[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     ABDUL JALAL WRITTEN BY AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) 1.1 Bismillahirrahmanirahim da sunan Allah me Rahma me jinkai Allah kayi salati abisa shugabanmu annabi Muhammad salallahu alaihi wassalam Bayan haka ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wataba nayishine domin nishadantarwa dkuma wa azantarwa kubiyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa Ina maraba da shawarwari, sharhi, kokuma gyara nagode. This is my first novel Misalin karfe biyu na ranaa a cikin garin kaduna, lokacine da rana ta kwalle tayi zafi sosai mutane wasu na hada hadarsu wasu Kuma sun koma gefe suna hutawa, tafiya take a hankali kaman batajin zafin ranar jikinta sanye da uniform take ratsa lungunan anguwarsu harta karaso wani matsaikacin Gida dayake rukunin gidajen layin dayakasance gamayyar masu kudi da masu rufin asiri, a kofar gidansu taci karo da wata hadaddiyar mota baqa, tana ganin mortar tayi murmushi ta shiga Gida da Sauri tundaga tsakar Gida tafara sannu dazuwa kawuna kuma babana, oyoyo da kyakyawar yata kuma ya tagari Cewar wani babban mutum dake zaune a daya daga cikin kujerun wani matsakaicin palour gefensa kuma wata matashiyar matace a zaune a kasa daka ganta kaga mahaifiyar wannan yarinyar saboda kamar dasukeyi, a kasa tazube tana gaida mutumin ya amsamata cikin sakin fuska yata ya makaranta lafiya kalau kawu aniyi mana Hutu yau mungama mock zanshiga ss1, masha Allah Ashe yarinyartawa ta girma shikenan faduwa tazo dai dai da zama kishirya anjima zan koma dake zan tafi muje kimana hutun acan to kawu d fara artata juyo ta kalli mamanta mama yau zan tafi ke Kadai zaki dinga kwana mhmmm Kawai mama tace amma har ga Allah bataji dadi ba batason yarinyarta ta yi nesa da ita amma yadda Alhaji imam yke nunawa yarinyarta so bazata iya cewa a'a ba kasancewar yarinyar yar Dan uwansa ce, ita kuwa murna take koba komai kwana biyu zata huta da fadan mama. Misalin karfe Biyar na yamma sukashigo garin kano ta dabo jalla babbar hausa, rukunin gidajen sharada NNDC quarters ananne Inda gidan alhaji imam yake, gidane babba Wanda akayiwa gini na zamani gidan yyi matukar tsaruwa, yaran gidanne sukafito domin Tarar mahaifinsu suna masa sannu dazuwa ai daganin shida wadda yake tare suka dau murna, murna farinciki ya mamayesu Nana ce tariqo hannunta tana naji dadi JALILAH Hutu zeyi dadi 💃💃 ta rungumeta suka shiga cikin gidan, matar gidan da fara arta take fadin sannunku dazuwa yau munyi babbar bakuwa murmushi JALILAH tayi tazube har kasa tana gaida matar amsamata tayi Nanace tajata dakinta tace shiga ki watsa ruwa kizo musha hirar yaushe gamo, karfe takwas na dare iyalan gidan suka hallara domin cin abincin dare, daga bakin kofa sukajiyo muryarsa kai kai kai wanake gani haka kaman wata Yar kauye nake gani cewar wani matashi dabaze wuce shekaru ashirin da biyuba yayin shigowa palourn dariya suka kamayi wuce nan wlh Niba Yar kauye bace, murmushi yayi yace to Yar birni saukar yaushe Nana tayi caraf tace saukar dazu da abbah yaje yataho da ita hakan yayi kyau Cewar matashin haka sukacigaba da hirarsu gwanin sha awa. ***************************** Zaune yake a cikin parlour yadora qafa daya kan daya yanata busa shisha sekace salansar tifa ta hanci ta baki gefensa mp ce ke fitar da sautin kida a hankali se lumshe ido yake alamu yanayin yayi masa dadi wayarsa ce ta dau ringing yanaji har ta katse be kulaba takuma ringing ya kallah seyaga mum a jiki ya kauda kai yacigaba da busa hayaqinsa karo na hudu wani kiran Yakuma shigowa a fusace yadaga wayar what's is it ne mum kinkira ban daukaba ai seki hakura kinsan INA wani abunne haba Dan Allah 😱😱😱 jalal kazo yanzu inason ganinka akace daga daya bangaren am having rest now komene let's meet tomorrow bejira mezata kuma cewa ba ya kashe wayarsa yasata a flight mode yacigaba da babbakar hayaki qaramar wayarsa ce itama tafara ringing yaja wani dogon tsaki ya dakko Dan duba waye jeje ne akan screen din wayar dagawa yai kara wayar a kunnensa be maganaba ya danyi shiru yace karkutafi gani nan... ............... Jalilah tawayi gari a cikin garin kano, da garin Allah ya waye tareda Nana suka Shiga kitchen suna hada breakfast sunayi suna hirar makaranta Nana CE ta dubi jalila tace sister dama kiyi zamanki a kano  sekicigaba da karatun a an an kinga bani da Yar uwa mace se jimmai house girl din Ummi inajin dadin zama da ita amma ita kullum cikin yawon biki take, hmmm ajiyar zuciya jalila tayi taace idan nadawo kano mama fa in barta ita kadai a Kaduna naana bazan iyaba kam, Dama nasan bazaki yaddaba dallacan matsa kiban guri murmushi kawai jalila tayi, suka cigaba da aikin dasuke, wajenkarfe shadaya suna dakin Nana suna hira jalila take cewa gaskiya Nana garin kano tanada kyau matuka na Dade rabona da kano, ai ba kya ziyara taya zaki Sani ba kya zumunci kullum kina like da mama, kudin zuwa kuke ai hargara ni kuma ai bazuwa kuke ba dalla bari mu tambayi Ummi muje kiga gari Yar kauye kawai wuce nan wallahi kema Yaya jawwad dince ko dariya sukayi sukasa hijjabai suka fito parlour Ummi ta dubesu se INA Ummi zamuje gidansu nusaiba ne jalila ta danga gari kinsan kifin rijiyace, murmushi Ummi tayi tace to adawo lafiya akula da kai kuma karku Dade to Ummi sukasaka kai suka fita sunata hirarsu gwanin sha away Layinn shiru se kukan tsuntsaye dasuke shawagi akan manyan bishiyoyin dasuke cikin wasu daga gidajen dake unguwar suna tafiya suna hira, a guje wata mota ta taho da gudu kaman zata tashi sama se uwar kura datake tashi kwata² tukin rashin hankali akeyi galalala jalila tabi mortar da kallo Nana ta tabota yadai tab amma nana direban motan nan bashi da Rabin hankali in akasamu akasi ya bige wanifa, hmm ko a jikinsa jalila me tukin nan baya ganin kowa da kima a anguwarnan babu me fadamasa yaji haka rayuwarsa take ko iyayensa basu ISA dashiba Yaya jalal kenan abokin Yaya jawwad ne, tab amma ya akayi Yaya jawwad yake abota da irin wannan Sam halinsu be kamaba, jalila kenan kema kyafada anyi2 arabasu abu yaci tira Allah ne yahada jininsu yana matukar son Yaya jawwad, hmmm Allah y kyauta Cewar jalila Nana tabita da Ameen, haka sukaje suka dawo suna ta hirarrakinsu, wayar hannun Nana Ce tafara ringing ta daga tayi sallama jalila bata iya jin abinda ake fada a wayar se dai murmushi da Nana tayi tace sorry mun Dan fitane sister tace tazo muka fita bari mu biyo, ta kashe wayar jalila zomuje wata qawatace tazo kai wannan hutun zemun dadi gaki ga ilham mtseww kekin cika gayyar kawaye wlh ni nagaji gaskiya, Dan Allah kizo muje to shikenan muje sarkin naci. Kofar palourn ya tura ya shiga yanufi kitchen kai tsaye ya Shiga yadakko abinci a Warmer's yana shirin fita jalal yaji ankira sunansa be waiga ba yatsaya INA ka kwana jiya matar ta jefomasa wannan tambayar yayinda take sakkowa daga kan bene ba magana nake maka ba INA ka kwana jiya juyowa ya kalleta a club yafada kansa tsaye batare da wata shakkaba jalal wato kai ko kimata baka gani kankaa tsaye kake gayamin a club ka kwana ohhh my God mum tambayata fa kikayi nagayamiki shima kuma laifi nayi I don't want the way u are treating me mum kibarni inyi abinda ya dace dani cikin daga murya da gadara yake maganar Wanda yayi dai² da shigowar su jalila tundaga waje suke jiyo hayaniyar jalal da mahaifiyarsa abin yyimatukar bawa jalila mamaki itakuwa Nana ko a jikinta Dan ta saba jin irin wannan rashin ta idon da abokin yayanta yakeyi yaja wani dogon tsaki yafito waje, mommy INA wuni yawwa sannunku nana, mummy INA ilham tamin waya tazo nuni mummy tayimana da dakinta cikin damuwa ta koma sama, mukuma muka nufi dakin data nuna mana muna Shiga  suka rungume juna suna murna, nana wannan sister dinkice kuna kama matuka eh kanwata ce sannu ya sunanta jalila nana tabata amsa hmm nice name thank u kawai jalila tace amma hankalinta na kan abinda tagani yau wannan Sa insa tsakanin da da mahaifiyarsa abin yabata mamaki kuma yadameta, bayan sun koma Gidane jalila ta kalli nana tace nana gidan da mukaje dazu wlh wannan din nan bashi da tarbiyya wallahi wakenan kike nufi oho ban San sunanshiba  wannan din nan me dogon hancin nan kaman tattasai tooo dariya nana takamayi tattasai ni banganeba mtseewww is not joke nana y kalli mahaifiyarsa yace mata a club y kwana yana mata shouting haka, mhmmn bakiga komaiba India jalal ne jalal ta maimaita sunan yeahp shine me driving a mortar nan dazu kafin kibar kano zakigane wayeshi bakiga komaiba, amma a haka Yaya jawwad yake abota da shi jalila ta tambaya cikin tuhuma, jalila ba se lallai hali yazo daya ake abota ba soyayya da shaquwa gamon jinine tsakaninsa da Yaya jawwad Allah ne yahada jininsu, Yaya jawwad se yasaka jalal ABU yayi amma mummynsa bata isaba, ga shaye shaye a cikinsa yawon club ba Wanda ba yayi, tabdijan nana wannan abotar bame yiwuwa bace inji jalila kaman yaya,  basu dace da abotar ba wannan Sam bashi da tarbiyya Dan haka sena rabasu bashida tarbiyya Nana  tirkashi!!!!!!!!!!! More comments more typing   🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  2 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.        _My first novel_    Kallonta Nana  tayi, ta ce    "kaman ya se kin rabasu, ina ruwanki dasu?  kinga Jalila ba ruwanki dasu, Maaama ma tayi ta Hakura, Jalal ba ze iya rabuwa da Jawwad ba, bayan abokansa na banza ina ga Yaya Jawwad  ne kawai mutumin kirki, kika sani ko Allah ya shiryeshi a sanadin sa? kawai muyi musu addu' a."          Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "Nana abotar Yaya Jalal da Ya Jawad sam bata dace ba, barazana ne ga tarbiya da rayuwar Yaya  Jalal mutumin dabe ji maganar Wanda suka kawoshi duniyaba ne kike zaton ze wani shiryu sanadin wan?i yau da gobe se Allah yasha giya ya kwana club yayi sa'insa da mahaifiyarsa shi kike tunanin ze shiryu sabodaa wani aboki Sam bashi da tarbiyya Nana ."      Jalila Allah shi yasan manufar hada abotarsu duk da banbancin halayensu, kawai muyi musu addua shine mafita mukuma muyi abinda ke gabanmu."    "Nana ni kam nacji amma ban gamsu da bayanan ki ba , zanyiwa Yaya Jawwad magana," " to Allah yatemaka inji Nana, amma kome zakiyi karki shiga harkar Jalal." Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "karki wani damu Yar uwata,  ni dai fatana yafita shirgin yayana, bana so yazama irinsa ya lalatamin Dan uwana, tunda shi lalataccene ma tayashi da addu a." "To Allah ya baki Sa' a, nima da naso hakan". ********************************               Sanye yake da kananan kaya, wando 3quater fari da Riga T-shirt itama fara, yayi kyau sosai, yasa hannu ya dauki turare ya feshe jikinsa dashi, ya dauki wayoyinsa dake kan mudubi da mukullin motarsa yafito.     Kai tsaye ya nufin inda akayi parking motoci, sekuma ya juya ya nufi cikin gidan.      yanazuwa kofar parlour ya budee ya Shiga, ba sallama ba komai fuskanan tashi a daure tam babu alamar fara'a parlour shiru se kamshin turaren wuta dana abinci da ya gauraye parlourn, gefe kuma Ilham  ke kwance kan kujera 3seater tana kallon Tv. "keee!!" ya fada cike da gadara , a dan tsorace ta dago Dan batasan ya shigo ba, "Yaya Jal sannu da zuwa" Ta fada tana kallon sa tare da yaba kyawun da yayi acikin ranta,  be amsa ba yace " Ina matar gidan nan take?" "matar gidan nan kuma?" ta maimaita tana dubansa   "ba kiji bane ko kuma tsabar rainin hankaline?" Adan daburce ta ce "ai jinai kace matar gidan nan, wai mummy kake nufi?" " Yaushe raini ya shiga tsakanina dake ne? har nake magana kina maimaitawa, akwai wata mata a gidan nan banda itane?" Mamakinta ne yakasa boyuwa, lallai yaya Jalal abin nasa ya girmama, mummyn tasa ma bata tsiraba wai matar gidan nan? tabdijan, amma ta dake ta boye mamakinta ta bashi amsa da    "ta fitane, taje saloon"     "mtseww" ya Dan jaa tsaki , "inta dawo ki ce ta kirani a waya, ina da magana da ita." Bai jira mezatace ba yasa kai yafita,   "ohh God ni Ilham,  yaushe Yaya Jalal ze fara sakarmin fuska ne yana kulani?  kullum mutum fuska a daure Yaya Jalal whyyyy?? " tafada tana jifa da pillon hannunta, "I must do something!"    tafada tare da mikewa tabar parlour. ********************************** JALILA ce zaune akan carfet tana waya da umminta,      "masoyiyya nayi missing dinkifa irin sosai din nan ummina", "bawani nan tunda kika iya tafiya kikabarni," "ummina kenan kina birnin zuciyata fa", " ke tafi can ya mutan gidan naku kowa lpy?" "ummi garin kano ya hadu kinsan na dade banzoba zuwan yayi min dadi" "to hakan yayi kyau",      "ke dazu wata kawarki tazo ta bani sako in gayamiki amma wayata babu caji in anjima mayi waya yanzu fita zany"' "ina zakije kuma ummi?" "inda kika aikeni" "huh ummina ta kaina adawo lafiya anjima zankiraki insha Allah" "to shikenan ki gaida ya'n uwannaki ki gaidamin da halima(Maman su jawwad) kar inkirata tazata dankina gidanne nakirata to Ummi zasuji insha Allah". "To shagwababbiya Yar gidan Ummi wannan shagwaba haka kinfa girma JALILA Cewar JAWWAD Murmushi JALILA tayi tare da fadin "Allah yatemaki babban Yaya ai ba a girma a gurin iyaye mussaman iyaye mata" Murmushi yayi tare da fadin "kekam halinki yana nan baki canza ba kome mutum yagayamiki kinada amsa dai dai da abinda yace JALILA baki abun magana, dariya sukayi gaba daya "yace ba wannan ba tukuna yanzu dai ya studies dinki komai lafiya dai ko?" "Alhamdilillah Yaya JAWWAD komai lafiya ina karatuna yadda yakamata," " to masha Allah haka akeso amma kamata yayi kiyi waec a ss2 se Asama miki admission a BUK kidawo kano gaba daya".    "Tab to umminawa fa shikenan in batta acan" " murmushi yayi yace haba JALILA wataran fa aure zakiyi kitafi gidan miji ko me rabawa taraba (MUTUWA!!!)" " Kaman yadda ta rabani da banana ko ta fada idonta cike da hawaye Yaya jawwad karkamin wannan fatan, idan narasa ummina yanzu wanake dashi daze soni kaman su, abbana yatafi yabarni bana fatan ummina ta barni, nafiso in mutu in barta" "Haba JALILA kinga share hawayenki kinji qanwata bahaka nake nufi ba yanzu idan Abba yaji furucinki na wa kike dashi baze jidadi ba Abba yana matukar sonki ya daukeki kaman yanda ya daukemu ko kinrasa kowa ni INA tare dake kanwata har abada yayanki yana tare dake duk wuya duk dadi zan kasance tare da ke".        Taji dadin kalaman yayannata mutum ne nagari me kirki tayama zata bari abotarsa ta dore da wancan sakaran yabata matashi baze yiwuba dole tayi wani Abu, "Yaya JAWWAD inason in maka wata magana.... Mamansu jawwad kuwa da tazo shigowa parlourn ta riski hirar tasu ta labe tana sauraransu abin se ya kular da ita, me jawwad yake nufi da ze kasance tare da yarinyar nan duk rintsi aikuwa baze yiwu ba, dole tayiwa tufkar hanci bazata taba bari danta ya auri jalila ba in ma sonta yakeyi danko maqiyinta tagani ze aureta tahanashi saboda gudun bacin suna ahaka dai gata kamilar yarinya tagari me da a amma babu asali me kyau ta danyi tsaki ( 😱😱😱 tooo wata sabuwa me ummu jawwad take nufi ne) Wayartace takama ringing Wanda yasa dole ta fito badan tagama jin hirar tasuba tare da kakalo murmushin yake Yaya da kanwarsa hira akene "wlh kuwa maaamaa, ni zan wuce zan raka JALAL wani gurine, gaban jalila ne yafadi jin ya ambaci jalal ta dago a Dan razane tana kallonsa, "to sekun dawo ka kula da kanka Cewar maaama", "sisy akwai damuwane" yafada yana kallon JALILA, girgiza kai tayi yace to sena dawo, "safe journey" tafada a takaice yace thank u sisy maaama sena dawo to asauka lafiya Allah yasa ya amsa yafice.        Maaamace ta amsa wayarta data cigaba da ringing salamu alaikum tafada ta danyi shiru to shikenan inkin dawo da magariba zan turo su Nana su karbarmin to nagode, ********************************      Banyan sallar magariba maaama ta aiki su Nana tace su shiga gidansu JALAL zasu karbo mata sako gurin mummynsa, da sallama suka shiga suka Tarar zata fara cin abinci, gaisawa sukayi suka fadamata Aiken " tace to bari in dakko muku sakon" "aa tunda kinzuba abinci kigama tukuna Cewar JALILA, Eh momy gama bari muje gurin ILHAM kafin kigama inji Nana to shikenan sekun fito. Tana zaune a palour tana cin abinci yashigo yasamu guri ya zauna ya kalleta "ILHAM bata gaya miki saqona ba?" "tagayamin" tabashi amsa a takaice, "meyasa baki kirani dakika dawoba?" nace inason magana dake "ban niyyaba" tabashi amsa Dakin ilham suka shiga ta kwanta rub da ciki tana kallon hotunan JALAL sallamarsu yasa tayi firgigit ta aje wayan "yan matan maama sannunku dazuwa "yawwa sannu" JALILA ta amsa haka kurum ILHAM intaga jalila se gabanta ya dinga faduwa tarasa meyasa, NANA takalli ILHAM "" daddawar daki wannan zuwannaki ba yawone?" " ke dai bari wani abu ke damuna wlh," " tooo menene inji Nana " kedai bari semun hadu kawai", jalila tunawa tayi zasuyi waya da umminta in anyi  sallar magariba tabaro wayar a Gida maybe tana can tana kirana, "Nana bari inje indawo inazaki inji Nana yanzu zan dawo tafito da Sauri "Dubai nakeson tafiya next months kudi zaki turamin a account" " mezakaje kayi a Dubai?" " aa meye kuma na tambayata ina daddy yace idan INA bukatar kudi abani to mene na tuhumata kuma" se kajira ubannaka yadawo seyabaka sangartaccen banza yaushe rabonka da makaranta Baka zuwa karewama sokake ka tsallake kabar kasar karatun ko oho ko? "Wait please meye kuma namin fada kibarni in tsara rayuwata yadda nakeso ba ruwanki da abinda nake aikatawa makaranta ko inje ko kar inje ai bada kudinki ake biyaminba duk kin takuramin kin tsaneni ni am doubting ma if u are my biological mother 😱😱😱 "Allah wadaran naka ya lalace tur da Dan daze tsaya gaban mahaifiyarsa tana fada yana mayarwa, Anya kana Neman albarka a rayuwarka asara ta tabbata ga me sabawa iyayensa Gaba daya suka waigo domin ganin me maganar........  More comments more typing 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  3 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.        _My first novel_ Gaba daya suka waigo suna kallon inda jalila take maganar, taci gaba da fadin "duk d'a nagari me fatan nasara a rayuwarsa, baya fad'i in fad'a da mahaifiyarsa wannan ba halin d'a nagari  bane me neman albarka, wannan ba komaibane kake face tsantsar rashin tarbiyya!!" ta kare maganar tana kallon cikin idon jalal, ta kalli mummyn Jalal tace "mummy seda safe Nana ta taho da sakon"       Idanuwansa ne sukayi jawur jijiyar kansa ta daddaga ganin yarinya Karama ta tsaya tana gaya masa miyagun maganganu,     Wani yunkuri yayi da nufi ya karasa inda jalila take ya hukunta ta mummy tasha gabansa ta rikeshi gam, duk da ta danji ba dadi da Jalila takira Jalal Mara tarbiyya amma ta dake tare da fadin "Karka kuskura ka tabata abinda tafada gaskiya tafada kadan kagani Indai haka zakacigaba dayiwa rayuwarka, indai zaka cigaba da gayamin maganganunu daka gadama kana wuakantani agaban mutane." fizge hannunsa yayi da karfi  "kicikani wallahi sena kakkarya yarinyar nan ni zata gayawa wannan maganganun wallahi sena koyamata darasin da harta mutu bazata mantaba," Da gudu jalila ta ruga ta fice daga palourn. hannunsa ya fizge daga cikin na mummy ya rufa mata baya a zuciye, amma kash kafin ya fito harta bace kaman walkiya yanemeta yarasa, har bakin gate yafito amma be ganta ba, yanufi dakin me gadi Yakama buga masa kofa iya karfinsa, a sukwane me gadi  ya fito babban mutum amma haka ya zube agaban jalal jiki na bari "ranka ya dade...." Begama ba JALAL ya katseshi "kaii yarinyar da ta fita yanzu INA tayi,"  jalal ya katseshi "Ranka ya dade sallah nakeyi banga fitar kowa ba" " shut up!!! Useless man Sam bakasan aikinkaba dakiki kawai," A fusace ya shiga part dinsa zuciyarsa na tafasa, he wish Yakama yarinyar nan da ya nuna mata waye jalal, 'me yasa kika rikeni kika hanani daukar mataki akanta yafada a fili Dan karamin flower base din dake kan side bed dinsa ya dauka yayi jifa dashi yana huci, "Waima Yar uban waye daga ina take" Kaman yataba ganinta amma yamanta a ina ne wayarsa CE tafara  ringing, bros jawwad ne yafito akan screen din wayarsa, yadaga wayar yakara a kunnensa, " "Dan uwana meyasameka  tun dazu nake nemanka kazo ka karbi ajiyarka, Wai yanaji kanata hucine me yafarune," "bari bros bakomai zan fitane inna dawo zamuyi magana wata Yar iskar yarinyace ta zageni kuma idona idonta sena lahira yafita jin dadi" JALAL yayi maganar a hasale, "Subhanallah haba Dan uwana ya kake fadin haka kaifa me hakurine fushi banakabane nasan maybe wani   Abun kayi mataa kamanta da ita kawai yanzu dai kana ina" "Bazan mantaba din wallahi sena koya mata hankali" cewar JALAL "Easy bross karkayi fushi Manzon Allah salallahu" "...........alaihi wassalam" Jalal yakarasa masa, "zaka fara Toni fita zanyi semun hadu da anyi magana sekace mutum yayi hakuri ka dauka kowa irin Kane" "Dan uwana ina maka nasiha kaji tsoron Allah Dan an bata maka rai kar in kafita kasha giya Dan Allah kar kasha giya koka aikata abinda ba shikenanba babu abinda zata qara maka se bacin rai, garaka... .." kitt JALAL ya kashe wayar in yatsaya cigaba da sauraron JAWWAD ze kuma bata masa rai, Lamabar Jeje ya nemo bugu biyu ya dauka ya kara wayar a kunnensa "Man where are u now?" Banji me akace daga daya bangarenba "OK I will be there" Ya kashe wayar yafice daga gidan Da gudu ta karasa cikin gidan sukayi karo da Abba a hanyar shiga gidan tanata haki kaman tayi wrestling, "Meyakoromin ke haka diya tagari" "Am..mmm... Maama CE ta aikemu shine nayo gaba wani kare yabiyoni tafada tana maida numfashi" "Shine kike wannan gudun in kika fadi fa matsoraciya kawai ba a yiwa kare gudu inbahakaba wataran seya cijeki" yafada cikin wasa "Tunda kin shigo Gida seki tafi a hankali" "To nadena abbana" "Good girl, kodayake yanzu tazama lady" Murmushi tayi tashige ciki kai tsaye ta tafi dakinsu tana kuma sauke numfashi "Tab daya kamani dana gane kuskurena yadda idonsa yayi ze iya sumar dani fa" Tayi maganar a zuciyarta wayarta ta laluba tafara trying lambar Ummi amma taki shiga har tagaji ta aje wayar, ta mike tashiga bandaki tayo Alwala tafara gabatar da sallar isha'i ta idar da sallah ta canza kaya zuwa na bacci ta nashirin kwanciya Sega Nana tashigo "Se yanzu?" "Eh nai ta zaman jiranki baki dawoba nagaji shine na karbi sakon na taho, dama atamfofine maama zata Cuba" "Hmm yayi kyau" cewar Jalila. Can na hango shi yana zaune kan wasu fararen kujeru matasa ne maza da mata suke kaiwa suna komowa daganinsu kaga yayan Hutu masu karancin tarbiyya,   fuskar nan tasa a tsuke kansa dauke da wani irin aski ga Suma fal akansa se cika yake yana batsewa da anjima yadan ja tsaki. "Man what's actually wrong with u tun dazu bakacemin komai ba what's happening" Jalal ya danja karamin tsaki kawai se yakasa gayawa jeje abinda yabata masa rai "Just forget" Shine abinda ya iya cewa ransa fal takaici "Anyway since u decide not to share ur problem with me Dan ja kaya at least it will help u reduce ur temper" Ya fada tare da tsiyaya masa Wayne a cup ya mikamasa ya Sa hannu ya dauka ya shanye ya kara masa yakuma shanyewa yana shirin kuma zuba masane "DAN UWANA KAJI TSORON ALLAH DUK INDA ZAKAJE KAR KASHA GIYA KO KA AIKATA ABU MARA KYAU BA ABUNDA ZATA KARA MAKA SE BACIN RAI" Kalaman Jawwad ne suke dawo masa se yaji haka nan jikinsa ya danyi sanyi. Hannu yadagawa jeje yacemasa"enough " "Kana nufin ta isheka" cewar jeje" "Yeah" yafada a takaice "Am going " Jalal yafada yana duba agogon hannunsa "But man kaman akwai abunda yake damunka" "Bakomai ni na wuce Gida" Yafice daga gurin. "Nana dakika baro gidansu jalal kinganshi kafin kifito" "Aa nadai ji fitarsa a mota amma bamu hadu ba, akwai matsala ne" "Aa babu koma". *********************************** Washegari da safe Jawwad ya shiga gidansu Jalal, seda ya shiga suka gaisa da mummyn jalal sannan ya fito ya nufi sashen Jalal,. Kofar bedroom dinsa ya bude ya shiga yana kwance yanata bacci, agogo Jawwad ya kalla 9:30am amma Jalal be tashiba, girgiza kai yayi. Ya taba Jalal " bross wake up gari ya waye fa kalli rana tayi sosai " Dan motsawa yayi kaman baze tashi ba, sannan ya tashi zaune yayi mika yana Dan yatsina fuska "Jalal anya kayi salla kuwa?" "Banyi ba" yafada hankalinsa kwance "Haba Jalal sekace ba musulmi ba quarter to 10 fa amma bakayi sallar asuba ba why?" "In kai zanyiwa innayi kar ka karba" yafada yana shirin mikewa "No am sorry jekayi sallar kazo muyi breakfast" Yafita yakoma palour yana jiransa Mikewa yayi yayo wanka tareda alwala yazo yayi salla itama dai sallar gata nan wata kilama badan Jawwad yazoba bazeyi ba, (Sallar karfe 10am Jalal kai lefunka naka sunyi yawa Allah ya yafe mana) Bayan ya idar ne yafito ya tarar da Jawad a palour yasamu guri ya zauna a kujerar datake fuskantar Jawad Jawad yayi gyaran murya yace "Jalal wai me akayi maka jiyane meyafaru" Yayi shiru kaman ba zece komai ba "Wata yarinya CE jiya da daddare ina magana da mummy kawai ta fito ta tsoma baki hadace min Mara  tarbiyya" Dan zaro ido Jawwad yayi aransa yace ai batayi karyaba abokina watakila ma rashin mutuncin kakewa mahaifiyarka agaban mutane amma a fili seyace "Wace yarinyar CE" "Toni ina nasanta naga dai kaman na taba ganinta amma namanta inda nasanta, Amma tabbas duk ranar dana ganta sena mata abinda bazata manta dani ba zan tabbatar mata bani da tarbiyya sha³ yarinya" "Yi hakuri bros yanzu taso muje gidanmu muci abinci tunda yanzu dai baka ganta ba kamanta kacigaba da harkokinka kawai" Ya janyo hannunsa suka fita daga gidan, zuwa gidan su Bayan sun kammala cin abincin ne Jawwad yayi gyaran murya yace "mutumina Jalilana fa tazo yau kwananta hudu a kano" "Wace hakan?" Jalal yafada cikin ko in kula " kaifa kafiye wulakanci kanwata fa danake gayamaka ta Kaduna" Murmushi Jalal yayi "to shine kake wannan fara ar haka?" "Bazaka ganeba Jalal irin yadda nakesonta, ba iya son yan uwantaka nake mata ba Jalal ina kaunarta ne sonake in kasance tare da ita har karshen rayuwata ganinta kawai yana Sani farinciki Ina  kaunar Jalila matuka zan iya komai akan farin cikinta" Kyakyacewa Jalal yayi da dariya tare da kunna sigarinsa ya fesa hayakin sama tare da wani kasaitaccen murmushi, "Gaskiya ka faller over bross irin wannan bege haka ina mamakin me akeji a soyayya ni har yanzu banga macen dazata Sani wannan sambatun ba" ya karashe maganar da wata irin, dariya "Jalal irinkune soyayya bata muku ta dadi wato dariyama nabaka ko hmm rai dai Allah yabamu rai da lafiya" "Yaya Jawwad barka da Sadiya INA fatan katashi lafiya, Abba yace kazo yanason ganinka," Daram kirjin Jalal ya buga muryarta ce!!, "Yar halak taki ambato barka da safiya kanwata, Jalal gata fa Jalila kenan danake gaya maka kanwata juyowa yayi suka yi ido hudu da ita Kallonta yayi tabbas itace, yarinyar da tazageshi agaban mahaifiyarasa jiya da daddare nan da nan annurin fuskarsa ya dauke yafara zaro idanu, Cikinta ne ya duri ruwa tafara rarraba idanu zuciyartace take bugawa da karfi yau kam ta shiga uku (Marar kunyar karya kin debo ruwan dafa kanki) More comments more typing........ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  4 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. I want comments not stickers😢😢😢😢 Comments dinku  shine kwarin gwiwata Special thanks to u my motivator I dedicate this page to you Anty MARYAM        _My first novel_ "Shigomana ya kika tsaya anan" Dagewa tayi ta boye tsoronta ta dai dai ta nutsuwarta, tashiga cikin dakin "Kanwata ga Abokina kuma Dan uwana wato Jalal dukda kin sanshi amma nasan bazaki tunashi ba lokacin kina Karama sosai " Kallon Jalal tayi taga mugun kallon dayake mata amma ta basar "Sannu" abinda tafada kenan ta maida kallonta kan Jawwad "Yaya naga kanada bako in kungama na dawo karka manta da kiran Abba" Ta juya tafita tana godewa Allah a zuciyarta da Jalal bemata komai ba "Wannan ce kanwartaka?" "Yeah ya kaganta so gentle and innocent" "Good" shine abinda yafada kawai Mikewa yayi tsaye zetafi "Bros yazaka tafi muna magana" "Inada abunyi ne" Ya fice wato ma kanwar Jawwad ce tabdijan yanzu ta zagi banza kenan anya kuwa ze kyaleta ko dai yagaywa Jawwad yaja kunnen kanwarsa tafita a harkarsa, to meye amfanin hakan, Tana ganin Jalal yafita ta koma gurin Jawwad tasameshi inda tabarshi be tashi ba, shiga tayi ta zauna tace "Yaya Jawwad magana nakeson muyi" "Am all ears sisyna ina jinki fadi abinda kikeso" ta Dan gyara zamanta tana fuskantarsa Wanda bayan kujerar dayake ya kasance window ne         Zancen zuci yacigaba gsky y zama dole ya dau mataki inma ya kyaleta taci bulus kenan yana cikin wannan tunaninne se jeje yafado masa bari ya kirashi yaji wani shawaran ze bashi ne, hannunsa ya zura a aljihu da niyyan ya dauka wayan se yaji babu yadan yi shiru seya tuna tana kan kujerar da ya zauna a dakin Jawwad "Yaya Jawwad meye hadinka da mutumin nan ne?" "Kina nufin Jalal?" "Eh shi nake nufi" "Abokina ne kuma Dan uwana" "Ta Yaya yazama Dan uwanka Yaya Jawwad wannan ba aminin arziki bane halinku Sam ba daya bane kallafa sigari yake shamaka a daki da ganin idonsa kasan tarbiyya ba ta wadace shi ba, kalli askin kansa, daganin bakinsa wannan yana shaye² Zamanka tare da shi mutane zasu zata halinku daya Sam bashi da tarbiyya" ta daga kanta wazata gani  kawai taga Jalal a tsaye a bakin window yana kallonta da jajayen idanuwansa Wanda hakan ya tabbatar mata yaji abinda tace Ras! Ras!! Ras!!! Gabanta yafadi      cikin palourn ya shigo ya dauki wayarsa bece komai ba ya fice    Jawwad be kawo komai a ransa ba Dan yasan halayen Jalal shiyasa bekawo yaji wani abuba kuma yabawa window baya Dan haka besan yazo wajen ba. "Kinaji kanwata Jalal mutumin arziki ne ba yadda kike tunaniba inayimasa addu a in Allah ya yadda wataran zakiga ya dena ze wuce kaman ba ayiba kema kisashi cikin adduo'inki kidinga masa fatan shiriya" "Yayana ka kula da kanka Dan Allah karka bari dabi'unsa su rinjayeka wataran Dan Allah" "Karki damu kanwata ba abinda ze faru mun Dade tare da Jalal da zan zama irinsa da tuni na zama shima abinda kikaga yanayi kaddara ce babu abinda ze faru da yaddar Allah" "To shikenan" ta fada tana mikewa "Karka manta da kiran Abba "to shikenan zanje insha Allah " Jalal kam Shiru yayi yana tunanin wani mataki yakamata ya dauka akan yarinyar nan gata kanwar amininsa kanwarma kuma wadda yakeso ta yaze hukunta yarinyar nan ya bakanta mata  ba tare da Jawwad ya gane ba baya son batawa abokinsa rai Dan tabbas in yayi mata wani abun Jawwad bazeji dadi ba, Ko in kira Jeje yabani shawara idan na kirashima mezemin? wata zuciyar taba shi amsa Mara tarbiyya!!! Wai nine bani da tarbiyya mtseeww yaja tsaki zakiga rashin tarbiyya ganin idonki. (Kai JALAL bafa karya tayiba ) Jalila kuwa Cikin gida ta koma tunda ta shigo maama ta bita da wani irin kallo na zanyi maganinki ita kuwa Jalila bata san tanayi ba, Gurin Abba nufa ta durkusa tace "Abba nagaya masa yace yana zuwa" "To shikenan diyata" Wucewa tayi dakin su ta je ta tarar da Nana tana ninkin kaya taje ta zauna kusa da ita "Nana kinsan me yafaru?" Nana ta juyo ta bata dukkan attention dinta "A'a sekin fada" "Ingaya miki Jalal nagani adakin Yaya Jawwad yana ta shan sigari" "Hmmm to ai bakiga komai ba Dan dai sigari kawai karewa har giya yake sha masa a daki wataran in yaje yasha yana tambelansa Yaya Jawwad ne yake nemo shi a club yakawo shi dakinsa ya kwantar da shi har giyar ta sake shi Ke baki San komai bane shiyasa nace miki rabashi da Jalal ba abune me sauki ba" Nana ta karashe zancen jikinta a sanyaye "Tabdijan kice abun babba ne ai in gaya miki dana ganshi a dakin bayan ya fita nakoma gurin Yaya Jawwad nai masa magana akan ya rabu da Jalal bashi da tarbiyya Ashe yadawo  daukar wayarsa  yaji duk abinda nafada bakiga kallon da yayi min ba" Dan zaro ido Nana tayi "Are u serious" "Wlh dagaske nake yaji me nace bakiga mugun kallon da ya dingamin ba" "Tabdijan Jalila garin Yaya haka tafaru aikuwa kinci sa a Yaya Jawwad yana gurin da wallahi inaga seya kusa sumar dake" "To dai Allah ya rufamin asiri Bari in Dan kwanta in huta" "Sarkin bacci ko gajiya ba kyayi Allah ya kiyaye haduwarki dashi" "Shi wa?" "Kinfini Sani" Murmushi kawai tayi ta hau gadon ta kwanta. Nana kuma tacigaba da ninke kayanta, Befi 10 minutes da kwanciyar Jalila ba Ilham tayi sallama "Mutuniyar kinji gori kenan yau se gashi kinzo anya makuwa bawani abun yakawoki ba" Nana tafada cikeda zolaya "Hmmm ke dai bari Nana akwai magana ne, sister dinki bacci takene?" "Eh bacci takeyi meyafaru" Cike da damuwa ta kalli Nana "Nana Yaya Jalal ne" "Wani abunne yasameshi?" Nana ta tambaya "Aa Nana kin San dai zancen, ta tsuniyar gizo bata wuce koki hankalin yaya Jalal Sam baya kaina wlh ko kallo ban isheshi ba komai nayi bana birgeshi ke mukwana gida daya mu tashi amma semu shafe kwanaki ko kallon inda nake beba Abun yana damuna Nana ina matukar kaunarshi amma shiko a jikinsa ni ban San meyake damun saba kaman ba mutum ba"   Nana ta dan dafata da sigar rarrashi "Ilham inso cutane hakuri maganine kicigaba da hakuri kina addu'a insha Allah komai zezo karshe" "Nana in ba ya Jalal na aura ba bazan iya zaman aure ba, dashi nake so na rayu yazama uban yayana , nifa ko karatu bazan iya cigaba ba sonake munayin SSCE ya aureni narasa yadda zanyi gashi mummy ma ba jin maganarta yake ba itama tayi kokarinta amma yaki saurarona Dama daddy ba a maganarsa don baze taba tursasa shi ba Ina cikin damuwa"   Daga inda Jalila take kwance ta tashi zaune Dan taji hirar dasuke ba bacci take ba, dannan waya take, "Aikuwa kina tattare da nasani a rayuwarki damuwa yanzu kikafara muddun kika zabi dan giya a matsayin uban yayanki karki biyewa son zuciya ki cutar da yayan dazaki Haifa a nan gaba auren Jalal babu abinda zaki kwasa bayan bacin rai da dunbin danasani" Kallonta Ilham tayi tana nanata Kalmar Dan giya aranta lallai Jalila bata da mutunci a gabanta take kiran Jalal Dan giya banda shishshigi da munafurci wayasakota a ciki Lallai bata sanniba akan Yaya Jalal banki imbata da kowace ce ba Ta kalli Jalila rai a bace "Kekuma wayasa dake a gabana kike cin zarafin Dan uwana kuma masoyina Dan giya wannan ba magana bace at least yana abokin yayanki ya cancan ci ki mutuntashi" "Taya kike tunanin in girmama Wanda be girmama mahaifiyarsa ba, Sam Jalal ba abin girmamawa bane, kema zuciya yace take rudarki, kokuma akwai wani sirri a ranki da kike boyewa, Wanda bakowa yasani ba in bahakaba babu macen dazatayi sha'awar rayuwar aure da Wanda bayajin maganar iyayensa inba kema irinsa bace fitinanniya"" Da sauri Ilham ta kalli Jalila, Jalila ta Dan daga mata gira "Nayi karyane" Gaban Ilham ne yafadi akwai wani abu danake boyewa da bakowa yasani ba ya akai tasan hakan??? "Ba abin mamaki ko tuhuma  a maganata, shawarace kawai tun wuri kisake tunani kinemi hanya me bullewa wannan shshashan be cancanci zama miji ba balle uba in bahakaba seyasaki kukan da kekanki bazaki iya hana kanki ba" cewar Jalila "Enough please meyasa baki da ta ido kinacin zarafin dan uwana kina kiransa da dan giya agabana!!" Ilham tafada cikin shouting "Hold on madam ba ayimin shouting" Jalila ta katseta "Haba mene haka kukeyine bafa yarane kuba wannan be kamata ba we are all sisters" Tabe baki Jalila tayi tace "Ilham nasan zakiji ba dadi amma gaskiya nagaya miki" Bari inje waje in Baku guri ina bukatar recharge card zani insiyo ta dau hijabinta tasaka tafice Gajiya yayi da kwanciya ga bacin rai yana fama a banza akan wannan shedaniyar yarinyar yafito kofar Gida da sigarinsa a hannu kaman kullum Bari yaje Jawwad yazo yarakashi su Dan zaga gari koze rage takaici ya sha sigari kusan kara 7 amma har yanzu ransa a bace yake Cikin gidansu Jawwad yakoma yanufi bangaren Jawwad wayarsa tafara ringing tsayawa yayi ya dakko wayar Cwt dad ne ke kiransa murmushi yadanyi yadaga wayar.    Tazo fita taganshi tsaye bangaren Yaya Jawwad yana amsa waya yana murmushi Kai amma wannan akwai nacin bala'i wai dama yana murmushi Dogon tsaki taja Wanda yasashi waigowa " dubeshi dan Allah kalli askin kanka daganin wannan askin bana mutanene kirki bane kullum baki cikin fidda hayaki kaman salansan tifa ko gajiya bakayi, kuma kazo ka likewa Dan uwana mutumin kirki kana nema ka lalata shi, Kai dashi akwai banbanci shi yana da tarbiyya yana girmama iyayensa sabanin kai kaga kunada banbanci!!!"". (Turkashi kindebota da zafi Jalila mekuke tunani zefaru keep following aakwai cakwakiya fa!!!!!!!!!) Please share ▶▶▶ more comments more typing............ https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL.  🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  6 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. I want comments not stickers😢😢😢😢 Comments dinku  shine kwarin gwiwata        _My first novel_ "Gobe ma in kikaga Jalal kikuma zaginsa useless creature kawai" Yayi tafiyarsa ya barta a gurin tana ta mimmikewa tana fama da numfashi ta galabaita har a tafara fita hayyacinta.   Mummy ce tafito daga sashen daddy zata shiga kitchen ta dinga jin kakari da nishi, dawowa tayi da baya a Dan tsorace, tana duba meke wannan nishin, Jalila tagani a zube a gurin tafita hayyacinta numfashinta nata fita da sauri (Lallai JALILA ta sha hayaki) " subhanallah ke Jalila meyafaru meke damunki??" Tazo tana taba ta "Ohh ni khadija meke damun ta kodama tanada athma ne " Ilham!,  Ilham!!,  Ilham!!!," Tashiga kwala mata kira "Ke Ilham kifito da sauri"     Itakam Nana gajiya tayi da jiran Jalila Dan haka kawai tayi tafiyarta ta shige Gida,kai tsaye taje dakin mummy "Mummy mun dawo " "To sannunku ina Jalilan?" "Wayarta ta manta ta koma dakkowa shine na taho" Kai inkuma Yaya Jalal ne yamata wani abunfa tai wannan tunanin a ranta da sauri tafito ta nufi gidansu Jalal    Shikuwa Jalal gurin Jawwad yatafi abunsa, kaman be aikata komai ba hankalinsa kwance Amma lokaci2 in ya tuna maganganun Jalila se ransa yabaci . Da gudu Ilham tafito "Mummy lafiya kuwa? " zo kiga Ilham dama tanada asthma ne ko wani cutan?" Ilham ta Dan zaro ido "Mummy ya za ayi in Sani"? " maza jeki gidansu kifada suzo akaita Asibiti kar ta mace min a Gida" "To bari in je" Mayafi Ilaham ta dauka ta fito da sauri a bakin gate taci karo da Nana " yawwa Nana Jalila dama tanada asthma ne kowani cutan?" A firgice Nana ta kalleta "Asthma kuma? Bata da wani asthma, me yasameta?" "Zo muje kyagani" Ilham tafada tana janyo hannunta zuwa cikin gidan "Subhanallah Jalila meya sameki?" Nana tafada tana jijjiga Jalila amma Jalila bata San me akeba tafita hayyacinta Da gudu Nana ta tafi gida domin sanar dasu abinda yake faruwa, tana shiga gida a harabar gidan ta ci karo da su Jawwad "Ke Nana lafiyarki kike gudu haka? sekace wata karamar yarinya mene haka" Jawwad ne yayi maganar a Dan fusace "Yaya Jalila CE" "Me yafaru da ita?" Yafada hankalinsa a tashe Nima bansaniba  yaya tana gidansu Yaya Jalal yanzu muke tare da ita takoma dakko wayarta yanzu kuma  ta suma bata iya numfashi sosai "Suma kuma"   Ai bejira tagama bayanin ba yayi hanyar waje da sauri Wani Dan guntun murmushi Jalal yayi sannan yabi bayan Jawwad   Itama Ilham ta karasa cikin Gida dan ta sanar da maama abinda yake faruwa Suna zuwa suka tarar da Jalila kwance akan cinyar mummy bata numfashi, se kadan² "Subhanallah Jalal bani key din motarka mu kaita Asibiti" Jawwad yafada da sauri   Key din ya danka masa memakon ya raka Jawwad sema ta shi da yayi yai ficewarsa Jawwad beyi wata² ba ya dauki Jalila yayi waje da ita yasaka ta a mota ya tada motar kenan Nana ta shigo  gidan ya tsaya ta Shiga motar "Yaya maama tace muyi gaba zata taho in Abba ya dawo" Be amsa mata ba yaja motar "Ilham ki bisu mana kirakasu ko Asibitinne kinga ni badamar in fita yau babanku ya dawo" maama tayi maganar tana duban Ilham "Ba inda zani wallahi Allah ya bata lafiya in nabisu ai bani zan bata lafiya ba" "Haba Ilham amma ai a gidanmu abun yasameta" "Ni wallahi mummy a gajiye nake ba inda zan iya zuwa yadda nagajin nan  hutawa nake sonyi" Ta wuce daki abunta "Ohh ni hadiza yaran nan se a hankali kowanne da halinsa       Suna zuwa Asibitin aka karbesu aka shiga da Jalila emergency don ceto rayuwarta   Wajen karfe Tara na dare Maama sukazo asibitin ita da Abba Wanda yai dai²Da fito da Jalila daga emergency aka basu daki Alhamdilillah numfashinta ya dawo dai² se dai tanata bacci ga drip da aka saka mata " Allah sarki diyata Allah yabaki lafiya, Amma nayi mamaki iya sanina bata da wani ciwo makamancin haka" Abba yafada cike da damuwa yana kallon maama Dan tabe baki maama tayi "A'a to ai ba dolene kasaniba watakila tana dashi mune bamu saniba kasan uwatta bakomai zata gaya mana ba tunda...." "Ya isa haka Zainab.." Abba ya katse maama "Yanzu lafiyarta muke fata ba wani surutu ba" Likitan ne ya shigo domin kara dubata Jawwad ne yayi gyaran murya "doctor meyake damunta ne?" "Eh blockage ne akasamu a airways dinta maybe ta kwarene ko kuma ta shide da wani abun, Zatasamu lafiya insha Allah munyi mata allurai zatayi bacci karku damu Allah yabata lafiya" suka amsa da Ameen Guraren sha daya na dare Abba da Jawwad suka tafi Gida akabar Nana da da maama suka kwana a gurin Jalila    Washe gari da sassafe Jawwad ya tashi ya shirya da nufin ya koma Asibiti, dayake motar Jalal a hannunsa ta kwana kafin ya wuce ya maida motar gidansu Jalal, Jawwad ya tsaya  suka gaisa dame Gadi yayai masa yame jiki dayake yasan meyafaru, ya" amsa da sauki," Jawwad ya juya zefita se yadawo da baya ya kalli me gadin "Jalal yana nan ne" "Eh yana nan yana bangarensa" "Nagode" Jawwad ya juya ya nufi part din Jalal Lamar kullum ya na kwance yayi dai² yana bacci babu alamar yayi salla Jawwad ya daddaki pillown da Jalal yake kwance A hankali Jalal ya bude ido "Tashi kayi sallah Dan nasan bakayi ba" Seda yadan ja seconds sannan ya tashi zaune yana hamma bece masa komai ba ya mike yaje Yai alwala yagabatar da sallar asuba karfe 7:30am "Jalal fushi nake da kai" Jawwad yafada tare da Dan hade rai Jalal ya kalleshi "Why" "Kanwata ba lafiya rai a hannun Allah amma ko ka tambayeni ya jikinta talk less of kace zaka min kara ka dubota to ni na roki arziki ka rakani Asibiti" Dabeyi niyyar zuwa ba amma yaga in yai haka be kyautawa amininsa ba wato Jawwad Dan haka yace "Sorry bross karkayi fushi dani bari in shirya muje" "Seda na roka?" Jawwad yafada yana Dan hada rai Murmushi Jalal yayi "to koma mene ai nace zani in kuma bakasone in koma baccina" "Kai ka isa ni yi Sauri karmu makara ni sonake tana farkawa tafara tozali da fuskata" Girgiza kai kawai Jalal yai a ransa yace ka dorawa kanka wahala saboda wannan banzar yarinyar Mara kunya    Kafin Jalal yagama shiryawa Jawwad yakira maama A waya bugu seda ta kusa tsinkewa sannan ta daga " salami alaikum maama barka da safiya " "Yawwa barka ya daddynaka"? "Muna lafiya dama tahowa zanyi nace ko kuna bukatar wani abun? " a'a bama bukatar komai ka hanzarta dai inaso indawo Gida in huta nibana son zaman Asibiti " "To maama yanzu zan iso insha Allah, nace ya kuwa Jalilan ta farka ne" "Ban saniba in kazo kaganewa idonka kaita wani rawar kai akan yarinyar nan ka kiyayeni wallahi" Ta kashe wayarta Shidai a iya tunaninsa beyi wani abu dabe daceba amma meyasa maama ta dau zafi haka yayi ta zancen zuci har Jalal yagama shiryawa suka tafi Sun isa asibitin dukda Jalal ya Dan bata musu lokaci room din da aka kai Jalila suka nufa Jawwad ne ya bude kofan tare da sallama Maama ce ta amsa dayi musu sannu da zuwa, yawwa tunda kunzo bari mu je Gida dama ruwa zasu karasa mata da allurai kawai su sallameta, Ninazata tun dazu zakazo Abbanku yazo ya dubata yanzu ya tafi. shikam gogan kujera ya janyo ya zauna abinsai be kula kowa ba Alhamdilillah jikin Jalila yayi kyau sun sameta tana rama sallolin dabatayiba "In ta idar Jawwad ka kira nurse din suzo su karasa mata abinda zasuyi mata seku taho Gida" Maama tafada tana shirin tafiya Sukagama abinda zasuyi maama da Nana suka tafi Gida. "Yaya ina kwana" Jalila ta gaisheshi "Lafiya qalau ya jikinnaki?" Jawwad yafada cike da kulawa da sauki Yaya "Waime yafaru dakene? Ya akai haka tafaru"? seda ta kalli inda Jalal yake suka hada ido, tai sauri ta dauke kanta Ta maida kallonta ga Jawwad "Kwarewa nayi" tafada a takaice "Kwarewa kawai numfashi ya dauke ko kinada asthma ne?" "A'a Yaya banida asthma" Duk abun nan Jalal danne² wayarsa kawai yake, ba Wanda ya kula a cikinsu "To tunda kin idar bari inje inkira nurse suzo su miki alluran dafatan kinci abincin?" "Eh naci abinci, amma ban idar da sallah ba zanyi walhane" "Kai sisyna bakida lafiya fa ai Allah yaga zuciyarki" Jawwad ya danyi maganar a shagwabe Jalal ji yayi kaman ya shake Jawwad yaga yanata wani lallabata hada yiwa mace shagwaba saboda shirme (Niko nace a ganinka ba) Itama a shagwaben tafada maganar "Nifa zan iya Yayana kasan sallah haske ce me girrma kuma tana hana mutum aikata wasu laifukan, Yayana abune mawuyaci kaga Wanda ya tsaida sallah yana aikata wasu miyagun laifuka da baya kunyar yinsu agaban mutane, Koda ze aikata yana kunyar mutane suganshi Kaga inka tsaida salloli biyar seka kara da nafila bakasan abinda Allah ze duba a ayyukanka ba yai maka rahama" "Nice one sisyna proud of you Allah yasa iliminki ya amfaneki ya amfani al Umma" Jawwad tafada yana murmushi "Proud of u too bros" Jalal yasan da biyu tayi wannan maganar amma yai kaman besan me sukeba Seda ta idar da sallah takoma kan gadon sannan Jawwad ya kalli Jalal "yace brother zomuje induba nurse din suzo susa mata ayi ai sallamemu" "Jeka dawo ina nan" abinda Jalal yace kenan "OK to bari inje" Gaban Jalila ne yafadi ta kalli Jalal idonsa yana kan wayarsa ba ita yake kallo ba To in yayi min wani abun fa Jawwad nafita Jalal ya kalleta " Kina tsoron in kumayi miki wani abun ne?"ya mike daga inda yake yadawo kujerar gaban gadonta "Meyasa baki gaya musu gaskiya cewa taba kika shaba, rashin sabone kawai, in bahakaba daga shan sigari seki suma kikusa shekawa lahira?" yafada yana murmushin mugunta Banza taymasa taki kallon sa "Yanzu sauranki giya da kwayoyi tunda ina sha kema sekin sha, Kwanan nan kema zaki fara zuwa mashaya" Yafada yana hade rai "Allah ya kiyaye ya tsareni, dazama irinka bazan taba zama irinka ba Mara tarbiyya... " ohoh wait ashefa Ke kin tsaida sallolinki biyar a rana hada nafila nikuma banayi shiyasa Ke ba irirna bace," Nima bani na saiwa kaina ba amma zanyi meyuwuwa inga kinzama Irina tunda jiya kinfara ki rubuta ki aje sauraanki giya da kwayoyi zaki zamaa abar kwatance kaman ABDULJALAL sha³ jahila, I hate u" "God forbid, over my death body kwatance in dai bana Alkhairiba indai irinnaka ne Allah ya kiyaye kuma niba Jahila bace wallahi" Hannu yasaka a aljihunsa ya dakko taba da lighter "naga kaman ta jiya bata isheki ba sokike in kara miki wata" girgiza kai tashigayi tana zare ido "Mara kunyar karya kawai" Yafada tare da maidasu aljihunsa Ya mike ze koma kujerar da ya taso kawai yaji muryarta tana fading "Kuma wallahi Allah ya isa abinda kamin jiya kodayake bakasan ma'anarta ba kona maka bazaka damu ba amma ban yafe wallahi azzalumi kawai me kama da yan daba" Ohh God yarinyar nan ba zata canza ba, Dawowa yayi inda take har gaban gadonta yasa yatsunsa biyu a side din kumatunta ya matsa da karfi Wani uban ihu tasaka saboda zafi jitayi kaman ze Huda mata kumatu da yatsunsa nan da nan hawaye ya shigo zubowa daga idonta wani nabin wani sedayaga fuskarta tayi jawur hawaye na ambaliya a fuskarta Sannan ya cikata Yakoma inda yake zaune da farko yana danna waya Jawwad ne yayi sallama tare da nurse Kallonta  Jawwad yayi "lafiya kuwa sisy kukan me kikeyi?" Seda ta kalli inda Jalal yake amma ba ita yake kallo ba "Ni Kaduna zankoma gurin Ummi'" Tai maganar tanakuma fashewa da kuka Se da Jalal yayi murmushi mugunta "Haba Jalila dama hayanzu kina wannan rikicin naki kiyi hakuri in muka koma Gida mayi wannan maganar" Kai kawai ta gyada masa Nurse din takarasa mata abinda yakamata aka sallemesu. Har suka Shiga mota suka kama hanyar Gida kuka takeyi shikuma Jawwad se aikin rarrashi yake Shikam Jalal Jawwad yafi bashi haushi se wani lallabata yake Itakuwa ita kadai tasan zugin da fuskarta takeyi ga kirjinta hayanzu ba dadi saboda wahalar yin numfashi da tayi (Nikam nace in rashin kunya abinyine gobe maki kara) Maama da Nana suka iso Gida Nana wanka tayi ta kwanta saboda batasamu tayi bacci sosai ba Daren jiya Maama kam datayi wanka seta shiga kitchen da niyyar Dora sanwar rana Sallama taji a parlour Dan haka ta aje abinda take ta domin ganin me sallamar Wata matace mekama da maama sekuma wata budurwa da batafi sa'ar su Nana ba "Yaya mairo sannu da zuwa yanzu kuke Tafe da ranar nan" Wadda takira da Yaya mairo tace "eh mune ai munzo tunsafe bakowa a gidan narasa INA kuka tafi da safe haka gashi ni ba waya a hannuna tasamu matsala, Kukuma makota kowa gate a rufe sekace marasa gaskiya" "Wallahi kinga Jalila ce tazo mana hutu se kuma ta yanke jiki tafadi jiya, A Asibiti muka kwana sedazu muka dawo, mun baro za a sallamata Jawwad ze taho da ita" Wani mugun kallo Yaya mairo tayi mata Sun iso gida lafiya sukayi parking Jalila fuska duk hawaye amma se cewa tayi "Yaya JAWWAD an kira azahar ka tsaya a masallaci kai salla Kasan sallar jam'i tafi lada akan sallar mutum daya kodayake garama Wanda yakeyi shika dai wanima bayayi" Jawwad ne ya kalleta da mamaki  da nufin yayi magana Ta bude kofa tafice da Sauri Shiko Jalal yasan dashi take sarai haka halinta yake bazata canza ba amma seyayi kaman beji me tace ba shi dariya ma taso bashi ganin fuskarta duk hawaye amma Neman magana take Ta nufi cikin gida abinta har yanzu jikinta babu kwari sosai, tana shiga ta nufi dakin maama domin ta Sanar da ita ta dawo an sallameta takama handle din kofar da nufin ta shiga amma maganganun datajine  Suka Sa ta daskare a tsaye zuciyarta ta fara bugawa da karfi "Gaskiya zainabu baki da hankali yanzu har asibiti kikaje jiyyarta kika barota da danki, dangin arna ababen kyama kika bari tana mu'amala da yayanki hartazo miki Gida Hutu koda take musulma ai daga tsatson arna tafito!!!""" Tirkashi wasa farin girki Please share More comments more typing...... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  5 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. I want comments not stickers😢😢😢😢 Comments dinku  shine kwarin gwiwata        _My first novel_ Haka ta tsaya daga inda take ta dinga caccaka masa maganganu son ranta maganganu masu ciwo ciki harda Kalmar dayafi tsana Mara tarbiyya sabida tasan baze iya cinmata ba "Inda zuciya kadena shaye shaye kazama mutumin kirki kacigaba da abota da yayana in ba zuciya kuma kacigaba da zuwa kana like masa cingam ko kuma ince Salansa sarkin hayaki "" Ta juya takoma cikin Gida abinta kaman batayi komai ba Maama ta tarar a palour tana tsifa "Maama kawo in tayaki naga tsifar dayawa " "To karbi kibiyar" Hmm yarinyar nan akwai shiga rai ba ruwanta dukda tasan abinda ke tsakanina da mahaifiyarta amma ko a fuskarta ban taba ganiba, inma dai salon wani makircinne duk zan iya daku d'a na ne dai ba a isa a hada min zuri a da wadda take da raunin nasaba ba, tayi wannan zancen a zuciyarta.      Shikam tsayawa yai cak kaman an dasa shi, yama rasa wani mataki ze dauka, fasa zuwa gurin Jawwad yayi ya koma gida ya shige dakinsa, ya dinga tuttulawa cikinsa giya seda yayi mankas sannan ya zube a gurin yana bacci.     "Nana gaskiya abinda Yar uwarki tamin ya mugun bata min rai, ya dace tafadamin haka agabana taci zarafin Dan uwana, wallahi taci albarkacinki dasena shukamata rashin mutunci wallahi" Itakuma tsayawa zatayi tana kallonki ba bakisan wannan uwarkice a fitsara ba kina ganinta haka shi kansa uban gayyar ina tsoron randa ze danketa (Jalal)Nana tayi maganar a zuciyarta a fili kuma Se cewa tayi "Nasani Ilham bata kyauta ba amma zanmata magana haka halinta yake bata boye abu a ranta komene ne zata fada a gabanka amma kiyi hakuri insha Allah hakan baze kuma faruwa ba" "Kinga ni tafiya zanyi bansamu biyan bukatana sema karamin takaici da kukayi" "Naface kiyi hakuri Dan Allah ki gaida mommy" Banza tayi mata tai tafiyarta a palour taga Jalila nayiwa Maama tsifa harara ta wurgawa Jalila  amma me ita seta maida mata da murmushi "Kigaida Gida sister Ilham agaida mummy da yayanmu" tafada dauke da murmushi a fuskarta Maama CE "Ilham kicewa mummynku in ankawo lesunan tamin magana zan turosu su zaba" "To zangaya mata" shine abinda ta iya fada saboda Jalila takawota iya wuya. Tana zuwa Gida dakinta ta wuce ta nemi guri ta kwanta maganganu Jalila suka shiga dawo mata {"Sedai in akwai wani sirri da kike boyewa Wanda bakowa yasani ba"!!} To ya akayi tasani, taga a iya tunaninta babu Wanda ta taba wannan zancen dashi balle ya gayawa Jalila To ya akayi tagane akwai wani abu a ranta haka taita tunane² Har bacci yayi awon gaba da ita    Se banyan  isha'i sannan giyar  da yasaha tasake shi ya farka daga nannauyan baccin da yayi, ji.yayi kansa yayi mugun nauyi kaman ba a jikinsa yake ba haka ya tashi yana rarraba hanya ya shiga toilet yayo wanka tare da alwala Ya fito palour ya shimfida sallaya yayi azhar yayi la'asar ya dauke sallayar (Nikam nace magariba da ishan fa?) Cikin gida ya shiga ya tarar mummy na waya, ya kai minti biyar yana jira amma wayar taki karewa har ya kosa yagaji da zama yafara tsaki "To Dan sarkin Mara kunya tsakin me kake" mummy tafada bayan ta kammala wayar "Tun dazu na shigo kina kallo amma kin tsaya kina surutu a waya kin barni ina zaman jiranki kuma kinsam gurinki Nazo" "Wayar da nake ne surutun JALAL?" Tafada tana kallonsa "Munyi waya da megidan nan dazu yace in gaya miki  yana dawowa jibi" yafada a takaice batare daya bata amsan tambayrta ba, inba hakaba yanzu zata fara masa fada Takara masa wani takaicin, kuma shi a rayuwarsa ya tasani fada. Ilham datake kitchen taga shigowarsa Dan haka ta aje abinda takeyi ta dakko juice da cup ta dorosu a tray ta fito palour tana yauki ta nufi India Jalal yake Cikin iyayi tafara magana "Yayana ga juice na kawo maka" Bece komai ba sema Kafeta da yayi da ido ko kiftawa ba yayi Nan ta sha jinin jikinta saboda kallon da yakemata "Mtsewwwww" yaja wani dogon tsaki ya mike ze bar palourn "Haba Jalal meyasa kake hakane? Ilham fa kanwarkace koba komai ai yakamata ka karba kasha" mummy tayi maganar adan hasale Ko takansu be biba seda yaje bakin kofa ya tsaya batare da ya waiwayo ba "Yace in gayamiki jirgin karfe hudu ze biyo" (yana nufin mahaifinsa) Yayi gaba abinsa "Na shiga uku mummy meyasa Yaya Jalal yakemin haka kwata² bana gabansa mommy kiyi wani abu Dan Allah wallahi ina son Yayana amma ni meyasa baya sona" Ilham takarasa maganar cikin sheshsheka kuka Rungumota mommy tayi tana rarrashi "kiyi hakuri Ilham ina iya kokarina ni kaina fama nake Jalal kinagani ina mahaifiyarshi amma ban isheshi komai ba Amma in dai ina raye Jalal bashi da wata matar inba keba insha Allah" Aikuwa daga ranar da burina yacika kingama yawo mummy dan sekinyi kuka da hawayenki Dan ba lefi bane in anmaka abinda kayi tafada a ranta amma a zahiri kuma secewa tayi "Allah yasa mummy kitemaka min burina yacika in mallakeshi Dan Allah wallahi in ba shiba bazan iya auren kowaba" "Karki damu Ilham keda Jalal duk abu dayane a gurina insha Allah zanyi duk meyiwuwa inga kin auri Jalal" "Nagode sosai mommyna inkikamin haka kingamamin komai"      Wai ni Jalal  yarinyar nan take cewa innayi zuciya indena kula yayanta saboda muna da banbancin tarbiyya Zanyi maganinta ai rana dubu ta barawo daya tak itace tame kaya zan kamata a hannu Haka yayi ta wannan zancen zucin Bayan kwana daya Gidansu Jalal suka tashi da aikace² saboda shirin dawowar magidan, sedai aikin yayiwa mummyn da Ilham yawa saboda me aikinta ta tafi kauyensu za ai bikin yayarta ga Ilham da shegen son jiki. Dan haka mummy ta Yanke shawarar kiran maama a waya tace Dan Allah tabata Aron su Jalila su tayata aikin dan yayi musu yawa,   kimanin wata hudu kenan rabon mahaifin Jalal da Nigeria Dan haka dole ayi shiri na mussaman domin tarbarsa. A waya ta kira maama ta sanarda ita Dan Allah inba abinda su Jalila suke ta turo su tayata aiki ayyukan dayawa Itakuma tace zata turomatasu Dakinsu mama taje ta sanar dasu sakon mummyn Jalal Nanace tace "To maama zamuje insha Allah" Itakuwa Jalila cikinta ne yayi wata kara me sauti kuuuuuuuu!!! "Na shiga uku ni Jalila !!? " me yafaru ne Jalila?" Nana ta fada tana kallon Jalila "Au tambayata ma kikeyi yanzu in Jalal ya ganni fa? Yanzu ni yazanyi" "Tab yanzu meye abunyi ainamanta da kinmasa rashin M, shiyasa nace miki ba ruwanki dashi Jalila yanzu ga irinta nan" (Nikuwa nace hmm danma bakomai kikasani ba jiyama tamasa rashin kunya" Jalila sarkin rawar kai da shishshigi) "Kinga ni ba wannan ba ko ince kawai bani da lafiya? Se in zamana base naje ba" "Kai Jalila wannan ba shawara bace yanzu fa Maama ta shigo ta ganki ras dake sannan kice baki da lafiya wannan ba shawara bace Sam" "To ya zanyi? Inkuma muka hadu fa ?" "Bazaku haduba insha Allah kitsaya a waje in leka in baya nan seki shigo" "To amma nikam ina jin tsoro Nana" "Ba abinda ze faru insha Allah, kwantar da hankalinki taso mu tafi" A kofar Gida Jalila ta tsaya tana  waige² itakuma Nana ta shiga domin dubawa in Jalal yana nan minti uku Sega Nana ta fito ta kalli JALILA ta girgizamata kai "Shigo baya nan" "Kin tabbata"? "eh na tabbata banganshi a ciki ba, Hmm waike dama kinsan kina jin tsoro amma kika tsokano shi" "Ke ni matsa in wuce tun kafin ya dawo ya ganni anan" Jalila tafada a gaggauce Tare suka shiga cikin gidan Jalila tana ta faman  rarraba ido    A palour suka ci karo da Ilham rike kwanuka zata shiga kitchen, bata kula suba tai shigewarta batace musu komaiba ta shige kitchen ta ajiye kwanukan sannan ta fito sewani shan kanshi take tana hura hanci "Waike Ilham har yanzu abinda yafaru be wuceba a gurinki kike ta wani kallonmu kina hade rai Indai Jalila CE ita tamanta ma kunyi kiyi hakuri Dan Allah" Jalila kuwa a ranta cewa tayi Tab lallai aiki yaganki indai nice bana gani inyi shiru "Hmm bakomai ya wuce kuzo mukarasa mummyn tana ciki" Suka bita gaba daya wani part suka nufa Wanda tunda Jalila tazo a rufe take ganinsa tana kyautata zaton shine part din mahaifin Jalal       Shigarsu yayi dai² da fitowar mummyn dauke da labulaye a hannunta, Nana daga inda suke ta Dan rusuna ta gaisheta ita Kuwa Jalila seda ta durkusa har kaasa, sannan ta gaisheta, fuskarta a sake ta amsamusu Har cikin ranta taji inama Jalal din tane haka yake girmamata Karasawa Jalila tayi gurin mummy ta karbi kayan hannunta "mummy kawo ina za akaisu?" "Dama wasu za a canza wannan zan badasu wanki biyoni seki karbo wasu a canza tace to" Juyowar nan dazatayi taganshi zaune akan kujera, alamu ya dade a gurin itace bata lura dashi ba Nana kuwa tun shigowarsu taganshi a zaune amma ta lura JALILA ba ta Ganshi ba, Be dago ya kalleta ba seda mummy tayi gaba tabiyo bayanta, sannan yayi mata kallon zamu gauraya dake   Itakuwa kallon up and down tayi masa hada murguda baki tayi sauri tabi bayan mummy Akajima Jalila ta dawo da labulaye a hannunta suka fara gyaran part din yana zaune beje ko ina ba " mummy tace Nana da Ilham suzo su siyo abinda babu saboda girki tunda taga Jalila tafisu rashin son jiki" "Mummy indai Jalilace intaga dama batajin aiki " "Ainima naga alama Nana" ILHAM da Nana suka tafi cefane yai saura Jalal, Mummy, se Jalila Mummy ce take kokarin Jan wata durowa na litattafai amma takasa, Jalila tazo ta tayata amma suka kasa, Takaici ya ishi Jalila ganin ga JALAL a zaune amma yakasa temakawa tsaki taja "Mtsewww mummy wannan Dan naki bashi da amfani Sam wallahi yana kallo muna fama amma ko a jikinsa" "India JALAL ne kadan kika gani bari in dakko bagco a rage litattafan mugani ko zamu iya janye durowan" Ita Jalila a hankali tayi maganar batai zaton yajiba, Sedai kawai gani tai yana kallonta Mummy na Barin dakin, ya tashi ya tako har gabanta yana muzurai yana mata wani irin kallo, yana zuwa gabanta yatsaya yadan kura mata ido Nan da nan jikinta ya dau rawa "Mara tarbiyya, Mara amfani, mutumin banza, mekama da yan daba, Dan shaye² Niko?" Yanuna kansa da yatsansa "To bari ingaya miki wani abu ba tsoronki nakeji ba Dana kkyaleki ban  kakkaryaki ba, bana son in batawa Dan uwana rai sedai kawai zan maidake Irina ne, shize tabbatar miki bani da tarbiyya kinga in mukazama mu biyu semunfi dadin kwatance Sha³ Jahila kawai dakikiya na tsani ganin ko fuskarki" Ya juya da nufin yafita yabar dakin " duk jahilcina nasan girman iyayenaa kuma inazuwa makarantar islamiyya, a islamiyyarmu ma nasan akwai ukuba game sabawa iyaye tundaga duniya, dukda Jahilcina bana zuwa mashaya ina girmama manyana, kaga sekanemi waye jahili" Yana jinta kalamanta suna dukan zuciyarsa amma ya fice ya kyaleta da sannu ze maganinta.       Haka sukayita aiki har yamma tayi suka shirya girke² suka gyara ko ina Wanda yakasance Jalila ce karfin aikin       "Karfe hudu da rabi dai² Jawwad da Jalal sukaje airport suka dakko Alhaji Habib Kamal, mahaifin Jalal ya karaso gidansa cike da farincikin ganin tilon dansa cikin koshin lafiya, dukda yawan korafin da mahaifiyar D`an nasa kanyi masa game da miyagun halayen yaron nasu.   Gaba daya sukashiga cikin gidan kowa se fara a yakeyi ana mass sannu dazuwa Daka ganinshi kasan mahaifin Jalal ne saboda  tsabar kamar dasukeyi, kaman yadda yake dabi'ar  Jalila, har kasa ta durkusa ta gaisheshi, Da sakin fuska ya amsa mata tareda cewa " wannan fa?" "Ai Yar wajen marigayi ce kanin babansu Jawwad" mummy tabashi amsa "Allah sarki, Ashe takwarar Jalalce ta girma haka, tubarkallah gata nutsatsiya Allah yaraya ma naku gaba daya" Suka amsa da "Ameen" gaba daya Banda Jalal dayake ta cin magani a ransa yace "wai wannance nutsatsiya munafuka Mara kunya yarinya" Watsewa suka farayi a hankali domin Barin daddy ya huta Ilham ta tafi dakinta tashiga wanka saboda tagaji, Jawwad yakoma Gida Shikuma Jalal yatafi part dinsa Jalila da Nana Suma suka nufi hanyar Gida har sun fito Jalila ta tuna wayarta tana gidansu Jalal inda ta kwaso labulaye daga Shanta "Au Nana wayata rakani in dakko please" "Gaskiya nagaji bazan koma b" "Dan Allah ki rakani, inkuma Jalal yakamani fa?" "A gabanki fa Yakoma part dinsa baya cikin gidan inajiranki anan jeki dakko" "To bari inje" Tashiga ba kowa a palourn Dan haka da sauri tashiga ta dakko wayar, tana zuwa corridor din daze sadata da waje taganshi a tsaye yabawa inda take baya yana waya na Shiga uku inya kamani na shiga uku, wata dabara ta fado mata Ta tako da gudu zata wuce tabayansa caraf ya riketa "Haba karamar Mara kunya kinzaci bansan da shigarki bane yau babu me kwatarki zanga karyar rashin kunya", " meye haka dalla malam cikani" Tafada tana kiciniyar kwace kanta "Ooh har kin manta da maganar mune Zan maidake Irina ne kawai in samu abokiyar shaye²" "Dalla ka cikani ni ba Yar iska bace " "Nima ba Dan iska bane kawai Mara tarbiyane, kema kuma hka nakeso kizama, yanzu sigari kawai zaki sha kema kizama salansa kaman ni kullum bakinki cikin hayaki" Wani mugun kallo tayi masa "Allah ya kiyaye in zama irinka kai halinka har wani abun sone  mara........... Bata karasaba yasaka sigarinsa a baki ya zuka hayakin a bakinsa Ya rikota yasa hannunsa daya ya toshe mata hanci, yasa bakinsa a nata ya dure mata hayakin nan tas a bakinta, aikuwa take numfashinta ya sarke, Yakuma zuka ya dura mata sau uku Sannan yasaketa ta zube tana wani irin tari tana Jan numfashi da kyar, idanun ta sukayi jawur, numfashinta yana sama yana kasa kaman me asthma Share please More comments more typing............ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  7 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Is a free book I want comments not stickers😢😢😢😢 Comments dinku  shine kwarin gwiwata        _My first novel_ Aimin afuwa Today's page isNot Edited "To wai Yaya mairo me kikeso inyine  yaje ya taho da ita yace anan zatayi Hutu to korarta kikeso inyi ko kuma yazanyi Kinsan halin Abban su Jawwad yanason Dan uwansa akan yarinyar nan beki yamin wulakanci ba" Maama tayi maganar cike da damuwa "Seki hade mata fuska yadda nan gaba in ance tazo miki Gida bazata zo ba akan me azo akoyawa yaranki dabi'un arna kinsan ba kunyace dasu ba har kibarta da danki su kwana daki daya da yarinyarki" Jikin Jalila a sanyaye ta saki handle din kofar ta koma da baya idanunta na zubda hawaye bazata iya cigaba da jin wannan miyagun maganganun da cin fuskar ba Wai itace dangin arna ababen kyama to shikenan su arna ba mutane bane Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka taja kafarta ta nufi dakinsu ta shiga ta tarar Nana da wata budurwa wadda batafi sa'arsu ba (wadda sukazo da yaya mairo) sallama tayi a hankali Nana na ganinta ta mike ta rungumeta "Oyo yo Jalilana sannu ya jikin" Murmushin dole Jalila tayiwa Nana Wanda iyakarsa bakinta " da sauki Nana nasaku wahala sannuku Nagode" " shhhh meye kuma wahala anan bana son irin wannan zancen gaskiya babu haka a tsakaninmu" "To na dena Ashe bakuwa kikayi"? " baki ganeta ba Sa'ada cefa Yar gidan Anty mero" "Eyya banganeta bane sannunki" Jalila tafada Sa'ada ta Dan dubeta a yatsine "yawwa sannu" "Nana bari in Dan watsa ruwa" "To a fito lafiya kiyi a hankali inda wani abu daba zaki iya ba kimin magana " Nana tafada cike da kulawa "Karki damu zan iya komai da kaina" Towel ta dauka ta shiga toilet dayake toilet din a cikin daki yake Tana shiga bandakin Sa'ada ta gyara zama cike da gulma "Ke Nana yanzu Dan Allah wannan danginsu arna ne?kuma kike zaune tare da ita ko kyamarta ba kyayi?" A fusace Nana ta kalleta "Mene haka Sa ada ina ruwanki? Waima tukuna ubanwa yagaya miki haka karki karamin irin wannan maganar bana so" Nana tai maganar a fusace "Daga fadan gaskiya se ki kama min jaraba, ai dai kinsan mamanmu bazatayi karya ba ke Yar uwata ce bazanso kishiga wani hali ba ni warin arna ma naji tanayi" "Ke Yar uwata ce Jalila ma Yar uwata ce ta shi kibarmin daki" Jalila kam taji komai duk zancen da sukayi taji a bayan kofa ta jingina jikinta tana zubar da hawaye me kona zuciya Jiki a sanyaye tayi wanka tafito wankan dabata da tabbacin tafita Tana fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa zatayi magana saboda tasan taji abinda Sa'ada tafada Amma Jalila cikin karfin hali da dakewar zuciya tace "Nanancy yau me za a girkamana ne ne yau?" "Kinga Jalila Dan Allah......... Jalila katseta tayi ta hanyar cewa " yau muyi dambu kinsan mutumina ne amma Allah yasa kin iya Dan kinsan nafiki iya girki" Duk yadda Nana taso suyi zancen maganganun da Sa'ada tayi domin tabata hakuri Jalila taki se ta basar da zancen Jawwad kam yakada ya raya Jalal ya bishi suje masallaci yaki yace shi inyaje Gida yayi sallarsa Haka Jawwad ya tafi massalaccin shikadai Bayan yadawone yace bari yaje cikin gida yakuma duba Jalila Dan haka ya nufo cikin gidan Nana ta kalli Jalila tace "Maama kuwa tasan kindawo"? "A'a naga tayi bakuwa shiyasa banjeba kar in takuramata" Jalila tabata amsa " bafa wata bakuwa bace Yaya mairo ce yakamata tasan kin dawo ai " "Hakane bari inje" Yana shigowa palourn ya ga Yaya mairo da Sa'ada gefe ga Maama a zaune "Yau manyan baki mukai kenan Anty mairo ina wuni" "Eh kace haka mana yausha rabonka da gidana baka da zumunci Jawwad Sam wannan halin naka a dangin ubanka ka samo shi Dan mu bahaka muke ba" Tafada cike da isa Shikam har ga Allah Jawwad baya zuwa gidan yaya mairo dukda kasancewarta yayar mahaifiyarsa irin matan nanne masifaffu Wanda basa raina abin magana ga ta da mugun Sa ido kuma intana guri kawai so take abinda ta yanke shiza a yi ga shiga abinda ba ruwanta Shiyasa Jawwad baya kaunar zuwa inda take yanzuma komeye na sako dangin babansa oho? "To yanzu Dai Allah yabaki hakuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allah zaki dinga ganina har kigaji da zuwana" "Kaji dashi dai" "Maama ya jikin Jalilan kuwa?" Ya fada cike da kulawa yana basar da zancen Yaya mairo Maama ta Dan yatsina fuska "Wace Jalilan kuma bayan wadda na baroku tare a asibiti " "Maama to ai tun dazu muka dawo baki ganta bane?" Har Jalila zata fita daga dakin " Nana tace tsaya mutafi tare karki fadi a hanya" "Hh Nana kenan yadda nake jina yanzu ko dambe zamuyi ai sena zaneki yi zamanki bari inje" Dariya Nana tayi lallai kinji sauki    "Hmmm kingani ko dan Allah ji yadda yake wani nuna damuwa akanta jikar arna wallahi in baki wasa ba Zainab, yarinyar nan da uwarta se ta shanye miki ya'ya, arna ba abun yadda bane karki tona sallar datake ganin idon mutane ne watakila a boye a can inda take ita da uwarta suna zuwa coci" "Wlh nima bakiga wulakancin da Nana tayimin ba saboda wannan yarinyar hadda in fita in barmata daki" Sa'ada ta tsoma baki, Sa'ada irin halinsu daya da uwata bata da kunya Sam Daka ganta zakasan idonta a bude take fuskarta tayi Jawur saboda bleaching Ran Jawwad ne ya baci matuka "Haba Anty mairo wane irin cin zarafi ne wannan kuma hada mahaifiyarta wannan....... " dalla rufemin baki sakarai Wanda besan me rayuwa take ciki ba ina magana kana gayamin wai cin zarafine, Yaya mairo ta katseshi a tsawace Kingani ko Zainab kinga abinda nake fada miki ko kalli Jawwad ina fada yana fada saboda rashin kunya wallahi ki raba yayanki da waccan Yar arnan in ba hakaba wallahi wataran zaki gansu a church suma "Kaga Jawwad ta shi kafita jeka" Maama tafada tana nuna masa hanyar fita Mikewar nan dazeyi yafita yaga Jalila a tsaye idanunta taf da hawaye alamun taji komai Girgiza kai yayi yafice zuciyarsa a cunkushe ji yake kaman shi akayiwa wannan cin zarafin Da gudu Jalila ta dawo daki ta shige bandaki ta rufe kofa Abin yabawa Nana mamaki meyafaru haka Kofar bandakin tafara bugawa a hankali "Jalila meyafaru ne?" Jalila ta daidaita nutsuwarta tace "Ina zuwa" "OK nagane inkin fito ga abincinki nan" Nana tafada Itakam Jalila gefen bath ta zauna ta dunga zubarda hawaye masu kona zuciya   Why meyasa akemin wannan cin zarafin nida ummina ake kiranmu arna naga dai ba Wanda zece kaf zuri'arsa tun saga farkonsu har karshensu musulmaine,   Ummi meyasa kika auri abina kika haifeni, tun tasowata dangin mahaifina kemin wannan cin zarafin har yanzu basu dena ba yaushe wannan abun ze kare, Wasu zafafan hawayene suka cigaba da zuba daga idonta Bata san tsahon lokacin data dauka a bandakin ba tana wannan kukan har tagaji ta fito, Ta canza kaya ta dai daita nutsuwarta ta fito palourn, Yaya mairo basu tafi ba Nana tana parlour tana karanta wani English novel "the wish" Maama kuma tana kitchen Kaman kullum har kasa Jalila ta tsuguna "Anty ina yuni" "Lafiya " Shine abinda ta fada a wulakance Tashige dakin maama zatayi salla Jalila kuwa seta nuna ko a jikinta Nana ta kalleta "Ashe Allah yayi miki fitowa daga bandakin, sekace me haihuwa kika shiga kikayi tsit" Murmushi Jalila tayi "To wayasani ko itan nayi" Sa'ada kallon Jalila  tayi a wulakance Ta tabe baki "A gurin arna haihuwar shege a bandaki ai ba sabon abu bane" Sa'ada tafa da A fusace Nana ta dago zatayi magana Jalila ta rigata "Aikuwa dai ba kunya sukeji ba tunda basa kunyar su raini cikin shege su Haifa su rains wasu kuwa zubarwa sukeyi Kinga, gara laifin arna Dana muna musulmi Wanda yasani ya take kodayake wasu ai sunan ana musulin cine ba asan ma'anarsa ba" Tana gama fadin haka ta shige kitchen gurin maama "Sannu da Gida maama" "Yawwa ya jikin " Maama tafada cike da basarwa "Naji sauki akwai abinda zan tayaki ne" "A'a jeki abinki" A parlour kuwa Nana ce ta dingayiwa Sa'ada dariya tace gobe ma kikuma in baki yasan meze fada besan abinda za a mayar masa ba Jalila kuwa daga kitchen din nan harabar gidan ta fito ta dauki kujera ta tafi gaban flowers ta zauna,, Tanata tunani zuciyarta sam ba dadi, ga wani Abu da ya tokaremata a kirji Wanda tasan Bacin Raine, gashi rabonta da abinci tun Wanda taci da safe a asibiti Wanda Nana takawo mata dazu bataci ba ko yunwar bataji, saboda Bacin rai taga hakan baze fishsheta ba dan haka tafara rera karatun Qur'ani cikin sauti me dadi A hankali taji zuciyarta tana sanyi yanayin yayi mata dadi ga yammaci ga flowers din na dauke da furanni masu kyau Dan haka taci gaba da karatun cike da jin dadi da kwarin gwiwa A hankali take jin taku ana tahowa inda take bata waigaba kuma bata dena karatunta ba "Masha Allah " Taji muryar Jawwad yafada seda ta kai karshen ayar sannan ta tsaya Ko ba a gayamata ba tasan tare yake da mayennasa wato Jalal saboda taji kamshin turarensa Gabanta ya zagayo ya tsugunna "Dafatan ban katseki ba ya sayyada?" Jawwad yafada "A'a  yayana, sannu dazuwa" " cigaba da karatunki" "Ai na idar dama Abeena nakewa Allah ya kaimasa ladan kabarinsa, Babban abinda zamuyi idan iyayenmu na Raye shine muyi musu biyayya kar mu yadda muyi sa'insa dasu ko mudaga musu murya, Fushinsu masifa ne a rayuwar mu, tunda bamu ISA mu biyasu ba dawainiyar dasukayi damu ba, in sun rasu kuma muyi musu addu'a saboda bamu da tamkarsu" "Wannan gaskiyane sister lyk no other ina alfahari dake" Lallai yarinyar nan kullum in muka hadu seta gayamin bakaken magana waini zatayiwa wa'azi Kijira zakiga yanda zanyi maganinki a karo na gaba Jalal yayi wannan maganar a zuciyarsa "Jalila nasan kinji abinda Yaya mairo tafada amma Dan Allah......... " shhhh ni banji komai ba Yaya kamanta kawai" Jalila tayi maganar tana murmushi "Kai ni nagaji malam Kasan banason jira ka ta shi muje kabani abinda zakabani in tafi seka dawo ka cigaba da shirmen" Hakan yayi dai² da fitowar su Yaya mairo Maama tayo musu rakiya "Zainab Dan Allah dubi danki kalleshi ga yadda ya gurfana a gabanta, kaman zata masa gafara wannan shegiyar yarinyar in baki da mataki akanta ba setasaki kika, Wannan yaronnaki yadda yake rawar kai akanta seta dilmiya shi" Jiki a sanyaye Jawwad ya mike ita kam Jalila sunkuyar da kai tayi "Bahaka bane Anty mairo ina mata sannune" "Ubanka kake mata ba sannu ba wadda kayi mata a asibitin bata isa ba sakarai kawai ka wani gurfana a gaban ta sekace uwarka"   Shikam Jalal tuni ransa ya gama baci yana kuma jinjina hakurin Jawwad da shine wallahi babu matar daze tsaya tana masa masifa haka "Dan Allah Jawwad kaje kabani in tafi nagaji Kasan bana son tsayuwa kuma wannan matar tazo tanawa mutane hayaniya da shirme aka zata sawa mutane ciwon kai 😱😱😱😱 JALAL  yayi maganar cike da masifa "JALAL itama mahaifiya tace fa yayar maama ce" Sakin baki Yaya mairo tayi tana kallon ikon Allah Itakam Sa'ada ganin JALAL seda gabanta tayi mummunar faduwa Maama tayi shiru saboda bata shiga shirgin abotar su tasan halin JALAL sarai "To ni Ina ruwana kai ka taba ganin me uwa biyu Dalla ka tsaya ana zaginka haifarka tayi meye na zaginka dan tana yar mamanka  haka akeyi?" "Wannan Dan iskan fa daga ina" Yaya mairo tafada tana kallon Jawwad "Emm da... " magana nake maka kana kame² nace wannan Dan iskan yaron Mara mutunci daga ina Zainab magana nake kunyi shiru kuna kallona" Itakam Jalila silalewa tayi tabar gurin JALAL yazo gaban Yaya mairo yatsaya " fadi da kyau ni dan iska ne Mara mutunci, amma kinfini kama dasu tunda kema kin haifi dan iskan boye da bakowa yasan shiba Dafa kafadarsa Jawwad tayi "Bros Dan girman Allah kayi shiru mana Yayar uwata  ai uwace ai yakamata kaimin kara" yafada jikinsa a sanyaye "A'a kyaleshi yacigaba da zagina" Tafada tana zare ido Jalal ya kalli Jawwad "a ganinka duk wannan ba kara nayi makaba, kai kasan in wanine yagayamin haka da wani zancen ake ba wannan ba Dalla cikani" ya fizge hannunsa yayi waje Da kyar Maama ta lallaba Yaya mairo ta tafi se zage² takeyi Yau dai ansha drama a gidansu Jawwad Jalal kuwa yana zuwa Gida  dakinsa  ya yatafi "Mtseww munafukar mata waini ne Dan iska itama fa tanada yan iskan nan amma ta zageni, wallahi badan Jawwad ba da yanzu hakoranta se dai asaka ranar Samata na roba" Haka yaita surutai shikadai wayarsa ce ta fara ringing Dagawa tayi yasaka a kunnensa "To ina zuwa" shine kawai abinda yafada, ransa duk a bace yake yau, haka ya fito ya nufi cikin gidan Ilham ce tai sallama ta kaiwa Jalila wayarta da ta Yar a gidansu lokacin data fadi Sannan taga yamata cewar baban Jalal yana kiranta "To Allah yasa ba laifi nayi masa ba" "In munje kya gani" Ilham tabata amsa "Nana zo muje ki rakani" "A'a aiki zatamin sekace za akamaki kije ki dawo" Maama tayi maganar a takaice Daddynsa ya tarar da mummy a zaune ba sallama balle gaisuwa fuskar nan ba fara'a "Daddy gani" "Yawwa Dan albarka dama magana nakeso muyi, mummynka tace ka dena zuwa makaranta, kuma wai Dubai zaka tafi? Ya akayi ne?" Wani mugun kallo yai wa mummyn "Eh hakane Dubai nakeso in tafi" "Karatun fa mummy tafada a fusace " bazanba" yabata amsa "Kaji ko? hakafa nake fama dashi bayajin maganata baya ganin girmana, Wallahi Jalal kar ka bari ka mutu baka dena abinda kake kana sabamin ba" Su Jalila tun dazu suka shigo suka tarar  ana wannan fafatawar Mikewa yayi ya nufi hanyar fita yana masifa idonsa Jawur "Ni akayiwa laifi ni yakamata anemi yafiya kece silar komai amma kin rufe idonki laifina kawai kikegani ni akayiw laifi kuma kece kika jamin duk wata kalar rayuwa Dana keyi" JALAL Yayi maganar cikin karaji "Bazaka taba canzawa ba, ba adagawa iyaye murya, ba a sa'insa dasu Amma kai hakan ba komai ne a gurinka ba, ta Yaya zakaga haske a rayuwarka Se mutane sunce Baka da tarbiyya kaji haushi, anya kanaso kagama da duniya lafiya?" ( Jalila kenan damusar kwali ga tsoro ga ban tsoro) Aikuwa gadan² JALAL ya nufi inda take idonsa babu alamar tausayi.. Share please More comments more typing........... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊 [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  9 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Is a free book Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤ I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage Wannan yarinyar kwai bakar Jarababbiya kome za ayi mata bazata dena magana ba in taga abin magana, kozaka kasheta setayi magana Kallon ta Jalal ya cigaba dayi yana jinjina bakin taurin kai irin na Jalila Itakam Jalila dariyarta ta cigaba dayi "Tab wai akan wannan kike wannan kukan aiki yasamu wata, tab sannufa Ilham kin dorawa kanki wahala wallahi....." Jalal kallon Jalila yayi cike da takaici Jalal girgiza kai kawai yayi ya fice saboda ya fuskanci in yacigaba da biyewa maganganun yarinyar nan to tabbas bakin ciki ze iya masa illa "Jalila meye hakane wai ina ruwanki dasu taho mu tafi" Nana tai maganar tana janyo hannunta "Munafukar banza kawai se tsabar shishshigi da Sa ido aikin banza kawai" Ilham ta fada tana jujjuya Ido Saboda cusa takaici se Jalila takara tuntsurewa da dariya "Allah ya temaki matar Dan giya wannan soyayyar kaman a Bollywood ke kinga wani hawaye kaman ta tsaya agaban director hh mrs. Jalal" "Na shiga uku nikam Jalila meye haka wai dama haka kike ba dadi fa Ni dai taho mu tafi" Nana ta fada tana kuma Jan hannun Jalila Ilham kam rasa bakin magana tayi kamewa tayi tarasa abin cewa Suna fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa "Haba Jalila why? Abinda kikayiwa Ilham be dace ba wallahi bazataji dadi ba" "Lallai Nana ke bakiga wulakancin da tayimn da farko ba har munafuka tacemin fa" " haba Jalila da baki kulasu da bazata gaya miki ba " "Sorry Nanancy kinsan bana gani inyi shirune kawai, in ta kwantar da hankalinta gobe insha Allah zan bar garin nan" "Jalila dena tunamin banason tuna gobe in Allah ya kaimu zaki tafi duk se inji na damu" Nana ta fada a sanyaye "Nima banason barinku amma very soon zan dawo insha Allah" "Allah yasa da gaske kike" "Da gaske mana" Dayake me Hali baya fasa halinsa sukaga Jalal a harabar Gidan yana kokarin bude motarsa "Wai akan wannan ake kuka, Allah ya kyauta, har ake Neman a zageni gaskiya Ilham Yar wahala CE" "Na shiga uku ni Nana, Jalila haka kike dama?" "Ai ni nafi haka ma duk abinda nasan ba a so ko akemin gadara akansa to nikuma shi nakeyi" Jalal da ya riga ya shiga mota yana jinsu dayake suna daf dashi tayi maganar shiru yayi bece uffan ba Sema kokarin tada motarsa da yake Washe gari da safe Jalila ji take kaman za asa ta a Aljanna yau zata koma gida gurin umminta, Kuma zata rabu da wannan mugun, kuma se yaya mairo taganta zata kuma cin zarafinta, se shirinta takeyi amma  lokacin kanta yana mata ciwo tunda Jalal ya mareta kanta kemata ciwo Nana tana wanka Jalila ta hada kayan ta cif Jawwad ya shigo dakin yasameta tana kallon akwatin ta "Yar gidan Ummi kingama shirin kenan?" Jawwad yafada yana zama a gefen gado "Eh Yaya nagama" "To insha Allah in an sakko daga masallaci zamu tafi kizama cikin shiri in ma dawo zamu tafi" "Aini ko yanzu kace mu tafi na shirya," "Eh kyace haka saboda kin gaji da zama damu ko?" "A'a nifa nace muku bahaka bane" Ta fada a shagwabe "To shikenan naji kar kimin kuka" Jawwad yayi maganar da sigar tsokana Daga nan ya tashi ya tafi Bayan fitarsa da ba dadewa Ilham ta shigo hannunta dauke da ledar bagco, ta tarar da Nana da Jalila su suna cin abinci suna hira Jalila tana ganinta ta sunkuyar da kai tana dariya kasa² "Mtseww" Nana taja uban tsaki ta direwa Jalila bagcon a gabanta "gashi nan Inji mummy, sakon daddy ma yana ciki" Ta fada tare da juyawa zata tafi "Haba Ilham kya tsaya kuyi sallama fa yau zata tafi" "Ta sauka lafiya " Shine abinda kawai Ilham tafada tai ficewarta Itakam Jalila ta kudure a ranta seta tsokani Ilham amma tasan in tayi a gaban Nana mita zatayi mata Dan haka se cewa tayi "Nana ina zuwa" "Ina zaki?" "2mint yanzu zan dawo" Ta biyo bayan Ilham se ta hangeta ta tsaya  tana waya a wajen flowers din gidan Seta nufi inda Ilham take amma kafin takarasa taji tana waya "Wallahi mami nafara gajiya wulakancin yau daban na gobe daban Sam Hankalinsa baya kaina jiyama bakiga wulakancin da yayimi ba am tired wallahi" Jalila Batajin me akace daga daya bangaren "Hakane mami, Allah ya nuna mana lokacin da burinmu ze cika zan cigaba da hakuri in cigaba da kokari se burinmu ya cika akan Jalal da mummyn Sa" Buri kuma, Wane irin buri ne haka hasashe na ze zama gaskiya kenan Jalila tayi maganar a zuciyarta Fasa abinda tayi niyya tayi takoma cikin Gida Kayan da aka aikomata daga gidansu Jalal taga Nana tana budewa Less ne me kyau da agogo se turare da wani Dan karamin kit Ja anyi rubutun larabci a jiki Qur'ani ne izu sitting a ciki me matukar kyau Se envelope da akasaka kudi dubu goma A jiki aka rubuta safe journey from daddy "Yanzu duk wannan nawane?" "Ai Jalila indai kyauta ne babansu Jalal akwai kyauta yana da kirki sosai" "Nana ni duk Qur'anin nan yafi min kyau bazan dinga bude shi ba ajiye shi zan in dinga kallonsa yayi kyau sosai ajiya zan masa me kyau" Nana ta kwashe da dariya "To ai saboda  ki karanta akabaki shi sekuma yazama abin kallo" "Eh mana koba komai zan dinga tuna baban zalimu ne yabani" "Me kikace Jalila?" "Ba komai, bari inje in nunawa maama kayan" Zuwa sukayi suka nuna mata ba fuskarta ba yabo ba fallasa tace yakamata taje tayi musu godiya Sannan itama tabata abinda zata bata Abba yayi mata nasiha sosai sannan yace university a kano zatayi in lokaci yayi zezo a Dakota daga Kaduna Jalila ko a jikinta bata dauki abun serious ba ita dai babban burinta taga sun kama hangar Kaduna haka yaimata alheri shima tare da yimata nasiha akan hakuri da rayuwa ta kula da tarbiyarta sannan tayi karatu. Misalin karfe biyu tagama shirinta tsaf JAWWAD kawai take jira after dress ce a jikinta baka se mayafin After dress din data yafa akanta tayi kyau matuka Taje gidansu Jalal tayi musu godiya Daddyn Jalal shima haka yayi mata nasiha tai musu godiya ta fito taga Ilham ta dawo maybe wani gurin taje "Juliet INA romeon naki,? Tafada cike da tsokana Nikam yau zan koma inda na fi wayo nasan na bata miki a Dan zaman damukayi kiyi hakuri Ilham ni duk abinda na miki wasa ne" Mtsewww Ilham taja wani dogon tsaki "Ke kikasani ma gulmaciyar banza kawai" Ilham ta fada tana ma Jalila kallon up and down Jalila tayi wani kasaitaccen murmushi "Nagode Yar wahala nice ma ke, let me tell u something ur mission will fail u will never succeed" Tafice daga gidan tabar Ilham tsaye tana juya maganar Jalila "Ur mission will fail" A harabar gidan taga Jawwad da mayensa Jawwad yasamata trolley dinta a boot Jawwad na ganinta yace "Masha Allah  looking so gorgeous sisyna let's take a pic" Kusa dashi Jalila taje ta tsaya sukai ta hotuna hada Nana Shikam gogan wani uban tsaki ya dinga Ja ganin yadda JAWWAD yake biyewa wannan fitsararriyar yarinyar Nana ce ta rungumo Jalila tana share kwalla "Dan Allah kikuma dawowa" "Insha Allah karki damu Nanancy na zankuma zuwa insha Allah" Suka shiga Jalila suka kuma sallama da maama sannan ta fito Jawwad ya Riga ya shiga ya kunna mota yana jira ta karaso ta faki idon Jawwad Tacewa Jalal to yau zan tafi se hankalinka ya kwanta bame kumayi maka shishshigi amma zan tuna maka ne ban yafema cin zalina da kaiba mugu kawai kuma insha Allah se...... Bige mata baki yayi "Ki barni da Wanda akayi min a baya yake wahal dani, in kika sake kikamin mummunar addu'a a sena baki mamaki A cikin gidan naku a gaban yayan ki zan tattakaki in koya mini hankali dama namiki alkawarin maida ke Irina amma tunda tafiya zakiyi yayanki zan mayar Irina, in ya aureki se aji dadin fada matar Dan giya wuce ki bani guri ko in barar dake anan Mara kunya sha³" Kaman munafuka haka ta wuce tana shafa baki taga ko Jini ya fito Nana tafito da karfi race "Jalila safe journey I will miss u" Daga mata hannu kawai Jalila tayi ta shiga gaban motar saboda bakinta ji take kaman banata ba Jalal ne yazagayo inda Jawwad yake dan uwana a sauka lafiya, ka dawo da wuri Dan Allah, akwai wani zazzafan guri dazaka rakani Jalila ta dago da sauri tana kallonsa Allah ka tsaremin yayana "Ta Allah bataka ba " Tafada a fili "Ya dai magana kike ne" Jalal yai mata tambayar "Bakina ne a haka tabashi amsa" "Na fuskanci dai ba kwa jituwa, Jalal ma fa yayankine" Jawwad  yai magNar yana kallon Jalila "Allah ya kiyaye" "Dan uwana ina dawowa zan raka ka insha Allah idan na dawo" Jalal yafada yafara Jan mortar "To seka dawo" Sun hau kan kwalta sosai Jawwad tuki yake a hankali cikin kwarewa Jalila tayi nisa cikin tunani "KE YAKAMATA KINEMI YAFIYATA , DUK WANI ABU DANAKE AIKATAWA KECE SILA, KINSAM GASKIYA AMMA KIN RUFE IDONKI KINAMIN FADA" "ZANCIGABA DA HAKURI HAR BURINMU YA CIKA AKAN JALAL DA MUMMYN SA" "KARKI SAKE KIMIN MUMMUNAR ADDU'A KIBARNI DA WANDA AKAYI MIN ABAYA YAKE WAHAL DANI"!!!!!! Gaskiya akwai abubuwa masu rikitarwa game da rayuwar Jalal haka nan taji tana son Sani " sisyna" "Na'am yayana" "Nasan abinda yasa kikeson komawa gida, yana da nasaba da abinda Yaya mairo taimiki, Amma Dan Allah kiyi hakuri ki dena bari irin wannan maganganun suna tasiri a zuciyarki kowa yasani dagake har Ummi mutanen kirki ne Ni kaina banji dadinin abinda tayi ba" "Yaya na nifa ba hakane yasa zan koma Gida ba kamanta kawai" "Kin tabbata?" "Eh na tabbata babban Yaya" "To yanzu se yaushe zaki dawo?" "Se wataran" "Se wataran kuma ba rana kenan" "Hhh da wataran zan dawo" "Hmm to shikenan" Shiru ya Dan ratsa "Yaya Jawwad" "Nana'am Anty JALILA" Murmushi tayi "Wadan dan Allah wace Ilham a gurin Jalal" "Yaya JALAL dai shima yayanki ne" Allah ya kiyaye Amma a fili se tace "To naji zan dinga fada" "Yawwa sisyna Yadda muke dake cousins haka ILHAM take da Jalal da mummyn Jalal da mamann ILHAM ubansu daya Gyada kai Jalila tayi " to meyasa Jalal yake haka, meyasa kuma ka ke abota dashi,? Gashi ya raina mamansa kaga abinda yake mata kuwa? "JALAL ko?" JAWWAD yafada yana kallonta "Au namanta Yaya JALAL" Ajiyar zuciya yayi yace "Se randa kika dawo kano zan baki amsoshin tambayoyinki" "Why not now? Ta tambayeshi " kawai sekin dawo Kano zan gaya miki ke dai in kinyi sallh kidinga Sa shi a addu'a Gyada kai kawai tayi Amma a ranta cewa tai tabdij nida kano ai seda wani babban dalili A gefe data kuma zuciyarta na kwadaita mata son sanin waye Jalal Share please More comments more typing....... Aimin afuwa page din yau bashi da yawa am busy that's why Naji shiru ba akawon ragon salla ba In ba abani ba nadena typing se bayan salla lolz😂 Inayinku masoya wannan novel irin sosai din nan ❤❤❤ comments dinku na kayatarr dani Ku biyoni a hankali domin ganin darrusan dake cikin littafin 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  8 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Is a free book I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage I dedicated this page to you sister like no other Saddika Adam (baby) can't love u less But stop asking silly questions if not zan hadaki da JALAL lolz        _My first novel_ Aimin afuwa Today's page is Not Edited Gadan² yanufi inda Jalila take, Kasa kwakwakwaran motsi Jalila tayi, ta kuramasa ido jira kawai take taga hukuncin daze mata   kawai se ya canza shawara ya koma ya fice daga palourn Ajiyar zuciya Jalila tayi dataga be mata komai ba Ilham ta kalli Jalila cike da bacin rai "Waike Dan Allah meyasa kika fiye shishshigine ina ruwanki da shi wannan fa sabgar family ce meye naki a ciki Yar karere"? Jalila ta kalleta tai maganar kasa² "Hmm so hana ganin laifi" Daddyn Jalal ne yayi gyaran murya yace "A'a Ilham abinda yayanki yake baya kyautawa abinda takwararsa tafada gaskiyane se dai muyi masa fatan Allah ya shiryeshi" Wani dam kirjin Ilham yayi takwararsa kuma? Tai maganar a zuciyar ta Jalila ta karasa cikin palourn ta durkusa har kasa ta gaishe da daddyn Jalal Mummy kuwa tuni tabar palourn ranta yana daci game da abubuwan da Jalal yakeyi Sam baya ganin kimarta a matsayinsa na Dan da ta haifa Fuskarsa a sake ya amsa mata gaisuwar "Jiya ake gayamin baki da lafiya har an kaiki Asibiti, dazu mummyn su zata je dubaki da safe akace Baku dawo ba, "Yanzu ya jikin naki"? " ai naji sauki daddy " Tayi maganar kanta a kasa "To dama kiran kenan in miki sannu Ya gurin mamanki ?" "Tana nan lafiya" "Masha Allah kin dawo nan ne gaba daya"? "A'a zuwa nayi nakusa komawa" "Allah sarki in kin tashi tafiya kizo muyi sallama kafin kitafi" "To daddy nagode" "Yawwa Allah yabaki lafiya" "Ameen" Ta amsa "To daddy seda safe" "Allah ya tashemu lafiya daddy nagode" "Ameen Yar albarka Allah yayi miki Albarka" "Ameen ta mike ta nufi hanyar fita" "Daddy dama kasanta ne?" Ilham tafada tana ya mutsa fuska "Nasanta Ilham amma tun tana Karama nasan mahaifinta kanin Alhaji Mahmud ne (baban su Jawwad) mutumin kirkine sosai" Dan tabe baki kawai Ilham tayi Jalila kam kama hanyar fita tayi taji an riketa a firgice ta waiwayo taga waye da wannan aikin Jalal tagani idon Sa Jawur yana wani irin huci Ya daga hannu ya wanka mata mari, ta gigice tana nema ta fadi, ya dagota yakuma wanka mata wani Marin Hannu biyu tasa ta dafe fuskarta lokaci guda kuma hawaye na zubowa daga idonta, "Why meyasa kike son shiga rayuwata? Ina ruwanki dani? Sa'anki ne ni ko dankinga ina kyaleki  saboda yayanki nake daga miki kafa, amma ki tambayeshi waye ABDULJALAL!!! ba a shigowa hanyata duk Wanda ya shiga rayuwata se na tabbatar Dana koya masa darasin da har ya mutu baze manta ba, Kifita daga rayuwata nagaya miki sha³ kawai I hate u!!!" Yafada yana kuma zazzaro mata ido "Bazan fita ba, in har bazaka rabu da yayana ba kuma bari in gayamaka baka isa kamin abinda Allah bemin ba" Ta fizge hannunta tai tafiyarta fuskarta na cigaba da radadi saboda Marin ya shigeta seda tai gaba ta tsaya ta waigo ta kalleshi "Ka rubuta ka ajiye Marin nan dakayi min seka biya shi kuma na fada Mara tarbiyya, in kaji haushi kadena abinda kake, sannan ka koma makaranta Dan wannan abinda kake ba alamar Ilimi a tare da kai in kaga dama ka yayyankani ka cinye I hate u too, Tai ficewarta ta tafi Gida, harta shiga gidan, ta tafi dakinsu bata ci karo da kowa ba, Nana ma bata dakin, dan haka ta dau wayarta da Ilham ta kawo mata dazu Missed calls din Ummi tagani a ciki dayawa sekuma na kawarta siyama " Allah sarki Ummi na nayi missing dinki, dole ma inzo in tattara kayana in bar garin nan tsakanin Jiya da yau nayi Dana sanin zuwa kano ga cin zarafin da wannan matar tayimin, ga kuma wannan Azzalumin Dan shaye² da yakeneman illatani In na tafi bazan sake zuwa kano ba insha Allah gobe zanyiwa Abba magana ni Gida zan koma" Tai dialing lambar Ummi bugu biyu ta dauka "Jalila meya faru nake ta kiran wayarki tun jiya da daddare amma baki daga ba?" Ummi tayi maganar cike da damuwa "Ummi wayace a silent kuma na manta inda na ajiyeta se dazu na ganta" "Jalila akwai matsalane? Naji muryarki wani iri, ko baki da lafiya ne?" "A" a lafiyata kalau mura nake ne" Badan Ummi ta yarda ba ta bar zancen "Ya gidan ya yan uwan baki?" "Kowa lafiya Ummi" "Ina fatan ba wata Matsala dai ko?" Matsala kam akwaita very soon ma zan dawo Gida amma a zahiri se cewa tayi "Eh babu wata matsala amma a satin nan zan dawo Gida insha Allah" "Kin fasa hutun a nan ne? " Eh nafasa kewarki ce ta dameni Gida zan dawo " Ummi ta fuskanci akwai matsala Jalila bata son gaya mata ne. "To shikenan se da safe ki gaida mutan gidan naku" "Zasuji insha Allah, mu kwana lafiya kyakykyawar uwa" "Ameen yar albarka" Tagama wayar kenan Sega Nana ta shigo "Yar uwa kin dawo Ashe ? Kiran me akayi miki ince ko lafiya" "Lafiya kalau, dama babansu Jalal ne yamin ya Jiki, sannan yace ranar dazan tafi inzo,"   "Allah sarki babansu Jalal akwai kirki kaddarace tasa Allah ya hada shi da tantirin da, kodayake yana Dan ganin girman babansa akan mummyn shi" "To Allah ya shiryeshi in me shiryuwane" Jalila ta fada tana mikewa domin ta gabatar da sallar isha'i Bayan sun kwanta Jalila takasa bacci se Juyi take kanta har ciwo yake saboda zafin Marin da ta sha "NI KIKAYIWA LAIFI YAFIYATA YAKAMATA KINEMA BANI ZANNEMI YAFIYARKI BA KIN SAN GASKIYA AMMA KIN RUFE IDO KINAMIN FADA KECE SILAR KOWACE RAYUWA NAKE A YANZU" Maganganun Jalal suka dawo mata To me hakan ke nufi lallai akwai wani abu a kasa Wai meyasa duk lokacin dazan hadu da yarinyar nan se tayi abunda zata konamin rai, seta gayamin maganganun dazasu bata min rai Meyasa ta kenema ta Shiga rayuwata, ba Wanda ya isa ya tsaya gabana yana gayamin abinda ya gadama, Ina daga mata kafa ne saboda aminina, Ire iren wannan tunanin Jalal ya dingayi ga mummy itama ta caza mai kai ransa yagama baci zuciyarsa a cunkushe Dan haka ya yanke shawarar abinda ze fishsheshi Dan haka ya dau motarsa ya tafi mashaya gurin Jeje. Jawwad ganin abinda yafaru dazu tsakanin Yaya mairo da Jalal yasan Jalal fushi yake dashi Dan haka ya yanke shawarar zuwa yabashi hakuri. Yaje part din Jalal amma bayanan, yashiga cikin gidansu nan ma bayanan Ya dinga kiransa a waya amma shiru be dauka ba. Dan haka ya koma Gida har ya kwanta yaji yanaso yasan inda Jalal ya tafi. Danhaka ya kuma komawa gidansu Jalal don ya duba ko ya dawo,dayake Jawwad yana shiga gidansu Jalal koda yaushene tunda iyakacinsa, part din Jalal be fiye Shiga cikin gidanba se da dalili Dan haka Jawwad yanazuwa me gadi yake bude masa ya shiga Dan shima Dan gidane. Har yanzu Jalal be dawo ba Har had JAWWAD  ya juya ze tafi, seyaga kawai so yake yaga Jalal yaji inda ya tafi haka Jeje kuwa yakara ingiza Jalal ya dinga tuttulawa Jalal giya, se dayaga yayi mankas ba iya komai ya dauko shi yasahi a mota yadawo dasshi gida. Rungumo Jalal Jeje yayi ya shige dashi part dinsa saboda Sam Jalal baya hayyacinsa tangadi kawai yake Tunda Jawwad yaji karar motar Jalal yafito kofar part dinsa ya tsaya yana jiran Sa amma seyaga Jeje rungume da Jalal ko ba a gaya masa ba yasan Jalal a bige yake, Jawwad be kulasu ba, Hanya yabasu Jeje ya wuce da Jalal bedroom dinsa ya kwantar dashi, yazo fita Jawwad yasha gaban Jeje "Me kabashi?sannan daga ina kuke?" Yayiwa Jeje tambayar ransa a bace Jeje ya kalli JAWWAD a wulakance "Wane irin tambaya ne wannan? Kaima kasan me yasha giya CE meye kuma na tambayata ina mukaje ai kasan inda yake zuwa " kashedi nawa nayi maka game da Jalal, kai kake kara hure masa kunne meyasa kake bibiyarsa haka? Why? " "Bani yakamata in baka wannann amsan ba kajira lokaci" Daga haka jeje yasa kai yai ficewarsa Jawwad kuwa ransa a bace yashiga bedroom din, Jalal ya tarar yana ta bacci, hade da surutai cike da maye Girgiza kai kawai Jawwad yayi Allah ka shiryi bawanka Allah ka nunamin Jalal yazama mutumin Arziki. Washe gari da safe iyalan gidan sun hadu a palour suna karyawa, kowa ya maida kai yanacin abinci amma banda Jalila wadda taketa juya cokali tana cakalar abincin JAWWAD ne ya kalleta "Lafiya kuwa sisy ba kyacin abincin fa ko akwai damuwane?" Jawwad yafada cike da kulawa "Nima na lura da hakan bros tun jiya naga bata walwala" Nana ta fada tana kallon Jalila Maama kaam Dan kallonta yayi ta tabe baki ta cigaba da cin abincinta "Duk Ku tsaya Yar albarka gayamin meke faruwa ne"? Abba yafada cike da kula yana kallon Jalila Hawaye ne yazu bo mata Wanda bata San zasu zubo ba, " subhanallah Jalila meyafaru, me akayi miki" Suka shiga hero mata tambayoyi Jimin munafukar yarinya wayamata wani abu dazata kama yiwa mutane kuka kalli yadda duk suka bats attention lallai maganar Yaya mairo akwai kamshin gaskiya maama tayi zancen a zuciyarta Gaba daya attention dinsu ya dawo kanta suna mata tambayoyi "Abba ni Gida nake so in koma" Tafada a hankali "Wani abun mukayi mikine?" Nana tafada kaman zatayi kuka "Kunga Ku tsaya, Jalila anyimiki wani laifinne in wani abun mukayi miki kigaya mana" Jawwad yayi maganar yana kallon cikin idon Jalila Abba yayi gyaran murya yace "Yarinyar kirki meyasa kikeso kikoma Gida? ko mune ba kyasan zama damu" Girgiza kai tayi "a'a  Abba ni ba abinda kuka yimin kawai ina kewar ummi ne, sonake inkoma gurinta" Maama ji tayi kaman ta kwashe Jalila da mari saboda gulma Dan kawai tanaso takoma Gida shine zata yiwa mutane kuka salon ace wani Abu sukayi mata (Wato maama taji zigar yaya mairo) "To shikenan yarinyar kirki yaushe kikeso ki koma gidan? Tunda kin gaji da zama damu" "A'a Abba ba gajiya nai da zama daku ba, ba abinda kukayi min, Gobe nakeso in koma" Tafada tana sunkuyar da kai "To kibari ranar juma'a insha Allah se Jawwad ya maida ke gida hakan yayi miki?" Murmushi Jalila tayi tare da gyada kai "Shagwababbiya kawai shine seki mana kuka Dan kina kewar Ummi?" Jalal yafada cikin zolaya Maama dai batace uffan ba Haka dai suka kammala breakfast din Suna komawa daki Nana ta kalli Jalila "Jalila me mukayi miki zaki tafi kibarni , hutu fa be Kareba Naji dadin zuwanki meyasa zaki tafi ki barni"? "Haba Nanancy na nifa bukuyi min komai ba kawai inaso in komane" "To yaushe zaki kuma zuwa"? "Zan kuma zuwa Nana karki damu" "To shikenan zanyi missing dinki" Nana ko zan kuma zuwa gidanku se bayan dogon lokaci, idan nacigaba da rabar Ku kiyayyar da mahaifiyarku kemin zata fito fili Ga wannan azzalumin makocin naku abokin Jawwad Amma a zahiri se ta rungume Nana Karki damu Yar uwata I will miss you too Ran Alhamis da daddare Shirin komawa Gida sosai Jalila takeyi ta hada kayanta cif ji take kaman ba itaba zata koma Gida gurin umminta Nana ce  ta raka Jalila gidansu Jalal domin tai musu sallama, Ilham suka Tatar tana shirya abinci a palour Kaman kullum Ilham se hararan Jalila takeyi kuma har Jalila tai kwanciyar Asibiti bata taba cemata ya jiki ba "Gurin mummy mukazo ba gurin Jalal ba naga kina hararata" Jalila tafada  da sigar Neman magana "In ma gurin nasa kikazo biki isheshi kallo ba Dan ba macen dayake gani bayan Ilham" Ilham tai maganar cike da tsiwa dakuma gadara Aikuwa Jalila tafara dariya "Shi Jalal dinko, yanzu akansa kike wannan abun hh wani jan idonsa kaman ansa masa tear gas" Jalila tai maganar tana dariya Iya kuluwa Ilham ta kulu amma kafin tayi maganar Nana tace "Dan Allah kuyi hakuri wannan wasannaku karshensa fadane Ina mummy? gurinta mukazo" Haka Ilham ta kaisu part din daddy Dan mummyn tana can Itakuma tadawo palour Jalila tayi musu sallama  cewa gobe in Allah ya yadda zata tafi Daddy yace to ta gaida mamanta yayi mata addu'a kuma insha Allah zemata aike haka sukayi sallama da mummy ma Suna fitowa daga part din Daddy kaman kullum wata dramar ake JALAL da Ilham se masifa yake zazzaga mata kaman ze dake ta tana bashi hakuri kaman wani ubanta "Kina abu kaman wata dabba kinfiye naci wallahi inkina da zuciya karki kara zuwa inda nake kokice zaki dafa wani abu kibani, bana so ko ana dolene?"   