[9/17, 3:34 PM] mom muhseen 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........1 Wani irin traffic ne aka had'a kan titin central park,wanda ya jawo tsaikon motoci.ko kad'an ma motocin basa tafiya tsaye suke,wasuna fitowa daga cikin motarsu suna hangen abunda ke faruwa,dan dazon mutane ne kan titin yayinda wasu keta fitowa kallon abunda ya faru.nima dai matsawa nai sosai don kashe kwarkwatar idona,mutane nake ta turewa ina kutsawa don isa inda wannan dan dazon mutanen yake..............wow oh may god masha Allah,wani tsalelen guy ne na gani kwance k'asa cikin jini,duk da yadda jini ya wanke fuskarsa da kirjinsa hakan bai hana tsananin kyawunsa fitowa ba,ko makaho ya shafa yasan wajennan akwai kyau na fitar sharia..............araina nace kai mutanen mu sai abarsu yanzu duk nan babu wanda zai iya kawo mashi d'auki......ban idasa tunani naba naga wani guy yashigo wajen a dari da hamsin yana shashsheka,,,,,bai tsaya ko inaba sai gaban wannan guy d'in dake kwance cikin jini.........kuka yake yana jijjigashi yana cewa mutanen dake zagaye dasu. "Don Allah ku tai makeni na kaishi asibiti,bana iya daukarshi....don Allah kuduba halin da yake ciki,ko numfashi fa bayayi."amman saboda rashin mutunci babu wanda ya kulashi saima tsogumi suke akan ya kauda masu shi suna da abunyi,wani babban mutun yakalleshi yace"wai ba d'an gidan ALH MAINAH bane,wannan tsinennen yaron zamu taimaka,ai baida wani anfani,tunda har iyayen dasu haifai ma sun yardashi basu so wa kuwa zai jefa kanshi cikin matsala,gara kabarshi ya mutu domin itace tafi dacewa da mai irin layyarsa la,anennen yaro kawai." Nanfa kowa yaita fad'an albarkacin bakinsa akan wannan guy dake wance har lokaci baisan wake kanshi ba,kuka guy din dake rike dashi yake yana neman taimako amman babu mai kulashi,daker yajashi gefen hanya yana kuka yana cewa. "Allah yana tare dakai *Alfah* insha Allah ba yanzu zaka mutuba,kowane mai rai da tashi jarabtar kai kuma haka taka tazo,Allah ya baka ikon cinyewa...........kwantar dashi yayi ya koma bakin titin yana tsayar damai taxi cikin ikon Allah yasamo,da gudu suka zo suka daukeshi shida mai taxin suka sashi cikin motar,basu tsaya ko ina ba sai asibiti. Cikin gaggawa suka ansheshi suna ta fad'an meyasa ba,a kawoshi cikin gaggawa ba shidai wannan bawan Allah baida bakin magana,domin shidai burinsa yaga aminin nashi yadawo hayyacinsa,card ya siya yaje aka rubuta mashi duk abunda ake bukata.ansa yai ya wuce pharmacy ATM yabada aka zara sannan aka bashi abunda ake bukatar,yaje yakai yadawo ya zauna yadafe kai.hawaye share share ga fuskarsa yake magana kamar mahaukaci shikadai. " babu abunda zai sameka *ALFAH* zaka tashi,insha Allah babu abunda xai faru,duk yadda kake kaunar mutuwa idan kwananka na gaba bazaka tab'a mutuwa ba,saidai kasha wuya kurun ban san har sai yaushe zaka gane abunda nake nusar dakai ba,ko mutuwar kayi Alfah bakada tabbacin acan din zaka dace da jin dadin daka rasa anan duniya,kayi hkr komi mai wucewa ne no condition is permanent.inaji araina watarana komi zai daidaita.........kuka yake yana tsananin tausayawa abokin nashi,baida kamar Alfah duk duniya shine gatanshi shine kominsa, duk abunda yasamai na dadi dana bakinciki tare suke raba wa,.........dafashi akai ya d'ago fuskarsa ta b'aci da hawaye wani likitane tsaye kanshi,saurin tashi yayi yana goge face d'insa cikin kermar murya yace"Dr ya farka yadawo hankalinsa ko,babu abunda yasamai." Murmushi Dr yayi yace"don't worry ur brother is a life,amman muje office i need to talk 2 u serious issure." Binsa yayi harma yaso wuce dr saboda sauri duk ya susuce,rik'oshi Dr yayi yana mashi dariya dafa kafad'arsa yayi suka k'arasa har office d'insa. 💞💞💞💞💞💞💞 "Assalamu alaikum." Wata tsaleliyar budurwa tayi sallama acikin wani gida wanda baza akirashi da gidan mai arzik'iba,haka baza ka kirashi da gidan talaka ba,gidane daidai wa daida ginin bulone na sumunti,saidai kallo d'aya zakayi mar kasan cewar ginin yasha jiki,kuma bana yanzu bane don wani wajen ma yad'an gugure,d'akuna ukune biyu ciki da falo saidaya single,sai kitchen acan daidai hanyar fita,public toilet daga can ciki yake.sai filin tsakargida mai d'auke da dalbejiyar umbrella tsakar gidan shafe da smuntu,dagani ba ajima da yin saba.duk dadai babu fenti tsakar gidan, saidai cikin d'akunan ya keda shi,shima yasha jiki dagani andauki shekaru dayawa dayinsa daga gefe idan kashigo zaka hango rijiya.gaba kadan kuma wajen kiwon dabbobine da kaji.........atakaice dai wannan gida mamamallakinsa yana da rufin asirinsa,daidai gwargwado daga waje kuma inzaka shigo akwai shaguna biyu jikin gidan,d'aya d'aki aka maidashi dayan kuma kayan masa rufine aciki ake siyarwa. "Assalamu akaikum" Wannan tsaleliyar budurwar tasake maimaita sallamarta tana yamutsa fuska,sai hakan yayi matukar sake k'awata fuskarta,farace fess don kadan zai hana ba kace mata zabaya ba,haskenta hade yake da jajaja amman saika lura zaka gane hakan........"wai gidan ba kowane sai sallama nake idan kuma nashigo ace ba ajiba saina sake,wlh nidai shigo zan nagaji da wage bakina har yafara ciwo." Wata matace ta fito daga wani lungu rik'e da buta da alamar ma daga ban d'aki take. "Wlh ina band'aki najiyoki nasan wasu kaya sai amale inba *SOFIYYAH* ba babu mai shigowa gida yayita kwala ihu yana hayagga." Turb'une fuska tayi tana sake yamutseta tace"wayyo Allahna mamana kefa kikace indaina shigowa gida banyi sallama anjiba,yanzu kuma nayi kince ina hayagaga ke kullum yasmeen ce keyin daidai,nadawo ma ko sannu bakiyi man ba,ga yunwa ga kishirwa ga gajiya,koma kice *FIYAH* yau kin dade meya tsaidaki aa sai kika hau yiman fad'a.......tafiya take zuwa d'akinsu tana wannan tsogumin. Murmushin matar tayi tana biye da ita tace"Allah yashiryaki bazaki tab'a canza waba fiyah." Binta tayi cikin d'akin tana cewa"to yi hkr uwar masu gida,yau lafiya kika jima haka ko lectures d'inne suka yi yawa." Kaya take tub'ewa tana turo d'an bakinta kamar na tsuntsu,tace "mama yau dawuri muka tashi wlh,inata murna zandawo intai islamiya,mama muna zuwa titin wajen central park wanda ya mik'e har zuwa *ALFAH STORE SHOPPING MALL* wlh mama traffic ya tsaidamu munkai one hour wajen,ashe wanine yayi had'ari amman akarasa mai taimakonsa,mafarin muka kai har kamar yanzu." Daga itasai undey da bra,sai surutu take ma maman.matsa kusa da ita tayi tace "mama ballemun donAllah." Girgiza kai uwar tayi tana balle mata bra d'in tace"baki tab'a canzawa fiyah ace katuwar budurwa dake fiyah kullum ni ko yasmeen mune y'an 6alle maki breziya,kinji kunya wlh aibanganin laifinta intayi maki dariya."turo baki take tana sun6ure sun6ure. "Bari naje in sauke miya kin d'auke man hankali karta babbake,ta fice ita kuma ta d'aura karamin towel d'inta daya bayyana santala santalan k'afafunta,farare tas idona yakai ga bombom d'inta zaro ido nai nace masha Allah madaidaita masu ban sha,awa,komi dai jikin fiyah masha Allah,komi yaji gashinta kwance yake kan tsakiyar bayanta,toilet dake cikin d'akin nasu tashige *fiyah* kenan matashiyar budurwa yar shekara ashirin cif. *********** "Dr kakirani kuma kanata y'an rubuce rubuce,na matsu naji wane hali d'an uwana yake ciki." Ajiye biron hannunsa yayi yana cewa"sorry abokina,ya sunanka ma dai." " *malik*" yafa d'a atakaice Dr yace"nice name,yi hkr malik ina rubuta wasu magungunan nanne,i think wad'ancan bazasuyi mashi aiki sosai ba." Shafa kanshi yayi yana fesar da iska yace"nifa ba wannan natambayeka ba cewa nai wane hali yake ciki yanzu,shine abunda nafi bukatar ji daga gareka." Ajiyar zuciya Dr ya sauke yace"ka kwantar da hankalika ya dawo ciki hayyacinsa,munyi masa d'inkin raunikan da yaji,sannan munyi kokari munga muntsayar dajinin dake fita ta jijiyar da aka yakesa.yanzu haka jini meke karamai........shiru yayi na wani lokaci kafin ya sake kallon guy d'in yace"amman ya akai kabari brother naka yakeshan giya,giyarma the most high one." Sadda kai yayi yana jin wani irin bakin ciki cikin ransa,mezaicewa dr shin cemai zai eh yasani yanasha.koko aa bai isa hana Alfah yin duk abunda yaga damaba,adacan ma bai dakatar dashiba balle yanzu daya sake rikicewa,babu maigane gabansa balle bayan sa.don yayi imanin muddin ya farka yasan cewa asibiti yake ba karamin rigima zasuyi ba........."kayi shiru abokina." Gyara zama yayi yace"nasani dr saidai banda yadda zanyi dashine yafi karfina wlh.nayi iyakar duk kokarin dazan wajen ganin yabarta abun yaci tura," Kallonsa dr yake fuskar sa ta nuna 6acin rai"mekake son gaya man,wannan ba reason bane ina iyayensa ina mahaifiyarsa duk yake wannan,sannan kaikuma bakaje ka sanar dasu ba kasan mekayi kenan?to kaci amanar su kai Allah zai kama da laifi tunda kasan hakin da d'ansu yake ciki bakaje kasanar dasu ba sud'auki mataki.to gashinan tafara mashi illah donma yayi sa,a ni ban ta6a ganin wanda yake ta ammalli da irin wannan win dinba bata kasheshi har lahira ba,yaci sa,a bawani dayawa ta ta6ashiba amman ka sanar da iyayensa su sai sudauki matakin dakatar dashi,tunda kace baijin maganarka." Maganin ya bashi yace yaje waje yasiyo don nan basu dashi gaskiya. Fita malik yayi yana cikin tsananin tunani da maganar dr. "Oh ni malik,yazanyi da Alfah taya zan tursasa sa yabar shan win,ban isa ma nayi mashi wanan maganar ba,ni na isa addua ce kurin maganinsa don ko hauka nafara sabon kamu ban ma tunkarar *maitama estate* ni yanzu ubanwa ya haifeni balle har nakai ga isa gidan *ALH MAINAH* ince d'ansa yana cikin matsala wlh kaf rayuwata gidan kurkuku zan k'areta.zandai yiwa Alfah Addua ubangiji ya kawo wani cikin rayuwarsa da zai tallafeshi,yafitar dashi daga cikin wannan *bakar rayuwa* Uhmm masu karatu yanzu muka fara,ko yatsa bamu tsoma ba,fatan za ku cigaba da kasancewa dani ahankali zan warware maku zare da kuma abawar.kudai kugyara zama *ABDOUL-NASSER (ALFAH) YANA TAFE SA ABUBUWA KALA KALA* MRS BB CE MOM MUHSEEN😉😘😘 [9/17, 3:34 PM]mom muhseen💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.....2 Taxi ya shiga yana cikin tsananin tunani,har tsoran farkawar Alfah yake,don shikadai yasan rigimar dasuke don dai Allah yabashi juriya da kuma hakuri,da zaman shi da Alfah bazaije ko inaba. Yadda kowa ya gujeshi shima da tuni yadade da kama gabansa,saidai alkairin da yayi mashi bazai iya saka k'afa ya shure shiba,bacin haka yayi alkawarin da bazai iya karya shiba,hkr dai shine zai cigaba dayi watan watarana komi zai zo ya wuce. Wani k'ayataccen pharmacy yaje kamar ba a nigeria ba yasiyo maganin,ya taho yana adduar Allah ya taimakeshi yasha maganin,duk da abun zai wuya Alfah ko ciwo me zai kasheshi idan ba yaga yana mashi kuka ba tofa bazai shaba,karshe har yagane inayin hakanne don yasha d'in.to dana fara kuka zaibar mun wajen.dafe kai yayi yana ajiyar zuciya kurun....... *********** "Mamana Zan wuce isalamiya,duk da dai na makara,idan yasmen ta dawo don Allah ga hijabina nan ka igiya mama don Allah ta wanke mun." Mahaifiyar tasu data fito daga d'akin sanwa tace"baki tausayinta Fiyah,tun safe fa bata gidanan. tana can tana wahala da gidan jamila,nasan in ta dawo ta gaji kiyi hkr kisaka wata mana." Tsaye take bakin k'ofar d'akinsu tana saka safah,tace"shikenan mama idan nadawo na wanke,daman abunda yasa nace haka jinai nafara atishawa ina tsoran tab'a ruwa,gashi kinga yau akwai sanyi sosai." Maman tace"subhanallahi,aikuwa in hakane kibari na wanke maki,inma dole sai ita zakisa,injin tsoran wannan lamoniyar taki Fiyah." Jikkarta tad'auka tana murmushi mai tsananin kyau tace"kibarshi mamana,zan saka wata bari natai saina dawo in babana ya dawo ki sumbatar mun shi amadadin." Duka ta kawo mata ta ruga waje tana dariya,ita ma uwar dariyar tayi tana cewa Allah ya shirya ki sofiyyah." Tafiya take cikin estate d'in wanda babu kowa cikin unguwar tasu,hakan yazama dabiar yan unguwar badai kasameta da mutane sosai ba,sauri take ta isa bakin titi tasamu taxi batason ta rasa qarin ahalarin da za,ai masu yau............get d'in estate din taga an wangale,bayanta ta waiga ta hango wata dan k'areriyar G wagon fara tas zatafita. ta saba ganin irin wad'anan motocin cikin unguwar tasu *maitama estate* domin kaf unguwar babu karamin mutun duk manya manyan y'an siyasane da masu manyan mauk'ami,gaba ki d'aya unguwar sune suka fita daban,sune kaskantattun talakawa ababen kyama,don babu mai hudda dasu cikin unguwar inbanda gida guda.......don ana kallonsu wulakantattu wad'anda talauci yayiwa katutu,bacin su sunsan suna cikin rufin asirin Allah basu rasa ciba,basu rasah shaba,mahaifinsu yananiyakar kokarinsa don gani ya kawar da idonu aka kallon nawasu,taaye kan iyalinsa......... wani uban burki aka taka gabanta,duk saurinta bata samu ta riga motar fita ba,ajiyar zuciya ta sauke tana kallon wadda ke cikin motar tana murmushi. "Kin bani tsoro rafeea,ashe kin dawo shiyasa ma ban shigaba." Dariya tayi tace "matoraciya kawai,shigo mu wuce baki ga time ba,nadawo wlh ko minty ashirin banba wanka nai nai salah naci abinci kurun nafito." Bud'e motar tayi tashiga tace"kinfi kowa sanin Fiya bata da waya aiko.rabona da time tunkan nafito gida " Dariya rafeea tayi tace"to uwar gasa magana namance,amman fah gaskiya ya dace ace yah jalal ya barki kirik'e waya hakanan." Murmushi tayi tace"kinmance waye yah ko,to ni ai ban mance ba,amman nasan soon zai siya man tunda daman jira yake saina fara jamia." Haka suka ringa fira har suka isa makarantar,kasancewar sometimes tare suke tafiya saidai idan daya bata dawo makaranta da wuri ba. ************ Kamar karya shiga d'akin don yana gudun ace ya farka,saidai kuma inhar Yafarka tokuwa bazai zaunaba ficewa zai...........ahankali yashiga d'akin ya ajiye ledar magungunan yana kare mashi kallo,yanajin tsananin tausayinsa yana ratsashi......kwallah suka cika idonsa ya kalli hannunsa da aka nad'e da bandeji ya girgiza kai yana tunano abunda yayi dalilin faruwar hakan. _Waiwaye_ Exercise yake d'akin motsa jikinsa,don shikadai yake yi malik baida ra,ayin sa yakai one awa yana gudu kan injin gudun,kafin ya sauka ya dauki wani gingimemen karfe yana d'agawa shima yajima yana d'agashi kamar ba karfe yake d'agawa ba saboda yadda yake d'ashi kamar wani tsinke.......malik ne yashigo wajen dauke da tiren breakfast,ya ajiye gefensa yana cewa"tun bakwai nasafe kake nan wajen gashi har sha biyu saura ka ajiye kasaka wani abu cikinka." Kamar yana magana da dutsi haka yayi mashi,kasancewar malik baya fushi da Alfah duk abunda zai mashi,saboda Nauyin da yadaukar wa mahaifiyarsa da kuma wanda ya daukar wa kanshi.............maganar yasake nanata mai yasake banza dashi tashi yayi ya isa inda yake,ya dafa shi yace "Alfah duk wannan abun da kake baya canza komi,kuma bazai canza ba kayarda da kaddara mana,akwai fa wad'anda suka fika shiga kunci kuma suka fawwalama Allah,saikai kace bazaka yi biyayya ga hukuncin Allah ba.sannan Nariga nayiwa momi alkawarin kulawa da............... *malikk!!!* ya kwatsa mai tsawar da saida tasaka malik firgita,jefar da karfen da yake d'agawa yayi yana zazzaro idanu,dandanan fuskarsa ta idasa rikicewa da tsananin masifa.......tunkaro shi yake yana ja baya har suka dangane da bango.hannunsa yana kerma ya daga shi ya kaiwa bango naushi,dan danan hannun ya fashe,saboda bangon ba kamar irin na bulo bane,wani sumfarine nadaban. donsa yayi masifar jaa cikin voice d'insa mai firgitarwa yafara magana cikin dakiya, "Wlh wlh wlh kajidai rantsuwa uku ko in kasake gigin anbata mun sunan wani cikinsu saina kashe kaina,har sau nawa zan jamaka kunne ne wai ehy." Furzar da iska yayi yana huci ya matsa daga kusada malik yana jan numfashi,duk da tsananin tsoran temper dinsa da yake,hakan bai hana shi sake magana ba,don yana ganin inyace zai ringa kyale shi bazai ta6a sauraren sa ba,balle har ya samu zuciyarsa tayi sanyi. "Wallahi Alfah kome zakai saina fad'a maka gaskiya,ayanzu bakada wani wanda zaigaya maka gaskiya saini,dole nafada maka kokayi aiki da ita ko karkayi nidai saina sauke nauyin alkawarin mahaifiyar.............wani uban naushi ya kawo wa malik,yayi aurin kaucewa azafafe,yanzu ma bangon ya kaiwa bugu amman saboda zafin rai bai damu da halin da hannun nashi yake ciki ba. Cikin wani irin yanayi ya ya kalli tiren daya malik shigo dashi,wata yar wuk'a ya gani baiyi wani tunani ba ya daukota,babu wani jinkiri ya saita hannunsa ga6ar hannunsa na dama ya yanke jijiyar dake wajen.dananan jini ya 6alle kamar an kunna famfo. Wata k'ara malik ya fasa yana tunkaro inda yake,shikuma yana ja baya yana cewa"karka nufoni,indan ka iso nan wlh saina sake yanke wata jijiyar,kafita anan inb fita ba nizan fita malik karka matsoni,kabarni na mutu kabarni natai inda zan fi samun jindadi,kuka malik keyi yana cewa"Alfah waya gaya maka mutiwa hutuce,mekayi wa Allah daza katai dashi matsayin guziri,inhar kamutu ahalin yanzu wlh wuta ce makomar ka......karka fita Alfah katsaya katsaya nace..........amman bai saurari malik ba ficewabyai daga cikin d'akin,waje ya nufa yannunsa jini kurun yake fitarwa b kadaba........kfi Malik yafoto tuni alfah yafice daga gidan,tafiya yake baisan inda yake jefa k'afarsa ba.........ko minute biyar bai da fitowa ba zai tsallaka titi,mota tayi sama dashi ya zube wajen babu numfashi. _back to story_ Likitanne yashigo yace"bai tashiba kenan,"malik yayi ajiyar zuciya yace"eh dr gashinan naga ma kun cire jinin,gashi ruwan shima ya kusan karewa.......akwai sauran ruwan da za asake saka maine." Dr have"sauran leda biyu hudu ce ansaka biyu,saura biyu da wani abune?" Shafa kai malik yayi yace"bani son ya farka ba agama saka ruwan ba,don ba lallai ya zauna ba daya farka zai iya fixge carnula ya fice." Jinjina kai yayi yace"wane irin mutunne shi haka,na lura yana da wata irin zuciya amma da gani akwai abunda ya faru dashi baya,don nidai nasan wannan fuskar sai yanzu na tuna inda nasanta.watarana na bar wajen aiki nan ina sauri zanje gida saboda maidakina tamun waya gidan babu lafiya,saurin danake yasa har nabanki wani mai anoconder kuma nai mashi babbar 6anna.........dandanan titin ya cika yafito yana ta bala,i saina biyashi gashi ko sisi ban dashi ga aljihuna,ga shi yaci kwalata duk hkrin da ake bashi ya rufe ido cewa saina biyashi,saiga wannan bawan Allah cikin mota shida driver sa,fitowa yayi yana tambayar lafiya? don titin ya cinkushe babu hanyar wucewa. Bayani nai mashi da halin da nake ciki na sauri inje ga iyalina.wlh malik check ya rubuta ma mutumen,na five hundred thousand bacin kuma kudin duka dubu dari uku ne..........naita mashi godiya ba karamin dadi najiba kullum ina adduar allah ya had'ani dashi inyana neman taimako nima nataimaka mashi." Malik ya yi ajiyar zuciya yace"Dr labarin mai tsayine kuma bazan iya baka shi ahalin yanzu ba,saidai ko nan gaba,amman tabbas Alfah yana cikin halin taimako,wlh nikad'ai bazan iya shawo kanshi ba." Gyara tsayuwa dr yayi yace"na fahimceka malik,karka damu ga ID card dina nan duk sanda kake bukatar taimakona,ga address dina nan ajiki da contact dina,insha Allah nima zan bada tawa gunmawar karka sare kacigaba dayin iyakar kokarinka har mukai ga ci...............shiru sukai ganin yana jujjuya kai yana ya mutse fuska,kafin ya bud'e idinsa yana kallon rufin d'akin..........idonsa ya sauka kan Malik da dr suna kallonsa suma. Da alama yana nazarin abunda yafaru dashi ne.duk sunyi zuru suna kallonsa gaban malik na fad'uwa saboda gudun abunda yake tunani.......ai baigama nazariba yaji wata irin shak'a da ya kawo mashi ya gama shi da bango,idonsa saboda tsabar masifa da zuciya kamar anzuba mashi garwashin wuta. "Meyasa kakawoni nan ehy,banace karka sake ka tab'ani ba,meyasa bazaka barni nabar masu duniyarba!"cikin tsananin tsawa yake maganar ya cigaba da cewa"malik!ka cuceni kacuce ni nace,yafada yana jijjigashi kafin ya tunkud'a shi ya fad'i. Kallon carnula dake jikin hannunsa yayi yayi mata wani irin fizga,dandanan ini yace yaga hanya k'ofa ya nufa atsananin fusace ya bude yafice tare da bankota da mugun karfi........Dr da malik binsa sukai agune don ahalin da yake ciki komi zai iya faruwa dashi yadda yake tafiyar zaka gane cewar gentle guy ne kuma k'ak'k'arfane.........gudu suke yana sauri shikuma amman sun kasa kamoshi,har sun bar titin asibitin sun yanki wata hanyar daban,duk yadda suka zo iskeshi abun yacitura........titin nasarawa suka hangoshi zai tsallaka kenan wata mota ta rugo da mugun gudu jikake..........kuuuuuuuuu karar burki da cin taya. Command share pls. Mrs bb ce Mom muhssen [9/17, 3:34 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.......3💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.......3 Iya kar karfinta ta taka burkin,hankalinsu inyayi duba ya tashi.don sunyi tunanin sun banke shin,amman sadda ta bud'e idonta taganshi tsaye yana jiran motar tabi ta kanshi........daidai sadda su malik suka karaso wajen sai shashshekar gudun dasuka yi suke,da sauri suka fito daga cikin motar duk sun rud'e.don *FIYAH* tuni ta fara kwallah don gwanace wajen tsoro ........cikin sa,a Dr ya rik'esa gam yana kallonsa,idon nan nashi ya canza launi ya tausasa murya yace"plsss Alfah miye haka ya kakeyin abu irin na marasa hankali,meyayi zafi har haka ka tausayawa kanka kakuma ji tausayin wannan bawan Allahn abokin naka." Rafeea duk ta tsure saboda tunaninta ta bankesa saboda yadda ta taka burkin daf da shi sosai. "Assalamu alaikum,bawan Allah bakaji ciwo ba dai ko,kuyi hkr wlh ina saurine shikuma ya hau titi bai duba gabansa ba." Wani kallon wulakanci yajefa mata ya fixge hannun sa daga na Dr yana dogon tsaki,fiyah na gefe tana goge kwallah ganin babu abunda ya same sa........ran rafeea ya b'aci ainun,da abunda Alfah yayi mata kallon shi tayi,cikin fushi tace"dallah malam miye nayi man tsaki,daga d'an kuskure kadan zaka wani yiman kallon wulakanci,kana jaman tsaki ni nace kahau kan titi babu kulawa, ko angaya maka titin dakin gyatumarka ne ehy,"taja dogon tsaki ta juyawa zata bar wajen. Jitai kurun anfizgota kamar kwali omo cikin zafin nama,wani irin jan rik'o yayi mata baiyi wata wata ba ya saka tafinsa tare da iyakacin karfinsa ya kwalhe ta da kyakkywan mari. Ga baki d'aya wajen sun shiga shock,Rafeea jitayi ganinta ya d'auke da jinta.......idonta sun kada sunyi jajawur kamar gauta wata k'ara ta fasa tana dafe da wajen...........aguje fiyah ta karaso wajenta tana rikeda ita,jikinta rawa yake saboda yadda karar marin tafita. tabbas kasan wanda akai mashi ba karamar d'imuwa zai shigaba.cikin tsananin tashin hankali Rafeea ke kuka tana dafe da fuskarta,cikin kaushin murya yace"daga yau zakiyi gigin zagin wani bama niba,don ubanki yar iska da iyayenta basu bata tarbiyya ba." Ya fizge daga hannun dr da malik,yajuya tari taxi zai shiga yajiyota tana cewa"shege d'an iska,azzalumi ban yafeba wlh saina yi silar zuwanka gidan yari mugu........azafafe yadawo wajen malik na rik'eshi yana cewa"haba Alfah karka biyeta macece zaka iya rauna ta tafa,wani irin juyowa yayi yana kallon malik yace"nasan da cewar macence ai shiyasa zan koya mata hankali yadda zata ji tsoron tunkarar namiji ko bani ba,don ubanki ba gidan yari ba kisaka akaini lahira inkikai hakan zan dawwama ina saka maki albarka jakar banza," Kuka take tana cewa"wlh sai babana yayi sanadin ajalinka,inhar yasan kaine ka mareni zaka gane kurenka mugu........k'afa yasa zai halbeta yaji anrik'e k'afar caraf cikin mamakin wanda yarik'e kafar sa yake kallon wajen........ *fiyah* ce tayi han zarin rik'e kafar tana hawaye duk sun wanke mata fuska,wani irin wurgi tayi da k'afar tana share kwallarta ta mik'e daga durk'ushen da take gaban Rafeea,cikin d'aurewar fuska kamar ba fiyah ba,cikin masifa da y'ar muryar ta kamar ta yan yara tace, "Kar ka sake gangancin dukanta,kai baka da imanine ehy,bakasan kima da darajar mace ba,ana gaya maka cewa macece karka biye mata kaji mata ciwo,shine kake son sake kaimata duka,to kasani wlh muddin mahaifinta yaji bakaiba kaf danginka sai akulle tsinann..........cikin fita hayyaci Alfah ya yunk'uro zai kwasa mata nata marin,tai saurin ja baya Malik da dr suka rik'eshi......cikin zafin xuciya yace"kubarni na lahanta yan isaka.....janshi sukai har cikin taxi d'in daya tsayar d'azun suka shigar dashi daker, sadda xai shiga saida ya juyo idonsa cikin na Fiyah ya nunata da yatsa,yana girgizashi alamun worning. Harara tabanka mashi tana mashi alama da hannu wuce kaidai. Dr yace wa malik"abokina kaban no dinka pls don koda kai baka nemo niba nizan zo har gida induba jikin nashi,don zamanshi babu kulawar likita hadarine ga rayuwarsa." Babu damuwa ya ansa wayar yasa mai sannan yayi mashi asauka lfy. Lallashin Rafeea take tana cewa"kiyi hkr muje gida kinga dare yayi nasan sai nasha fad'a wajen baba da mama,tashi kiyi hkr inkinje gida kisanar da Abbanku nasan dole zai daukar maki mataki,dole ne ma wannan." Tashi tayi tana share kwallarta don har ga Allah mari ya shigeta ba kadanba. Dr ne ya iso wajen yana cewa"kiyi hkr Rafee,atu karki sanar da Alhaji kiyafe mashi bai cikin hayyacinsa hakan tafaru." Cikin masifa tace "shine zai juye haukanta sa akaina wlh saina fad'a ai gabanka yayi man wannan zalincin ko kuma baka dauki mataki ba",ta nufi motarta tana masifa. Tafiya suke zuwa gida fiyah tace"kinsan dr ne Rafeea." Tsaki taja tace"likitan kakane shike zuwa har gida yana dubata duk karshen wata." Jinjina kai tayi tace"amman baza kiyi hkr ba Rafeea kiyafe mai tun da kinji cewar baya cikin hayyacinsa hakan tafaru,don inkin lura hannunsa jini yake fitarwa,kuma sai yanzu na ganeshi shine wanda d'azun na taso makaranta aka bankeshi kan titin central park,na yarda da dr da yace bai cikin hayyacinsa ki yafe mai." Tsaki taja tana kara gudun motar don tuni angama sallar mangaruba, "Ki kyaleni fiyah,wlh saiya gane cewa ya tab'o yar gidan Alh muazzam Canji." Shiru fiyah tayi don daman tasan za,ai hakan Rafeea na da fada aji wajen mahaifinta,don kuwa ita dayace mace wajensa,jida ita yake sosai duk abunda takeso yi mata yake,kuma duk wanda ya tab'ata yashiga uku don bazai kyaleshi ba. Saboda haka mahaifin fiyah baison alakarsu,don dai kurun mahaifiyarta macece mai tsananin kirki da mutunci,shiyasa yake d'an barinta tana shiga gidan kuma take hudda da Rafeea,badan ransa yasoba.don yadda duk estate din suka kafa mashi k'ahon zuk'a akan zamanshi cikinsu,shiyasa yake iyakar yinsa don ganin ya kiyaye abunda zai saka suci mashi mutunci. Har suka isa gida fiyah bata sake cewa komi ba godiya tayi mata da kuma saida safe kowace ta shige gidansu. "Assalamu alaikum...........ina kika tsaya sofiyya badai kijin maganata ko,bance inkinga wannan yarinyar zata shiriritar dakeba ki kamo hanya kidawo gida,banson wannan alakar taki da ita ko kad'an kinsani,amman ina hakuri ne saboda mutuncin uwarta,amman inbacin haka bazan bari kina shigewa wadannan mutanen a da basu san mutuncin mu ba." Duk Malam kabir El-ladan ne yake wannan fadan watau mahaifi ga sofiyya. Sadda kai tayi tana idasa shigowa cikin gidan,durk'usawa tayi gabanshi cikin ladabi da biyayya tace"baba kayi hkr wlh akullum ina kokarin kiyaye duk abunda kake gaya man,matsala aka samu shiyasa amman dawuri muka taho." Ta zayyane mashi duk abunda yafaru tacigaba da cewa"wlh baba dagaske Rafeea take zata iya fa da ma Abban su kuma har prison yana iya kaishi." Baban yace "Allah ya kyauta,ni shiyasa banson kina shiga motarta yanzu dada tsotsai wani abu yafaru fa,ki kiyaye ba koda yaushe zaki ringa shiga motar ta ba kinjiko mamana." D'aga kai tayi tace"insha Allah baba zan kiyaye kayi hkr." "Shikenan,nayi tashi kije kiyi sallah Allah yayi maki albarka." Tashi tayi tana ansawa da Ameen maman tace intayi sallar tazo ga abincinta nan ta d'auka,shigewa tayi d'akinsu tana magana da yesmin dake ta faman gugar uniform. "Yaushe kika dawo yesmin." Tace"Adda nah nima ban jima ba uncle yahya ya ka woni bajima wa,anty tace gobe inkin taso kibiya tana da magana dake." Kayan ta ke cirewa tare da cewa"uhm ni wlh Anty zata matsaman kan wani kanen mijinta,ki kyaleta kawai yesmin ni 6allemun wannan abar." Tana juya mata baya ta 6alle mata bra d'inta. ************* Tunda suka dawo gidan malik baiyyi gigin sake mashi magana ba,don yasan yanzu zai sake burkicewa babu mai taimakonsa kuma,don unguwarsu ba sosai mutane ke shiga sabgar da batasu ba. Malik ya dawo daga masallaci sallar isha,i ya samai falo shima ya gama tashi sallar agida yana d'auke praymate d'in. Girgiza kai yayi kawai don baisan yadda zai yasa Alfah cigaba da yin sallah cikin jam,i ba,ko masallacin bai zuwa duk sallar dazai tofa cikin daki zaiyyita.fuskarnan kamar kullum tur6une babu walwala babu rahma kanta. Zama yayi yana kallonsa kafin yace mashi. "Me zakaci abokina" Kallon banza ya wurga mai kurun yana cigaba da opreting system d'insa,xuwa can ya ajiye ya tashi yaje gaban frig ya bude win d'insa ya dauko ya cire hancin,ya bulbula ga cup ya koma mazauninsa yana kurb'a yana aikinsa,....kallon bakin ciki da takaici kawai malik kemashi,don baima san yazaiyyi da Alfah ba,idan akwai abunda yatsana cikin halayyarsa sabbi to bai wuce wannan shan win d'in da yake ba. Kasa hakuri yayi yace mashi"Wai Alfah mai yasa kakeson kashe kanka,meyasa kai rayuwa baka daukar komi da sauki,duk abunda Allah ya kaddara maka baka hkr karok'esa sassauci,ina anfanin wannan halayyar daka k'irk'iro ma kanka...........cikin masifa dazafin zuciya ya jefar da cup din glass din dake hannunsa ya fashe kasa,yana huci. Yanuna malik da hannu yace"kafita harkata malik,kadaina takurani da kalamanka,komi nake komi zanyi is not ur business." Hawaye suka cika idon malik yace"komi zakace kuma kome zakayi man Alfah wlh saina gaya maka gaskiya,koda kuwa kasheni zakai wlh saina fad'a,don kuwa ina kaunarka inason rayuwarka idan kai bakason ta,ka taimakeni ka kulaman da ita,idan narasaka Alfah yakake son inyi,banfa da kowa saikai.Allahne gatana kaine gatana.plsss karage shan win d'inan koda baka bari dukaba dr ya sanar dani yadda tayi maka illah." Kwallarsa suka silalo kan fuskara yaciga ba da cewa"Allah yasan da abunda yafaru baka da laifi,amman ya6oye gaskiyarsa saboda yana son jarabtarka yaga iyakar imanin ka,duk wannan ba daidai bane,kuma kaima kasani kake take sanin.....cikin sanyin murya ya katse malik da cewa"enough!and i'm sorry to hut u." Tashi yayi yashige bedroom d'insa da system d'in sa ga hannu. Murmushi malik yayi yace "thank god,yaushe rabon da naji irin wannan sweet voice d'in naka Alfah,ina maka fatan Allah ya sanyaya zuciyarka ya kuma kawo mani matai makin da zamu taru mudawo dakai cikin rayuwa mai kyau. *sorry jiya banyi update ba in busy ne kuyi hkr.* Mrs bbce Mom muhseen😘 [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........4 Tun asuba da ta yi salla bata koma ba,kasancewar itakeyin duk ayyukan safe kafin tatafi makaranta,sharar tsakar gida ta farayi sannan ta gyara wajen dabbobi,ta samasu abinci da kajin suma.sannan ta wanke bayinsu ta fiddo wanke-wanke ta share kitchen din,sanwar kalaci ta dora sannan ta fara wanke-wanken,sai lokacin yesmin ta fito daga cikin d'aki tana hamma. Kallonta tayi tana murmushi tace"kasa uwar bacci sai yanxu aka samu damar tashi,to azo ayimun d'auraya." Dariya tayi tana kallon gidan tace"sannu Adda nah,kina kokari fah ni ban sanma baccin ya sace ni ba bayan sallar asuba." Tana d'auraye plet cikin ruwa tace"hada gajiya ke damunki bakya samun hutu sosai,don ma kun samu interval aida abun ya maki yawa." Zama tayi tana yi mata d'aurayar suna hira. Tsakaninsu Babu nisa don ashekaru,duka shekara biyuce ta shiga tsakaninsu,suna matukar son junan su duk abunda ya samu guda kamar suduka yasama,mahaifiyarsu tayi tsaye wajen tarbiyyarsu,don suna girmama yayunsu jamila da jalal,watau babban wansu yana aiki ne a kaduna,bai cika zama ba wata secondary school yake koyarwa. Malam kabir El-ladan shima malamin makaranta ne,amman ya jima dayin retire tun tuni yanzu yana zuwa wani karamin company na hada kujerun amare da gadaje,yana aiki wajen babu laifi yana d'an samun na rufin asirin sa,don kullum ake biyanshi. Ita kuma maman su kiwo take na dabbobi da kaji,tana daukar d'aid'ai tana siyarwa idan bukatar hakan tatashi,kuma ta kafa shagon sayar da kayan masarufi ak'ofar gidan,babu laifi suna ciniki don duk unguwar babu shago sai nasu,don dole masu kudin unguwar suke siyayya wajen,don inkana son abu dole saika je bakin titi.,ganin wiyar fitar yasa suka hkr suna siye awajensu,don bayarda suka iya,don basu son duk abunda zai hadasu da wannan kaskantaccen talakan,cewarsu kenan. Kafin mamansu ta fito har fiyah ta dama koko,ta dora juluf din taliyar hausa da zasu had'a da ita.......kafin karfe takwas har tagama komi tayi wanka ta shirya,sai albarka maman take saka masu baban daman tun shidda yake fita,sai goma yadawo ya karya sanan ya koma sai kuma dare don can yake cin narana. Yesmin ta fiddo wankinsu nata dana Addar ta dana maman,tana yi don yau bazata ko ina ba kasancewar weac da suke amman sun samu hutun kwana biyu. Fiyah ce ta fito sanye da doguwar rigar atamfa purple and pink sai lemon green,tayi masifar daukarta duk da babu kwalliya fuskar sosai,hakan bai hana tsananin kyanta bayyana ba,purple din hijab tasa iyakar guiwa mai hannu,sai jikarta itama purple din da takalmata,fiyah badai daukar wankaba ta iya had'a matching color,bata yarda tayi hadin gambiza,kuma antyn ta jamila ta koyar da ita salon daukar wanka.........ruwa tasha tana tambayar maman su karfe nawa tace mata , "Kina da sauran lokaci ki natsu kigama." Tana goge takalminta tace"mama jiya ban samu morning lecture ba yadda ya kamata,yau bazan so haka ba." Takalmin ta sa mamar tana mik'o mata dari biyar tace, "Gashinan Dari uku yabaki naga bazata isheki ba yasa nace yesmin ta anso maki dari biyu wajen dalha kikara." Rungume maman tayi tana murmushi"nagode mamana Allah ya barmana ke." Ta sun baceta ta fice tana ma yesmin by by. Sauri sauri haka ta fita cikin estate din zuwa bakin titi ta tari taxi. 💞💞💞💞💞💞 Tun safe malik ya fita zuwa company don yana aiki da company Alfah,mai suna *FATION&DESIGNER'S BANGLES COMPANY* nasa ne na kansa,suna siyarda sumfarin yan kunne yan hannu,sark'a da links na maza,agoguna new moden design ba karamin kudi suke samu ba,daga kasashe ake zuwa wajensu siyen d'ai d'ai ko sari,babu kasar da Alfah baya zuwa shida malik akan wannan kasuwancin,gefe guda kuma ga shopping mall d'insa duk malik ke kulawa dasu,bakamar yanzu da abubuwa suka rikice komi yake neman tsayawa ya lalace,dole malik ya tashi tsaye don ganin basuyi asara ba kuma basu rasa customers ba,dafarko cewa yayi yabar aikin bazai sake zuwa ba,saida malik yatusasa gaba yana kuka da ban baki sannan ya amunce yake yin aikin kan computer,duk abunda zaiyi acan office yana yinsa ga computer,saidai guiding din ma,akaitan da ya saka shakikansa dake cikin company suke mashi CID,kuma yana lura da komi ta computer shima,don kwanakin baya saida yakori wasu ma,aikata dasuka so sujawo masu matsala. haka zalika malik tsaye yake akan dukiyar abokinsa safe rana dare ,kuma duk wata yana fidda albashin ma,aikatan su aba kowa hakkinsa. don ma kayan yanzu sunyi ramai ramai,suna bukatar sabbin kaya amman yayi-yayi da Alfah su shirya sutai paris da sauran kasashen dasuke zuwa saro kaya masu inganci,yace bazaije ba inkuma ya matsa mashi wlh saida company zai ya kyautar kudin,mafarin ya kyakesa kenan. Kwance yake wajen swimming yana shan iska,ga table dinsa nan kwalaben win d'insa wajen uku,ya shanye biyu saura guda itama ya sha rabi. Ko ka dan giya bata bugar dashi,irin yadda take bugar da wasu sukoma kamar mahaukata,zaiji shi yana layi amman daya kwanta yayi bacci zai wartsake,amman idan akai kuskuren tunkarar sa cikin wannan condition din tofa akwai damuwa,don shikanshi baisan 6annar da zai aikata wa kowaye ba,hakan da malik ya lura yasa idan yana cikin mayensa baya kulasa.fita yake yabar mashi gidan har sai ya tabbatar ya lafah sai yadawo. Malik ne ya iso wajen yana rik'e da computer akwai wasu bayanai da yake son nuna mashi,na email,don sakonnine na abokan kasuwancinsu suka turo suna bukatar zuwa cikin satinan idan ya anshi gaiyyatar, zasuyi wani ciniki idan yana da lokaci. Idonsa arufe yake yad'ora d'aya kan d'aya,girgiza kai malik yayi zai juya don yasan bazai bashi hadin kai suyi magana ba inhar yanancikin wannan halin. Jiyai yace mashi"kafasa abunda kazo yine" Ajiyar zuciya yasauke yana dawowa ya zauna,laptop d'in ya tura mashi gabanshi yana cewa"bak'i garemu suna neman iznin zuwa don suna son siyen kaya,gashi kayan babu masu kyau sosai duk an zab'e shiyasa nace maka yadace kaban dama ni naje idan kai bazaka ba." Tura mashi system din yayi yana cewa"katura masu acceptance latter,zuwa opper week sai suzo kafinan har kaje kadawo." Dadi yaji koba komi yau ya sauraresa duk da yana cikin halin maye,mikewa yayi zaibar wajen wayarsa tayi kara,ya duba yaga ba suna dauka yayi yana sallama. "Wa'alaiku mussalam,da malik nake magana." Malik yace"yes i'm malik muazzam." "OK Dr ne don Allah katuro mun address din inda zan sameka." Kallon Alfah yayi daya kai cup din win dinsa bakinsa yana sha cikin kwanciyar hankali,amman fa kokadan hakan bai nuna kan fuskarsa ba,malik yace"ok dr bari na turo maka ina gida ban kaiga fita ba." Text ya tura mai sunan unguwar da kuma stress dinsu da no. Gidan nasu. Wucewa yayi cikin gidan don cigaba da aikinsa. ******** "Yallabai gashi yaturo,amman don Girman Allah yallabai karka saka adaure wannan bawan Allahn,wallahi nagaya maka baicikin natsuwarsa hakan tafaru,kuma naba Rafeea hkr cewar baiyyi don yana sane bah." Cikin fushi Alhaji kwangila yace"karka raina man wayau Dr fahad,ya d'aga kantamemen hanunsa k'azamin hanunsa ya wanke y'ata da mari,sannan ya zageta har ya hada dani sannan kace inkyalesa wlh ko waye ubansa yau sai ya gane kurensa,saidai shi yaji tsoron sake aikata haka akan wata badai Rafeea ba." Shiru Dr yayi yana daya sanin sanar dashi cewar yasan sa. Waya Alhajin yake cikin fushi cewar"yanzu yanzu nakeson kuje ku kama shi,karku ragar mashi har sai nazo zan biya na dauko feea makaranta zamozo tare,ga address din gidan nan zan turo maka." Kashe wayar yayi yana kallon dr daya sha jinin jikinsa"kodai dan gidankune sai haka dr jibeka yadda duk kawani lafke,garama katashi katai don wlh bazan ragar masa ba,da dai wani yata6o mani ba Yarlelena ba to da saina sassauta mashi,amman wlh bazan lamunci abunda zai ta6a man feea ba." Ta shi Dr yayi yana jin babu dadi kuma yasan malik zaiga yayi anfani dashi don ya cutar da Alfah bacin ba haka yaso ba,abun yafi karfinsa Alhji kwangila baida tausayi ko alama. Malik na cikin gida yaji an danna bell d'insu tashi yayi yasan ko za,a shekara dubu ana danna wa Alfah bazai tashi ba balle ya bude. Ajiye aikin dayake yayi yasaka rigarsa akan singlet din dake jikin sa. Wuce Alfah yayi yana exercise dinsa,awajen swimming d'in. Bude k'ofar yayi yana cewa"Dr u Are welcome.......wad'an da yagani ne yasa gaban sa faduwa sosai,bankesa sukai suka shigo cikin gidan,biyosu yayi yana magana cikin tsananin rudewa"yallabai lafiya,ya zaku shigo mana gida kai tsaye," Wani daga cikinsu ya shak'osa yana tambayarsa ina guy din daya mari diyar Alhaji kwangila. Duk abunda kefaruwa Alfah yana hange,ganin yada suka shak'e malik ne abun ya tunzurashi ya jefar da karfen dayake d'agawa ya doso wajen cikin wani irin fushi da zuciya. Basu san da tahowar shiba kawai ya finciko dan sandan da yashake malik ya wurgar dashi gefe har yana fad'uwa kasa. Malik ya sha gaban Alfah yana mazurai duk ya gigice don yasan tabbas aikosu akai su kama Alfah......."Aa Kadaina karka jawo mana wani tashin hankali",ogansu da sukazo tare yace"ku fiddo mana wanda ya mari y'ar Alhaji,kokuma mutai daku kuduka." Cikin muryarsa dakakka yace"nine nan sai akai yaya." Kallon mamaki suke mai ogan yace"u are under arrest." KO akwalar rigarsa ya mik'a masu hannunsa suka sa mashi unka,malik duk ya gigice yace"wlh saidai mutai tare bazaku daukesa ba wlh. kunko san kowaye shi kushiga taitayinku kafin .........cikin tsawa yace mashi " *malik!!! Karka sake wata magana anan"* Ya kalli ogan yace "muje." Aguje malik ya fito ya bisu abaya taxi ya tara yarufa masu baya,sai station. Fiyah da Rafeea school din su guda,amman kowa da couse dinsa sun fito hutun minty talatin Abbanta yakirata yace ta taho da qawarta da abun yafaru jiya zasuje police station.........jikin fiyah yayi wani irin bala,in sanyi tace"yanzu fisabilillah feea kin kyauta,saida kika sanar da Abbanku wlh baki kyauta ba to ni innaje mezance sokike nabada shedar dazata saka akullesa,nidai banji dadi bah wlh." Rafeea itama duk taji jikinta yayi sanyi tace"wlh fiyah shine ya gane bani na sanar dashiba ,ganin shatin marin yayi ga kuncina yace inban fada mashi abunda yafaru ba saiya b'ata man rai,kuma koda nasar dashi cewa nai yabarshi na yafe mashi basai ya dauki mataki ba amman wlh su yah hashim suka tirashi cewar karma araga ma kowaye." Jinjina kai fiyah tayi tace amman inkinje ai kina iya sake rokon sa asake shi kin yafe kilan ya hakura." Tace"to zan jaraba muje yace yana bakin get yana jiranmu." Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.......5 Tunda take ba ta tab'a shiga mota irin tasu Abban feea ba motar kamar ba tafiya take ba ga wani irin sanyi mai dadin bala,i mai tsananin shiga jiki. Kan kace me har sun isa station din mamaki ya cika fiyah idan da akan taxi ne sai sunyi tafiyar one hour basu je ba saboda dan banza nisan dake akwai. Kamar karta fito taji amman dolenta ta fito dandanan kuma taji gabanta yayi wata irin fad'uwa,"nashiga ukuna fiyah, idan mama ko baba yaji labarin zuwa na police station ya zanyi wlh wannan karon baba dukana zai.saida Rafeea ta jawota sannan suka fara dosar cikin station din,gabanta yana faduwa dan danan tausayin wannan bawan Allah ya kamata,tana adduar Allah yasa Aban feea yayi hkr asakesa. Malik suka fara cin karo dashi yabuga uban tagumi idonsa duk yayi ja saboda yasha kuka. ba karamar kauna ce tsakaninsa da Alfah ba,duk abunda ya samu guda to dayan yana shiga tashin hankali,wanda zaka ce shine abun ya faru dashi,haka inhar na farin cikine tofa bazaka gane wanda abun yasama ba,ko yanzu babu irin roko da magiyar da bai masuba,akan su sakeshi zaibasu ko nawa sukeso. Amman sai DPO din yace wanda yasasu aikin yafi karfin su anshi cin hanci da dai wanine bashiba,dasai su ansa su sakeshi." Alfah dake kulle cikin cell yace"malik idan har kasake magana wlh kaji narantse zanyi abunda bakaso,donme zaka ringa masu kuka iyayenka ne su don ubura ubansu wlh karka sake kask'antar da kanka kana masu magiya,idan sunga dama su barni nan har mahdi ya bayyana." Wannan maganar ta janyo tashin hankali,don kuwa ran DPO yakai mak'ura wajen b'aci yace sushiga su mashi dukan mutuwa. Malik yace"yallabai,karka yi haka wlh zaiyyi b'anna fah karsu tab'ashi za,a samu matsala." Amman bai sauraresa ba ya tura wasu constable guda biyu suyiwa Alfah mugun duka,yana jinsu baice komi ba ko motsawa baiyi ba zuciyarsa takai mak'ura rabon ma dayaji irin wannan temper d'in shikanshi bai saniba.............jiyai kurun an kai mashi duka ga baya da wata k'atuwar k'ota, cikin tsananin zuciya ya d'ago ya kalli wanda ya buge sa,ganin zai sake kawo mashi bugun.baisan ma sadda ya kai mashi duka ga fuska ba,dan danan hakorinsa guda yafita. dukanshi yake kamar Allah ya aikoshi saida yaga baya motsi sosai ya juya kan gudan wanda yafara jin fitsari don ganin irin dukan da akaiwa dan uwansa.ko kadan Alfahbai ragar masuba k'wanjinsa ya saki ya dunga naushinsu iyakar karfinsa. banda kiran sir babu abunda suke,sun kasa kwatar kansu saida Alfah yayi masu dukan da suka kasa tashi,ya bud'e kofar ya watsosu waje.....daidai shigowar su Fiyah da feea da Abban su kallon su yake yana mamaki,baki bude yake kallonsu kafin yace"mezan gani haka meye haka" Duk sunyi tsuru tsuru suna kallon kallo,koshi DPO din ya kasa cewa komi saida ya daka masu tsawa sannan yace"yallabai wlh wannan guy din dan dabane,zaginmu yayi nasa adakeshi shine yayi masu haka." Kallon Alfah Alhaji kwangila yake cikin tsananin mamaki,takowa yake yazo har gabansa yana kallonsa ya dora hannunsa kan kafadar Alfah. Cikin fusata Alfah ya ture hannun daga jikinsa yana ma Alhaji kwagila wani irin k'ask'antaccen kallo.ya jefar da hannun na Alhaji kwangila cikin wata irin murya yace masa tare da nuna sa da hannu "Kar ka sake hannunka k'azami ya sake tab'ani." Dariya Alhaji kwangila yayi yana kallon sa k'asa zuwa sama yace"ban yi mamaki ba,ai indai kaine zaka aikata abunda yafi haka,domin iyayenka ma basu iya dakai ba balle.........cikin wata irin anger yace"stop telling nonsense about my parent,if......" Shima Alhajin cikin fushi yace"if me ehy,kai har mutunne,nace kai mutunne har da zaka daga kazamin hanunka ka mari y'ata,idan iyayenka da kayiwa sun kyaleka to kuwa banga ubanda ya isa ya hanani kulleka ba wlh,muddin ba hkr kabayar ba." Feea dake bayansa idonta yaraina fata don ganin yadda fuskar Alfah tayi