka ya makale a kasar kanada ya ki dawowa" dariya mus,af ya danyi yace Kay uncle Allah harkasa na ji kunya" uncle ABDALLAH fa ya girmeni shiya kamata yafara yin sure bani ba" uhm barshi ay yana sane yaki dawowa Sabi da karnamasa maganar aure kuma wallahi Aka zansa kakawomin shi Nan " zaro Ido mus'af yayi yace Kai uncle MEJO ABDALLAH Zan dakko haba ay dawasa kake uncle kasan abin da bazai yuwuba " to shikkenan kirawomin shi a waya" wayarsa ya dakko tare da shiga Kira ya danna wata numbar wadda akayi seve da MEJO bugu daya ana biyun ya daga tare da cewa" assalamualaikum cikin muryarsa me da Karen dadi" Wa, alaikumussalam" my bae yakake "dariya mus,af ya kwashe dashi yace" Kai agaban uncle nefa "shima dariya yayi cikin jin kunya yace "Abba Ina wuni?" "Yar harara Abba ya watsa masa kamar Yana ganinsa yace "bansani ba uban marasa kunya wato Kai bazaka taba girma ba ko "mus,af ne yace uhm uncle rabu dashi ay muddum yaci gaba dacemin bae saï nayi maganinsa kato dani dan iskanci yadinga cemin baby sai kace wata budurwar sa, "Kai Kai suine har da wayancewa zaka tsokano Abba yayimin maganar aure ko to sai anjima MEJO ya katse wayar kitt dariya duka su biyun suka kwashe da ita alhaji ABDULHAMID yace" kagani ko aduniya bayason zancen aure shikkenan tun da bakuso duk n'a hakura n'a kyleku duk Randa kukayi niyya kwayi " Yana Gama fadar Haka ya Mike tare da yiwa mus,af sallama ya Shiga ciki. 12.. *Shikuwa MEJO ABDALLAH tun da ya katse wayar ya fada tunanin abin da ya dameshi,Shiba aurenne bayaso ba kawai dai har yanzu Bai samu matar da tayi daidai da tsarin rayuwarsa ba ,Amma Kuma Babu yadda ya iya tun da mahaifinsa yanason yayi auren zai cigaba da addu,ar Allah ta hadashi da wadda zatayi daidai da ra ayinsa , Yana Gama tunanin Nan ya tashi ya cire farar rigar da take jikinsa Nan take asalin kirar jikinsa Wanda ubangiji yamasa ta bayyana gawani kwantaccen gashi a kwance luff a kirjinsa sai Kelli yake ,hannu yasa ya zare wan Dan jikinsa ya koma daga shi sai gajeran wando namaza wow Masha Allah duk da wan don da yasaka Bai Hana kaga yadda baiwar Ni,imar da Allah yamasa ta gaban wan dinsa ba , sai da ya Dan jima a Haka kafin ya Dada bathroom ya somayin wanka ,BAYAN yagama me ya fito bedroom kaitsaye gaban mudubinsa ya nufa tare da daukar wani Mai me kamshin gaske ya saka akansa sannan ya dauki wani ya shafa a jikinsa bayan yagama ya dakko turare kala kala ya fesa sannan ya juya drowa ya dakko wata black din shadda me tsadar gaske yasanya ajikinsa Tasha dinki me kyau da tsari Daman shi Abu ba Baki ba fari balle ace zasu saje ,gaskiya nayar da da akace namijin novel badai kyau ba iya kyau da tsarin halitta MEJO ABDALLAH ya hada sai dai muce Masha Allah domin da MEJO ABDALLAH da GENERAL MUS,AF ban San wayafi wani kyau ba shiyasa komai nasu yazo daya hatta jininsu yafi haduwa Daman can aminai ne tun suna kanana Allah ya hadakansu atare sai dai bayan sun girma Tasanarin ayki aka canzamusu gari . Tun da MEJO ya fito ake binsa da kallo shikuwa MEJO ABDALLAH ya tsani kallo Dan kallo Yana daya daga cikin abin da ya tsana to sai Kuma gashi Allah ya bashi abin da har maza kallon sa suke balle kuma mata ,Tun Kan yakaraso gurin aka bude masa murfin motar rannan a hade ya nufi bakin motar ya shiga tare da kunna motar dreba yashiga ja har suka fita daga cikin gidan zuwa bakin titi ,Tun da suka Sona tafiya suke sharara gudu a kantiti Basu tsaya ba sai da suka Isa wani katafaren geshause me matukar kyan gaske Kai da kaga wannan gida kasan mamallakin gidan ya amsa sunan sa alhaji ,Tun kan su karasa Aka wangale musu get din gidan bayan sun shigane suka nufi parking space sukayi parking sannan ya fito ya budewa MEJO murfin mitar,sai da akafi kusan minti 5 kafin MEJO ya fito da kafarsa waje sannan yasako ragowar jikinsa ya fito ,sai da ya daga kansa ya Dan kalli gefe daya yakara kallon gefan damarsa sannan ya kallli gabansa ya Soma takawa,har suka Isa cikin gidan ,wow wayyo Allah na zokuga aljannar duniya acikin gidannan iya haduwa da tsaruwa ya hadu batare da ya ce komai ba ya nufi wata kofa wadda zata sadashi kofar falon gidan ,Kai tsaye ya shiga gurin sai da yadan tafi kafin ya iske libta danna babobi yayi kana ya shiga tafara sama sannan ta tsaya cak ya fito run da ya Soma dosar gurin nakejin karar ihun garadan maza cikin isa da kadai ta MEJO ya karasa cikin dakin ,ashe rundunar sojoji ne acikin dakin sun saka wasu maza su uku a Gaba saï jibgarsu sukeyi kamar Allah ya aykosu, batare da MEJO ya kalli gurinba ya karasa ya zauna a can gefe guda ,me ayki ne sanye da Kayan sojoji ya dakko shayi me kauri ya ajiyewa MEJO a gurin sannan ya Sara yakame guri guda, MEJO ABDALLAH kuwa shayin yasoma Sha Yana lumshe idonsa Kama da na masu jin bacci ,cikin voice dinsa me dadi MEJO yace" ina CANAL FARUQ ?" Yallabai faruq yace ranka yadade" alama yamasa da yazo ya zauna ,zama faruq yayi yace "yallabai sun ki fadar wada yake da kamfanin sassaka kayan garamtarciyar madarar da aka fito da itayanzu Kuma sunki fadar ainda company yake sunce akan suyi bayani gwara akashesu ""okay ka kasgesu tun da bazasuyi bayani ba" "angama yallabai" daga Haka MEJO ya Mike yanufi kofar futa batare daya sake xawa komai ba. *Jos* Tun da doctor ya koma ma,aykata sir muhsin yasakashi agaba sai ya fito da inda yakai NINEE shikuma doctor ya ki fada yace saï dai in ya kasheshi,wannan abin da doctor yacene yasa ran muhsin ya baci sosai Dan Haka ya bada izinin akashe doctor har sir muhsin ya juya zai bar gurin doctor yace"to saime idan na mutu wallahi kokadan bazanyi danasanin mutuwa a gurinki ba ,Ni farinciki nayi dawannan abun ko Babu komai ubangiji zai yafemin zunubin Dana aykata a baya"mugaye kawai kunsa n'a dakko "yata tacikina nabaku kunyi anfani da kwayar halitttarta sabi da dan zuciya irin naku insha Allah saï asirinku yatonu bazaku taba ganin daidai ba mugaye kuma wallahi saï Allah ya sakawa duk budurwar