Idon Ilham taf hawaye   "Dan Allah kayi hakuri Yaya bazan iya dena zuwa inda kake ba" Aikuwa dariya Jalila ta kwashe da ita "Tab laila majnun amma gaskiya iska tana wahalar dame kayan kara" Wannan wace irin mayyar yarinyace tantiriya me bakin naci Share please Nasan kunada Tarin  tambayoyi but keep following me amsoshin suna nan tafe cikin littafin ABDUL JALAL (2020) More comments more typing............... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  11 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Is a free book Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤ I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage              -my first Novel- Kafin su Ankara takuma yi musu wani shouting din "Ku tafi kubani guri" Sun² suka fice su ka bar gurin dakinta ta koma ta cigaba da sintiri to yanzu ya zatayi meye mafita washe gari takuma sawa aka nemo mata Abiola da yarabanci sukayi magana wannan karon (kunsan dai ni ba yarabanci nake ji ba Dan haka bansan me suka ce ba) Naga Abiola ya daga kai ya kalleta a razane "Ko bazakayi ba" ta tambayeshi "Zanyi yanda kikece" Ya fada Kansa a kasa "Mark u idan maganar nan ta fita wani yajita hukuncinka shine.. Tai taku biyu " life imprisoned!!! " Ya dago da sauri ya kalleta "Yes " tafada tana kallonsa "you can leave" Da la'asar har camp Abiola yaje ya lallabo Aliyu ya fito da shi kan cewar za suje yawon shakatawa ne, Wani hadadden lambu ya kai Aliyu, an kawata lambun da kayan itatuwa masu matukar kyau gurin yayiwa Aliyu kyau matuka, "Gaskiya gurin nan yayi kyau so cool" Aliyu yayi maganar yana murmushi tare da shafa Kansa "Dagaske gurin yayi maka kyau" Sukaji muryar mace a bayansu Abiola yasan muryar wace dan haka yakara nutsuwa tare da sunkuyar da kai Aliyu ne ya waigo yaga me maganar sanye take da riga da skirts na atamfa kanta ba Dan kwali matashiyar budurwace bazata fi shekara goma sha takwas ba ba dai fara ce ba amma tana da kyau black beauty ce Takuma maimaita abinda tace    "dagaske gurin nan yai maka kyau" Tafada tana murmushi, Wanda seda dimples dinta ya lotsa ta kara kyau Shima Aliyu murmushi yayi mata "Sosai makuwa gurin yayi matukar kyau kuma da kikazo seyakara haskawa kyansa ya kara fitowa" Murmushi ta kuma yi "That's good" Tafada tana kallonsa "Akwai gurare masu kyau a garin nan gurare masu saka nishadi, Wanda nasan babu su a garinku" Tafada tana Dan kashe masa Ido "Kinsan garin namune kika fadi haka" "No ba kayi kama da yan garin nan ba shiyasa nasan ba Dan garin nan bane kuma bana tunanin kanajin yarenmu" Shikam abiola gefe yakoma ya nutsu kaman bashiba "Hmm to garinmu yafi naku kyau" "Wane gari kenan?" Ta tambaya "Se dai ki canka" Ta Dan kalleshi "Kana kama da hausawa" "Yes ni bahaushene" Jikinta ne ya danyi sanyi ta dan tafi tunani "Akwai matsalane?" Girgiza kai tayi "A'a babu" "Bari in tafi kar mamana tai min fada na Dade" Ta juya tafara tafiya "To ai baki gayamin sunanki ba" "Marry" Tabashi amsa a takaice "Maryam, a nice name" "Ki ban lambarki mu dinga gaisawa mana kinga semuje ki nunamin inda yafi garinmu kyau" Murmushi tayi masa ta bashi lambarta sannan ta tafi "Abiola naga tunda yarinyar nan tazo kawani kame a gefe ko kasanta ne kokuma akwai matsalane baka gayamin ba?" MatsalaBabba ma kuwa Amma a fili se yace "A'a bawani matsala kawai dai na Baku gurine" Tun daga nan Aliyu ya jone da marry kullum cikin waya suke in tanaso ta ganshi se tace su hadu a lambu Yayi² ta nuna masa gidansu amma se tace in mamanta ta ganta da wani zatayi mata fada ne Sunyi matukar shakuwa soyayya suke sosai mussaman tayi masa girki sufita guraren bude ido Dukda kasan cewarta kirista bata shigar banza sedai yawo ba dan kwali shima Aliyu ya hanata In lokacin salla yayi zata jirashi yayi salla koma ta tuna masa, suka shaku matuka amma besan wacece ita ba,  tanayin abubuwan dasu kan bashi mamaki, indai zasu hadu ko Suyi waya setayi masa sallama, gashi lokaci zuwa lokaci yakan ji tace masha Allah, subhanallah da maka mantansu Se yayi zaton kawai saboda yana yawan fada ne itama takeyi A kwana a tashi gidansu marry aka fuskanci sauyi a tare da ita sakamakon yawan fita datakeyi, Kuma fitar ma ita kadai dan haka aka tsaurara mata tsaro ta shiga damuwa sosai rashin ganin Aliyu da batayi sedai suyi waya abun ya dameta matuka, Aliyu yace tabarshi yazo shi Inda take amma tace masa baze yiwu ba, Wasa² suka shiga matukar damuwa saboda rashin ganin juna Abiola yake gayawa abinda yake faruwa Abiola ya tausayawa Aliyu ganin yadda marry ta jashi fage me matukar wahala dakuma hatsari (Wato soyayya) Gakuma banbancin addini da kabila ga kuma uwa uba dokar masarautarsu Aliyu yasaka ranar zuwa kano domin yaga gida don kusan watansa hudu a kogi state haduwarsa da marry ne ya mantar dashi kewar Gida datake damunsa da farko,      Wata rana Suna waya da daddare shida marry yake gayamata yanaso yaje kano domin ganin Gida Kuka sosai ta kama yi masa ya shiga damuwa "Haba maryam ya haka zaki tayarmin da hankali kin hanani zuwa inda kike kinki bari mu hadu,    bakisan yadda nakeji ba ne naga kaman baki damu ba ko baki yadda dani bane bansani ba" "Noo bahaka bane nima ina cikin damuwa an samun tsaro sosai, am sorry Aliyu akwai abunda na boye maka amma inaso mu hadu kafin ka tafi" "A ina zamu hadu ?" Yai mata tambayar cike zakuwa "Inda muka saba haduwa a garden" "To shikenan kaman karfe Nawa?" "Da yamma by God will" "Allah ya kaimu da rai da lafiya" "I love u Aliyu" "Love u more my dear" "Kamin wani Alkawari" "Wane Alkawari ?" "Will u marry me?" "I will me sunan mum insha Allah in dai family dinku zasu yarda dani su bani auren ki, bantaba soyayya ba se akanki, akanki nafara kuma daga kanki nagama insha Allah" Ajiyar zuciya tayi "Aliyu ka kwanta karka makara sallar Asuba kaimin addu a lamuran suzo da sauki" "Kullum inayimana kiyi bacci me dadi zanzo a mafarkinki muje yawo" Dariya sukayi suka kashe wayar Kaman yadda tayi masa Alkawari haka tayi kokari seda ta fito daga Gida bawanda yasani Inda suka saba haduwa yauma anan suka hadu Se dai sabanin sauran kwanaki dasuka saba haduwa yau fuskarta dauke take damuwa Kusa dashi ta zauna shiru ya Dan ratsa Sannan ya kalleta "Baki da lafiyane?" Ta girgiza masa kai   "Ya akai kikayi wannan ramar haka meyake damunki, tell me, meyake faruwa" Idonta taf hawaye ta kalleshi "In ka tafi yaushe zaka dawo?" "Bazan Dade ba insha Allah" "Dagaske kake zaka aureni?"   "Am serious ina sonki son da bantaba zaton zanyiwa wani makamancinsa ba bayan Dan uwana I love u with all my heart" "Aliyu ina sonka Dan Allah in kagama service ka tafi dani garinku ka aureni musulunta zanyi" Mamakine yacika Aliyu ba maganar da tayine ya bashi mamaki ba illa magana da tayi da harshen Hausa Wanda be taba zaton ko zo tasani da hausaba " Noor (sunan da yake kiranta dashi kenan) Dama kin iya Hausa?" "Na iya Hausa" Tabashi amsa "How comes ban taba ji kinyiba" Wata nannauyar ajiya zuciya ta sauke "Mamana kiristace babana kuma musulmi ne kuma ba haushe ne family din babana dukansu musulmai ne kuma musulmi suke aure Baba nane kadai ya auri kirista wadda ta kasance ya mace tilo a masarautarmu yan uwanta duk mazane dan haka ake matukar sonta a cikin masarautar da ta ISA aure ta dage akan wannan musulmi take so akayi² ta hakura taki Dan haka aka kyaleta ta aureshi   Tunda ta aureshi ya tafi da ita take samun cusgunawa daga dangin mahaifina suka takura mata da kyama da tsangwama a daddafe ta haifeni ta yayeni babanta yece sedai ta dawo Gida a hakura da auren ba za adinga wulakanta masa ya ba a matsayinsa na sarki me fada a aji amma ace ana wulakanta yarsa a gidan aure Dangin mahaifina suka kwaceni shekarata takwas a hannunsu babana ya rasu a gurin kakata na zauna ita ke koyamin karatun addini shekarata takwas amma na haddace izu ashirin na Qur'ani Da  mamana taji rasuwar mahaifina ta daga hankalinta akan se an batani , An kai ruwa rana seda kakana ya hada da karfin mulkinsa sannan aka karbeni daga dangin mahaifina A gurin kakannina ni musulma ce na iya abubuwa dayawa kuma na tashi da Hausa a bakina dana dawo nan mamana ta maidani addinin ta sannan tayi Alkawari bazata bari inyi gangancin datayi ba, family dinmu ba a auren Wanda ba yarenmu ba ko kuma ba addinin mu ba  tun daga kan mamana akasaka wannan dokar" Tana kaiwa nan ta sauke ajiyar zuciya   "Meyasa tun farko kika boyemin hakan, why"? Idonta taf da hawaye ta kalleshi " please Aliyu don't leave me tun randa kukazo da abiola na ganka naji ina sonka kate makamin Aliyu, in kai haka zaka ceceni daga halaka danakee ciki zan samu damar komawa addnina na musulinci" "Lallai abiola munafiki ne shine ya kyaleni nake ta fama ko Ashe yasan komai" "Ni nahana shi yagaya maka Dan Allah Aliyu kar kaarabu dani kayi Alkawari zaka aureni"   Kuka take sosai "Is OK ai bance miki nafasa ba Dan haka kiyi shiru zansan yadda za ayi zanzo innemi aurenki a gidanku" Zaro ido tayi tace baze yiwu ba ita dai kawai ya tafi da ita basu saniba     "Idan nayi haka banyiwa iyayenki adalci ba kibari inje kano in dawo zamuyi abinda yakamata" Haka sukayi sallama kaman bazasu rabu ba    Aliyu ya dawo kano cike da tunanin noor (marry) sunyi farinciki da ganinsa, dayake da weekends ya dawo yaita zuba ido yaga Jawwad amma be Ganshi ba   "Wai INA Dana ne" ya tambayi Usman "Hmm wallahi wani yaro ya hadu dashi a kusa da makarantarsu, sun likewa juna yaita kuka se an kaishi gurin yaron, shima yaron in aka tashi daga tasu makarantar seyabiyo shi gida direbansa da malaman makarantarsu suyita nemanshi se mun maida shi makarantarsu yayita kuka, To shine babansa yace Dan Allah da weekends  akai Jawwad kokuma shi akawo shi akawo shi nan" "wannan wane irin shirmen banza ne kawai Ku dauki da Ku kaiwa mutanen da Baku Sani ba to ni ban yaddaba, akan me kawai ni gayamin inane inje in dakko shi" "Sannu sarkin azarbabi kai ko kara babu, gidan mutanen kirki ne har nan mahaifin yaron yazo ya roki alfarma yanzu yasakasu a islamiyya daya" Inna mairo ce take wannan jawabin "Au saboda wulakanci had da canza masa makaranta haka akeyi kaikuma kana zaune"   Seda aka gaya masa gidansu yaron yana gadon kaya Yakama hanya ya tafi dakko JAWWAD, yana zuwa ya tarar an shiryasu me gidan ze fita da su Jawwad da wani yaro da befi sa'an jawwad ba   Da gudu Jawwad ya tafi ya rungume Aliyu ganin haka yasa shima Yaron ya tafi ya rungume Aliyu, ya rungume su gaba daya Suka gaisa da mutumin Aliyu Yace masa "Dana Nazo dauka" "Wanne kenan?" Mutumin ya tambayeshi   "Jawwad mana" "To ai har gida na tura aka dakko shi da izinin mahaifinsa" "To ai nine babansa tafiya nayi ne kuma na dawo abani Dana ban yadda ya dinga zuwa wani guri yana zama ba" Yayi maganar yana janyo hannun Jawwad aikuwa Jalal ya fashe da kuka ya bisu yana "daddy kace ya dawo min da shi" Aliyu ba yadda beyi ba adena kai Jawwad gidansu jalal amma abu yaki, Inma ba akai Jawwad ba za akawo JALAL sekace tagwaye A yan kwanakin da Aliyu yayi a kano Dan uwansa ya fuskanci akwai abunda yake damunsa saboda Sam baya walwala sosai  Usman ne yaje ya sameshi adaki yana waya da marry ya jirashi ya gama sannan ya mai tambayar "Dan uwana me yake damunka ne naga Sam Baka da walwala ko akwai wata damuwa ne"? " akwai kam yayana" "Me yafaru?" Usman ya fada yana kallonsa Be boye masa komai ba ya gaya masa halin dayake ciki Jinjina kai yayi "Gaskiya Dan uwa ka debo da zafi shawarar da zan Baka ka hakura bana tunanin abin nan ze yiwu kasamu wata anaan ka aura" " a lokacin da ka dakko naka Auren waya hanaka, kamin addu a kawai bana son wanna shawarar taka , tashi kabani guri'" Aliyu ya fada yana nuna masa hanyar fita Satinsa daya a kano ya koma kogi state an kai ruwa rana sosai a gidansu marry da aka gano tana soyayya da musulmi kuma bahaushe Kwanci tashi Aliyu ya kammala service dinsa Dayazo da maganar auren marry Gida malam yace be yadda ba, ga yayan musulmi nan a garin nan dan haka ya hakura da maganar yarinyar nan. Marry kuwa taita rashin lafiya saboda Aliyu ya tafi ga kuma anki yadda da ya aureta, mamanta ta dena kulata sarki yayi fushi da ita duk da soyayar da yake mata, ita kuma ta kafe tace ita se Aliyu   Shima nan haka Aliyu yake ta fama da malam amma yaki yadda, inna mairo CE kawai ta goyi bayansa amma malam ya kafe yace be yadda ba sedai ya auri musulma Da wannan rikicin seda aka shafe shekara biyu ana fafa tawa da wannan rikicin Marry taje ta samu maman ta tace itafa gaskiya zata tafi kano gurin Aliyu shi takeso bazata iya zama a garin nan ba A gigice Maman ta taje tasamu sarki ta gaya masa, juyin duniya marry ta kafe tace itafa gaskiya tunda bazasu yadda ba tafiya zatayi, Dan haka sarki yace to ya sallameta basu ba ita har abada karta kara dawowa, marry tace ta yadda, Tana kuka mamanta na kuka haka ta hada kayanta ta nufo kano......... Bayan la'asar marry ta sauka a kano layin Aliyu ta shiga kira bugu biyu ya dauka "Aliyu kana ina ne?" ta tambayeshi "Ina gida" Yabata amsa "Kazo ka tafi dani Dan Allah" "Ahh wai kina ina ne?" "Aliyu kazo ka daukeni ina kano fa yanzu na karaso" Zaro ido yayi "Are u serious?" "Dagaske nake" A kidime ya tashi ze fita sukayi karo da Usman "Dan uwa ina zaka, naganka a kidime haka"   "Dan uwa marry ce ta biyoni kano" "What are u serious" " yanzu mukayi waya da ita ta fadamin" "Muje tare" Usman ya fada yana Jan hannunsa suka fice Kaman yadda ta fadamasa a tasha sukaje suka sameta rungume da akwatinta Haka suka Dakkota suka taho gida Suna zuwa Zainab ta karewa marry kallo "Wannan fa daga ina"? Tafada a yatsine saboda ta ganta tare da Usman ga kuma uban akwati " bakuwace" Shine kawai abinda Usman yace mata suka wuce bangaren inna mairo Lokacin ana ta kiraye² sallar magariba dan haka suka kaita dakin inna mairo suka tafi masallaci Bayan inna ta idar da salla ne tare da lazimi Ta kalli marry tace mata "Sannu da zuwa"   "Yawwa mama ina wuni" Tafada da hausa amma a hausan tata zaka fuskanci ba cikkakiyar ba haushiya ce ba "Lafiya kalau, amma banganeki ba " Dan sunkuyar da kai tayi "Tare muke da Aliyu" Nan inna mairo ta gane wace ce Tabata Abinci da ruwa tabata guri ta huta Se bayan sallar isha'i sannan su Aliyu suka dawo gidan a dakin inna mairo suka hadu suna jiran zuwan malam Imam suji me ze yanke, Zainab se sintiri take so take taji wace wannan bakuwar dasuka zo da Usman da Aliyu harda su trolley ita dai bata san taba Akajima se ga malam imam ya dawo yazo ya samesu a zaune jungun² a dakin inna mairo "Ya akayine na ganku a zaune kunyi shiru, bakuwa mukayine" Inna mairo ce ta shiga korawa mamalam imam bayani Ransa ne yayi matukar baci da jin inda jawabin NATA ya dosa, ya tashi ya bar gidan gaba daya Seda yayi kwana biyu baya shiga harkarsu Zainab kam ta uzzurawa Usman setaji wace ce yarinyar nan amma yaki gaya mata A kwana na uku Aliyu ne yasamu malam a tsakar gida yaje gabansa ya durkusa "Baba na dama akwai lokacin da zezo kayi fushi dani haka kadena kulani Aliyun ka nefa dan autanka Kasan bantaba dakko maka magana ba meyasa bazaka yadda da niba" "Ya raina baze baci ba, seda na jamaka kunne akan yarinyar nan, amma saboda baka jin maganata kaje ka ja jubota ka kawomin ita gida haba Aliyu yaushe kafara dena jin maganata"?    Marry tanajin abinda ya faru a hankali ta tako ta karaso gaban malam imam ta zube "Baba ba laifin Aliyu bane ni na kawo kaina dan girman Allah karka koreni, kafison in koma inda na baro kan addinina na baya? Baba kaifa malamine kuma ubane dan Allah baba musulunta zanyi, ka auramin Aliyu idan na bar nan bazan koma gida ba wani gurin zanyi in ka koreni bansan inda zani ba," Duk wannan maganar da take cikin kuka takeyi Aliyu ma gaban malam ya durkusa ya rike hannunsa "dan Allah baba na ka amsa mana ka yadda in auri maryam dan Allah baba inba ita na aura ba wallahi bazan iya auren wata mace ba" Usman ma gaban malam yaje " baban mu tun tasowarmu kake sonmu kake kula damu, kake son abinda mukeso, baba ka amince da bukatar dan uwana, Baba ka girmama son da maryam da Dan uwana kema junansu Wanda yasa ta baro daular da take ciki ta taho gurin mu, inka yadda da auren nan kaman kayi jihadi ne" Inna mairo ma cewa take "Malam a duba lamarin nan d'a na kowa ne mukanmu misaline munzo garin nan. Bamu da kowa" Ajiyar zuciya yayi ya nisa sannan yace........ Share please More comments more typing................. Mss~dyjeer naga rago godiya nake😂 Anty Jamila a soye tabani ta hutaddani suya Afshan Rahmatoulaye Salma Afshan Fatima zahrahs (tsofaffi) And the remaining members Ina alfahari daku ❤❤❤❤❤ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  10 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Is a free book Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤ I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage Haka suka cigaba da tafiya sunayi suna hira jefi² har suka shiga garin Kaduna Karfe 4 dai² suka iso kofar gidan su Jalila, suna parking Jalila ta fito bata tsaya bi takan JAWWAD ba balle trolley dinta, ta sakko ta ruga da gudu cikin Gida, Ummi tana tsakar gida ta idar da salla Jalila ta shigo da gudu ta fada jikinta tana murna "I really miss you ummina" "To karyani ki huta sarkin fitina ga yanda kika shigo da gudu kaman an koroki," "Bikiyi missing dina ba ko ni duk na damu saboda rashinki a kusa dani amma daga zuwana kin faramin fada" Ana haka  JAWWAD ya shigo da trolley din Jalila, "Au shi kikabari da dakon kayannaki? Kekam se a hankali" Ummi tafada tana ture Jalila daga Jikinta "Ba komai Ummi naga ta kagu ta ganki ne yasa ta manta da trolley" Yafada yana murmushi Murmushi Ummi tayi Har kasa ya tsuguna ya gaida Ummi ya zauna Ta amsa fuskata cike da fara'a haka ya zauna sukayi ta hira da ummi, Ummi tana kaunar Jalal kodan yadda yake son diyarta dakuma yadda mahaifinsa yake tsaye akan lamuransu ita da yarta Bayan haka kuma JAWWAD yarone me matukar biyayya da hakuri Sallar la'asar yayi, be wani dade ba yace tafiya zeyi, "Jawwad tun yanzu" "Ummi bana son tafiyar dare ne" "Hakane kam bata da dadi" To Dan jirani ina zuwa daki ta shiga ta dakko wani turare me kyau tabawa JAWWAD yayi godiya sosai Yayiwa Jalila alama da ido ta tashi tarakoshi waje "Sisyna zanyi missing dinki zuwan nan naki yayi min dadi gashi kin dawo kin barmu" "Allah sarki yayana nima banji dadin rabuwa daku ba " "Sisyna kiyi karatu kinji nasan ke mutuniyar kirki ce, banda kula kawayen dabasu zuwa makaranta Banda tsokana da shagwaba" Ya karasa maganar da sigar tsokana "Insha Allah yayana" "Good very good sister, insha Allah very soon zan dawo mukoma" Dan turo baki tayi batace komai ba Mortar ya bude ya dakko wani jaka yabawa Jalila "Thank u very much my brother" "Shhhhh don't mentioned dear" "Wish u safe trip brother thank u very much ka gaida min da Nana ta" "Zan gayamata and karki manta dayiwa yayanki addu a" "Addu a mekakeso in maka"? "No bani ba Jalila yayanki Jalal" "Yaya kaikam narasa wanan kaunar da kakewa Jalal" "Hmm sisy na kenan zakiji komai insha Allah in kinkuma zuwa kano zakiji dalili" Yabude mota ya shige yatada mota yana daga mata hannu Seda ya bace ma ganin Jalila sannan ta koma cikin Gida "Ummina gayamin me yafaru bayan tafiyata ?" "Ke dai bari Babyna gidan ba dadi daba kya nan, kawayenki na islamiyya se sintiri suke min, nayi missing dinki sosai daughter na" Ummi tafada tana shafo fuskan Jalila Jalila ta riko hannun ummi "Allah sarki ummina haka kike sona dama?" "Hmm Jalilana a duniyar nan a yanzu wanake dashi bayan ke kin ko son soyayyar dake tsakani da da uwa, da baki tambayi haka nakesonki ba" To amma ya akai tsakanin Jalal da mummyn Sa basa jituwa shi bayajin wannan soyayyar ta mahaifiyarsa a ransa, Jalila tai maganar a zuciyarta Da daddare bayan Ummi da Jalila sunci Abinci Ta je ta dakko trolley din ta, ta dakko  kyautukan da ta zo dasu ta nunawa Ummi sannan ta dakko Wanda ,Jawwad yabata Katuwar teddy ne Ja da kuma manyan kwalin chocolate kusan guda biyar "Allah sarki yayana Allah ya karemin Yaya Jawwad har yanzu be manta abinda nake so ba " Ummi kallonta ta tayi tai murmushi "Hmm Jalila kenan, Jawwad ya biyewa shirmenki hada siyamiki teddy da girmanki" "To ni ummi har wani girma nayi Yawwa Ummina tambayarki zanyi" "Allah yasa nasani" " Naga nabaki abunda akabani a gidansu Jalal baki tambayeni waye Jalal ba ko kinsanshi ne?" "Eh nasan yaron koba makotan su Jawwad ba"? " Ummi shine, amma kinsan yazama dan shaye² bashi da tarbiyya Sam bakiga yadda yakewa mamansa ba ya akayi kika sanshi?" "Allah sarki Jalal da ba haka yake ba daga baya yazama haka abokin Jawwad ne tun suna yara kanana Daga baya yakoma haka saboda wani abokinsa ko wayake oho? Amma naji ance hada laifin mahaifiyarsa amma bansan ya akayi ba nikam" "To Ummi ya akayi mahaifiyarsa tabari yazama haka" "Ke rabu dani nima ban saniba sarkin tambaya meyasa baki tambayesu a can ba ni rabu dani bacci nakeji" "To shikenan Ummi " Har sun kwanta bayan wasu mintuna da kwanciyarsu, Jalila ta nisa "Ummina" "Na'am Jalilana" "Yaushe zaki kaini garinku inga yan uwanki?" "Jalila meyasa kikayi min wannan maganar,  so kike ki hanani bacci ko rigimar zakimin daga dawowarki ko baby, bana so yi baccin ki kawai nasan kingaji" "Ummi bazan iya bacci ba sekin Sa ranar dazaki kaini garinku ni wallahi ko wasu irine ina so inje in gansu Dan Allah Ummi koba Sa sanmu ni inasonsu a haka Ummi kitemaka" Jilila ta karashe magNar tare da rike hannun Ummi tana hawaye" Fizge hannunta Ummi tayi "Nemi gurin kwanciya kafin in wanka miki mari" Ummi ta daka mata tsawa haka Jalila ta kwanta ta juya wa Ummi baya tana kuka Har cikin zuciyarta Ummi takejin kukan Jalila tareda tausayinta. Tayi rigingine tana tuna abubuwa da dama dasuka shude ********* Aliyu Imam Habib shine cikakken sunan mahaifin Jalila su biyune kawai a gurin iyayensu shida  yayansa Usman Imam Habib (babansu Jawwad) Mahaifansu sun haifi yara dayawa sun rasu su biyune suka rage asalin iyayensu Fulanin Adamawa ne ne akayi wata rigima yan fashi suka je rigar fulanin  aka karkashe wasu, yawan hare² da ake kaiwa fulanin ya tilasta wasu suka watsu a Sassan Nigeria an kashe musu yan uwa da dama malam imam da shi da me dakinsa mairo sukayo hijira zuwa kano.   an kashe musu yan uwa dayawa, wasu daga cikin yan uwan Nasu kuma basu San inda suke ba abinda suka tsira dashi bashi da wani yawa, duk da kasan cewar su masu arziki a rugarsu amma haka suka siyar da abinda ya rage musu suka taho kano (ta dabo jalla babbar Hausa kodame kazo an fika) Zuwansu kano a lokacin duniya tana kwance , a lokacin in akayi baki masarautar kano zamanin sarki Ado bayero ke bawa baki masauki Dan haka masarautar kano su sukabawa su malam imam masauki, inda akabasu katon Gida a unguwar mandawari Gidansa ya kasance kusa da gidan wani alaramma malam shehu, malam shehu yanada Tarin almajirai dan haka zuwan malam imam kano basu San kowa ba wannan makocinasu shiya zama kamar Dan uwansu Shi ya kai Imam kasuwa ya hadashi da wani almajiransa ya koya masa san'ar takalma a kofar wambai Sannan in ya dawo sukan zauna da malam shehu ya koyamasa karatun addini Imam yasamu Ilimi me tarin yawa a gurin malam shehu wanda ya kaishi ga zama mahadddacin qurani, sannan yana samun alheri a kasuwancinsa yA tsaya akan gaskiyarsa dai² gwargwado, yana samun rufin asiri a sana'arsa     Haka bangaren matan malam uwar gidansa ta dauki mairo kaman Yar data Haifa yayinda amaryarsa takasance masifaffiya Dan bata shiga shirgin mairo tunda taga uwargidamta ta dauketa kaman ya, uwargidan malam shehu ta iya saka Dan haka ta dinga koyamata sakar kayan sanyi A zamansu a kano  mairo ta haifi yaronta na farko ya rasu a ranar da ta haifeshi yarasu bayan wani Dan lokaci ta Haifi na biyu Suka masa sunan Usman wato sunan malam shehu, yatashi da ilimin addini da soyayyar iyayensa gashi malam shehu ya daukeshi kaman jikansa yana matukar kaunarsa da ya isa sakawa a makaranta akakai usman makarantar boko Seda mairo ta kuma haifan yara biyu suna mutuwa sannan ta haifi Yaronta namiji akasamasa Aliyu Addu'a Imam yayi tayi Allah ya bar masa Aliyu Usman ya samu Dan uwa, Usman ya tashi da matukar kaunar Dan uwansa kullum yana tare dashi har Goya masa shi mairo takeyi, Ba 'a Dade ba Ta kuma haifar mace itama ta rasu daga nan bata sake haihuwa ba, Haka suka rungumi yaransu suna kula dasu malam imam be sakasu a harkar kasuwanci ba se dai ya tsaya musu akan Neman Ilimin su, na islama Dana zamani, A kwana a tashi malam shehu Allah yayi masa rasuwa, sun shiga matukar damuwa da tashin hankali haka akayi zaman makoki kowa ya watse. Rayuwa tacigaba a haka malam imam be taba tunanin sunemi wani daga danginsu ba, yana ta kula da yaransa , yakuma siyan gidajen kusa dasu ya hade a cikin gidansu. Usaman da Aliyu suka girma da matukar kaunar junansu, gasu masu matukar biyayya duk da kasancewar su maza amma daga kan shara gyaran gado wanke² bawanda basu iyabaan Usman yafi Aliyu hakuri, shi     Aliyu akwai kafiya da taurin kai sannan yana da zafi, halin babansu ya dakko, gashi shine karami amma in ya dau zafi sedai Usman ya kyaleshi amma duk da wannan halin nasa kaf kayan gidan nan shi yake wankewa ya goge sannan yana matukar son yayannasa amma wataran in kaga yasa Usman a gaba yana masa fada seka dauka shine babba (Ashe JALILA ba a banza ta dakko ba) shidai malam imam kullum zancensa be wuce " Ku rike junanku Ku rike zumunci, kunga bayan imu IMU bamu da wasu dangi duk sun watse wasu sun mutu Ku rike junanku Ku nemi ilimi ko bayan ba raina karku yada zumunci" Kwanci tashi asarar rai Usman yagama makarantar secondary ya shiga Jami'a yake karantar engineering, Bayan ya kammalla jami'a ne aiki be samuba ya dawo Gida ya zauna yake dan bin babansa kasuwa, ana haka ya hadu da wata yarinya Zainab da farko dai suna mutuncine kawai kafin daga baya abin yakoma soyayya, Lokacin daa malam Imam yasamu labarin Usman yana zuwa tadi gurin yarinyar ya kirashi yayi masa nasiha yace tun wuri in yasan ba aurenta zeyi ba ya dena zuwa gurinta Shidama Aliyu be tsaya iya karatu ba yana taba kasuwanci In yafita abinda yasamo se yabawa Dan uwansa yace yafara Tara kayan aure tunda ya fuskanci yana matukar son zainab, Duk randa Aliyu beje makaranta ba haka zewuni Neman kudi ba abunda zeci a ciki haka ze dauka ya bashi,    Sannan dayake  mutane dayawa sun San Aliyu saboda yana da baki ba kaman Usman ba salihi ne kaman mairo, Aliyu ya dinga shiga yana fita domin yaga danuwansa yasamu aiki amma abu yafaskara kai kace shine yake nemawa kansa aikin   Shekarar da Aliyu yasamu admission, babansu ya dauki kudin Registration ya bashi amma daya tashi se ya hada kudin da Wanda ya dinga Tarawa ya tafi yaje kasuwa Yakama shago aka zuba takalma ya dankawa Dan uwansa yace gashi nan ya dinga juyawa yasamu yayi aure Dafarko Usman kin amincewa yayi seda yaga Aliyu yadena kulashi, yadena cin abinci tare dashi yayi fushi sosai sannan ya yadda ya karba Malam imam yace aikuwa badi se dai kanemi naka kudin kashiga makaranta, we da Aliyu yabata shekara biyu be fara makaranta ba saboda yaga kasuwancin da ya kafawa yayansa ya bunkasa Duk wannan abun baya hana in Usman yayi masa laifi ya zauna ya kare masa masifa, amma beta ba yimasa gori ba.   Shekara ta zagayo Aliyu sannan ya Shiga Jami'a Usman ya cigaba da kula da shago yasamu Sana'a yafara core ransa saga batun samun aiki Ahaka har Allah yasa Usman ya auri Zainab aka ware masa bangarensa a cikin gidan yasata a ciki, tana zaune da mairo lafiya saboda ita Sam bata da hayaniya Dan haka Zainab bama Shiga harkarta take ba balle kyautatawa ko akasin haka ya Shiga tsakaninsu. Allah ya Albarkaci kasuwancin usman, aciki ya dinga tallafawa karatun Aliyu dakuma iyayensu da girma ya cinmmusu,    A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, matar Usman ta haihu ta haifi da namiji, aka sakamasa sunan Aliyu suke cemasa Jawwad, Zainab taji haushi ga mahaifinta memakon ayi mata kara a saka sunanshi se a wani saka sunan Aliyu Aliyu yayi murna da haihuwar JAWWAD dakuma karar da dan uwansa yayi masa kullum yana tare da Jawwad, yaronma yana matukar kaunar Aliyu Jawwad, soyayyar da Aliyu yakema Usman Yakoma kan Jawwad, Jawwad yana da shekaru biyar cif, Aka tura Aliyu bautar kasa kwara state yaji babu dadi sakamakon rabuwar dazeyi da gida gakuma dansa JAWWAD dayake matukar kauna Haka Aliyu yayi shirin tafiya yayi sallama da mutan gida iyayensa sun masa nasiha sosai akan ya kula da Kansa da addininsa, Usman beji dadi ba ya Shiga damuwa sosai, saboda shi lokacin da yayi NASA bautar kasar a kano yayi beyi nisa da Gida ba. Haka Aliyu ya shirya ya tafi kwara, wani babban kamfani aka turashi kamfanin yakasance mallakin masarautar garin Wanda ya kasance na construction ne na gine² dakuma tituna Aliyu yaga mutane daban² wanda suke da banbancin addini da al'adu da zaman takewa na rayuwa Aliyu ya hadu da wani bayerabe a kamfanin me suna Abiola Wanda ya kasance kuma hadimi ne a cikin masarautar garin dukda banbancin addininsu amma tasu tazo daya shiyake zagawa da shi gurare a cikin garin In Baku manta ba kusan halin Aliyu da shige² Dan haka yace yana so abiyola ya Shiga dashi gidan sarautar yaga  yanda take, haka akayi ya dauke shi ya Shiga da shi cikin masarautar ya dinga nuna masa abubuwa, haka ya dinga kallonsu wasu iri saboda yanayin saraautarsu  yayi daban da masarautar kano Wasu abubuwan sun kayatar dashi wasu kuma sun bashi haushi haka abiola ya dinga bashi labarin masarautar da abubuwan data kunsa  ciki kuwa hada labarin shalelen masarautar wadda akan a batamata rai gara abatawa sarkin saboda tsananin kaunar da sarkin yake mata Sarki yana matukar kaunar yarinya nan, shikam Aliyu duk surutun nan da abiola yake besan me yake cewa ba saboda ya shagala da kallon abubuwan kayatarwa da suke a masarautar, Wani part suka karaso kai bakace a Nigeria ne ba ya hadu karshen haduwa an kawata shi da abubuwan zamani da kawatuwa "Nan kuma inane?" "Ai nan shine bangaren yarinyar danake gaya maka jikar sarki ce, bangaren shalelen gidan ne" "Ehenn mushiga inga mene a ciki mana" Zaro ido abiola yayi "sokake in kwana a kurkuku baza ja min wahala ba iyakacin mu nan" "To meye a ciki gani fa kawai zanyi" "Dan Allah kabari ka zo mutafi kaga akwai masu tsaronta Dan haka kazo mu tafi" Da kyar abiola ya shawo kan Aliyu ya yadda suka tafi. Abiola ne durkushe a gabanta, ta hakimce tana cin kayan marmari Tayiwa hadimanta umarnin sutafi subata guri Sannan ta mike zaune sosai "Abiola" Takira sunan shi Ya Dan kalleta ya maida kansa kasa "Waye wannan Wanda kuka shigo da shi dazu?" Gabansa ne yayi mummunar faduwa ya tsorata, nan da nan gumi ya rufe shi ya kama in'ina "Abiola bafa abu me wahala na tambayeka ba kawai na tambayeka waye shine Ina kallonku dazu ta saman bene kuna jayayya waye shi? Daga ina yake? Mekuma ya zo yi nan"? Da kyar abiola ya hadiye wani yawu ya daidaita nutsuwarsa Ya dan suka da Kansa yace " your royal Highness Dan bautar kasane an turoshi kamfani domin yayi aiki sunanshi Aliyu daga kano state yazo nan" A kidime ta kalleshi kana nufin musulmine "Eh bahaushe ne kuma musulmi" Gigicewa ta danyi tare da bashi umarnin ya tafi seta nemeshi Nan ta Shiga sintiri a gurin Da karfi tai shouting "Impossible!!!!!!" Wanda ya janyo hankalin masu yi mata hidima ,kafin su an kara........ Wata sabuwa Share please More comments more typing............... Love u all Abdul jalal novel fans 🌹🌹🌹 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  12 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Is a free book Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤ I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage     Takabbalallahu minna wa minkum eid el Mubarak alaina wa alaikum Allah ya karbi ibadunmu yasamu a Wanda yYafewa a wannan kwanaki goma na dhul hajj          -my first Novel- Numfasawa yayi ganin yadda yaran gaba daya suke durkushe a gabansa ga maryam da take ta kuka Ko ba komai Aliyu yaron kirki ne tun tasowarsa ba taba dakko masa magana ba dukda fadansa da shige shigensa baya dakko magana Kuma ya duba misalin da inna mairo tai masa Suma yadda sukazo basu San kowa ba malam shehu ya daukesu kaman yayansa Dan haka ya numfasa "To shikenan na amince Allah ya tabbatar mana da Alkhairi yayi muku albarka gaba daya" Marry ta dago da sauri "Baba dagaske ka yadda in auri Aliyu" Ya gyada mata kai Da gudu marry ta tafi gurin Inna mairo ta rungume ta "Mama bani da bakin godiya mama kiyimin godiaya gurin baba, kun gama min komai a rayuwa da kuka karbeni nagode sosai. " ba komai maryam nima nayi diya dama bani da ya mace" Inna mairo tayi maganar tana sharewa marry hawaye Aliyu da Dan uwansa haka suka dinga yiwa mahaifinsu godiya tare da adduo'i Usman yaji dadin yadda baba ya amince ko ba komai shima Dan uwansa ya samu farin ciki Bayan malam imam ya koma daki ya kira Aliyu yayi masa nasiha  ya ja kunnensa game da rike amana da yi masa gargadin zama jakada nagari na addinin musulinci da kuma kabilar hausawa    Haka marry ta karbi musulinci  ta koma maryam Amma aliyu yake kiranta da noorat saboda sunan mahaifiyarsa ne Abubuwa sunzo mata da sauki saboda tasan addinnin musulinci se Dan abinda ba a rasa ba. Itakuwa Maman Jawwad tunda taga abunda yafaru gashi kuma mutanen gidan sun karbi maryam.ta fara jin haushi, yadda inna mairo take kula da maryam kamar yarta amma ita dasukayi kusan shekara shida da ita bata wani shiga sabgarta, Dan haka ta shiga yayatawa a anguwa kanin mijinta Aliyu ze auri kirista dukda tasan ta musulinta, hakanan se yan unguwa su shigo dan aga matar da Aliyu ze aura. Duk surutun da ake a gari Aliyu da yan gidansu suka toshe kunnensu, dama ba a tunkarar Aliyu da maganar Dan ansan masifaffe ne Sedai ayiwa Usman ko magulmata in sun shigo suyiwa inna mairo Aka ware musu bangarensu a cikin gidan, dukda kasancewar maryam kabila kuma wadda tayi girma a gidan sarauta amma tana da matukar biyayya da girmama manya ba ruwanta da hayaniya, mamansu Aliyu ana kiranta inna mairo amma ita se dai tace mata mama Malam ya tsaida ranar daurin auren maryam da Aliyu sati biyu Usman shi ya hadawa Aliyu lefen da aka bawa maryam itakuma tace ai tana da kayan sawa Inna mairo tace mata wannan itace Al'adarmu ana hadawa mace kayan lafe abata A lokaci kankani mutan gidan nan suka saki jiki da maryam ta shiga ransu saboda tsabar nutsuwa da biyayya gashi kullum tana tare da Jawwad yaron yana sonta wataran hada JALAL in an kawo shi, amma banda Zainab wadda ba ruwanta da ita yan gidansu Zainab musamman sukazo don ganin maryam suka dinga Yar mata da bakaken magana yayarta wadda suke cewa Yaya mairo ta dinga ziga Zainab, "Ba ruwanki da ita kuma karki kara yadda danki yaje inda take don arna mugayen kazamai ne gasu da asiri na bala'i dan haka ki rike kanki karki bari a mayar miki d'a da irinta dan wannan tuban nata be kai zuci ba mumafuka CE yaudararku kawai takeyi" Haka sukayi ta zigata sannan da yamma suka fito zasu tafi suka tarar maryam tana wanke² a tsakar Gida Se Yaya mairo ta waigo ta kalli Zainab "wai ya sunan ta ne" Ta tabe baki "Wai maryam" Zainab ta fada a wilakance "Kutt dan wulakanci sunana aka samata" Itakam maryam tana ganinsu ta fara murmushi "Sister zaki tafi ki gaida gida Allah ya kiyaye hanya mungode" Tai maganar tana dan durkusawa "Au dama ta iya hausa, tab wai Allah ya kiyaye Ashe tasan Allah" Yaya mairo tafada tana wani kebe baki Da maryam ta fuskanci wulakanci zasuyi mata seta cigaba da aikinta "Tab an baro iyaye an fake da za a musulinta an ta ho bariki, Allah dai ya kiyayemun kanwata" Ido taf hawaye maryam ta dago tana kallonsu "Meye kuma na kura mana ido to indai kurwarmu ce kwalelenki dangin maita, banda jaraba wannan kanin mijin naki yarasa wadda ze aura se tubabbiya tir"    "Nawa ubanki yabani gudunmuwar auren da zanyi?" Sukaji yo muryar Aliyu dama shi ba sabgar matar wansa yake shiga ba saboda ya fuskanci bata da mutunci ita da yan gidansu    "Zainab bari in gaya miki wani abu guda daya tunda iyayena suka karbi maryam banga matar da ta isa tazo tana zaganmin mata ba muddin kika kuma kuskuren zaginta zan baki mamaki munafukan banza kawai marasa tarbiyya" "Noorat aje wanke² kikoma daki rabu da su jahilai kawai" Lokaci² maryam kanyi kuka inta tuna da iyayenta tana kewarsu       Yayinda ya kasance bangaren iyayen maryam ma haka mamanta kullum setayi kukan bakin cikin rabuwa da yarta kullum cikin tunanin Allah yasa kar yarta ta fuskanci kalubalen da ta fuskanta a gurin al ummar hausawa ubangiji yasa tana hannu nagari. Ranar wata juma'a bayan sallar juma'a aka daura auren Aliyu da kuma maryam Malam imam shi yayiwa maryam kayan daki yayinda Usman shi yabiya kudin sadakin maryam Suma aka basu guri a cikin gidan ranar maryam bakinta kasa rufuwa yayi ji take kaman mafarki waita mallaki Aliyunta     Haka rayuwa tacigaba da gudana yayinda maryam ke fuskantar wulakanci daban² daga bangaren Zainab, danginta, kawayenta da kuma  sauran yan unguwa Ko ruwa maryam ta sha da Kofi Zainab bazata kara taba kofin ba datayi abu zata fara cemata tubabbiya ta baro danginta ta taho yawon ta zubar indai Jawwad yaje inda take har dukansa takeyi amma kullum shida Jalal suna manne da maryam Maryam bata taba kulata ba, ita soyayyar da Aliyu da iyayensa suke mata yafiye mata komai dayake Allah besa ta samu haihuwa da wuri ba Aliyu ya maida ita makaranta takuma yin waec bata samu admission ba dan haka se ta shiga poly ta karanta catering   Rashin haihuwar da batayiba ya dameta matuka Aliyu ke kwantar mata da hankali, yana cemata gasu da Jawwad ga Jalal suma yayan sine    yayinda Zainab take cewa tunda an saba zubar da ciki sannan akai aure ya za ayi yanzu asamu haihuwa tunda angama barar da kwayayen a titi sannan aka tsallako aka taho wai an tuba, Itakam maryam bata tanka mata, se dai in Aliyu yaji yazo ya kare mata tas, malam imam ya sha Jan kunnen Zainab akan wannan abubuwan data ke wa maryam amma bata fasa ba dan ba kunyace da ita ba.    Katsam maryam tasamu ciki ta fara laulayi tayi farinciki sosai da wannan cikin dukda kasancewar cikin na wahalda ita Aliyu shiyake mata komai har cikinta ya fara girma sannan tasamu sassauci Amma bangaren cin mutinci daga yan uwan Zainab da sauran yan unguwa se abinda yayi gaba yayinda Zainab ta dinga cewa watakila ma cikin bana Aliyu bane cin zarafi daban² Babban bakin cikin Zainab maryam bata kulata kome zatayi Wata tara cif Allah y sauki maryam lafiya ta haifi ya mace me matukar kyau kamanta daya da Yaya mairo kalar Fulani sosai Tunda aka haifi yarinyar nan JAWWAD da JALAL suka zama yan raino JALAL baya tafiya Gida kullum yana manne da jaririyar nan, JALAL Ya dinga bin Aliyu yana cewa Abee (yanda JAWWAD take kiransa) yana cewa dan Allah Asama jaririyar JALAL dariya Aliyu ya dinga yi yana cewa JALAL kataba ganin ansawa mece sunan maza Shidai ya dage asawa babyn sunansa "Kar ka damu yarona ko dan kaunar da kakewa dana Jawwad zanyima yanda kakeso" Ranar suna ta zagayo akasawa jaririya suna Jalila    Watan Jalila 3 Zainab ta haihu itama ta haifi ya mace lokacin Jawwad yana da shekaru Tara Ranar suna akasama yarinya Nana Fiddausi sunan Jakarta   Nana da JALILA suka tashi kamar yan biyu Jalila ba abinda ta bari bangaren halin mahaifinta na fada da Neman magana in tafita bata da aiki se Neman magana da cin zalin yayan mutane, sukuma iyayensu su kamata su daka  tare da yimata gorin Yar tubabbiya jikar arena Abin yana bakantawa maryam da shikansa Aliyu maryam ta dauki son duniya ta dorawa Jalila in dai aka taba Jalila ji take har cikin zuciyarta amma se ta kauda kai, A cikin Gida ma Maman jawwad yimata take ko Yaya Jalila ta kwace Abu a hannun Nana, in dai Nana tayi kuka Zainab ta dinga zage² kenan tana cin mutuncin maryam   Wata rana hakan ya kuma kasancewa inna mairo bata nan, Jalila tasaka Nana kuka Zainab kuwa  ta wankawa Jalila mari sekace sa'arta, Jalila seda ta fadi tana kuka, sannan Zainab ta dinga zaginta tana cemata Yar gaba da al fatiha jikar arna   "In kika kuma sheganta min yarinya zan baki mamaki dukanta ne kiyi tayi kezaki ji kunya dan anjima tare zasu cigaba da wasa kuma ko kinki yan uwanta ne" Maryam ta fada tanaama Zainab kashedi   "Na fada Yar gaba da alfatiha Yar arna ai ba karya nayiba, kuma Ya"ya na daban ita daban su duk danginmu musulmine tun daga farkonmu har karshe"   Murmushi maryam tayi   "Kina bakanuwa kike cewa kaf zuri'arku musulmine watakila ma hada kakanki ake zagaye Dala tsirara kinga watakila garani damuke kiristoci akan Wanda suke bautawa tsunburbura Jahilar banza se fadan musulinci abaki amma ke babbar Jahila ce manyan sahabban manzon Allah salallahu alaihi wassalam a cikinsu wasunsu bautar gunki sukayi amma daga baya suka zama manyan hadiman musulinci babu banbanci a musulinci annabi be taba kyamatarsu ba" (Kunsan me hakuri be iya fushi ba) "Nice kakana ya zagaye Dala tsirara" Zainab tafda tana nunkanta da yatsa   "Au tambayata kike kina bakanuwa wata kilama shine barbushe" Maryam tabata amsa Ana haka Sega Yaya mairo sunzo ta Tarar ana wannan rigimar Sukazo suyiwa maryam taron dangi Sega Aliyu ya dawo ba shiri suka watse don suna tsoronsa yanayin fuskar maryam ya nuna masa akwai Matsala dan haka da suka shiga daki Ya kalleta "noorat meyake damunki ne, gayamin me ya faru" Batai aune ba se taji hawaye "Habiby bana jindadin yadda ake treating baby(JALILA) ana mata gorin wai ita Yar arna CE ga baby da Neman magana aita zaginta nafara gajiya nafara rama mata am tired suma dasukazo a musulmi ai ba dabarar su bace" Ta karasa maganar cikin kuka Ajiyar zuciya yayi   Ya janyo ta jikinsa yana share mata hawaye "Tunda naga wannan matar tazo nasan a Rina maybe itace ta taba minke, kiyi hakuri Nima abun yana damuna amma kibani dan lokaci wani mataki nake shirin dauka" "My love wani matakin zaka Dauaka AbU ya Riga yazaga gari"   "don't mind u will see" "To shikenan bari naje na wanke mana kaya" "Just relax baby zanyi mana, yanzu ki huta kawai" Bayan wani dan lokaci Aliyu ya nemi aiki a Kaduna ya kuma samu aikin sannan ya nemawa maryam admission a ABU Zaria Malam yayita fada dan meyasa ze bar Gida ya koma wani gari da bashi da kowa Yaiwa malam bayanin yana tsoron abunda ya faru da mahaifiyar maryam itama ya faru da ita a dalilin cin zarafin da ake mata kar itama ta karaya ta koma cikin ahalinta ta koma addininta na baya, haka malam ya yadda badan yaso ba Usman ma da inna mairo sunyi bakin ciki nesa  da Aliyu ze yi  dasu tun tasowarsu suna tare amma yanzu ze tsallake ya barsu shima Aliyu ba a son ransa ba sedan samun nutsuwar matarsa da kuma kare mutuncin iyalansa daga wannan kyama da cin zarafi da ake musu ze bar gidansu da yan uwansa Haka ya tattara matarsa da yarsa suka koma Kaduna inda ba Wanda yasansu Su Jawwad ma har kuka sukayi dukda sun fara girma lokacin baban Jalal yana ta shirin kaisu boarding school Jawwad da Jalal in zasu shiga Jss 1 Akasaka Jalila a makarantar Islamiyya da zamani halin Jalila na Neman magana yana nan bata denaba yayinda maryam ke zuwa makaranta kuma take taba kasuwanci Aliyu ma aikinsa yake yana samun rufin asiri dai² gwargwado har ya mallaki gidan kansa Hankalin maryam ya kwanta sosai yanzu ba Wanda yasan asalinta balle yayi mata gori Lokaci² suna zuwa kano su gaishesu Usman ma yana zuwa ya dakko Jawwad Jalal da nana yazo dasu amma koda wasa Zainab bata taba zuwa inda suke ba Bayan shekaru biyu da dawowar Aliyu Kaduna Allah yayiwa malam imam rasuwa Sunyi bakin ciki sun shiga tashin hankali ba kadan ba sunyi kuka har suka hakura Bayan rasuwar ne Zainab ta hurawa Usman wuta cewar tunda yana samun kudi sosai tun da har kasashen waje yafara fita kan harkar Kasuwanci, dan haka dole Suma subar gidan nan dan be kamata ace kamarta tana zaune a wannan Gida ba Usman yayita nuna mata saboda inna mairo karsu barta ita kadai gashi ta Riga ta saba da unguwar, amma Zainab ta rufe ido taitamasa fitina Haka yaje yasamu inna mairo da zancen ta shi daga Gida tace ba komai ita subarta anan su su tashi, Amma yaki yadda, wataran inna mairo ta ta shi da amai da gudawa aka kaita Asibiti ta galabaita matuka dan haka Usman ya kira Aliyu ya sanar masa da safe Be dau wani lokaci ba Aliyu yayo kano dan maryam bata San ya tafi ba Se bayan la'asar kawai setaga Usman yazo yace mata su shirya kano zasu tafi, "Me zamuyi a kano INA abu Jalila"? " shima yana can" "Dan Allah abban Jawwad in wani abu ne yake faruwa ka gayamin" "Babu komai inna CE ba lafiya" A kidime ta shirya ita da Jalila suka yo kano Kai tsaye Asibiti suka nufa inda ya kaisu wani daki Tana shiga Aliyu ta gani a kwance akan gado rai a hannun Allah jini na fita ta hanci ta bakinsa gashi ko kwarzane babu a jikinsa amma da yayi numfashi ze gudan jini ta hanci ta bakin...... Share please More comments more typing Ina amfani da wannan dama domin mika barka da sallaha layya ga al ummar musulmi a duk fadin duniya sekuma Allah ya kaimu bayan salla Saura aki bani naman salla Love u all Abduljalal novel fans ❤❤❤❤❤❤ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊 [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  13 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Domin joining group dina follow this link What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Is a free book Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤ I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage     Ina amfani da wannan damar gurin mika sakon barka da sallar layya ga dukkan al ummar musulmi Ubangiji Allah ya maimai tamana          -my first Novel- Da sauri maryam takarasa bakin gadon da Aliyu yake kwance yana ta fidda jini ta hanci tabaki ga wani wahalallen numfashi da yake saukewa da kyar, da gudu take ta zube a gabansa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu meya sameka haka" Shine abinda maryam tafada cikin kuka Jalila ma da gudu ta tafi gurin abbanta cikin karfin hali ya rungume Jalila tareda janyo maryam kirjinsa   "Noor kiyi hakuri na taho kano ban gayamiki ba Usman ne yakirani jikin innarmu yayi tsanani shine na taho muka samu accident a hanya" "Sannu abu Jalila Dan Allah ka warke ka tashi mucigaba da rayuwa u are my life habibi"   "Is not complicated dear kawai internal injury ne kuma likitoci zasuyimin aiki zan warke insha Allah Dama haka kike matukar sona noor irin wannan rikicewa haka I love u too my dear u mean a lot to me maryam" Yafada cikin karfin hali da son kawar wa da maryam damuwa   "Abu Jalila is not time for joke lafiyarka tafiyemin komai nikam, inaso mu rayu tare kacigaba dabani farin ciki nida baby Kaine garkuwarmu kai ka dai ka ragemin " Tafada tana zubda hawaye "I love u too ummu Jalila, kije kuduba inna se ki turomin Dan uwana zamuyi magana" Harta yunkura zata tashi "Maryaman Aliyu" Ya kira sunanta dawowa tayi ta zauna ta kuma riko hannunsa "Dan Allah ko bayan raina kar abinda matar usaman take miki yasa ki raba zumuncin dake tsakanin yayanmu" Gyada masa kai tayi sannaan Ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar fita, Usman yana waje a bakin kofa yanajin duk hirarsu gwanin ban tausayi, haka usman ya dinga share hawaye kaman karamin yaro Jiki a sanyaye Tafito daga dakin Usman ya nuna mata dakin da aka kwantar da inna Usman ya koma dakin da Aliyu yake yaje gaban gadon Aliyu ya zauna ya riko hannunsa   "Dan uwana ya jikin naka ya kake ji yanzu" "Yayana mutuwa zanyi bazan rayuba inaso in barmaka amana ne da duk duniya bame rikemin se kai" Aliyu ya fada yana Jan numfashi da kyar Yacigaba da cewa "Dan Allah karkabari babyna tai kukan maraici, ko aure maryam tayi ban yadda ta tafi da yata agolanci ba, inason baby tayi karatu me zurfi, na addini Dana zamani idan ta isa Shiga Jami a inaso takoma hannunka kasan tarbiyar ya mace seda tsayayyen namiji," Yayi tari jini yana fitowa daga bakinsa Usman ne yake share masa jinin yana masa sannu, Sannan ya cigaba da cewa "Kar kayi yinkurin raba baby da maryam yanzu, seta isa shiga Jami a nakeso takoma hannunka, sannan ka tabbatar in baby ta girma maryam takoma garinsu tanemi yafiyar iyayenta, nasan kafin nan sun huce daga fushin dasuke da ita baby taga dangin mahaifiyar ta Tunda kaga mu kenan bamu dayawa, Yayana bana so iyalina suyi maraicina in baby na ta isa aure kazaba mata miji nagari karka manta ka rike alkawarinmu dan uwana, Kacewa innarmu ta yafemin, kagayawa maryam da diyata da soyayyarsu zan koma ga Allah" Ya kalli Usman dake ta zubarda hawaye INA kaunarka Dan uwana" Tarine yakuma sarke Aliyu yana numfashi da kyar Kalmar shahada ya dinga nana tawa, sekuma yayi shiru jikinsa ya saki Usman rungume gawar Aliyu yayi ya fashe da kuka seda yayi me isarsa sannan ya mike ya nufi dakin da aka kwantar da inna mairo, maryam ya gani a gabanta tana bata ruwa tana shan ruwan da kyar wani yana dawowa Yana shigowa inna ta dago kai ta kalleshi tare da fadin ya mutu ko Usman, Aliyu na shima ya tafi," Ta fashe da kuka tacigaba da fadin " Allah ya karbi bakuncinka Aliyu na yafe maka duniya da lahira Maryam kikula da kanki ki rike mana Jalila kaima Usman kakula da amanar da Dan uwanka ya bar maka, maryama  karki manta da abunda nagaya miki inna mairo tayi maganar tana kuka tare da numfar fashi. Lokacin da Aliyu yayi hatsarin aka kawoshi asibitin da inna take, an  turota a wheel chair ta dubashi,, tunda ta Ganshi taga halin da dannata yake ciki ta karaya jikinta ya kuma rikicewa, Duk abin naan da ake Zainab bata taka kafarta Asibiti ta duba jikin inna Mairo ba balle Aliyu da ba Sa shiri Da gudu maryam ta fita ta koma dakin da Aliyu yake ta tarar da shi an rufeshi da bargo dagaske dai Aliyun ta ya mutu "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un maryam ta dinga maimaitawa tare da silalewa kasa sumammiya Kafin akawo motar daza a dau gawar Aliyu inna mairoma ta cika *************************     Ummi na zuwa nan a duniyar  tunani ta fashe da wani matsanancin kuka tare da furta Allah ya jikanka Aliyu na" ta fada hankali.   "Ummina kiyi hakuri idan magana ta ce tabata miki rai kiyi hakuri banyi Dan in bata miki rai ba " Jalila tayi maganar daga inda take kwance ba tare da ta juyo ba Ummi bata CE mata komai ba taci  gaba da kukanta daga karshe ma ta fita ta dauro alwalaa ta tada salla Washe gari da safe Jalila ta fuskanci still umminta bata walwala fuskarta ta kumbura saboda kuka Jalila aikace² kawai take ba tare da ta kula ummin na ta ba seda tagama komai ta hado musu breakfast ta shiga dakin ta tarar da Ummi ta baje hotuna a gabanta tarike guda daya tanata kuka Ajiye tray din hannunta tayi ta karasa gaban Ummi ta Sa hannu ta zare hoton da yake hannun ummin nata ta duba Hotonta ne ita da Aliyu sun kalli juna suna dariya Jalila ta dago ta kalli umminta, " "Ummina soyayyar ce ta motsa kika Sa hoton abeena a gaba kina kuka,?" Jalila tai maganar tana dan murmushi wanda iyakacinsa lebenta, saboda in da Sabo Jalila tasaba da ganin umminta ta dau hoton abeenta tasa agaba tana kuka, kokuma hoton family ta Jalila ta cigaba da cewa "haba ummina idan ina ganin karaya a fuskarki me kike tsammani daga gareni duk lokacin danaga hawaye a idonki karaya nakeyi ummina bana son ganin hawayenki kaddararmu kenan semu karbeta a haka muciga ba da hakuri Allah shiyasan abunda yake boye" Jalila Tafada jikinta a sanyaye tana sharewa Ummi hawaye yayinda itama take zubda hawayen Dukda karancin shekarun Jalila, in tana magana tana tsara zance daki² dukda tarin kuruciya dake dawainiya da ita wani lokacin tana tunani irin na manya Riko hannun Jalila Ummi tayi tare da ajiyar zuciya, "babyna Kidena kuka nima na dena ina tuna abubuwan dasuka wuce ne a baya Jalila bazan manta da halaccin mahaifinki ba a gareni, da kakaninki sunmin halacci ina miki fatan samun managarcin miji me kaunarki kaman mahaifinki sukuma Allah ya kai rahama kabarinsu" "Ameen Ummi" Sukayi breakfast bayan sungama ne Jalila takuma Cuban umminta tace "ummina amma meyasa ba kyason muje garinku, nifa nagaji da cin zarafin da akemin akan danginki ni ko Yaya suke ina so nagansu a haka ko basu da addini ina sonsu ummi" Jalila Ummi takira sunanta Jalila ta dago ta kalleta ba tare da ta amsa ba "Meyasa kika dawo gida hutunku be kare ba nasan akwai damuwa me ya faru"? Turo baki Jalila tayi "To ni Ummi meye be faru ba, wannan Yaya mairon tazo tana cin zarafina,  tun ina yarinya bana gane kyamar da take min har na girma nagane ba ta dena ba why?" Ajiyar zuciya Ummi tayi "Nasan abun da matukar wuya amma kiyi hakuri, kaman yadda kikace qaddararmu ce haka"     "To Ummi su mutane basu San kaddara bane dan mutum ya musulinta daga baya se yazama laifi yazama aabin kyama, wannan wane irin abune Ummi ni mukoma danginki ya fiye min wannan cin zarafin Indai zasu bari muyi addinin mu, gara mu zauna a cikinsu da hujja insan ni jikar kiristoci ce, a fada da hujja tun INA zanin goyo bansan komai ba Ummi mutane ke nunamin kyama saboda kawai daga baya kika tuba, ina kema a da musulma ce uminna enough is enough am tired asarar hawayen damuke yayi yawa"     Ummi kallonta kawai takeyi gaba daya setaga Jalila ta juye takoma mata Aliyu sak irin halinsu daya Jalila akwai saukin kai ita dai batta da Neman magana tana da kawaici amma bata iya fushi ba gaba daya hargitsewa take sekace Aliyu   Janyota Ummi tayi jikinta ta zaro wani hoto "Baby na kinga hoton ki kina Jaririya kamanki daya da kakarki, wani lokacin kuma in kikai abu senaga kaman mahaifiyata"   "Haba Ummi yakike kokarin basar da maganar damukeyi, Ummi I mean what I said fa tun kafin ki haifeni kike fuskantar wannan matsalar, Ummi irin wannan cin mutunci da hausawa keyiwa Wanda suka musulinta daga baya har ina"   "A'a Jalila yan adamne mu in an mana ba dai² ba se muduba Alkhairan mutum kinsan wani Abu, baby na Alkhairan mahaifinki Dan uwansa da kakaninki gareni se in manta da laifin da wasu daga cikin hausawa maraasa fahimta suke min kinemi yardar Allah bana mutum ba Kiduba tunda mahaifinki ya rasu dan uwansa yake dawainiya damu bamu taba kukan babu ba, a garin nan kalli yadda Mike zaune da kowa lafiyaa, indai bazaki dinga duba alkhairan mutane ba se sharri to bazaki taba yi musu adalci ba"   Nannauyar Ajiyar zuciya JALILA ta sauke "Am proud of u ummina kinsa jikina yayi sanyi, to shikenan amma meyasa ba kyason zuwa Gida?" "JALILA inason zuwa amma sekinyi aure in muka je yanzu bazasu kara bari in taho ba nikuma nafiso sekin yi aure semuje ki gansu,  tsawon lokacin danayi ba tare dasu ba zuciyata na tare da su, nafiso koni zasu rikeni ke yazamana kina dakin mijinki shizesa hankalina ya kwanta" Ya mutsa fuska Jalila tayi "Ke kullum zancenki aure²"   "To ai shine cikar mutuncin ya mace nidai fatana kirike mutun cinki a rayuwa Jalila kizama ya tagari abar Alfahari, kuma kizama garkuwa ga mijin dazaki aura ko ya yake," "Insha Allah ummina bazan baki kunya ba" Ummi ta cigaba da cewa "sannan kirike zumunci da yan uwanki Jalila kar abunda mahaifiyarsu da danginta kemana yasa ki gujesu wannan shine abinda mahaifinki yaita gayamin kan ya rasu" "Naji amma bazan kuma zuwa kano ba in sun damu dani su suzo inda nake" Dan zaro ido Ummi tayi "Meyasa?" "daf nake da wataran in wankawa Yaya Mairon  nan mari wallahi," "Jalila ni ban koya miki wannan tarbiyyar ba, duk abinda hakuri bebaka ba rashinsa baze Baka ba" "To Ummi tuba nake" Ta fada tana mikewa tsaye " ga wannan azzalumin shima Dan giya yadda ya dinga cin zalina bazan kuma zuwa kano ba" Tayi maganar a hankali "Me kikace ?" "Ba komai Ummi, cewa nayi siyama bata zo nemana ba tunda na tafi bamuyi waya ba" Tafa Dan kar Ummi ta gane me tace   "Tazo amma jiya da safe kafin Ku iso seda takuma zuwa nace mata baki dawo ba" Murmushi Jalila tayi tareda cewa "Allah sarki Aminiya" Jalila tafada tana murmushi Allah sarki babyna kin makara komawarki kano yazama dole Ummi tayi maganar a zuciyarta    Sallama akayi Ummi ta amsa Jalila kam bata tsaya ba data ji me sallamar ta fito da gudu daga dakin suka rungume juna dame sallamar "Aminiyata nayi missing dinki" Tureta siyama tayi ta Dan hade rai "eh shiyasa naga kullum semunyi waya, nakiraki ba kya dagawa duk cikin missing din nawane" A hankali Jalila tai mata magana "Sorry aminiya Akwai labari" Gyda kai siyama tayi ta Shiga suka gaisa da Ummi sannna ta fito suka koma dakin Jalila, Dakin da dashi da babu kusan daya a gurin Jalila Dan komai Nata yana dakin Ummi se dai in sunyi fada seta koma dakinta kokuma in kawayenta sunzo Suka shiga suka samu guri gefen katifar dakin suka zauna   "Bari Azumi baki San meyafaru bane amma ni kaina nayi missing dinki" "Wallahi kika kuma cemin Azumi tashi zanyi in tafiyata ya za ayi a samun siyama ki dinga wani cemin Azumi kamar wata tsohuwa" "Yi hakuri aminiya siyama na dena" "Kin temaki kanki, wato kikaje kano kika tare kin manta da batun haddar islamiyya, gashi baki ba da uzurinki ba kinsan malam nazeeru ba afuwa Waima ya akayi kika dawo Ummi tace min se hutun school ya kare zaki dawo" Jalila ta nisa "Kinga yanzu bar batun malam Nazeeru nasan yadda zanyi dashi" Jalila ta kwashe kaf abunda yafaru zamanta a kano ta gayawa siyama ciki hada dramar su da Jalal, Jin siyama take kamar Yar uwata ta jini basa boyewa juna komai Jalila tacigaba da cewa "Siyama bazan kuma zuwa kano ba," Jalila ta fada in a serious tone   " aikuwa ke zuwa kano ya kama zaman Kaduna banaki bane" Siyama ta bata amsa "Azumi ki kiyayeni dagaske nake bani ba kano" " kina kuma cemin Azumi zan dinga cemiki matar Jalal" "Allah ya kiyaye, ya za ayi in gayamiki magana kina Neman jamin bala'i Dan giyane fa, naji bazan kuma cemiki Azumi ba amma meyasa kikace dole in koma kano" "Yanzu a ce yaya Jawwad ne yake abinda Jalal yake kikaji abinda Ilham tace zuba ido zakiyi kenan??" "Allah ya kiyaye Yaya na ba irinsa bane bahaka muke ba Narasa dalilin dayasa ya mannewa Yaya Jawwad"   "Aminiya babu Wanda yafi karfin kaddara" "Siyama abinda Jalal yake ba kaddara bane son zuciya ne".      Jalal ne kwance akan wani makeken gado ya tada kai da hannunsa yana ta baccinsa cikin nutsuwa fuskarsa tayi fes kaman Wanda yake jinya, gashi ya rame sosai Wata matace da Wasu mutane a bayanta suka shigo dakin da Jalal yake kwance, suka zagaye gadon da yake duk sun rufe fuskokin, su matar tasaka kaya tundaga sama har kasa ta rufe ko ina da bakaken kaya Hannunta ta mika baya daya daga cikin mutanen dasuka zo tare ya mikomata wata zukekiyar wuka se kyalli takeyi Ta zo kan Jalal ta saita cikinshi da tsinin wukar nan ta daga wukar sama Share please More comments more typing....................  Proud of u my fans wannan page din barka da salla ne 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ ️[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  14 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage          -my first Novel- "Karki caka masa, dan Allah Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!!" Shine abinda Jalila tafada da karfi ta farka daga mummunan mafarkin da take Wanda ya kasance tsakiyar dare Da gudu Ummi ta yanke sallar da take ta taho kan gadon ta dago Jalila "Lafiya me yasameki Jalila,?" "Bakomai Ummi mafarki nayi"   "Kinyi adduar kwanciya bacci?"   Gyada kai Jalila tayi alamar eh "Alwala fa" "Itama nayi Ummi" "Jeki sake alwalar sekizo ki kwanta" Mikewa Jalila tayi taje ta yo alwala ta dawo ta kwanta tayi shiru tana kuma tunanin mafarkin da tayi A hankali Ummi ta zo ta rungume Jalila tana mata addu a, amma har yanzu kirjin Jalila bugawa yakeyi da sauri²   Washe gari da safe suna karyawa, amma hankalin Jalila yana kan mafarkin da tayi jiya Ummi ta lura da ita dan haka, ta yanke shawarar  tambayar Jalila mafarkin da tayi take ihu cikin dare "Jalila mafarkin me yasaki ihu cikin dare jiya"? "Ba komai" Jalila tabata amsa "Kaman ya ba komai kin firgitani" "Ummi ni dai nasan nayi mafarkin tsoro amma na manta me nagani" Kallonta Ummi ta yi "Baby kenan adinga addu'a dai" "Inayi ai Ummi amma zan kara insha Allah" "Yayi kyau kici abinci kidena wannan tunanin" Gyada kai Jalila tayi ta Dan cakali abincin ta bari Uniform din islamiyyarta ta dakko tana gogewa, amma duk kokarin ta, ta cigaba da harkokinta tana tuna mafarkin nan se gabanta yayi mummunar faduwa "Subhanallah" Shine abinda Jalila take fada in ta tuna mafarkin, haka ta karasa gugar tasaka uniform din islamiyya tana zaman jiran siyama ta karaso su tafi islamiyya Qur'anin da Daddyn Jalal yabata ta je ta dakko tasamu guri tazauna tana kallonsa tana shafawa se jujjuya shi take a hannunta Sallamar Siyama ta ji amma bats motsa daga inda take ba Siyama suka gaisa da Ummi a tsakar gida "Ummi ina Jalilan take?" "Tana cikin dakinta yau narasa meyake damunta yau tun safe tana daki" "To Ummi bari ingani kinsan ta wani lokacin se a hankali" "Aikam halin Jalila ai se hakuri" Dakin Jalila ta shiga ta tarar da ita tana ta jujjuya Qur'ani a hannunta "Aminiya lafiya dai yau kuwa,wannan Qur'anin fa me kyau, kice har babban guzuri kika taho mana da shi" Ita dai Jalila ba tace mata komai ba ta mika mata "Masha Allah gaskiya yayi kyau box din da yake ciki ma gwanin sha awa bari in sashi a Jaka mutafi da shi Islamiyya munyi sabon Al Qur'ani "Bani" Jalila tasaka hannu ta karbe Al Qur'anin daga hannunta Jalila "wannan ba na zuwa islamiyya bane kallonsa kawai zan dinga yi" "Kamar ya "? " kamar yadda nagaya miki" "Allah yabaki hakuri naga yau tambotsai kikeji" Jalila bata kuma kulata ba ta dauki hijjabinta ta saka ta maida Qur'anin cikin cover dinsa ta adana shi   Suka fito "Ummi zamu tafi" Siyama tayi maganar tana risinawa "To adawo lafiya Allah yayi Albarka" "Ameen Ummi" duk wannan maganar da ake Jalila batace uffan ba Har sunkusa fita Ummi tace "Ke madiga ina taki Jakar makarantar?" "Ban gan taba sena dawo zan duba" Tafada tana sunkuyar da kai Girgiza kai kawai Ummi tayi sukuma suka tafi Daga office dinsa ya dinga jiyo hayaniyar  Jalila ta dawo daga ajin dake gaban office dinsa Tsaki ya ja ya kalli dayan malamin "Aifa bismillahi wannan baki abun maganar ta dawo yanzu bamu da sakat saboda surutun dalibai" Daya malamin ne ya kalleshi "Lallai kam malam naziru indai Jalilace baki abun magana, ga surutu ga Neman magana, inda take birgeni kwakwalwarta tana Ja sosai, kuma duk tsiwarta intai laifi akwai bada hakuri" "Hmm kaidai bari kawai idan nafara lissafo maka halin yarinyar nan ai se dai addu'a" Murmushi daya malamin yayi sukayi musabiha ya bar office din Mamakine ya cika shi kodai kunnensa beji dai² ba yaji ana Jalila ta dawo amma yaji ajin shiru kaman an cinyesu se Dan surutu da suke kasa²   Har yayi gaba ya dawo ya leka Ajin aikuwa itance amma fuskarta Sam ba walwala ta koma gefe tayi shiru se Siyama dake gefenta tana mata magana Kai tsaye ya dawo kofa ya shiga ajin gaba daya suka nutsu "Baku San me yakawoku nan bane Ku dakko Qur'anin Ku kufara tilawa," Ya kai dubansa kan Jalila "Ke yau kwananki kusan goma bakizo makaranta ba, kuma baki bada wani uzuri ba" Siyama tai saurin cewa "Malam Naziru nafa gaya maka.." "Ke rufemin baki marasa da'a ina magana zaki katseni" Ya maida dubansa ga Jalila "in anjima zanzo karbar hadda duk na kwanna Goman nan sekin bani haddasu Kukama Ku dakko Qur'anin Ku nace" Kowacce kokarin dakko Qur'anin Sa yake banda Jalila wadda kamar an dasata "Ke ina naki Al Qur'anin"? Ya dakamata tsawa Qur'anin hannun Siyama ta nuna masa Ya kalli siyama " ke ina naki?" Itama Qur'anin ta nuna masa "rainamin hankali zakuyi kenan?" Fita yayi be dade ba se gashi da wata katuwar dorina yana zuwa ya fara takan Siyama ya zaneta sannan ya nufo inda Jalila take Zumbur ta mike ta fara ja da baya "Dawo nan ki tsaya, fara bani haddar yanzu zan karba" Yafada yana muzurai yana nuna mata gabansa "Ni wallahi banyi haddan nan ba kuma in kada keni da wannan bulalan suma zanyi"   "Ai ko mutuwa zakiyi yau sena zaneki Dan kun rainamin hankali wai Qur'anin Ku daya Ku biyu" Aikuwa Jalila ta dage ta kwala ihu tare da fadin "Malam babba kazo ka temakeni, danka ze kasheni, za a daki amanarka Dan Allah kazo" Daga ajin da dattijon yake zaune yana biyawa dalibai karatu ya jiyo ihunta tana kiran sunansa Malam babba shine mamallakin makarantar malam, Naziru kuma dansa ne dabasa jituwa da Jalila Wataran ya daketa tayi suman karya, aka kaita Gida lokacin Abban su Jawwad yazo, hankalinsa ya tashi sosai yazo har makarantar ya samu malam  babba akan dukan da akayiwa Jalila yayi yawa, malam babba yaita bashi hakuri, shine Abban Jawwad   "yace malam ga yata nan Amana dan Allah a hannunka marainiya CE adinga hakuri da halinta" shikuma yace ya karba, indai za a daketa har cikin zuciyarsa yakeji bayason kukanta Itakuma Allah be hada jininta da malam Naziru ba, kusan kullum Seya nemi abinda zesa ya daketa Tashi yayi da sauri ya taho ajin dayake jiyo ihunta yaganta ta makale a lungun ajin tanata kuka ga kuma malam Naziru a tsaye da bulala "Naziru lafiya nakejin kukan 'yata" Nan malam Naziru ya shiga gayamasa abunda akayi da Wanda ba ayiba "To ina nema mata afuwa bana son ana samun ita kuka dukda Yar tawa tafiye Jan magana" Gyada kai malam Naziru yayi ya fita daga ajin zuciyarsa fal bakin cikin rashin Zane yarinyar nan. Malam babba ya hada litattafan makaranta yabawa Jalila sannan yace ze aikomata da Jakar makaranta Itakam siyama har aka tashi daga Islamiyya kukan dukan da akayi mata take Dan tana tsoron bulala, mafi akasari in Jalila tai lefi akanta abun yake karewa. Da aka tashi Har Gida Jalila ta  raka siyama tana ta bata hakuri Kwana biyu  Jalila tacigaba da harkokinta hankalinta kwance amma data tuna mafarkin nan se ta ji jikinta yayi sanyi Tana kwance a dakinta gidan bakowa tanata tunani bacci ya kwasheta Ummi bata nan ta tafi kasuwa Jeje ne zaune yana ta busa shisha, shikuma Jalal yasaka Bluetooth a kunnensa ya jingina da kujerar da yake kai Jeje yadan taba shi alamar yanason zeyi magana da shi cire Bluetooth din kunnensa yayi yana kallon Jeje alamun ina jinka Jeje yai gyaran murya "Man wai ya batun tafiyarmu Dubai ne naji ka shiru" Lumshe ido Jalal  yayi "Tafiya tana nan daddy ya turomin kudi nayi arranging din next week ne insha Allah" "That's good my man but a yanmatan nan baka ganin yakamata mu tafi da wasu abun zefi dadi inda mata a harkar" Hade rai sosai Jalal yayi murya a kaushashe yace "Amma kasan a tsarina babu mata ko? bana gayyatowa kaina ciwon kai, in kaga bazaka ba seda mata to  kawai ka zauna, ba Y'ar Wanda zan dauka in tafi da ita" Lallai gayen nan, amma a hankali da matan zamu kafa maka tarkon dabaka Isa ka tsallake ba, tarkon daza mu rikeka a wuya jeje yai maganar a zuciyarsa A fili kuma yace "As u wish my boss abar maganar mata mutafi kawai" Jalal bekuma tanka masa ba Yakoma ya jingina da kujerar da yake "Are u serious Jalal wai damaa dagaske kake tafiya Dubai zakayi, mahaifiyarka fa bata so mahaifinka ma ba a son ransa zaka tafi ba meyasa bazaka hakura ba? Haba Dan uwana kayi tunani mana" Jawwad ya karasa maganar a sigar rarrashi "Ina ruwana da rashin yaddata data yadda da karta yadda duk matsalarta ne, daddy kuma tunda ya yadda ya turamin kudin ai ya yadda kenan"   "Haba Jalal duk abunda kayi ba da yadda iyaye ba kosa albarkarsu ba karshen al'amarin lalacewa" "Indai albarkarta ce banaso ta babana ta isheni" JALAL yai maganar yana hade rai A fusace Jawwad ya kalleshi "JALAL uwa uwace komai lalacewarta balle babu lalacewa a iyaye meyasa kai baka yafiyane? Kamanta mana komai ya wuce hawayenta masifa ne a rayuwarka" "Idan na tsallake nabar Nigeria seta manta dani kafin na dawo kaga ta huta ta dena hawayen" "Haba Jalal mahaifiyarka CE fa meyasa kafiye taurin kai ne meyasa baka yafiyaa me"? "Dole kace haka tunda ba kai kake irin rayuwar danake ba, ba kai ka samu kanka a halin da nake ciki ba, mutane na kyamarka shiyasa kake cewa in manta komai ya wuce, Idan nabar kasar nan seta ganni zatayi kukan ai lokaci² nazo inga daddy" "Jalal anya Kasan soyayyar dake tsakanin d'a da uwa kuwa baka tunanin halin daza ta shiga in ka tafi?" Jawwad ya fada yana kallon Jalal da yake shirya kayansa a trolley Be dago kai ya kalleshi ba yabashi amsa "Kai kasanta ita soyayyar d'a da uwar, gobe insha Allah zan bar kasar nan kudena ganina balle ranku ya cigaba da baci akaina" Jalal ne da Jawwad ke zaune suna hira gwanin sha'awa sunayi suna dariya suna cin yayan itatuwa a wani lambu me matukar kyau da korayen bishiyu Wani mutum ne ya zagayo ta bayan su Jalal ya rife fuskarsa ba a iya gane waye, yabawa Jalal wani abu, Jalal ya karbi abun yafito da shi ya dubi kirjin Jawwad ya zaro wata siririyar kibiya Yar Karama ya sokawa kirjin Jawwad din saitin zuciyarsa, nan take Jini ya balle, sekuma Jalal ya yadda kibiyar ya rungume Jawwad yana kuka, wannan matar ce ta rannan tazo tafara Jan Jalal, Nan da nan gurin Yakoma baki bishiyoyin gurin suka bushe, Ta dinga janshi zuwa wani katon rami ita da wani mutum Jalal mikowa Jawwad hannu yake "Dan uwa ka temakeni kar kabari sujani cikin Ramin nan" Jawwad dafe da Inda Jalal ya sokamasa kibiya jini na zuba yake fadin Bazan iyaba Dan uwa Jalila!Jalila!!Jalila!!! Kitema kawa Jalal karki bari su jashi cikin ramin nan Siyama dake sallama a tsakar Gida ta jiyo kukan Jalila da Sauri ta karasa Inda take jin kukan nata Tana kwance akan gadon Ummi ta hada gumi se kace tayi dambe da zaki ga hawaye a fuskarta, se jujjuya kai take tana fadin "A'a nima bazan iyaba Yaya Jawwad bazan iya temaka masaba nima zasu hada dani" Subhanallah siyama tafada tare da jijjiga Jalila A firgice Jalila ta farka daga mummunan mafarkin datake tana haki "Jalila lafiyanki kuwa meyasameki? ina ummi? Tun dazu na shigo nake sallama ba Wanda ya amsa me yasaki wannan kukan" "Bakomai" Tabawa siyama amsa "Kamarya ba komai kalli fa yadda kika hada gumi ga kuka kinayi" Siyama tafada tana nunata Mikewa Jalila tayi ta tafi gaban mudubi Ta kalli kanta taga yadda ta hada gumi ga hawaye, idonta har yayi ja kaman ta wani tana kuka Wayarta ta ta dakko ta dawo inda ta tashi ta zauna "Aminiya waime yake damunki ne akwai matsala ne?" Girgiza mata kai Jalila tayi tana duba wayarta lamabar Yaya Jawwad tayi dialing bugu biyu ya daga sekuma tayi shiru tarasa mezata CE Jalal ne ya katse shirun ta hanyar Sa wayar a hands free  sannan ya yimata sallama "Salamu alaikum warahmatullah sisyna yakike ya Ummi" Ajiyar zuciya tayi Alhamdilillah yana raye "Me kikace?"   "Duk Muna lafiya ya maama da Nana" "Muna lafiya sisyna, ya karatu" "Yaya Jawwad" Takira sunansa "Na'am sisyna ya akayi?" "Kana inane?" "Akwai matsalane? yau weekends muna gida ina tare da yayanki Jalal ina ta fama dashi wai se ya tafi Dubai ya barni, in ya tafi kuma wai baze dawoba   Dan karamin tsaki Jalila tayi sannan tace " to Yaya seme? kabarshi yaita tafiya daga nan har bangon duniya ya tafi ai gara hakama tunda baze karatu ba kaman sauran mutane ba seya tafi yayi abunda ya dace dashi kaima ka nutsu ka maida hankali akan naka karatun" Cak ya tsaya da hada kayan dayake saboda yanajin duk abinda Jalila take fada saboda Jawwad a hands free yasaka wayar wannan Jarababbiyar yarinyar bazata fasa aibata shiba kenan Shikam Jawwad saroro yayi yama rasa meze ce Da kyar Jawwad  ya hadiye yawu yayi gyaran murya "Sisy bana gayamiki addu'arki Jalal yake bukata ba shima fa dan uwanki ne kidena fadan maganganu marasa dadi akansa kinji ko" "To naji nadena ka gaida maama da Nana" Haka dai suka gama wayar da Jalila Jawwad ne ya kalli Jalal sannan ya kira sunansa da nufin yaba shi hakuri akan abinda Jalila take masa Daga masa hannu Jalal yayi " gara in bar muku kasar hankalinku ya kwanta hankalin kanwarka ya kwanta kar in lalata ka" yacigaba da abunda yake "Jalal bahak..... Daga masa hannu Jalal yayi " no need to say anything " "Aminiya wai bazaki gayamin meke faruwa ba"? Siyama takuma tambayarta " ke kin isheni nace miki ba komai amma kin isheni kibarni inji da abunda yake damuna!" Jalila tayi Wa siyama maganar a hasale Dan zaro ido siyama tayi "Sorry Allah yabaki hakuri laifina ne danazo inda kike kuma na damu da damuwarki dama zuwa nayi in gayamiki dazu malam babba yace agayamiki akwai musabaka next week insha Allah" Tana zuwa nan ta tashi tafita tabawa Jalila guri Sam Jalila jinta take wani iri wannan wane irin mafarkai takeyine akan Jalal A haka Ummi tadawo ta tarar da ita wani iri kaman Mara lafiya tana nuna mata abubuwan data siyo amma hankalinta baya kanta "Baby waime ke damunkine?" "Ummi marata ce take ciwo kuma na sha magani" Dayake tana cikin period ta wayance da hakan "Allah ya sawwake" "Ameen" Ummi ce tayi musu girkin dare "Wai har yanzu marar ce tashi kici abinci ki kuma shan magani" "Ummi na koshi da abincin" "Baby kin fiye taurin kai shiyasa bana son rashin lafiyarki kin fiye gaddama tashi ko tea kisha" Tea din kawai ta sha ta nemi guri ta nema ta kwanta amma fargabar yin baccin take saboda bata San mezata kuma gani ba Se jujjuya mafarkan da tayi takeyi a zuciyarta dayake bacci barawone haka yayi awon gaba da ita dukda tarin fargabar da take ranta "Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi........... TURKASHI MORE COMMENTS MORE TYPING......... YAYINDA COMMENTS DINKU YAYI KASA ZAN DENA TYPING KULLUM KUNA COMMENTS INA JIN DADI INA MUKU TYPING 💃💃💃 KUNA BARI INA LALACI LOVE U ALL ❤❤❤❤❤ INA ALFAHARI DAKU MASOYA NA INA GODIYA ❤❤❤🌹🌹🌹🌹🌹 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  15 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage Aimin afuwa the page is not edited          -my first Novel- Ni bazan iyaba wallahi, idan suka kashe nifa, niba abunda zan iya yatafi ina ruwana "Ke Jalila wai meye hakane Ba magana nake miki ba" Tashi Ummi tayi taje ta jijjigata a firgice ta tashi tana rarraba ido "Wai meyake damunki a yan kwanakin nan kusan kullum sekin tayar min da hankali in dare yayi ko dai gamo kikayi da Aljanu" "Niba wasu aljanu kawai tsorata nake" Jalila tafada tana ya mutsa fuska "Au tsoratanne kawai, to tunda kawai ne kika kuma min kuka a cikin bacci bulala zan saka in zaneki ta shi kije kiyo alwala kiyi salla ki dau Qurani ki karanta Allah yasa kina Azkar" "Ummi bana salla" "To jekiyo Alwala kibiya Wanda kika haddace" Ba musu taje tayo alwala tazo taita bitar Qurani da ka bacci kam gagararta yayi se dai juye²   Yauma kamar kullum haka ta tashi jikinta kaman Mara lafiya ko abincin kirki takasa ci ga idonta daya kumbura saboda rashin bacci Ummi kallonta kawai take dakinta ta koma ta nemi guri ta kwanta tayi shiru (Karki bari Jalal yayi tafiyar nan in har yayi tafiyar nan rayuwarsa zata lalace fiye da da burinsu ze cika, Wanda abun ze iya shafar rayuwar Jawwad , ze lalace fiye da baya kiyi wani abu a kai Jalila kar ki bari Jalal ya tafi!!!) Tas kalaman da akayi mata a mafarki suke dawo mata kwakwalwarta Wanda yayi dai² da wani mugun bugawa da zuciyarta tayi da karfi, kanta ya Sara "Nashiga uku ni Jalila wannan wani irin bala'i ne meye hadina da wannan mutumin ake tsoratani akanshi wani tsautsayin ne ya kaini kano wanannan wani irin jarabane ana nema a haukatani why?" Tafada tareda yin jifa da pillows din kan katifar ta yage bedsheet din kan gadon ta kifa kanta akan katifar "Dan Allah ji abinda nake kamar mahaukaciya Ta Yaya zan hanashi tafiya ina nan yana can how? Be duba amincinsu da Yaya Jawwad yafasa tafiyar ba se ni da bama shiri to ni ya zanyi? Kawai shirmen mafarkine kimanta kicigaba da harkokinki Wani bangare na zuciyarta ya gayamata, aikam ta yadda da abinda zuciyarta ta gayamata na ta manta shirmen mafarkine Ga bacci a idonta kanta har ciwo yake amma bazata iya ba saboda fargabar inta kwanta me zata gani Duk yadda taso ta manta takasa zuciyarta se bugawa take da sauri² hankalinta yaki kwanciya " Nashiga uku ni Jalila meke shirin faruwa dani haka ya zanyine? Ko ingaya Ummi me Karki kuskura hakan be dace ba mussaman intaji abinda yayi miki bazataji dadi ba, wani sashi na zuciyarta ya gargadeta Siyama ce ta fadomata a rai, dan haka da sauri ta mike taje ta wanke fuskarta tasaka hijjabi ta fito, ta tarar da Ummi tana saka a dakinta "Ummi inaso zanje gurin siyama" "Adawo lafiya kigaidamin da ummanta saura ki dade inkika dade kin kori gaba kinsan halina" Gyada kai Jalila tayi ta fita ta nufi hanyar gidansu siyama Haka nan take tafiyar kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, haka takarasa gidansu siyama.     