RASHIDA Bismillahir Rahmanir Rahim Zamu fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai ya Allah yanda narafa wannan littafin Allah ka sa na gama shi lafiya By SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️✍️ 08080304152☎️📱 PAGE NA ƊAYA 1 📝 Wa ni Babban gida ne shi ba za'a ce na ma su kuɗi ba kuma baza'a ce na talaka ba. Gidan ya haɗu ba ƙarya wasu ƴan mata ne a zazzaune tsakar gidan su na aikin danna waya. ɗayar na sanye da yellow atamfa da ratsin pink a jiki ta na chatting da wayar hannu ta. Ɗayar na sanye da riga da skirt ƴan kanki ta na game hankali ƙwance. Ɗayar kuma jikinta sanye da Jersey, sai Wando wan da alamu sun nuna, kawai daddana wayar ta ke. Wacce keda yellow ɗin atamfa ce ta kalli mai ragi da skirt ɗin tare da faɗin."Fatima wai menene na ji Kaka na faɗi ne kam?, na ji kamar ta na magana a kan Yaya Rufa'i. Wacce ke da riga da skirt ɗin ta ce "ashe dai ba bacci ki ke ba tun da har ki ka ji maganar da Kaka ta ke, A'ishah ai na san tun da a ka kawo rayuwar ki na san za ki farka". Fatima bari wallahi ina son Yaya kamar na yi hauka. Fatima ta ce "ke dai A'ishah ba ri soyayya ta yi wallahi sai dai wa su kam in bar su a ba ya". ta na maganar ne ta na kallon mai jersey ɗin. A'ishah ta ce "ke dai bar ta Kaka ta haɗa ta da Yaya Rashid ta kai karshen soyayya", hahaha su ka sa ka dariya. Wacce ke san ye jersey ɗin ta ce "ɗan Allah ku bar ni na huta duk kun cika min kunne da surutun ku mtsww, kuma wallahi Allah ya tsaran da bakin ku wannan ɗan baƙin halin, za wani ce a haɗa ni da shi". Fatima ta ce"ha ba Yayana ne fa kuma ki ke wa ni kiran shi da ɗan baƙin hali", ta na maganar ta na dariya. Mai jersey ɗin ta ce "ni kam ba ra na yi tafiya na sai ku ci ga ba da in da ku ka tsaya", ta shi da yi da ni yar shiga falon gidan ta ci karo da mutum ƙamshin turarin shi ne ya sa ka ta ga ne ko wa ye ta ce "na shiga uku ni Ummi. Ɗauke ta da maruka ya yi har sau uku sannan ya wullar da ita a ka sa ji ka ke tim. Ya ce "ke wacce irin mahaukaciya ce ke, bakya gani ne?,ko bakya ji ne?, kuma ko rai na ni ne ki ka yi ehhe?. Cikin kuka ta ce "wallahi Yaya ba da niya na yi ma ka haka ba cikin falon zan shiga kawai..." Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya sa ke ɗauke da mari har 2 ya yi tafiyar shi. Kuka ta ke ba kaɗan ba har ƴan gidan sai dai suka fito su na tambayar ta lafiya?. Wata mata ce kyakkyawa gaske haushe ya ishe ta, ta hau bala'i,ta ce "ai rainin wayo ne wannan". Dan iskanci ana magana kin yi wa mutane banza ta yi kan ta gadan-gadan, ai ta na ganin ta yi kan ta ta shi ta yi bayan wata mata kyakkyawa ita ma. "Daka ta Maryam mai za ki yi ne?, ba dai dukan ta za ki yi ba?,ba ki da tausayi ne kam eh?". Amma ba ki ganin jama'ar da ke kan ta ana ma ta magana ta yi wa banza. "Yarinyata faɗa min waye ya dake ki Rufa'i ne, ko Ma'aruf ne, ko ɗan baƙin halin can ne"?. "Eh Mama Yaya ne wai na je shiga falo ne mu ka yi karo da shi, shine ya kwaɗamin maruka har sau biyar". "Capp sau biyar fa ki ka ce?, wallahi ko yau sai ranshi yaɓaci a gidan nan, Rufa'i kira min shi". "Ai ko ran da yawa zai ɓaci kenan" cewar Maryam. Mai ki ke nufi da ran mutane da yawa zai ɓaci?. Wallahi idan ki ka ɓatawa yarona rai sai na ɓata na wannan sha-sha-shar. Mama hanun Ummi taja suka shige cikin gida ɗakinta ta kai ta toilet ta shiga ruwa ma su zafi Mama ta haɗawa Ummi, sannan ta zo ta kama hanun Ummi su ka shiga toilet ɗin, ta ce "ki yi wanka kinji yarinyata Allah ya miki albarka", toh kawai Ummi ta ce. Shi ko Rashid su na can ɗaki su na fira da Su Ma'aruf. Ma'aruf ya ce " babban Yayanmu dan Allah ka yi wa su Mama magana idan aka tashi auren su A'ishah a bamu su wallahi Ni dai ina son Fatima sosai saboda Fatima akwai hankali ga nutsuwa uwa uba tarbiyya gaskiya Fatima maƙura ce", ta na maganar ya na murmushi. Rufa'i ya ce "babban yaya ni ma ina son A'ishah sosai saboda A'ishah ta iya shagwaɓa ga hankali da sanin ya ka ma ta wallahi A'ishah idan ta na kiran Yayana sai naji kamar na sun baceta saboda ina son mace mai shagwaɓa". Ma'aruf ya ce "ai Rufa'i shagwaɓa duniya ce wallahi bazaka san mace ba sai ka samu mai shagwaɓa saboda shagwaɓa duniya ce malam". Rashid ya ce "kai dallah kumin shiru sha-sha-shan banza ko bakwa da magana sai ta yarannan idan son su ku ke yi kuje can ku faɗa masu mana amma kunzo kun cika min kunne da surutun banza". Ma'aruf ya ce" kai malam wallahi idan soyayya ta ka ma ka bazata zo maka da sauƙi ba ga ra kabi komai a hankali naybe ita ma ta bika a hankali". Rashid ya ce"Ma'aruf wallahi zanci uban ka ɗan iska kawai ni za ka na wa maganar nan dan iskanci toh ka sa ni ba yarinyar da na ke ga ni a mace duk maza na ke gani a kayan mata har yanzun". Ma'aruf ya ce" a a malam ka dai ce zakaci uwata ba dai ubana saboda Uwata ce sa'arka ba ubana ba", ya faɗi maganar ya na dariya. Rashid sarai ya san Ma'aruf zagin sa ne ya yi amma sai ya basar, ya ci ga ba da abin da yake wato danna laptop ɗin sa Rufa'i ya ce "wai babban Yaya sai yaushe za ka fitar da matar aure ne kasan Kaka fa sarai za ta iya haɗa ka da ƴar banzar da tazo gidan nan wallahi yarinyar da gani ba ta da natsuwa". Ma'aruf ya ce "wallahi ni kam yarinyar ga ba ki ɗaya bata birge ni ba saboda ko shigarta ba ta ma su hankali ba ce Rashid ya nisa ya ce "ku bar su kawai wallahi ni yanzun a haɗa ni da mace ban san mai zance ma ta ba saboda ga ba ki ɗaya ban tsara yin aure a yanzun ba". kasan maike da mu na a yanzun wallahi na samu hanyar barin garin nan har komai ya lafa?". "haba Yayanmu aure fa Rahama ne ba za ka san aure Rahama ne ba sai ka shiga da ga ciki, ka sa mu budurwa cikin ƴan matan da ke sonka ka ga, ga Rufaida, Ilham,Rumaisa, A'ishah, musamman A'ishah yarinyar na son ka sosai wallahi", cewar Rufa'i. Tsaki Rashid ya ja ya ce "wai mai ya sa a kullum zancen ku, ba zai wuce na mata ba ne ehhe, kun zo kun cika min kunne da surutun ku mtsww, kura sa wa zaku saka min a zancen sai ƴan iskan can"., cikin ɗaga murya ya ke maganar saboda sosai maganar ta ɓata ma sa rai , falon su ya zauna. Ma'aruf ya ce "wai mai yasa ba ka san maganar aure ne Rashid ko ka san aure Rahama ne, ko dai ka na da Aljanu ne kariƙa sassauta ran ka mana bana son ɓacin ranka wallahi dan Allah ka yi hakuri ka je ka yi wanka mu fita na gaji da zaman gidan nan". Rufa'i ya ce "ka yi hakuri my lovely brother ka yi hakuri muje na yi maka wankan sai na shirya ka na goya mu tafi kaji yayanmu". Hahaha dariya maganar shi ta ba shi wai muje nayi ma ka wankan sai ka ce ɗan shekara 2&3, cewar Rashid. Idanuwa suka bishi da su su ma sun san ɗan uwan su kyakkyawa ne dole ƴan mata su haukace a kan shi, maza ma idan yana dariyar birge su yake ina ga mata. Dariya ya dai na ganin duk sun saka ma sa idanu ya sa ya hade rai. Yi hakuri brother ka je ka yi wanka mu na jiran ka fa. Tsaki ya yi ya yi shigewar sa toilet. Ma'aruf ya ce "wai ba ka fahimce wa ni abun da ga gare shi ba ni sai na ke ganin kamar akwai wacce yake so kawai ya faɗa ma ta ne ba zai ba". Rufa'i ya ce "ka san halin shi aii irin su ne soyayya kewa kamun mahaukaciya. "Bara na kira Ummi ta kawo mana abinci saboda yunwa nake ji, kiranta ya yi ya ce ta kawo musu abinci", ta ce "Yaya ba na jin daɗi ne ka cewa Fatima ta kai maku abincin, Ummi na ki muke so dan haka ki yi sauri tun ran ki bai ɓaci ba. ɗip wayar ta katse. Ta shi ta yi ta je kitchen ta ɗauki abincin ta kai ma su. Ta ce "Assalamualaikum". "Waalaikamussalam" suka amsa ma ta. Ta na shiga ya na fitowa daga shi sai kajeren tawul a ƙogun shi duk rabin cinyar shi a waje. Kallo ɗaya ta yi tsoro da farga suka isar ma ta. Shi ko kallon mamaki ya ke ma ta mai yasa yarinyar nan ta raina ni ne har ha ka. Kamin ya gama tunanin shi tuni ta gudu ta bar ɗakin. Shiryawa ya yi su ka ci abinci suka fito zuwa inda iyayensu. Part ɗin Umma su ka fara zuwa suka gaida ta suka fito zuwa, part ɗin Mama a can suka tarar da su Fatima Ma'aruf ya tsurawa Fatima idanu shi ko Rufa'i A'ishah ya ke kalla shi kam gogan naku ya ka sa ga ne meyasa Idan ya ga Ummi ya ke jin wani iri. Ta na shirya saboda su ma fita zasu yi. Ma'aruf ya ce " Ummin Mama ina zuwa wannan wanka haka". Wallahi Yaya fita za mu yi ne za mu je gidan wata ƙawata ne. "Ok mu ma fita za mu yi, ko zo muje mu ajiye ku a gidan ko". cewar Rufa'i. Fatima da A'ishah kam baki har kunne saboda daɗi. Mama ta ce "kai ku tashi ku bar ɗakin nan mai ku ka zo yi ne ehhe?". "Ayya mama yi hakuri ina wuni mun sa me ki lafiya suka faɗa a tare". "Humm." kawai Mama ta ce sannan ta du bi Ma'aruf ta ce "ina za ku ne yanzun wannan wanka haka ko dai an sama mana sirika ne?." Hahaha "kai Mama sirika Kuma yanzun ai har yanzun yara ne mu. cewar Ma'aruf". Rufa'i ya ce "Mama ai idan muka samu matar aure ke ce zamu fara faɗawa, amma yanzun kin ga yara ne mu yanzun haka Umma ce ta yi mana wanka fa". Dariya sosai su Ummi ke yi shi kam gogan naku har ya san da re saboda kyau da ya ga Ummi ta kara yi ma sa ya ce ma sha Allah, bai san maganar ta fito fili ba. Sai ji ya yi Rufa'i ya ce "aboki menene ma sha Allah ko ka samu budurwar ne. Fuske wa ya yi ya ce "ina ruwan ka ɗan sa ido kawai", ya ta shi ya yi tafiyar shi ya yi ko Kaka basu gaida ba suka yi tafiyar su Su Ummi na a bayansu su ka isa a harabar gidan wajen ajiye motoci suka je. Rashid ne zai yi Driving saboda ha ka Ma'aruf da Rufa'i su ka koma ba ya A'ishah da Fatima bayan suka shi ga a ka bar Ummi a wa je... Rashid ya watsa ma ta kallan banza da idanunsa ma su rikitarwa rai a ɗan ɓace ya ce "wai wanne irin wulaƙanci ne ana jiran ki kin share mutane sha-sha-shar banza wallahi sai na yi tafiya na?". "Am... Yaya ban san in da zan shiga ba ne, kuma Yaya Rufa'i sun shige baya". "Ai sai ki hau kan su ki zauna banzar yariyar kawai, shi wannan kujerar ba abin zama bane ko?". Saurin shiga gaban motar tayi ba shiri tun ba gama gyara zamanta ba dan ko marfin motar bata rufe ba yaja motar a tsiyace aiko ta kame shi sosai tana kuka. Ma'aruf ya ce "haba Rashid idan ka hallaka min ƙanwa fa wanne irin baƙin halin wannan ka yi parking ɗin motar nan wallahi", cikin fushi yake yin maganar saboda sosai hakan ya ɓata ma sa rai. Parking ya yi ya kama hannun Ummi ya jefar da ita a kasa sannan ya ce "kan wannan jakar za ka ɗaga min murya toh wallah..." Bai bari ya Ida maganar ba ya katse shi da faɗin. dallacan ana jaki bayanka ne kuma wallahi ka sa ni duk abin da ya sa mi Ummi sai na rama ma ta sha-sha-shan banza kawai mara imani", ya na faɗan haka ya fita daga motar Ranshi a ɓace. Rufa'i ma fita ya yi daga motar shima Ranshi ba daɗi. Tashinta ya yi ya shigar da ita cikin gida koda suka shiga gidan a falo suka tarar da su Umma. Ta shi Mama ta yi ta ce "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un mai yasa mai ta ne haka?" ta faɗa cikin san jin abin da ya faru. Amsarta Mama ta yi ai ta na taɓin jikin ta ta ji shi zafi sosai ga Ma'aruf sai huci yake ganin haka yasa tayi shiru har zuwa komai ya lafa. Rashid ta kira kan yazu ya duba ta sai ya ce ai ba ya gida ya fito Unguwa ne, haka dole Mama ta kira likita ta faɗa ma sa abin da ke faruwa ya ce ta bashi minti 30 yana zuwa, dole haka Mama ta cigaba da jiran zuwan likita. Rashid tafiyar shi ya yi amma zuciyar shi ba daɗi. Aiko likitan bai fi minti 30 ɗin ba yaƙaraso, jikin ta ya duba ya ce zazzaɓi ne mai ƙarfi ya kamata, maganin ya ba ta ya yi tafiyar. Rashid ba shi ya dawo gida ba sai dare, ya ba shiga ɗakin su ya tarar da Ma'aruf da Rufa'i su na maganar wulaƙancin Rashid saboda ya yi yawa. "Assalamualaikum" "Waalaikamussalam" suka amsa ma sa a ta re. "Ma'aruf kira yaran can su kawo min abinci saboda ba zan iya zuwa dainning ba". Ma'aruf ta shi ya yi yaje ya kwanta abinshi. Rashid ya ce "wai ba da kai na ke Magana ba ne ehhe bana son wulakancin Nan fa"?. Mtsww banza kawai tun da gani ɗan aikin ka ba ai dole zan kira ma ka su kuma kasani wallahi-wallahi-wallahi idan yau baka barni na huta ba duk abin da nayi ma kai kaja banza jaki. Shima kanshi yasan baiyi dai-dai ba dan haka ya shiga bawa Ma'aruf hakuri. Shi dai Rufa'i sai bin su yake da idanu sannan ya ce "Rashid ka san ba ka yi gaskiya ba saboda ko ba komai Ma'aruf ɗan uwanta ne kuma Yayanta kana wulakanta ta a gaban shi, amma baya Mu sa ma ka haka ba ya na nufin jin tsoro ba, a a girmama juna ne amma gaskiya nima yau ka ban haushi sosai. RASHIDA BY SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️✍️ 08084277827☎️📱 PAGE NA BIYU 2 📝 Rashid ya ni sa cikin muryar ne man afuwa ya ce "haba Ma'aruf ka yi hakuri dan Allah na san ƙanwar kace, amma wallahi yarinyar ba ta ji ne saboda su Umma duk sun sangarta ta amma dai kayi hakuri ɗan uwana". Ma'aruf ta shi ya yi ya yi tafiyar shi part ɗin Mama. Shiga ya yi sallama ɗauke a bakin sa "Assalamualaikum" Mama ce zaune ta na lazumi ta amsa ma sa sallamar "waalaikamussalam" Zama ya yi tare da cewa "Mama ina wuni"?. Amsawa ta yi ta ce "kawuni lafiya Ma'aruf"?. "Lafiya ƙalau Alhamdulillahi" Mama ina Ummi ta ji sauƙi kowa?. Eh kam ta ji sauƙi sosai ma yanzun su ka fita ina tunanin ko su na part ɗin Ummansu ne. Toh shi ke nan zan wuce sai da safee. Da ka ta kaji Ma'aruf mai yasa mai Ummi ne ɗazun saboda lafiya ƙalau ku ka fita a ɗakin nan sai ga shi ka kawo min ita ba lafiya mai ke faruwa ne ka faɗa min gaskiya?. Mama ba komai kawai kin san shi lafiya ba ya zama a jikin ɗan adam dole ne wani lokacin za ka ji zazzaɓin kamar yadda ta yi ɗin nan, ko dai ma wani ki ke zargi a kai ne Mama ?. Ya faɗa ya na dariya. Mama ta ce "ok ai na yi tunanin ko ɗan baƙin halin can ne ya dake ta dan nasan halin shi kullum fuska a haɗe". Ma'aruf ya ce "kai Mama wai mai ya sa ki ke kiran mu da ɗan baƙin rai ne haba ni kam tafiya ma zanyi sai anjima?. Mama ta ce "au saboda da nace ɗan baƙin rai ne zai saka ka tafiya?. Tashi ya yi ya ce "Mama zan wuce sai mun haɗu a dainnin". Toh shi ke nan sai na sauko. Toh Mama sai anjima. Yana fita ɗakin Umma ya shiga a can ya tarar da su A'ishah A'ishah suka haɗa baki wajen kiran"Yaya ina wuni?. Amsawa masu ya yi ya ce " lafiya ƙalau A'ishah ina Umma ne"?. Ya tambaya. "Yaya ta na toilet ne cewar Ummi. Fatima sannu ko ansha kyau amma fita ba ta samu ba. Fatima ta ce "wallahi dai Yaya gashi saurayina ya ce zai zo anjima yaga wanka tun da ban fita ba kaga ko ai su Ummi suka yi asarar wankan su". Ta faɗa cike da shaƙiyanci. Shikam tuni ya ji kamar ta duka ma sa wani abun mai nauyin gaske cikin jarumta ya ce "to ashe yaran Umma sun girma har samari ne da ku kuna ƙananin nan". ya faɗa cikin nauyin murya. Ummi ta ce "Yaya wallahi ƙarya ta keyi Bama da samari". Idan ma suna da samarin mai za ka yi ne ehhe, maganar Umma suka ji aiko saurin ɗago kansa ya yi ya ce "Umma ina wuni"?. Umma ta ce "ban san in da ya ke ba tashi kabar ɗakin nan tunkan ranka ya ɓaci kazo ka takurawa yara". Laaaa Umma waye ya ce ya takura mana ne Umma. cewar Fatima. Fatima karɓi wannan zagin naki ne idan nasake magana kika ce ba haka bane sai na ɓataranki. Hakuri suka bata sannan suka kama hanyar zuwa part ɗin Mama. Mama ta ce "kai ma tashi kabani wuri ko ba za ka je masalaci bane ana kiran sallah ka wani kafe ni da idanuwa"?. Yi hakuri ban ji ba ne wallah bara nayi Alwala idan na je sallah kawai zanyi. A ina za ka yi Alwalar?. Umma a toilet ɗinki idan naje sallah kawai zanyi. Umma ta ce " wallahi ba ka isa ba ka je can ai akwai kayan alwala sai ka yi Alwalar a can". Ya ce "toh shi ke nan Umma sai anjima". Yana fita ya ci karo da su Rashid amma bai tsaya ba kawai ya yi tafiyar shi abin shi, tare suka isa masallacin dake ƙofar gidan su. Magarib suka idar amma ba su su ka ta shi ba sai da aka idar da isha'i Sannan su ka shiga gidan amma har lokacin Ma'aruf bai kula Rashid ɗin ba. A falo suka tarar da mutanen gidan saboda su ma sun idar da ta su sallar. Shaga falon su ka yi bakin su ɗauke da sallama "Assalamualaikum". Mutanen falon su ka amsa da ko "waalaikumussalam". Gai da iyayen nasu suka yi sannan su ka zauna. Ashe mutumen kan hankalin shi ya kar ka ta a wajen Ummi saboda shigarta ba ƙaramin kyau ta yi ba, riga da wando ne na Pakistan a jikinta. Ita ko jikinta ya ba ta cewa ana kallon ta ai ko ido huɗu suka yi haɗe fuska ya yi kamar ba shine ke kallon ta ba ya dallah ma ta harara, ka sa da kai kawai ta yi jikinta har rawa yake yi. Umma ta ce "Rashid ku tashi mu je dainnin kafin Ummi ta fara yiwa mutane ehun abinci ta ke so". Hahaha dariya su ka sa ka ma ta tako har da kukan ta wai su dai na ma ta da dariya. Mama ta ce " Rufa'i ko dai na ma ta da dariya ha ka ta isa". Ta shi suka yi su ka nufi dainnin zama kowa ya yi ku da masoyin shi amma ban da Ummi da Rashid. Wajen Umma taje ta zauna Umma tace ta sakawa kowa abinci aiko ha ka aka yi ta sa ka wa kowa tazo zuba ma sa ya ce "shi team za ta haɗa ma sa jikin ta na rawa ta haɗa ma sa team ɗin garin ta bashi kofin ya faɗi sai a jikinsa. Maruka masu kyau da tsada ya saukar ma ta a fuskarta, ha de fuska ya yi