da kuka ciri kwayar halitttarta "kun Dade Kuna sani Ina aykata zunubi bansan iya adadin "yan matan dakuka sa Aka cire abin jikinsu Aka hada Kayan sayarwa kawai sabi da rashin imani irin naku Allah bazai barku ba kudin azzalumai ne ay kafin ta Dora wata maganar yaji saukar bulet n'a bundiga a tsakiyar zuciyarsa Nan take doctor ya Fadi kasa macacce ko motsi Bai sake yiba...... 13... Zainab kuwa tun da NINEE ta samu tafita rayuwarta tamata zafi da kunci bakaramin tashin hankali tashiga ba gashi yanzu iska bata fiye zuwa dakin da takeba kullum cikin kunci da damuwa take Babu Hutu kullum a tunanin yadda zata fita daga cikin gidannan take akowacce Rana dazata fito ta Fadi tana sa yakini a zuciyarta akwai wan da zaizo ya taimaketa. Yau juma,a itace juma,are da ta fi kowacce mata zafi da kunci agareta aduk ranar datafi kowacce Rana itace ranar juma, a ranar da takasance me dunbun kada da falala saï ita ranar tazamemata ranar bakinciki ranar tashin hankali ranar da akamata cin xarafi ranar da itace takasance ranar bankwana da tayi da duniya. Yana zaune saiga wadannan mutanen sunxo sun dauketa kamar yadda aka fita da ayna,u tun da aka tafi da ita take kuka da ihu da neman dauki zuciyarta kuwa zafi da daci take mata kamar grwashi Allah sarki baiwar Allah komai nata yasaki sabi da tsananin tunanin mezai sameta, Kai tsaye dakin sir muhsin suka ajiyeta wannan karan be taba zainab ba sai da ya dakko wani abu kamar sirinji a hannunsa Yana nufo gadon da aka dorata batare da yace komai ba wadannan mazan su uku suka daddanne kafafuwanta da hannayenta kaitsaye Yana zuwa gabansa ya da suka tala kafarta kamar wadda zata haihu Haka Aka bankareta indakasan bankararriyar kaza ,hannu yasa ya daga doguwar rigar dake jikinta Nan take fant din jikinta blue ya bayyana yayi bakkikkirin sabi da datti Dan yau kusan watanta uku acikin gidan batare da ta canza Kaya ba shiyasa wan don ya yidauda , safar hannu ya dauka ya saka sannan yasa hannu ya cizge wandon jikinta innalillahi wa'inna ilaihirraju un dasauri ta rintse idonta Sabi da tsaraicin gabanta daya bayyana a waje Babu abin da baka gani Sabi da bankaratan da sukayi ,zainab jin wannan cin xarafi da akemata hakan yasa zuciyarta tayi rauni jikinsa yayi sanyi ayanzu kuwa tagama tabbatarwa mutuwa zatayi idanko Bata mutuba to tabbas kashe kanta zatai ta huta da wannan bakinciki idonta ta Kara runtsewa hawaye na bin kuncinta bakinta ta ambaton sunan Allah ,ahaka sir muhsin Babu tausayi babu imani ya dauki wannan sirinjin me girman gaske ya dannashi acikin tsakiyar gabanta atake zainab tayi Kara me karfi Sabi da jin bakar azabar da taji Bata ankaraba tasake jin ya danna wannan sirinjin ciki ay kafin kaceme jini ya wanke gurin zainab kuwa Allah yayi cikawarta tun a sakawa ta biyu dayayi ,Haka suka Gama ayki akanta sannan aka nannadeta da farin kelle aka fita da ita. *DORAYI* Nafisa ce kwance kan cinyar mahaifiyar ta tana Kuka harda shashsheka tana cewa" umma me namasa waini shikkenan kowa baya sona laifine dannaso wannan mutumin me kirki shine za,Amin wannan Dukan kinaganifa bayan marin da wannan balaraben mutumin yamin shugaban makarantar mu ma sa akamin duka " kiyi hakuri nafisa insha Allah komai zai huce keyanzu meyakaiki rungumarsa ?" Umma ganinai idan ban rungumesa ba zanta mafarkinsa Allah umma Haka kurum naji soyayyar mutumin azuciyata " shiru ummansu tayi kamin Tace" nafisa "naam umma"meyasa kullum ake nuna kyama akankine mekikayiwa mutane me yasa ba,a keymar auwal saike eh" uhm umma kece SILAH meyasa bazaki fadamin gaskiyar me yake faruwa ba dafarko mutanen gari suna kyamatata sucemin shegiya sukirani da mummuna su cemin Yar shege duk nikadai meyasa wannan mummunar kaddarar ta kasance akaina Ni kadai umma Dan Allah kifadamin Ina mahaifina yake kodai dagaske ne ni sgegiyace?" Ya Isa Haka nafisa ke ba shegiya bace da ubanki bana bukatar n'a karajin irin wannan kalmar abakinki mahaifinki mutumin kirkine kuma Yana sonku daga ke har dan,uwanki auwal" "wallahi umma bazan taba yadda dawannan maganar dakuke fadamin dake da Inna ba nagaji nagani kunki kufadamin gaskiya shin menayi muku wane zunubi Haka na aykata?" Dafarko kince mahaifina Yana Sona Kuma kince mutumin kirkine to Ina yake"idan gaskiya ne mahaifinmu daya da auwal meyasa saï nikadai ake shegantawa meyasa ko kama bamayi ya akai shi yakasance fari kekkewa kina ganinsa Kinga jinsin larabawa shine zaku hadani dashi kingannifa hargorin kyau akemin umma kun Dade Kuna fadamin badaidai ba nagaji wallahi daga yanzu hakurina yakusa zuwa karshe daga Rana irintayau muddum Baku fadamin Ina mahaifina yakeba saina kashe kaina" tana Gama fadar Haka tatashi tafita daga dakin, Yana fita ummanta tasaki kuka kamar ranta zai fita tana cewa nashiga uku wannan wane irin masifane innace ta shigo tare da zama a kusa da umman nafisa Tace" fa'iza meyasa kikeso kisakawa kanki damuwa haba fa'iza yakamata komai yazo karshe inason ki fadamata wanene mahaifinta karda takashe kanta" a,a Inna ko da na fada mata bazatataba Yar daba yakamata mujira lokaci akwai lokacin danake jira Inna tabbas lokacin zaizo nafisa zatasha mamaki gabakidaya wannan muzguna mata da ake zai koma mata farinciki zai Bata daukaka aidon mutane ayanzu kowa gudun nafisa yake kamar wata mecutar janjamau to ki jira Inna akwai lokacin da zaizo mutanen ne zasu so zama da nafisa sai dai ita Kuma lokacin tamusu nisa" Ajiyar zuciya Inna tayi Tace to Amma kiyayyar datake tsakanin auwal da itafa tun farko mutanene sanadi dakuma kabiru tun da kaberu yadawo ya ga nafisa Kuma mutane suna aybatata shikkenan ya tsaneta nadauka cewa da na fadamasa gaskiyar lamari zai yadda Amma Ina sai yace an rainamasa hankali gashinan Abu kamar Wasa ya sakawa auwal tsabar "Yar,uwarsa aransa" um Inna shima zai so Yar,uwarsa ne ninasan nafisa tanason auwal kamar ranta tana iya Hana kanta ci tabawa auwal yaci karki damu kabiru bazaiyi nasara Akan