babu rahma ko kadan,kiris yake jira yajuye tirar dake cinsa. "Abba kabari wlh nidai dayayi wa na yafe,na hakura kazo mutai." Zare mata ido yayi yace wa DPO "ku kullesa har sai nina bada damar fiddoshi"aguje malik ya iso wajen yana tare Alfah agigice yace"baza su sake kullesan ba wlh,sannan kushiga taitayinku zaku yi dana sani akan hakan." Alhaji kwangila shima cikin bala,i yace"ubansa kadai zaizo nan na hakura kuma bazai tab'a zuwaba domin kuwa wannan dan iskan yaron ya riga yafita daga cikin zuriar su,kunsan kuwa abunda yayi kunsan irin bala,in dayayi har iyayensa suka korai to bari kuji wannan dakuke gani,matar.............jikake tas tatas Alfah ne tsaye gaban Alhaji kwangila ya wankesa da kyawawan maruka har uku. idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,dai-dai sadda wani babban mutun yashigo station din wada tacika da mutane,cikin shakewar murya da ta dishe saboda tsananin bacin rai "wlh kasake furta magana marar dadi akaina saina kasheka,saina fiddo yan hanjinka don ubanka katon banza katon wofi,b'arawon gwamnati baka iya komi ba sai yad'a karya da sharri.........kai *Abdoul-nasser* kul akul nace in ka sake magana saina sasab'a maka awajen nan." Wannan babban mutumen daya shigo yanzu yake fad'ar haka. Ajiye hannunsa yayi da yake nunnuna Alhaji kwangila dashi kamar zai kaimashi naushi,huci yake fiddawa yanajin kamar yadunga dukan bango kozai huce haushinsa......yace"Daddykabarni na koya mai hankali,kabarni na keta mashi rashin mutunci.ni....ni..zai....wulak'anta.......sai wasu zafafan hawaye suka shiga zarya kan kuncinsa. Malik kanshi hawayen yake na tausayin amininsa kuma dan uwansa. Mutumen yace"nadai ce karka sake magana idan ba haka ba zaka ga b'acin raina. tunda ya shigo duk aka k'ame ana sara mai,saboda shine comissioner of police. kallon su yake shima fuskarsa babu walwala ya kalli Alhaji kwangila yace" kagani ko,u see i tall u last time ka guji tun karar shi kar watarana ya baka kunya,Abdoul ba kunya ce ta isheshiba tun wancen karon balle yanzu da yasake firgicewa baijin kunyar yaga maka rigar mutunci,gashi kuma hakan akai bacin malik yaje ya kirani da banson iyakar abunda zai maka ba wlh awajen nan." Zufa yake share wa yana jinjina kai duk ya gigice,feea na gefe na kuka ganin yadda aka wanke ubanta da mafi,wanda yafi nata. fiyah kuwa kamar kazar da aka tsamota daga cikin ruwan zafi,duk ta firgice. Cikin taushin murya Alhaji kwangila yace ma mutumen daya ke magana "nagane hakan Alh maude,zan kiyaye." Alh ya kalli Alfah dake huci kamar tukunyar da aka gama sanwa da ita yace mashi. "Abdoul." Kallonsa yayi ido jawur batare da yace komi ba,yace"wuce kutai gida zanzo in sameku,malik idan yayi wani misbehave tell me." Jinjina kai malik yayi yana cewa"thank u Daddy." Jinjina kai yayi kurin yana cewa Alhaji kwangila "kana iya koma wa ga aikin ka,amman ka kiyaye don wataran abunda yafi haka zai maka,kekuma kiyi hkr kiyiwa Abdoul uziri ba halinsa bane." Feea dake hawaye tace"wlh ni daman nace mashi nayi hkr shine yace sai ya kullesa." Girgiza kai Alh maude yayi yace "uhm shikenan kawai kuna iya tafiya zanje namasa nasiha anjima." Kamar kububuwa Haka Alfah yafito daga station d'in,malik binsan yake cikin sauri don yasan wannan fushin sai yayi kwana uku yana yinsa,inbai samu wanda yajuye haushin sa akai ba. Tuni fiyah ta yanki hanyarta,don tace ma feea bazata bisu ba akwai inda zata bata d burin daya wuce tasan waye wannan guy d'in,ita sai take ganin kamar yana mata kama da yaran gidan *ALH MU'AZZAM CANJI* amman zuciyarta ta kasa yardar mata da haka,saboda in d'an gidanne mezai fiddoshi daga gidan yazo yana irin wannan rayuwar,girgiza kai tayi tanajin matukar tsananin tausayinsa na cika zuciyarta. Hango malik tayi ya tare masu taxi gudu-gudu sauri-sauri haka take had'awa har ta samu ta tari itama taxi d'in tace mai yabisu baya,binsu yake har k'ofar gidansu tace yayi parking daga nesa, Azafafe ya bude kofar motar yafito, sai soka hannunsa yake cikin kansa yana ya mutsa kyakkyawar sumarsa kamar ta larabawa,isa yayi bakin get din gidan nasu yana jiran malik dazai sallami mai taxi,dora hannunsa yayi ga bango sannan ya aza kanshi sama,daka kallai kasan yana cikin wani irin hali. Hawaye taji sun sulalo mata bata ma sani ba. malik ya iso inda yake yana bude masu karamar kofar shiga,yana mashi magana amman bazata iya juyo abunda yake cemai ba.saida taga shigarsu sannan tace ma mai taxin ya kaita maitama estate. Don lectures din da zata koma tayi anriga angama,kuma daman ita kadai ta rage mata. Har taje gida tana hawaye,ganin sun kusa isa yasa ta goge kwallarta tana daidaita natsuwarta,sallamarsa tayi ta wuto zata shiga gidan, ganin buta tayi bakin shagonsu ta dauka ta wanke fuskarta,yadda baza,ai mata tambayar kukan me tayi ba. "Sofiyya yau ba magana." Maitsaron shagonne yayi mata maganar,watau dalha cousin dinsu ne ta wajen mahaifiyarsu,sadda aka gama had'a shagon ta je har rimi ta daukoshi don daman zaman banza yake acan. Rimi garine cikin katsina Cikin rashi kuzari ta juyo tana yak'e tace"ayya d'alha wlh nagaji ina sauri inshiga gida,sannu da aiki ya kasuwar." Murmushi yayi yace"da godiya,maza hanzarta kar acinye babu ke." Murmushi mai kyau tayi ta shige tabarsa. Sallama tayi yesmin dake kwashe shanya ta ansa mata. "Sannu Adda kin shawo rana." Jinjina kai tayi ba ta bata ansa ba,bin bayanta tayi da kallo cike da nazarinta,da alama Adda na cikin damuwa. Mamace tafito daga cikin daki tace"kamar sallamar fiyah naji ko." Yesmin dake linke zane tace cikin rashin jin dadin ganin yayar tata haka "itace mama,amman kamar bata da lfiya tashige d'aki." "Subhanallahi,bari inje inji." D'akin nasu ta shiga tana kiranta,bata cikin dakin amman jiyo karar ruwa cikin bayinsu yasa tajuya, tabarta ta fito. Haka Allah ya yi sofiyya da daukar damuwar wani ta zama tata,mace ce mai tsananin tausayi abu kadan zai karya mata zuciya,duk da halayenta sunda yawa amman abu mafi bayyana tare da ita shine,san yinta kafin kaga zafin ta zaka jima sannan akwai zurfin ciki sosai,tana da shanye damuwa abu zai jima yana damunta bata bayyana shi ba. Wankan ta fito tana shafa amman yanayin fuskarsa take hangowa,da zafafan kalaman da abban feea yake gaya mai,runtse ido tayi hango yadda idonsa yayi jajawur gwananin ban tsoro........haka ta gama murza man ta saka kaya marasa nauyi tayi sallar azahar da la,asar sannan ta fito tsakar gidan. Mama da yesmin nata hira tazo ta zauna,ta dora kanta bisa cinyar maman tana shagwabe fuska. "Mama yunwa nakeji." Shafa kanta take tace"yesmin dauko wa Addarki d'anwakenta yau mutumen ki akai zakici ko." Daga kai tayi tana sake narkewa daman fiyah badai shagwaba ba,ajiye mata yesmin tayi tana cewa"Adda d'azun ina magana baki tanka niba." Murmushi tayi mata mai sanyi tace"sorry my little,ban cikin natsuwa ne kiyi hkr kinjiko." Tana murmushi tace "bakomi Adda nayafe maki,kinje gidan Antyn." D'an waken take ci cikin rashin kuzari,har yanxu amon muryarsa takeji sadda yake mayar wa da Abban feea magama cikin,kunci da bayyana bakin cikin da yake ciki.kamar bazata tan ka ba tace"banje ba yesmin,ban samu time ba kilan sai gobe." Ko kwatar dan waken bata ciba ta ajiye tace "na k'oshi mamana." Cikin kulawa tace"haba yar sofyna mekikaci anan kefa kikace yunwa kikeji,anya kuwa bakina b'oye man wani abuba." *wlh saboda ku yau banci abincin rana ba sai la,asar kuyi manage pls,sannan inhar banga comment 70% ba gaskiya zan dakata da typing,don haka na nuna bakwa jin dadinsa.* Mrs Bb Mom muhseen. Lov u all masoyana😘😉 [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........6 Runtse idonta tayi ta bud'e tace"Aa mamana,babu abunda nake boye maki kawai dai banjin dadi ne kwata-kwata." Yesmin duk ta koma kalar tausayi don jin halin da yayarta ke ciki. Wayar maman ce tayi kara yesmin ta dauko ta tana cewa"wlh Anty ce ai daman nasan tunda kikace bakije ba wlh saita kira." Mika ma maman wayar tayi tana zama kusada Addarta. Daukar wayar maman tayi tare da sallama. "Mama ina fiyah,wlh ranta sai yayi mugun b'aci yesmin bata gaya mata sakona ba." Shiru maman tayi har saida ta gama sannan tace"sallama ta ma bazaki ansa ba jamila zaki hau yimun sababi,ko nice sofiyyar ne ban sani ba." Cikin tausasa murya tace"Aa mama ba haka bane kiyi hkr." Itama cikin d'an fad'a tace"aikin tambayi dalilin rashin zuwanta bawai kihau yin fad'a ba,." Sake kwantar da murya tayi tace"to mama kiyi hkr don Allah,meyasame ta ina take ban ita." Fiyah na kwance har lokacin kan cinyar mamar idonta lumshe eyelashes dinta sun wani kwanta gwanin sha,awa tunani take ta yadda zata shiga rayuwar *ALFAH* taji waya kan kunnenta maman ta aza mata. Cikin cool voice dinta tace"Anty ina wuni." Daga can ita ma face"lafiya lau fiyah,lafiyarki kuwa naji muryarki tayi sanyi sosai." Gyara kwanciyar ta tayi tace"Anti kiyi hkr wlh nataso banda isassar lafiya,kaina naciwo ga gajiya shiyasa ban biyo ba,amman insha Allah gobe ina nan zuwa." Ajiyar xuciya ta sauke tace"daman muhseen ne yake son kuyi bankwana zai koma spain,yama tafi aman yabar sak'o abaki." Haushi taji ya kamata yadda Antyn ta matsa mata akan wani muhseen,itafa bata ra,ayin wannan guy din mai shegen yangar tsiya kamar mace,ta gode Allah ma daya tafin. "Toba ma saina zo ba kenan." Cikin fad'a tace"ban son iskanci bacin kinji nace maki yabar sak'o,to mezanyi dashi in baki zo kin ansa ba." Dariya tayi k'asa k'asa tace"to zanzo goben insha Allah agaida man uncle da onborn baby." Ta fad'a tana dariya. Tace"marar kunya kawai zakizo ki saman." Tana dariya ta kashe wayar. Antynsu akwai zafi itada yayansu jalal,ga saurin hagula,dan danan zaka bata masu rai amman dan danan zasu sauko,daga mamansu har baban su babu mai tsananin su,suma wajen kakanni suka gado. Itada yesmin kuwa sanyin su har yakusan yawa,amman ita fiyah akwai lokutan da takeda zafi,zafinma sosai amman tana daukar lokaci baka ganta cikin irin wanan yanayin ba. 💞💞💞💞💞💞💞 Tun da suka shiga cikin gidan Alfah ya zube cikin falon yana wani irin huci na ban tsoro,malik ya rasa gaba d'aya natsuwarsa duk ya gigice yana jin wani tsananin tausayinsa yana cika zuciyarsa,bai wuce abunda ya faru tsayin shekaru ba yake dawo mashi sabo,saboda aduk sanda akai wani abu daya tuno mashi abun,ko yaga wani nashi ko wanda abun ya shafa,to fah wannan halin yake kasancewa cikinsa,koma fiye da haka........tunaninsa ya katse jin sautin kukan sa kallonsa yayi cikin tausayawa jin yadda yake kukan cikin bayyana tsananin kuncin da zuciyarsa take ciki,duk da yana tsoron tun kararsa ahaka cikin wannan yanayin nasa. zuciyarsa takasa hkr ya nufesa shima kwallar cike da idonsa. Durk'usawa yayi gabansa yadafa kafad'arsa yace"kayi hkr Alfah Allah yana sane dakai............cikin wani irin yanayi na zuciya da fushi ya watsa malik gefe muryarsa har lokacin bata fita sosai yace"hkr,hkr fa kace inyi. bazan ba bazan tab'ayin hkr ba malik,antozartani anci mutuncina an goge duk wani kallon kima da mutunci da masoyana kemun,an yayatani ga media........cikin sarewa ya silale k'asa cikin shashshekar kuka kamar ransa zai fita ya cigaba da magana wadda ba sosai kakejin taba muryar ta dishe sosai cikin kuka da tarin kunci yace. "Suka Koran,sun aibatani sun zagan sun wulakantani sun lalata man carria,sun lalata sunana duk inda na shiga k'yamata ake aibatani ake,zagina ake babu maisona........malik babu maisona duniya ta tsaneni duniya na mun kallon fasik'i,wlh malik niba fasik'i bane ban fab'a ba bazan tab'a ba kayarda niba d'an iska bane kamaryadda sukace ko,?kayarda ni mutumen kirkine ko?" Malik kuka yaci karfinsa isowa inda yake yayi ya rungumeshi yana kuka iyakar karfinsa shima ya matseshi kamar zai ballashi tare suke kukan kamar yanzu abubuwan ke faruwa. Cikin kuka malik yace"kai mutumen kirkine,kai ba dan iska bane kai ba fasik'i bane ABDOUL-NASSER kamilin matashine,natsatstse mai addini mai girmama nagaba dashi,burinsa shine ya tallafawa masu karamin karfi,mai biyayya g iyyensa..........yaja numfashi yanajinsa yana ajiyar xuciya bugun zuciyarsa yana raguwa cigaba yayi da cewa"sharrin macene yaja maka duk wannan Alfah,kaddarsrka tazone ta wajenta karka zargi iyayenka abunda suka gani dashi zasuyi anfani.........fincikoshi yayi daga jikinsa idon nan babu kyan gani yatura shi kan kujera kamar ba shine yanzu yayi sanyi ba. "Karkasake mun maganarsu,natsanesu ban sonsu har abadan bazan sosu ba." Malik na hawaye yace"Alfah kagane mana...........bazan tab'a gane wa ba,kafita anan ban son ganin kowa karka sake zuwa inda nake,nagane cewar kaima munafukine baka kaunata nace kafita!!! Yafada cikin ihu da har gagi. Malik na kuka ya fita ya barshi. table din glass dake tsakiyar falon Alfah ya dunga duka har saida ya tarwatse,ya dunga boll da duk wasu kaya dake cikin falon,masu fashewa nayi masu watsewa nayi.hankalin malik inyayi dubu ya tashi kuka yake yaciro wayarsa yana kokarin kiran Daddy,tsotsai yasa wajen sauri wayar ta silale ta fad'i aikuwa fuskar wayar ta fashe,..........cikin haushi da takaici ya zube kasa yana dora hannu saman kai. "Wannan wace irin rayuwace haka,har sai yaushe abubuwa zasuyi sauki,cikin kuka da magiya yake rokonsa,Alfah karka raunata kanka,inbaka son rayuwarka ni inasonta kayiwa girman Allah kadai na." Amman Alfah baijin ma komi malik yake fad'a saida ya hauka ta falon yajiwa kanshi raunika sosai. ya zube yana kuka mai cin Xuciya,yanajin wani irin ciwo cikin zuciyarsa jiyake kamar yacirota ya jefar ko zai daina jin wannan ciwon amman kamar tira mashi ciwon ake frig ya nufa ya dauko kwalaben giyarsa ya cire masu hanci yadunga bulbulawa cikinsa,daya shanye sai ya dauko wata itama ya gama mata aiki,atakaice saida Alfah yasha kwalba biyar,amman baiji koda kadan cikin ciwon daya keji yaragu ba,a haukae ya dauko kwalbar daya shanye giyar ya buga ta da kasa ta fashe,ya dauki b'allin kwalbar ya saita jijiyar hannunsa zai yanke yaga hakan bai mashi ba,ya jefar da kwalbar yafasa wata irin kara yabuga kanshi ga bango sai gashi ya xube kasa babu numfashi. 💞💞💞💞💞💞 Da dadare bayan sun gama cin abincin dare wanda har lokacin fiyah bata daidai taba,gata nan dai kadaran kada han ko baban su saida ya tambaya ko tana lafiya tace kanta ke ciwo amman tasha magani yayi sauki. Bayan ya gama cin tuwonsa yafita waje wurin d'alha da radion sa ga hannu. Hira suke cikin gidan yesmin ce keta ba mama labarin yadda jara barawar su ta gobe zata kasance masu,fiyah dai tayi lamo gefe tana sak'awa tana kwancewa tab'ota mama tayi tai firgigi ta juyo tana kallon maman. "Sofiyya,kallan ninan bazaki iya boye mun damuwarki ba saboda yana yinki ya nuna cewar damuwar babbace,kuma tana damunki matuk'a don najima ban ganki cikin wannan yana yin ba,don haka maza gaya mun abunda ke damunki yanxu nan." Raurau tayi da ido zatai kuka don bata san taya zata gaya ma mama abunda ya faruba,amman dole zata boye wani abun don tasan makamar abunyi. Cikin dakoya da kokarin boye abunda ke ranta "tace mama bafa wani abu bane kawai dai wani abune daya faru yake daure man kai tunda abun yafaru duk nakejin babu dadi." Duk natsuwa sukai suna saurarenta mama tace "inajinki meye ne Allah yasa ba akan karatunki bane." Kwanciya tayi jikin yesmin dake gefenta tace"wanine yayi hadari bakin titi,yawwa mama inkin tuna rannan wanda nace maki ankasa tai makarshi." Cikin kulawa da maida hankali kan abunda take cewar tace mata"eh natuna sofyna meyafaru bayan nan." Ta sake mazewa yadda maman bazata gano komi ba tace"wlh mama abunne yaketa damuna tun rannan to yau naga mutumen kamar wani mahaukaci bakin titi yaci kwalar wani mutun daker aka kwaceshi,ni mama sai nake ganin kamar nasan shi wlh,kuma abunda yaban tausayi gareshi mutane sun zagayeshi sai duka suke ga wani Alhaji sai tijara yake yana zaginsa maganganu marasa dadi hada ce mai wai iyayensa ma sun gaza dashi balle wasu,abun dai babu dadin ji wlh harfa cemai yake dan iska fa mama.wlh yaban tausayi ya kira yan sanda suka tai dashi. Naji mai taxi din daya taho damu nida wani yana cema wanda ya dauko mu tare wai kowa yasan shi dan iskane kuma da iyayensa masu hali akwai abunda yayi suka korai." Shiru mama tayi tana jin abunda fiyah ke sanar da ita taso d'ago wanda take maganar kanshi amman bata tabbatar ba,cikin kulawa tace mata"dawa kikace yake maki kama." Aranta tace yawwa anzo wajen don daman so take tasan dagaske dan gidanne kuma me ya fiddashi inhar dan gidanne. "Mama yama sunan wancen mutumen mai kudin unguwar nan,uhmmmm yesmin yama ni wlh mance sunansa nake ma saboda mugun halinsa." Tayi hakane don ma kar mamar tagane dagangan tayi haka........cikin sauri yesmin tace "nagano shi wlh,mu'azzam canji tabbas sunan kenan ko mama." Wani irin kallo mama kewa Fiyah cike da tuhuma ganin haka yasa fiyah takiyarda su hada ido da maman don tabbas idan suka hada ido tasan zata gane karya tasheka mata do dai ta samu wani bayani. More comment more typing. Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........7 Kallon fiyah mama tayi tace"mama lfy,naga kinyi shiru kina kallona." Numfashi taja tace"babu komi ina nazarin yaron dakike magana akai ne." Yesmin tace "Adda daman kinsan shi ne." Girgiza kai tayi tace"nace maki nasan shine,bakiji ina cewa yana man kamada yaran wancen gidan." Mama tace"yaron gidanne shine babban gidan gaba d'aya." Wani dadi ya kamata tasamu abunda take son ji,canza fuska tayi kamar bata damuba tace"kinsan sa kenan mama,to abun mamakin shine meyayi haka da zafi zasu korai." Mamar yitayi kamar batasan me take fada ba,saida fiyah ta sake magana tace"mama kinji meya yi masu da zafi haka,wlh yaban tausayi." "Sofiyya bakijin mutuwar sarki bakina,babu ruwana ni kamar kisake baban ku yaji kina wannan maganar,don ranki zai mummunan b'aci.keda damuwar wani sai ta zama taki,kirufa ma kanki asiri ma kibar wannan halin don yana iya jefaki cikin matsala." Shiru sukai suduka don maganar mama ta daure mata kai,har ta kasa hkr tace"mama don ka ji tausayin halin da wani yake ciki kuma kayi niyyar taimakonsa sai yakoma matsala,tunani na aikin ladane taya zaka shiga matsala." Wani irin kallo mamar ke mata kamar zata maketa tace"mekike nufi sofiyya,dake nake nace mekike nufi karki cemun zaki saka kanki cikin wannan abun,wallahi karki kuskura kiyi gigin farawa,ina ruwanki ina abunda ya shafeki da rayuwar da yake.wannan halin na shegen tausayi saiya kaiki ga nadama,kisake kuma babanku yaji wannan maganar." Idon ta yayi rau rau k'iris takejira ta yi kuka,daman kuma sofiyya gwanace ta iya kuka da abunda ya kai da wanda bai kaiba. "Yanzu mama tsakani da Allah kinji nace wani abu,daga kawai nace haka ni wlh kibarcewa haka kuma ma ina ruwana dashi ina ma zan ganshi balle in taimakeshi ehy." Tatashi ta nufi dakinsu tana kuka yesmin duk taji babu dadi itama tashin tayi tacewa maman saida safe karfe takwas suna da pratical. Koda fiyah ta shige d'aki kukanta tayi mai isarta sanan ta kwanta,bakuma don ta hkr da cikar burin ta ba. Dr daya duba Alfah wancen karon wannan karon ma shi malik ya kira,ya samai drip yayi mashi allurai inda yaji raunika yayi dressing. Dr yace ma malik"Alfah ya na cikin jarabawar rayuwa,amman a bun damuwar shine yadda zuciyarsa ta k'ekashe babu wani abu dake girgizashi,babu kuma abunda ke sata tayi laushi.malik zama bai gammuba don kuwa idan ya cigaba DA zama haka wataran zaima kanshi illar da mu likitoci bazamu iya gyara taba." Jan numfashi malik yayi yana jinjina maganar Dr tabbas duk abunda ya fada gaskiyane,a bun ya isa haka yana bukatar matai maki cikin kulawa da Alfah. "Haka ne Dr nima zuwa yanzu na gaji da halin Alfah,shekara biyar ba kwana biyar bane yadace zuwa yanzu ansamu sauki,don haka Zan San abunyi insha Allah duk sanda nake bukatarka Zan maka a bun ya isheni haka dole asamu mafita." Haka sukai da dr ya sake yiwa Alfah wata allurar sannan ya tafi,bayan ya gama nuna ma malik yadda zai cire mashi drip din idan ya kare. Tunda Dr ya tafi malik yashiga tunanin abubuwan dasuka faru baya,yana son ya kamo bakin zaren duk yadda yake za to lamarin a bun yaci tura,don ya kasa fahimatar yadda lamarin yake,yana bukatar dogon nazari da kuma abokin shawara don samun taimako wajen yadai zai kamo makamar matsalar. ************ Tun data tashi yau bata koma ba saida ta gama duk ayyukan gidan,sannan tashiga wanka yau tana son ta samu ganin malik,sufara magana kafin komi ya daidaita.don tayi alkawarin taimakonsa koda yanaso ko baiso,yesmin tariga ta fita sannan itama ta tafi,bayan ta anshi kudin taxi da na break. Bata da lectures din safe shiyasa ta yanke shawarar Fara zuwa tayi magana da malik,idan ta fito karfe sha daya ta shiga wata 11:30 ta fito 1:00 bata sake komawa kuma sai 4:00 kafin nan har taje gidan Antyn tadawo. Unguwar ta kwatanta ma Mai taxi din tanajin kirjinta yana dukan Tara tara,runtse idonta tayi tana karanto adduoi,akan Allah ya bata Sa,a. Biyansa tayi ta tsaya tana kallon get d'in faduwar gabanta yana yawaita,kamar kwai yafashe Mata aciki take takawa zuwa wajen karamar kofar.hanunta yana karkarwa ta danna bell din kirjinta yana duka,ba komi take tsoro ba irin bak'ar zuciyar guy din,karya kafta mata irin Marin da feea tasha rannan. Saida ta danna sau biyu sannan taji alamun tahowar mutun,ai jitai kamar ta kwala da gudu,saboda tsananin tsoro da fargaba.........budewa akai suka tsurama juna ido itada malik,duk ta dirirce saboda yada yayi Mata kwarjini,kasancewar shima malik ba daga baya ba wajen kyau. Murmushi ta sakar mashi Mai tsananin kyau tace"ina kwana." Kallon ta yake fuskarsa da yalwar Fara,a yace"morning,what u want." Sai yak'e take tace"I'm sofiyya El-ladan Amman anfi Kira na da fiyah,I want discous serious issue nida Kai don zai anfanemu." Shiru yayi yana nazari kafin yayi murmushi yace"about what." Tace"ur friend or brother." Ajiyar xuciya yayi yana waigen bayansa sannan ya juyo yace"ur welcome come in." Ya bata hanya alamun ta shigo kallonsa take cike DA tsoro tace"inajin tsoronsa ya rik'e fuskata zai iya mun wani abu." Rufe kofar yayi yace"bai tashi ba ma,har mun gama maganarmu karki damu,muje." Yashiga gaba ya rufa mashi baya tana adduar ubangiji ya taimaketa akan niyyarta,ya kareta daga sharrinsa Allah yaga zuciyarta abun alkairi take niyyaryi. FTN ZAKUYI MUN UZIRI SABODA HIDIMAR DAKE KAINA WLH DAKER NAYI MAKU WANNAN,INSHA ALLAH GOBE ZAN MAKU LAST PAGE NA ABIN CIKIN RUHINA,NAGA SAKKONNIKU DA ADDUARKU AKAN BABYN DA MUKA SAMU NGD SOSAI GODIYATA BATA DA IYAKA ALLAH YABARMU TARE. Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️..........8 Kallon gidan take cike da sha,awa shuke shuke ne masu ban sha,awa take kallo dake can cikin guiden. Yana gaba tana biye dashi baya har zuwa inda wata rumfa take ta cicci,irin dai rumfunan nan da akeyi na shak'atawa.kujerune masu kyau wajen,yaja mata daya ta zauna,sannan yace"Ina zuwa plz." Hanya ya dauka yashiga cikin gidan nasu,don inda ya sauke tan cikin compound din gidan ne. Bai Jima ba yadawo yana rik'e da Dan tire na silver mai shegen kyau. Ya ajiye gabansu ya zuba mata ruwan Lipton cikin wani d'an cup Mai daukar ido,ya tura Mata wani had'ed'den cake yace"bismillah." Murmushi tayi tace"am OK banajin yunwa." Rungume hannu yayi ga kirji yace"bakiso mu yi magana kenan." Rausayar da Kai tayi tace"yi hkr zansha." Ta dauki cup din ta d'an kurb'a ta ci cake d'in kadan shima sannan tace"kamar yadda kaji sunana haka yake,zuciyata ta cika da tsananin tausayinsa bansan dalili ba,amman abunda na sani shine inason taimakonsa,yadda abunda ya faru station hakan ya nuna man Abokinka yana cikin tsananin bukatar mataimaki,duk Wanda zaigansa sai ya gane cewa yana cikin tsananin damuwa da kuncin.malik da zuciya guda nazo wajenka don Kaine zamu had'u mu fiddosa daga cikin duhun da yashiga,akoda yaushe fuskarsa babu walwala babu rahma,duk da ganina dashi bai wuce uku ba Amman na lura da hakan.ya kake ganin za,ai,don tun jiya dana koma gida ban samu natsuwa ba saida na samu wasu bayanai wajen mahaifiyata." Shiru malik yayi yana saurarenta wani dadi yakeji jin irin abunda tazo dashi,hakika hakan yayi matukar yimashi wannan wata dama ce tazo mashi don haka bazai yi sanya ba,jin kalaminta na karshe yasa ya nisa yace"me mahaifiyar taki ta sanar dake." Sauke ajiyar zuciya tayi tace"nayi Mata tambaya ne akan abokin naka." Sake jefo Mata wata tambayar yayi yace"mekika ce Mata kenan." Murmushi tayi tace"nace mata ne Abokin ka yana mun kama da yan gidan Alh muazam shine take sanar da cewa ai Karon gidanne shine babba,naso na sake samun wasu bayanan Amman tace baza,aji mutuwar sarki bakinta ba." Jinjina Kai yayi yatashi daga kwanciyar dayai cikin kujerar yana gyaran murya yace"naji dadin maganarki sofiyya,ko dai ince fiyah kinfi jin dadinsa." Dariya tayi tace"no i like inji ankirani da full name dina." Smile yayi ya cigaba da cewa"tabbas kamar kinsan neman wacce zata taimakeni nake,don kuwa lamarin Alfah kullum sake hauhawa yake,tsawon shekara biyar da wata biyar kenan.hakika Na yarda dake sofiyyah,kuma insha Allah Allah zai cika mana burin mu,sannan kamar yadda kikaji cewar Alfah dan gidan Alh Muazzam ne haka maganar take,dan sane na cikinsa,Ku ma shine first born agidan,haka zalika shine kadai namiji sai karamin kanensa.mahaifiyarsa itace Mata tabiyu agidan Alh muazzam.labarin rayuwar Alfah labarine Mai tsawo fiyah,don cikin kwana d'aya bazan iya gama maki shiba,Amman tunda wanna Karon farkone na had'uwarmu insha Allah next inmun had'u Zan Fara warware maki labarin *ABDOUL-NASSER ALFAH.*." Shiru tayi tana jinsa kafin tace"shikenan malik,xanjiraka akoda wane lokaci kabukaci gani na namaka alkawarin zuwa,Amman banda waya kaban no d'inka Zan nemeka idan nakoma gida,yanzu makaranta zanje inada darasi." Murmushi yayi yace"babbar budurwa like u kice bakida phone har kuma kinshiga jamia,gaskiya baidace ba to yanzu ina Zan rubuta maki no d'in tawa." Itama kyakkyawan murmushi tayi tace"karanto mun zakai Zan iya rik'ewa." Tafi yayi yana mik'ewa yace"good fiyah,gaskiya dagani kina da k'ok'ari a school." Itama dariyar take sun jera suna tafiya zuwa k'ofar fita. Tace"aa kawai dagiya ce irin tamu ta ma rasa galihu,kasan irinmu kobamuda kokari tofa zamu dage don ganin mun fita kunyar iyaye mu." Murmushi yayi yace"kin fad'a ne don inyarda ko?" Tad'aga Kai yace"to ban yarda ba." Dariya tayi itama har zuwa sanda suka k'arasa bakin k'ofar yafara karanta Mata no dinhar karshe,yana gama fad'a ta maimaito masa itama exactly yadda ya karanto mata. Alamar jinjina yayi Mata da hannu yace"good,dan banyi wanka ba dana saukeki,Amman duk da haka bari ga driver can saiya ya kaiki." Tace"aa malik wlh ngd,Zan idasa da kaina sai munyi waya." Sukai bankwana ta tari taxi ta wuce makaranta. Lectures sukai yau masu zafi,don semester tazo karewa shiyasa KO wane malami soyake yayi covering Kan lokacin exam yayi don har sunfara test ma. Sun had'u da feea cap wajen cin abinci take cema ta. "Fiyah ashe guy d'inan bakaramin k'usa bane aharinnan,kinsan kowaye babansa kuwa." Fiyah saita nuna kamar bata sani ba cikin mamaki da al,ajabi tace"Kai haba,bani insha." Tace"kinsan Alh muazzam canji,na cikin estate dinmu,to wlh shine ya haifesa wani babban laifi ya aikata ma shi ya korai tsawon shekara da shekaru kenan,nayi nayi da momi aman tace baruwanta wlh." Jinjina kai kurin fiyah keyi tace"lallai banyi mamaki ba,saboda tun farko naga muguwar kamarsa da y'angidan.Allah ya kyauta gaba ya sasatanshi da iyayensa." Feea tayi tagumi tace"wlh yaban tausayi jiya,tsoro naji ai karya shak'oni ya dunga jibga karshe ya kasheni abanza.don naga jiyake da karfi kamar doki." Dariya fiyah tayi tace"ba take yake ba lokacin ai." Feea tace"wlh kuma guy din ya gama had'uwa ban tab'a ganin ruwan kyau ga namijiba irin nashi Zan so in samu saurayi kamarsa." Dariya fiyah tayi tana kallonta tace"kozaki shiga daga ciki naimaki hanya." Zaro ido feea tayi tana rufe baki tace"rufaman asiri wlh ko k'ashina bazai bari ajikina ba,keee wannan guy d'in banga fitsararrar dazata tunkarai da maganar soba,aikoba so wannan ixxarsa ma da kwarjininsa sun sata rugawa,balle yadda naga yana da bakar zuciya." Dariya kurin takeyiwa feea ganin duk ta rud'e lokaci guda alamun dai wannan Marin bata manta dashi ba. Karfe d'aya da kwata tafito daga cikin makarantar,feea tace tazo suwuce tace ai bagida tayi ba,zata dawo karfe hud'u suna da test. Bata sha wuyar samun abun hawa ba tawuce gidan Anti jamila,don yau idan bata jeba tashiga ukunta wajenta,takakkiya zatayo Mata har gida. Babu laifi mijinta yana dashi,don babban gidane Mai plat biyu shiga tayi tana doka sallama,Mai aikinta ce take ta ansawa,shiga tayi cikin falon tana kallonsa an sake mashi kujeru da TV plasma,ansaka wata kantamemiya ga sabon canis kafet Mai shegen laushi,andai gyara falon kamar na sabuwar amarya,bama falonba ta lura gyaran duka gidanne. Magana tajiyo cikin bedroom d'in kamar ita da wata ne, kasa kunne tayi tajiyo muryar wata tana cewa"wlh jamila maganin nan shayanzu magani yanzu,kinsan da kanwata tayi anfani dashi,saigata da kanta tana nemana ruwa ajallo,dakau kamar bazata siyaba,kinga wannan sunan sa rijiya tunjum,wlh shima badai aiki ba nake gaya maki makociyaya data siyai,can cikin dare naringa jiyo ihun maigidanta,washe gari saigata wai insiye matashi duk,Abban Ahmad bai tab'a Mata kuka ba insuna tare sai jiya,ai ban sayar da kayan banza kinsani.yo in gaya maki da mijin yayata dan rainin wayau ne,yaraina ta nake gaya maki,baya kusantarta saiya ga dama haka bai zaman gida,ke Abu yazo har yakai ga Saki jamila,dakerfa iyaye suka shiga lamarin,lokacin Ina Ibadan Dana dawo lokacin ta koma najefa na tsumata,nahad'ata yadda yakamata karshe saigashi duk inda zata shine kekaita yana rik'eda jikkarta." Ajiyar xuciya ta sauke tace"lami ya isa haka,ki ajiyemun wannan da wad'annan,na wane kud'insu." Tana washe baki tace"wlh don kece Zan maki sauki ki bada 10k ai babu cuta tsakaninmu." Tace"toshike nan ki ajiyemun sy wajenki karki sugar wa da kowa,in na ta shi zan ansa." Dahaka suka fito tana yimata sai anjima,ganin fiyah falon yasa ta rik'ebaki tace"shegiya kin zo shine baki sallama." Matar ficewa tayi tabarsu fiyah tace"anti ya za,ai kiji bayan kunshige ciki sai ciniki kuke,wai anty da wannan uban cikin ma sai kinsha kayan Mata,baki bari ki haihu." KUYI HKR WLH NAGAJI,MUHADU GOBE IDAN ALLAH YASA MUNKAI DA RAI DA LAFIYA. MRS BB MOM MUHSEEN. [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞 💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........9 "Don ubanki cewa nai zan sha." Dariya fiyah tayi tana kunna kayan kallo tace"Allah yabaki hkr,naji ai sai bayani take kora maki kuma inba siye zakiyi ba mezai kawota." Tsaki taja tana shigewa wata k'ofa tana cewa"to siyen zan don uban mutun ya hanani,ince kud'i nane bana wani ba." Fiyah dai dariyar take don sun saba indai halin anty jamcy ne. Fitowa tai da wata fation leda ga hannu ta zauna daker don cikinta yatsufa. Tace Mata "inkina jin yunwa ga abinci can kan dining,akwai kunun aya a frig don naga kinaso nasa akai maki." Cikin jin dadi tace"aikuwa wlh ngd Anty kinsan kuwa na kwana biyu ban sha ba,Allah yasa baiyyi k'ankara ba." Ta fad'a tana isa wajen frig din ta dauko"aikuwa baiba nagode anty,Allah yaraba lfy." Hararata tayi tana murmushi "baki cin abincin kenan" Kunun ayar take sha tana lumshe ido tace"aa anty ban jima da cin julluf a cap ba,barni da wannan ma wlh ya isan.ina uncle yahya." Gyara kishingidar ta tayi tace"bai kai ga dawowa ba,mezai maki." Dariya tayi "aa nikuwa mezai mani anty,daga tambaya." Tab'e baki tai tace"ga sak'onki inji muhsen,naso ku had'u kuyi bankwana da Allah kadai yasan arzikin da zaki samu." Fara,ar dake kan fuskarta ta ragu sosai,cikin halin ko in kula tace"ni wlh da baki ansa ba,banson wannan bibiyar da yake mun ni nace bayanzu zan fara soyayya ba,balle akai ga maganar aure duk wannan hidimar bata da anfani ki ajiye mashi kayansa sadda ya dawo kibashi ni gaskiya bana so." Wani kallo take mata cike da haushi,cikin fad'a tace"iyye,oh ke baki tashi soyayya ba balle ai maganar aure,kina nufin duk godolon da yake akanki baida wani anfani,yaro natsatstse kyakkyawa son kowa k'in wanda yarasa,kimaida hankali ki sakeshi ba fata nake maki ba daker zaki samu kamar sa." Turo baki take tana k'unk'uni k'asa k'asa. Dungure mata kai tayi tace"ubanme kike cewa halan ma zagina kike." "Ni anty ba zaginki nake ba,wlh idan baba yasan ina kula wani fada xai man kuma yace aure zanyi in bar karatuna." Harara take dalla mata "dallah can sokuwa ni ba saida nai aure na gama karatun ba,meyasa man kuma shikanshi baban idan yasan kin samu tsayayye ai murna zaiyyi,tunda baida wani buri daya wuce yaganki gidan miji." Murmusa ido take tana y'an harare harare aranta tana cewa "wlh insha Allah kozan aure saina ga bayan matsalar *ABOUL-NASS*." "Ubanme kike cewa kikiyayeni wlh,kibar ganina da wannan cikin ubanki zanci anshi nan kisata caji kafin sadda zaki tai,kuma inkinje gida kicewa mama da baba uncle dinku ya baki nasan bakinsu zai mutu." Cikin rashin walwala ta ansa tana dubawa kwalin waya ne sabuwar Samsung galaxy s9 pink color dandanan kaunar wayar ya kamata,badan komi ba saidan suringa communicating da malik,murmushi tayi tace"ashe wayace anty,aikuwa ngd kice ina mashi godiya."n harare harare aranta tana cewa "wlh insha Allah kozan aure saina ga bayan matsalar *ABOUL-NASS*." "Ubanme kike cewa kikiyayeni wlh,kibar ganina da wannan cikin ubanki zanci anshi nan kisata caji kafin sadda zaki tai,kuma inkinje gida kicewa mama da baba uncle dinku ya baki nasan bakinsu zai mutu." Cikin rashin walwala ta ansa tana dubawa kwalin waya ne sabuwar Samsung galaxy s9 pink color dandanan kaunar wayar ya kamata,badan komi ba saidan suringa communicating da malik,murmushi tayi tace"ashe wayace anty,aikuwa ngd kice ina mashi godiya." Kallon mamaki take mata da tuhuma. "Ai nai zaton wani abunne na daban ba waya ba don yanzu nafi bukatar ta wlh." Sake dungure mata kai tayi tace"banza kawai ki hanzarta kisa caji ga no dinsa nan ki kirasa don har sabon layi yasa maki da katin dubu da dari biyar,don Allah fiya kikirashi wlh muhseen yana masifar sonki,zanso ki samai kinga gani gaki kuma mahaifiyarsu batada wata matsala wlh lafoya lau zaku zauna kina ganin dai yadda nake zama dasu kamar zasu goyani." Tabbas maganarta haka take iyayensu mutanen kirmine kuma yan gidansu basu wata matsala,muhseen da uncle yahya uwa daya uba daya suke,kuma suka dai ne maza sai kannensu mata su biyu,sun matukar son Anty jamila kamar yaua haka suka dauketa mamansu kau d'iya ta dauketa,sunada arx'iki sosai kuma baisa sun dauki kansu wata tsiya ba. Kasai muhseen dinne ya cika yaga ko wata macen bata gwada mashi iyayi,kilan in iya saurarensa idan nagama da matsalar su ABDOUL-NAS. murmushi tayi tana kallon Antyn tace"sorry anty zanty tunani akai don allah kiban lokaci,kuma zan kirashin idan naje gida yanxu test zan je nayi makaranta." Cikin jin dadi antyn tace"kokefa sofyn mama,wlh muhsen baida matsala zakiji dadinsa." Nata ce komi ba ta tashi ta sata cajin sannan suka cigaba da hirar su kamar komi bai faru ba. Sai wajen karfe uku tatafi kasamcewar tayi waya da wata yar class dinsu cewar malamin bai zoba yace kowa yatai sai gobe da yamma. Gida ta wuce tana murnan wayar,don asaukake basai tayi ta daukar ma mama waya ba. KO da taje gida da wayar mama said mamaki take saida taji daga inda wayar take sannan hankalinta yakwanta,amman duk da hka tana tsoron abunda baban su zaice kan wayar. Yes min kuwa kamar itace mai wayar sai jin dadi take,wayar tashiga dubawa kasancewar irin wadannan wayoyin tasan su tana anfani dasu wajen y'an class dinsu,yanzu kuwa ta huce wulakanci idan zatai browsing,basai taje tayi ta are are ba. No din malik ta saka tayi save da sunan sa Abdul-malik. Bayan dawowar baban su mama take sanar dashi wayar da mijin jamila ya ba fiyah,kiranta yayi tazo da wayar ahannu yace"sofiyya bazan hana ki rik'e waya ba,amman don Allah zan rokeki kirike mutuncinki,kar waya ta canza maki d'abi,u kar waya ta canza maki hali kar ta jaki ga abunda kika san zaki samu damuwa kisaka kanki." Gabanta yafadi saitake ganin kamar Baban yasan manufarta,amman ai Allah bazai kamata da laifi ba tunda dai harga Allah taimako take niyyar yi tana son mai doshi cikin rayuwa irin wadda yayi duk da dai basanin abunda ya faru dashi tayi ba. Cikin sanyin jiki tace"insha Allah baba zan kiyaue kasa mun Albarka to" Murmishi yayi yace"sofiyna kenan to Allah yayi maki Albarka ya baku miji na gari." Yesmin ta shagwabe fuska tayi tace"baba nifah to." Dariya duk aka yi mata yace "kema Allah yayi maki Albarka ya baki miji nagari." Tana jin dadi tace "ameen baba." Bayan sun koma d'aki ta shiga kiran no d'in malik,lokacin ma yanata aiki don cikin satin yake saka ran zuwa switzerland saro kaya. Alfah yana zaune kan kujera idonsa a lumshe ya shiga duniyar tunani,ahankali kuma zaka ga hawaye suna bin gefen idonsa,gorgiza kainkawai malik yake don baisannya zayyi da Alfah ba,yakasa daukar kaddara yakasa hkr da rayuwar ya ansheta ayanda tazo mashi. Wayarsa yaji tayi kara ya dan kalla yaga babu suna kamar zai share saikua ya tsaya da aiki ayakin ya dauka, tare da sallama. Tana kwance lokacin ma harnyesmin tayi bacci don bata da wuyar bacci . Itama cikin cool voice d'inta tayi mashi sallamar. "Assalamu alaikum,ina wuni yah malik." Jingina yayi daga jiin kuerar yaa maida hakalinsa kan wayar don yamaso saiwaye. "Wa,alaiki salam wake magana pls." "Sofiyya E-ladan." Murmushi yayi yace"okyy fiyah ce,ykk yakika koma gida." Idonsa nakan Alfah da har lokacin bai bude idonsa ba kuma ba bacci yake ba. "Lafiya lau wlh yah malik ya na barka ya kuma rikitacce abokin ka." Murmushinsa ya fidda mai sauti yace"bari nabaki shi sai ku gaisa." Zaro ido tai kamar yana gabanta tace"rufan asiri ina zaman lfy wannan ai saika yah malik,wazai iya da wannan rikicin." Dariyarsa ta fito har Alfah ya bude idonsa yana kallonsa "kin cika tsoro wlh,amman soon zaku saba yanzu ya zai muhad'u gobe around 4:00." Ajiyar zuciya tayi tace "inada test lokacin yah malik amman mezai hana da safe zuwa yammar." "OK hakan ma is ok 10:am yayi mki ko." Murmushi tayi tace "yes yayi insha Allah amman ina zan sameka." D'an shiru yayi yana kallon yadda alfah yake mashi kallon tuhuma yace"zan maki text da safen." "OK yah malik sai da safe zan kwanta." Sallama sukai ya ajiye wayar har lokacin idon Alfah na kanshi yasan soyake yayi mashi bayanin wacece amman miskilancinsa bazai barshi ya tamaya ba,shima kuma sai ybiye shin yayi shiru ya cigaa a aikinsa. Zuwa can ya tashi cikin fushin sa na farillah yayi ball da table d'in dake gaban sa ya wuce bed room d'in sa. Malik yace "Allah ya yaye maka ya kawo maka sauki cikin lamarinka." DON ALLAH KUYI HKR HIDIMAR SUNA MUKA SHIGA SHIYASA BAKWAJINA KULUM,AMMAN DAMUN GAMA INSHA ALLAH ZAKUJINI KUYI MALEJI DA WANNAN. MRS BB CE MOM MUHSEEN. [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* *Wannan page d'in nakune masoyana,inhar kinsan ke masoyiyata ce mai nuna kauna gareni to nakine na sadaukar dashi gareku,saboda irin soyayyar da nake samu daga wajenku,Allah yabarmun ku ya kuma kara mana kaunar juna,kuma baby humaira tana gaida kowa da kowa da irin aduar da take samu daga gareku.* 🅿️.........10 Fiyah ta gama komi yau da safe kasancewar yau Wednesday baba baya fita da wuri sai takwas na safe koda ya fito yaganta har takwas bata yi shirin fita ba yace"sofiyya yau babu makarantar ne." Tana sauke tukunyar danwaken da zasu ci da safen tace"baba ina kwana" Ya ansa cikin kula tace"aa baba akwai amman sai ten saboda malamin bazai zo ba da zai ma na seven to nine thirty baida lafy" Ta gilla mai karya nashi ta zubo mashi da kununsa na gyada data dama,yana kalacin suna hira har sadda mama ta fito daga d'akin sa ta gama gyara mai,itama ta zauna aka hau hirar tare yesmin ce cikin uniform na makaranta ta fito tana ma su saita dawo,naira dari yabata ta yi break sannan ya bata dari uku tayi abun hawa. Godiya tayi sosai ta fita tana d'aga ma addarta hannu. Shima tashi yayi bayan ya gama yaba fiyah kudin ta itama ya yimasu saiya dawo suka bishi da addua,mama tace"tunda bazaki makarantar ba ki tashi ki kwab'a alkubus yayanku yana tafe yace mun kiyi mashi." Gabanta ya fad'i don sunyi da malik zasu had'u karfe goma,intace saitayi wani alkubus bata san ranar fita ba,cikin murna tace"mama dagaske yah zaizo aikuwa zanso in shirya mashi abinci wlh,amman karfe goma inada lecture wlh kuma kanta zai mana test gobe,bacin haka aida bama zan je ba." Maman tace"to abunda zai ai kafin lokacin yayi tashi ki d'ebo fulawar ki kwab'a mun,saina idasa nima da fita zanyi inje gidan yaya balara ba,ingano hasana bata da lfy." Tashi tayi ta je ta dauko kayan had'in tazo ta fara kwab'in tana cewa"meyasa meta mama" Tace"kinsan tana da iska to daga makaranta aka maidota sun matsa mata wlh,basu bari ma tayi karatun karshe dai kilan day zata dawo." Nan suka ci gaba da hirar suna jajanta abun,hasana diyar yayar mamace dake can wata unguwa bama nan cikin abujar suke sosai ba. Karfe tara da rabi tayi wanka ta shiga shiryawa doguwsr riga tasa mai dan karen kyau,don Antynsu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta tare masu sitira,duk da shima baban ba baya ba duk salla kala biyu yake masu,jamila ta kara masu kala gida da gyaluluwa da takalma,har mada kayan kwalliya da turaruka shikuwa jalal shike dauke duk rabin hidimar gidan,yana da kokari sosai don inzai zo daga kaduna d'unkuna yake zoma baban dasu da kuma takalmomi kayan abinci da dadai sauransu. Tana cikin saka turare text d'insa ya shigo wayarta,saurin ajiye turaren tayi taduba. _ina silver bird place guiding yanzu haka ina jiranki._ Shiru tayi tana tunanin yadda zatai ta isa wannan wajen,anya Malik yasan kuwa inda yake cewa ta samai,wannan wurin ai ba na irinta bane,kuma kudin taxi kansu sun isheta don dari bayar bata kaita ta maidota..........abayarta milk ta saka tana jimamin abun,wsta yar jakace mai kyau ta dauka ta fito mama na tsakar gida tana yankan alayyahu na taushen da za,ai tace"har kin fito." Tace"mama don Allah in anshi dari uku wajen dalha,hand out zan siya na manta ban gaya ma baba ba." Kalonta take kafin tace"shikenan kije ki ansa allah ya kiyaye kiyi addua idan zaki fita." Sallama tayi mata ta fita ta anshi kud'in ta wuce. Taxi ta tata bakin titi ta gaya mai inda zai kaita saoda sukai ciniki sannan suka tafi. Sadda suka je get din arufe ta rasa yadda zatai don wajen yana da k'a idoji wayarta ta fiddo ta mashi text cewar ta iso yazo yayi mata iso. Tana nan tsaye na wasu minty na sannan taji an bude wajen,malik ne yasha kananan kaya sunyi masifar ansar jikinsa,don shima malik badai kyau ba,murmushi yayi mata yayi mata nuni da cewar ta taho. Itama ansar murmushin ta bashi ta isa inda yake suka jera har cikin palace din,waje ya had'u yahad'u iyakar had'uwa,fad'an yadda yake b'ata bakine don wajen sai wane da wane suke zuwa don wajene na shak'atawa ne. Wajene na musamman ya sauketa rumface wayayya anjera kayan cinye cinye da lashe lashe. Zama tayi shima ya zauna yana kawata fuskarsa da murmushin shima,lemu ya samata tare da tura mata plet d'in snacks gabanta. "Bismillah tukunna,kafin infara zuba maki surutu in kwareki." Dariya tayi tace"haba dai yah malik." "Ehy mana,inason in sanar dake waye ABDOUL-NASSER ALFAH,don kisan ta ina zamu shawo kan abun." Jinjina kai tayi ta d'an kurb'i lemun ta d'anci springros ta goge bakinta da tishu. "Yah malik ina jinka,naci ai wlh bana jin yunwa nayo kalaci sosai." Baice komi ba ya gyara zaman shi yafara magana kamar haka cikin sanyi da tausasa harshe. "Abdoul Nasser muazzam kabir canji d'ane ga Alh muazzam canji shugaban y'an canjin Abuja gaba d'aya,yyi suna yayi fice a k'asa baki d'aya,domin bai anan kadai arxikin sa ya tsaya ba,ya rik'e minister a oxport sannan yana da kamfanin motoci M.K motors dake cikin garinnan,wande kika sani sannan yana kasuwancin shinkafa babu inda motocin sa basa zuwa,legos,ibadan,adamawa,maiduguri state daban daban.atakaice Alh muazzam mashahurin mai arzikine na bugawa ga jarida,babu inda sunansa baiyyi yawo ba sannan manyan yan siyasa Suna hudda dashi saboda jama,arsa mutunne shi da Allah bai hore mashi yawan kyauta ba,ba marowaci bane amman kafin ya bayar ana jimawa,baidamu da talaka ba hasalima baisonsu baison su rab'eshi ko kadan,inkinga wani na cin arxikinsa to kuwa abokinsa ne mai kudi irinsa,ko wanda bai kaisa ba.wannane babban kalubalensa. Agefe guda Alh muazzam matansa biyu hajiya mariya itace uwar gida,Allah ya basu zuria itada Alh duk mata guda hud'u,akwai Amina da Haulat zuwairat sai khadija.sai agolarta data zo da ita gidan zakiyya duka yarinyar bata wuce shekara ashirin da daya ba ayanxu sa,ar ni'imah ce kanwar Alfah. Amina da haulat yayyene ga Abdoul-naseer yayinda zuwairat da khadija suke k'anensa,hajiya Ushe itace mata tabiyu ga Alh muazzam kuma uwa ga Abdoul,Allah