kamar bai taɓa dariya a duniya, kuka ta ke yi sosai saboda ba ƙaramin shigar ta marukan suka yi ba. Mama ta tashi dan ramawa Ummi sai Umma ta dafe ta Mama ta ce "sakar ni Maryam kina ganin wannan mari da ya saukar ma ta ba kice komai sannan yanzun za ki wani da fe ni"?. Haba Amina ki yi hakuri na ga ita ta zuba ma sa ruwan zafi a jiki meyasa idanuwan ki basu ga abin da ta yi ma sa ba sai na shi za ki gani kuma a gaban ƙannan sa za ki da ke shi ha ba Amina. Ma'aruf ya ce "wai kai kam Rashid meyasa bakada hankali ne jakin banza kawai mara hankali, toh wallahi duk ranar da ka sake dukan ta sai na rama ma ta saboda ba wani girma na kayi ba shekara 2 ne kawai kuma bazan ji ƙunyar ka ba wallahi. Umma ta ce "toh sannu uban shi ai kai ne jakin bashi ba saboda ko ba komai Rashid Yayanka ne kuma wallahi ko da wasa na ji an ce ka yiwa Rashid rashin kunya sai na saɓa ma ka". Ta shi Ma'aruf ya yi ya bar wajen saboda yaji haushin maganar Umma sosai . Haba Maryam menene ha ka ne yanzun ga shi kin sa ke ɓatawa wani rai akan mutum ɗaya ta shi Mama ta yi ta ji hanun Ummi su ka bar dainnin ɗin su ka yi shigewar su part ɗin Mama. Ka yi hakuri ka ji Rashid kar abin da ya fa ru ya ɓa ta ma ka rai ka ji ni Ko, "eh Umma" ya faɗa. Kwanciya kuwa ya yi saboda gobe ne mazan su za su dawo. Amma Ma'aruf ba a ɗakin su ya kwana ba a part ɗin Umma ya kwana cikin uwar ɗaka ya kwanta kar Umma ta ganshi dan yasan ba za ta ba ri ya kwanta ma ta a ɗaki ba. Rashid ba ya son fushin Ma'aruf ko ka ɗan saboda ko ba komai Ummar su na son shi kuma ba za ta ta ba su Ma'aruf gaskiya ba sai dai shi, ha ka ya kwanta ranshi cike da tambayoyin da ba mai amsa ma sa su. Rufa'i ma bai yiwa Rashid magana ba saboda haushin shi yake ji sosai saboda Ummi ƙanwar sa ce. Asuba ta gari. London Wa ta matashiyar mata ce sanye da baƙaƙen ka ya ta na waya da alama da wa ta ƙawarta ce ta ke waya ta can ɓangaren aka ce, "wai Balkisu ke shegiya ki na can ki na can ki na jin daɗi kin manta da abin da Boka ya ce kuma na ji ya ce za ki dawo Nigeria gobe ba shiri dan ha ka sai kin ba da bakar akuya a yanka saboda zafi-zafi ake dukan ƙarfe". Balkisu ta ce "kamar nawa ne zan bada saboda wallahi natsani Maryam da yaranta sannan kuma inason arabamin Rufa'i da shegen yaronnan na ta yanzun dai zan ba da dubu ɗari biyu na san dai za su yi ko"?. Hajara ta ce "toh sai dai an ji wajen boka shi zai faɗa idan sunyi kin san aikin ba ɗaya ba ne". Eh Hajara zan kira ki anjima yanzun tsohon banzan nan ya shigo zan kashe waya,ɗim ta yanke kiran. Balkisu ta ce "ka ce gobe za mu koma gida amma banga tikiti ba kuma ban ga tsaraban yarana ba mai ka ke nu fi ne toh"?. Abban Ma'aruf ɗin ya ce "ai na yi tunanin kin yiwa yarannaki tsaraba ne yanzun toh ki shirya mu je siyayyar ko". Balkisu ta ce "toh shi ke nan ni ma akwai abin da na ke son siyawa Maryam da Amina ni ma na kai mu su". Toh shi ke nan ga tikitin na siyo jirgin safe za mu bi. Toh kawai ta ce. Shiryawa ta yi amma kayan ne a jikinta fita suka yi, siyayyar mai yawan gaske su ka yi sannan su ka koma gida, ko wanka bata yi ba ta yi kwanciyar ta abin ta. Nigeria Kiraye kirayen sallah ne ya tashi ƴan gidan mazan su ka wuce masallaci matan ma sallah su ka yi, sannan yaran su ka koma bacci Umma ɓangaren ma su aiki ta je ta ce su gyara gidan da kyau saboda za su yi baƙi sannan ta ce ita za ta yi abinci da kan ta. Aiko Mama ita da Mama suka yi abincin farfesun naman kaza, dambu naman rago, Farfesun kayan cikin rago, da sauran su kai komai ma sha Allah. Bangaren ma su aikin ta sa ke komawa ta ce su je su bangaren Balkisu su gyara ma ta shi sosai ha ka kuwa akayi an gyara shi sosai da sosai. Bangaren Mama kuwa ha ka ne ita ma an gyara ɗakin ma sha Allah. Bangaren su Balkisu su ma sun shirya tsab za su airport jirgi safe su ka shiga sai gida Nigeria. Mama ta ce "Maryam yanzun sai yaushe yarannan za su yi hankali dan Allah kinji sunce idan su ka dawo ba su fitar da matar aure ba toh za su yi sadakar su ne amma gashi shiru". Uhmm wallahi yaranan ba sa ji ko kaɗan ai idan aka yi sadakar su za su huta ne ai.. ba ta ƙara sa maganar ba sakamakon wayar ta mai neman agaji. Ta ce "Assalamualaikum" Ta can ɓangaren aka amsa "waalaikimussalam" Barka da safiya Abban yara ko kun iso ne. Eh gamu a airport kicewa Ma'aruf yazo ya ɗauke mu har da Daddyn su gashi a airport ɗin mu ka tarar dashi. Laaaa har da Yaya kenan amma ko bai faɗawa Amina zai dawo ba saboda ga mu tare amma banji ta na maganar dawo War sa ba. Toh mu ma anan muka tarar da shi sai kicewa yaran suzo su ɗauke mu. Toh Abban yara zan kira Rashid ɗin. Ma'aruf ɗin fa. Am toh ai duk ɗaya ne ni dai sai ka gansu. Amina kinji wai har da Yaya ya na airport ɗin. Wane Yaya ɗin cewar Mama. Wane Yaya ne a gidan nan in ba mijinki ba. Uhmm kawai Mama ta ce. Rashid Umma takira tace suje su ɗauko Mahaifan su a airport su na jiranku. toh Umma kawai ya ce ya kashe wayar. Kiran Ma'aruf ya yi amma har wayar ta katse bai ɗauka ba sa ke kira ya yi nan ma shiru ba amsa. Bangaren Ma'aruf kuwa ya na ganin kiran amma yaƙi ɗagawa saboda haushen sa da ya ke ji. Kiran Rufa'i ya yi sannan ya faɗawa Rufa'i cewa su Daddy na airport ya zo su je ɗauko su. Shiryawa suka yi su ka nufi hanyar airport su ka ɗauko su sai gida. A hanyar ta zuwa gida Rashid ya ma su barka da fita jirgi lafiya. Shima Rufa'i barka da fita jirgi lafiya ya yi ma su. Sannan Rufa'i ya ce "Daddy munyi kewarku fa sosai wallahi". Abbah ya ce "au Daddyn ku kawai ku ka yi kewa ban da mu kenan?. Rufa'i ya ce "ai Abba har da kai da momy duk munyi kewarku sosai". Daddy ya ce "toh za ka haɗa kan ka da mahaifin su ne . Rashid ya ce "Daddy yaranka sun gagara su ganku fa saboda kullum tambayar ku suke yi. Momy ta ce "ayya ni ce kawai ba wanda yadamu da ni saboda ga shi Rufa'i ko kallo na bai ba. Wace irin magana ce wannan Balkisu ba sunyi mana barka da fita jirgi lafiya ba, ba yanshi mai ki ke son su yi ma ki ehhe. Allah yabaka hakuri Abban Ma'aruf. RASHIDA By Sha'awanatu faruk diggi✍️✍️ Wtspp 08084277827☎️📱 Saƙon miƙa gaisuwa ga sister's Ina miƙa gaisuwa ga aunty Saratu Ina miƙa gaisuwa ga sister Shamsiyya Ina miƙa gaisuwa ga bro Abubakar Ina miƙa gaisuwa ga ƙawata Firdausi Ina miƙa gaisuwa ga ƙawata Rashida Ina miƙa gaisuwa ga sister Yasira Ina miƙa gaisuwa ga ƴata Salma Ina miƙa gaisuwa ga my son hafeez Ina miƙa gaisuwa ga duk kannin musulmi Allah ya barmu tare da masoyan mu ameen ya Allah. 3 📝 Da haka dai har su ka isa gida, su na shiga gidan su ka tarar da mutanen gidan har da Kaka, ran da Ummi ta ga sun sa ka hancin motar cikin gida ta sheƙo a guje ta budewa Daddy ƙofa, ya na fitowa ta ɗale shi ta na ehun ganin su shima rungume ta ya yi sosai ya sakar ma ta kiss a goshi ya ce "innan Daddy har yanzun ba ki girma ba ko"?. Hahaha dariya ta yi sannan ta ce "ai Daddy ni yarinya ce ga su aunty A'ishah da aunty Fatima can gefe da ya ke su sun girma", ta na maganar ne cikin shagwaɓa da ita ma ba ta san da ta na da ita ba . Rashid ga ba ki ɗaya hankalin shi ya koma kan Ummi dan shagwaɓar ba ƙaramin kyau ta ƙara ma ta ba, ya na nan ya na tunani ji kawai ya yi an mangare ma sa kai da sauri ya dawo hayyacin shi, Kaka ya gani ba kowa har su Rufa'i sun tafi su ka barshi. Kaka ta ce "ashe Bokan turai ka na nan amma ba mai laiƙani saboda Allah daga kai har su Ma'arufa ba mai laiƙani". (Ma'aruf ta ke nu fi). Ya ce "kai Kaka surutun ki ya yi yawa kin cika min kunne da surutu toh yanzun dai yaranki su zo ai sai kije Ku zanta ko". Tafiyar shi ya yi ya barta a nan sa ke da baki. Falon ya shiga ya ƙara gaida iyayen nasu sannan ya zauna a kasan ƙafafun Abba. Abba ya ce "inna ina wuni mun sa me ki lafiya"?. Inna ta ce "lafiya ƙalau Iro barkanku da fita jirgi lafiya". Yauwa barka dai Inna cewar Daddy. Ummi ta ce Abba mu je dainnin ko dan ni kam yunwa nake ji. Umma ta ce "ba in da zashi sai sun yi wanka tukunna sannan ai maganar cin abinci", sannan Balkisu ki je ki yi wanka ke ma ki zo mu ci abinci. Balkisu ta ce "uhmm ni ai sai na gyara ɗaki na dan nasan ba gyara min aka yi ba". Mama ta ce "haba Balkisu ya za'ayi ace kuna ta fe mu ƙi gyara maki ɗakin dan Allah kiriƙa tauna magana kamin ki fitar da ita ". Balkisu ta ce "atoh ni kam nasani dan naga ba a murnar dawo wa ta". Abba ya ce "wai Balkisu mai yasa ke kullum fitina ce kawai ke ma ki daɗi yanzun yaushe rabon da mu yi zama da yaran mu da sauran ƴan uwanki yanzun gashi mun samu dama kina shirin warga za ta haba dan Allah ". Abban yara ki yi hakuri dan Allah mu je ka yi wanka sai ku ci abinci, Ummi ku je ra mana abincin a dainnin ɗin. Ƙin tashi ya yi hanu ta sa ta kama hannun shi kamar yaro su ka shiga ciki . Ummi ta ce "Umma mu na nan fa ko kin manta ne"?. Mama ta ce "kai Ummi kin cika sa ido", fa ta na maganar ta na dariya saboda ita abin ya ba ta dariya. Mama ta ce "Daddyn yara ta shi mu je ka yi wankan kai ma ko sai na goya ka ne". Hahaha su Ma'aruf su ka sa ka dariya. Rufa'i ya ce "kai Mama mu ma Allah yabamu matan da za su yi mana ha ka dan naga ko ƙunyar mu Umma ba ta ji ba kema Mama ha ka". Abba ya ce "ku na nufin ba ko tsaida matan aure ba shi ke nan zan ba da ku sadaka ga mai bukata ". Ma'aruf ya ce "haba Daddy ka san mu yara ne har yanzun ba mu san dai-dai ba da ba dai-dai ba saboda yara ne mu dan Allah ku yi hakuri Daddy har mu girma Please". Mama ta ce "ai ba ku isa auran ba amma ku ka san Allah ya ba ku matan aure irin mu". Dariya su Ummi ke yi sosai . Fatima ta ce " Mama jiya fa Yaya Ma'aruf cewa ya yi shi kam aure ya ke so dan Allah na bashi ƙawata Ihsan". Ma'aruf ya ce "wallahi Mama ba gaskiya bane ina ma naga ƙawar ta da zance inaso". Dariya su ka sa ka sosai har da Rashid sai da ya dara. Mama ta ce "Daddyn yara ta shi muje tun kan su fito". Ta shi ya yi su ka yi shigewar su ɗakin Mama. Ma'aruf ya ce 'ke Fatima ni za ki wa sharri a gun Daddy saboda ki na son a yi sadaka na ko". Fatima ta ce "haba Yaya ai wasa ce na ke yi ai ni nafi da son ka sama mana aunty Mai kyau da hankali". Rufa'i ya ce "ka san mai za ka yi ka rama abokina"?. Ma'aruf ya ce "a a sai ka faɗa". Rufa'i ya ce "ka cewa Daddy ai Fatima ta ce ta na sonka kuma kai za ta aura idan babu kai ba za ta iya rayuwa ba", nan ta ke Daddy zai yi amanna da ha ka shi ke nan ka rama abin da ta yi ma ka. Yaya dan Allah ka yi hakuri wallahi ba zan sa ke ba yau idan ka faɗi maganar nan ai nasan ba zanyi sati a gidan nan ba dan Allah ka yi hakuri na rantse da Allah ba zan sa ke ba. Cewar Fatima kamar za ta yi kuka. Dariya su Ummi su ka sa ka ma ta Ummi kam kan dariya har hawaye ta ke yi. Ma'aruf da Rufa'i ma dariya su ke ma ta sosai shima Rashid ɗin ya na murmusawa sakamakon dariyar da Ummi ke yi. Balkisu ta na shiga ɗakin ta tarar da shi fes-fes-fes kiran Hajara ta yi a waya ta ce ma ta "sun iso a Nigeria yanzun ha ka ta na gida ". Hajara ta ce "toh shi ke nan sai na zo zan faɗa ma ki abin da Boka ya ce". Toh ta ce "sai kin zo ɗin ina jiran ki fa Hajara " yanke wayar ta yi. Wanka ta yi ta canza kaya sannan ta fito falo ta tarar da su Ummi sai dariya su ke yi. Ummi ta ce "kai ma Yaya Rufa'i sai mu ce kai ka ce ka na son A'ishah shi ke nan mu kam musha shagali a gidan nan wallahi". Rufa'i ya ce "ai da A'ishah za ta kashe ni wallahi wannan ƴar Bala'in zan aura. Su ka suka dariya har da Rashid. Momy ta ce "yau nishaɗi kawai ku ke yi toh na ji kamai kai Ma'aruf zance kai ka ce ka na son Fatima, kai ma Rufa'i ka ce ka na son A'ishah, kai ma Rashid ka ce ka na son Ummi duk ku bari Abban ku yazo sai na faɗa ma su". Rashid ya ji gaban shi ya ba da tim, sai da ya dan rufe idanunshi kaɗan kamin ya biɗe a kan Ummi. Ummi ta ji kamar Momy ta zuba ma ta ruwan zafi ta ce "Momy dan Allah ki yi hakuri wallahi ba ha ka ba ne kawai mu na faɗa ne amma ba gaskiya ba ne dan Allah". ta na maganar ta na hawaye. Momy ta ce a zuciyar ta dole tun da ta ga Ummi ba ta son ana haɗa ta da Rashid dole ne ita za ta yi shiga da fice sai an ɗaura auren Ummi da Rashid duk a zuciyar ta ke zan cen nan. A fili ta ce "mai ya sa ki ke kuka ne Ƴarinyata ai basai kinyi min a sarar hawayen nan na ki ma su daraja ba kawai faɗa na ke yi amma bazan faɗawa Abban ku ba kinji ƴata hankalin ya kwanta, Fatima kawo min ruwan sanyi ta sha ko ranta zai yi sanyi. Fatima ruwa ta kawowa Ummi tasha sannan hankalin ta ya dawo kan ta. Su Umma su ka fito, ba su jima ba su Mama su ka fito Umma ta ce "su je dainnin Ummi wajen tsakanin Abba da Daddy ta kai kujeran ta ta zauna. Umma ta ce "Ummi sa ka wa kowa abincin", Abba ya ce "ba za ta sakawa kowa ba sai dai kar su ci", haka Umma ta tashi zuwa sakawa kowa abinci. FARKON LABARIN Wani dan karamin ƙauye ne mai suna gada a jahar sokoto. Wata mata ce mai kimanin shekaru 24 ta na aiki a tsakar gida. Wata mata ce mai kimanin shekaru 55 tana aikin masifa ta ce "ke Rashida wai wannan abin aikine ki ke yi haka a bu kamar ba ki da jini a jiki tun da ki ka ki haihuwa toh wallahi aiki yanzun ki ka fara". Iya dan Allah ki yi hakuri bana son musu da ke saboda ke mahaifiyata ce amma kin san da rai da mutuwa da haihuwa duk suna ga Allah Yee-yee kuka Iya ta saka tana cewa Rashida yau ni ki ke zagi lallai yau kin tabbatar min cewa ke ba tagari bace saboda ko uwar ki ba ki bari bale ni uwar miji tana maganar ne tana kuka sosai har da fece majina. Rashida ta ce "haba Iya yaushe na zageki wallahi ban zage ki ba dan Allah ki yi hakuri ". tana maganar ne tana kuka ita ma. Wani matashi ne ya shigo ɗauke da sallama a bakin sa "Assalamualaikum" Iya Mai yasamai ki ne ehhe, Rashida Mai yasami Iya ne naga tana kuka"?. Ai dole za ka tambayi uwarka tun da ni kam banza ce ba ni na haife ka ba kuma ka sa ni wallahi na gaji zama da wannan juyar dole ka zaɓa ko ni ko ita. Ita dai Rashida kuka kawai take yi saboda da mutum ba shi ba kan shi cikin da sai ta bawa kanta. Ya ce "Iya dan Allah ki yi hakuri ki bani ɗan lokaci in sha Allahu za ki ga jikan ki amma dan Allah ki yi hakuri yanzun wallahi bazan iyawa Rashida kishiya ba saboda ina son ta sosai". Toh ni za ka faɗawa cewa kana sonta lallai Mustapha dole za ka yi min yan da ta ke so. Ita dai Rashida kuka kawai take yi da taga abin yaƙici yaƙican yewa ya sa ta bar wajen da gudu ta na kuka. Mustapha dai gabaki ɗaya hankalin shi ya tashi saboda ya na son Rashida sosai. Bin Rashida ya yi ɗaki ya na ba ta hakuri ya ce "Rashida dan Allah ki yi hakuri wallahi Ni ma na gaji da wannan abin da Iya ke yi ma ki kuma nasan bakya jin daɗi amma ha ka za ki yi hakuri dan Allah". RASHIDA By Sha'awanatu faruk diggi✍️ Sha'awa marubuciya✍️ Wtspp 08084277827☎️📱 PART 4 📝 Amma fa cewa ta yi dole cikin mu ka zaɓi ɗaya ko ita ko ni yanzun dan Allah saboda ban sa mu haihuwa da wuri ba ne za ta tsane ni har ha ka, ai ba ni ke ba wa kai na kuma shirun da haihuwa ta yi min ba shi zai sa Allah ya manta da ni ba Kum.... Kuka ya ci ƙarfin ta ya sa ba ta ƙarasa maganar ba. Nisawa Mustapha ya yi ya ce "ni dai ba zan gaji wajen ba ki hakuri kuma da ki ke maganar cewa wai na zaɓa wallahi bazan sake ki ba saboda ina son ki sosai dan Allah Rashida ki dai na sa ka damuwa a ranki. Toh shi ke nan ba na son yin musu da kai mijina ka yi hakuri na dai na amma dan Allah idan ta buƙaci ka sake ni dan Allah kar ka yi ya yayya da ita saboda ba na son fushin iyayye akan mijina. Hahaha toh shi ke nan amma fa ba na fata ki ka san ko na yi ajiya a cikin cikin nan na ki. Hahaha dariya ta yi sosai sannan ta ce "toh Allah ya sa da gaske ne mijina, mijina ina son ka ina ƙaunar ka." Matata ina son ki ina kaunar ki ina ma ki son da idan Iya ta matsa rabuwa na ta ke toh wallahi za ta yi biyu babu bu. Rufe ma sa baki ta yi sannan ta ce " haba mijina mai ya sa ka ke faɗan wannan maganar dan Allah ka dai na in sha Allah a tare zamu yi rayuwa har lokacin da Allah zai bamu yara". Rungume ta ya yi sosai a jikin shi ya ce "ina son ki matata" ai da ga nan na fito na bar ma su dakin saboda um a bar shi kawai. A kwana a tashi a sarar mai rai yau Rashida ta shi da matsanancin ciwon ciki abu kaɗan ta ci sai amai, Mustapha ya ga ciwon ya yi yawa ya ɗauke ta zuwa ɗan ƙaramin asibiti likita ya yi yawan da ya ke yi ya ce idan za ta iya tashi ta je ta yo fitsari ya bata ƴar ruba ya ce ciki zata yi fitsarin ta je tayo ta ba shi ya yi awon da ya ke yi ya ce "ta na da aure ne"?. Mustapha ya ce " eh". Likitan ya ce "ina mijinta"?. Mustapha ya ce "likita ga ni ko wa ni abun ne ke damun ta saboda wallahi ta ji jiki sosai dan Allah kar ka ce min ta na da matsala ne likita". Likitan ya ce "kwantar da hankalin ka abokina ba abin da ke damun matar ka ta na nan lafiya, congratulations abokina matar ka na dauke da cikin wata biyu. Mustapha ya ce "mai ka ce likita ban ji da kyau ba dan Allah ka sa ke faɗa min wallahi kunne na wani abun ya ji da ban"?. Hahaha dariya likitan ya yi ya ce "abokina na ce matar ka na ɗauke da juna biyu na wata biyu". Mustapha sujada ya yi ya na wa Allah godiya, sannan ya ce "likita da mai zan saka maka wallahi da mai kuɗi na ke ta yau zaka sha kyauta ta musamman saboda wannan albishir ɗin da kai min". Likitan ya ce "akwai abin da za ka bani amatsayin tukuici". Mustapha ya ce "likita kafaɗa min menene shi har in baifi ƙarfi na ba zan ba ka shi in sha Allah". Likitan ya ce "abota kawai nake son mu yi idan ka amince saboda wallahi kabirge ni sosai ina son namiji mai irin halayyar ka". Mustapha ya ce "yau kam tazo min a Sa'a Allah na gode maka da wannan alkairin da ka ke nuna min, na amince in sha Allah ba zanci amanar ka ba sai dai idan kai kaci tawa amanar". Likitan ya ce "abokina na gode sosai nima saboda wannan abin da kace min yasa na ƙara jinka a rai na, Allah yabawa matar ka lafiya Allah ya sauke ta lafiya abokina". Tashi ya yi likitan ya ce mu je na raka ka saboda bana son iska ya ta ɓaka, hahaha dariya su ka gabaki ɗaya. Barin asibitin su ka yi sai gida su na shiga Iya ta tasu su da bala'i sunje sunyi zamansu a can. Rashida ta je wucewa ɗaki sai Iya ta riƙe ma ta hijab ta ce "ai daga nan gidan ubanki za ki koma dan nagaji da wahalar min yaro da ki ke yi ". Mustapha ya ce "Iya ba dai haihuwa ce matsalar ba toh shi ke nan tazo ƙarshe in sha Allah, yanzun daga asibiti muke kuma sunce ta na ɗauke da cikin wata biyu". Ciki fa kace Mustapha Rashidar ce mai ɗauke da cikin ko aure ka yi ban sa ni ba?. Iya Rashidar dai ce mai ɗauke da cikin yanzun kam ai sai ki nuna ma ta soyayyar da ba ta samu ba tun da. Allah sarki Rashida ƴar albarka Allah ya maki albarka Allah ya rabaki lafiya dan darajar Annabi Muhammad s a w ameen ya Allah. Ameen ya Allahu Iya cewar Mustapha. Iya ta ce "ƴata sannu kin ji mai zan dafa maki yanzun eh dan nasan ki na buƙatar wani abun ta ɓawa"? Iya ba komai Na gode sosai yanzun ba na jin yunwa bacci daina ke ji. Toh shi ke nan ƴata ki je ki kwanta ai nasan kina bukatar hutawa. Iya toh yanzun ya maganar ƙara auren kisama min mata kawai . Iya ta ce "Mustapha ai yanzun kam ba zancen ƙara auren dama jikokina na ke son ga ni shi ya sa wallahi nace sai ka yi aure amma yanzun kam ba wannan zancen". Toh shi ke nan bara na shiga ciki sai na fito. Ɗakin ya shiga ya tarar da Rashida na riƙe da cikin ta tana kuka. Ya ce "Rashida lafiya daina ga ki na kuka ko wani abun ya faru dan Allah ki faɗa min"? Cikin kukan ta ce "ba komai mijina kawai ina tunanin maganar Iya ne kenan idan ba wannan cikin ba yau rabamu za ta yi". Haba Rashida kawai Iya na faɗa ne ba gaskiya bane ki dai na wannan tunanin ba mai rabamu in sha Allah mu na ta re da ke har abada. "Allah ya nufa". A kwana a tashi sai yaro ya za ma babba . Rashida na ga ni da ƙatan cikin ta sai wa ni ni shi take yi da alama na ƙuda ce tazo ma ta ta ce "Iya Iya ki na ina cikina zai zube". Iya taji ehun ya yi yawa taje ta leƙa sai taga Rashida a yashe a kasa. Ta ce "Rashida Meya same ki ne ha ka ko naƙudan ce"? tazo aiko ta taimakon Iya ta haihu ɗanta namiji murna wajen Iya ba a magana. Ruwan wankan mai jego Iya ta haɗawa Rashida taje ta yi wanka sannan ta zauna, Iya ta ce "ƙarfe shi ki bashi madarar shi yasha". Rashida ta ce "Iya kibari har Mustapha ya zo sai na bashi madarar dan Allah Iya". Iya ta ce "yau ni naga ta kaina toh idan yazo shine zai bawa jaririn mamarshi ne". Haka ba dan tasu ba tabawa yaron madarar shi, tana cikin bashi madarar sai ga Mustapha ya ce "Rashida kice kuwa nake gani da jariri a hanu?. Iya ta ce "eh itace ko da wani abun ne"?. A a kawai na tambaya ne ya ce "Iya dan Allah ruwa nakeso zan bawa yaron wani abun ne". Toh shi ke nan bara na ibu ruwan ta na fita ya zauna a kusa da Rashida ya ce "wai yanzun ni ne na zama uba amma kamar a mafarki". Ruwa Iya ta kawo ya ce ai ya gama abin da zai yi . SATI ƊAYA Yau ne ranar suna yaro yaci sunan Muhammad. Haka dai rayuwa ta ci ga ba da gudana . Rashida na gani da wani ƙatun cikin ta ta na zaune baƙin murhu ta na hura wuta. Wani yaro ne ɗan kimanin shekaru 4 ya ce "Inna banga jaka ta ba kuma a makaranta dukan litti a ke yi"?. Rashida ta ce "toh ni kam ina nasan in da ka yada jakar ka yaron nan kawai ka duba a cikin jakar mahaifin ka". Dubawa ya yi sai ko ya ganta ya ɗauka sai makaranta. Ya na fita ita ko Rashida naƙudar ta tashi da kyar ta samu ta shiga ɗaki ta na shiga ta na haihu ɗanta namiji, Iya ta kira ko da Iya ke shaga ɗaki ta tarar da jariri, aiko daɗi har kunne. Waje taje ta ce akira ma ta Mustapha yana shigowa Iya ta ce bani abin da za ka bani na faɗin haihuwa dan matar ka ta haihu ɗa namiji.. Kamin Iya ta rufe baki har ya shige ɗaki. BAYAN SATI Ɗa yaci sunan Ibrahim an sha shagali sosai Mustapha ya faɗawa likita haihuwar matar shi dan ha ka likita yazo suna . BAYAN SHEKARU 5 Bayan shekara 5 wasu yara ne nagani sun dawo daga school ɗayan ba zai wuce shekara 9 ba, ɗayan ma bazai wuce shekara 5 da rabi ba mai shekaru 9 ne riƙe da mai shekaru 5 su na tafiya hankali ƙwance gwanin birgewa. Wa ni ƙaramin gida na ga sun shiga wata mata ce tsugunne ta na fama da wuta su ka "Assalamualaikum" Inna sannu da gida su ka cewa matar ɗago kan da zata yi sai naga Rashida na ce toh su Rashida manya . Ta ce "a a ƴan makaranta har kun dawo"?. Su ka "ce mata eh Inna". Rashida ta ce "Ibrahim nawa ya hanya Allah ya sa dai malaman ku ba su dake ka ba"?. "Eh Inna" ya ce Rashida ta ce "kai yaron nan ku je ku cire kayan sai ku zo ga abincin ku". Toh wai ina Iya ne. Mustapha ya shigo bakin sa ɗauke da sallama "Assalamualaikum". "Waalaikamussalam" ta amsa ma sa ta ce "sannu da zuwa malam" saboda yanzun karantas suwa ya ke yi. Yauwa barka da gida kawai ya ce ya yi tafiyar shi. Bin shi ta yi a ɗakin ta ce "malam lafiya na ganka ha ka dan Allah ka yi hakuri Allah yabamu ita kuma shi ya amshi abarsa". Ni sawa ya yi ya ce "wallahi Rashida ba ki san yadda mutuwar Iya ta tsaya min a rai ba saboda itace kawai na ke kalla na ji daɗi". Ayya Allah sarki Iya Allah ya gafarta mata ni daina ce. BAYAN SHEKARU 7 wa ta ƴar tsohowa na gani kwance da alama ba tada lafiya wata yarinya na a kusa da ita yarinyar ta ce "Inna wai ina su Yaya suka yi ne har yanzun basu dawo ba kuma yunwa nake ji"?. Wacce aka kira da Inna ta ce "A'ishah ki yi hakuri zasu dawo in sha Allah kuma za su sama ma ku abincin da zaku ci kinji". "Assalamualaikum". "Waalaikamussalam" ƴar tsohowar ta faɗa Babban cikin ƴan samarin ya ce "Inna ya jikin"?. Sannan ƙaramin ya ce "Inna kin ji sauƙi"?. Ta ce "eh naji sauƙi sosai sai dai abin da ba a rasa ba". Inna dan Allah ki fitar da mutuwar nan ta Baba a ranki yau fa shekara 2 amma kullum sai ki yi kuka ga shi ke ba lafiya ba. Cewar babban. Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba. A a Inna mun samu abinci ga shi kwano ɗaya ne dai ba yawa. Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi ma ku albarka Allah yabaku sana'a mai albarka". Muhammad ya ce "Inna mai zai ha na ki bari naje Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah". Humm me yasa ka ce kar na hana ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne. Ƙaramin saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen waharmu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi yatafi ai Inna ina tare da ke". Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne. Eh to Inna duk ranar da ki ka ce tayi maki ni Ashirye nake. Toh shi ke nan sai na gani sai na faɗa maka kuma Kanada kuɗin tafiya ne. Mustapha ya ce "a a Inna amma ai ba zasu yi wuya ba saboda akwai wata ƴar wahala wai sona take sai nace ma ta tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuɗin mota". A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi nasan kuɗin zasu yi ma ka . Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci . Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a . Ameen ya rabbin alamina. BAYAN SHEKARA 2 Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe zamu koma birni dan naji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can zamu koma da zama"?. A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko bakya son ya yi aure. Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shine ya ce min wai can zamu koma da zama?. A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali. "Assalamualaikum" a a Inna kina nan da ƴar ki ko?. "Waalaikamussalam" Toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni". A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuɗin maganar ya yi ne kuma kin san ƙurota zasu yi. Haka ne kam toh Allah ya sanya alkairin amma ka ji Yayanka yau kuwa. Eh Inna ya na ma shigowa gobe in sha Allah. Yeeeee Yaya na birni zai zo Allah ya sa ya siyo min abin daɗi birni. Kai kedai bakya barin shirme toh Allah ya kawo shi lafiya. Ameen kawai ya ce. A Kano Muhammad gadi ya ke a wani babban gida duk wata ana biyan shi dubu 20 goma ya kai gida goma kuma yaba da ajiya ga ƴar mai gidan, har yasa mu kuɗi masu yawa ya siya siminti da yashi har da fili, budurwar san ye da atamfa ta ce "Yaya ga abincin ka". Muhammad ya ce "Toh Hajiya na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi Allah ya ba ki miji na gari Hajiya". Ta ce "Ameen Yaya amma ai Allah ya bani sai dai idan shine ya ce ba ya sona". Ta ce "Ah Alhamdulillahi ce har kin samu amma ba wanda yazo gidan nan dan banga wanda ya taɓa zuwa ya ce akira ma sa ke ba sai dai auntyn ki". Ta ce "Yaya kaine ina son ka ina ƙaunar dan Allah karka ce ba ka sona wallahi zan iya cutuwa". Amma Hajiya ai ke ba sa'ata ba ce saboda ni talaka ne sosai kuma banada karatu mai zurfi dan Allah ki yi hakuri amma bazan iya ba Hajiya. Ta ce toh shi ke nan idan na mutu dan Allah ka min wannan alfarmar kazo kan gawata ka ce kana so na ko zan ji salama. Ya ce "Haba Amina dan Allah ki dai na wannan maganar ba da amfani ga". Da gudu ta bar wajen sai ɗakinta kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Mamartace ta ce "Amina me yasa meki ne naga kin shigo ki na kuka kifaɗa min mana"?. Mama Yaya ya ce ba ya sona wallahi Mama idan ban aure shi ba, ba zan rayu ba dan wallahi guba zan sha na mutu kuwa ya huta cikin kuka ta ke wannan maganar. Mama ta ce "Yanzun saboda Muhammad mai gadi ki ke wannan uban kukan ki kwantar da hankali in sha Allah Muhammad bai da mata sai ke kema bakyada miji sai Muhammad kin ji ƴata". Amina ta ce "Mama kimin alƙawarin cewa Muhammad zai auran"?. Mama ta ce "Na yi maki alƙawarin Muhammad na ki ne kibari mahaifin ki yazo sai na faɗa ma sa". Ta shi ta yi taga toilet ta ɗauro alwala tazo ta yi nafila raka'a biyu dan neman samu masoyan ta. Shi ko Muhammad Ibrahim ya kira ya ce "Ibrahim ina cikin damuwa". Ibrahim ya ce"Yaya meke faruwa ne"?. Muhammad ya ce "Wallahi yarinyar gidan ce wai ta ce tana sona ni kuma gaskiya banada lokacin aure yanzun saboda su nake na gina gida harda kai da yaran da zamu haifa nan gaba, amma yanzun duk shirina zai lallace ne kuma wallahi yarinyar ta ce zata kashe kanta idan ban amince ba ya zan yi Ibrahim"?. Ibrahim ya ce "Yaya ka amince kawai har in kana sonta saboda buri baya cika sai an shawuya dan Allah ka amince kawai". Ibrahim idan na ce maka bana sonta toh wallahi nayi ma ƙarya ina sonta dan yarinyar mutum niyar kirki ce. Toh shi ke nan ka amince kawai mukam musha shagali abin mu kaga A'ishah kullum kwaɗayin komawa birni ta ke Inna ta ce ba Inna da zata sai ka yi aure tukuna. Toh shi ke nan Allah yazaɓa abin da yafi Zama alkairin. Ameen ya Allah cewar Ibrahim. Yanke wayar ya yi sakamakon hon ɗin da akeyi. Get ya buɗe mai gidan ne shiga ya yi shima ya rufe gidan. Ya ce "Alhaji Barka da shigowa". Alhaji ya ce " Yauwa barka da gida Muhammad". Gida ya shiga ya tarar da Amina a falo ya ce "Mamana lafiya daina ganki ke ɗaya", shiru ya ke ji hakan ya sashi zuwa kan kujerar ya zauna ya ta ɓa ta sannan ta dawo hayyacin ta. Ta ce "Alhaji Barka da zuwa". Ya ce "Amina meke damunki ne tun ɗazun nake kan ki ina maki magana amma shiru". Laa Alhaji ba komai kawai bana jin daɗi ne. Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya?. Lafiya ƙalau Maman Amina . Mu je kayi wanka sannan ka ci abinci sai mu yi maganar. Wace irin magana ce wannan?. Magana ce akan Amina . Amina kuma kizo ki zauna sai mu yi maganar kawai nayi wanka daga baya. Haba Alhaji kaj.., bai bari ta ƙarasa ba ya ce "Ina jin ki faɗa min menene ke damunta"?. Alhaji wai yarinyar nan ta rasa wa zataso sai Muhammad mai gadi. Muhammad mai gadi kuma?. Eh shi dai har guba ta ce zata sha in da ba a aura mata shiba sai da na ce mata na yi ma ta alƙawarin aura ma ta shi. Ai wannan abin farin ciki ne Hadiza saboda wallahi yaron na da hankali da nutsuwa nima na kwaɗayi ba shi Aminar sai dai nayi tunanin ko ba za ta amince ba. Toh ai shi ke nan yazo gidan sauƙi kiran min ita Amina, Amina "na'am" Mama zo in ji Alhaji. "Alhaji gani". Kiramin Muhammad. Alhaji ka aiki Mama ta kira maka shi dan Allah. Ya ce "Amina na ce ki kira min Muhammad". Toh kawai ta ce sannan ta tafi kiran shi. Ta ce "wai kazo in ji Alhaji". Ya ce "yau ba ko Yaya kawai kazo in ji Alhaji". Toh kai Yayana ne da zanci gaba da kiran ka da Yaya aikin banza kawai. Tafiyar ta ta yi shi ko bayanta yabi dan jin kiran da Alhaji ke yi ma sa. RASHIDA By SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️ Sha'awa marubuciya ✍️ WhatsApp number 08084277827☎️ PAGE NA BIYAR 5 📝 Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba. A a Inna mun samu abinci ga shi kwano ɗaya ne dai ba yawa. Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi maku albarka Allah yaba ku sana'a mai albarka." Muhammad ya ce "Inna me zai ha na ki bari na je Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah." "Humm me yasa ka ce kar na ha na ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne." Ƙara min saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen wahar mu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi ya tafi ai Inna ina tare da ke." "Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne. Eh to Inna duk ranar da ki ka ce ta yi maki ni a shirye nake." "Toh shi ke nan sai na gani, sai na faɗa maka, kuma Kana ma da kuɗin tafiyar ne." Mustapha ya ce "A a Inna amma ai ba za su yi wuya ba saboda akwai wata ƴar wahala wai su na take, sai nace mata tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuɗin mota." A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi na san kuɗin zasu yi ma ka . Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci . Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a . Ameen ya rabbin alamina. BAYAN SHEKARA 2 Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe za mu koma birni dan na ji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can za mu koma da zama?." "A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko ba kya son ya yi aure." "Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shi ne ya ce min wai can za mu koma da zama?." "A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali." "Assalamualaikum a a Inna kina nan da ƴar ki ko?." "Waalaikamussalam toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni." "A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuɗin makarantar ya yi ne kuma kin san kurota zasu yi. "Haka ne kam toh Allah ya sanya alkairin amma ka ji Yayanka yau kuwa." "Eh Inna ya na ma shigowa gobe in sha Allah." "Yeeeee Yaya na birni zai zo Allah ya sa ya siyo min abin daɗi birni." "Kai ke dai ba kya barin shirme toh Allah ya kawo shi lafiya." "Ameen kawai ya ce." A Kano Muhammad gadi ya ke a wani babban gida duk wata ana biyan shi dubu 20 goma ya kai gida goma kuma yaba da ajiya ga ƴar mai gidan, har ya sa mu kuɗi ma su yawa ya siya siminti da yashi har da fili, budurwar san ye da atamfa ta ce "Yaya ga abincin ka." Muhammad ya ce "Toh Hajiya na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi Allah ya ba ki miji na gari Hajiya." Ta ce "Ameen Yaya amma ai Allah ya bani sai dai idan shine ya ce ba ya sona". Ya ce "Ah Alhamdulillahi ki ce har kin samu amma ba wanda yazo gidan nan dan ban ga wanda yata ɓazuwa ya ce akira ma sa ke ba sai dai auntyn ki." Ta ce "Yaya kai ne ina son ka ina ƙaunar dan Allah karka ce ba ka sona wallahi zan iya cutuwa." Amma Hajiya ai ke ba sa'ata ba ce saboda ni talaka ne sosai kuma bana da karatu mai zurfi dan Allah ki yi hakuri amma bazan iya ba Hajiya. Ta ce "Toh shi ke nan idan na mutu dan Allah ka min wannan alfarmar kazo kan gawata ka ce kana so na ko zan ji salama." Ya ce "Haba Amina dan Allah ki dai na wannan maganar ba ta da amfani ga." Da gudu ta bar wajen sai ɗakinta kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Mamar ta ce, ta ce "Amina me yasa meki ne naga kin shigo ki na kuka ki faɗa min mana?." "Mama Yaya ya ce ba ya sona wallahi Mama idan ban aure shi ba bazan rayu ba dan wallahi guba zan sha na mutu kuwa ya huta cikin kuka ta ke wannan maganar." Mama ta ce "Yanzun saboda Muhammad mai gadi ki ke wannan uban kukan ki kwantar da hankali in sha Allah Muhammad bai da mata sai ke kema ba kya da miji sai