hakaba. *DOGUWA* Tun da NINEE take tafiya a hanya jikinta yake rawa da kerma Tama rasa inda zatasa ranta Sabi da tashin hankalin da tashiga kenan idan su amra bara doguwa ina sukaje innalillahi wa'inna ilaihirraju un tana tafe tana salati zuciyarta cike da tunani kala kala Haka tadinga tafiya jiri na dibanta tana tafe tana hutawa ga takalmin dake kafarta duk ya sude yazama falankatai daga kasan kafarta tana iya jiyo azabar ranar dake tabata, ga yunwa da kishiruwa ga gajiya gashi tun da tadawo daga Jos batayi wankaba ta bazami neman NABEHA sai dai kash darabon zatazo taga wata masifar a gidansu tabbas yayarda mutuwa ta masu yankan kauna tayarda da akace da zaman gidan wani gwara zanman gidan ubanka Koda baza aci kullum ba tasani da mahaifinsu Yana da Rai Babu abin da zai sa sukoma gudan ABBO FAHIMNA da zama ABBO tacuce su ta tarwa tsa rayuwarsu ta lalata zumuncin dake tsakanin su kuma wallahi walalhi tayi rantsuwa bazata taba kyake suba ta Sawa ranta itace ajalin ABBO FAHIMNA da yaranta ,abin takaicin ma batasan aina dangin iyayan su ummanta suke a nijar ba gashi batasan dalilin dawowarsu doguwa ba itadai tashi t'ai kawai ta tsinci kanta a kano kuma gashi ko zuwa zatai Bata da kudin mota idan ma tasamu kudin motar taje watasani ay basu santaba " Haka dai NINEE ta dinga surutai ita kadai tana tafe kamar wata zararriya hijabin dake jikinta kuwa Rana ta Dada dafar dashi ya Dada yagewa indakasan akansu fatara ta kare komai Babu abin arziki. 14... *JEJIN FALGORE* Yau kamar kullum Amrah da sauran kannenta suna zaune a "Yar bukkar da suka hada suna Shan iska da mahaifiyar su sai jisukai UMMI ta zab ga kara nan take dukkansu suka juya suna kallonta mezasu gani wani zabgegen macijine ya gasamata cizo har sau biyu ,Allah sarki baiwar Allah sai gumi take tana ihu tana mukususu da sauri su NABEHA suka nufi inda take suna jijigata kafin kace me harta suma Abu dayane kake iya tantance Bata mutuba shine kirjinta dayake bugu lokaci bayan lokaci, a gigice NABEHA ta dauketa tayi cikin jejinnan da ita tana gudu tana kuka har tafuta bakintiti ,suma ragowar kannenta maza da mata wasu suka zauna a gurin mahaifiyar su wasu kuma suka bibayan NABEHA harsuka isa inda take, zaune suka isketa bakin titin tana rusa kuka duk mitar da zata huce saï ta tsayar tana rokonsu da su taimaka musu zuwa asbiti Amma Ina Babu Wanda ya saurari inda takema balle ya tsaya taimakon su, kuka sukeyi daga amrah har ragowar yan,uwanta , innalillahi wa'inna ilaihirraju un amrah tana tsaka da kukan taji jikin UMMI ya tsaya chak Bata ko motsi kirjinta dayake harbawa ma yadaina harbawa yanzu jiki Babu kwari amra tashiga jijjigata tana Kiran sunanta tana kuka tanacewa UMMI UMMI kitashi kitsashi Dan Allah kada kicemin kin mutu ummi kuka suke kamar ransu zai fita , lokacin da suka tabbatar ta mutu Babu ko sauran Rai ajikinta ,Haka Amrah ta juya da ita da kannenta jiki Babu kwari suka koma cikin jejin inda suka baro mahaifiyarta da sauran kannenta ,suna Isa suka tarar da idon mahaifiyar su cike da kwalla a fuskar ta Nan danan tausayinta ya Kama mahaifiyar su ,tashin hankali Mara iyaka gashi kafcikinsu Babu namiji babba basusan yadda zasuyi da gawarba gashi duk cikinsu Babu Wanda ya je makarantar islamiya balle susani, Amrah ce takalli Jafar Tace" jafar ba daku aka sallaci baba ba?" Eh damune nasan yadda akai" tom shikkenan maza ku tashi saï amata wanka kusallaceta sai a bunneta a Nan gurin ,Haka kwa akai Aka sallaceta sannan suka Haka rami su ka bunne ta . *ADAMAWA* NABEHA kuwa tun da ta bude Ido take kallon saman silif din asbitin cike da mamaki ita dai tasan tana tafi taji kamar an bigeta daga lokacin Bata Kara sanin inda kanta yakeba, kenan a asbiti nake"innalillahi wa'inna ilaihirraju un "afili tare da cigaba da cewa" meyasa baku Bari n'a mutuba dan Allah kukasheni n'a huta meya sa kuka ceci ran yarinyar da bata da kowa batasan inda zataje tasa ranta ba meyasa dan Allah kukasheni "nan danan tashiga cizge ledar ruwan datake hannunta tana sumbatu kamar mahaukaciya ADEENA dake kwance kusa da ita bacci ya dauketa da sauri ta bude idonta Tace"subahanallahi meyake faruwa ne meyasa zakiyi Haka lafiyarki fa ake so aceto kidaina "tana maganar tana rikemata hannu,kuka NABEHA take tana cewa"Dan Allah meyasa baku barni n'a mutu ba mezanyi da wannan bakar RAYUWAR komai nacikinta ya rainamin dadi banason zaman duniyar Nan ancuceni anci zarafina an lalatamin rayuwa narasa komai narasa ummana "yan,uwana yayata duk sun barni kowa baya sona dan Allah ki taimaka ki kasheni kada kiyi tunanin ko za a kasheki idan kika kasheni a,a wallahi Babu Wanda zai kasheki Ni ba kowa bace bani da kowa Ni banzace Mara galiyu Mara tushe kinsan yadda ake kashe cinnaka a zauna lafiya to kamarhaka Zaki zauna lafiya idan kika kasheni" ADEENA kuwa zuba mata Ido Tai tana kallonta yadda taga tana nemowa kanta mutuwa da kanta bayan tasan ita "Yar babban gidace, kallonta sakeyi cikin nutsuwa Tace" haba MUFIDA meyasa kikeson ki kashe kanki kinmanta yadda GENERAL MUS,AF yake sonki kinmanta kwanar da ke tsakaninmu dake da yayanki duk danginki suna sonki kowa Yana kwaunarki to danme Zaki kashe kanki" meee" ta fada tare da zaro ido Tace"Ni wace MUFIDA kuwa eh waye GENERAL MUS,AF ni bansan suba ni ba "yar kowa bace" "kar ki raina min hankali bakece MUFIDA kanwar GENERAL MUS,AF ba ?" A,a ni ba ita bace ni ban sansu ba bantaba jin masu wadannan sunan ba Tun da nake Ni sunana NABEHA Kuma Ni ba Yar kowa bace" runtse ido ADEENA tayi tare da dafe Kai azuciyarta tana cewa "ah God meyake damunane ko dai idonane yake bani kamannin MUFIDA a fuskar wannan yarinyar Kay no sai na Kira KHADEEJA ta ga abin da nake fadamata indai itama taga dagaske ne ba ido n'a bane to dole sai nanemo inda GENERAL MUS,AF yake domin namasa albishir da wannan abin farinciki tayuwu MUFIDA ce ko tasamu tabun kwakwalwa ne bansani ba shiyasa take wannan abin. Wayarta ta