makeken Gida ne Wanda yayi matukar haduwa da tsaruwa baban siyama yana da kudi sosai custom ne daga shi har Maman siyama mutane ne masu saukin kai kuma sun yaba da hankalin Jalila shiyasa suka kyale kawancen nasu Siyama Sam bata da girman kai a makarantar boko suka hadu da Jalila tun primary suke tare makarantar 'yay'an masu kudi ita Jalila takeyi saboda Jajircewa da rikon amana na baban su Jawwad Kawancensu har tsakanin iyayensu mata Wanda yakai har kasuwanci sukeyi tare, umman Siyama ta San komai game da rayuwar ummin Jalila ta dauketa kaman Yar uwatta ummin Jalila bata fiye shiga harkar mutane ba amma tana mu'amala sosai da umman Siyama A tangamemen parlour Jalila ta tarar da Umma (mahaifiyar siyama) "Hajiya Umma brk da rana" "Anya Jalila zan amsa gaisuwar nan taki, kinyi tafiya ba sallama kin dawoma bakizo mun gaisa ba balle insa ran tsaraba to ni nayi fushi" Umman tafada cikin zolaya "Haba Umma tuba nake yau ai gani Nazo" "Bawani kinzo dai gurin Siyama sekije tana daki, Nikuma zamu gauraya dake naganki wani iri ko baki laafiya ne"? "Hajiya Umma kenan, lafiyata kalau, bari inje gurin siyama, Ummi tana gaisheki " "Ina amsawa" Jalila ta mike ta haura sama dakin siyama Siyama ce kwance akan katafaren gadonta tayi rub da ciki tana game a waya, Sallama Jalila tayi, siyama ta amsamata ba tare data daga kai ta kalleta ba "Aminiya gurinki nazo akwai matsala" Banza siyama tayimata tacigaba da abinda take "Aminiya magana fa nake kika min banza" Jalila ta maimaita "Ni a wa zan San matsalarki, ni na isa ko kin manta wulakancin dakika yimin A gidanku" Siyama ta bata amsa ba tare da ta dago ba "Ohh God am sorry aminiya lokacin ina cikin tashin hankaline, Dan Allah kimin afuwa ki saurareni, right now ma a cikin wata matsalar nake siyama jinake kaman zanyi hauka, yanzu haka zuciyata bikiji bugun data keyi ba"   A razane siyama ta mike zaune tana kallon Jalila "Kaman Yaya? Meyafaru?" Ajiyar zuciya Jalila tayi sannan ta labarta mata duk halin da ake ciki "Ni yanzu babban tashin hankalina aminiya ni bansan ta Yaya zan hana shi tafiyar nan ba yana kano ina Kaduna, Tunda na fara mafarkan nan bana nutsuwa se inji kaman zan haukace" "Easy, don't said that again please karki kuma batun hauka Kinga maganata ce fito  dama nagaya miki zaman Kaduna bana kibane inkika temake shi kanki kikayiwa kamar kin temaki Jawwad ne" "Kinga ni ba wannan surutun ba kigaya min mafita siyama kaina ya kulle" "Aikuwa dole kibude shi, shi tunanin naki, yaya Jawwad zaki kira ki zigashi akan kar yabarshi ya tafi saboda besan meze faruba in ya tafi zuciyar Yaya Jawwad zzaki karya yadda zaki ingiza shi ya hana shi tafiya" "Siyama bana tunanin hakan me yiwuwa ne, nasan Yaya Jawwad zeyi iya yinsa kan yahana shi tafiya tunda kika ga ya hakura to abun yafi karfinsa, Dama da ganin idon nan na Jalal zeyi azababben taurin kai" "A'a Jalila ki dai gwada kigani, kema ai taurin kan yana damunki" Mummy ce take ta rusa kuka "Yanzu Jalal dagaske tsallakewa zakayi kabarni, kai kana ganin hakan shine dai² a rayuwarka bani da kowa se kai zaka Sa k'afa ka tafi, har kana fadin inka tafi bazaka kuma dawowa ba" "Idan na tafi hutun mune ni dake gaba daya ki huta dasaki bacin rai danakeyi" Ilham ce tafito tazo gabansa "Haba Yaya Jalal yanzu in... " ke!!!!! Kikasake kika Sa min baki sena tattakaki ina ruwanki dani mayya kawai" Ya fice daga parlour lambar Jeje yakira "Karka manta fa kazama cikin shiri karfe hudu insha Allah jirginmu ze tashi" Ya katse wayar ya tafi dakinsa "To siyama bari in jarraba amma nikam na karaya Allah kabani iko " "Ameen don't waste time yi sauri" Siyama ta fada a gaggauce Lambar Jawwad Jalila ta kira Aikuwa tayi sa'a ya dauka "Barka da rana yayana" "Yawwa autar Ummi ya ummina ya Gida" "Lafiya kalau, amma yanaji muryarka wani iri ko duk Dan tafiyar Yaya Jalal dinne" "Kedai bari sisy na Daren Jiya banyi bacci ba Jalal ya kafe wannan karon tun tasaowata tare muke dashi jinsa nake wani bangare na zuciyata amma ze tafi ya barni gani nake Lamar da wasa yake" Ajiyar zuciya Jalila tayi "Ya tafinne?" Jalila ta tambaya "A'a jirgin karfe hudu zebi yau zetafi" Cikin Jalila ne yayi wata kara ta kalli agogo karfe daya da rabi "Yaukuma ?" Tafada a tsorace Siyama ce ta kalleta ta girgiza mata kai alamar kwarin gwiwa "Eh yau sisy haka dai yacemin, yau ban yi tsammanin Dan uwa zetafi ya barni ba" Jalila ta numfasa tace "To waime yasa ze tafine?" "Cewa yayi gara ya tafi mummy ta dena ganinsa, yadena sata bacin rai" "Allah sarki mummy ko yazataji idan ya tafi, ya daddynsa zeji in ya bude ido yaga baya kusa dashi, Yaya Jawwad abokinka bashi da tausayi baka tunanin me ze faru Idan ya tafi kasar da babu me Sa shi babu me hanashi, Baka tunanin wasu abokai ze hadu dasu a can, Allah sarki nasan dole mummy ta zubda hawaye inya tafi, kuma Kasan hawayenta matsalane a rayuwarsa, Yaya yakamata kahana shi tafiyar nan, ka temakawa rayuwarsa daga masifar hawayen uwa Yanzun ma karkayi mamaki abokanan banzarsa ne suka ziga shi shine zeyi tafiyar" Da sauri Jawwad ya tashi zaune tare da furta "Abokanan banza Jeje" "Mekace Yaya" "No bakomai zanyi kokari inkuma jarraba hanashi tafiya nagode sosai da gudunmuwarki kanwata, da na hakura amma kin tunatar dani wani abu me mahimmanci nagode" Sukayi sallama Jalila tayi ajiyar zuciya "Good dear kinyi yadda yakamata sekace Jarumar film" "Hmm ba wannan ba aminiya Allah yasa ya yadda kar yayi tafiyar nan" "Ameen insha Allah bazeyiba Addu'a zamuyi tayi" "Allah ya amsa amma nakaraya saura awa biyu ya tafi fa" "Ba komai calm down mucigaba da addu'a Allah ya bawa Yaya Jawwad sa'ar hanashi tafiya" "Ameen" Jalila ta amsa a sanyaye Da sauri Jawwad ya tashi ya nufi gidansu Jalal kai tsaye part din Jalal ya nufa yaje ya tarar yashiga wanka Gefe ga katuwan trolley dinshi ya hada ta tsaf A hankali Jawwad ya shafa trolley yayi ajiyar zuciya, ya nemi guri ya zauna yana jiran fitowarsa ya shafe akalla mintuna sha biyar yana jiransa sannan ya fito daga wankan "Kana nan banji shigo warkaba ai" JALAL ya fada yana goge jikinsa da Dan karamin towel "Jalal" Jawwad yakira sunansa da dan sauri Jalal ya kalleshi saboda da wuya ya ambaci sunansa "Baka saba yimin karya ba yanzun ma bana fatan kayimin kaida wa zaku tafi dubai"? Jalal ya danyi shiru sannan ya yi magana " nida Jeje ne"? Da sauri Jawwad ya kalleshi Jeje fa kace Jalal "Jalal kasan me kake cewa kuwa yanzu kaida shi zaku tafi, Ka fifita tafiya kabar iyayenka saboda wannan Dan iskan Mara mutuncin Kazabi ka tsallake kawai katafi garin da banaka ba, ka zauna, Dama nasani he is behind all what u are doing" "No Jawwad don't blame him u know who is behind all this kasani kasan komai karka Dora masa, nan da wani dan lokaci shi  jeje ze dawo nizanyi zamana a can in karatun Yakama in cigaba a can" "Jalal kasani ba kaunarka yake ba, baze bari kayi kyakykyawa rayuwa ba kullum burinsa ya kuma rusaka" "Ouhhh don't mind me bros, kabani gudunmuwa a rayuwata bazan mantaba, bana tunanin ko ciki daya muka fito da kai zansamu fiye da haka , Amma gara in barka kaima ka huta, kanwarka bata son  mu'amalarka dani banaso mutane sucigaba damin kallon zan bata maka rayuwa kamar yadda tawa tasamu illa, Banason mutane sucigaba da kyamata da miyagun halayena Gara inje rayuwar da naga dama Inda ba Wanda yasanni balle ya damu dani" Cigaba da shirinsa Jal yayi yasaka kananan kaya wando jeans da T-shirt blue, ya taje sumar kansa ya daura agogo sannan ya dakko bakin glass yasaka Yayi kyau matuka, duk abin nan da ake Jawwad yana zaune yana kallonsa, "Dan uwana kazama me min addu'a aduk inda kake kaman yadda kake min abaya Jawwad bazan manta da kai a rayuwata ba" Jalal yafada jikinsa a sanyaye "Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni, Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai, Da second daya bantaba kyamarka ba amma sekai akan wani dalili naka Mara amfani Zaka tsallake ka barni, Akan wannan Mara imanin zaka tafi kabar kasarka ta haihuwa iyayenka yan uwanka ka tafi, wannan shine sakamakon abota wannan shine yan uwantakar dake tsakanina da kai This is what I deserve from you nagode da kauna Jalal" Jawwad yayi maganar cikin fada Jalal ya tako gaban Jawwad ya dafa kafadarsa idonsa dauke da kwalla, muryarsa na rawa yafara masa magana "Am sorry dan uwana baka cancanci haka daga gareni ba but am sorry ba yadda na iya" Yaja trolley dinsa yayi waje da sauri "Siyama nifa wallahi gabana faduwa yake ganinake wallahi seya tafi Bakisan halin Sa da taurin kai ba" "No kwantar da hankalinki, kome zezo da sauki insha Allah yanzu kira Yaya Jawwad din muji ya ake ciki" "Anya zan iya magana kuwa bakiji bugun da zuciyata take ba" "Calm down kirashi kiji" Layin Yaya Jawwad takuma kira Sedata kusa tsinkewa sannan ya daga "Yaya Jawwad ya ake ciki ne yafasa tafiyar kuwa" "Jalila ya tafi bashi da niyyar fasawa ya tafi yau ze bar kasar nan" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Share please More comments more typing...... Love u all my fans 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ Daga Alkalamin Yar baba [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  16&17 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage Aimin afuwa the page is not edited          -my first Novel- Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Jalila ta fada jikinta a sanyaye A hankali ta sauke wayar daga kunnenta ta kashe wayar Takalli siyama "Aminiya ya tafi" Yasalam shine abinda siyama ta furta "Kwantar da hankalinki har yanzu da sauran lokaci ai" "Kwanciyar hankalifa babu shi Aminiya dan bakiji yadda zuciyata take min bane Bari in tafi Gida uumi tace kar in dade kuma kinga nabata lokaci bari in tafi kawai" Har gate Siyama ta rakota tana bata kwarin gwiwa, tare da bata shawarar cigaba da addu'oi Sannan ta mata alkawarin zatazo har gidan taji yadda akayi Haka Jalila ta tafi Gida jikinta a mace Yanayin fuskar Ummi ya nuna mata tayi fushi da ita Dan se basar da ita take Jalila ta rasa meyake mata dadi Jeje ne a tare da wani mutum a cikin mota me tint glass yasaka wando three quarter da wata Yar Riga Mara hannu suman nan tayi tsage² Kai daka ganshi ka ga dan iska "Katabbatar kayi abinda yakamata in kukaje kasan abinda ya dace kayi shima wannan aikin naka akwai kaso me tsoka ka tabattar da aikin nan ya tafi dai² " Mutumin yayiwa jeje maganar "Considered it done my boss zan tabbatar da aikin nan ya tabbatat" Jeje yafada yana dan risinar da kai "Good" mutumin yafada cikin Isa Sannan jeje ya bude kofar motar ya fita ya dauki akwatinsa Inda sukayi zasu hadu da Jalal yaje ya tsaya ya kirashi a waya yan mintuna kadan sega Jalal ya karaso Shima "hmm yau kayi abun arziki ka cika alkawari" Murmushi Jeje yayi "ba dole ba my boss ina ciki farin ciki" "Good yanzu se mu tafi ko" Gaban Jalal ne yai mummunar faduwa Meyake damuna ne haka, menake shirin yine" Jalal yake maganar a zuciyarta "Yanaga kana tafiya kuma a hankali yanzu ko akwai abunda yake damunka" Jeje ya tambayeshi Girgiza kai Jalal yayi Jeje ne yafara mika passport dinsa aka duba aka bashi ya danyi gaba yana jiran a duba na Jalal, Jiki a sanyaye Jalal ya mika passport dinsa (Karka kara kirana dan uwanka Jalal niba dan uwanka bane, tunda zaka iya manta soyayya da shakuwar dake tsakaninmu ka tsallake ka barni, Tun tasowata bani da dan uwa namiji ban budi ido da kowa ba a matsayin aboki dan uwa sekai,!!!!!) Maganganun Jawwad ne suke dawo masa dakuma tsantsar damuwa da hawaye da ya gani kwance a idon Jawwad su yake tunowa se yaji zuciyarsa ta cunkushe bakin ciki ya ziyarci zuciyarsa, gaskiya ba karamin kauna Jawwa yake masa ba in ya tafi beyiwa kansa adalci ba Jawwad wani bangarene me mahimmanci a rayuwarsa ga kuma mahaifinsa, anya inyayi tafiyar nan yayiwa kansa adalci jikinsa ne yayi matukar yin sanyi, hannu yasa ya karbi passport dinsa ya juya dabaya yafara tafiya "Jalal ya haka lokaci fa inazaka jene" Jeje ya tambayeshi Bebashi amsa ba yacigaba da tafiya da gudu Jeje ya taho ya sha gabansa "Man wai meyafaru ne ? Ina zakaje yanzu fa jirginmu ze ta shi"   "Zaka iya tafiya nikam na fasa" Zaro ido Jeje yayi "why meyasa zaka fasa" "Saboda haka naga dama nace in zaka ka tafi ni na fasa" Ya bashi amsa JALAL yayi maganar a tsawace Wayarsa ya dakko ya kira Jawwad, amma be daga ba taita ringing Jawwad yana kallon kiran yaki ya amsa seda takusa katsewa sannan ya daga wayar "Kazo ka daukeni a airport" "Kamar ya?" Jawwad ya tambayeshi "Ina airport nafasa tafiyar kazo ka daukeni" "Bazan zo ba dacan ni na kaika" "Idan bakazoba zan tafi u know I mean what I said" "Ohh sorry gani nan zuwa" Wai dagaske ya fasa tafiyar Jawwad ya tambayi kansa da sauri ya mike ya dau mota ya nufi airport Ummice take lazimi akan dadduma gidan shiru kaman ba me rai a cikinsa Jalila tana can dakinta tana duniyar tunani Ummi ce ta dinga kiranta takirata ya kai sau uku sannan taji ta amsa "Jalila zonan" "To Ummi gani nan zuwa" Mikewa tayi ta nufi dakin Ummi taje gabanta ta zauna "Ummi gani" "Naganki ai, Jalila wai meyake damunkine kwata² yan kwanakin nan kaman baki da lafiya baki da walwala Sam Meyake damunkune baki da Wanda zaki gayawa matsalar ki fiye dani baki da aiki se tunani My dear tell me what's actually wrong with you bana jin dadin ganinki a haka" Tausayin ummine yakamata taji kaman ta gayamata gaskiya amma seta fasa "Ummina babu abunda yake damuna kawai surutan danake da daddare ne da mafarkai bana so" "Eyyah sorry my dear kinji tunani baze hana faruwar komai ba addu'a zaki dingayi nima inayimiki Komene Allah zemiki maganinsa" Haknan se Jalila taji hankalinta ya Dan kwanta Zame jikinta tayi a hankali ta kwanta akan cinyar ummi Tanata ambaton Allah a zuciyarta domin tasamu zuciyarta ta rage bugun da take Ba a dau dogon lokaci ba Jawwad ya karasa airport Jalal ya hango a zaune jeje yanata lallaba shi "Tir da wannan dan iskan bawan, mtseeww" Jawwad yafada a hankali Jalal yana hango Jawwad ya mike "Dan uwa dagaske ka fasa tafiya" "Nafasa Jawwad kona tafi bazan samu nutsuwa ba zuciyarta tana Nigeria tare da Dan uwana" Rungume juna sukayi kaman zasu shige jikin juna Wani mugun kallo Jeje yayiwa Jawwad "Wai dagaske fasawar zakayi?" Jeje ya tambayeshi a fusace "Jeje nafasa tafiya bazan juri ganin kwalla da bacin rai a idon Jawwad kamar yadda nafada maka kona tafi dubai zuciyata tana Nigeria" Jawwad ne yaja trolley Jalal yasaka a boot, ya bude masa motar ya shiga Jeje ne ya zagayo gaban Jawwad yai masa magana kasa² "Yadda ka bakantamin yau ka rubuta ka ajiye komai Daren dadewa se na bakanta maka fiye da yadda kayimin" "Allah ya fika" Shine amsar da Jawwad ya bashi Ya shiga ya kunna mortar suka tafi Jeje kaman yayi hauka gaba daya shirunsu ya rushe shi beasan meze gayawa boss dinsa ba Naushi ya kai cikin iska kamar mahaukaci "Fuck you Jawwad, indai muna raye sena kuntata maka kamar yadda kayimin " A hankali wani bacci me dadi ya dauke Jalila akan cinyar Ummi se ajiyar zuciya take kaman wadda ta wuni tana kuka A hankali Ummi ta shafa kanta Allah yayi miki maganin abunda yake damunki baby na Duk da yamma tayi Ummi bata tashe ta ba ta kyaleta saboda in tayi wannan farkawar cikin dare bata komawa bacci Se gefin magariba Jalila ta farka tana farkawa da bugun zuciyar nan ta farka "Ya salam" ta fada a hankali "To dagani tunda kin tashi" "Ummi ki Dan kyaleni mana in gama hutawa ni dama xaki goyani" Ture kanta Ummi tayi ta mike ta tafi dauro alwala A hankali taji bugun zuciyarta tana komawa normal Ringing din wayarta ta jiyo a dakin ta da sauri ta mike ta tafi ta daga wayar lambar siyama CE "Aminiya ya ake ciki kuwa ?" "Oho" "Kaman ya oho ya tafin ne? Kinkuma tambayar Yaya Jawwad?" "Aminiya mezan tambayeshi ne ?ya rigada yacemin ya tafi se dai kuma addu'a kawai" " banji dadi ba aminiya Allah ya kiyaye ya tsare se mucigaba da addu'a amma ina ji a jikina kaman betafi ba" "Tab wannan uban taurin kan to Allah yasa amma tunda ya furta seya tafi" "Insha Allah be tafiba gobe in Allah ya kaimu ki shirya da wuri mutafi islamiyya karki jamana dukan makara" "Insha Allah aminiya" "Wani irin sha³ ne kai jeje why do you failed this mission, after all u know na Dora burina akan wannan tafiyar dazukuyi meyasa?' a wannan tafiyar naso dawwamar da bakin ciki a zukatan ahalinsa na har abada"? Mutumin dazune da ya kai jeje airport a motarsa yake maganar cikin fada "Am sorry sir amma ba laifina bane wannan abokinnasa ne ya hana shi" "Wa kenan" Mutumin ya fada cikin fada "Wannan mayen nasa Jawwad, saboda shi ya fasa tafiyar" "Jawwad ko? Yayi kyau zan tabbatar masa da ba a shiga hanyata semun bar masa mummunan tabo a cikin zuciyarsa Wanda har gaban abada baze goge ba, dama shine yakemana karan katsaye a al'amuranmu zamuyi maganinsa" "Hakan shine mafita ayi maganinsa kawai" Jeje yayi maganar da sauri Har cikin Gida Jawwad Yakama hannun Jalal yashiga dashi yan gidan duk suna parlour ILHAM.tana zaune  tayi shiru tana tunani Yayinda mummy keta rusa kuka daddy yana rarrashinta Jawwad ne yayi sallama gaba daya suka daga kai domin amsa sallamar Kawai sesuka ga Jawwad tare da Jalal Jawwad ya janyo hannunsa zuwa cikin palour "Gashi nan ya fasa tafiyar hankalinku ya kwanta, mummy kukan ya isa gashi ya dawo" Jawwad ya fada yana kallon mummy To Alhamdilillah nima ba a son raina ya tafi ba, ba yadda zanyi ne tunda ya dawo se muyiwa Allah godiya Ita kam Ilham bakinta ne yaki rufuwa Mummy da gudu ta mike taje ta rungume Jalal tana cigaba da kuka hada sheshsheka Kunsan d'a da uwa karo na farko bayan lalacewar Jalal da yaji kukanta ba dadi a zuciyarsa "Kukan ya isa ai tunda gani na dawo Ki godewa Allah ki godewa Jawwad Bazan iya tafiya in barshi da kewata ba" Jalal yai maganr yana kallon Jawwad Mummy kasa magana tayi se daddy da yake kokarin godewa Jawwad "Haba daddy kar kasa inji kunya mana bakomai " Nima Jalila ce takara fargar dani abu me mahimmanci Dana kusa mantawa thank you sweetheart Yayi maganar a zuciyarsa Sannan ya mike yai musu sallama ya tafi Gida yana zuwa ya dau wayarsa Layin Jalila ya kira domin ya gaya mata Jalal ya fasa tafiyar amma bata dauka ba ILHAM tana Shiga daki tayi wani tsalle tare da jefa hannunta sama tace yes key tasaka wa kofar dakin ta sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira layin mahaifiyarta "Hello Mami" "Na'am ya ake cikine?" "Albishirinki" "Goro" "Yafasa tafiyar nan dazu Jawwad ya kawo shi Gida yafasa" "Ke dan Allah dagaske koda wasa" "Wallahi mami ya dawo" "Kai amma Jawwad din nan ya kyauta, ya saukaka mana aiki" "Wallahi kuwa mami" "To yanxu dai ba sanya zamuyi ba, ki kara dagewa Ilham duk randa burinmu ya cika sekin fini amfana" "Insha Allah mami zan dage" "Yawwa yarinyar kirki se na jiki" "To mami ki gaida mutan gidan" "Yawwa zasuji" "Jalila kinga gidan Maman annur ta haihu ban samu na shiga naga babynba zo muje, Muyi mata barka" "Ummi wai ita barkan nan dole ce tunda dai bata mutu ba da ranta" "Ohh ni maryam Jalila mutum ya dau ciki wata Tara ya sauke lafiya tsakanin mutuwa da rayuwa ai aje acemasa barka" "Ummi naje gobe in Allah ya kaimu yanzu bana jin dadin jikina" "To Allah ya sawwake miki zo ki rufe kofar gidan" Jalila tabi Ummi ta rufe gidan sannan dawo cikin Gida ta dakko wayarta ta dawo palour ta Missed call din Jawwad ta gani "Yasalam yaushe Yaya Jawwad ya kirani ban Sani ba" Kiransa tayi ya katse kiran sannan ya kirata "Abunda zan gaya miki ya Riga ya wuceki tunda baki daga wayar ba, se yanzu" Cike da shagwaba Jalila ta fara magana "Haba yayana na kaina bangani ba ne se yanzu amma tuba nake ranka ya Dade" Murmushi yayi "Sisyna ta wa ni kadai" "Nanan fa?" "A'a banda ita" "Sena gaya mata" Dariya sukayi gaba daya "Yayana me yasaka farinciki hakane labarta min" "Kece Jalila" "Nikuma" "Eh mana" "Ya akayi nasaka farincki" "Saboda kin tunatar dani abu me mahimmanci Jalal wani abokinsa ne ya zigashi yayi tafiyar nan Wanda ni da Sam banyi tunanin hakan ba kuma nasan da wata manufar ya zigashi, kuma wai tare zasu tafi Yanzu dai zancen danake miki Jalal yana Gida yafasa tafiyar ya dawo" Wata nannauyar ajiyar zuciya Jalila tayi "Alhamdilillah am glad to hear this from you Allah yakara kiyayewa ya shiryeshi" "Ameen sisyna muna godiya da gudunmuwarki Allah yasaka da mafificin Alkhairi ya jikan Abeenmu" "Ameen dan uwan da babu irinsa" "Ki gaida ummina" "Zataji insha Allah na gaida maama," Sukayi sallamaa Jalila tace Alhamdilillah Siyama ta kira ta labarta mata sukayi ta murna tare bakin Jalila yaki rufuwa Bayan Ummi ta dawo ne ta lura da farin cikin da Jalila take sewani walwala take "Waime ya farune naga kinata wannan farincikin haka baby gayamin mana" Dariya Jalila tayi "Hajiya Ummi ba komai kawai tsintar kaina  nayi cikin farin ciki Mara misaltuwa" "To Allah yasa alkhairine" "Ameen ummina" Haka Jalila tayi kwanan farin ciki Allah ya temaketa yau batayi mafarkan ba balle a tsorata ta Lokacin tafiya islamiyya yayi yan matan sun dau guga a cikin dogayen hijjaban makaranta suna tafe suna hira yau fuskar Jalila fes ba wata damuwa Dan haka yau ajinsu suka tabbatar ta dawo banda hira da surutu ba abinda sukeyi ana hirar yaushe gamo wasu na mata tambayar meyasa randa tazo bata walwala kwanakin nan sunyi missing dinta Hayaniyar ce ta ishi malam Naziru ya fito Dan ya tsawatar musu Yana zuwa Jalila yayiwa kashedi "Yau malam baya nan balle ya ceceki wallahi naji surutu a ajin nan babu ruwana ke zan zanewa jikinki" Befi yan mintuna da tafiya ba Jalila tabasu sabon topic suka barke da hira hada shewa itakuma ta silale ta gudu ta bar ajin ta nufi babban aji Malam Naxeeru ne yakuma komawa domin casa yan ajin kuma ya kudiri takan Jalila ze fara Yana zuwa ajin ya nemeta yarasa ya tambayi tana ina sukace basu saniba aikuwa suka sha jibga yayinda uwar gayya ta fece sun daku ragwaye na kuka, yayinda masu karfin hali kena zuci Dan malam Naziru ya iya bulala, "Tsinanniyar yarinya ta jamana duka ta gudu shegiya azzaluma wallahi ban yafe ba" Cewar wata daliba aikuwa a fusace siyama ta juyo "Allah ya isanki ta biki haba lubabatu ai ba matsa bakinki tayi tace kiyi magana ba kuma Jalila ba shegiya bace" "Nafada wallahi ban yafe ba" Lubabatu ta maimaita "Ke nima ba yafewar nayi ba wallahi wannan azabar dukaa itakuma ta gudu" Wata dalibar tayi magana Siyama na kokarin tarewa Jalila wasu suka hayayyako mata ana haka Sega Jalila ta dawo gaba daya sukayi tsit saboda sunsan hali indai bakine Jalila akwai baki Ba'a kada ita a fanni surutu "Yanaji ana surutu amma ina shigowa naji anyi tsit" "Aminiya ba komai hira kawai mukeyi, Amma fa malam Naziru yace yau in yakamaki kashinkj ya bushe" Siyama ta fada tana dariya "Hh base ya ganni ba ai bazan bari mu haduba indai yaune" Ilham ce ta sha kwalliya kaman ka saceta ka gudu se karairaya take ta shirya abinci a Warmer's ta nufi part din Jalal ba kowa a parlour dan haka ta aje a parlour ta karasa bedroom dinsa Dogon wando ne ajikinsa se vest ya na gefen gadonsa yana ta busa shisha Sallama tayi da mamakinta taji ya amsa, a hankali ta tako gabansa cikin iyayi tafara magana "Yaya dama mummy ce tayi girki tace in kawo maka" "Ina abincin"? Yai maganar kaman ba yaso "Yana parlour" Gyada kai yayi "Thank you" "Amma zakaci ko?" "Maybe" Shine kawai abinda yace seda ta juya zata tafi ya daga kai ya kalleta Ganinta yayi kamar wata balbela, gashi se wani kariraya takeyi sam bata da wani shape se tsawo amma fara ce tas Murmushi yayi a ransa yarinya Karama amma ta iya wannan shirmen ya Dan ja tsaki Itakam fita tayi tana addu'ar Allah yasa yaci abincin nan Kamar yadda Jalila tafada har aka tashi bata hadu da malam Naziru ba sunyo ayari guda yan ajin su daba yan ajinsu ba kowa na kokarin bin hanyar gidansu, Anzo layinsu lubabatu suka tarar da yayan lubabatu a bakin hanya da abokansa se shan sigari suke ga tarin karnuka a gabansu kaida kagansu kaga yan daba Jalila tare suke tafiya da su lubabatu seda sukazo dai² inda matasan nan suke Jalila secewa tayi "Tab Siyama kinsan wani abu ga irinsu Jalal da gayyar abokanan Sa baki kullum cikin hayaki, kalli yadda bakin yayan lubaba yayi saboda zukar taba lebensa duk ya zazzage, Ni bansan ya akayi bakin Jalal bezama haka ba wai shantu" Wata ashar yayan lubaba yasaki yayo kan su shida abokanansa tareda karnukan kankace meye wannan ayarin yan makaranta sun watse ba kowa a hanyar Jalila ta dinga dariya yan mata manya da kanana sun zage sun kwashi gudu Sukace gaskiya gobe insha Allah se mun kai karar yarinyar nan gurin malam aja mata kunne "Jalila lafiya kike ta haki haka ?" "Bakomai Ummi karnukan bakin anguwane suka biyomu" Jalal ya bude Warmer's dinda Ilham ta kawo yaga cous² tsaki ya ja lallai ma yarinyar nan tasan bayacin wannan abun amma shine aka kawo masa rufewa yayi ya tafi gidansu Jawwad Dan samun abinda zeci a can Ya tarar Jawwad yatafi masallaci dan haka ya nemi guri ya zauna yana jiran dawowarsa Wayar Jawwad ce ta dinga ringing ta cikawa Jalal kunne Dan haka yaje ya dauka da nufin fadawa me kiran me wayar baya nan Ya daga wayar yasaka a kunnensa "Hello yayana " Shiru yayi be amsa ba "Yaya Jawwad yanaji kayi shiru bakajine?" "Bashi bane" Ya bata amsa a takaice "Au Ashe Kaine ya akayi kafasa tafiyar, Kacigaba da rashin ji kana biyewa abokan banza wataran se sun jaka inda zasu kasheka" Share please More comments more typing........ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  18 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- "Da kasake ka tafi da yanzu ka gane illar hawayen iyaye" "Kinmanta kashedin danayi miki game dani ko? Har yanzu baki fasa min shishigi ba ki ji da rayuwarki, ba ruwanki da rayuwata" Ya katse wayar ya aje tare da fadin "Jarababbiya kawai, ko ina ruwanta dani oho, zan sauke mata wannan taurin kan" Jawwad ne ya dawo ya tarar dashi "Yunwa fa nakeji, find something for me to eat" "Kamar me kake so" "Komeye ma amma banda tuwo Yarinyar nan ta kaimin abinci nazata wani abun kirkin ne ashe wannan abinne dabana ci saboda tsabar ta rainani aikuwa zan koyamata hankali" "Ai kai abunda baka ci dayawa wanne daga ciki" "Kaga ni abar wannan maganar me kukayi yau" "Nima banci abincin ba alala sukayi yau" "What alala kuma," Ya Dan girgiza kai "Kasan itama bana ci" "Anyway bari in canza kaya muje restaurant se muci" "Kar ka kaini inda za abani abunda za bata min ciki kasan bana son jagwal gwalo" Murmushi Jawwad yayi "Jalal kaima yakamata ka canza kayan nan kasaka manyan kaya" "Nifa bana son wannan kayan nauyin isa ta suke da zafi" "Please dan Allah kasa manyan kaya" Jawwad ya fada yana Ciro masa wata hadaddiyar Shadda coffee colour yaita lallaba shi har ya yadda ya karba ya canza kayan yasaka shaddar nan, Ba karamin kyau Jalal yayi a cikin kayan nan ba manyan kaya ba karamin fito da kamalar namiji yake ba Jawwad yaita koda shi, yana masa hotuna yana yaba masa yayi kyau, Haka suka shirya suka tafi restaurant cin abinci Jalila ce a office din malamai ta inda suka shiga ba ta nan suke fita ba suna mata fada akan rashin ji Saboda ankawo kararta akan jiya ta tsokanowa yan uwanta dalibai yan daba, masu zaginta sunayi irinsu malam Naziru, masuyi mata nasiha sunayi ita dai Jalila shiru tayi batace komai ba  suka gama ta tashi ta koma aji tanata cika tana batsewa   Ba a jima ba malam Naziru ya shigo ajinsu da hanzari yana kiranta "Jalila zancen musabakar nan ne ya taso wadda za ayi a Abuja  sati me zuwa insha Allah" Wani irin mugun kallo Jalila tayi masa tai masa banza   "Jalila da ke nake fa kije ki jadadda hadda abun yazo mana a bazata dukda nasan bani da damuwa akanki" "Ba inda zani kunemi me zuwa karkuje inja muku magana, yaza ayi kamata taje musabaka " Tafada tana hade rai Sekuma ya Dan sha jinin jikinsa "Wai meye hakane Jalila ana magana kina wani zance daban ina miki magana" Mikewa tsaye tayi tare da kara hade rai "Nace fa bazani ba anemi wasu suyi ni bazani ba," Ta dau Jakarta ta bar ajin Office malam Naziru yakoma yana mita "Kajimin ja'irar yarinya nizata cewa bazata je musbaka ba wai anemi me zuwa" Malam Yusuf ne yace "Banga laifinta ba nan kuka sata a gaba da fada bama kai se yanzu kuma bukatarku ta taso kuce tazo tayi muku, irin wannan yaran nasiha ake musu ba zagi ba duk abu suna da irin baiwarsu" "Hmm ni ba wannan ba tunanin mafita nake kasan ta da taurin kai abune me wahala taja ga malam baya nan" Jawwad ne ya tashi ya tafi amsa waya yayinda Jalal ya dukufa yana cin abinci saboda yunwar dayake Ji "Masha Allah" Wata budurwa ta fada, mikewa tayi daga inda take tazo kujerar gaban Jalal ta janyo ta zauna "Sannu dai barka da wannan lokacin" Dan dagowa yayi ya kalleta, ya maida kai ya cigaba da cin abincinsa "Ehmm nace ba Dan Allah magana nakeso muyi da kai" Still shiru yayi mata yaki magana haka tacigaba da surutun ta ko kallonta yakiyi Jawwad ne ya dawo yasamu guri ya zauna "Sannunku da fatan ban takura muku ba" Jawwad yafada yana murmushi "Mtseww kaga ci abunda zakaci mutashi mu tafi ni nagama kasan bana son kallo" Jalal yayi maganar a fusace "Dama yana magana?" Budurwar ta tambaya Dariya Jawwad yayi "yanayi mana, gashi kuwa kinji" "Amma nayi masa magana ya shareni" Se Jawwad yai niyyar tsokanar Jalal "Au be kulaki ba, aikuwa yana magana, haba bros ya zata na maka magana ka shareta" Wani takaici ne ya tokare wa Jalal shi Sam baya San sabga da mata dan haka banza yai musu "Au bazakayi maganar ba kuwa" "Inaga nidin ce baze kulaba, ba komai nagode" Ta mike zata tafi "Kiyi hakuri fa Dan uwan nawane se a hankali" Murmushi tayiwa Jawwad sannan ta mike ta bar gurin Wani uban tsaki Jalal yayi yana hararar Jawwad Sunkuyar da kai Jawwad yayi yana dariya Jalal ji yayi kamar ya naushi Jawwad Haka Jawwad yagama cin abincin suka nufi Gida Tunda Jalila ta koma gida sedata shafe kwana uku bata zuwa makaranta Ummi tayi² tagaya mata meyasa bata zuwa makaranta amma taki, kullum seta ce mata bata da lafiya, Seda malam Naziru da wasu malamai suka biyo Jalila har Gida akan takoma makaranta saboda batun musabaka Ummi tace musu ba komai indai Jalila ce zataje musabakar insha Allah sukayi mata godiya suka tafi Ta dawo Gida taitama Jalila fada meyasa zatace bazatayi musabaka ba har malamanta su biyota Gida suna lallabaki Dan tsuke fuska Jalila tayi "Ummi bakiga abunda sukayimin ba suka dinga min masifa kuma se yanzu yawani zo wai inje musabaka wallahi Dan kinsa bakine kuma Dan malam babba zani wallahi da bazanje ba" "To yanzun ma kice bazakiba mana in dai za a biyewa halinki ai kullum se an zanekima ba fada ba" Kayan da Jawwad yabashi yasaka ne duk suka isheshi da zafi Dan haka suna dawowa gidan su ya wuce domin ya canza wasu kayan zuwa kananan kayan daya saba sawa Yana bedroom dinsa yana kokarin canza kaya yaji motsin Ilham a palour zata kwashe Warmer's din data kawo masa abinci, bubbudewa tayi taga baici ba Fitowa parlour yayi ya tsaya a bakin kofa Dan dago kai tayi ta kalleshi masha Allah wani irin kyau taga yayi me daukar hankali kayan sun masa kyau sosai ta Dan kura masa ido "Ke me ye haka uban me kike kallo, saboda tsabar kin rainamin hankali kika kawomin wannan abincin, kuma kinsan banacin wannan abun amma kika dakko kika kawomin yaushe nafara wasa dake dazaki min wannan rashin mutuncin" Yasalam ta manta baya cin cous² "Am...am wallahi Yaya namanta....." "Shut up kwashe su kibarmin daki sokuwa kawai komai kin manta shiyasa kike dakikiya both islamiyya da boko kanki Sam baya Ja fita ni" Ai garani ina zuwa kaifa Ta fada a zuciyarta ta kwashe kayan tana zumbura baki tana kunkuni "Ke ni kikewa kunkuni na tattakaki wallahi kinsan halina sha³ kawai" Sum² ta bar dakin "Indai zaka biyewa mata se Jininka ya hau" Yai maganar a fili tare da yin tsaki Jalila ta dage da tilawar haddarta malam Naziru se kuma lallaba Jalila yake saboda yana son taje musu musabaka Abuja Kullum dare se tayi waya da Jawwad se suyi kwanaki basuyi waya da Nana a wayaba, amma kullum suna manne da Jawwad a waya Yauma yana dakin Jalal suna hira Jalila ta kira waya in suna wayar nan Jalal bata masa rai sukeyi  Jawwad kuma yaita biye mata "Yayana saura kwana uku insha Allah zamuje Abuja musabaka" "Masha Allah, badaban inada lectures ba ranar dase nazo garin Abuja naga yadda kanawata zatayi musabaka in bata kwarin gwiwa" "Koba ka nan kalamanka zasu bani karfin gwiwa, kasani a addu'arka Dan Allah"   "Addu'a kullum cikin yimiki nake Insha Allah zakiyi nasara" "Godiya nake yayana ka gaida mutan gidan" "Zasuji insha Allah, muna tare da yayanki Jalal zan gaya masa shima ya yi miki aduu'a" Jalila dariya ta kwashe da ita tare da kashe wayar "Jalal kanwarka zataje musabaka Abuja ranar Juma a insha Allah kasata a addu 'a" Jawwad yafada yana kallonsa   "Kanwarka dai kasan ni bana kalen dangi" "Kanwa tawace kalen dangi Jalal? kaima kanwarka ce Jalila ce fa" Shiru Jalal yai be kuma cewa komai ba Dama wannan yarinyar har wani karatu ta iya zata je musabaka kil ma karya take dama dai Neman magana ne ko Shiga abunda ba ruwanta ne yai maganar a zuciyar sa Yarinyar dasuka hadu dasu Jalal a restaurant ce zaune akan gado Jeje na gabanta a tsaye yana rarrashinta "Gaskiya Jeje ni bazan iya ba gaskiya zeyi taurin kai ko kallona fa be yiba har na gama surutuna na tashi be kulani ba se abokinsa ne yamin magana"   Tai maganar tana yatsina fuska Jeje ne ya Dan gyara tsayuwarsa "Hanna kiyi hakuri, dama tun farko seda nagaya miki, mugun Dan wulakancine baya saurarar mata Sam amma kicigaba da bibiyarsa kidage Hanna zaki iya"   "Amma dai kasan bana son wulakanci ko nida maza ke min layi, amma ace ana wulakantani Dan ma dai ya hadune gayen da bazanyi aikin nan ba" "Kiyi hakuri Hanna seda na duba naga babu me iya min wannan aikin se ke, Hanna ki dage tunda naga gayen yayi miki" "Anyway I will try my best ka barni dashi da Hanna yake zancen zan sauke masa wannan taurin kan bani lambarsa" "That's good Hannah shiyasa nake ji dake" Jeje yafada yana jin jinamata Jalila ce tayi sallama da Ummi Ummi tayimata nasiha da fatan samun nasara Haka taje islamiyya sukayi sallama da kawayenta da sauran malaman daba dasu za a tafi ba sunata musu fatan alkhairi da fatan samun nasara Daga nan suka kama hanyar Abuja da sauran dalibai dazasu tafi tare, Sun sauka lafiya aka basu masauki su huta da la'asar guri ya cika da manyan mutane daga gurare daban² aka fara gudanar da musabaka Ilham suna parlour da mummy suna hira, mamanta tayi mata waya ta mike tace wa mummy tana zuwa Daki ta nufa taje ta daga wayar "Hello Mami ina wuni" "Ke bar batun gaisuwar nan Ya akayi yaci abincin" "Ina fa yaci abincin na kai masa kaman zeci namanta bayacin cous² da ba shi na girka ba da tuni yaci" "Ke ni yimin shiru tunda beci ba, kina wani shirmen kika dafa abinda baya ci Yanzu yana ina" "Yana part dinsa mana" "To ke kina me ki tashi ki bar abinda kikeyi kije ki tayashi hira mana" "Maami dan baki san halinsa bane mugun Dan rainin hankaline" "Kiyi hakuri Ilham, ribarki CE fa da kin aureshi burinmu yacika zan dau fansar abinda uwarsa tayimin, a wuce gurin, in kina yawan zama a inda yake dahaka zaku shaku, in Allah ya kaimiu weekends kizo akwai turaren Dana karbo miki sannan yanzuma ki shafa wancan turaren Dana baki malam yacemin yayi aiki sosai a cikin turaren" "To maami bari inje " "Yawwa Ilham koke fa" Mikewa ILHAM tayi tafara shiryawa tasaka wata doguwar Riga Ja me kama Jiki, ta shafa turare ta Dan Dora siririn mayafi akanta ta fito parlour bakowa a palour mummy ta tashi, Dan haka ta fito ta nufi part din Jalal Yana kwance da gashi se dogon wando da vest ya kwanta ya lumshe Ido jinsa yake jikinsa Sam ba kwari kaman anyi masa duka Ilham ce ta shigo parlour ta sameshi a kwance akan three seater yanajin shigowarta amma be motsaba kan kujerar dayake taje ta zauna daga karshen kafafuwansa ji yayi jikinsa ya kuma mutuwa A hankali ta kai hannu ta dan matsa yatsunsa na kafa taji yayi shiru bece mata komai ba Dan haka ta cigaba da matsa yatsun kafarsa a hankali "ILHAM" Taji ya kira sunanta a hankali "Na'am Yaya Jalal" Ta amsa masa "Wane irin turare ne wannan kikasa?" "Me turaren yayi?" Ta tambayeshi "Ji nayi ya kashemin Jiki, kamar ya karamin ciwon kai" Abun yabata mamaki dataga be hantareta bako ya koreta Kashe murya tayi cikin shagwaba da iyayi ta fara magana   "Haba Yaya Jalal turaren da kasanni dashine fa" Mikewa yai zaune tare da fadin "No ILHAM this one smells different" Kusa dashi ta matsa ta kwanta akan kafadarsa "Kaine dai kaji haka amma ni ban canza perfume ba" Dan tureta yayi kadan ya Dan kalleta " dakkomin Wayne a fridge ki hadon da cup" "OK angama my J" Ta mike tanata karairaya, tare da mamakin wannan sakin Jiki da Jalal yai da ita haka Shikam da ido yabita yanajin kaman ba shiba Wayne din takawo masa ta bude ta zuba a cup ta mika masa ya Sa hannu ya karba itakuma ta dawo kusa dashi ta kwanta a jikinsa Hannu ya mika ya dakko remote ya kunna Tv Yana kunnawa yaci karo da fuskar Jalila Tana murmushi tasha hijjabi blue ga farin glass tasaka ga sufiku a gabanta na karatu gani yayi kamar shitake kallo Gabansa ne yafadi yaji tsigar Jikinsa ta tashi Share please More comments more typing................. Ina alfahari daku masoya wannan novel Irinsu Jamila Zakiyyat Ummu hanif Mabruka Zainab Da wannan tsofaffin Fatima zahras Da duk members Na ABDUL JALAL NOVEL FANS Wanda na fada da Wanda ban fada ba nasan daku ina alfahari daku 🌹🌹🌹🌹🌹 [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  19 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- Malamai ne suka jeru suna shirin janyowa Jalila inda zata karanta Itakam tayi shiru ta kurawa camera ido haka nan taji gabanta na faduwa dukda tasaba zuwa musabuka amma takejinta wani iri Jalal ne ya kurawa TV ido gani yake kaman shi Jalila take kallo so yake ya tabbatar itace kuwa a jikin allon TV kokuwa kamrun dayasha ce tafara gaya masa karya(giya) Ita kam Ilham kara shige masa take tana kuma zuba masa Wayne tana mika masa "Ilham ki kyaleni please" "Yaya J why?" Tayi maganar tana kuma kwanciya a jikinsa Shikam yakoma kaman wani karamin yaro "Bana so Ilham ki kyaleni kwanciya zanyi kaina ciwo yake" Dan dagashi tayi ya koma ya kwanta akan kujerar yana kallon TV kasa² A hankali Ilaham ta mika hannunta tana shafa sajensa "Sannu Yaya J" Gyada mata kai yayi "Ilham karki kuma saka turaren nan inzakizo inda nake banaso" Yai maganar a hankali "To na dena" Tv ya kuma kalla Jalilan ce dai sedai wannan karon annurin fuskarta ya gushe ta dai²ta nutsuwarta aka janyomata inda zata biya A hankali tayi bismillah tafara karanto Qur'ani cikin sauti me dadi Ture Ilham yayi daga Jikinsa ya lumshe idonsa jin sautin karatun nata yake yana ratsa ko ina na jikinsa yana saukar masa da nutsuwa Ji yayi kasalar tana sakinsa duk yayinda ya bude Ido seyaga kaman Jalila shi take kallo jinsa yake kaman ba Shiva Ilham hannu ta kuma mikawa zata taba shi ya daka mata tsawa "Ke wace irin banzar yarinya ce waima tukuna me kikemin anan gurin ne tashi kibar min daki kafin in zaneki banza kawai" "Haba Yaya amma " bazaki fitan ba kenan kalli Tv duk rawar kanta kalli yadda take karatun Qur'ani gwanin burgewa keko sha³ baki iya komaiba se hauka get out from my room" Idonta ta kai duba kan Tv Jalila tagani tana zuba kira'a kaman ba itace me shegen surutu da Neman magana ba, wani abu taji yazo ya tokaremata zuciya wato tun dazu da ya kurawa Tv ido ita yake kallo kenan Wani mugun kallo taimasa "To ai gara ni inazuwa Islamiyyar kai........... Bata rufe bakiba yasaka kafafuwansa ya take nata kafar wani irin ihu tayi da karfi kuma yaki dagawa " Dan girman Allah kayi hakuri, wallahi bazan kuma ba" Kara takesu yayi "Dan ina daga miki kafa ina nan a Jalal dina da kikasani, yanzuma Sa a kikaci da wallahi sena zaneki da belt, tashi kifita wawiya kalli rigar jikinki sokuwa kawai" Da kyar taja kafa ta fita kafarta se zugi takeyi ta koma dakinta ta hau gado ta kama kuka Wani uban tsaki ya ja yanemi guri ya zauna Tashar da suke haska musabakar su Jalika sun tafi talla dan haka ya dauki cup din giyarsa ya cigaba da sha yakuma zubawa ze sha aka kuma hasko Jalila haka nan se ya aje giyar hannunsa shima ya kuramata ido, yanayin Jalila ne ya nuna kaman bata da nutsuwa Aka kuma janyomata karatu amma tayi shiru ta tafi tunani kowa ita yake kallo Jikinta ne yayi sanyi jitake kaman wani abune ke shirin faruwa, mafarkanta datakeyi yan kwanakin nan ne suke fado mata a rai taji gabanta yacigaba da faduwa. a hankali tayi ajiyar zuciya ta Dora inda aka janyomata da karatun ta cikin birgewa Bacci ne yafara fusgar Jalal dan haka anan gurin ya zube ya lumshe ido yana sauraren karatun Jalila har bacci yayi awon gaba da shi Da safe Jawwad ne yazo ya tarar dashi yana bacci a parlour a kasa kan carpet ga kwalbar giyarsa yasha fiye da rabi Girgiza kai Jawwad yayi "Allah ya shiryeka Jalal" Yasa hannu ya kwashe kwalbar da kofin ya fita dasu ya dawo ya tashi Jalal don yasan be salla ba balle ya karya Hannu ya kai ze tasheshi yaji kansa yayi zafi, bayansa ya Dan bubbuga a hankali Jalal ya bude ido ya mayar ya lumshe "Ka tashifa gari yayi haske kayi salla kazo mu karya" Jalal ne yake tunano abubuwan dasuka faru jiya da daddare gaskene kokuma mafarki yayi ji yai kansa yakuma sarawa "Kaina ne yakemin ciwo sosai Jawwad" "Sannu ka tashi in muka karya seka sha magani" Da kyar ya lallabashi yaje yayi wanka yai sallar asuba, Jawwad ya dakko musu Abinci Ilham CE ta fito tana taka kafa da kyar mummy ta kalleta "Meyasameki kike taka kafa da kyar" "Dutse na taka jiya a garden" "Subhanallah bakiji ciwo ba dai ko?" "A a banjiba kafar ce dai kawai take ciwo" "To ko asibiti za a kaiki a duba kafar" "A'a mummy zata dena ne Insha Allah" "To shikenan ni zan fita ne zanje ganin likitan Ido, ga breakfast can na gama in wancan Dan zeci yazo ya dauka kema kije ki dau naki" "To mummy adawo lafiya" "Allah yasa" Mummy ta fita Jalal ne ya dakko wayarsa ze kira daddy yaga message ya shigo wayarsa Dan haka ya bude message din bakuwar lambs ce       "Barka da safiya jarumin              maza fatan kana lafiya               Zanso ace a halin yanzu        Muna tare ina kallon                  wanna kyakykyawar fuskar       Amma lokaci na nan zuwa        Dazamu kasance tare kaji          Dadinka masoyina              From ur lovely bae" Wani uban tsaki Jalal yayi "Nasan Ilham ce zataci kaniyarta zata gane innin sa,'anta ne" "Ya dai meyafaru ne kake surutai haka"? Jawwad ya tambaheshi "ba komai ci abincinka kawai" Ya mike ya nufi cikin Gida tundaga parlour yake kiran sunan Ilham amma bata nan dakinta ya nufa yana zuwa ya tarar tana dakinta tana karyawa A firgice ta dago tana kallonsa "Uban meye wannan kika turomin a waya wai meyasa ba kyajine Ilham" Kallonsa tayi cikin rashin fahimta "Wane sako kuma ni ban turomaka komai ba" Ransa ne ya kuma baci wato raina masa hankali zatayi gadan² ya nufi inda take da niyyar ya ci kaniyarta Ta mike tsaye tafara kuka tana "Wallahi Yaya bansan laifin danayiba" Yana karasowa Inda take yaji tana warin wannan turaren na jiya kansa ne ya Sara yaji yana Neman ya fadi, da sauri ta taho inda yake "Yaya menene?" "Dalla tsaya karki karaso inda nake" Bango ya daddafa yabi kofa ya fice da kyar ya koma part dinsa Jawwad ne ya ganshi ya rike kai yana dafa bango "Subhanallah Jalal kanne dai" Jawwad yafada yana riko JALAL "Jawwad kaina kaman ze fashe" "Bari mu tafi asibiti ina key din motarka?" "Kaga kyaleni bazani wani asibiti ba" "Meyasa meye amfanin ka zauna a Gida baka da lafiya" Guri Jalal yanema ya kwanta ji yake duniyar tanata jujjuyawa   Kai tsaye cikin gidan Jawwad ya tafi ya nufi part din daddyn Jalal yasameshi a parlour yana breakfast Suka gaisa Jawwad yagaya masa halin da Jalal yake ciki, tare da daddy suka taho gaba  daya part din Jalal Suka tarar dashi a kwance yanata juyi akan gado ya rike kai Juyin duniya ya tashi su tafi Asibiti yace baza shi ba kunsan mutumin da taurin kai Se wani likita aka kirawo yaimasa allura se yasamu yayi bacci Alhamdilillah Jalila ita tazo na biyu a gasar musabaka da akayi tasamu kyautuka da dama kuma an karrama malamanta Ita Jalila duk ba haka taso ba na daya taso tazo "Duk wannan sakaran ne yajamin haka kawai naita mafarkinsa nazo musabaka ya hanani sukuni" Haka taita mita suka kamo hanyar dawowa Kaduna suna murna amma ita haushi duk ya isheta Har Gida motar makaranta takai Jalila, siyama tana gidan tana Jiran isowar Jalila Ummi tana ganinta ta rungumeta tana murna, amma Jalila tai kicin² da fuska "Lafiya kuwa babyna?" "Ummi ta biyu fa Nazo" Tafada kaman zatayi kuka "Haba baby Wanda yazo na karshe kuma yace me? Daga na daya fa seke haba babyna" "Gaskiya aminiya inkakiyi haka baki kyauta ba kullum zakiyita zuwa na dayan, hakan ma mu munyi murna" "Yawwa ai gara kigayamata siyama, adinga godewa Allah Baby" Ummi tayi maganar tana dungurewa Jalila kai Dan turo Baki JALILA tayi Taje tayi wanka suka kule dakii itada siyama suna hira "Kinsam wani Abu aminiya" JALILA tai maganar tana kallon Siyama "A'a sekin fada" Siyama ta bata amsa "Wallahi Jiya agurin musabaka naji gabana yanata faduwa ina tuna mafarkin nan danake" "Kai Aminiya meye kuma na tunawa ABU ya Riga ya wuce kimanta kawai Bari inbarki ki huta kishirya ranar Monday insha Allah za a koma school" "Can ta matsemusu bazan komaba senagama hutawa ki gaida umma" "Aminiya halinki seke tararki za aci fa in baki koma ran Monday ba" "Hhh tab Tara sedai a ci wasu Tara ba dai niba" Sukai sallama ta Raka Siyama kofar Gida ta dawo dakinta ta kwanta akan katifa domin huce gajiya Mummy ce ta dawo Ilham tagaya mata ai Jalal ba lafiya suka tafi part dinsa, yana kwance akan gadonsa yana bacci jijiyoyin kansa duk sun daga dagani baccin ba dadi yakemasa ba, warin turaren Ilham yakuma shaka dukda bacci yake seda ya yamutsa fuska ya juya wani bangaren A hankali mummy ta kai hannu ta shafa sumarsa tana fadi "Allah yabaka lafiya son" ILHAM ta amsa mata da "Ameen" Se bayan azahar ya farka Jawwad ya shiga cikin gida yace Ilham ta hado tea ta kawowa Jalal, Jawwad ne gefen Jalal yana masa sannu "Ya kakejin jikin naka yanzu"?Jawwad ya tambayi Jalal "nifa har yanzu yanamin ciwo, amma bakaman dazu ba" "To ai kaima ance muje asibiti kaki ka manne a Gida" "Ni ba wani asibiti da zanje" Sakone ya shigo Wayar Jalal, Jawwad ya miko masa wayar          "Barka da wannan lokaci            Lovely am missing ur            Handsome face wish to            See u soon            Love u so much            From ur lovely bae" "Mtseww wannan wace irin jaraba ce" Yana aje wayar tafara ringing an kira yafi sau uku yaki dagawa "Jalal wayarkace fa ke ringing Ka daga mana" "Bazan daga ba in ka gaji da karar kai ka daga" Girgiza kai Jawwad yayi halin JALAL se hakuri Hannu yasa ya daga wayar se yaga unknown number muryar mace yaji "Hello babyna fatan kana lafiya" "Sorry ba me wayar bane, me wayar baya jin dadi amma wa za ace masa" "Eyyah shiyasa naji ni bani da lafiya nima ko abokinsa ne JAWWAD" "Dan uwansa dai" "To amin afuwa Dan uwansa" "Eh nine" "Hannah ce ai masa sannu, ko zaka bani address din inzo in dubashi" "Ohh no daga nan ma kiyi masa addu'a mungode" "Anyway Allah yabashi lafiya amma banajin zan iya komai bayan mallakin zuciyata ba lafiya, Ka gaisheshi please" "Zeji insha Allah" Jawwad ya katse kiran ya kalli Jalal "Mutumin yaushe kafara soyayya ba labari wace kuma Hannah" "Mtsewww soyayyar banza kai kasanta" "Easy mutumina adena cika baki wadda takiraka din nan bakaji kalaman data fada tace agaya maka ba" "Dan Allah ka kyaleni inji da kaina" "Ohh sorry nadena sannu, Yanzu za a kawo maka tea" ILHAM kam wani tunani tayi this is another opportunity for her to use that medicine again Tunda wancan lokacin be Ciba a abinci yanzu tasan zesha a tea da rawar jiki Ilham ta mike taje ta nufi kitchen ta hada tea ta zuba wani maganin a ciki ta juye tea din a flask ta doro cups akan plate ta nufi sashin Jalal A cikin bacci Jalila taji kirjinta ya tsanan ta bugawa Ilham kawai take gani a mafarkinta a hankali ta bude ido gabanta ne yacigaba da faduwa meke Ilham ke shirin yine nake ganinta a bacci na "Laila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" Shine abinda Jalila taita maimaitawa kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta  mike zaune ta dakko wayarta Sallama Ilham tayi tana kokarin shigowa Jalal ne ya Daka mata tsawa "Tsaya a nan malama karki karaso inda nake" "Haba Jalal wai meyasa kai ba a maka gwaninta ne" Saroro Ilham ta tsaya tana kallonsu "Eh naji ba amin gwaninta amma karta shigomin nan" Mikewa Jawwad yayi ya karbo tray din hannunta "Kiyi hakuri ILHAM kinji zedena ne nasan ba kyajin dadin abunda yake miki, nan gaba in ance yayi koda kudi baze miki ba" Gyada masa kai kawai Ilham tayi tabashi tray din kayan tea ta koma Gaban Jalal ya dawo ya zauna "Bross Ilham kanwarka ce yadda kake treating dinta Sam be dace ba" "To mekakeso in mata indinga goyata ko kuma in zauna ina mata dariya a hakanma kana ganin rashin kunyar da takemin har ta kalleni tace ni take so sa'anta ne ni?" "Jalal Ilham itama yarinya ce, kuma so ba karya ne ba bazaka gane hakan ba se ranar da yai maka kamun kazar kuku" "Naji labarin ya isheni haka, hadamin tea in sha" Jawwad na cikin hada masa tea dinne Jalila takira wayar Jawwad Murmushi yayi sannan ya daga wayar "Sisyna am sorry nayi laifi ban kiraki naji yakike ba yau hankalina ne ba a kwance baya musabakar?" Seda ta tura baki kaman tana gabansa "Yaya Jawwad ta biyu fa nazo" "Kai amma nayi murna, dole inzo Kaduna muyi celebrating" "Wani celebrating bafa ta daya Nazo ba wai ta biyu" "To ai kinyi kokari baby meye kuma na bata rai? Aini a hakan ma kinfiyemin Wanda yazo na daya"   "Dan Allah ka aje wayar nan, ko kabani tea din in hada da kaina" Jalal yai maganar a fusace "Ohhh sorry bari in hada maka" Jawwad yai maganar yana kashewa Jalal ido   "Yayana kaida waye ne?" Jalila ta tambaya "Nida yayanki ne bashi da lafiya tun jiya yake fama da ciwon kai an masa allurai amma har yanzu kan bedena ciwo ba, shine zan hada masa tea yakemin masifa" Dan tabe baki Jalila tayi "Dama yana salla ne se ince ko beyi Azkar ba, to Wanda be salla ba ya za a tambayeshi yayi Azkar ma, kasan in mutum ya nisanta kanshi da Allah komai ma seya sameshi" Dan kallon Jalal Jawwad yayi yaga idonsa a lumshe se yayi tunanin ko bayajin me Jalila take fada, amma tsaf yaji me tace "Hmm Adduar ki kawai muke bukata baby" "To Allah ya shirya ya bashi lafiya, ka kama kansa ka karanta mai bismillah kafa sha Tara se ka biya masa ma tayassara minal Qur'an" "Godiya muke ya sayyada, Allah yakara hasken makaranta Brother tashi ka karbi tea din" Yafada yana Dan jijjiga Jalal Tashi zaune Jalal yayi ya karbi tea din ya kai bakinsa ya Dan fara sha "What!! tea naji kace" "Eh tea zan bashi ya sha kinga yana da dumi" "Waye ya hada tea din?" "Ilham ce ta hada masa mana" Jawwad yabata amsa Dan tunani Jalila tayi Meye yasa ta dinga faduwar gaba tun agurin musabaka har yanzu bashi taita ganin Ilham da sauri tace "What Ilaham kuma? Karya sha tea din nan Yaya Jawwad ka karbe tea din nan" Tafada cikin karaji Share please More comments more typing...... Comments dinku yayi kasa zanyi yajin typing 😈😈😈 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  22&23 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- Not Edited Jinine ya wanke mata fuska ta fasa kara yarinyar tayi, itako Jalila ko ajikinta, hakan yayi dadi² da isowar class mastern su Jalila hankalinsa ne ya tashi ganin duk saurin da yayi Jalila ta riga tayi aika² be kara tsurewa ba seda ya tabbatar da wadda aka fasawa goshi salati yayi, Hanan Abdurrasheed Yar gidan babban captain din sojan ruwa da aka kawo ranar litinin ita Jalila ta fasawa kai shi kansa ba yadda beyiba ya canzawa Hanan gurin zama saboda yasan me gurin tafi kashi doyi wato queen J,  amma hanan yarinyar akwai izza da jin kai, tace ita dole nan gurin takeson zama, yanzu yasan ba Jalila ba su Kansu makaranta Ta janyo  musu "Jalila mene haka kika aikata, wannan wane irin shirme ne, yaushe ma kika dawo ne bansaniba memakon kizo kigayamin seki dauki doka a hannu kalli haukan da kikayi" "Niba hauka nayiba daba ta mareni ba inaga da hakan bata faruba" "Shut up zaki gane kuranki ubanta sojane insuka casaki inaga daga yau kindena Neman magana" "Wai da anyi magana se afara maganar babanta sojane, Allah sarki mukuma 'ya'yan Allah bani marasa gata, wallahi ko Yar gidan rocket ce bata isa ta mareni in kyaleta ba" Ya fuskanci babu alamar nadama tareda Jalila Dan ko kadan bata tsorata da abinda tayi ba itakuwa Hanan tuni aka tafi da ita school clinic akaimata dressing daga nan Hanan bata saurari kowa ba ta fice daga makarantar duk yadda akayi a dakatar da Hanan amma tayi waje ta tafi gida Jalila aka kira office din director Aka dinga mata fada kowa da abunda yake fada a cikin malamai wasu abun kirkinta wasu akasin haka ciki hadda wata malama ta zage ta dinga zagin Jalila matar a bayan layinsu Jalila take, Jalila ta taba fada da Yar malamar, Dan haka dama tanajin haushin Jalila "Dama wannan yarinyar ba tarbiyyace da ita ba, bata da mutunci Sam dama ina za a samu wata tarbiyya a gurin Yar mace" Jalila ce ta daga kai da sauri ta kalleta "A'a madam adinga hakuri Jalila yarinyar kirkice, tana da tarbiyya ita dai matsalarta da students ne ga tarin alkhairanta ga makarantar mu dabazamu manta ba" Cewar director "Hmm yallabai baka San yarinyar nan bane uwatta Sam bata son laifinta ita ta sangarta ta lalace, amma yarinya sekace Yar daba, takama Yar mutane ta fitar mata da jini, dama charity begins at home duk abunda yarinya takeyi to haka taga uwatta tanayi" "Sir kaimata magana kartakuma zaganmin uwa duk zaginta ta tsaya kaina takuma zagina sena rama, uwa ba tafi uwa ba" "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Jalila ta daban ce Jalila koma class dinku yanzu" Cewar director ita kuwa Jalila ta mike ta koma ajinsu "Dan Allah kalli yadda take ikrarin zata zageni yarinyar nan kawai a koreta shine mafita" Inji malamar dazu "Korarta ba shine mafita ba yarinya ce me matukar kwazo in muka koreta munyi asara babba" Cewar wani malami "Hakane kam wan mahaifinta abokina ne bazan taba korar masa ya ba, kuma duk fitinarta bantaba ganin tayiba se yau yanzu dai mahifiyarta zamu  gayyota tazo mu zauna da ita dakuma wakilinta Dan na tabbatar, Yar gidan sojan nan se sunzo makarantar nan" "Allah yasa suci kaniyarta sumata dukan tsiya" "Haba madam in "yarkice fa baza kice haka ba ai shi da na kowa ne addu'a yakamata ayi mata Allah ya shirya Allah kalli dai yasan abunda zata zama nan gaba" Inji director Hanan ce ta shiga tangamemen palour tana kuka wata babbar mace ce zata yi shekaru arba'in da takwas amma Hutu yasa in ka ganta seka zata batafi shekaru talatin da biyu ba, gefenta kuma ga wani babban mutum shima yana shan tea "Ke Hanan meke faruwane ne yasameki haka a fuska" Matar Tai maganar cikin iyayi da isa Mutuminne ya kalli hanan shima "Auta meyasami goshinki haka meyafaru?" Hanan kuma fashewa da kuka tayi ta kwashe abinda yafaru da karya ta fada tace Jalila tamata duka ta dinga gwarata da bango tana zaginta "Amma auta kin bani kunya kamar ba Yar Dana Haifa a cikina ba ki tsaya wata yarinya tamiki duka hada fasa miki goshi kamata yayi insa bulala in zaneki ai"   "Wannan wace irin magana ce kakeyi haka a dakar min yarinya haka daga shigarta makarantar, wace Yar marasa galihun ce ta isa tayiwa y"ata haka in kyaleta wallahi senaga gatanta a gurin nan senaga uban da ya tsaya mata, se nasa an kulleta daga ita har ubanta" "No ban yadda ba kinsan ita Hanan din metayi yarinyar tayi mata haka mubi komai a hankali ki bari gobe in Allah ya kaimu da kaina zanje makarantar indai yarinyar ce bata da gaskiya semusan abinda yakamata muyi' " daddy ance mata baba na soja ne fa amma secewa tayi wai ko Yar gidan bullet ce, Allah yasa Kaine AK47" Abun ma dariya yabawa baban Hanan "Lallai yarinyar nan tana da karfin hali" Itakam Maman Hanan iya wuya ta kulu taso ace baban Hanan ya kyaleta data nunawa yarinyar banbancin civilian da kuma kaki, zata so taga uban daya tsayawa yarinyar nan ko baban Hanan be saniba seta koyawa yarinyar nan darasi seta nuna mata banbancin dake tsakanin yayan farar hula dakuma "ya'yan rainon bullet.     Tun kafin a tashi daga school wannan malar taje gidansu Jalila tagayawa Ummi abunda Jalila tayi bayan haka hadda cewa itama Jalila ta zageta tsaf Hankalin Ummi yayi matukar tashi da jin abunda Jalila tayi taita bawa malamar hakuri Ilham ta dawo daga makaranta amma har taje ta dawo bata fuskanci komai ba, kamar yadda Daren jiya batayi bacci ba tunda Jalal ya nuna mata messages din wayarsa da yake tuhumarta akai, hankalinta yaki kwanciya tun jiya take takura kwakwalwarta domin kokarin gano wadda ke turowa Jalal wannan sakon amma takasa tuna komai, a iya saninta ba ya muamala da mata, to ta Yaya? wacece wannan take kokarin rusa nawa shirin ita ta kafa kanta, Jikinta a sanyaye taje tayi wanka amma takasa cin abinci "ko gurin Nana zanjene ko zata tayani gano wacece ta, tambayi kanta Kodayake yanzu ta dawo daga makaranta kar in takuramata koma inje tana wayar da wannan sha³ Yar uwatta ta Da sauri Ilham ta mike JALILA tafada a fili, tabbas JALILA ce itake turomasa wannan sakonin dan babu Wanda yakewa Jalal shishshigi in ba itaba iya sanina Jalal baya kula mata ko a family   Amma indai na kara bincike na tabbatar Jalila ce sena yi maganinta babu wata "ya mace data isa tayi takara dani a soyayyar Jalal, wallahi JALAL nawane ni kadai, duk macen datayi yinkurin yin takara dani senaga bayanta se yanzu nagane wato duk wannan shishshigin da take masa Ashe sonsa take To ba ta isaba wallahi Koda aka tashi daga makaranta Jalila hankalinta kwance ta taho gida tare da kudurcewa a zuciyarta setaje gidan malaman nan data ce mata 'Yar mace ta mata warning dan bata hakura ba, Gida ta tafi ta shiga da sallama amma Ummi bata amsa mata ba dan haka kai tsaye dakin Ummi ta nufa Ummi nakan sallaya ta idar da salla tana lazimi Jalila ta wuceta ta canza kaya zuwa towel taje tai wanka tai salla tasaka uniform din islamiyya amma still Ummi bata kulata ba "Ummi wai baki ganni bane, yau ko sannu dazuwa bakice minba se fushi kike wai mena mikine?" Still Ummi batace mata komai ba gaban Ummi taje ta zauna "Ummi wai meyene"? Janyota Ummi tayi gabanta ta zuba mata kyawawan maruka guda biyu " wato Jalila duk kokarin danake akanki inkika fita abinda zuciyarki tagaya miki shi kikeyi, Kin fasawa Yar mutane goshi, kinzagi malamanki wannan itace tarbiyyar danayi miki ko? To yanzu zankira Abban Jawwad in aka kashe case din nan gobe in Allah ya kaimu, Koshi ko Jawwad wani yazo ya daukeki sukoma can kanon dake, Lokaci yayi dazan koma dangina kema kikoma hannun wan ubanki tunda ba kya tausayina, "Yar gidan babban captain fa na sojoji Jalila me nake dashi da Zan iya wannan rigimar dakika dakko, kano zaki koma nagaji, gaskiyar mahaifinki kafin yarasu da yace tarbiyyar mace seda tsayayyen namiji bazan iyaba Jalila nagaji" "Har anzo angaya miki karya da gaskiya kekuma kin yadda ko Ummi to walla..... " rufemin baki Dan ubanki" Da sauri Jalila ta kalli Ummi bata taba jin Ummi tayi zagiba "Akan kujerar zama ko? kikayi wannan aikin ko ubankine ya sassaka kujerar kokuma akai na  haifeki dazaki daki Yar mutane akai kujerar banza, Kuma saboda baki da kirki ki dubi malama ramatu Dan an miki magana ki zageta ko Jalila" Se yanzu Jalila ta gane malama ramatu CE tazo tagayawa Ummi "Wallahi Ummi malama ramatu munafuka ce bafa haka.. " Ai bazaki canza ba, hali indai nakine bazaki canza ba agaban nawa ma kuma zagin malamar ki kike ko? "Wallahi niba malama ta bace yan primary take koyarwa bata taba koyamin uwar komai ba" "Yayi miki kyau ina fada kina fada" "A'a Ummi Dan Allah kiyi hakuri karkiyi fushi bazan karaba" "Aini nagama yanke hukunci Abbanku zan kirawo azo a maidake kano, nima gurin nawa dangin zan koma" "Ummi wai dagaske kike, dan girman Allah kiyi hakuri nace mikifa bazan karaba ni wallahi bazan koma kano ba" "Sekuma kiyi ai tunda ni kin rainani gara kikoma gaban Zainab itace daidanki" "Na shiga uku wallahi Ummi kafata kafarki ko bangon duniya zaki tafi ko a kafa sena biyoki, wallahi bazan kuma ba dan Allah Ummi, wallahi banason zuwa kano" Banza ummi tayi mata ta dakko wayarta tana kiran Abba yayinda Jalila ke gabanta tanata faman kuka Jawwad ne ya dawo daga makaranta ya gaji matuka kaya wanka yayi yai salla ya tafi gurin Rabin ran nasa wato Jalal "Dan uwa ka dawo daga makarantar kenan sannu da zuwa" "Yawwa bros Sannu da hutawa" Jawwad yafada yana Neman gurin zama "Nagaji sosai Jalal," "Nagani a idonka ai yau kukayi tests din ko?" " eh yaune Alhamdilillah test din duk se godiyar Allah sunyi sauki sosai kuma hada jajircewar ka da addu'arka proud of you dan uwana rabin jiki" "Kajika kaifa kake karatunka bani nake maka ba wannan kan naka akwai ja mutumina i wish nike da kwanyarka" "Amma fa ka zageni Jalal, kasan ban isa inyi karatun dakayi a bayaba in kana waje wayake Neman irinmu, Jalal wai yaushe zaka koma makaranta ne kai?" "Zan koma amma ba yanzuba, bana son wannan zancen zomuje muci abinci" "A ina kuma ga abinci can a Gida zuwa nayi muje mu ci" "koma inane muje daganan kasha ice cream ka dan huta, ka huce wannan gajiyar " "Kaikake koyamin kwadayi fa" Dariya sukayi gaba daya "Kasan wani abu Jawwad?" "A'a seka fada? " wallahi wata mayyace take uzzurawa rayuwata gashi tayi hiding number balle insata a black list, kullum seta kirani kota turomin messages ni na rasa yadda zanyi, wallahi na gane wacece setayi Dana sanin wannan gangancin da take min" Dariya sosai Jawwad yayi "To kai meye abun damuwa aciki, dan ance ana sonka"? "Mtseww kai kafiya shirme Jawwad ni bani da lokacin wannan shirmen, inyi rayuwata ni kadai ya fiyemin, duk yayinda ka gayyoto mata cikin rayuwarka kamar ka gayyatowa kanka matsalane" Dariya  Jawwad ya dingayiwa JALAL seda Jalal yafara jin haushi sannan ya dena "Jalal wayagaya maka mata matsalane, mata ni'ima ne, tabbas akwai daga cikinsu masu matsala, amma akwai na kirki sosai, soyayya akwai dadi mussaman in kayi dace da mosoyi na kwarai, bazaka gane hakan ba seka fada tarkon soyayya" "Hmm mata duk matsalane indai irinsu Ilham ne duk matsalane" "Hmm bazaka gane ba Jalal" "Eh naji bazan ganeba" "Lokaci ze ganar da kai ai" "Eh naji mutafi" Jeje ne yakira Jalal yana son su hadu Jalal Shikuma yace masa ya fita shida Jawwad bazeyiwu su hadu yanzu ba Gurin cin abinci suka tafi shida Jawwad Bayan sungama cin abinci ne suna hira aka kira Jawwad lambar Ummi yagani ya kara nutsuwa ya dau wayar "Salamau alaikum Ummi barka da rana" "Yawwa barka Jawwad ya kake ya mutan gidan" "Kowa lafiya Ummi ya Jalila" "To lafiya kalau za a ce meyasamu lambar abbanku nakira bata shiga" "Inaga inda yake ne ba network, amma lafiya Ummi" Ajiyar zuciya Ummi tayi ta kwashe kaf abunda yafaru tagayawa Jawwad "Yasalam Ummi kiyi hakuri insha Allah komai zezo da sauki, yanzu bana Gida idan na koma zanwa Abban bayani insha Allah, kiyi hakuri Ummi dan Allah kinsan har yanzu yarinya ce" "Ba batun yarinta  Jawwad tsabar rashin hankaline kawai " adai yi hakuri Ummi " Haka dai sukayi sallama Jawwad ya dafe kai "Ohhh my God sisy ba dai rigima ba" "Ya dai meyafarune?" Jalal ya tambayeshi, Jawwad ya kwashe komai ya gayawa Jalal, Dariya Jalal ya dinga yi kaman wani tababbe "Kan bala'i wannan yarinyar Yar bala'ice wallahi, kaga zancena ko Jawwad, nagaya maka mata matsalane, mussaman irin wannan kanwar taka zama da ita seda panadol" "Hmm haba Jalal kaima kanwarka ce, Jalila bata son raini bata yadda da wulakanci ba nidai fatana Allah yasa kar baban yarinyar yayi mata wani abu" Wata dariyar Jalal yakumayi "Kamar ya kar yayi mata wani abu "yarsa fa ta Daka, aigara suko yamata hankali yadda gobe bazata kuma ba," Yayi maganar yana dariya "Haba Jalal Yar gidan Abee ce fa, in duniya da gaskiya bekamata kace haka ba" "Hakane Jawwad kaima kace wani abu amma kasani bataji, in mutum yana rashin kunya in besamu dai² da shiba baze dena ba   "Wow tauraro a cikin taurari kaina mussaman ne ban taba tunanin kana dariya haka ba, bakaga yadda dariya kemaka kyauba" Gaba daya suka waiga domin ganin me maganar Hannah ce budurwar dasuka hadu da ita wancan karon, tayi maganar tana karasowa inda suke guri tanema ta zauna "Jarumin maza meyabaka nishadi kake wannan dariyar haka ka fi ko yaushe kyau ko dan uwan ne yake baka nishadi" Ta karasa maganar tana kallon Jawwad "Uban wa yace kizo inda nake, me kike Nema a gurina ne kin uzzuramin kindami rayuwata meye hakane, waima wayagaya miki ina nan da kike bina"?   Wani kasaitaccen murmushi Hannah tayi "Call me by my name Hannah, or any special name u choose, Kasan ita zuciyoyin masoya kaman wireless ne, our hearts and souls are always connected, dan hakazuciyarkace tagayawa tawa zuciyar kana nan shiyasa nazo kuma nayi sa'a nasameka zuciyarka kawai nake bukata Jalal, in har kabani zaka huta da nacina, akasin haka kuwa zan cigaba da hanaka sukuni cikin dare ko rana har sekabani abunda nakeso" Wani wulakan taccen kallo Jalal yai mata ya watsar da ita bece mata komai ba Jawwad ne ya danyi gyaran murya "Kinaji Hannah already Jalal akwai wadda takeson Sa kanwarsa ce kuma kinga..... Dagawa Jawwad hannu Hannah tayi " haba dan uwan masoyina meye laifina anan dan ina kokarin cikawa zuciyata burinta, kowa iya allonsa ya wanke, tayi nata kokarin nima inyi nawa wadda tai galaba ta kafa soyayyarta a zuciyarasa shikenan, ni Hanna babu macen data isa tayi takara dani akan soyayya, Jawwad son danakewa dan uwanka ko matansa hudu sena kori biyu ya aureni saboda space din daya yamin kadan, Kar ace rashin adalcin nawa yayi yawane da se ince seya kori kowa ya aureni saboda shidin nawane ni kadai" Saroro Jawwad yayi yana kallonta "In kagama jin tatsuniyar kazo mutafi inada abunyi" Jalal yafada yana mikewa Hanna ma mikewa tayi tazo gabansa kaman zata shige jikinsa se wani irin fitinannen kamshi take "Babyna kabani dama ko sau dayane in gwada maka yadda nake sonka mana, kuskurewa bukatata shizesa incigaba da uzzura maka har gidanku nasani zaka iya ganina a kowani lokaci, karkayi mamaki nasanka farin Sani a yadda kake a haka nake sonka, zan iya komai akanka, kagayawa kanwarka ta janye kudirinta na sonka ta barmin kai in bahakaba" Ta kashe masa ido daya daga nan tai tafiyarta,p babban abunda yabawa Jalal mamaki dayakasa yimata komai Jawwad ne ya janyo hannunsa suka hau motarsu suka nufi Gida "Jawwad ka yadda mata matsalane, abunda zuciyarsu ta raya musu kawai shi sukeyi, yanzu ga haukan da wannan tayi min, amma zan dau mataki akai" "Kabi komai a hankali Jalal, kasan in mutum yana kan ganiyar so makancewa yake so ba karyane ba, ka dena wulakanta Wanda yace yana sonka kai baka san a ya zaka fara taka soyayya ba, Amma wannan Hannah ka nemi tsari da sharrinta because Dana kalli cikin idonta ya tabbatar da she mean what she said" Haka suka cigaba tattaunawa har suka iso gida Bayan sallar isha'i Jawwad yaje part din Abba ya tarar dashi shi ka dai, yagaya masa abunda ya faru jinjina kai Abba yayi "Hmm Jalila iya rigima, halin mahaifinta ta dakko bata son raini Allah ya kaimu goben, zan San yadda za ayi" Da asuba Abba ya taho kano be gayawa maama abunda ya faruba ya dai cemata zeyi fitar asuba zashi wani guri   Still wannan Daren ma messages din Hannah suka dinga shigowa wayarsa seda yagaji ya kashe wayar Washe gari da safe Jalila ta shirya ta tafi makaranta, Daren ranar addu a ta kwana  tanayi Ba wai Allah ya sassauta fitinar da ta dakko ba, se dai Allah yasa kar Ummi ta korata kano   A hanyar makaranta ta hadu da yayan lubabatu data tsokana ranar akayi Sa a ya ganeta, ta Ganshi sarai amma taki guduwa tacigaba da tafiya a hankali, Zuwa yayi ya sha gabanta "Ke karamar Mara mutunci ni kika zaga ranan ko waike Yar iska" "Wallahi kasake ka tabani sena tara maka jama'a nace zaka lalata ni shekara goma sha hudu ce zakayi a gidan yari bayawa" "Au tunaninki barazanar ki zata hanani in casaki senaga uban da ya tsaya miki" "Bari kaji in gaya maka idan kana shan kwayarka tagaya maka karya kayiwa mutane hauka, to karkayi gangancin gwada kwayarka akaina, Dan wallahi sena kulla maka sharrin dazaka kare rayuwarka a prison" Kafin kace meye wannan Jalila ta ware murya ta fara ihu iya karfinta hankalin jama'a ne yafara dawowa Kansu ana fara taruwa ta silale ta gudu ta nufi makaranta Abunda yasa ta guduma gudun kar takuma shiga wata cakwakiyar bata fita daga wadda take ciki ba ga Ummi tace zata maida ita gidan su Jawwad da setasaka anmasa duka   Tana zuwa ajinsu ta tafi taje gurin zamanta ta hakimce ba tareda ta kula kowaba, "Allah ya biya Queen J Dama tunda yarinyar nan tazo kanta yake hayaki, se wani takama take, malamai ma kaman wani tsoronta sukeji segashi kinyi maganinta" Haka dai seatmates dinta suka dinga zigata ita dai Jalila hankalinta yana kan batun Ummi Bayan anfita break an dawo ba dadewa Hanan ta shigo ajin tana kallon kowa a wulakance ga malami a ajin amma Hanan batabi takan malamin ba ta tako Tazo gaban Jalila "Sannu uwar rashin kunya, dama na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki, Yau zakigane kin taba Yar gidan bullet kizo office bullet yazo da kansa" "Amma kin bani kunya da kikazo da bullet kawai, ai na dauka barikin zaki dakko gaba daya su taho da egwa yadda in sun markadeni baza ageneniba dan dai bullet, ai bullet yayi kadan aga bayana dashi" Jalila takarasa maganar hade da tsaki"nonsense " Mikewa Jalila tayi tai gaba ta wuce hanan Wato Jalila Yar bala'ice babu alamar risina a tare da ita tun tasowar Hanan take taka Wanda taga dama take jefa tsoro a zukatan duk Wanda yai kuskuren shiga hanyarta saboda takamar ubanta wani ne amma yau ta hadu da wadda tafita rashin mutunci Haka ta bi bayan Jalila suna zuwa harabar ofishin director Jalila sukayi clashing da malama ramatu aikuwa Jalila ta tsaya "Ita wutar munafiki ko tana karkashin jahannama ne, Kekam baki dace da malamar makaranta me bada tarbiyya ba kema kina bukatar me baki" Jalila ta gayawa malama ramatu sannan tai gaba abinta Tana shiga office din director ta tarar da mutane ba Wanda ta kula kuma bata kalli suwaye a ciki ba ta shige Share please More comments more typing............. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  20&21 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- "Meyasa kikace kar ya sha" "Nidai kawai kahana shi sha kar ya sha tea din nan" Jawwad ji yayi gaba daya ta firgice masa "Amma meyasa kikace kar ya sha?" Sekuma tarasa mezata ce masa "Am...emm.. Idan ya sha ze iya yin amai gara kaimasa tofi na ayoyin Qurani ya sha kafin kabashi abinci in Bahaka ba, ze iya bashi matsala eh..m.. In...nima malaminmu ne yafada mana a Islamiyya"   Da Jawwad yaji haka da sauri yasa hannu ya karbi cup din tea Daga hannun Jalal Jalal ne ya kalleshi "Meye haka kuma?" "Kanwarka tace karka sha tukuna, Dan huta ina zuwa" "Kaga ni bani yunwa fa nakeji yaushe zan tsaya biye maka yarinya Karama tana juya ka" ya yunkura ze karbi cup din tea daga hannun Jawwad yaji kansa ya kara nauyi dan haka ya koma ya zauna yana jujjuya kan "Sannu bros" Jinjina kai kawai Jalal yayi Kamar yadda Jalila ta gayawa Jawwad yaje fridge ya dakko ruwa ya karanta ayoyin Qurani ya busa masa a ruwan yazo ya tsiyayo a cup ya bashi Hannu yasa ya karba ya shanye ya ajiye kofin, ko minti biyar beyi da shan ruwan ba ya mike ya tafi bandaki ya dinga wani irin bakin amai Jawwad ne ya bishi yana masa sannu ya kwashi mintuna yana amayar da wani bakin abu Seda Jawwad ya Dan tsorata "Jalal mutafi Asibiti your condition is getting worst jin ciwon nan nake kaman a jikina" Ture Jawwad yayi ya tafi ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu ga wani mugun Jiri dayakeyi Jawwad ya biyo bayansa, Dan kura masa ido yayi yaga jijiyoyin kan Jalal duk sun mike fuskarsa tayi Ja Gefen gadon ya zo ya zauna yasa hannunsa akan Jalal yana masa karatun Qurani a hankali Wani baccin wahala ne ya kuma awon gaba da Jalal abun mamaki a cikin baccinsa ya dinga Jin sautin karatun Jalila Wanda ya dinga jin nutsuwa tana saukar masa Jawwad ne ya mike ya nufi gida don tafiya masallaci lokacin salla la'asar yafara gabatowa Cikin Gida ya shiga ya tarar da Nana tana video game maama kuma ta Dan kwanta a akan kujera tana kallon Nana Sallama yayi suka amsa gaba daya "Maama sannu da Gida" "Yawwa ya jikin Jalal din"? "Da sauki maama" "Allah ya sawwake" "Ameen" Ya amsa "Nana babu abunda kika iya se shirme, Jalila tana can tayi abun arziki ke kam shirirtarki ta fiye miki" Attention dinta gaba daya Nana ta bashi "Allah Yaya me Jalilan tayi" "Gasar karatun Qurani sukaje abuja jiya, tazo na biyu, amma se rikici takewa Ummi wai ita na daya take so" "Dan Allah Yaya dagaske amma naji dadi, ga fitina ga kwanya Allah sarki Jalila Allah yakara hasken makaranta" "Ameen kema se ki dage kidena wannan shirmen" Duk abun nan maama bata ce uffan ba   "Amma shine ko ta gayamin amma kai ta gaya maka dani take zancen" Nana tafada tana Dan bata rai "Aini kullum se munyi waya da ita" "Ai Yaya dole muje Kaduna we have to celebrate the victory of my great sister bari Abba ya dawo" Nana tai maganar tana murmushi    "Karki fara, kwata² yaushe ta bar gidan nan kike zancen, wani zakuje to babu inda zaku, nasake naji kin tambayi abbanku zakije sena bata miki rai sha³ kawai, Kaikuma naga zakewarka akan yarinyar nan yafara yawa ka kiyayeni  Jawwad in bahakaba daga kai har ita senaci mutuncinku," Maama ce tayi wannan maganar cikin fada da fushi gaba daya suka bita da kallo Ajiyar zuciya Jawwad yayi ya dan girgiza kai "Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki za a kiyaye insha Allah" Ya Fita yabar parlour itakuwa Nana zunbura baki tayi itama ta barwa maama parlour "Lallai in ban dageba maganar Yaya mairo na shirin zama gaskiya zakuci kaniyarku sena raba Ku da yarinyar nan" Se bayan magariba Jalal ya kuma ta shi wannan karon seya jishi sakayau babu ciwon kan se rashin kwarin jiki Wanka yaje yayi ya rama wasu daga cikin sallolin dabe ba ya bar wasu Jeje ya kira a waya yaji yana ina yagaya masa Kaya ya canza ya dauki motarsa ya bar gidan kai tsaye club din da yake haduwa da Jeje ya tafi kamar kullum yauma club din cike yake da "ya'yan da suka rasa mafadi maza da mata kowa na sharholiyarsa matan nan wasu sunyi shiga half nicked wasu na rawa yayinda wasu suka kama daki suna shagalinsu Jeje naganinsa ya washe baki yana masa sannu da zuwa gaisawa sukayi Jalal yasamu guri ya zauna Jeje ya tafi kawo masa mutuniyar tasa wato giya Duk gigin matan gurin nan basa zuwa inda Jalal yake saboda sun San halinsa basa gabansa shidai ze sha giya yayi mankas amma be yadda yayi zina ba Jeje ne yasamu guri ya kira Hanna " kina ina ne?" "Ina Gida mana" Hanna taba shi amsa "Muna tare da mutuminki fa yanzu haka" "Dan Allah dagaske dazu Dana kirashi abokinsa yace min bashi da lafiya" "Ke dalla rabu da wannan sakaran kilma karya yakeyi" "I wish in samu dama in fito yanzu inzo in ganshi" "Ke rufamin asiri yanzu ma abu zan karbo masa ke dai kicigaba da kokari" "Karka damu kaman yazo hannuna ya gama ne" "That's good seda safe" Sukayi sallama da jeje ya tafi bar domin karbo giya Bayan ya karbo ne yazo ya nemi guri ya zauna ya Tarar da Jalal yanata salansa yana bawa sama hayaki tabarsa kawai yake sha Jeje ne ya tsiyayawa Jalal giya a cup ya tura masa gabansa Wayar Jalal ce ta fara ringing ya Dakota seyaga unknown number seyaki dagawa ya cigaba da abunda yake haka wayar taita ringing "Maza wayarka fa ake kira" Sedayaja wasu seconds sannan yabawa Jeje amsa "Nagani" Dan tabe baki Jeje yayi yacigaba da shan giyarsa Messages ne suka dinga shigowa wayarsa Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din        "Haba fitilar rayuwata         meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby          From your lovely bae" Ire² wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad? Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar "Jalal kana ina?" Jawwad ya tambayeshi "Na dan fitane" "Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe" Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice Jeje ya kalleshi "Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?" "Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri" Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka, Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane² dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai "Naji kaman kinyi bakuwa se anjima" Jalila tayi maganar "Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa" "Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi" Dariya Nana tayi tare da fadin "To Ilham kinji dai sakon Jalila" Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta "Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali" Ilham tai maganar tana mikewa Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar "Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka" Da Sauri Ilham ta kalleta "kamar ya?" "Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi" "Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka" "A'a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu" "Ai nasani" Ilham tabata amsa "Ya akayi kika Sani?" "Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni" Ta karasa maganar cike da damuwa Nana ta dafa ta "Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara" Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa "Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?" "Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane" "Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba" "Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa" "Allah yasa haka Nana" "Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be" Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas akai Jalila tana daki tana gugar uniform zasu koma makarantar boko Ummi kuma tayi bakuwa Jalila taji kaman ana harbe² a waje da sauri ta fito tsakar Gida "Ummi bakiji karan bindiga ba" Bakuwar Ummi tace "Wani captain ne na sojoji yake tarewa a anguwar nan bakiga wani kerarren Gida ba da aka gama kwanan nan ai nasane wallahi gidan ya keru kaman a kasar waje " "To shine kuma za a zo a cikamana kunne da karar bindiga saboda shirme, ni gidan ma nakeso in gani inga iya keruwarsa" "Allah yabaki sa'a kije Neman magana duk yadda zasuyi dake se dai suyi dan ba abunda zan iya indai sojojine zaki yabawa aya zakinta" Ummi tai maganar cikin bacin rai shiru Jalila tayi ta koma daki Jawwad ne yakema Jalal fada akan fitar da yayi daga samun saukinsa Yayinda Jalal ke bashi hakuri "Ai gani dai na dawo ban zauna a can ba hankalinka ya kwanta" "Bawani hankalina ya kwanta kabata min raine ka dinga sassautawa kanka wannan abubuwan dakake durawa cikinka" Hade rai Jalal yayi "naji kuma ina nace kayi hakuri " "Haka ka iya ai saura ka kara fita" Jawwad yayi maganar da alamun gargadi Dariya Jalal yayi "Sorry yayana bazan kuma fitaba a yau insha Allah" Murmushi Jawwad yayi sannan ya fita Bayan fitar Jawwad Jalal ya saka wayarsa a caji ya mike yatafi cikin Gida part din daddy yaje suka sha hira Cikin hikima daddyn yake masa nasiha "Daddy nima bana jin dadin abunda nake amma kacigaba dayimin addu'a wataran zakaga kaman banyiba" "Nima ina fatan hakan yaron kirki" Se kusan shabiyundare Jalal ya fito daga part din daddy shima mummy ce taje part din daddy shiyasa ya fito Ilham tana kwance akan kijerun parlour tana kallon Bollywood Waiwayawa tayi taga Jalal "Sannu Yaya ya jiki?" "Da sauki" Rannan a hade Yabata amsa ya fice Yana zuwa dakinsa ya tarar missed calls kusan takwas Da wannan unknown number din Tsaki yayi yaje yayi wanka yazo ya nemi gurin kwanciya ya dakko wayarsa hotonsa ne da Jawwad akan wallpaper dinsa kallon hoton yayi sunyi kyau a hoton matuka murmushi yayi ze bude what's app dinsa message ya shigo wayarsa budewa yayi     "Haba baby at least ko sau daya yakamata ka dau wayata kasan kuwa yadda zuciya ta takeyi I feel u in my every heart beat, nayi missing innocent face dinka gashi kaki yadda ko muryarka inji help me baeb na damu da kai            From ur lovely Bae" "Wai wannan wace irin Jaraba ce haka, wace ce wannan take Neman yimasa kutse haka a cikin rayuwarsa shi baze iya wannan shirmen ba wannan soyayyar duk haukane da bata lokaci" Yana cikin wannan mitar ne wayarsa kuma takama ringing unknown number din ce dai Dagawa yayi a fusace "Waike wace irin mahaukaciyace karfe nawa yanzu nibana wannan haukan ki kyaleni tun kafin ta kaimu ga bata miki rai"            "Wow komai naka birgeni     yake baby jin muryan nan taka kawai ta isheni bacci me dadi, Mark you ba abunda zakamin Wanda ze batamin rai Love u....... Katse wayar yayi ya kasheta gaba daya ya jefa wayar kasa nonsense yafada a hankali Washe gari bayan sallar asuba Ummi taga Jalila ta koma bacci " ke baby ba ankoma school ba kwana biyu da komawa amma kina nade a Gida tashi ki shirya yau makaranra zaki tafi" "Ummi bangama shiryawa ba in nagama zan koma" "Aikuwa sekin koma yau din nan" "Ummi bani da socks fa, kuma ni sekin canzamin school bag zan koma" "Kibari inzo gurin nan baki tashi kinyi shirin makaranta ba ni da kene" Ummi ta fita daga dakin Ummi na fita Jalila tacigaba da baccinta har kusan karfe bakawai Ummi tazaci Jalila ta tashi amma tana zuwa ta tarar da ita a cikin bargo Ran ummjne ya baci ta yaye bargon ta Dala mata duka tashi dan kaniyarki dama baki tashi ba tashi kisa uniform kitafi "Ummi dan Allah kiyi hakuri,  banga socks dina bane" Girgiza kai Ummi tayi "Allah ka shiryamin yarinyar nan, ai tunda baki gadama ba nasan bazakiba zakiga tsiya" Wunin ranar Sam Ummi taki kula Jalila Ta dinga binta tana bata hakuri tana mata magiyar ta saimata wata jakar daga karshe seda Ummi ta bata kudin Jaka da socks din hankalinta ya kwanta Amma Ummi tace bazata fita ba seda yamma Washe gari se bayan sallar la'asar sannan Jalal ya kunna wayarsa amma yana kunnawa sakonine sukacika masa waya wasu na bin wasu "Wannan wane irin Jaraba ce haka" Sakonta na karshe ya duba  "Baby in baka bude wayarka    ba zanzo har inda kake, tun safe nakasa nutsuwa ko har yanzu baka da lafiya ne? Na damu da kai baby          From your lovely Bae" "Wannan wace irin Jarababbiya ce da take uzzurawa rayuwata ne" Yana cikin wannan tunanin Sega Ilham ta shigo da kayan abinci ta samu guri ta ajiye "Yaya ga abinci inji mummy Harta mike zata fita ya kira sunanta "Ilham" "Na'am" "Zo nan" seda cikinta yayi kara gabanta ya fadi Allah yasa ba wani abun nayi masa ba jiki a sanyaye ta nufi inda yake guri ya nuna mata kusa dashi ta zauna wayarsa ya dakko ya shiga messages din nan ya nunamata "Ke kike turomin wannan shirmen ko?" Gabanta ne yafadi ita ba tuhumar dayake matane ta sata faduwar gaba ba se fargabar wace wannan take shirin yi mata kutse "Tambayarki fa nake" Jiki a sanyaye ta daga kai ta kalleshi "Bani bace ba" Jawwad ne ya shigo "Inyee yau zumunci ake jine Yaya da kanwa" Basu kulashiba ya karasa ciki ya zauna yaga ran Jalal a bace Yana ma Ilham magana "To waye?" Jalal Ya tambayeta "Ya za ayi in sani yaya, nidai nasan bani bace" Tabashi amsa hawaye na gangarowa daga idonta "Uban me na miki zakimin kuka" Wani irin kallo tayi masa "Yaya Jalal tambayata kake meyasa nake maka kuka ko? Ina nuna kulawata akanka, baka damu dani ba bakajin me nake ji a raina hasali ma ka tsaneni, amma wata a waje tana shirin rusani ga sakonin da take turomaka, kuma kake tuhumata ni ina naga fuskar da zan turo maka wannan sakonnin " Cikin hargowa ya mike ze zazzaga mata bala'i Jawwad ya ga tsananin kishi kwance a idon Ilham, tausayinta ne Yakama Jawwad dan haka  ya dakatar dashi "Ilham gaskiya ta fada Jalal" Jawwad Ya kalli Ilham yace "Tashi kikoma ciki" Sannan ya kalli Jalal Yamma nayi  Jalila ta shirya ta dau kudin safa da Jakarta tayi waje Kai tsaye inda ake fadan gidan sojan nan ta nufa daga waje ta karewa gidan kallo Aranta take fadin gaskiya gidan nan ya hadu saura kuma inshiga inga meye a ciki yadda ya hadu daga wajen nan cikin kuma ai nasan yafi haduwa Daga nan ta mika ta nufi inda zata sayi jaka amma seta hango wani kanti da sojoji a bakin gurin dan haka ta yanke shawarar zuwa taga meye akeyi a gurin Kai tsaye ta kutsa cikin kantin wani soja ne ya daka mata tsawa yace ta tsaya a waje se sungama sun tafi tukuna "Dan Allah kabari abu zan siya kawai in tafi ni ba gurinka nazo ba " Zekuma magana wani sojan yace ya batta ta shiga Tana shiga taga wani babban mutum a zaune akan kujera fuskar nan tashi murtuk babu annuri "Ina wuni" Jalila ta gaisheshi be amsa ba "Baba gaisheka fa nake nace ina wuni" Dan juyowa yayi ya kalleta ya danyi murmushi jin takirashi da baba "Lafiya kalau sannu yan mata" "Yawwa" Ta sai chocolate dinta ta mutumin nan yace abawa Jalila shize biya Seda ta risina sannan tace "Baba nagode sosai" "Bakomai adinga shan chocolate din a hankali yana kashe hakori" Murmushi Jalila tayi ta  fito "aikin banza na daukama wani abun ake a gurin to me sojoji suke anan ko gadinwa suke oho" Ta siyo Jakarta ta fito dayake kusa da kantin ake saida jakunkuna ta hangi mutumin dazu ya fito daga kantin nan ze shiga mota se ya yadda wallet dinsa da sauri ta je ta dauka, amma tuni sunyi nisa sun bar gurin sun nufi layin gidan wannan sojan Ta dinga jujjuya wallet din nan kawai ta tafi Gida da wallet din Bata nunawa Ummi ba ta boye wallet din Ta faki idon Ummi taje ta dau wallet din ta bude kudin kasar wajene a ciki da ID card bata tsaya bin ta ID card dinba ta aje wallet din cikin sabuwar jakar makarantar ta cikin litattafanta Washe gari Ummi ta tursasata ta shirya ta tafi makaranta, ta wannan layindai na gidan nan Jalila tabi dan takuma ganin gidan nan kuma ko Allah zesa taga mutumin nan Tanata kallon gidan wani soja ya kalleta "Ke me kike kallo wuce ki tafi makarantar ki" Ya mutsa fuska Jalila tayi "Ina ruwanka da makaranta ta?kallo kawai zanyi in tafi" "Ba a son yawan ganin mutane a arear gurin nan saboda tsaro dan haka wuce ki tafi" "Did I look like criminal, da uniform dina na makaranta balle kace wani abun zanyi, sekace gidan shugaban kasa naga dai gidan mutum ne ba aljan ba in me gidan yasan bayaso a dinga wucewa ta hanyar gidan ai da seyaje duniyar wata ya Gina gidan ba duniyar mutane ba" "Kut wace irin yarinya ce wannan?" Aikuwa sojan nan beyi wata² ba ya zare beilt da nufin ya koya mata hankali se su kaga wasu motoci suna shigowa Latin manyan motoci ne glasses din duk tint ne mutumin jiya da ya sai mata chocolate ne ya fito daga daya daga cikin motocin Wannan sojan da ya zare belt ne ya kame yana saramasa da ido yai masa magana sojan ya tsaya "Laa baba ina kwana" Jalila ta tsuguna tana gaisheshi "lafiya kalau Yar baba, meyahada ki da wannan" Ya nuna mata sojan nan da ya biyota Bata boye masa komaiba ta gayamasa murmushi yayi a ransa yace lallai wannan yarinyar Yar rigima ce amma a fili yace "Yar baba yanzu kin makara ki tafi makarantarki rabu da shi Kai baka ganin Yar makaranta ce kawai daga kallon Gida se a ce za a bigeta ina nema mata afuwa" Jalila tasaka hannun a Jakarta ta dakko wallet din nan ta mika masa "Jiya ka yaddashi bayan kafito daga kantin nan" Hannu yasa ya karba tasan ce kuwa yana ta dubawa tun jiya be ganta ba yayi zaton yayi miss placing dinta ne Murmushi yayi "nagode sosai Yar baba Allah ya albarkaci rayuwarki " "Ameen nagode" Ta juya ta tafi hanyar makarantar su ta makara sosai amma taci sa'a ba malami a ajinsu dan haka ta shige tanufi ajinsu Class dinsu ne ya kaure da hayaniya ga Queen ta dawo nickname dinta kenan a makarantar boko Queen J Kai tsaye bayan sungama murnar ganin juna da yan ajinsu gurin zamanta ta nufa amma me setaga wata hakima ta hakimce mata a seat Jalila dai bata Santa a ajinsu ba maybe newcomer ce dan haka Jalila tace "Sannu dai excuse me gurin zama nane ina bukatar zan zauna" Banza yarinyar tayiwa Jalila "Ko kurma ce ne? Nace kifito nan gurin Jalila ne fada tace" "Wallahi mun gaya mata har malamai sun San nan gurinkine amma tace ita kuma dole anan zata zauna" Cewar wata daliba Ita kuwa sabuwar zuwan nan bata da niyyar magana balle Jalila tasa ran zata tashi sema wani kashingida tayi ta kurawa Jalila ido tana hura hanci tana kallon Jalila up and down "Ke yau kome kikeji zan sauke miki shi yau koda uban me kike yawo wallahi sekin bar seat din nan uwarkice ni a rashin mutunci" Dariya yarinyar tayi "ok yi abinda zaki iya nikuma na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki a yau base gobe ba" "Queen J dan Allah kiyi hakuri ki kyaleta babanta fa babban sojane ranar Monday aka kawota" Wata dalibar tai maganar tana kokarin Jan hannun Jalila dukan benci Jalila tayi "Wallahi ko Yar gidan bullet ce, ke Allah yasa baban tane AK47 wallahi seta tashi this is my kingdom, in ubanta ya tsaya mata ni Allah ya tsayamin, Kafin kiyi maganina ni zan fara maganin wannan izzar taki, ko kina wa kowa hauka ba ayiwa Jalila" Hannu biyu Jalila tasaka ta fizgo yarinyar nan daga cikin benci aikuwa yarinyar nan ta wankawa Jalila mari, Wasu daga cikin dalibai suka tafi kirawo malamai domin raba fadan nan Amma tuni Jalila ta rama marin nan ta kara mata wani, Jalila ta dage ta hankada yarinyar nan kan bencina nan take goshinta ya fashe jini yashiga fita Share please More comments more typing....... Proud of you my fans INA jin dadin adduoinku nagode kwarai Allah yabar kauna ❤❤❤❤❤ Team JALILA kunga abinda yau ta dakko to ni ba ruwana😎😎 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  22&23 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- Not Edited Jinine ya wanke mata fuska ta fasa kara yarinyar tayi, itako Jalila ko ajikinta, hakan yayi dadi² da isowar class mastern su Jalila hankalinsa ne ya tashi ganin duk saurin da yayi Jalila ta riga tayi aika² be kara tsurewa ba seda ya tabbatar da wadda aka fasawa goshi salati yayi, Hanan Abdurrasheed Yar gidan babban captain din sojan ruwa da aka kawo ranar litinin ita Jalila ta fasawa kai shi kansa ba yadda beyiba ya canzawa Hanan gurin zama saboda yasan me gurin tafi kashi doyi wato queen J,  amma hanan yarinyar akwai izza da jin kai, tace ita dole nan gurin takeson zama, yanzu yasan ba Jalila ba su Kansu makaranta Ta janyo  musu "Jalila mene haka kika aikata, wannan wane irin shirme ne, yaushe ma kika dawo ne bansaniba memakon kizo kigayamin seki dauki doka a hannu kalli haukan da kikayi" "Niba hauka nayiba daba ta mareni ba inaga da hakan bata faruba" "Shut up zaki gane kuranki ubanta sojane insuka casaki inaga daga yau kindena Neman magana" "Wai da anyi magana se afara maganar babanta sojane, Allah sarki mukuma 'ya'yan Allah bani marasa gata, wallahi ko Yar gidan rocket ce bata isa ta mareni in kyaleta ba" Ya fuskanci babu alamar nadama tareda Jalila Dan ko kadan bata tsorata da abinda tayi ba itakuwa Hanan tuni aka tafi da ita school clinic akaimata dressing daga nan Hanan bata saurari kowa ba ta fice daga makarantar duk yadda akayi a dakatar da Hanan amma tayi waje ta tafi gida Jalila aka kira office din director Aka dinga mata fada kowa da abunda yake fada a cikin malamai wasu abun kirkinta wasu akasin haka ciki hadda wata malama ta zage ta dinga zagin Jalila matar a bayan layinsu Jalila take, Jalila ta taba fada da Yar malamar, Dan haka dama tanajin haushin Jalila "Dama wannan yarinyar ba tarbiyyace da ita ba, bata da mutunci Sam dama ina za a samu wata tarbiyya a gurin Yar mace" Jalila ce ta daga kai da sauri ta kalleta "A'a madam adinga hakuri Jalila yarinyar kirkice, tana da tarbiyya ita dai matsalarta da students ne ga tarin alkhairanta ga makarantar mu dabazamu manta ba" Cewar director "Hmm yallabai baka San yarinyar nan bane uwatta Sam bata son laifinta ita ta sangarta ta lalace, amma yarinya sekace Yar daba, takama Yar mutane ta fitar mata da jini, dama charity begins at home duk abunda yarinya takeyi to haka taga uwatta tanayi" "Sir kaimata magana kartakuma zaganmin uwa duk zaginta ta tsaya kaina takuma zagina sena rama, uwa ba tafi uwa ba" "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Jalila ta daban ce Jalila koma class dinku yanzu" Cewar director ita kuwa Jalila ta mike ta koma ajinsu "Dan Allah kalli yadda take ikrarin zata zageni yarinyar nan kawai a koreta shine mafita" Inji malamar dazu "Korarta ba shine mafita ba yarinya ce me matukar kwazo in muka koreta munyi asara babba" Cewar wani malami "Hakane kam wan mahaifinta abokina ne bazan taba korar masa ya ba, kuma duk fitinarta bantaba ganin tayiba se yau yanzu dai mahifiyarta zamu  gayyota tazo mu zauna da ita dakuma wakilinta Dan na tabbatar, Yar gidan sojan nan se sunzo makarantar nan" "Allah yasa suci kaniyarta sumata dukan tsiya" "Haba madam in "yarkice fa baza kice haka ba ai shi da na kowa ne addu'a yakamata ayi mata Allah ya shirya Allah kalli dai yasan abunda zata zama nan gaba" Inji director Hanan ce ta shiga tangamemen palour tana kuka wata babbar mace ce zata yi shekaru arba'in da takwas amma Hutu yasa in ka ganta seka zata batafi shekaru talatin da biyu ba, gefenta kuma ga wani babban mutum shima yana shan tea "Ke Hanan meke faruwane ne yasameki haka a fuska" Matar Tai maganar cikin iyayi da isa Mutuminne ya kalli hanan shima "Auta meyasami goshinki haka meyafaru?" Hanan kuma fashewa da kuka tayi ta kwashe abinda yafaru da karya ta fada tace Jalila tamata duka ta dinga gwarata da bango tana zaginta "Amma auta kin bani kunya kamar ba Yar Dana Haifa a cikina ba ki tsaya wata yarinya tamiki duka hada fasa miki goshi kamata yayi insa bulala in zaneki ai"   "Wannan wace irin magana ce kakeyi haka a dakar min yarinya haka daga shigarta makarantar, wace Yar marasa galihun ce ta isa tayiwa y"ata haka in kyaleta wallahi senaga gatanta a gurin nan senaga uban da ya tsaya mata, se nasa an kulleta daga ita har ubanta" "No ban yadda ba kinsan ita Hanan din metayi yarinyar tayi mata haka mubi komai a hankali ki bari gobe in Allah ya kaimu da kaina zanje makarantar indai yarinyar ce bata da gaskiya semusan abinda yakamata muyi' " daddy ance mata baba na soja ne fa amma secewa tayi wai ko Yar gidan bullet ce, Allah yasa Kaine AK47" Abun ma dariya yabawa baban Hanan "Lallai yarinyar nan tana da karfin hali" Itakam Maman Hanan iya wuya ta kulu taso ace baban Hanan ya kyaleta data nunawa yarinyar banbancin civilian da kuma kaki, zata so taga uban daya tsayawa yarinyar nan ko baban Hanan be saniba seta koyawa yarinyar nan darasi seta nuna mata banbancin dake tsakanin yayan farar hula dakuma "ya'yan rainon bullet.     Tun kafin a tashi daga school wannan malar taje gidansu Jalila tagayawa Ummi abunda Jalila tayi bayan haka hadda cewa itama Jalila ta zageta tsaf Hankalin Ummi yayi matukar tashi da jin abunda Jalila tayi taita bawa malamar hakuri Ilham ta dawo daga makaranta amma har taje ta dawo bata fuskanci komai ba, kamar yadda Daren jiya batayi bacci ba tunda Jalal ya nuna mata messages din wayarsa da yake tuhumarta akai, hankalinta yaki kwanciya tun jiya take takura kwakwalwarta domin kokarin gano wadda ke turowa Jalal wannan sakon amma takasa tuna komai, a iya saninta ba ya muamala da mata, to ta Yaya? wacece wannan take kokarin rusa nawa shirin ita ta kafa kanta, Jikinta a sanyaye taje tayi wanka amma takasa cin abinci "ko gurin Nana zanjene ko zata tayani gano wacece ta, tambayi kanta Kodayake yanzu ta dawo daga makaranta kar in takuramata koma inje tana wayar da wannan sha³ Yar uwatta ta Da sauri Ilham ta mike JALILA tafada a fili, tabbas JALILA ce itake turomasa wannan sakonin dan babu Wanda yakewa Jalal shishshigi in ba itaba iya sanina Jalal baya kula mata ko a family   Amma indai na kara bincike na tabbatar Jalila ce sena yi maganinta babu wata "ya mace data isa tayi takara dani a soyayyar Jalal, wallahi JALAL nawane ni kadai, duk macen datayi yinkurin yin takara dani senaga bayanta se yanzu nagane wato duk wannan shishshigin da take masa Ashe sonsa take To ba ta isaba wallahi Koda aka tashi daga makaranta Jalila hankalinta kwance ta taho gida tare da kudurcewa a zuciyarta setaje gidan malaman nan data ce mata 'Yar mace ta mata warning dan bata hakura ba, Gida ta tafi ta shiga da sallama amma Ummi bata amsa mata ba dan haka kai tsaye dakin Ummi ta nufa Ummi nakan sallaya ta idar da salla tana lazimi Jalila ta wuceta ta canza kaya zuwa towel taje tai wanka tai salla tasaka uniform din islamiyya amma still Ummi bata kulata ba "Ummi wai baki ganni bane, yau ko sannu dazuwa bakice minba se fushi kike wai mena mikine?" Still Ummi batace mata komai ba gaban Ummi taje ta zauna "Ummi wai meyene"? Janyota Ummi tayi gabanta ta zuba mata kyawawan maruka guda biyu " wato Jalila duk kokarin danake akanki inkika fita abinda zuciyarki tagaya miki shi kikeyi, Kin fasawa Yar mutane goshi, kinzagi malamanki wannan itace tarbiyyar danayi miki ko? To yanzu zankira Abban Jawwad in aka kashe case din nan gobe in Allah ya kaimu, Koshi ko Jawwad wani yazo ya daukeki sukoma can kanon dake, Lokaci yayi dazan koma dangina kema kikoma hannun wan ubanki tunda ba kya tausayina, "Yar gidan babban captain fa na sojoji Jalila me nake dashi da Zan iya wannan rigimar dakika dakko, kano zaki koma nagaji, gaskiyar mahaifinki kafin yarasu da yace tarbiyyar mace seda tsayayyen namiji bazan iyaba Jalila nagaji" "Har anzo angaya miki karya da gaskiya kekuma kin yadda ko Ummi to walla..... " rufemin baki Dan ubanki" Da sauri Jalila ta kalli Ummi bata taba jin Ummi tayi zagiba "Akan kujerar zama ko? kikayi wannan aikin ko ubankine ya sassaka kujerar kokuma akai na  haifeki dazaki daki Yar mutane akai kujerar banza, Kuma saboda baki da kirki ki dubi malama ramatu Dan an miki magana ki zageta ko Jalila" Se yanzu Jalila ta gane malama ramatu CE tazo tagayawa Ummi "Wallahi Ummi malama ramatu munafuka ce bafa haka.. " Ai bazaki canza ba, hali indai nakine bazaki canza ba agaban nawa ma kuma zagin malamar ki kike ko? "Wallahi niba malama ta bace yan primary take koyarwa bata taba koyamin uwar komai ba" "Yayi miki kyau ina fada kina fada" "A'a Ummi Dan Allah kiyi hakuri karkiyi fushi bazan karaba" "Aini nagama yanke hukunci Abbanku zan kirawo azo a maidake kano, nima gurin nawa dangin zan koma" "Ummi wai dagaske kike, dan girman Allah kiyi hakuri nace mikifa bazan karaba ni wallahi bazan koma kano ba" "Sekuma kiyi ai tunda ni kin rainani gara kikoma gaban Zainab itace daidanki" "Na shiga uku wallahi Ummi kafata kafarki ko bangon duniya zaki tafi ko a kafa sena biyoki, wallahi bazan kuma ba dan Allah Ummi, wallahi banason zuwa kano" Banza ummi tayi mata ta dakko wayarta tana kiran Abba yayinda Jalila ke gabanta tanata faman kuka Jawwad ne ya dawo daga makaranta ya gaji matuka kaya wanka yayi yai salla ya tafi gurin Rabin ran nasa wato Jalal "Dan uwa ka dawo daga makarantar kenan sannu da zuwa" "Yawwa bros Sannu da hutawa" Jawwad yafada yana Neman gurin zama "Nagaji sosai Jalal," "Nagani a idonka ai yau kukayi tests din ko?" " eh yaune Alhamdilillah test din duk se godiyar Allah sunyi sauki sosai kuma hada jajircewar ka da addu'arka proud of you dan uwana rabin jiki" "Kajika kaifa kake karatunka bani nake maka ba wannan kan naka akwai ja mutumina i wish nike da kwanyarka" "Amma fa ka zageni Jalal, kasan ban isa inyi karatun dakayi a bayaba in kana waje wayake Neman irinmu, Jalal wai yaushe zaka koma makaranta ne kai?" "Zan koma amma ba yanzuba, bana son wannan zancen zomuje muci abinci" "A ina kuma ga abinci can a Gida zuwa nayi muje mu ci" "koma inane muje daganan kasha ice cream ka dan huta, ka huce wannan gajiyar " "Kaikake koyamin kwadayi fa" Dariya sukayi gaba daya "Kasan wani abu Jawwad?" "A'a seka fada? " wallahi wata mayyace take uzzurawa rayuwata gashi tayi hiding number balle insata a black list, kullum seta kirani kota turomin messages ni na rasa yadda zanyi, wallahi na gane wacece setayi Dana sanin wannan gangancin da take min" Dariya sosai Jawwad yayi "To kai meye abun damuwa aciki, dan ance ana sonka"? "Mtseww kai kafiya shirme Jawwad ni bani da lokacin wannan shirmen, inyi rayuwata ni kadai ya fiyemin, duk yayinda ka gayyoto mata cikin rayuwarka kamar ka gayyatowa kanka matsalane" Dariya  Jawwad ya dingayiwa JALAL seda Jalal yafara jin haushi sannan ya dena "Jalal wayagaya maka mata matsalane, mata ni'ima ne, tabbas akwai daga cikinsu masu matsala, amma akwai na kirki sosai, soyayya akwai dadi mussaman in kayi dace da mosoyi na kwarai, bazaka gane hakan ba seka fada tarkon soyayya" "Hmm mata duk matsalane indai irinsu Ilham ne duk matsalane" "Hmm bazaka gane ba Jalal" "Eh naji bazan ganeba" "Lokaci ze ganar da kai ai" "Eh naji mutafi" Jeje ne yakira Jalal yana son su hadu Jalal Shikuma yace masa ya fita shida Jawwad bazeyiwu su hadu yanzu ba Gurin cin abinci suka tafi shida Jawwad Bayan sungama cin abinci ne suna hira aka kira Jawwad lambar Ummi yagani ya kara nutsuwa ya dau wayar "Salamau alaikum Ummi barka da rana" "Yawwa barka Jawwad ya kake ya mutan gidan" "Kowa lafiya Ummi ya Jalila" "To lafiya kalau za a ce meyasamu lambar abbanku nakira bata shiga" "Inaga inda yake ne ba network, amma lafiya Ummi" Ajiyar zuciya Ummi tayi ta kwashe kaf abunda yafaru tagayawa Jawwad "Yasalam Ummi kiyi hakuri insha Allah komai zezo da sauki, yanzu bana Gida idan na koma zanwa Abban bayani insha Allah, kiyi hakuri Ummi dan Allah kinsan har yanzu yarinya ce" "Ba batun yarinta  Jawwad tsabar rashin hankaline kawai " adai yi hakuri Ummi " Haka dai sukayi sallama Jawwad ya dafe kai "Ohhh my God sisy ba dai rigima ba" "Ya dai meyafarune?" Jalal ya tambayeshi, Jawwad ya kwashe komai ya gayawa Jalal, Dariya Jalal ya dinga yi kaman wani tababbe "Kan bala'i wannan yarinyar Yar bala'ice wallahi, kaga zancena ko Jawwad, nagaya maka mata matsalane, mussaman irin wannan kanwar taka zama da ita seda panadol" "Hmm haba Jalal kaima kanwarka ce, Jalila bata son raini bata yadda da wulakanci ba nidai fatana Allah yasa kar baban yarinyar yayi mata wani abu" Wata dariyar Jalal yakumayi "Kamar ya kar yayi mata wani abu "yarsa fa ta Daka, aigara suko yamata hankali yadda gobe bazata kuma ba," Yayi maganar yana dariya "Haba Jalal Yar gidan Abee ce fa, in duniya da gaskiya bekamata kace haka ba" "Hakane Jawwad kaima kace wani abu amma kasani bataji, in mutum yana rashin kunya in besamu dai² da shiba baze dena ba   "Wow tauraro a cikin taurari kaina mussaman ne ban taba tunanin kana dariya haka ba, bakaga yadda dariya kemaka kyauba" Gaba daya suka waiga domin ganin me maganar Hannah ce budurwar dasuka hadu da ita wancan karon, tayi maganar tana karasowa inda suke guri tanema ta zauna "Jarumin maza meyabaka nishadi kake wannan dariyar haka ka fi ko yaushe kyau ko dan uwan ne yake baka nishadi" Ta karasa maganar tana kallon Jawwad "Uban wa yace kizo inda nake, me kike Nema a gurina ne kin uzzuramin kindami rayuwata meye hakane, waima wayagaya miki ina nan da kike bina"?   