Muhammad kin ji ƴata." Amina ta ce "Mama kimin alƙawarin cewa Muhammad zai auran?." Mama ta ce "Na yi maki alƙawarin Muhammad na ki ne kibari mahaifin ki yazo sai na faɗa ma sa." Ta shi ta yi tashi ga toilet ta ɗauro alwala tazo na yi nafila raka'a biyu dan neman samu masoyan ta. Shi ko Muhammad Ibrahim ya kira ya ce "Ibrahim ina cikin damuwa." Ibrahim ya ce"Yaya meke faruwa ne?." Muhammad ya ce "Wallahi yarinyar gidan ce wai ta na sona ni kuma, gaskiya bana da lokacin aure yanzun saboda so nake na gina gida harda kai, da yaran da za mu haifa nan gaba, amma yanzun duk shirina zai lallace ne ku ma wallahi yarinyar ta ce za ta kashe kanta idan ban amince ba ya zan yi Ibrahim?." Ibrahim ya ce "Yaya ka amince kawai har in kana son ta saboda buri ba ya cika sai an shawuya dan Allah ka amince kawai." "Ibrahim idan na ce maka bana son ta toh wallahi na yi ma ƙarya ina son ta dan yarinyar mutum niyar kirki ce." "Toh shi ke nan ka amince kawai mu kam musha shagali abin mu, kaga A'ishah kullum kwaɗa yin koma wa birni ta ke Inna ta ce ba Inna da za ta sai ka yi aure tukuna." "Toh shi ke nan Allah yaza ɓa abin da yafi Zama alkairin. Ameen ya Allah cewar Ibrahim. Yanke wayar ya yi sakamakon hon ɗin da a ke yi." Get ya buɗe mai gidan ne shiga ya yi shi ma ya rufe gidan. Ya ce "Alhaji Barka da shigowa". Alhaji ya ce " yauwa barka da gida Muhammad". Gida ya shiga ya tarar da Amina a falo ya ce "Mamana lafiya daina ganki ke ɗaya", shiru ya ke ji hakan ya sa shi zuwa kan kujerar ya zauna ya ta ɓa ta sannan ta dawo hayyacin ta. Ta ce "Alhaji Barka da zuwa." Ya ce "Amina me ke damunki ne tun ɗazun nake kan ki ina maki magana amma shiru." "Laa Alhaji ba komai kawai bana jin daɗi ne." "Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya?." "Lafiya ƙalau Maman Amina ." "Mu je ka yi wanka sannan ka ci abinci sai mu yi maganar." "Wace irin magana ce wannan?." Magana ce akan Amina . Amina kuma kizo ki zauna sai mu yi maganar kawai na yi wanka daga baya. Haba Alhaji kaj.., bai bari ta ƙarasa ba ya ce "Ina jin ki faɗa min menene ke damunta?." "Alhaji wai yarinyar nan ta rasa wa za ta so sai Muhammad mai gadi." Muhammad mai gadi kuma?. "Eh shi dai har guba ta ce za ta sha, in dai ba a aura mata shiba sai da na ce mata na yi mata alƙawarin aura mata shi." Muhammad ya ce "Ai wannan abin farin ciki ne Hadiza saboda wallahi yaron na da hankali da nutsuwa, ni ma na kwaɗayi ba shi Aminar sai dai na yi tunanin ko ba za ta amince ba." Toh ai shi ke nan yazo gidan sauƙi kira min ita Amina,Mama kiran Amina ta yi. Amina ta ce "na'am" "Mama zo", in ji Alhaji. "Alhaji gani." Kiramin Muhammad. Amina ta ce "Alhaji ka aiki Mama ta kira ma ka shi dan Allah." Ya ce "Amina na ce ki kira min Muhammad." Toh kawai ta ce sannan ta tafi kiran shi. Ta ce "wai kazo in ji Alhaji." Ya ce "yau ba ko Yaya kawai kazo in ji Alhaji." Toh kai Yayana ne da zanci gaba da kiran ka da Yaya aikin banza kawai. Tafiyar ta ta yi shi ko bayanta yabi dan jin kiran da Alhaji ke yi ma sa. "Assalamualaikum ya ce "zan iya shigowa Alhaji." "Waalaikamussalam ya ce eh." Shiga ya yi ya tarar da Amina zaune a ƙasa . Alhaji ya ce "Muhammad ka san me yasa na kiraka?." Muhammad ya ce "A a Alhaji sai ka faɗa." Alhaji ya ce "Wata alfarma na ke son ka yi min idan zan samu." "Alhaji alfarma kuma ai kawai ka faɗa cikawa ne nawa." A a Muhammad alfarma dai da ka ji na ce shi ne za ka min. Toh shi ke nan Alhaji ina ji . Toh Muhammad da farko dai ba dole akan wannan abin idan ba ka sonta kawai ka faɗa min. Alhaji ya ce "Ina son ka auri Amina idan babu damuwa, kuma idan kana son ta idan ba ka son ta toh dan Allah kar ka takura kanka ka ji Muhammad." Gaban Muhammad ne faɗi ya ɗaga kai ya na kallon Amina ita ma shi take kallo tana son jin abin da zai ce. Ya ce "Shi ke nan Alhaji na amince zan auri Amina sai dai ni ba mai kuɗi ba ne talaka ne ni sosai." Alhaji ya ce "Muhammad da talaka da Mai kuɗi duk su na a hanun wa ye?." Muhammad ya ce "Allah." Alhaji ya ce "Toh saboda haka ka dai na maganar cewa wai kai talaka ne, halam ita bata san da cewa kai mai gadi ba ne amma ta ce tana sonka, ka ga ko ai kai ma mai kuɗi ne." Amina ta ce "Da gaske Muhammad ka amince za ka aure ni na ji daɗi sosai wallahi Alhaji na gode Allah ya sa ka da alkairi." Mama ta ce "Yanzun kam Amina sai a fasa shan guba ko?." Rufe idanuwanta ta yi ta ce "Ai Mama shi ne ya ce bazai auran ba." Dariya su ka yi ga ba ki ɗaya sannan Alhaji ya ce "ya tashi ya tafi." Fita ya yi sai wajen zaman sa kiran Ibrahim ya yi ya ce "Ibrahim an bani yarinyar fa yanzun da ga can na ke." Ibrahim ya ce "Toh Yaya kai kace kana son ta ne ko ita tace tana sonka?." "A a mahaifin ta ne ya kira ni wai dan Allah ya na son na auri yarinyar shi, amma kabari idan na shigo gobe sai mu yi maganar har da Inna." "Toh shi ke nan sai ka shigo." "Toh Inna dai na lafiya ko kuma ya karatun ka da na A'ishah komai ya na tafiya dai dai ko?." "Eh Yaya Alhamdulillahi dan mun kusa rubuta jarabawar." "Toh shi ke nan Allah ya ba da sa'a. Ameen ya Allah." WASHEGARI Muhammad ya shirya cikin shaddar sa ma sha Allah, Amina ta ce "Yaya ka yi kyau sosai wallahi dan Allah zan bika mu je tare tun da ba can za ka kwana ba." Ya ce "A a Amina ba zan je da ke ba saboda Inna za ta yi min faɗa ne." "Toh shi ke nan sai ka dawo amma fa zan yi ke warka sosai." Leda ce babba Amina ta ba da ta ce ya kaiwa Inna. Ya ce "Amina mene ne a ciki dan Allah wannan ledar ha ka?." Ta ce "Yaya kawai turare ne da kayan kwalliya fa." "A a wannan kan ai sai A'ishah me Inna za ta yi da kayan kwalliya." "Dama kana da ƙanwa amma ba ka faɗa min ba?." Muhammad ya ce "Eh ai ba ki nemi sa ni ba." "Eh haka ne yanzun dai sai ka dawo." "Toh shi ke nan." Fita ya yi sai tasha ya shiga motar Sokoto. Muhammad ba shi ya isa ba sai la'asar, ya na shiga gidan ya tarar da A'ishah na hura wuta, da gudu ta ce "Laa Yaya Inna ga Yaya ya zo." Kayan hanun shi ta karɓa su ka shiga ɗaki ko da Ibrahim ya ji zuwan Yayan shi, da sauri yazo gida shima sai murna ya ke yi. Gaishe-gaishe suka yi sannan ya fara labarta ma su abin da ke faru a Kano . Ita kam A'ishah daɗi kawai ta ke ji wai Yayanta zai yi aure. Ita dai Inna Allah ya sanya alkairin kawai ta yi . Haka dai su ka yi maganganun su har har aka kira sallar magarib. Ya ce "Tafiya zai yi." Inna ta ce "Ba dai yau ba ko?." Ya ce "Inna bai ce na kwana ba fa." "Toh kace ma sa ni nace sai ka kwana." Shi dai Ibrahim dariya kawai ya ke wa Inna. WASHEGARI Ya tashi tun da safe ya ce "Koma wa zai yi", wannan karun Inna ba ta hana shi ba dan ta san aikin shi . A'ishah ta ce "Yanzun Yaya sai yaushe za ka dawo"? . Ya ce "Zan dawo ba da jimawa ba zan kawo ma ki auntyn ki." Ehu ta saka da murna . Haka dai rayuwa ta ci gaba da gudana, ciki har da auran Muhammad da Amina da taimakon Amina ya sa mu aikin yi gidan ma da taimakon Amina ya gina shi. Shiryawa su ka yi shi da Amina zasu ƙauye In da Inna. Muhammad Ya ce "Amina dan Allah idan mu ka je ki saka baki ko Inna za ta dawo nan da zama." Ta ce "Toh shi ke nan zanyi maganar in sha Allah." Kama hanya suka yi sai ƙarfe 2 suka isa zo kaga murna wajen Inna saboda ganin sirikarta ma sha Allah. A'ishah ta ce "aunty bara na kawo maki abinci saboda na san kin sha hanya." Hutawa suka yi Sannan aka zo fira da dare Amina ta ce "Inna Dan Allah dan darajar Annabi Muhammad s a w, Inna ki bimu mu tafi tare wallahi gidan ba daɗi dayake ba kowa acikin shi amma idan ki ka je zan samu mahaifiya a cikin gidan dan Allah kar kice a a Inna." Inna ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un yanzun ƙara ta ka kai mata ne shine ka wani kawo min ita ashe dan ku cuceni ne kura ba ni da gari na, kuma kurasa da wa zaku haɗa ni sai da wan da ya fi ni haba dan Allah." Muhammad ya ce "Haba Inna ni ban San da za ta yi wannan maganar ba ai da ba zan zo da ita ba dan Allah ki yi hakuri, kuma yanzun Inna ya za ki yi." "Kai ɗan nan ka ji tsoron Allah sai ka ce ba da kai aka haɗa baki ba." Amina ta ce "Inna yanzun ba zan samu wannan alfarma ba, shi ke nan amma gaskiya ban ji daɗi ba wallahi Inna." Ke yar nan ai ba yanda na iya saboda kin haɗa ni da Allah har da Annabi Muhammad s a w, ai dole zan biku. Saura ƙiris Muhammad ya rungume Amina a ga ban Inna akan daɗi. Ya ce "Inna gobe zamu tafi ko?." Ta ce "A a ni kam ba zan je gobe ba sai dai ku ta fi da Ibrahim da A'ishah." Amina ta ce "Haba Inna ba yan kin ce min za ki je kuma yanzun ki ce a a dan Allah ki yi hakuri Inna", Amina yi tayi kamar za ta yi kuka ganin haka ya sa. Inna ta ce "toh shi ke nan na yarda amma ai sai na shirya kaya na ko." Amina ta ce "a a Inna akwai komai a can." Toh shi ke nan zan je ban kwana saboda tafiyar tazo min a bazata. Toh shi ke nan Inna na gode sosai da ki ka yarda. Maƙota Inna ta je ta yi ma su sai wata rana. WASHEGARI Tun da safe su Inna suka kama hanyar Kano, A'ishah kam sai surutu ta ke bu gawa idan mota ta ga ni mai kyau sai ta yi magana da haka dai har suka isa gidan su. Inna ta ce "Yanzun yaron nan kai ne mai gidan Allah Mustapha da kana raye da yanzun muna tare cikin gidan yaron ka", hawaye ne suka shiga anbaliya a fuskar ta. Ibrahim ya ce "Haba Inna Dan Allah ki yi hakuri ki dai na wannan kukan ai farin ciki za ki yi saboda Allah ya nuna ma ki ranar da yaronki ya gina gida kuma gaki cikin shi sai ki godewa Allah." Inna dan Allah ki yi hakuri wallahi mutuwa bata da daɗi ko ta tsofa bale yanzun da Allah ya nuna maki cewa yaranki sun girma har gaki a cikin gidan shi dan Allah ki dai na kukan nan kin ji Inna. Cewar Amina. Muhammad ya ce "Inna mu shiga da ga ciki kinga A'ishah kuka za ta yi, ganin kina kuka dan Allah ki bar haka nan Inna idan ba so kike muma mu yi kukan ba." Hannun ta Ibrahim ya ja sai cikin gida, cikin gidan ma sha Allah. Part ɗin ta da ban da nasu gidan dai ga baki ɗaya part 6, part ɗin Amina, part ɗin Ibrahim idan ya tashi nashi auran, sannan part ɗin Inna, part ɗin yaran su na mata da ban na maza da ban, toh ɗayan ban san na meye ba. Part ɗin Inna Amina ta nuna mata sannan ta haɗa mata ruwan wanka ta ce "Inna ga ruwan wanka can kije ki yi wankan." Toh kawai Inna ta ce ta na jin wani sabon al'amari a jikin ta. Amina in da mijinta ta je ta haɗa ma sa ruwan wanka sannan ta ce "Mijina ka je ka yi wanka sai warin dauɗa ka ke yi ta faɗi maganar ta na dariya." Ya ce "Amina ban san da wane baki zan gode maki ba saboda wannan abin da ki ka min na gode sosai mata ta Allah ya sa ka da alkairi." Hmm kar ka manta nima mahaifiya ta ce fa dan na yi wannan abin ai ba komai ba ne, ni dai ka je ka yi wanka dan Allah. Rungume ta ya yi ya fa ra shafata ni dai na ce nayi nan na rufe ƙofa na yi tafiya ta . Inna ce ta fito da ga wanka ta tarar da kayan ta a waje ta ce "A'ishah me yasa kika ɗauko min kaya eyye." Kai Inna bani bace aunty ce tace nace idan ki ka zo ki sa ka su . Humm kawai ta ce. WASHEGARI By Sha'awa marubuciya✍️✍️ WhatsApp number08084277827☎️ RASHIDA PART 6 📝 Amina ta ce "A a Maryam ba du ka suke ɗaya ba sannan me su ka yi da kike faɗar wannan maganar akan su?." Maryam ta ce "Amina Ibrahim ya ci amana ta, Ibrahim ya yaudaran, Ibrahim bai yarda da Allah ba, ku ma wallahi a gidan mu zan kwana dan ba zan kwana ta re da shi." Muhammad ya ce "Ibrahim me kayiwa yarinyar mutane ne da har ta ke faɗan wannan maganar akan ka?." Ibrahim ya ce "Wallahi yaya na ga ji da rashin haihuwar nan ina bukatar na sa mi ƴan yarana nima." Muhammad ya ce "Anya Ibrahim kai ne wai saboda Ibrahim ɗin da na sa ni ba irin wannan na yanzun ba ne, ok idan na fahimta so ka ke ka ƙara aure ko?." Ibrahim ya ce "Eh. Maryam ta shi ki je ɗakin ki zan je da shi wajen Inna. Maryam ta ce "Dan Allah Yaya kar ka kai ƙarar shi wallahi bana son na ji ana ma sa faɗa saboda ina son shi." Muhammad ya ce "Maryam wacce irin mata ce ke mutum na son rabaki biyu ina son nagyara abin kina son lalata shi?." "Dan Allah ka yi hakuri Yaya cewar Maryam. Rashid ya ga Umman shi na kuka ya zo ku sa da ita ya ce "Umma waye ya dakeki na rama ma ki?." Duk cikin gwalancin shi ya ke yin maganar. Rungume shi sosai Maryam ta yi ta na kuka abin tausayi. Ganin haka shima yafara kukan. Muhammad ya je ya kira Inna tazo ta tarar da Maryam na kuka ita da Rashid. Inna ta ce "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, me zan gani ne amma kai Ibrahim wallahi sai hakkin yarinyar nan ya bi ka, saboda Allah wannan abin ita ke bawa kan ta ne ka san lokacin da na ke yarinya kamar ta?." Kamin shiru kabani amsa mana. Ibrahim ya ce "A a Inna." Ta ce "toh lokacin da nake yarinya kamar ta na shekara 5 ban Haihu ba sai da ga baya Allah ya ba ni Ku, sannan yanzun akan rashin haihuwa wai za ka Rusawa yarinya rayuwa." Maryam ta ce "Dan Allah Inna ki barshi kawai ya yi auran idan dai zai samu abin da ya ke so kawai ki barshi ba komai, nima ina son na ga yaran shi Allah ya ba ka mace ta gari Allah ya sa auran ne alkairi a gare mu." Amina ta ce "Amma Ibrahim wallahi ka ban mamaki yanzun duk yadda Maryam ke son ka kai ma kake son ta amma wai za ka yi ma ta kishiya haba Ibrahim." Maryam ta ce "Amina dan Allah ki dai na faɗar haka ni ina mai farin ciki da auran nan kawai matar da zai auran ce ban san halin ta ba, wallahi Amina kishiya idan ba mai rabaka da mijinka ba ne, ko mai rabaka da lafiyar ka ba ne, ko mai rusamaka rayuwa ba, ai abar su ce ke dai kawai Allah ya sa mai zuciya ɗaya ce." Inna ta ce "shi ke nan Maryam tun da haka kika ce ba damuwa Allah ya sa shine mafi alkairi sannan Allah ya sa ba ƴar biyan bokaye ba ce." Su Amina Ameen ya Allah kawai su ka ce. Muhammad ya ce "Ibrahim yanzun idan ka je ka auro yariyar da kake ganin za ta haifa ma ka yaran a ka zo bata haihuwa me za ka yi?." Amina ta ce "Ni ba komai na ke dubawa ba na ga shi likita ne makin ya binciki kan shi ya bincike ta ai zai gane mai matsalar amma babu sai kishiya, toh yanzun ka je ka yi aure ka tarar da ita da ciki me za ka yi?." Muhammad ya ce "Ciki kuma?." Amina ta ce "Eh." Muhammad ya ce "Ai da ya ji kunya wallahi." Amina ta ce "Wallahi duk alamomi sun nuna cewa Maryam na ɗauke da ciki, ka dubi fuskar ta, sannan ga ƙirjinta ya yi yawa sosai, sannan idan mu ka shiga kitchen toh wallahi abu za ta ne ma dan rufin hancin ta idan na tambaye ta sai ta ce min wai ba da lafiya." Ibrahim ya ce "Aunty wallahi ba wa ni cikin da ta ke da amma ba ku san ko auran nan alkairi ba ne." Maryam ta ce "Ibrahim ni ma na san ba na da cikin kawai ka je ka yi auran ka ba damuwa." Inna ta ce "Toh yanzun me ake ciki ga me da auran". Ibrahim ya ce "Inna cewa su ka yi na tura iyayena da kuɗin an ga ni a na so da kuɗin sadaki." Muhammad ya ce "Ƴar wa ne gida ce?." Ibrahim ya ce "Yar gidan Alhaji Murtala ne." Amina ta ce "Wane Alhaji Murtala ɗin ka ke nufi?." Ibrahim ya ce "Ɗan kasuwa." Amina ta ce "Murtala ɗan kasuwa kuma yanzun ka rasa wa za ka haɗa kishi da Maryam ƴar masu kuɗi kuma ƴan dangi wulakanta mutane?." Muhammad ya ce "Kin san su ne?." Amina ta ce "sosai ma." Muhammad ya ce "budurwa ce ko bazawara?." Ibrahim ya ce "budurwa ce sunan ta Balkisu." Amina ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, amma lallai Ibrahim ka cika butulu wallahi, yanzun wannan ƴar iskar ka ɗaukar wa kan ka." Maryam ta ce "Yaya, Inna, Amina, dan Allah ku bar shi ya yi auran shi wallahi ni dai idan ba ƴar bokaye ba ce ba zai daman ba." Muhammad ya ce"Toh shi ke nan zan je dan kai kuɗin auran, amma ka sa ni duk abin da kayiwa amarya toh sai kayiwa Maryam ka ji ni ba." Maryam ta ce "Yaya dan Allah ka dai na wannan maganar kawai barshi ya yi abin da ya fiye ma sa." Inna ta ce "Nima ina bayan ka yaron nan dan dole sai ya yiwa ƴata sabin kaya." Da haka dai su ka watse . Da dare aka je kai kuɗin auran. Aka sa ka ranar aure nan da sati ɗaya. Suka dawo gida su ka sanar da ƴan gidan. Su ka ce Allah ya kaimu. Maryam ta ce "Dan Allah Yaya gida na ke son zuwa kuma na tambaye shi ya ce ba zan je ba sai an ɗaura auren kuma ina da wata matsala ta zuwa gida." Muhammad ya ce "A kan mi za ka hana ta zuwa gidan su?." Ibrahim ya ce "Yaya saboda ba na son wani abun ya faru da auran ne." Maryam ta ce "Ibrahim yanzun ni kake zargi da lallata ma ka aure saboda mi zan lallata ma auran naka, halam duk namiji dan mace ɗaya a ka yi shi duk namiji zai iya auran mace huɗu toh ni a kam mi zan hana ka raya sunnar Annabi." Muhammad ya ce "Maryam ki yi hakuri ki je gidan idan kika ga ma abin da kike sai ki kirani zan ɗauko ki kin ji." Maryam ta ce "A a Yaya na fasa wallahi tun da har yafaɗi wannan maganar ba zan je gida ba sai ya ban hanya da kan sa." Tafiya part ɗin ta ta yi wayar ta ɗauka ta faɗawa mahaifiyar ta abin da ke faruwa. Mahaifiyarta ta ce "Maryam ki yi hakuri ko wacce irin mata ce zai ɗauko da talaka da Mai kuɗi duk suna a hanun Allah, dan Allah haka ki kwantar da hankalinki ki yi kamar abin bai miki zafi ba, sannan ki da ge da addu'a saboda ita ce katangar zarfe tsakanin ki da