dakko tare da danna numbar KHADEEJA, KHADEEJA kuwa tana daga kangado a kwance taji wayarta na ruri cikin sauri ta Mike tare da dakko wayar taga me kiranta sunan ADEENA taga ya bayyana tsaki tayi ta ajiye batare da ta dagaba tace mtseeeew wannan matar ko Yar kwaya inaga ma ganar MUFIDA ce ance mata yarinyar ta mutu ta mutu takiyar da metseeeeew shegiya yar kwaya kawai" bata karasa rufe baki ba taji karar waya Kiran ya sake shigowa tsaki tayi ta daga tare da cewa "KHADEEJA meyasa kikemin hakane wallahi dagaske nake Miki MUFIDA ce kanwar GENERAL MUS,AF ki taimaka ki zo asbitin nan domin ki tabbatar da gaskiya ko dayake kafin ki cigaba da karyatani maza hau WhatsApp na nuna Miki ta video call ", okay Bari ya tabbatar da karyarki" tana Gama fadar haka ta katse wayar ta kunna data sannan ta hau online ta Kira ADEENA video call ta daga" KHADEEJA kina karyatani kina tunanin abin da nake fadamiki karyane ko to Bari kiga ikon Allah"tajuya cemara wayar baya ta saita wayar daidai kan fuskar NABEHA dake zaune tana faman sharbar kuka, agigice KHADEEJA ta zaro Ido Tace what mezangani ADEENA kodai Ido nane MUFIDA fa nake gani Anya kuwa ADEENA mufida fa ta Dade da mutuwa waini bangane meke faruwa ba" uhm yanzu kin tabbatar ba kwaya nasha na bugu ba ko kinyar da gaskiya nake fada miki?" Tana fadar haka ta katse wayar ta rufe datar ta ta cigaba da kallon NABEHA cikin zuciyarta tana cewa" yanzu kuwa na tabbatar da ba idonane yake nunamin MUFIDA nake gani ba tabbas itace to kenan idan itace meyasameta Haka waya aykata mata Haka meyasa tabar gida ta wace kofa ta iiya fitowa daga cikin rundunar sojojin Nan na gidan su ",Kai to wa Akaje Aka bunne amadadinta aka ce ta mutu "ADEENA dai gani tayi zuciyarta na da kwakwalwar ta na neman fashewa hakan yasa ta nutsu ta sai ta tunaninta Sabi da Kar ta zauce. *UHM NI Daman nasani Yaya bazaka taba daina tunanin MUFIDA ba meyasa ko su momy da suka hayfeta sun fawwalawa Allah balle Kai dakake yayanta dan Allah yaya kadin ga rage damuwarnan a ranka " uhm Abdul bazaka ganeba ne kamanta nine nayi rainon MUFIDA ba su momy ba meyasa baza kumin uzuri Akan Haka ba mufida kanwatace Kuma Yarinyar da nafi kowa so a duniyar Nan meyasa kakeson takuramin akan Haka" Yaya lafiyarka nake gudu ance karafe yawan tunani da zafin Kai Amma kaki kofa sallamarka ba ayi daga asbiti ba Haka kasaka kafa katafi gurin taron anan ma ka hadu da wata yarinya ka sharara mata maruka har biyu Yaya Wai mece da muwarka ne" bansani ba meyakawoka daki n'a kazo ka isheni da tambayoyi Haka?", Daman inason zan je doguwa domin inason naje Naga halin da su Amrah suke" tofa wacece Kuma amra?" Yarinyar Dana Baku labari lokacin da Inna ta dawo Dani gidannan Yaya naso yarinyar Amma tacemin bazata aureni ba sai ta ga RAYUWAR kannenta ta inganta Tace indai Dan tashiga RAYUWAR farinciki ne ta bar kannenta a wahale do gwara ta hakura da aurena ,shiya naga tun da muna da dukiyar da zamu iya rukesu na fadawa Abba zanje na dakkosu "okay yayi kyau sai kadawo Allah ya kiyaye hanya daga Haka ta juya ya runtse ido tacigaba da tunanin sa , shiko Abdul juyawa yayi ya turo kofa ya sauka kasa tare da yiwa su momy sallama ya dauki hanyar tafiya . Kai tsaye jirgi yabi Abinka da "yayan masu kudi hakan yasa yayi saurin isa ,Tun da ya nufi hanyar layin gidan su Amrah yaga ko Ina nagidan ya canzamasa komai har ya karasa kofar gidan abin da yaganine ya dagamasa hankali kofar gidan a datse durum gabansa yashiga faduwa to Ina suka shigane ya watsawa kansa wannan tambayar Yana kallon gefe dagefe, wasu mazane samari sukazo hucewa suna tafe suna gurmarsu suna cewa" oh agaskiya wadannan yaran Basu da da,a kuga sai da akamusu korar karnuka sannan masu kudi suke zuwa gidan rannanmafa Naga NINEE ta dawo tab to Allah ya kyauta" shiko abdul rintse Ido tayi tare da budewa jin yadda zuciyarsa ke tafasa da zafin abin da akamusu Nan take yasake maimaita kalmar "korar kare innalillahi wa'inna ilaihirraju un"yafada tare da bude idanuwansa sun kada sun Yi jajur kamar garwashi sannan ya juya yanufi gidan su abokin sa usman wan da yabashi amanar su amra kafin ya tafi chamaru. Yana Isa gidan yaga wani dattijo a kofar gidan da sallama ya karasa kusa dashi yace" barka da wanan lokacin baba" barkadai yaro ya hanya" lokay kwau Ina wuni?"lafiya Lau sannu dazuwa" yauwa baba Daman Ina neman Usman ne mutanen dake zaune a gidannan saï dai naga kamar bakowa " ayya Allah sarki amma Kai bakone ko?" Eh yau nazo "Allah sarki ay Usman yadade da rasuwa mutanen dake gidanma sun tashi" dasauri Abdul ya dafe kansa tare dacewa" innalillahi wa'inna ilaihirraju un "baba ya rasu kenan wayyo ni to yazanyi kenan " shidai baba besake cewa komai ba sai dai dayaga Abdul Yana kokarin shidewa yace" yaro sai hakuri duk merai sai ya dandani zafin mutuwa yau Kaine gobe ba kaibane" shidai Abdul tashi yayi jiki a sanyaye ya nufi hanyar koma wa inda yafito. Tun da Abdul ya bar unguwar yarasa inda zai nifa ya ji dadi Gaba kidaya abin duniya ya hadu yayiwa Abdul yawa komai yamasa zafi tinani yakeyi idan ance an Kori su Amrah daga dida to kenan Ina suka nufa shidai yasan kaf cikin garin kano su amra Basu da kowa sai Allah to kodai ADAMAWA suka nufa Anya kuwa haka dai ya dinga tunani ta inda ya shiga batanan ya fita ba zafi da zugi Gaba daya sun vaibayesa ,Babu yadda ya iya Haka ya fawwalawa Allah ya Kama hannya domin yasamu gurin da zai kwana kafin gobe ya huce Abuja . *KHADEEJA kuwa tun asba ta ke ta shiryawa domin taje ta ganewa kanta abin da idonta yake nuna mata shin Wai dagaske mufida tagani jiya a video call ko dai aljanar Tace Allah masani ,BAYAN tagama shiryawa be ta fito harabar gidansu tashiga mota ta nufi bakin get me gadi ya budemata get ta fuce ,tun da ta hau kan titi take tsuga gudu har ta Isa katafaren asbitin da aka kwantar da NABEHA,Kai tsaye tana shiga numbar ADEENA takira bugu daya ADEENA ta daga tare da karawa a kunne