ya azurtata da samun d'a namiji daya tamkar da dubu ko ma ince miliyan,don shine d'a na farko wajenta dayar macece maisuna ni,imah don su biyu kadai Allah yaba mami. Hakikanin gaskiya zaman lfy yayi karamci gidan Alh muazzam,domin hajiya mariya wadda ake kira da umma wstau uwar gidan tana bala,in jin zafin mami badan komi ba saidan ita kadai ce wadda ta haifa ma Abbi magaji,kuma magajin jarumi mai dakakkar zuciya,mai tsayuwa kan lamarin gidan baki daya,don komi dakika sani game da dukiyar Abbi Abdoul shine ja gaba wajen tafiyar da komi,har su matan nashi komi suke so to shi zasu tambaya,haka kannensa da suma yayyen nashi. Wannan ne ya jawo matsanan ciyar tsana da kiyyyar su wajen umma da yaranta. Bata kaunar Abdoul ko miskala zarratin,yayinda shikuwa kamar ya kwanta mata wajen biyayya,domin wannan umurnine daga mami ta bashi shida ni'imah,cewar kome umma zatayi masu karsu kuskura suyi mata koda kallon banza. Bayan yaran yaran umma daga baya ta d'auko d'an kanwarta rik'o gidan mai suna Mamman.saika rantse anan aka haifeshi,Abbi bai ce don me ba don shi bai cika damuwa da irin wadannan abubuwan ba,sannan rigimar cikin gidanshi yasan da ita amman bai tab'a magana ba. Shiyasa umma take tsula tsiyarta yadda takeso sannan abu na mai ciwo ga halayen Abbi shine duk abunda akazo akace mashi wane yayi,bazai tab'a bincike ba zai yarda kuma yayanke hukunci,ko waye kau amman banda Abdoul,don babu wanda yayiwa yar da irin wadda yayi wa Abdoul.umma tasha kai mashi karar Abdoul cewar yayi mata kaza yayi mata kaza amman kullum maganarsa guda itace "Naseer baxai yi abunda zai b'ata rai na ba mariya,kidai ji tsoron Allah." Shiyasa ta dauki tsawon lokaci batayi nasara akan Alfah ba,don kuwa Abdoul ya zama tauraro mai haske xuciyar iyayensa,mutunne mai fara,a koda yaushe zakiga fuskarsa cikin walwala,ko b'ata mashi kayi zaiyyi murmushi kawai ya wuce bazai tab'a ce maka don me ba yanada jama,a sosai don yana hud'd'a da talakawa sosai,yana kuma sakarmasu aljihunsa ko fita sukai da Abbi marok'a suka rufesu tofa shizai ringa masu b'arin kudi.Alfah Allah yayi shi mai dogon hannu,jin dadinsa da Abbi keyi yasa ya gina mashi Wani kantamemen store dake cikin garinnan nasan zaki sanshi ALFAH STORE SHOPPING MALL ya cikashi da kaya ta ko ina kuma du abunda kikeso na b'angaren more rayuwa inkika shiga Alfah store kin samu. Bacinan ya sakarmashi ragamar kamfanin MK motors duk wasu kudi dake shiga da fita to sai sun biyo ta wajen Alfah sannan suje ga Abbi. Fiyah ta katseshi tace"waye daddy wanna da muka ganshi station." Ajiyar zuciya yayi yace"Daddy babban aminin Abbi ne,kuma d'an uwansa guda tal dasuka fito ciki guda,shima yana cikin estate dinan cikin mai tama." Shiru tayi ta sake cewa meyasa aka samai Alfah." Murmushi yayi yace"wannan sunan daga mami yake,don tace tunda tataso wajen yayarta bayan rasuwar iyayensu take son yaron yayarta mai suna Alfah,sunyi soyayya kamar su cinye juna karshe uwar mijin yauar tata ta zab'a mashi mata.mafarin kenan mami data haifi Abdoul tace inkiyarsa kenan Alfah shikenan Abdoul-naseer ya b'ace saidai Abbi kawai ke kiransa da ABDOUL-NASS,wlh fiyah Abdoul ya fuskanci bak'in ciki ta dalilin umma,don kau umma tun Abdoul yana cikin ciki take son ganin bayansa Allah bai bata dama ba,domin kuwa Allah yace sai yafito saiya rayu rayuwa mai kyau.Abdoul yana son y'an uwansa yayinda sukuma babu abunda suke son gani irin mutuwarsa,don mahaifiyarsu ta riga ta dasa masu tsamarsa tun suna y'an kususan su,haulat da Amina sunyi aure suna gidan mijinsu sai zuwairat da khadija da kuma zakiyya. Ana cikin wannan hali fiyah Abdoul ya fad'a soyayya da zakiyya diyar umma agolarta data zo da ita gidan. Wanda zakiyyar itace ta fara nuna mashi tana sonsa,don tunda tazo gidan Allah ya dasa mata kaunarsa,amman komi suke yi babu sanin uma,ab'oye sukeyin kaunarsu ni kadai na san da wannan soyayyar." Sake katseshi tayi da cewar "yah malik ina kai banji taku alak'ar ba,nai tunanin kaima d'an gidanne." Ruwa ya d'ansha sannan yace....... Mrs bb ce Mom muhseen. *Comment and share it* [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........11 "Banda wata alak'a da Alfah sai abota ko nace amintaka,na had'u da Abdoul wajen dawowarsa daga taron siyasa ya wakilci Abbi wajen taron rantsar da wani minister.abunda kuwa ya had'a mu shine Richard card na waya,go slow ya tsayar dasu nikuma Ina bin layin layin motoci ina masu tallar wani sabon layi da kuma katin waya,Ina daidai motarsu naji drivern yakirani abunka da maison ciniki aguje na iso har ina ingije wani mai Babur,ya dunga antayo man zagi nibama tashi nake ba,cinikin da kekirana nake ma hanzarin isa gareshi.Ina shashsheka nace. "Gani" Driver yajuya baya yace"yallabai gashi nanawa zai mik'o." Abdoul dake baya hakimce yasha wat a arniyar gizner yace"anso duka kona na wane." Jinai kamar anmun gafara,don kuwa wannan cinikin yayi masifar yimun dadi Ina rawar jiki na ciroshi duka na mika mashi daman na 5k ne kawai. Maimakon naga 5k fiyah sai naga 15k kankace me tuni idona yacika da kwallah,godiya zanyi Amman baibani dama ba yamiko min card dinsa yace on Tuesday inasamai maitama around 6:30 haka suka barni da farinciki kamar me,ranar har kukan dadi nayi. Don ban tab'a samun kyauta makamanciyar irin wannan ba,na shigo Abuja cikin bakin talauci da rashin gata,nine buga can nine buga can,haka nake rayuwa. Shago na Kama Ina za man haya,duk bayan wata uku nake biyan dubu goma sha biyu. Aranar da ana gobe zanje wajensa, sai naga dare ya jima bai kare ba,har gajiya nai da kwanciya haka dai har gari ya waye,na fita buge bugen dana Saba,don wanan kudin bai hana ni fita nema ba. Still titin na nufa na hanyar lugbe na had'a omona ina wankin glass Ana bani naira dari...........inata aikina har sadda lokacin tafiyata yayi shagona na koma na unguwar gwagwalada nashirya na hau taxi zuwa maitama estate. Numfashi ya sauke idonsa akan na fiyah datayi shiru ta na saurarensa yace"kinga munsaki layin Maigida Abdoul-naseer mun Kama wani ko,inason na baki ansar tambayarki kafin mukoma ga asalin abunda ya zaunar damu kafin lokaci yayi." Gyara zama tayi fuskarta duk tayi kalar tausayi tace"yah malik kenan duk hasashena akan alakarka da.....Abd...abokinka Ashe ba haka bane inson inji naka labarin rayuwar don har ciki xuciyata ahaka ma ya nuna mun kasha wuyar rayuwa." Ruwa yasa Mata ya mik'a mata yana murmushi Mai kyau da tsari yace"abun kuma yayi mun yawa hajiya sofiyyah,kibari na karashe maki na mutumen mana tunda naji sunansa ma wuyar fada yake maki." Dariya ta d'anyi tasha ruwan kad'an tace"uhm Ina jinka ka cigaba." Cigaba yayi da cewa"sanda muka isa unguwar daker jamian tsaron dake area wajen suka barni na k'ara gidan,don card din daya bani duk address din naciki. Sanda naga wannan daula ta gidan numfashina saida yaja,najinjina irin mahaukatan kudin da aka narkar wajen,maigadi nagaida yana tambayata wanake nema. Kallon card d'in nayi nafada ma shi sunansa yace to nazauna nan bari yaje yasanar dashi aciki. Inanan zaune yaje ya hadawo yace muje nakaika masaukin bak'i,haka nabisa baya Ina sake kalle gidan kamar Wanda yazo daga riga. Haka nazauna tsawon awa guda cikin wani tsalelen falo sai fitar da ni'ima yake ga k'amshi kamar me. Amman fa ankawo mun lemo da kayan cinye cinye. Babu jimawa saiga shi ya shigo fuskar nan kamar gonar auduga,sai Fara,a yake tashi nai Ina mayar mashi da martanin murmushi Zan zauna k'asa,saurin rik'oni yayi yace"haba dai abokina,meye haka tashi don Allah zauna anan kusadani." Haka muka zauna kujera guda ya mik'o mun hannunsa mukai musabaha. Bai jani da nisa ba yace"hakikanin gaskiya abokina na yaba kwarai da hankalinka da natsuwarka da kuma jajircewarka,gaskiya ka burgeni kabani sha,awa domin ba kowane matashine kamar ka zai iya yawon siyarda card ba,sanan ba kowane zai iya yawon wankin glass ba Ana bashi naira dari har yayi godiya ba." Kallonsa nai nace"ka ganni rannan ne yallabai." Kafad'ata ya dafa yana dariya yace"bama rannan ba ABDOUL-MALIK na sha ganinka different places,naganka kana jan taxi don har dauka ta kayi,sanan kayi gadin NI'IMA MEMORIAL SCHOOL kafin akoreka,sannan ka siyar da youghout da purewater.......duk nasani,dalili kuwa shine nasa ana bibiyar Mani Kai." Idona kamar zai fad'o nake kallonsa cike da mamaki daker na iya cewa"yallabai.......not yallabai kakira ni da ALFAH ko ABDOUL-NAS don inajin dadin sunyen fiye da tunani." Shiru nayi Ina jinjina karamci da mutunci irin nashi kallonsa nasa ke yi nace"Amman taya haka,menayi maka mai dadi yasa duk haka tafaru." Donet d'in dake cikin bowl da aka kawo Mani ya dauka ya gutsira yace"ranar da ka d'aukoni motatace ta tsaya nabaro driver DA maigyara bakin hanya nikuma na tsayar dakai ka kawoni gida. Akan hanyar ne naji wani Wanda kuka gaba dashi yana ce maka,malik kadai baka gajiya yau kaine wannan aiki gobe kaine wancen,wlh ni bazan iya wannan wahalar ba duk inbi inkare ga aikin wahala.gara inzauna har sadda aikin office zaizo,Kai ko kunya bakaji wace mace xata soka kana wannan Sana,ar haba shiyasa duk aka gujeka." Ansar daka bashi ita ce tayi masifar yimun dad'i cewar dakai. "Ai babu babban malalaci irin Wanda zaikwanta sai anciyardashi sannan kake maganar wahala,duk namijin dayasan ciwon kanshi dole yayi wahala wajen Neman nakanshi,sannan aikin office daka ke magana,inhar ba hanya gareka ba bakasan wani ba babu ta yadda za,ai kasameshi kuma ni na gode ma ALlah daya bani rai lafiya da nake iya Neman na kaina har na iya yiwa wani alheri. Basai naje nayita maula ana cimun fuska azagan azagi iyayena sannan aban awulakance,ahaka ahaka Allah zai bud'aman don yace tashi in taimakeka." Wannan maganar itace tasa naji kayi masifar burgeni kuma naji sha,awar taimakon ka saida nasa akaringa bimun Kai aka tabbatar mun da Cewar kai din jajirtaccene kuma jarumi Mai yin iyakar kokarinsa don ganin ya rufa ma kanka asiri.wannan yasa nace Zan taimakeka zaka zamo abokina aminina kuma d'an uwana,don haka daga yau kadawo d'anan gidan kuma kai zanba wa amanar company nina da store Dina,don nauyin dake kaina yayi mun yawa,Amman tamabayata anan malik itace inane asalinka kuma ina iyayenka,sannan miye matakin karatun ka?.............. 😊sorry wlh banda caji Ku hadu gobe. Comment and share Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........12 "Nisa wa nai nace mashi iyayena sun rasu,tun ina dan shekara goma a duniya,mu y'an Asalin katsina ne anan iyayena suka yi aure har suka haifeni ni kadaine d'ansu watarana b'arayi suka shigo mana suka kashesu,suka sama gidan wuta Allah kadai ya rayani bacin bakar wuyar danasha asibiti.saida nayi wata uku kwance,wata diyar yayar babana ta yi jinyara,itace ta cigaba da rik'eni har Allah yasa na mallaki hankalin kaina.ninake dauwainiya da kaina in biya kudin karatuna,babu irin sana,ar da ban ba ahaka har na samu nasarar shiga jamiar yar aduwa university.anan nayi karatuna na business administration,Alhamdulilah nasamu result mai kyau ina yin graduation mijinta yace inzo muje abuja inda yake kasuwancin sa,ahanyarmu ta zowa aka kirasa matarsa da d'ansu mota ta banke su sunrasu. Juya wa mukai muka koma akai zaman makoki naji wannan mutuwa kamar kamarme nadade ban dawo daidai ba,karshe shi bai dawo abuja ba sainine na biyo hanya nazo na kama hayar shago inda yan kudina naja jari nacigaba da yan buge buge na.kaji asalina kaji karatuna yanzu haka banfi shekara biyu dana gama service ba.inanan ina tara kudi zan koma masters." Jinjina kai kawai Alfah yake yana kallona kafin yace"gaskiya kai namijin gaskene malik ka burgeni Allah yajikan iyayenka yakuma gafarta masu da ita ma marik'oyar taka,abunda za,ai tashi zakai muje part dina kaga d'akinmu don gado daya zamu ringa kwana,zan gabatar dakai wajen mami da Abbi idan ya dawo don tuntuni nayi mashi maganar itama mami harta zak'u da son ganinka inyaso anjima ida kahuta saimuje kakwaso kayanka zuwa safe saimu fita muje kaga komi yadda yake,fatan zaka daukeni kamar d'an uwanka na jini don ni tun randa na fara ganinka ka kwanta man Arai naji ina sha,awar taimakonka don allah malik kazama mai rikon amana karka bari wani yabiyo ta wajenka ya cutar dani,zan iya yafe komi amman banda cin amana banda munafurci Don Allah ka kula,Allah yabamu sa,a ya karemu daga makiya." Tundaga ranar nazama d'an gida mami mahaifiyarsa jitake dani kamar dai Alfah haka ni'ima yaya sama yaya k'asa,haka wajen Abbi ma na samu karb'uwa sosai don min saba kamar yadda yakeyi da Alfah haka nima yakeyi dani,saidai bangaren umma ko kusa hakan yayi wuya,itadasu zuwairat kamar su cinna man wuta zakiyya budurwar Alfah kawai muke gaisawa sosai ta dalilin kaunar da takewa Alfah,soyayya suka buga kamar zasu cinye juna,basa iya yini zungur basu ga juna ba ko basuni muryar juna ba,duk irin yadda Alfah yake cikim busy to kau yana da time d'in zakiyya. Kwatsam rannan ya kirani yace ina dauko zakiya intaho da ita nan company sa na fation&designer's gallery's,yinin yau bai ganta ba kuma basuyi waya ba,gashi bazai dawo ba sai dare can. Waya mukai da ita nace ta saman bakin titi don ma karwani cikin su haulat ko khadija wani yaganta da ni don ranar saita ci bugun tsiya. Tayi sa,ar samuna bakin titi muka wuce can wajensa,duk yana yin ta babu dadi nace mata"zakiya lfy dai ko,naga duk fuskarki babu walwalah." Idonta ya kawo ruwa tace"yah malik ina son yah Abdoul,wlh nikaina ban son irin son danake mashi ba,duk wannan bashine damuwata na damuwata itace yadda umma taketa bin kwakwkwafina,ko unguwa nace zanje sai tayi tayi man question daker nake samun nasarar kuccewa,yauma kamar bazata bari na fito ba saida nayi mata karyar cewar makaranta ake nemana,duk abunda su khady keyi dasu yah Amina bata yi masu wannan bin kwakwkwafin saini da nake iyakar kokarina don ganin na kare mutuncina." Hkr na bata ina kwantar mata da hankali har mukaje company har office d'in sa yana fa fama da files,da resit. Ya na dora idonsa akanta ya lumshe idon,yana sassanyar murmushi mik'ewa yayi ya fito daga cikin sit din yana bude mata hannunsa.nidai gefe nai ina kallonsu don Alfah ya iya soyayya idan yana son mace,to kau babu abunda zai iya dauke mashi hankali akanta,kuma baya jin kunyar nuna ta gaban kowa. Isowa yayi gabanta yana langabar dakai idonsa akanta murmushi yayi yace"Alhayat,meke damunki ban saba ganin haka ba karki cutar dani zuciyata baza ta dauki wannan canji naki ba." Kwallah suka cika mata ido zatai kuka ya tallabo hab'arta yana kallon idonta,cikin sanyin murya yace mata"nasan damuwar,yauma an maki abunda aka saba ko,plss karkiyi kuka nima zan iyayi bazan iya jurar kwallarki na zuba ba,insha Allah komi zai wuce kwanan nan zan jewa Abbi da maganarmu,ayita takare abunda kawai zan ja hankalinki shine duk rintsi duk wuya karki jiya man baya,karki yarda abiyo ta wajenki a dakile mana farinciki.zakiya ban tab'a son wata kamar ki ba,haka bazan sake son wata ba har duniya ta nad'e da kina raye da baki raye.duk bala in umma gabanta zan daukeki na bar gidan dake ranar da kika zama mallakina,naje har bakorin na samu yayan babanku munyi magana wlh zakiya idan kinga ban sameki ba to kece kikace bakiyi dani." Share kwalla take tana jin tsananin kaunarsa taya ma zata bari umma ta rabata da wannan tsalelen guy,tasan har abada bazata sake samun kamar sa ba,bacin haka Abdoul na da kudi bata da burin daya wuce ta zama matarsa,kodan ganin ta tsunduma cikin dukiyarsa. Cikin zubar kwallah tace"ka dauka kaine mukulli da kwadon xuciyata yah Abdoul,daga kan ka na rufe na jefa dan mukullin cikin rijiya mai gaba dubu,wlh ni kaina nasan bazan iya rayuwa mai dadi babu kai ba,ina jinka kamar yadda nakejin numfashina,amma ina tsoron kaidin umma kasancewarta uwa ta amman wlh kaidinta yafi karfina don Allah ka sama mana mafita in fita daga cikin wannan tsoran." Lallashinta yayi tayi malik dai karshe fita nai nabarsu sukaci kaunarsu yadda suke so sai shidda suka tashi tare suka koma gida.wai ashe tun bayan tahowar mu khady na biye damu har wajen company. Dadaddare muna cikin harabar dake gaban part dinmu ta kirashi. "Yah Abdoul kana shan kunun aya dakaina na yi inason kasha kaban maki yah zuwairat ce tace wai baiyyi dadi bah." Murmushi yayi yana operating system yace"aike Hayaty ko kasa kika dama dadi take balle kunun aya,wow zan so insha inji how fah." Dariya tayi tace "kana ina inzo yanzu " Gyara zama yayi yana jin dadin muryarta yace"cikin rufa gaban part dinmu." Saida suka gama magana nace mashi"Alfah ina ganin akwai damuwa,dazun fa khady ta biyomu har company,kudaina yawan had'uwa ina jin tsoron kaidin umma,ba kamar idan tasan aboye kuke soyayyar." Mirmushi yayi yace"kyaleta ai gobe zan ma Abbi maganar nasan zai mata magana awice wajen,inason zakiya bana jin dar akan duk abunda umma zatai inhar zakiya bazata kwaremun baya ba." Ban sake magana ba saiga ta tazo ta kawo nan suka shiga kaunarsu kamar ma bana wajen,daga nesa na hango kamar inuwar mutun,na sake kalla wa sosai na gango mutunne kuma hoto yake dauka,tashi nai na nufi wajen kafin na isa ta gudu amman bazan iya gane ko wacece ba. Dawowa nai ban dai sanar da kowa ba sun jima suna hirarsu sannan tatafi. Haka lokaci yayata ja Abbi baya zaune Alfah bai samu damar sanar dashi kaunarsa da Zakiya ba,shima kuma ayyuka sun tasushi gaba,don ya fara shirin yin wata tafiya zuwa paris zai d'an jima,ni kuma switheland zanje shigo da wasu kaya da za,a xuba cikin store din Alfah. Hakanan naji ban son intafi mami ce keta ban kwarin guiwa har nasamu natsuwa,nariga Alfah tafiya da kwana uku sannan ya tafi. Awannan tafiyar fiyah komi ya faru,don ya rigani dawowa ranar dana dawo na iske wannan tashin hankali,Abbi yasa sojoji sun rik'e Alfah sai dukanshi yake yana halbinsa,yayinda yake kuka yana cewa. Nayi dana sanin haihuwarka,na gwammace ace b'arin cikinka uwarka tayi da dai inga wannan ranar,matata Abdoul bayan ka gama lalata d'iyarta shine ka dawo kan uwarta,ashe kai mazinacine dan iskane kai,har giya kakesha Abdoul,giya kasha giya agidana menayi maka mena tare maka kakeson kasheni da bakin ciki........kuka yake sosai an rasa mai cetonsa. Yayinda umma ke gefe tana cewa "Alh in baka kori wannan dan iskan agidan nan ba ni zanbar gidan,kuma wlh saina gurfanan dashi gaban hukuma,Allah na godema da bai bani d'a namiji ba da dai wannan masifar......ta rushe da kuka gefe guda ma ga zakiya kukan take kamar ranta zai fita. Zuwaira da haulat suna gefe saidai su shige cikin abaya suyi dariya,idan kika ga Alfah awanan rana saikin masa kuka,jikinsa ko ina jinine saida Abbi ya gaji ya kyalesa. Mami saboda tashin hankali ta kasa kuka saidai ni'imah dakeyi. Kan kace me harabar gidan ta cika da mutane,anan Alh kwangila yake tambayar Abbi lfy yake sanar dashi cewa cikin kuka. "Kwangila nai nadamar haihuwar Alfah,Alfah ya kasheni Alfah ya wulakanta ni matata ta sunna yasha giya yayi tatul yayi mata fyad'e,bayan lalata yarta da yayi zakiya ya mata ciki kuma saboda rashin imani ya kaita aka zubar,gashinan yarinyar ta samu matsala.......mezanyi da Abdoul arayuwata na tsaneka na tsaneka Abdoul har abadan abada baxan yafe maka ba.......afusace ya nufesa yana kukan yace"tashi don ubanka d'an iska wulakantacce,babu ni babu kai na yafeka daga cikin zuria ta,idan kabari nasake ganin fuskarka arayuwata saina ga bayanka......wlh kasheka zanyi. Nan fah mutanen wajen suka ringa zagin Alfah suka ringa tsine mashi albarka,ba kamar Alh kwangila yafi kowa zak'ewa har Alfah ya kasa jurewa cikin wata irin xuciya da ban tab'a ganin Alfa ciki ba ya shak'esa yana wani irin kururuwa saboda zafin xuciya. Ya d'aga hannu kenan zai kai mashi duka Abbi ya daka mai tsawa yace"kana dukanshi ina tsine maka Alfah,wlh tsine maka zan kabi duniya......zaka sakai ko kuwa" duk ga yan jarida nan yau sun samu kanun labaran da zasu yad'a su samu kud'i. "Inajin mutsaya nan fiyah kije kiyo test dinki zuwa gobe ma k'arasa,duk da mun kusa karashewa." Kwallar dake zubar mata ta share tana kallonsa shikuma yana mata murmushi tace"yah malik Gaskiya abokinka yaga rayuwa,ko ince yana cikin gani meyasa haka ta faru waye da alhakin wanan,wlh zan iya rantsewa bazai aikata haka ba.ayadda naji halayensa naji araina akwai wata ak'asa don Allah ka karasa man na yafe test din anmun makeup." Dariya yayi yace"rufan asiri kije kiyi test dinki wlh,kodai malamin saurayinkine da har zaiyarda yayi maki wani make-up." Murmushi tayi had'ad'd'e tace"aa yayan qawata ne kawai muna mutunci." Mik'ewa yayi yana kiran wani dake wajen yace ya hade abubuwan yayi takeaway dinsa,ya je ya nad'o naman dubu uku mai zafi. "Kitashi Allah bazan bari ki rasa test din kiba,muje ga mota na can saina saukeki." Ana kawo mashi ya jawo jakarta ya saka kallonsa tayi tace"yah malik duk nid'aya don Allah kabarshi za,amun fad'a agida fah." Hanya ya bata yace"no karki bari amaki fad'a in kinje school kici keda qawar fadan Alfah." Dariya sukai suna dosar inda motar sa take. *inhar banga comment daya wa ba bazan kara typing ba har sai sabuwar shekara.* Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* INA TAYA DUK KANIN MASOYANA MAZA DA MATA MURNAN BARKA DA SALLAH,FATAN ANYI SALLA LAFIYA UBANGIJI ALLAH YAYI MANA TSAWON RAI DA LFIYAR GANIN SHEKARA MAI ZUWA MOM MUHSEEN TANA MAKU FATAN ALKAIRI. 