ita, Maryam ban san ki da fitina ba kar na ji kar na gani kishi ba akan ki aka fara ba kuma baza a gama akan ki ba ki yi hakuri ki bi mijin ki sauda ƙafa idan wuta ya ce ki faɗa toh ki faɗa, amma abu ɗaya zance karki aikata shine bin hanyar da Allah ya haramta kin ji." Maryam ta ce "Toh shi ke nan Mama nago de sosai kuma zan sa ke fuska ta ayi komai da ni in sha Allah Mama kuma ba zanyi sake da addu'a ba da ga ni har yaran da zan haifa ba zan bari ko ɗaya ya yi wasa da ibada ba." Mamarta ta ce "Allah ya yi maki albarka autana." Maryam ta ce "Ameen Mamana." Sai anjima su ka yi rayuwar kowa ba daɗi. Amma Maryam rayuwarta ta yi sanyi akan ɗazun. BAYAN SATI ƊAYA Maryam ce zaune da Amina da amaryar wato Balkisu. Maryam ta ce "Wai Amina ina yaro na ne ko har yanzun bai dawo daga school ba ne?." Amina ta ce "Ai na huta ni kam saboda yaron nan wallahi akwai shi da baƙin rai ko dariya fa ba ya yi tun yana jariri." Balkisu ta ce "Ba wani nan kawai sharri kike ma sa." Maryam ta ce "Ke dai Balkisu kya faɗa mata." Amina ta ce "Wallahi ku yi sauri ku bani yarona ko yarinyata idan ba ha ka ba ko humm basai na ida ba." Maryam ta ce "ki ka sa ni ko Balkisu ta ɗauka maki yaronki ko yarinyar ki." Balkisu ta ce "A a Maryam rufamin asiri ai ni kam tun da ba kaza nake ba sai na jima ban Haihu ba sai dai ke." Amina ta kalli Maryam su ka haɗa ido. Maryam ta ce "Ban gane ba saboda mi za ki mana wannan fatar toh bata saɓu ba gaskiya." Balkisu ta ce "akan mi wallahi ni kam ban ki na shekara 5 ban Haihu ba saboda ai saurin haihu na tsufar da mutum." Amina ta ce "Toh a bar maganar kawai." Rashid ne ya dawo da ga school tare da Ibrahim Rashid ya ruga aguje ya yi in da Maryam ya ce "Umma na dawo." Maryam ta ce "Toh yaron albarka sannu da dawo wa ya hanya?." Ya ce "Lafiya ƙalau Umma ina abinci na?." Balkisu ta ce "ga shi can a dainnin na haɗa ma." Ya ce "Ni ba na son naki na Umma na ke so." Ran Balkisu ya ɓaci sosai kenan har yaron ya fi son ta akan ta. Maryam ta ce "haba yarona Momyn ka ce fa ka je ta ba ka abincin." Rashid ya ce"Ni kam Umma na ki na ke so yafi daɗi." Balkisu cikin zafin rai ta ce "Kana nufin ban iya abinci ba ne ko meye ehe?." Maryam ta ce "Haba Balkisu mene ne na biyewa shiriritar yaro toh ko mahaifiyarshi ya ce wa ba ta iya abinci ba bale ke da ba ma sabo kukayi ba." Balkisu ta ce "Ai dole za ki faɗa haka tun da kowa ke yake so ni ba mai su na kowa ya tsanan." Maryam ta ce "Meki ke nufi ne Balkisu kamar ya kowa yatsaneki?." Amina ta ce "Ya ko za ayi yaro ya saba da ke bayan ita ya tashi da ita ba ke ba ai dole zai fi sannan ta." Maryam ta ce "Dan Allah Amina ki bar faɗar wannan maganar ba daɗi fa." Balkisu ta ce "Ai dole za ta nuna miki cewa yaron ta ne banaki ba ne dan haka ki je zuwa haifar naki." Maryam ta ce "Dan Allah ku dai kubar maganar." Maryam ta ce "Rashid ka je kaci abincin da Momyn ka ta dafa maka ka ji yaron albarka." Ya ce "toh Umma." Ta shi ya yi ya ce "Momy mu je ki bani abincin." Ibrahim ya ce " haba dai Balkisu ai sai ke yi hakuri saboda yaro ne duka duka yaushe kika zo kinga ko ai bakwa ɗaya". Balkisu ta ce "Ai dole ne za ka ce haka amma ba komai da sunnu zai san Ni." Maryam ta ce "Yi hakuri Balkisu kin san yaro ne sai an bi shi a hankali." Da haka dai har su ka watse Rashid bai ci abinci ba. Ya na ɗakin Amina ya ce "Mama wai sai yaushe Umma za ta haihu a samamin kane?." Amina ta ce "Kai dai duk wanda ya ga girman ka toh ya shiga uku tun yanzun sai tambayar masifa." Maryam ciki har ya fara fitowa saboda ya fara girma, sai kwaɗayi ya ke sa ka ta. Sai yanzun hankalin Ibrahim ya bashi lallai fa ciki ne da Maryam, aiko murna ba a Magana wajen Ibrahim. Ya ce "Yanzun Maryam ciki ne da ke amma ba ki faɗa min ba kuma akan mine kika ƙifaɗamin?." Maryam ta ce "Saboda yanzun ba na burge ka ko kaɗan, kuma bana a ranka ba ka sona ba ka ƙaunata ka gaji da zama da ni kawai ina zaune ne alfarmar Inna da Yaya ne." Ibrahim ya ce "Bangane ba Maryam meki ke nufi da waɗan nan maganganun nan naki?." Maryam ta ce "Wallahi ko da na rantse ba zanyi nadama ba yanzun ba ka sona." Ibrahim ya ce "Wallahi Maryam ina son ki ina ƙaunar ki meki ka min da har zai sa nace ba na son ki dan Allah ki dai na wannan maganar Please my love." Maryam ta ce "Toh shi ke nan tun da kace na bar maganar toh na dai na in sha Allah, amma ka sa ni cikin nan cikin wata na 6 ya ke dan haka kasan yadda za ka yi kuma dan Allah kar ka bari matar ka ta sa ni dan Allah." RASHIDA Sha'awanatu Faruk diggi✍️ Sha'awa marubuciya✍️✍️ WhatsApp number 08084277827☎️ 8 📝 Fita ɗakin Balkisu ta yi part ɗin ta shiga ta tarar da Ibrahim. Ibrahim ya ce "Balkisu a ina ki ka fito ne haka?." Balkisu ta ce "Haba dai mijina muna tare da Maryam ne fa, ina kwance ta zo ta ce min mu fita mu je fira." Ibrahim ya ce "Toh shi ke nan dan Allah hakkina nake son ki bani Please Balkisu." Balkisu ta ce "Gaskiya ba zan iya ba sai dai ka yi hakuri saboda ko jiya fa ni ka saukar wa gajiyar ka, toh yau kam ba za ta saɓu ba gaskiya." Ibrahim ya ce "Yanzun idan ke baki bani hakkina ba waye zai ba ni, Maryam ce kuma yanzun jego take yi ya zan je in ce ta bani hakkina." Balkisu ta ce "Au kana nufin gorin haihuwa ka ke min?." Ibrahim ya ce "Allah ya baki hakuri ni ban maki gori ba." Balkisu ta ce "ga abincin ka can idan zaka iya ci." Tashi ya yi yaje ya ɗauko abincin ya dawo ya fara cin abincin, ya manta bai yi bismillah ba kawai ya fara cin abincin. Jin kanshi ya yi kamar an buga ma sa wani abun mai nauyin gaske ga baki ɗaya fita ya yi a hayyacin shi. Ibrahim ya ce "Mata ta abincin nan ya yi daɗi sosai." Balkisu ta ce "Ai na sani." Tashi ya yi dan zuwa part ɗin Maryam amma sai ta ce "Ibrahim ina zuwa ne haka?." ya ce "Ba in da na yi kawai falo zan je." Ta ce "Kar na ji an ce wai kaje in da Maryam, wallahi idan ba ni na baka hanya ba kaje sai na ɗau mummunan mataki akan ka." ya ce "Bama zan je ba wallahi." ta ce "Toh ta shi ka je." Ibrahim da sauri ya fita a ɗakin sai ɗakin Maryam ya tarar da ita ta na shayar da Rashid. Ganin shi kawai ta yi ba sallama ba komai . Maryam ta ce "Yaya meke damunka naga ka shigo ba ko sallama?." Ibrahim ya ce "Idan na yi maki sallama cinta za ki yi ne?." ta ce "A a ka yi hakuri." Zama ya yi yana son yin magana amma ba maganar taƙi fitowa. Maryam ta ce "Dan Allah Yaya ka faɗa min meke damunka na ga kana cikin damuwa." RASHIDA By Sha'awanatu Faruk diggi ✍️ ✍️ Wtspp 08080304152☎️ 10 📝 Su Ma'aruf ne zaune a falo rike da littafan school suna rubutu . Maryam ta ce "Rashid kai da ƙanen ka Rufa'i ku zo ku ci abinci kubar rubutun haka nan." Rashid ya ce "Umma aboki na Ma'aruf fah." Ta ce "Abokinka ko ƙanen ka?." Ya ce "Umma ai Abokina ne kuma ƙanena ne." Ta ce "Toh ku tashi mu je ku ci abincin." "Toh" su ka ce Amina ce zaune da ƙaton cikin ta a kan dainnin tebur. Balkisu ma da cikin ta, na Maryam ne ƙarami bai girma ba. Amina ta ce "Wai Maryam ba za ki bar wannan yaron ba, wallahi baƙin ranshi ya yi yawa ji dan Allah ko dariya ba ya yi." Ta ce "Eh ba komai yana dai jin maganar mahaifan shi ko." Amina ta ce "Wallahi ba gaskiya bane ba, saboda Ma'aruf akwai shi da jin maganar mahaifan shi, amma wannan ɗan baƙin rai ba mutunci." Balkisu ta ce "Ai Amina baki san mai mutunci ba wallahi, saboda ga bakiɗaya Ma'aruf bai da mutunci, kina ganin shi haka kin san ba ɗan mutunci ba ne." Amina ta ce "Kamar ya ba ɗan mutunci ba ne, meki ke nufi da wannan kalmar." Maryam ta ce "Ai gaskiya Balkisu ne, saboda ga baki ɗaya ɗan ki ba ya jin magana ko kaɗan." Ta ce "Wallahi wannan maganar ba gaskiya ba ne ba ehhe." Rashid ya ce "Umma sai yaushe za ki haifa min ƙanwa ne?." Ta ce "A a Rashid ƙanwa ka ke so ne?." Ya ce "Eh Umma." Ta ce "Toh kwantar da hankalin ka ta kusa zuwa in sha Allah." Ya ce "Toh Umma." Amina ta ja tsaki mtss aikin banza kawai. Dariya Maryam ta yi ta ce "Toh su kishi har ya bayyana Amina ai da kin ɓoye shi." Ta ce "Ni ce zanji baƙin cikin wannan abin." Ta ce "Eh mana." Ibrahim ne da Muhammad su ka shigo bakin su ɗauke da sallama su ka ce "Assalamualaikum" "Waalaikumussalam" su ka amsa ma su. Su Rashid da gudu su ka tarbi mahaifan su amma abin mamaki Ibrahim Rufa'i kawai ya amsa wa sannu da su ke ma sa shida Ma'aruf. Ma'aruf ya ce "Abba sannu da zuwa." Nan ma shiru Ibrahim ya yi ma sa. Muhammad ya ce "Wai Ibrahim mene ne haka, baka ji sannu da Ma'aruf ke ma ka bane?." Ya ce "Yaya ban ji ba ne ba." Ma'aruf yi ya yi kamar zaiyi kuka sai Muhammad ya ce "ma sa yazo." Maryam ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba amma haka ta share shi. Ya ce "Balkisu sa ka min abinci na." Ta ce "Gaskiya ba na iyawah saboda cikina ciwo ya ke min ka ce wa Maryam ta haɗa ma." Ya ce "Maryam haɗa min abincin." Tashi ta yi ta yi tafiyar ta ta bar su nan a dainnin ɗin. Sakin baki su ka yi ga baki ɗayan su . Rashid sauka ya yi daga jikin Muhammad ya ce "Abokina mu je in da Umma." Shima Ma'aruf sauka ya yi su ka yi tafiyar su in da Umman su. Muhammad ya ce " Wai Ibrahim me ya sa har yanzun kai yaro ne, yanzun dan Allah wulakanta yaron nan na ta da ka yi a gabanta daidai ne ehhe?." "Nifa Yaya ban kula da shi ba ne" Amina ta ce "Wallahi Ibrahim ban taɓa ce ma ka ƙarya ka ke ba, amma yau kam zan faɗa wallahi ƙarya ne, ka ce wai baka ganshi ba." Ya ce "Wai dan Allah a kan wannan yaron ne kowa zai zo ya na gaya min Magana." Muhammad ya ce "Toh fa ko ramawa za ka yi?." Balkisu ta ce "Ibrahim ka min shiru dan Allah duk kunci ka min kunne da surutu." Shiru Ibrahim ya yi bai sake magana ba. Amina ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un Maryam kin banu, tashi ta yi ita ma." RASHIDA By Sha'awanatu Faruk diggi ✍️ ✍️ Wtspp 08084277827☎️ 11 📝 Muhammad ji jiga kan sa kawai ya yi shima ya bi bayan Amina. Sallama ya yi. "Assalamualaikum" "Waalaikamussalam." Amina ta amsa. Ya ce. "Maman yara mai ya sa ki ka tawo ba a gama cin abincin ba?." Ta ce. "Wallahi Maryam na cikin matsala sosai, shi ne ke wayan sa ka ta ciwo kenan amma ba ta faɗa min ba." Ya ce. "Ban fahimci zancenki ba." Ta ce. "Abin da na ke wa Ibrahim gudu kenan ga shi ya faru." Ya ce. "Amina ki faɗa min yan da zan fahimci maganar ki." Ta ce. "Ta asirce Ibrahim sai yan da ta yi da shi dan Allah ku ta ya shi da addu'a, ni dai zan ta ya Maryam in sha Allah." Ya ce. "Ai ba yau ba na ke ganin Maryam cikin wani hali, kawai saboda ta na jin nauyi na ne ya sa ban yi mata magana ba." Rashid ne ya zo da gudu ya ce. " Mama Mama Umma ba ta da lafiya sai kuka take yi." Barin ɗakin Amina ta yi, da sauri Muhammad ya riƙe hannunta ya ce. "Ki bi a hankali kar ki ji ciwo kema." Ta ce. "Toh". Sakin ta ya yi amma duk da haka sai da ta haɗa da gudun. Ɗakin Maryam ta je ta tarar da Maryam a kasa sai kuka take gata riƙe da kanta . Ta ce. "Maryam mene ne haka, idan ki ka hallaka kanki fa, kuma gaki da ciki, haba dan Allah ki yi hakuri ki barwa Allah komai shine zai saka maki, ba wani ba ke dai addu'a ne ta ki." Ta ce. "Amina na shiga uku tun auren nan na Ibrahim ban da kwanciyar hankali, kullum da abin da zai min wallahi na ga ji gidan mu zan ta fi." Ta ce. "Haba Maryam kenan ta yi galaba a kan ki?, ki yi aiki da hankalin ki ba zuciyar ki ba." Ta ce. "Amina Ibrahim ba ya sona kuma ba ya son yaron ki, ai idan bai soni ba toh ya so yaronki amma mu duka bama samun hakan." Ta ce. "Maryam ki yi hakuri zan ta ya ki da addu'a in sha Allah, na san Mama tana can tana ta ya ki da addu'ar in sha Allah zai dawo dai dai kamar yadda ki ka san shi." "Toh" kawai Maryam ta ce. Jikin ta Amina ta taɓa zafi ta ji sosai ta ce. "Maryam ba ki da lafiya ne har haka?." Ba ta tanka mata ba kawai kai ta ɗaga mata. Ta ce. "Rashid ya je ya kira Abban su yazo ya duba Umman ku." Da gudu su ka fita a ɗakin sai part ɗin Balkisu. "Assalamualaikum." "Waalaikumussalam." "Momy wai Mama ta ce Abba yazo ya duba Umma." Ta ce "Baya nan sai ya dawo." "Toh" su ka ce Fita su ka yi sai ɗakin Umman su. Mama ta ce "Mai ya ce ne?." Su ka ce. "Wai cewa ta yi baya nan sai ya dawo, kuma Mama mun gan shi a zaune." Mama ta ce "Zaune fa ku ka ce?." "Eh" Mama Ta shi ta yi ta je ta kira Muhammad ta faɗa ma sa halin da a ke ciki. Ran Muhammad ya ɓaci sosai ɗakin ya nufa, ya na zuwa ya wankawa Ibrahim mari har sau biyu ya ce. "Ibrahim ka na da hankali kuwa ehe, maike damunka ne da za ka hallaka ƴar mutane?." Amina ta ce. "Na shiga uku Daddyn yara dan Allah ka yi hakuri, wallahi da na san abin zai kai ku haka da ban faɗa ma ka ba." Muhammad ya ce "Za ka bani amsa ko sai na ci uban ka a nan ne?." Ya ce. "Yaya ka yi hakuri ni wallahi ba na son ta ne." "Baka son ta fa kace Ibrahim?." "Eh" Ibrahim ya faɗa . Amina ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Ibrahim kai ne wai kuwa gaskiya ba kai ba ne, Ibrahim da na sa ni mai son Maryam sosai." Maryam da ke ba kin ƙofa ta ce. "Ai na sa ni Ibrahim ba sai ka faɗa masu ba, kuma na gode sosai da sakayyar da kai min." Cikin kuka ta ke maganar abin tausayi. Muhammad fita ya yi ya kira Inna ya faɗa mata duk abin da ke faruwa. Inna ta zo ta ɗauke shi da mari ta ce "Sha-sha-shan banza mutumin banza, toh yadda ka yi mata nima na san za ka iya yi min shi." Balkisu ta ce "Wai wane irin wulaƙanci ne wannan, a ga ba na a zo a na ciwa mijina mutunci toh wallahi ba zan yarda ba." Mari ta ji a kuncenta da sauri ta dafe kuncin na ta . Muhammad ne ya ce "Duk wulaƙancin ki ya tsaya a kan shi, idan ki ka ce za ki wulakanta, mahaifiya ta a ga ba na, toh wallahi komai zai iya faruwa." Amina ta yi saurin riƙe shi ta ce. "Haba Daddyn yara bafa muharramar ka ba ce ba fa, kuma har ka iya ɗaga hannu ka dake ta?." Wayar Maryam ce riƙe a hannun Rashid kiranta a ka yi sai kawai Rashid ya ɗaga kuma bai yi magana ba. Maryam ta ce. "Dan Allah Yaya ka yi hakuri in dai a kai na ne wannan abin ke faruwa, wallahi na warware sosai jiki na ya ji sauƙi dan Allah mu ta fi." Ya ce. "Maryam mu je part ɗin Inna zan yi magana da ke." "Toh" kawai ta ce. Fita ya yi itama Maryam bayan shi ta bi. Inna ta ce "Ka sa me ni a ɗakina ina jiran ka." Sannan su ka fito ita da Amina. RASHIDA PAGE NA 12 BY SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️ WhatsApp number08084277827 ☎️ 12 📝 Tashi ya yi da niyyar fita ta ce "Ina za ka je ne?." Ya ce "Zan je wajen kiran Inna ne." Ta ce "Ba za ka je ba." Ya ce "Toh shi ke nan." Zama ya yi sai bacci. Kiran hajara ta yi ta ce "Hajara wallahi bokan aikin shi na kyau, ga shi sai juya dan iskan nan na ke yi, yanzun kuɗin sa na ke son na fara ɗibawa." Ɗaya bangaren ta ce "Ai Balkisu gara ki juya ɗan iska, ai shi ma ya san ruwa ba sa'ar kwando ba ne." Ta ce "Ke dai bari yanzun haka ana kan wata dirama a gidan nan, kuma ba zan ba shi hanyar zuwa can ba." "Hahaha kai ƙawata shegiya ce ke wallahi." Ta ce "Balkisu wai ya maganar ƴar iskar kishiyar nan taki ce, har yanzun ta na nan da addu'ar tan ne." Ta ce "Ai ki barta wallahi ba zan kya le ta ba, kuma ba zan kyale yaranta ba, saboda suma ina jin kamar kishiyoyina ne." Hajara ta ce "Gaskiya ne kinsan da zafi zafi a kan duke ƙarfe." "Gaskiya ne kam" cewar Balkisu Sallama su ka yi. Amina ji ta yi cikin ta na mata ciwo amma ba ta yi magana ba. Maryam ta ce "Amina meke damunki ki ne naga kamar ba Kya jin daɗi?." Ta ce "Maryam cikina ne na ke jin yana min ciwo sosai." Inna ta ce "Ayya ko naƙodan ce?." Muhammad ya ce "Naƙoda kuma Inna cikin wannan halin." Amina ta ce "Maryam dan Allah ka ma min na tashi zan je ɗakina." Ta taimakon Maryam Amina ta isa ɗakinta. Tana shiga ɗakin cikin ikon Allah ta haihu lafiya. Maryam da gudu ta yi part ɗin Inna ta ce "Inna Amina ta haihu." Inna ta ce "Yanzun idan kika ji ciwo fa wannan gudun haka." "Inna wallahi ina murna ne ban san yadda zan yi ba, saboda farin ciki ƴa mace fa ta haifa." Muhammad ya ce "Kai Maryam ki rage wannan abin, yanzun idan kika hallaka min ƴarinya ko yaro fa?." Cikin jin kunya ta ce "Yaya yi hakuri wallahi ina son ƴa mace ne sosai da sosai." "Ya ce "Toh Allah ya baki mai albarka." Ta ce "Ameen Yaya na gode sosai." Tashi su ka yi zuwa in da Amina ita da Balkisu su ka tarar zaune. Balkisu ta ce "Maryam ko baki faɗa min ba toh na ji sai hakuri." "Amma Balkisu yanzun nake da niyar kiranki, kawai dai na kira su Inna ne." Ta ce "Amma ai na ga kamin ki kai ga resu sai kin wuce ni." Maryam ta ce "Amina meki ke bukata yanzun?, dan Allah ki yi hakuri kwanciya nake son na yi." Ibrahim ne ya shigo Inna ta lallai Muhammad ya ce "Ibrahim Ina ki ran da Inna ta yi ma ne, ko kafi ƙarfin zuwa ne?." Ya ce "Ni fa wallahi na gaji da wannan abin, kullum ana takurawa mutum." Inna ta ce "Ai sai ka koma in da ba'a takura ma." Su Ma'aruf ne su ka shigo ɗakin su ka ga jariri, sai Ma'aruf ya ce "Laa Mama waye ya haihu?." Balkisu ta ce "Ai Mamarka ce ta haihu." Rufa'i ya ce "Laaa wallahi Mama ta na da kyau sosai." Rashid ya ce "Umma sai yaushe za ki haifa min ƙanwa ne?." Umman ta shi ta ce "Yarona sai lokacin fitowar shi ya yi." Ya ce "Shi