Tace" hello kina inane"inna harabar asbitin kufa Kuna Ina?" Muna bangaren "yan Bari daki me numbar 226 ki shigo Nan"tana fadar Haka ta katse wayar, tabdijan KHADEEJA tafada tare da fadawa wani dogon tinani jikinta ya dauki rawa zuciyarta ta shiga bugu a hankula ta ce" wai meyake faruwa ne to meyakaisu dakin masu Bari Anya kuwa wace tayi barin to kodai ADEENA to ay ADEENA Bata da aure to indan ba ita bace kenan wace MUFIDA "Haka tadinga saka da warwara azuciyar ta har ta karasa daki me numbar 226 ,Kai tsaye kofar ta tura ta Shiga bakinta dauke da sallama tace " assalamualaikum ay Bata karasa maganar ba sukayi Ido hudu da NABEHA wadda ke zaune idonta cike da ruwan hawayen da yakasa tsayawa kullum zuba yake kamar famfo, jakar da ke hannunta tasaki tashiga nuna ta da hannu bakinta harrawa yake wajen furta"mu mufidaaa kece ?" Itako NABEHA kallon mamaki take binta dashi Wai ya za ay kowa yazo yadinga cewa mufida meyake faruwa da itane Haka Anya kuwa ba wata duniyar ta koma ba "cike da mamaki Tace" Wai Ni kike nufi" bakin KHADEEJA kasa rufuwa yayi da hanzari ta karasa bakin gadon tare da murxa idonta ko zata farka daga mafarkin da take Amma Ina tana sake budewa dai ita dince tasake gani ba wataba,hannunta yasaka ta shafa fuskarta Tace" tabbas itace wallahi itace ADEENA bakiyi karya ba wannan kanwar GENERAL MUS,AF ce to Amma yanaga ta kankance mufida tafi wannan girma sannan tafita harken fata abin tambayar shine metasame ta Haka tawace hanya kika iya fitowa daga cikin gidansu bayan gidan cike yake da tarin rundunar sojoji da masu tsaronsu kay Anya kuwa itace?" ADEENA ce Tace" meyasa kike kokonto akan Haka bayan ga zahiri kina gani" laaa bazan yardaba nafara ko konto akan Haka kina da numbar general mus,af "? Eh jiya nasa wata "Yar uwarsu ta turamin sai dai nakira shi Bai dagaba Kuma be biyo ba" hmm halayyarsa ce Haka kinsan indai namiji ta hada komai ga kyau ga kudi ga mulki Dole yayi gadara da girmankai maza kara kiransa muji" 15... Wayar ta ta zaro tashiga Kiran numbar GÉNÉRAL amma shiru bai daga ba har Kira bakwai ,haushine ta kama ADEENA Tace" Wai shi wannan dame yake takama da bazai daga Mana kiraba aykin banza taimakwansa zamuyi Yana wulakan tamu"to wallahi bazan Kara kiraba sai dai in ke KHADEEJA ki kirashi nagaji" karbar wayar KHADEEJA tayi tashiga Kira amma shiru. Shiko général Yana kwance a kan makeken gadonsa idonsa alumshe Yana aykin da yasa ba wato tunanin kanwarsa mufida ,jiyayi an dameshi da Kira hakan yasa yayi tsaki tare da janyo wayar ta daga, shiru yayi bece komai ba daga Can bangaren kuma KHADEEJA Tace" assalamualaikum " cikin voice dinsa me shegen dadi yace Ameen wa, alaikumussalam "lumshe ido KHADEEJA tayi sabo da tsananin jin dadin muryar tasa da tajita har tsakiyar kwakwalwar ta"shiko genaral jiyayi shirun Yaya yiwa hakan yasa yasake cewa" lafiya ?" Dasauri KHADEEJA Tace "dama dama uhm mufida ce" what "yamike zumbur yace mufida Kuma Ina mufidann take?" Gata anan asbiti "dagaske Dan Allah ?" Kujirani ganinan zuwa"ya katse wayar a furgice ya ciro jallabiyar sa fara tas bema sani ba Sabi da kidimewa a baibai ya sakata ya dauki mukullum mota yayi waje ,momy da abba dake zaune kallonsa sukayi cikin furgici dan basu taba ganinsa a irin wannan yanayin ba, cikin zafin nama abba ya sha gabansa yace" son Ina zaka?" Abba Ina dawowa yanzu" Babu inda zakaje sai kafadamin inazaka kaganka kuwa hauka kafara mutuwa ay tana kan kowa jibi rigar jikinka abaibai kasaka ta gabadaya duk ka koma kamar wani sususu haba son" uhm abba mufida zanje n'a gani tana asbiti"what mufida Kuma "ah yanzu kuwa batambatar da hankalinka ya bar jikinka "Yar ta Fadi ta mutu da hannuna na bunneta shine zakace wani tana asbiti to wallahi ko ka dawo cikin hankalinka ko yanzu na sabar maka kujini da yaro Mara hankali kagirma Amma bazaka iya yarda da kaddara ba wannan ay shashancine zaka koma kazauna kosai basa an horaka yanzu" jiki Babu kwari mus,af ya zame a gurin yace Dan girman Allah Abba kabarni naje nagano mufida wallahi tana asbiti yanzu wasu suka kirani suka fadamin Abba kada kace a,a" momy dai kuka ta fashe dashi na tsananin tausayin Dan nata tabbas saiyanzu ta Kara tabbatar da shakuwar dake tsakanin Yaya da kanwar "jiki a sanyaye cikin lallashi Abba sa hannu ta dagoshi" sannan ya zaunar dashi a kujera shima ya zauna yace" mus,af "afurgice genaral ya dago idonsa yakada yayi jajur Dan tun da yake bai taba jin abba yakirasa da asalin sunansa ba saï dai yace son yaugashi sabi da wannan abun da yafaru ya kirasa da asalin sunan sa ,indai hakane akwai abin da yake damuna menene shi"meyasa bazan danganaba"abbane ya katsemasa tunani dacewa" inason ka kwantar da hankalin ka kabari ni baje n'a fara ganota tukunna kazauna agida domin naga kamar baka da lpya idan naje daganan sai na taho maka da ita" dakamar mus,af bazai amince ba saï kuma yace"shikkenan abba ga wayar tawa wannan ce numbar da Aka kirani idankuka fita suyimuku kwatancen asbitin "Yana gama fadar Haka ya Mike tare da komawa daki jiki Babu kwari. Abba kuwa bayansa yabi da kallo har ya Shiga dakin sannan ya juyo ya kalli momy yace ni zantafi "Ina zaka? Asbitin" au kaima kabiye masa kenan yarinyar ta fadi ta mutu ka ka bunneta da hannunka kuma kace zakaje pleace kada kayi sabo mana" a,a kitashi dai muje muga ikon Allah" oky momy ta tashi tashiga daki ta dakko hijabi ta saka sannan suka futa, Kai tsaye asbitin da su KHADEEJA suka musu kwatance suka nufa bayan sun isane Abba ya sake Kira suka fada masa numbar dakin da bangaren da zasu zo, cikin mintina kalilan su momy suka nemo dakin sannan suka kwankwasa, ADEENA ce ta taso ta bede musu, cikin fara,a ta gayshesu suka amsa tare da matsa musu hanya suka Shiga mezasu gani"photocopie mufida sak ajikin NABEHA zaro ido momy tayi tare da nunata da hannu takasa magana jikin momy saï rawa yake hakama Abba da ko motsawa ya kasayi domin ki yake kamar mafarki yake ba