Wani kasaitaccen murmushi Hannah tayi "Call me by my name Hannah, or any special name u choose, Kasan ita zuciyoyin masoya kaman wireless ne, our hearts and souls are always connected, dan hakazuciyarkace tagayawa tawa zuciyar kana nan shiyasa nazo kuma nayi sa'a nasameka zuciyarka kawai nake bukata Jalal, in har kabani zaka huta da nacina, akasin haka kuwa zan cigaba da hanaka sukuni cikin dare ko rana har sekabani abunda nakeso" Wani wulakan taccen kallo Jalal yai mata ya watsar da ita bece mata komai ba Jawwad ne ya danyi gyaran murya "Kinaji Hannah already Jalal akwai wadda takeson Sa kanwarsa ce kuma kinga..... Dagawa Jawwad hannu Hannah tayi " haba dan uwan masoyina meye laifina anan dan ina kokarin cikawa zuciyata burinta, kowa iya allonsa ya wanke, tayi nata kokarin nima inyi nawa wadda tai galaba ta kafa soyayyarta a zuciyarasa shikenan, ni Hanna babu macen data isa tayi takara dani akan soyayya, Jawwad son danakewa dan uwanka ko matansa hudu sena kori biyu ya aureni saboda space din daya yamin kadan, Kar ace rashin adalcin nawa yayi yawane da se ince seya kori kowa ya aureni saboda shidin nawane ni kadai" Saroro Jawwad yayi yana kallonta "In kagama jin tatsuniyar kazo mutafi inada abunyi" Jalal yafada yana mikewa Hanna ma mikewa tayi tazo gabansa kaman zata shige jikinsa se wani irin fitinannen kamshi take "Babyna kabani dama ko sau dayane in gwada maka yadda nake sonka mana, kuskurewa bukatata shizesa incigaba da uzzura maka har gidanku nasani zaka iya ganina a kowani lokaci, karkayi mamaki nasanka farin Sani a yadda kake a haka nake sonka, zan iya komai akanka, kagayawa kanwarka ta janye kudirinta na sonka ta barmin kai in bahakaba" Ta kashe masa ido daya daga nan tai tafiyarta,p babban abunda yabawa Jalal mamaki dayakasa yimata komai Jawwad ne ya janyo hannunsa suka hau motarsu suka nufi Gida "Jawwad ka yadda mata matsalane, abunda zuciyarsu ta raya musu kawai shi sukeyi, yanzu ga haukan da wannan tayi min, amma zan dau mataki akai" "Kabi komai a hankali Jalal, kasan in mutum yana kan ganiyar so makancewa yake so ba karyane ba, ka dena wulakanta Wanda yace yana sonka kai baka san a ya zaka fara taka soyayya ba, Amma wannan Hannah ka nemi tsari da sharrinta because Dana kalli cikin idonta ya tabbatar da she mean what she said" Haka suka cigaba tattaunawa har suka iso gida Bayan sallar isha'i Jawwad yaje part din Abba ya tarar dashi shi ka dai, yagaya masa abunda ya faru jinjina kai Abba yayi "Hmm Jalila iya rigima, halin mahaifinta ta dakko bata son raini Allah ya kaimu goben, zan San yadda za ayi" Da asuba Abba ya taho kano be gayawa maama abunda ya faruba ya dai cemata zeyi fitar asuba zashi wani guri   Still wannan Daren ma messages din Hannah suka dinga shigowa wayarsa seda yagaji ya kashe wayar Washe gari da safe Jalila ta shirya ta tafi makaranta, Daren ranar addu a ta kwana  tanayi Ba wai Allah ya sassauta fitinar da ta dakko ba, se dai Allah yasa kar Ummi ta korata kano   A hanyar makaranta ta hadu da yayan lubabatu data tsokana ranar akayi Sa a ya ganeta, ta Ganshi sarai amma taki guduwa tacigaba da tafiya a hankali, Zuwa yayi ya sha gabanta "Ke karamar Mara mutunci ni kika zaga ranan ko waike Yar iska" "Wallahi kasake ka tabani sena tara maka jama'a nace zaka lalata ni shekara goma sha hudu ce zakayi a gidan yari bayawa" "Au tunaninki barazanar ki zata hanani in casaki senaga uban da ya tsaya miki" "Bari kaji in gaya maka idan kana shan kwayarka tagaya maka karya kayiwa mutane hauka, to karkayi gangancin gwada kwayarka akaina, Dan wallahi sena kulla maka sharrin dazaka kare rayuwarka a prison" Kafin kace meye wannan Jalila ta ware murya ta fara ihu iya karfinta hankalin jama'a ne yafara dawowa Kansu ana fara taruwa ta silale ta gudu ta nufi makaranta Abunda yasa ta guduma gudun kar takuma shiga wata cakwakiyar bata fita daga wadda take ciki ba ga Ummi tace zata maida ita gidan su Jawwad da setasaka anmasa duka   Tana zuwa ajinsu ta tafi taje gurin zamanta ta hakimce ba tareda ta kula kowaba, "Allah ya biya Queen J Dama tunda yarinyar nan tazo kanta yake hayaki, se wani takama take, malamai ma kaman wani tsoronta sukeji segashi kinyi maganinta" Haka dai seatmates dinta suka dinga zigata ita dai Jalila hankalinta yana kan batun Ummi Bayan anfita break an dawo ba dadewa Hanan ta shigo ajin tana kallon kowa a wulakance ga malami a ajin amma Hanan batabi takan malamin ba ta tako Tazo gaban Jalila "Sannu uwar rashin kunya, dama na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki, Yau zakigane kin taba Yar gidan bullet kizo office bullet yazo da kansa" "Amma kin bani kunya da kikazo da bullet kawai, ai na dauka barikin zaki dakko gaba daya su taho da egwa yadda in sun markadeni baza ageneniba dan dai bullet, ai bullet yayi kadan aga bayana dashi" Jalila takarasa maganar hade da tsaki"nonsense " Mikewa Jalila tayi tai gaba ta wuce hanan Wato Jalila Yar bala'ice babu alamar risina a tare da ita tun tasowar Hanan take taka Wanda taga dama take jefa tsoro a zukatan duk Wanda yai kuskuren shiga hanyarta saboda takamar ubanta wani ne amma yau ta hadu da wadda tafita rashin mutunci Haka ta bi bayan Jalila suna zuwa harabar ofishin director Jalila sukayi clashing da malama ramatu aikuwa Jalila ta tsaya "Ita wutar munafiki ko tana karkashin jahannama ne, Kekam baki dace da malamar makaranta me bada tarbiyya ba kema kina bukatar me baki" Jalila ta gayawa malama ramatu sannan tai gaba abinta Tana shiga office din director ta tarar da mutane ba Wanda ta kula kuma bata kalli suwaye a ciki ba ta shige Share please More comments more typing............. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  20&21 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- "Meyasa kikace kar ya sha" "Nidai kawai kahana shi sha kar ya sha tea din nan" Jawwad ji yayi gaba daya ta firgice masa "Amma meyasa kikace kar ya sha?" Sekuma tarasa mezata ce masa "Am...emm.. Idan ya sha ze iya yin amai gara kaimasa tofi na ayoyin Qurani ya sha kafin kabashi abinci in Bahaka ba, ze iya bashi matsala eh..m.. In...nima malaminmu ne yafada mana a Islamiyya"   Da Jawwad yaji haka da sauri yasa hannu ya karbi cup din tea Daga hannun Jalal Jalal ne ya kalleshi "Meye haka kuma?" "Kanwarka tace karka sha tukuna, Dan huta ina zuwa" "Kaga ni bani yunwa fa nakeji yaushe zan tsaya biye maka yarinya Karama tana juya ka" ya yunkura ze karbi cup din tea daga hannun Jawwad yaji kansa ya kara nauyi dan haka ya koma ya zauna yana jujjuya kan "Sannu bros" Jinjina kai kawai Jalal yayi Kamar yadda Jalila ta gayawa Jawwad yaje fridge ya dakko ruwa ya karanta ayoyin Qurani ya busa masa a ruwan yazo ya tsiyayo a cup ya bashi Hannu yasa ya karba ya shanye ya ajiye kofin, ko minti biyar beyi da shan ruwan ba ya mike ya tafi bandaki ya dinga wani irin bakin amai Jawwad ne ya bishi yana masa sannu ya kwashi mintuna yana amayar da wani bakin abu Seda Jawwad ya Dan tsorata "Jalal mutafi Asibiti your condition is getting worst jin ciwon nan nake kaman a jikina" Ture Jawwad yayi ya tafi ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu ga wani mugun Jiri dayakeyi Jawwad ya biyo bayansa, Dan kura masa ido yayi yaga jijiyoyin kan Jalal duk sun mike fuskarsa tayi Ja Gefen gadon ya zo ya zauna yasa hannunsa akan Jalal yana masa karatun Qurani a hankali Wani baccin wahala ne ya kuma awon gaba da Jalal abun mamaki a cikin baccinsa ya dinga Jin sautin karatun Jalila Wanda ya dinga jin nutsuwa tana saukar masa Jawwad ne ya mike ya nufi gida don tafiya masallaci lokacin salla la'asar yafara gabatowa Cikin Gida ya shiga ya tarar da Nana tana video game maama kuma ta Dan kwanta a akan kujera tana kallon Nana Sallama yayi suka amsa gaba daya "Maama sannu da Gida" "Yawwa ya jikin Jalal din"? "Da sauki maama" "Allah ya sawwake" "Ameen" Ya amsa "Nana babu abunda kika iya se shirme, Jalila tana can tayi abun arziki ke kam shirirtarki ta fiye miki" Attention dinta gaba daya Nana ta bashi "Allah Yaya me Jalilan tayi" "Gasar karatun Qurani sukaje abuja jiya, tazo na biyu, amma se rikici takewa Ummi wai ita na daya take so" "Dan Allah Yaya dagaske amma naji dadi, ga fitina ga kwanya Allah sarki Jalila Allah yakara hasken makaranta" "Ameen kema se ki dage kidena wannan shirmen" Duk abun nan maama bata ce uffan ba   "Amma shine ko ta gayamin amma kai ta gaya maka dani take zancen" Nana tafada tana Dan bata rai "Aini kullum se munyi waya da ita" "Ai Yaya dole muje Kaduna we have to celebrate the victory of my great sister bari Abba ya dawo" Nana tai maganar tana murmushi    "Karki fara, kwata² yaushe ta bar gidan nan kike zancen, wani zakuje to babu inda zaku, nasake naji kin tambayi abbanku zakije sena bata miki rai sha³ kawai, Kaikuma naga zakewarka akan yarinyar nan yafara yawa ka kiyayeni  Jawwad in bahakaba daga kai har ita senaci mutuncinku," Maama ce tayi wannan maganar cikin fada da fushi gaba daya suka bita da kallo Ajiyar zuciya Jawwad yayi ya dan girgiza kai "Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki za a kiyaye insha Allah" Ya Fita yabar parlour itakuwa Nana zunbura baki tayi itama ta barwa maama parlour "Lallai in ban dageba maganar Yaya mairo na shirin zama gaskiya zakuci kaniyarku sena raba Ku da yarinyar nan" Se bayan magariba Jalal ya kuma ta shi wannan karon seya jishi sakayau babu ciwon kan se rashin kwarin jiki Wanka yaje yayi ya rama wasu daga cikin sallolin dabe ba ya bar wasu Jeje ya kira a waya yaji yana ina yagaya masa Kaya ya canza ya dauki motarsa ya bar gidan kai tsaye club din da yake haduwa da Jeje ya tafi kamar kullum yauma club din cike yake da "ya'yan da suka rasa mafadi maza da mata kowa na sharholiyarsa matan nan wasu sunyi shiga half nicked wasu na rawa yayinda wasu suka kama daki suna shagalinsu Jeje naganinsa ya washe baki yana masa sannu da zuwa gaisawa sukayi Jalal yasamu guri ya zauna Jeje ya tafi kawo masa mutuniyar tasa wato giya Duk gigin matan gurin nan basa zuwa inda Jalal yake saboda sun San halinsa basa gabansa shidai ze sha giya yayi mankas amma be yadda yayi zina ba Jeje ne yasamu guri ya kira Hanna " kina ina ne?" "Ina Gida mana" Hanna taba shi amsa "Muna tare da mutuminki fa yanzu haka" "Dan Allah dagaske dazu Dana kirashi abokinsa yace min bashi da lafiya" "Ke dalla rabu da wannan sakaran kilma karya yakeyi" "I wish in samu dama in fito yanzu inzo in ganshi" "Ke rufamin asiri yanzu ma abu zan karbo masa ke dai kicigaba da kokari" "Karka damu kaman yazo hannuna ya gama ne" "That's good seda safe" Sukayi sallama da jeje ya tafi bar domin karbo giya Bayan ya karbo ne yazo ya nemi guri ya zauna ya Tarar da Jalal yanata salansa yana bawa sama hayaki tabarsa kawai yake sha Jeje ne ya tsiyayawa Jalal giya a cup ya tura masa gabansa Wayar Jalal ce ta fara ringing ya Dakota seyaga unknown number seyaki dagawa ya cigaba da abunda yake haka wayar taita ringing "Maza wayarka fa ake kira" Sedayaja wasu seconds sannan yabawa Jeje amsa "Nagani" Dan tabe baki Jeje yayi yacigaba da shan giyarsa Messages ne suka dinga shigowa wayarsa Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din        "Haba fitilar rayuwata         meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby          From your lovely bae" Ire² wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad? Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar "Jalal kana ina?" Jawwad ya tambayeshi "Na dan fitane" "Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe" Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice Jeje ya kalleshi "Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?" "Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri" Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka, Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane² dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai "Naji kaman kinyi bakuwa se anjima" Jalila tayi maganar "Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa" "Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi" Dariya Nana tayi tare da fadin "To Ilham kinji dai sakon Jalila" Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta "Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali" Ilham tai maganar tana mikewa Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar "Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka" Da Sauri Ilham ta kalleta "kamar ya?" "Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi" "Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka" "A'a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu" "Ai nasani" Ilham tabata amsa "Ya akayi kika Sani?" "Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni" Ta karasa maganar cike da damuwa Nana ta dafa ta "Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara" Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa "Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?" "Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane" "Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba" "Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa" "Allah yasa haka Nana" "Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be" Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas akai Jalila tana daki tana gugar uniform zasu koma makarantar boko Ummi kuma tayi bakuwa Jalila taji kaman ana harbe² a waje da sauri ta fito tsakar Gida "Ummi bakiji karan bindiga ba" Bakuwar Ummi tace "Wani captain ne na sojoji yake tarewa a anguwar nan bakiga wani kerarren Gida ba da aka gama kwanan nan ai nasane wallahi gidan ya keru kaman a kasar waje " "To shine kuma za a zo a cikamana kunne da karar bindiga saboda shirme, ni gidan ma nakeso in gani inga iya keruwarsa" "Allah yabaki sa'a kije Neman magana duk yadda zasuyi dake se dai suyi dan ba abunda zan iya indai sojojine zaki yabawa aya zakinta" Ummi tai maganar cikin bacin rai shiru Jalila tayi ta koma daki Jawwad ne yakema Jalal fada akan fitar da yayi daga samun saukinsa Yayinda Jalal ke bashi hakuri "Ai gani dai na dawo ban zauna a can ba hankalinka ya kwanta" "Bawani hankalina ya kwanta kabata min raine ka dinga sassautawa kanka wannan abubuwan dakake durawa cikinka" Hade rai Jalal yayi "naji kuma ina nace kayi hakuri " "Haka ka iya ai saura ka kara fita" Jawwad yayi maganar da alamun gargadi Dariya Jalal yayi "Sorry yayana bazan kuma fitaba a yau insha Allah" Murmushi Jawwad yayi sannan ya fita Bayan fitar Jawwad Jalal ya saka wayarsa a caji ya mike yatafi cikin Gida part din daddy yaje suka sha hira Cikin hikima daddyn yake masa nasiha "Daddy nima bana jin dadin abunda nake amma kacigaba dayimin addu'a wataran zakaga kaman banyiba" "Nima ina fatan hakan yaron kirki" Se kusan shabiyundare Jalal ya fito daga part din daddy shima mummy ce taje part din daddy shiyasa ya fito Ilham tana kwance akan kijerun parlour tana kallon Bollywood Waiwayawa tayi taga Jalal "Sannu Yaya ya jiki?" "Da sauki" Rannan a hade Yabata amsa ya fice Yana zuwa dakinsa ya tarar missed calls kusan takwas Da wannan unknown number din Tsaki yayi yaje yayi wanka yazo ya nemi gurin kwanciya ya dakko wayarsa hotonsa ne da Jawwad akan wallpaper dinsa kallon hoton yayi sunyi kyau a hoton matuka murmushi yayi ze bude what's app dinsa message ya shigo wayarsa budewa yayi     "Haba baby at least ko sau daya yakamata ka dau wayata kasan kuwa yadda zuciya ta takeyi I feel u in my every heart beat, nayi missing innocent face dinka gashi kaki yadda ko muryarka inji help me baeb na damu da kai            From ur lovely Bae" "Wai wannan wace irin Jaraba ce haka, wace ce wannan take Neman yimasa kutse haka a cikin rayuwarsa shi baze iya wannan shirmen ba wannan soyayyar duk haukane da bata lokaci" Yana cikin wannan mitar ne wayarsa kuma takama ringing unknown number din ce dai Dagawa yayi a fusace "Waike wace irin mahaukaciyace karfe nawa yanzu nibana wannan haukan ki kyaleni tun kafin ta kaimu ga bata miki rai"            "Wow komai naka birgeni     yake baby jin muryan nan taka kawai ta isheni bacci me dadi, Mark you ba abunda zakamin Wanda ze batamin rai Love u....... Katse wayar yayi ya kasheta gaba daya ya jefa wayar kasa nonsense yafada a hankali Washe gari bayan sallar asuba Ummi taga Jalila ta koma bacci " ke baby ba ankoma school ba kwana biyu da komawa amma kina nade a Gida tashi ki shirya yau makaranra zaki tafi" "Ummi bangama shiryawa ba in nagama zan koma" "Aikuwa sekin koma yau din nan" "Ummi bani da socks fa, kuma ni sekin canzamin school bag zan koma" "Kibari inzo gurin nan baki tashi kinyi shirin makaranta ba ni da kene" Ummi ta fita daga dakin Ummi na fita Jalila tacigaba da baccinta har kusan karfe bakawai Ummi tazaci Jalila ta tashi amma tana zuwa ta tarar da ita a cikin bargo Ran ummjne ya baci ta yaye bargon ta Dala mata duka tashi dan kaniyarki dama baki tashi ba tashi kisa uniform kitafi "Ummi dan Allah kiyi hakuri,  banga socks dina bane" Girgiza kai Ummi tayi "Allah ka shiryamin yarinyar nan, ai tunda baki gadama ba nasan bazakiba zakiga tsiya" Wunin ranar Sam Ummi taki kula Jalila Ta dinga binta tana bata hakuri tana mata magiyar ta saimata wata jakar daga karshe seda Ummi ta bata kudin Jaka da socks din hankalinta ya kwanta Amma Ummi tace bazata fita ba seda yamma Washe gari se bayan sallar la'asar sannan Jalal ya kunna wayarsa amma yana kunnawa sakonine sukacika masa waya wasu na bin wasu "Wannan wane irin Jaraba ce haka" Sakonta na karshe ya duba  "Baby in baka bude wayarka    ba zanzo har inda kake, tun safe nakasa nutsuwa ko har yanzu baka da lafiya ne? Na damu da kai baby          From your lovely Bae" "Wannan wace irin Jarababbiya ce da take uzzurawa rayuwata ne" Yana cikin wannan tunanin Sega Ilham ta shigo da kayan abinci ta samu guri ta ajiye "Yaya ga abinci inji mummy Harta mike zata fita ya kira sunanta "Ilham" "Na'am" "Zo nan" seda cikinta yayi kara gabanta ya fadi Allah yasa ba wani abun nayi masa ba jiki a sanyaye ta nufi inda yake guri ya nuna mata kusa dashi ta zauna wayarsa ya dakko ya shiga messages din nan ya nunamata "Ke kike turomin wannan shirmen ko?" Gabanta ne yafadi ita ba tuhumar dayake matane ta sata faduwar gaba ba se fargabar wace wannan take shirin yi mata kutse "Tambayarki fa nake" Jiki a sanyaye ta daga kai ta kalleshi "Bani bace ba" Jawwad ne ya shigo "Inyee yau zumunci ake jine Yaya da kanwa" Basu kulashiba ya karasa ciki ya zauna yaga ran Jalal a bace Yana ma Ilham magana "To waye?" Jalal Ya tambayeta "Ya za ayi in sani yaya, nidai nasan bani bace" Tabashi amsa hawaye na gangarowa daga idonta "Uban me na miki zakimin kuka" Wani irin kallo tayi masa "Yaya Jalal tambayata kake meyasa nake maka kuka ko? Ina nuna kulawata akanka, baka damu dani ba bakajin me nake ji a raina hasali ma ka tsaneni, amma wata a waje tana shirin rusani ga sakonin da take turomaka, kuma kake tuhumata ni ina naga fuskar da zan turo maka wannan sakonnin " Cikin hargowa ya mike ze zazzaga mata bala'i Jawwad ya ga tsananin kishi kwance a idon Ilham, tausayinta ne Yakama Jawwad dan haka  ya dakatar dashi "Ilham gaskiya ta fada Jalal" Jawwad Ya kalli Ilham yace "Tashi kikoma ciki" Sannan ya kalli Jalal Yamma nayi  Jalila ta shirya ta dau kudin safa da Jakarta tayi waje Kai tsaye inda ake fadan gidan sojan nan ta nufa daga waje ta karewa gidan kallo Aranta take fadin gaskiya gidan nan ya hadu saura kuma inshiga inga meye a ciki yadda ya hadu daga wajen nan cikin kuma ai nasan yafi haduwa Daga nan ta mika ta nufi inda zata sayi jaka amma seta hango wani kanti da sojoji a bakin gurin dan haka ta yanke shawarar zuwa taga meye akeyi a gurin Kai tsaye ta kutsa cikin kantin wani soja ne ya daka mata tsawa yace ta tsaya a waje se sungama sun tafi tukuna "Dan Allah kabari abu zan siya kawai in tafi ni ba gurinka nazo ba " Zekuma magana wani sojan yace ya batta ta shiga Tana shiga taga wani babban mutum a zaune akan kujera fuskar nan tashi murtuk babu annuri "Ina wuni" Jalila ta gaisheshi be amsa ba "Baba gaisheka fa nake nace ina wuni" Dan juyowa yayi ya kalleta ya danyi murmushi jin takirashi da baba "Lafiya kalau sannu yan mata" "Yawwa" Ta sai chocolate dinta ta mutumin nan yace abawa Jalila shize biya Seda ta risina sannan tace "Baba nagode sosai" "Bakomai adinga shan chocolate din a hankali yana kashe hakori" Murmushi Jalila tayi ta  fito "aikin banza na daukama wani abun ake a gurin to me sojoji suke anan ko gadinwa suke oho" Ta siyo Jakarta ta fito dayake kusa da kantin ake saida jakunkuna ta hangi mutumin dazu ya fito daga kantin nan ze shiga mota se ya yadda wallet dinsa da sauri ta je ta dauka, amma tuni sunyi nisa sun bar gurin sun nufi layin gidan wannan sojan Ta dinga jujjuya wallet din nan kawai ta tafi Gida da wallet din Bata nunawa Ummi ba ta boye wallet din Ta faki idon Ummi taje ta dau wallet din ta bude kudin kasar wajene a ciki da ID card bata tsaya bin ta ID card dinba ta aje wallet din cikin sabuwar jakar makarantar ta cikin litattafanta Washe gari Ummi ta tursasata ta shirya ta tafi makaranta, ta wannan layindai na gidan nan Jalila tabi dan takuma ganin gidan nan kuma ko Allah zesa taga mutumin nan Tanata kallon gidan wani soja ya kalleta "Ke me kike kallo wuce ki tafi makarantar ki" Ya mutsa fuska Jalila tayi "Ina ruwanka da makaranta ta?kallo kawai zanyi in tafi" "Ba a son yawan ganin mutane a arear gurin nan saboda tsaro dan haka wuce ki tafi" "Did I look like criminal, da uniform dina na makaranta balle kace wani abun zanyi, sekace gidan shugaban kasa naga dai gidan mutum ne ba aljan ba in me gidan yasan bayaso a dinga wucewa ta hanyar gidan ai da seyaje duniyar wata ya Gina gidan ba duniyar mutane ba" "Kut wace irin yarinya ce wannan?" Aikuwa sojan nan beyi wata² ba ya zare beilt da nufin ya koya mata hankali se su kaga wasu motoci suna shigowa Latin manyan motoci ne glasses din duk tint ne mutumin jiya da ya sai mata chocolate ne ya fito daga daya daga cikin motocin Wannan sojan da ya zare belt ne ya kame yana saramasa da ido yai masa magana sojan ya tsaya "Laa baba ina kwana" Jalila ta tsuguna tana gaisheshi "lafiya kalau Yar baba, meyahada ki da wannan" Ya nuna mata sojan nan da ya biyota Bata boye masa komaiba ta gayamasa murmushi yayi a ransa yace lallai wannan yarinyar Yar rigima ce amma a fili yace "Yar baba yanzu kin makara ki tafi makarantarki rabu da shi Kai baka ganin Yar makaranta ce kawai daga kallon Gida se a ce za a bigeta ina nema mata afuwa" Jalila tasaka hannun a Jakarta ta dakko wallet din nan ta mika masa "Jiya ka yaddashi bayan kafito daga kantin nan" Hannu yasa ya karba tasan ce kuwa yana ta dubawa tun jiya be ganta ba yayi zaton yayi miss placing dinta ne Murmushi yayi "nagode sosai Yar baba Allah ya albarkaci rayuwarki " "Ameen nagode" Ta juya ta tafi hanyar makarantar su ta makara sosai amma taci sa'a ba malami a ajinsu dan haka ta shige tanufi ajinsu Class dinsu ne ya kaure da hayaniya ga Queen ta dawo nickname dinta kenan a makarantar boko Queen J Kai tsaye bayan sungama murnar ganin juna da yan ajinsu gurin zamanta ta nufa amma me setaga wata hakima ta hakimce mata a seat Jalila dai bata Santa a ajinsu ba maybe newcomer ce dan haka Jalila tace "Sannu dai excuse me gurin zama nane ina bukatar zan zauna" Banza yarinyar tayiwa Jalila "Ko kurma ce ne? Nace kifito nan gurin Jalila ne fada tace" "Wallahi mun gaya mata har malamai sun San nan gurinkine amma tace ita kuma dole anan zata zauna" Cewar wata daliba Ita kuwa sabuwar zuwan nan bata da niyyar magana balle Jalila tasa ran zata tashi sema wani kashingida tayi ta kurawa Jalila ido tana hura hanci tana kallon Jalila up and down "Ke yau kome kikeji zan sauke miki shi yau koda uban me kike yawo wallahi sekin bar seat din nan uwarkice ni a rashin mutunci" Dariya yarinyar tayi "ok yi abinda zaki iya nikuma na miki alkawarin kawo karshen rashin kunyarki a yau base gobe ba" "Queen J dan Allah kiyi hakuri ki kyaleta babanta fa babban sojane ranar Monday aka kawota" Wata dalibar tai maganar tana kokarin Jan hannun Jalila dukan benci Jalila tayi "Wallahi ko Yar gidan bullet ce, ke Allah yasa baban tane AK47 wallahi seta tashi this is my kingdom, in ubanta ya tsaya mata ni Allah ya tsayamin, Kafin kiyi maganina ni zan fara maganin wannan izzar taki, ko kina wa kowa hauka ba ayiwa Jalila" Hannu biyu Jalila tasaka ta fizgo yarinyar nan daga cikin benci aikuwa yarinyar nan ta wankawa Jalila mari, Wasu daga cikin dalibai suka tafi kirawo malamai domin raba fadan nan Amma tuni Jalila ta rama marin nan ta kara mata wani, Jalila ta dage ta hankada yarinyar nan kan bencina nan take goshinta ya fashe jini yashiga fita Share please More comments more typing....... Proud of you my fans INA jin dadin adduoinku nagode kwarai Allah yabar kauna ❤❤❤❤❤ Team JALILA kunga abinda yau ta dakko to ni ba ruwana😎😎 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊 [9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  24 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢 Your comments give me courage               -My First Novel- Not Edited Yayan Hanan se kallon Abba yake kaman yasan shi. Tunda Jalila ta shiga office din taje tasamu guri ta durkusa kanta a sunkuye kai kace wata mutumiyar kwarai ce Ga director na makarantar, ga Ummi, da Abban su Jawwad, sekuma baban Hanan da yayanta, se mukarabbansa da suke waje bakin office din sekuma Jalila da hanan dasuka shigo yanzu Baban Hanan Bin Jalila yayi da kallo sannan yayi Murmushi a zuciyarsa indai wannan ce zata aikata don bata da tsoro Kanta a sunkuye tace "Abba ina kwana" "Lafiya kalau Jalila ya rashin ji"? Shiru tayi ba tace komaiba "Abbanki kawai kikasani ko Jalila,?" Director ya tambayeta batace komai ba still shiru tayi "Was nake gani haka kadai ace Yar baba ce wannan?" Da sauri ta dago ta kalleshi dan murmushi tayi se yanzu ta ganeshi mutumin nan ne daya hana wannan sojan zaneta, Wanda ta tsinci wallet dinsa "Sannu baba ina kwana" "Lafiya kalau Yar baba" "Dake akayi fadan kenan, dama haka kike da fada, ai wannan sister dinki ce" ya nuna hanan "Ni ba sister na bace nikadai Ummi ta Haifa, se kanwata daya Nana" Jalila tai maganar ba tare data dago ba Dariya tabasu gami da mamaki babu nadama a tare da Jalila ita haryanzu a ganinta ba laifi tayiba tunda ita aka takala da fada "Daddy wai kasantane"? Yayan Hanan yai tambayar yana kallon mahaifinsu "Eh nasanta 'yata ce shekaranjiya Allah yabani ita" Baban Hanan yabada amsa Ya kalli Abba da Ummi "Ai Dana San itace ma bazanzo ba yarinyarku mutuniyar kirkice, fitina CE kawai ta yara kuma ga dukkan alamu bata son wargine ko Yar baba?" Ya tambayeta yana murmushi "Komai ya wuce amma Yar baba kidena Neman magana kinji yarinyar kirki kin dagawa mamanki hankali da babanki, gaskiya suna sonki dayawa" Gyada masa kai Jalila tayi "To baba na dena insha Allah" A ranta kuwa tace dama wai wannan shine captain din da ake ta fada wani salihi dashi haduwar mu biyu be tabamin rashin mutunci irin na sojoji ba Ni na daukama zanga tunda ga bakin office anfara kwallo dani "Daddy wai yanaga ka maida abun jokes jini fa ta fitar min kuma ta zageka" Hanan tai maganar cikin shagwaba da hawaye a idonta "Ohh sorry dear itama yata ce daga yau na hadaku kawance" "What ba dai dani ba wallahi, Allah ya kiyaye" Hanan tai maganar cikin tsiwa "Baba nikuma na karbi kawancen nagode sosai daga yau tazama kawata" Jalila tai maganar tana murmushi tare da kallon hanan "Allah yayi miki Albarka Yar baba" Abun ya daure musu kai yaushe mutumin nan yazo anguwar amma har yasan Jalila gaskiya a sojojin ma yana da matukar kirki, gaba daya kasa cewa komai sukayi "Daddy ni gani nayima tana kama da Hanan wallahi" Yayan Hanan ya fada yana kuma kallon Jalila "Nima nagani Abdallah" "Kinsan Aliyu Usman Imam" Yayan Hanan ya tambayi Jalila Dagowa Jalila tayi ta kalleshi "Kai Yaya Jawwad kake nufi ga Abbanmu nan" ta nuna masa Abba "no wonder naga suna kama kuma ance  shine abbanki shine class ref dinmu a BuK yana da kirki ga kokari amma gaskiya shi ba fitinanne bane kamarki" "Waze hada ma shi Jawwad yaron kirkine kaman ma ba  sunansa Aliyu ba amma wannan sekace kura saboda fada" Ummi tayi maganar tana nuna Jalila "Dan Allah kuyi hakuri bazan karaba Insha Allah" Takoma gaban Abba shima ta tsuguna " Abbana Dan Allah kaima kayi hakuri nadena insha Allah, Dan Allah kuyi hakuri" Kara birge baban Hanan tayi tasan tayi laifi kuma ta bada hakuri, ita damuwar iyayenta ce bata so yaji inama Hanan ce keda wannan tarbiyyar tayi laifi tabada hakuri ai sedai in kaga dama ka kasheta ko ka barta da rai amma bata laifi ta bada hakuri indai Hanan CE Director ko a ransa yace lallai wannan yarinyar ita fushin iyayenta ne a gabanta bata damu data bawa su Hanan hakuri ba suda akayiwa laifi a fili kuwa yace "To Alhamdilillah tunda itama 'yarka ce mungode da wannan karamci naka yallabai, Kamar yadda ka fada Jalila yarinyar kirkice saboda a dalilinta makarantarmu tasamu awards, tana da kokari ga hazaka, muna alfahari da ita a cikin dalibai, ita babba damuwarta ita da dalibaine, shima kuma insha Allah daga wannan shikenan tace bazata karaba" Director yayi maganar yana kallon Captain Abdurrasheed "Hakane dama dan Adam Tara yake be cika goma ba, muna kara bada hakuri dai ayi hakuri" Abban Jawwad ne yai maganar yana kuma kallon baban Hanan Itakam Jalila bataga dalilin bada hakurin dasu Abba suke tayi ba "Karku damu ba komai yariga ya wuce ai, Allah ya shiryamana yara gaba daya, yayi musu albarka" Suka amsa da Ameen gaba daya Haduwar da akayi domin hukunta Jalila da yin sasanci se yakoma haduwar hada zumunci inda hira ta barke a office din director Malaman da suke ta jira suga an fara casa Jalila se sukaga akasin haka Daddyn Hanan ne yagaya musu yadda yasan Jalila daga ranar da ya saimata chocolate zuwa tsintar wallet dinsa, har exchanging lambar waya captain yayi da Abba, sukayi sallama kowa ya watse Ummi ta saka Jalila a gaba Abba ya dauke su zuwa Gida "Impossible wallahi a fitarwa da yata Jini sannan kace wai ba komai ka kyale yarinyar ta daki banza akan me? " look safiyya shi da na kowane, kinsan halin Hanan sarai itama wani lokacin ta fiye fitina, da wulakanta mutane, for now ayi hakuri na rufe wannan case din" "Aikuwa be rufu ba ni a gurina, dan mene Za a daukarmin yarinya sannan kace ka rufe case, waye uban yarinyar da yatsaya mata ta dokarmin yarinya" "Ohhh my God mum Abdallah kinfiye rikici fa, wallahi ba Yar wani bace ba kawai dai she's so kind, yarinyar and she regrets what she did, ni yarinyar ma tausayi tabani wallahi mamanta duk ta damu, gashi kuma kanwar abokin Abdallah ce" "Kaga ya isa haka bana bukatar jin wani abu ya isheni haka, ko uwar abokin Abdallah ce senasa an koyamata hankali balle wata kanwar aboki, in kai ka hakura ni ban hakuraba wallahi... " Enough " Ya daka mata tsawa nan take ya juye ya koma sojansa fuskar nan kaman be taba dariya ba "Idan kika kuskura kikayi wani abu akan yarinyar nan kinsan meze biyo baya kinsanni sarai" Yayi maganar cikin tsawa sannan ya fice ya bar mata dakin "Wai Jawwad meyake damunka ne tun dazu ka kasa zama, ka kasa tsaye se zagaye kakeyi" Jalal ne dake kwance akan gadon Jawwad yai maganar yana kallon Jawwad "Ta yaya zan iya zama bansan wani hali akeciki ba ko sojan da Jalila ta dakarwa yarinya ya hakura, bansan me ake cikiba nakira wayoyinsu gaba daya basu daga ba Allah yasa dai lafiya, Allah yasa basuyi mata wani abun ba" Jawwad yai maganar cikin damuwa Dariya Jalal yayi "to meye abun tada hankali in suka karairayota se ka tafi Kaduna jiyya" Jalal ya karashe maganar yana dariya Tsaki Jawwad yayi Wanda yayi dai² da ringing din wayar Jawwad Da sauri ya dakko wayar yadaga a zatonsa Abbana "Hello hey Aliyu yakake" "Ina lafiya Alhamdilillah , amma ban gane me magana ba" "A Rasheed ne" Aka bashi amsa "Ohhh Abdallah ban dauki muryarka bane, kuma bani da wannan lambar taka" "Wallahi kuwa na canza layine" "Allah sarki ya kake ya mutan gidan" "Kowa lafiya Alhamdilillah, yau naga kanwarka" "Kanwata wacce kenan ai Nana tana kano" "Ba itaba wata Jalila" Gaban Jawwad ne yafadi "A ina kaganata ya akayi kasan kanwata CE?" "Sabani suka samu da Hanan mummy ta daga hankalinta mukaje nida daddy, har muka hadu da abbanku" Ajiyar zuciya Jawwad yayi sanan yace "Alhamdilillah Abdallah ya ake ciki Dan Allah kuyi hakuri kabawa daddy hakuri," "Karka damu, ai ba abunda yafaru daddy yace "yarsace itama, kanwartaka ce Yar daruce Aliyu bata da tsoro" "Nagode sosai Abdallah," "Ba komai Aliyu, nima kanwata CE, kuma wani abun mamaki suna matukar kama da Hanan din" "Allah sarki Dan Allah kayimin godiya agurin daddy" "Ba komai Aliyu girmankane " Sukayi sallama, nannauyar ajiyar zuciya Jawwad yayi tare da fadin "Allah gatan bawansa, kaga abun mamaki Jalal, Allah ya tsallakar min da baby, basuyi mata komai ba, Ashe kanwar abokina CE sukayi rigimar da ita, kanwar A rasheed CE yarinyar" Dariya Jalal yayi "U escape this time around, se Ku kiyayi gaba, Dan ba kullum ake kwana a gadoba" "Eh munji, for now we are safe, se dariyarka ta koma ciki" Jawwad yayi maganar yana kallon JALAL yai murmushi tareda shafa sumarsa Jalila CE da umminta se Abban Jawwad a parlour "Inaga lokaci yayi dazaka cika wasiyyar mahaifin JALILA, ka dauketa ta koma gabanka, nima in koma Gida, JALILA ba ta jin magana, kullum cikin Neman magana take, bataji Sam abunda zuciyarta ta raya mata shi takeyi, ayi mutum ba hakuri kullum cikin Neman magana" "Haba ummina tun jiyafa nake baki hakuri ashe baki hakura ba Nace fa bazan kara ba" Jalila tayi maganar idonta taf hawaye "Yi min shiru bazan hakuranba, ke banda Allah yasa mutumin kirki ne baban yarinyar nan da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, Ke ba Yar uban kowa ba, amma har kina ikrarin ko Yar gidan bullet ce ko, Kanaji har wallet ya Yar ta dauka, da sunyi bincike suka ganota a gurinki sunanki barauniya, wannan halin naki in kika cigaba a haka to wahala zaki sha, ayi mutum fada kaman kura" Abba ne ya nisa ya danyi murmushi sannan yace "Haba ummu Jalila, babynki fa ba haka kwai takeyiba, Kin manta marigayi shima haka yake baya daukar raini, gashi na jama'a kinfi kowa sanin halinsa ba wasa" "Amma be kai wannan yarinyar ba, JALILA fa da kudinta seta saka ta sai rigima koda uban waye, Duk rigimar Abu Jalila mutumne simple kuma yana da kawaici, amma ita sun raba hanya da hakuri" "Ummu Jalila kenan kin manta biyuce ta hadarwa Jalila, kefa jinin sarauta ce akwai wannan izzar ta sarauta a jikin Jalila, haka zalika mahaifinmu, babansa shine sarkin Fulani a rigarsu, kinga ba yadda za'ayi Jalila ta yadda, da raini Jinin sarauta na zagayawa a jikinta Mikewa Jalila tayi ta bar dakin ta koma dakinta ta kifa akan katifa tana kuka, bataji sallamar Siyama ba saboda kukan da takeyi se kawai ganinta tayi a gabanta, dafa Jalila Siyama tayi "Aminiya meya faru? Garinya haka ta faru a school? Jiya da yau banjeba bana jin dadi dazu ake gayamin abunda yafaru tsakaninki da hanan nasanta babanta abokin Abba ne Sam bata da kirki Yar gadarace" Siyama tayi maganar cikin damuwa "Kinga ni ba itace agabana ba Aminiya kinji wai Ummi sena koma kano gidansu Yaya Jawwad nikuma wallahi bazan komaba bana son zaman garin nan" "To aminiya saboda me? Meye a ciki Dan kin koma?" "Au haka zakice ko? Dama ba kya sona, hmm Dan bakisan abunda dangin Maman su Nana din nan sukemin ba, ga wannan mugun abokin Yaya Jawwad din, Siyama bana son rabuwa da Ummi wallahi tun jiyafa nake bata hakuri amma taki hakura yanzuma zancen takeyiwa Abba fa" "Ki kwantar da hankalinki aminiya, nasan kawai dan kin bata mata Raine amma bazata bari kikoma yanzu ba" Mikewa Jalila tayi ta dakko wayarta ta fara kiran wayar Jawwad Lokacin Jawwad ya tafi masallaci yabar wayar a dakin Dan haka Jalal ya duba wayar cwt sisy ya gani akan screen din wayar Tsaki Jalal yayi, ya daga wayar amma yayi shiru bece komai ba "Yayana dan Allah ka kira Ummi kabata hakuri, tun jiya nake bata hakuri amma taki hakura, tace sena dawo kano, dan Allah yayana, ka tayani bata hakuri maybe kai inka bata hakuri ta hakura wallahi nadena sata magana, bazan iya rayuwa babu ita ba " Tai maganar cikin sheshshekar kuka Bece komai ba ya kashe wayar "Fitinanniya kawai yanzu ma kin kira danki kuma daga masa hankali, shikuma duk yabi ya wani rude ya biyemiki, kina son ummin kike daga mata hankali " Yai maganar cikin mita bayan h ya katse wayar, kuma kira Jalila tayi amma yayi rejecting kiran ya kashe wayar gaba daya, Jalila ta dubi Nana "Nana Yaya Jawwad yayi fushi dani, yaki cewa komai, kuma ya kashe wayar Sa" Share mata hawaye Siyama tayi "Calm down Aminiya, seta yiwu beji dadin abunda kikayi bane, amma shima ze huce" Abun duniya duk ya ishi Ilham tarasa abunda yake mata dadi gaba daya wani mugun kishine yake damunta akan Jalal, se yanzu take tabbatarwa kanta tafada soyayyar Jalal fiye da yadda take tunani, Dan haka bayan an tashi daga makaranta gidansu ta wuce taje tasakawa maminta kuka ta gaya mata abunda ke faruwa "To kekam meye na damuwa duk kin daga hankalinki kalli yadda kika rame fa, naga dai Soyayyar ta wucin gadi ce burinmu na cika shikenan" Mami a gurinki ce soyayyar dan lokaci ce se yanzu nagane dagaske soyayyar Jalal ta Huda zuciyata bana tunanin zan iya rabuwa da shi ILHAM tai maganar a zuciyarta A fili kuma tace "Mami duk da soyayyar wucin gadi ce amma kuma in shirinmu ya rushe fa?" "Inkinga shirinmu ya rushe to sakacinkine, indai kika dage komai zezo dai² da yadda muka tsara, kedai kicigaba da amfani da magungunan danake karbo miki, sannan duk abunda zemiki na wulakanci kidena fushi kici gaba da binsa, Randa ya shigo hannunmu kuma" Bata karasaba se wani Murmushi da mamin tayi "Kiyi kokari ki gane wadda take turamasa sakonnin, itama zamuyi maganinta" gyada kai Ilham tayi cike da kwarin gwiwa, Aranta tace "da kaina zanyi maganin ko wace, Jalila kinyi gangancin fara soyayya da abunda nakeso zakiga tsiya"(nikam nace Allah sarki Jalila bata San anayi ba) Haka Ilham ta shirya ta nufo hanyar gida, harta wuce part din Jalal kawai ta dawo ta nufi hanyar part dinsa tana zuwa kofar bedroom dinsa ta tsaya tana tunanin me yakamata tayi Shikam Jalal Yana kashe wayar Jawwad shikuma tasa wayar tafara ringing lamba ce amma ba suna dan haka beyi tunanin komai ba ya dauka "Oughhh baby tun safe banji muryarka ba ina kewarka sosai A ina zamu hadu ne please, am missing you so badly, said something please, ko muryarka inji mana" "Waike wace irin mace ce Mara kamun Kaine? Ki rabu dani nagaya miki meyasa kike min shishshigi ne bana son yi miki rashin mutunci fa"   Wani murmushi Hannah tayi cike da kissa ta kara kashe murya cikin shagwaba tace   "Babyna komai zaka kirani dashi fa bazanji haushi ba, ni komai naka burgeni yake, ko da zakamin duka ne a gaban jama'a, I wish halinku daya Da Jawwad da komai yazomin da sauki, nasan da shine ze tausayamin halin danake cikin amma a yanzu ma karkayi tunanin zan karaya, yanzu ko ka fadamin inda kake ko inkira Jawwad in tambayeshi, kuma ko inane biyoka zanyi" "Karki fara Jawwad daban ni daban, Jawwad ne yake lallabaki, kuma shi yahana tun farko in nuna miki waye Jalal, kishiga hankalinki, wannan shine gargadina dake na karshe Ilham dake bakin kofa kuwa daskarewa tayi Ya tabbata Jalila ce Wato dama Jalila ce kenan, itace take son Jalal take turo masa messages haka, gashi yana cewa yana kyaleta saboda Jawwad, lallai Jawwad ma munafiki ne Wani baking kishine ya ciwota Bata San lokacin data karasa dakin ba tasa hannu ta fizge wayar daga hannun Jalal tayi jifa da ita tana wani irin huci wayar ta tarwatse a gurin Share please More comments more typing.................. My group members inajin dadin comments dinku da addoinku nagode sosai Allah yabar kauna 🌹🌹🌹🌹 Kuna comments ina muku typing💃💃💃 Kuna bari ina lalaci 🥱🥱🥱😉😉 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  25 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa Dama dukkan masoya wannan novel ina alfahari daku ❤❤❤               -My First Novel- Not Edited Kallonta Jalal yayi da mamaki ya kalli inda Ilham ta tarwatsa masa waya ya dawo da dubansa kanta "Baze yiwu ba Yaya Jalal, kana wahal dani kana garani kawai dan nace inasonka amma kalli yadda wata take bayyana maka soyayyarta baka dau wani mataki ba amma ni kalli yadda kake wulakantani sau daya baka taba kallona da idon tausayiba Meye laifina dan nace ina Sonka?" Shi mamakima ya hana shi magana be ce mata kala ba ya durkusa yana tattara pieces din wayarasa, ya tattara ya nufi waje ze bata guri tazo ta sha gabansa "Magana fa nake maka Yaya Jalal, let me tell you something wallahi kai nawane ni kadai babu wata Jaka data isa tayi takara dani wallahi kowace sena kauda ita gefe" Hawayene ke fitowa daga Idonta wani irin kallon baki da hankali yayi mata ya kuma zagayeta da niyyar ya fita Janyo shi tayi takuma tsayawa a gabansa ta kalleshi ido cikin ido cikin masifa tace "Jalal baka isaba ina magana ka maidani mahaukaciya zaka tafi ka barni, I mean what I said wallahi, zan iya komai akan cinma burina, gara tun wuri ka gargadi zuciyarka kattayi gangancin fara soyayya kaidin nawane" Bata rufe baki ba ya sauke mata maruka biyu masu kyau, "Har kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin maganganun dakika ga Dama, kin fasamin waya na kyaleki be isheki ba shine zaki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama ko yaushe ma nafara wasa dake, da kika iya tsayawa kina gayamin wannan haukan," "Wallahi kozaka kasheni na dena boye soyayyata a gareka koni ko ita wallahi" Hannu yadaga ze kuma marinta "Jalal meye haka kakeyi" Jawwad ya karaso da sauri ya rike shi "Haba Jawwad ba girmanka bane dukan mace, me tayi maka haka, kake dukanta" Dawo da kallonsa yayi kan Ilham "Ilham koma cikin Gida yi hakuri banni da shi tashi kikoma Gida" Wani mugun kallo tayiwa Jawwad a ranta tace munafiki ai kasan komai amma a zahiri ta mike ta nufi cikin Gida tana kuka "Haba Jalal me kayi hakane abunda kakewa Ilham yafara yawa gaskiya, koba komai kanwarka ce kuma mace ce, kadena dukanta hakan baze canza komai ba Fa" Nunawa Jawwad wayarsa yayi "Kalli abunda tayimin be isheta ba, ta tsaya a gabana tanamin hauka" "Dukda haka kadinga hakuri, halin mata sekana hakuri, kasan shi so makahone waima tukuna, waima ya akayi wayarka taje hannunta har hakan tafaru?" "Mtseww manta kawai" Shine abunda Jalal ya fada kawai ya bi hanyar fita waje Itakuwa Ilham tana zuwa cikin gida taga mummy a palour jikin mummy tafada tana kuka "Ilham lafiyarki kuwa me akayi miki kike kuka,?" "Mummy Yaya ne baya sona kwata² ya tsaneni, ni kadai nake sonshi mummy kiyi wani abu akai Dan Allah, zuciyata zata fashe" Tausayinta ne Yakama mummy "Is OK my dear, yi hakuri kidena kukan, Insha Allah Jalal bashi da matar data wuceki insha Allah, komai ze wuce" "Mummy me nayiwa Yaya Jalal ne dabaya kaunata baya so naje inda yake" "Bikiyi masa komai ba Ilham, haka dai halinsa yake na rashin son mutane, ya za ayi yace baya son mace kamarki, karya yakeyi, kidena kukan haka kar kanki yayi ciwo" Haka mummy tai ta kwantarwa da Ilham Hankali Maman Hanan ce hakimce akan kujera dauke da remote a hannunta, yayinda Hanan ta kwanta akan cinyarta tana kallon TV Sallama Abdallah yayi yayan Hanan Sannan yasamu guri ya zauna "Da girman kujerarki mum barka da Gida" Ya mutsa fuska tayi ta nisa " "Yar uban waye ta dakarmin yarinya kunje kaida daddyn Ku amma ba wani mataki daya dauka, waye ubanta a garin nan" Kallonta Abdallah yayi da mamaki "Ohh I think dad has already closed this case, meyasa kike kokarin dawo da maganar nan, an sulhunta komai" "Dalla yimin shiru, a gurina be wuce ba tambayarka kawai nayi Yar inace waye ubanta?" Tai maganar cikin fushi "Amm Mum Dan Allah kiyi hakuri zancen nan ya wuce wallahi kanwar abokina CE, kuma mum dinta tabada hakuri sosai, tundaga kano Wan babanta ya taho yau duk Dan subada hakuri fa, to mu suwaye daba zamu hakura ba" "In kaga ma yimin nasihar tashi kabarmin parlour" Be kuma cewa komaiba ya fice Hanan ce takuma fashewa da kuka "mummy ciwon zafi yakemin kaina se ciwo yake wallahi ni ban hakura ba" Tayi maganar tana kuka "Yi shiru mana sannu, nima ba hakuran nayiba ai, ai jininki baze zuba a banza ba nasan matakin dazan dauka" Abbane ya fito ze tafi, Jalila tafito da sauri daga dakinta tana kallonsa domin jin wani hukunci aka yanke akanta Siyama ce tabiyo bayanta itama "To se yadda ta yuwu, ummu Jalila ki hada mata kayanta in Allah ya kaimu sati me zuwa koni ko Jawwad zamuzo mu tafi da ita, tunda bata jin magana" Abban Jawwad yayi maganar yana kallon Ummi Kuma fashewa da kuka Jalila tayi "Ummi nace na dena fa bazan kuma ba Dan Allah kiyi hakuri" Girgiza kai Abba yayi "A a senaga kindena din tukuna, a yanzu dai ban yaddaba zuwa sati me zuwa insha Allah in kin canza halinki, shikenan ta fiya kano bayan zuba" Gyada kai tayi tana goge hawaye itakam Ummi banza tayi mata taki kulata "Abba insha Allah bazata karaba ta dena" Cewar siyama "Anya kuwa wannan kawar taki batta kawai akwai rashin ji" Abba yafada yana nuna Jalila Haka Jalila ta cigaba da kuka tana magiya akan suyi hakuri Abba yayi musu sallama ya koma, kano yayinda still Ummi taki kula Jalila Abun duniya ya ishi Jalila, Jalila tayi trying lambar Jawwad har tagaji amma akashe "Haba Yaya Jawwad kaima Fushin kake dani haka, shikenan kowa ya tsaneni" Haka dai Jalila ta cigaba da sake² aranta tana kuka Hannah ce take ta trying lambar Jalal taki shiga tayi messages din ba adadi amma shiru Layin Jeje ta kira "Da girman kujerarki, gimbiya sarautar mata farar mace Alkyabbar mata, Zara acikin mata, daya tamkar da goma, tauraruwa me wutsiya ganinki ba alheri ba" Murmushi Hannah tayi da jin wannan kirari da jeje yake mata "Jeje ya akayi ne dazu muna cikin waya da Jalal naji ta dauke nayi trying tun dazu wayar bata shiga" "Wow har ya fara yadda ya amsa wayarki kice tarkon ya fara kamashi" "Ina fa da sauran aiki Ja wallahi, shammatarsa kawai nake naji ya daga wayar, yanzu dai yana ina ne?" "Nima bansan inda yake ba rabona dashi tun last week, wannan mayen ya hanashi zuwa inda nake" "Allah sarki simple dashi abokin nasa da akansa zanyi aikin nan da yanzu nakusa nasara, shikam taurin Kaine dashi" Dariya jeje yayi "Lallai baki San Jawwad ba zahirinsa kika gani, tsawon shekaru shiya hana aikinmu tafiya yadda ya kamata anyi masa barazanar amma, bashi da niyyar hakura duk abunda kikayiwa Jalal, kai tsaye kamar kinyiwa zuciyar Jawwad ne" "Tab amma gaskiya yana kaunar JALAL, yanzu dai ka bincikomin inda Jalal yake, inason zuwa" "To bari in jarraba" Jawwad ne yabi bayan Jalal "Yanzu dai kayi hakuri zomuje se a siyo wata wayar" Bece komaiba yabi Jawwad sukaje suka siyo sabon waya, yabada wadda Ilham ta tarwatsa aka gyara, domin ya kwashe abubuwansa masu mahimmanci na kan wayar, wayar ta daku, Dan karfinta Ilham tasaka ta buga wayar,   Jawwad ne ya dakko wayarsa don kiran Abba yaji koya dawo, seyaga wayar tasa akashe, be tunanin komaiba ya kunnata Abba ya kira yaji ko yakaraso, yace masa yana hanya. Ya kashe kiran kenan message ya shigo wayarsa Jalila ce ta turomasa message,    "Yaya kaima fushi kake dani       Shikenan kowa yatsaneni      Abba yayi fushi, Ummi ta           Dena kulani, Dan Allah kai       Kar kayi fushi dani" "Allah sarki sisyna ni Sam bana fushi dake" Jawwad yai maganar a fili Jalal da yake driving ya Dan kalleshi ya basar Jawwad ne yaketa kokarin kiran Jalila amma taki dagawa, be fushiba haka ya dinga kiranta har daga karshe ta daga tana daga wayar sautin kukanta yaji "Yaya  Jawwad kaima fushi kake dani ko? Nakiraka dazu ka daga kaki magana daga baya kuma ka kashe wayarka" "Nidin Jalila? Ni na isa in miki haka sedai matsalar network, a duniya banga laifin dazakiyi min in ki daga wayarki ba baby" "Yaya Jawwad Ummi sunyi fushi dani wai se sun dawo dani kano, Dan Allah kabawa Abba hakuri," "Kai sisy to meye a ciki kinga seki dawo kusa damu naji dadin hakan" Cikin shagwaba tace "Ni wallahi, Yaya bana son zaman kano, ni nafi son zama a gurin Ummi" "Hmm mune ba kyason zama damu ko"? "A a Yaya nifa bahaka nake nufi ba, Ummi tace wai in na dawo kano garinsu zata koma" "No, calm down sisy, dena kuka nan is OK ko so kike nima kisani kukan, bana son kukan nan" Jalal da haushi ya isheshi Hannu yasaka ya fizge wayar daga hannun Jawwad "Kana ta shirme da yarinya ko kunya bakaji, se wani shagwaba take kana lallabata" Jawwad ne ya bishi da kallon mamaki "To ina ruwanka dani so kake in kyaleta taita kuka in kanta yayi ciwo fa?" "A'a bindiga kan nata zeyi ba ciwo ba, kukan dadi take da sojoji basu karairayota sun zubowa Abba a boot ba yakawo maka" "To naji ban wayata" Kashe wayar Jalal yayi, "Na hana in munkoma Gida idan nabar gurin seka cigaba, kokuma in baka wayarka in tsaya ka sauka, seka samu gurin zama a titi, ka cigaba da shiriritar" "Yanzu kiri² bazaka bani wayata ba"? "Eh bazan bayar ba" "Allah sarki baby, nasan kukan zata cigaba, Dan Allah kabani in rarrasheta" "Aiko sedai ta mutu, in seka rarrasheta zata dena" "Shikenan zan ramane" Haka suka tafi Gida suna tafe suna fad'a Memakon  Jalal ya kaisu Gida se ya canza hanya "Ina kuma zamuje" Jawwad ya tambayeshi "Yunwa nakeji ice-cream kawai zan siyo ko fura" "Kwadayayye kawai" "Eh naji kwadayayyen ne nasan duk haushina kake ji Dan na hanaka waya, kuma bazan bayarba" Yasa hannu ya dau wayar Jawwad, ya bar wayoyinsa sabuwa da tsohuwar a cikin mota ya bude motar ya fita Dan murmushi Jawwad yayi Jalal kaima ai rigimammen ne Jawwad ya furta hankali Jeje tun dazu se trying lambar JALAL yake amma baya shiga Yanzun ma kuma trying yayi by luck wayar ta shiga Jawwad dake kashingide a cikin mota yaji wayar Jalal tana ringing da ya duba ba suna ya daga yasa a kunnensa ba sallama ba komai Jeje yafara magana "Ina ka shigane tun dazu nake kiran wayarka amma yaki shiga" "Sorry ba shi baneba wayarsa ce ta Dan samu matsala" Jeje yagane muryar Jawwad amma alamu ya nuna shi Jawwad be gane shiba Dan da ya ganeshi baze daga wayarba ma "OK Dan Allah yana ina yanzu" "Mun Dan fita dashi, yanzu muna kabuga ya Dan fita ne yanzu zamu karasa Gida insha Allah" "OK nagode" "Wa zance masa?" "No bakomai zan kuma kira" "OK" Jawwad ya katse kiran Jeje ne ya kira Hannah a waya Bugu biyu ta dauka "Ya"? " ke kin ban wahala gaskiya tun dazu nake kiransa a waya se yanzu na same  shi a waya, shima ba shi ya daga ba mayensa ne ya daga wai wayar Jalal dince ta lalace, sun Dan fita yanzu zasu koma Gida" "Au nice ma nasaka wahala kamanta aikin naka ne?" "Hakane fa tuba nake me idon zinari" Murmusawa Hannah tayi "Weldon yanzu kuma zanyi nawa aikin, zan Dan jefa masa fargaba a zuciyarsa" "Meye shirin naki?" "Ba ruwanka kai dai zuba ido" Jawwad yafara gajiya da zaman jiran Jalal "Kome ya tsaya yi oho" Jawwad yai maganar tareda duba wayar Jalal don ganin lokaci message ne yake shigowa wayar   "Yau kaki daga wayata, ka jefa Zuciyata cikin matsala, ko Abinci nakasa ci dan haka Kaima zan saka taka zuciyar a damuwa Ina hanyar zuwa gidanku Zakazo ka sameni a gidanku Cikin dakinka, kuma komai Ze iya faruwa in aka ganni a Dakinka, in baka son hakan Ya kasance mu hadu a   Restaurant din damuka hadu Da farko mintuna goma sha Biyar kawai kake dashi           From your lovely bae            (Hannah) Wannan wace irin jaraba ce, haka Jalal yai maganar hankalinsa a tashe, bayaso sunan Jalal ya kuma baci, da sauri yayi dialing number da aka turo message din da ita amma taki dagawa, Yasalam Jalal ina ka tafine ana shirin jefaka cikin matsala Daren ranar ma Jalila batayi ishashen bacci ba ko abinci taki sakin jiki taci, Ummi se rayuwarta take ita kadai ba tare da ta shiga sabgar Jalila ba dukda a cikin zuciyarta bata jin dadin abinda takewa Jalilan amma yazama dole ta nuna mata bacin ranta akan abunda Jalilan takeyi    Washe gari da safe Jalila haka Jalila ta shirya ta tafi makaranta, tana zuwa yan ajinsu yan son jin gulma sun so su tambayeta yadda akayi amma ba fuska ta hade rai se muzurai take, suna tsoron su tambayeta suma ta juye musu kwandon bala'i Mummy Hanan dakanta tare da wasu sojoi Guda biyu suka kawo Hanan makaranta cikin wata CRV me tint glass, sojoji guda biyu na gaban motar, sun dan jima a kofar makarantar koza suga wucewar Jalila amma basu ganta ba daga baya, mummy tace Hanan ta shiga school ita tasan abunyi Tsakanin Jalila da Hanan ba Wanda ya kula wani, duk yanda yan aji sukaso jin gulma basu samu dama baa bayan tafiyar Hanan ba dadewa sega malama ramatu an sauketa a napep zata shiga cikin makarantar Dan sauke glass mummy Hanan tayi "Sannu dai" Mummy Hanan tafada cikin ISA da iyayi Malama ramatu na ganin mota Ta washe baki da durkusa "Yawwa sannu madam ina kwana" A dan wulakance mum Hanan ta amsa "Yawwa lafiya, if u don't mind please I have an issue to discuss with you" "A a ba wata damuwa, madam ina jinki" Alama tayiwa malama ramatu data shigo cikin mota Ba tayi tunanin komai ba ta shiga Mummyn Hanan ta numfasa "Da alama kema staff ce a school din nan ko?" "Yea of course" "Good, kinsan case din da akayi a school din nan da akayi fada tsakanin dalibai biyu aka daki yarinya Yar gidan captain rasheed " Se a lokacin malama ramatu ta kalli suwaye a gaban motar taga sojoji nan take ta sha jinin jikinta "Emm...e..eh nasani madam amma wallahi bana gurin akay...." "Inma kina gurin ke kikasani tambayarki zanyi kikamin karya, zaki gane kurenki ne" "Zanma fadi gaskiya wallahi" "Wacece Jalila Aliyu Imam Yar uban waye ita?" Nan take malama ramatu ta karkace ta dinga rattaba bayanin karya da gaskiya "Ba Yar uban kowa bace ba, a sanina ma bata da uba, amma naji ana wai ya mutu ko karya akema ohoo, daga  ita se uwattta suke zaune baata da wani gata, se tsabar iskanci da Neman rigima" Haka taita zuba, kaman ruwa ba comma ba full stop "Ke surutun ya isa haka bani address din gidan su" Malama ramatu ta bata address Maman Hanan Tabawa malama ramatu 5k a wulakance sukaja mota sukayi gaba Kuma trying lambar Hanna Jawwad yayi da wayar Jalal seda taja aji, azatonta Jalal ne sannan ta daga cikin yanga tafara magana "Baby lokacinka ya fara karka dauka da wasa nake wallahi dagaske nake in samu haduba gidanku zanje" "Amm Hanna ba  JALAL bane nine Jawwad dan Allah karkiyiwa Jalal haka, dama yan anguwa sun samasa ido, yanzu in kikayi haka zaki kara bata masa suna kisa akuma tsanarsa dan Allah karkiyi haka duk abun Jalal baya bin mata kuma mahaifinsa yana gari in ya ganki bazeji dadi ba" Nisawa Hannah tayi "Jawwad dan uwanka yafiye taurin kai yaki karbar bukata ta, gara in biyo masa ta inda yakamata, mintuna sha biyar ne kacal daku, in bakuzoba wallahi zanyi shigar danaga dama ince karuwarsa ce ni kuma har Gida xanje, ko dayake nasan hakan ba lallai yabata masa ba but at least ze gane da gaske nake, ganinsa kawai nakeso nayi in samu sauki a raina, zabi ya rage naku dan uwa na gari" Ta kashe wayar "yasalam wannan wane irin abune, Allah ya fidda kai sharrin wannan yarinyar Jalal, ohhh gara muje mu sameta karta bishi Gida daddy bazeji dadi ba dama ga yan unguwa sunsawa Jalal ido, inaga kuma aga karuwa taje gurinsa " Jawwad ne Ya bude motar da sauri ya fita Neman Jalal Ko islamiyya Jalila ba taje ba, kuma Ummi batace ta shirya taje ba, ta kyaleta idonta duk ya kumbura saboda kuka "Allah sarki baby na banajin dadin ganinki a haka amma kedin ce Zuma seda wuta, gara in horaki" Ummi tayi maganar a zuciyarta Da yamma likis su Jalila sukaji tsayuwar mota a kofar Gida, Jalila tana tsakar Gida ta zurawa Ummi ido kaman bata Santa ba, Ummi tanaa shan fura, Cikin izza sukaji sallama Ummi ce ta amsa sallamar tare da jiran shigowar Wanda yayi sallama Jalila tana zaune bata amsa sallamar ba balle ta motsa daga inda take, "Sannu da zuwa shigo" Ummi tayi maganar tana mikewa tsaye bata gane matar ba tayi zaton irin customers dinta ne "Ba zamane ya kawoni ba" "To lafiya meyafaru?" Ummi ta tambaya "Nasan baki sanni ba nice Hajiya Safiyya Mrs. Captain Rasheed " Da sauri Jalila ta daga kai tayi arba da Hanan da mamanta Maman Hanan ce ta janyo hannun Hanan "Kalli duba ta'addancin da y"arki tayi kina tunanin kunci bulus ne?" Gaban ummine ya fadi da taga Hanan Share please More comments more typing............ Ina alfahari da masoyana da masu yi min addua ina godiya ❤❤❤ Masu bukatar shiga group dina akwai link din group din Asama amma akwai dokoki 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  26 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa            -MY FIRST NOVEL- Wani mugun kama Ummi taga Hanan tanayi da Jalila, ciwon goshin Hanan ta kalla "Eyya kiyi hakuri ai munje makaranta akan case din, mun bada hakuri, babanta yace komai ya wuce kiyi hakuri Dan Allah" "Keda kinsan da bada hakurin kika haifi Yar da bata da tarbiyya, kika haifi yarinyar Datafi karfinki ni na dauka ma Yar wata hamshakin ce Ashe ba Yar uban kowa bace face Mara galihu?" "Duk me ya kawo wannan maganar, haba ke kuwa Jalila tana da tarbiyya rashin ji ne kawai na yara, kuma batun gata kowa gatansa Allah," Wani abune yakawo wa Jalila iya wuya motsa baki tayi da niyyar rashin mutunci cikin tsiwa sukayi ido hudu da Ummi seta hadiye maganarta tayi shiru "Da wallahi niyyata ubanta zansa akoyawa hankali in yaso gobe yabawa yarsa tarbiyya ya banbance mata matsayin yayan gata da marasa galihu" "Kar a kuma sakomin uba, a barshi ya kwanta cikin aminci a kabarinsa, ni nayi laifi ba shiba" Jalila tayi maganar tana jujjuya idanu "U see mummy wannan yarinyar bazata yi nadama ba memakon tabaki hakuri rashin kunya zatayi miki, in bakiyi Sa a bama zaginki zatayi, kawai kisa a dauketa a je a horata" Hanan tayi maganar tana kallon Jalila Da yarabanci Ummi tayiwa Jalila magana, Jalila ta yamutsa fuska ta Dan kara hade rai "Naji yata ba Yar uban kowa bace bamu da gata se Allah mu bamu su arziki bane, amma kiyi hakuri batun a dauki Jalila a horata be taso ba, bazata karaba" "Tsiyar talaka kenan ko ince matsiyaci, ya dakko abunda yafi karfinsa, karshe yazo yana karya murya," Ta maida idonta kan Jalila "Kekuma kinci Sa a da ubanki zan Sa akama, wannan uwataki ce ma tabani tausayi, ba dan haka ba da sena Sa an sauya miki halittu, kibari kitaka wani matsayi kisamu me tsaya miki in kinyi rashin mutunci, a yanzu dabaki da galihun nan wahala zaki sha Mara tarbiyya kawai" "Nice ma ke saboda rashin tarbiyya kuma kar...... Jalila ce tafara magana ummi ta dakatar da ita Ummi ta kalli mummy Hanan sannan tace, " nace kiyi hakuri ko, se magana kike akan gata se dai ko nan gaba amma a yanzu dai banajin kinsamu gatan dana samu a rayuwata, sannan yata ba Mara galihu bace ba, da gatan ta, daliline yasa kiga ganmu a haka, amma bazan gazaba Allah yabaki hakuri" Tsaki mum Hanan tayi taja Hanan suka fita, ga magana fal abakin Jalila amma Ummi ta hanata magana, Wata kwallar bakin ciki ce ta taru a idon Jalila, meyasa Ummi ta hanata magana daki ta wuce ta kyale Ummi a tsakar Gida Jawwad Yana ta duba ta inda Jalal ze taho ya hangoshi yana nufo inda motarsu take da ledoji a hannunsa da sauri Jawwad ya karaso "Ina ka tsaya daga siyen abu" "Au fitowa kayi nemana, da nasani kulleka nayi a cikin mortar" "Bar wannan maganar ban mukullin mota ni zanyi driving dinmu" "Me yasa?" Jalal ya tambayi Jawwad da mamaki, be bashi amsaba yasa hannu ya karbi key din daga hannun Jalal, suka shiga suka tada mota Jalal ne ya kalli Jawwad "Nifa bangane wannan abun da kakeyiba, ina kuma zamuyi , ba gida zamu tafi ba?" "No wani guri zaka rakani" "Ina kenan?" "Just watch" inda sukayi zasu hadu da Hannah ya kaisu, ya kulle Jalal a motar ya fita da wayar Jalal kaman yadda shima yayi masa dazu lambar Hanna ya kira "Kina dai² ina gamu munzo restaurant din" "Nabar nan gurin ina bayan layinku rukunin sababbin gidajen nan" "Haba Hannah amma ba haka mukayi da farko ba" "Na canza ra ayine ina daf da zuwa gidansu Jalal in bakuyi Sauri ba" katse kiran yayi ya koma motar da sauri ya kunna ya ja motar ya bar gurin "Nikam naksa gane ma'anar abunda kakeyi Jawwad wai meye haka?" "Zaka gane ma'anar abunda nake yanzun nan" Inda Hanna tayiwa Jawwad kwantace nan Jawwad ya kaisu ya kirata yace gasu sunzo, sannan yacewa Jalal ya fito daga motar, ba musu ya fito daga motar yana kallon Jawwad, daga cikin tata motar Hannah ta fito tana wani taku cike da iyayi da isa wata shedaniyar rigace a jikinta straight found ce amma yadin roba² ya kwanta a jikinta yakamata tsam se Dan kwali data daure kanta dashi ta fito da Wig's dinta ya bazu a gadon bayanta, Da mamaki Jalal ya kalli Jawwad cike da tuhuma da sauri Hannah ta karaso domin rungume Jalal amma yayi saurin matsawa baya "Meye haka wannan wane irin shirmene baki da hankali niza ki hugging? Meye ma anar hakan daka kawoni nan gurin Jawwad? Yai maganar a fusace yana kallon Jawwad, Jawwad bece masa komaiba " ba laifinsa bane, ni nace yakawomin kai ko in maka ba dai² ba kuma Dan na rungumeka ai ba laifi bane,  Jalal why are you avoiding me? do you thinks am Jocking danace ina sonka, se wulakanci kake min haba Jalal kalleni sama da kasa banyi kama da irin matar daza a wulakanta ba meye aibuna" Kallon Jawwad yayi "You see, meye amfanin hakan dakayi, ka dakkoni ka kawoni gurin wannan mahaukaciyar yarinyar, kalleta kalli jikinta, dan ta rainamin hankali kuma tace tana sona, koda nake shan giya nasan abunda ya dace dani" Jalal se fada yakeyiwa Jawwad duk yadda Jawwad yaso ya kwantar da hankalinsa yayi masa bayani yaki yadda se fada yakeyi, murmushi Hannah tayi sannan tace "Masoyina naji kana kasan abunda ya dace da kai, ai babu wani abu me kyau da yadace da kai babyna, nidin dai nina dace da kai, kai duba da yanayin taka rayuuwar, da kuma tawa suna kamanceceniya babancin kadanne kawai" Kurawa Jawwad ido Jalal yayi"kagani ko ka kyauta" shine abunda Jalal yafada Yakama hanyar tafiya, da sauri Jawwad ya bishi "Dan uwa Dan Allah ka saurareni" "Nika rabu dani babu abinda zaka gayamin, wallahi in kayi wasa sena Sa an batarmin da yarinyar nan, Dan me zaka dinga cusamin ita dolene sena dinga shiga sabgar matan, I hate her" Ya juya yayi tafiyarsa yabar Jawwad a nan gurin a tsaye Hannah kuwa dariyar farin ciki tayi saboda tayi nasara, so take dama ta Dan janye Jawwad daga jikin Jalal don tasamu damar gudanar da abinda tayi niyya, tayi nasara tunda Jalal har yayi fushi haka Jawwad ne ya dawo inda yabar Hannah cikin damuwa ya dubeta "Haba Hannah baki kyautamin ba kalli yadda yayi fushi, ba  haka mukayi dake ba, anya son gaskiya kike masa?" "Kwarai kuwa son gaskiya nake masa, kayi kokari nagode daka yi dalilin dayasa naganshi at least dukda yaji haushi amma ka faranta min" "Dan Allah ina rokonki, karki je gidansu Jalal a hakan ma fama ake akan ya canza halayensa, in kika kuma sanadin lalacewarsa biki kyauta ba, Hannah ke mace ce baza kiso ace Jalal danki ne ko yayankine a haka ba" Yadda Jawwad yai maganar abun tausayi har Hannah taji yana nema ya kashe mata gwiwa Dan haka da sauri tace "Thank you, ni na tafi semun kuma haduwa" Ta juya tai shige motarta, bashi dazabin da ya wuce shima ya tafi, Dan haka ya hau motar da sukazo ya tafi Bayan sallar magariba Jalila durkushe agaban Ummi tana kuka"Ummi Dan Allah kiyi hakuri, najanyo anzo har Gida anci zarafinki nasan laifinane amma insha Allah bazan kuma ba kiyi hakuri Dan Allah " Hannu Ummi tasaka tana gogewa Jalila hawaye"ya wuce baby amma ki canza halinki ki rike maraicinki ki dena dakko mana magana" "Ummi na dena insha Allah"" yawwa baby nima ba a son rains name fushi dake ba" rungume Ummi Jalila tayi"nagode Ummina Allah yabaki tsawon rai me amfani" "Ameen, Allah ya shiryamin me yabaki miji nagari" shiru Jalila tayi tareda kuma gyara kwanciyarta a jikin Ummi "Ummi amma kinfasa maidani kano ko? " tafiyarki kano tana nan" "Ummi meyasa?" "Haka mahaifinki yace kafin ya rasu" dagowa tayi ta kalli Ummi "To amma ai yanzu baban nawa baya nan," "Zaki kumako ai bazaki canza halinki ba dagani ni" Mikewa tayi daga jikin Ummi taje ta samu guri ta zauna tana tunani Duk yadda Jawwad yaso ya shawo kan Jalal ya nuna masa dalilin dayasa ya kaishi gurin Hannah amma Jalal yaki saurarensa Haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi gida, yaje yayi salla sannan ya shiga cikin Gida bangaren Abba, ya tarar dashi yana kallon labarai "Sannu da zuwa Abba ya kabarosu ya hanya" "Lafiya kalau Jawwad, ai tun dazu na dawo naita zuba ido in ganka, amma banganka ba" "Mun Dan fitane da Jalal, Abba ya akayi da case din, munyi ways da wani Dan ajinmu yacemin ai ita yarinyar kanwarasa CE" "Eh kam mun hadu yace ya sanka, ajinku data, Ai Allah ya temakemu abun yazo da sauri," Abba ya labartawa Jawwad abunda ya faru Jinjina kai Jawwad yayi"amma Abba Jalila takirani a waya tana kuka, tace kunce nan zata dawo, zama tare damu" Murmushi Abba yayi "Hakane amma Dan mu tsorata ta ne mun yanke seta kammala wannan ajin da take, sannan zata dawo nan, kasan wasiyyar kanina kenan, gara ta dawo nan maybe sekaga ta nutsu" "Hakane, to Abba ita ummin fa haka zata cigaba da zama ita ka dai" "A a Jawwad itama zata koma gurin iyayenta ne, intaje insun karbeta se akai Jalila taga dangin mahaifiyarta, ina ganin in Jalila ta dawo nan bata ganin idon umminta zata dena fitina" "Hakan yayi kyau Abba Allah yasa mudace," "Ameen Jawwad" Haka suka cigaba da tadi daga baya Jawwad ya fito ya koma gurin Jalal amma da yaje baya nan ya kirashi a waya amma baya dagawa, Girgiza kai Jawwad, yayi yasan ba makawa Jalal ya tafi mashaya Aikuwa hasashen Jawwad yazama gaskiya domin kuwa don kuwa bayan abunda yafaru tsakaninsa da Hannah da Jawwad, Jalal yakoma Gida yaji ransa yakiyi masa dadi, ransa yagama baci Dan haka ya fita ya tafi mashaya Aikuwa Jeje ya takewa Jalal cikinsa da giya yayi mankas ya fita hayyacinsa sannan ya kalli Jalal "Mutumina wai me yabata maka raine haka naganka some how" Cike da maye Jalal yafara magana yana tangadi "Wata usless creature ce take son takurawa rayuwa ta, ga Jawwad shima ya bata min rai mtseww, wai meyasa mata suke da matsala kasan mene ma"? Murmushi Jeje yayi "sekafada nawan" "Kasan wannan kanwar tawa ko? Ilham itama fa hadamin zafi tayi da safe so nayi in tattakata amma Jawwad ya hanani kaga itama wannan banzar da take takuramin wallahi so nake inyi maganinta" Seda Jeje yakuma banka masa giya sannan yace "To meye a ciki man Hannah ta kai macen daza a sota she's so beautiful fa" Jeje ya dakko waya yana nuna masa hotunan Hannah da wasu irin kaya a jikinta me bayyana surarta Ture hannunsa Jaalal yayi yana tsaki "Kai jeje ni bana sonta bana son shirme aikin banza kaima batamin rai zakayi meye hakane kakeyi" Jalal Ya mike yana tangadi yana shirin tafiya Jeje a ransa yace lallai gayen nan akwai taurin kai a bugen ma yana da lissafi amma muje zuwa zaka gane kuskuren ka A zahiri kuma mikewa Jeje yayi ya riko Jalal in bahakaba ze iya faduwa, Dan baze iya tuki ba Dan sosai yake tangadi Ilham ce take ta kaiwa tana kawowa a dakinta tana tunanin me yakamata tayine, dan tayi Alkawarin fitinar Jalal tako ina bazata bari yafara soyayya da wata banza ba, ba itaba Dan hakan dai² yake da rushewar shirinmu ana samun kuskure komai ze lalace, dabara ce ta fado mata Dan haka gaban mudubi taje ta zauna, ta fara shafa mayuka a jikinta, tareda fara tsara simple make up a fuskarta, dogon wando tasaka skin tied se wata karamar Riga body hook, ta dakko wannan turaren ta shafe jikinta da shi, parking din gashinta tayi ta Dan Dora mayafi akanta ta nufi hanyar fita Jeje ne yakawo Jalal gida a buge part dinsa ya kaishi ya kwantar da shi Jawwad da yake kofar gida yaga wucewar motar Jalal koba a gaya masa ba yasan Jeje ne yakawo Jalal, kuma ba makawa a buge yake, girgiza kai Jawwad yayi cikin bacin rai yakoma cikin gida Bayan jeje ya kwantar da Jalal ne yazo fitowa daga part din Jalal sukayi clashing da Ilham "Wow so cute, common beb u look so beautiful" Jeje yai maganar yana mata wani shedanin kallo "Kai kashiga hankalinka, ka kiyayeni, bani hanya" "Meyasa kikeso in baki hanya me zakije kiyi masa? Gaskiya na kyasa ya za ayine?" Wani mugun kallo Ilham tayi masa "Eh kaman ba gidan ubanka bane nan, meye na tambayata me zanyi masa kai me kayi masa, ka kiyayeni ka fita hanyata, niba Sa arka bace sakarai kawai" Ta hankade Jeje ta wuce ajiyar zuciya Jeje yayi "gaskiya yarinyar nan ta hadu I have to do something" Yasa kai ya fice, Ilham har cikin bedroom din Jalal ta shiga ta ganshi kwance yayi dai² akan gado yana bacci. Murmushi Ilham tayi ta shiga cikin dakin ta samu gefen Jalal ta zauna hannu tasa ta Dan shafa sajensa zuwa cikin sumarsa Dan jijjigashi take "Yaya Jalal wake up please" Share please More comments more typing................ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  27 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa            -MY FIRST NOVEL- A hankali ya bude idonsa da sukayi jawur, saboda buguwa ya mayar ya lumshe sannan ya fara magana a cikin mayae "Ni wannan yarinyar bana sonta, narasa meyasa Jawwad yayi min hakane, nace masa bana so amma shi......se wani" Sekuma yayi shiru, Ajiyar zuciya Ilham tayi tace"munafukan banza daga Jawwad har kanwar tasa, zasu gane kurensu Matsawa takuma yi ta kwanta a jikinsa sannan ta Dan dago ta kalleshi "Meyasa baka sonta" "Mtseww nifa bana son tambaya, bana sonta kawai bata da hankali," ya Dan girgiza kai ya yamusta fuska warin turaren nan yaji da yabaya so "Itakuma Ilham meyasa baka sonta?" Dan bude ido yayi ya mayar ya lumshe"wannan fa kanwata ce, meyasa zanyi wani soyayya da ita, kanwata ce kawai" Shigewa jikinsa ta kumayi sosai "But I love you, karkayi soyayya da wata bayan ni, Ilham ce kawai take sonka, sauran duk bamasu kaunarka bane, Ilham tana sonka kaima kasota kaman yadda take sonka" Dukda yana cikin maye setaga yayi murmushi"ka yadda zakaso Ilham" "Bacci nakeji ki kyaleni da wannan mafarkin" "Mafarki kake?" Ya gyda mata kai "ya kusa faruwa a zahiri" Tai maganar tana shafa gashin kirjinsa ya mutsa fuska yayi ya rike mata hannu"kidena bana so" "Meyasa bakaso?" Shiru yayi be ce mata komai ba "Shikenan tunda bacci zakayi bari in tafi," Durkusowa tayi da nufin tayi kissing dinsa se ya juyad da kansa alamun baya so, kallonsa tayi "Why?" "Ki tashi ki bani guri nace miki bacci zanyi" Gabanta ne ya fadi dataji yayai normal magana ba tare da maye ba, kallonsa tayi taga ya bude idonsa fes akanta, sekuma ya mayar ya lumshe yacigaba da bacci Ajiyar zuciya tayi tare da fading"Allah ya temakeni na dauka giyar tasakeshi ne" Kissing dinshi tayi akan lips dinsa sannan ta mike ta fita ta nufi cikin Gida, me gadi ya hango fitowarta daga part din Jalal "Kai me yarinyar nan take a bangaren yaron nan a wannan tsohon daren, Allah ya kyauta bayan shan giya kuma yafara biye² mata, abun kunya kuma da kanwarsa Allah ya shirya" Da safe Jalila tanata shirin makaranta, wata makwabciyarsu bata  wuce sa ar Jalila ba ta shigo tacewa Ummi Dan Allah ta sammata abunda ta girka ita tayi girkin takasa ci dayake tsohon ciki ne da ita "Allah sarki hawwa'u Allah yaraba lafiya bari azuba miki Jalila zubomata abinci" Jalila kam zuwa yanzu Hawwa haushi take bata gani take tsabar kwadayine da iskanci komai bazata iya Ciba sena gurin ummi, Ummi kuma bata taba hanata ba ko kyararta Jalila tana zumbura baki taje ta zubomata dataga ummi bata kallonta ta dungurar mata da kwanon da kayan tea "Gashi nan kwadayayyiya seki hada Sa kanki niba Yar aikinki bace" "Eh naji kwadayaiyiyyar ce ke in naki yazo maga yadda zakiyi" "Bawani nan komai kidorawa ciki, dayana da baki se yace karya kike masa" Dariya Hawwa tayi ta hada abincinta ta fara ci suna hira da ummi tana gama ci ta kama aman abincin nan dataci seda ta amayar tsaf "Kai kekam kin banu sekace akanki aka fara ciki ga rakin tsiya ni bari in bar gidan nan tun kafin nima kisani aman" Jalila tai maganar tareda daukar jakar makarantarta tayi waje Girgiza kai ummi tayi indai Jalila ce bazata canza ba Wajen karfe Tara sannan Jalal ya tashi daga nannauyan baccin da yayi kansa yana ciwo, jiyayi yana warin turaren Ilham tsaki yaja yafara tunanin abunda yafaru wannan wane irin sha³ mafarki yayi kuma ma da Ilham (shi a zatonsa abunda yafaru mafarkine) Mikewa yayi yaje yai wanka ya fito yayi sallar asuba karfe Tara na safe Jalila tana kokarin shiga makaranta taji ana tayimata horn bata waiga ba ta koma gefe akakuma tahowa inda take a fusace tajiyo tana masifa "Wai meye hakane anyi Horn na canza hanya ankuma biyoni if you like bi ta kaina komawaye" Bude motar yayi ya fito tana dariya Allah yabaki hakuri Yar baba, Yayan Hanan ne Abdallah yakawo Hanan makaranta murmushi Jalila tayi "Au ai bansan kai bane ina kwana" "Lafiya kalau ya mamanki" "Tana lafiya" Juyawa yayi ya kalli motar yace"ke Hanan fito mana kin wani Zauna a cikin mota" Sannan ya dawo da kallonsa kan Jalila "Yar baba kaman kuwa kinsan daddy yace agaisheki har yabada sako abaki" Hanan ya kalla wadda se wani cika take tana batsewa "Hanan bani sakon nan" A wulakance ta bude Jakarta ta miko masa wata Leda Ya karba yabawa Jalila "Kai amma nagode sosai Yaya Abdallah ka cewa baba Yar baba ta gode, Allah yasaka masa da Alkhairi yabashi abunda yake nema duniya da lahira, Allah yabashi ladan kyautatawa marainiya" Ba Karamun burge Abdallah tayi ba,"zangaya masa insha Allah" Tsaki Hanan tayi ta wuce abunta cikin school, Jalila ma cikin makaranta ta shige, duk zafin kan Hanan bata kuma kallon seat din Jalila ba balle takuma sha awar zama a gurin, Zama Jalila tayi ta dakko abunda akabata chocolates ne kala² a ciki murmushi tayi gaskiya mutumin nan yana da kirki Bayan anfita break Jalila taje seat din Hanan ta zauna a kusa da ita kawata ya kike Wani mugun kallo Hanan tayi mata ta dauke kai, bude chocolate dinta tayi tafara sha sannan ta kalli Hanan kawas "Bismillah" "Abun ya fito daga gidanmu sannan kice insha ke dai da kike kwadayaiyiyya seki sha dama Dan talaka akwai iya shishshigi," Murmushi Jalila tayi sannan tace "duba ajin nan akwai yayan Wanda sukafi mahaifinki dukiya, amma abun be baki mamaki ba ina Yar talaka amma nake makarantar yayan attajirai kaman Hanan rasheed, ashema Baku wani Tara ba tunda har Yar matsiyata kamar Jalila Aliyu take a irin makarantar Ku" Mike kafa Jalila tayi ta Dora a saman bencin "In ana batun gata Hanan, be kamata kisaka baki ba, Dan baki da gatan da Jalila take dashi" Jalila se gayamata bakaken maganganu take tana shan chocolate dinta, Hanan tana fargabar ramawa saboda gani take Jalila bata Risina ba zata iya maimaita mata abunda tai mata amma duk da haka ta dake tana ramawa Jawwad ne yakuma dawowa gurin Jalal amma Jalal yayi masa banza yaki kulashi, haka ya hakura ya tafi ya kyaleshi Bayan an tashi daga makaranta Jalila ta dawo Gida amma ummi bata nan wani bakin ciki Jalila taji ta tsani ta dawo Gida taga ummi bata nan Waya ta dakko ta kira ummi "Ummi ina kika tafi ne?" "Kinganmu a asibiti Hawwa muka kawo ta haihu Dan ba rai yanzuma Karin jini ake mata" Zaro ido Jalila tayi "Wace hawwan dazu fa da safe tazo" "Bayan tafiyarki tafara nakuda" "To meyasa akayimata aure yanzu se wahala takesha?" "Aa seki bari in danginta sunzo ki tambayesu" "Allah yabaki hakuri itakuma Allah yabata lafiya amma Dan Allah ki dawo Gida" "Bazan dawo ba din a can zan zauna" Ummi ta kashe wayar Seda Jalal ya shafe sati baya kula Jawwad, sekuma daga baya Dan kansa ya sakko, suka shirya yayinda kullum se Jalal yaje mashaya, Hannah tasamu damar cigaba da cusa kanta, a gefe daya itama Ilham tanata nata kokarin, sunsaka Jalal a gaba, Jalal dai se kara shirircewa yake Alhamdilillah Neman maganar Jalila daga Islamiyya har boko yayi sauki, ta fara nutsuwa, yayinda mahaifin Hanan keta kyautatawa Jalila, amma Jalila ta takurawa Hanan, kullum tana manne da ita, Hanan ta zageta ta gaya mata bakaken maganganu amma Jalila batajin haushi takance mata"Hanan mahaifinki yana da karamci, yana kyautata min, komai zakiyi min bazanji haushi ba, shiya hadamu kawance kuma ni na karba" Hanan mulkinta take zubawa a cikin makarantar daga malamai har dalibai shakkata sukeyi,amma banda queen J Watarana anayiwa wata Yar ajinsu Jalila birthday a aji, kunsan yayan masu kudi aka dinga jijjiga champaign suna sakinta a sama, suka dauki turare suka dinga fesawa a ajin sun ware kida suna cashewa Hanan ce ta nufo ajin ta shiga tana shiga wannan kamshin turaren da akasaka ta shaka nan take ta fadi kasa dama tanada asthma, da sauri Jalila taje kanta tana jijjiga ta Yan ajin tsayawa sukayi suna kallon Hanan data ke ta fama da numfashi, Jalila ta dinga jijjigata "Hanan meyafaru, ki tashi" Jalila taga hakan bazeyiba tasa ta dago Hanan ta rungumeta zata fita da ita amma jikinta yariga ya saki yan ajin suna kallo ba Wanda yabi takan Hanan saboda rashin mutuncinta balle ayi tunanin me temakamata Jalila ce kawai taketa kici² da hanan, ana haka Sega siyama "Jalila meyasameta?" "Nima bansaniba amma kaman asthma ne," Jalila da siyama ne suka kama Hanan suka kaita school clinic akaimata abunda yakamata amma babu wani cigaba duk ta fita hayyacinta Aka kira gidansu hanan aka sanar dasu, sukace akaita wani asibiti private anan likitan dayake duba hanan yake, a motar makaranta aka saka hanan Jalila tana rungume da ita tana mata fifita Suna zuwa aka karbeta aka fara yimata abunda yakamata har tasamu bacci "Likitan ya kalli Jalila yace sister din kice" Gyada masa kai tayi "Ya akayi bansanki ba kuna kama sosai" Banza  Jalila tayi masa tacigaba da kallon hanan har cikin zuciyarta ta kejin ba dadi halin da hanan ta shiga, saboda bata manta lokacin da hakan yafaru da ita a kanoba lokacin da Jalal ya duramata sigari, ta sha wahala amma condition din Hanan yafi worst Se da baccin Hanan yayi nisa sosai, ga lokacin ta shi yayi Dan haka Jalila ta mike ta tafi Gida aka bar Hanan da wata malama a harabar asibitin taga daya daga cikin motocin gidansu Hanan ta shigo, Ba ta tsyaba tayi tafiyarta Gida, Ummi ke tambayarta ina ta tsaya tagaya mata abunda yafaru Dan kallonta ummi tayi taga duk ta damu a ranta tace Allah sarki baby halinki halin abbanki ba kya riko sam, "To Allah ya sawwake yabata lafiya" "Ummi zakije dubata?" Hararar Jalila tayi ta cigaba da aikin ta, Washe gari da safe Jalila ta shirya ta dama kunun gyada ta zuba a flask ta tafi asibitin da aka kwantar da hanan, room din da Hanan take taje ta bude kofar ta shiga, mum Hanan ce a zaune tana ta fama da Hanan taci abinci taki, "ina kwana" Jalila ta gaida Maman Hanan "Ke mekikazo yi nan"? "Hanan nazo dubawa" "Waya nemeki, munji mungode, jeki Allah yabada lada" "A a mummy dubanifa tazo, shigo kawata" Hanan tayi maganar tana kallon Jalila,mikewa Jalila tayi taje gefen gadon Hanan ta zauna "Sannu Hanan ya jikin baki"? " da sauki Jalila, yau za a sallamemu ma" "Allah yabaki lafiya, ga kunun gyada na kawomiki ni zan tafi makaranta" "Jalila nagode sosai da abunda kikayimin jiya," "Bakomai manta kawata, Allah yabaki lafiya" Jalila ta mike ta kalli mummy Hanan "Mummy se anjima" Dauke kai mummy tayi batace komai ba, Jalila na waigowa zata fita taci karo da Abdallah abakin kofa a tsaye, yaga duk abunda yafaru gaisawa sukayi ta ratseshi ta wuce Bakin gadon Hanan yaje ya zauna"sannu autar mummy " "Yaya kasan wani ABU?" "A a sekin fada" "Yanzu nakejin ban kyautaba abunda na dingayiwa Jalila a baya ba, bakaga yadda ta dinga kula dani jiyaba, kaman Yar uwata, ban tabajin naji babu dadi ba saboda na wulakanta mutum ba se akan Jalila" Murmushi yayi"auta kinga illar wulakanta mutum ba, yanzu dai kwanta ki huta" Tsaki mummy tayi ta tashi tabar dakin   Tundaga wannan ranar Hanan ta sake da Jalila har ziyara take kaiwa Jalila, ga kyautatawa da mahaifin Hanan yake yiwa Jalila, a sanadin Jalila Hanan ta dena wasu daga cikin halayenta marasa kyau Haka lokacin ya dinga tafiya Jalal ya cigaba da fuskantar barazana a cikin rayuwarsa ga Hannah tasashi gaba, gefe ga Ilham da itama take uzzurawa rayuwarsa danma ita Ilham yanacin kaniyarta, ga Jeje da yake ta kuma rusa rayuwar Jalal, lalacewa har tafi baya, danma Jawwad yana kokari akan Jalal Lokaci² Jalila takan yi miyagun mafarkan data sabayi da Jalal Abun yana damunta sosai a rai, Duk mafarkan da take dashi se dai taganshi a mawuyacin hali. Yaune ake taron iyaye da yan uwa na kimanin dalibai arba'in na set dinsu Jalila, taron ya kunshi manyan mutane da iyayen dalibai, taro yayi taro inda aka karrama dalibai da dama, can na hango Jalila cikin graduation gound tayi kyau matuka takara girma tayi wani irin kyau, Jalila tana cikin dalibai naga ba da aka karrama da iyayenta, ta karbi kyautuka da dama sunyi hotuna da malamai da dalibai yan uwanta, mussaman Hanan da siyama ga Jawwad da Abba gefe ga ummi sunji dadin yadda sukaga ana ji da Jalila a cikin dalibai, a matsayinta na shugabar dalibai tayi speech me matukar ma'ana, ta birge mutane da dama, sunyi kukan rabuwa da dalibai sakamakon shakuwa da sukayi, haka taro ya tashi farin ciki fal zukatan dalibai   Bayan sunkoma gidane Jalila da Jawwad suka tafi yawo cikin garin Kaduna yayinda Abba da ummi suke tattaunawa akan makomar rayuwar Jalila, Jalila taji dadin fitar da sukayi da Yaya Jawwad sunsha yawo sosai tare da hira "Baby naji dadin ganin yadda aka karrama ki gashi kinkara kyau kin girma u look so beautiful" Murmushi Jalila tayi "Yayana na kaina, jajircewar Abba ce tasa na taka duk wani matsayi a yanzu bazan manta karamcin Abba ba Allah yasaka masa da alkhairi" "Ameen baby?" "Amma Yaya Jawwad,Ina Jalal?" Subucewa maganar tayi taji ta fito ba tare da ta shirya ba Kallonta Jawwad yayi "Meyasa kike tambayarsa bayan ba kyayimasa addua" "Kawai tambaya nayi amma ina yimasa addu'a" Gyada kai Jawwad yayi "Jalila al amuran Jawwad se a hankali abun nasa sedai addu a kawai Yana nan yadda kika sanshi, yama fida" "Kuma har yanzu kana tareda shi?" "Eh muna tare Jalila bazan iya rabuwa da shiba" "Amma meyasa?" "Kin manta alkawarinmu sekinzo kano zan gaya miki" Gyada kai Jalila tayi sannan suka nufo Gida Bayan sunkoma ne Abba da Jawwad suka tafi, tun bayan tafiyarsu Jalila ta fuskanci ummi bata da walwala tana cikin damuwa sosai lokaci² takan share hawaye "Ummi wai meya farune me akayi miki, meyasa ki damuwa haka, kona bata miki Raine?" "A a Jalila lokacine yayi daza a cika wasiyyar mahaifinki, zaki koma gurin wan mahaifinki, nima zanje ganawa dangin, munyi magana da Abba sati me zuwa insha Allah zezo ya tafi dake" Ummi tayi maganar cikin kuka "Gaskiya ummi ni ba inda zani ina tare dake, bazan iya zuwa wani guri in rayu ba tare da ke ba," "Am sorry baby wannan karon dole kiyi hakuri, nima zani inga iyayena, komawarki kano ba yana nufin mun rabu baneba" "No ummi seda na rayu da soyayyarki for all this years lokaci daya acemin wai sena barki dama dagaske kike, ummi dama uwa zata iya Barin yarta?" "Baby illa ne ga ratuwarki a matsayin ya mace ace kin girma an ta shi aurenki amma ace babu namiji tsayayye akanki, kiyi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa, Zankoma ahalina kicigaba da zama a dangin mahaifinki ya aurar dake" Kuka sosai Jalila ta dingayi ranar da take ta farinciki a gareta ta koma mata ta bakin ciki tayi kuka har ta gaji, haka nan yan kwanakin nan ta dinga yinsu ba kuzari se aikin kuka kawai ummi kuma se rarrashinta take tare dayi mata nasiha "Baby duk inda kika samu kanki kizama me tsoron Allah, ki rike mutuncinki, kizama me tsoron Allah ki rike amanar tarbiyyar danayi miki, ina kaunarki baby nima ba a son raina hakan zata faru ba" Ita dai Jalila jin ummi kawai takeyi Saura kwana biyu tafiyar Jalila taje yiwa Siyama sallama sun sha kuka sosai Maman Siyama tai ta bata hakuri tayiwa Jalila alheri Siyama ta tafi raka Jalila gidansu Hanan, Hanan rudewa tayi "Jalila meyasa zaki tafi Zuwanmu Kaduna na kiyi abubuwa da yawa a gurin ki, meyasa zaki tafi bani da wata Yar uwa sama dake" Duk yadda Jalila taso dakewa kasawa tayi suka dinga kuka Hanan tai musu jagora har gurin daddy, haka nan yaji ba dadi mussaman yadda yaga sunata kuka Jalila tasoyi masa godiya kan alkhairan da ya dinga yimata amma kuka ya hanata nasiha yayi mata shima sannan yace insha Allah har kano zasu dinga kawo mata ziyara Haka ta koma Gida ummi ta hada mata kayanta cif, data kalli kayan seta kuma fashewa da kuka "Baby kukan nan ya isa haka, kirike abubuwan danake gaya miki, kizama me hakuri da rayuwa duk inda kika tsinci kanki, ki zauna da kowa lafiya, ki rikemin amanar kanki da tarbiyyar danayi miki, Baby duk mijin da Allah yabaki ki masa biyayya, kiyi hakuri dashi" "Ummi wai ya kikemin magana kamar me wasiyya" Murmushi kawai ummi tayi tanaji a jikinta akwai wani abu daze faru da Jalila a kano amma ta dake taketa kokarin kwantar da hankalinta To kome ze kasance in ummi ta koma garinsu? Wace rayuwa Jalila zatayi a kano? Ya makomar rayuwar Jalal? Waye Jalal ? Meze faru da Jalila zamanta a kano? Meye alakar Jalila da Hanan da suke kama? Tskanin Jeje dasu Ilham suwa ke nasara akan Jalal Dama sauran tarin tambayoyinku Ku cigaba da bina sannu a hankali domin samun amsoshinku Daga alkalamin (daddy's girl) Share please More comments more typing................... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  29 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa Ummu hanif really enjoy u comments and prayers Allah yaraya mana hanif ya bar kauna 😍😍😍              -my first Novel- Tsayawa Jalila tayi daga inda take a tsakanin flowers tana kallon su Jawwad Ilham ce takarasa shigowa gidan Su Jalal ke kokarin shiga mota Ilham ta danyi sauri ta je gabansu "Yaya Jalal ina zaka ne?, inason zamuyi magana da kai" Dama tunda tafara suspecting Jalila ke son Jalal ta dena kula Jawwad, yarasa me yayi mata "Yaushe kika zama uwata dazaki ce kina son magana dani, kokuma yaushe kikazama ISP da kike tuhumata ina zani" Jalal ya tamvayeta Dan tabe baki tayi sannan tafara magana cikin shagwaba "two minutes kawai Dan Allah" Bude mota yayi ya shige ya batta a gurin kaman gunki Jawwad ne ya kalleshi, "haba bros Dan Allah fa tace, ka saurareta mana kasan mezata gaya maka" "Indai wannan yarinyar ce babu wani abu me amfani dazata fada, komai nata daga shirme se hauka, bawani abun hankali a lamuranta" Ya karasa shigewa motar ya kulle kofa ya batta a tsaye Jalila daga inda take tana jin abunda suke cewa mamakine yacika Jalila tun wancan lokacin har yanzu Ilham ba ta dena son Jalal ba kuma har yanzu yana wulakanta ta amma tana manne dashi, tirkashi Allah kayi mana tsari da wahalalliyar soyayya dama wani mutumin arzikin ne takeso da da sauki amma Jalal wannan Dan wulakancin uban shaye² Wayar da Jalila ta tabaji Ilham tayi a wancan zuwan nata ta tuna "" ZANCIGABA DA HAKURI HAR LOKACIN DA BURINMU ZE CIKA AKAN JALAL DA MOMMYNSA"" Jalila bata manta ba wannan sune abunda taji Ilham tafada shekaru biyu dasuka wuce, "Lallai akwai wani abu a kasa ba a banza Ilham take jure wannan wahalalliyar soyayya ba" Ringing din wayarta ne ya fargar da ita daga dogon tunanin data tafi, lambar Siyama ce da sauri ta daga seda suka sha hira, takira Ummi ma suka gaisa sannan ta mike ta koma cikin Gida Dakinsu ta nufa don aje wayarta tana shiga ta tarar da Ilham da Nana suna hira kuma dai ga dukkan alamu hirar akan Jalal ne, cikin dakin ta shiga tana fadin "Juliet ta Romeo kokuma ince laila majnun, ya labarin soyayyar takune, domin labarin soyayyar nan akwai kayatarwa" Jalila ta karasa maganar tana zama a gaban Ilham tareda yimata murmushi Hade rai Ilham tayi kaman taga mutuwarta tareda tsurawa Jalila ido na wani lokaci, JALILA ma kallonta take kafin daga baya tace "Manyan yan mata a cikin garin kano wannan kallon fa" Wani mugun kishine ya tokarewa Ilham ganin Jalila takuma girma ta kara kyau, maganarta ma gwanin burgewa, Nana ce tai farat tace "Ilham Jalila fa ta dawo kano da zama, tabar garin Kaduna, anan zata cigaba da zama damu" Ras!Ras!!Ra's!!! Ilham taji gabanta ya fadi "Ta dawo kano da zama?" "Eh mana munkara yawa" Dagawa Ilham gira Jalila tayi "Ko ba kya farinciki da zuwana in koma" (Mhmm kaman ba Jalila data gama kuka akan zuwa kano ba kunga harta ware tafara sana ar Neman magana 😂😉) Wani matsiyacin kallo Ilham takewa Jalila aranta take fadin "Lallai yarinyar nan muguwar Yar rainin hankali ce ga yadda take pretending kaman ba wani abu a ranta game da Jalal" A zahiri kuma cewa Nana tayi "Kinga mubar zancen nan mayi wataran, in mun sake haduwa" Tai maganar tana yinkurin tashi tsaye riketa Jalila tayi "No baza ayi hakaba ina lefin kice in baku guri, sha zamanki ai Jalila ba bakuwar zafi bace" Jalila ta tashi tsaye ta bar musu dakin Ta koma Kitchen tayi wanke² ta gyara kitchen din ta dawo parlour tana gyarawa, sallama akayi ta amsa wata budurwa ce wadda bata fi Sa arsu ba dauke da bagcco a hannu ta amsawa Jalila tayi tareda yimata sannu da zuwa, yarinyar Ta kalli Jalila tace "ina mutan gidan ne?" "Suna ciki wani abunne?" Jalila ta tambayeta "A a dama dawowa nayi" "Kokece Halima" "Eh nice" "Allah sarki sannu da zuwa karasa suna ciki" "To nagode" Dakinta halima ta nufa taje ta aje kayanta ta fito domin fara aikace² taga kusan an gama komai Jalila ta kalleta "kije ki huta mana dagani kinyo tafiya" "A a kaida ba Hutu kazo ba ina batun Hutu" "Jikin Dan Adam yana bukatar hutu, ni nagama komai na dauke miki aikin yau" Suna cikin haka Nana ta fito ita da Ilham, Nana ce ta kalli halima "sarkin biki, suna, ko mutuwa, se yau kinje kinyi zamanki a kauye ko" "Wallahi bahaka bane Nana ni dince na danyi jinya" "Haka dai kika iya kin barni aikin Gida kaman ya kasheni" "Kai Nana Dan Allah wani irin aiki kaman ya kasheki ina aikin anan" Jalila tafada tana hararan Nana "Kenima wallahi in Yar aikin mummy ta tafi bana iya wannan wahalan tuni nake sawa a sallamesu a canza wata bana son shirme" Ilham tayi maganar tanayiwa Halima kallon banza Jalila kuwa kwashewa tayi da dariya a ranta tace kaga Yar masu Gida hada sawa a kori me aikin a fili kuwa cewa tayi "Halima kyalesu na dauke miki aikin yau jeki sha zamanki"   "Mtseww shirme kawai" Inji Ilham, "nice ma ke, akan shirme" Jalila ta bata amsa "Enough please narasa wannan rashin jituwa a tsakaninku, Ku indai zaku hadu sekunyi fada, wuce muje" Nana tafada tana tura Ilham "Muje zuwa zangane abinda kike kullawa ne Ilham narasa inda kika dosa," Jalila tayi maganar a zuciyarta ta nufi dakin maama, da sallama ta shiga Maama ta amsa mata da kyar amma dayake Jalila ta iya siyasa se ta nuna kaman bata San abinda Maama take mata ba, ta karasa kusa da ita ta zauna "Hajiya Maama hutawa kike? Me za a dafa miki yau" "Kinga ban saki ba balle Abbansu Jawwad yace daga zuwaanki an fara takura miki" "Haba Maama wani irin takura, aikin Gida ai dolene ga ya mace ba batun takura" "Kinga ga kitchen din nan jeki abinda kika gadama" Maama ta karasa maganar cikin kosawa" Mikewa Jalila tayi ta fito ta bata guri, ta nufi kitchen, ta tarar da halima tana kokarin dora abinci tare sukayi komai da Jalila sukayi girkin suka gama suka gyara kitchen din Jalila tanayiwa Halima gyare² a wasu abubuwan Yayinda Nana tana daki a kwance tana chatting Jalila ce ta shigo ta sameta "Nana gaskiya mijinki ze sha fama" Dan kallonta Nana tayi "Kaman ya?" "Kallifa tunda garin Allah ya waye daga chatting se bacci haba Nanancy gaba fa akeji ba yanzu ba" "Jalila kenan in Allah ya nufi ka huta kawai ka huta, kema ke kikasa kanki, wannan wahalar shikenan mutum baze huta ba" "To naji tashi ki kaiwa Yaya Jawwad Abincinsa, in munyi salla se muci namu" "Ba inda zani, in yanason ci in sun dawo daga yawon yazo ya dauka" "Kai Nana Yaya Jawwad din?" "Eh shidin, ina zuwa ze fara Sani aiki yana min masifa, bakiyi kazaba, wannan ba dai² bane, ga Yaya Jalal ma yaitawa mutum wani gani² mistake kadan seyace bazeci abincin ba, kuma in beciba Yaya Jawwad ma baze Ciba, shiyasa Halima ce take kaimasa itama haliman in basu gadama ba in ta kai bazasu Ciba, Yaya Jalal yafi kowa wannan tsirfan, kokuma yanzu susaki dafa wani abincin, shiyasa ko yazo ya dauka da kansa,ko halima ta kaimusu, bana son wahala" "Tabdijan indai Yaya Jawwad ne meye a ciki se in masa amma Jalal kam yayikadan" Dariya sosai Nana tayi, "Tab cakwakiya Ashe kuwa zakuiyi fada da Yaya Jawwad" "Ke ni bari in wanka in yazo se ya shigo ya dauka,abincin" "Kin temaki kanki kema seki huta"     Se bayan sallar la'asar sannan su Jawwad suka dawo ko ina sukaje? Oho nima bansaniba Jalila tana tareda halima sunata hira, Jalila ta sha mamaki da halima tace mata ta taba aure amma tasha wahala gashi auren dole akayi mata, tanata bata labarin kauye Yaya Jawwad ne ya shigo ya tarar dasu a parlour, cikin grimamawa halima ta gaida Jawwad ya amsa mata a mutunce sannan ya kalli Jalila "Baby mun dawo, atemaki cikin gayu, munajin yunwa" "To babban Yaya yanzu kuwa bari in kai" "God bless you my sister" "Ameen Yaya Jawwad" "Bari in shiga in duba Maama" "To Yaya a fito lafiya" Ta mike ta nufi kitchen ta shirya kayan abincin akan tray ta dauka tayi hanyar waje A kashingide ya tarar da Maama tana waya Dan haka yajira ta gama sannan ya Dan dubeta "Maama mun dawo" "To sannunku, ina fatan komai lafiya?" "Komai normal Maama, kayan ma suna boot" "To shikenan Bari zan tura Nana ta kai musu" "To shikenan Maama nasa JALILA ta kaimana abinci mun debo yunwa" Yafada yana mikewa "Yawwa dawo ka zauna zamuyi magana" Guri ya nema ya zauna ya bata attention dinsa "Ba kaga yarinyar nan ta dawo gidan nan ba, bana son shishshige mata daka keyi, wannan rawar kan da kake akanta kana wani janta a jiki duk banaso, ga Yar uwaka nan cikinku daya ta isheka bana son yayime² da cusa kai kanajina ko?" Mamakine ya cika Jawwad wai Jalila ce yayime² Allah sarki Jalila itama Yar uwassu ce ai suke nan ba yawane dasu ba amma meyasa Maama har yanzu batason alakar my da Jalila, ya numfasa sannan yace "To Maama za ayi yadda kika ce, insha Allah za a kiyaye" "Gara dai itama Nana zan mata magana naga zakewar taku tayi yawa, Tashi kabani guri" mikewa yayi ya fito, jikinsa a sanyaye Jalila ta kai Abinci part din Jawwad kaman dazu yanzuma Jalal yana nan amma bata kulashi ba be kulata ba ta ajiye zata fita, taga wani key holder akan center table da keys na mota a jiki dakuma wasu keys din, key holder din yayi kyau wani Dan Teddy ne a jiki me kyau, kai tsaye Jalila taje ta Sa hannu ta dauka, ta jujjuya shi yayi mata kyau sosai, tafara kokarin cire teddyn jiki, ita a tunaninta na Jawwad ne, Jalal ne yake satar kallonta yaga ikon Allah, seda ta cireshi tsaf daga jiki, tabar keys din haka ta mayar kan center table din ta ajiye, ta dau Dan Teddy zata fito Jawwad ne ya shigo dakin jikinsa a sanyaye sakamakon maganganun da Maama tayi masa "Kinkawo abincinne"? "Eh na kawo gashi can" "Mungode sosai" Murmushi yayi, hannunta ya kalla, yaga abin key holder din Jalal, "Baby waya baki wannan"? "Yaya sonake a jikin keys dinka naganshi" "To wayace miki nawane?" "To ai duk abunda yake dakin nan nakane" "Dagaske"? " eh mana duk abunda ya shigo cikin dakin nan yazama Naka" Dariya Jawwad yayi "to na oga ne dafatan kin tambayeshi kafin ki dauka"? Dan zaro ido Jalila tayi " waiwa kake nufi" Da ido ya nuna mata Jalal, Dan bude baki tayi "Ni cirewa kawai nayi, na dauka nakane" Kwaikwayonta Jawwad yayi "Eyya na Yaya Jalal ne a tambaye shi tukuna" Jalal yana jinsu yayi musu banza ya sakko ya fara kokarin zuba abincinsa salad din data hada ya bude tayi masa wani decoration yayi kyau sosai,, maida hankali yayi yafara zuba abincinsa "Jeki tambayeshi mana?" Jawwad ya maimaita, noke kafada tayi, "Meyasa bazaki tambayeshi ba" Dan tura baki tayi "ai nakane" Jawwad ne yadan kalli Jalal yaga shi ta abinci yake, Jalila  ta shammaci Jawwad tayi waje abunta da Dan Teddy a hannunta A parlour ta tarar da Maama tana lissafawa Nana Atamfofi da less "Yawwa Jalila zomuje tare, kayan nan zan kaiwa mommy Jalal" "To shikenan Ku gama kirgawa" Akagama kirgawa suka zuba a manyan leda suka dauka suka nufi gidansu Jalal Shigarsu yayi dai² da fitowar Mummy daga part dinta, Dan bude baki mummy tayi, "yan mata saukar yaushe?" Durkusawa Jalila tayi ta gaisheta ta amsa da fara a "kinzo mana Hutu kenan"" Nana tai farat tace"a a mummy ta dawo nan gaba daya" "Masha Allah hakan yayi kyau, ya Maman naki?" "Lafiya kalau ta bata amsa" "Masha Allah toku shigo ciki mana" suka shiga cikin parlour shima yasha gyara kaman parlour amarya, kayan suka zube agabanta, dubawa ta shigayi dayake suna business sosai tsakaninsu da Maama "Kai amma lesses din nan sunyi kyau, kafin akaisu bari Ilham tazo ta zaba, Jalila Dan kirawo Ilham tana dakin ta " Ba musu JALILA ta tashi ta tafi dakin Ilham, tayi ruf da ciki tana jin music a wayarta, duk tasaka Bluetooth a kunnenta, tana bin wakar a hankali, tayi ruf da ciki tabada attention dinta akan waya shiyasa bataji shigowar Jalila ba Bakin gadon Jalila ta karasa ta Dan leka wayar Ilham, hotunan Jalal, takewa wannan kallon kurillan, Jinjina kai Jalila tayi tareda furta "Yar wahala, kina nan kina shirme yana can yana shagalinsa" Hannu Jalila ta kai ta girgizata "To uwar soyayya kije ana kiranki" Dan dagowa Ilham tayi ta kalleta a wulakance, jitayi kamar hannun Jalila na kamshin turaren Jalal zumbur ta mike tana kallon Jalila "Meye haka? Kin shigomin ba sallama" "Kina can kina ibadar dababu lada taya zakisan nazo" Hannun Jalila ta kalla taga teddyn jikin key holder din Jalal Kwalalo ido Ilham tayi ta kai hannu kan abun tareda fadin "Wayabaki wannan aina Jalal ne" "Kamarya waya bani? Dan na Jalal ne kuma shi kadai akayiwa? Kinji mace kinga ni cewa akayi kawai nakiraki" "Inba nasa bane ya akai naji kamshinsa, kamshin turaren Jalal ne a jiki fa, kuma tabbas nasane" "Au Jalal din har wani kamshi yake na daban, banda warin hayaki meyakeyi, kullum cikin zukar hayakin taba har wani kanshi yake" Mikewa Ilham tayi tsaye tana kallon Jalila sannan ta nunata da yatsa "Naga wannan karon kin karo wulakanci, kuma wallahi bazan saurara miki ba koni ko ke, tuntuni nagane take² ki, se yanzu nagane inda kika dosa, am ready for you" Share please More comments more typing.......................... Love you all my fans really appreciate your comments and prayers ❤❤❤❤ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 30 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa           -MY FIRST NOVEL- Yatsan da Ilham ta nuna Jalila dashi, Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Ilham "Dukda Ban gane inda kalamanki suka dosaba, banga abunda nayi miki kike tada jijiyoyin wuya hakaba, sedai bansaniba ko kema Jalal yafara baki giyar saboda naga alama daga wannan maganganun naki, yanzu dai kije matar gidan tana kiranki" Jalila na zuwa nan a zancenta tasaki hannun Ilham, tayi waje abunta "Ina Ilham din?" Mummy ta tambaya "nagaya mata amma naga kaman batajin dadine amma nagaya mata" "Bata jin dadi kuma? "Meyasameta dazun nan fa tabar palour" Ita dai Jalila shiru tayi, Jalila na fita Ilham ta koma kan gadon ta zauna kanta kaman ya fashe ta rike kanta lallai ma wato Jalal har yayi sakewar da abunsa ze shiga hannun Jalila, Wato Jalila tayi galabar fara soyayya da Jalal, kuma kalli yadda takemin kamar bata San metayiba to ni ina me hakan yake shirin faruwa impossible Ilham tafada da karfi Muryar mummy taji tana kiran sunanta Dan haka da sauri ta kwanta akan gadonta ta rufe ido, cikin dakin Ilham mummy ta shigo ta ganta a kwance "ke Ilham meyasa meki" Bata juyoba bata bude Ido ba tabata amsa "Kaina kemin ciwo" "To bazaki sha magani ba, se kizo ki kwanta" "Nasha fa" "To Allah ya sawwake, in bedena ba kiyi magana akaiki Asibiti dama kaya aka kawo nakeso ki dauka bari insa abarsu anan in kinji sauki seki duba ki zaba" "to" Shine abinda Ilham itace, mummy ta juya zata fita Ilham taraka bayan mummy da harara tareda yin kwafa, tana fita ta mike taje ta kulle kofarta tasa key ta dawo kan gadonta ta zauna "munafukan banza zanga bayanku daya bayan daya, gara in fara kauda wannan banzar yarinyar gefe tukuna, naga zakewarta tayi yawa inna bari tayi galaba, abunda ake gudu yafaru to shirinmu gaba daya ya rushe," Mummy ce tafito tace musu subar mata kayan anan zata aiko da Wanda ba a siyaba suka mike suka fito Itakam Jalila mamakine ya cikata metayiwa Ilham takemata wannan maganganun harata na wani zatayi maganinta, lallai bata sanni ba kafin tayi maganina zanyi maganinta idan na gano metake kullawa Nana ce ta Dan kalli JALILA "Baby wai ko kunyi fadan da kuka saba ne naga da fara a kika shiga gurin Ilham amma kin fito wani iri ko akwai matsalane?" "Bakomai me zatamin daze Sani bacin rai aitayi kadan" "Nikam narasa meyasa ba kwa jituwa da ita" Murmushi Jalila tayi "Niba abunda yahadamu da ita kawai dai tanada saurin fushi ne" "Kekuma kinada tsokana ba" Nana tafada a tare sukayi dariya suka shiga Gida Jalal ne yazo ya giftasu yana waya, "Bazan fito ba dan uwa yace, kar in sake in fito, dan haka yau ina gida kayi hakuri" Dan shiru yayi sannan ya cigaba "Wani mamaki zaka bani, nayiwa Jawwad rakiya duk nagaji, Wai dole yau kakeso in zo abari se gobe zanzo kwana zanyi a gurin" Jalila ce ta Dan tsaya yayinda Nana take kokarin Janta su tafi dan kwace hannunta tayi daga na Nana "Yi gaba zan amsa wayane" "Waya kuma waya kiraki a waya? Anfara kiran sallar magariba ki zo mu shiga basekiyi wayar a ciki ba" "Ke dai kiyi gaba yanzu zan karaso," Wucewa Nana tayi abinta, yayinda Jalila tabi bayan Jalal, ta tsaya nesa kadan dashi amma tana jin meyake cewa "Hannah kuma, Hanna ta fiye rigima, mezatayi a gurin nan da daddare in dai zata gurin nan bazanzo ba, dazu naga kiranta ban dauka ba, muna tareda Jawwad indai zata ganni a guri seta fitineni, nikuma banason shirme" Shiru ya dan kumayi Jalila batajin me ake cewa daga daya bangaren "Waiku meyasa kuka takura lallai senazo, taya zan taho karfe biyu na dare, ina laifin afara ten agama one Anyway zanyi kokari in fito" Karfe biyun dare mezeje yayi karfe biyu a wani guri shikadai JALILA tai maganar a zuciyarta gyaran murya tayi Wanda hakan yasashi waigowa dukda duhu yafara amma yagane Jalila ce, "Karfe biyun dareko zaka fita, Allah yatemake ka kafita, kai ko tausayin iyayenka bakayi, ga dan uwana kullum bashi da cikakken kwanciyar hankali saboda kai, yakamata ka tausaya masa" Ta karaso inda yake ta miko masa dan teddy nan "Ungo abunka kanwarka zatamin hauka dan taga wannan abun banzan a hannuna," Dan kurawa Jalila ido yayi, na yan sakanni bece komai ba kawai ya juya ya fita "Yan wahala kai da kanwartaka Allah yayiwa Yaya Jawwad tsari da kai da fitinarka, dan kai Jarrabawane a rayuwarsa, ba dangin iya ba na Baba amma kullum hankalinsa ba akwanceba saboda kai kuma ko tausayinsa bakaji, wallahi in kaje gurin nan aka maka wani abu Alhakin Yaya Jawwad base barkaba" Cak Jalal ya tsaya jiyayi kaman Jalila ta soka masa mashi a zuciyarsa Girgiza kai yayi ya nufi hanyar gate, "Allah yasa kar ya FIta" Jalila tafada a fili son jikinta nabata wannan fitar ba alheri bace akwai abunda aka shirya yi masa Ta wuce cikin gida ta tarar da Halima a zaune a palour tana kallo "Anty Haleema kallo ake haka anyi sallar magariba fa" "Wallahi inkikacemin Anty kunya kike bani" "Kunya kuma saboda me nake baki kunya" "Ina aiki a gidanku, kumafa watakila kin girmeni amma kidinga cemin Anty" Dariya JALILA tayi "haba leemart har aure fa kikayi kuma kin haihu kin cancanci a girmamaki" "Wannan sunan yan gayunfa dakikace yanzu" "Ya miki dadine?" "Eh wallahi" "To shikenan, bari inje inyi salla kema kije kiyi, inzo kibani labarin kauye" "To shikenan bari intashi" Jalila taje ta tarar da Nana tana salla dan haka ta ajiye wayarta itama taje tayi alwala zata tada salla tana kallin Nana tana idar da salla ba Azkar ba komai ta shafa fuskarta, taja gefe ta dau wayarta ta kama sana'ar tata ta chatting Har Jalila ta idar da sallah tayi Azkar dinta, sannan ta waigo ta kalli Nana "waini Nana mekike a cikin wayar nan haka ne ke idonki baya miki ciwo" Dariya Nana tayi "lallaima wani irin ciwo kuma ba wani ciwo" Gyda kai Jalila tayi ta tashi ta tafi dakin halima itama ta idar da sallar tana ninkin kaya "Yawwa gani nazo zo kibani labarin kauye" "Kekam Jalila meyasa kikeson kauye" "Wallahi inaso inje amma bantaba zuwa ba kauye yana birgeni" "Tab kinemi tsari da rayuwar kauye, yanada dadi in kayi dace da mutanen kirki a garin Amma kinganni nasha wahalar zaman kauye ga maraici ga rashin gata, ina Jss 2 akamin auren dole da dan hakimi ga jarabar kishiyoyi da yayansu, uwargidansa ma takusa Sa ar kakata" "Zaro ido Jalila tayi Sa ar kakarki, keko waya aura mikishi" "Kanin mahaifina Jalila, matan mutumin nan su hadu sumin duka, shi kansa jibgata yake a haka nasamu ciki ga laulayi, amma babu tausayi ranar aikina senayi, wanke² ma kawai na gidan nan bala'i ne balle girki" "Subhanallah kuma kanin mahaifin naki yasan halin dakike ciki" Jalila tayi maganar kaman tayi kuka "Wallahi yasani Jalila, an azabtar dani a rayuwata maraici babu dadi, danginmu suna kallo amma babu me iyayi masa magana" Jalila kaman ta fashe da kuka saboda tausayin halima, nan Takara jinjina rikon Amana irin na abban Jawwad ko mahaifinta yana raye tasan iyakar dawainiyar daze da ita kenan, bata taba kukan rasa wani abuba saboda maraici" Tana wannann tunanin JAWWAD ya kirata "Baby atemaka da coffee please" "To Yaya ban yan mintuna" "To shikenan" Ta kashe wayar ta kalli halima "leemarta bari inje in hadawa Yaya coffee, amma zan dawo, ko in taho miki dashi" girgiza kai halima tayi "A a ni ban iya wannan ciye² yan gayun ba, kedai sekin dawo" Murmushi Jalila tayi ta fita Murmushi halima tayi itama gaskiya Jalila tanada kirki yadda take sakin jiki da ita bata ISA ta zauna Inda Nana takeba mussaman insuna tareda Ilham, taita zigata tayi mata rashin mutunci, Kokuma taita sakata aiki kaman baiwa Jalila tahada coffee ta tafi ta kaiwa Jawwad, wannan karon shikadaine a parlour "Yawwa sisy nagode sosai, dama Jalal ne ya kirani yacemin yanaso shiyasa nasaki, nagode" "Kutmelesi JALAL nema ze sha, wallahi Dana San shine bazan hada ba" Jalila tayi maganar a zuciyarta a fili kuma hanyar fita tayi ta koma cikin gida   Jawwad ya kaiwa Jalal coffee din jiyayi yafi na ko yaushe dadi "Waya hada tea din nan?" "Jalila ce, ita nasa ta hada maka, kasan Nana in batasa kanta abu ba se a hankali, JALILA ce komai kasata ba kyuya zatayi maka a nutse" Jalal be kuma cewa komaiba yacigaba da shan coffee dinsa, seda ya kammalla tukuna sannan Jawwad ya dauki flask din ze fita, har yayi hanyar fita ya dawo, "Jalal dan Allah karka fita ko INA yau kazauna ka hutawa ranka karkaje gurin shan giyar nan yau dan Allah" Yakarasa maganar da sigar rarrashi, tausayinsa ne Yakama Jalal gaskiyar kanwarsa datace ba dangin iya ba na baba amma kullum hankalinsa a tashe saboda ni Ajiyar zuciya yayi, "ba inda zanje insha Allah, ina gida" "Are you sure" Jawwad ya tambayeshi, murmushi Jalal yayi masa "am sure, bros ba inda zan fita yau" "Thank you very much, Allah ya tashemu lafiya" "Ameen" Jalal ya amsa, sannan Jawwad ya fita ya koma gida Bayan fitar Jawwad ne, Jalal yafada tunani, Tabbas Jawwad ya dade yana dawainiya dashi, kullum bashi da kwanciyar hankali saboda shi, abokansu da Dama suna kyamarsa basa mu'amala dashi saboda halinsa, iyaye dayawa sunyiwa yayan su Katanga tsakaninsu da Jalal saboda miyagun halayensa, amma Jawwad be guje shiba tabbas wani abu yasamu rayuwarsa hakkin Jawwad baze barshiba "Mummy why kalli halin da danki yakeciki, ga rayuwar danakeyi mummy saboda ke ga yadda ake kyamata mummy why meyasa kika aikata haka a rayuwarki, abun Yakoma kaina". Haka Jalal ya dinga surutai hawaye nafita daga idonsa, " Thank you very much Jawwad bazan iya biyanka wannan kaunar ba" Ya furta a hankali Jalila bayan takoma cikin gida bata koma gurin halima ba Ummi takira a waya suka sha hira take tambayar Ummi yaushe zatayi tafiyar ne? "Se nan da wani dan lokaci, akwai shirye² danakeyi sonake sena gama" "Ummi wani shirye² kuma, nifa sonake kije ki dawo, in dawo gida mucigaba da zama tare" "Hmm Jalila kenan in na tashi tafiya kafin in tafi zanzo kano muyi sallama" "Yawwa Ummina har naji dadi wallahi dama inkinzo ki daukeni mutafi tare" "Mutafi ina, bana son rigima, ai bahaka mukayi dakeba senaje na dawo tukuna semuje tare" "To shikenan ummi, Allah ya kaimu lokacin" "Ameen ya Allah, ki gaida mutan gidan naku" "To ummi zasuji insha Allah" Haka sukayi ta hira da Ummi kaman bazasu dena ba kafin daga baya sukayi sallama, Nana ce ta shigo da kwano a hannunta "Babyn ummi dawa kike wayane?" "Nida ummine wallahi" "Au ai na dauka da wani gayen kike waya" Dan zare ido Jalila tayi "rufamin asiri gaye kuma" "Eh mana karya kike dai kice baki da saurayi" Hararta Jalila tayi "au tambayata ma kike" "Au tuba nake ai namanta, na dauka an masa kishiyane" "Nana kinfiye shirme, mekike da kwano haka" "Abinci zanci" "To aci lafiya ni kwanciya zanyi" Jalila ta bude akwatinta ta dakko kayan bacci, Nana ta kalleta "Jalila nayiwa Abba magana za acanza mana wardrobe, semu maida kayanmu ciki, naga kayannaki dayawa" "Kin doramasa nauyi, dakin bari se inbar wasu a akwatin ba ai duk dayane" "Hmm Jalila kenan kome zakice nidai nagaya masa" Jalila tasamu guri ta kwanta, Bacci ya gagari Jalal se tunani yake, Jeje ya kirashi a waya ta dinga ringing amma yaki dagawa Ya kalli wayar yaga yadda sunan Jeje ke yawo akan screen din wayarsa, Yasan batun party nan ze masa tsaki yayi "Kaine mafarin komai" Yayi tsaki ya kashe wayarsa gaba daya ya zame ya dan kashingida ya runtse idonsa yana tunanin abubuwa da dama dasuka wuce a haka bacci barawo ya dauke shi Washe gari da asuba bayan  Jalila ta idar da sallar asuba, tanaso ta danyi tilawa amma taga Nana na kokarin komawa bacci dan haka saboda karta takuramata seta koma palour ta fara karatunta cikin sautin muryarta me dadi, seda gari yayi haske sosai sannan ta tashi da nufin shiga kitchen Halimace ta fito ta kalli Jalila "Barka da safiya sayyada Jalila" "Rufamin asiri inani ina zama sayyada Jalila dai" "Haba wannan karatu haka, kuma daka fa kikayi dama nice na iya" "Kema zaki iya in kinaso" Halima ta dan zaro ido "dagaske?" "Dagaske mana" "To ta yaya?" "Yanzu dai bari mu kammalla aikin gida semuyi maganar" "To shikenan bari inje in fara gyara kitchen din kafin kifito" "To shikenan bari in maida sallayar nan daki" Yadda ta tabar Nana haka ta dawo ta tarar da ita, a dukunkune tana bacci a cikin bargo, dan girgiza kai Jalila tayi ta aje hijjabin ta da sallayar ta fito palour, a kitchen suka hade da halima  suka cigaba da aikin breakfast dinsu suna hira, koko da kosai sukayi "Anya mutan gidan nan za suci koko da kosai, ko kowa zeci wannan abokin Jawwad din, me Suma a tsartsaye, gashi duk yayiwa gashinsa kala, gashi jarababbe da kyar yaci wallahi dan ya fiye iyayi," Halima tayi maganar tana kallon Jalila "Wai Jalal kike nufi?" "Eh shi wallahi, jarababbe ne, har fargabar kaimusu abinci nake" "Aikuwa sedai kar yaci din, yatafi gidansu mana yaci, ai naga gidansu ma akwai abincin" Dan zare ido halima tayi "Tab ba ruwana," Haka suka gama girki suka gyara ko ina Se bayan karfe Tara na safe mutan gidan suka dinga tashi daya bayan daya Sunyi farinciki da ganin abincin da akayi kowa yacika cikinsa suna murnar wannan sakakken abincin da Jalila tayi musu Karfe taran nan ta nufi part din Jawwad kai  Abinci amma seta kai na mutum daya iya na Jawwad banda Jalal dan jaraba da sassafen nan yana sashen Jawwad daga harabar part din Jawwad akan kujera yanata shan taba, da ganin yanayin shigarsa kaman motsa jiki yagama, Seda Jalila tazo gifta shi sannan tace "Dan Jaraba da sassafen nan mutum be karya da komaiba se hayaki" Ko kallonta beba yacigaba da shan tabar Sa Cikin palour Jawwad ta kai abincin amma baya palour, bedroom din Jawwad taje ta danyi knocking amma shiru, ta tura kofar bedroom din ta Dan bude zubar ruwa taji a toilet alamun yana wanka Dan haka ta fito har tazo zata kuma gifta Jalal takoma gaban Jalal sannan tace masa "In Yaya Jawwad ya fito kace masa ga abincin Sa nan, in yagama ya kirani zan gyara masa daki" Ko motsi beba balle ya kalleta yacigaba da aikin shan tabarsa, ga kwalin wata tabar da lighter akan table din gabansa Har zata wuce ta dawo, tasa hannu ta dauke kwalin tabar da lighter ta fizge na hannunsa "Wai kai wani irin mutum ne, baka San wannan abar illa ce ga lafiyaba da sassafe baka zubawa cikinka komai ba se hayaki, karka kuma shamana wannan abar a cikin gida, inzaka sha ka zauna ka sha a gidanku, dan uwana yafika cutuwa da wannan hayakin dakake busawa ba yau ba gobe" Turkashi Share please More comments more typing........................ Love you all my fans ❤❤❤❤❤ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 31 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa           -MY FIRST NOVEL- Dagowa yayi ya kafeta da Jajayen idanuwansa kyar ko kiftawa bayayi Seda gaban Jalila yafadi tozali da wannan idanuwan na Jalal masu kama da garwashi dagani ransa a bace yake Dukda ta razana, ta dauka ze mareta ne, ta dake ta juya ta bude dustbin ta watsasu ciki tayi hanyar cikin gida bin bayan Jalila yayi da kallo ya kai makura a tunani bayajin komai tunaninsa yayi zurfi sosai, jiyayi an dafa shi yadaga kai Jawwad yagani a tsaye " dan uwa zomuje mu karya naga baby takawo abinci" Girgiza kai Jalal yayi "banaci" Yafada a takaice tareda mikewa tsaye "kamar ya bakaci Abincin ne beyimakaba kokuwa wani abun Jalila tayi maka"? Girgiza masa kai Jalal yayi, yana kokarin tafiya, dakatar dashi Jawwad yakumayi "Haba Jalal kagayamin me akayi maka mana, na lura tunjiya da magariba baka walwala, meyasane"? Dan kurawa Jawwad ido yayi yaga yadda yadamu "Calm down ba abunda yake damuna jinayi kawai bana son cin Abincin" "No Jalal ban yaddaba" Juyawa Jalal yayi ya tafi, yabar Jawwad a tsaye, "Ohh God, meyake damunsa ne" Komawa Jawwad yayi ya duba abincin kunun gyadane da kosai Mikewa yayi yabi Jalal gidansu, Jalal yakoma gida yaje, ya kwanta akan gadonsa ya lumshe ido Jawwad ya karasa ya zauna gefen gadon ya dafa Jalal "dan uwana kagayamin meyake damunka?, lokaci daya duk ka canzamin, kagayamin ko Jalila ce tayi maka wani abun" dan bude ido Jalal yayi ya kalli Jawwad, idonsa Yakuma yin Ja girgiza masa kai Jalal yayi "To yanzu kayi hakuri, kazo muje kaci abinci" Mikewa zaune jalal yayi "Jawwad ba abunda yake damuna, kaje kaci abinci ni na koshi, karka damu dani banajin cin Abincin nan" Mikewa Jawwad yayi ya koma gida yana tunanin meyafaru da Jalal, yaje ya tarar da Jalila a part din Sa tana kokarin gyarawa yana shigowa Jalila ta kalleshi "Yaya Jawwad bakaci Abincin ba meyafaru" "Baby ko kinyiwa Jalal wani abune naga yaki cin Abincin kuma ya tafi gida" "Cemaka yayi nayi masa wani abun?" "A a becemin ba amma naga yanayinsa ya canza tun jiya" "To tunda bayaci kaikaci naka karabu dashi mana" Dan zaro ido Jawwad yayi "A a baby bazan iyaba akwai abunda yake damunsa amma yaki gayamin" "To Allah ya kyauta, dama gyara maka dakin zanyi" "Ke ba kya gajiyane? Kije ki huta" "Karka wani damu bawata gajiya gyaran part din naka ai ba wani lokaci ze dauka ba" "Bani da bakin godiya baby Allah yayi miki Albarka" "Ameen yayan" Flask din kunun gayadan da cups ya dauka yayi waje, Jalila ta girgiza kai Abincin ne baze iya Ciba in Jalal baeci ba tab agaida Yaya Jawwad Nan da nan Jalila ta gyara part din ta kukkuna tiraren wuta se kamshi yake ta rufo ta koma cikin gida Maama ta tarar a palour da nail cutter tana kokarin yanke farce, Nana kuma na kan two seater tana kallo, karasawa tayi gurin Maama ta karbi nail cutter din "Kawo in yanke mini, inna gama sekice Allah yayi min Albarka" Ta karba takama hannun Maama ta na kokarin yanke mata farce, kallon Jalila Maama takeyi "wannan wace irin yarinyace dabata San wulakanciba, duk hade mata ran danake taki ta nuna tasan inayi balle taji haushi" Haka Jalila ta yanke mata farce tsaf, sannan tabar palour Jawwad da kyar ya lallaba Jalal yaci abincin safe kusan karfe daya na rana, amma dukda haka Jalal baya walwala, daurewa kawai yake ya boye damuwarsa saboda Jawwad,   Kwana biyu Hannah Sam bata ganin Jalal, baya daga kiranta, ta dan shiga damuwa saboda haka ta yanke shawarar kiran Jeje tagaya masa, shima complaints din da yayi mata kusan kwana biyar bega Jalal ga kuma baya daga wayarsa, yaje gidansu baya nan besamu ganinsa ba yarasa meyake damun Jalal Haka take ma gurin Jawwad kowa yarasa ganewa Jalal abinci se Jawwad ya takura masa sannan zeci, baya walwala yadena shiga gidansu Jawwad sam, Jawwad yarasa dalili, Jalal ya dena zuwa ko ina se zaman daki Yau kusan satin Jalila biyu a kano amma har yanzu Ummi batayi tafiyar nan ba, tun JALILA tana tambayar Ummi har tagaji ta kyaleta, Jalila tana rayuwa a kano ba yabo ba fallasa, Jawwad da Nana da Abbansu suna kaunarta, yayinda Maama Sam babu ruwanta da ita, bata shiga sabgar Jalila kwata² hakan bayamata dadi amma bayadda ta iya Tun ranar da Jalila suka samu wannan sabanin da Ilham bata kuma haduwa da ita ba Jalila tana zaune a palour tana chatting da Hanan, Halima ta fito sanye da hijabi Jalila ta Dan dubeta "Anty halima ina zuwa haka?" "Kinga Hajiya ce ta aikeni zan kai kayan nan, gidan wata kawarta" "Bari in tambayeta se in rakaki" "To shikenan tambayota semuje" Dakin Maama Jalila taje ta ganta tana waya ta jirata tagama sannan tace "Maama naga kin aiki halima zan rakata Dan Allah" Kallonta Maama tayi a wulakance ta dauke kai "Ba a karkashina kike zaune ba yadda kika gadama kiyi" Kallonta Jalila tayi ta Dan girgiza kai, ta mike ta bar dakin ta fito ta tarar da halima, "Bari insaka mayafi in rakaki" "To ina jiranki" Jalila taje ta dakko gyalenta tayi rolling ta fito Ba karamin kyau Jalila tayi ba doguwar Riga tasa baka tayi rolling da Jan mayafi suna shirin fita Nana suka shigo ita da Ilham "Wow looking so masha Allah sister kina wuta kinga kyan da kikayi kuwa, ina zuwa haka"? Murmushi Jalila tayi " bana son zolaya Nana, Halima zanyiwa rakiya" Banda aikin harar Jalila da kallon banza ba abunda Ilham takeyiwa Jalila "Gaskiya kinyi kyau, sekun dawo, amma gaskiya ayi a hankali karki hada go slow a hanya" Nana ta fada tana kashemata ido "Nana kenan ba kya rabo da tsokana" Jalila ta Dan kalli Ilham "Kawata Ilham ba fada me yakawo gaba, fatan kina lafiya" "Nakasa kika gani a jikina kokuma, a kwance kika ganni kike tambaya ina lafiya" "Ba ko daya na dai ga kaman u are psychologically abnormal" Tana zuwa nan a zancenta tanufi hanyar waje, tabar ILHAM a tsaye sororo, tama rasa mezatayi, Halima tabi bayan Jalila, Nana kam gimtse dariyarta tayi ta kalli Ilham "Don't mind her please, muje ciki" "Wallahi Nana badan ina jin kunyarki ba da na Dade da ketawa Jalila rashin mutunci, nizata kalla tace am looking psychologically abnormal" "Yi hakuri, nidai bazan gaji da Baku hakuri ba, sannan kidena nuna mata kinji haushi Yanzu dai bar batun Jalila ban labari meyake faruwa ne" "Mtseww meyema be faru ba kwana hudu kenan banga yaya Jalal ba, idan naje part dinsa a kulle duk na damu, ko yau mukayi aure da Yaya Jalal na azabtu Nana" "Calm down, Jalal ba karamin yaro bane, maybe yana tare da Yaya Jawwad, sannan tunda ba wata budurwar CE dashi ba ki kwantar da hankalinki, a hankali komai ze wuce, kinsman yanada gaddama" "Wani irin hakurine banyiba, narasa meyake damunsa, kullum shine tension dina, kina batun bashi da budurwa to yanada ita kuma nasanta indai na haifu senasata tayi danasanin Sanin Jalal da tayi" Dan zare ido Nana tayi "Are you serious Jalal yanada budurwa, Dan Allah wace wannan"? "Ai ba sonta yakeba ita take masa shishshigi, da zarginta nake yanzu na tabbatar da wacece, zan dau mataki na karshe, daze kawo karshen komai" "Wani mataki kenan?" Nana ta fada a tsorace "Just watch, bari inkoma Gida anjima zanzo in tambayi Yaya Jawwad ko yasan Inda yake" Tana gama fadin haka ta mike tayi waje da sauri Jawwad be fushi ba yakoma gurin Jalal amma ya tarar ya rufe kofar palour Sa Jawwad yayi iya kokarinsa da rarrashi amma JALAL yaki budewa, gashi tun safiyar ranar beci komai ba haka Jawwad yagaji yakoma gida Shikuwa Jalal yana ciki yanajin Jawwad yaki bude kofar tabbas Jalila tayi gaskiya yakamata ya bar Jawwad ya huta haka tsawon shekaru yana fama dashi da matsalolinsa "Wai meyasa nake hakane, meyasa bazan yi rayuwa kaman sauran mutane ba" Jiyayi zuciyarsa tana tafasa, kaman zata tsga kirjinsa ga wani nauyi da kansa yayi kaman ya fashe yai jifa da Wayne cups din kan karamin table din dakinsa, ya dinga jifa da duk abunda yaci karo da shi ya dinga jifa da abubuwa, da kwalaben giyar da ya shanye Yakoma ya zauna idonsa suka kara Ja, ya runtse idonsa yanajin kansa yana juyawa Mikewa yayi zumbur yabi takan fasassun kwalaben nan ya dauki keys din motarsa ya fito a sukwane, motarsa ya nufa ya Shiga ya fisgeta da gudu yayi waje Su Jalila dake daf da bakin Layin suna tafe suna hira itada halima, sukaga motar Jalal ya dannota a guje, ga uban kura ya tayar ko gane motar ba ayi saboda gudu "Tab anya Jalal kansa daya, wannan gudun yanzu inya bige wani fa?"  Jalila tayi maganar cike da mamakin wannan mahaukacin tukin na Jalal "Hmm kema dai kya fada, shi kota ransa ma ba yayi" "To Allah ya shirya" "Ameen" Haka sukaje inda zasuje suka dawo, daf da magariba ne Dan haka suna idar da salla suka Dora sanwar dare Ana idar da sallar magariba Jawwad Yakoma gurin Jalal yaga ya bude kofar, da sauri ya shiga amma Jalal baya ciki, ya duba bedroom dinsa da toilet baya cikin, se tarin kwalaben giyarsa, ya sha wasu, ya zubarda wasu, ya farfasa wasu kwalaben yayi kaca² da dakin tundaga palour har bedroom "Ya salam" Jawwad ya furta ya dakko wayarsa ya fara kiran Jalal amma seyaji wayar tana ringing a kasan pillows akan gado Cikin gidansu Jalal ya shiga a rude, ya tarar da mummy tana kallo a palour "Mummy Dan Allah kokinsan inda Jalal yake?" "Kamarya nasan Inda yake, ai kai yakamata in tambaya, baya part dinsa?" "Baya can na duba, kamaar akwai abunda yake damunsa mummy tun jiya baya cikin nutsuwa," "Ni rabona da shi yau kusan kwana hudu" Dan zaro ido Jawwad yayi "Kwana hudu mummy, kuma baki nemeshiba yana part dinsa baya zuwa ko ina, yau kawai yafita kuma be gayaminba" "To kai kenan daya daukeka da mahimmanci kana sanin inda yake, ni ko inda nake seya ga dama zezo, ina gani kuma Duk inda yaje ze dawo" Jikin Jawwad ne yayi sanyi jin abinda mummy ta fada, Da sauri Ilham ta karaso palour da sauri "Au wai kaima baka San inda yakeba, na dauka kana tare da shi" Ilham tai maganar a firgice "Eh amma ki kwantar da hankalinki zanje nemansa insha Allah ze dawo nasan ba nisa yayi ba, ni abinda yafi dagamin hankali dana je na tarar ya farfasa abubuwa a dakinsa" Zare ido mummy tayi "Haba dai?" "Eh mummy shiyasa ma nazo na tambayeki, narasa meyake damunsa" "Watakila giyar ya sha tagaya masa karya, amma muje bangaren nasa" Tare suka tafi da mummy da Ilham suna zuwa suka tarar da mugun aika² da Jalal yayi duk wani abu me fashewa Jalal ya fasashi, hankalin mummy ya ta shi sosai "Na shiga uku Jawwad meyasami Jalal hakane? Be taba irin wannan abunba fa" Ita kanta Ilham abun yabata mamaki sekace dakin mahaukaci ya farfasa abubuwa Jawwad ne cikin muryar rarrashi yafara magana "Ki kwantar da hankalinki mummy, insha Allah ze dawo gida, amma yanzu bari in fita in dudduba inda yake zuwa na San tabbas akwai abunda yake damunsa" Gyada kai mummy tayi tana share hawaye   Bayan mummy da Ilham sun koma cikin gidane mummy se kuka take "Allah yasa yaron nan ba haukacewa yayi ba," "Haba mummy ya kike fadin hakane, insha Allah lafiyarsa kalau" Ilham ta fada cike da kwarin gwiwa sannan ta nufi dakinta tana zuwa dakin ta kule tasaka masa key Sannan ta kira mahaifiyarta "Hello maami" "Na am Ilham, yakike akwai labarine" "Eh Mami, Jalal ne ya haukace fa" "Kamar ya ya haukace ban gane me kike nufi ba," "To hauka mana kwana hudu yana kulle kansa a daki Jawwad kawai yake budewa, yau kuma shima din be bude masa ba, ya fita dazu da yamma, amma duk ya farfasa kayan dakinsa bakiga dakinba kamar mahaukaci" "Ina baze yiwuba, bahaka nakeso ya kasance ba, ba hauka nakeso yayi ba, idan yayi hauka Dan gatan mahaukaci ze zama, Sonake se yazo hannunmu mun wulakanta hadiza, mun tozarta ta, setayi kuka fiye da Wanda tayi a baya" "Amma Mami ta Yaya kina gani kullum shirinmu rushewa yake, abinda ya kawoni gidan nan shekara da shekaru mun kasa samu" "Amma kinsan duk laifinkine da rashin kokari Ilham ni narasa ma zaman me kikeyi abu yakici yaki cinyewa tsawon shekaru" "Maami dukfa abinda kikasani inayi, amma kinsanshi muguwar gaddama CE dashi gashi jarababbe" "Hakane amma zankoma gurin malamin nan inji mekuma zecemana" "To Mami, yadda kukayi kya gayamin, amma da gani nake kawai inyi me gaba dayan nan ina fargabar aikinmu ya lalace" "Har yanzu kina ganin alamar yana da budurwa ne?" "Eh mana Mami shiyasa duk na tsorata fa" "Ki kwantar da hankalinki babu abunda ze faru just focus" "To mamina nagode, amma bakiga kukan da mummy tayiba" "Ita tasani ni be dameniba" Haka sukayi sallama da mamanta Jalila ce ta fito harabar gidan da parker a hannunta taga Jawwad a sukwane ze bude motarsa, da sauri Jalila taje gurinsa "Yaya lafiya ina Zaka haka naganka a firgice" "Jalila Jalal ne banganiba gashi ya farfasa abubuwa a dakinsa bansan inda ya tafiba, shi zan tafi nema" "To ai dazu da nafita raka halima naga fitarsa a mota kamar ze tashi sama, yana ta gudu a mota" "Are u serious?" "Of course naganshi dazu, amma Yaya Jawwad ka nutsu mana, duk ka tayar da hankalinka" "Jalila, Jalal be taba hakaba bakiga dakinsaba kamar ba dakin Dan Adam ba ya fasa komai" Gabanta ne yafadi "to ko in raka ka ?" "No kizauna bari inje" "To adawo lafiya Allah ya kiyaye, amma kayi driving a hankali" Gyada mata kai yayi ya shige motar yajata da sauri Share please More comments more typing....................... Inajin dadin comments dinku, kuna comments ina muku typing Am proud of you all ❤❤❤❤ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 32 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Jawwad ya ja motar yabar cikin gidan, fara zagawa yayi clubs din da yasan Jalal yana zuwa amma be sameshi ba, tun bayan magariban nan yake yawo amma be samu ganinsa ba, Gida ya koma yabar motarsa a bakin layi yakoma part din Jalal ya dakko wayar Jalal ya koma inda yabar motarsa, ya shiga ya zauna cire wayar yayi daga key dayake yasan password din, call log dinshi ya duba yaga kiran Hannah dayawa amma be daga ba lambar Jeje itace ta karshe da aka kirashi dashi kuma shima be amsaba, Dafe kai Jawwad yayi "ohh my God Jalal ina kashiga ne karka yiwa kanka Illa mana" Lamabar Jeje ya kira, yai Sa a kuwa Jeje ya daga "Ina Jalal yake?" "Kamar Yaya?" Jeje ya tambayeshi "Kamar yadda na tambayeka" Jawwad ya bashi amsa "Ohhh in ka damu da shi seka zagaya mashayar da yake zuwa kaneme shi," Jeje ya kashe wayarsa Girgiza kai Jawwad yayi ya kuma kunna motarsa ya marasa ina ze dosa Neman Jalal Haka ya dinga zaga clubs har gurin goman dare, club din dayaje da farko ya koma Wanda nan Jalal yafi zuwa, Jawwad ya duba ko ina amma bega Jalal ba, Yazo ze fita ya hangi motar Jalal a can wani guri da sauri ya fito ya nufi inda motar Jalal take, bude motar yayi da sauri Jalal yana zube a cikin motar ya fita hayyacinsa sosai, gashi nan dai shiba sumamme ba kuma shiba me bacci ba Dagoshi Jawwad yayi yana jijjiga shi Da sauri Jawwad ya koma ya bada ajiyar motarsa gurin masu gadin club din ya shiga motar Jalal ya jata ya nufi Gida   Jalila kam tagagara yin bacci tunda Jawwad ya fita tana palour a zaune tana jiran dawowarsa tun suna hira da Halima har Halima ta tafi ta kwanta tabar Jalila a palour Karfe sha dayan dare taji motar Jawwad ya dawo Da sauri ta fito setaga motar Jalal, tana nan tsaye taga Jawwad ya fito daga motar "Yaya lafiya kuwa naga ka Dade?" "Baby da kyar Nagano Jalal, yanzu dare yayi bari inkira Me gadin gidansu Jalal ya kama minshi in kaishi part dina" "To shike nan" Jawwad ya juya da sauri, Jalila takarasa bakin motar ta leka, Jalal yana kwance Kamar gawa, ba a dadeba Sega Jawwad sun dawo dame gadi Suka fito da Jalal suka shiga dashi suka kwantar da shi akan gadon Jawwad Jalila ta kalli Jawwad "yaya wai meyasameshi? Bashi da lafiyane" "Wallahi ban saniba Jalila inaga giya ya sha dayawa" Dan zare ido Jalila tayi "To se yaushe ze tashi" "Se lokacin data sake shi, amma akwai abunda yake damunsa a rai, Wanda bansaniba" Jawwad yafada cike da damuwa "Yaya kalli yadda yake numfashi ko bashi da lafiya, kalli jijiyar kansa fa duk sun daga" Jawwad ya kai hannu goshin Jalal yayi zafi sosai "Da alama kansa yana ciwo ma" Kafarsa Jalila ta kalla ta mike da sauri "Yaya Jawwad kalli kwalabe sun fasa masa kafa" Da hanzari Jawwad yazo ya duba kwalabe duk sun shige kafarsa "Ya salam inaga bari in fita akwai wani abokinmu likitane, bari inga in yana nan yazo ya duba shi inba ya nan kuma, inzo in kaishi asibiti" Ya Ciro wayar JALAL ya ajiyeta akan side bed "To kayi sauri danni tsoro nakeji palour zan koma danaga ya taso in zura da gudu" "Jalila da hankalinsa ba haukacewa yayiba kinji, ki zauna a parlour kiji rani" Gyada masa kai tayi, ta fito parlour ta zauna shikuma Jawwad ya fita lokaci² Jalila seta leka dakin taganshi a kwance yadda a aka barshi, motsi taga yafarayi a hankali yana yamutsa fuska yana surutai cikin maye "Hannah meye hakane, bakida hankaline,? Mtseww nace miki bana so fa, bana son yimiki rashin mutuncine amma ba kya ganewa" A hankali Jalila ta Dan shiga dakin tana kallonsa "To wace kuma Hannah," Jalila tayi maganar a zuciyarta Cigaba yayi da surutai idonsa a rufe ya cigaba "Nifa Jeje giyar nan yau kaman ba irin wadda nasaba sha bace kamar akwai wani abu a ciki, mtseww, nii ban San meyake damuna ba Jawwad baya son giyar nan danake sha fa" Jalila ta kalleshi "Kai ni dalla ka isheni ka cikamin kunne, kayimin shiru, nina aikeka ka sha kalleka Dan Allah, mutum har mutum amma ba hankali, ko kunya bakaji kake shan giya kai ko tsoron Allah bakaji ma bana tunanin kayi sallar isha'i, kana kwance kana maye, kasa Yaya se wahala yake in bakayimin shiruba nida kaine" Jalila se rashin M takewa Jalal shikam baya hayyacinsa, yacigaba da surutansa "Ko wace kuma Hannah oho masa" Wayar Jalal ce tafara ringing ta kalla sunan Hannah ta gani a kan screen din wayarsa, "Hmm kishiyar Ilham ce Ashe" Tayi banza da wayar takoma palour, wayarce ta cigaba da ringing ta cikawa Jalila kunne Dan haka ta mike ta koma bedroom din ta kai hannu ta daga wayar "Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, me wayar kin ganshi a kwance, tunda kika kira be dagaba ai seki hakura ko, saboda shirme a tsohon Daren nan haba, kinkira ba adagaba sekace mayya duk kincikamin kunne" Jalila tai tsaki ta kashe wayar ta kai hannu zata aje wyar ya rike hannunta gam ya bude Jajayen idanuwansa fes akan JALILA Kwalalo ido Jalila tayi ta firgita matuka "Meye haka kacikamin hannuna" Ko kyafta idonsa bayayi akanta gashi ya riketa gam ko motsa hannun bata iyawa, idonsa tsoror yake bata "Na shiga uku nika cikani, dama ance watakila ka haukace" Kara karfin rikon yayi mata "Wai meye hakane" Setaga hawaye na bin gefen idonsa can yayi wani yunkuri se yafara amai kumface kawai take fita daga bakinsa, yasaki hannun Jalila a hankali Zare ido tayi dataga irin aman dayakeyi "Nikam ina Yaya Jawwad ya tsaya haka"   Itakam Hannah mamakine ya cikata wace ta dauki wayar Jalal a Daren nan, OK ko Itace kanwar tasa da Jawwad yake fada, to me take masa a wannan lokacin haka? "Tabdijan to wallahi da sake akwai matsala" Jalila ta koma bakin kofa ta zuba masa ido Dan tarasa meya kamata tayi can jimawa Sega Jawwad ya dawo shida wani "Sorry Jalila kinganni ban dawo da wuriba, seda naje Asibiti na dakko likitan" "To gashi can dai wani irin amai yakeyi yana surutai" Da sauri Jalal da likitan suka shiga cikin dakin Likitan ya kalli bakin Jalal duk wannan kumfar fara "Subhanallah" ya furta yasaka abu ya goge masa kumfar yayi masa wasu allurai Jalal ya dinga aman abunda yaci Likitan ya kalli Jawwad "Jawwad Jalal wasu miyagun kwayoyi yasha Wanda besaba shan irinsu BA, suke nema suyi masa illa" "Bayan giyar kuma hada kwayoyi" Jalila tafada cikin mamaki "To gashi nan dai, kuma da alama ya Dade beci abinci ba" Likitan yabata amsa, girgiza kai kawai Jawwad yayi, Jalila ta koma palour Shida likitan suka gyara gurinda Jalal yai aman suka canzamasa kaya zuwa Jallabiya Kafar Jalal aka ciremasa kwalaben daya taka, sannan yasa masa drip, ya rubuta magunguna yacewa Jawwad da safe yaje ya siyo masa, "Yaya ni Bacci nakeji seda safe" "To baby mungode sosai, kiyi bacci me dadi" "To Yaya kaima ka kwanta haka dare yayi" Ya gyda mata kai likitanne ya kalli Jalila "Baby ni baza ayimin sallama ba?" Dan murmushi tayi "Seda safe tafada a takaice" Jawwad kam Dan hade rai yayi, ya kalli likitan "muje in maida kai" "Jawwad dan Allah wannan babyn fa nifa na faller wallahi, Yar gayu da ita ga iyayi" "Ina ruwanka da wacece, nifa banason irin wannan abun salis, muje in saukeka ni" "Tuba nake sirikina amma nikam naga guri" Fusata Jawwad yayi "kaga wuce muje" Haka suka tafi ya maida doctor, se bayan karfe daya sannan Jawwad yasamu nutsuwa lokacin drip din jikin Jalal ya kare ya cire masa, sannan ya kwanta   Bayan sallar asuba Jalila take gayawa Nana a gidan Jalal ya kwana, yanata a man kwayoyin da yasha "Tab to indai wannan ne sun saba, amma iya sanina baya shan miyagun kwayoyi, sedai giya da taba, watakila Suma yafara watsa abunsa wayasani, kice hadake akai jinya" Nana tafada Dan Neman magana "God forbid indai Dan ta shine, yaje ya karata ni Yaya Jawwad ne abun tausayi wallahi" "Mutane dayawa na mamakin kaunar da sukewa Juna, Allah ne ya hada jininsu" "Kuma a haka Aminiyarki take sonshi"? " mhmm kema dai kyafada" "Hakane, amma Nana Dan Allah wace Hannah" "Hannah kuma? A ina take" Se Jalila ta fuskanci Nana batasan zancenba Dan haka tace "OK don't mind me kwanta kikoma baccinki, Dan nasan yanzu shiya dameki" "Aikuwa kamar kuwa kinsani" Jalila kam mikewa tayi ta tafi kitchen Dan sarrafa abunda za a bawa ciki, Jalila tana matukar son harkar girke² Tunda sauran duhun asuba ta shiga kitchen zuwa bakwai da rabi ta kammala A palour ta hadu da halima "Anty leemat barka da safiya" "Barka dai sayyada Jalila, naji kamshi yana tashi ba dai kingama girkin ba" "Nagama, kina bacci ne shiyasa ban tasheki ba" "Sannu da kokari, ke ba kyajin aiki Sam, amma tun asuba kika fara" "Eh halima, wallahi kinga Jalal ne ba lafiya za a bashi magani da safe nasan Yaya Jawwad ni ze roka in hada musu breakfast, kinga gara ayi tunkafin yayi maganaa" "Gaskiya kam, bari inje in karasa, aikin da ya rage" Zuwan Jalila gidan nan ba karamin amfani yake musu ba Sam batada kyuya, ba ta San kazanta Sam, shiyasa Jawwad yake jin dadin sakata aiki ba kyuya, amma Nana yanzu zata bata rai tana tura baki, ga son jiki a cikin Nana, kuma Maama take biyemata Ta hado kayan Abincin ta kai part din Jawwad, ta tarar yana zaune a palour da Azkar a hannunsa, sallama datayine yasashi dagowa Murmushinsa ya fadada "Sannu da kokari baby, yanzu nake tunanin yaza ayi da breakfast, naga jiya baki kwanta da wuri ba kar in takura miki, nagode da kulawar da kike bamu, sannu da kokari" Karasawa tayi parlour ta ajiye kayan abincin ta  kalleshi "Barka da safiya, Dan uwa rabin jiki," "Au bazaki amsa sannun nawa ba" "Ni lafiyata kalau, wancan mutumin na cikin dakinka zakayiwa sannu, shine Mara lafiya" "Kinganki baby, Jalal dinne mutumi ko? In yajiki ba ruwana, kinsan boss din ba wasa" "Hmmm lallai boss naga alama" Sukayi dariya a tare JAWWAD yace "Jikin nasa da sauki, ya tashi tun dazu yanzuma wanka yakeyi" "To Allah ya sawwake" "Ameen baby" Kallonsa Jalila tayi sannan tace "Dan uwana" "Na am kanwata" "Bakayi bacci sosai ba idonka ya nuna" "Kema bakiyi bacci ba gashi kuma nasan kin gaji" "Ni bangajiba" "Dagaske" "Eh mana, kasan wani abu" "A a baby sekin fada" "Yayana kaina mussamanne a cikin mutane, halinka halin Abba, kanada kirki yayana, Allah yaabamu itaku" "Baby ni banga wani kirki danake dashi ba, kinfini kirki baby, sedai ince Allah yabamu itaku" Zumbura baki Jalila tayi "Nida ake cemin masifaffiya, uwar Neman magana," Dariya Jawwad yake sosai "Wayagaya miki haka"? Bude kofar bedroom din Jalal yayi ya fito yana dingisa kafarsa Jallabiyar Jawwad ce a jikinsa tayi masa kyau sedai fuskarsa ta rame Karasowa yayi ya zauna a kusa da Jawwad "Sannu Jalal ya jikin naka?" Jawwad yafada cikin damuwa "Da sauki, Nagode Jawwad" Jalal yafada a hankali "Kasan zamuyi fada ko tom yanzu ga breakfast baby ta kawo, ka karya se inje in gayawa mummy kadawo daga nan in siyo maka magani" Gyada masa kai kawai Jalal yayi "Baby bakiwa Jalal ya jiki ba" "To ai naga ya warke tunda gashinan da kafarsa" "Jalila sarkin magana yanzu dai jeki kawo mana ruwan dumi Wanda za a gasa masa kafarsa" "To" ta mike tabar parlour, Jawwad yahada masa breakfast din sannan ya mike "bari inje in siyo maganin, in ta kawo ruwan dumin in bazaka iya gasawa ba kabari in dawo" Jinjina kai Jalal yayi, har Jawwad ya nufi hanyar fita ya tsaya ya waigo "Yawwa idan na dawo kuma zaka gayamin meyasa ka fasa kwalabe ka taka seka gayamin meyake damunka" Still dai bece komai ba Jawwad seda yaje yagayawa mummy yaga Jalal yanzu haka ma yana gidansu, amma bashi da lafiya Mummy taita godiya tana sawa Jawwad albarka, Ilham kuwa najin haka ta gashi ta tafi gidansu Nana domin ganin Jalal, Jawwad kuma yatafi  karbo magun gunan Jalila ta kawo ruwan zafi a flask tai sallama amma yamata shiru tazo ta dire flask dina gefen Jalal "Wai ba nace ka dinga amsa sallama ba, Gashi nan ruwan zafine in kaga dama ka dumama ka gasa kafar taka in baka ga damaba ka zuba a haka" har zata fita dawo ta tsaya a gaban Jalal "Saboda wauta waya gaya maka in abu na damun mutum haka akeyi kafasa kwalabe kabi ta kai, kuma kaje ka sha kwayoyi, kakusa kashe kanka daka mutu haka zaka farka a kabari Ga laifin sabawa iyaye, ga shan giya, ga kashe kanka dakayi da abun yamaka yawa, in abu yana damun mutum a zuciyarsa addu a yakeyi ya koma ga Allah, ba ya aikata wannan shirmen da kakeyiba, duk Wanda be kiyaye salollinsa akan lokaciba haka kunci zeta damun rayuwarsa" Yana jinta ya cigaba da cin Abincinsa dukda bawani ci yakeba cakala kawai yake, yana tausayawa ranar daze hukunta Jalila, se yanzu ta kai duba ga cin abincin dayakeyi, da hannun hagu yakecin Abincin "Subhanallah Kaikam komai naka na dabanne, komai naka ba irin na mutane ba" Tasa hannu ta karbe cokalin hannunsa daga hannun hagu ta zira masa a hannun dama "Shedan ne yake cin Abinci da hannun hagu, Allah yasa kayi bisimillah kan kafara cin abincin" Dago idonsa yayi yasaka a cikin na Jalila "Kin manta waye Jalal ko?" "Eh namanta seka tunamin" Ilham ce ta shigo palourn ba ko sallama a tare suka waigo suka kalli Ilham Ilham ce tayi mutuwar tsaye ganin Jalila a tsaye a gaban Jalal shikuma yana kallonta ga abinci agabansa kamar wasu masoya Watakilama a baki take bashi abincin wani sashi na Zuciyarta ya zigata "Mezan gani haka? Yaya Jalal menayimaka haka, kake kokarin cin amanata wannan itace sakamakon soyayyar dana dau shekaru inamaka, lokaci daya kayimin haka dama abunda na Dade INA zargine yau Allah ya nunamin" Saroro Jalila tayi tana kallonta Ilham ta dawo da idonta kan Jalila "Munafuka kina cemin Yar wahala Ashe kece babbar Yar wahala, Ashe hasashena ya tabbata son Jalal kike, to wallahi baki isaba kinyi kadan kiyi takara dani akan abunda nakeso bans..... " enough malama karkiga nayi miki shiru kicigaba da zagina, mezanso anan" ta nuna Jalal "Ni abu na kawo nake masa magana akan abunda ya aikatawa kansa banda haka ni babu abinda ze hadani da shi" Shidai Jalal bece musu uffan ba sema mamakin hakikancewa da Ilham take, yakeyi "Karya kike wallahi ko duk jikina kunne ne bazan yaddaba kuma wallahi Jalila sekinyi danasanin abunda kikayimin, sena baki mamaki " ya isheki malama" Jalila ta karaso gaban Ilham "bude idonki da kyau, ki bude kwakwalwarki kiga da wacce kikeyi, inkin manta bari in tuna miki  Jalila ce dawo hayyacinki, Dan kinga ina lallabaki ba amin hauka wallahi yanzun nan zan saukemiki abunda yake damunki Me akai akayi Jalal meye abinso a tareda Jalal wannan makakken Mara tarbiyya, shi kike nufi  Jalila taso, ko ta nuna a matsayin uban yayanta, a tunaninki zan tsaya ina daga murya saboda shi Yadda yake a maken nan ai se makakkiya Yar uwarsa, badai Jalila ba ni mutumin arziki zan aura Dan babu uban me hankalin daze bawa wannan yarsa a haka Kema da kike sonnashi kinada manufar hakan badan hakaba yadda yake wulakantashi yaci ace kin hakura useless and hopeless creatures dagake harshi" Tirkashi Share please More comments more typing......................  Ina alfahari daku a kullum masoyana da masuyimin addu a Ina godiya me tarinyawa inajin daddin comments dinku❤❤❤ SANARWA!!! wasu suna tambayata ko nayi joining wata kungiyane na online writers Gaskiya ni banyi joining kowace kungiya ba, kamar yadda kuke gani wannan shine Novel dina na farko, kuma basirata ce nake amfani gurin nishadantar daku tareda aikawa da wasu sakonni, babu wata ko wani marubuci dayake bani gudunmuwa Dafatan masu tambaya kun gamsu Game gyara, comments, tambaya ko korafi, akwai lamabata danake sakawa a farkon kowane page a tuntubeni ta wannan lambar nagode Taku har kullum Yar babanta(daddy's girl) 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 32 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Jawwad ya ja motar yabar cikin gidan, fara zagawa yayi clubs din da yasan Jalal yana zuwa amma be sameshi ba, tun bayan magariban nan yake yawo amma be samu ganinsa ba, Gida ya koma yabar motarsa a bakin layi yakoma part din Jalal ya dakko wayar Jalal ya koma inda yabar motarsa, ya shiga ya zauna cire wayar yayi daga key dayake yasan password din, call log dinshi ya duba yaga kiran Hannah dayawa amma be daga ba lambar Jeje itace ta karshe da aka kirashi dashi kuma shima be amsaba, Dafe kai Jawwad yayi "ohh my God Jalal ina kashiga ne karka yiwa kanka Illa mana" Lamabar Jeje ya kira, yai Sa a kuwa Jeje ya daga "Ina Jalal yake?" "Kamar Yaya?" Jeje ya tambayeshi "Kamar yadda na tambayeka" Jawwad ya bashi amsa "Ohhh in ka damu da shi seka zagaya mashayar da yake zuwa kaneme shi," Jeje ya kashe wayarsa Girgiza kai Jawwad yayi ya kuma kunna motarsa ya marasa ina ze dosa Neman Jalal Haka ya dinga zaga clubs har gurin goman dare, club din dayaje da farko ya koma Wanda nan Jalal yafi zuwa, Jawwad ya duba ko ina amma bega Jalal ba, Yazo ze fita ya hangi motar Jalal a can wani guri da sauri ya fito ya nufi inda motar Jalal take, bude motar yayi da sauri Jalal yana zube a cikin motar ya fita hayyacinsa sosai, gashi nan dai shiba sumamme ba kuma shiba me bacci ba Dagoshi Jawwad yayi yana jijjiga shi Da sauri Jawwad ya koma ya bada ajiyar motarsa gurin masu gadin club din ya shiga motar Jalal ya jata ya nufi Gida   Jalila kam tagagara yin bacci tunda Jawwad ya fita tana palour a zaune tana jiran dawowarsa tun suna hira da Halima har Halima ta tafi ta kwanta tabar Jalila a palour Karfe sha dayan dare taji motar Jawwad ya dawo Da sauri ta fito setaga motar Jalal, tana nan tsaye taga Jawwad ya fito daga motar "Yaya lafiya kuwa naga ka Dade?" "Baby da kyar Nagano Jalal, yanzu dare yayi bari inkira Me gadin gidansu Jalal ya kama minshi in kaishi part dina" "To shike nan" Jawwad ya juya da sauri, Jalila takarasa bakin motar ta leka, Jalal yana kwance Kamar gawa, ba a dadeba Sega Jawwad sun dawo dame gadi Suka fito da Jalal suka shiga dashi suka kwantar da shi akan gadon Jawwad Jalila ta kalli Jawwad "yaya wai meyasameshi? Bashi da lafiyane" "Wallahi ban saniba Jalila inaga giya ya sha dayawa" Dan zare ido Jalila tayi "To se yaushe ze tashi" "Se lokacin data sake shi, amma akwai abunda yake damunsa a rai, Wanda bansaniba" Jawwad yafada cike da damuwa "Yaya kalli yadda yake numfashi ko bashi da lafiya, kalli jijiyar kansa fa duk sun daga" Jawwad ya kai hannu goshin Jalal yayi zafi sosai "Da alama kansa yana ciwo ma" Kafarsa Jalila ta kalla ta mike da sauri "Yaya Jawwad kalli kwalabe sun fasa masa kafa" Da hanzari Jawwad yazo ya duba kwalabe duk sun shige kafarsa "Ya salam inaga bari in fita akwai wani abokinmu likitane, bari inga in yana nan yazo ya duba shi inba ya nan kuma, inzo in kaishi asibiti" Ya Ciro wayar JALAL ya ajiyeta akan side bed "To kayi sauri danni tsoro nakeji palour zan koma danaga ya taso in zura da gudu" "Jalila da hankalinsa ba haukacewa yayiba kinji, ki zauna a parlour kiji rani" Gyada masa kai tayi, ta fito parlour ta zauna shikuma Jawwad ya fita lokaci² Jalila seta leka dakin taganshi a kwance yadda a aka barshi, motsi taga yafarayi a hankali yana yamutsa fuska yana surutai cikin maye "Hannah meye hakane, bakida hankaline,? Mtseww nace miki bana so fa, bana son yimiki rashin mutuncine amma ba kya ganewa" A hankali Jalila ta Dan shiga dakin tana kallonsa "To wace kuma Hannah," Jalila tayi maganar a zuciyarta Cigaba yayi da surutai idonsa a rufe ya cigaba "Nifa Jeje giyar nan yau kaman ba irin wadda nasaba sha bace kamar akwai wani abu a ciki, mtseww, nii ban San meyake damuna ba Jawwad baya son giyar nan danake sha fa" Jalila ta kalleshi "Kai ni dalla ka isheni ka cikamin kunne, kayimin shiru, nina aikeka ka sha kalleka Dan Allah, mutum har mutum amma ba hankali, ko kunya bakaji kake shan giya kai ko tsoron Allah bakaji ma bana tunanin kayi sallar isha'i, kana kwance kana maye, kasa Yaya se wahala yake in bakayimin shiruba nida kaine" Jalila se rashin M takewa Jalal shikam baya hayyacinsa, yacigaba da surutansa "Ko wace kuma Hannah oho masa" Wayar Jalal ce tafara ringing ta kalla sunan Hannah ta gani a kan screen din wayarsa, "Hmm kishiyar Ilham ce Ashe" Tayi banza da wayar takoma palour, wayarce ta cigaba da ringing ta cikawa Jalila kunne Dan haka ta mike ta koma bedroom din ta kai hannu ta daga wayar "Dan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, me wayar kin ganshi a kwance, tunda kika kira be dagaba ai seki hakura ko, saboda shirme a tsohon Daren nan haba, kinkira ba adagaba sekace mayya duk kincikamin kunne" Jalila tai tsaki ta kashe wayar ta kai hannu zata aje wyar ya rike hannunta gam ya bude Jajayen idanuwansa fes akan JALILA Kwalalo ido Jalila tayi ta firgita matuka "Meye haka kacikamin hannuna" Ko kyafta idonsa bayayi akanta gashi ya riketa gam ko motsa hannun bata iyawa, idonsa tsoror yake bata "Na shiga uku nika cikani, dama ance watakila ka haukace" Kara karfin rikon yayi mata "Wai meye hakane" Setaga hawaye na bin gefen idonsa can yayi wani yunkuri se yafara amai kumface kawai take fita daga bakinsa, yasaki hannun Jalila a hankali Zare ido tayi dataga irin aman dayakeyi "Nikam ina Yaya Jawwad ya tsaya haka"   Itakam Hannah mamakine ya cikata wace ta dauki wayar Jalal a Daren nan, OK ko Itace kanwar tasa da Jawwad yake fada, to me take masa a wannan lokacin haka? "Tabdijan to wallahi da sake akwai matsala" Jalila ta koma bakin kofa ta zuba masa ido Dan tarasa meya kamata tayi can jimawa Sega Jawwad ya dawo shida wani "Sorry Jalila kinganni ban dawo da wuriba, seda naje Asibiti na dakko likitan" "To gashi can dai wani irin amai yakeyi yana surutai" Da sauri Jalal da likitan suka shiga cikin dakin Likitan ya kalli bakin Jalal duk wannan kumfar fara "Subhanallah" ya furta yasaka abu ya goge masa kumfar yayi masa wasu allurai Jalal ya dinga aman abunda yaci Likitan ya kalli Jawwad "Jawwad Jalal wasu miyagun kwayoyi yasha Wanda besaba shan irinsu BA, suke nema suyi masa illa" "Bayan giyar kuma hada kwayoyi" Jalila tafada cikin mamaki "To gashi nan dai, kuma da alama ya Dade beci abinci ba" Likitan yabata amsa, girgiza kai kawai Jawwad yayi, Jalila ta koma palour Shida likitan suka gyara gurinda Jalal yai aman suka canzamasa kaya zuwa Jallabiya Kafar Jalal aka ciremasa kwalaben daya taka, sannan yasa masa drip, ya rubuta magunguna yacewa Jawwad da safe yaje ya siyo masa, "Yaya ni Bacci nakeji seda safe" "To baby mungode sosai, kiyi bacci me dadi" "To Yaya kaima ka kwanta haka dare yayi" Ya gyda mata kai likitanne ya kalli Jalila "Baby ni baza ayimin sallama ba?" Dan murmushi tayi "Seda safe tafada a takaice" Jawwad kam Dan hade rai yayi, ya kalli likitan "muje in maida kai" "Jawwad dan Allah wannan babyn fa nifa na faller wallahi, Yar gayu da ita ga iyayi" "Ina ruwanka da wacece, nifa banason irin wannan abun salis, muje in saukeka ni" "Tuba nake sirikina amma nikam naga guri" Fusata Jawwad yayi "kaga wuce muje" Haka suka tafi ya maida doctor, se bayan karfe daya sannan Jawwad yasamu nutsuwa lokacin drip din jikin Jalal ya kare ya cire masa, sannan ya kwanta   Bayan sallar asuba Jalila take gayawa Nana a gidan Jalal ya kwana, yanata a man kwayoyin da yasha "Tab to indai wannan ne sun saba, amma iya sanina baya shan miyagun kwayoyi, sedai giya da taba, watakila Suma yafara watsa abunsa wayasani, kice hadake akai jinya" Nana tafada Dan Neman magana "God forbid indai Dan ta shine, yaje ya karata ni Yaya Jawwad ne abun tausayi wallahi" "Mutane dayawa na mamakin kaunar da sukewa Juna, Allah ne ya hada jininsu" "Kuma a haka Aminiyarki take sonshi"? " mhmm kema dai kyafada" "Hakane, amma Nana Dan Allah wace Hannah" "Hannah kuma? A ina take" Se Jalila ta fuskanci Nana batasan zancenba Dan haka tace "OK don't mind me kwanta kikoma baccinki, Dan nasan yanzu shiya dameki" "Aikuwa kamar kuwa kinsani" Jalila kam mikewa tayi ta tafi kitchen Dan sarrafa abunda za a bawa ciki, Jalila tana matukar son harkar girke² Tunda sauran duhun asuba ta shiga kitchen zuwa bakwai da rabi ta kammala A palour ta hadu da halima "Anty leemat barka da safiya" "Barka dai sayyada Jalila, naji kamshi yana tashi ba dai kingama girkin ba" "Nagama, kina bacci ne shiyasa ban tasheki ba" "Sannu da kokari, ke ba kyajin aiki Sam, amma tun asuba kika fara" "Eh halima, wallahi kinga Jalal ne ba lafiya za a bashi magani da safe nasan Yaya Jawwad ni ze roka in hada musu breakfast, kinga gara ayi tunkafin yayi maganaa" "Gaskiya kam, bari inje in karasa, aikin da ya rage" Zuwan Jalila gidan nan ba karamin amfani yake musu ba Sam batada kyuya, ba ta San kazanta Sam, shiyasa Jawwad yake jin dadin sakata aiki ba kyuya, amma Nana yanzu zata bata rai tana tura baki, ga son jiki a cikin Nana, kuma Maama take biyemata Ta hado kayan Abincin ta kai part din Jawwad, ta tarar yana zaune a palour da Azkar a hannunsa, sallama datayine yasashi dagowa Murmushinsa ya fadada "Sannu da kokari baby, yanzu nake tunanin yaza ayi da breakfast, naga jiya baki kwanta da wuri ba kar in takura miki, nagode da kulawar da kike bamu, sannu da kokari" Karasawa tayi parlour ta ajiye kayan abincin ta  kalleshi "Barka da safiya, Dan uwa rabin jiki," "Au bazaki amsa sannun nawa ba" "Ni lafiyata kalau, wancan mutumin na cikin dakinka zakayiwa sannu, shine Mara lafiya" "Kinganki baby, Jalal dinne mutumi ko? In yajiki ba ruwana, kinsan boss din ba wasa" "Hmmm lallai boss naga alama" Sukayi dariya a tare JAWWAD yace "Jikin nasa da sauki, ya tashi tun dazu yanzuma wanka yakeyi" "To Allah ya sawwake" "Ameen baby" Kallonsa Jalila tayi sannan tace "Dan uwana" "Na am kanwata" "Bakayi bacci sosai ba idonka ya nuna" "Kema bakiyi bacci ba gashi kuma nasan kin gaji" "Ni bangajiba" "Dagaske" "Eh mana, kasan wani abu" "A a baby sekin fada" "Yayana kaina mussamanne a cikin mutane, halinka halin Abba, kanada kirki yayana, Allah yaabamu itaku" "Baby ni banga wani kirki danake dashi ba, kinfini kirki baby, sedai ince Allah yabamu itaku" Zumbura baki Jalila tayi "Nida ake cemin masifaffiya, uwar Neman magana," Dariya Jawwad yake sosai "Wayagaya miki haka"? Bude kofar bedroom din Jalal yayi ya fito yana dingisa kafarsa Jallabiyar Jawwad ce a jikinsa tayi masa kyau sedai fuskarsa ta rame Karasowa yayi ya zauna a kusa da Jawwad "Sannu Jalal ya jikin naka?" Jawwad yafada cikin damuwa "Da sauki, Nagode Jawwad" Jalal yafada a hankali "Kasan zamuyi fada ko tom yanzu ga breakfast baby ta kawo, ka karya se inje in gayawa mummy kadawo daga nan in siyo maka magani" Gyada masa kai kawai Jalal yayi "Baby bakiwa Jalal ya jiki ba" "To ai naga ya warke tunda gashinan da kafarsa" "Jalila sarkin magana yanzu dai jeki kawo mana ruwan dumi Wanda za a gasa masa kafarsa" "To" ta mike tabar parlour, Jawwad yahada masa breakfast din sannan ya mike "bari inje in siyo maganin, in ta kawo ruwan dumin in bazaka iya gasawa ba kabari in dawo" Jinjina kai Jalal yayi, har Jawwad ya nufi hanyar fita ya tsaya ya waigo "Yawwa idan na dawo kuma zaka gayamin meyasa ka fasa kwalabe ka taka seka gayamin meyake damunka" Still dai bece komai ba Jawwad seda yaje yagayawa mummy yaga Jalal yanzu haka ma yana gidansu, amma bashi da lafiya Mummy taita godiya tana sawa Jawwad albarka, Ilham kuwa najin haka ta gashi ta tafi gidansu Nana domin ganin Jalal, Jawwad kuma yatafi  karbo magun gunan Jalila ta kawo ruwan zafi a flask tai sallama amma yamata shiru tazo ta dire flask dina gefen Jalal "Wai ba nace ka dinga amsa sallama ba, Gashi nan ruwan zafine in kaga dama ka dumama ka gasa kafar taka in baka ga damaba ka zuba a haka" har zata fita dawo ta tsaya a gaban Jalal "Saboda wauta waya gaya maka in abu na damun mutum haka akeyi kafasa kwalabe kabi ta kai, kuma kaje ka sha kwayoyi, kakusa kashe kanka daka mutu haka zaka farka a kabari Ga laifin sabawa iyaye, ga shan giya, ga kashe kanka dakayi da abun yamaka yawa, in abu yana damun mutum a zuciyarsa addu a yakeyi ya koma ga Allah, ba ya aikata wannan shirmen da kakeyiba, duk Wanda be kiyaye salollinsa akan lokaciba haka kunci zeta damun rayuwarsa" Yana jinta ya cigaba da cin Abincinsa dukda bawani ci yakeba cakala kawai yake, yana tausayawa ranar daze hukunta Jalila, se yanzu ta kai duba ga cin abincin dayakeyi, da hannun hagu yakecin Abincin "Subhanallah Kaikam komai naka na dabanne, komai naka ba irin na mutane ba" Tasa hannu ta karbe cokalin hannunsa daga hannun hagu ta zira masa a hannun dama "Shedan ne yake cin Abinci da hannun hagu, Allah yasa kayi bisimillah kan kafara cin abincin" Dago idonsa yayi yasaka a cikin na Jalila "Kin manta waye Jalal ko?" "Eh namanta seka tunamin" Ilham ce ta shigo palourn ba ko sallama a tare suka waigo suka kalli Ilham Ilham ce tayi mutuwar tsaye ganin Jalila a tsaye a gaban Jalal shikuma yana kallonta ga abinci agabansa kamar wasu masoya Watakilama a baki take bashi abincin wani sashi na Zuciyarta ya zigata "Mezan gani haka? Yaya Jalal menayimaka haka, kake kokarin cin amanata wannan itace sakamakon soyayyar dana dau shekaru inamaka, lokaci daya kayimin haka dama abunda na Dade INA zargine yau Allah ya nunamin" Saroro Jalila tayi tana kallonta Ilham ta dawo da idonta kan Jalila "Munafuka kina cemin Yar wahala Ashe kece babbar Yar wahala, Ashe hasashena ya tabbata son Jalal kike, to wallahi baki isaba kinyi kadan kiyi takara dani akan abunda nakeso bans..... " enough malama karkiga nayi miki shiru kicigaba da zagina, mezanso anan" ta nuna Jalal "Ni abu na kawo nake masa magana akan abunda ya aikatawa kansa banda haka ni babu abinda ze hadani da shi" Shidai Jalal bece musu uffan ba sema mamakin hakikancewa da Ilham take, yakeyi "Karya kike wallahi ko duk jikina kunne ne bazan yaddaba kuma wallahi Jalila sekinyi danasanin abunda kikayimin, sena baki mamaki " ya isheki malama" Jalila ta karaso gaban Ilham "bude idonki da kyau, ki bude kwakwalwarki kiga da wacce kikeyi, inkin manta bari in tuna miki  Jalila ce dawo hayyacinki, Dan kinga ina lallabaki ba amin hauka wallahi yanzun nan zan saukemiki abunda yake damunki Me akai akayi Jalal meye abinso a tareda Jalal wannan makakken Mara tarbiyya, shi kike nufi  Jalila taso, ko ta nuna a matsayin uban yayanta, a tunaninki zan tsaya ina daga murya saboda shi Yadda yake a maken nan ai se makakkiya Yar uwarsa, badai Jalila ba ni mutumin arziki zan aura Dan babu uban me hankalin daze bawa wannan yarsa a haka Kema da kike sonnashi kinada manufar hakan badan hakaba yadda yake wulakantashi yaci ace kin hakura useless and hopeless creatures dagake harshi" Tirkashi Share please More comments more typing......................  Ina alfahari daku a kullum masoyana da masuyimin addu a Ina godiya me tarinyawa inajin daddin comments dinku❤❤❤ SANARWA!!! wasu suna tambayata ko nayi joining wata kungiyane na online writers Gaskiya ni banyi joining kowace kungiya ba, kamar yadda kuke gani wannan shine Novel dina na farko, kuma basirata ce nake amfani gurin nishadantar daku tareda aikawa da wasu sakonni, babu wata ko wani marubuci dayake bani gudunmuwa Dafatan masu tambaya kun gamsu Game gyara, comments, tambaya ko korafi, akwai lamabata danake sakawa a farkon kowane page a tuntubeni ta wannan lambar nagode Taku har kullum Yar babanta(daddy's girl) 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 34 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Ja da baya ta dingayi yana Binta, har seda ta kai karshen bango sannan ta tsaya tana zazzare ido "Kingama gudun?" Saboda karfin hali irin na Jalila ta dubeshi "Wallahi kasake ka karaso inda nake sena maka Illa, akan me baza a fadi gaskiya ba, ai duk abunda nake fada ba karya nayimaka ba haka kake" Daka mata tsawa yayi, Wanda yasa taji hanjin cikinta sun nannade guri daya "Shut up, akwai wata illa dazakiyimn Wanda yafi miyagun maganganun da kikeyimin, ke badan darajar Jawwad ba da tuni na dade da kakkaryaki na karya banza" Dagowa Jalila tayi da sauri ta kalleshi, "Eh in karya banza mana, in ban mantaba a wancan karon nagaya miki ba ruwanki dani kifita a sabgata kome nake aikatawa babu ruwanki, meyasa kike da taurin kai da shishshigi,? Dakamata tsawa ya kumayi ba tambayarki nakeba Banza tai masa ta dauke kanta " kaga ni ban guri in wuce" Ba musu yabata hanya, ta sa kai zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa yakamo hannunta guda daya, yai masa wata muguwar murdawa, Wanda in yakuma murdawa ze iya ballata Bata San lokacin datayi wani uban zilloba ta fasa kara Ya kalleta "da zafine?" Kasa magana tayi se wani uban fitsari dataji ya matsota, gashi ko kwakwakwaran motsi takasa balle ta kwace hannunta Be saketa ba, da daya hannun nasa yasaka yakamo kunnenta, cike da mugunta ya murda iya karfinsa, wannan karon batayi ihunba sedai taji kaman fitsarin yafara fitowa, Allah ya temaketa hawaye yafara zubowa daga idonta, yana daf da ita sosai Dan suna iya jin numfashin juna, ya Dan tsura mata ido sannan yace "Nikike cewa makakke ko? Kuma Useless and hopeless creature ko, ke gaki wadda ta haifowa duniya rashin kunya, daga yau in kinga Jalal, kikuma kallon ko inda nake sena yi maganinki Hada cewa kinfi karfin makakke irina, ke meye abunso a gurinki,, yana ina wata mummuna dake, banda rashin mutunci da rashin kunya  baki iya komaiba" Motsa baki take, tanaso tayi magana amma takasa Har yanzu be saketa ba, yadan kalleta "Ko kinada maganane"? Girgiza kai tayi, fuskarta tayi jajawur, se ruwan hawaye dayake zuba wani nabin wani," Da kyar ta tattaro kalaman dazata fada "N..Ni kasakeni, zan karye fa" Yadda tayi maganar cikin kuka da kuma shagwaba, seyaji jikinsa yayi wani iri "Au bakinki be mutu bako" yafara a hankali Yasa kafarsa ya take mata yatsun kafarta "Wayyo Allah Ummi, ze kasheni, Allah ka temakeni" Yadda taketa kuka gwanin ban tausayi, Dan zuwa yanzu ji take kamar hannunta ya karye, sannan ta saddakar ya cire mata kunne, ga yatsun kafafuwanta dake wani zugi, kunenta yafara saki sannan yacika mata hannunta Daya hannun tasaka ta rike hannun dayayiwa muguntar danji take kamar ya karye, Dan kallonta yayi kamar yayi dariya amma ya dake "Gobema kikuma sena tabbatar miki ni makakke ne, da giya naso nabaki kisha senaga bake yakamata in bawaba Jawwad zan bawa, in yasha kaman kinsha ne, stupid girl, tafi kibani guri" Dukda haka be ishi Jalal ba Dan Sam be huce ba akan abubuwan data keyi masa, seda yamata kyakyawan rankwashi a tsakiyar kanta, aikuwa nan take ta tsuguna kasa ta fashe da kuka, Shikuma yakoma kan kujerar da yataso yai zamansa yacigaba da abunda yake, Kuka take sosai saboda batason atabamata kai ko kitso bata sonyi setace zafi yake mata, balle wannan katon ya rankwasheta, kuka take sosai hada sheshsheka "Idan baki tashi kinbar dakin nan ba nazo gurin nan, sena danneki na baki giya, and I mean it" Bashiri ta mike ta nufi hanyar fita, tana Jan kafa seda ta bude kofar, ta waigo ta kalleshi, "Allah yasakamin wallahi, mugu kawai, kuma wallahi niba mummuna baceba," Shiru yayi mata, "bazata iya yin shiruba, bakinta baze mutu ba" Tsayawa tayi ta share hawayenta daga waje Dan gujewa tambayoyim Nana, tana daf da shiga cikin gida Jawwad suka karaso shida doctor salis "Munzo a dai² Jawwad waccan ba mutuniyar bace?" Doctor salis yai maganar yana nunawa Jawwad Jalila" Banza Jawwad yai masa yanemi guri yayi parking, Jalila tana kallonsu amma bata tsayaba tayi cikin gida, Allah ya temaketa bakowa a parlour tashiga dakinsu ta tarar halima tana ninkewa Nana kayan sawarta "Halima ina Nana"? " hajiyace ta kirata,afiya kuwa" "Lafiya kalau" Jalila ta shige toilet Dan kar halima ta dameta kunnenta yayi Ja ga hannunta da ya sage ji take kamar banata ba Gaskiya Jalal azzalumine, ya iya salon mugunta, babban abunda ya dameta wannan rankwashi da yayi mata Dan tunda yayi mata take jin Jiri har yanzu, kanta har yafara ciwo, lallabawa tayi ta watsa ruwa, ta wanke fuskarta tayi alwala Dan magariba ta gabato sannan ta fito ta canza kaya, bata iya amfani sosai da hannun da Jalal ya murda mata, guri daya takoma ta dunkule lokaci² tana share hawaye Nana tazo ta sameta a haka "Lafiya kuwa?, daga zuwa duba Yaya Jawwad kinzauna" "Naje baya nan yanzun nan ya dawo" Jalila tabata amsa a takaice "Wai meya sameki naga yanayinki ya canza?" "Kainane yake ciwo" "Eyyah sannu inada paracetamol inkinyi salla seki sha" Jalila ta gyada mata kai, Nana kuma tayi waje "Azzalumin banza wainice mummuna makaryaci kawai, wallahi ko makaho yasan niba mummuna bace" Jalila taita mita tana kunkuni, Doctor salis ya duba kafar Jalal yace masa babu sauran kwalba a ciki, Dan haka acigaba da gasa kafar da ruwan dumi yana shan magunguna zata warke gaba daya insha Allah "To mungode sosai salis" Jawwad yafada yana dafa salis, Dan ture hannunsa salis yayi, ya kalli Jalal "Jalal a gaskiya Jawwad bashi da kirki, har innemi alfarma a gurinsa yakasa yimin" Kallonsa Jalal yayi "Anya zan yadda Dan uwana bashi da kirki, amma me yayi maka?" "Wai ace inga kanwarsa ince inaso ya hademin rai, yace baze baniba" Dan murmushi Jalal yayi, yayinda Jawwad yakuma hade rai, Jalal yace wace yarinyarce "Wadda mukazo muka tarar da ita a gurinka ranar dabaka da lafiya, wata me iyayi, baby sunanta kome? Nidai kaman haka naji Jawwad yana cemata, ranar tana nan har karfe daya, seda kayi bacci Jawwad yatafi maidani sannan ta koma cikin Gida, yau muna shigowa na hangeta INA yiwa Jawwad maganarta amma ya shareni" Kallon Jawwad Jalal yayi, aransa yace wannan Mara kunyar, sannan a fili yace "Ba ruwana kaida shi, in yabaka shikenan, ina maka murna" Doctor salis yadan bude baki "Au hakaama zakace, bazaka tayani lallabashi ba" "Niba ruwana" Jawwad mikewa yayi "In kungama ni natafi masallaci" Akayi sallar magariba, da kyar Jalila ta mike tayi salla, tana idarwa ta zube a gurin saboda azababben ciwon dataji kanta yanayi, Nana takuma shigowa ta tarar Da Jalila ta dunkule akan dadduma, durkusawa Nana tayi ta dafata "Jalila har yanzu kanne yake miki ciwo" Jinjina kai kawai Jalila tayi, mikewa Nana tayi ta dakko mata magani ta kawo mata, Jalila ta kalli maganin "Nana ki bar maganin nan, ni banaso" "Saboda me haka zaki zauna da ciwo" "Kibari kawai ze dena, idan na sha maganin nan amai zanyi" "Ohh my God, sannu amma kina cuta bazaki sha magani ba"?     Har wajen isha doctor salis yana gidan suna hira jefi², ya zauna ne koda Allah zesa yaga Jalila amma shiru be ganta ba, Halima tayi sallama, ta kawo musu abinci, Jawwad ya kalli Halima yace " Halima ina Jalila ne?" "Bata jin dadine, ta kwanta nikadai nayi girki yau" "Subhanallahi me yasameta haka" Jawwad yafada a Dan tsorace Halima tace "Naji tacewa Nana kanta yana ciwo" "Ta sha magani ne"? "Wallahi ban saniba" "OK jeki, ki kirawomin ita, inzata iya zuwa, tunda salis be tafiba seya dubata" "To bari inje" Ta mike ta koma cikin gida, Jalal yana jinsu bece komaiba, Doctor salis ya kalli JALAL "Wace kuma JALILA, naga Dan uwanka ya damu, nidai nasan Nanace kawai kanwarsa" "Kabari ta zo sekaga wace" Jalal yabashi amsa Halima ta koma cikin Gida, ta tarar da Nana tana bawa Jalila tea, "Jalila yayanku yace kije likita yana nan ya dubaki" Nana ta kalli halima "Daga zuwa kai abinci Harkin gaya masa" "A a tambayata yayi" "To jeki angode" Seda Jalila tagama shan tea sannan ta kama hannun Jalila suka fito Suna daf da Barin palourn Maama ta hangosu "Me Nana INA zakuje haka" "Jalila CE bats da lafiya , shine Yaya JAWWAD ne yace taje doctor salis yazo se yadubata " Allah ya sawwake" Shine abunda Maama tace tashige kitchen, itakuma Nana suka fito Nana ce tayi sallama, suka amsa Jawwad ya mike da sauri, "Subhanallah baby, abin har ya kai haka, sannu" Jin ance baby yasa doctor salis saurin waigowa Jalilace fuskarta duk tayi ja hawayene kawai ke fita daga idonta "Subhanallah Ashe babynmuce ba lafiya" Doctor salis yafada yana mikewa tsaye Guri tasamu ta zauna,Nana ta zauna a kusa da ita Nana takalli Jalal "Yaya Jalal ina wuni" "Lafiya sannu" Hada ido sukayi da Jalila ta galla masa harara, kawai se yayi murmushi yacigaba da latsa wayarsa Jawwad se jera mata sannu yake Doctor salis ya kalleta "Sannu baby dama sunanki Jalila, a very sweet name" Shiru Jalila tayi masa ta kwantar da kanta akan cinyar Nana Jawwad ya hade rai "Kaga cewa nayi ka dubata ba ka dinga yimata shirme ba, in bazaka dubataba zan dauketa mutafi Asibiti" "To ai dubatan zanyi, kake min masifa" Doctor salis yakuma kallon Jalila "Baby kidena kukan mana, kinfiye shagwaba in mutum bashi da lafiya ba kuka akeba, Yaushe kan yafara miki ciwo?" "Dazune" tafada a kasan makoshinta Nana ce tayi yinkurin dagota tareda cewa "Jalila ki tashi kiyi masa bayani, bayajinki fa" Jalila ji tayi Nana ta fama mata hannunta da Jalal ya murda da sauri ta furta "Wayyo Allah Nana hannuna" Jawwad yakuma rudewa "Baby mekuma yasamu hannun naki" Jalal ta kalla, amma shi ya maida hankalinsa kan wayarsa, shi yadda Jawwad ya rudene yake bashi haushi Wani hawayen takaicine ya zubo mata "Bigewa nayi da kofan toilet" "Gaskiya zanyi fama, baby haka kike shagwababbiya komai kuka" Doctor salis yai maganar cikin zolaya Wani mugun kallo Jalila tayi masa cikin tsiwa tace "Sunana Jalila karka kuma cemin baby" "To yi hakuri na dena, yanzu inane yake miki ciwo"? Murmushi Jalal yai a ransa yace indai wannan yarinyar ce kacigaba dayimata shishshigi, ba karamin aikinta bane ta zageka Doctor salis yagama yimata tambayoyin daze mata yace a Alluran dayayiwa Jalal akwai guda daya da ze mata sekuma magani daze bata Zumbur ta mike zaune " Allura kuma, Yaya Jawwad ina tsoron Allura," "Yi hakuri a hankali zeyimiki" Shidai doctor salis wannan shagwabar ta Jalila birgeshi yake Nana tace "To ai maganinma ba sha kike ba gara ayi miki allurar" Aka zuko Allura, Jalila tace sedai ayi mata a hannu, salis yace ta miko hannun, ta mika masa sannan tace "A hankali Dan Allah" "To shikenan a hankali zanyi miki" Ta mika masa hannun, da kyar akayi allurar nan tana ta kuka, Shikam goga ko uffan bece musuba dayaga suna biye mata haushi ya isheshi ya tashi yabar musu dakin Salis yace allurar da yayiwa Jalila ta isa sedai in ciwon kan yaci gaba ai masa magana Nana takama hannun Jalila suka koma cikin Gida a zaune tayi sallar isha'i saboda ciwon da kan yake mata tana idarwa ko canza kaya batayiba ta haye gado takama baccin wahala, Dan ta manta da batun duba Jarrabawa (Gaskiya Jalal ya iya rankwashi,) Da safe bayan tayi sallar asuba takoma baccinta, ranar ko tsinke bata dauke a gidanba balle tayi musu girki Aikuwa dai Abincin yau da banbanci don Sam be kai dadin na Jalila ba Har LA asar Jalila bata fitoba, sedai Yaya Jawwad har daki yazo ya dubata ya tarar tana bacci Salis yakira Jawwad a waya ya tambayi ya jikin Jalila, Jawwad yace masa da sauki, "Jawwad Dan Allah ka hadani da baby mana in mata ya jiki," Jawwad kashe wayarsa yayi, yana mita Jalila tana daki da yamma, taji hayaniya a harabar gidan, Dan haka tafito dama wunin ranar bata fito ba, Abbane ya dawo daga lagos, ya canzawa Jawwad dankareriyar mota, duk anje an kewaye motar, yayinda Jalal ya kame a cikin motar sekace tasa Murmushi Jalila tayi Abba sannu da zuwa gaba daya suka waigo suka kalleta, ta Dan rame sosai, idonta yayi wani iri Abba ya kalleta "Baby meyafaru ko bakida lafiya ne?" "Lafiyata kalau bacci nayi" Nana tai saurin cewa "A a Abba batajin dadine" "Eyya Nagani fuskanta ya nuna" "Abba ciwon kaine fa kuma na warke" Takalli motar "Masha Allah, Abba mota tayi kyau Allah yasaka maka da mafificin alkhairi, Allah yakara arziki, amma wa aka saiwa motar naga me motar daban Wanda ya kame a cikin motar daban" "Lallai yarinyar nan har yanzu bakinta be mutuba ga muryarta har ta dashe saboda kuka" Jalal yai maganar a ransa Abba yayi murmushi "Jalila kayan Jalal aina Jawwad ne, Dan haka tasuce su biyun" Jalila ta kalli Jawwad "Yaya congratulations Allah yasa rai da lafiya akayiwa" "Ameen baby mungode" "Abba to mu se yaushe za a saimana?" Nana tai maganar a shagwabe "Ku tambayi yayanku, shize saimuku, gata mamanku can Ku dinga hawa ko Jawwad yabaku tsohuwar tasa, in kunshiga university seku dinga Ja" "Abba ta Yaya Jawwad dinfa duk ta tsufa wallahi," "Yana jinki dai, in kun gama Ku nabaku naku tsarabar a cikin Gida" Daga nan Abba yai cikingida yana dariya, Maama tabi bayansa Jalila ta kalli Jawwad "Yaya muje a danamu a motar, dama zamuje duba exams" "To ku taho muje daga nanma muje shan ice cream" "Amma Yaya yaushe zaka fara koyamana mota,?" Nana ta tambaya "Ku tambayi Jalal seya koyamuku rigimanmun Abba kawai" "Tabdijan, waye ze koyamana tukin, ba tukin jirgin sama mukeso akoyamana bafa tukin mota Yaya Jawwad, wannan ai tukin jirgin sama yakewa mota" Jalila tai maganar tana hararar Jalal, yana kallonta ta cikin mudubin motar "Ba ruwana ke dashi" Jawwad yafada yana dariya, cikin Gida suka nufa suka dakko hijjabai, da wayoyinsu suka fito Tunda Jalila taga, Jalal a mazaunin direba taga shi ze tuki jikinta yayi sanyi, Dan tana ganin yanda yake Jan nasa motar Share please More comments more typing........................... Love u all my fans comments dinku na kayatar dani dakuma Sani nishadi Love you all❤❤❤❤ SANARWA!!! wasu suna tambayata ko nayi joining wata kungiyane na online writers Gaskiya ni banyi joining kowace kungiya ba, kamar yadda kuke gani wannan shine Novel dina na farko, kuma basirata ce nake amfani gurin nishadantar daku tareda aikawa da wasu sakonni, babu wata ko wani marubuci dayake bani gudunmuwa Dafatan masu tambaya kun gamsu Game gyara, comments, tambaya ko korafi, akwai lamabata danake sakawa a farkon kowane page a tuntubeni ta wannan lambar nagode Taku har kullum Yar babanta(daddy's girl) 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 35 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Nana ta bude motar ta shiga, motar tayi kyau matuka, Jawwad ya kalli Jalila "baby shigo mana" Jikinta a sanyaye ta bude motar ta shiga, Jalal yai musu banza yacigaba da danna wayarsa Jawwad ya kalleshi "muje ko" "Ina zuwa" yacigaba da aikin wayarsa sun shafe kusan minti goma shabiyar a zaune sannan yayiwa motar key, aikuwa kamar yadda Jalila take fargaba a guje ya fafari motar nan kaman zasu tashi sama, Jalila se rarraba ido take tana karanta adduo'i daban² a zuciyarta, tabbas Jalila ta yadda sun hau motar Dan giya, yadda yake gudu dasu sekace a Action movies kaman ba mutane ya dakko ba haka yake ratsa manyan motoci yana overtaking "Wayyo Allah Nikam nashiga uku gaskiya a tsaya in sauka wallahi, na hakura da duba Jarrabawar, ni kadai Ummi ta Haifa baza a kasheni a wannan gangancin ba" Jalila tayi maganar da karfi "Yi hakuri baby, Jalal Dan Allah sassauta gudun nan Jalila a tsorace take, guri yasamu yaja wani arnen parking " ta sauka ta fita in bazata iya zama ba" "Wallahi bazan sauka ba sedai kai ka sauka ai ba......." Bata gama ba Jalal ya juyo yana kallonta tai saurin yin shiru Jawwad yace "Baby kiyi hakuri babu abinda ze faru lafiya zamuje insha Allah" "Ni gaskiya tsoro nakeji" Nana ta kalli Jalila tana dariya "Runtse idonki ki kwanta akan cinyata zaki denajin tsoron" Ba musu ta kwanta akan cinyar Nana ta runtse ido Jalal ya Dan kalleta, ya maida kai ya cigaba da bawa sabuwar motar Jawwad wuta Jalal Ya samu cafe a hanya yayi parking Suka fito daga motar gaban Jalila se faduwa yake tana fargabar me zata gani a result dinta, Jalal yana zaune a cikin mota be fito ba Jawwad yai musu Jagora suka nufi shiga cafe Jalila ta tsaya a kofar shiga "Ya dai muje mana" Nana tai maganar tana janyo hannun Jalila Jalila tayi ajiyar zuciya "Nana karbi exam card dina ni bazan shigaba abinda kuka duba seku gayamin" Ta karasa maganar kaman zatayi kuka "Haba Jalila in kika karaya nikuma ince me, karki damu taho mushiga" "Nana Allah bazan shigaba, ina nan sekun fito" Haka Nana ta hakura ta kyale Jalila, tabi bayan Jawwad yayinda Jalila ta tsaya a kofar gurin, kallon da mutane kewa Jalila ne yafara bata haushi Dan ita bata San kallo Jikin motarsu ta koma taje ta jingina ta tsaya, Jalal ya bude kofar motar ya kashingida a jikin kujerar mota Jalal ne yake waya tana iya jiyo abinda yake cewa dukda a hankali yake maganar "Hannah meyasa kike takuramin a rayuwata, kin uzzuramin wallahi, Ke ko zuciya baki da ita, haba Dan Allah nifa bazan iya wannan shirmen nakiba, kozanyi aure Hannah kinsan bazan iya auren mace kamarki ba" Jalila ta Dan waiga ta kalleshi, Taja tsaki "Mtseeew shirme, sekace wani mutumin kirki, suna zubarwa da Kansu mutunci a gurin wannan Dan giyar, wahalallu dagasu har shi, kowace wannan Hannah oho" ta cigaba da mita daga inda take Wayarsa yacigaba da yi Dan besan tanayi ba Jawwad ne da Nana suka fito daga cafen, fuskarsu babu annuri suka nufo inda Jalila take Hankalinta ne yai mummunar tashi ganin yanayin fuskarsu, suka karaso bakin motar "Na fadi ko yaya, banciba, na fadi Jarrabawar ko?" Mikomata paper yayi sannan yace "Congratulations my dear u got it, am proud of you" Yai maganar yana murmushi tareda Jan hancin Jalila, bude result din tayi A¹ bakwai tasamu B guda biyu Rungumeta Nana tayi "Ina tayaki murna Babyn Abba" Jalila ta kalleta "Nana me kika samu" "Nine credits ne" Murna suka cigaba dayi "Is  OK murnar ta isa haka, kushiga muje, aje shan ice cream, proud of you all, Allah yayiwa karatunku albarka" "Ameen suka fada a tare" Suka bude motar suka shiga, Jawwad ya dubi Jalal yace "Jalal kaga results din su Nana, Alhamdilillah, result yayi kyau, mussaman na Jalila" Dan kallon papers din hannun Jawwad yayi yana kokarin kunna motar "Mmm yayi kyau Allah yasa ba satar amsa tayiba" Kutmelesi Jalila taso gayamasa bakar magana Dan dai Jawwad yana gurinne, Jawwad ya kalleshi "Wuce nan bros, duk cikinsu ba wadda take satar amsa" "How sure are you?" Jalal ya tambayeshi "Obviously na yadda da kannena, ranar graduation dinsu Jalila awards din da aka bata sun isa su tabbatar daba ta satar amsa" "Hmmmm" shine abinda Jalal yace ya fizgi motar a guje yabar gurin Jalila kuwa se kunkuni take tana magana a ranta, ita kuwa Nana se hira take mata, tana kuma jinjinawa Jalila dangane da result dinta, itakuwa Jalila Kalmar satar amsa ta bakanta mata rai sosai "Ashe dai ba iya Neman maganar aka iyaba kan yana kawo wuta, shiyasa kike burgeni mutuniyata, baki da wasa" Nana ta fada tana Jan hancin Jalila Jalila ta rirrike Nana, saboda gani take a kowane lokaci motar nan zata kife saboda tukin da Jalal yake A wani joint sukayi parking Jawwad yayi musu rakiya sukaje suka sai abinda sukeso, sannan suka fito suka nufo hanyar gida Suna cikin tafiya Jawwad yace "Baby, Nana dai mass com takeso, kekuma fa?" "Yaya ni nursing nakeso," "Wow, u can do it, Allah ya temaka" Wayar Jalila tafara ringing bakuwar lamaba ce, kamar karta daga, sekuma ta daga tare da yin sallama "Wa alaikum salam, Jalila Ashe kinkoma kano babu labari?" Jalila ba ta dau muryava Dan haka tace "wake magana" "Kai Yar baba, kardai kice baki ganeniba" "Subhanallah, Yaya Abdallah yi hakuri kasan banida lambarka se yanzu nagane, barka da yamma" "Yawwa Jalila, yakike?" "Lafiya kalau ya daddy" "Yana lafiya, Ashe kinkoma kano, nazo Gida attending birthday Hanan, take gayamin" "Aikam dai Yaya Abdallah ina kano," "Kice zamu dinga haduwa kinsan a bayero nake karatu, na dinga kawomiki ziyara" "To shikenan Yaya nagode sosai" "Insha Allah weekends din nan zamuzo, da daddy da Hanan" "Dagaske Yaya" "Dagaske nake" Zuwa yanzu Kishine yake cin Jawwad jin yadda Jalila ta saki jiki tana waya, da wani namiji, Jalal ya Dan kalleshi yaga yadda ya wani hade rai, Dan murmushin gefen baki Jalal yayi yacigaba da tukinsa Jalila suka gama waya da Abdallah ta kalli Nana "Nana da weekends insha Allah usainata zasuzo, zasu kawomin ziyara" "Wa kenan?" "Hanan mana" "Dan Allah dagaske" "Wallahi Nana" Jawwad ya Dan gyara zama "Baby da wa kike waya?" "Yaya Abdallah ne" "A ina yake?" "Abokin nan nakafa, Dan gidan captain Rasheed" "Hmm nagane" Daga nan be kuma cewa komai ba harsukaje gida, lokacin ana kiran sallar magariba, Suna zuwa gida suka tarar Maama tana salla Abba kuma ya tafi masallaci, Dan haka suka tafi dakinsu, halimace ta biyosu a baya, tana fadin "Jalila ya akayi,? Ya jarrabawar kuwa?" Jalila ta tsaya tana murmushi, Nana kam bata tsayaba ta wuce dakinsu "Leemart jarrabawa Alhamdilillah, kinga results dinmu" Jalila ta mikamata result din Karba halima tayi ta duba "Masha Allah, Jarrabawa tayi kyau kam, Allah ya sanya alkhairi, Yasa a ci gajiyar karatu" "Ameen my leemart, bari inje zanyi salla" "To shikenan" Bayan sunyi sallar magariba suka tarar da Abba a part dinsa Maama ma tana part din, suka bashi result din yayi murna sosai yai musu addu a, da fatan alkhairi Sannan ya dauki kayan da yakawo musu tsaraba yabasu, na Jalila harda brown din Teddy da kayan sawa na alfarma, sukayi masa godiya Nana se tsokanar Jalila take wai ta ci sunanta baby ta girma amma tana wasan teddy Maama ta tabe baki "Nima haka Nagani, yarinya da girmanta amma kana sai mata teddy, wannan ai sangarta ce" Murmushi Abba yayi "A ganinkine sangarta, ni a gurin kyautatawane" Da Jalila taji haka ta mike ta bar part din gaba daya ta koma dakinsu Suturar da Abba yabasu manyan suturune masu tsada matuka Bude trolley dinta tayi ta debo wasu kaya masu kyau kala hudu, ta Dora turare body spray da roll on, ta bude kayan dasuka siyo, dazu dasuka fita ta dakko ice cream roba daya ta hada ta fito, sukayi clashing da Nana ta kalli kayan hannunta "Wannan kuma fa? Me zakiyi dashi" " Halima zan bawa" "Saboda me"? "Nima Allah yabani wasu, ba tare da yayi shawara daniba" "Kudi fa ake biyanta meyasa zaki dauki kayanki masu kyau kibata" "To meye a ciki Nana, naci jarrabawa Alhamdilillah Abba yamin kyautuka, yakamata mu farantawa wasu muma" Dan tabe baki Nana tayi ta wuce daki yayinda Jalila ta nufi dakin halima    Ilham tarasa abinda yake mata dadi yan kwanakin nan takasa gane inda Jalila tasa gaba shin da gaske Jalila tana son Jalal, kokuwa, amma in tana sonshi ya za ayi tagaya masa wannaan miyagun maganganun, Amma kuma ya akayi Jalila take gaya masa maganganu son ranta amma be dau wani mataki akanta ba, Wanda ta tabbatar ita  bata  Isa tayi masa haka ba, Kenan shima yana son Jalila, tunda take gaya masa maganar data ga dama amma ya kyaleta "Kan uba karyane wallahi ina wani shirmen hakan ze faru" Tai maganar a fili "Ko mami zan kira in gaya mata abinda yake faruwa, yanzu ina gaya mata ni zatayiwa fada tace laifinane, kuma baze yiwu in gayawa Nana ba tunda Yar uwattace za a iya hada kai da ita a cuceni, yanzuma watakila bakinsu daya" Tayi nannauyar ajiyar zuciya to ni yazanyine? Ko gidan malamin nan zanje da kaina innemi yaseera ta rakani(kawar Ilham ce) hakama za ayi inje inji ya za ayi aimin maganin wannan tantiriyar Da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta samu nutsuwa Halima ta kalli Jalila "Jalila inani inasaka wannan kayan masu tsada" "Leemart to meye a ciki, ba wani kaya masu tsada, sedai in abun hannuna ne bazaki karba ba" "A a Jalila ba haka bane," "To in ba hakabane kawai ki karba" "Nagode Jalila, Allah ya faranta miki kaman yadda kikayimin" "Ameen leemart" Jalila ta koma daki ta kira Ummi a waya tagaya mata abinda tasamu a result dinta Ummi tayi murna sosai, sannan tace "Jalila ya yanayin zamanki a kano? Naji muryarki cikin farin ciki ina fatan komai lafiya?" "Komaiafiya Ummi, bakiga Mayan da Abba ya siyo mana ba," "Masha Allah, haka nakeson ji, yacigaba da hakuri da rayuwa Jalila," "To Ummi insha Allah, Ummi da weekends insha Allah Hanan zasu kawomin ziyara" "Dagaske baby" "Dagaske Ummi, dazu Yaya Abdallah ya gayamin" "Allah sarki gaskiya suna kaunarki Jalila, Nima next week insha Allah zanzo, daga nan zan wuce garinmu" Haka nan se Jalila tayi jikinta yaysanyi "Ummi tafiyar tana nan Ashe zakiyi,? "eh tana nan zanyi insha Allah" "To Allah ya kaimu, next week din" "Ameen ki gaida mutan gidan" "Zasuji insha Allah" Nana ta Dan kalli Jalila "Yanaga jikinki yayi sanyi" "Nana banason tafiyar nan da Ummi zatayi" "Haba Jalila, Ummi yakamata tayi tafiyar nan yana da kyau taje taga danginta" "Hakane Nana" "Yawwa to kidena tayarda hankalinki, kiyimata addu a kawai" "To Nana" "Yawwa babyn Ummi"   Daren ranar Ilham batayi baccin kirkiba se tufka da warwara kawai tekeyi, kamar ta janyo safiya tayi domin taje gurin malamin nan Washe gari da safe wajen karfe goma Ilham ta shirya tacewa mummy zataje gidansu Ummi tace seta dawo, tana fita ta tafi gidan su yaseera, suka gaisa da Maman yaseera sannan ta wuce dakin yaseera, ta tarar yaseera ta shirya ita take jira ko zama Ilham batayiba suka fita ita da yaseera sukayi gidan malamin nan Share please More comments more typing................................ 