ke nan." BAYAN SATI ƊAYA Anyi suna yarinya ta ce sunan Goggonta A'ishah ma sha Allah. Har da A'ishah ta zo sunan dan sun dawo da tafiyar ta su ka yi . A'ishah ta ce "Aunty Maryam wai Aunty Balkisu nan na da hankali?." Ta ce "A'ishah saboda mii za ki kirata da maras hankali, kin ganki idan Yayanki ya ji ki, toh wallahi sai kunyi faɗa tam." Ta ce "Yanzun aunty Saboda na ce mata maras hankali shine za mu samu matsalar?." Ta ce "Eh sosai ma." "Allah ya kyauta" kawai A'ishah ta ce Amina ce ta kira Maryam ta ce "Ta zo ta karɓi A'ishah." A'ishah ta ce "Wallahi aunty ni zan karɓe ta, saboda yanzun ba zama na ke ba tafiya zan yi na barki da ita." RASHIDA SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️ WhatsApp number0808427727 ☎️ 13 📝 "Toh shi ke nan ɗauke ta ɗin ba damuwa." "Yauwa aunty na." Wata yarin ce tafi toh rike da lemo ta ce "Mama wai ina so Yaya Rashid ne?." Umma. "Su Rashid na can lambo." Mama. "Ba ki iya gaisuwa ba ne?." "Na manta ne ina wuni Umma." Umma. "Ba damuwa yi tafiyar ki ƴar albarka." Mama. "Wallahi aunty na rasa laifin me na yi wa Allah da ya bani wannan yarinyar, bata dubin kowa da idon rahama, aunty wallahi har mahaifin ta bata bari ba, ya yi dukanta har ya gaji ya daina." Umma. "A'ishah ki yi hakuri kici gaba da yi mata addu'a in sha Allah za ta nutsu da yarda Allah, ki yi addu'a ki riƙa yawan yin sadaka, shi ma ya riƙa fitar da Zakka in sha Allah,Allah zai cire mata wannan abin." "Toh shi ke nan aunty na gode sosai, shi ya sa nake son faɗa maki damuwa ta saboda kina bani shawara mai amfani." "Hahaha toh ai nima yarinya tace saboda ai dole zan baki shawara, saboda nima ban san wace irin yarinya zai ban ba ko yaro." "Na gode sosai Allah ya saka da alkairi Allah ya mayar maki hankalin Yaya." "Ameen". Inna su ka ji a bayan su ta na faɗin toh mata da miji ai sai ku tashi kuje dubin Balkisu, ta haihu amma bakwa wajen. Umma ta ce. "Inna me ta haifa ne?". Inna. "Yarinya ce". "Toh ma sha Allah." Tashi sukayi dan zuwa in da Balkisu. "Assalamualaikum". "Waalaikumussalam". "Balkisu a she kin haihu bamu sa ni ba, muna can muna shan fira." Balkisu. "Ai dole zaku barni ni ɗaya tunda ni ba sona ake yi ba daga ke har su Innar." A'ishah. "Dakata Balkisu karki sa ke ki zagi mahaifiyata a gabana, dan wallahi na fiki rashin mutunci, idan kika sa ke zagin ta wallahi sai naje har gidan tsofinki naci mutuncin su." Balkisu kuka ta saka ta ce. Yanzun A'ishah ni kike zagi saboda nace Maryam ta kawo min ruwa." Ibrahim. Ya kwashe A'ishah da mari sai da ta yi tingil tingil za ta faɗi. Umma ta ce. "Haba Abban yara mene ne haka daga faɗan gaskiya sai duka, Inna ce fa take ciwa mutunci, kuma kake sa ran A'ishah ta barta." Ibrahim. "Wallahi kema zan ɗauke ki da mari idan ba ki bar wajen nan ba." Umma. "Ai da ka bala'i wallahi dan ba zan kwanta ka dakeni akan kishiya ba, ko kishiyar wacce bata san darajar mahaifan ta ba bale ta san na mahaifan wani." Ɗago hannu ya yi ta niyar sharara mata mari sai ya ji saukan mari a kumatunsa. Inna. "Yanzun kana nufin za ka daketa akan Balki?, lallai yau ka nuna min kai ba Ibrahim ɗina bane, saboda Ibrahim ɗina ba ragoh bane." Balkisu. "Yanzun kana nufin kyale ta za ka yi marin ka fa ta yi." Ibrahim. "Inna yanzun ni kika mara saboda wannan bagi dajiyar ƴar talaka?." Umma. "Ibrahim yau kaine ke kirana da ƴar talaka?, na gode sosai Allah ya saka da alkairi." Fita ta yi daga ɗakin, ɗakinta taje ta ɗauki mayafin ta tana fita A'ishah da Amina na kawowa. Amina. "Umman yara ina zuwa haka, ba dai tafiya za ki yi ba?." Umma. "Wallahi tafiya zan yi kuma ba zan dawo ba sai ya ne meni da kansa sannan zan dawo." A'ishah. "Haba aunty dama haka ne take so fa kenan kina nufin taci galaba akan ki." Umma. "A'ishah Amina ba galaba ta yi akaina ba kawai ina son in ni santa kaina da shi ne ." Amina. "Humm haka kika ga yafi maki." "Eh" "Toh shi ke nan ki tafi kawai". Tafiya ta yi A'ishah da Amina sai kuka suke yi. Amma Maryam Ma'aruf fa idan ya dawo me zamu ce ma sa. Maryam. "Dan Allah karki tura min shi, ya yi zaman shi in da kike, ga su Rashid da Rufa'i nan." RASHIDA BY SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️ WhatsApp number08084277827☎️ 14 📝 Ga su Rashid da Rufa'i nan sai ya zauna in da suke. Cikin kuka ta ja hanun Maryam tana cewa "Yanzun da gaske tafiya za ki yi, ki barni bayan kin san cewa kece ƙawata a gidan nan, amma duk da haka za ki tafi?." Cikin kuka ta janye hanunta tana cewa "Haba Amina ai ba mutuwa zan yi ba kuma zan dawo in sha Allah". "Haba aunty ya za kice za ki dawo ai tafiyar ce bama so, yanzun idan Ma'aruf ya nemi mahaifiyar shi me kike son a ce ma sa?." "A'ishah karki damu ai baiyi rashin uwa ba saboda ga mahaifiyar shi nan." Bata sa ke magana ba ta yi waje abinta. Fita tayi daga cikin gidan cikin sanɗa dan kar ƴan gidan su san fitar ta. Tana fita ta tare mai machin ta mai kwatancen gidan sai ƙofar gida, kuɗi ta biya mai machin ɗin ya yi tafiyar shi. "Assalamualaikum" "Waalaikimussalam" Oyoyo oyoyo Gwaggo sannu da zuwa, wasu ƴan yara ne su ke gaida ta. "Yauwa sannu ƴan albarka ina kabar ne?". "Gwaggo yana can yana bacci." "Ok toh ma sha Allah." "A a a ƴata sannu da zuwa, amma yana ganki da kaya niƙi niƙi haka ina zuwa?." "Mama ba komai kawai na kawo maki ziyara ne fah." "Toh shiga daga ciki dai ina zuwa." Kayan ta je ta ajiye sannan ta dawo tana cewa "Mama wai su Yaya nan kuwa?." "Eh lafiya dai." "Ba komai kawai na tambaya ne saboda na yi missing ɗin su ne sosai?." "Toh Allah yashirya min ke." ta faɗa cikin dariya. "Ina Ma'aruf ne?." "Yana can na barshi idan yazo baya barina na sa ke sosai." "Toh shi ke nan." Faɗa min meke faruwa ne Maryam na san zuwan nan naki ba a banza yake ba. Mama wallahi na gaji da wulaƙancin da Ibrahim yake min saboda gaba ki ɗaya baya sona baya ƙauna ta. Haba Maryam kin san ba a cikin hankalin shi yake ba sai kici gaba da hakuri har Allah ya yi ma sa sauƙin walahar nan. Ni kam yanzun sai dai na yi ma sa addu'ar shi a nan amma ba zan da wai ba sai yazo biko na da kan shi. Toh wannan cikin fa idan kika tashi haihuwa fa. Haihuwa ba yanzun ba sai nan da wata uku in sha Allah. Toh shi ke nan. Cikin sanyin jiki ta ce . "Mama meke damunki ne naga duk kin rame haka kamar ba ke ba wallahi?." "Ba komai lafiya ƙalau nake." "Haba Mama ki faɗa min dan Allah." "Maryam ina son ki riƙe mijinki tsakanin ki da Allah idan kika cuce ɗan mutune wallahi ban yafe ba ko bayan raina ne, kuma ki riƙe addu'a ban da wasa da ita yanzun ke ba ƙaramar yarinya bace, ki riƙe ibada ki riƙe karatun azkar safe da yamma kar ki bari maƙiya suyi nasara akan ki, ki riƙe Allah shine gatan ki shine mahaifiyar ki shine Mahaifin ki, sannan ki riƙa roƙon Allah ya shirya mana zuri'ar mu, ki kula da yaran ki sosai ki ɗaura su akan hanyar daidai kar kuɗi su ja ki ki bar yaranki su lallace." Cikin sanyin jiki take cewa "Mama in sha Allah zan yi duk abin da kika ce in sha Allahu ba zan ba ki kunya ba." "Maryam bana da lafiya sosai olsa ce ke damuna kuma taci ƙarfi na ban so, faɗa maki ba amma ba yanda na iya dole sai na faɗa maki." "Olsa Kuma mama me ya sa ba ki faɗa min ba bane, yanzun Mama idan kika mutu wallahi sai nafi kowa damuwa...." Bata ƙarasa ba saka makon kukan da ya ci ƙarfin ta. Ke kukan mi kike ne haka ce maki na yi ance mutuwa zan yi ne ehhe. A a amma .. Yi min shiru bana son Wata magana. Kiran sallah magarib aka yi hakan ya sa suka tashi zuwa yin sallar. BAYAN WATA UKU Maryam ce zaune a cikin daƙi Mama na a waje zaune ita ma . Cikin ta ne ya murɗa mata sosai wani danshi danshi taji aiko tana dubawa taga jini na bin kasan ƙafarta. Cije baki ta shiga yi saboda a zabar da take ji cikin ikon Allah ta haihu lafiya. Mama jin kukan jariri ya sa ta tasowa ɗakin ta shiga jariri tagani cikin murna ta furta cewa "Ma sha Allah Allah na gode ma." Dubawa ta yi sai taga ƴa mace ce aka haifa murna ba ƙadan ba ta ji . Gyarata Mama ta yi sosai da sosai sannan ta gyara Umma . "Kira ƴan gidan can ki faɗa masu haihuwar." Bangaren Ibrahim kuwa komai yake yi sai yaga Maryam idan bacci yake yi ita yake gani abin ya dame shi ba kaɗan ba ya je wajen Amina yana sanne kai ya ce "Aunty dan Allah ki taimaka min ki dawo min da matata wallahi ina son ta kamar raina amma wani lokacin sai naji na tsane ta ba kaɗan ba." RASHIDA BY SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️ WhatsApp number08084277827☎️ 15 📝 Shiryawa su Amina suka yi sai ga Ma'aruf, Rashid, Rufa'i sun dawo daga school. "Ma'aruf Mama ina zuwa naga kin shirya haka?, kuma ni Umma nake son na gani Mama". "Gidan Ummarku zamu je ita ta haihu dan haka je ka shirya mu tafi Rufa'i je ka shirya kai ma." Toh suka ce sannan suka je shiryawa . Rashid ya ji daɗi sosai da a kace Ummarshi ta haihu sai ji ya matsu baiga yarinyar ba. Fitowa suka yi sai gidan su Maryam Rashid yariga kowa shiga gidan sallama kawai ya yi sai cikin daɗi da yake ta saba zuwa dashi . Yana shiga ya tarar da yarinya kwance sai bacci take hankali ƙwance kafe ta da idanu ya yi haka kawai ya ji yana son yarinyar fiye da su A'ishah. "Umma yarinyar nan akwai kyau ji bakinta jawur kamar janbaki a ka saka mata, kuma ga ta fara ga ta kyakkyawa, kai ma sha Allah." "Hahaha kai Rashid wannan yabawan haka, ko kana son ta ne a baka ita har sai ka tashi aure." Hahaha kai shirme ke kam ko neman mu bazaki yi ba. "Ayya yi hakuri Maman yara wallahi ban kula da ku bane." "Wai ina kishiyar tawa ne naji shiru?." Cewar Inna "Da yake ba kya da ido ba ai ba za ki ga in da take ba ya cilla mata harara." "Kai ɗan baƙin rai wallahi ka kiyaye ni in ba haka ba sai na saɓule Yanzun ka ji min mai ƙatun kai." "Mtsww sai ki saɓule ni ɗin mai warin goro kawai." Kai Rashid ya isa haka . Toh ai saika bamu yarinyar ko, Inna ta faɗa tana shararar shi. "Ba zan bada ba sai ki yi ta ƙarfi ni wallahi kin saka min ciwon kai saboda wannan surutun naki mai bakin aku kawai." "Ga mai bakin aku nan zaune ba ni ba." Banza ya yi da ita saboda gaske kanshi ciwo yake ma sa ɗan wannan maganar da ya yi. Maryam ta kalli in da Inna ta nuna wa Rashid kawai sai taga Ibrahim yana kallon ta. "Umma nayi kewarki sosai dan Allah ki dawai gida." Yi ta yi kamar bata ji shiba. Ibrahim Maryam dan Allah ina son magana da ke idan babu damuwa. Bana da lokacin magana da wanda ba ya sona kuma baya ƙaunata. "Haba Maryam cikin yara muke fa, kuma yanzun sun mallaki hankalin kansu, ba yara bane. Cewar Amina Yi hakuri Maryam yanzun ya fara jin sauƙi, saboda addu'ar mu ta taimakon Allah dan Allah ki saurare shi. "Toh" kawai ta ce dan ko ba komai ta ɗauki Inna a matsayin Uwa. Tashi suka yi dan basu waje su gana. "Dan Allah Maryam ki yi hakuri wallahi bana cikin hankalin kaina, kema kin sani dan Allah ki yi hakuri wallahi idan ina tare da ita, duk abin da take so shine zan yi, ko Inna bata isa ta hanani abin da ta ce ba, nima ban san meye dalili ba." Ba komai amma ba zan koma sai anyi suna . Kamar ya sai anyi suna gaskiya a gidan Ubanta za'ayi mata taro. Toh shi ke nan ba damuwa. Anjima nake son ki koma ni zanzo na ɗauke ki. Toh sai nayi shawara da Mama. "Assalamualaikum wai har yanzun baku gama maganar ba, tafiya muke son yi amma kazo ka yi zaune". Mun gama mutafi kawai sai anjima Umman yara. "Toh". "Umma karki bari kowa ya ɗauke sai ni." Cewar Rashid. Umma "Toh Rashid ba wanda zai ɗaukar maka matarka ." Dariya kowa yasa ka har da Mamar Maryam. Dare nayi aka zo ɗaukar Maryam sai gidan su Ibrahim murna wajen Rashid, Ma'aruf, Rufa'i, ba a magana Ita ma Maryam ta ji daɗi saboda ko ba komai mijinta ya yo bikonta Kuma taji daɗi sosai. Rashid ya ɗauke jaririyar wai ba mai ɗaukar ta sai shi Ma'aruf da Rufa'i har sun ga ji da magana sunyi shiru. "Kai ɗan rainin hankali ba ni ita na riƙa dan Uwarka, zoka riƙe yarinya kace ba mai amsar ta sai kai, dan iskanci da samun waje". cewar Amina "Haba dan Allah Maman yara ki barshi har ya gana da matarshi mana, kin taƙurawa yaro ke akwai mai rabaki da Yaya ne, da za ki raba shi da tashi." "Wallahi bana ciki da bakin ki, Allah ya tsere ta da auran wannan, ɗan baƙin rain." "Ai kam dai dan baza ta aura min miji ba, salon ya ganta yarinya ni tsohowa ya ce ita yake so ba ni ba, toh ba zai yiwu ba tam." "Mtsww wai ke kam mai zan yi da ke ne kina warin goro ji bakin ki." Kai ya isheka haka idan nasake jin maganar nan sai ranka ya ɓaci, wanda bai san wasa ba." BAYAN SATI ƊAYA Anyi suna yarinya ta ci sunan Inna wato Rashida su na kiranta da Ummi. Su A'ishah kam har sun saba da rashin ɗaukar da Rashid baya yi amma kullum yana riƙe da Ummi sun yi kuka har sun daina. Idan fita ya yi sai ya siyowa Ummi chocolate da Sweet sai su Mama sunyi da gaske sannan su samarwa su Fatima. Ummi ta saba da Rashid sosai. "Idan mutum baya sona toh dole yaso takwarata kuma sai najawa mutum aji sannan zan ba shi auranta ehhee." cewar Inna "Wai ni kam ba Kya da zuciya ne ki kyale ni mana karki sakamin ciwon kai Please." Aiko kan shiya daɗe bai cire ba dan rainin hankalin kawai." "Haba Kaka me ya sa kullum sai kin ɓatawa Abokina rai ne." Ma'aruf ya faɗa Kaci gidan ku mai kai kamar na mangoro. Hahaha dama mangoro na da kai ne . Haka suka sa ka Inna a gaba su na dariyar ta. "Kai Rashid bana son rashin kunya ya zaku saka mana Inna a gaba kuna dariya, saboda rashin kunya ai ga Uwayenku nan baku saka su a ga ba kuna dariya ba, sai Inna da ku ka raina." cewar Muhammad mai shigowa ya ji abin da suke wa Inna Sai cewa ta yi "Ai kai ne sukewa ba ni ba saboda ni nafi ƙarfin su har mahaifan nasu." Harara Ma'aruf da Rashid suka aika mata lokaci goda. Ai sai dai idon mutum ya ya tsiyaye ehhe na faɗa maku. Rufa'i "Haba Inna wai ke kullum sai kin zagemu hankalin ki zai kwanta, mai warin goro kawai ji bakin ki duk ya yi jan goro." Ga mai warin goro nan zaune kai jama'a wai ba zakuwa yaranku magana ba kun min shiru haka kuna kallona . "Yi hakuri Inna Rashid, Rufa'i kaima ku yi wa mutane shiru yanzun ko sai na mutuncin ku." BAYAN SHEKARA BIYU Haka rayuwa ta ci gaba har tafiya zuwa London ta kama Abba da Daddy dan ƙarfafa officer ɗin su. Abba ya ce "Rashid idan muka je zan kira akai mana kai, saboda da Umman ku zan je sai ka zauna a nan." "No ba zai yiwu ba kawai ka bar shi idan ya isa zuwa sai yaje da kan shi, idan suma su na da ra'ayin zuwa can sai suje tare."cewar Daddy "Toh shi ke nan ba damuwa Yaya ki shirya dake zan je." "A a ni kam gaskiya ina nan ba in da zan je, kawai ka ɗau matar ka ku tafi wallahi na yafe ina tare da Maman yara." "Amma dan Allah ka ce kar taje da Fatima ta ta barta a nan kawai." "Eh gaskiya ne tun da yanzun ba Nono suke shaba."cewar Mama "Toh shi ke nan." Ummi tana ta jagol jagolo abin ta sai daɗi take sha a hannun Rashid. Su Fatima Ma'aruf sun fara jan su a jiki idan suka fita sai son siyo masu abu ko bai kai na Ummi yawa ba. Yarinyar tasha gata da musamman dau su A'ishah basu samu gatar ta ba Ummi. Masu tafiya sun shirya komai yau ne ranar tafiyar su. Rashid, Ma'aruf, Rufa'i, duk kujini da idon rahama, kamin mu dawo ku tabbatar da kun fitar da matar aure, dan yanzun ba zamu dawo ba sai nan da shekara goma ,ku kam kun kai ashirin da hayi sama. Rufa'i ya sakawa Daddy dariya, "Daddy duka duka yaushe muka tashi da har ake mana zancen aure." "Idan na dawo baku fitar da matar aure ba, duk wacce nasa ma ita zan haɗa ku da ita tam, a sannan ne zaku tabbatar da cewa kun isa aure." Rashid "Daddy Yi hakuri amma karatun mu fa?, ni gaskiya bana son karatu a Nigeria nafi son India ko London, saboda ga baki ɗaya na gaji da wannan makarantar wallahi, kuma maganar aure gaskiya Daddy ba Yanzun ba." Abba "Ok toh shi ke nan ba damuwa sai ka tashi kamin magana." "Amma Ibrahim kana da hankali ya zan kai shi India karatu ina laifin London ɗin, amma India basa da tarbiyya ko kaɗan." Da India, da London, da Nigeria, duk kabar wa Allah zaɓi shi zai shirya mana su ba dibarar mu ba dan haka kabar shi ya yi karatun shi a in da yake so." RASHIDA SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️ WhatsApp number08084277827 ☎️ 19 "Assalamualaikum" "Waalaikumussalam" "Kaka Barka da safiya kintashi lpy." "Lafiya lau masu ƙantan kanu yau kam albarka kuke so shine ku ka zo gaida ni?." "Wai Kaka me ya sa bakin ki baya gajiya da cin goro ne?, ɗakin nan sai wari yake. Rashid ya faɗa yana yamutsan fuska "Toh sannu mai hancin jin wari sai in uwayen ka ne da uban nan ka ke warin ba ni ba." "Kai ku tashi mu tafi zanyi amai wannan warin haka." Ya faɗa yana miƙewa "Ka kiyaye ni fa Rashida {Rashid take nufi} wallahi zan ci gidan ku idan nasake jin kana cemin warin goro nake." Dariya Rashid ya yi saboda sosai Kaka ke saka shi nishaɗi idan suna faɗan su na kaka da jika, sai dai shi baya juriyar surutu da yawa sai kain shi ya yi ciwo. "Au dariya kuke min dan kun raina ni." "Kai Kaka wane mu ai baza mu maki dariya ba sai dai muyi maki kishiya, har gayu mai Sabon jini ba tsoho ba." "Rufa'i kaci gidan ku ɗan naima mai kan