gaskiya bane to yahaka kenan innalillahi wa'inna ilaihirraju un Wai meke faruwa danine meyasa ake mamakin ganina Wai menazama ne kodai n'a mutune "NABEHA tafada idonta cike fal da hawaye da majina a hanci ,idanunta cike da hawaye bakin ta n'a rawa ta kasa jure abin da take gani hakan yasa ta fine su Tace"Dan Allah kifadamin suwaye ku meyasa kuke mamakin ganina shin ko na aykatamuku wani abune?" Dan Allah kuyi gaggawar sanar Dani dafari wadancan sunata cewa Ni kanwar GENERAL MUS,af ce yayin da suke nakalamin sunan wata wadda ni bansan taba gashi kuma kunzo kuna ambatona da wannan sunan menayi muku suwaye ku?" *Jiki a sanyaye Abba da momy suka karasa gefan gadon tare da ruke mata hannu, Abba kuwa junata Ido yayi Yana kallonta cikin mamaki,momy kuwa cewa tayi" tabbas son yayi gaskiya dayace saiyazo ya dakko "yar,uwarsa sai dai Kuma wannan ba mufida bace ""me ba mufida bace to idan ba ita bace wannan wace? Cewar ADEENA "Mufida tafi wannan girma sannan mufida akwai dugon tawada a gefan idonta Kuma fatar wannan yarinyar data mufida da banbanci sannan yanayin idonsu kwayar idon nufi da bakace itakuma wannan blue ce kuma kunsan mufida ta rasu meyasa bazamu yarda da kaddara ba duk mutumin da yamutu baya dawowa kuma muma Dole saï mun je inda tatafi ,wannan dakuke gani kamace kawai da ubangiji yayi halittarsa daman ance duk mutum irinsa su bakwaine a duniya tayuwu Allah ya bamu wannan yarinyar domin ta mayemana gurbin mufida Allah sarki son yanacan Babu bacci Babu cin abinci duk Sabi da damuwa saikuma gashi Allah ya dawo Mana da madadinta tabbas Babu abin da zamuyi was Allah sai godiya" tun da momy ta soma magana sai yanzu KHADEEJA ta kula da gaskiyar lamarin tabbas itama yanzu ta tabbatar wannan ba nafisa bace domin ko a tsarin halittarsu fuskar wannan yarinyar tafi ta nafisa kyau . Shiko Abba bece komai ba sai juyawa dayiyi ya kalli ADEENA yace" yarinya yaushe akace za a sallemeku daga asbitin Nan Kuma kanwarkice wannan din" uhm a,a Abba ba kanwata bace Nima bigetanayi cikin wani hali Mara kyangani shine na kawota asbiti ananne nake ganin kamatsu da mufida shine nace afada muku" Kuma yanzu ma an sallame mu ku muke jira kawai" ayya Allah sarki munko gode sosai ina fatan zaku barmana ita murike ahannunmu ko" eh Abba mu yanzuma hucewa gida zamuyi daganan saiku huce da ita" oh Babu damuwa mungode kkwarai daga Haka abba yayi musu kyauta meyawan gaske sannan suka fito momy ta kama hannun NABEHA, Tun da suka Shiga mota NABEHA babu abin da take sai kallonsu cike da tsoro da fargaba kaddai ace dagaske tamutu wannan aljanna ne tasamu gata Haka?,bata karasa tunaninba taga an yankwa kwana sunshiga wani katafaren get Wanda shikadaine gida alayin inda kasan duk mutanen duniyane zasu zauna aciki Haka girman gidan yake ga sojoji ta ko Ina ka huce saï kaga suna dagawa su abba hannu, saï da sukayi tafiya me nisa sannan suka nufi get na beyu ananne suka karasa parking space sukayi parking sannan suka fito ,Kai tsaye gidan suka shiga a falo suka samu genaral saï sintiri yakeyi a falo Yana muzurai , tun da yaji sallamar su momy ya karaso dasauri Nan take idanunsa sukayi arba da NABEHA wadda fuskarta tayi jagajaga da majina da kwalla, Allah sarki jikinsa har rawa yake yakaraso gabanta ya Kama kafadarta yasaki wani kuka kamar karamin yaro can Kuma ya mannata a kirjinsa da saki kuka,ita kanta NABEHA batasan meyasa ba kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka,dasauri ya dagota ya Kama fuskarta ya dauki lallausan hannayensa ya dorasu a kan fuskarta yashiga gogemata wahaye da majina Yana rarrashinta murya asanyaye ya ce" jery na meyasa za ahada Baki dake Amin irin wanan wasan eh meyasa eh kinsan halin da nashiga wallahi badaban irin son danake mikiba saina dakeki" Baki da hanci NABEHA tasaka murya adashe Tace" waye Kai nifa bansanka ba " Dan Allah kufuddani a haski duk kunsa nashiga rudani" zame hannunsa yayi daga kan fuskarta yayi baya kadan a razane sabi da abin da yagani" tabbas keba jery n'a bace saiyanzu nakula da kwayar idonki sanan da maganarki muryarku ba iri daya bace Wai shin dagaske jary na ta rasu hmm bakomai momy koma dai menene inason wannan domin nadinga ganinta a madadin jery inason ki barta a part Dina kamaryadda muke zama atare da jery "gabaki daya Abba da momy dago ido sukayi cikin kaduwa suna cewa"baka da hankali bazai yuwuba idan mufida maharramar kace wannan ba maharramar kabace "Abba koma dai menene Ni inason ta zauna a tare Dani" bazai yuwu ba Abba ya shiga daki fuu momy kuwa hannun NABEHA takama sukayi bangarenta suka bar genaral a tsaye idonsa cike tab da hawaye. *Tun da suka shiga dakin momy ta zaunar da NABEHA a gefan gadon tare da fuce wa batace mata komai ba Kai tsaye bathroom ta shiga ta hada ruwan zafi wan da zai kwarara jikinta domin likita yayi mata bayanin abin da yasameta bayan ta hada ruwan ne ta dawo Bédroom d'in ta kamo hannun NABEHA suka Shiga bathroom ,zaunar da ita tayi sannan ta Kama gashin kanta tawanke shi sosai da sabulu masu kamshi sannan ta daure da tawul Tace"Zan fita Ina jiranki adaki kiyi wankan maza ki fito kada ki manta ki gasa kanki sosai" tama Gama fadar Haka tayi waje,itako NABEHA kallon tabita dashi tare da dawo da idonta cikin bandakin ganin yadda komai ya tsaru kamar ba bandaki ba ruwan wankan takalla yadda kamshi ke tashi a cikin kwamin wankan kamar ba ruwaba gashi ya canza kala daga fari ya koma blue , mikewa tayi tsaye duk da batasan yadda ake amfani da kayan bandakin ba Haka ta daure tayi wankan ,sosai taji dadin jikinta bayan tagama ne ta dauki tawul ta daura a jikinta sannan ta fito ,azaune tasamu momy hannunta dauke da wasu Kaya ruga da wando farar riga bakin wando na jins sai hula a hannun ta itama fara me tatsin Baki , tasowa tayi ta karaso ta Kama hannunta sannan ta jata zuwa gaban mudubi ta zaunar da ita,kanta ta bude Nan take yalwataccen gashinta ya bayyana dogaye masu sheki ,wayuka ta dakko ta shafa mata sannan ta taje ta gyra shi sosai tayi nata kitso daya jelar ta fada gadon bayanta tayi kyau sosai Kayan ta Mika mata bura da fant ta saka sannan ta bata farar rigar ta sa daga bisani kuma tabata wandon wayyo allah kuzokuga yadda NABEHA Takoma baturiya ay bakiga komaiba sai da tasaka hular sak baturiya Haka tazama idan ba ni danasan NABEHA ce ba da Haka zance wata balarabiyar ce ta kawo musu ziyara Masha Allah daman komai Yana bukatar gyra. Kwallace kwance a idon momy ganin yadda taga NABEHA Takoma sak mufida Babu abin da take tinawa irin ranar da zata rasu kayannan sune a jikinta Daman ita can ba ma,abociyar sa manyan Kaya bace, allahu akbar rungumeta momy tayi Tace" Dan Allah yarinya kizauna tare damu wallahi Ina sonki" kuka NABEHA tasaki acikin zuciyarta Tace"oh wasu suna gudinka wasu Kuma suna sonka " yasunan ki" kalmar da NABEHA taji momy ta fada kenan" uhm sunana NABEHA "Masha Allah suna me dadi NABEHA zo muje kici abinci" atare suka fita falon momy rike da hannun NABEHA ,ashe Ain da suka tafi suka bar genaral yanan a zaune Yana ay kin dayasa ba wato tunanin MUFIDA, zumbur ya Mike ganin yadda yake ganin mufidansa sak ajikin NABEHA kallonta yake kamar zai hadiyeta itako NABEHA kallon sa take cike da tsoro da fargaba . BAYAN sun ci Abincinne abba ya zo falon suna zaune itama NABEHA na zaune gefan momy sai genaral ma a Zaune ya kuramata ido kamar zai cinyeta. Gurinne yadauki shuru hakan yasa Abba yayi gyran murya yace " yarinya yasunan ki" sunana NABEHA "Masha Allah sai gashi bakisan muba nasan abin da kikeson sani kenan yanzu suwa ye muko to insha Allah yanzu xakiji takaitaccen bayani akanmu Amma kafin Nan inason ki sanar Mana da wacece ke"wasu zafafan hawaye ne suka Shiga ambaliya aruskar NABEHA jitake zuciyarta na tukuki bakinta yakasa fadar abin da akeso tafada, abbane yasake cewa" ki kwantar da hankalin ki kiyi Mana bayani?" Sallamar Abdul ce ta katse musu maganar da suke abba kuwa juyawa yayi yace wa, alaikumussalam Abdul yanaga kadawo ina fatan andace ko" Abdul karasowa yayi jiki a sanyaye Babu kwari yace", Abba wallahi naje basanan bansan yadda zanyi ba.... Sai yayi shiru da maganar da yake ganin NABEHA a zaune "zaro Ido yayi tare da cewa keee NABEHA mekike anan" Ina su Amrah?" Genaral be yace Kai wannan fa mufida ce kamakance ne" a,a yaya wallahi wannan NABEHA ce ay nataba fadamaka nasan wata yarinya a doguwa me gama da mufida amma ita yarinyace to ay itace wannan" ke NABEHA ina sauran suke?" Kuka NABEHA take ta tashi dasauri ta karasa gaban Abdul Tace Yaya Abdul Ina su Adda Amrah da ummana?" Tayi maganar idonta cike fal da hawaye" tabdijan to kenan idan Baku tare ke Ina kika tafi wai ni ban ma ganeba mené yakawoki Abuja"? Yaya bama tare da su Tun ranar bwai na mahaifinmu ABBO FAHIMNA tatafi Dani da Adda NINEE ,Nan dai takwashe duk abin da yafaru tana kuka tana fadamasu har yadda akai ta baro gidan kuka take tana cewa" Yaya ABBO ta ci amanar zumunci danta ta cutar dani gashi bansan inda Adda NINEE takeba " gabaki daya gurin saï da suka tausaya mata hatta abba saï da ya goge kwalla shiko genaral cewa yayi", Ashe dama' akwai marasa imani aduniyarnan irinsu ABBO tabbas sun aykata babban kuskuren dasai sun karbi laifinsu sunyi shuka Kuma sai sungir ba " Allah sarki bayin Allah kenan wannan kaddara Haka gaskiya kunyi gamo da jarabawa daban daban ammma Allah baya zalinci cewar abba itako momy kara janyo NABEHA tayi jikinta ta rungumeta domin yanzune ma takejin son yarinyar yakara shigarta. 16... Shikuwa genaral sai a lokacinne ya yadda wannan ba mufida bace Amma kuwa indai hakane dolene yasan yadda zaiyi NABEHA ta zauna a tare da su ko Babu komai zata mayamasa gurbin kanwarsa, Yana tsaka da wannan tunanin yaji wayarsa tashiga ruri cikin sauri ya dauki wayar ya duba MEJO ABDALLAH ne, dagawa yayi tare da cewa assalamualaikum "wa, alaikumussalam aka amsa daga can bangaren "yauwa baby Ina tunanin gobe Zan iso Abuja da yardar ubangiji" Kai wai dagaske kake ko dawasa?" Allah dagaske ko dady ban Kira nafada Masa ba " tom shikkenan kace nafadawa su momy su fara Shirin tarbar bako ko" eh to kasan aykine fa Zai kawoni akwai wani atisaye dazamu je yi " ayya Tom badamuwa ina ne zakuje?" Jejin falgore munason zamuyi ayki acan sabi da kasan habyarnan bata da kyau masu kidinafin sunyi yawa a gurin ga yan daba "oky Tom saï kadawo nima idan kazo akwai labari "Tom shikkenan ammafa dan Allah kada ka fadawa dady cewa zani wannan jejen "Tom ba damuwa insha Allah bazan fadawa UNCLE ba" daga Haka genaral ya katse wayar . Yana katsewa sai ga wani Kiran yasake shigowa cikin hanzari ya daga tare da cewa "barka da wannan lokacin uncle "barka dai son ka ina Haka" ina gida " yauwa maza maza kazo muje makarantar nan inason zuwa domin nagabatar da wani sako" oky uncle ay badai kajeba kabari nazo sai nakai" a,a muje tare nasan halinka zaka iya cewa zaka Nemo wannan yarinyar domin ka daketa" no uncle kokadan" koma dai menene maza kazo mutafi" okay yakatse wayar tare da mikewa yashiga daki ,BAYAN yashiga ruwa ya watsa yafito ya dauki milk din yadi mesantsi da tsada ya saka sunmasa kyau sun amshi jikinsa sosai ,bayan yasa ne ta fito yasamu su momy azaune inda suke ga NABEHA a kwance a cinyarta taci kuka har ta gaji ta Yi bacci ,sallama kawai yayi musu sannan ya nufi hanyar fita har yaje bakin kofa kana ya dawo ya durkusa ya kurawa kekkewar fuskar NABEHA Ido sannan ya shafa kanta ya fuce,momy kuwa ikon Allah suka tsaya kallo" shiko Abba Haka yace" ah abin da mukeso yayine tun tuni yaki sai yanzu Allah ya kawo yakamata muyi amfani da wannan damar mu aurawa mus,af wannan yarinyar nasan bazaiki ba suba da yadda yake sonta har cikin zuciyarsa" a,a Anya kuwa ayi Haka shifa mus,af son dauakewa wannan yarinyar Yana kallonta ne tamkar kanwarsa mufida bawai Masoyiya wadda zai aura ba amma dai bazan tari numfashin ka ba mujira ya dawo muga