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 36 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Ilham ce da yaseera gurfane a gaban malamin nan, malamin ya kalli ilham sannan yace "Ya kikazo keka dai yau ina babartaki?" Ilham ta Dan gyara zama "Malam akwai matsalane fa" "Matsalar me?" "Malam, nifa na fara gajiya da wannan wahalar danakeyi akan Jalal, ina ta nawa kokari amma, wata Matsala na kokarin kunno kai, duk wannan wahalar danake yana kokarin fara soyayya da wata yarinya daban, hankalina duk a tashe yake" Malamin ya numfasa ya kalli Ilham sannan yace "Anya kuwa dagaske kike yafara soyayya, a aikin damukayi akansa bana tunanin ze iya fara soyayya cikin sauki, har se burinku yacika," "Malam nifa tsoro nake, kar inje shirin ya rushe gaba daya" "Hakane in dai ba wancan sharadin ne ya afkuba, to aikin damukayi masa yana tareda shi har yanzu, koda kuwa yayi soyayya da wata, sedai in wancan sharadi ya karya" "Wallahi ji nake kamar kawai in aiwatar da me gaba dayan tunda har yanzu yaki yadda ya soni, balle ya aureni" "Wannan kuma ya rage naki sekije kicigaba da kokari, ko be sokiba daya aureki shikenan aiki ze kammala" Yaseera ta kalli malamin "To yanzu malam babu yadda za ayi da wannan shedaniyar yarinyar, tunda akwai yiwuwar ya iya fara soyayya" "Wannan kuma Ku zakuyi wannan aikin ni nayi muku kokarin da yakamata sekije ki bada himma, zanyi bincike akanta, muga abinda za ayi akanta" "To shikenan malam zanje in cigaba da kokarin" "Yayi kyau, abinda ake ciki zan sanarda ke" Suka mike suka fito yaseera ta kalli Ilham "Wai Ni kuwa Ilham wace wannan yarinyar" "Hmm wallahi kanwar abokinsa ce wata Mara mutunci da ita, yaseera yarinyar nan bata da mutunci Sam, idan banyi wasa ba fa zata bata min aiki, kinga rashin mutuncin da take masa amma ko kallonta ba yayi balle ya dau mataki, kuma da nice na gayamasa abinda take masa da tuni ya hukuntani" "Kince sonshi take, kuma kince tana masa rashin mutunci, anya kuwa son nashi takeyi" "Nima abinda nake ta tantama kenan, amma nafi tunanin borin kunya suke a gabana amma sonshi take, kinga a yadda nagansu kuwa ranar a gidansu, wallahi bantaba tunanin haka kishi yake ba se ranar" "Wai ma inane gidansu"? "A gidansu Nana take fa cousin dinsu ce" "Muje gidan inga wace ce, inga iya rashin mutuncin nata se mu San ta inda zamu bullo mata" "To shikenan mu karasa, ki ganta,"     Hannah ce kwance akan gadonta tana zancen zuci, "mace kamarni ace Jalal yake wulakantawa, ga yadda maza kemin layi amma akan wannan Dan tahalikin, nake wahala har wani cewa yake ko ze aure baze aureniba, na tabbatar ranar Dana kirashi wannan kanwar tasa ce ta daga har take zagina, zanyiwa Jeje aikinsa sannan itama kanwartasa senayi maganinta, nita zaga saboda tana son Jalal, zata ga tsiya, indai Hannah ce ta taro daidanta"      Nana ta fito ta tarar da Jalila a kwance akan kujera tana danna waya "Jalila zan Dan fita, zanje bayan layi ne Maama ta aikeni" "To sekin dawo" Fitar Nana ba dadewa aka turo kofar palourn ba ko sallama, mutane taji tsaye akanta "Dan Allah ina Nana"? Shiru tayi ba tako daga kai ba, balle ta ga suwaye " magana fa nake miki" Ba ta dago kanta ba tabada amsa "Taje akoya mata sallama, inzaka shiga guri" Yaseera ta kalli Ilham, sannan tace "Yi hakuri Dan Allah, salam alaikum" "Wa alaikum salam warahmatullah" Jalila ta amsa sannan ta tashi zaune Ta dubesu ta danyi murmushi "Sannunku da zuwa bismillah ga guri Ku zauna" Ilham se wanj hura hanci take Jalila ta Dan kalli Ilham sannan ta maida idonta kan yaseera "Nana ta Dan fitane ba nisa tayiba yanzu zata dawo insha Allah" Yaseera ta danyi murmushi, "To mungode" Suka samu guri suka zauna Jalila tace "Ilham ya kike,? Ya Gida" Ilham tai mata wani irin kallon up and down "Da nazo nayi miki maganane? Kokuma ke a dole sekinshiga harkata" "Ko in shiga harkarki ko kar inshiga harkarki babu abinda zaki kareni dashi ko ki rageni dashi, tunda ba abunda nake nema a gurinki nayi hakanne kawai Dan sauke hakkin addinina, ke Yar uwatace musulma, kuma makociya, muna da hakki akan juna shinake kokarin saukewa kawai, bawai wani abuba" Tabdijan yaseera a zuciyata tace "lallai wannan yarinyar yar duniya ce tana da baki, gashi komai nata abin birgewa yanayin yadda take magana kawai ya isa ya dau hankalin mutum, ga iyayi kuma dajin maganarta kaga shgwababbiya gashi ta iya juya ido in tana magana" yaseera kallon Jalila kawai take "Bakuwa bari in kawo miki abin tabawa kafin Nanan ta dawo, naga Ilham se wani cika take tana batsewa bansan menayi mataba" Jalila ta mike tana tafiya a gayance ta nufi fridge Lallai dole Jalila ta tafi da imanin duk Wanda yai tarayya da ita dukda Ilham tace mata bata da mutunci amma tana ganin hakan duk cikin iya takunta ne Lemo Jalila ta kawo musu da ruwa sannan ta kira Nana a waya, ta gayamata tayi baki, Nana tace mata takusa karasowa tana daf da Gida Yaseera ta kalli Jalila "Nagode Yar uwa" "Bakomai yiwa Kaine bakin Nana ai baki nane" Ilham bata kuma cewa komaiba, tunda Jalila takuma gaya mata magana, sema haushin yaseera daya kamata ganin yadda ta zage suna hira da Jalila kamar sun saba Ana haka Nana ta dawo, "Yawwa ga Nana nan ta dawo" Nana ta kalli inda su Ilham ke zaune "Yaseera dama talaka na ganinki gaskiya akwaiki da zumunci" "Yanzunma unguwa mukaje nacewa Ilham mu biyo mu gaisa kwana biyu bamu haduba" Nana tace "hmm kin kyauta ya Gida ya kwana biyu?" "Lafiya kalau" Jawwad ne yayi sallama a palourn suka gaisa dasu Ilham Sannan ya kalli Jalila "Baby yunwa fa mukeji kuma munji ki shiru, Jalal ze sha magani beci abinci ba" Kallon Jawwad tayi ta danyi murmushi "Aini yau banyi girkiba, in kuma kunajin yunwa to kuzo kuyimin wanke² wani yayi gyaran kayan miya" murmushi Jawwad yayi  ya nufi hanyar kitchen Jalila ta mike tabi bayansa, Ilhaam kam Dan bude baki tayi "Hmm Yaya Jawwad manyan" Nana ta fada tana Dan murmushi Ita dai yaseera ta jinjina yadda Jalila take gudanar da al amuranta cikin nutsuwa, lallai indai da Jalila, Jalal yake Shirin fara soyayya to se Ilham tayi dagaske, don Jalila bazata sha wahala gurin sace zuciyar duk Wanda taso ba Jawwad ne yake bubbude kwanuka a kitchen "What are you looking for?" Yaji muryar Jalila a bayansa, juyowa yayi ya kalleta "yunwa fa  mukeji baby" yai maganar yana kwaikwayon JALILA "Yi shiru karkayi kuka jeka zan kawo" "Inyi kuka sekace wani baby, Babyce me kukan allura, kuma nasan in tanajin yunwa ma setayi kuka" Dariya sukayi gaba daya Wanda hakan yayi dai² da fitowar Maama tana kallonsu ta window kitchen, kwafa maama tayi ta nufi parlour Su yaseerana suka gaida maama ta amsa musu sannan tace ma Nana taje tacewa Halima tana kiranta, tajuta ta koma dakinta Su yaseera suka mike sukace zasu tafi, dama ba ziyarar Allah da annabine ya kawosu ba Dan ILHAM ta nunawa yaseera Jalilane, suna shirin tafiya Jalila suka fito ita da Jawwad, suna dariya, Ilham ta kallesu taja uban tsaki Jalila ta kallesu "har zaki tafi, yaseera, mungode ki gaida Gida, Ilham ki gaida mummy" Ilham bata kula Jalila ba itama Jalila bata damuba Dan tasan ILHAM ba amsawa zatayiba, tai waje da kayan abincinsu Jawwad Nana ta kalli Ilham "Haba Ilham, Jalila tana miki magana amma kin wani shareta" "Kinsan bana son rainin hankali, kuma kinsan halintane dan haka ni bana shiga sabgar mutum inaga hankali be isheshiba" "Kut lallai Ilham amma kinsan da a gabantane dase ta gaya miki wadda tafi takin zafi" "To yanzu tunda bata nan seki rama mata" Ilham ta fada tana Harar Nana "Rufamin asiri, ina ni ina iya shigarwa Jalila fada ai sedai inyi kallo" "Ya fiye miki" Haka Nana tarakasu ILHAM had bakin gate suna tafe suna fada,    Jalila tabi bayan JAWWAD da kwanukan abinci zuwa part dinsa, oga Jalal yana zaune yana kallo sekace dakinsa, Jalila ta ajiye kayan abincin tareda fadin "wash" JAWWAD ya Dan kalleta "kai baby har kin gaji" "Niba gajiya nayiba" "Hmm dagaske?" "Eh mana" "OK tunda bakgajiba serve us" Seda ta kalli Jallal ta Dan hade rai Ta dau plate tayi serving Jawwad, ta kalli JAWWAD "sekuma me? "Baby Jalal fa, serve him too" Yamutsa fuska tayi "Ni na gaji" "No Jalila, kefa kikace Baki gaji ba, hakan ba halinki bane" Kafin tayi magana Jalal ya taso daga inda yake cike da gadara, yasa hannu ya dauke plate din gaban Jawwad da Jalila tayi serving din Jawwad, ya dau spoon ya samu guri ya zauna, ya fara cin Abincinsa Bayan sun fitane yaseera ta kalli Ilham "Tab wai yanzu kina nufin wannan itace budurwar JALAL din" "Hmm gata nan kin dai ganta ko? " ai ko ta hadu" "Kamarya ta hadu, kinsan dai na fita kyau ko?" "Ke dalla wayake ta wani kyau Ilham, duk kyanki akwai qualities din da in kika rasa, to kyan yazama shirme, banda abinki ma dame kika fita, hasken fatarne kawai amma wallahi kyakykyawa CE" "Au yaseera hakama zakice dame ta fini?" "Kallifa mu matama kalli da yadda take mana magana INA ga in agaban namijine, gashi ta iya iyayi da siyasa, kincemin fada kuke, amma dukda munzo tare kalli yadda ta mutuntani, gata Yar gayu" Ilham ta hade rai sosai sannan tace "Ni duk ban iya wannan abubuwan ba kenan?" "Bahaka bane ba, amma kin San meyake cutarki" Ilham ta girgiza kai "Rashin hakuri, saurin fushi, ga garaje, gaki da sakaci, kinga in bakiyi dagaskeba akwai matsala kina ganin yanda take wani juya ido in tana magana" "To yazanyi yaseera,?" "Waima tukuna naji yayan Nana yana batun akai musu abinci shida Jalal, Abincin ma ita take kai musu" "To inaga ita take kaimusun mana" Ilham tai maganar cike da damuwa "Cab wato ita take kaimusu abinci, lallai ILHAM da sauranki, gaskiya akwai tendency na JALAL yafara soyayya, kuma abinda kike gudun yafaru" Ilham ji tayi kaman ta Dora hannu a ka ta fashe da kuka "Yaseera ya zanyi, nikam indai nabari shirin mami ya rushe batareda ta dau fansar nan ba nayi asara Wallahi yaseera se yanzu nagane son gaske nakewa Jalal, wallahi zan iya komai akansa" "Kina wannan sakalancin zaki iya komai akansa? Malama ki dage Dan wallahi wannan yarinyar da bariki zatayi zata Tara abun duniya, Yanzu ki saurareni, batun kice kin gaji be taso ba, duk masifar daze miki kidena zuciya da shi, sannan kidena jin tsoransa, sannan kidinga kokari kema kina dafa abinci ki bashi, in wataran beci ba wataran zeci" Ilham ta Dan girgiza kai "Yaseera gani kike shawo kan Jalal abune me sauki ko? Mugun Dan taurin Kaine, ga shi jarababbe, yaseera tsawon shekarun nan danayi a gidansu ko inda yake bayaso inje, am about to give up" "Ita Jalilan dayake daga mata kafa ba mace bace kamarki, iya bariki kawai tafiki, ki bar wani batun seya soki malama kawai ya aureki a wuce gurin" "To yaseera insha Allah zan kuma jajircewa, Wallahi nida zuciyata tafara bani kawai inyi duk me yiwuwa kawai inyi me gaba daya" Da sauri yaseera ta kalleta "Baki da hankaline? Inkuma aka samu akasi fa" "Nima abunda yasa nafasa kenan" "Karki kuskura ki fara, kibi komai a hankali" "To shikenan yaseera, zan cigaba da kokari" Haka yaseera taita zigata sannan sukayi sallama, Ilham ta shiga Gida yaseera kuma ta tafi   Hannah ta kira wayar Jalal harta gaji dama seyaga dama yake amsa wayarta, yau ta kudurce wa ranta kome ze faru sedai yafaru Dan Gida zata bishi, lokaci yayi da yakamata tafara wasan kwallo dashi daga shi har kanwar tasa dole sugane wace Hannah, Jalila bin Jalal tayi da kallo, wannan akwai Dan rainin hankali, shima Yaya Jawwad sekace Jaraba kowa da gidan ubansa ya zauna a can amma shi inbe bishiba shi ze biyo shi, a ranta tace kacigaba zan rama ne wannan wulakancin da kakemin bakaci bulus ba A zahiri kuma ta ba sar ta kuma serving din Jawwad "Yawwa Yar Baby, mungode sosai" "To yayan Baby, permit me to leave" "U can leave dear" Tana komawa cikin Gida Maama ta kuma aikenta gidansu Jalal, waita karbo kaya anjima wasu customers zasuzo tun safe Jalila take aiki bata huta ba gashi bata son abunda ze hadata da Ilham, ba tayi musu ba ta juya ta kuma tafiya aiken da akayimata, Tana fitowa taga wata mota a tsaye a kofar gidansu Jalal, harta gifta mortar, aka danyi reverse da motar saitin inda Jalila take, sauke glass din motar akayi wata matashiyar budurwa ce a cikin motar "Sannu dai" tacewa Jalila "Yawwa sannu" "Dan Allah tambaya nake"? " Allah yasa nasani" "Naga kamar  cikin gidan nan zaki shiga" "Au kamace baki tabbatarba" "Ohh sorry Dan Allah Jalal nake nema" Kallonta Jalila tayi, tayi nazarinta na wasu yan mintuna sannan tace "Me Jalal ze miki"? " inason ganinsane" "Baki da lambarsane?" "Nakira bata shiga" "Injiwa zance masa"? "Kawai kice masa yayi bakuwa" "Bahaka nakeba, inkina son ganinsa kifadi sunanki" "Hannah ce, koke ce Ilham din da Jawwad yake gayamin kanwarsa da kike sonshi" Da sauri Jalila ta kalleta, ta Dan kuramata ido wasu yan mintuna sannan tai murmushi "Hannah" Jalila ta maimaita "Yeah I am Hannah" Jalila ta kuma murmushi "Zata iya yuwuwa nice Ilham kuma zata iya yuwuwa bani baceba, for now bazaki ga Jalal ba ki tafi kawai inma kin tsaya bazan bari ya fitoba, kune masu kara ingiza lalacewarsa, kalleki, kalli shigar jikinki a matsayinki na ya mace kina yawo half nicked, kinzo gurin namiji saboda abun kunya, me kike tsammani in mutane suka ganshi da ke, kibari in yaje inda kuke haduwa kya Ganshi amma ba anan ba, juya kikoma inda kika fito" Jalila ta hade rai tareda nuna mata hanya Share please More comments more typing......................... Masoyana abun alfaharina comments dinku yana kayatar dani Allah yabar kauna 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 37 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Karewa Jalila kallo tsaf Hannah tayi, ta tabbatar Jalila Sa ar kanwarta ce, badan kartayi karyaba setace kanwa ta biyu ma, bude motar tayi sannan ta fito ta kalli Jalila sama da kasa, ta danyi murmushi sannan tace "Ni kike kora kike cewa in tafi in bar nan gurin" "Au tambayata ma kike, lallai na fuskanci saboda irinku ake double period a class, saboda ba kwa dauka a daya" Mamakine yacika Hannah, tace "Bari in gaya miki wani abu dabaki saniba ni..... Jalila ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tareda fadin " NO need saboda babu wani abu me amfani ko me mahimmanci Wanda ze amfaneni dazaki fada, as I said it before, kibar nan gurin in ba hakaba zan baki mamaki" "Ni Hannah zaki bawa mamaki" "Kwaraikuwa kedin" Nuna Jalila tayi da Dan yatsa zatayi magana, batayi maganarba Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Hannah "Duk wata magana muyita amma ba a nunani da Dan yatsa, daga haka nagama magana dake, nabarki lafiya, inkin gadama kicigaba da tsayuwa" Jalila na zuwa nan a zancenta ta shige gidansu Jalal tabar Hannah tsaye sororo tana mamaki Jalila ta shiga cikin gidan da sallama, Ilham tana palourn tana danna waya tayi mata banza, Jalila ta kuma nanata sallama amma Ilham mirsisi taki amsa sallamar Jalila Karasawa Jalila tayi tasa hannu ta fizge wayar hannun Nana "Haba kekuwa, kome nayi miki a rayuwa be kyautu inyi sallama kimin banza ba" A fusace Ilham ta kalleta "Bani wayata malama" "Kiramin mummy, seki karbi wayarki" "Ke kin isa kisani aiki," "Ban isaba alfarma na nema" Sannan ta bawa Ilham wayarta, Ana haka mummy tafito da alama unguwa zata fita Suka gaisa da Jalila, Jalila ta gayamata Aiken da akayi mata, mummy tace taje yanzu fita zatayi in ta dawo zata aiko, Da haka Jalila ta fito ta tafi gida,.data fito ta tarar Hannah ta tafi, Jalila a ranta tace kin kyautawa kanki dakika tafi ai     Hannah tana barin gurin takira wayar Jeje ta tambayeshi ina zasu hadu yagaya mata, ta nufi gurin kai tsaye, tana zuwa ko tasameshi a can, yanayin fuskarta kawai ya nuna masa akwai matsala, saboda yadda take huci "Me idon zinare, lafiya kuwa"? " ina fa lafiya, gidansu Jalal naje, saboda yan kwanakin nan baya daga wayata, naje nasamu wata a kofar gidansu, wata yarinya taci min mutunci" "Kamarya taci miki mutunci, miye hadinki da ita?" "Ina kyautata zaton itace budurwar tasa, da Jawwad yake fada Ilham take kowa, hada cewa bazata bari ya fito ba, sedai injira muhadu inda mukasaba" "Jalal din, to karya takeyi barazana ce kawai, uwar da ta haifeshi ma bata isa ta hanashi abinda yyi niyya ba, balle wata Ilham, gayen da soyayya bata gabansa, kema kinciri tuta ne da yake sauraronki, amma ya akayi kika San Ilham dince"? "Na tambayeta amma ta rainamin hankal, Amma nayi mamaki, yanda nake zaton Ilham din na dauka wadda zanyi maganice a take amma naga itama a tsaye take Dan bata da kunya" Dan shiru Jeje yayi sannan yace "Tabbas Ilham ma masifaffiya ce amma bana tunanin ta kai yadda kike fada haka" "Hmm, bakaga wulakancin datayi minba kuma na girmeta, sena raina rashin kunyata Dan fafur hanani magana tayi, mamaki da takaici suka cikani" "Gaskiya Hannah kin bani kunya duk bakin naki, kinsan a duniya Jalal ya tsani mace ta dinga juyashi" "Ba a nan takeba Jeje hausawa kance yaki Dan zamba ne Dan haka, zan nuna mata duk Wanda yarigaka kwana ze rigaka tashi, idan takamarta rashin kunya, nikuma takamata bariki, zan daga shi har ita zan basu mamaki"    Jalila ta sanar da Abba zuwan captain Rasheed da yayansa domin kawo musu ziyara, Yaya farinciki sosai da jin haka, Jalila ji take kamar ta janyo ranar Saturday su Hanan suzo, se murna takeyi Daren yau dai Jalal yasaci jiki ya tafi gurin shan giyarsa, yaje babu dadewa be fara shaba, mayyar tasa tazo wato Hannah, tazo ta nemi guri ta zauna tai shiru batace komaiba Ya Dan kalleta, yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa, "Ya akayine sarkin matsala, mekuma ya faru?" Ta dago ta kalleshi, tayi kalar tausayi sannan tace "Jalal kwana nawa ina kiranka kaki ka daga wayata, naturomaka messages kaki reply haba Jalal, gashi aka cimin mutunci saboda kai, yakamata ka tausayamin" "Ya akayi aka cimiki mutunci sabodani?" "Kanwarka mana" "Wake nan?" "Wace kanwar kake da ita, banda wadda Jawwad yacemin tana Sonka?" Shiru ya danyi yana kallon Hannah, tacigaba da magana "Ranar nakiraka baka dagaba, ita ta daga ta min rashin mutunci ni kana cemin Mara kamun kai amma me kanwarka take a gurinka shabiyun dare, har tana gayamin bacci kake ta zageni hadda cemin mayya" Shikam Jalal kasa cewa komai yayi se ido da ya zuba mata, "Har yanzu ni banga cin mutuncin dakike fada tayi miki ba" Kallonshi tayi "Au hakama zakace? Metakeyi a gurinka shabiyun dare harta daga wayarka?" "Meye kuma na bin diddgi ina ruwanki dame take a gurina shabiyun dare?" " haba Jalal,Yauma nakasa jurewa da rashin ganinka Dan haka naje gidanku, na hadu da ita a kofar Gida daga tambayar kana ina ta dinga zagina Harda cewa baka isa tahanaka abu kayi ba Dan haka bazata bari ka fitoba, saboda baka tsallake maganarta, tana juyaka yadda taga dama, haka ta dinga fadar maganganu, abun ya dauremin kai" Dan dagowa yayi da sauri "Inji Ilham din?" "Eh mana, ni babban bakin cikina yadda ta dinga gayamin miyagun maganganu saboda kai, wallahi Jalal ba Dan kanwarka bace senasa ankoyamata iya magana, harni zata cewa mutuniyar banza? Ita ma ai ta banzarce tunda zata iya zuwa dakinka shabiyun....... " Enough malama, karki kuskura ki zagi kanwata, kuma wallahi duk abunda yasameta a kwanan nan kikuka da kanki, Ilham ba mutuniyar banza bace, ni shedane, ki kiyaye baki isa ki zageta a gabana ba, and then zanje gidan in sameta, zatayi bayani" Yana zuwa nan ya tashi ya tafi yabar Hannah baki a bude, saboda mamaki se yanzu takuma tabbatarwa kanta tsawon wannan lokacin, har yanzu Jalal be fada tarkon sonta ba kenan tunda har ya fifita Yar uwarsa akanta kenan ya fara son Ilham, amma ko ba komai tasan abunda ta fada din nan ze tunzirashi, gaba dayanku, sena nuna muku ni gogaggiyace a bariki Jalila hartayi shirin kwanciya Abdallah ya kirata suketa hira dashi da ita da hanan, a wannan lokacin kiran JAWWAD yaita shigowa amma line busy, Jawwad ransa babu dadi ya kwanta, yana tunanin dawa Jalila take waya tsawon wannan lokacin           Tunda Jalal ya tafi yake tunanin ya akayi Ilham ta daga masa waya, meya kaita part dinsa shabiyun dare ( besan Jalilace ta amsa wayarba, lokacin da bashi da lafiya") Shi babban takaicinsa ma cewar da tayi inta hanashi abu be isa yayiba, yaushe yake shiga harkarta dazatayi masa karya, ta zubar masa da kima a gurin wata mace daban aikuwa se ya hukunta Ilham Dan baya son karya (Ilham zata amsa query maimakon JALILA 😂😂) Ya koma Gida yana zuwa ya tafi part dinsa don kuwa by now yasan mutan gidan sunyi bacci, yanazuwa yai wanka ya canza kaya sannan yasha giyarsa iya son ransa sannan ya kwanta bacci Daren ranar Ilham tayita sake² yadda zata canza takunta na zama a gidan, domin Janyo hankalin Jalal kanta Dan wannan karon ta sawa zuciyarta lallai seta cika burinta. Da safe Jalila kaman yadda ta saba tayiwa halima Karin karatun Qur'ani sannan suka  tashi sukayi aikace² daya kamata suka hada breakfast Kamar kullum Da sassafe Jalal yake zuwa saboda suna motsa jiki, in sukayi suka gamane we yayi wanka ya canza kaya, a gidan, Ya lura da rashin walwala na Jawwad amma bayaso yafiye takura masa, bayan sungama exercise ne Jawwad yai wanka yaketa shirin tafiya makaranta, saboda ze shiga lectures karfe tara JALAL ya kalleshi " wai yanaga Janata shirin tafiya makaranta breakfast dinfa"? "Nakoshi" Dan zare ido Jalal yayi "ka koshi kuma, me akayi maka ne? Naga se fushi kake, meyasa kake so ka tafi makaranta bakayi break fast ba" "Haka nan, yau bana son cin abincine" "Ban yadda da abunda kafada ba, baka fiye yin fushiba, kana iya boye damuwarka, amma tunda nagane kana cikin damuwa nasan matsalar babbace," Dan murmushi kawak Jawwad yayi "meyasa bazaka yadda ba ne?" "Shikenan naji amma ban yadda ba" Jawwad ya cigaba da shirinsa, Jalila ce tai sallama Jawwad ya amsa tareda basar da ita yacigaba da shirinsa, dama JALAL ba amsawa zeyiba "Barka da safiya Yaya Jawwad" "Yawwa barka" "Naga kana shirin fita abincinfa?" "Nakoshi" "Meyasa?" Shiru yayi mata yasamu guri ya zauna yana kokarin daura agogonsa, JALAL yana kallonsu bece musu uffan ba kan hannun kujerar da Jawwad yake JALILA ta je zauna, tasaka hannu ta karbe agogon hannunsa Dagowa yai yana kallonta, ba tareda ta kalleshi ba tace "Gayamin meyasa yau bazakaci abincina ba? Laifin menayi maka?" Y miko mata hannunsa tareda fadin "Babu abinda kikayimin, ban agogona kar in makara" janye hannunta tayi "Ko shine yayi maka wani ABU?" "Shiwa" "Wancan" tafada tana nuna JALAL, gaskiya JALILA Yar rinin hankali ce Jawwad yace "ba sunansa wancanba," "Yaya Jawwad na fuskanci ninayi maka laifi, Dan Allah kayi hakuri" Dan kuramata ido Jawwad yayi, ta damu sosai "Jalila me kikeso ayi yanzu?" "Kaci abincin, sannan ka dinga kulani" Murmushi Jawwad yayi Wanda seda hakoransa suka fito yanayin yadda tayi maganar ya birgeshi matuka "Baby meyasa baki daga wayata ba jiya da daddare for more than 30 minutes wayarki busy" "Yasalam Yaya Jawwad Hanan ce fa kasan gobe in Allah ya kaimu zasuzo, ita ta kirani taketa min surutu labarin makaranta, Gida, da sauransu, muna gamawa siyama ma takirani, naso in kuma kiranka, se nayi tunanin kayi bacci ne, Amma tuba nake yayana bazan kumaba insha Allah" "Baby bazan iya fushi dakeba Sam, kawo abincin" Jalal ji yayi kaman yasamu bulala ya zanewa Jawwad jikinsa, saboda bacin rai dama akan wannan, shugabar marasa mutuncin yake ta wannan fushin gaskiya Jawwad Dan wahala ne Tea Jalila ta hada masa ta zuba doya da miyan sos ta bawa Jawwad "Nagode sisyna, amma kinsan mu biyune yaya Jalal fa, shima a bashi" "Ya jira Ilham in tazo ta hada ta bashi," "Kai Baby, meyasa hakane nida Jalal dayane, indai zakiyiwa Jalal haka nima zaki iya yimin" "A gurinka ne daya ni..... Bata gama maganar ba Kamar yadda yai mata jiya yanzunma Jalal zuwa yayi ya kwace na hannun Jawwad yai tafiyarsa kan kujerar da ya taso "Yaya kana kallonsa ko?" "To Baby ya zanyi indai bazaki bashi Abinci ba abun akaina ze kare, nawa ze karba ya cinye" Zuciya Jalila tayi ta mike tareda fadin "Ai sekuyi tayi," Murmushi Jawwad yayi sannan ya kalli Jalal "Bros meyasa ba kwa jituwa da baby ne, why"? " saboda bazan iya wannan shirmen da rashin aikin yinba, kalli saboda abunda be taka kara ya karyaba kake ta fushi, na dauka wani abun akayi maka, Ashe saboda wannan uwar rashin kunyan ne, shirme kawai" "Allah yabaka hakuri, amma bazaka ganeba Jalal" "Ameen naji bazan ganeba din" Jawwad yagama breakfast dinshi ya tashi ya shiga cikin Gida suka gaisa dasu Abba, sannan yacewa Halima Dan Allah in Jalila tagama abunda take ga dakinsa nan a temaka a gyara masa daga nan yai waje domin tafiya makaranta    Ilham da kanta ranar tayi breakfast, bata bari masu aiki sunyiba, dukda ba wata kwararriya bace a fannin girki, tagama tayi kwalliya  ta kai part din Jalal amma baya nan ta ajiye masa takoma dakinta, har gurin karfe Tara ba Jalal babu alamarsa, se zarya take koya dawo amma bata ganshiba    Halima taje daki ta sanarwa da Jalila sakon Jawwad Nana ta kalleta "Aifa ke yanzu kin kade haka zasu maida ke kamar baiwarsu" "Nana kenan meye abun bauta a ciki,?" "Tab lallai aikuwa zasu rainaki, tun yanzuma gashi, ke zakiyi musu girki, ki gyara musu daki, agaisheki nikam bazan iya wannan wahalar ba" Jalila tayi murmushi "Nana kenan, meye a ciki, duk abunda nayiwa Yaya Jawwad ko wani Wanda ya rabeshi ban fadiba, kaina nayiwa" "Hmm Allah ya temaka, kema wataran zaki gaji Dan matsalarsu bata karewa" "Ai bazan gajiba Hajiya Nana, kema gara kisaba gaba akeji" Jalila ta mike ta tafi gyarawa Jawwad daki, ta tarar Jalal yagama karyawa ya bar kwanukan a gurin, ko tartare kwanukan guri daya beyiba Jalila ta kalleshi ta kalli gurin da Jalal ya bata "Mtsewww Dan Allah malam in an gama cin abinci hade kwanukan akeyi ba a cinye abincin ciki a bajesuba," Jalila tafada a fili tareda kwashe kwanukan tai cikin gida, kodaga kai beba Balle ya kalleta   Ilham tagaji da jiran da Jalal, tasan dai baze wuce gidansu Jalal ba Dan haka ta dau mayafi ta nufi gidansu Nana, tana zuwa part din Jawwad ta nufa, kaitsaye Dan tasan baze wuce nan ba tunda motarsa tana Gida, taje ta tura kofar palourn Jalal ta hanga a zaune a kan carpet din palourn  Jawwad, da remote a hannunsa, shiga tayi cikin palourn da sallama ya Dan dago ya kalleta, ta karasa shigowa cikin dakin "Ina kwana Yaya Jalal" "Lafiya kalau" Ta Dan gyara zama, "Yaya na hada maka breakfast ne shine..... " da can ke kike hadamin?" "A a Yaya amma.... " tsaya dama ina son magana dake, me kika cewa yarinyar da tazo nemana jiya"? "Ni kuma?" "Akwai wata a gurin nan bayan ke?" "To aini jiya ban hadu da kowa ba" "Nima rainamin hankalin zakiyi"? "A a Yaya Jalal ni ba wata wadda tazo nemanka damuka hadu" "Ilham wallahi zan tattakaki, Sa anki ne ni? Nace me kika cewa Hannah jiya, nizakiyiwa karya!!!" Hade rai tayi itama dan bata gane inda rainin hankalin Jalal na yau ya dosa ba, ta mike tsaye ta kalleshi "Ni ban San mezance maka ba kuma, nagayamaka abunda nasani ni ba wata wadda muka hadu jiya, kasake dai tambayarta" "Ni kike gayawa haka?" "To me kakeso ince?" Share please More comments more typing........................... Comments dinku nabani nishadi am proud of you masoyana masoya wannan littfi 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️      [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 38 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Ransa ne ya kara baci ya kalli Ilham "Ni kike kallo kike gayawa wannan maganar? Ke kinyimn laifi kuma ki tsaya kina gayamin magana, kuma uban wayasaki kika dagamin waya har kike zagin Wanda ya kirani? Kwana biyu kinga nayi sanyi shine kikemin rashin kunya ko?" Mamakine yacika Ilham wannan wace kasurgumar makaryaciyar ce take mata sharri haka, to mema zatace masa ne Maganar yaseera ce ta fado mata "kidena jin tsoransa" "Au to kar in kare kaina, kana gayamin magana akan abunda bansan nayiba, sekuma inyi shiru wannan lokacin ya wuce Yaya Jalal nima nadena daga maka kafa ina kallonka kana min wulakanci, se wasu maganganu kake Wanda bangane inda suka dosaba, duk saboda kawai ina sonka, so fa ba karya bane ba, kuma ina nan akan bakana, duk macen datayi gangancin shigowa rayuwarmu senayi maganinta, ka dawo hayyacinka Dan ni...... Tas ya dauketa da mari, dafe inda ya mareta tayi, tana kallonsa " ke kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama, kinje kinyimn karya, kina cewa wai ban isa inyi abunda ba kyaso ba ke a wa? Wani matsayi kika taka a gurina da kike da wannan ikon,"? Sauke hannunta tayi daga kuncinta, ta kalli cikin kwayar idonsa "Matsayin kanwarka kuma masoyiyarka na taka, ka gayawa ita wadda ta gaya maka hakan, ta tinkareni ni da ita tayimin, ba wai ta koma bayan fage ba, kuma wallahi daga yanzu kadena jibgata a banza kasawa zuciyarka bashi kakeci seka biya wannan abun da kakemin, kuma wallahi indai ina raye baka da wata mata in baniba seka aureni, baka da imani Jalal ko sau daya yakamata ka dubeni da idon rahama, kodayake kai babu tausayi a zuciyarka" Kuma harzuka yayi, "Ni kike gayawa haka, ke wace irin Jaka ce da ba kya ganewa ana so dolene, bana sonki kuma bazan taba sonki ba, Jahila kawai fita kibani guri kafin in sauya miki, kamanni, kinsanni sarai bana son hauka amma kullum ke haukanki kara yawa yake shiyasa ko shirginki bana shiga fita dallah" Tundaga waje Jalila take jiyo hayaniyarsu Dan haka da sauri takarasa, ILHAM ta kalleshi sannan tace "Jalal duk haukan da yake kaina be kai Wanda yake kanka ba amma na dage nakesonka a haka wani irin mutum ne kai" Wani Marin yakuma bata,.yana shirin karamata ne Jalila ta shigo da air freshener a hannunta, zata gyara dakin Jawwad ganin abunda yake faruwa yasata rugawa da sauri ta shiga tsakanin Jalal da Ilham, ta janye Ilham baya, sannan ta kalli Jalal "Wannan abun kunya kake aikatawa karasa inda zaka zage kwanjinka se akan mace, macen ma kanwarka, me yake damunka haka" Daka mata tsawa yayi "Matsa ki bani guri ko in hada dake, in tattakaki" Itakam Ilham gefe tayi tana maida numfashi saboda taji zafin marukan da yayi mata, JALILA ta kalleshi up and down "To ka tattakanin mana ragon maza, karasa inda zaka nuna karfinka sekan mace, in karfi kakeson nunawa seka tafi gaidan dambe, jarumin namiji bada zuciyarsa yake yanke hukunciba da kwakwalwarsa dakuma hikima yakeyi, ba wai jibgar mace ba" Kallon  JALILA yayi idonsa cikin nata yana nazarin meze mata Ilham daga inda take tsaye sukaji  tace "Wallahi Yaya kowace tayimin wannan sharrin idona idonta kagaya mata senaga bayanta, kuma Marin dakayimin bashi ka dauka, don ka dauki alhakina, niba wadda muka hadu jiya amma ka hukuntani akan abunda bani nayiba, duk laifukan nan ba Wanda nasan nayi maka kowace karya tayimin, Tayi nasara wannan karon nima ta saurari abunda zan mata koma wace munafukarce dani take zancen wallahi" ta karasa maganar tana hawaye, se yanzu JALILA tagane inda fadan nasu ya dosa, amma ta juyo ta kalli Ilham "Kekam Iska na wahalar dame kayan kara, kalli tun ba yauba kike shan wahala a hannunsa ya dakeki, ya zageki, sekace ubanki kekuma dayake zuciyarki kin Yar kare ya cinye se manne masa kike kumayi, ni banga abun mannewa a gurin wannan abunba" Tafada tana kallon Jalal, wani irin huci Jalal yakeyi, yama rasa me yakamata yayi, "Ke saurara, ba ruwanki a cikin rayuwarmu, uwar shishshigi, kuma ma inda Sa hannunki acikin abunda yake yimin zan baki mamaki wallahi," Ta daga jajayen idanuwanta ta kalli Jalal "Wallahi Jalal wahalar dani din nan dakake shekara da shekaru, wallahi se ka biya duk randa kazo hannuna seka zubar da hawaye fiye da Wanda na zubar, zan fito maka a ainihin Ilham dina babu daga kafa ko ragawa tsakanina da kai, koni ko kai kokuma duk wani munafiki dake shiga tsakaninmu" Yinkurowa yayi zeyi kan Ilham, JALILA takuma shan gabansa "Dan girman Allah ka kyaleta" Hannu daya yasa, yai wurgi da Jalila daga gabansa tayi gefe Ilham kuma ta tsaya kyam taki tafiya Tas! Tas! Guda biyu a jere "Dan kaunar da kakewa manzon Allah karka kuma dukanta, jininka cefa, kanwarka ce, indai so yana zama laifi, Ashe wataran zaka iya rabuwa da Jawwad" Cak ya tsaya be juyoba amma Jalila tacigaba da fadin "Kome tayi maka kishinka ne  yasa tayi, baka tunanin alhakinta yakamaka ne, at least kaima ka sota mana koda irin na yan uwantaka ne kalli yadda ta................. (Zancigaba da hakuri, har lokacin da burinmu ze cika akan JALAL da mahaifiyarsa) Wannan kalaman da Jalila ta haba ji Ilham ta tabayi a wayane suka dawowa Jalila Wanda hakan yasa takasa karasa abunda tayi niyyar fada Juyowa yayi ya nufo inda Jalila take, Ilham na ganin haka ta sulale ta gudu, yazo gaban Jalila ya tsaya " meyasa ba kyajin maganane? Ke dole sekin gayamin me zanyi? Rayuwarki daban tawa daban, meyasa kike hakane, ke in dai baki shiga harkata ba ba kyajin dadi, meyasa ba kya ganewa ne, kinsan metayimin ne? Ya karasa maganar cikin shouting, Dan ja da baya Jalila tayi kadan "Eh nasani, nasan me tayi maka, kuma ba ita tayiba nice nan nayi" Kallon Jalila yayi "Kana mamakine? Ni ce nan matar tagani tace in kirawoka nace bazakazoba, ban damu da koma me tagaya makaba, saboda zatayi hakane dan tasa kamin wulakanci, Dan mace irin wannan dayawa maganganunsu karyane dakuma makirci, a zatonta nice Ilham shiyasa tagaya maka karya da gaskiya, abun kunyane a ganka da mace irin wannan, Haba Dan Allah koba ka dena abunda kake Dan komaiba kabari Dan Allah, dakuma kare mutuncinka, abokananka dayawa, wasu suna karatu, wasu suna sana a, kowa na kokarin Gina rayuwarsa amma kai kullum kokarin wargaza taka kakeyi, kaji tsoron Allah kuma ka kiyayi matan bariki, wannan data zo gurinka kowa ya ganta yasan mutuniyar banzace, amma kalli abunda kayiwa kanwarka saboda ita, kukwana Gida daya Ku tashi amma baka da abokin gaba se ita dakuma mahaifiyarka Wanda hakan shine babban abun kunya, kayi tunani maana, kayi wani abu akan rayuwarka," Idanuwansa ne suka kuma yin ja, jijiyoyin kansa suka daddga, ya rintse ido kalaman Jalila na cigaba da dukan zuciyarsa, wani irin huci yake kaman kumurci, wani abu yake kokarin tunawa amma yakasa, sema jiyayi kansa yana jujjuyawa, bude idonsa yayi akan Jalila Gabanta ne ya fadi! Ganin idon Jalal yana caccanza kala, daga Ja zuwa baki, gashi kuma ta kasa matsawa daga inda take, "Fita ki bani guri, bana son irin wannan maganar, kifita nace!!!" Ya dinga maganar cikin karaji daga baya kuma ya sulale, ya yanke jiki ya fadi Tsorata Jalila tayi ta Dan ja da baya amma taga ko motsawa beyiba daga inda yake, a hankali ta tako tazo inda yake kwance, ta leka fuskarsa, taga idonsa a rufe amma fuskarsa tayi Ja sosai ga jijiyoyin kansa duk sun daga sun kumbura, sekuma hawaye da yake fita ta gefen idonsa, se sauke numfashi yaketayi  hankali, a hankali ya Dan motsa yasa hannunsa biyu, ya danne kansa yana girgiza kan nasa "Wai meyasameka?" Ta tambayeshi Bece mata komaiba, sema numfashinsa da yake fita da sauri yanzu "Yasalam na shigesu toni ya zanyi, kar ace wani abun nayi masa" Ta kuma kallonsa "kanka ne yake maka ciwo?" Shiru bece komaiba Tarasa ma mezatayi, ko Yaya Jawwad zan kira a waya wata zuciyar tace A a karki daga masa hankali yanzu yana makaranta Ruwa ta debo a kofi, ta karanta wasu ayoyi saga cikin al Qur'ani Ta daga kofin ta Dan dinga zuba masa a kansa A hankali numfashinsa yafara komawa normal, a hankali ya sauke hannunsa daga kansa, sekuma yafara bacci "To ko aljanune da shi in ba hakaba ya za ayi idon mutum ya dinga canzawa" Tashi tayi ta fara gyra inda yakamata a dakin tanata tunani kala² yana nan yanata bacci a gurin ta wuceshi ta fita ta Koma cikin Gida Tana zuwa dakinsu Nana ta dubeta "Kekam INA kika zauna haka tun dazu nake nemanki fa" "Yaya Jawwad na gyarawa daki daga nan, na zauna a gurin flowers nayi tilawa" "Hmm yayi kyau" Daga nan JALILA ta bar dakin in bahakaba Nana zata cigaba da yimata tambayoyin Daba tasan dame zata bata amsa ba Tunani ne yacika zuciyar JALILA to dama maza ma suna da Aljanu, Dan tafi kyautata zaton JALAL aljanu ne dashi, Jalal kam bayan wani lokaci ya tashi daga baccin da yayi, ya mike yaje yayi wanka, ya koma kan gadon Jawwad ya kwanta abunda yafaru dazu yake tunawa, ji yayi zuciyarsa na kokarin fara bugawa da karfi Dan haka da sauri ya kauda tunanin daga zuciyarsa Koda Jawwad ya dawo daga makaranta, ras ya Tarar da JALAL kaman ba abunda ya faru Jalila kokari take ta kauda tunanin Jalal tayi harkokinta, takoma shirin karbar bakinta dazatayi, amma abu ya gagara abunda tagani yau tareda Jalal yau yabata mamaki, a hankali mafarkan da ta dingayi akansa a baya suke dawo mata kaman lokacin takeyi, yau Sam bata da nutsuwa kaman wata Mara lafiya haka take gudanar da al amuranta na yau. Hankalinta ya karkata akan son sanin waye Jalal dakuma son gano ainihin abunda ke ran Ilham game da son Jalal da ta keyi Tayi nisa sosai a tunaninta Halima ta dafata "Sayyada Jalila meyake damunki yau naga ba kya walwala, ko akwai matsala ne?" Jalila ta danyi firgigit "Leemart ba wani matsala," "Gaskiya ban yaddaba akwai abunda yake damunki" "Kawai tunanin ummina nake" "Allah sarki, ai kince tana zuwa sati me zuwa ki kwantar da hankalinki" Murmushi Kawai Jalila tayi, suka cigaba da aikinsu Da daddare Jalila ce ta kaimusu abinci amma taga Jalal normal kaman ba shiba, ko kallon inda take beba, balle ya kulata itama batasa akanta ze kulatanba amma se kallon mamaki take masa mussaman in ta tuna yadda idonsa ya dinga canza kala, ga kumburowa da jijiyoyin kansa suka dingayi Jawwad ne ya dinga tsokanar Jalila wai duk murnar zatayi bakine yasa jikinta yayi sanyi haka ita dai sedai tayi murmushi kawai tai musu seda safe Bayan sun gama cin Abinci ne Jalal ya tafi Gida Dan soyake ya kwanta da wuri bacci yakeji, yana kwanciya maganganun Jalila suka dinga dawo masa Tashi yayi ya zauna, yai shiru ya Sa hannunsa a sumarsa ya rike yana Dan juya kansa a hankali "Why meyasa nake aikata wannan abubuwan, meyasa bazan dena ba, nima banaso," Bugun zuciyarsa ne yafara karuwa yaji kansa yana kokarin fara juyawa Da hanzari ya mike ya nufi fridge dinsa ya cika cikinsa da giya ya baje a gurin Jalila tayi shirin kwanciya Hanan takirata ta dinga yimata surutu amma Sam Jalila sama² take amsamata Dan ba komai take ganewa ba, haka sukayi sallama da Hanan, Jalila wadda a wannan lokacin dazaka tambayeta me sukace a wayar bata saniba Dan hankalinta ba akan wayar yake ba Haka Nana ma ta isheta da tambayoyin meyake damunta, tarasa amsar dazata bata Daga karshe tace mata bacci takeji Sukuku haka Ilham ta wuni tareda tambayoyi fal zuciyarta na son gano, abunda yafaru makircin Jalila ne kokuma wani abu daban, gaba daya tarasa meyake mata dadi Ta kira yaseera ta gayamata komai ita kanta yaseera kanta ya kulle amma tace ta bari da safe zatazo su hadu    Koda Jalila ta kwanta bacci gagararta yayi, se tunani, da tambayoyi fal zuciyarta, a haka bacci barawo ya saceta Jalal ta gani a daddaure da sarka a cikin wani daki a galabaice, se a man gudan jini yake, wasu mutane masu bakaken kaya a zagaye dashi se kara matseshi suke da sarkar, JALILA tanata magiya su sakeshi kar ya mutu, daka mata tsawa wani yayi a cikin su "Ke uwar shishsigi!!!! Kinfara mana katsalandan a cikin aikinmu damukayi shekaru munayi, kishiga hankalinki, inba hakaba kema zaki shiga cikin aikin Dan bazamu bari ki rusamana aiki ba" Daga can taga Ilham ta shigo dakin ta zare wata wuka ta nufi Jalal "Ilham me zakiyi haka, Dan uwankine fa in kika kasheshi fa" Share please More comments more typing.......................... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [8/31, 8:30 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 38 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Jalila na zuwa daidai nan a mafarkinta tai firgigit ta tashi zaune tana gumi, Ta juya ta kalli Nana tana ta baccinta, ita kuwa se maida numfashi take kamar wadda tayi dambe, tanata jujjuya mafarkin nan datayi "Tabbas akwai wani abu a boye amma ta Yaya zan Sani, taya zan gane," gani tayi zaman tunani baze mata magani ba Mikewa tayi ta dauro Alwala ta koma kan gadon ta zauna tafara karanta Qur'ani a hankali, a haka har bacci yakuma dauketa wayewar garin yau da Nana da Jalila tareda Ilham sunata hada² shirya abinci domin bakin dazasuzo wato su hanan, suna cikin aikinne, Naja'atu tazo Naja kanwar Sa'ada ce wato "ya'yan Yaya mairo, yayar Maama, daka ganta kasan kanwar Sa'ada ce saboda kamar dasukeyi, Da Halima ta fara clashing a parlour, " ke ina Maama take da sauran mutanen gidan naga bakowa?" "Sunana Halima" "Bazance Haliman ba, ke zance, kina Yar karere Yar aiki, zan tambayeki, kicemin wani sunanki Halima, koma wace, matsiyaciya kawai mara galihu" Halima tayi saroro tana kallonta, daga baya kuma tace "Allah yabki hakuri, hajiya tana bangaren Alhaji, sauran mutan gidan kuma suna dakin girki" Jalila ce tafito daga kitchen da roba a hannunta "Ya dai nakejin hayaniya, leemart meya faru" "Bakomai bakuwa akayi" Jalila tana kallon Naja, taga kamanin Sa'ada, tasan Yar uwarsu ce seda gaban Jalila ya fadi "Sannu da zuwa, bari akira maaman" "Kekuma daga ina, tambayarki nayi ko gurinki nazo"?, Jalila ta dan murmusa "ai banyi kalarkiba dama balle kice zakizo gurina" Halima a ranta tace yawwa uwar dakina shiyasa kike burgeni, Jalila ta kalli Halima "Leemart ga robar ki debo sugar a cikin" Daga nan suka watse sukabar Naja a parlour, Naja tai kwafa lallai "Yan aiki har sun fara samun wannan damar haka a gidan nan" Dakin Maama Naja taje amma bata ciki, Dan haka tanemi guri ta zauna, bata dadeba Sega Maama tazo "Naja saukar yaushe,?" "Tun dazu nazo" "Amma ban saniba, meyasa Nana bata kirawoniba"? " oho ni ina na ganta, masu aiki nagani, sukamin rashin kunya a parlour, Maama yaushe yan aikinki suka samu wannan damar," " yan aiki kuma? Ai Halima ce kawai Yar aiki " "A a hadda wata, tanemi tazageni danni bansanta ba, wata Mara mutunci" " Ke ba Yar aiki bace ba, Yar kanin megidan nan ce Jalila ce fa" "Wai itace ta girma tazama haka,? Har tanemi ta zageni" "Ai indai wannan yarinyar ce zatayi fiye da haka" "To me ta keyi a gidan nan"? " hmm ta dawo nan da zama" "Aikuwa zan saita miki ita kafina in tafi, bari inje kitchen din in karemata kallo" Duk sun maida hankalinsu akan aikin dasukeyi sunayi suna tana hira, Naja ta shigo kitchen din ba ko sallama "Nana aiki kuke haka" Waigowa Nana tayi "Naja yaushe kikazo," "Tun dazu nazo, masu aikinku sukayimin rashin mutunci" "Suwa kenan?" Nana ta tambayeta, saboda wulakanci seta nuna  Jalila, Jalila a ranta tace "wato hali zanen dutse, yadda mahaifiyarsu Sa'ada ta tsenata har y'ayanta haka suke mata wannan tsanar Nana ta kalli Naja, lallai ma Naja, Jalila tayi miki kalar masu aiki? To Yar masu gidace me cikakken iko" "Yar masu Gida kuma?, to ai ya'yan masu Gida mutum biyu nasani, yaushe kuma wannan tazama Yar masu Gida" Jalila kam tayi kaman bata San da mutum a gurin ba, Nana a hasale tace "Kai Naja Wai baki gane JALILA bane"? Saboda iya gulma secewatayi " ke haba itace tazama haka, tai wannan kilewar, Yar gidan kiristan nan ko?" "Kekam Naja wallahi keda Yaya Sa'ada ban San wadda tafi wata rashin hankali ba" Duk yadda Naja taso  Jalila ta tankamata taki, dan ita yanzu bata ita take ba abubuwan dasuka dameta ma sun isheta, sema karatun Qur'ani data fara a fili, cikin kira arta me dadin sauraro (😂😂 Jalila Yar duniyace wato ta maida Naja shaidan, gara tanemi tsari da ita) Karfe sha biyu da rabi suka kammala, shirya abincikan dasuka yi, Sukaje sukayi wanka suka canza kaya   Yaseera da Ilham sun kule a daki suna tattaunawa, Ilham fuskarta cike da damuwa take magana "Wallahi yaseera kaina ya kulle nakasa gane ma meyake faruwa, kullum abu kara hargitsewa yakeyi, babu cigaba, kinga rashin mutuncin da yayimin, wai yayi bakuwa namata rashin mutunci namasa krya, waikuma ranan ankkirashi a waya na daga na zagi wadda takirashi, ni abun tambayar wacece, haka hardayake kumfar baki akanta, iya sanina baya shiga sabgar mata, nakasa gane wace ce, da nayi tunanin ko Jalila ce amma kuma naga itama yana kokarin yimata rashin mutunci da kyar nasamu na gudu, Dan rashin mutuncin da nayi masa jiya daya kamani seya kusa kasheni" Yaseera ta nisa sannan tace "Abun da daure kai Ilham, amma fa seta yiwu wani makircin Jalila ta hada" "Anya kuwa Jalila ce tunanina yafara bani ko wata ce daban" "Ke bar mutum kawai Ilham yanzu abunda ze faru, kama ta yayi mu bigi cikin Jalila maybe mugane wani abu" "Ta Yaya? Wannan me mugun wayon" "Da hikima zamuyi ai bada fadaba, amma sekin boye wannan fushin naki, sannan abu na karshe da zamuyi shine, duk yadda za ayi kawai, ayi Auren nan a wuce gurin"    Kiran Hanan Jalila tayi, Dan yaci ace sunzo "Wai yanaji shirune, har yanzu"? " hh sarkin mita, semu koma, " "Ke kin isa kukoma, na kagu in gankune," "Yi hakuri munkusa, kara turomin address din namanta, na farkon" Jawwad ya dawo daga masallaci ze shiga Gida shida Jalal, wata arniyar Mota tayi parking a kofar gidan, Dan tsayawa su Jawwad sukayi, Abdallah ne yafara fitowa ya tunkaro su Jawwad da fara'arsa, yana zuwa Jawwad ya ganeshi rungume juna sukayi, Abdallah ya kalli Jawwad "Aliyu mazan fama dama ana ganinka, tunda muka rabu a school bamu kuma haduwa ba" Jawwad yai murmushi "Aikam dai kazama wani babban mutum" "Kaima haka ai" Abdallah ya maida kallonsa kan Jalal, sannan ya mika masa hannu sukayi musabaha "Aliyu wannan brother dinka ne?" "Eh kanina ne" Jalal ya kalli Jawwad, ya Dan harareshi "Ko kuma dankaba sukayi dariya gaba daya" Yarinyar data fito daga cikin motarce tasaka Jalal, da Jawwad sukayi saroro, suna kokarin gane wacece Jalilace ko wata daban, takaraso inda suke, "Abdallah ka barmu a mota daga ganin abokanka, kamanta damu, nima yakamata inga Yar uwata, daddy ma ya matsu yaga 'Yar baba" Takalli su Jawwad "Sannunku, ina wuninku" Jawwad ne ya amsa mata, A yanayin maganar hanan da Jalila akwai Dan banbanci ita Jalila maganarta dauke take da tsiwa, ita kuma hanan da Izza take magana Ta kalli Jawwad "If I guess Kaine Yaya Jawwad din namu ko"? Abdallah yace " kin canka dai² shine" Captain Rasheed ne shima ya fito ya karaso inda suke, Gaisawa sukayi cikin fara a, sannan JAWWAD yayi musu jagora zuwa cikin gidan, JAWWAD yaje yagayawa Abba ga baki nan sun karaso Hanan se rarraba ido take taga Jalila Abba yayi farincikin ganin captain Rasheed suka gaisa cike da girmama juna Jalila jikinta yabata, kamar sun karaso Dan haka tafito palourn da gudu hanan ta tashi ta rungume Jalila "Ke in kika karyani fa, matsa inje in gaida Baba"? Hanan ta harareta " ni ba kya murnanr ganin se Baba ko"? Babansu hanan yayi dariya "Karaso mu gaisa Yar baba" Jawwad binsu yake da kallo yana kuma jinjina wannan kama ta Jalila da hanan suke kaman yan biyu Nana ma fitowa tayi domin ganin Hanan, ita kanta Nana abun yabata mamaki, Abba yacewa Jalila taje ta kira Maama su gaisa, Jalila ta tafi kiran Maama yayinda Nana taja Hanan dakinsu Jalal ma Jan Abdallah yayi zuwa part dinsa Nana na shiga daki da hanan Naja ta kallesu, "Wai hayaniyar me nakeji a gidan nan?" "Jalila ce tayi baki"Nana tabawa Naja amsa tareda cewa hanan " bismillah Hanan" Hanan ta shiga dakin tareda fadin "Thank you dear" Kallo daya Hanan tayiwa Naja tafara kokarin tuna inda tasan fuskarta Mamakine yadan kama Naja "Wata tsirfa yaushe kuma ta canza suna zuwa Hanan," Basu kulataba, Nana takuma fita don kawowa Hanan abun tabawa Naja se kallon Hanan take, kamar Jalila kamar ba itaba kuma Jalila dai ba wannan kayan tasakaba Hanan ta kalleta "Baiwar Allah banason yawan kallo, kalli gabanki Dan Allah" Naja ta mata wani kallo "Uban me zan kalla a jikinki, ina cewa akayi kinyi baki, meye kuma na zuwa ki zauna anan, dukda nasan baze wuce danginkune na arnan ba sukazo" Hanan ta fuskanci Naja ta dauka Jalila ce "Ba arna bane cocine sukazo da Kansu, ba arna ba, keba gara arna dakuba, nasan abunda baki saniba, kokuma kinsani amma kuke boyewa, ki kiyayeni " Sallama Nana tayi da tray a hannunta ta doro ruwa da lemo se glass cup, ta ajiye a gaban Hanan "Sannu da kokari" Hanan tai maganar cikin kasaita, "Bakomai" "Nana nakasa ganewa, waiba Jalila ba ce" "Amma gaskiya Naja ba kya ganewa, to ba ita ba ce, abun mamaki ko, suna kama sosai" Jalila ce ta shigo dakin, hanan ta kalleta "Wai ina kika zauna kuka barni" "Ina gurin Baba, ashema tafiya zeyi"? " Eh zebi jirgin, Karfe 2 zeyi tafiya" "Eh Su Yaya Abdallah sun tafi kaishi airport" Nan suka zauna suka kama hira hada Nana, Hanan akwai saurin sakewa da mutane in taga dama, taita basu labarin yadda tayi missing Jalila, da kuma yadda suka cigaba da kawance ita da siyama, sunayi suna dariya ita dai Naja kallonsu kawai take tana tabe baki ga mamakin maganganun Hanan sun cikata, to me take nufi? Ga kuma kamanin da taga sunayi da Jalila tanaso ta tambaya, amma tsakanin Jalila da Hanan bata San wadda tafi iya wulakanci ba. Nana tace musu tana zuwa ta fita, ta Dan basu guri, yayinda Naja ta kame a dakin taki fita Hanan ta kalli Jalila "Queen kinsan wani abu kuwa"? "A a sekin fada" "Ina ganin Yaya Jawwad nagane shi yanada yawan fara'a" "Ai Yaya Jawwad duk inda yake tauraro ne haskensa ne kawai yake bayyana shine," Murmushi sukayi gaba daya, Hanan takuma kallon Jalila, sannan tace "Kuma kallo daya nayiwa Jalal nasan shine" Da sauri Jalila ta kalleta "Ya akayi kikasan Jalal, har kika ganeshi?" "Hmm nasan komai,kin manta ranar dazaki taho kano keda Siyama kunyi zancensa, Dan haka Siyama na tambaya ta gayamin," "Hmm Siyama ko shine tagaya miki, bayan nace mata amana" "To meye a ciki Dan ta gayamin, nida naganshi, he's looking so innocent" "Waye din looking innocent? Amma ba Jalal ba"? "Shidin Jalila, dukda na gaishesu be amsaba, kuma ban zauna da Shiva, amma yanayinsa miskilanci ma yana matukar damunsa" Jalila ta tabe baki "tab wannan Jarababben" "Trust me miskilanci yana damunsa, dakuma kadaici Jalila, yanayin yadda Siyama tabani labarin, akwai wani abu a boye game dashi, amma kafin mutafi zaki gane hakan,"   "Mtseww gulmar banza, munafuncin yabar kan yan Gida harda ya'yan makota" inji Naja "Kee!! Naga kanki yana wata rawa, this should be the last warning, har in bar gidan nan, kika kuma shiga harkata akwai matsala, Jalila ki gayamata bana bakunta, zanyi ba dai² ba" Hannan tayi maganar tata cikin isa "Hmm manta da ita nima tunda tazo nabawa banza ajiyarta, saboda gaba dayanata suffar karyace, da halin Jakuna," Bude baki Naja tayi "Ni kikewa haka Jalila"? "Wallahi kina kuma cewa tak, zan keta miki rashin mutunci, ba a shiga sabgata" Mikewa Naja tayi ta bar dakin tana zage²dan taga inta zauna sesu daketa Hanan ta dawo da kallonta ga Jalila "Waike dama haka kike zaune a gidan nan ana miki wulakanci duk bakin naki, Tun dazu take wani zage² ta dauka kece" "Manta da ita yau tazo, taketa wannan shirmen, abunda yasa ban biye mataba abunda yake damuna daban" "Jalila wai wannan ba kanwar Sa'ada bace ba"? "Eh kanwarta ce ina kika Santa"? "Shedanu karuwan banza kawai" Zare ido Jalila tayi "Haba Hanan wannan wace irin maganace"? "Eh ba karya nayiba, yayarta Sa'ada kawar murjace Yar autar su mommy su ukune, group dinsu Da murja da Sa'ada da Hannah, school daya sukayi, tun daga makaranta suka lalace, duk ina ganin hotunansu a wayar ta, ba inda basa zuwa a Nigeria club² suke zuwa, gurin manyan masu kudi da yan siyasa, daga bayane sukayi fada da Hannah yanzu saura su biyu," "Na shigesu ni Jalila," "Karki kara yadda wata jaka tacewa danginku arna suma duk gayyar tsiyane, ita batasan nasantaba ai, ita kanta Sa ada bata sanniba amma ni duk nasansu, a wayar murja, manta dasu mucigaba da hirarmu" Jalila rasa me zatace tayi, se mamakin abunda Hanan tafada ta keyi, Jalila ta nisa "naso ace hada Siyama kukazo, ina cikin damuwa, bata karasa maganar ba Nana ta shigo da sallama, tacewa Jalila "Jalila su Yaya Jawwad sun dawo, yakamata akai musu abinci" "To bari in kaimusu" Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi, tareda fadin "muje in rakaki" Suna zuwa parlour Maama tana zaune, zata ci Abinci, seda ta Dan bude baki tana kallon Hanan da Jalila Jalila tace "Hanan ga Maama" Hanan ta danyi murmushi "Mamansu Yaya Jawwad kenan"? "Eh itace" daga tsaye Hanan tace Maama ina wuni "Lafiya kalau ya hanya" Maama ta amsa mata ba laifi da faraa a fuskarta saboda ta gaisa da baban Hanan, taga babban mutum ne me Iko Daga nan Hanan tabi su Jalila har kitchen suka dakko kayan Abinci Hanan ta kalli manyan kulolin sannan ta kalli Nana "Ta saku wahala ko? Kalli wannan kayan a wani cikin za a zubasu" "Wane irin wahala, a cikinku zaku zubasu" Nana tabata amsa, sukayi dariya gaba dayansu Suka kwashi kaya se part din Jawwad tunda suka shiga, Jalila taga yadda Jalal yake dariya se abun yabata mamaki, dama Jalal yana dariya kamar haka mutum kullum fuska kamar fuskar shanu ba fara a, amma yasamu Jawwad da Abdallah se dariya yake Sukaje suka ajiye kayan Abincin, Jawwad yana tayi musu sannu Hanan ta kalli Abdallah "Yaya kalli wahalar da Queen tasa sukayi, kasan niba wani Abinci nake ciba lemo da biscuit ya isheni, kaikuma zaka iya zama bakaciba, tunda in katashi ci na mutum biyar kakeci lokaci daya" Zare ido Abdallah yayi "Ke hanan Dan sharri" Hanan ta kalli Jawwad "Yaya Jawwad ba a zuwa da abokinka bakunta, kunyata mutane yake" Dariya sukayi gaba daya ciki harda Jalal Jawwad yace "kalli ikon Allah kamannin Ku har mamaki yake bani" Abdallah yace "ba kai kadaiba farkon fara ganina dasu nikaina nayi mamaki, Inaga Allah ne yahadasu saboda kamanin dasu keyi" "Eh amma nasha wuya ba" Hanan ta fada tana shafa goshi Jalila ta Dan girgiza kai "mhmm bari inje in dakko plates" ta juya ta fita, Nana ma guri ta nema ta zauna Hanan ta Dan gyara zama ta waiga taga Jalila ta fita "Hmm Yaya Abdallah kana Allah ne ya hadamu da Jalila amma nasha wuya," "Wuyar me kuma?" Nana ta tambayeta hanan ta kwashe haduwarsu ta farko a school ta basu labari, Sannan tace " Yaya Jawwad wallahi kanwarka kakkarfa ce mari daya nayi mata Dan mugunta tayimin biyu, Wanda kowane mari daya datayimin dai² yake da nawa uku, ai ban gama shiga hankalina ba, seda naga tayi wurgi dani Jini yana bin fuskata, na dago ina dubawa kowanj malaminne yazo rabamu yayimin haka, yai Jifa dani Ashe Queen ce" Dariya suka kamayi sosai, Yadda Hanan tasaki Miki take zuba kai lace sun Dade tare, kuma tanayi ne Dan monitoring din action din da JALAL ze dingayi Jalal yai murmushi sannan yace "ko y'ar gidan bullet ce" Hanan ta danyi murmushi a ranta, tace hasashena yafara zama gaskiya Abdallah yace "Jalal Ashe kaima kasan zancen" Jalal ya nuna Jawwad "a lokacin ya damu sosai, shi yagayamin" "Nikam ban San labarin nan ba" Nana tafada cikin dariya, Hanan takuma gyara zama sannan tace "Yaya Jalal bakasan wani abuba, tacemin Yar gidan bullet, nazo da daddy ina shirin a casa queen, abun haushi wai Ashe yasanta kwana uku kafin hakan tafaru, Bayan anyi hakan ta dinga like min kaman chewngum kullum setazo inda nake muyi fada ina mata rashin mutunci amma batajin haushi" Duk abun nan da Hanan ta keyi tana monitoring yanayin Jalal ne, Hanan ta danyi murmushi "Se dai Queen duk inda taje kokuma Wanda yai tarayya da ita seyasamu wani benefits a tareda ita Wanda mutum baze mantaba, kamar daini ta saukemin rashin kunya, Dan tundaga ranar na nutsu Dan tanada luck a rayuwarta" Jalila ta dawo takawo musu plates, abun yabata mamaki ita kuwa Hanan metake fada yasa hada Jalal a cikin masu dariya, Jalila ta kalli Nana "Ku tashi mu tafi muci abincin muma" Hanan ta kalleta, "Tab anan zamuci anayi ana hira, ni bani da yayye ko kanne a gidanmu masu debemin kewa nikadaice, Abdallah in ya fice koyakoma makaranta sena ganshi, yanzu ga dama ta samu nasamu Yayye" Jalila har mamakin wannan zakewa da Hanan tayi take Jalila ta kalli Nana sannan ta kalli Hanan "A gabannasu zamuci Abinci?" "To meye a ciki ba yayyanmu bane, ko Nana"? "Aikuwa dai Hanan, gaskiyarki" "Gaskiya yau ranace ta mussaman Dan tayimin dadi" Abdallah yafada yana murmushi "Nima haka Abdallah, kobahakaba Jalal?" Gyada kai Jalal yayi yana murmushi Nana ta fara serving dinsu Abinci Fried rice ce, da sos se simple salad ga juice nan na kwali da Wanda aka hada Abdallah yace "Jalila meyasa Baku girka tuwo ba na masar miyar kuka" "Kutmelesi wallahi da bazanciba" Hanan tafada tana hararar Abdallah, JAWWAD yace "Sha kuruminki Hanan Jalal ma da bazeciba, bayason miyar kuka" "Hh Ashe makiya tuwon dayawa, me fadarma bayaci" Nana tai maganar tana kallon Jawwad Murmushi Jalal yayi, sannan yace "wani abu na tuna, Bros ka tuna lokacin da daddy yake kaimu Maiduguri, abamu biskin shinkafa da miyar kuka, Hajjo tace semunci" Jawwad yayi dariya "Allah sarki rayuwa, kokuma ta dumama tuwo tace shi zamuci, ka wuni da yunwa" "Mu wuni dai, ai kaima bakaci" Suka kuma kwashewa da dariya, Hanan ta Dan taba Jalila sannan tai magana a hankali "Jalila kin yadda da abunda nagaya miki game da Jalal,?" Abdallah ya jefoma Hanan handkchief dinsa "Kai Hanan kiji tsoron Allah me kike gayamata haka" "Ina ruwanka sirrine" Wayar Hanan ta fara ringing, ta mike zata fita ta amsa wayar, Jalila tace "Kunyarmu akeji dabaza a amsa a gabanmuba" "Allah ya kiyaye inji kunyarki, inma kunyarce kunyar Nana zanji itace sirikata" Abdallah yace "ji Mara kunya to wa Nana zata baki" "Idan ma Nana bata baniba nasan Yaya Jalal ze bani" "Wa kikeso in baki" Nana ta tambayeta "Rabu dasu sirrine se mun kebe da Nana zan gayamata" Tayi waje abunta Tafito tana amsa waya turo gate din gidan akayi, yaseera da Ilham suka shigo Kai tsaye suka nufi inda Hanan take Share please More comments more typing.......................... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 40 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Suka karasa inda Hanan take waya, tagama wayar ta juyo ta kallesu, sannan tace "Lafiya naga kunzo kunsani a gaba"? Yaseera tayi murmushi " baki gane niba ne"? "Eh ban ganekiba, yauma nafara ganinki" Aikuwa Ilham a fusace tace "kingani ko yaseera tsabar rainin hankali wai bata ganeki ba, nagayamiki muguwar Yar rainin hankalice" "Haba Ilham meye hakane? Meye Dan bata ganeni ba seta iya yuwa ta manta ne" "Kizo shekaran jiyan sannan yau tace ta mantaki" Hanan ta kallesu "In Baku da abin cewa, ni ina da abunyi" Yaseera tace "A a Jalila, Yaseera ce fa, da mukazo shekaranjiya" Hanan ta fuskanci basu San ba Jalila bace, Hanan a ranta tace wannan ce Ilham kenan, hada ita a cikin labarin da Siyama tabata, na Jalal Ta kallesu tai musu kallon tsaf sannan tace "wannan Hanan ce ba Jalila ba" "Kamar ya?" "Kamar yadda nagaya muku mana" Yaseera tace "Dan Allah Jalila a dena Jokes din nan gurinki mukazo zamuyi magana" Hanan tace "Maganar Me?" "Akan abunda yafaru jiya har Jalal ya huce akan Ilham, abunne yabamu mamaki kwarai" Hanan a ranta tace lallai wannan basu da hankali su nan gaba daya sun yadda Queen ce,.to ni mema zance musu nida bansan meya faruba, "Nima abun yabani mamaki kam, amma yanzu ina wani abunne, kubari anjima,.semu hadu" "To shikenan ina Nana?" Yaseera ta tambaya "Nana tayi bakine tana part din Jawwad" "OK mungode se anjima" Suka juya suka fita Ilham ta kalli yaseera "ji wani sabon iyayi, ga yadda ta canza magana, tanawa mutane magana da isa sekace wata basarakiya" "Nima nagani Ilham ai wannan se munbi a sannu" Suna fita Hanan ta dinga dariya sannan tace amma gaskiya wannan sakarkarune, Takoma ta tarar sunata cin abincinsu banda Jalila da take ta tsakura duk a takure take Hanan ta danyi murmushi sannan tace "Yaya Jalal kufa ci Abincin nan sosai, inba hakaba Abdallah cinyewa ze ya barku" Jalal yai murmushi, "Meyasa kika takurawa yayankin nan haka"? " Abdallah yace tambayeta dai, ni dai ba kunyarku zanjiba Dan in ban koshiba zan karane" Hanan tace "Nima ai haka kake min kaita kunyatani a gaban mutane" Jalila tace "To suda uwar magana ki zauna kici abinci ni bansan yadda akayi bakinki ya bude hakaba, kika koyi surutu" "Hh au haba zama dake ne yasa na koya, ni na manta ma kinyi baki fa, yanzun nan" Jalila tace mata "suwaye"? " ban sansu ba,.wasu matane su biyu suka ganni a waje sun dauka kece suka faramin surutu, nikuma nace sutafi aiki nake sudawo anjima" "Dan wulakanci gaskiya baki kyautaba" Cewar Abdallah, Hanan ta kalleshi " Abdallah bana son ganin gushewar wannan farincikin da nake gani a fuskokinku, nasan in Jalila ta tashi tsareta zasuyi da surutu, Dan daganinsu ba wani abun kirkinne yakawosuba" JALILA tace "Ni mamakima nakeyi suwaye haka?" Hanan tace "wata fara dai me kwalakwalan idanuwa, se wani kallon banza takemin da wata kuma me surutu, se magana take wai lallai sena ganeta sunzo shekaranjiya ko baseera kowa oho dai" Jalila ta kalleta "kai Hanan meyasa kikace su tafi" "To me zasuyi miki, wannan me kwalkwalan idanuwan sewanj kallon banza takemin, shine ya tabbatar min ba abun arziki ya kawosuba" Nana tai dariya "Kanwar Yaya Jalal ce fa, Ilham ko?" Dan zare Ido Hanan tayi, "Dagaske amma basa kama, wata Mara.. Sekuma tayi shiru Jawwad yace " Hanan kanwar Jalalce cousin dinshi ce" "Sedai cousin din Dan basa kama, gashi se wani.. Bata karasaba Jalila ta janyota " haba Hanan zubar ya isa kici Abinci mana" "To nayi shiru" Suka cigaba da cin Abinci Jalal a ransa yake jin wani nishadi, Wanda rabon dayaji shi har ya manta, a ransa yake jin inama a ce wadan nan duk yan uwansa ne shima yace yau yanada yan uwa amma shikadaine kamar rai Suka gama cin Abincin sannan su Hanan suka kwashe kayan suka tafi cikin gida Suka koma dakin su Nana, Nana ta tafi dakin Maama don basu guri Naja se masifa take wai Nana ta rike bare ta manta da ita   Hanan ta kalli Jalila "Queen do you believe now Jalila, nagaya miki Jalal yana bukatar kulawane kawai, kadaici yana taka rawa a rayuwarsa" "Hanan gaskiya nayi mamaki, bantaba ganinsa cikin nishadi ba, koyana dariya kullum fuskarsa babu fara a, kinga wadda sukazo nemana din nan farar, cousin dinsa ce a gidansu take itace take sonshi bakiga dukan dayaake mata ba baya shiga harkar mata, Nima fada muke, yabani mamaki danaga ya kulaki" JALILA ta kwashe labarin Jalal zuwa yadda suke fafatawa dashi, halayensa dayakewa mahaifiyarsa, har zuwa mafarkan da takeyi dashi" Hanan ta kyalkyale da dariya "Jalila ta kalleta, meye haka kuma, Maya baki dariya" Hanan ta sassauta dariyarta "Ashe bani kadai rashin kunya ba taiwa ranaba, kut naso inga idonki lokacin daya baki sigari, kut gaskiya Jalal Dan duniyane yayi maganinki" Tafada tana kuma kyakyata dariya "Mtseeww nifa bana son wulakanci" "Yi hakuri queen, let's be serious, Jalila kiyi wani abu, zaki iya temakon rayuwar Jalal" "Ta yaya zan iya wannan Jarababben Dan taurin kan" "Bashi da taurin kai Jalila, he is simple, yanzu dai yakamata kisan meyasa bayason mahaifiyarsa, ki gano wayeshi, Jalila ke Alkhairi ce a duk inda kikaje, kiyi wani abu sannan kidingayi masa addu a kidena yi masa rashin kunya naga alamar bayason rainin" "Hmm mugun Dan rainin hankaline Hanan bazaki ganeba" "To kicigaba dayimasa rashin kunya randa yabaki giya, kya kirani kibani labari" "Allah ya kiyaye" Halima tayi sallama suka amsamata Ta kallesu sannan tace "wacce ce Jalilan ne tunda tazo na dena ganeki" JALILA tayi dariya "Ya akayi leemart" "Dama Cewa akayi wai kushirya in anyi sallar la asar, Hanan zasu tafi" "To shikenan" Sukayi sallar LA asar Hanan tanata Nanatawa Jalila, ta temaki rayuwar Jalal,.sannan duk abunda ake ciki ta kira ta a waya tagaya mata, Hanan ta fito tayi sallama da Maama, Maama  tabata kyautar agogo, sannan Sukafito A harabar gidan suka tarar dasu Jalal Suma sun fito Abdallah ya kallesu, yace "Yakamata muyi hotuna fa, domin tarihi" "Gaskiya kam" cewar Jawwad "A fara yimana nida JAWWAD" Inji Hanan Ta tafi kusada Jawwad akayi tayi musu Sannan akaimata itada Jalal, da Abdallah dakuma Nana Takalli Jalila "Queen come forward" Ta janyo hannun Jalalila zuwa kusada Jalal, Kallon Jalila yayi, Jalila kuma ta hade rai Hanan tace "Haba queen meye haka kiyi dariya mana, kin wani hade rai kamar wata boss" Dariya sukayi, Hanan tai musu photo, a haka aka dinga hotunan nan, Naja ce ta fito harabar gidan tai tozali da Abdallah gaba daya ta rikice tarasa nutsuwarta, kai Allah yayi Halitta a nan, basu kula da itaba sukaji gaba da hotunansu, Nana ce suka kuma dawowa da Yaseera suka tarar anata budurin hotuna Jalal kamar bashiba, se fara a Se yanzu suka gane, ashe dazu ba Jalila suka ganiba tsabar kamace kawai dasukeyi, Jalal na ganin Ilham ya hade rai, suka karaso inda su Jalal Suke, Yaseera ta kalli Jalila tace"dazu munzo gurinki Ashe bake bace" Jalila tayi dariya tace "bani bace Hanan ce" "To shikenan bari muje naga kunada baki," "A a bakomai bari inzo" "A a ki bari zamu dawo" Jalila tace"to shikenan " Ilham, Jalal kawai take kallo da mamaki, ya kalleta, maganar Hanan ya tuna wai fara me kwalakwalan idanuwa Kawai yadanyi murmushi. Su Hanan sukayi haramar tafiya har bakin mota su Jalila suka rakasu, Hanan ta kallesu "Kamar kar mu rabu, haduwar nan tayimin dadi, muna fatan kuma wataran zaku kawo mana ziyara" "Insha Allah, muma zamu kawo muku ziyara" Ta kalli Nana sannan tace "Nana zanyi missing din murmushinsa, Dan Allah kibani shi" Nana tace "wa kenan?" Ta kalli Jawwad "Gashi nan" Gaban Jalila yafadi, shikansa Jawwad sedaya kalli Hanan, Abdallah yace "Aliyu kaga ku kyale Hanan, wani lokacin bata da hankali" Ya bude mata mota "wuce muje" Ta rike murfin motar sannan ta kalli Jalal "Yaya Jalal da Nana da Queen bakinsu daya naga kamar bazasu bani ba, Dan Allah kai kabani shi" Jalal ya kalli JALILA ya kalli Jawwad yaga duk Jikinsu yayi sanyi kaman Wanda akace za a kashe se yayi murmushi "Yace indai Jawwad ne nabaki shi," Abdallah ya kalleshi "Tab Jawwad kar ka yadda ka auri fitsararriya wannan, kyanta tsayayyen soja Wanda ze zaneta in tayi ba dai² ba" Dariya sukayi amma banda Jalila Hanan ta shiga gaban mota ta sauke glass ta kalli Jawwad, "I will miss you Yaya Jawwad dina, keep me close to your heart" Juyawa Jalila tayi ta shige cikin Gida, saboda ji tayi wani abu ya tokaremata a kirji, takasa tsayuwa Hanan ta jingina da Jikin kujera, tayi murmushi tareda lumshe ido a hankali ta furta "am sorry queen" Abdallah ya kalleta "ya dai uwar magana" "Ba komai, ina cikin farincikine kawai"    Ilham ta kalli yaseera tace "yaseera Dan Allah mubar batun yarinyar nan kawai munemi mafita" "Wace mafita Ilham, so muke mu tabbatar da zarginmu tukuna" "Yaseera lokaci fa kuremin yake, nagaji zanyi abunda naga ya dace" "Ilham kibi komai a sannu kar garaje yakaiki ya baroki" "Nasan yadda zan tsara komai ki manta da ita kawai" "To Allah ya taimaka" Suna shiga Gida Jalila bata tsaya ko inaba ta nufi dakin su, Jawwad jikinsa yayi sanyi sosai, Jalal ya kalleshi yaga Jawwad yayi wani iri kaman Wanda yayi wani babban zunubi Dariya Jalal yai "Wai meya sameka ne kawaniyi shiru" "Hmm ba komai," inni Jawwad "Dan tace tana sonka shine kawani damu, meye a ciki to, naga dai su biyun duk dayane" Jawwad ya kalleshi "Allah ko? Eh ai shiyasa kai gakanan kun jone da Ilham, Dan tace tana sonka, kana sonta kaima" "Mtseww Dan Allah idan ina magana kadena sakamin maganar banza" "Ilham dince maganar banza?" "Ban saniba" Ya mike yai waje yabarwa Jawwad dakin Jawwad yayi murmushi "Ashe ba dadi"   Yana zuwa Gida yaji yanason shan madara, Dan haka ya duba fridge dinsa, bawani lemon kirki a ciki duk se giya, rufe fridge din yayi, ya mike ya tafi cikin Gida, yana zuwa yatarar da Ilham a palour bebi takanta ba ya wuce fridge ya bude ya dau abunda yakeso, yana rufe fridge din ya juyo yaga Ilham tsaye a bayansa Gefenta yayi ze wuce, takuma dawowa gabansa Ya kalleta "meye Haka?" "Abunda kagani mana, Yaya Jalal meyasaka nishadi haka? yau, naganka kana dariya dakuma fara'a abunda ni bakayimin," "Zaki bani hanya kosena barar dake a gurin nan" Hannu ta mika masa "bani in tayaka daukar kayan" "Jalal dama kana gidan nan, amma baka Neman inda nake" Suka jiyo muryar mummy, ya juyo ya kalli mummy "Idan nazo mezan miki? Bani da wani amfani dazan miki, be kamata in dinga zuwa ba" "Ni kake gayawa haka ko?" "Yau nafara gaya miki? Kina son maida hannun agogo bayane kawai" "Jalal kaji tsoron Allah, anya kanaso ka gama da duniya lafiya" "Mummy ke yakamata kiji tsoron Allah tun a farko ba a yanzuba da aikin gama ya Riga ya gama" Ilham ta Dan juya baya tayi murmushi, a ranta tace Ashe kana sane da komai, Jalal mahaifiyarka tayi kuskuren da kake karbar hukuncin Mummy ta kalli Jalal "Yanzu JALAL.... " Enough mummy, baki da abunda zaki gayamin in saurareki" Yana zuwa nan a zancensa yai waje, yayinda mummy ta zauna akan daya daga cikin kujerun palourn tafara kuka   Naja ta shigo dakin su Nana ta tarar da Jalila kwance akan gado Nana kuma tana gyara dressing mirror, kalli Nana "Nana wai bakin sun tafine?" "Eh sun tafi" ta kuma gyara tsayuwa sannan tace "Y'an uwansu Jalilane?" "Eh ya akayi"? "Naga suna kamane sosai da wannan yarinyar, amma wannan namijin dasukazo tarefa?" "Yayan Hanan ne" Nana tabata amsa Jalila tana jinsu tayi musu banza NaJa takuma cewa "Yana da aurene"? Nana ta dan bude baki, ta kalli Jalila sannan ta kalli Naja "To ai Jalila zaki tambaya bani ba" Jalila ta kalli Naja "Kinada damuwa da hakanne, ina ruwanki ne, Suma daga dangin arnan suke, kinada matsala da hakanne?" Jalila tayi maganar a fusace, da son huce takaicinta akan Naja, ta mike ta shige toilet Nana kam dariya takama yi, "to hajiya Naja, kinji dai inma sokike seki hakura" Bayan sallar magariba Jalila ta kira Abdallah, yace mata sun isa Kaduna lafiya tai masa godiya da bangajiya Nana ta shigo da katon Leda a hannunta "Nima bari in Dana Queen inji Hanan" "Sarkin tsokana," "Ba wani tsokana, zomuje kirakani please" "Ba inda zani" "Maama ce fa tace kirakani" "Ina?" "Gurin mummy" "Waike kullum sekinje gidansu Ilham ne? " to queen ya zanyi Maama ce ta aikeni," "Ba sunana queen ba," "To Baby Jalila, na dena" "Kyaji dashi dai" Jalila tasaka hijjabi tabi Nana zuwa gidansu Jalal Suna zuwa suka tarar da mummy tana kuka a palour Ilham kuma tana kan kujera tana chatting, Ilham tace "mummy lafiya kuwa?" Ta goge hawaye, "bakomai Nana bari in dakko miki kudin" Ta karbi kayan hannun Nana ta wuce dakinta Nana ta kalli Ilham "Ilham me akayiwa mummy take kuka?" "Ta tsuniyar gizo ai bata wuce koki, ita da danta ne, yamata rashin kunya ya fita" Nana ta girgiza kai "kai abun ba dadi Allah ya shiryi Yaya Jalal" Jalila ce kawai tace Ameen yayinda Ilham ta maida kai kan wayarta Jalila tace "yawwa Ilham nikam Neman me kukemin dazu?" Ilham ta Dan daga kai ta kalleta "Manta kawai ya Riga ya wuce" Daga nan Jalila bata kuma cewa komaiba Mummy ta fito tabasu kudin ta koma dakinta Ilham ma ta mike tabasu guri Dan zuwa yanzu ba Jalila ba har Nana ma haushinta takeji. Suka koma Gida Nana ta tafi kaiwa Maama kudi, Jalila kuma ta shiga dakin Halima Suketa hirar zuwansu hanan Jalila take gayamata farincikin datayi, Tace kinsan wani abu Halima Halima tace "a a" "Yau abunda yabani mamaki ganin Jalal yana dariya" "Naganku kunata hotuna kaman bashiba" "Wallahi kuwa,Allah sarki mahaifiyarsa ce babban abun tausayi, tanada da kamar Jalal da yakamata ace, tana cikin farinciki amma kullum cikin tashin hankali take" Halima ta kalli Jalila "Tab wannan matarce abun tausayi, amma bata taba shukamiki rashin mutunciba"? Jalila ta kalleta da mamaki "Me kike nufi Halima?" Share please More comments more typing.................... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_            (2020)       _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE- 41 PART 1 Share please   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar 07063065680 Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din 🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa ABDUL JALAL NOVEL FANS Love u all guys ❤❤❤❤❤           -MY FIRST NOVEL- Halima ta kalli Jalila sannan tace "Hmm Jalila kenan abar zancen kawai Allah ya kyauta" "Amma halima yakamata kigayamin" "Jalila fadan bashi da amfani, amma kiyi hankali da matar nan" Daga haka Jalila ta mike ta tafi dakinsu, itakam takasa gane kan wannan al'amari ita dai a haka bataga aibun Mummy, amma meyasa Halima tace bata da kirki, kuma gashi taki gayamata meyasa, Da wannan tunanin ta shiga toilet tai wanka tai alwala tazo ta tayar da sallar shafa'i da wuturi Shikam Jalal daya koma part dinsa ji yayi baya kaunar shan madarar Mummy tagama bashi haushi, Dan haka ya kunna sigarinsa ya dinga sha, dayagama kuma ya sha giyarsa iya son ransa, sannan ya baje a gurin   Jeje ne a gaban wannan mutumin na rannan, mutumin ya kalli Jeje fuskarsa Sam babu alamar tausayi sannan yace "Jeje nagaji fa, a wannan karon na raina kokarinka, har yanzu abu yaki karewa, har yanzu ace kunkasa aikata abunda nakeso" "Jeje yace haba Oga KB duk kokarin danayi abaya, se wannan zaka kasa hakuri, aiko iya haka muka kyaleshi nayi maka kokari, balle ma ina kokari fa" "Hakane amma gani nai yanzu kana nema kayi sanya, a wannan shekarun da kunyi tafiyar nan Dubai da dayan biyu ko akama shi saboda miyagun kwayoyin damuka Sa akayansa, ko kuma da kun tsallake da yanzu munyi arziki fiye da yanzu" "Hakane Oga abun ne da matukar wahala, wannan Jawwad din shiyake hana ayyukan mu tafiya yadda yakamata, Hannah ma tanata nata kokarin amma hankalinsa baya kan mata, yafi ganewa shaye²" Wanda aka kira Oga KB ya nisa sannan ya kalli Jeje "Bawata yarinyar da za a iya sakawa aikin dole se Hannah?" "Oga a matan da nasani na bariki a irin taurin kan Jalal inba, Hannah ba ba wadda zata iya," "To shikenan amma ka ninninka kokarinka, gaskiya sonake yaron nan ya lalace fiye da yanzu, sonake yazama kaman Dan akuya sabida bin mata, yasha miyagun kwayoyi yayi safararsu, sonake bakin cikin ABDUL JALAL Yayi sanadiyar rasa ran Hadiza sannan ya kare rayuwarsa a gidan yari" "Kwantar da hankalinka Oga komai ze tafi yadda kakeso mu dai ka Dan karamana lokaci" "To shikenan ina jira inji kyakykyawan labari" "Kar kadamu zakajine Oga, kwanan nan ranar zagayowar haihuwarsa zeyi, zamu shirya masa party, a nan zamuyi kokarin ganin komai ya kasance" "To shikenan ina saurarenku" Da safe Jawwad yaita zuba ido yaga Jalila ta kawo musu breakfast amma shiru, ga Jalal ma bezo ba daga karshe ma Halima ce ta kawo breakfast din, Jawwad ya tambayi Halima, "Halima ina Jalila?" "Tana cikin Gida" "Meyasa bata kawo Abincin da kanta ba"? "Wallahi bansaniba, kawai tacemin in kawo" Ya gyada kai "OK shikenan, Nagode" Daga nan ya mike ya dau kayan Abincin zuwa gidansu Jalal dan yau be zoba, Kamar yadda yai tsamanni, Jalal be tashi daga bacci ba, yana kwance a parlour, ko kayan jikinsa be canza ba, ga kwalaban giya da yasha da ragowar sigarin da ya zuke, Dan girgiza kai yai sannan ya  tashi Jalal yasashi yai wanka yai sallar asuba, Jawwad ya kalli Jalal "Jalal baza kayiwa kanka fada ba ko? Lafiyarka fa Jalal, zasu iya yi maka illa" Kallon Jawwad yayi ya sunkuyar da kai "Jiya nayi iya kokarina kar in sha matar gidan nan tabata min rai, shiyasa na sha" "Haba Dan uwa, in rai yabaci hankali baya gushewa, ka dinga hakuri, Mummy mahaifiyar kace, ka dinga hakuri da ita" "Jawwad kasan komai Dan haka karka kuma batamin rai" "Shikenan yi hakuri bari mu karya"   Jalila ta na gyara gadon su dan Nana ta tashi daga baccin ta shiga wanka, wayar Jalila ta fara ringing, tana dubawa taga Hanan setaga bata kyautaba bata kira Hanan tayi mata ya hanya ba, tasa hannu ta daga wayar Hanan tace "Queen shine ko ki kirani kimin ya hanya ko?" "Am sorry Hanan nakira Yaya Abdallah" "Shi daban ni daban" "To Allah yabaki hakuri" "Ameen kin temaki kanki da kika bani hakuri, da baki banba ko hmmm" "To ai ya wuce tunda nabada hakurin" "To naji, yanzu dai ya Yaya Jawwad dina fatan ya tashi lafiya" Jimm Jalila ta yi taki cewa komai "Magana fa nake Jalila, nace ya Jawwad dina, kwana nayi ina mafarkinsa, yanamin wannan kasaitaccen murmushin, kaman inyi tsuntsuwa inzo in kuma ganinsa" "Mhmmm" shine kawai abunda Jalila ta ce "Tunda bazaki gayamin ya yake ba shikenan, ni nakirashi inji, ya Jalal dinki"? "Jalal dina kuma?" "Eh mana, tunda bazaki gayamin ya, Jawwad Dina ba, se in tambayeki ya Jalal, tunda bakya iya danne kishinki queen" Dan dabarbarcewa Jalila tayi "Kin fiye shirme Hanan, wane irin kishi, ya Mummy da Yaya Abdallah" "Ya kike kokarin canza maganar ne, anyway kowa lafiya, hau what's app kiga status dina" "To naji, saura inga shirme" Hanan ta yi dariya "Koma dai meye zaki gani" Jalila ta bude what's app dinta taga Hanan ta turomata messages, ta bude hotunan dasukayine, hotunan sunyi kyau, tana duba dp din Hanan taga hoton Hanan da Jawwad, gashi be iya hade raiba, yayi murmushi, sunyi kyau shida Hanan, Jalila ji tayi kaman ta buga wayar da kasa Dagaske kishin Yaya Jawwad nake, "yasalam" status din Hanan ta bude hotunan ne dai akan status din nanma ta rubuta kalaman soyayya, akan hotunanta da Jawwad "Wai dagaske Hanan Yaya Jawwad takeso ko wasa, Hanan karkimin haka mana" Tana kuma shiga daya hoton setaga hotonta da Jalal, wanda hanan tasata tai dariyar dole, shikuma Jalal yana kallonta Hanan ta rubuta "perfect Match, Jalal and Jalila" "Kutmelesi baki da hankali, kinci kai Hanan, Allah yayi min tsari, da mutum irin Jalal," Ta turawa Hanan daga nan ta rufe data dinta ta kashe wayar gaba daya Sakkowa ta yi ta karasa gyaran gadon Sannan tabar dakin gaskiyar Hanan Jalila kishi take, tarasa meyake mata dadi, harabar gidan ta fito, tana son ganin Jawwad, yau ba ta kaimasa abinci ba rabon data ganshi tun jiya da su Hanan suka tafi, "Maybe ma Hanan ta kirashi suna shan soyayyarsu" wata zuciyar ta raya mata, tsaki Jalila tayi a fili, tarasa abunyi, kawai ta shiga gayaran flowers din harabar gidan, lokaci² tana tsaki Abba ne ya fito ze fita yaganta tana gyaran flours, yayi murmushi yakarasa inda take yace "Barka da safiya, yarinyar kirki, da kanki kike gyaran flowers din" Murmushi ta yi "Abba barka da fitowa" "Yawwa Yar albarka, dakanki kike wannan, akin nasaka a nemo wani megadin daze dinga kulada flowers din" "Abba dan dai gyaran flowers ai ba wuya koni se indingayi" "A a baza ayi hakaba inkika fara zuwa school fa, wannan ba aikinki bane, Yawwa munyi waya da umminki, tacemin tana nan tafe next week insha Allah, zatayi tafiyar nan" "To Abba nima tagayamin," "Masha Allah, Allah yakawo mana ita lafiya" "Ameen Abba" Abba ya kalleta "Ina fatan ba wata matsala zamanki a gidan nan ko"? " babu wata Matsala Abba" "Masha Allah, in akwai wani abu dai kimin magana" "To Abba, Adawo lafiya" "Allah yasa Jalila" Daga haka Abba ya shiga motarsa ya fita Bayan sun gama breakfast Jawwad ya kalli Jalal yace "Am going" "Where?" Jalal ya tambayeshi "Gida mana ina son ganin Baby, naga kaman tana fushi dani, tun jiya ban kuma ganintaba, yauma ba ita ta kawo min Abinci ba" Jalal ya mike kafa ba tareda ya kalli Jawwad ba yace "Laifin me kamata, zatayi fushi?" "Nima bansaniba Jalal, zan tambayeta dai, na damu da rashin ganinta" Tsaki Jalal yayi "Kafiye abun Haushi," "Eh naji, nikam se an nima" "A sauka lafiya" Daga haka Jawwad ya tafi Gida a harabar gidan ya Tarar da Jalila  ta na gyaran flowers, tabawa gate bata, dan haka batasan ya shigo ba, a hankali ya karasa inda take, juyowa tayi kawai tai tozali da Jawwad, seda ta dan tsorata Murmushi yayi mata "matsoraciya ga idonki, am sorry nabaki tsoro ko" Murmushi itama tayi masa ta girgiza kai, kallonsa take ta tuna maganar Hanan "Kwana nayi ina mafarkinsa yanamin wannan murmushin" Dan hade rai Jalila ta yi, wata zuciyar ta ce mata "wata kilama sunyi ways da Hanan" kara bata rai tayi, Karasowa yayi daf da ita ya kalleta "Baby laifin menayi miki hakane, kike hademin rai, yau duk bana jin dadi ban gankiba" Rasa me zatace masa tayi dan kuwa babu laifin da yayi mata "Yayana bakayimin laifin komaiba" "Are u sure, naga kina fushi dani" "Bazan iya fushi da kaiba" "To shikenan kin tashi lafiya"? " lafiya kalau,? "Meyasa baki kawomin Abinci ba yau"? dan sunkuyar da kai tayi kasa "Bakomai" Maama ce tafito zata fita unguwa ta gansu tare, kallonsu ta yi ta dauke kai, Jawwad yace "Maama fita zakiyi?" "Ka aikeni ne?" "A a Maama a dawo lafiya" Ta amsa da "Allah yasa" Jalila ma tace "Adawo lafiya" Kallon Jalila tayi ta dauke kai, taje ta bude motarta, ta shige tai waje, Jawwad ya dawo da kallonsa kan Jalila "Baby me yake damunkine naga baki da walwala tun jiya?" Rasa mezatace tayi kawai setace masa "Yaya Jawwad, meyasa abokinka bashida kirki? Jiya munje gidansu da daddare Mummy tanata kuka saboda shi Yaya ka dinga yi masa nasiha, ni a ganina tarayarka dashi bata da amfani" Dan kurawa Jalila ido yayi na wasu sakanni, ya dan sunkuyar da kai sannan ya kuma kallon ta "Jalila" ya kira sunanta "Na am Yaya Jawwad" ya mike tsaye sannan yace mata "Biyoni" Ba musu ta bi bayansa, har palournsa sannan ya nuna mata guri ta zauna "Jalila rabuwata da Jalal ba mafita baneba, ina tareda shima kalli halin da yake ciki, inaga inna rabu dashi, babu wasu abokan arziki a rayuwarsa kowa yayiwa dansa kashedi akan mu amala dashi, babu wasu mutanen kirki da yake rayuwa dasu, ko ransa ya baci sune mutanen da suke tarairayarsa, kowa yana kyamarsa shiyasa abune mawuyaci ya rabu da shaye² indai mutanen kirki sukayi karanci a rayuwarsa" "To Yaya meyasa bazaka masa fada ba ya canza rayuwarsa haka yaga kowa yana yi, babban abun damuwar yadda yake treating mahaifiyarsa, Sam be dace ba" Jawwad yayi ajiyar zuciya "Abunda yake tsakanin Jalal da mahaifiyarsa sirrine na rayuwarsa, amma dai a da mutumin arziki ne, bahaka yake ba, wani azzalumin aboki ya hadu dashi waishi Jeje shine silar lalacewar Jalal nayi iya kokarina ya rabu dashi, amma yaki, akwai wani mummunan kuduri da Jeje yake dashi akan Jalal Wanda ni kaina ban saniba, yanzu ga wata shedaniyar yarinya data shigo rayuwarsa, wadda nake kyautata zaton bakinsu daya da Jejen wai ita Hannah" Dan dagowa JALILA tai ta kalleshi "Hannah kuma?" "Eh Hannah, ta shigo rayuwar Jalal, iatama, Jalal kaman Wanda akayiwa asiri, gashi cutar dashi suke amma baze iya rabuwa dasuba, duk lokacin da nayi yinkurin yi masa nasiha, idan yayi kaman ze dauka seya birkicemin ya dingamin tsawa jijiyoyin kansa su kumbura, wani lokacin seya suma, shiyasa na barwa Allah komai nake masa addu a" Shiru Jalila tayi wato Jawwad yasan Jalal yana wannan abun Jawwad yabata labarin nan a dukunkune bata wani gane komaiba amma waye Jeje she needs to know him Jawwad ya kuma dubanta "Yana daga abunda yasa bazan iya rabuwa da Jalal ba halaccin mahaifinsa Jalila bayan Abba da Abee, daddyn Jalal yana cikin mutanene daba zan mantaba,Jalal ya kaunaceni tun ina dan talaka na, Jalilalokacin ina zuwa gidansu Jala, y'an fashi suka shigo gidan da daddare, tashin hankalin daddyn Jalal karsu yimin wani abu da sukaga haka se sukai kokarin harbina, Jalal ya taremin harbi, aka sameshi a memakona, Jalal seda yayi jinya a kasar waje, badan ya tureni ba ya tsaya.dani zasu samu " Zare ido Jalila ta yi, ya gyada mata kai "Da gaske Baby, idan nafara gaya miki halaccin da yayi min dayawa, dan haka idan na gujeshi nayi butulci, naci amanar kauna da soyayya da yayi min, kitayani yi masa addu a komai ze zama dai² insha Allah" Nannauyar Ajiyar zuciya Jalila tayi "zan dinga yi masa addu a insha Allah" "Yawwa baby in kakayi haka kingama min komai" Daga nan JALILA ta tashi ta koma cikin Gida Tunani ya hadu yayi mata yawa, Yaya Jawwad be bayyana mata komai sosai ba, yagayamata abubuwan a takaice kuma a dukunkune, ko wazata tambaya Yana da kyau tasan waye Jejen nan, amma to kuma meya kawo Hannah cikin lamarin nan akwai kanshin bakinsu daya da Jeje kenan "Kai JALILA karki bari kwakwalwarki tayi bindiga mana kin takurawa kanki akan wannan sha³ dabe masa ciwon Kansa ba mutumin da giyarsa tafiye masa komai inyi rayuwata mana, haka Jalila ta cigaba da takura kanta, seta dena wannan tunanin son sanin waye Jalal" Maama kuma tunda ta fita zuciyarta ke tafasa kan wannan kusanci da shakuwa dake tsakanin Jawwad da Jalila, saboda gani take abun nasu na shirin komawa soyayya, idan kuwa tana Raye bazata taba bari hakan tafaru ba, dama gidan wata abokiyar kasuwancinta zataje dan haka tana zuwa a gurguje tai abunda zatayi ta fito ta tafi gidan yayarta mairo Tana zuwa kuwa tayi Sa a tana Gida dan gantalalliya ce ta innaniha dillaliyace yau tana nan anjima tana can Ga ta da 'yan mata manya irinsu Sa ada da Naja da sauran mannensu amma har shabiyun rana ko wanke² ba suyiba Daki suka shige da Maama da Yaya mairo, suka gaisa sannan Yaya mairo ta kalleta "lafiya dai Zainab naganki haka?" "Inafa lafiya game da wannan yarinyar ne" "Wace yarinyar?" "Jalila mana" Yaya mairo tayi mutmushi "Kice Jalila ta gurin arniya, ai jiya Naja data dawo tabani labarin komai, yarinya ta samu sakewar yin abunda taga dama,wai ta dawo gidanki da zama, narasa wace irin macece ke Zainab, ya akayi kika bari ta dawo miki Gida harta samu wannan yancin? Ashe kinshirya ganin ya'yanki sun fara binta coci" Maama tai ajiyar zuciya "Ni duk ba wannan ba Yaya, yaron nan fa Jawwad alamu sun fara nunamin kamar Santa yakeyi" Zare Ido Yaya mairo tayi "ita wa din?" "Haba Yaya mairo ya zaki dinga tambayata kaman baki San akan Wanda nake maganaba" Yaya mairo ta jinjina kai "Tirkashi, se yau na tabbatar da Zainab baki da wayo kina me hakan ke shirin faruwa garin Yaya?" "Kedai bari duk yadda na kesa musu ido amma alamu sun fara nunamin hakan" "To yanzu wani mataki kika dauka?" "To Yaya mairo da na dauki wani mataki ai da banzo nanba" "Gaskiyane, yanzu abunda ze faru zanzo gidan naku, zan zo in samesu, nasan abunda zanyi" "To shikenan har na danji sanyi, wallahi" "Karki damu kibar komai a hannuna" Da haka sukayi sallama Maama ta koma Gida Jeje ne ya kalli Hannah, "Hanna akwai bukatar kara himma akan Jalal, idan mukace zamu cigaba da bin komai a hankali muna lallabashi to aikin nan base yiwuba" "Nima nayi tunanin hakan amma me kake gani za ayi?" "Birthday Jalal saura wata daya, a wannan lokacin nakeson mu kaddamar da komai, ko ya rayu yayi abunda mukeso, ko kuma................... Ilham tana kwance ta lumshe ido, da alama tana son yin baccine, wayarta ta fara ringing, yamutsa fuska tayi takai hannu da niyyar yin rejecting kiran taga sunan malam Wada a jikin screen din, da sauri ta tashi zaune taje tasawa kofar dakinta key ta dawo ta daga kiran Suka gaisa, sannan yace " dama batun Yarinyar nan da kikayi min magana akanta ranan ne" "Nagane Jalila kenan" "Yawwa ita nayi bincike akanta amma akwai Matsala............ Share please More comments more typing.......................... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  42 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa        _My first novel_ Sassauta murya Ilham tayi sannan tace "Malam matsala kaman yaya? " eh nayi bincike akan yarinyar nan, amma abune mawuyaci asiri yayi tasiri akanta, zanyi kokari inga aikin dazanyi akanta amma kema sekin dage danaki kokarin domin samun nasarar kawar da ita gefe" Ajiyr zuciya Ilham tayi, "to shikenan malam nagode" Sukayi sallama Ilham ta yi shiru nawani lokaci sannan tai kwafa "indai makircine Jalila tasamu daidanta, nasan abunda zanyi" Hanan tacigaba da kiran Jalila tana takuramata akan Jawwad, in Jalila taki dagawa tabita what's app, duk Yadda Jalila taso ta dinga kokarin danne kishinta amma takasa, itakuma hanan kaman Jalila tana zigata, ta dage ita Jawwad takeso. Wajen karfe shadaya na safen yau yaya mairo tazo gidansu Jawwad, tunda matar nan tazo gaban Jalila yake faduwa, dan tasan yau ranar cimata mutuncine, tunda yaya mairo bata kaunarta, Aikuwa tunda tazo take bakaken maganganu, ita dai Jalila ta makale a daki taki fitowa     Jawwad sun gama breakfast dinsu, suna hira da Jalal, Nana ta kira Jawwad a waya "yaya kana ina? Nazo part dinka baka nan? "Nana ya akayine? Muna tareda Jalal" "Yaya Jawwad, yaya mairoce take nemanka fa" Gabansa ne yafadi "Nana nikuma, me yafaru? Wani abun nayimata? "wallahi bansaniba, se faman fada take niban san akan me take fadan ba, tace lallai kazo" Ajiyar zuciya yayi "to gani nan, ina zuwa" Ya sauke wayar a hankali, Jalal ya kalleshi "ya akayine?" "wai yaya mairoce tazo tana nemana bansan me nayi mata ba, banason fadan  nan nata" Tsaki Jalal yayi "ni wallahi kana  bani mamaki, to dolene sekaje ai ba dole bane," "haba Jalal itama kamar uwa take a gurina fa, ya za ayi takirani naki zuwa" "to haifarka tayi, sekayi tayi, tashi muje, akwai abunda zanyi a dakinka" Jawwad ya Mike suka fito, suka tafi gidansu Jawwad, Jalal yayi part din Jawwad shikuma Jawwad yai cikin gida, Jawwad yana zuwa ya tarar da Yaya mairo, A palour Maama na kusa da ita, ya shiga cikin palour ya tsaya daga bakin kofa, ya durkusa yana gaida yaya mairo "shigo mana kawani tsaya daga bakin kofa, kaman mara gaskiya, dama ba gaskiyarce da kaiba" Karasawa yayi gabanta ya zauna ya da n risinar da kansa, sannan yace "Nana tace kina nemana" "eh ai naganka, takanas nazo gidan nan domin in maka Jan munne, Mahaifiyarka taje har gida ta sameni akan taga take2nka na shigewa wannan yarinya, yar gidan arniyar nan, to bari kaji kaf zuriarmu babu arna dan haka bazamu hada zuria dasuba jan kunne nake maka, karka kuskura kasawa zuciyarka zamu bari ka aureta, bamu shirya ganinka tsakanin massalaci da coci ba" Dagowa yayi ya kalli yaya mairo "haba Yaya, Jalila fa ba arniya bace kuma koba komai itama kanwata ce, kuma batada wani aibu" Maama ce ta kalleshi "au Jawwad abun har ya Kai ana maka magana kana mayarwa" Yaya mairo ta kalleta "ai shiyasa nace kinyi sake zainab," Jalila kam ga gaji da zaman daki ga shi ko karyawa batayiba, cikinta yafara kullewa ga sauran aikin gida, dazatayi, dan haka ta mike ta fito Aikam karaf miyagun maganganun Yaya mairo suka fara dira a kunnuwanta "muna da ya'n mata a dangi ga su Naja nan da kannenta ka duba a ciki, kasamu matar aure amma ka kiyayi kanka da fara soyayya da wannan yarinyar arniyar ragowar titi, suda basu san abun kunyaba, Allah ka dai yasan mazan da take bi, ni muslincin nasu ma ban yadda dashiba" Gani sukayi ya kurawa kofar corridor ido suna juyawa, sukaga Jalila a bakin kofar tana hawaye Yaya mairo ta tabe baki "to almira da kika tsaya kina mana kuka ai ba karya nayiba" Maama tace "to tama ce karya kike mana, aikowa yasani, nidai fatana a kyalemin yarona, ato bana son wannan shishshigin da ake masa" Jawwad yace "haba Maama harda ke?" Maama a tsawace tace "dalla rufemin baki," Yaya mairo ta juyo ta gyara zama sosai ta fuskanci Jalila "ke ki bude kunnenki da kyau kijimu, gida dai gashi nan kinzo kin zauna, amma Jawwad karki sakawa ranki zamu bari ya aureki dan Zainab tace kusancinku da kuma zakewar dakike yayiwa kashedi nake miki yanzu, kisani 'yar dangi' yar cikakkun musulmai zamu aura masa, yar asali yar dangin uwa da uba ba wadda take da raunin nasaba ba, ba wanda yasan uwarki daga ina tazo ya akayi suka.... Juyawa Jalila tayi cikin kuka ta koma dakinsu, bazata iya jure wannan maganganunba, dan inta cigaba da tsayuwa za a iya samun matsala, Jawwad yabi Jalila da kallo, yana jin kukan Jalila har cikin ransa ya dawo da kallonsa kan Yaya mairo "haba Yaya mairo, be kamata kisata gaba kina cin zarafinta ba, babu wanda Allah yayi shawara dashi lokacin da ya shiryamana kaddararmu, meye laifin Jalila anan" Maama ce tace "wallahi ka kuma magana sena mareka, mu zaka gayawa abjnda ya dace muyi, kaika haifemu? Koka fimu sanin abunda ya dace da kai" Yaya mairo tace "kyaleshi ya dakeni, se insan kaji haushi" Halima tana daga dakinta amma tana jin duk abunda akeyi, ranta ya baci matuka, bataji dadin abunda akayiwa Jalilan ba, cin mutuncin yayi yawa, Ita kam Jalila tana zuwa dakinsu da kuka ta shiga, Nana tasan Yaya mairo ce tayi mata wani abun, dan girgiza kai Nana tayi ta Mike ta fito palour Itama tazo ta tarar yaya Jawwad ya sunkuyar da kai yayi shiru Yaya mairo tanata  surfa masa fada hadi da cin mutuncin Jalila da mahaifiyarta, ita kanta daba ita akayiwa ba seda taji ba dadi, dakinsu ta koma ta tarar da Jalila tana kuka hada sheshseheka zama tayi tana rarrashinta, amma Jalila taki yin shiru Seda yaya mairo tayi me isarta Maama tana tayata, Jawwad ko kai bekuma dagoawa ba balle yace zece wani abu seda sukagama sannan yace "Allah yabaku hakuri za a kiyaye Insha Allah" daga nan ya tashi ya fita Yaya mairo ta dawo da kallonta kan Maama sannan tace "to kema bazama zakiyi ba ki mike tsaye ki tsaya akan yaranki ki tabbattar kin rabasu, ba ruwanku da ita in tagaji ta tattara ta koma inda ta fito, baze yiwuba ankawo miki arniya an ajiye tana mjamala da yayanki ba"   Jiki a sanyaye Jawwad ya shiga dakinsa, yasamu guri ya zauna, ya kashingida a jikin kujera ya lumshe ido, Jalal dayasaka systems agabansa yana dannawa ya dan dago kai ya kalleshi ya maida kansa kan abunda yakeyi, Jalal gani yayi Jawwad bashi da niyyar yin magana, Jalal ya dan gyaran murya "Me yafarune, me kayi mata?" Seda Jawwad yaja wasu seconds sannan ya dago ya zauna sosai ya kalli Jalal "Jalal narasa me Baby tayiwa Yaya mairo ta tsaneta haka ba" Dan tabe baki Jalal yayi "Maybe Rashin kunya take mata" "No Jalal, Jalila ba abunda tayi mata ta tsaneta, yanzu ma kiran datakemjn wai Maama taje ta sameta akan wai Jalila tana zakemin, wai kar insa ran zasu bari in aureta, babban abunda ya Kuma bata min rai, kiran Jalila da suke da arniya, me raunin nasaba, kuma Jalila taji, amma matar nan takiyin shiru tacigaba da cin zarafinta, ina jin kukan Jalila a cikin zuciyata" Dan kurawa Jawwad ido yayi sannan yace "Wannan matar bata da hankaline? Kokuma bataje Islamiyya ba, ita Jaleeelan shashashar inace ta tsaya, aka dinga zagin mahaifiyarta, Uwa tafi Uwane?" Jalal yai maganar a hasale "No Jawwad, nasan Jalila kara take mana amma tabbas da a wajene, bazata yaddaba, ni nasan hakan" "Ba wata kara Jawwad kadinga gayawa yayar mahaifiyarka gaskiya, dan tana zaune a gidanku bekamata a dinga cin zarafinta ba, koni nan" Ya nuna kirjinsa, "koni bazan bari wani banza a gari yazagarmin uwaba, dukda abjnda ke tsakanina da mahaifiyata ba, me yasa za a dinga dawo da abunda ya riga ya wuce?" "Haba Jalal ya kakeso inyine nayi kokarin nusar da ita amma itada Maama sun rufeni da fada" "Mmm ba yadda zakayi, amma Jawwad mahaifiyar Jalila, Mutum ce, ba abar yarwa bace agurinmu, be kamata a ci zarafinta a gabanmu ba" "Nasani Jalal, amma ka fahimceni, ba yadda na iya ne, nasani kowaye akayiwa haka baze Ji dadiba, Ina iyajin pain din da Jalila takeji amma ba yadda na iya, da nayi tunanin ko Abba zan gayawa, amma hakan ba mafita bane, ze kuma haddasa fitinane kawai" "to wai ma tukuna zuwa kayi kace musu kana sonta" Kallon Jalal yayi "Jalal koban fada ba shakuwar dake tsakanina da Jalila, bata y'an uwanta bace kawai, Jalal ni son Jalila nakeyi dagaske aurenta nakesonyi" Wani dogon tsaki Jalal yayi "Wannan yarinyar mara kunya ita zaka aura, lallai kaci kai," "kaman ya naci kai? Meye aibunta? "Babu kam, bayanma bata da kunya ka aurarwa Ummi yarta, wannan matar tazo tana zagin mata mahaifiya, ni danta wannan yarinyar komeyema akmata ban damu ba, amma cin zarafin Mace kaman Ummi be kamata ba, bekamata a cigaba da wulakanta taba saboda kanason yarta ba" Jawwad ya dan gyara zama sannan yace "Jalal ina fatan komai ze daidaita insha Allah, amma ina son Jalila, so bana wasa ba" "to shikenan Allah ya kyauta"   Cikin gida kuwa Jalila tayi kuka, har ta gaji, Nana taibata hakuri, se ajiyar zuciya Jalila take, Nana ta tashi ta tafi palour domin dakkowa Jalila ruwa, tana zuwa itama Yaya mairo tafara saukemata nata fadan, itakuwa Nana ta hade rai tana kunkuni Jalila tana Cikin kukanne ummi ta kirata a waya, ta dinga kallon screen din har wayar ta katse, kuma kira ummi tayi amma wannan karon se ta Kai hannu ta daga Ta tattaro nutsuwarta, suka gaisa da ummi "lafiya kuwa naji muryarki kaman kina kuka" "lafiya kalau Ummi banajin dadiine" "meyasame ki?" "Ummi ciwon marane fa kawai" "Hmm Allah ya sawwake" tafada ba dan ta yaddaba" Kaman an tsikari Jalila tace "ummi yaushe zakije garin naku dan Allah ummi kije ki dawo, in dawo gurinki" "akwai matsala kenan?" "ummi ta tambayeta " ba wani matsala ni dai kawai sonake kije ki dawo, bazan iya rayuwa ba kya kusadaniba, sannan na kagu inga yan uwanki ummk, " Jikin Ummi yayi sanyi tasan akwai matsala ne take kokarin boye mata, " Baby wayace miki idannaje dawowa zanyi? Bazan kuma dawowa ba nima a cikin ahalina zan zauna" "haba ummi karkiyimin haka mana, wallahi ko ina kika tafi sena biyoki, bazan iya rayuwa babu ke a kusa daniba" Ta karashe maganar tareda fashewa da Kuka, dama kukan take ta boyene dan kar ummi tagane "is ok my dear, ina nan zuwa jibi Insha Allah, a satin nan zanje gida Nima kidena kukan haka" Ummi taita rarrashinta, sukayi sallama Wunin ranar Jalila a daki tayishi tana kuka, gashi ko abinci bataciba, Nana tayi juyin duniya akan Jalila taci abinci amma taki ci, haka take ma a bangaren Jawwad shi yayi breakfast amma bayan nan beci komai, Jalal ya kalleshi "kai nifa yunwa nakeji, kaje kace ta kawo mana abinci" Jawwad ya kalleshi "wakenan?" "kafini sani ai, ni yunwa nakeji" "haba Jalal nagaya maka halin da take ciki, ya za ayi ta wani dafa abinci"? "Ina ruwana da halin da take ciki? Halin da cikina yake ciki ne ya dameni," Jawwad ya kalleshi "toni na damu da halin da take ciki, ina ji a jikina har yanzu kuka take" "Ko? Da gaske ka damu,? Aini ban saniba, tunda banga kana kukan ba kaima, sharokhan sarkin soyayya, kagani ka tashi kasamomin abinci" Wani mugun kallo Jawwad yayi masa, ya tashi yashige bedroom ya bar Jalal a palour Jalal yai murmushi ya girgiza kai   Bayan la'asar Maama ta kira Nana tasata a gaba suka fita, tareda Yaya mairo, sannan ta aiki Halima, akabar Jalila a gida, Jawwad yaji karar motar Maama ya leka ta window palournsa yaga fitar Maama da Nana da Yaya mairo, Jalal ya uzzurawa Jawwad se ya tashi ya rakashi cin abinci, dan baze bari yjnwa tayi masa illa ba Badan Jawwad yanasoba ya tashi suka fita, Fitarsu Nana, hakan yabawa Jalila damar yin kukanta yannda take so Tabbas da watace ta gaya mata abunda aka gayamata yau a cikin gidan nan to da setayiwa Yaya mairo rashin mutuncin da harta mutu baza akuma yimata makamancinsa ba Amma kash koba komai yakamata tayi al kunya ko dansu Jawwad, ga nasihar umminta data dingayi mata akan tayi hakuri dazaman da zatayi da mutane, gajiya tayi da zaman cikin gidan, zuciyarta na ayyana mata abubuwa, tasan tunda aka fara haka, lallai Maama zata dau shawarar cigaba da cuzgunamata, kuma yau da gobe se Allah dan wataran zata iya marin mace akan taba mata uwa. Tashi tayi ta fito harabar gidan, zuciyarta na saka mata abubuwa dayawa Ilham ce ta shigo gidan, ta hangi Jalila tsaye a wajen kofar shiga cikin gidan, ta nade hannuwa tayi shiru alamun tana tunanin wani abune, Zuwa tayi zata wuce amma Jalila na tsaye a bakin kofar bata fito ba bata shigeba, Seda su Jalal suka je karshen layi, sannan ya tuna yabar wayarsa, yace Jawwad yayi parking ya jirashi yaje ya dakko baxe dade ba, Jawwad yayi parking, Jalal ya sakko ya tafi. Ilham ta karasa inda Jalila ke tsaye "Zan wuce" Ilham ta fada tana kallon Jalila "basa nan masu gidan, ki koma inda kika fito" Jalila ta fada a takaice "ke bana son shirme, ba gurinki nazo ba ai" "Nasan ba gurina kikazoba, bazaki shiga bane kawai tunda ba kya ganewa nace miki ba sa nan" A tsawace Ilham tace "Ke dakata Malama, karki gayamin magana mana, da kikemin wannan gadarar, aiba gidan ubanki bane, dan nasan ubanki ko taku daya bashi dashi a gidan nan" aikuwa Jalila tayi niyyar sauke fushinta akan Ilham, takuma kallon Ilham "Ke daga inda kike gidan naki ubanne ai, saboda tsabar arzkin ubannaki shiyasa naga yabarki kina ragaita tsakanin gidan yan uwa, saboda kwadayi" "Hmm Aida tuni gidan ubanane, wasu dalilai suka hana faruwar hakan, amma wataran dukiyar da kike magana zatazama mallakina" Kallonta Jalila tayi baki bude "A matsayinki nawa, dukiyar uban wani zata zama taki kwadayayyiya, aje ai takama da dukiyar uba, bata uban waniba, malama kijuya inda kika fito, " Karki gayamin maganar banza malama, kodamene ubana yafi ubanki, tunda nasan kowa kika tambaya ze gaya miki inada Uba, amma ke wayasan naki uban Wani wawan Mari Jalila ta saukewa Ilham batare data bari Ilham tagama maganar ba " Karki kuma dukanmin kanwa, inkika kuma sena rama mata"Muryar Jalal ce, suka waiga gaba daya Share please More Comments More Typing............................. Love u all my Fans Ina me baku hakuri bazan cigaba da posting kullum ba, saboda zankoma online lectures, amma zan cigaba da kokarin cigaba dayi muku posting nagode sosai 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/13, 10:27 PM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  43 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa        _My first novel_ Jalala ya karaso inda suke, ya kalli Jalila, "kina kuma marinta kema sena mareki, mara kunyar kawai, Ilham sa'arki ce?" Wani banzan kallo Jalila tayi masa "Ilham din banza Ilham din wofi, wallahi ta kuma zagina sena kuma wankamata mari dama Jakace kaima kasaba jibgarta, sha3 Karya banza Mamakine ya cika Ilham wai ita yake tarewa fada, kallon Jalila tayi " Kece babbar karya baniba" Jalila tace "kinga karnuka nan" ta nuna Ilham da Jalal, Ilham tace "Nida yaya Jalal dinne karnuka" Tsaki Jalila tayi, ta shige ciki, ta hankado kofa, Ilham ta kalli Jalal Zatayi magana kawai yai tafiyarsa, yabar gurin dama dan ya kuma kunna Jalila yayi, ba nufinsa ya shigarwa Ilham ba, suka batta a tsaye baki bude "to me suke nufi da hakan?" Babu me bata amasa dan haka ta juya ta koma gida, se bayan sallar isha'i sannan su Nana suka dawo, Nana tai tabawa Jalila hakuri akan sun tafi sun barta ita kadak, Jalila ta nuna mata bata damu ba, tun ranar da Yaya mairo tazo tayi wannan cin mutuncin Jalila bata kuma bari sun hadu da Jawwad ba, ya damu sosai ko wayarta inya kira bata dagawa, ko palourn ma ta dena fitowa se dai ta zauna a daki,       Yau ta tashi da murnar ummi zatazo, amma haryanzu ba saki jikinta ba abunda su Yaya mairo sukayi mata yana taba mata zuciya, sannan idan ta tuna ummi tafiya zatayi ta barta a gidan, setaji ba dadi, Nana da halima ne sukayi wa Jalila kara sukayi girki domin tarbar ummin Jalila, amma ita kam ko san fitowa batayi, seda Abba yasa aka kirata ya tambayeta ko akwai matsala kwana biyu baya ganin gilmawarta, amma tace masa ba komai, Jawwad ma yayi sintiri a cikin gidan amma baya samun ganin ta, gashi yana tsoron yaje dakinsu Jalilan, saboda Maama, in yakira Nana yace tabata wayar se taki karba, Jawwad ya damu sosai Karfe sha biyun rana ummi ta iso gidan, Jalila kaman ta shige cikin ummi dan farin ciki, tayi murna matuka, Abba yana gidan saboda zuwanta, Maama dai ba yabo ba fallasa ta tarbeta saboda idon Abba, Jawwad ya shigo domin gaida ummi, se lokacin yaga Jalila, ta dan fada idonta yayi zuru2 tana manne  a jikin ummi, tausayinsune yakama shi, suka gaisa da ummi, daga nan ya shantake akayi ta hira, ya tashi ze fita ya waigo ya kalli Jalila yace "Jalila, dan Allah kawomin coffee" Abba yace "Yayana kafiye takura, tana zaune tana jin dumin ummin zaka sakata aiki, murmushi Jawwad yayi yana dan sosa keya, Maama kam wani mugun harara tayi masa, suna hada ido da Maama ya sunkuyar da kansa kasa, ummi kuma tace " Ai ba wani takura dan yasata aiki, ai kanwarsa ce, tashi ki kaimasa" Jalila ba dan tasoba ta mike taje ta hado masa, ta fita domin kai masa, Maama a ranta tace "lallai Yaron nan, wato beji maganar da mukayi masa ba kenan?, aikuwa sena saba masa" Jalila tana kaimasa, ta ajiye ta juyo zata fice Jawwad ya kira sunanta "Jalila" cak ta tsaya amma taki yadda ta kalleshi, Tasowa yayi yazo gabanta ya tsaya, suna iya jin numfashin juna, muryarsa a sanyaye yace, "Baby menayi miki na cancanci wannan hukuncin? Kin kauracewa ganina, tsawon kwana biyu, kinki daga wayata, kinsani cikin damuwa, Baby why?" Dan dagowa tayi ta kalleshi, idonta sun ciko taf da hawaye, ta sunkuyar da kai, kallonta yayi ya kuma sassauta muryarsa "Ohhh no Baby, nagane, Jalila you are not suffering alone, i also feels what you feel, Baby dan Allah kiyi hakuri akan abunda akayi miki, kar hakan yasa ki kuma, kauracemin kwana biyun nan na shiga damuwa, sannan kidena zubar da hawayen nan, banaso, kuma in Ummi, taganki cikin damuwa bazata ji dadi ba" Gaba daya jiknta yayi sanyi, duk yabata tausayi, ta gyada masa kai alamun ta gamsu da maganarsa "Kindena kukan?" Ta gyada masa kai, ya ciro handkechief a aljihunsa yabata, ta goge hawayen da yake idonta, ta mika masa, sannan ta fito, ta koma cikin gida, Ta tarar ummi tana cin abinci, spoon ta dauka tazo ta zauna, suna ci da Ummi, Zuciyar Ummi fal tausayin Jalila, akwai abunda yake damunta, amma taki fada mata, Nana ta fito taga Jalila da ummi suna cin abinci tare, ta kalli Jalila "Wato dan ummi tazo shine, yau bazaki ci abinci dani ba?" Dan murmushi Jalila tayi, wanda iyakacinsa lebenta "Ni na isa, Nana" "gashi nan makuwa nagani" Ummi ta kallesu tana murmushi "kema dakko spoon dinki, kizo muci" Haka kuwa akayi, suka zauna suna cin abincin tare Ummi tagayawa Abba, kwana daya zatayi, ta wuce, Maama ta shige daki ta kira Naana, ta hanata fiyowa, karshe ma ta aiketa tabar gidan, ta bar Ummi se Jalila da Halima, dakinsu Jalila taja Ummi, ta dinga mata magiya ta tafi da ita, amma Ummi tace mata baze yiwuba, Yanayin yadda taga Maama ta karbeta, tasan akwai matsala amma Jalila tace komai lafiya kalau suke zaune Haka Jalila sukai ta hira da Ummi wanda hakan ya rage mata bacin ran da take ciki , Rabin hirarsu da Ummi, Nasiha ce take mata akan hakuri da karbar kaddara a duk lokacin datazo mata, Da dare yayi ma Maama cewa tayi Nana ta kwana a dakinta, tabar musu can, dan bazata kwana a gurinsuba bata san me za a koyamata ba.   Washegari tunda safe Ummi tafara shirin tafiya, tun wayewar garin Jalila take kuka, ko karyawa takiyi, karfe goma na safe, Ummi tagama shirinta tsaf ta fito, Jalila janye da trolley din Ummi tana share hawaye, Nana kuma ta dakko karamin jakar Ummu, hakan yayi dai2  da fitowar Abba wanda shi zeje yasa Ummj a motar garinsu, Abba yace a kirawo Maama suyi sallama da Ummi, Maama ba dan tasoba ta fito, sedan kar Abba yayi mata fada, Abba ya kalli Jalila yace "Baby muje, asaka kayan a mota" Jalila tayi gaba ita da Nana, ya bisu a baya, suna zuwa harabar Gidan, suka tarar da Jawwad ya kunna motar ya bude kofofin, suna zuwa yaje ya karbi trolley din hannun Jalila yana kokarin bude boot   Ummi ta kalli Maama da take tayi mata kallon banza, ta danyi murmushi sannan tace "Zainab har yanzu ina ganin kiyayyata a idonki, bansan dalilin hakan ba, amma ina rokonki ga Jalila nan amana, kar kiyayyata ta shafeta, ki dubi Allah ki dubi maraicinta, in kikaci amana Allah yana kallonki, badan wasiyyar mahaifinta ba Zainab, babu abunda zesa in bar yata a gidanki, tunda nasan ba kya kaunarta, keda danginki, da da ita zan tafi, ko ina ne" Maama ta katseta ta hanyar cewa "kinga saurara, amanar yarki a hannun dan uwan mijinki take baniba, dan ba muhada dangin komai dake ba, ni ban hada jini da arna ba balle abani amanarsu in karba" Murmushi Ummi tayi me ciwo sannan tace"shikenan Zainab ki fadi abunda kikeso, kema kin haifa, bazan fasa fada ba Jalila amana ce, zan iya yafe duk abunda zakiyi min amma banda cin amanar gudan jinin Aliyu, wato Jalila " Ummi na zuwa nan a zancenta tayi waje tana share hawaye, tareda tausayin tilon Babyn ta. Harabar gidan ta fito, suka koma gefe, da Abba suna magana, Jalal ne ya shigo gidan, ya hangi Ummi yana ganinta ya karaso da sauri yana murmushi, yace " Ummi saukar yaushe"? "Abdul Jalal haka ka girma, Jalal ka yadani, ka manta dani" Ya dan girgiza kai "ummi wane ni in manta dake ni na isa, yanzu kikazo ne?" "A a tafiya zanyi, tun jiya nazo" Kallon Jawwad yayi, sannan ya kalli Ummi "Ummi Jawwad be gayamin ba danazo mun gais, yaushe rabon da naganki" Abba yace "Lallai Jawwad baka kyauta ba tunda baka gaya masa ba" Jawwad yace "Abba ba laifina bane jiya throughout ban ganshiba, ban san inda ya tafiba" "amma lambar wayata ma baka ganta ba itama ta tafi yawon" Jawwad yayi dariya "Allah yabaka hakuri" Jalila mamaki takeyi yadda ya ke girmama Umminta haka, yasan Ummi kenan, amma ranan datayi mata zancen waye JALAL tace mata bata saniba Ummi tace "Abdul Jalal ina Mummynka?" "tana nan Ummi, yanzu nan ta fita", daddy kuma baya gari," Ummi tace Allah sarki, dan Allah a gaishesu " zasuji Insha Allah Jmmi" Jalal ya kalli Abba yace "Abba ka bari, semu rakata" Abba yace masa "ai ba kano zata koma ba, tasha zasu kaita, zataje garinsu" "Ba komai Abba, bari mu kaita" "to shikenan yarona, karbi mukullin" Jalal yasa hannu ya karba, Seda Jalila ta zare ido, ko dai Abba besan irin tukin da Jalal yake ba, yabashi mukullin motarsa Abba suka gama maganar dazasuyi da Ummi, Jalila da Nana suka shiga bayan motar, sannan Ummi ta shiga, Jawwad kuma ya zauna a gaban mota, sekuma Jalal da zeyi tuki Suna tafe Jalila tana kuka, Nana, da Jawwad suna rarrashinta yayinda Ummi ta maida hankalinta kan JALAL sunata hirarsu, bawai dan batajin kukan Jalila ba sedai kar garin rarrashinta itama tayi kukan, Ummi tace "Jalal ya karatu fa?" Yace"Ummi kicigaba da yimin addu'a, very soon zakiji labari me dadi" "to Allah ya tabbatar da alkhairi, yabaku mataye nagari kuyi aure" Dariya Jalal yayi "Aure kuma Ummi" "Eh mana Jalal, aure ai shine cikat mutum" "ko ba hakaba Jawwad" "hakane Ummi" Jalal yai murmushi, tareda dan girgiza kai, Haka suka cigaba da tafiya, har suka je tasha, Jalal hira suke da Ummi, aka samawa Ummi mota, suka saimata ticket, Rirriketa Jalila tayi tana kuka, "Ummi dan Allah kidawo da wuri, karki tafi ki zauna Ummi" Ummi ta dan goge kwalla tana dan dukan bayan Jalila, alamun rarrashi, sannan ta kalli su Jawwad "ga sister dinku nan, asaka ido akanta, kuyi hakuri da halayenta, dan Allah," Nana tai saurin cewa "Ummi karki damu, Jalila bata da wani damuwa, lafiya kalau muke zaune" Jawwad ma yace "ummi karki damu shagwaba nsme kawai takeji, shiyasa take kuka, amma ba wani damuwa," murmushi Ummi tayi sannan ta dago Jalila tace "Baby na is ok, bazan dadeba zan dawo insha Allah, zamu dinga waya, Baby kiyi hakuri da rayuwa, sannan kizama me hakuri da kaddararki, kizama me yafiya da kauda kai, akan al amuran rayuwa, banda tsokana da neman magana duk abunda yasameki kiyi tawwakali ga Allah kinji baby" Gyada mata kai Jalila tayi "Yawwa Allah yayi muku albarka, ya hada kanku gaba daya" Jawwad yace "Insha Allah Ummi" Ummi ta kalli Jalal "Abdul Jalal ni zan tafi, Allah ya jishemu alkhairi, in ka koma makaranta, a ko bikin yazo kar a manta dani" Dariya yayi yace "Hajiya ummi, kidena batun auren nan fa, zan karbi lambarki gurin Jawwad mudinga gaisawa" "to shikenan ku koma haka nagode sosai," Ta dan rungume Jalila tai kissing dinta a goshi "kidena kuka, addu a zakiyimin" Daga haka Ummi ta shige motar Jikin Jalila a sanyaye, suka koma motarsu suka dau hanyar gida, Jawwad se bawa Jalila baki, yake kan tayi hakuri amma kaman yana zigata, ta kwanta akan cinyar Nana, se kuka take, Kukan Jalila ne yacikawa Jalal kunne, ya samu guri, yayi parking, sannan cikin tsawa  yace "dallah Malama ki rufewa mutane baki, se wani lallabaki ake kina cigaba da kukan, Wani abunne yasamu, Ummin dazaki dinga yiwa mutane kuka haka, in baki rufemin bakiba sena makeki wallahi" Yadda yayi maganar seda hantar cikin Jalila ta kada, saboda cikin tsawa yayi maganar, Jawwad yace wa Jalal "dan Allah kayi hakuri ka kyaleta " Bazan kyaleta dinba Wallahi ta cigaba damin kuka seta sauka, bana son shirme" Nana tace "Yaya Jalal dan Allah kayi hakuri, tadena, Jalila dan Allah kiyi shiru" Banza Jalila tayi musu, amma ta rage sautin kukan, da kyar Jawwad ya lallabashi, yaja motar suka tafi, Bayan sun koma gida Jalila kaman wata marainiya, abun duniya duk ya dameta. Halima ta lura da damuwar da Jalila take ciki, dan haka  Halima taita rarrashinta "sayyada Jalila dan Allah ki saki ranki, gidan ba dadi in bakya walwala, Ummi zata dawo fa" Jalila ta danyi yake "leemart baki san yanake Jiba, wallahi zuciyata ba dadi" "Nasani Jalila, amma kiyi hakuri, damuwa ba shine mafita ba" "hakane nagode" "yawwa kisaki ranki" Jalila taita kiran Ummi tana tambayarta ko ta karasa, Ummi tace mata in taje zata kirata, Hakanan Jalila taji hankalinta yaki kwanciya, bayan la'asar ta kuma kiran wayar Ummi amma taki shiga, da farko tayi tunanin ko network ne amma wasa2 har karfe tara na dare wayar Ummi a kashe, hankalinta ya tashi matuka, Nana tace "dan Allah Jalila ki nutsu ki kwantar da hankalinki, maybe bata da cajine" "Nana cewa kike in kwantar da hankalina, ta yaya? Dazu fa muka gama waya amma ace yanzu wayar bata shiga" "To kika sani ko network ne, kinsan hanyar, akwai dazuka, dan haka ba lallai asamu Network ba" da haka hankalin Jalila ya dan kwanta, Amma har gurin karfe sha biyun dare, Jalila takasa hakuri trying lambar Ummi ta kumayi, amma still switch off Jifa Jalila tayi da wayar ta fashe da kuka Share please More Comments More typing............................... Aimin afuwa rashin samun posting da wuri, ina busy ne sosai Amma ina godiya da addu"oinku 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/13, 10:22 PM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  44 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode. Ina me neman afuwarku masoyana, kwana biyu banyi typing ba wayata ta dan samu matsalane Sannan ina kuma neman afuwarku bazan samu dinga yi muku posting kullum ba saboda zan koma lectures online, Nagode da kulawa        _My first novel_ Sosai Jalila take kuka, tareda surutai, "Haba Ummi dan Allah ki daga wayata mana, hankalina ya tashi" Sam bacci ya gagari Jalila, tayi trying lambar Ummi bata san adadi ba amma a kashe, Nana kam tuni tayi bacci, yadda Jalila taga rana haka taga dare, bacci ko barawo be dauketa ba, ta kagu gari ya waye, Da asuba Nana tashi tayi taga Jalila akan dadduma, ta sunkuyar da kai, bata san Jalila batayi bacci ba ta dauka dai ta tashi da wurine, Kamar kullum Nana tayi sallar asuba ta koma baccinta, mikewa Jalila tayi ta fita daga dakinsu idonta ya kumbura, yayi jawur, ga rashin bacci ga kuma kuka da tasha, kai tsaye kofar part din Abba ta nufa, a hankali tafara knocking, tayi ya kai sau hudu, sannan taga an bude, Maama ce ta bude, ta kalleta a wulakance "Ke! Meye haka zakizo kinamana knocking da safiyar nan" Jiki a sanyaye Jalila tace "Kiyi hakuri gurin Abba nazo" "ikon Allah yaushe kika zama matar gidan nan dazakizo gurinsa da sassafe haka" "A a Maama dama wayar Ummi ne tun jiya da yamma ya dena shiga shine... " Shine Me? Fitowa zeyi ya tafi nemo miki ita, Allah ka dai yasan gidan uban data tafi, dalla matsa kibani guri" Maama ta maida kofa ta rufe, silalewa Jalila tayi a gurin, tacigaba da kuka kuka "Kingani ko Ummi dakin tafi dani da koma mene ze faru ina tareda ke" Se karfe tara na safe Abba ya fito, yaga Jalila a kofar part dinsa a zaune, tana kuka, "Subhanallah Jalila me yasameki haka,?" Kuka takuma fashewa dashi "Abba, Ummi tun jiya da yamma, lambarta ta dena shiga," Tabbas dan shima ya kirata amma taki shiga, cikin sigar lallashi yace "Kiyi hakuri kinji diyata, yanzu kije kiyi breakfast, zan cigaba da trying lambarta, in be shiga ba zanje tashar motar da kaina inji me ake ciki" Gyada masa kai tayi ta mike ta koma palour ta zauna tayi shiru, se hawaye dayake bin fuskarta Wasa2 har azahar babu labarin lambar Ummi, taki shiga, Jalila fa tafara fita hayyacinta, babu cin, Abinci takasa nutsuwa, Jawwad da Abba suka tafi har tashar da akasaka Ummi a mota, amma aka tabbatar musu da cewa motar taje har garin sun juyo, sedai sunyi tsaye2 sun sauke fasinjojii, amma lafiya sukaje suka dawo, Se dare su Abba suka dawo, amma ba wani labarin samun Ummi, Wunin ranar babu batun nutsuwa a tareda Jalila, kuka kam idon harya kafe, babu hawaye se ajiyar zuciya kawai da take yi, Maama ko kallon Jalila ba tayi ba balle wani magana me dadi ta fito daga bakinta, Nana da Halima ne kawai suke rarrashinta, Su Abba suna dawowa Jalila ta mike, tana tambayarsu, ya akayi? " Abba yakama hannunta ya zaunar da ita, sannan yace " ki kwantar da hankalinki, kinji, munje tashar motar, sunce mana motocinsu sunje lafiya, sun sauke fasinjojin su lafiya sun dawo, dan haka muna da tabbacin Ummi ta sauka lafiya, watakila wayarta ce tasamu matsala amma sunje lafiya, zuwa gobe Insha Allah nida Jawwad zamu kuma komawa, in takama mu bibiya har can garin nasu zamuje, amma muna fatan komai lafiya " hankalin Jalila ya dan kwanta kadan, Abba ya mike, ya koma part dinsa, Jawwad yasa halima ta zubo Abinci ta hado da tea, ya zauna yasaka Jalila a gaba, ya takura mata, amma ta tsakuri kadan tace ta koshi, karbar Abincin yayi, ya dan hade rai, sannan yafara bata a baki, karba take tana ya tsuna fuska, "Yanaga kina bata raine, kiyi hakuri kici Abincin mana" ta yamutsa fuska, muryarta kasa2 tace "kaina fa ciwo yake" "to yi hakuri, ci Abincin, se in kawomiki magani" ta gyada kai Yana cikin bata Abincin ne, Maama ta fito, wani mugun kallo tai musu "Kai Jawwad meye haka, ban isa in gaya maka kaji bako?, meye nawani zama kana bata Abinci, tashi kabar nan malam, tashi kafita sha3 kawai, jiki a sanyaye ya mike yana waiwayen Jalila, yayinda ita kuma ta sunkuyar da kai, Maama ta kalli Jalila sannan tace" Mayya kawai, Mara zuciya" dagowa Jalila tayi ta kalli Maama, ta mike ta bar mata palourn, takoma dakinsu, Jawwad ya koma dakinsa abun duniya ya dameshi, yayi wanka yayi sallar isha'i ya dawo ya zauna a palour, yayi shiru yana tunani, Jalal ne ya shigo, yazo ya tarar da shi a palour ya samu guri, ya zauna ya kalleshi "Ina kashigane nazo baka nan, ina ka tafine?" Ajiyar zuciya Jawwad yayi sannan yace "Akwai matsalane Jalal" "matsalar mene?" "jiya bayan mun kai Ummi tashar mota, tun bayan la asar har yanzu danake maka magana ankasa samunta a waya, lambobinta basa shiga, har tashar motar mukaje nida Abba, amma sun tabbatar mana motocinsu sun isa lafiya sun dawo," "To ya akayi haka tafaru?" Jawwad yace "nima ban saniba Jalal, gashi Jalila ta daga hankalinta fiye da yadda kake tunani, ko abinci taki ci, yanzu na tursasata ina bata, Maama ta koreni, kuma hada gayamata munanan magana, Jalal narasa me zanyi, a halin Yanzu Jalila na bukatar me kwantar mata da hankali, ta damu kwarai" Ajiyar zuciya Jalal yayi sannan yace "to yanzu wani mataki aka dauka amma da mamaki ace wayarta bata shiga kuma by now, dai nasan ta isa, kwara state, kuma nasan bazata kasa kiran wayaba" "Koni jiyan da azahar munyi waya da ita, Gobe in Allah ya kaimu zamu koma tashar, in takama mutafi can garin nasu se muje, ina tausayin Jalila," "Allah yasa komai lafiya" Jawwad yace "Ameen" Jalal ya dafa kafadar Jawwad "Ka kwantar da hankalinka, karkasa damuwa a ranka, komai zezo da sauki, bana son ka damu" Dan murmushi Jawwad yayi sannan yace "to naji" Daga haka Jalal ya tashi ya tafi gida, yunwa duk ta ishi Jalal dan ba wani Abincin kirki a cikinsa, saboda Jawwad baya nan, gashi baya son shiga cikin gidansu, dan yasan inya shiga kafin ya fito se an bata masa rai, har ya kwanta, ya tashi ya nufi cikin gida bakowa a palourn, dan haka ya wuce kitchen zuwa yayi yaita bude2, ji yayi kaman da mutum a tsaye a bayansa yana waigowa yaga Ilham a tsaye, da wata yar riga a jikinta, iya gwiwarta, dauke kansa yayi, yacigaba da abunda yake, a hankali ta tako ta karaso cikin kitchen din, ta dan kalleshi "My star, me kake nema ne?" Be amsamata ba balle ya kalleta, "Ko kanajin yunwa ne?" shiru yayi mata, ya nufi fridge, bayansa ta kuma bi "haba star, ka kalleni mana, ka amsamin" A fusace ya juyo "Ohhh God, haba wai meye hakane? Kinyimin magana nayi miki shiru, base ki kyaleniba, kalleki kalli Jikinki, ya dace kizo inda nake a haka, get out from my side" Ita a tunaninta shekaranjiya da ya shigar mata fada ko yafara sakkowane, amma yanzu setaga abun bahakaba, shi har yawani san abunda ya dace, ko be daceba, bayan giya yake sha, ga sauran lefuka, amma ta maze ta matso inda yake "Yaya Jalal kenan, nasan yunwa kakeji, kawo in dafa maka wani abun kaci" "No need" shine abunda yace mata kawai, kuma matsawa tayi daf dashi, yana juyowa suka hade, zuciyarsa ta buga da karfi, Ta dan tsura masa ido, "Meyasa kullum baka da burin daya wuce azabtar da zuciyata ne, kasan ko yadda nakeji? Please Yaya na, love me too" Shiru yayi mata yasa hannunsa biyu, ya tureta gefe, yakama hanyar waje, sauri takumayi tasha gabansa, tana kallonsa, Ajiyar zuciya yayi sannan yace "bana son yi miki wulakanci, u are pushing me to the wall, meye haka ne? Meyasa bakida kamun kai Ilham, a hakan kikeso in aureki,? Kalli yadda kikemin ba kya tunanin haramcin hakan, kina tunanin ko na aureki zan yadda dake" Ta dan nisa "Yaya Jalal kome nayi kaine sila, meye laifina dan Nace inasonka, da soyayyarka na budi ido why Yaya Jalal? Msyasa baka sona" Hade rai yakuma yi "Ana so dolene? Tun farko nagaya miki, niba na ra ayinki, kije kisamu wani, ni bani da niyyar aure yanzu, ki hakura mana, nagaya miki gaskiya bazan aureki ba, " "Yaya Jalal agaban idona kake gayamin bazaka aureniba, to bari ingaya maka, kayiwa duk wadda zaka aura Albishir din, ta tari bala'in dabata san karshensa ba, wallahi kowa ka aura, sena hana muku farinciki baka isa ka auri wata baniba indai ina raye a doron kasa, kuma ko bana raye fatalwata seta hanaku sukuni," Murmushi yayi kawai yai waje, ya fasa daukar abunda yayi niyya, a ransa yace" lallai yarinyar nan bata da hankali" Ilham takoma dakin tana jujjuya maganganun Jalal "Wallahi karya kakeyi Jalal, kozan tafi tsirara se nacikawa Mamina burinta, zakaga tsiya, senayiwa Jalila abunda se ta mutu da bakinciki, dan na lura itake kara, batamin aiki, da raina wallahi bazakayi aure ba da wata mace inba niba, if not inyi abinda zan karya asirin kowa ya huta, haka Ilham taita surutai marasa kan gado, Shikam Jalal, Ya fita harabar gidan ya tsaya, yana nazari, ya Kalli agogon hannunsa daga baya ya dau motarsa ya fita, Club ya tafi abunsa yaje aka cashe aka sha giya, yai manksa abunsa, yana tangadi  se kawoshi gida akayi.   Dare yaraba, Jalila se nafila takeyi, tana addu a Allah ya bayyana mata Umminta yasa tana lafiya, se gefin asuba bacci yasaceta akan daddumar datayi salla, a cikin baccinnata maimakon tayi mafarkin Ummi tunda itace a ranta, setayi mugun mafarkin data saba yi akan Jalal, a firgice ta farka, tana ambatar sunan Allah gaban ta na faduwa, Nana ta taso tazo inda take, ta dafata "Jalila lafiya kuwa?" rirrike Nana tayi ta fashe da kuka "is ok dear, yi hakuri, Insha Allah komai zezo da sauki, a yau za a ga Ummi Insha Allah" gyadawa Nana kai kawai tayi, seda ta dan samu, nutsuwa sannan ta mike tayo alwala tazo ta tayar da sallar asuba, Da sassafe karfe shida Jalal ya tashi yai wanka yai salla, ya dau motarsa ya fita ba tareda wani yasan inda ze tafiba, dan ko Jawwad be gaya masaba. Karfe takwas na safe Abba da Jawwad suka hadu a palour zasu kuma fita, Maama ta Kalli Abba "wai Dan Allah yanzu fita zaku kumayi, ko karya bakuyiba, nasan wallahi wani gurin tai tafiyarta amma duk ka daga hankalinka" Abba ya kalleta "kina tunanin, zata iya tafiya wani gurin batareda sanin yarta ba, bari in tunamiki abunda kika manta, Maryam da Jalila amanar dan uwana Aliyu ce dasu Inna, idan naci wannan amanar Allah baze barniba, dolena innemo abunda yasamu Maryam dan na tabbatar, da taje lafiya, da komai lafiya nasan, komae ake ciki, zata gayamin" "kai kake ganin hakan amma a gurin su aikata irin wannan ai ba wani abun damuwa bane, ai abun kunyane ta koma garinsu da yarinya bayan basu san tayi aureba, kodayake su ina suka san wata kunya" "Ya isheki haka Zainab, Wallahi zan bata miki rai fiye da yadda kike tunani, akan cin zarafin matar Dan uwana, babu bawan da ya isa ya kuskurewa kaddararsa," Jawwad ganin sa' insa na neman barkewa tsakanin iyayennasa, se ya kewaye ya tafi dakinsu Nana, ya tarar da Jalila ta dora kanta akan cinyar Nana, tana zubda hawaye, yayinda Nana take bata hakuri, karasowa yayi ya tsuguna "Baby baki dena kukan bako? Dagowa tayi ta kalleshi, sannan ta sunkuyar da kai, kiyi hakuri yanzuma fita zamu kumayi da Abba Insha Allah zamu gano inda take, ki dena kukan nan kinji, ze iya kawo miki matsala" Ta dan Jinjina masa kai, ya Kalli Nana yace "Nana dan Allah ki tabbatar taci Abinci" "to Yaya Insha Allah" daga haka ya mike yafita cike da tausayin Jalila, Yana fitowa palour yaga ba kowa dan haka ya fita harabar gidan ya tarar da Abba a zaune a cikin motar yana Jiransa, Jawwad ya shiga motar ya kunna suka fita, Har la'asar babu wani kyakykyawan labari, dasu Jawwad suka samu game da Ummi, kuma har yanzu wayarta bata shiga, haka suka gaji suka dawo gida, koda Jalila taga sun dawo, da sauri ta tashi, ta fita domin sanin me ake ciki, Abba  yasa aka kiramasa Jalila, Jalila tazo, ta durkusa a gabansa Koda taji Abba yafara dayi mata nasiha ta karaya ta kuma fashewa da kuka "Shikenan na rasa Ummina, Ummi dama haka zakiyimin, kikayimin wayo kika tafi kika barni, yanzu ba Abee ba Ummi" Jawwad yace "haba Jalila duk bagamuba, kuma Ummi fa bacewa akayi ta mutuba tana nan da ranta, kuma mun bada cigiyarta gurin" 'yansanda, insha Allah za a sameta, kidena kuka" Daga Abban har Jawwad din Jinsu kawai take, dan bata san me suke fada ba, hankalinta sam baya kansu, dan wani abune yazo saitin zuciyarta ya tsaya, shibe fitaba, shi be komaba, har magariba, Jalila kaman wata mara hankali, batun Abinci dama babu shi, dan ko ruwa bata zubawa cikinta ba danba Yadda Nana batayi da itaba amma taki cin komai, banda aikin kuka ba abunda take, ga gefe cikinta da ya kulle saboda rashin Abinci, Bayan sallar Isha'i kaman me tabun hankali ta mike ta nufi part din Abba, ta tarar dashi da Jawwad da Maama a palourn sa, tsayawa tayi tana tunanin to intaje mezatace masa, Wayar Abba aka kira, yasa hannu yadaga, yayi sallama sannan yadanyi shiru "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya furta" Jawwad ya kalleshi a kidime "Abba lafiya kuwa?" "Jawwad, wai Ummin Jalila wai motace ta bigeta kafin sukarasa garinsu, ta sauka yin salla, kuma wanda ya bigetan yasata a mota ya tafi da ita" Da jin haka Jalila ta kwalla kara, sekuma ta kame a tsaye, gaba daya suka juyo suka kalli inda take tsaye, idonta a kafe a kansu, mikewa Jawwad yayi da sauri ya nufi Inda take amma ko motsawa batayi ba, kuma ko kyafta idon batayiba, Yana tabata ta tafi zata fadi, da sauri Jawwad ya rikota, Abba ya taso da hanzari "lafiya kuwa, meyasameta?" Idonta a bude kar, amma bata mosti bata numfashi "Innalillahi wa inna ilaihi raji un Abba Jalila ta mutu" Maama na jin haka ta taso da sauri "kamarya ta mutu?" Share please More Comments More typing........................................ Love u all my fans ina godiya, da adduo'inku, da kaunarku, Allah yabar kauna 🌹🌹🌹❤️❤️❤️❤️ Team Jalila su ummu Hanif kuzo jana'iza 😂😂😂😂💃💃💃 queen ta wula 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/13, 10:27 PM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  45 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680 Ina godiya matuka Allah yabar kauna        _My first novel_ Abba ne yasa hannu ya janye Jalila daga hannun Jawwad, yana jijjigata amma idonta a kakkafe, hannu Abba yasa ya rufe idon Jalila babu alamar tana numfashi, Jawwad ya kalli Abba "Abba wai mekake nufine, ba dai ta mutu ba," shiru Abba yayi bece komai ba, Jawwad yakuma cewa "Abba kayi magana mana," Nana ce ta shigo palourn Abba, "lafiya kuwa Maama inajin hayaniya tundaga palour" hankalinta ya kai kan Jalila dake kwance a jikin Abba, Jawwad kuma, kaman baya hayyacinsa, da sauri takarasa inda suke "Abba meyafarune" Maama ta kalleta "Ke meye haka ki nutsu mana, mutuwa tayi" zarewa Maama ido Nana tayi, "wallahi karyane" ta cacimo Jalila daga jikin Abba "Yaya Jawwad dagaske Jalila ta mutu, meyasameta, wallahi bata mutuba Abba kajifa ta janyo hannun Abba ta dora a wuyan Jalila, jiyayi alamun jijiyar gurin tana motsawa a hankali, ya kalli Jawwad sannan yace " tashi maza ka fito da mota, mu tafi Asibiti, da sauri Jawwad ya fita, mintuna kadan ya dawo, ya dauki Jalila kamar gawa yayi waje da ita, kafar Nana bako takalmi tabi bayan Jawwad da gudu, Halima da ba tasan me akeba ganin an wuce da Jalila rai a hannun Allah yasa ta firgice, ga Abba ya fito da sauri shida Maama, Halima ta nufi Maama tana fadin "Na shiga uku meyasami, Jalila ne, Hajiya dan Allah meyasameta?" "Ke dallah rabu dani, ina ruwanki dame yasameta zakiyi mata maganine, Abba yace" Halima kwantar da hankalinki, suma tayine batajin dadi, amma asibiti zamuje" Halima a rikice tace "Allah yabata lafiya, dan Allah ku tafi dani Asibitin" Abba yace "karki damu Halima, kiyi mata Addu a zataji sauki" daga haka yayi waje, itakuwa Maama tasamu guri tai zamanta a palour, Asibitin doctor salis suka nufa, ba karamin gudu Jawwad yakeba, se kace ze tashi sama, Jalila na kwance akan cinyar Nana, ga sanyin AC amma tana nan yadda take ba wani canji, ko motsi batayi, suna zuwa Asibiti Jawwad ya fita da sauri ya shiga cikin Asibitin ba a dadeba segashi ya taho da doctor salis, Nurses sun turo gado, Abba na tsaye a jikin motar, Jawwad ya karaso ya bude motar ya dakko Jalila, ba wanda zece ba gawa bace, aka dorata akan gadon aka turata, zuwa cikin Asibitin, su Abba suka bi bayansu, suna zuwa kofar emergency suka tsaya, aka shiga da Jalila, su Abba da Nana suka dinga sintiri a kofar emergency tunda aka shiga da Jalila ba wanda ya fito balle su tambayeshi me ake ciki, Nana se kuka take, Abba ya kalleta "Nana kiyi shiru kinji muyi mata addu a zata samu lafiya Insha Allah" Jawwad kam yarasa meyake masa dadi, sam besan mezeyi yaji dadiba, Maama ce ta kira Jawwad "ya akayine naga har yanzu baku dawoba ta mutune"? " A a Maama bamu saniba, sun shiga da ita emergency tunda mukaje ba wanda yace mana komai" Daga haka ta kashe wayarta, Halima se addu oi take, tana yi wa Jalila adduar samun sauki, sun shafe awanni a gurin nan kafin doctor salis ya fito, yana share Gumi gaba daya suka nufi inda yake Abba cikin zakuwa yace "Ya ake ciki" ya kalli Abba sannan ya kalli Jawwad Jawwad yace "Dan Allah kayi magana mana" Doctor salis ya nisa sannan yace "ku kwantar da hankalinku, Alhamdilillah mun samu nasarar ceto rayuwarta cikin ikon Allah, Blood pressure dinta yayi high fiye da tunani, wanda yasa tasamu stroke, yanzu Alhamdilillah tana iya numfashi, kuma bugun zuciyarta yazama normal, sedai har yanzu bata farfadoba, zamu ajiyeta a ICU tukuna muga abunda hali zeyi, Dan murmurshi Nana tayi tareda fadin "Alhamdilillah, Allah yabaki lafiya Jalila" Doctor salis yace "Abba kubiyoni office akwai magunguna dazan rubuta" Abba yace to shikenan muje, suka bi doctor salis office dinsa, akace Nana ta tsaya a waje, Abba da Jawwad suka shiga, doctor salis ya kalli Abba "Muna bukatar Jini koda leda dayane zuwa gobe insha Allah , zamu kara mata, mun gwada PCV dinta shima yayi kasa, kaman ta dade tana rashin lafiya, ya akai condition dinta ya zama worst haka lokaci daya,? Jawwad ya gaya masa komai, yayi rubuce2 yabasu magungunan da ake bukata su siyo, Jawwad yace "doctor zamu samu ganinta kuwa" Doctor salis yadan girgiza kai "No bazaku iya ganinta yauba gaskiya, zaku iya tafiya, in yaso gobe in Allah ya kaimu seku dawo, daga nan a duba Jinin da za asamata," Abba yace "Kana ganin ba komai in an barta anan" "Eh Abba ba wani matsala, za a kula da ita Insha Allah, ko wani ya zaunama bata hayyacinta bacci take, ba lallai ta farfado a yauba" Sukayi sallama da doctor, sukaje suka biya bill dinsu, daga nan suka taho gida, a palour suka tarar da Halima, ta sha kuka, tana ganinsu tafara tambayar Abba, "Ya jikin nata" "Ki kwantar da hankalinki ta farfado, tana baccine, an kwantar da ita" "Allah yabata lafiya" Abba ya amsa da Ameen, dama Nana bata tsaya ba dakinsu ta wuce, jin dakin tayi babu dadi, ta kalli gurin kwanciyar Jalila, da yanzu ta kwanta kokuma tana salla, Hawaye yazubowa Nana, "Allah yabaki lafiya Yar uwa"daga nan taje tayo alwala, tai sallar Isha'i, ko kayan jikinta bata canzaba ta haye kan gado tayi shiru tana tunani, har bacci ya dauketa, Koda Abba ya shiga part dinsa Maama tayi dai2 akan gado tana baccinta, ko a jikinta, wanda da yartace da bataga tayin bacciba, shigewa yayi yai wanka, yafito ya dakko sallayarsa ya dawo palour dukda ya gaji matuka yau, wuni sukayi yawon neman bayanin inda zasu samu Ummi, ga wannan abu daya samu Jalila, Bangaren Jawwad ya dakko wayarsa ya kira Jalal amma bata shigaba, dan haka ya tashi yatafi gidansu Jalal, da mamakin Jawwad, Jalala baya nan, yasan baze wuce yana mashaya ba, dan haka ya hakura, ya koma gida ya rama sallolinsa ya kwanta, se dai bacci ya kauracewa idonsa, se tunani Doctor salis ya koma inda aka kwantar da Jalila, ya dan tsura mata ido, ta rame sosai akan lokacin daya fara ganinta, idonta a rufe ga oxygen da aka samata, a hankali numfashinta yake sauka, sedai bugun zuciyarta ne har yanzu be daidaita ba, kallonta ya cigaba dayi, dukda ta rame amma setayi kyau, goshinta kwance da gashi, ga girarta itama a cike take da bakin gashi, doctor salis y shagala sosai da kallonta, tareda tunani2 daban2 akan Jalila, yaji an taba shi waigowa yayi, yaga Abokin aikinsane, wanda zeyi night, suka gaisa "Salis har yanzu baka tafi ba? ai nazata katafi tun dazu" "A a doctor ban tafi ba," "Dare yayi sosai fa, yakamata ace ka tafi" "eh anan zan kwana" doctor Khalid ya kalleshi "naga kai kayi dutyn yamma" "Eh, ina da patient ta mussaman" Salis ya nunamasa Jalila Gyada kai doctor Khalid yayi, yai gaba abunsa   Da sassafe Nana ta tashi ta kintsa, Halima ta dama kunun gyada dan Jalila na matukar sonsa, har Abba ya tashi ya shirya Maama bacci takeyi, suka kintsa suka tafi Asibiti, Jawwad ya kira lambar Jalal har ya gaji amma Jalal be daga ba, yaso yaje ya kuma dubawa ko yadawo, amma da wuri suka fito, dan gari da sauran duhu, dan haka be samu damar komawa yaduba ko Jalal ya dawoba, Suna zuwa asibiti, Jawwad ya nemo doctor salis, doctor salis yace su kara hakuri har yanzu bata farfado ba, amma za a gwada Jinin Abba kona Jawwad wanda yayi zasu dauka, domin sakawa Jalila, aka duba jinin Jalila da nasu, amma babu wanda yazo daya dana Jalila, cikin damuwa Jawwad yace "to yanzu meye abunyi?" Doctor Salis yace " A yanzj gaskiya mu   a lap dinmu bamu da irin Jinin ta, sedai inmaka kwatancen Asibiti wani abokina kaje can, in akwai kace nina turoka sesu baka," Abba yace "to hakan yayi kyau," doctor salis ya dakko wani takadda yayi rubutu, yabawa Jawwad, Abba yace " salis, baze yiwu muganta ba ne?" Doctor yace "Abba ka kara hakuri tana, karkashin kulawa ta mussaman bazaka samu ganinta ba amma insha Allah zuwa anjima in akasamata Jinin zamu fito da ita" Abba yace "to shikenan, Jawwad muje ka ajiyeni, zan yi wani abunne, kai seka wuce ka karbo jinin, insha Allah anjima kadan zan dawo" Suka tashi suka fito, Jawwad yace Nana tazo su tafi tare ba yanzu za a fito da Jalila ba, Maama ta tashi, ta duba bataga Abba ba, taji gidan tsit, ta fito palour taga halima tana aiki, "Ke halima Abban Jawwad ya fitane" Halima ta dan risina "Eh hajiya sun fita gaba dayansu, sun tafi asibiti" Wani dogon tsaki Maama tayi, ta koma dakinta Halima tabi bayanta da kallon mamaki, tacigaba da aikinta, Karfe tara Jalal yai parking motarsa a kofar gidansu Jawwad ko daga ina yake oho, da sauri ya nufi part din Jawwad, amma yaje ya tarar Jawwad baya nan, gashi kuma wayarsa ba caji balle ya kirashi, yana fitowa yaga halima tana gyaran harabar gidan "ina Jawwad ya tafi"? ya tambayeta, cikin isa "Suna Asibiti an kwantar da Jalila" Kallonta yayi sannan yace "me yasameta" "Nima bansaniba amma a asibiti ta kwana" Daga haka yafita waje ya hau motarsa, ya nufi asibitin, dan yasan asibitin dasu Jawwad ke zuwa, yana zuwa ya tafi office din doctor salis, Jalal yayi sa a, doctor salis yana nan be tafiba, Ya mika masa hannu suka gaisa, Jalal ya kalli doctor salis "Wani patient su Jawwad suka kawo?" "haba kacemin baka saniba? Kanwarku ce fa, wadda Jawwad ya hanani ce Baby" "me yasameta?" Jalal ya kuma tambayar sa Doctor salis ya gyara zama, ya zayyanewa Jalal rashin lafiyar ta ta, Jalal yace "Yanzu ina Jawwad din yake"? "eh sun tafi neman jinin da za a saka mata, daana Abba dana Jawwad duk beyiba, nima nawa baze mataba dana wa zansaka mata," Jalal ya kalleshi ya dan tabe baki, sannan yace "Meye blood group dinta? " "Meyasa kake tambaya" Hade rai Jalal yayi, "Meye kuma na tambayata, kaima kasani patient din Jawwad nawane" Doctor salis yace "Allah yabaka hakuri, O+ ne" Jalal yace "irin nawane, a dibi nawa akai lap, inba matsala a saka mata" doctor salis yace "to shikenan muje lap din" Sukaje aka duba, jinin Jalal, irin natane, kuma anyi gwaje2 amma jininsa lafiya kalau, Kafin a dibi Jinin ya kalli salis yace "Wannan sirrine tsakanina da kai, ko Jawwad bana son yasan nina bada jinin, dukda nayine saboda Allah, kuma saboda Jawwad, amma bana son yasani, kace masa kawai wanine yazo yabada jininsa sadaka" "To shikenan, bazan gaya masa ba Insha Allah, yanzu ka zauna se su diba" Jalal ya zauna aka dibi jininsa, suna gamawa ya mike, aikuwa jiri ya debeshi, yakusa faduwa, lap attendants dinne suka rirrike shi, aka maidashi ya zauna wani ya tambayeshi "Kaci Abinci kuwa?" Jalal ya girgiza kai, dan rabonsa da Abinci tun jiya da safe, youghurt akasamo aka bashi ya dan yasha, ya dan huta sannan ya mike, shi yanzu so yake ya tafi, bayason Jawwad yazo ya tarar dashi anan, Doctor salis se sannu yake jerawa Jalal, Jalal ya kalleshi "Muje ka kaini inganta" Doctor salis yace "A a Jalal tana karkashin kulawa ta musamman, baze yuwu ka gantaba" "kamar yaya, ganinta zanyi nace ba wani abuba" Jalal ya fada a tsawace, ba shiri salis yayi masa Jagora zuwa inda Jalila take, Jalal ya dan tsorata da ganinta, ta rame sosai, ga oxygen a hancinta, gefe kuma ga drip, a hankali numfashinta yake fita, dan girgiza kai Jalal yayi, yai waje dan ko sallama beyiwa Salis ba yayi waje abunsa, motarsa ya nufa ya hau ya tafi gida, Jawwad suka dawo Asibiti shida Nana, sun samo Jinin amma doctor yasanar dasu an samu Jinin, wani yabada nasa sadaka, kuma yayi dai2 dana Jalila an samata, Cikin damuwa Nana tace "wai har yanzu bata tashiba?" Doctor Salis yace, "kiyi hakuri zata tashi ne, ana samata jininne, Insha Allah, zuwa magariba zaku iya ganinta" Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace "to shikenan, magungunan ban samosu duka ba, sedai in nafita inkuma dubawa" Doctor yace ba matsala, daga nan su Nana suka tafi gida, Jalal kam kwanciya yayi, ya kama bacci, dan ya gaji matuka, dukda yunwar da yakeji, gajiya ta hanashi neman Abinci, baccinsa yake sosai, Jawwad ya shigo yaje part dinsa ya tarar Jalal na bacci, se yazata ko giyar ya sha, ya nemi guri a dakin Jalal yayi sallar azahar. Nana koda ta koma gida, batabi takan Maama ba ta shige tayi wanka tai sallar azahar, sannan ta nufi kitchen, ta dakko Abinci, tana zuwa palour ta tarar da Maama zata fita unguwa, Nana ta kalleta "Maama fita zakiyine?" "Eh zanje kasuwane zan karbo kaya," "Adawo lafiya" Daga nan Maama bata kuma cewa komai ba balle ta tambayi yame jiki, ita kanta Nana abun setaji ba dadi, taga Sam Maama bata kyauta ba, haka ta wuce ta zauna ta fara cin Abincinta a palour, Halima ta fito daga dakinta tace "Nana ya jikin Jalila kuwa" Nana tace mata da sauki, daga nan tacigaba da abunda take. Jawwad yana nan yana zaune, har Jalal ya tashi daga bacci, becemasa komaiba shima be kulashiba, ya shiga toilet yai wanka, sannan ya zo ya zauna ya kalli Jawwad "ya akayine ina ka tafi, da sassafe?" Jawwad yace "kai zan tambaya ina ka tafi, tun jiya ban ganka ba, wayarka kuma bata shiga" Jalal ya gyara zama "mmmm to na danje wani gurine,?" "wani gurine? , bashi da suna" "Eh bashi da shi" Jalal ya bashi amsa, Jawwad yace "Shikenan" Jalal yace "Kai yunwa nakeji, zomuje inci Abinci, ban karyaba, ga rana tayi banci abincin rana ba, nasan gidanku an gama Abinci" Jawwad ya kelleshi "Can inda kaje basu baka abincin ba"? "Eh basu banba, dan Allah ka tashi inajin yunwa sosai fa" "Me dafawar an kwantar da ita a asibiti" "Wa kenan?" Jalal ya tambayeshi kaman besan meyafaruba "Baby mana an kwantar da ita a asibiti, a can ta kwana" "Allah ya sawwake, ya labarin Ummi fa?" Jawwad yai ajiyar zuciya, "shine dalilin dayasa ta kwanta a asibiti, Abba aka kira, aka gaya masa wanine ya bige Ummi, kuna ya dauketa ya tafi da ita, tunda taji haka ta fadi, mu mundauka ma ta mutu a jiyan nan" Jalal ya gyara zama, ya dakko sigarinsa ya kunna, ya busa hayakin sannan yace "waye ya kira Abban yagaya masa?" "nima bansaniba ina tunanin, ko daga tashane da yabada lambarsa yace in ansamu bayani a kirashi" Jalal yace "Hmmm" yacigaba da shan sigarinsa, Jawwad ya kalleshi "anjima kadan zan koma semuje tare ka ganta," "inga wa?" "ka duba Jalila mana," "da kyar ne inje, ai nace Allah ya sawwake" "haka zakace?" Jawwad ya tambayeshi "yeah" yafada tareda busa hayakinsa sama Jawwad yaji haushi, dan Jalal ko a jikinsa, ya mike ya fice ya barwa Jalal dakin, yana fita Jalal yai murmushi Jawwad kenan dan uwana na kaina, wani lokacin akwaika da rashin hakuri Jawwad yakoma gida, yasamu abinci yaci, ya tambayi Nana wai ina Maama, ta gaya masa ai ta fita kasuwa, abun yabatawa Jawwad rai amma yai shiru bece komai ba. Seda akayi sallar magariba sannan Maama ta dawo, lokacin Abba ma yadawo, yakuma bibiyar report din daya kai gurin yansanda, ko ansamu wani labari akan wanda ya bige Ummi, amma wunin ranar yagama yawonsa ba wani labari, Maama salla tayi kawai, taje ta dauki Abincin Abba ta kaimasa part dinsa, taje ta ajiye masa, amma bece mata komai ba ta kalleshi "Abban Jawwad ka dawo bana nan ko? Wallahi fita ce ta kamani" A fusace Abba ya dago "dole fita ta kamaki Zainab, tunda ba yarki ce a kwance a Asibiti ba, yarinyar nan tun jiya an kwantar da ita a Asibiti, babu tabbacin zata farka daga suman da tayi, amma koda wasa baki taka kafa inda take ba, ina sane da duk abunda kikeyi, ni bazanci amana ba, dan uwana ya nunamin soyayya, bazan iya wulakanta masa yaba, amma kema kin haifa, Wallhi zainab akan Jalila zan iya rabuwa da kowaye, bakeba har yayan cikina, ita nake kallo inji dadi, Aliyu baya raye amma har yanzu Alkhairinsa muke mora, kije kiyi harkarki inyi tawa, ko kije ko karkije dubata hakan baze sauya komai ba, ki dauke Abincin ki, ki fita karki kara zuwa inda nake!!! " Jawwad yai sallar isha i ya koma Asibiti yasamu, doctor salis yana tambayarsa ya jikin Jalila, ya gayamasa sunfito da ita, an bata daki, daga yanzu zuwa kowani lokaci zata iya farfadowa, amma a tanadi Abinci, dan in tafarka a samu a bata, daga nana yagayawa Jawwad lambar dakin da aka kai Jalila, yana zuwa dakin da mamakinsa yaga Jalal a zaune, a can gefe yana shan sigarinsa, gefe kuma ga Jalila a kan gado ana samata ruwa, tana kwance. Jalal ya kalleshi yai murmushi "Sarkin fushi, ya akai na rigaka, zuwa" Share please More Comments More Typing.............................. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/13, 10:27 PM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  46 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680 Ina godiya matuka Allah yabar kauna        _My first novel_ Murmushi Jawwad yayi, "kasan ban zaci zaka zoba, na dauka dagaske bazaka zoba" "nima na fada ne ai dan in tsokaneka, kuma kaji haushi" "aikam dai naji haushin da farko amma yanzu na huce, ya me jiki?" Jalal ya kalli Jalila, sannan ya kalli Jawwad "Nima bansaniba, yanzu aka fito da ita" Jawwad yace "nayi mamaki da haryanzu bata farkaba," "hakane, amma zata tashi very soon, karkayi kuka, baban soyayya" Murmushi Jawwad yayi tareda girgiza kai, "Jalal kafiye neman magana, nine baban soyayya ko?" "eh mana nagani ne zakayi kuka" Sukayi Murmushi gaba daya    Maama ta sha jinin jikinta yadda Abba ya rufe ido yake ta fada, yana da matukar hakuri, rabon da taga yana fada kaman haka harta manta, duk abunda zatayi masa yana dauke kai, amma yanzu ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, Duk yadda taso ya tsaya ya saurareta yaki, balle ta bashi hakuri, seda yayi mata wankin babban bargo sannan ya fice ya barmata palourn, Yana fitowa palour yakira Nana, yace tazo suje asibiti, ko shi seya kwana da Jalila, tunda yayi waya da Jawwad yace masa anfito da ita kuma ana sa ran zata iya tashi a kowane lokaci, Nana ta fito suka tafi a Asibiti. Sukaje suka tarar da su Jalal, suka gaisa da Abba, Abba yaje kan Jalila ya tsaya yana mata addu a, ta rame kwarai, kuma har yanzu bata farkaba, Abba yace "Jawwad ku koma gida, mu semu kwana anan, nida Nana" Jalal yace " A a Abba, Jawwad da Nana dai su zauna kai ka koma gida, be kamata ace kai zakayi jinya ba bayan gasu" Jawwad yace "hakane Abba kabar Nana anan ka koma gida kawai" haka suka lallaba Abba ya koma gida, bayan tafiyar Abba Jalal ma ya mike yace ze tafi, Jawwad ya rakoshi waje, Jalal ya kalleshi sannan yace "Jawwad meyasa mamanku bazatazo ta zauna da ita ba, be kamata ace Abba yazoba, har yana batun ze kwana a gurinta ba" Jawwad yai ajiyar zuciya "Jalal kaima ka fada, Maama bata da wani dalili na kyamar baby, tunda ta kwanta batazo ko Asibitin nan bafa ina tsoron inyi magana ne" "shikenan seda safenku, nina tafi" "to Jalal nagode, Allah ya saukeka lafiya" Jalal ya jinjina kai daga nan ya nufi motarsa, Jalal yana barin asibiti ya nufi club, dayaje be samu su Jeje ba dan haka shika dai ya sha giyarsa, seda dare ya raba sosai , sannan ya tafi gida, Maama ta kira wayar yaya mairo ta sanar da ita abunda yafaru tsakaninta da Abba, da fadan da yaitayi, tsaki yaya mairo tayi "to ba seyayitayi ba dalla ki rabu dashi, mezakije kimata, baiwarta ce ke, ai Allah be doramiki wahalar ta ba, in yagama fushin ma ze sakko" "A a yaya mairo kinga kuwa yadda yaimin yau, yana ikrarin ze iya rabuwa da kowa akanta, haka kurum aurena ya mutu, gaskiya dai banda wannan shawarar, idan yasakeni ina na kama, baniba harku se mun shiga matsala" "Kuma fa hakane, amma kurarine baze iya sakinkiba, to ki dai kula karki saki jiki sosai, suma su Jawwad din kisa ido akansu, dan bana son su fiye shige mata, in kin samu lokaci ki leka ki ganta ko yan mintuna ne, shima dan ki rufe bakinsa, amma baze iya sakinki ba" Motsin dawowar Abba, Mama taji, dan haka tayiwa yaya mairo sallama ta tafi gurinsa, ta shiga dakinsa tana zaune Abba yaje yai wanka, yai salla yazo ya nemi guri ze kwanta, " Abban Jawwad gurinka nazo" Banza yayi mata ya nemi guri, ya kwanta, "Dan Allah Abban Jawwad kayi hakuri" "kinga tashi kibani guri bani da lokacin jin maganganunki, indai zaki guji Jalila nikika guda tunda jinin dan uwana ce, ki kyaleni" "Dan Allah.... " Zainab fita kibani guri, koni in fita in baki guri" Haka Maama ta fita ta bar dakin, lallai yayi fushi, abune mawuyaci kaga fushinsa, bashi da hayaniya sam amma wannan karon ransa ya gama baci.    Dare yayi Nana ta samu guri ta kwanta, Jawwad kuma ya zauna akan kujerar dakin a haka bacci ya daukesu, cikin dare Jalila tafara motsawa tana atishawa, da sauri Jawwad ya tashi yana kiran sunan ta, tana gama atishawar tacigaba da baccinta, ba tareda ta tashiba, tunda ga wannan farkawar da tayi, Jawwad be kuma komawa bacci ba har gari ya waye, Da safe Abba ya shirya ba tareda ya kula Maama ba, a palour ya tarar da halima da hijjabinta, ta gaishe da Abba ya amsa, tace "dan Allah sonake in bika inga jikin Jalila, tunda aka kaita Asibiti ban dubata ba" Ta karashe maganar kaman zatayi kuka, Abba yace ta taho su tafi, da sauri Halima taje kitchen ta dakko, kayan tea data dafa ta bi Abba, Abba a ransa yace "Baby ko bayan raina, nasan bazata rasa mutanen kirki dazasu kula da itaba, kodan saboda kyawawan halayenta, Halima me aiki duk ta damu, hada dawainiya haka, amma matarsa dayake tareda ita yake kyautata mata da danginta amma takasa yimasa alfarma akan yar dan uwansa saboda wani dalilinta mara tushe" Haka Halima ta  shiga bayan motar suka tafi Asibiti, koda suka isa Asibitin, Halima taga Jalila da yadda ta rame seta fashe da kuka, Abba yace tayi shiru ta dinga yimata addu a, bayan Abba ya duba Jalila ya tafi gurin aikinsa, Hawaye halima ta cigaba da sharewa, Jawwad yace "Halima kidena kuka cikin dare tayi atishawa akwai yuwuwar, ta farka a kowane lokaci, daga yanzu, kidena kuka, kimata addu a" gyada kai Halima tayi sannan Jawwad yace tunda ga Halima tazo, bari ya kai Nana gida tayi wanka taci Abinci, Nana ta tashi suka  tafi, aka bar Halima a gurin Jalila, halima ta mike ta koma kujerar gaban gadon Jalila, ta kifa kanta a gefen Jalila tana share hawaye, "Allah yabaki lafiya, Jalila, Allah ya dubi maraicinki, ya baki lafiya" Doctor salis da kansa ya shigo yayiwa Jalila allurai, ya samata wani ruwan, yauma tsayawa yayi yana karewa Jalila kallo, Halima ta dan kalleshi, "Likita wai yaushe zata farkane? kwananta biyu a haka fa" doctor salis ya kalli Halima, "karki damu muna sa ran zata tashi ba dadewa," Halima tace "Allah yasa" Daga haka doctor ya fita, Yayi awa daya da tafiyar su Jawwad, Halima taji an turo kofar dakin, dan dago kai tayi ta waiwayo, da mamakinta taga Jalal ne, seda gabanta ya dan fadi, dan batayi zaton ganinsa ba, ran nan nasa a hade ba fara a, babu alamarta, mikewa halima tayi daga kan kujerar da take, ta koma gefe Ta dan risina sannan tace "Ina kwana"  be amsaba yace mata "Ina Jawwad?" "dazu suka koma gida, amma zasu dawo" Gyada kai yayi ya jawo wata kujerar ya zauna ya harde kafa, yana karkadawa sekace wani basarake, ya zaro sigarinsa ya kunna, Halima ji tayi duk ta tsargu, ga mara lafiya a kwance amma taba yake sha, ji tayi duk ta takura, dan haka ta mike ta fita ta bar dakin, Yana nan zaune yana shan tabarsa, yaga kafar Jalila tana motsawa, a hankali ta fara motsawa, tana kokarin bude idonta, a hankali ta cigaba da motsawa, ta bude idonta, dishi2 take gani kafin daga baya kuma ta bude idonta fes akan Jalal zaune kan kujera da taba a hannunsa, kallon dakin dake ciki tayi, tana kokarin gane mafarki takeyi kokuma a gaske ne, yunkurawa tayi zata tashi zaune amma taji cikinta ya kulle, ta kasa tashi, Jalal yana kallon ta amma be cemata uffan ba, Yunkurawa tayi zata kuma tashi zaune, ga drip da yake shiga jikinta, tana nema tasa ya goce, Jalal ya kalleta, "Malama kikoma ki kwanta, idan ruwan ya goce kuma fa, wayace ki tashi zaune daga farkawarki," ya fada a dan tsawace se yanzu Jalila ta tabbatar da ba mafarki take ba, tashi yayi yaje ya zare ruwan da ke shiga jikinta, Yai waje, office din doctor salis yaje ya gaya masa Jalila ta tashi, da sauri salis ya Mike yana fadi" Alhamdilillah, gani nan zuwa " Jalal yakoma ya tarar Jalila ta lumshe ido, tanajin motsin Jalal ta dan bude ido tana kallonsa, ko ta kanta be kuma biba yasamu guri ya zauna, doctor salis ya shigo, yai sallama, ya kalli Jalila, ya kira sunanta a hankali ta bude ido ta kalleshi, " sannu ya jikin naki" gyada masa kai kawai tayi, doctor salis yace "Yanzu me yake miki ciwo" cikin muryar marasa lafiya, tareda shagwaba tace "Ni sonake in tashi in zauna, cikina kuma ciwo yakemin, nagaji da kwanciya amma nakasa tashi" ba karamin jin dadin muryarta doctor salis yaiba "Ok zaki iya tashi zaunen"? "A a nakasa tashin" "Ok let me help you, sit up" ya kai hannu yana kokarin tabata, da sauri tace "A a nika kyaleni zan tashi da kaina" "Bazaki iya tashiba, ki bari in temakamiki" Yamutsa fuska tayi, "Nace maka ka kyaleni" Jalal dake gefe yace "to ka kyaleta mana dolene, tunda tace bata so, base tayi ta kwanciyar ba," Kallon Jalal tayi ta dauke kai, salis yana jin tsoron Jalal, saboda yanada matukar kwarjini, dan haka yabar maganar temakamata ta tashi zaune, yace, "in Jawwad yazo, akwai magani daze siyo abata, amma a tabbatar taci abinci, dan zata bukaci abinci, asamu abu me dan ruwa2 abata ta sha," Jalal bece komai ba, doctor yai waje, Jalila trying ta kumayi ta tashi amma gefen cikinta a kulle, taji kamar an soka mata wani abu a cikinta zuwa zuciyarta, a hankali ta danyi kara, ta koma ta kwanta, kukanta ne ya karu yanzu hada sauti, da sheshsheka, takeyi, Jalal ya kalleta yai tsaki "Malama kimin shiru kincikamin kunne," Banza tayi masa ta cigaba da kukanta "Ni wallahi nagaji da wannan kwanciyar bayana ciwo yakemin" Shiru Jalal yai mata, yacigaba da danna wayarsa, ita mamaki ma takeyi, me take a asibiti ita da Jalal ina yan gidansu, tanaga dai mafarki takeyi, kukanta tacigaba hawayene na bin gefen idonta, tashi Jalal  yayi ze fita, har yaje bakin kofa, ya dawo ya kalli Jalila yasa hannu ya dago Jalila daga kwanciyar da take, ya jinginar da ita, ji tayi gefen cikinta ya kara kullewa, saboda ba a hankali ya dagata ba Ihu tayi ta rike hannunsa da karfi tana fadin "Wayyo Allah cikina, ni cewa nayi ka dagani, saboda mugunta, bakasan me nakejiba, zaka dagoni a haka wayace ka tabani" ta fada tana hawaye, dan tsuramata ido yayi, ita dai bazata canzaba da kyar take magana, kai dakaji muryarta kasan tanajin jiki, amma bazatayi shiruba "yimin shiru ko in maidake inda kika taso" dauke kanta tayi, kamshin turaren Jalal da warin sigarin dayakene Yasa Jalila taji tana yinkurin amai, dama gashi kwanakin nan cikinta ba komai, shi ya haddasa mata kullewar cikin, Daga haka Jalal yai waje ya barta, Halima tana reception taga wucewar Jalal dan haka ta mike ta nufi dakin da Jalila take, tana zuwa ta tarar da Jalila a zaune, zare ido Halima tayi, ganin Jalila a zaune "Jalila kin tashi sannu" Murmushi Jalila tayi, kafin tayi magana, Jawwad yai sallama, shima da mamaki yaga Jalila a zaune, da sauri ya karasa gaban gadon "Baby kin tashi sannu, ya jikin" "Da sauki yaya Jawwad, ina kuka tafi kuka barni, anan ni kadai, waima me nakeyi anan" "Bakida lafiya ne muka kawoki nan, yanzu me ke damunki" "Cikina ne yakemin ciwo, da kirjina," "Ok Sannu bari inkira salis" Halima tace "likitan yazo dazu yace abata abume ruwa2 ya mata allurai" "Ok temakamata tayi brush, ina zuwa" Jawwad na fita Jalila tace "Halima wai meyasameni ne, aka kawoni Asibiti" "Bakida lafiyane kawai" Halima ta dakko toothpaste da brush amma Jalila takasa sakkowa daga kan gadon, dan data motsa ko ina ciwo yake mata, bama ya cikinta, Haka ta hakura, ta zauna akan gadon tayi brush tai alwala, ta kalli Halima "Halima yaushe aka kawoni nakasa tuna komai, bansan sallan me zanyiba yanzu" Dan shiru Halima tayi, dan bata san mezatace mata ba, Jawwad ya shigo da leda a hannunsa, "sannu halima tayi brush dinne?" "Eh tayi," Tea yasa halima ta hada, yazo gaban gadon Jalila ya zauna, yace "Baby karbi kisha se kisha magani" Ta kalleshi "Yaya Jawwad salla zanyi, amma meyasameni aka kawoni asibiti" "kinga kiyi hakuri, fara sha tukuna zamuyi magana" Karba tayi ta dan sha kadan, yana shiga cikinta, taji ya murda ajiyewa tayi, idonta ya ciko da hawaye, zeyi magana wayarsa tafara ringing, Yana dakko wayar yaga Abdallah ne yake kiransa Dagawa yai yasaka a kunnensa tareda yin sallama, suka gaisa da Abdallah, "Aliyu meyasamu wayan Jalilane? Hanan ta kirata tagaji bata shiga" "Eyya batada lafiyane, kwananta biyu tana asibiti" "Subhanallah me yasameta haka?" seda Jawwad ya kalli Jalila sannan yace "ba ta jin dadine, amma taji sauki Alhamdilillah" "Allah sarki, amata sannu dan Allah, zan gaya ma Hanan din insha Allah" "to shikenan a gaida mutanen gidan" Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, hawaye ya gani shabe2 a fuskarta "meya farune, Dan Allah baby kisha kinji" "Yaya Jawwad ni na koshi, cikina ciwo yakemin" Ana haka Jalal ya dawo, "Jawwad kana nan". "eh Jalal nakoma gida na maida Nana ne, sannu da zuwa dan uwa" "Yawwa yanemi guri ya zauna" Jawwad ya maida hankalinsa kan Jalila, suka cigaba da fafatawa da Jalila taki cin Abincin, Jawwad se wani lallabata yake tana wani shagwaba, taki cin Abincin balle ta sha maganin, Jalal ransa yabaci ya dan kalli Jawwad "Namanta ban gaya maka ba, dazu kafin inshigo doctor Salis yace kaje, yana son ganinka" "Ok bari ta ci Abincin se inje" "No kaje kaji kowani abunne mana" Jawwad ya mike " to Bari inje," ya juya ya kalli Jalila"baby dan Allah kisha tea din nan kinji, yanzu zan dawo" Jawwad ya juya ya fita, yana fita ya rage daga Jalila, Halima se Jalal, Jalal ya kalli halima yace "hada wani tea din a katon cup" ba musu Halima ta hada, yasa hannu ya dauka ya mike ya nufo gadon Jalila, yana zuwa ya dire cup din a gefenta, ya hade rai "dauki ki shanye" Zunbura baki tayi "nina koshi, tayaya zan iya shan wannan uban shayin" tsawa ya dakamata "Ki dauka nace, se wani shirme kikeyi shikuma yana biye miki, inkin ki sha, wa kikayiwa inba kankiba, ki dauka ki shanye nace, kokuma wallahi in danneki se kinsha katon cup din nan biyu, danni ba Jawwad bane" Kallon cup din tayi, ta kalleshi yanayin fuskarsa ya tabbatar mata he mean what he said, fuskarsa babu alamar annuri, Halima kam tana gefe tana kallon ikon Allah, hannunta na rawa ta dau cup din, tana fara sha seda taji kaman ana kuma nannade mata hanji, yamutsa fuska tayi, tana dan sha a hankali, shikuma ya kakkafeta da jajayen idanunsa duk ya takurata, dire kofin tayi "ni gaskiya na koshi" Bece mata komai ba, ya cigaba da kallonta, itama kallonsa tayi, "to waini bana koshi ba" wani mugun kallo yacigaba dayi mata, ba shiri takuma daukan kofin tana sha tana haawaye ga wani amai dayake tasomata, "Wallahi kikayimin amai sekinsha cup uku" Da kyar da nishi Jalila ta shanye tea din nan tana zare ido tana kuka, seda ta shanye shi tas, sannan ya koma inda ya tashi ya zauna, Jawwad ya dawo da magani a hannunsa, ya duba cup din tea yaga ba komai a ciki yace "Yawwa baby ashe kinsha saura magani kuma" shima maganin da kyar tasha, taji dadin jikinta sosai, har tasamu tafara rama sallolin da suke kanta Jawwad ya kira Abba yagaya masa Jalila ta tashi, Abba yayi murna yace Insha Allah yana dawowa zezo ya dubata, anci sa a Maama tazo ta dubata, bisa shawarar yaya mairo, amma ta tsorata dataga Jalila dan ba karamar rama tayi ba, Jalila tace "Maama ina Nana" "anan ta kwana, shiyasa yanzu nahanata zuwa, gara ta zauna ta huta" daga nan Jalila bata kuma cewa uffan ba, Mama batafi minti goma da zuwaba ta tafi abunta, Bayan tafiyar Mama, Jalila ta kalli Halima tace "Halima wai kwana na nawa a asibitin nan ne? Ni dai nasan lafiya ta kalau" "Kwananki biyu cif" "Kwana biyu kuma"? Jalila tayi shiru tana tunani kaman an tsinkuleta ta fashe da kuka ta kalli Jawwd "Yaya Jawwad ina Ummi ba a ganta ba ko? Wai dama duk abun nan ba mafarki nakeba, Jawwad ina Ummi, ta mutu ko?" Jawwad yace "A a Baby Ummi bata mutu ba har yanzu ana nemanta" "Yaya Jawwad kacemin ta mutu kawai, shikenan nikam ita kadai taragemin dama, nasan ta mutu, haba Ummi, meyasa kika tafi kika barni, dan Allah Ummi ki dawo" "Ke dalla kiyi mana shiru, daga farkawarki kina ma mutane kururuwa a asibiti, wayace miki mutuwa tayi,? Zaki dinga yimana ihu, kowa ba gatansa Allah ba" "Ba ruwanka dani nayi kukan, ko dan kai bakasan darajar uwaba kake gani kowama haka ne agurinsa, dole inyi kuka, bansan halin da uwata ke cikiba, dakasan soyayyar da da uwa dabakamin tsawa ba, ita kadaice dani, ba uwa ba uba ba dangin uwa, " tana maganar tana hawaye numfashinta na fita da sauri Jalal zuba mata ido yayi, wani abu na sukarsa a zuciyarsa, tabbas besan soyayyar tsakanin da da uwaba, " Jalila meye haka, sa ankine shi, kike gaya masa haka" Jawwad ya dakawa Jalila tsawa abunda be tabayiba Share please More comments more typing............................. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ 🌹🌹[9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  47 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680 Ina godiya matuka Allah yabar kauna        _My first novel_ Mamakine yakama Jalila jin yadda Jawwad ya mata tsawa, abunda betaba yi mataba, "Jalila meyasa kike haka, na sha gayamiki Jalal ma kamanni yake agurinki yayanki ne shima" Dauke kanta Jalila tayi, ta cigaba da zubar da hawaye, Jalal juyawa yayi ya fita yabar dakin, Jawwad ya bi bayansa "Jalal dan Allah kayi hakuri, rashin fahimta ne tsakaninka da Jalila amma bazata karaba, yanzuma tana cikin damuwane shiyasa" Murmushi Jalal yayi "Never mind dan uwana, nima ba fushi nayi ba, Allah yakara sauki" daga haka ya nufi motarsa ya shige, sam Jawwad beji dadin abunda Jalilan tayiba bata kyauta ba, be kamata ace tagayawa Jalal wannan maganar ba dukda basa jituwa, yasan ba danshiba babu wanda ya isa yagaya masa wannan maganar ya kyale, Ya juya ya koma cikin Asibiti, yaje ya tarar da Still Jalila tana kuka, tana surutai akan Ummi, Halima nata bata hakuri, bebi takanta ba, ya kwashi wayoyinsa ya kwasa ya fice daga dakin. Ana idar da sallar magariba Abba yazo, yaji dadin ganin Jalila, ta farfado ta fara samun sauki, sedai tarame sosai, ta danyi duhu, shima Abban haka ta dinga masa kuka, tana surutai, ita ummi, Abba ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki "Jalila ki karbi kaddararki a duk yadda tazo miki, nima inata kokarin inga munsamu inda take amma abun ya gagara, inkika mika al amuranki ga Allah komai zezo da sauki, jikina yana bani har yanzu tana raye, kuma zata dawo, karki cutar da kanki da wannan kukan da kikeyi, " Abba ya kalleta sannan ya kira sunanta" Jalila" "Na am Abba" Ya cigaba da cewa "nidin nan ma misaline a gurinki, ba uwa ba uba, ba danuwana, gashi bamu da wasu dangi nakusa kona nesa, nasan bazaki rasa sanin tarihinmu ba nida mahifinki a gurin umminkiba, mu biyune kawai a gurin iyayenmu, kuma suma ba yan garin nan bane, gudun hijira sukayo, a yanzu haka bani da kowa, daga Allah seku ya'yana, ku nake kallo inji dadi, lokacin da nake kan ganiyar bukatar kulawar dangina, Allah ya karbesu gaba daya, amma hakan be hanani rayuwa ba, dukda har yanzu inata fafutuka ko Allah zesa insamu wani daga cikin danginmu, Dan haka ki kwantar da hankalinki, kinada Allah kuma ni mahaifine a gurinki, duk rintsi duk wuya, babu abunda zesa in juya miki baya, ko Ummi na nan kobata nan, ina kaunarki yata ce ke jinin dan uwana, kicigaba da addu'a ki kwantar da hankalinki, kinji yarinyar kirki, zuciyata na shiga kunci idan naga hawayen marainiyar nan kuma amanar Aliyu, bana son zubar hawayenki, kiyi hakuri duk lokacin da kike kuka ji nake kaman naci amanane, " Sosai nasihar Abba ta ratsa zuciyar Jalila, wanda yasa jikinta yin sanyi matuka ga kuma tausayinsa daya kamata "insha Allah, Abba zan cigaba da addu'a in tana raye Allah yasa tana hannu nagari, inta rasu kuma Allah ya.......... Kawai seta fashe da kuka Sosai tausayinta ya kama Abba, Halima dake gefe ma kuka take, Jawwad ma ji yayi kaman ya tayata Abba yace" tana rayema Insha Allah, kuma zamu gano inda take " Gyada masa kai tayi, Jawwad yace "Abba Maama tazo dazu ta dubata" "yayi kyau" shine kawai abunda Abba ya fada, ya tashi ya tafi, bayan tafiyar Abba, Jawwad ma barin dakin yayi, yaje office din doctor Salis, bayan sun gaisa, Jawwad yake tambayarsa yaushe ze sallami Jalila "se ta dan kara hutawa, nan da ko kwana biyune, tana bukatar kulawa, saboda abunda ze iya biyo baya, amma nan da kwana biyu ze sallameta Insha Allah" daga haka sukayi sallama ya fito, Jawwad koda ya fito bekoma gurin Jalila ba ya tafi gida, seda akayi sallar isha'i sannan ya dauki Nana ya kaita Asibiti, daya kaita ma a gate ya tsaya ta sauka ya juya, Nana tayi murna ganin Jikin Jalila da sauki, hira Nana take tayi mata amma tayi shiru, zuciyarta duk babu dadi, dakewa kawai takeyi, "Nana ina yaya Jawwad"? "Ai yana ajiyeni ya juya, inaga ko wani gurin zashi" Jalila ta dan jinjina kai,     Jalal kwance a dakinsa ya kurawa ceiling ido, dagani yayi zurfi sosai cikin tunani, dan lumshe ido yayi, tareda yin Ajiyar zuciya, kirjinsa yamasa nauyi matuka, ya mike zaune ya dafe kansa da hannunsa biyu, sallama tayi a palournsa, yai shiru be amsa ba, ta karaso da tray a hannunta ta nemi guri ta zauna a kusa da shi, hannunta biyu ta saka ta cire masa tagumin "Yaya Jalal meyake damunka tagumi fa babu kyau" dan kurawa Ilham ido yayi ya dauke kansa "Yaya kayimin magana mana, naganka wani iri" "Me kikazo yimin nan?" "Fruit na kawo maka, kuma naga kwana biyu baka zama a gida, kwana uku banganka ba, duk na damu, ko cikin gida baka lekamu" "Inkingama ki tashi kibani guri" "Haba yaya Jalal, in damu da kai har inzo inda kake amma ka koreni, please yaya Jalal kabani dama mana a rayuwa, wallahi I love you Yayana, please marry me, in ba kaiba rayuwata tana cikin hatsari ina bukatar kulawarka, bazan iya auren wani ba kaiba" "Idan kika bari na kuma yi miki maganar ki barmun dakina, sena miki abunda baki taba zatoba, sha3 mahaukaciya kawai" daga haka ya tashi yabar palourn ya shige bedroom dinsa, Mutuwar zaune tayi, gaba daya notin kanta ya kwance tarasa mezatayi, ita namiji yake wulakantawa haka, dole tanemi mafita, Jalal yafara kaita bango matuka, tana cikin nazarinne wayar Jalal daya bari a hannun kujera tafara ringing, amma setaga lambace ba suna, hannu ta kai ta daga wayar tasaka a kunnenta, da dagawarta taji muryar mace tafara magana "Haba my Jalal, kwana na uku ban ganka ba, ban saka a idona ba duk na damu, gashi baka daga wayata ina ka shigane, I want surprise you" Ran Ilham ne ya baci, dan haka cikin masifa tace "Ke dalla Malama dakata mahaukaciya, dabbar inace ke, to Wallahi bari kiji in gaya miki, ko ke kika kaso maita duniya bakisa ki auri Jalal ba, Jalal nawane ni kadai, inbiki kiyayeni ba wallahi se kinyi danasanin zuwanki duniya, gara tun wuri kisan inda dare yai miki, Jalal bashi da wata mata in ba niba, munafukar banza data wofi, maci amana" Hannah tace "Ke saurara Me kike da suna, karki kuskura kice zaki zageni, bani da lokacin ki, haduwarmu ta farko kin gayamin magana son ranki, na kyaleki, bani da lokacinki, kuma idan ina raye Wallahi karya kike kema ki auri Jalal muzuba nidake, dan halak ka fasa, sokuwa kawai" Jin hargowar Ilham ne yasa JALAL fitowa daga bedroom dinsa, yana zuwa ya tarar da Ilham rike da wayarsa tanata bala'i da surutai, karasawa inda take yayi, yasa hannu ya karbe wayarsa, ya juya ya nufi dakinsa, mikewa Ilham tayi tabi bayan Jalal tana masifa, a kunnensa ya kara wayar "Ya akayi?" "haba Jalal, meyasa kanwarka mahaukaciya ce, toka gayamata idan a wancan lokacin mun hadu ta zageni na kyaleta ta kiyayeni(a zatonta Jalila ce Ilham) , kasan halina zan mata rashin mutunci, kuma ka gaggauta gaya mata, nida ita shege kafasa" "meyasa ke baki gaya mata ba"? "Hakama zaka ce? Shikenan Jalal, ina ta wahala akanka, amma wata tana cimin mutunci ko, shikenan zatasan wata zaga wallahi, kasani duk me shirin kawomin matsala tsakanina da kai, sena gwada masa ni a mata ta dabance" "Look Hannah bana son shirme kaina kemin ciwo, kuje kuyi tayi, tunda daga ke har ita baku da hankali, banzaye kawai" Hannah kuma Ilham ta faada a hankali ba Jalila ba, wace kuma hannah, inma rainamin hankali suke, zasuga tsiya, yana gama wayar ya ajiyeta, wannan jarababbun sun kara hargitsa masa lissafi ransa a matukar bace yake, ya balle rigarsa ya aje kan gado ya juyo, yaga still Ilham tana tsaye, tana huci "Meye haka ina cire kaya kinzo kin sani gaba, malama ki wuce ki bani guri, bana son shirme ds hauka" "Wallahi Yaya Jalal, bazaka tabbatar da nayi hauka ba se ranar dana fara yimaka haukan, ni kake cewa mahaukaciya ko?....... Tinkarota yayi gadan2 ta juya da gudu ta fice, dan data bari ya karaso ta san sauran, amma shi a gurinsa yayine dan ya tsorata ta, saboda tun ranar da Jalila tace masa ragon namiji shike dukan mata, be kara dukan Ilham ba, sedai yayi mata tsawa, shiyasa tasamu damar kara yi masa shishshigi, tana juyawa ta tafi, ya dawo ya zauna yai shiru, sun kara dagula masa lissafi, ga maganganun Jalila sun tsaya masa a rai, daga baya yaga bashi da mafita, ya tashi ya dakko mutuniyar tasa, yaiwa kansa caji ya kwanta anan, yafara bacci. Jalila ta fuskanci Jawwad fushi yake, a lokacin itama taga rashin dacewar abunda tayi amma ba yadda zatayi, itama bata san tayiba, tana cikin dimuwane, shikuma yasata gaba da jaraba, tana wannan tunanin bacci yai awon gaba da ita Yana kwance akan cinyarta, tana shafa sumarsa, tafara magana cikin sigar rarrashi, da daddadar muryarta me cike da iyayi da shagwaba "AbdulJalal dina, kadena shan giya kaji, banason abunda kakeyi, bana son ganinka a irin wannan yanayin raina bayamin dadi, sonake kazama mutumin kirki kaman kowa, mutane sudena kyamarka," Murmushi yayi, "To Babyna, nima bana son abunda nakeyi, zuciyata bataso bansan meyasa nakasa denawa ba, amma ki dinga yimin addu'a zan dena, amma nima kidena yimin wulakanci a gaban mutane banaso" "Kullum ina yimaka, addu a, idan naga kana rashin kyautawa, gaba daya rainane yake baci, shiyasa nakema ka haka, amma nima na dena, amma promise me kaima zaka dena" Murmushi ya kumayi "Allah yayi miki albarka My queen u mean a lot to me, Insha Allah ze wuce kaman banyiba, yayinda mutane ke guduna da kyamar halayena, lokacin kuke kaunata ke da yayanki, can't forget your sacrifice "same to me, u mean a lot to me, ABDUL JALAL, fuskarta ta sunkuyo zata sumbaci goshinsa, " "Jalal ka tashi rana tayi haske fa, nasan ko salla bakayiba, se wani Murmushi kake a cikin bacci, wai me kake ganine a baccin"? Se yanzu Jalal ya gane mafarki yakeyi, Kallon Jawwad, Jalal yayi yayi tsaki Jawwad yace "Ya dai?" Ajiyar zuciya Jalal yayi "Bakomai" "Bakomai kake ta murmushi a bacci haka, gayamin mafarkin me kake?" "Kaga ni ka rabu dani" "Anyway kaje kayi salla, takwas da rabi fa" Jalal bekuma cewa komai ba ya mike yaje yai wanka, yai alwala yai salla Ilham ta boye damuwarta tayi breakfast, bayan tagama breakfast ta mike ta nufi gidansu Nana, bakowa a palourn gidan, dan haka ta wuce dakinsu Nana, taje ta tarar da Nana tana wanka, amma bataga Jalila ba, neman guri tayi ta zauna, ta jira Nana ta fito, Nana ta kalleta "Lafiya kuwa da safiyan nan? Naga kwana biyu ma bana ganinki, ko kun jone da Yaya Jalal ne no more matsala, shiyasa kika yadani" "Nana ba wannan ba ina yar uwarki?" "aini dama a kule nake dake Ilham, kwanan Jalila uku a Asibiti se jiya ta farfado, amma kokice tana ina, ta sha jiki kaman zata mutu" Ilham a ranta tace " A a tana asibiti to wace ce mukayi waya jiya,? cikin ko in kula Ilham tace "Niban saniba, bansan bata da lafiya ba, Allah ya sawwake" "Ah haba zakicemin baki saniba, bayan yaya Jalal ya jejje Asibiti dubata" Ji Ilham tayi kaman Nana ta soka mata kibiya, "yaje dubata fa kikace" "wallahi kuwa, kullum se yaje, nima yabani mamaki, amma kinsan kobeje dan kowaba yaje dan Yaya Jawwad" Jinjina kai Ilham tayi, ta Mike "na tafi se anjima" "daga zuwanki zaki tafi" "eh naga kaman fita zakiyi" "A a ba inda zani Asibiti ne se anjima zani" Bata kuma bi takan, Nana ba, Daga haka tai waje, zuciyarta fal takaici, wai kullum se yaje asibiti tunda aka kwantar da ita, "ko uban me yake zuwa yi, ta tabbatar ko uwarsa a aka kwantar baze je dubata kullum ba, tokuma wace ta kirashi, jiya? Karfa inje ina can ina hauka, aikin gama ya gama ina gefe, kai da sake wallahi, dole in tada balli" daga nan tai gida kaman mahukaciya. Bayan su Jalal sun gama breakfast, Jawwad ya tafi asibiti be takurawa Jalal seyaje ba dan ko shine baze komaba sabida abunda baby tayi masa. Doctor salis ya shigo yai mata allura ta cannula, bayan yagama ne ya kalleta "Baby ya jikin" banza tayi masa "ya kikayi shiru?" "nace maka ba sunana Baby ba" "Amma yayanki yake gaya miki" "to ba Yayana kace ba, ko kai yaya nane? " "am sorry, Jalila ya jiki" "da sauki Alhamdilillah" "Masha Allah, Allah yakara miki lafiya, jinake ciwon nan kaman ya dawo jikina, duk na damu wallahi" Dan ya mutsa fuska tayi "dan Allah ni ka sallameni yau" "Amma meyasa?" "To zaman me nake bayan na warke, ni kawai ka sallameni nagaji da zaman asibitin nan, gara in  koma gida" "Dan Allah kiyi hakuri nasan in kika tafi ba lallai inkuma ganinki ba" "wani mugun kallo Jalila tayi masa, to in zauna in maka mene? Ni gaskiya nagaji gida nakeson komawa, kobaka sallameniba sena tafi, ko in Abba yazo in gaya masa mekace" "A a yi hakuri, zan sallameki yau Insha Allah tunda kin warware" "da dai yafi maka" A ransa yace lallai haka wannan yarinyar take da tsiwa, lallai Jalal yayi gaskiya, amma shidai a hakan yana sonta don komai nata yana birgeshi, ana haka Jawwad yazo suka gaisa da doctor salis, ya gayawa Jawwad yau ze sallami Jalila, tace ita tagaji da zaman Asibitin, Jawwad yai murna sosai yace "indai ba wani matsala ai gara a sallamemu," Bayan fitar doctor Salis, Jawwad ya nemi guri zauna, ko kula Jalila beyiba, "Yaya Jawwad, ina kwana?" "lafiya kalau" shine abunda Jawwad yace, Daga nan bekuma cewa komai ba, wayarsa ce ta fara ringing ya dakko ya daga "Salamu alaikum" "Wa alaikum salam, My Jawwad barka da safiya," Muryar ya dauka, ya gane me maganar, dan haka yayi murmushi "Hanan kin tashi lafiya" seda Jalila ta waigo ta kalleshi "Lafiya kalau, yame Jiki, Abdallah yacemin batada lafiya, da sauki jikin nata? Ko kuwa? " "Kwantar da hankalinki, Hanan taji sauki, muna sa ran Insha Allah yau za a sallameta" "Me yasameta ne"? "Ta samu stroke ne, amma yanzu ta farfado tana lafiya" "Allah sarki na kira wayarta ne bata shiga, itakam baby me yayi zafi haka, har tasamu stroke? in kana kusa da ita bani muyi magana" Wayar a hansfree take Jalila tana jin komai Ya kalli Jalila sannan yace "Bacci take in ta tashi zan gaya mata" "to shikenan" "kayi saving lambata, mu dingayin waya" "to shikenan, karki damu" sukayi sallama da Hanan Ya mike ze fita Jalila ta kira sunansa, tsayawa yai ya waigo yana kallonta Idonta taf hawaye "Yaya Jawwad fushi kake dani ko? Dan Allah kayi hakuri, bazan, kuma ba" takarasa maganan hawaye na gangarowa daga idonta, ita dai zubda hawaye baya mata wahala Dawowa yai yazo gefen gadon ya zauna "Baby sam banji dadin abunda kikayiwa Jalal ba, haba baby, gaba yake dake fa, indai zakiyi masa haka nima zaki iya yimin kenan" Girgiza kai tayi "A a Yaya dan Allah kayi hakuri, nima ba a son raina na fada ba, raina ne a bace, shikuma yafaramin masifa, amma kayi hakuri" "Bani zaki bawa hakuri ba, inkina so in hakura, Jalal zaki bawa hakuri" Da sauri ta dago ta kalli Jawwad Share please More Comments More typing.............................. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  48 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680 Ina godiya matuka Allah yabar kauna               _My first novel_ Jawwad ya dan daga mata gira "Yes se kin bashi hakuri, sannan nima zan hakura", lallaima wai sena bashi hakuri, ajiyar zuciya tayi "to yaya Jawwad, zan bashi hakuri Insha Allah" "Yawwa baby, Allah yaba ki lafiya" Jikinta a sanyaye, tace "Ameen" Kamar yadda doctor yai mata alkawari, da yamma aka rubuta musu sallama, jikinta yayai kyau sedai rama, duk yadda doctor Salis yaso Jalila ta dan sakarmasa fuska ya samu kafa kansa taki, dan ita wannan shishshigin daya kemata haushi yake bata, shiyasa kome yace setayi masa shiru, ta hade rai, haka ya gaji ya hakura, suka shirya suka hada kayansu, Jawwad ya daukesu se gida, Abba yayi murna matuka da ganin an sallamo Jalila, Nana ma se murna take, Jalila ta dawo, saboda Jalila ba karamin alkhairi bace a gidan Har yanzu Abba yana fushi da Maama akan Jalila, tayi mamakin tsawon lokacin daya dauka haka, yana fushi akan wannan yarinyar, yanzu takuma tabbatar da idan har batayi taka tsan2 ba aurenta ze iya mutuwa saboda ita, se yanzu taga gaskiyar maganar yaya mairo, su Nana ma ba bi takanta sukeba, duk saboda Jalila, lallai tayi kuskuren yadda da Jalila ta zauna mata a gida, gashi tafara hada mata husuma a gida, dole tasan abunyi.   Kwana biyu da sallaman Jalila daga asibiti ta kara murmurewa, ta shiga sabgoginta, amma takan kebe ita kadai tayi kuka me isarta, gudun tayarwa da mutan gidan hankali, sannan tanata addu'a In Ummi na raye Allah ya bayyanata, tana cikin matukar damuwa amma, tayi iya kokarinta domin dannewa, kar a gane duk abunda take karfin haline kawai, Jalila ta lura Abba baya kula Maama, da tasaba kullum ta rakoshi in befita da wuriba, sucu Abinci ai wasa ai dariya, amma yanzu taga ko magana tayi se yayi mata banza, Jalila setaga hakan ba dadi, gidan ma ba dadi da suke zaune a haka, itako Nana ko a jikinta sabgoginta take.   Yau Maama ta fita bata gida da yamma, har magariba bata dawo ba, dan haka bayan an idar da sallar maghariba, Jawwad yasamu damar kiran Nana a waya yace ta tura masa Jalila, Ba musu Jalila ta tashi ta dau dan sirin gyale tasaka akanta, ta fita, part dinsa, da sallama ta shiga, taje ta tarar da shi yana aiki akan system dinshi, tana zuwa ya kashe system din, ya dago ya amsa sallamarta, karasawa tayi taje ta zauna a kasan carfet "Yaya gani, Nana tace kana kirana" "Eh Jalila, ya jikin naki" "da sauki Alhamdilillah yaya" "masha Allah haka akeso, dama kiranki nayi inji ya maganarmu ta rannan, kin bashi hakurin kuwa"? Dan hade rai Jalila tayi "To yaya ni ina zan ganshi, niban bashiba" ta fada tana dan zumbura baki "To taso muje" "Yaya ina zamu?" "Zo muje seki gani" yafada yana tashi tsaye Ba musu itama ta mike tabi bayansa, waje ya fita tana biye dashi, gidansu Jalal ya nufa, suna zuwa yai musu jagora zuwa part din Jalal, Jalila tayi mamaki duk yadda take ganin kyan dakin Jawwad amma na Jalal ya fishi dayake Jalila bata taba zuwa part dinba, babban part ne, dan seka zata amaryace a ciki, an zuba dukiya a ciki sosai, Suna shiga ta karewa dakin kallo, palournsa katone sosai da dakuna biyu a ciki, akwai kitchen da toilet a palourn, ba laifi ko ina tsaf yake, ga katon tv plasma kusan rabin bango, palourn yasha labulaye da kujeru,sekace dakin amarya, ga kamshin turare yana tashi, kai bakace dakin mashayi bane Jalal yana kwance akan 3 seater daga shi se wando 3 quarter da vest, yana ta danna wayarsa, yanajin sallamar Jawwad ya amsa a hankali, inba ka kalli Jalal ba bazaka san ya amsa ba, idonsa a lumshe yace, "Jawwad kai nake jira dama" "to gani ai, tashi kabani abunda zaka bani" Jawwad ya amsa suna karasa shiga cikin palourn, Jalal sam be san Jawwad shida Jalila bane, sedayaji Jawwad yace "Jalila, karaso ki zauna mana" Jalal ya bude idonsa ya waiga yaga Jalila ce dagaske, seda gabansa ya fadi, doguwar riga ce a jikinta na material, se karamin mayafi da ta dora akanta, rigar kaman a jikinta aka dinka ta, se yanzu ya kara ganin ta rame sosai se idanuwa, gashi ta danyi duhu amma tayi kyau sosai, dauke kansa yayi daga kanta, be kuma cewa komai ba, Jalila ta shigo cikin palourn ta samu guri ta zauna a kasa kan carfet, kusa da kafar Jawwad, se zumbura baki take, Jawwad yace "Jalal gurinka mukazo fa" "Ina jinka" "Ka tashi mana, kaji dame mukazo" Ba musu ya mike zaune, yana kallon Jawwad, "ina jinka" "Dama abunda ya farune a Asibiti tsakaninka da Jalila shine mukazo mu baka hakuri, dan Allah kayi hakuri nasan bata kyauta ba, amma gata nan munzo tabaka hakuri" Wallahi ba dan Yaya Jawwad ba babu abunda zesa Jalila tabawa wani Jalal hakuri kome zatayi masa na rashin kyautawa kuwa, Jawwad ya kalli Jalila "Jalila kibawa Yayanki hakuri" Sedata yatsuna fuska, dayake Jawwad baya ganinta, amma tana facing Jalal, "Dan Allah kayi hakuri, bazan kara ba" Jalal yace "Hmmm Jawwad kenan, ni nacemaka nayi fushine?" "A a baka cemin ba, amma bamu kyauta bane, dole mu bada hakuri, da fatan an hakura" "Se anwa mutum laifine za a bashi hakuri, ai har a tambayi koya hakura" "Haba Jalal wannan ai gwalewa ne, tunda ta baka hakuri kayi hakuri mana" Wani mugun hara Jalila takewa Jalal ganin se wani raina musu hankali yakeyi, Wayar Jawwad ce tafara ringing, Hanan ce ta kirashi, bazeso yadaga agaban Jalila ba, dan yaga Hanan itama muguwar yar rigimace, yanzu setayi abunda Jalila zataji haushi, dan haka yace "please excuse me, Jalila jirani ina zuwa" ya tashi ya fita amsa waya, Jalal ya dora kafarsa daya kan daya, shima yaja tasa wayar, yana dannawa, Jalila se jan tsaki take, wayar Jalal ta fara vibration, ya saka a  kunnensa "Ya JJ ina jinka" Jalila ta dan kalleshi, Jeje in bata mantaba Jawwad ya gaya mata shine farkon lalacewar Jalal, "Birthday kuma Jeje, ni kuka shiryawa birthday, yaushe kenan"? Ya danyi shiru sekuma yace "Ok Allah ya kaimu, zanyi shawara ingani, if i can attend" yakuma cewa "Eh kwana biyunne akwai abunda nakeyine, shiyasa bakwa ganina, amma zanzo very soon" Jalila a zuciyarta tace "gaskiya zanso inga wannan Jejen, inga ya yake, kuma meye manufarsa akan Jalal" Jalal ya gama wayar yayinda ta danyi nisa a cikin tunani, kamar an tsunkuleta ta daga kanta kawai sukayi ido hudu da Jalal yana kallonta, cikeda tsiwa, da gadara tace "Meye haka zaka wani tsuramin ido, lafiya?" Jalal yace "idan kika kuma, zuwa inda nake da wannan dan gyalen, zan nuna miki ba lafiya ba, kalli dan gyalen da kika saka" dan bude baki Jalila tayi da mamaki, "to ina ruwanka dani, dazaka dinga kallona, ni banason kallo, inma tsirara nake yawo meya shafeka" "meye abun kallo a jikinki, mummuna dake, kwaila" Jalika rasa meza tace tayi, dan batayi zaton jin wannan maganar daga bakinsa ba, shi kuma ya dauke kansa ya kunna sigari, Ya tashi ya dakko, giya a fridge ya dawo ya zauna, binsa Jalila tayi da ido, ya bude ya dakko wayne cup dinsa ze zuba, da sauri tace "Giya ce fa? Kai yanzu baka kunyar ubangiji, baka kunyar kowa, zaka sha giya a cikinka, meye hakane?" Shiru yamata yafara zubawa a cup "Wai dagaske shan zakayi,? Mikewa tayi cikin zafin nama, ta nufoshi a fusace daa nufin ta fizge, ko a jikinsa kuma be fasa abunda yai niyya ba " in kika karaso inda nake zan baki mamaki, stay where u are, wallahi kikazo sekema kinsha, kuma ko a gaban Jawwad ne, se dai ya hadiyi zuciya" ba shiri Jalila taci birki, "Wallahi tir da halinka, me abun kunya, angirma amma ba hankali, Allah ya tsareni da shan giya, yamin tsari da hali irin naka, gaba daya ka gama bata rayuwarka, baka da wani amfani daza kayiwa kanka ko kayiwa wani, a dai canza hali" Banza yamata, yaci gaba da abunda yake, yayinda ta cigaba dagaya masa magan ganu son ranta, ganin bashi da niyyar denawa yasata nufi hanyar fita aiko tai karo da Jawwad " Am sorry na barki kina jira ko, yi hakuri dan jirani kadan ss mu tafi? " Ranta a bace tace" ni tafiya zanyi gaskiya " " Me yasa? Ko fadan kuka sakeyi? " "ni bazan cigaba da zama ana sabon Allah a gabana ba, ko kunya bayaji ya dakko giya yana sha, ni tafiya zanyi," daga hakka fuuuuu tai waje, Jawwad ya kalli inda Jalal yake, tabbas giyar yake sha, jikin Jawwad a sanyaye ya taka ya karasa gurin Jalal, sannan yace" Jalal yakamata kadinga boyewa in zaka sha giyar nan, bayyanar da lefunka ze cigaba da zubar maka da mutunci a idon mutane, bekamata ka sha giya a gaban Jalila ba, Jalal u have to do something good for your life rayuwa bazata tafi a haka ba" A hankali JALAL ya aje cup din hannunsa ya dan kalli Jawwad "Jawwad in har banji kunyar ubangiji ba na sha giya, meye kuma abun boyewa wani abun halitta, da bashi da wuta bashi da aljanna, Jawwad i don't know what to do, nasani abunda Jalila take fada gaskiyane bani da wani amfani dazanwa kaina ko nayiwa wani, ban san meyakamata inyi ba, ban san meyake damuna ba, fita kabani guri Jawwad, ka tashi kabarni, leave me alone i want have some rest "     Ilham tana kitchen tana hada tea zata sha, dayake window kitchen a bude yake, kuma kana ganin harabar gidan ta nan, kawai taga Jalila ta fito daga part din Jalal, ta tsaya ta dan gyara mayafinta sannan ta nufi gate, mutsukke idonta takumayi don tabbatar da gaskiyar abinda ta gani, anya kuwa itace, da sauri ta juya ta bar kitchen din   Jalal yafara fita hayyacinsa, idonsa yafara wannan abun, ga jijiyoyin kansa sun tashi, ya fadi kasa,Jawwad ya zo gabansa ya dutkusa ya dan dafashi "Allah yaye maka wannan matsalar" daga haka Jawwad ya Mike ya fito, dan haka shine samun nutsuwar Jalal, jawwad ya girgiza kai tareda yiwa Jalal fatan samun sassauci a rayuwarsa, Fitar Jawwad keda wuya, Ilham ta fito daga cikin gida, ta nufi part din Jalal, sam bata hadu da Jawwad ba, tana zuwa kamshin turaren Jalila ya daki hancinta, tana kokarin tabbatarwa ne taga handkchief a tsakar palourn, da sauri takarasa ta dauka, ta kai hancinta ta shinshina, tabbas na Jalila ne, ga Jalal taganshi zube a kasa yana bacci, dora hannu tai aka ta fasa ihu, sekuma tayi saurin toshe bakinta, "Na shiga uku Allah yasa ba abunda nake tunani bane, Jalal in kamin haka bakamin adalci ba, kaci amanata, kuma wallahi na tabbatar da abunda nake zargi sena kasheka na kasheta wallahi," shikam yafadi a gurin yana baccinsa Surutu ta cigaba dayi, tana zambarwa a gurin, Jalal besan tanayi ba, tagaji tayi waje ta nufi cikin gida, dakinta ta shige ta kulle kofa, ta dinga zarya, wayarta ta dauka, ta kira malamin su, akayi sa a bugu biyu ya daga "Malam akwai matsala fa" "Mastalar mene haka?" "sonake ka bincikamin, kagani aikin nan kuwa ba a samu wata matsala ba?" "Matsala kuma kaman yaya, wani abu yafarune"? "ni dai kawai ka bincikamin dan Allah," "To shikenan amma kibari seda safe, zan kiraki" Sukayi sallama da malam, amma fafur batun bacci ya kauracewa idon Ilham se surutai da zage2, kaman ta zare, kai kace mahaukaciya ce, yadda taga rana haka taga dare. Da safe Jalila dan cin Abinci tayi kadan bata wani ci dayawa ba takoma daki, dan tunda aka sallamota daga asibiti a daki take wuni, seda wani dalili take fitowa, Nana ta tafi gidan kawarta yau, ga Halima taje ganin gida, dama Maama ba shiga sabgarta take ba, tunani duk ya addabi Jalila, ga batada nutsuwa saboda rashin Ummi, ga kuma tunani daya addabeta akan rayuwar Jalal, hankalinta ya karkata kan son zuwa birthday Jalal, domin ganin waye Wannan Jejen, Tunani duk ya dameta, dan haka ta tashi ta fito harabar gidan, tasamu guri ta zauna, tai shiru tana kallon flowers, Da safe Ilham ta kuma kiran Malam a waya don tambayarsa ko ya bincikamata, yace "Na duba, nayi bincike amma ba abunda ya sauya, aikinmu yana nan a tareda shi, aikin da akayivakansa har yanzu yana tareda shi" Ajiyar zuciya Ilhan tayi, "har naji dadi, nagode sosai malam har naji hankalina ya kwanta" "Ai bakiga ta kwanciyar hankali ba indai baki kauda wannan yarinyar ba, yakamata fa kisan halin da kike ciki don tabbatar da cikar burunku keda mahaifiyarki, asiri kawai baze tasiri akanta ba dole ki tashi kisan meya kamata kiyi, ina ganin itace zata kawo wa aikin nan matsala, ni nariga nagaya miki yanzu, shawara da dabara yarage naki" "To shikenan nagode sosai, nikuma zan san abunda zanyi," sukayi sallama ta dakko handkerchief din Jalila ta fito se gidansu Nana, tayi sa a Jalila tana harabar gidan a zaune, gurin Jalila ta nufa, tana zuwa ta kalleta "Gurin ki nazo zamuyi magana" Banza Jalila tayi mata, "magana fa nake miki" "in har zakizo inda nake bakimin sallama ba, banida lokacin saurararki" Ilham tasan inbatayi yadda Jalila take so ba, bazata kulata ba dan haka tai mata sallama Jalila ta amsa sannan tace "ina jinki" Ta kalli Jalila ta nuna mata handkerchief din tace mata "wannan kaman naki ko?" Jalila ta kalli hannunta tace "ba kama bace nawane" "A ina kika barshi?" "A inda kika tsince shi" Jalila tabata amsa cike da rainin hankali "zuwa nayi muyi magana ta fahimta, bata fada ba" "Inma ta fadan kikazo a shirye nake" "Jalila meya kai handkerchief dinki dakin Jalal, meye hadinki dashi?, Jalila ina miki kashedi na karshe tun kafin insa ki zubarda hawayenki, inma akwai wani abu a ranki akan Jalal gara ki cire, kishiga hankalinki dan wallahi zan iya illata kowaye akansa, duk wanda yai niyyar hana min cikar burina senasashi zubda hawaye, Jalila wannan ne kashedina dake na karshe, kifita a harkar Jalal, tun kafin ta kwabe miki" Jalila tai mata kallon tsaf sannan tace "A matsayinki nawa kike min wannan kashedin haka? Matsayin uwata ko ubana ko wadda ta isa dani? Hmmm gaskiyar dan uwanki dayake cewa bakida hankali, ni kinga wani abu me kama da soyayya tsakanin da wannaan bugaggen dabe maida sabon Allah komai ba,? Ilham ko mazan duniya sun kare ba abunda zanyi dashi, banga abun so a gurinsa ba, Allah ya tsareni son Jalal, bashida kamala da cikar dazesa inso mutum kamarshi, baya jerin irin mazan dasuke birge Jalila, dukda bansan naki kudurin akansa ba, nima ina da nawa kudirin akansa, babu soyayya, ko auren Jalal a kudurina, kuma ki dena wannan tunanin, amma kisani idan har kudurinki yaci karo da nawa akan Jalal to tabbas kisawa zuciyarki sena tarwatsa naki!!! Ban taba sa abu agabana nakasa ba Ilham, ina iya tarwatsa ko shirin uban waye domin biyan bukata ta, wallahi Ilham kinyi kadan kisani kuka, idan harkika sani kuka, nikuma namiki alkawarin zan illataki a inda babu wanda ze gani balle ya miki magani, Ilham zuciyarki zanwa Illa ta har gaba da abada, ganin Jalila kike bakisan wace itaba, tunda kika zabi zaman takun saka dani am ready for you "daga haka Jalila ta fizge handkerchief dinta tai cikin gida, yayinda Ilham ta sandare a gurin Share please Dan Allah kuyimin afuwa rashin jina akan lokaci, dakuma karancin pages din wasu lokutan, ayyuka ne sunmin yawa, in baku mantaba a baya kullum nake mumu posting, yanzu abubuwa ne sukamin yawa amma ina neman afuwar ku, Ina alfahari daku, kuma ina sonku irin sosai din nan masoya, muje zuwa kucigaba da bina a sannu domin jin yadda zata kaya a cikin wannan novel Taku har kullum Daddys girl 😍😍😍😍😘 More Comments More typing.............................. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  49 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680 Ina godiya matuka Allah yabar kauna Ina amfani da wannan dama, domin mika ta a ziyyata ga yan uwa mutanen zazzau da dukkanin al ummar musulmi, na rashin sarkin zazzau Alhaji shehu idris, ina fatan Allah ya jikansa yasa mutuwa hutuce, dashi da dukkanin al ummar musulmi da suka gabacemu Allah ya rahamshesu in tamu tazo Allah yasa mucika da imani               _My first novel_ Jalila na zuwa dakinsu ta kife akan gadonsu, "Nikam Jalila nashiga uku, wace kaddara ce ta kawoni kano har nasan Jalal ne, wanda har rayuwarsa take neman hanamin tawa nutsuwar, Ummi dan Allah in kina raye duk inda kike ki dawo, nagaji da zaman nan ina cikin damuwa, Allah ka temakeni, kabani ikon jarraboyina na rayuwa" Ta karasa maganar tan zubda hawaye, tayi me isarta sannan ta mike ta duba wayarta ta kira Hanan, seda ta kusa katsewa sannan Hanan ta daga, tana dagawa tace "Tace afuwan ranki ya dade, ina wankane, ya jiki Jalila? " Da sauki Hanan, ya Baba na dasu Abdallah " " Baba baya gari yana bauchi, Yaya Abdallah ma haka dagani se mummy, ya jikin kinji sauki" "jiki Alhamdilillah na warke ganima a gida" "masha Allah, nakira Jawwad nace ya hadani dake amma se yacemin ba kya kusa, siyama ma takiraki bata shiga ki kirata dan Allah" "zankirata Insha Allah" Hanan ta ce "nikan Jalila meyasameki haka har ya kai ga kisamu stroke ko wani abu na damunki ne?" Se Jalila taji kaman Hanan ta sosamata inda yake mata kaikayine, batasan lokacin da hawaye yafara fita daga idonta ba "Hanan ni meye ma baya damuna, ko kinsan cewa a halin yanzu sati biyu kenan, bansan inda ummi takeba ko a raye ko a mace ban saniba" "Kamar yaya baki saniba, naje gidan fa ranar dazata taho kano, tacemin zatazo kuyi sallama zata wuce garinsu, kuma kice bakisan inda take ba" "Hanan tunda Ummi ta tafi, mukayi waya da ita, wayanta be kara shiga ba anyi trying har angaji, karshe aka kira Abba aka gayamasa, wai wani me mota ya bigeta, kuma ya dauketa ya tafi da ita, bawanda yasan ina ya kaita, kotana raye kota mutu bamu saniba" "Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Jalila meyasa baki gayamin ba tunda wuri, kuma angayawa"yan sanda"? "Hanan Abba yana iya kokarinsa amma har yanzu ba labarin Ummi ni harna hakura na fawwalawa Allah komai" "kiyi hakuri Jalila, nasan abun da wuya a gurinki, amma mucigaba da addu a, insha Allah za a ganta, in daddy ya dawo zan sanar masa koda wani abu da za a iyayi akan matsalar, kiyi hakuri, Jalila insha Allah ummi tana raye za a ganta". Hanan ta ke rarrashin Jalila yayinda itama take zubarda hawaye, har cikin zuciyarta takejin matsanancin tausayin Jalila, "Addu a ina nan inayi hanan, sedai kuma ina bukatar taku adduar" "Insha Allah zan tayaki addu a, kinji kidena damuwa sosai, kar wani ciwon yakamaki" "Karki damu kanwata na fawwalawa Allah komai, shi ze bani mafita" "Masha Allah haka akeso queen muzama masu karbar kaddararmu a duk yadda tazo mana," domin kokarin kauda damuwar Jalila, se tace mata "nace ya gidannaku, ya mutuminki?" "waye kuma mutumina?" "kinfini saninsa Jalal mana" "Yana gidansu" "kai queen har yanzu kina masa rashin mutunci ko?" "ko jiya ma seda mukayi, yau kuma wannan mahaukaciyar kanwar tasa tazo zatamin hauka, wai ita alallai son Jalal nake, wai in ban fita harkar saba seta sani kuka kiji fa," Dariya Hanan tayi, sannan tace "queen J nasanki da kafiya, dan Allah karki bari Ilham tayi nasara, kizama silar shiryuwar Jalal, u can do it, kibata mamaki, kamar yadda kika bani" "ke nina fara gajiya, gashi jarababbe, ga taurin kai gashi mugu, itakuma gani take sonsa nake ko uwar me zanyi da wannan makakken, dan wahala daga ita harshi" "A a dai, banda cika baki, daga baya kizo kina zare ido akansa" "Kut me kike nufi, mezanyi da wannan Allah ya rufamin asiri" "Oho dai inda rabon an jone ne.... Jalila bata bari takarasa ba ta kashe wayar tareda fadi" ji muguwa zatamin mugun baki, ta Allah ba taki ba" Daga haka Jalila ta Mike ta fito palour don samun dan abunda zata ci, Maama tana palour a zaune tana kallon Aljazeera, Jalila tace "Maama sannu da gida" Kallon Jalila tayi ta dauke kai ba tareda ta amsa mataba, har Jalila zata wuce kitchen, Abba ya shigo, ya dawo da wuri yau, da alamu ko mantuwa yayi, Jalila tace "Abba sannu da zuwa" "yawwa Jalila ya jiki ya gidan," "lpy qalau Abba" Maama tacewa Abba "Sannu da zuwa" Banza yayi mata da nufin shigewa dakinsa, Jalila tai farat tace "Abba, Maama na maka sannu da zuwa fa, bakace komai ba" Abba ya wayance da "Yawwa maman Yara, yi hakuri banji bane" ya wayance kar Jalila ta gane, sannan yace "Jalila dan kiramin Jawwad, kice ina son ganinsa, a dakina" "To Abba bari inje" Jalila ta tafi part din Jawwad, Jalila na fita Abba ya shige part dinsa ya bar Maama a palourn, binsa tayi itama, tana kuka, Abba ya kalleta "meye haka zaki biyoni kina kuka, se yaranki sunce wani abun nayi miki" "Meyema bakayimin ba ina tabinka ina baka hakuri amma kaki kulani, sati kusan biyu kana gaba dani, kaki saurarata haba Abban Jawwad, dan Allah kayi hakuri, kadena fushin nan haka" Kukan dayaga tanayi seta bashi tausayi, "Zainab, komenayi miki ke kika jawa kanki, nima ba a son raina naimiki hakaba sedan in nunamiki kuskurenki, akan abunda kikayimin," "kayi hakuri hakan baze kuma faruwa ba Insha Allah" "Zainab kenan indai halinki ne ba wanda ban saniba, bana tunanun wannan maganar har cikin zuciyarki"   Jalila tana zuwa part din Jawwad ta tarar suna fada da Jalal, "JALAL dan me zasu shirya maka wani birthday, dacan ma aibasu suke hada maka ba, bayan kasan mutanan nan bana kirki bane, su kaika wani guri su hada maka birthday kuma ace shabiyun dare haba Jalal kayi tunani mana," "Jawwad ya kakeso inyine? Sokake ince musu bana so ko inki zuwa, ko wa akayiwa haka baze ji dadi ba, mene a ciki abu na lokaci daya ayi a watse, basu taba hadamin ba, wannan karon sunmin se ince banaso, kana ganin idannayi hakan na kyauta, shikenan bance kaje dole ba fa, dama zuwa wannan gurin da daddare ai da irina ya dace ba da kai ba" daga haka Jalal ya juyo fuuu ze fita, da sauri Jalila ta bashi hanya kar ya bigeta, bayan ya fita ta shiga palourn, Jawwad yanemi guri ya zauna yayi shiru "yaya Jawwad ya dai? " Bari Jalila, Jalal ne yake neman ya cazamin kwakwalwa, kullum fatana in janyeshi daga jikin wannan miyagun abokannasa shikuma yana kara shige musu, " " Meya farune? " " Wai an hada masa birthday, se sha biyun dare zasu fara har gari ya waye, kuma a baya tare muke hadewa muyi dashi kuma  a gida amma wannan karon wai su suka shirya masa, nasan kwana zasuyi shan giya, nace kar yaje kuma yana neman yayi fushi, seyaje yai tayi ai, am tired da halin Jalal" Sosai taji tausayin yayan nata, taga kokarinsa ma tsawon wannan lokacin yana tareda Jalal, duk da miyagun halayensa, ga shi da wuyar sha'ani amma haka Jawwad yake tare dashi, kuma tasan wannan fushin na dan lokacine, dole se daya ya nemi daya, ta numfasa tace "Yaya Jawwad ai be kamata kayi fushi ba fa, tunani yakamata kayi, tsawon shekaru suna tareda shi basu taba cewa zasu shiryamasa birthday ba se wannan karon, kuma ma wai se tsakiyar dare zasu fara, baka tunanin wani abun suka shirya akansa? Bakayi tunanin suna da manufar yin hakan ba? Kn kayi fushi kace yaje yaitayi, kaga sunyi galaba zasu kara janyeshi, shikenan yazama  nasu gabadaya" Shiru Jawwad yai yana kallon Jalila Taci gaba da cewa "Kayi tunani yaya na, dan uwanka ne fa, u have to think" Ajiyar zuciya yayi "Hakane baby kema kinyi magana, amma yanzu me yakamata inyi" Jalila aranta tace yawwa, nima ga dama ta samu, A fili tace, "Yaya dole ka shiga cikin lamarin nan, kawai ka yadda da maganar birthday din nan, ka lallabashi kasashi a maida partyn kaman daga karfe ta kwas zuwa goma, sannan dolenka ka halarci gurin domin sakamasa ido, in takama har abokanan ku da yanuwa ku gayyata, hakan ze hana faruwar wasu abubuwan, karfe goma nayi, ka janyeshi daga gurin, yanzu kayi hakuri ka sakko, har ya gaya maka shirye2 da sukeyi, kaima seka san shirin dazakayi, amma inka barshi ya tafi shi kadai jikina na bani akwai dalilin dayasa suka shirya hakan, sun san babu wani dan uwansa daze yadda ya bishi guri irin wannan karfe shabiyun dare" Murmushi Jawwad yayi, tareda yiwa Jalila salute "Gaskiya baby kina da tunani me zurfi, hankalina be kai kan hakan ba ni, gaskiya nagode, zan jarraba insha Allah" Murmushi Jalila tayi "nifa aikoni akayi, Abba yace kazo yanzu" "To shikenan ina zuwa"   A ranar bayan Jawwad yaje kiran Abba, ya je yanemi Jalal suka shirya, yace masa ya yadda, zeje birthday dinsa amma gaskiya zasu gayyaci mutane, dan haka sedai a canza lokacin daga shabiyun dare zuwa karfe takwas, Jalal yace ya yadda.    "Jeje wannan ce dama ta karshe dazan baka, a wannan karon banason asamu kuskure, dukda tsawon shekarun nan kayi aiki tareda ni, kamin duk abunda nake bukata to wannan karon, sonake komai ya kare, sonake a wannan lokacin komai yazo karshe, karka bari wannan shirin ya rushe, " " Oga kb baka da matsala, munyi iya kokarinmu gurin ganin hanyoyin dazamubi domin gabatar da aikin cikin shiri, burinka ze cika, a wannan ranar zamuyi yadda zamuyi muga mun karasa wargaza rayuwarsa, " Wanda aka kira da oga KB ya gyara tsayuwa yai ajiyar zuciya " shikenan ina jira zan saka ido inga kokarin ka, a wannan karon, aje acigaba da shiri," " Shikenan oga, wannan karon komai zezo karshe" Daga haka sukayi sallama, Hannah na gaban dressing mirror tana kwalliya, Jeje ya kirata, seda ya kira sau uku tana kallon wayar sannan ta dauka "Hannah ina kika shiga ne inata kiran wayarki, ya za ayi mu hadu ne?" "mu hadu kuma, akwai matsala ne?" "eh haduwar tamu tanada mahimmanci sosai, akan shirunmune, yanzu haka daga gurin oga KB nake, akwai bukatar mu hadu" "To zanzo, muhadu inda muka saba" "To shikenan sekinzo"          Ilham se safa da marwa take, a cikin dakinta, ta rasa inda maganganun Jalila suka dosa, tace ita ba son Jalal take ba, amma itama tanada kuduri akansa, kuma inyaci karo da nawa, to tabbas zata rusa nawa, koda tazo nan a tunaninta seda ta zare ido, ta rusa nawa burin saboda nata muradin, to ko ta san menene shirina ne, to amma tayaya zata sani bayan ko Nana bata saniba, Dakko wayarta tayi, zata kira yaseera, sekuma ta fasa, dole in dau mataki, bazanyi wahalar banza tsawon shekaru ina kallo wata sakarya ta rusamin shirina ba, gara tun yanzu in rusata ita danata shirin, ta mike da sauri ta nufi dakin mummy, tana zuwa ta tura kofar dakin, ta sameta tana waya, taje kusa da ita ta zauna, tana jiranta tagama, Seda mummy tagama waya, sannan ta kalli Ilham tace "Ilham ya akayine, naganki wani iri haka kaman mara lafiya" Fashewa tayi da kuka, ta fada kan cinyar mummy "Mummy wallahi nakusa mutuwa, in har yaya Jalal be aureni ba, zan iya mutuwa, Mummy ina sonshi, dan Allah asaka ranar aurenmu," "Yi shiru kiyi hakuri, kinji nima naga kamatar yin hakan, kila in kika aureshi ma ya shiryu sanadin haka, yanzu kidena kuka, bari daddynku ya dawo, muga me yakamata ayi, amma karki kuma zance zaki mutu saboda shi, aini na miki alkawari, indai ina raye Jalal shine mijinki, indai nina haifeshi baze taba auren wata mace inba keba, kidena kukan nan haka ya isa" Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Ilham tayi, tareda yin murmushi a boye, a fili kuma tace "dan Allah mummy asaka da wuri, ina tsoron ya auri wata baniba," "ki kwantar da hankalinki, shi kinga alamar ma zeyi soyayya da wata, ko kina tunanin akwai wadda zata aureshi a haka, aini kingama min komai da kikeson Jalal a haka, dan haka bari daddyn sa ya dawo, zamuga yaushe yakamata asaka" Ilham ta riko hannun mummy, "Nagode sosai, mummy" "bakomai, kidena kuka"    Hannah zaune akan fararen kujerun dake  gurin, fuskarta dauke da wani arnen glass dayake barazanar cinye fiye da rabin fuskarta, ga barima da tasaka a akan dogon hancinta, se tauna chew gum take, tana fuskantar Jeje, "Hanna daga gurin oga KB nake, kuma yace lallai wannan itace damarmu ta karshe akan Jalal, yazama dole muyi yadda zamuyi mukammala aikin nan," hannah ta dan nisa ta cire glass din fuskarta, sannan tace "Idan ban mantaba shekaru uku zuwa hudu muna aikin nan, duj wani salon makirci, da kisisina ba wanda banyi ba, tunda nafara bariki, bantaba ganin dan bala'i ba kamar Jalal, ban taba haduwa da mutum me azabar taurin kai ba kamar Jalal, babbar nasarar dana samu a rayuwa akansa shine, a labarin daka bani, bayan sauyawar Jalal, ina cikin jerin matan daya sake dasu, har yake shiga harkata, amma naiyi iya kokarina alakarmu ta wuce haka amma yaki yadda, ni yanzu bani da wata dabara, Nagama nawa, bansan meye shirinka ba" "Hakane Hannah, nasan kinyi mana aiki, kinyi iya yinki kinmana kokari, abaya a koda yaushe ina galaba akan sa amma yan shekarun nan, nafara ganin sauyi a tareda shi, koda nagama aikina akan Jalal, sena tabattar da nayiwa Jawwad babbar illa shima, saboda tsawon wannan shekarun shiya hana cikar burin mu, Jalal yanajin maganar Jawwad fiye data uwar data haifeshi, wadda ita ta haddasa komai, " " Baka ganin ina aka cutar da Jawwad ba a masa adalci ba, shi meye nasa aciki " " yana da laifi Hanna kuma dole ya karbi hukunci, yanzu ki tsaya ki saurareni" "ina jinka" "a gurin birthday din damuka shirya masa komai ze kare," hannah ta kalleshi sannan tace "bangane mekake nufi ba" "zaki gane ne Hannah, nagama shirya komai, kinsan meze faru?" "No seka fada" "kamar yadda muka shirya, shabiyun dare zamu fara gabatar da taron, a cikin cake din dazamu bawa Jalal ke zakiyi wannan aikin, zaki saka kwaya, a dai2 inda za a bashi, saboda sonake ya bugu ya fita hankalinsa yadda baze iya komai ba, za sakama a lemon da zs sha, da zarar ya fita hayyacinsa zamu dauke shi, mu kaishi wani gurin, kekuma zaki gabatar da aikinki" Dan tsaki Hannah tayi "Ni gaskiya ba a haka naso aikin yazo ba" "to ya za ayi se hakuri, tunda shi dan taurin kaine, zamu nuna masa munfishi iya bariki" Wayarsa ce tafara ringing, jeje ya kalli Hannah "Dan halak shike kirana" Tai murmushi tace "Pick it" Dagawa yayi yasa a hands free "Allah ya temaki, mazaje, namijin duniya sha gwagwarmaya, namjin damusa bakason raini"  Jalal yace "Kai Jeje ya isa haka, magana nakeson yi maka akan maganar partyn nan" "ok inajinka" "Munyi magana da Jawwad, dan haka dole a maida shi eight Jawwad yace baya son ya kai karfe shabiyu in bahakaba baze attending ba, dan haka ina so amaida shi eight pm, saboda inason Jawwad ya kasance a gurin" What!!!!!!! Jeje yafada da karfi yana mikewa tsaye Share please More Comments More typing............................. Akodayaushe kuna raina masoya comments dinku ke bani karfin gwiwa da sani nishadi, amma in naga ba kwa comments sosai, se inji kamar inkoma posting duk sati 😂😂😂😂😂 Ina godiya da adduoi Allah yabar kauna 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/23, 10:45 PM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  49 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680 Ina godiya matuka Allah yabar kauna Ina amfani da wannan dama, domin mika ta a ziyyata ga yan uwa mutanen zazzau da dukkanin al ummar musulmi, na rashin sarkin zazzau Alhaji shehu idris, ina fatan Allah ya jikansa yasa mutuwa hutuce, dashi da dukkanin al ummar musulmi da suka gabacemu Allah ya rahamshesu in tamu tazo Allah yasa mucika da imani               _My first novel_ Jalila na zuwa dakinsu ta kife akan gadonsu, "Nikam Jalila nashiga uku, wace kaddara ce ta kawoni kano har nasan Jalal ne, wanda har rayuwarsa take neman hanamin tawa nutsuwar, Ummi dan Allah in kina raye duk inda kike ki dawo, nagaji da zaman nan ina cikin damuwa, Allah ka temakeni, kabani ikon jarraboyina na rayuwa" Ta karasa maganar tan zubda hawaye, tayi me isarta sannan ta mike ta duba wayarta ta kira Hanan, seda ta kusa katsewa sannan Hanan ta daga, tana dagawa tace "Tace afuwan ranki ya dade, ina wankane, ya jiki Jalila? " Da sauki Hanan, ya Baba na dasu Abdallah " " Baba baya gari yana bauchi, Yaya Abdallah ma haka dagani se mummy, ya jikin kinji sauki" "jiki Alhamdilillah na warke ganima a gida" "masha Allah, nakira Jawwad nace ya hadani dake amma se yacemin ba kya kusa, siyama ma takiraki bata shiga ki kirata dan Allah" "zankirata Insha Allah" Hanan ta ce "nikan Jalila meyasameki haka har ya kai ga kisamu stroke ko wani abu na damunki ne?" Se Jalila taji kaman Hanan ta sosamata inda yake mata kaikayine, batasan lokacin da hawaye yafara fita daga idonta ba "Hanan ni meye ma baya damuna, ko kinsan cewa a halin yanzu sati biyu kenan, bansan inda ummi takeba ko a raye ko a mace ban saniba" "Kamar yaya baki saniba, naje gidan fa ranar dazata taho kano, tacemin zatazo kuyi sallama zata wuce garinsu, kuma kice bakisan inda take ba" "Hanan tunda Ummi ta tafi, mukayi waya da ita, wayanta be kara shiga ba anyi trying har angaji, karshe aka kira Abba aka gayamasa, wai wani me mota ya bigeta, kuma ya dauketa ya tafi da ita, bawanda yasan ina ya kaita, kotana raye kota mutu bamu saniba" "Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Jalila meyasa baki gayamin ba tunda wuri, kuma angayawa"yan sanda"? "Hanan Abba yana iya kokarinsa amma har yanzu ba labarin Ummi ni harna hakura na fawwalawa Allah komai" "kiyi hakuri Jalila, nasan abun da wuya a gurinki, amma mucigaba da addu a, insha Allah za a ganta, in daddy ya dawo zan sanar masa koda wani abu da za a iyayi akan matsalar, kiyi hakuri, Jalila insha Allah ummi tana raye za a ganta". Hanan ta ke rarrashin Jalila yayinda itama take zubarda hawaye, har cikin zuciyarta takejin matsanancin tausayin Jalila, "Addu a ina nan inayi hanan, sedai kuma ina bukatar taku adduar" "Insha Allah zan tayaki addu a, kinji kidena damuwa sosai, kar wani ciwon yakamaki" "Karki damu kanwata na fawwalawa Allah komai, shi ze bani mafita" "Masha Allah haka akeso queen muzama masu karbar kaddararmu a duk yadda tazo mana," domin kokarin kauda damuwar Jalila, se tace mata "nace ya gidannaku, ya mutuminki?" "waye kuma mutumina?" "kinfini saninsa Jalal mana" "Yana gidansu" "kai queen har yanzu kina masa rashin mutunci ko?" "ko jiya ma seda mukayi, yau kuma wannan mahaukaciyar kanwar tasa tazo zatamin hauka, wai ita alallai son Jalal nake, wai in ban fita harkar saba seta sani kuka kiji fa," Dariya Hanan tayi, sannan tace "queen J nasanki da kafiya, dan Allah karki bari Ilham tayi nasara, kizama silar shiryuwar Jalal, u can do it, kibata mamaki, kamar yadda kika bani" "ke nina fara gajiya, gashi jarababbe, ga taurin kai gashi mugu, itakuma gani take sonsa nake ko uwar me zanyi da wannan makakken, dan wahala daga ita harshi" "A a dai, banda cika baki, daga baya kizo kina zare ido akansa" "Kut me kike nufi, mezanyi da wannan Allah ya rufamin asiri" "Oho dai inda rabon an jone ne.... Jalila bata bari takarasa ba ta kashe wayar tareda fadi" ji muguwa zatamin mugun baki, ta Allah ba taki ba" Daga haka Jalila ta Mike ta fito palour don samun dan abunda zata ci, Maama tana palour a zaune tana kallon Aljazeera, Jalila tace "Maama sannu da gida" Kallon Jalila tayi ta dauke kai ba tareda ta amsa mataba, har Jalila zata wuce kitchen, Abba ya shigo, ya dawo da wuri yau, da alamu ko mantuwa yayi, Jalila tace "Abba sannu da zuwa" "yawwa Jalila ya jiki ya gidan," "lpy qalau Abba" Maama tacewa Abba "Sannu da zuwa" Banza yayi mata da nufin shigewa dakinsa, Jalila tai farat tace "Abba, Maama na maka sannu da zuwa fa, bakace komai ba" Abba ya wayance da "Yawwa maman Yara, yi hakuri banji bane" ya wayance kar Jalila ta gane, sannan yace "Jalila dan kiramin Jawwad, kice ina son ganinsa, a dakina" "To Abba bari inje" Jalila ta tafi part din Jawwad, Jalila na fita Abba ya shige part dinsa ya bar Maama a palourn, binsa tayi itama, tana kuka, Abba ya kalleta "meye haka zaki biyoni kina kuka, se yaranki sunce wani abun nayi miki" "Meyema bakayimin ba ina tabinka ina baka hakuri amma kaki kulani, sati kusan biyu kana gaba dani, kaki saurarata haba Abban Jawwad, dan Allah kayi hakuri, kadena fushin nan haka" Kukan dayaga tanayi seta bashi tausayi, "Zainab, komenayi miki ke kika jawa kanki, nima ba a son raina naimiki hakaba sedan in nunamiki kuskurenki, akan abunda kikayimin," "kayi hakuri hakan baze kuma faruwa ba Insha Allah" "Zainab kenan indai halinki ne ba wanda ban saniba, bana tunanun wannan maganar har cikin zuciyarki"   Jalila tana zuwa part din Jawwad ta tarar suna fada da Jalal, "JALAL dan me zasu shirya maka wani birthday, dacan ma aibasu suke hada maka ba, bayan kasan mutanan nan bana kirki bane, su kaika wani guri su hada maka birthday kuma ace shabiyun dare haba Jalal kayi tunani mana," "Jawwad ya kakeso inyine? Sokake ince musu bana so ko inki zuwa, ko wa akayiwa haka baze ji dadi ba, mene a ciki abu na lokaci daya ayi a watse, basu taba hadamin ba, wannan karon sunmin se ince banaso, kana ganin idannayi hakan na kyauta, shikenan bance kaje dole ba fa, dama zuwa wannan gurin da daddare ai da irina ya dace ba da kai ba" daga haka Jalal ya juyo fuuu ze fita, da sauri Jalila ta bashi hanya kar ya bigeta, bayan ya fita ta shiga palourn, Jawwad yanemi guri ya zauna yayi shiru "yaya Jawwad ya dai? " Bari Jalila, Jalal ne yake neman ya cazamin kwakwalwa, kullum fatana in janyeshi daga jikin wannan miyagun abokannasa shikuma yana kara shige musu, " " Meya farune? " " Wai an hada masa birthday, se sha biyun dare zasu fara har gari ya waye, kuma a baya tare muke hadewa muyi dashi kuma  a gida amma wannan karon wai su suka shirya masa, nasan kwana zasuyi shan giya, nace kar yaje kuma yana neman yayi fushi, seyaje yai tayi ai, am tired da halin Jalal" Sosai taji tausayin yayan nata, taga kokarinsa ma tsawon wannan lokacin yana tareda Jalal, duk da miyagun halayensa, ga shi da wuyar sha'ani amma haka Jawwad yake tare dashi, kuma tasan wannan fushin na dan lokacine, dole se daya ya nemi daya, ta numfasa tace "Yaya Jawwad ai be kamata kayi fushi ba fa, tunani yakamata kayi, tsawon shekaru suna tareda shi basu taba cewa zasu shiryamasa birthday ba se wannan karon, kuma ma wai se tsakiyar dare zasu fara, baka tunanin wani abun suka shirya akansa? Bakayi tunanin suna da manufar yin hakan ba? Kn kayi fushi kace yaje yaitayi, kaga sunyi galaba zasu kara janyeshi, shikenan yazama  nasu gabadaya" Shiru Jawwad yai yana kallon Jalila Taci gaba da cewa "Kayi tunani yaya na, dan uwanka ne fa, u have to think" Ajiyar zuciya yayi "Hakane baby kema kinyi magana, amma yanzu me yakamata inyi" Jalila aranta tace yawwa, nima ga dama ta samu, A fili tace, "Yaya dole ka shiga cikin lamarin nan, kawai ka yadda da maganar birthday din nan, ka lallabashi kasashi a maida partyn kaman daga karfe ta kwas zuwa goma, sannan dolenka ka halarci gurin domin sakamasa ido, in takama har abokanan ku da yanuwa ku gayyata, hakan ze hana faruwar wasu abubuwan, karfe goma nayi, ka janyeshi daga gurin, yanzu kayi hakuri ka sakko, har ya gaya maka shirye2 da sukeyi, kaima seka san shirin dazakayi, amma inka barshi ya tafi shi kadai jikina na bani akwai dalilin dayasa suka shirya hakan, sun san babu wani dan uwansa daze yadda ya bishi guri irin wannan karfe shabiyun dare" Murmushi Jawwad yayi, tareda yiwa Jalila salute "Gaskiya baby kina da tunani me zurfi, hankalina be kai kan hakan ba ni, gaskiya nagode, zan jarraba insha Allah" Murmushi Jalila tayi "nifa aikoni akayi, Abba yace kazo yanzu" "To shikenan ina zuwa"   A ranar bayan Jawwad yaje kiran Abba, ya je yanemi Jalal suka shirya, yace masa ya yadda, zeje birthday dinsa amma gaskiya zasu gayyaci mutane, dan haka sedai a canza lokacin daga shabiyun dare zuwa karfe takwas, Jalal yace ya yadda.    "Jeje wannan ce dama ta karshe dazan baka, a wannan karon banason asamu kuskure, dukda tsawon shekarun nan kayi aiki tareda ni, kamin duk abunda nake bukata to wannan karon, sonake komai ya kare, sonake a wannan lokacin komai yazo karshe, karka bari wannan shirin ya rushe, " " Oga kb baka da matsala, munyi iya kokarinmu gurin ganin hanyoyin dazamubi domin gabatar da aikin cikin shiri, burinka ze cika, a wannan ranar zamuyi yadda zamuyi muga mun karasa wargaza rayuwarsa, " Wanda aka kira da oga KB ya gyara tsayuwa yai ajiyar zuciya " shikenan ina jira zan saka ido inga kokarin ka, a wannan karon, aje acigaba da shiri," " Shikenan oga, wannan karon komai zezo karshe" Daga haka sukayi sallama, Hannah na gaban dressing mirror tana kwalliya, Jeje ya kirata, seda ya kira sau uku tana kallon wayar sannan ta dauka "Hannah ina kika shiga ne inata kiran wayarki, ya za ayi mu hadu ne?" "mu hadu kuma, akwai matsala ne?" "eh haduwar tamu tanada mahimmanci sosai, akan shirunmune, yanzu haka daga gurin oga KB nake, akwai bukatar mu hadu" "To zanzo, muhadu inda muka saba" "To shikenan sekinzo"          Ilham se safa da marwa take, a cikin dakinta, ta rasa inda maganganun Jalila suka dosa, tace ita ba son Jalal take ba, amma itama tanada kuduri akansa, kuma inyaci karo da nawa, to tabbas zata rusa nawa, koda tazo nan a tunaninta seda ta zare ido, ta rusa nawa burin saboda nata muradin, to ko ta san menene shirina ne, to amma tayaya zata sani bayan ko Nana bata saniba, Dakko wayarta tayi, zata kira yaseera, sekuma ta fasa, dole in dau mataki, bazanyi wahalar banza tsawon shekaru ina kallo wata sakarya ta rusamin shirina ba, gara tun yanzu in rusata ita danata shirin, ta mike da sauri ta nufi dakin mummy, tana zuwa ta tura kofar dakin, ta sameta tana waya, taje kusa da ita ta zauna, tana jiranta tagama, Seda mummy tagama waya, sannan ta kalli Ilham tace "Ilham ya akayine, naganki wani iri haka kaman mara lafiya" Fashewa tayi da kuka, ta fada kan cinyar mummy "Mummy wallahi nakusa mutuwa, in har yaya Jalal be aureni ba, zan iya mutuwa, Mummy ina sonshi, dan Allah asaka ranar aurenmu," "Yi shiru kiyi hakuri, kinji nima naga kamatar yin hakan, kila in kika aureshi ma ya shiryu sanadin haka, yanzu kidena kuka, bari daddynku ya dawo, muga me yakamata ayi, amma karki kuma zance zaki mutu saboda shi, aini na miki alkawari, indai ina raye Jalal shine mijinki, indai nina haifeshi baze taba auren wata mace inba keba, kidena kukan nan haka ya isa" Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Ilham tayi, tareda yin murmushi a boye, a fili kuma tace "dan Allah mummy asaka da wuri, ina tsoron ya auri wata baniba," "ki kwantar da hankalinki, shi kinga alamar ma zeyi soyayya da wata, ko kina tunanin akwai wadda zata aureshi a haka, aini kingama min komai da kikeson Jalal a haka, dan haka bari daddyn sa ya dawo, zamuga yaushe yakamata asaka" Ilham ta riko hannun mummy, "Nagode sosai, mummy" "bakomai, kidena kuka"    Hannah zaune akan fararen kujerun dake  gurin, fuskarta dauke da wani arnen glass dayake barazanar cinye fiye da rabin fuskarta, ga barima da tasaka a akan dogon hancinta, se tauna chew gum take, tana fuskantar Jeje, "Hanna daga gurin oga KB nake, kuma yace lallai wannan itace damarmu ta karshe akan Jalal, yazama dole muyi yadda zamuyi mukammala aikin nan," hannah ta dan nisa ta cire glass din fuskarta, sannan tace "Idan ban mantaba shekaru uku zuwa hudu muna aikin nan, duj wani salon makirci, da kisisina ba wanda banyi ba, tunda nafara bariki, bantaba ganin dan bala'i ba kamar Jalal, ban taba haduwa da mutum me azabar taurin kai ba kamar Jalal, babbar nasarar dana samu a rayuwa akansa shine, a labarin daka bani, bayan sauyawar Jalal, ina cikin jerin matan daya sake dasu, har yake shiga harkata, amma naiyi iya kokarina alakarmu ta wuce haka amma yaki yadda, ni yanzu bani da wata dabara, Nagama nawa, bansan meye shirinka ba" "Hakane Hannah, nasan kinyi mana aiki, kinyi iya yinki kinmana kokari, abaya a koda yaushe ina galaba akan sa amma yan shekarun nan, nafara ganin sauyi a tareda shi, koda nagama aikina akan Jalal, sena tabattar da nayiwa Jawwad babbar illa shima, saboda tsawon wannan shekarun shiya hana cikar burin mu, Jalal yanajin maganar Jawwad fiye data uwar data haifeshi, wadda ita ta haddasa komai, " " Baka ganin ina aka cutar da Jawwad ba a masa adalci ba, shi meye nasa aciki " " yana da laifi Hanna kuma dole ya karbi hukunci, yanzu ki tsaya ki saurareni" "ina jinka" "a gurin birthday din damuka shirya masa komai ze kare," hannah ta kalleshi sannan tace "bangane mekake nufi ba" "zaki gane ne Hannah, nagama shirya komai, kinsan meze faru?" "No seka fada" "kamar yadda muka shirya, shabiyun dare zamu fara gabatar da taron, a cikin cake din dazamu bawa Jalal ke zakiyi wannan aikin, zaki saka kwaya, a dai2 inda za a bashi, saboda sonake ya bugu ya fita hankalinsa yadda baze iya komai ba, za sakama a lemon da zs sha, da zarar ya fita hayyacinsa zamu dauke shi, mu kaishi wani gurin, kekuma zaki gabatar da aikinki" Dan tsaki Hannah tayi "Ni gaskiya ba a haka naso aikin yazo ba" "to ya za ayi se hakuri, tunda shi dan taurin kaine, zamu nuna masa munfishi iya bariki" Wayarsa ce tafara ringing, jeje ya kalli Hannah "Dan halak shike kirana" Tai murmushi tace "Pick it" Dagawa yayi yasa a hands free "Allah ya temaki, mazaje, namijin duniya sha gwagwarmaya, namjin damusa bakason raini"  Jalal yace "Kai Jeje ya isa haka, magana nakeson yi maka akan maganar partyn nan" "ok inajinka" "Munyi magana da Jawwad, dan haka dole a maida shi eight Jawwad yace baya son ya kai karfe shabiyu in bahakaba baze attending ba, dan haka ina so amaida shi eight pm, saboda inason Jawwad ya kasance a gurin" What!!!!!!! Jeje yafada da karfi yana mikewa tsaye Share please More Comments More typing............................. Akodayaushe kuna raina masoya comments dinku ke bani karfin gwiwa da sani nishadi, amma in naga ba kwa comments sosai, se inji kamar inkoma posting duk sati 😂😂😂😂😂 Ina godiya da adduoi Allah yabar kauna 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/24, 8:35 PM] Ayshercool: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  50 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680                _My First Novel _ Jalal yace "Lafiya naji kana wani what, ko baka gane menace bane?" "Amma meyasa zakayi manaa haka Jalal, mun riga mungama shirya komai, sannan kace wai se a maida shi eight, haba Jalal dan Allah, dolene se Jawwad yaje gurin, mene a ciki dan munyi iyamu da abokanmu yanzu.... " Kaga Jeje ba dole ai bani na rokeku ba dama tun farko dan haka, inbazaku canza lokacin ba bazan zo ba" yana zuwa nan ya kashe wayarsa, jeje ya daki tabur ya zuba ashar, "kingani ko Hannah wallahi dole a hukunta Jawwad, a koda yaushe shi ke bata mana shiri," Hannah tace "Kaga kaifa fushi banaka bane a yanzu, ka yadda kawai, in ba hakaba wannan damar ta wuce aiki ze kuma komawa baya, gara ka kirashi kace ka yadda" , jinjina kai Jeje yayi "Shikenan amma Jawwad seyaga abunda zanmasa" Haka jeje ya kira Jalal, yace masa sun yadda, Washe gari babu zato babu tsammani, Daddyn Hanan sukazo shida Abdallah, suka duba Jalila, taji dadi sosai da zuwansu, dukda ba wani dadewa sukayiba, dayake hanan  gaya masa abunda yasamu Jalila, daga bauchi suka dawo suka biyo suka tsaya a kano domin dubata, Daddyn Hanan yace Insha Allah shima ta bangarensa zesa aimasa bincike game da batan Ummin, sannan yaita rarrashin Jalila tareda yimata nasiha, Daddyn Hanan yacewa Abba "gaskiya wataran zanzo kabani Jalila, mutafi da ita bauchi, gurin kakarsu Hanan, itama taga wannaan kamannin nasu, daga bata labarin Jalila se magiya take dan Allah akaita ta ganta, dayake ta tsufa bata iya fita aida da ita zamu taho" Abba yace "Allah sarki insha Allah randa kuka shirya kuzo ku kaimata ita" "To shikenan, nagode kwarai da karamcinka Alhaji usman" Sukayi musu sallama suka nufi kaduna Kwanan su Abdallah biyu da zuwa, su Jalila suna cikin farin ciki, sun samu admission a BUK daga ita har  Nana, ranar litinin zasu fara zuwa makaranta, Abba yayi musu nasiha sosai game da rayuwar dazasuyi a cikin Jami a, ita Nana mass communication zatayi, itakuma Jalila catering craft zatayi, da farko Jawwad yaita mata mita akan mezatayi da wani catering duk kwakwalwarta, itakuma tace shi takeso, dan tana son harkar girke2 da sanao'in hannu. Anata shirye2 birthday Jalal, Yanzuma Jalal ne da Jawwad a harabar gidan akan fararen kujeru, suke zancen yaya birthday din ze kasance, Jalila ta fito zata fita, "Yaya barka da yamma" "Yawwa baby ina zuwa haka?" "Maama zan karbowa kaya, a jambulo" "Bari mu tafi tare, semu ajiyeki dama fita zamuyi" "To yaya, bari inje waje in jiraku" Jawwad ya kalli Jalal, "Dakko motar, bari inje insaka kaya" Jalal ya fito da motar waje, Jalila bata shiga motar  ba tana tsaye a waje har Jawwad ya fito, suna shirin tafiya sega wani abokinsu Jawwad yazo wucewa, tsayawa yayi suna gaisawa, dayake  tsohon abokinsune kuma sun dade basu hadu ba, Jawwad yace "kai faruk ba a ganinka ko a gari, ina ka shige haka ne?" Wanda aka kira da faruk yai dariya "ina nan Jawwad, makaranta ce munata fama, kasan yanzu ina ABU zaria bana zama sosai a kano, yanzuma wani filin baba mukazo gani unguwar taku, Jalal nema bana ganinsa sam" Jalal ya kalli Faruk ya danyi murmushi, sannan yace "Nima ina nan haduwa ce dai tai wuya, ya karatun? " "Alhamdilillah Jalal, y garin, ya karatu ko har yanzu baka koma makarantar ba" Jalila dai na tsaye jikin mota tana jinsu, Jalal yace "Gari gamu a cikinsa, makaranta kuma bana zuwa har yanzu" Jawwad yace, "Faruk, yana Jalal yana shirin komawa makaranta kwanan nan insha Allah" "To Allah yasa" Jawwad yace "au Jalal nayi mantuwa, bari inje in dakko wayata, ka karbi lambar faruk mudinga gaisawa" Jalal yace "Ok seka fito" Jawwad ya shiga gida, faruk ya kalli Jalal, yace "Jalal wannan kuma wacece?" jalal ya dan kalli Jalila sannan yace "gata nan tambayeta mana" "Hmm Jalal halinka yana nan dai" faruk ya kalli faruk "y'an mata yakike? " "Lafiya kalau" faruk yakuma cewa "Jalal ban san wannan ba, kanwarka ce kota Jawwad, kokuma.... Jalal ya katseshi ta hanyar cewa " kai faruk, kaima surutun nan naka yana nan da shegen son mata" dariya sosai faruk yayi, ana haka sega wata mota tazo wucewa, amma akayi parking mutumin ciki ya fito, babban mutum ne, ya tunkaro su a fusace da farko faruk be ganshiba seda gabaya, dan bude baki yayi ya zaro ido, mutumin yana zuwa ya kalli Jalal sannan ya kalli faruk, "Kai faruku, ban hanaka kula wannan dan iskan yaron ba, danayi sa a na rabaka dashi, shine yauma kakuma lallabowa, gurinsa ko, sekaima ka lalace kamar sa, kai ko kyamarsa ma bakayi, dubeshi kana kallonsa kaga mutumin banza wuce kabar nan gurin ko in kifa maka mari, " Faruk ya fara in ina" A a Bab... Baba, dan Allah kayi hakuri, gaisawa kawai muke "Zaka wuce ko sena marekan, nahanaka hulda da yaron nan, inkuma kaima kafara shaye2 ne kaima se inji, ba Shiri faruk yai gaba, yana waiwayensu Jalal dai bece komaiba ya sunkuyar da kai yai shiru, Haka nan se Jalila taji ba dadi, mussaman da Jalal ya sunkuyar da kansa bece komai ba, Mutumin ya juyo ya kalli Jalal, ya nunashi da yatsa "kaikuma bakai ba dana, idan nakuma ganinka dashi wallahi hukuma ce zata rabamu da kai, dana ba lalatacce bane ba kamar kai, ni dana kamiline, baze yiwu ka koyamasa shaye2 da rashin tarbiyya ba," Jawwad ne ya kawo kai ya fito ya tarar da cin zarafin da akewa Jalal, tsayawa yai cak yana kallon ikon Allah, mutumin ya cigaba da bala'i " ni banyi sake ďana ya lalace ba dan haka bazan bari ka lalata min shiba, niba nusarin ubane ba kamar ubanka, daya bari ka lalace kalleka, kowa ya ganka yaga dan iska mara tarbiyya sha3" harzuka Jalal yayi, ya kura ma baban faruk ido, amma abun mamaki still Jalal yaki cewa mutumin nan uffan "Shima baban nasa bashi ya saiwa kansa ba, kuma ba laifi yayiwa Allah ba ya jarrabeshi da fitinanne yaro ba, haba baba, a haka gaka dattijo amma aji wannaan maganganun suna fita daga bakinka, to in Allah ya doramaka ya zakayi? Akan wani dalilin zaka dinga zaginsa dan kawai ya gaisa da danka, shi Jalal din shi yaiwa kansa, ka gayamin wanda akayi shawara dashi kafin a halicceshi, ko kaddara abunda ze faru a rayuwarsa" Gaba daya ido suka zuba mata baki bude, suna kallonta, tsagwaron bacin raine kwance a idonta, bil hakki take fadan maganganun da take, kana kallonta kasan har zuciyarta ranta ya baci, Jawwad ne yai yunkurin cewa "Jalila meye haka, ba kya ganin babban mutum ne? Baba kayi hakuri insha Allah Jalal baze kuma... " Wai yaya Jawwad laifin me akayi masa kake bashi hakuri, ABDUL JALAL ne ya taka kafa yaje inda dansa yake kokuma shi yakawo kansa, baba irin wannan abubuwan da akewa mutane irinsu Jalal shike kara lalatasu, yazama bame jansu a jiki, kowa se kyama da tsangwama, danka da kake fada akansa ma mutum ne, kuma baka isa ka hana Allah ikonsa akan shiba, in Allah ya jarrabeshi shima, yazakayi a ganina in bakayimasa addu a ba bekamata ka zage shi haka ba, da kake cemasa mara tarbiyya kazagi mahifinsa da ya dau mataki akanka fa, kasan a hakan nan se ya zageka tsaf bazaka iya masa komai ba, kuma kaga hakan baze maka dadi ba" Jawwad yace na shiga uku, halin Jalila yana nan ashe, bata canza ba, shiru2 da take na kewar Ummi ne ashe, yayinda Jalal yai shiru yana satar kallonta, Jawwad yace "Ke kiyimin shiru, meyasa kike haka, sa ankine" Baban Faruk yace, "Kyaleta i like her confidence, kin birgeni sosai yarinya at least, kin tunamin abunda na manta, nagode sosai" ya kalli Jalal yace "Am sorry my son, nasan na bata maka rai, kayi hakuri" yajuya ya wuce ya hau motarsa ya tafi Jalal be taba tunanin tsiwar Jalila ta kai haka ba, babban abunda yabashi mamaki yadda ta zakakalkale haka, bayan itama rashin mutunci takemasa, juyawa tayi ta bude bayan mota ta shige abunta kamar batayi komaiba, Jawwad yacewa Jalal "taho mu tafi" ba musu Jalal ya bishi, amma Jawwad ya zauna a mazaunin direba, Jalal yana kusa dashi, Jawwad dan waigo ya kalli Jalila sannan yace "Baby ya haka, abunda kikayi kin kyauta kenan? Babban mutum ne fa, haba baby dama baki canza ba?" "ka taba ganin an haifi mutum da hali ace ya canza, in tsoho beji kunyar hawa jaki ba jaki baze ji kunyar kada tsohoba, a matsayinsa na babba abunda yayi ya dace kenan, kozakayiwa mutum rashin mutunci karka hada da mahifinsa, shima daganinsa kaga criminal idonsa kawai zaka kalla kasan ba mutumin kirki bane" Shi Jawwad Jalila ta dena bashi mamaki tsoro take bashi "Ke Jalila ya akayi kikasan criminal ne, karki kuma, baban wanine koba komai ya haifeki" "Yaya nifa ba karya nayiba bakaji yadda yake magana ba ne? Shima wannan nusarin Jalal din yanaji ana zaginsa yai shiru, inkaga yana masifa to akan Matane, yadinga wani muzurai, matsalar mutum ya dinga abunda bashi da kyau kenan wanda ya isa da wanda be isaba sunemi suci mutuncinka" Bude baki Jawwad yayi ya waigo yana kallonta, dama haka take, tunda ake fadar iya tsiwa na Jalila be taba tunanin ta kai nan ba, rasa bakin magana yayi, shikuwa Jalal ko motsawa beyiba daga inda yake balle ya nuna yasan dashi take, sema tunani da yayi zurfi a ciki, amma yana jin duk abunda take fada, haka motar tai tsit har sukaje jnda zasu sauketa, tace "Yaya Jawwad ka jirani man in shiga in karbo, semu tafi bannaa son tafiya ni ka dai, kasan ban san kan garin  nan ba" "gashi kuma ba gida muka nufa ba, zamuje siyayya ne" cikin shagwaba tace " eh naji, ko ina zakuje dai, dan Allah kujirani" "To yi sauri karkimin kuka" tayi murmushi ta bude motar ta fita" Jawwad ya dan kalli Jalal sannan yace "Jalal, Jalila ba karamin mamaki ta baniba, ban taba zaton zata iya haka ba, babban mutum kaman wannan sam bata da tsoro, amma kaima bazan gaji da baka hakuri akan abubuwan datake yimaka ba, kuruciya na damunta, har yanzu yarinya ce" "Wane kalan kaya kakeso musaka ranan, so nake muyi shiga iri daya" "A a ya ina maka magana kaikuma kana min wani zancen daban" "Kasan akwai kaya da daddy ya turo dasu zamuje mu duba, in bamu samu wanda mukeso ba semu siyo wasu, i wish daddy yana Nigeria zanyi birthday" Jawwad ya fuskanci Jalal rainin hankali yakeji, wato baya son wancan zancen da sukeyi, dan haka ya rabu dashi.   Bayan barin Alhaji kabiru gurin nan, ya dinga tunanin wace wannan yarinyar haka, wace ce ita, mene alakarta da Jalal haka, wayarsa ya dakko ya kira lambar Jeje, bugu biyu Jeje ya dauka, "Allah ya temaki, oga KB" "Jeje tambayarka zanyi" "to Oga Allah yasa nasani" "akwai wata yarinya danagani a gurin Jalal, ko kasan wacece dinsa" "ya take oga?" Ya fasalta masa siffar Jalila, jeje yace gaskiya be santa ba amm ze bincika masa. Jalila ta fito, tazo ta bude motar ta shiga, Jawwad yace "har kinfito" "Eh Yaya banason bata muku lokacine" Jawwad ya kunna mota, suka hau titi, suna hirarsu da Jalal, aka jima se cewa tayi "waimu ba za a gayyacemu bane?" Jawwad yace "mu mun isa dole a gayyace ku mana" "hadasu Nana, da Ilham" "Eh mana hadasu" shidai Jalal bece uffan ba, baze so zuwan Jalila gurin nan ba dan yasan tabbas setayi surutu intaga abunda be mata ba, kuma yasan dole ayi shaye2 a gurin, meyasa Jawwad ya amsa mata suje gurin nan, a titi suka sauketa, sukuma sukayi gaba, ta dade tanajira sannan ta samu napep ta karasa gida, a palour ta tarar da Maama da Abba ta kaiwa Maama kayan, Abba yana mata sannu da zuwa, Maama ta bubbude kayan ýan kunnaye da sarka masu matukar kyau, Jalila tace "Maama bari in daukesu a waya a tura social media, za a samu costumers tunda new design ne" dayake a gaban Abba ne se Maama ta sakar mata fuska, "eh hakan yayi kyau, in anjima dan Allah ki mikawa mummy, dama saboda ita nasa aka karbosu tacemin ana so" "to shikenan bari inyi salla" harta mike zata tafi, Abba ya kirata ta dawo Yace "daukar muku, keda Nana kowa biyu, se a gayamin kudin" "to Abba mungode Allah yasaka da Alkhairi, Allah yasa afi haka" "Ameen ya Allah, Allah yayi Albarka" Jalila ta tashi ta tafi dakinsu, yauma Nana bat nan, Jalila tayi salla taci Abinci, ta kwanta tana hutawa, ta dau wayarta tana ta tura kayan nan social media a haka har bacci ya dauketa   Jawwad sun sha yawo, shida Jalal se kusan la'asar sannan suka dawo sun gaji matuka, sallar la'asar sukayi, sannan Jawwad ya kira Jalila a waya yace dan Allah akai musu Abinci, ji tai kamar tace A a saboda batason yawan zuwa inda yake tunda mahaifiyarsa bata so, amma Nana bata nan Halima ma haka, badan haka ba da bazataje ba, "to Yaya gani nan zuwa, bari in kawo" "to shikenan muna jira" Jawwad ya kalli JALAL, bari in shiga in dan watsa ruwa kafin ta kawo abincin" Jalal yace "to kifi, sarkin ruwa seka fito" befi 3min da tafiyar Jawwad wanka ba Jalila ta shigo da kayan Abinci, tai sallama amma Jalal ya mata banza dama bata sa ran ze amsa ba, ta ajiye Abincin, harta juya zata fita taji muryarsa "Ke zo nan" kutmelesi wai ke, juyowa tayi da niyyar yi masa rashin mutunci, kawai taga yamata wani mugun kwarjini, gashi ya kafeta da ido, "gani mene?" tazo kansa ta tsaya tana zumbura baki, hannayenta ya janyo da karfi seda ta durkusa akan gwiwoyinta, seda ta danyi kara ta dago ta kalleshi tareda fizge hannunta, saboda taji zafi "Idan na kuma kiranki, kikatsaya min aka, kamar itace sena miki abunda zaki karye, mara kunya kawai" kallon up and down ta masa ta dauke kanta "Ubanwa kike cewa nusari dazu, wait tukuna ma, uban wayasa kiyiwa mutumin nan rashin kunya, ke yayiwa koni, meye alakarki dani da zakiyi wa babban mutum kamar wannan rashin kunya, inkinyi dan ki birgeni ne, to baki birgeba dan JALAL bayasin shishshigi" Murmushi Jalila tayi wanda yai matukar yi mata kyau, "wayace maka saboda kai nayi, aini birgeni yayi da yayi maka haka, kasan wanda yasan darajar dambu shike zuba masa mai, duk inda naji ana cin mutuncin iyaye koba nawa bane raina baci yakeyi, saboda karya zarce da zagin daddy shiyasa nai magana domin dakatar dashi, ba wai dan kai ba, kwakwalwarka ta dinga lissafa maka dai2 mana" kuramata ido yayi baya ko kiftawa, sekuma yayi dariya "Karya kikeyi, idonki ya nuna abunda kike fada  a yanzu karyace kawai, Sekuma ya hade rai " Zan miki wani kashedi, idan kika kuskura kikazo gurin birthday na duk abunda yasameki kekika jiyowa kanki, danban gayyaceki ba, tashi kbmibani guri, mummuna uwar magana kawai" mikewa tayi ta danyi gaba sannan ta waigo ta kalleshi "wallahi senaje, ai ba dan kai zaniba, saboda yaya Jawwad zani, tunda shi yace inje, dayake abun na rashin gaskiyane shine wai ba a gayyaceniba, to wallahi senaje, inyaso in naje a dakeni, ragon maza kawai nusari. Share please More Comments More Typing.............................. 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🌹[9/26, 8:49 PM] Ayshercool: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  51 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680                _My First Novel _ Tana gama fadin haka ta juya tai tafiyarta, dan girgiza kai Jalal yayi, ya cigaba da danna wayarsa, Jalila na komawa taga Maama tafito daga kitchen "Ke daga ina kike?" "Yaya Jawwad ne ya kirani yace in kaimasa Abinci" tsaki Maama tayi sannan tace "inkinyi sallar magariba, ki mikawa Mummy kayan nan" "to zan kaimata Insha Allah" Maama ta wuce, Jalila kuma ta shige dakinsu tana zuwa ta tarar Nana ta dawo, "Nana Ashe kin dawo, sarkin kawaye" "bawani sarkin kawaye, zumunci dai" "hhh to naji, ya kika baro su" "suna lafiya amma naso tare mukaje, ke kullum kina gida" "ai bayan tafiyarki nima na dan fita Maama ta aikeni" "inyee kinfara gane gari" "sosai makuwa" sukayi dariya sannan Jalila tace "Nana wai ranar Saturday za ayi birthday din Jalal" "Are you serious, ya akayi kika sani?" "Yaya Jawwad ne yagayamin" "Amma ya haka duk shekara tare sukeyi fa" "nima bansaniba, guri zasu kama amma muma zamuje" "dan Allah ai basu gayyacemu ba" "Injiwa Yaya yace zamuje muma" "kai amma naji dadi Jalila dama an kwana biyu banfita wani outing ba" "Haka kika iya sarkin yawo"    Bayan Jawwad sun gama cin Abinci suka fito suna hira, a harabar gidansu Jalal suka koma suna basket ball, se magariba suka bar gurin, bayan sallar magariba Jawwad yacewa Jalal, yazo suje gurin Mummy "muje muyi mata me?" "yakamata dai muje kwana biyu ban ganta ba bamu gaisa ba" "kaje kai kadai mana, ba dolene se naje ba" "Jalal ba shawararka nake nema ba, ka tashi mu tafi" Ganinda Jalal yai Jawwad ya hade rai sosai, shiyasa shi mikewa, "tashi muje" Jawwad ya tashi suka tafi cikin gidansu Jalal, Jalal ne a gaba Jawwad yana binsa, Ilham ce kadai a palourn kwance akan three seater tana daddanna wayarta, mikewa zaune tayi tareda fadin "sannunku da zuwa" Jawwad ne ya amsamata, "yawwa Ilham, ina Mummy ne?" "tana dakinta, inaga salla takeyi bari inje in kirata" ta mike ta nufi part din Mummy, Jalal dai se cika yake yana batsewa sekace wanda akayiwa wani laifi, ba a dadeba sega mummy ta fito, Ilham na bayanta, ta karaso ta nemi guri ta zauna a palourn, dan risinawa Jawwad yayi "Mummy ina wuni" "lafiya kalau Jawwad kwana biyu ya gida, yasu Maaman" "tana lafiya" "Kwana biyu bamu hadu da ita ba, ina jira zata aikomin da kaya" "eh dazu naga an karbo, amma zata aikomiki ne" "Yayi kyau" shidai Jalal bece uffan ba, sema mike kafarsa da yayi ya kashingida, Jawwad yace "Mummy ranar Saturday yakama birthday din Jalal fa" "ina sane Jawwad, wannan karon ba tare zakuyi ba" "eh mummy, nashi zamu farayi tukuna, nace bari agaya miki" "Assalamu Alaikum" gaba daya suka amsa sallamar tareda waigawa, ko be juyoba yasan muryar Jalila ce, karasowa tayi cikin yanga, ta kalli Jawwad tai masa murmushi sannan ta durkusa kasa tace "Mummy ina wuni" "lafiya kalau 'yan mata kwana biyu, kin buya bana ganinki" murmushi Jalila ta kumayi "ina nan Mummy bana fitane kawai" "amma baki da lafiya ne, naga kin rame haka?" Jawwad yace Mummy ta danyi rashin lafiya kam""Allah sarki ba labari, Allah ya sawwake" suka amsa da Ameen banda Jalal da Ilham dan tunda ta shigo Ilham ke mata kallon banza Mummy tace "Jalila yi hakuri bari in dan saki aiki, jeki dakina akwai drowern mirror dina akwai, key ki dauka ki bude wardrobe dina, zaki ga akwai wani kit kibude ki dakko kudin ciki Ilham seda ta kalli Mummy dan sam Mummy bata sata harkar kudinta, amma yau ta tura Jalila har bedroom dinta ta dakko kudi, seda Jalila tayi Jim kaman bazata ba sannan ta mike, ta nufi dakin Mummy, "Yawwa Jawwad ina jinka, yi hakuri na tsaya surutu" "bakomai Mummy dama cewa nayi, ko zaki halacci gurin birthday din nasa" Jalal ne ya dago da sauri yana wa Jawwad wani mugun kallo, shikuma ya dauke kai kaman besan me yake ba, murmushi Mummy tayi "waceni Jawwad, Allah ya temaka, ya raya Jalal sannan ya shiryamin shi" Koda Jalila tashiga taga part din Mummy ma ya tsaru, katon palour ne, me dauke da kayan alatu, se tangamemen kofar bedroom dinta, ya tsaru matuka, kaikace a kasar wajene, Jalila ta nutsu ta dau abunda aka sata ta fito. Jawwad ya gyara zama sannan  yace "Mummy in bazakije ba ga Ilham, ko yan uwa ai yakamata sumana kara suyi attending" Jalal ji yake kaman ya make Jawwad, shi bayason gayyar surutu, amma Jawwad se gayyato masa tarkace yake Ilham tace "Jawwad aini ko ba ku gayyaceni ba zuwana gurin birthday din yayana dolene, dan haka zanje nida kawayena" wani uban tsaki Jalal yayi, duk suka juyo suka kalleshi, Mummy tace "kagani ko Jawwad, nikam Allah yakawo silar shiryuwar Jalal, yanzu a haka kake tunanin inyi attending gurin birthday dinsa, ya dizgani a gaban abokansa, Sam baya ganina da mutunci" Ai kuwa Jalal a fusace yace "kagani, nidama bance tazo gurin birthday na ba, seda nace bazanzo ba amma ka janyoni kaga har zata faramin korafi sek....... Sekuma sukaji yayi shiru, ya koma ya kashingida, fitowar Jalila taji Jalal yana wannan masifar suka hada ido, ta girgiza masa kai, alamar ya dena, shine abunda yasashi yin shiru, yakoma ya kashingida, duk abun nan ba wanda ya lura dame ya faru se Ilham, wadda taji kaman an dakko dutse an sakamata a zuciyarta. Jalila ta karaso ta durkusa tabawa mummy kudin, Mummy tace "tafi dasu, kibawa Maama kice kudin wancan kayanne, ban mata transfer bane saboda wayata, ta dan samu matsala" "to zan gaya mata Insha Allah, seda safenku" Jawwad yace "bazaki jirani ba" "a a yaya, seka taho" Ilham ce tafara mikewa ta tafi dakinta, sannan Jalal, shima tashi yayi ya bar dakin, dan Jawwad yagama bata masa rai, Jawwad kuma ya tsaya, yaita rarrashin Mummy kan halayen Jalal, sannan yai mata sallama ya tafi. Koda Ilham ta koma dakinta ji tayi kaman ta dora hannu akanta ta fasa ihu, wannan wace irin masifa ce, tunda take a gidan nan, mummy bata shigar da ita cikin sha anin kudinta, amma yau da kanta ta tura Jalila kan kudinta, kuma karewar abun takaici wai hartayiwa Jalal signa ta hanashi abu, kuma ya hanu, lallai akwai sauran aiki, meyasa wannan yarinyar ta shigo rayuwarmu tayi kane2 haka, me yakamata inyine, kozan yi yawo tsirara se burin mahaifiyata ya cika, amma ta yaya? Wata zuciyar ta tambayeta, shiru tayi zuwa can kuma tayi wani irin shu'umin murmushi, tareda jinjina kai, "muje zuwa, Jalila kin tara kin samu, senayi sanadiyar da mujiya seta fiki farinjini a cikin al umma"      A satin ranar Monday su Jalila suka fara zuwa makaranta, Abba ya daukar musu driver saboda Kar a dorawa Jawwad nauyi dayawa shima ga nasa karatun, Jalila taji dadin fara zuwa makaranta, in ka ganta kai kace irin salihar nan ce, dan ko magana batayi sosai, wanda yana cikin halin Jalila in taje guri seta karanci kowa tsaf sannan zaka san wacece, ko magana bata fiyeyi ba, sannan bata yadda tayi kawa ba har yanzu, a satin nan tunda tafara zuwa hijjabi take sakawa har kasa, se farin glass, yauma uban dogon hijjabinta dark blue har kasa ne a jikinta, se jakarta data rataya, sunfito daga lectures tana jikin wata bishiya inda suke haduwa da Nana, taji  wasu suna zundenta wai ga ustazan jami a, gigin secondary ne ta shigo a ustaziyya kafin afita kuma anyi clean, irinsune mugayen tantiran makaranta in suka waye, itakam ko ta kansu batabiba, dan ko kallo basu isheta ba, a ranta tace "kucigaba karku fasa, ku bari in zama yar gari, zaku gane baku da wayo dan ba ruwana da wata jami a, mutun yayimin senayi masa, but now kuci karenku babu babbaka" tana tsaye nan Nana ta karaso, suka nufi motarsu, a hankali Jalila take gane halin yan ajinnasu, da yaran masu kudi, dana talakawa masu dorawa kansu karya, yan rainin hankalin lecturers, da masu iyayi, kowa tana ankare da halinsa, tana ganesu, amma still ba ruwanta da kowa, wasu suyi gulmarta a gabanta wasu a bayan idonta, seta nuna musu ita magana ma abun wahala ce a gurinta, Nana kam hartayi kawaye daga zuwanta, yayinda dabi un Jalila suka tafi da imanin kawayen Nana, ta iya gayu maganarta kawai abun burgewa ce balle tafiyarta da sauran mu amalarta, sedai suna mata kallon me girman kai, saboda gani suke kaman wulakanci take musu, inba Nana ba bata kulasu, dan ta yanayin shiga da mu amala tana iya gane, mutanen banza dana kirki, Jalila kenan me abubuwan ban mamaki Ilham ta gayyaci kawayenta gurin birthday din Yayanta kuma masoyinta wato Jalal, se wani rawar kai take tana shirye2, ta gayyaci su yaseera da sauran kawayenta, se shiri takeyi, taje sabon gari ta sha kitso, tayi booking din make up, hatta shigar da zatayi sabon kaya ta siya. Jalila ma nata shirin takeyi, saboda mugayen mafarkan da take da Jalal, dan haka da shirinta, zataje gurin birthday din nan, tanason tayi taka tsan2 sosai a gurin nan dan ita sam bata yadda da wannan birthday dinba, tana so taga suwaye abokan Jalal ne, mussaman Jeje, dakuma wasu abubuwa da take shirin yi a gurin, tanason tabattar wa Ilham Jalal baya gabanta, Bangaren Jeje ma shidasu hannah da abokan shaye2 sun shirya tsaf domin gudanar da mummunan kudirinsu akan ABDUL JALAL. Ranar juma a da daddare, wanda yakama jajibir din birthday din Jalal, Jalila ta tafi Dakin Jawwad domin tana son magana dashi, tai sa a kuwa shikadai ta tarar a palourn, taje tasamu guri ta zauna, Jawwad ya kalleta"Babyn Yaya Jawwad, ya akayine?" "gurin Yaya nazo" "to Yar gidan Yaya, ina jinki" "Yaya Jawwad , gaskiya abokinka tunda mutane masu hankali zasuje gurin nan, dan Allah ka kaishi a rage mai gashin kansa, sannan kar kabari yasaka sarkan nan dayake sakawa sekace wani kare, ga wan..... Kai tsaye ba sallama sukaga Jalal ya shigo, hade rai Jalila tayi" a dai dinga yin sallama" banza Jalal yai mata, ya kalli Jawwad "kai gurinka nazo" Jawwad yace"ai gani, Allah yasa lafiya" wayar Jawwad tafara ringing "excuse me bari in amsa waya" yadaga wayar yasaka a kunnensa tareda yin sallama "Assalam Alaikum" Muryar Hanan Jalila taji "wa alaikum salam barka da yamma Taurarona fatan kana lafiya?" "lafiya kalau Hanan, ya gida, yasu Abdallah da daddy?" "suna lafiya, nice dai bani da lafiya" "yasalam meyasameki" "kewarka mana, itace take damuna, yanzu yaya queen take, naga kwana biyu haushina takeji" "tana lafiya, yanz... Juyawa yayi da nufin yabawa Jalila wayar, yaga Jalila ta cika ta batse, ta hade rai sosai, fasa bata wayar yayi, yace " Queen dinki tana lafiya" "Masha Allah ina sirikata Nana, kodayake ita muna waya, dan Allah Yaya Jawwad yaushe zakuzo Kaduna ne, inaso inkuma ganinka, kullum senayi mafarkinka fa" Jalal dake gefe ya kalli fuskar Jalila kawai ya kwashe da dariya ganin yadda ta hade rai, Jalal ya tashi ya fita daga palourn, yana kuma yin dariya, ba karamin kyau Jalal yakeba idan yana dariya, Jawwad seda ya sha jinin jikinsa yakuma kallon Jalila, muryar Hanan ya kuma ji "my Haidar bakace komai ba, dan Allah yaushe zakuzo?" mikewa Jalila tayi ta fice daga palourn dan bazata iya cigaba da jin wannan hirar ba, ashe Hanan dagaske take son Jawwad tajeyi, kishi ya lullube Jalila ta fito ko ganin gabanta batayi, tazo fita taga Jalal a tsaye, a kofar fita, shiru tayi ba ta cemasa komaiba ya kalleta, yadda ta hade rai, tuntsurewa yakumayi da dariya, "kinji abunda Ilham takeji ko? Kinji yadda takeji idan taga kinamin shishshigi ko?, are u jealous of your brother" wani mugun harar tayi masa "ni matsa in wuce" Jalal yace"in naki fa? Ji yadda kike wani hade rai" sekuma ya hade rai kaman bashi yake dariyar nan ba yace "to bari in gayamiki, dakaina zan dauki Jawwad in kaiwa Hanan, ubanme Jawwad zeyi dake gaki mummuna gaki kwaila, se tsabar iyashege da rashin kunya da kikasa a gaba, ni zan tsayawa Hanan seta auri Jawwad, in yaso kije kinemi me tsautsayin daze aureki, wanda ze iya tolerating wannan nonsense din naki, sokuwa kawai, wuce ki ban guri" murguda masa baki tayi, tazo zata wuce ya kuma rufe hanyar, ya kalleta "Kashedina dake na karshe, gobe in Allah ya kaimu kika sake na ganki gurin birthday na, duk abunda ya sameki kekika jawa kanki, idankuma kinkiji kinje gurin, idan kika sake kikayi wannan karambani a gurin, shima kome ya biyo baya ke kika sani," Cikin bacin rai tace" waini kadai ka tsana zakace bazanje ba, wallahi senaje, sedai in baza ayi ba, kuma wallahi niba mummuna bace ba, Mummuna tana gidanku wato Ilham" kallonta ya kumayi tsaf, sama da kasa, be kuma cemata komai ba,  yabata hanya ta wuce, tana tafe tana mita, harta je dakinsu, Nana ta kalleta "lafiya dai, naganki kina fushi hada mita" "Ke rabu dani ba komai" Sallar isha i tayi ko Abincin dare bataciba, tanemi guri ta kwanta, banda kishi da bacin rai ba abunda yake damunta, "haba Hanan yazaki min haka, meyasa kikeson Jawwad din, kema ina sonki, zan iya sadaukar miki da komai nawa da kikeso, saboda kaunar da nakemiki, amma banda yaya Jawwad dina" haka taita juye2 da kyar bacci ya dauketa Jalal yana tsaye se fara a yakeyi, ga wani katon cake 🎂 agaban sa, ga mutane nata hada2 Hannah ta yanka cake ta dakko tasaka masa a baki, cake din na shiga bakinsa yazama baki, jini yafara zuba daga bakinsa ya fadi a gurin, da gudu Jalila ta karasa ta kifar da tebur din da cake din kafin ta juyo ba kowa a gurin daga ita se Jalal, ta tafi tana lekawa taga koda wanda ze temaka mata ya dauki jalal a kaishi Asibiti tana dawowa taga, Ilham ta shake Jalal tana kokarin kasheshi    "Subhanallah!!!" ta furta da karfi Share please, More Comments More typing............................... 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ [9/28, 8:10 PM] Ayshercool: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  52 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680                _My First Novel _ A firgice ta mike zaune tana waige2, Nana ta tashi zaune itama, "lafiya Jalila, meyasaki ihu haka" Jalila ta hada zufa, se haki take hannu tasa ta dafe kanta "bakomai Nana, yi hakuri na tasheki, kwanta abunki, na dan tsorata ne kawai" "to shikenan, ki kwanta kema, darene sosai yanzu" "to zan kwanta" Nana ta cigaba da baccinta, yayinda bacci ya kauracewa idon Jalila, se tunani da yacika mata zuciya, da taga baccin ya gagareta, ummi ce ta fado mata a rai, dan tasan da ummi na nan da yanzu tana sallar dare, tashi tayi itama taje ta dauro alwala ta tada salla, tayi addu a sosai wanda galibin addu'ar ta ta, tana fatan Allah ya bayyana mata Ummi, dakuma fatan Allah ya shiryi Jalal, ya bata nasara akan makiyansa, a haka tasamu bacci yakuna daukanta.    Yau Saturday yakama ranar birthday din ABDUL JALAL, shirye shiryensu suke yayinda Jalila banda aikin tunani ba abunda takeyi, Jawwad ma a wani bangaren ya damu ganin yadda Jalila kishinta ya fito karara a fuskarta, duk ya damu gashi ya kira layinta amma a kashe, gashi yana tsoron ummi dayaje da kansa gurinta. Ilham se shiri take kaman wadda zata biki tun safe take hada2, tana waya da kawayenta akan yadda abun ze kasance, Abun duniya duk ya ishi Jalila dan haka ta dau mayafinta ta fita, se azahar ta dawo, ba wanda tagayawa ina taje, tana dawowa ta hadu da Jawwad a harabar gidan, yaji dadin ganinta sedai besan mezece mata ba yana ganin har yanzu tana fushi dashi, "Baby daga ina haka da ranan nan?" fuskarta a sake tace masa "Yaya na dan fitane, ai ban dade da fita ba" "to shikenan kidena yawo a rana, kar kanki yayi ciwo, bazan so hakan ba" murmushi Jalila tayi "to Yaya, amma kaima ai naga a ranar zaka fita, kaima bazanso kanka yayi ciwo ba ai" "Baby dolene yasa zan fita ai" "Amma ranar da zafi fa" ta fada a shagwabe, dariya yamata "zaki fara rigima ko" tuno wayar da sukayi da hanan jiya tayi, nan da nan taji ba dadi, ranta ya baci dan haka ta wuce cikin gida ta barshi a gurin. Jeje yanata jadaddawa Hannah, karta bari a samu matsala akan aikin dazasu gabatar yau akan Jalal babbar dama ce suka samu, karta bari ta kubu cemusu. Allah ya temaki Jawwad ya lallaba Jalal ya kaishi aka rage masa sumar kansa, anyi masa gyaran fuska yayi kyau sosai, amma shi Jalal se mita yake wai Jawwad yasa an masa aski an maida shi mummuna, bayan sun dawo daga gurin askin ne suka hadu da Nana da Jalila a hanya sunje sunyo siyayya suka dakkosu, Jawwad yace "in anjima tare zamu tafine kokuma yaya?" Jalila tai farat tace "A a tafiyarku daban tamu daban" Jawwad yace "meyasa?" "bakomai amma bazamu tafi daku ba, ka dau abokinka ku tafi, dan bana son mita da korafi" "Wane me mitar da kuma me korafin" "nidai ban kama suna ba" dariya Nana tayi "hmm Allah ya shirya Baby Jalila" "Ameen" duk abubuwan nan da takeyi karfin haline, dan ji take duk jikinta yayi sanyi, Bayan sallar magariba, Ilham ta shirya tsaf, ta dawo daga gurin make up, tayi kyau ba laifi abunka da farar mace ga kwala2 idanuwa inji Hanan, dogon wando tasaka baki, da t shirt blue wadda tazo har cinyarta, kanta ya sha kitson attach, ta dakko dan karamin bakin mayafi tasaka akanta, wrist watch dinta ma baki ne ga wani takalmi me uban tsini shima baki, se dan karamin jakarta data rataya, tayi kyau matuka, ta fito palour ta tarar da mummy, mummy tana ganinta tai murmushi "Masha Allah, uwargidan Jalal kinyi kyau fa" murmushi Ilham tayi "Mummy har kinsa naji dadi wallahi" "se tafiya" "eh mummy tafiya zanyi" "to a dawo lafiya, kikula da kanki" "to mummy, ki bani key din" mummy ta mikomata key din mota tace gashi nan "ayi tuki a hankali" Ilham ta karbi key ta fita Nana ma tayi kyau ba karamin haduwa tayi ba, dan ita high west tasaka baki da jan body hook se ta kawo mayafi tayi rolling din kanta dashi, Har Nana ta gama shiri Jalila bata da niyyar ta shi ta shirya tayi wankanta tsaf amma ta nemi guri ta zauna, seda Nana ta fara mita sannan ta tashi, Nana tasata a gaba tayi mata light make up, kamar wadda kwai ya fashewa a ciki Jalila ta tashi ta dakko wata doguwar riga purple wadda ta sha adon duwatsu, ta taje gashinta tasaka masa ribbon, kasancewar kanta ba dan kwali, gashin gaban kanta me laushi irin na fulani ya kwanta kai dagani kasan kan akwai gashi, ta dauki mayafin rigar ta dora akanta, Nana tai murmushi "fa tubarakallahu ahsanil khalikin, wallahi Jalila kinyi kyau sekace y'ar sudan, dressing din ya miki kyau" "ke rufamin asiri, wani irin larabawa ana zaman lafiya, da an cuci larabawa" "amma kinsan fulani koba mu kai larabawa ba da kyanmu" "ji wani cika baki ina kyan anan" dariya Nana tayi "ni karasa shiryawa mutafi" Jalila ta dau Jakarta purple, se takalmi me tudu. Tayi kyau kaikace wata yar hamshakin attajiri ce. Suka jero suka fito Maama ta kallesu, sedai hassada amma ita kanta tasan Jalila ba laifi tayi gadon dangin mahaifinta sosai a kyau, kamanta daya da babanta, mahaifiyarta ma ba baya ba wajen kyau, Nana ma ba laifi tana ds kyau amma sam bata kai Jalila ba "har kunfito?" "eh Maama zamu tafi" Nana ta bata amsa "to Allah ya kiyaye, kar kuyi dare ku dawo da wuri" Jalila tace Insha Allah " suna fitowa harabar gidan Driver su yake jira, suka bude mota suka shiga, suna tafe Nana tana ta musu hotuna, ana zuwa wani guri Jalila tace a tsaya zata karbi sako, ta fita ta karbo sakon tabude boot ta saka, sannan ta dawo mota tace a tafi, Nana tace" mekika karbone? " " abune "" abu wane iri" "kinji mace kin aikenine?" "a a ban aikeki ba jarababbiya" "eh naji jarababbiya" haka suka tafi suna fada Suna zuwa gurin Nana ta bude mota ta fita yayinda Jalila ta kame a cikin mota taki fita "fito mana" "yi gaba zan taho" Nana ta wuce cikin gurin. Abunda ya daurewa Jeje kai be wuce ganin yan uwan Jalal dake ta zuwa ba, dukda matasane amma abun ya bashi mamaki, dole sukara shiri su saka ido sosai, saboda kar a samu matsala. koda Nana ta tafi Jalila tacewa driver "manu dan Allah karkayi nisa akwai ajiyata a cikin motar nan anjima kadan zanzo in dauka" "karkiji komai Uwadakina, ina nan ina jiranku harku gama" Jalila ta bude motar ta fito seda ta karewa harabar gurin kallo, taga yanayin mutanen dasuke shiga suna fita, mutanen kirki dana banza, wasu daga cikin wanda tagani suna kama da mummy dan haka ta tabattar yan uwan su Jalal ne, dama Jalal sunada yan uwa haka, amma basa zuwa gidansu Jalal, gakuma yan iskan abokansa nan wanda da gani base an gayamaka ba kasan yan giya ne, kowa se hada2 yake, a hankali ta bude jakarta ta dakko katon glass baki tasa a idonta, tafara wannan tafiyarta ta me daukan hankali, hall din ya hadu yana da girma, kaikace biki ake ba birthday ba, an kawata gurin matuka guri ta samu a gefe ita ka dai ta zauna a wata kujera tana kallon kowa one by one, ta hangi table din da Ilham take ita da kawayenta su yaseera da wasu yan uwansu, se hotuna suke suna dariya, Hannah ta hango tasha kananan kaya tana up and down cikin maza ko kunya bataji, murmushi Jalila tayi a ranta tace "yakamata hanna su san juna itada Ilham" tanata kalle kallenta wani matashi yazo ya zauna a kujerar kusada Jalila, "sannu yan mata" banza tayi masa tama kara dauke kanta "haba yazaki dauke kai haka, nazone in tayaki hira kawai kafin a fara, naga ke kadaice" juyowa tayi "to cemaka nayi na damu senayi hira da wanine" gani tayi yana dan kaama da Jalal, hakan yasa ta gane dan uwansane "to in bakyason hirar ni inaso, muryarki da dadi gaskiya, gashi kinyimin kyau sosai" shiru takuma yi masa Hannah ce tazo wucewa taji anata Ilham, da sauri ta dan tsaya ta juyo, amma setaga ba wadda take tunani bace, "may be sunan ne dai yazo daya" Jalila gani tai wannan gayen ya cika mata kunne da surutu, dan haka ta mike ta bashi guri ta tafi gurin Nana, ta ajiyewa Nana jakarta "Nana ina zuwa dan Allah" daga haka ta tafi dan nesa dasu Ilham, Hannah ce takuma dawowa taji Ilham tana "kai wai ina yaya Jalal ya tsaya haka, by now yaci ace anfara fa, Yaya Jalal kenan, zuma seda wuta" Hannah tsayawa tayi cak ta dan dawo da baya tace "dan Allah kece Ilham, kanwar Jalal fa" Ilham ta mata kallon up and down "yeah nice, kanwarsa kuma matar daze aura" Hannah tace "anya kuwa, last time kaman ba dake muka haduba" "ke wai meye haka zakizo kinamin tambayoyi hakane, ke wace niban taba ganinki ba se yau, meye hakane" "Hannah manyan mata, kuma me da'awar soyayya  a gurin ABDUL JALAL, gaskiyarki wannan itace Ilham ba niba" Jalila tasa hannu ta cire glass din fuskar ta, "yes itace Ilham nikuma Jalila" gaba daya suka tsaya suna kallon Jalila, suka ma rasa abun cewa "dama ya dace kusan juna, Ilham ga Hannah, Hannah ga Ilham yanzu kusan juna, so u should count me out of your troubles, Ilham, Hanna, niba budurwar Jalal bace, bani da lokacin da zan bata akan soyayya da wani Jalal, dan haka idan kuna abunku to ku cire Jalila a ciki" tana gama fadin haka tai tafiyarta ta kyalesu, kallon kallo aka shigayi tsakanin Hannah da Ilham, wani shu'umin murmushi Hannah tayi, Ilham tace "ashe kece Hannah, ni na dauka zanga wata hamshakiyar mace meji da kanta, ashe ma karyar bariki ce kawai" Hannah ma tayi wata shu umar dariya sannan tace "ashe kece opponent dina ba waccan ba, thank God kece, bazam sha wahala ba, da waccan me siffar aljanunce da sena damu, dan ba karamin daukar hankali zatayi ba, amama me ban daukeki cikakkiyar mace ba ma balle in damu kaina, dan dake da namiji ba ku da banbanci" taana gama fadar haka ta wuce tabar Ilham, Jalila kam tafita harabar gurin, tana waige2, tana tsaye taji ance Jeje da sauri ta waiga, tana ganinsa taga yaci sunan nasa jeje kai kace wani kasurgumin arne ne, gajeren wandone a jikinsa, da riga amless duk damtsensa a waje sekace dan dambe, gashi ya tara suma duk yamata kala, haka wani dan gemunsa shima ya samasa wannan kalar, ga katon sarka a wuyansa, lebensa baki kirin kaman gawayi, idonsa jawur, jeje ne ya tsaya suna gaisawa da wasu abokansu, muryarsa ba dadin ji, muryarsa a bude take, kai da kaji kasan kasurgumin dan shaye2 ne, ajiyar zuciya Jalila tayi tace "No wonder, wannan ko kisan kai akace yayi bazatayi musu ba" tana shirin komawa cikin hall din taga Hannah ta fito ta tafi inda yake, suka tsaya suna maganganu, Jalila bata iya jiyo me suke cewa, sun jima suna magana sannan taga Hanna ta koma cikin hall din, Jalila ma komawa tayi cikin hall din, tana zuwa taga an shirya high table cakes sun kai biyar manya2 kuma kala2, ga wasu manyan kwalabe, gurin Nana ta koma ta zauna, Nana na tayi mata mita ta cika yawo, ita dai tai mata shiru. da Jalila ta bada fuska da samarin da zatayi a gurin dayawa daga na kirkin har na kwarai, kowa se kawomata farmaki yake, ita kuma ta tsare gida, ta hade rai ba raini, suna nan zaune aka sanar da karasowar Jalal, mutumin naku ya hadu, suka shigo shida Jawwad kaman twins, sedai Jalal yafi Jawwad murdewa sosai, kuma shi Jawwad kalar ustazaine, shikuma Jalal kaman wrestler, yau anci sa'a da fara'arsa ya shigo, Jeje ji yayi kaman yai tsuntsuwa yaje ya shake Jawwad, ganinsu tare, ba karamin bata masa rai yayiba, gaba daya hall din ya dauki tafi, ana shewa cikin takunsa na kasaita yaje har kan stage din ihu aka dingayi ana masa tafi, akaita daukarsa a hotuna, MC yace to kafin Jalal ya yanka cake za a dan shakata tukuna. Nan aka shiga cashewa maza da mata ana watsin kudi a gurin. Jalila dai na zaune tana kallon stage din amma tunaninta baya kan me akeyi kamar an mintsineta ta waiga, tana waigawa tayi tozali da Jeje ido hudu sukayi da ita, kwata2 bashi da kyan gani a idon Jalila, se yanzu ta lura da zanen tatoo a damtsensa na hagu da kuma gefen wuyansa, harda pink dasu blue a kalolin gashin kan Jeje, wai yanzu wannan ne abokin Jalal, gaban Jeje ne yayi mummunar faduwa da yaga Jalila, kallon kallo suka shigayi, ko kyafta ido ba yayi akanta, haka nan yaji be yadda da itaba musamman dayaga kallon da take masa, amma fa yarinyar ta hadu iya wuya, komai yaji a jikinta, idanun nan nata ma kawai sun isa daukar hankali, wayarsa ce tafara ringing ya kalli wayar ya kalli Jalila ya juya ya fita, yana fita Jalila ta rufamasa baya, harabar gurin ya fita Jalila tana binsa a baya, dan nesa kadan ta tsaya daga inda yake "Hello oga KB, ina nan nasaka ido komai ze tafi yadda ya dace, nasaka ido akan komai, kuma Hannah ma tana lure da komai, yanzu dai fatanmu yafara cin cake din nan, zakaji Labari me dadi a daren nan" Jeje na gama wayar ya juyo yayi tozali da Jalila a tsaye kyam tana kallonsa, wani murmushi yayi na rikakkun yan iskan duniya "Hi beb what are you looking for?" shiru tayi ta cigaba da kallonsa "kinada damuwa ne, can i help you? " "u have nothing to help me with" jin muryarta ba karamin burgeshi tayi ba "wow muryarki da dadin sauraro" "Kai dakata, am not here to listen to your useless and dramatic words, am here for a porpose, waye kai meye hadinka da ABDUL JALAL kakeson cutar da rayuwarsa" Kallon tsaf yayi mata, sannan yafara takowa a hankali gabanta yace "Kekuma wacece? Haba beauty why trying to involve your self in this case, gaki little baby with beautiful body, baki dace da shiga rigimar manya ba da babu ruwanki" "na fuskanci kai karamin dan iska ne kai kake mun kallon yarinya, bari kaji ingayamaka ni bana fadar abu idan zanyi sedai kaganshi a aikace, wallahi indai da raina sena ga bayanka daga kai har wanda ya tsaya maka" hade rai Jeje yayi "da farko na dauka abun naki wasane, meyasa kikeson shiga abunda babu ruwanki, a kaf dangin Jalal ban sanki ba, meye hadinki dashi da kikeson kare rayuwarsa, kekin isa ki rusa shirin da aka dade anayi kusan shekaru goma sha biyar ke awa, kodai kina sonshi ne? Baki dace dashiba da irina kika dace musaki a harka ba karamin wuta zakiyi ba a duniyarmu ta manyan yara, da ina ganin kaman da Ilham zan tafi, amma kinfita haduwa" "Ni a mutum, duniyar ku ta dabbobi dai, marasa amfani, and i will show you what am capable of doing, wallahi sena rusa shirunku ko shekara dubu kukayi kunayi, Allah ya tsayamin muzuba mugani, sha3 dan asara, Allah yayi min tsari da kai, banza whalalle mara imani, ni ba son Jalal nakeba ina tausayin rayuwarsa ne da iyayensa, zanbaka mamaki, ka tsaya kagani a yau base gobe ba zan fara nuna maka, waceni useless and hopeless creature" ta juya tai tafiyarta, Share please More Comments typing........................ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ [9/30, 9:37 PM] Ayshercool: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹     _ABDUL  JALAL_       _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_     (Daddy's girl)                PAGE-  53 PART 1   _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam) Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa. A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske, Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what's app akan wannan lambar wayar 07063065680                _My First Novel _ Kasa motsawa Jeje yayi daga inda yake, ji yayi kaman an daddaure shi, yama rasa me zeyi, babu alamun wasa a cikin maganganun yarinyar she has a full confidence, yana hango tsantsar bacin rai dakuma kwarin gwiwa a kwance a idonta, da sauri ya nufi cikin hall din, dan zeso yaga mezatayi Jalila komawa hall din ta tarar Jalal na shirin yanka cake din, ga gifts da yan uwa suka dinga bashi da abokanansa, da sauri ta koma gefe ta kira Jawwad tai masa magana, sannan ta fita harabar gurin ta nufi motarsu ta bude boot din ta dakko kwali Hannah se rawar kai take ta kafa ta tsare ta janyo wani cake gaban Jalal tanaso lallai shi ze yanka yaci. Announcement sukaji MC yanayi "Babban yaya, kuma Man of the day, mun samu sanarwa yanzun nan, ance dan Allah ka dakata da yanka cake din nan your sisters want surprise you, zamu zuba ido muga wannan surprise din" mamaki ne yakama Jalal, sisters kuma wanne kenan. gaba daya hankaline ya koma kan kyakyawar budurwar da take tunkaro stage din, tana taku cike da iyayi da izza kai kace yar wani basarake ce, tana tafe Nana na binta a baya hotuna wasu suka fara yi musu, Jalila ko a jikinta ta karaso kan stage din, Jawwad ya tareta da murmushi, ya kamo hannunta yasata a tsakiyarsu, Nana kuma ta tsaya a gefen Jawwad, ture cake din gaban Jalal tayi ta aje kwalin gabanta, ta fito da wani katon cake, wanda ya sha ado da launin ja da fari, tana gama bude cake din mutanen gurin sukace "Wow" shikam Jalal mamaki ya hanashi magana kallonta kawai yake, Hannah tace "A a am sorry sister, gaskiya ba za ayi haka ba, wannan cake din naki ajeshi zakiyi, se yafara cin na friends dinsa, yakamata amana kara mussaman ma ni, ko Jalal" Hannah ta karasa maganar tana kallon idon JALAL cike da salon yaudara da jan hankali, Jalila tai murmushi cikin muryarta me cike da shagwaba tace "gaskiya Yaya Jalal cake dinmu zakaci, kannenka kafin kaci na soyayya" ihu aka dauka ana ta daukansu hoto dan wasu sun zata budurwarsa ce, kodayake abun da mamaki dan sanin halin Jalal na jin kai baze barshi yai budurwa ba, shi mamakine yakama shi Saboda tsabar gulma yaushe Jalila tafara cemasa wani yaya, shida a bun kirki ma baya hadasu, shine hada wani kawo cake tace ya yanka, ko duk salone na ta bakantawa Ilham, Jawwad aka kira, ya sauka ya tafi amsa waya, Jalal ya kalli Jalila ga Hannah, sannan ya daga kai sukayi ido hudu da Ilham da ta kafe shi da ido, taketa hura hanci, ture cake din Jalila yayi, ya janyo wanda Hannah takeso ya ci, gurin yayi tsit ana kallonsu, ya kalli Jalila yaga yadda ta tsira masa ido, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata yace mata "ya dai, na canza mikine kikemin wannan kallon? " banda Jalila, na kusa dashi ma basa iya jin meyace, itama a hankalin tace masa "koka canza din kasan ba birgeni zakayi ba, sedai ka birge makakku irinka, dakuma waccan mummunar kanwar taka jarababbiya, shawara zan baka,  dan Allah karkaci cake din nan" "kema ba kyan ne dake ba ai, dan Ilham tafiki kyau meyasa ba kyaso inci cake din, kinfini son rayuwata ne?" ya karasa maganar da wani murmushi na rainin hankali, itakuma tana kallonaa Hasken camera ne keta haskasu kota ina MC yace "Wannan soyayya haka, atemaka abar manashi ya yanka cake din nan, Jalal me masoya da yawa, jin abunda MC ke cewa yasa Jalila dan ja da baya kadan, gaba daya abun duniya ya addabi Jeje, dama Jalal yanada budurwa ya akayi hakane, amma be taba gaya masa ba, anya wannan shedaniyar yarinyar zata bari komai ya tafi dai2 ga yadda tasa se bata lokaci ake, yana cikin wannan tunanin yaga Jalal ya yanka cake din dasukeso yaci, tafi gurin ya dauka, ana rera masa HAPPY BIRTHDAY TO YOU Ya yanko cake din har ya kai bakinsa, se yafasa, ya ga gadda Jalila ta kafeshi da ido, ya waiga ya janyo hannun Hannah ya doshi bakinta da cake din, nan da nan ta firgice, amma dayake yar duniya ce seta maze ta rike hannunsa tana murmushi, Jawwad ne ya dawo kan stage din ya kalli Jalal sannan yace "ya dai an yanka cake bana nan, gaskiya se an sake yankawa, kuma nasu baby za a yanka" ya janye hannun Jalal, ya dakko cake din gurin Jalila, yakama hannun Jalal suka yanka cake, amma Hannah ta tsargu da irin kallon da Jalal yake mata, dan har tafara tunanin kodai Jalal ya gane me suke kullawa ne. Ilham kam data san abunda ze faru kenan a wannan gurin da batazoba, domin ranta yayi matuka a baci, an cimata zarafi, kalli abunda Jalila tayi mata, ga abunda sukayi itada Jalal, bayan ita tunda tazo gurin kota kanta bebi ba, gakuma Hannah, yadda ya wani riko hanna ze bata cake, tsabar sun raina mata hankali, bama Jalila tafi uban kowa raina mata hankali ga yadda suke nema su hade fuska kaman zasuyi kiss itada Jalal, abunda ita be taba yi mata ba kuma tana ikrarin ita ba son Jalal take ba, dan haka a fusace  ta mike ta bar gurin, ko takan kawayennata bata biba, taje ta hau motar data zo da ita ta fizgeta da gudu, tana tuki kaman mara hankali, idan ta tuno Jalila seta ji zuciyarta kaman tayi bindiga, bata san lokacin da ta fara zubad da hawaye ba, tafara tunanin takanwa zata fara Jalila ko Hannah Jalal ya yanka cake din gurin Jalila yaci yabawa Jawwad a baki, aka cigaba da cashewa, Jalila tanata lura da cake din nan karsu dauka su bashi. Nana ce ta janyo hannun Jalila zuwa kasan stage din can gefe, ta kalli Jalila tace "Jalila kinsan wani abu kuwa?" "A a se kin fada" "Ilham fa ranta ya baci, abunda kukayi keda Jalal, ta tafi gida a fusace" "niba wani abu a raina game da wani Jalal, da ta kwantar da hankalinta niba abunda zanyi wannan makakken, nayine kawai saboda Jawwad, kuma da wani dalili, kinga ina zuwa" ta wuce ta bar Nana a gurin, tana dubawa taga babu Jalal a gurin, hankalinta ne ya tashi, se abokansa dasuketa rawa a gurin, dubawa ta shigayi amma bata ganshi ba, da sauri ta fita harabar gurin tana lekawa, hangoshi tayi akan wata mota acikin duhu, suna bashi giya, yana sha yana dariya, gashi Hannah ta manne a jikinshi kaman zata shige jikinsa, da gani yafara fita hayyacinsa, gefe Hannah ta koma tana waya, daga baya kuma ta bar gurin da wayar a hannunta, dan haka Jalila ma da sauri ta dauki wayarta ta kira Jawwad "Yaya kai sauri, kafito ka dauke Jalal, kaman akwai wani abu da ake shirin yi masa kai sauri dan Allah" tana gama wayar ta nufi gurin motarsu ga tarar da direbansu manu yanata goge2 mota, da sauri tace "Manu dan Allah temakamin zakayi, zomuje ka gani, ba musu yabita a baya, suka tsaya dan nesa da inda Jalal yake a cikin wannan duhuwar, ta kalli manu tace" zan dauke hankalin wancan, dan Allah ka dauke ABDUL JALAL, ka kaishi gida" "Amma me....... " Manu kawi ka tafi da shi dan Allah, zan dauke hankalin wancan matashn, daka daukeshi ka tafi dashi, inkunfita waje ka kirani a waya, tana gama fadin haka ta nufi inda Jalal yake, matashin dayake gefensa yanakuma dura masa giya taje ta kalleshi "sannu dai yaya na" "Yawwa yan mata ya akayine?" "Temakamun nakeso kayi" "Akan me fa?" kaga kudin motana na yar, dan Allah kozaka rage min hanya kokasa wani a abokanka ya ragemin hanya" "haba yan mata kamanki ace an rasa me kaiki gida hakan be dace ba, bakece budurwar Jalal ba" "A a niba budurwars bace brother na ne, dan Allah yi sauri dare yanayi" matashin ya kalli Jalal yace "Man kajirani anan karkaje ko ina, ina zuwa yanzun nan" ya kalli Jalila "bari in kira wani a waya, yazo ya kaiki" "A a kaga muje kawai ka biyamin kudin motar se in tafi" "A a be kamata ki hau napep ba muje" har sunfara tafiya ya tsaya ya juyo "to ni mene tukuicina" "karka damu, se abunda kakeso shi za a baka" ya washe baki "to shikenan muje" shiya shiga gaba tana binsa a baya Manu yana ganin sunyi gaba yai maza yaje ya rungomo Jalal, gaba daya jikinsa ya saki dan a mugun buge yake, tangadi kawai yakeyi, ga Jalal da nauyi amma haka manu direba ya daukeshi, dan babu abunda Jalila zata sashi yakasa yimata, saboda mutuncin datake masa, ya kinkimi Jalal yasashi a mota ya kunnata ya bar gurin. Jalila kam suna shiga hall din, taga matashin ya doshi wani gungun yan shaye2 ta shige cikin mutane, Jawwad ya kirata amma bata dauka ba, ta koma gefe ta kirashi "Baby kina ina, naduba ban gankiba, kuma banga Jalal dinba" "Yaya Jawwad ka fito kaida Nana mu tafi mu hadu a can waje, kuyi sauri" ta kashe wayar ta fita, tasamu wani guri ta tsaya can nesa da hall din, tana nan tsaye ta hango wata arniyar bakar jeep ta shiga harabar gurin, ba a fito daga motar ba, kuma ba a bude ba taga Jeje, ya fito yazo gaban motar ya tsaya, aka sauke glass din motar, wanda ta ganine ya sata zare ido, baban faruk ne da yadinga cin mutuncin Jalal ranar, saboda ya gaisa da dansa meye hadinsa da Jeje? Bata gama tunanin ba taga motar tajuya ta mike titi, shikuma jeje yabar gurin, Jawwad yazo yai parking a gabanta ta shiga da sauri, tana cewa "yaya yi sauri mubar gurin nan" da sauri yaja motar suka bar gurin Jawwad yace "Baby nifa ban ganeba wai meye haka kikeyi ne? Nifa dole in koma gurin nan saboda Jalal, Jalila tace " Jalal yana gida ai, manu direba ya tafi kaishi gida" "meyasame shi? Ya akai ni ban saniba, tukuna ma naji kince wai wani abu ze sameshi" "da wasa nake dama sonake kazo mutafi" dagajin abunda ta fada kasan karyane, amma yai shiru ya kyaleta. Suna zuwa gida Jawwad yai parking din motarsa, ya tafi gidansu Jalal. Su Jalila na shiga cikin gida suka tarar su Maama ma sun kwanta, Jalila batace ma Nana komai ba itama bata cemata ba, Jalila ta shiga tai wanka, tai kwanciyarta jinta take sakayau hankali kwance, amma idan ta tuno fuskar baban faruk data gani tareda Jeje, se abun ya bata mamaki matuka, Jawwad na zuwa ya tarar da Jalal a kwance kaman matacce, an kwantar dashi akan gadonsa, girgiza kai Jawwad yai ya fito ya koma gida, yana son yayiwa Jalila tambayoyi amma by now yasan ta kwanta bacci.       Tashin hankli, tas mutumin ya dauke Jeje da mari, "baka da hankali ne, har gurin nan naje ka tabattarmin da komai ze tafi dai2, mahaukacin inane kai, kaikamin alkawarin zaka tabattar da cikar burina amma meyasa haka, na kashe kudi akan wannan shirin, an tanadi komai, a daren yau naso akaishi gurin nan da kwayoyi suke, a ajiye mugayen makamai da yan mata, muyi ikrarin yana musu fyade, sannan mu shuno hukumaa suzo su kamashi, a wulakanta shi a gaban uwarsa ta zubda hawaye fiye da yadda tasani nasa tawa uwar, kuma saboda hauka kabari damar nan ta kauce mana, in baka saniba har cin hanci na bayar cewar in ankama Jalal asashi a cikin ya'n fashi yadda, ko ubansa zeyi amfani da dukiya gurin kubutar dashi, se sun wulakanta se fiye da rabin dukiyarsa ta girgiza, sannan saboda jakanci kabari ya gudu" "Wallahi oga KB na tsara komai, yaran naka ne basuzo da wuriba, muka nemeshi muka rasa, kuma har gadinsa nasa ayi aka bashi giya da kwayoyi a ciki wata hatsabibiyar yarinya ce ta hana shi cin cake din nan, muka samasa kwaya, amma muka neme shi muka rasa" "hatsabibiyar yarinya ta hanashi cin cake" oga KB ya maimaita, "wacece ita yar uban waye ita da bakuyi maganinta ba" "Wallahi oga ban santa ba nima a gurin nafara ganinta" "tasan sirrinmune?" "a a ba wanda yasani ko Hannah da take mana aiki bata sani ba" " ina bukatar ganin hotonta sannan ka ganomin yar uban waye, tashi ka bani guri maza2 tashi ka tafi bana son sake ganinka a gabana, kuma kaima zakaga abunda zanmaka, zan nuna maka sakamakon gaza cikamin alkawarina, tashi kabani guri" Jiki a sanyaye Jeje ya tashi ya bar gurin, abun duniya ya isheshi, bacci sam ya gagari Jeje, se tunani yake, yarasa menen mafita. Maganganun da Jalila tayi dazune suka dawowa Jeje, anya ba ita ta dauke shiba, kodai tasan sirrinmune, hakane ma to amma waya gayamata? to amma taya karamar yarinya kamar wannan zata iya dauke Jalal, shikam tiger wani irin banza ne haka, har yabari Jalal ya gudu, to amma mutumin dayake a buge taya yaya ze iya guduwa, to waima wacece wannan yarinyar? Anya bada tiger aka hada bakiba Jalal ya gudu?. Hannah ma abun yabata mamaki ya akayi, Jalal da suka bugar da kwaya ya akayi ya iya barin gurin nan, waye da wannan aikin haka, kuma taga tafiyar Jawwad shida Nana, ba bu Jalal, to ya akayi lamarin nan yazo a haka, ya akayi Jalal yabar gurin partyn nan ba wanda ya ganshi. Ilham ma bacci ya gagareta, kwana tayi kuka da tunani, da tufka da warwara akan me zatayiwa Jalila da Hannah ta huce, nan ta kudurce wani mugun abu a zuciyarta. Washe gari da safe, Jawwad yakoma gurin Jalal, amma Jalal ko tashi beba yana kwance yanata fama da bacci, ya gwada tashin Jalal amma still be tashi ba yanata fama da bacci, Jawwad ya tabbatar da Jalal ba karamin buguwa yayi ba. Jawwad ya koma gida yakira manu direba suka gaisa sannan yace masa "manu ya akayi ka kawo Jalal gida jiya ban saniba"? "nima Jalila ce ta sani na dakko shi an bashi giya ya sha, wani yana gadinsa, shine tace zata dauke hankalin me gadinnasa, nikuma in dauke shi, in kaishi gida" Jawwad yai ajiyar zuciya yace "to shikenan nagode" daga nan ya tafi Jeje ya kudurce wa ransa cewar ko da yaya se ya gano, wace ce yarinyar nan kuma seya gano ya akayi Jalal yabar gurin nan ba tareda kowa yasani ba, tabbas idan hasashensa ya tabatta itace to tasaka kanta a cikin mummunan hatsari, dan seta karbi hukuncin Jalal. Seda la'asar sannan Jalal ya tashi daga  baccin da yakeyi, Jawwad yasa shi a gaba da kyar yai salloli, sannan ya tafi dashi gidansu ya  bashi abinci yaci, Jalal yace "Jawwad ya akayi muka dawo jiya"? "Kai zan tambaya, me yasa kasha giya jiya?" "ai kadan na sha bansan zan bugu haka ba" "kai kasani, seda namaka kashedi amma saboda taurin kai seda kasha" Banza Jalal yai masa yacigaba da cin Abincin sa  Jeje ne yake ta masifa "Hannah wane irin hauka ne wannan, mun shirya komai amma kin bari komai ya tafi a banza, saboda tsabar shirme irin naki wannan wane irin haukane, kinsa oga KB yacimin mutunci jiya hada marina, wane irin sakarcine haka, meyasa ba kya abu da tunani" cikin tsawa tace "Kai dakata, ka iya bakinka wallahi, karka sake ka zageni ka tuna da wadda kake magana Hannah ce, baka isa ka zageni akan wani banzan oganka ba, ai nayi iya abunda nace zan iya ko, to dan haka nagama nawa daga jiya, nagama yimuku aiki, tunda damar ta subuce muku, yanzu kaina zanyiwa aiki, zannemi soyayyar Jalal ta gaskiya dan duk Dunia babu namjin da yayimin sama da shi, dan haka zan tuba auren Jalal zanyi, bayan na tabattar danayi maganin wannan banzar kanwartasa, sannan in Gano wacece wannan hatsabibiyar yarinyar, dan in har da ita nasan Jalal baze aureni ba" A fusace yace "Hanna kidawo hayyacinki, tawaye zakiyimin, kinsan dagani harke ba tsira zamuyi daga sharrin oga KB ba muddin asirinmu ya tonu" "Kai ta shafa kuma wannan, dan daga kai har ogannanka ban daukeku tsiyar komai ba, bari inkuma tuna maka dawa kake magana, Hannah ce duk hatsabibancin da kukeji dashi na fiku wallahi" Tirkashi!!!! Share please More Comments More typing.............................. Laifin dadi karewa anan na kawo muku karshen littafin ABDUL JALAL (2020) kashi na daya, zan dan huta na takaitaccen lokaci domin cigaba da kawo muku wannan littafi, ina godiya da yadda kuka jure bibiyata sannu a hankali a wannan littafi n farko, yanzuma ku biyoni a hankali, domin warware muku kulle kulle, da tarin tambayoyin da suke cikin wannan littafi Yan group din ABDUL JALAL NOVEL FANS masoya wannan littafi wanda nasani da wanda bansaniba masu turomin sakkoni da addu'oi ina alfahari daku inakumabkaunarku nima, dukda kasancewar shi littafina na farko amma kuna bibiyata kuna bani kwarin gwiwa nagode kwarai masoya na da yan uwana ina matukar godiya Se mun hade a littafi na biyu, taku har kullum Aisha humaira (daddy's girl) Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a tuntubeni a ta what's app akan wannan lambar 07063065680. 🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️