saniya ai daga ni baƙari, ku tashi ku bar ɗakin nan ku naci mutuncin ku yanzun." Dariya Rashid ya yi ya ce "Kaka sai anjima zan kawo maki baccin rana a ɗakin ki." "Bana so kai da ku mutsi mutum ba zai yi idan kana bacci har sai ka tashi, ni kam ba zan mutu ba da raina ehhee." Tafiyar su suka yi sai ɗakin Umman su kwance suka tarar da ita kamar mai bacci kuma ba bacci take ba. Sallama suka yi mata shiru sake sallamar suka yi sai lokacin ta amsa . "Umma meke damunki ne naganki haka kamar ba Kya jin daɗi?." "Eh Rashid bana jin daɗi ne amma yanzun Alhamdulillahi." "Umma ki fitar da komai a ranki dan Allah kar ki cutar mana da kan ki." A jiyar zuciya ta sauƙe mai nauyin gaske. "Ai ko da mutuwa na yi kuna da mahaifiya a cikin gidan nan, kuma na san zata aurar da Ummi a hannun miji na gari." "Umma dan Allah ki daina maganar mutuwar nan, wallahi ba daɗi in sha Allah kina tare da mu har tsufa." "Rashid abu ɗaya ne zaku min ku yi aure naga matan ku, ko banga yaranku ba ba damuwa." "Haba Umma ki daina zancen mutuwa dan Allah in sha Allah muna tare sai kinga jikokin ki." "Toh Allah ya sa." "Ameen ya Allah." Rashid kan gadon Umma ya haye abin shi ya yi kwanciyar shi abin shi. "Kai ɗan iska ya zaka kwanta bayan kasan in da muka yi." "Ba in da zanje ku yi tafiyar ku." "Wallahi baka isa ba sai kaje." "Ina zaku je ne haka toh?." "Umma in da yarinyar da Momy ta ce naje ne zan je." "Ah toh ma sha Allah Allah na gode maka, yi hakuri Rashid ka rikaye shi yau kawai." "Toh shi ke nan Umma zan je amma dan kin sa baki ne." "Umma na gode da wallahi ba zan je ba." "Toh ku tashi kuje ku shirya amma manyan kaya zaku saka har kai ma Rashid." "Umma manyan kaya kuma gaskiya ba zan iya saka su ba." "Sai ka saka su ko yau ɗinnan dan ubanka." "Yi hakuri Umma zan saka amma zan zo ki kyara min idan ban saka dai-dai ba." "Toh shi ke nan jeki sai kun fito." "Toh kawai suka ce." Shiryawa suka yi ko wanne ya yi kyau sosai har dai Rashid kam. Shadda ce mai ɗinkin zamani fara ce sosai taji ado sosai ya gyara sajen nan nashi gashin kan shi ya kwanta kamar na turawa hasken nan ya ƙara fitowa sosai . "Wai Aboki ko kaine zamu riƙa ai sai haka wannan wankan." "Mtsww aikin ba zan kawai." Fita ya yi dole suka bi bayan shi . Ɗakin Umma yaje ya ce ta gyara ma sa. Zama Umma ta yi ta kama rigar shi ta saka ma sa biton, sannan ta ɗauko mayukan da take shafawa gashin ta, ta sakar ma sa sai sheƙi yake, fauda fara ta goga ma sa ma sha Allah, sai kace mace ba ƙaramin kyau ya yi ba, turaruka ta fesa ma sa har kala goma ba Rashid ba har su Ma'aruf ƙamshin turarin suke yi . Ma'aruf Ya ce "Umma rikiya ne zamu yi fa ba zance zai je ba amma sai wani gyara shi kike yi." "Ina ruwan ka bana son saka ido fa." Fita suka yi sai gidan su Nafisa hon suka shiga yi sai da ga baya mai gadin gidan ya fito yana tambayar waye suka faɗa ma sa sannan ya shiga gidan ya sanarda matan gidan suka ce su shigo. Komawa ya yi ya ce ance ku shiga falo tana zuwa . Rashid ya ce ba in da zai je su tafi idan ta fito sai su kira shi amma ba zai jira mace ba sai dai ta jira shi. Ba yanda suka iya dole haka aka yi sun jima kaminta fito tafiya suka ji ta kun takalmin ta. Ko sallama babu haka kawai ta faɗo "Sannu ku da zuwa na barku ku ɗaya dan Allah ku yi hakuri." Ma'aruf ya ce "Ba komai amma baki iya sallama bane naji kamar baki yi." "Ayya na manta ne toh barana koma sai nayi sallamar." Komawa ta yi sannan ta yi sallamar suka amsa sai ta shigo. "Amma ban gane wane ne angon nawa ba saboda duk kan ku kyakkyawa ne." "Ga angon ki nan ba ni bane ni ɗan rikiya ne." "Toh shi ke nan." "Assalamualaikum" "Waalaikimussalam" "Ina wunin ku?." "Lafiya ƙalau." "Ga ruwa ku sha mun barku ba abin taɓawa." "Ai ba matsala mun gode sosai." Ma'aruf ya faɗa yana kallon ta "Baku faɗa mana sunan ku ba ko amaryar mu." "Ayya sunana Nafisat sunan ƙawata Ruƙayyat." "Allah sarki suna mai daɗi Ruƙayyat." Saura ku, ku faɗa mana sunan ku "Ok sunana Ma'aruf Abokina ma sunan shi Rufa'i sannan akwai wani Abokin mu a waje sunan shi Rashid." "Amma me ya sa bai shigo ba?." "Zai shigo yana waya ne." "Kira shi mana Aboki ko mu bar wajen nan yanzun wallahi." Rufa'i ya faɗa dan shi yaushe take ba shi Kiran shi Ma'aruf ya yi ya ce ga shi nan shigowa. Ya kusa kwashe minti 30 bai shigo ba sai daga ba ya ƙamshin turarin shi ya nuna masu alamar ga shi nan zuwa. "Assalamualaikum." "Waalaikamussalam" "Ina wuni ranka ya daɗe?." Shiru ba amsa . "Ina wuni Yaya Rashid?." "Lafiya." "Yakike?." "Lafiya ƙalau." Kafe shi da idanuwa Nafisa ta yi shiko yana ji a jikin shi ana kallon shi team ne a gaban shi hannun ya sa ya ɗauki kofin kamar sha zai yi sai ya zuba mata shi a idanuwanta Aiko ihu ta hauyi ba Rufa'i har Ma'aruf duk sun ruɗe amma shi kam ko a jikin shi. Mamar ta ce ta fito da gudu tana tambayar me ya sa Meta ne?. Rashid har yanzun yana zaune abin shi sai danna waya yake yi. Mamar Nafisa ta ce "wai me ya sa Meta ne ina magana kun min shiru?." "Yanzun mu kai ta asibiti please." "Abokina Dan Allah ka duba min ita ka taimaka min."Rufa'i ya faɗa "Wallahi ba zan taɓi wannan abin ba kuma tafiya zan yi, idan ku ka gama ku tari abin hawa." Haka ko ya yi tafiyar shi ya yi kan hanyar ta zuwa gida tsallake titi ya hangi Fatima da A'ishah har da Ummi. Parking ya yi ya tsallaka titin da ƙafa yana zuwa ya ji Ummi ta ce "Ai kai ka ɗaine ba ƙari sauran maza duk mata ne tana dariya sosai." Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci fuskar nan kamar wani zaki haka ya tunkari saurayin . Saurayin na tsaye kawai ya ji an taɓa shi . "Lafiya dai malam?." Saurayin ya tambaya. Naushi Rashid ya aikawa saurayin Fatima kuka take yi sosai "Yaya dan Allah ka yi hakuri wallahi ba saurayin ta bane, saurayina ne dan Allah ka yi hakuri." Yana huci yana ƙari ran maza yaɓaci . "Me ya sa naji tana kiran shi da shi ka ɗaine dan iskanci, kema zamu haɗu a gidan, ku wuce mu je gidan ko sai na ɓallaku anan." Mamaki ya cika cikin Ummi toh akan mi zai yi faɗa akan nace shi ka ɗaine toh ina ruwan shi. Shiga motar suka yi su duka a baya ya ce tun da Driving sune ba. Fatima ta fita ta dawo gaba harara ya cilla mata dole ta fita suka ce Ummi ta koma gaba, fita ta yi ta zauna jan motar ya yi a tsiyace da sauri Ummi ta faɗa jikin shi tana kuka tana faɗin "Dan Allah Yaya ka yi hakuri ban yi maka laifin komai ba, dan Allah ka rage gudu wallahi tsoro nake ji." Ƙara gudun motar ya yi saura kaɗan ya buge mai machin. Ƙara riƙe shi ta yi sosai tana magiya amma a banza, sai da suka shiga kwanar gidan su sannan ya rage gudu. Hon ya yi mai gaɗi ya ɓude gidan a guje ya shiga da motar a cikin gidan saura ƙiris ya taka ƙafar mai gadi. Parking ya yi a wajen parking lot su Fatima a guje suka fita a motar, kamin ta fita tuni ya sa kawa motar key jan marfin motar ta yi da niyar buɗewa, amma ta ji shi rufe duban shi ta yi tana kuka har da majina. "Waye shi wancan ɗan iskan yaron?." "Yaya wallahi saurayin Fatima ne." "Za ki faɗa min gaskiya ko sai na ɓallaki a cikin motar nan." "Wallahi Yaya saurayin Fatima." A jiyar zuciya ya sauƙe mai nauyin gaske har Ummi sai da taji. "Toh ki kiyaye idan ba haka ba, toh wallahi sai na ɓallaki idan na sake ganin ki da wani saurayin." "Yaya bana da saurayi fa kuma ba mai sona ba mai kulani." "Akwai masu sonki kawai su nuna ne basa iyawa, saboda haka idan kika kula so wallahi wallahi wallahi kin ji na rantse ko sai na rabaki da kowaye." "Toh ba zan kula kowa ba wallahi dan Allah ka ɓuɗe min na fita." "Cinye ki zan yi ne da kika matsu kibar motar?." "A a Yaya yi hakuri." Buɗe mata motar ya yi da sauri ta ɓude zata fita taji an riƙe mata mayafi, da sauri ta kai duban ta gareshi wani kallo ya ke mata da ita ma kan ta bata san kallon mene ne ba. "Yaya dan Allah ka sake ni wallahi fitsari nake ji." "Yi hakuri jeki sai mun haɗu." "Toh ." RASHIDA Sha'awa marubuciya diggi ✍️ number08084277827 20 Fita ta yi daga motar saboda ga ba ki ɗaya ta kasa gane me maganganun shi ke nufi. Tana shiga gidan su Fatima suka saka mata dariya suna faɗan . "Wai me Yaya ke nufi ko dai ko dai?, hummm da abin yaba da citta🤪." "Ko dai ko dai mii zonan dan Ubanki Fatima." Suka ji an faɗa daga bayan su aii da gudu Ummi ta shige ɗakin Mama. Murmushi Rashid ya yi saboda ba ƙaramin dariya ta ba shi ba. Mama na zaune ta ji mutum ya faɗa kanta da sauri da ta shi yana salati. "Ummi mai ke faruwa ne haka?, ke da waye kuma haka?, ki faɗa min mana, duk lokaci ɗaya ta yi ma ta waɗan nan tambayoyin. Shiru Ummi ta yi saboda bata da amsar tambayoyin nan na Mama. Rashid ya nufi in da Fatima da A'ishah suke ai su na ganin haka suka rugu a guje sai ɗakin Mama. "Ashe ƙaryar iskanci kuke yi da kun tsaya." "Bana son ta mutu amma ina son a haukatar min da ita, saboda matar ta isheni wallahi ga yaran nan duk ita suke so, sai abin da ta ce suke yi." Mommy ce ke waya da alama da Hajara ta ke wayar. "Hahaha kar ki damu ba kince tana da ciwon zuciya ba, toh a nan ne zamu samu abin da muke so." "Toh shi ke nan nawa zan tura miki yanzun, dan kin san saunan can ya rage sakin hanu." "Ba komai ki tura ko nawa ne ma, zan ma sa bayani, amma dole ne wani lokacin kije da kanki." "Eh nima ina son yin hakan amma ki bari zamu yi magana da ga baya." "Toh shi ke nan sai anjima." "Wai mai ke faruwa ne?, na ganku hakan kamar an jeho min ku." "Mama ba komai kawai wulaƙanci suke ji da shi wallahi." "Toh ina kayan da ku ka siyo mana ne?." "Mama wallahi Yaya ne ya koro mu, wai har da kiran idan ya sa ke ginin mu da samari sai ya ɓallamu." "Ai dama na san ba zai wuce kan shi ba, saboda kullum shine ke takura maku a gidan nan." "Wallahi kam Mama haka ne." "Assalamualaikum." "Waalaikimussalam" "Ina wuni Mama?." "Lafiya" "Mama dama so na ke mu yi wata magana dake dan Allah." "Ina mahaifiyarka kaje can ku yi maganar." "Haba Mama wannan maganar ai sirrin ne tsakani na da ke." "Kai ku bar ɗakin nan ku ta shi ko na zane ku yanzun." "Allah yabaka hakuri Yaya" cewar A'ishah. "Babu in da zaku je kuna nan." "Shi ke nan Mama sai anjima." "Zan je wajen Ummana kuma za ta kulani , in sha Allah za ta fahimce ni" cikin ɓacin rai ya bar ɗakin. "Mama zan je na yi wanka." "Ke kun manta su Yaya Rufa'i sun je zance kuwa." Gaban A'ishah sai da ya buga sosai. "Laaaa wallahi na manta mu je mu yi wanka, sai mu je su bamu labarin" Ummi ta faɗa tana dariya. "A'ishah mene ne naji kinyi shiru lafiya dai, ko har yanzun ba ki hakura bane" cewar Mama. Dariya da bata kai ciki ba A'ishah ta yi dan ɓuye abin da ke ranta. "Ba komai ai na hakura Mama, yanzun a matsayin Yayana nake kallon shi, ba saurayina ba." "Toh Allah ya maku albarka." "Ameen ya Allah 🤲". Da dare ana zaune sai Ummi ta kalli Fatima da A'ishah suka yi dariya sannan Ummi ta ce . "Yaya Ma'aruf ku bamu labarin auntyn mu mana dan Allah, tun ɗazun sai rabon ido muke amma kun yi shiru." "Ai nima tun ɗazun su na ke jira amma sun yi min shiru, ko dai baku da gaskiya ne" Umma ke faɗar maganar. Hahaha 🤣 dariya suke yi idan suka kalli Rashid, dan ba ƙaramin dariya ya basu ba lokacin. Ganin rashin mutunci da suke sun ma sa ne ya sa ya kaima Rufa'i duka. "Wai me ya sa ku ke ma sa dariya ne haka?." "Umma bari mu baku labarin zuwan mu zance", hahaha 🤣 suna maganar suna dariya. Labari suka ba su kabba abin da suka rage masu . Dariya suka shiga yi har Mama sai da tadara saboda abin da Rashid ya tsiyanta a gidan. Ummi kan dariya har wani hawaye take yi. Umma ta ce. "Yanzun Rashid abin da ka yi a gidan mutane kenan, ai dana sa ni da ban barka kaje ba", ta faɗa tana dariya. Kiran wayar Ma'aruf aka yi amma yana dubawa ya ga sabuwar number ɗagawa ya yi sai ya ce "waye?". Tacan bangaren aka ce "Ruƙayyat ce." Ta shi ya yi niyar yi amma Ummi ta dafe shi wai ba in da zai je sai dai ya yi wayar a gaban su. "Hello Rayyan yakake ina gida idan na fita zan kira ka." Dariya suka saka ma sa wai Rayyan. Rufa'i ya yiwa Ummi alama da ido ta amshe wayar da mace yake waya, iko da sauri ta amshe wayar. "Hello auntymu yakike ya gida ya su Umma." Ma'aruf ya ce. "Amma dai Wallahi baka da mutunci Rufa'i, yanzun ga shi ko magana bamu yi amma ka wani zo sai faɗawa mutane ku ke yi." Abba ne da Daddy suka shigo dama su suke jira dan su ci abinci. "Ah ah ƴar Daddy dariya mi ake yi haka ne?, ko waya ce ake yi da sirikina?." Dariya ta yi sosai sannan ta faɗi cewa. "Ai budurwar Yaya ce." "Toh zu mu je dainnin." "Wace ce budurwar ta shi, idan dai har ma ta min ba toh ba zai aure ta ba, kuma sai Rufa'i ya yi aure ko shima zai yi." "Abin da ba zai yiwu ba kenan dukan su rana ɗaya ne zan aurar da su, amma kai Rashid wace ce yarinyar da kake so saboda rana ɗaya ne zan aurar da ku." Ƙasa da kai kawai Rashid ya yi saboda ya san ba wacce yake so. "Ai Rashid kunya ne da shi, shi ya sa bai faɗa maku ba, amma jiya ya same ni ya faɗa min cewa...... Yana son Ummi da aure." Ba Ummi har Rashid sai da maganar ta girgiza shi dan bai yi tunan ko zata ɓollo ma sa ta wannan hanyar ba. Ummi mutuwar zaune ta yi saboda ko ka ɗan bata taɓa tunanin wannan maganar Mommy za ta faɗa ba. Rashid cikin hikima da ilimi ya faɗi. "Eh haka ne ina son Ummi saboda ai ko ba komai akwai aure a tsakanin mu, kuma in sha Allah sai mun yi nasara a kan maƙiyan mu, kuma ina son ku sa ni duk wanda ya sake yiwa matata wani abun a cikin gidan nan ko na sa ni, ko ban sa ni, sai na ɗau mummunan mataki akan shi yanzun Ummi tawa ce ni ka ɗai." Dariya Mommy ta yi . "Ai ka kwantar da hankalin ka matar ka ce kai ɗaya ba mai so idan ba kai ba, kaima saboda ta zamar maka ƙurjin ƙafa ne." "Hahaha 🤣 Idan ba ki sa ni ba toh yau nake son ki sa ni, taimaka min kika yi saboda ina son ta, kawai yanda zan faɗa ma ta ne ban sa ni ba, amma yanzun ga shi kin taimaka min Mommy, a na son zuwa yawon bara da kurege, sai dai ana tsoron cizon sa." Wani irin faɗuwar gaba Mommy ta ji amma sai da dake. "Ai na san kana son ta, shi ya sa na faɗa amma kuma ka sa ni buhun gishiri ko gidan mahaukaci ya isa miya.." "Rashid ya Isa a bar maganar haka tun kan ya dawo Wani abin rikici" Umma ta faɗa. Ummi kam kuka kawai take yi dan ita ko kaɗan bata son auran Yaya Rashid. "Umma ki bar ta kawai ni nan naje nace ma ta ina son Ummi." "Kai ɗan iskan yaron ita ɗin ba mahaifiyarka bace?, da kike ma ta wulakancin." "Ni ba mahaifiyata bace Umma ce mahaifiyata ba ita ba, kuma na faɗa maka kaima idan kana wulakanta min mahaifiya na faɗa maka." "Kai ɗan Umma ya isa mahaifinka ne fa amma kake faɗa ma sa wannan maganar" Daddy ya faɗa. "Ai Yaya kai ka jamin duk wulakancin da yaronna ke min, kuma ƙaran takaici a kan wannan bagidajiyar matar." "Haba Abba Gaskiya ni na gaji da wannan kalmar taka, kai kullum abu ɗaya ko mene ne sai dai kace Umma ta yi shi, gaskiya na gaji da hakuri wallahi daga yanzun idan ka yi ma ta sai na rama ma ta, saboda ita ma ai matar kace," Ma'aruf ya faɗa a hasale. "Sannu mara kunya ina ruwanka da duk abin da yake min, kai ne yake ma ko ni, toh daga yau bana son ƙara jin maganar anan" Umma ta faɗa cikin faɗa. "Umma sai dai ki yi hakuri, amma lokacin da ba kyada mu ya yi miki, Yanzun ma kika damu kuma bai dena ba, gaskiya sai dai ki yi amma idan ya yi sai na rama miki." "Umman yara ki yi hakuri ki bar shi saboda ba zai yiwu ba ana wulakanta ki a gaban shi." "Haba Maman yara yanzun ke ce ke faɗan wannan maganar gaskiya ba dai dai bane." Abba ta shi ya yi, fita ya yi daga ɗakin wajen parking ya yi, jan mota ya yi sai waje yana fita ya ɗau hanya yana tafiya yana ganin wata mota na biye da shi, shan gaban shi suka yi, ai ba shiri ya yi parking fitowa suka yi daga motar su, suka buɗe ta shi motar fitar da shi, suka yi suka rufe ma sa fuska sai cikin daji, wani gida ne mai kyaun gaske ya haɗu sosai gidan ba za ka dare bane. Wani kyakkyawan saurayi ne san ye da fesmerk shima baƙi komai na shi baƙi ne. Kujera a ka a je ma sa ya zauna yana yiwa mutumen kallon banza. "Ku buɗe ma sa fuskar shi." Buɗe ma sa fuska suka yi, yana kallon in da mutumen yake ya ji gaban shi ya faɗi. "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un dan Allah ku min rai wallahi ban yi komai ba yanzun haka daga gidan nake." "Wani ɗaya daga cikin ƙattan ya kai ma sa duka a baki." "Kai bashar baka da hankali me ya sa ka dake shi?." "Allah ya huci zuciyarka ranka shi daɗe." "Kasan me ya sa nakawo ka anan?." "A a wallahi." "Toh saboda kana cin zaluncin ƴar uwar mu, kuma kana wulakanta ta da yaranta, saboda haka kana da zaɓi biyu zuwa uku." "Wane irin zaɓi ne wallahi zan yi." "Ka kira ɗaya daga cikin matan ka, ka ce musu anyi kidnapping ɗinka, sai ɗaya daga cikin su tazo sannan zamu sake ka." "Toh shi ke nan wallahi zan kira yanzun." Balkisu ya kira. "Balkisu dan Allah ki min rai wallahi ina cikin ta rshin hankali dan Allah ki zo ki fitar dani." "Wai me ke faruwa ne? kamin yanda zan gane." "Kidnapping ɗina aka yi sane suka ce sai matata ɗaya tazo sannan zasu sake ni." "Kutmar ubancan shine ka kira ni Wallahi ba in da zan je sai anjima idan sun iya su kashe ka ba ruwana." RASHIDAH Sha'awa marubuciya diggi ✍️✍️ WhatsApp number 08084277827 21 "Haba Hajara dan Allah ki taimaka min wallahi zasu kashe ni, ki yi hakuri ki taimaka min dan Allah." "Wallahi wallahi wallahi sai dai su kashe ka ba in da zan je."