yadda abin zai kasance bamu sani ba ko zai amince," *Kano* *DORAYI* Tun da nafisa ta kulle kanta a daki Taki bude,sai dukan kofar ummanta da Inna suke Amma Ina Taki ko motsawa balle ta bude "dan Allah nafisa kada ki aykata Haka ki bude kinji Dan Allah idan su mutanen gari basa kaunarki mu muna kaunarki ki bude nafisa nafisa dan Allah ki bude" cewar fatima datake ta kuka kamar ranta zai fita ,umman nafisa ce ta janyo hannun fatima Tace" Dan Allah Fatima ki fadamin meyasamu nafisa take rufe fuska yanzu Kuma tashiga daki a rufe kofa metakeson aykatawa kanta?" Kuka Fatima tasaki tare da cewa"wallahi umma baba kabiru ne ya mata duka har sai da ya fasamata jiki da fusa " nashiga uku fatema Akan me metayi masa" wai yagaji da ganinta a cikin ahalinsa ita gurbatacciya ce gwara ya kasheta ya huta"Innalillahi wa'inna ilaihirraju un nashiga uku yanzu ina kabirun yake" wallahi Nima bansan inda yake ba " kuka umman nafisa ta fashe dashi tanufi kofar zata bude Fatima Tace "kiyi hakuri umma Ayanzu ko kallon fuskar NAFISA bazaki iyayi ba domin ta kone"azafafe umma ta zaro Ido Tace "takone takonefa kika ce kada ki fadamin yanzu nafisata bata da fuska shin dagaske meyasa waya konata?" Umma bayan baba kabiru yagama dukanta ne shine ta futa Tace zuwa zatayi takashe kanta tahuce ,tanatafe ta hadu da wasu maza su uku dayan yace Mada dama ita yakeson gani ance idan yaganta ya illatata Kuma dama' shi yatsani ganinta shine suka watsamata asit a fuska "asit fakimace umman nafisa ta sulale agurin sumammiya, dagudu Inna ta debo ruwa ta watsa mata sannan ta bude Ido a hankula tashiga zub da hawaye tana cewa"nashiga uku suncuce Ni tabbas natabka babban kuskure arayuwata Dan Allah fatema kuje ku samo wasu a balla kofarnan mutafi asbiti" dasauri fatima ta Mike harda tuntube wajen futa sannan taje ta kirawo mutane a ka zo Aka balla kofar "innalillahi wa'inna ilaihirraju un nafisace kwace cikin jini kirjinta n'a bugu zuciyarta kuwa kamar zata bullo waje fuskannan tata ta kiné kamar waina innalillahi wa'inna ilaihirraju un abun Babu kyen gani hannunta kuwa wukace Yar madaidaiciya wadda ta caccakawa kanta domin tanason mutuwa tabar duniyar"Kara suka kwada ganin halin da nafisan me ciki da sauri mahaifiyar ta ta dauketa ta sabata a kafada ta watsa a guje tana kuka tana neman taimako har tafita bakin titi jini kuwa duk ya wanke mata jiki itama, gashi wani tashin hankali duk motar da zasu tsayar Bata tsayawa hakan yasa umma ta jage tana tafiya tana kuka har taci Karo da wata mota tazo hucewa ta sha gabanta tsawa motar t'ai sannan mutanen dake ciki suka fito Alhaji ABDULHAMID ne yayi saurin cire karamin Glass d'in idonsa tare da kura mata ido Yana mata kallon mamaki shimuwa genaral mus,af haushine ya isheshi hakan yasa yace" uncle mutaimaka musu zata mutufa" lokacin ne alhaji ABDULHAMID ya kula da nafisa wadda ke kafadar mahaifiyar ta tana numfarfashi cikin sauri alhji ya sa hannu zai dauki n'a fisa umma ta dakatar da shi dacewa" dakata malan bama bukatar taimakon ka ayanzu ina tsananin bukatar taimako amma ba awajen kaba muddum Kai zaka taimaki yarinyar nan saï dai tamutu a kafadata ahaka," genaral bejira abin da suke fadaba yasa hannu ta funciki nafisa daga kafadar mahaifiyar ta yasata Amota sannan ya janyo hannun umma yasata a ciki ya kulle sannan suma sukashiga aka soma tafiya zuwa asbiti. 17... *ABUJA* Tun da NABEHA ta kwanta momy ta kasa mikewa Sabi da Bata kaunar ta motsa tatashi hakanyasa tayi tazama har karfe 5 na yamma ,abin da ya Bata mamaki shine hanin yadda tsawan lokacin NABEHA Bata farka ba hakan yasa hankalin momy ya tashi tashiga daba NABEHA Amma jikake shiru Babu NABEHA Babu alamun tashinta, Abu kamar Wasa tun tana tashinta a hankula har tadawo tashinta da karfi Amma NABEHA ko motsi batayi tashin hankali sai yanzu ma takula da ko numfashi baya futa daga jikin NABEHA innalillahi wa'inna ilaihirraju un meyasameta Haka" dasauri ta dauki wayarta tashiga Kiran numbar GÉNÉRAL amma shiru be daukaba hakan yasa ta hau sama ta duba dakin Abdul shima bayanan amma ta kirawo awaya Yana office Yana saita wasu takardu yaga Kiran cikin sauri ta daga tare da cewa Assalamualaikum" Bata ko amsa ba Tace" kana Ina inason kadawo yanzu NABEHA fa .. "meyasameta "Kai dai kadawo gida akwai matsala" oky Ina muhsin baya nan ki kirashi Yana kusa" no kasan muhsin Yana Jos yaje wani aykine" a,a dazu yakirani yace yau zai dawo gida Ina tunanin ma yanzu yasauka " Bata karasa maganar ba saiga sallamar sir muhsin"cikin sauri Tace yauwa gashima ya karaso ta katse wayar" yauwa muhsin maza taimaka yarinyar nan mukaita asbiti bansan me yasameta ba" yarinya kuma Wace yarinyar "? Kaga kataimaka mukaita asbitin mayi wannan maganar daga baya" oky muhsin ya dagota cak abin da yaba shi mamaki yasashi ya tsora ganin mufida Kai momy mufidace" nace mayi magana daga baya haba" batare da yace komai ba suka nufi mota don zuwa asbitin. Tun da jirgin su MEJO ABDALLAH ya sauka suka hau mota basu isa kaduna ba saï karfe 9 n'a dare a hanyarsu ta dawowa ne yaci karo da wata matashiyar buduwa har ya bigeta besani ba,dakamar bazai tsayaba ganin kamar aljana ce dan yasan Babu abin da zai fito da mutum kumama mace a wannan lokaci can dai yace wani soja ya fita ya duba, Yana dubawa yadawo yace"sir wannan yarinyar fa mutumce Kuma Babu abin da ya sameta nagama tana motsawa okay maza shigo da ita cikin nan mutafi, Babu musu sojan ya damki hannun NINEE yasata acikin motar suka cigaba da tafiya . ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO KARSHEN BABBAR SAKAYYAH BOOK 2 SAI MUN HADU A 3 WANDA ASHINE ZAKU GANE ASALIN LABARIN DA INDA MUKA DOSA SANNAN ANANNE ZAKU SAN ASALIN SU AMRAH DA ITA KANTA NAFISA . WANNAN LABARIN ME DOGON ZANGO KADA KUBARI AYI BABU KU BOOK 3 PAID NE 500 BABU TSADA NO. 09166764540 . GODIYA TA MUSAMMAN GA DUBUN DUBANAR MASOYA LITTAFIN BABBAR SAKAYYAH INAGODIYA KWARAI DA GUDUMMAWARKU A KAINA.