🅿️.........13 MALIK har cikin makarantar ya sauke ta tana masa godiya tare da cewa. "Yah malik sai yaushe kenan" Shafa kansa yayi yana murmushi yace"i think sai kin samu time,don naga satar hanya kike." Dariya tayi tace"wlh yah malik kamar kasani,amman insha Allah gobe zan kokarta infito don hankalina bazai kwanta ba har saina naji karashen wannan labarin,wlh yah malik abokinka yayi matukar ban tausayi,anya zan iya bacci kuwa?wlh labarin yasa na sakejin tausayin sa na kara jin kwarin guiwar taimakonsa." Jinjina kai yayi yace"karki damu kiwuce karki bata lokaci good luck Allah ya sa ki cinye Duka." Tana dariya sukai sallama ta wuce ciki bin bayanta yayi da kallo yana ayyana wani abu aransa,murmushi yayi mai tsananin kyau yace "wannan takun ma zai bada kala,zai taimakemu sofiyyah." Tashin motar yayi yabar cikin makarantar,gida ya wuce don duba Alfah. Motar Daddy ya gani alamar yazo parking yayi ya fito ya doshi cikin falon. Alfah na durk'ushe gaban Daddy shikuma Daddy yana ta faman yi mashi fad'a kamar zai ari baki,waje ya samu ya zauna yana kallonsu gaida shi yayi yace"rik'e gaisuwarka Abdoulmalik,yanzu gabanka Abdoul-Nasser yake shan win amman bakai kokarin sanar dani ba,giya fah giyar ma d most high one wadda zata iya kashe sa cikin k'an k'anen lokaci." Cikin biyayya da taushin murya malik yace"Daddy wlh Allah yasani nayi iyakar yina,nayi nayi da Abdoul akan shan giyar nan amman kamar tunzura shi nake,nasha kwashe duk na cikin frig din gidannan in zubar amman saiyayi kamar bazai barni da raina ba akan haka,sannan yaje ya kwaso wasu wlh Daddy ban san yadda xan da shi ba,gashinan baya jin nasiha baya yarda da hukuncin Allah,yaki hkr yaki fawwala ma Allah lamarinsa,saboda an masa k'azafin shan giya to bari yasha d'in dagaske.kuma har likita yayi mun bayanin cewa yaci sa,a babba da matsalar da take kokarin bashi ba babba bace,don duk mai ta ammali da wannan giyar baya kai labari." Jinjina kai Daddy yake cike da b'acin rai yana kallon alfah da ya sadda kai k'asa yana jin kamar ya kamasu yayi masu shegen duka. "To yayi kyau,ni zan kwashe su na zubar don Allah ka sake siyowa kaji ko,nace ka sake siyo wasu kaikuma muddin baka sanar dani ba halin da yake ciki kaida Allah.idan shi yaya ya wofintar dashi hakan bai nufin Abdoul baida sauran na gaba dashi,don haka duk abun da yake ciki ka sanar dani zan dauki mataki mummuna akanka." Ya tashi malik na tayashi suka kwashe duk wata giya dake cikin gidan suka je suka zubar............ko ajikinsa don ya sa aransa saidai giyar tayi ajalinsa,amman bazai daina ba. Bayan tafiyar Daddy malik ya dawo cikin falon amman abunda yabashi mamaki cup ne hannunsa da win din aciki yana kurb'a yana lumshe ido........... Sorororo yake kalon sa yana mamakin ina ya b'oye wannan har basu ganta ba,takowa yake cikin falon ya iso har gabansa ya durk'usa gabansa yana dafa guiyawunsa cike da karyewar xuciya yace"haba Abdoul,meyasa meyasa bazaka barmu muhuta ba,bazaka bar kanka ya huta ba.duk abunda muke munayi me don gyaran gobenka,ina tsoron mutuwa ta riskeka acikin wannan halin,Allah babu ruwansa da kazafin da aka maka,har ka yanke wannan hukuncin,don babu ina haka yazo acikin qurani balle hadisi.kayiwa rayuwarka gata ka dawo cikin hayyacinka,kadawo kakoma ga mahaliccinka duk wannan zafin rai bazai canza komi ba,kakoma ga Allah ka rokesa ya bayyana gaskiya.amman ba ka nemi kaucewa addininka ba." Saika rantse bada Alfah yake ba,shan win dinsa yake idonsa rufe yana girgiza k'afa,nan kuwa banda tafasa babu abunda zuciyarsa keyi,jiyake kamar ya cirota ya jefar,yana shanye win din yayi wata irin jifa da cup din yana bude idonsa akan malik. Saboda masifa da tsananin xafin rai idon nan yayi wani irin fitinennen ja,da sauri malik yaja baya biyosa yayi shikuma yana sake ja baya,har yayi nasarar shak'osa ya dagane sa dabango idon nan kamar zai fado yake mashi wani irin kallo,cikin kakkausar murya yace. "Bazan bar shan giyar ba,ehy nace bazan bari ba kabarin mu guda ne? to kashiga taitayinka ina d'aga maka k'afa baka gani ko,to kuskuren da zakai muyi hannun riga shine sanar da Daddy Wani abu akaina marar dadi." Ya watsar dashi nan kasa ya nufi hanyar fita falon,har ya kai k'ofa ya juyo yana kallonsa yace"inhar na sake ganin fuskarta agidannan saina kasheta ka sanar da ita wannan." Mekenan yaga fiyah kenan rannan,Oh Allah na gode maka da bai zo yayi mata wata illar ba,kai wannan bawa naka ya Allah ka kawo mashi sassauci. A makaranta fiyah sun had'u da feea,take mata maganar Alfah. "Wai fiyah kinko sake ganin guy d'in nan." Fiyah na duba question din da suka gama test akanshi yanzu ta ga ko ta ansa daidai,tace mata. "Ni kuwa ina zan ganshi rafeea,wannan dan zafin kai ai haduwa dashi hadarine." Dariya tayi tace"haka maganarki take amman kinsan tun daga wannan rana kullum yana cikin raina,tausayinsa nake sosai,inama zan iya taimakonsa inama ace ya dawo cikin natsuwarsa wlh ina jin kamar ina sonsa." Dagowa fiyah tayi tana kallonta cike da mamaki da al,ajabinta tace"kina cikin hayyacinki kau feea,kirasa wanda zaki kamu da sonsa sai wannan guy d'in,to wlh ki shiga hankalinki inba so kike kirasa jinki ko ganin ki ba.yo daki tunkari wannan damisan mutumen ba gara kin rungumi transformer ba ki huta kawai." Me feea zatai ba dariya ba,yitake har tana duk'awa saboda dariya. Itama fiyah dariyar tayi tace'wlh kau kedai kiraba kanki da wahala kurin,kii da d'an salim dinki." Haka suka ringa hirar suka wuce gida tare. Sanda ta je gida har yayansu jalal ya dawo ta iske uwar tsaraba,rabin buhun dankalin hausa dana turawa,ga kayan miya kamar banza,ga ayaba da yayo masu kayanta. Sai takalma na mata masu shegen kyau itda yesmin sai dinkunan baba kala uku hada babbar riga. Duk na sallah ne dake gaba towa don azumin baifi saura wata daya ba,mama kuwa atamfarta maikyau da tsada da yafin abaya. Gaskoya yah jalal badai hidima ba Allah yayisa mai zuciyar nema. Don ko acan ba zaune yake ba yana noman rani acan,ga sim card dayake siyarwa yana samu babu laifi ga kuma albashinsa. Ranar mun yini cikin farin ciki da annnashuwa don yah jalal yana sake mamu,duk da shima wani lokacin kamar Anty yake. Baba daya dawo yaga wannan abun arxiki ya ringa saka mashi albarka,yana mashi addua masu kyau.bamu kwanta ba ranar sai sha biyu. Da asuba na kira malik saida na kaikaici yesmin tana bayi. "Yah malik na tasheka da sassafe ko." Gyara kwanciyar sa yayi baccin bayan sallar asuba daya dawo,muryarsa cike da bacci yace "kin cancanci tashina ai,ya kika kwana." "Lafiya lau yah malik,dama nace ina zan sameka zan fito karfe sha biyu." Murmushi yayi yace" gida zaki saman." Zaro ido tayi kamar yana ganinta tace"yah malik gida kuma?nidai aa kafito sai muje wani wajen gaskiya nidai ina tsoron wannan mutumen." Dariya yayi mata don ya cire mata tsoron zuwan yace"ai bainan yau na samu na turashi company." Ajiyar zuciya tayi tace"shikenan,amman ni gaskiya yah malik inajin tsoron sa karya mun wani abun don nasan wlh ya rik'e fuskata." "Karki damu babu abunda zai maki ai inanan." "Shikenan sai anjima." Kashe wayar tayi tana sauke ajiyar xuciya gabanta yana faduwa,tana tausansa tana tsoronsa kuma.sannan burin taimakonsa baixai gushe daga ranta ba har sai taga Abdoulnaseer ya dawo ainahin Abdoul din da kowa ya sani.yesmin ce ta tab'ota tace"Adda tunanin me kike nafito inata magana bakijini ba." Firgigi tayi yadawo natsuwarta "ba komi yesmin,ina tunanin test dina ta jiya kona rubuta ta da kyau gashi yau zai bada ita." "Kai Adda keda duk abunda kika rubuta kinsan kinci kimabar wani kokwanto,ke ai cinyedu ce wlh." Dariya tayi tace"ban son xiga fah,waya kaiki cinyewa keda yah jalal." Nan suka ringa maida magana har gari ya idasa wayewa sukan hau ayyukansu na yau da kullum. Bayan sun gama kalaci yesmin zata wuce makaranta tace ma mama"mama banga baba ba tunda na tashi,gashi zan ta makaranta karna makara." Mama dake shan kunun ta tace"wlh ankirashi ne tunda bayan asuba,har yanxu baidawo yayi kalaci ba,amman kije kisamu yayanku ya baki kudin taxi karki makara." Haka tayi masu sallama ta wuce itama fiyah bayan ta gama duk abunda zatai ta yi wankata kamar yadda ta saba,tasha kyau tsantsagoran sa don fadarsa ma b'ata bakine. Yah jalal ya bata kudin taxi don har lokaci baba baidawo ba. Tana isa k'ofar gidan kirjinta ya buga ta sallami mai taxi din ta shiga koran malik. "Kayo ka shigo dani wlh atsorace nake." Kashewa yayi ya fito yasha wanka malik badai gayu ba."wannan toron naki dole saikin barshi inhar kina son mucimma nasara,don idan yagane kina tsoronsa shikenan kin bani.don haka daure fuska zakiyi kisha mir kuma fuk maganar daya gaya maki kema kigaya mashi fiyeda wacce ya sanar dake,hakan da zakiyi shine zaizamo kamar makari daga zafin ransa akanki,don tabbas gamonki dashi dake nafarko nasan akwai dabi,kinsan randa kika fara zuwa nan gidan ashe yaganki,amman baimun magana ba sai jiya." Gabanta ya fad'i amman tasa dakiya ranta tace"meyace yah mali." Dariya yyi yace"cemun yayi ingayabmaki inhar yasake ganin fuskarki agidan nan saiya ka.......kafinmanyanidasa harta ruga ta koma wajen k'ofa. Mezaiyyi ba dariya ba binta yayi har waje yana dariya yace"kekuwa ya da rugawa karai kicemun kinfasa wlh fadane kurun yake aibazai iya kisaba kalmrce ke bshi nishadi idan yana fad'a don ya torataka.......zomuje don Allah yau nakeson na idasa maki lbr abunda yafaru ko kinyafe." Idonta yayi kwalkwal zatai kuka yadan sausauta dariyar yace"kinga wlh bazai iya yi maki wani abu ina nan ba nagaya maki ma baya nan ba yanzu zai dawo ba,karki damu kinko sofiyya." Badan taso ba ta sake binsa abaya amman fah zuciyarta zillo kurin take........... Mama nata hidimar sanwar rana dambu takeyi masu mai dadi na shinkafa,har ta dora hawan karshe saiga wasu mutane sunyi sallama gidan,abaya ta sanyo ta leko cikin zauren idinta na sauka kansu hankalinta yatashi cikin rudewa tace"jamiai lfy kodai b'atan kai kukai." Daya daga cikinsu yace"munzo sanar dake ne mininki yana police station,an kamashi ne da laifin rashin d'a,a ga Alh muazzam canji don haka karku sha wuyar nemansa don yana wajenmu,ba kuma zai fito don yanzunba mun barki lfy,amman karku sha hawalar zuwa belin sa don babu beli saiyaje yari." Silalewa tayi kasa cikin zauren ta fashe da kuka. Mrs bb ce Mom muhseen 09034722970. Muddin comment bai haura 70% ba *ABDOUL-NASEER ZAI KOMA NA KUDI KOKUMA NA DAINA TYPING HAR SAI NAGA CANJI DAGA GAREKU.* [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........14 Wajen da ya sauketa wancen lokacin nan ya sake saukarta,bayan ta zauna yadan rusuna yace"hajiya me zakisha." Murmushi tayi tana waigen nayanta tace"rufan asiri kaganni ko airport ni ban tab'a zuwa ba,amman karka damu kanka wlh bana son komi nidai kayi ka idasa mun infece kafin wannan boss din naka ya dawo." Dariya yayi yana jan kujera ya zauna yace"kinga can gashi can cikin d'akin exercise yana ta faman G-ming kawai dai abunda zakiyi ya taimakeki fiyah shine jajircewa,da fitar sa tsoro acikin ranki koda kinajin tsoron karkibari ya fito kan fuskarki kisha mur kuma duk abunda ya fada maki kiyi kokarin maida mashi wadda ya gaya maki,koma fiye da haka ki fetsare idonki gabanshi,shine zaisa ya sassauta maki kuma hakan zai baki damar shiga jikinsa kuma duk abunda kika zomashi dashi zai yarda." Murmushi tayi tace"uhmmm yah malik kenan nidai ina jinka kawai aman ina ni ina mayarwa da wancen gagaren magana." Dariya yayi ya cigaba da sanar da ita cewa. "Alh kwangila ne yace ma Abbi Alh muazzam zaman wannan yaron cikin iyalinka masiface babba,kamar yadda hajiya umma tace ka korai tokuwa hakan yafi dacewa,ka rabashi da kai ka ahalinka wannan shine mafita inba haka ba............cikin zafin rai da kunan zuciya Alfah ya shak'oshi iyakar karfinsa,ya ringa naushi ga fuska har hakorinsa ya fita,kuka yake yana cewa muryarsa duk ta dishe don kuka karya kake munafuki wlh baka isa ba kana gudun na fallasa.......kafin ya idasa abunda yakeson fada Mutanen wajen suka ringa janshi suna raba shi da Alh kwangila,daker aka rabasu inkinga yadda kirjinsa yake d'agawa saikin zata xuciyarsa fitowa zatai.Abbi ne ya iso wajen yana huci ya fizgoshi bai diresa ko inaba sai gaban mami wadda sai lokacin ta samu hawayen yin kuka,cikin kakkausar murya yace"zan fad'a gaban kowa kuma gabanki,daga rana mai kamar ta yau babuni babu Abdoulnasser na yafeshi daga cikin zuria ta,na barshi har abadan abada sanan wlh wlh wlh duk wanda na kama cikin yaran gidannan yana muamala dashi aboye ko azahiri wlh zaibisa,yadda na korai shima haka zaibisa.ba ga yara ba harke ushe muddin kika bibiyesa ko awaya ko zahiri daga ranar abakin aurenki,kidauka koda ban gani ba to ranar zakibar gidana..........yanzu ba sai anjima ba nakeson ka tattara komatsanka da wancen yaron da ka kwaso ka kawo mun agida,waya sani koshine ya koya maka kufitar mun agida yanzu,kuma karka bari ink'arayin arba da bakaken fuskokin ku,inba haka ba wlh sawa zanyi adaureku har tsawon rayuwarku........bazan anshe duk abunda ka samu daga jikina ba don wannan nayi makane domin Allah da wahalar da dakakemun........muryarsa tayi rauni sosai fiye da lokacin da ya fara magana.........bakayi mun Adalci ba Abdoulnasser ba ka kyauta ma rayuwata ba,duk cikin zuria ta babau wanda nakeso kamar ka,babu wanda ke kyautata mun kamarka,shine zaka yimun haka dole zaka ar jikina kuka Abi yake kamar yaro,kai idan mai hankaline zaka san cewar abun anfi karfinsa ne baida wata mafita........barin wajen yayi yana shashshekar kuka.ina daga can jikin bango ina nawa kukan,inajin inama ace mafarki nake ba gaske bane wannan wace irin bakar rana ce.umma kau tana ganin tafiyar abbi ita dasu haulat mezasuyi ba darinba,har gaban mami tazo tace to sai abi wani sarkin don yaudai tauraron gidan nan haskensa ya dishe har abadan abada mamman shine zai maye mana gurbinsa. Mami tana durk'ushe gaban Abdoul tana kuka ita da ni'ima bata maida kai ga umma ba. Cikin karfin hali da danne ciwon da yakeji ga xuciyarsa yace ma mami"mamina kuta shi kubar nan wajen wannan kukan da kuke bazai canza komi ba,kunfi kowa sanin waye Abbi baya magana daya don haka ni da ya fidda zan fita ba ka zan sake bari fuskata da tashi ta hadua sai in munje lahira sai Allah yayi mana hisabi." Ta shi yayi yana yafitoni akan inzo muje mu hada kayan mu, Alh kwangila da wani amininsa murmushi suke suna magana k'asa k'asa ba zan iya jiyo kome suke tattaunanwa ba dariya sukai suka fice daga gidan,yan jaridar suka rufa masu baya don da gani sune suka kirasu. Har mun fara nisa da barin filin wajen saiga zakiya ta rugo da gudu ta rungumeshi ta baya,tana wani irin kuka kar ramta zai fita tana cewa"yah Naseer wlh banda yadd.........wata irin fizga yayo mata daga bayansa,yayi mata wani kalar rik'o kamar ya rik'e doki ko wani k'ato girgizata yayi iyakar karfinsa harsaida numfashinta ya kusan fita,kokarin kwatar ta nake ua daka man wata tsawa da tun da nazo duniya banji irinta ba,ban tab'a ganin Alfah cikin irin wsnnam condition din ba,cikin tsawa da hargagi yake mata magana still yana rik'e da shoulder dinta "uban me zaki gaya man,mekike dashi da zaki gaya man,ashe daman kaunar banza kike mun ashe daman soyayyar cin amana muke nida ke,ahada kai dake acimun mutunci a wulakanta ni wannan tozarcin ya isheki ko da saura,jijjigata yake yana sake cewa nace ya isheki ko da saura to bari kiji zakiya wlh nai nadamar amuncewa dake arayuwata,natsaneki zakiya na tsaneki ban kaunar sake ganin fuskarki gabana,kuma kin ban darasi kin nuna man halinku na mata ashe duk haka kuke wannan ma ya isheni kibarni da wannan jeki kibar nan wajen. Yayi jifa da zakiya gefe saida kanta ya bugi wani tudu dandanan wajen ya fashe,yaja ni muka shiga tattara kayanmu muka bar gidan fiyah tunda ga wannan ranan har yau ban sake shiga maitama ba,bamu sake hada ido da wani daga cikin yan unguwar ba sai fah Alh kwangila da abun nan ya faru.ko mami bama waya da ita,saboda ranar da zamu taho ta kirani tana kuka kamar me duk ta tashi hankanlinta tana cewa kakula man da Abdoul malik ka kula man dashi,daga shi sai ni'imah nake dasu don Allah karka bari ya illata kanshi,Abdoul yana da zuciya xuciyarma kamar ta mahaukata muddin akaimashi abunda yafi karfin tunaninsa zai iya aikata komi akan shi,na rokeka karka barshi shikadai duk abunda zai maka don Allah malik karka barshi ya cutar da rayuwrsa,ta ban wsu iyayen kudi nikaina lokacin bansan adadinsu ba ina kuka tana kuka haka ma ni'ima tanayi muka baro gidan,lokacin daddy bai gari abun yafaru daga baya ya nememu yabamu hkr tare da cewa duk abunda muke so muzo mu samai. Amman lokacin Alfah sai ya kwana uku bai gidan nan,yana can club wajen wasu abokansa tun suna secondary,wanda sukaita kokarin ganin sun jawoshi cikinsu amman abun ya gagara sai yanzu da ya idasa rikicewa dafari har wiwi yakesha. yasha shisha duk wani abu da kikasan d'an maye yana sha Abdoul yasha abuguda ce baisha ba,itace sigari taba kenan. Nasha bak'ar wuya kafin na iya samo kanshi yana zaman gida,sannan nafara yak'in ganin ya daina shan sauran kayan mayen amman har yau Allah baisa giya ta barsa ba,nasha wuyar Alfah koma ince ina cikin shanta.kinji waye Malik sannan kinji waye Abdoulnaseer Alfah.yanzu zan bar maki wuk'a da nama sai d'an abunda ba arasa ba da zan kama maki dashi" Tana dafe dakai tasha hawayenta ta gode ma Allah. Cikin sanyin murya tace"yah malik wlh labarin ku yaban tausayi,yatab'a man zuciya nama rasa sanin ta ina zan fara kama abun,don akwai abubuwan tambaya aciki da basu da iyaka,amman kaban lokaci inyi tunani sosai akwai bukatar inkulla kawancen dole da zakiya,inhar Allah baisa tayi aure yanzu ba." Gyara zama yayi yace"zakiya nanan batai aure ba mun tab'a had'uuwa a store din Alfah tazo itada wasu kawayenta,taso muyi magana mai tsawo amman muna tare da alfah idan yasan intare da ita zamu samu matsala,tabbas hangen ki yayi daidai tunda bata sanki ba zaki iya bugar cikinta kisan gaskoyar komi kafin musan yanhar da zamu bayyana ta ga kowa.na jinjina karfin tunaninki wannan ma alamace ta kinda tsananin kokari makaramta." Dariya tayi tana duba wayarta alamar kamar sak'o taga har hudu tayi, "Yah malik inga zan wuce sai munyi waya kome kenam zamu tattauna." Ta shi yayi shima yana taka mata suna hira da dariya afuskarsu,kamar daga sama suka ganshi gabansu fuskar nan banu alamun rahma akanta ko miskala zarratin........fiyah jitai kamar zata saki zawo cikin wando har saida cikinta yabada sautin kulululu........tunkarota yake yana daure da fuska bata yi kokarin matsawa ba amman fah cikin xuciyarta k'es za ace mata ta ranci na kare. Ga wayar ta yah jalal nata faman kira babu halin dauka. Fiyah anshigo komar Alfah koya dramer zata kasance😂 Mrs bb ce Mom muhseen. 09034722970 Karku manta sanyin idaniya Abin cikin ruhina return,yana nan bisa hanya akan farashi mai tahusa darin ki biyu kacal ta nisha dantar dake,labarin mai tafe da rikita zuciya da d'okantuwa zuwaga ainahin inda zamuje.labarin yana dauke da salo salo da zaisaka mai karatu nishad'i da kuma d'okin jin yadda Ayman da sanyin idaniyarsa zasu kasance. Ku kasance da mom muhseen domin nishadantar da masoyanta. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........15 Wani irin kerma kafafunta ke mata amman iyakar dauriya ta aro ta yafa akan fuskarta,malik kau gefe yaja yana kallonsu yana jin tsoron abunda zaije yazo. Saida ya kusan shigewa jikinta sannan yaja burki idonsa akanta,wanda ta kasa cigaba da kallonsu saboda tsabar abunda yake fitowa daga cikinsu. Cikin kakkausar murya wadda kaushinta bai hanata fitar da wani sauti mai dadin amo ba,runtse ido tayi saboda har sautin maganarsa yana sauka akan fuskarta. "Kee ubanwa ya kawoki nan gidan,bai gaya maki sak'ona ba cewar idan na sake ganin bakar fuskarki saina kasheki.to in bai sanar dake ba yanzu kinji,don haka wlh in na sake hada ido dake ko ahanya ne saina kwalkwale idonki idiot stupid girl oya get out wawuya village girl dake." Sai lokacin ta d'ago dara daran idonta tubar kalla masha Allah farare tas kamar takarda ta zuba mashi su,idan da yasan yadda xuciyarta ke masifar bugawa da baikai ga gaya mata irin wannan zafafan kalaman ba,amman baka tab'a gane hakan akan fuskarta wani dak'ik'in kallo take watsa mashi,tana juya kwayar idonta kamar ba tata ba,kafin taja baya tana dad'e hanci da baki kamar taga kashi ko wata k'azanta.bacin salon nata kenan don dai kawai itama ta rama dizginsa da wulakancinsa,ja baya tayi tace cikin wata siririyar murya mai dadin saurare "dallah malam matsa ya zaka wani matsoni kana wannan smelling d'in,ka kuwa ji yadda kake tashi da alamar hancinka baya jin kamshi balle wari,aida kai kanka ka kyamaci kanka.har kake kirana stupid akwai wani stupid bayan ka,dubeka don Allah a haka kamar duka kenan,yo taya ma mutane zasu rab'eka kana warin giya mts!!! Move me kana wani tsaye bisa kaina." Dalalo idanu yayi kamar yaga sabuwar halitta,yana jin kalamanta kamar sukar mashi cikin kirjinsa juya wa tayi tana sauri don ta fice kafin ya kai ga saka mata kafa ya tad'oyeta,banda bugawa babu abunda kirjinta yake,har wani fitsari takejin yana taho mata bata wani buri daya wuce ta ganta tabar unguwar.........saidai kashhh tunaninta bai ci ba jitai anyomata wata irin fizga kamar zaitai da hannun nata. Afirgice ta ganta zube k'asa gabanshi fuskar nan ta sake rinewa cike da zafin xuciya ya daga k'afarsa zai taka mata hannu,cikin zafin nama malik ya karaso yajanye ta cike da b'acin rai yace mashi. "Mekake shirin yi Alfah,ina ruwanka da ita gunka tazo kokuwa ta kula da lamarinka banson cin zalin kaga kawuce kabarta tunda dai kaine ka fara tada wannan fitinar." Wata ingiza ya yiwa malik yace"karka gaya man nonsense malik,meye hadinka da ita miye alakarta da nan gidan,wallahi inka bari ta sake takowa nan yafada yana doka kafarsa da k'asa cike da mazan taka yacigaba da cewa to billahil azim za,a kwashi gawarta." Malik xai magana ta rigashi cike da tsiwa da rashin kunyar data aro babu jimawa tace"ni kuma saina zo,nan gidan dai ko to kadauka kamar gidan ubana yake haka xan mayar dashi,kwana ne kurun bazan ba kama hangoni gani can har dakin baccin ka,angaya maka kowa sakaraine da zaka ringa yiwa mutane hauka,yo waye bai iya haukan ba dallah can da kai mtsss!!cike da bala i yace"ke don ubanki ni kike gayaa magana tun kararta yake yana zaro ido tatare siket dinta tayi zata baza aguje don idan ya kamata ta bani ta lalace.......kotaki guda batai ba ya cabko hannunta ya dage cicin karfinsa ya watsata gefe tayi wata kalar fad'uwa har tana gurje guiwa..........ta fashe da kuka bakinta bai mutu ba tace"Allah ya isa na mugu Azzalumi macuci.......faske mata baki yayi yana huci "don kutumar ubanki tashi kifita shigiya mayya." "Kaine maye azzalumi macuci kuma sai Allah ya sakaan mugu mashayin giya.......tana fadar haka ta rarumi jikarta ra ranta cikin na kare......shima ya rufa mata baya aguje malik shima yabisu yana son yin dariya amman halin yinta bai zoba sai yaga yar mutane ta bar unguwar sannan. Cikin sa,a tama fita taga taxi ta tareta tashiga cikin azama. Tace"maza muje karka tsaya muje muje maitama estate zamu." Shashsheka kurin take ta leko ta danna mashi dak'uwa tana mashi gwalo. Zubewa malik yayi bakin k'ofar yana kwasar dariya harda rik'e ciki,don wannan wasan yayi masifar burgesa,koba komi fiyah zata ringa saka Alfah magana ta wannan hanyar zafin ransa zairagu tun yama biyeta wataran dole zai dawo hankalinsa idan yaga tana niyyar mayar dashi cikekken mahaukaci. Huci kurin Alfa keyi yana jin bakin cikin rashin kamata da baiba kallon wulakanci yayi wa malik cike da haushi yace"kana sane kayi haka ko,don ka b'ata man rai to kayo nasara amman kasani bataci lallai ba zanso ta sake zuwa zakaga abunda zai faru,saina cire mata kafar baya alokacin zata gane ko waye ni don ubanta." Ya wuce malik yana dariya gaskiya fiyah ta mamesa baizaton haduwar farko zatayi irin wannan karfi halin ba. Tana isowa gida taji kafarta ta rik'e sai yanzu faduwar da tayi takejin ciwonta,daker ta fito daga taxi ta salamesa ta nufi gidan cikin karfin hali.........mama tafara cin karo da ita zaune tsakar gida tabuga tagumi,ga yesmin gefe tana ta kuka......dandanan taji ciwon ya b'ace ta isa garesu cikin tsananin damuwa bakinta har kerma yake tace"mamana lafiya meya faru,naganku cikin wannan yanayin....yesmin daina kuka gani sanar dani don Allah meya faru." Mama kasa tankata tayi tana share hawayenta yesmince ta iya kallonta tace cikin kuka"Adda sofiyyah babane........sai kuma ta fashe da kuka ai fiyah najin ance baba ne cikinta yayi wata irin katsawa cikin rikicewa tace"sanar dani kanwata daure ki sanar dani meya samu baban yana ina babu dai abunda ya samai ko kigaya man don Allah." Tuni itama idonta ya fara zubar da kwallah ta tashin hankali komawa tayi wajen mama dake sharen hawaye tace"haba mama kunbarni cikin duhu don Allah kusanar dani ahalin da yake ciki,don Allah xuciyata bugawa take." Mamarce ta iya cewa cike da raunin xuciya "safiyyah babanku ne aka kama yana police station,tun bayan fitarsa ashe yaa can suka kamashi,kuma sunk'i fadar ainahin abunda yayi kuma sun hana belinsa,tun shabiyu jalal yake can shida dalha amman babu magana ingantatta da sukafada,hardai korarsu sukai cewa kozasu kwana anan bazasu canza umurnin da aka basu ba." Zaman dirshan fiyah tayi tana zubar da kwallah cikin kid'ima ta riko hannun mama tace"innalillahi wa inna ilaihir raju,un mama waye yasa aka yiwa baba haka,meyayi mashi wlh mama inada yak'inin baba bazai abunda ba shine ba waye shi wane macucinne azzalumi." Cikin jan majina tace"Alh muazzam ne bansan abunda ya hadashi dashi ba,amman daman ai yana cike dashi yanada wani kudiri aransa tsawon shekaru,kullum hanya yake nema dazai wulakanta shi allah bai bashi ba sai yau tsotsai nasan komi ma yafaru wlh babanku bada niyya zai ba,saidai tsotsai da rabon wahala." Hawaye take sharewa cike da jinjina magamar mama,Alh muazzam yasa aka kama baba,kenan banu wanda ya isa yasaka asakesa idan har ba shine yaga dama.........yanzu ya zasuyi wagaresu waye zai tsaya masu dazai ceto masu mahaifi. Cikin hawaye tace"yanzu kenan mama babu wanda zai taimakemu waye zaitsaya mana mama bamuda kowa daya wuce yah jalal,shikuma ba wani abin hannune dashiba sai rufin asirin Allah......mama haka zamu zuba ido baba yayita zama can." Itama cikin halin k'unci tace"Allah shine gatanmu sofiyyah,shine zai taimakemu shizamu kaiwa kukanmu kutashi kuyi Alwallah ga magruba can anfara kira mukaiwa Allah kukanmu don Alh muazzam baida wani mak'iyi cikin unguwar nan daya wuce mahaifinku,bai shiga gonarsa ba ma ya ya iya dashi balle yashiga,muje musanar da Allah kukanmu shine zai share mana hawaye. Daidai sallamar yah jalal kenan shida dalha maitsaron shago. *kuyihkr yauda kullum ce sai Allah* Mrs bb ce Mom muhseen. I really proud of u fans Allah ya kara mana kaunar juna. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........16 Duk idonsu akan su suna jiran ganin baba ya shigo suka ka shiru,zama jalal yayi cikin damuwa dalha kuma ya dauki buta ya zuba ruwa yafita don yin Alwallar magruba. Cikin zak'uwa da sonjin halin da akeciki fiyah ta dawo gabansa ta rik'o hanunsa cikin damuwa "yaya mesuka ce kenan can baba zai kwana,yaya ya zamuyi bamuda wani matakin dauka kenan." Shima muryar sa cike da damuwa yace"me zamu iya yi sofiyyah,kawai kuyita mashi addua itace kawai mafita,munyi iyakar yinmu amman mutanem nan sun runtse idonsu akan baza su bari ma muganshi ba,Allah shine maganinsu shine kawai." Mama na gama jin haka ta wuce taje tayo alwallarta tashige d'aki shima tashin yayi yafita. Kuka yesmin da fiyah sukeyi sosai daker sukai sallar magruba,rokon Allah kau sunyisa kamar me akan Allah ya kawo masu mafita ya kuma saka ma baba. Ranar abincin kirki ma babu wanda ya iya sawa ga baki,anayin isha,i kowa ya wuce masaukinsa don ko hirat da suka saba yi bayan sallar isha,in yau babu natsuwar yinta.damuwar da suke ciki tafi karfin hirar. Bayan yesmin ta kwanta saida fiyah taga tayi bacci sannan tafiddo wayarta ta kunna,ta shiga kiran malik. Suna tare da Alfah yana mashi bayanin kudaden sa zasu fitar don yin tafiyar dasuke so,sai shan mur yake daker yake maida mashi ansa,don tundazun abun da yafaru bai wuce mashi ba,jiyake inama yasamu damar karya shegiya. Daker suka gama tattaunawar sun tsayar da lokacin tafiyar wayar malik tashiga ringing,kallon Alfah yayi yana murmushi yace"mutuniyarka ce kozaku gaisa." Wani jakin kallo ya watsa mashi ya tashi yabar falon,dariya malik yayi yana daukar wayar. "Yadai matsoraciya." Cikin halin kunci tace"yah malik inaciki tsananin tashin hankali." Cikin mamaki da rudewa yace"kina lafiya dai ko badai yaji maki mummunan ciwo ba." Cikin zubar kwallah tace"Aa ba Abdoul bane mahaifinsa ne ya kama mana babanmu,yana can caji office sun ma hana ganinsa balle aji ta bakinsa,suma kuma basuce komi ba sunce kuma bayanxu zasu sakeshi ba." Kuka take k'asa k'asa. Cikin tausayawa yace"yi hkr fiyah,daina kukan insha Allah baba zaidawo yanzu kinga dare ne kiyi bacci zuwa safe saimuyi magana.ai kinada class gobe ko." Cikin shashshekar kuka tace eh ina dashi 9:00am to 12:00am imfact sai hudu zan dawo gida kila." Yace"don't worry kisa ma xuciyarki natsuwa kiyi bacci insha Allah xantai makamaki zuwa gobe." Godiya tayi mashi yace"Abdoul dai baiji maki rauni ba ko?" Tace"targade ne amman zan gasa dasafe inshafa magani." "OK sorry Allah ya sawake muhadu goben ki kwantar ma da mama hankali babu abunda zai faru." Haka dai yayita lallashinta da tausarta sukai sallama tayo Alwallah tayi nafila sannan tayi karatun qur ani ta kwanta. Washe gari kowa sukuku daker ma yesmin tasha koko taci waina gira sannan jalal ya bata kudin taxi tatafi jarabawar ta.don ma xuwa jibi suke gamawa. Ta riga fiyah tafiya ita saida ta gama ayyukanta tanayi tana tausar mama,tana kara bata hkr da kalamai masu sanyaya zuciya har ta samu tayi kalaci don cewatai azumi tatashi dasi d'ore. Jalal da fiyah suka tilasta mata ta ajiyesa don zata sha wahala tunda batai sahur ba,ga damuwa kuma har saida fiyah ta ragewa mama ayyukan gidan,har jajjagen kayan miya tai mata ta gyara shinkafa ta dora mata ruwan zafin wanka. Albarka kawai mama ke samata don sofiyyah badai kokari ba,tana da tausayi fiyeda sauran yarata. Don saida ta makara ma don wajen tara da kusan rabi ta samu tafiya bayan ta gasa k'afarta ta shafa magani. Fuskarta yau babu walwala sosai daka kalleta kasan bata da walwala sosai,makaranta ta wuce taci sa,ar malamin baida zafi yabarta tashiga,rabida kwatar lectures din ta yau basu shigeta ba yadda ya ka mata,haka dai ta samu ta silale duk da yadda feea ke son yin magana da ita,amman ta sace ta barta don abunda ke gabanta yafi tattauna wa da feea muhimmanci. Bata ma sanar da malik cewa tana hanya ba,kawai dosar gidan tayi saida tazo bakin kofar shiga abunda ya faru jiya itada Alfah ya fad'o mata arai. Turus tayi kirjinta yana dukan tara tara,wayarta ta fiddo ta maka mashi kira tace"Allah yasa wannan tafasheshshen abokin naka baya nan,don wlh inhar yana nan baxan shigoba ya idasa karya mun k'afa." Yar dariya malik yayi yace"oh matsoraciyar kanwata to baya nan kina iya shigowa." "Aa yaya malik karkamun wayau kamar jiya." Dariyar yake yace"Allah I'm serious he is not here" Ajiyar zuciya tayi ta shiga da bismilah don bata shirya wata hayaniya dashi yanxu ba,har saita ga baba ya fito. Yana cikin main falon su akan computer yana aiki daga shi sai singlet. Kunya taji ta kamata ta d'an juya baya,murmushi yayi ya jawo rigarsa dake gefensa ya saka yace"to sarkin kunya kina iya juyowa yanzu." Idonta ak'asa ta idasa shiga falon tana yabawa da tsarinsa zama tayi kan oneseater tana kallon wani chanis films da sukeyi wata tasha. Gaisawa sukai yana jajanta mata akan abunda ya faru dasu,taji dadi sosai malik yana da kirki,kuma ya iya mu,amala da mutun kallonsa tayi tace"ina wannann mugun yake." Shafa sumarsa yayi yana idasa aikinsa kanan ya rufe computer yace"yau Alfah yaje supervision na store d'insa da company,yau ya tashi da rigima daker idan bai kori wasu ba,don ni banma san fitar sa ba saida nakira drivern sa yace suna tare." Tab'e baki tayi kurin tana wasa da yatsunta kamar ba ita ta tambayesaba.........mukullin mota ya dauko yace "zomuje akwai inda zamu yanzu,kash ko ruwa ban baki ba sorry don Allah." Tashi tayi tana smile dinta kamar yadda ta saba tace"no karka damu yaya malik banga tashan ruwa ba tukun,muje bana jin k'ishi bare yunwa." Fita sukai yaja motar suka bar gidan,wata unguwa suka nufa maidan nisa,sanan suka tsaya bakin wani get aka bude masu suka shiga,gida ya had'u sosai do fiyah irin wadannan gidajen ba bak'inta bane don duk irinsune a unguwarsu. Bai bata halin tambayar inasuka zo ba.ta bisa abaya suka shiga kofar da xata sada su da cikin gidan,duk jami ai sun kewaye gidan da alama dai babban mutunne ubangidansu. Babban falone mai kujeru royel set biyu sai k'amshi yake,zama sukai yana danna wayarsa zuwacan yakafa ga kunne yace"eh Daddy munzo muna nan main falo." Daga haka ya kashe wayar kallonta yayi cikin tsokana yace"wajen yankar kai na kawoki mai cire kan yana zuwa yanzu." Duk da ta san wasa yake hakan bai hanata jin faduwar gaba ba,yak'e tayi tace"uhm yaya malik kenan,zatonka zanyi tunanin wani abu ko?ai yardar dana maka ba raguwa bace na yarda dakai 100% don haka duk inda zaka ce muje bazan maka jayayyaba,don nasan bazaka iya salwantar da ran kanwarka ba." Kalamanta sunyi masifar faranta mashi har ya kasa cewa komi ya dora mata idanunsa yana kallonta,murmushi akan fuskarsa. Kawarda kai tayi gefe kafin suji alamun shigowa,wani kukune d'auke da tire na wasu kuloli masu kyau da plax da cups. Ajiyewa yayi yabar falon yama gaidasu still har lokacin idonsa akan fiyah,wadda takejin duk ta takure saboda kallonda malik yake mata,fitowar Daddy ya ceceta daga kallon da malik yake jefanta dashi. Duk saukowa sukai daga kan kujerar suna gaidashi.......cikin fara,a da karramawa yake ansa masu yace sukoma su zauna amman suka k'iya dole ya k'yalesu. "Abdoulmalik bakuci komi ba naga." Kansa akasa yace "Daddy nidai i'm oky wlh." "To ai ka yi serving din ta ita ko." Fiyah cikin ladabi tace"Aa daddy wlh nima na k'oshi kayi hkr." "Shikenan tunda kun k'icin abincin gidana,malik naji duk abunda ka sanar dani jiya abunda yasa nace kazo mun da yarinyar don naji ta bakinta." Malik yace"fiyah ki sanar dashi abunda ya faru yadda zai fahimta." Cikin natsuwa ta fada masa iyakar abunda tasani wanda taji bakin mama,katseta yayi cikin mamaki yace"kardai kice mun mahaifinki malam kabir El-ladan." Colin tabbatar wa tace"eh Daddy shine tun jiya yana wajensu anyi anyi su sakesa sunk'iya kuma sunk'i fadar abuda yafaru,jiya bamu samu isashshen bacciba." Jinjina kai daddy yakeyi cike da gamsuwa da kuma jimamin abun.........yace"am ya sunan ki diyata,cikin ladabi tafada masa ya ciga ba da cewa "sofiyya wannan lamarin tsohuwar gabace tsakanin mahaifinki da yayana wato Alh muazzam.zan iyacewa tun kafin a haifeku wannan gabar take,kuma har gobe yaya yana kan tsanar babanki saboda wani dalilinsa marar tushe.amman yanzu tunda dai naji haka zanyi kokarin ganin koyau ko gobe babanki ya fito,zanje na bibiyi yaya naji ko babanki ya aikata mashi wani abun,inhar bashida laifi sofiyya insha Allah babanki zai dawo gida cikin k'oshin lafiya." Godiya taringa yimasa harda kwalarta cikin tausayawa yace"kibar kuka,kinjiko ai babanki abun ataimaka masa ne don kuwa mutumen kirkine,nima ai a unguwar taku nake nasanshi yasanni tun shekarun da suka wuce,duk unguwar nan nake gaya maki kowa yasan sa da mutunci ya iya rik'e mutuncinsa,kasancewarsa mutun shidaya talaka marar karfi hakan baisa ya wulakanta kansa ba,baita zuwa kofar gidan wani wai maulaba ko bara.aa bayayi taye yake iyakar karfinsa yake hidimta ma gidansa,wannan dab'iar ce taja masa bak'in jini cikin unguwar,don su ganinsu tunda baida shi dole yazo ya durkusa masu yana masu maula su bashi awulakance yana masu godiya,shikuma yak'i hakan shiyasa kowa yakejin haushinsa baya sonsa amman hakan baisa ya yi abunda suke so ba,nai maki alkawarin malam kabir zaidawo gida kinjiko diyata,ai babanki nawane zanyi iyakar kokarina kuje Abdoulmalik,ka kara bata baki kajiko.anshi wannan ki kaiwa maman ki kice inji Alh mawalle." Kudine ya bata rafar yan dubu guda daya hawaye take sharewa tana girgiza kai tace"aa daddy fad'a zatayi mun yaya jalal kuma zai dakeni." Jinjina kai yayi yace"Allah yayi maki albarka zanzo gidan da kaina karki sanar danita kinzo nan." Har bakin mota ya rakasu saida fiyah tashiga sannan malik ya kewa daddy bayanin kokarin fiyah akan Alfah,kuma za,adace insha Allah shikanshi daddy yaji dadin bayanin yace mashi"to don Allah malik ku rik'e amana karka bari wani abu ya sameta,tunda iyayenta babu wanda yasani,muddin sukaji babanta ko kofar gida bazai barta tasake fita ba,ya gwammace tabar zuwa makarantar,don haka kazama mai kulawa Allah yabada sa,a still har yanzu inkuna bukatar taimakona kuna iya nemana zanyi iyakar yina akanku." Ahaka sukai sallama malik yatada motar suka fita. Nasiha yake mata dabkalami mai dadi da kwantar da hankali,yana sakowa da tsokana da ban dariya har yasamu ta sake yace"gida zan kaiki ko makaranta." Cikin sanyin murya tace"ban gama lectures ba school zaka kaini." Tafiyar so silent har suka isa makarantar,yace"mubar komi sai baba ya samu fitowa fiyah,don munfi samun natsuwa." Tana cikin motar bata kai ga fitowa ba tace"inason information akan zakiya da inda zan sameta,karka damu yaya malik hankalina ya kwanta daba yanin Daddy zamu iya cigaba da kokarin mu kafin lokaci ya kure mana zan shiga aji kamun sending komi ta waya,ngd sosai ka isa gida lfya........harta saka kafarta guda waje yace"bakiji ba." Juyowa tayi ya sakar mata lallausan murmushi mai sanyaya xuciya,gabanta yafad'i tayi saurin ficewa tana rufe k'ofar.ko waigowa bata yi ba har saida taji yabar wajen ajiyar xuciya tayi ta shige aji. Bayan sunfito wajen karfe hudu harda rabi feea ta rugo ta rik'e hijab din fiyah tace"washh Allahna naka maki,kinban wuya yau wlh kinga irin neman da nayi maki makarantar nan,ina kika shiga haka." Ajiyar xuciya fiyah tayi tana cewa"sakeni tundaba sata nai maki ba." Dariya tayi tace"waceni nace kinman sata kawai dai inada magana dake,mushiga mota ko mu gama tattaunawar sanan mutai." Kallonta take cike da tuhuma kafin tace"wlh nagaji gida nakeson naje mezai hana mubari idan munje gida saiki tambayi mominki kizo gidanmu." Jinjina kai tayi tace "shikenan muje to yau bazan bari kihau tax ba." Murmushi fiyah tayi tana wucewa gaba kawai hakanan taji tun batasan me feea zata gaya mata ba taji kirjinta yan bugawa,har sukaje gida daker take maida ma feea ansar labarin datake bata. Mrs bb ce. Mom muhseen. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........18. Parking tayi wajen da suka saba ajiye motar suka fito kowace rataye da jikarta,fuskar fiyah tayi fresh bata saka komi ba yau bayan cream din da take shafa wa,saboda duk bata cikin sukuni. Class din babu kowa na su fiyah sai wani namiji daketa karatu shikadai,sallama tayi mashi tace"ina y'an ajinne." Yace"ashe tunjiya malamin yakira classrame yafada masa bazai xo ba ya samar da mu,to mafarin kenan duk wasu basu shigo ba sai anjima." Jinjina kai tayi tafita feea ta hango tana nufo department dinsu,ajiya tana ta d'okin jin abunda feea zata gaya mata,amman ayau saita samu kanta da rashin son jin koma miye takeson sanar da ita,don kawai taji aranta abun azai mata wani dadi ba. "Kuma babu kowa ajinko?inajin sun canza time din lecture din muje can muzauna." Cewar rafeatu fiyah bata mata musu ba ta jera da ita suka nufi wani block suka zauna,shiru shiru babu mai cewa komi fea tace "niban tambayeki ba,daman kinyi waya baki gaya man ba." Murmushi fiyah tayi ta mik'a mata wayar cikin sanyin murya tace"kinganta uncle yahya ne ya siyamun bata wuce 2 week ba fah." Jinjina kai feea tayi tace"tayi kyau wlh,Kingode." Daga haka suka sake daukar wani shirun,fiyah nata nazartar ta ta lura akwai magana bakinta,amman tana shayin fada kokuma don bata san ansar da za,abata bane.kawar da shirun fiyah tayi da cewa"ina maganar da mukai dake zaki sanar dani." Ajiyar xuciya feea tayi tana kallon fiyah dandanan fuskarta ta canza,ta koma kalar tausayi cikin rauni tace. "Fiyah,banda wata qawa data wuce mun ke wadda zamuyi magana mu kashe murufe tare,kece kadai zan ita sanar da damuwata kiban shawara kuma kitai makeni batare da wani yaji ba." Kirjin fiyah yabuga tace"inajinki Allah yasa lafiya.?" Girgiza kai tayi idonta ya cicciko da ruwa take cewa" *SOFIYYAH*,Ina cikin damuwa wlh na farko dai abunda yafi tada man hankali shine Abbana zaiyi aure kuma yarinyar da zai aura class mate d'ina ce,wallahi munyi primary da secondary duk tare,kuma d same class.sannan wlh bata da kunya ta raina kowa idan Abba yayi haka munshiga uku,momi zuciyarta bugawa zatai duk tsawon shekarun nan baitashi auren ba sai yanxu kuma yarinya karama diyar cikinsa,saar diyarsa wlh tunda aka fara maganar momi bata da kwanciyar hankali kullin tana cikin damuwa hat jininta yahau.tace ita ba auren take mawa ba wlh ya aure koma wacece amman banda sa,ar yarta yaje ya nemo babba wadda zata iya zaman kishi da ita ba diyar cikinta ba.amman Abba yaruntse ido yace bazai fasa ba duk ubanda yaji bazai iya zama da shiba yafita.in takaice maki jiya nakoma gida momi ta tafi zaria gidansu." Hawaye suka zubo mata tana sharewa cikin kuka ta cigaba da cewa, "Bayan wannan sai abunda ya hana xuciyata samun natsuwa,bana bacci mai dadi banda wani aiki sai tunani,zuciyata banda azalzalara da take babu abunda takeyi,har ciwo take mun wlh safiyyah bana iya cin abinci saboda halin da nake ciki." Cikin tausayawa take kallonta har idonta ya cika tab da kwallah tace mata"menene kuma bayan matsalar su Abba. Share kwallar tayi ta d'ago tana kallon fiyah cikin karyewar murya tace "ina sonsa, fiyah soyayyarsace ta ke hanani cin abinci take hanani bacci,ta kuma sani kukan da ba abigeni ba." Kallon mamaki da al,ajabi take mata bakinta har rawa yake. Tace"way...e......waye shi......in..a yake kuma." Sadda kai tayi tace" *ABDOULNASSER ALFAH*" Duka idonta ta fiddo tana kallon rafea kirjinta taji yayi wata irin ansawa,daker numfashinta yake fitowa yana komawa,maganar tayi masifar dukanta bakinta har wani k'afewa yayi saboda iskar data cikashi don abude tabarshi.........kanta taji ya sara xuciyarta tace"duk wannan rudanin na miye,inhar ba kina jin wani abu akansa ba." Cikin abunda baifi minty biyu ba ta koma yadda take,amman still kirjinta bugwa yake tayi kokarin daidaita muryarta takalli rafea data sadda kai tana hawaye,matsowa tayi tana rik'e da hannunta cikin tausayawa tace"rafeea,Abdoul kikeso? Alfah zuciyarki ta kamu da son sa?gaskiya bazan b'oye maki ba banji dadi ba,ko kadan banji dadin maganar ba meyasa zaki bari xuciyarki ta kamu da son wanda aduniya baida abun tsana sama da mace,idan yaganta jiyake uwa ya kasheta.bansan taya zan lallashi xuciyarki ba gaskiya don datayi shawara dani da bakamu da son sa ba.amman yanzu kinyi nisa bakijin kira." D'agowa tayi tana kallon fiyah cikin dishewar murya tace"dake na dogara,dake na laru don ke nakeson ki shigemun wajen wannan aikin,fiyah zaki iya inba keba babu wanda zanje na dorama wannan nauyin." Mik'ewa fiyah tayi cike da b'acin rai tace"oh ni dayake ban son ciwon kaina ba!zanje na samu namiji irin Abdoulnasser nayi maki feating love dinki,karshe duk zuciyarsa dayakeji da ita yajuye bisa na ya illatani yayiwa iyayena sara,koda yake ai su ba masu hannu da shuni bane basu san ciwon y'arsu ba." Ta juya tabarta nan wajen,aguje fea ta isa wajenta tasha gabanta tashare wayenta tace"karkimun mummunan fassara fiyah,niba nufina kenan ba kema kuma kinsan bazan iya maki wannan gorinba,inda dalilin daya sa nace haka." Wani kallo fiyah ta watsa mata tace"dalili,! wane irin daliline zaisa kice inje ga wannan mahaukacin ince masa kina sonsa injawo ra,ayinsa akanki haba rafea kinmun adalci kuwam." Jawota tayi suka zauna tace"abun da yasa nace haka fiyah tsawon lokacin da kika dauka kina hidden abubuwanki,nikuma na ringa binki abaya ina guiding dinki,har gidan dakike zuwa nasani har abokin Alfah da yake d'an kawoki makaramta ina sani,abunda kawai ban sani ba shine mekike zuwa yi gidan? meke tsakaninki da wannan abokin Alfah?din wata zuciyar ta cemun soyayya kuke kuma Abdoul zai sani kuma dagani kuna gaisawar mutunci." Idon fiyah ya rine da masifa fizge hannunta tayi dake cikin na rafeea tace"watau saboda tsabar munafurci bibiyata kikeyi ko rafeea?har xuciyarki take gaya maki wani banzan tunani ko,to inso kike kisan menake zuwa yi zangaya maki tun kafin sakarar zuciyarki ta kuma gaya maki ina bin maza.......yadda fiyah ke daga murya yasa feaa ta rufe mata baki,ita kuma cikin fushi ta fizge tace "barmi na gaya maki abunda nake ciki tunkan kije gidanmu kice ina bin maza,naga makauniyar soyayyarki ta rufe maki ido komi ma zaki iya........banda wata alaka ta soyayya tsakanina da malik abunda ya hadani dashi kuma aikin ladane,tun ranar da wannan abun yafaru da abbanki yasa aka rufe Alfah police washe gari na yanke shawar zuwa muyi magama da malik akan jin mafarin llacewar abokinsa. Fiyah ta juye mata halin da ake ciki na kokarin ganin sun dawo da Alfah cikin hayyacinsa. "Don haka ni babu wata alaka bayan wannan tsakanina da malik,ni babu wani namiji da zan gani inji ina sonsa,kuma taimakon da nayi niyya insha Allah zanyi sai inda karfina ya kare,ina sanar dake cewar haryanxu ban samu zarrar tunkarar Alfah da wata magana ba sai rannan shima kuma Allah kadai ya ceceni kiris ya rage bai karyani ba,saboda ganina dayayi gidansa.to inga inje ince masa wai wannan da kukai rigima bisa titi tace tana sonka ai wlh ranar ba bakina zai fasa ba idanuna tas zai tsoyayar dasu don ba imani ne dashi ba,shida mahaukaci banbancin kadanne. Idan kinji zaki iya tunkararsa wlh zan maki rakiya har k'ofar gidan,shima kuma dana kaiki zanyi kwana.inkindawo da kafarki kintsira.don naga baida abun sha,awa sai karya kafafun jama,a kome sukai mashi oho" Jin abunda fiyah kesanar da ita yasa gabaki daya taji jikinta yayi la,asar to wannan wace irin xuciyace Allah yayi masa,bai daukar komi easy Fiyah tace"zanje inshiga aji ga malam can yazo,tajuya tabar feea nan zaune tana tunani. 