ɗiff ta yanke wayar. "Hahaha a she ma ba son ka take ba." "Dan Allah ku bari nakira ɗaya matata ku taimaka min." "Ok kirata ɗin." Kiran wayar Umma ya yi bugu biyu da ɗaga. "Maryam dan Allah ki taimaka min, wallahi anyi kidnapping ɗina, kuma sunce sai kunzo dan Allah ki taimaka min, kinji matata." "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, kidnapping fah kace?, toh yanzun kana ina ne?, wallahi zanzo, yanzun nan, kawai ka faɗa min kana ina?." Amshe wayar hannu shi suka yi sannan ɗaya daga cikin su wanda yake babba a gare su. "Yanzun wace ce matar ka ta fari daga cikin su?." "Maryam ce wallahi." "Ok idan na fahimta Hajara ce amarya ko?." "Eh ita ce." "Toh shi ke nan yanzun dai ka ji abin da ta faɗa ko?." "Eh wallahi na ji sosai ma." "Wace ce yanzun mai sonka da gaskiya, kuma wace ce wadda bata son dukiyar ka." "Wallahi nima ina son Maryam, kawai bana iya nuna ma ta ko ka ɗan, saboda ina jin wani iri a jikina, kuma idan Hajara ta ce na yi toh wallah ko mene ne sai na ai watar da shi, zan ji salama." "Ok yanzun ba abin da zan yi maka, amma ina son kariƙa yin addu'a, kariƙa karatun Alkur'ani mai girma, kariƙa yin azkar na safe da yamma, idan kana gida kariƙa yin karatun Alkur'ani, sannan idan ka fita ka saka shi a motar ka, in sha Allah za ka dawo dai dai, ba zamu yi maka komai ba, amma idan muka ji ko mu ka gani kana wulakantar da Maryam, toh wallahi wallahi wallahi sai munje har gidan ku mun kashe ka ka ji ba." "Eh ranka shidaɗe wallahi ba zan kara ba, kuma daga yau zan ci gaba da yin addu'ar, da karatun Alqur'ani, da azkar, da addu'a, na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi." "Ok ta shi ka nan ka je motar ka na nan a in da ka yi parking." "Toh na gode sosai, yana faɗar hakan ya ruga a guje kawai daji yake kaura sannan ya kai bakin titi, can ya hango motar shi, da gudu ya ƙarasa in da motar ta shi ya fige ta a ɗari, tunanin maganar da ɗan kidnapping ya faɗa ma sa karatun Alkur'ani mai girma ya kunna a motar wani gumi ya ji yana bin jikin shi duk in da tsikar jikin take zufa take fitarwa, da haka dai har ya isa gida ko parking bai yi dai dai ba ya fita daga motar. Kiran Rashid aka yi a waya murmushi ya yi sannan ya daga kiran. Toh wai su waye ƴan kidnapping ɗin nan ne kuma waye ya tura su dan ɗauke Abba duk ku biyu ni dan jin amsoshin ku, nice taku sha'awa Faruk marubuciya diggi ✍️✍️. Ina son ku masoya na kamar yanda ku ke sona 💞💞. Da gudu Abba ya shiga falon duk mutane na zaune, Inna da gudu ta nufi hanyar ɗakin ta, sai da Mama ta riƙe ta. "Haba Ibrahim wane irin wulaƙanci ne wannan ya za ka shigo mana falo ba ko sallama?." Dariya Ummi da Fatima har da A'ishah suka sakawa Kaka. Rashid da Ma'aruf har da Rufa'i dariya suke yi sosai Rufa'i ya ce Kaka dama kin iya gudu har haka, toh idan kika gudu ina za ki je ne, a she ke ba tsohowa bace, hahaha 🤣 suka kwashe da dariya. "Kai kunci gidanku ku yi mana shiru ko ku bar ɗakin nan", Daddy ya faɗa. "Allah yabaka hakuri Daddy mun daina" suka faɗa a tare. "Yaya wallahi kidnapping ɗina aka yi lokacin dana fita, Allah ya sa ba masu kashe mutane bane, da yanzun gawata za su kawo maku." "Gawarka kuma ana zaune ƙalau?." "Eh Yaya suka saka ni sai na kira matana sun je, amma abin mamaki na kira Hajara wai ita wallahi ba in da zata je, idan kashe ni za a yi sai dai a kashe ni, amma ba in da zata je." "Abban yara ka dawo ko gizo kike min, dan Allah idan kizo kake min ka daina bana so, ni mijina nake so ba kizo ba." "Nine nan Abba yaranku ban mutu ba, kuma ba zan mutu ba yanzun in sha Allah." "Alhamdulillah Allah na gode maka da ka fitar mana da mijinmu lafiya." "Abban Rufa'i sannu da dawowa ka fito kenan, wallahi har hankali ya ta shi nayi tunanin ko na rasaka." "Toh wallahi sai dai uwayenki su rasaki ba dai shi ba, kuma kowa lokacin shi yake jira idan ya mutu ke ki zauna gadin duniya." "Inna dan Allah ki daina magana bana son kina faɗan irin wannan maganar, ke fa uwace a gare su dan Allah ki daina." "Ba ruwana wallahi su kake in zoba ido ta wulakanta min ɗa, nifa ni na haife shi, amma duk tabi ta asirce min shi, sai yadda taga dama take yi." "Ke dallah yiwa mutane shiru kin cika mana kunne da surutu, ya kina fama da warin baki duk kin haukata falon nan da wari" Rashid ya faɗa. "Uban nan kane masu warin baki ba daini ba wallahi." "Kai kaci Uwarka ka ta shi ka bar nan kamin naci mutuncin ka" Mama ta faɗa. Dariya ya yi sannan "Allah ya ba ki hakuri Mama, na daina." Abba ya ce. "Dan Allah Maryam ki yi hakuri ki ya fe min, sunce ƴan uwanki ne, kuma sun san duk abin da nake miki dan Allah ki yi hakuri." "Ba komai Wallahi ai kai mijina ne, yanzun kai ne Uwata kai ne ubana Abban yara, dan haka na yafe maka, ba komai Allah ya yafe mana gaba ɗaya." "Ameen ya Allah 🤲," "Mommy ina maganar da muka yi dake ne ban ji Abba sunce komai ba" Rashid ya faɗa yana murmushi. "Dan Allah ka kyaleni bana son surutun nan Please." "Toh shi ke nan sai anjima zan tuna miki." Daddy ya ce. "Maryam shiga da shi ciki dan Allah dan naga yana bukatar kulawa sosai." "Toh Yaya." "Wallahi ni zan tafi da shi kamarya ta ɗauke shi bayan ɗakina yake ba nata ba." "Yi hakuri Balkisu jeki da shi toh." "Kuma ku ta shi ku je ku kwanta sai da safen ku." Kiran Rufa'i aka yi a waya yana dubawa ya ga Nafisat tsaki ya yi sannan ya ɗaga kiran. "Masoyi na barka da dare da fatan kana lafiya?." "Lafiya ƙalau wai me ya sa kika tsani yin sallama ne?." "Ayya yi hakuri na manta ne wallahi amma daga yau in sha Allah zan yi sallama." "Ok shi ke nan ba damuwa meke tafe da ke ne cikin daren nan." "Wallahi haka kawai na ji ba zan iya kwanciya ba sai na ji zazzaƙar muryar masoyina." "Ok toh shi ke nan yanzun ai kinji ko?." "A a ban gama ji ba gaskiya." Fisge wayar Ummi ta yi tana kiran. "Aunty ina wuni." "Lafiya ƙalau amma wace ce ke?." "Ni ƙanwar sa ce mana, amma nice amaryar da zai yi, bayan auran ku." "Kutmar ubancan dama kishiya yake son yi mini dan zalunci." "Eh mana nice ma nan shine nace yabani wayar dan mu saba da juna." Dariya su Mama ke yi sosai. "Ai wallahi bai isa ba sai dai a fasa auran nan, kuma gaskiya ba zan iya bar miki shi ba wallahi." Umma ta fisge wayar ta miƙa wa Rufa'i. "Zan kwanta sai da safe zan kiraki." "Dan Allah ka bani minti biyu please." "Ina jinki." "Dan Allah wacece wannan da muka yi wayar da ita?." "Ƙanwa ta ce." "Laaa Fatima ce amma take haukata ni." "Ba Fatima bace Ummi ce." "Ummi kuma yarinyar kishiyar Mommy, amma gaskiya matar nan bata kyautatawa Mommy, kullum fa Mommy ta ce sai da je gun boka, duk ta asirce ku." Umma mutuwar zaune ta yi saboda wayar a hashfirin ta ke. "Ke dallah yi min shiru wane ubanki ne, ko uwarki ya faɗa miki cewa Umma na zuwa gun boka." "Wallahi Mommy ka ce ta faɗa ba ni ba." "Toh gobe idan Allah ya kaimu ki shirya da safe zanzo na ɗauke ki, na kawo ki, gidan ki wuni, sannan za ki san mai biyan bokayen." "Toh shi ke nan sai gobe amma ban ji daɗin zagi da ka yi min ba" ɗiff ta yanke wayar. Shima sai daga baya ya ji ba daɗi. Haka kowa ya ta shi dan kwanciya. Rashid mamaki yake wai shi zai auri wannan mitsitsiyar yarinyar. Wata zuciyar ta ce ma sa ai tana da abin da kake so a jikinta sai mi dan ka aure ta. Da haka ya bar tunanin har bacci ya yi gaba da shi. "Wai yanzun ana nufin nace zan aure Yaya Rashid? toh me zanyi da shi wannan ɗan baƙin rai, gaskiya ba zai yiwu ba, bana son shi kuma ba zan so shi ba." Amma fa yana da halin kirki sai dai rayuwar sa ce bata min ba, haka dai tai ta tunanin ta, ba mai bata amsa. Kwanciya ta yi ita ma sai bacci. "Ke dai Hajara wallahi na haɗa yaran nan aure kinga dole aikin mu zai yi aikin akan shi", Balkisu ke faɗan hakan. "Hahaha ai dama ki kwantar da hankalin ne kawai ba za ki yi ba, amma ai wannan ɗan sauƙi ne." "Haka ne kam sai da safe bacci nake ji sosai saboda yau hanawa idona bacci nayi." "Toh shi ke nan sai da safe." WA SHE GARI Kowa ya fito dan cin abinci, kowa dainnin tebur ya nufa. Mama da Umma kujerar su na kallon juna, Momy da Ma'aruf suma haka sai A'ishah da Rufa'i, sai Rashid da Ummi, Abba da Daddy. Mommy ta kalli Rashid ta yi murmushi. Shima murmushin ya yi ma ta dan ya san da magana a bakin ta. Gyaran murya Mommy ta yi sannan ta ce. "Yaya Muhammad dama Rashid ne ya ce wai dan Allah ku yi ma sa aure da wuri, wai wallahi ya matsu bai yi auran ba, amma nace ma sa ya bari sai a haɗe dana ƴan uwansa gabaki ɗaya." "Toh pah Rashid dama aure kake so amma ba ka faɗa ba tun da sai yanzun, ai sai ka citar da kanka." Mama da Umma sun san ƙarya ne takewa Rashid amma suka yi shiru dan jin abin da zai faɗa. "Daddy ai naga aure ba haramun bane kuma dole duk namiji zai buƙaci yin sa, dan nima na buƙata ai ba laifi bane." "Toh shi ke nan zamu saka ranar nan ba da jimawa ba in sha Allah kaima Ma'aruf ka shirya har ma kai Rufa'i." "A a su nake ayi na Rufa'i kamin nasu." "Eh dayake ke ce uban shi ba ai dole za ki sanar damu abin da ya dace da su." Dariya Rashid ya yi sannan ya ce . "Abba kai ba za ka ce komai ba ne ka yi shiru ko duk abin da Mommy ta ce shine za ka bi." "Ai dolen shi saboda shi ya san wacece Balkisu saura kai." "Kai Rashid ko ba a son ka, Allah ya sa kai aka fara haifuwa, idan ma ba ka yi kudi ba, ka san dangi" Rashid ya faɗa yana dariya. "Haka dai ya kamata, mai gona ya kori biri da kan sa, Rashid kamin ƙarami da sa in sa, saboda a tafin hannun na katashi, amma idan za ka iya ja dani bismillah ka fili ga mai doki." "Idan babba bai ji kunyar hawan jakki ba, jakki ba zai kunyar kada shi ba, kuma mu zuba mu gani ni da ke Mommy." "Rashid ya isa haka mahaifiyar ka ce fa." "Ga mahaifiya ta nan zaune, wannan sai dai sharan mahaifa ba dai mahaifiya ba." "Rashid nace ya isa kabar wannan maganar haka nan ta isa ka ji ni Ko?." "Allah ya ba ki hakuri yake mahaifiyata na daina, ba zan sake magana ba sai in ke ce kika ce nayi." "Toh shi ke nan, ku ta shi zuwa aikin ku musamman ma kai Rashid mai aikin likita, amma kana wasa da aikin naka." "Ummana yau zan je aiki ai in sha Allah, kawai addu'a nake son ki yi min dan maƙiya suna kallona." "Toh wacece maƙiyar taka ba dai ni ba wallahi dan ka san karmami, kaikai da dussa duk arzikin gero ne." "Sanadi ba ya kadan an kashe giwa da sanda, mai zurfin ido tun da wuri ya ke fara barci. Rashid ya faɗa. Ummana sai na dawo zan je asibiti yau sai na dawo."cewar Rashid "Toh ta shi zuwa sai kun dawo." "Yaya dan Allah ka siyo min alawa"Ummi ta faɗawa Ma'aruf. "Ba ki da aiki sai shan zaƙi Ummi kuma kinfi kowa sannan ilar shi." "Eh dai naji kawai ka siyo min alawar." RASHIDA Sha'awanatu Faruk diggi diggi ✍️ WhatsApp number 08084277827☎️ 22 "Mama kin ji abin da take faɗa dai ko?." "Eh naji kawai ka siyo ma ta ba ruwan ka ." "Idan ba ka ta shi ba na yi tafiya ta, dan iskanci ka na makarar da mutane, da surutun nan naka na tsiya." "Mu je to ɗan iska kawai." Tsaki ya yi sannan ya yi tafiyar shi, Mama da kallon ta bi shi har ya ɓacewa ganinta. "Lafiya wai? Kike kallon yarona haka, kuma kin ƙi yi ma sa magana, ai dacewa ya yi kina magana da shi, saboda dole akwai maganar da ba zai iya faɗa min ita ba, amma ke zai iya faɗa miki ita, dan Allah ki rage wannan abin, ki riƙa yin magana da shi kina tambayar matsalar shi, yanzun kin ga Balkisu ta saka shi a gaba dole yana da maganar da zai faɗa miki akai, dan Allah ki zauna ki tambaye meke damunshi." "To shi ke nan amma....." "Dakata dan Allah kar ki ce komai dan Allah kawai ki tambaye abin da ke damunshi, saboda ni na tambaye shi amma ya ce ba komai, kuma ba da gaske yake ba, dan na san idan yana cikin ɓacin rai, kuma na san farin cikin shi." "Hummmm toh na ji idan ya dawo zan tambaye shi." "Dan Allah Maman yara ki taimaka ki yi ma sa magana, sannan maganar auren shi da Ummi, idan ba ya so kar ki saka shi dole dan Allah, dan wallahi na ga kamar ba ya son ta." Da haka suka cigaba da magana, suna cikin magana sai ga Balkisu ta na taunar cingam, ta na musu kallon banza, zama ta yi kusa da Umma ta na dannar hanci, ta na yamutsan fuska. "Toh pah Balkisu yau wari kike ji ne?, naganki ki na dannar hanci ko kin sa ma mana baby ne", Mama ta faɗa amma ta san abin da take nufi kawai ta fakaice ta hanyar wannan tambayar. "Gaskiya yau falon nan ba daɗi kamar ba ayi shara ba, sai wari yake ko dai masu warin ne a zaune a falon." Umma dai shiru ta yi ta na kallon sarautar Allah yau wai ita ake cewa mai wari to warin mi take yi?, ko dai wulaƙancinne yazo da haka. "Haba Momy ke kullum sai takura rayuwar Umma kike, kuma Umma ba ruwan ta dake, amma kullum sai kin tsokaneta, kuma ta yi Magana Abba yabi bayanki ya ce ita ce mara gaskiya, ba yan kuma ita ce mai gaskiyar", Fatima ta faɗa cikin takaicin samun mahaifiya irin wannan. "Fatima kar na sake jin maganar ki a nan, idan ba haka ba sai na saɓa miki", Umma ta faɗa dan ba garma ba ne yarinya ƙarama tana yiwa iyayenta rashin ƙunya ko da mahaukaciya ce tun da ta haife ta ai ta zama mahaifiyar ta." "Amma Umma..." "Bana son jin komai daga gare ki, kuma ku bar nan kamin naci mutuncin ku." "Lailahailallahu Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, yanzun Fatima uwar wata tafi ni kike nufi ko mi?, ni za ki dubi idona kina faɗa min cewa wai ba ruwanta dani, sai dai ni ke neman ta rigima." "Maryam gaskiyar maganar Fatima ce tun ta shin su har yanzun ba wanda ya ji kina neman rigima da ita, sai dai ita ta nemeki, sannan kuma ko a gaban yara sai ta nuna halin ta, ya za ayi ƴaranta su ji daɗi kullum sai dai a ce mahaifiyar ku ce ba tada gaskiya, ai wannan ba daɗi bane kuma ita ma kanta zubarwa kanta ne take da mutunci dan in ba zubewar girma ba, yaro ƙarami kamar Yaronki ba zai raina ta ba" Mama ta faɗa cikin takaicin Momy. "Ba zubarwar mutunci ba ne kawai kin san kowa da halinshi, sannan kowa da halinshi zai zauna, dan haka ni zan shiga da ga ciki sai anjiman ku, idan ina nan wallahi yau ba na tunanin zan jure wannan kalar wulakancin." "Ki yi hakuri dan Allah Maryam, ki nuna ma ta cewa ke ba yarinya bace, kin girme ma ta, saboda abin da take yi ko yaro ƙarami ba ya yin shi, kina ji wai Fatima ke buɗan baki ta faɗawa Uwa gaskiya anji kunya dai wallahi." "Ai kece mai kunya bani idan ba munafurci ba ina ruwanki na shiga tsakanina da ita, yau ko Inna zata shiga tsakanina da kishiyata bale ke banza." "Ke ce banzar ba su ke dai wallahi kin yi asara ta duniya, aiko kana faɗa ana wulaƙantaka amma kullum sai ka yi." "Dakata Inna bafa haifata kika yi ba dan haka ba za ki zo kina min wulaƙanci ba, ina kallonki wallahi ba ki kai min can ba." "Ta fuce da saninki sannan Umma da Mama duk abin da kika kirasu da shi na ji kijira tsammani." Su Fatima jin murya Rashid ya sa suka fito da gudu. Suna fitowa ya suka ji ƙarashin zancan shi. Ido ya zuba wa Ummi ganin haka ya sa ta yi in da Mama. Ni nafi ƙarfin faɗa da kai sai dai waccan karyar da ka ɗauka Uwa. Ba Rashid har Umma sai da maganar ta dake kunnen ta. Rashid kallon Rufa'i ya yi dan ba ya son ciwa Uwar shi mutunci a gaban shi. Rufa'i ya gane abin da Rashid ke nufi dan haka ya yi tafiyar shi. "Momy da kata karki sake kin ran Ummana da karya, ana wata karyar bayanki ne, ku...." Umma bata bari ta ƙarasa ba ta ɗauke ta da mari sai da ta faɗawa kujera. "Bana hana miki magana da manya haka kina ƴa mace ba, sha-sha-shar wannan da zan miki gobe sai ya na yau dan ban sameki da kyau ba." Rashid da gudu ya ƙarasa in da dake ya tallaɓo fuskar ta haka, Mama ta da katar da shi da faɗin. "Kai mai zaka yi haka da wani uban gudu idan ka taɓa sai ranka ya ɓaci." "Am...Am..da..ma.... Mama abu zan ɗauka ." "A ina yake abin da za ka ɗauka ɗin?." "Am....am...." can ya hangi cingam ɗin take hannun Ummi marin da Umma ta yi ma ta ya sa ya faɗi. "Ka yi shiru sai am...am... Kake min." "Mama cingam zan ɗauka fa." Dugawa ya yi sai tin in da take ya ce . "Ba ki ji ciwo ba dai ko? Sannu ki yi haƙura akan ta marin nan zai sauka, ba dai ita ce sila ba ko ki kwantar da hankalin." Da ido Ummi ta ba shi ganin yaƙi janye idon shi ya sa ta janye nata saboda wani kwarjini idanuwan shi ke ma ta. "Har yanzun ɗaukan cingam ɗinne?." "Hm..hum..eh ban gan shi ba ne sai yanzun." Ta shi ya yi ita dai Ummi da ita ta bi shi . "Kika sa aka mari matata a gabana ko?, to ki sa ni wannan marin ba zai tafi a banza ba , kuma ni ba zan mareki ba, amma hmmm ba sai na faɗa ba ma aiii." "Rashid zonan." "Umma lafiya dai ku nima mari na za ki yi." "Eh idan baka zo sai kaci ƙaniyar ka." Yana zuwa kunnen shi ta ja suka shige ɗakinta . Alhamdulillah Alhamdulillahi Alhamdulillahi Duka duka anan na kawo ƙarshen na bati Duk mai bukatar complete sai ya siya 500 ne ba yawa Ga number na 08084277827 Ko 08080304152