💞💞💞💞💞💞💞💞 Yau Abdoul zai yi tafiya zuwa Australia,zasu yi ani meeting daabokn kawancinsa na kwana biyar,sanan zaibiya ya bada oder kayanshi akawo ashi har nan abuja. Kayan sa malik yake had'a mashi shikuma yana kan computer,yaudai fuskar akwai sassaucin rahma ba kamar lokutan baya ba......shiyasa malik ya ma fiyah text inta taso ta biyo ta gidan yana son ganinta. Tun ranar da tayi masa gorin shan giya bai sake ganin yasha ba,saidai in ya fita don yazu dakin sa bedroom dinsa yake ajiyewa cikin frig dinsa. Babu riga jikinsa duk halittar da Allah yayi mashi ta bayyana,daka kallai kasan mutunne mai motsa jikinsa always. Yana da baiwar galgasa irin kwantacciyar nan maibin jiki,kirjinsa ma haka da kafafunsa amman ta kirjin saika rantse salon yake mata(🤭lol),har wani shalk'i take tana walk'iya. Haka gashinsa na kansa dana fuskarsa,yanada saje wanda yake had'e da gemunsa,kasancewar irin gashin nan na fulani garai kamar na larabawa,sai yasake hasaka fuskar sa idan yagyarasa kyau yake sosai. Baidamu da manyan kaya ba koda can daya na gida sai idan wani daurin aure zaije kozai raka Abbi wajen manyanmutane,sanan yasaka amman shi yafison kanana don kayansa mostly inyaje waje yake shigowa dasu,ko in malik zaije yabashi sakon da combus kala kala haka yake sawa kuma suna hawan kayan sa suna masifar yi masa kyau, Malik ya gama hada mashi akwati guda said yar traveling bag dinsa da ake rataya wa ga hannu guda. Kallonsa yayi cikin tsokananyace "yallabai na gama saura wankan." Cikin mamaki da al,ajabi yaga ya d'ago yana mashi wani irin smile wanda tunda suka baro gida malik bai samu wannan damar ba ga Alfah..........cikin jin dadi ya iso garesa yace"don Allah sake maimaita wa wlh kabaji yadda naji wani sanyi cikin raina ba,Abdoul inda kasan yadda murmushi yake haskaka fuskarka da baza ka so ka daina ba." Rufe systems din yayi yana nufar bayi baice masa komi basaida yakai kofar shiga yajuyo yace"fuskarce banso tayi haske,don baida wani anfani akanta muddin haske ya bayyana akanta mata zasuyi kokarin kawo kansu gareni nikuma bana sonsu,nafi kaunar mutuwata akansu." Yana gama fadar haka ya shige yabar malik da rik'e hab'a,tabbas da ace Alfah yana k'wata fuskarsa da murmushi da fara,a y'anmatan da zasu biyosa basuda iyaka,amma hakan ba hujja bace. Fita yayi zuwa main falonsu yana jiran isowar fiyah yana son su had'u da Alfah kafin ya wuce. Karfe uku yau suka tashi ko alamar jiran feea batai ba don tana cike da jin haushinta,tama rasa wanda zatace tana so sai wannan gantalellen mahaukacin,mts aka taringa jera tsaki ta fito daga makarantar,kirane yashigo mata mama ta gani saurin dauka tayi tace"Assalamu alaikum mama lafiya ko." Cikin farin ciki taji mamar tayi magana cewa"daman ince maki babanku ya dawo babu jimawa." Itama cikin farinciki tace"dagaske mama?wayyo mungode Allah mungode ma Alha ganinan zandawo insha Allah." Kashewa tayi sai lokacin taga sakon malik na biyu ayau din nan. _fatan lectures sunyi dadi,inba damuwa kisaman gida yanzu pls._ Tarar taxi tayi ta gaya mai unguwar dazaikaita suka tai. KOfar gidan ya sauketa tayi addua sannan tashiga......compound din gidan banu kowa inda suka saba zama bata ganshiba tayi shahadar nufar main falonsu kirjinta yana amsa wa,amman ta saka dakiya da natsuwa kadan aranta ta shiga. Yana tsaye wajen taga yana shan win din sa ga wayarsa yana danna wa,malik kuma yana cikin daki baikai ga fitowa bah.tunda tayi sallama ta shiga ta hangoshi can tsaye kirjinta ya tsanan ta bugawa,zama tayi tana karanta duk adduar da tazo bakinta. Juyowa yayi bai sauke idonsa ko ina ba sai inda take zaune kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi haka tayi. Shan mur tayi ta kauda kai kamar bata ganshi ba,nan kuwa kamar ta saki zawo taji,ganin dagaske wajenta yayo tsoro yasa takasa cigaba da zaman ta mik'e cike da dakiya tana ja baya fuskarta aya mutse idonta a kan cup d'in hannun sa.tai saurin toshe bakinta da hancinta har saida ta dangane da bango sannan ta tsaya,babu sassauci kokadan ga fuskarsa daf da ita yatsaya idonsa tar akan fuskarta,farare tas said shining suke kamar anzuba mangyada aciki.banda daddad'en k'amshinsa da yake nusar hancinta bata jin komi amman saboda ta k'ular dashi yasa ta ringa kauda kai tana yamutsa fuska.hannu tasa tana dakatar dashi da had'e duk kusancinsu cikin yar muryarta tace"dallah malam miye haka,matsa kaban waje nace kamatsa,kar namaka amai ga jiki nibada shan giya ba nida warinta." Duk cikin kalamanta babu abunda yake b'ata masa rai irin tace yana warin giya.shak'o wuyanta yayi yana huci iyakar karfinsa bayan ya hade hannayenta baya yasake matseta ga bangon. cup dinner giyar yake k'okarin kaiwa bakinta ta guntseshi ga shida ker take nishi idonta duk sun yo wake sun fara canza kala,cikin dakakkar murya yace. "Naga alamar kwa'ayinta kike ko,to sha inbaki shata ba saina fiddo mak'ogwaronki shegiya yar iska maibiyo maza gidajensu,ke akaruwancin nakin ma marar aji kikeyi banza gantalalla.ai tsirara zakiyi yawo asan cewar kedin yar tasha ce." Duk yadda ya shak'eta da yadda ya murd'e mata Hannu duk bataji zafinsu kamar yadda kalamansa suka tsaya mata garai suke sukarta ga rai.jitai wasu kwallah zasu zubo mata tai saurin maidasu.....afusace yayi watsi da ita bakin k'ofa kadan yarage batabfad'a bisa hannunta ba fitowar malik kenan aguje ya iso wajenta yana sallallami "Wai Alfah baka da hankaline?wajen ka tazo ne?banson rashin tausayi." Hannu ya mikabmata ta kama amman ta k'iya ta dafa bango tana mik'ewa daker,cikin zuciya Alfah yace "muddin bata bar zuwa gidan nan ba wlh watarana ferfesun ta zanyi incinye,wawuya kawai ya watso mata sauran win din dake cikin cup din hannunsa,ga fuska......runtse ido tayi tana jin wani k'ullutun bak'in ciki yana d'awainiya da ita........kadan yarage bata fashe da kuka ba amman saboda gudun karyaga wallanta tasake maxewa.....ciki muryarta dake rawa tace"macucu azzalumi mak'etaci baka san komi ba sai zallar cuta da shaye shaye,taya zakaji feeeling din tausayi cikin ranka ai bana tantama inkace zakai kisa don kuwa y'an shaye shaye kamar ka abu abunda ba sayi,wannan la,anannanr giyar babu abunda bata sawa. wani saboda ita har uwarsa yake yiwa fyad'e." Innalillahi zo kaga tashin hankali wajen Alfah gabaki d'aya fuskarnan ta koma jajir don bala,i Idonsa kamar anrura garwashi. Ganin haka da tayi tajawo jikkarta takalminta ga hannu ta ranta cikin nakare,shima kamar wani mahaukacin gaske yabita yana haki baida burin daya wuce ya kamata burinshi ya danne wuyar shegiya,ya tabbatar mata da cewar yes zai iya kashetan don ubanta. Malik ma ya rufa mashi baya don hankalinsa ya tashi muddin Alfah ya kama Fiyah wlh komi zai iya aikata mata,baiwar Allah fiyah tana gudu tana faduwa tana tashi,duk ta guggurje k'afafu.data waiga taganshi sai tasake runtumawa har Allah yasa ta fice bata tsaya jiran taxi ba ta yanki titi saida taga tabacewa ganinsa.......... Mrs Bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........17 Har k'ofar gida ta sauke ta yah jalal da wani abokinsa sai d'alha duk suna bakin shagon kofar gidanmu zaune,sukuku haka na nufo gida gaidasu nai na wuce cikin gidan........tun a soro na jiyo muryar Anty jamila nasan itace tazo,kowa ya sanar da ita da wannan tsohon cikin haihuwa yau ko gobe. Sallama nai ina idasa shiga suna cikin inuwa zaune har lokacin dai fuskokinsu babu wata walwala sosai. Sannu mama take mun itada yesmin dake duba littafinta,zamewa nai kusa da anty ina mata sannu da xuwa. "Kamar wadda tadawo k'asa fiyah." Murmushi tad'anyi tace"wlh yau ban samu nasaka komi cikina ba har nadawo yunwace keta cina nan dakika ganni." Cikin mamaki mama tace"au dasafe dana ce kin karya me kikace mun safiyyah." Yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka tace"mama wlh bakina ne babu d'and'ano." Cikin fad'a mama tace"in haka ne kowa ma aida baici na,kimaida hankali wannan ulcer banzar tatashi wlh zaki gane kurenki,maza tashi ga abinci can kije ki zuba kina girma kina kara rashin wayau." Daker ta mik'e ta wuce d'aki ta zube kan gadonsu tana sauke numfashi.saida ta huta sannan ta shige wanka tafi minty talatin tana wanka sannan ta fito. Duk kayan fiyah dogayen rigunane siket basu wuce biyar ba.tayi shafa sannan taje tasa abincin ta dawo tsakar gidan suna ci gaba da hirar,mostly duk akan rufe baba ne da akai,saida nai rabin abincin nace"mama an samu wata nasara ne akan abun,yaushe zasu sakesa." Tab'e baki tayi tana cewa"wace nasara kuma safiyyah,?nan yayanku ya sake komawa station din da duka suka rufesa cewa inyasake xuwa zasu hada dashi,wannan masifa dame tai kama nidai gaskiya nagaji wlh nagaji,shekara ashirin ana fama da abu guda nidai inhar yadawo to tashi nan unguwar yazama dole,ina dalili ina d'an mafari mutumen nan inba gani yayi munbar masa unguwar ba bazai shafa mana lafiya ba wlh haba." Anty jamila tace"Aa mama wlh babu inda zaku aiba filin ubansa bane balle na uwarsa,dayake son ganin dole saikun tashi duk bakincikin sa wlh nan gidan yafi karfinsa.munafuki annamimi don dai uncle bai gari wlh da tuni baba yadawo,idan ta k'amarsa yana da kud'i ai bashi kadai Allah ya bawa ba,akwai wad'anda suka fisa." Mama tace"Gara da baya nan jamila banson maganar tafita har takai ga wataran aimaki gori duk da bana fata,kuma dangin mijinki basu da wannan amman abun gudun shine yauda gobe." Haka suka cigaba da hirar fiyah na jinsu ta kasa cigaba da tsoma baki............bayan sallar magruba driver anty yazo yadauketa suka tai gida. Ina daki ina ta duba handout dina,naga sakon malik a wayata. Na jima ina kallon text din kafin naduba abunda yace. _FATAN MA,ABOCIYAR MURMUSHI DA FARA,A TA ISO GIDA LFY,ZANSO YAU TA KARE FARINCKI NA LULLUB'E DA XUCIYARKI KI KWANA LFY MUTUMENKI YANA GAIDAKI._ ta jima tana bin rubutun da kallo me yake nufi kuma oho abunda take fada kenan cikinn xuciyarta.......balaifi sakon ya yi mata dad'i amman bata mayar masa da ansa ba,karatunta take yesmin kuma tana can tare da mama dakinta.yah jalal ne ya shigo yana ma mama magana tayi bak'o yana son magana da ita,kasa kunne nayi sosai don nasan bai wuce daddy ba shine mukai dashi zaizo. Saigashi kuma shid'inne ban fito ba inaji suna magana yana bata hkr,kuma ya je yasamu yayansa watau Alh muazzam na shawo kansa zuwa anjima ko gobe za asakesa.ashe yar hatsaniya ce tahad'asu,shi yaya yazo fita daga unguwar shikuma malam yazo shigowa shida mai taxi,sai mai taxi din ya banki motar yaya,to daman mai neman kukane aka jefa da kashin awaki nanfa yaringa yiwa malam rashin kirki har malam shima ya gaza hkr yashiga rama wa shine fa ya kira yan sanda suka tai dashi.....aman komi ya warware malam yana nan dawowa insha Allah,yanzu can zan nufa. Godiya mama tayi tare saka masa albarka yace"haba ba komi ai malam namune sai inda karfinmmu yakare,Allah ya kiyaye gaba ga wannan asaima yara wani abu,ya jiye mata kudin da yaba fiyah bata ansa ba. Har mota yaya jalal ya raka shi har yake tambayar dama yana nan,yace ai yazo hutune yana kaduna yana aiki....sundan tattauna sannan ya wuce gidansa ake cikin estate din. Fitowa nai na samu su mama suna yabonsa don sunce tun zuwan su unguwar shine na farkon daya fara masu mutunci,bacin shi babu mai kallonsu da kima. Anan mama take basu labarin abunda yafaru tsawon shekarunan dayasa Alh muazzam basa shiri shida malam kabir. "Abun ya farune lokacin duk watan mu guda da aure nida mahaifinku,sai babansu ya rasu kasancewar da abuja bata kai haka ba don nan wurin idan kun ganshi shekarun baya zakuce wani sansanine. Gidajen ake wajen basu fi bakwai ba,kuma ba wasu gidaje ne na azo agani ba,mahaifinku shikadai ne ga mahaifiyarsa sai yan uba su uku duk maza,Allah yayiwa mahaifinsa arziki alokacin daidai misali,kuma yabar kadara mai yawa yabar gidaje biyu yabar gidan gona daya da filaye.wannan gidan yana daya daga cikin filin mahaifinsa,kuma shikadaine mahaifinku ya samu sauran du yan uwansa sunyi sama da fad'i da dukiyar,kasanewar gidan haya muke lokacin kuma samun kudin hayar yana wahala,sai malam ya yanke hukuncin zowa nan ya gina mucigaba da xama. Kwatsam daya fara zuwa da yan aiki wurin sai sukaci karo da Alh muazzam,lokacin ana mashi nashi sabon ginin dake amman ba wannan dayake ciki ba,sunda ga can baya na hayane yanzu. Kamar gaske suka fara gaisawa da malam,har wataran idan yazo aiki yakance yazo suci abinci ahaka har sukadan saba,rannan suna hira yace masa ni kuwa malam wata shawara nazo da ita,inason filin nan naka tun randa na ganka anfara aikin nan naji sha,awar wajen ta zomun inson yin wani gini awajen,kasiyar mun nikuma konawa kaimashi kudi za siya.lokacima baikai wanan matakin ba dayake kai. Kaitsaye babanku yace bayarda ba shibadan yasiyar ya mallaka ba,don haka yayi hkr shi ginawa zai yazauna,shine abu guda daya dayake tunawa da mahaifinsa don haka yayi hrk. Wannan magana ta b'atawa muazzam rai ainun baitanka mashi ba daga ranar ya canza wa babanku,bai mashi magana duk yasa mutanen unguwar suka tsanesa,wai shiba kowan kowa ba amman yazo unguwar masu hannu da shuni zaiyyi wani tsugunnennen gida,aikuwa zaka zama shaniyar ware don babu maiyin hud'd'a dakai kana fak'iri.Alh muazzam yake sanar da babanku haka alokacin saida sukai rigima saida babanku yayi wata uku daure agidan yari,sannan aka sakoshi. Sadda zai dawo yasamu an rushe mashi ginin daya fara tas sai filin wajen........munshiga tshin hankali ba karami ba,karshe ya shigar da kararsa kasancewar yana da lawyer kuma Allah ya tsaya mashi sai alkali ya ansar mashi hakkinsa,cewa Alh muazzam saiya biya tarar dubu dari takwas ga babanku.amman wlh har yau har gobe bai bashi ba,ba kuma don baidashi ba aa k'etace don yaga yadda zaiyyi yayi wani ginin,babanku bai sake bi takanshi ba tunda yasamu anyi masu tsakani,ya cigaba da hidimar gininsa yasha bak'ar wuya kafin ya yi gidan nan,duk yan kudadensa dayake samu na albashi nan yake zuba su mahaifiyarsa tana taimakonsa daga can wani kyauye dake jahar katsina waishi dutsi,bayan mutuwar mijinta ta koma wajen danginta.........cikin ikon Allah gida ya kammala don har na haifi Abdouljalal lokacin ina wankansa muka dawo nan unguwar,munsha wulakanci babu mai kulamu kowa kallon kaskanci yake mana,ahankali kuma unguwar tafara cika suna gidaje na nuna ma sa,a gasunan gidajen kamar baza mutu ba......ahaka mukaita rayuwa Alh muazzam kullum cikkn neman rigima da mahaifinku yake,shikuma yaki biyewa kunji dalilin wannan gaba nan unguwar duk sunbi bayansa basa mutuntamu.matar Alh kwangila ce kawai hajiya Asiya take huddar arxiki dani shima aboye mijinta baisani ba har gobe,saifa wannan maigidan da yazo daga katsina babu laifi suna gaisawa da malam kuma matarsa tana shigowa don ma basu fiye zama garin sosai ba zuwa suke sutai. To saifa kanensa Alh matawalle daya zo yanzu don shi sunfi ma shiri da babanku sosai da sosai" Yanzu shekara nawa babu wata fitina tsakaninsu sai wannan karon ashe bai manta ba ya aikata mashi haka,don haka basai na ja kunnenku ba babuku babu hudda da yaransa,kai koda wasa karnaji labarin ganinku tare dasu balle ace kun shiga gidan. Gashinan dayake Allah ba azzalumin sarki bane d'an cikinsa yayi zina da matarsa uwar gidansa,sannan yayi lalata da agolarta,wannan kadai ya ishesa ishara." Kirjin fiyah yaba da ras jin kalamin mama na karshe,dagowa tai tana kallonta maganar batai mata dadi ba har cikin k'ok'on ranta bataji dadin yadda ta fadi magana marar dadi akan Alfah ba,bacin ba haka abun yake ba. Kasa jurewa tayi tace"mama bafa haka akai ba sharrine aka masa." Duk kallonta suke cike da mamakin maganarta ba kamar yaya jalal kamar ya kai mata duka yace"don ubanki ke ina kika sansa ma da kike karesa." B'ata fuska tayi tace"nifa yaya ba karesa nai ba,kawai dai abunda naji ana fada kenan." Mama cikin fad'a tace"koma dai miye bbu ruwanki dasu miye naki inma gaskene inma ba gaske bae ba,kifita idona akan wannan maganar kuna iya tashi na gama magana." Ranar da maganar nan fiyah ta kwana kamar tayi kuka har cikin ranta bataji dadin maganar ba,kuma wannan matsalar ba zata sata ta fasa abunda tayi niyya ba,insha Allah sai inda karfinta yakare akan Alfah sai mutane sun dawo tausaya masa suna yabonsa,badai tsinuwa ba saboda tausayinsa har kuka tayi ranar daker bacci ya sace ta. Tana mamakin rashin zuwan feea kila mominsu bata barta ba,sun had'u school gobe taji maganar me take son fada mata. 💞💞💞💞💞💞💞💞 Alfah haduwar sa da fiyah ta zame masa damuwa,don babu wanda yafada masa magana datayi mugun tsaya masa kamar ta tun bayan barinsa gidansu,ya kwana ya yini da bakinciki shiyasa dayaje company yayi tijararsa yadda yakeso kuma ya kori duk wanda yakama da laifi,haka store dinsa duk abunda yaga ba daidai ba yi yake kamar zai cinye ka d'anye,kan yadawo gida saida ya kori mutun uku ba kuma maganar dawowa. Allah Allah yake yadawo yasameta don yaci burin muddin suka sake haduwa saiya zubar mata da hakora,daga lokacin zata san waye shi bata san shi rayuwarsa yanzu da yaga mace kusada shi gara ya kwana baici komi ba. (😂yo Abdoul ai cikin ka kaima wa nidai in na cika tunbina ai lfy lau lol🤭) Washe gari tun takwas saiga feea ta biyowa fiyah,itace ma taringa taya fiya aikinta da takeyi,tana mamakin feea yarinyar da agidansu banda taci ta kwanta bata san komi ba,saigashi itace dayin shara harda yi mata d'aurayar wanke wanke. Yau tea sukasha da indomi har da kwai sai soyayyen dankalin hausa......sosai feea taci kalacin don ita ata ma tab'acin dankalin hausa ba,su mama nata mata dariya yesmin yau ake exam din karshe sai murna tae tace kafin ta dawo kowa ya ajiye mata gift dinta.Tare suka tai saida suka ajiye yasmin sannan suka isa makaranta. Suna kan hanya text din malik yashigo wayarta dubawa tayi da murmushi akan fuskarta . _INA FATAN MA,ABOCIYAR MURMUSHI TA TASHI LFY,I KNOW U ON UR WAY TO SCHOOL,ALLAH YA BADA SA,A IDAN KIN DAWO I WANT SEE._ Kallonta feea tayi tace"duk da ban sani ba kuma baki gaya man ba da alama dai fiyah tayi sabon kamu,kinsan kuwa maganar mu tana da nasaba da haka zanso nima kimun wannan hanyar." Kallon waje fiyah take tana sauraren kalamanta tana komarin dorasu bisa ma,auni amman iyakar tunaninta tagaza hasaso komi. *aradu nagaji sorry mu hafu gobe* Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* *INA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA WANNAN LABARIN DA KUKA NISHAD'ANTU DASHI WATAU _ABIN CIKIN RUHINA_ TO KU MATSO KUJI GA WANI SABON SALON KONACE SABUWAR TAFIYA,KONACE TAKU NA BIYU ACIKIN WANNAN LABARIN WATAU CIGABAN ABIN CIKIN RUHINA MAI TAKEN _SANYIN IDANIYA_ SABODA IRIN KAUNAR DANAKE MAKU YASA BAZANSO WANNAN DAMAR TA WUCE KU BA,DON KUWA WANNAN KARON SAI KUNCE KHAIRAT DA AREEF BASU IYA KOMAI BA.DAURE KI FIDDA NAIRARKI DARI 200 KACAL DOMIN MALLAKAR NAKI,KUNSANI MOM MUHSEEN BATA LITTAFIN BANZA.INA KASA KUNNE DON SAURARENKU.* 🅿️..........19 Wani lungu ta samu ta shige tana haki,kirjinta d'agawa kurin yake saboda tention.silalewa tayi k'asa ta fashe da kuka kalamansa suna sake dawo mata ras ga kunne,babu abunda yayi bala,in kuntata mata zuciya irin yadda yakirara karuwa tana biyo maza har gida..........cikin kuka tace"Allah kana gani niba haka nake ba,wlh niba yar iska bace kaga zuciyata kaga abunda ke cikinta,kasan niyyata ban fara wannan aikin don kusanta kaina da malik balle shi,hasalima banda abunda nake k'yama kamarsa.Allah kasani bana kaunarsa wannan kalamin ya sake jefaman k'insa,natsani kalamr karuwa balle a alak'anta ni da ita,kaida Allah Nasser wlh sai Allah yasaka man.bazan yafe maka ba.......kuka take iyakar karfinta tana kallon yadda guyawunta duk suka guggurje,banda zafi da rad'ad'i babu abunda suke mata,wani hamami da ya nusar mata hanci shine ya tuna mata da giyar daya antaya mata ga fuska,runtse ido tayi tana jin zafin hakan har cikin ranta. Hawaye suka sake b'alle mata "d'an iska matsiyaci wlh Allah ya isana." Tashi tayi tana d'an gasa k'afar ta fito titi,wani shop ta gani ta gangara taje ta siyo ruwa ta wanke fuskarta tas,amman har lokacin tanajin warin giyar yana nusarta,har wani tashin zuciya takeji. Daker da taimakon mai wajen ta samu abun hawa,ganin yadda take bukatar taimako shiyasa yaga yadace ya taimaketa. Tana sauka tayi kokarin daidaita kanta amman ta kasa,ciwo raunikan suke mata duk ta tattare rigarta sama.d'alha ke mata magana bata tsaya saurarensa ba ta shiga gidan tana kuka..........gabaki daya suka yo kanta da tambayar lafiya,yesmin na ganin halin da take ciki ta rushe da kuka tana cewa. "Mama Adda taji ciwo zokigani wlh kafafunta duk sun gurje." Mama dake cikin kitchen tana shirya ma baba abincin dare ta fito da sauri jalal dake saka takalman kwallo yace"garin yaya haka fiyah." Kukan take tana jin inama ta sanar dashi abunda yafaru,amman tasan itace aciki inta sake wani yaji wannan labarin. "Yaya motar muce ta kife wani mai mashinne ya shigar mana gaba,yawancin sauran y'an cikin motar suna asibiti ganin ni ban jigata sosai ba yasa nace ni akawoni gida." Salati duk suke suna jajanta karyar data lafka masu,jalal yace "sannau aida anje dake anyi maki checkup ko kinji rauni k'ashinki." Girgiza kai tayi tace"Aa yaya banji ba kawai dai wannan ne." Sannu kawai suke jara mata tana ansawa daker. D'aki ta wuce ta cire kaya ta daura towel,ruwan zafi yesmin ta jona mata ga heater cikin d'akin tana ta mata sanni cikin tausayawa. Sai lokacin tace"yesmin ina baban yake,ban ganshi ba." Tace"Addana baba yafita kasancewar basuyi masa komi ba,yana gama cin abincin rana yatai wajen aikinsa." Girgiza kai fiyah tayi tace"baba bai ko hutawa cikin iyalinsa ya kwana biyu bamu hadu ba,amman daga fitowa ya fice wajen aiki,mutanen da ko cigiyarsa ba suzo ba kwana biyu mts!me ma akedasu marasa mutunci." Ruwan yana zafi ta juye mata ta had'a mata tace"Addana gashican kiyi wankan sai na tayaki shafa magani." Cikin kulawa tace"sannu yesmin ngd kinjiko." Murmushi tayi tana fita daga d'akin. Haka Allah yayisu suduka kowa yana son d'an uwansa,idan abu ya samu guda kamar shi ya sama,kulawa suke da junansu sosai kuma wannan duk tarbiyyar mama ne. 💞💞💞💞💞💞💞💞 Alfah yana ganin ta b'ace masa ya dunk'ule hannu ya kaiwa bango naushi nan take hannunsa ya fashe jini ta samu hanyar fita,amman saboda zafin da zuciyarsa take masa yasa ko ajikinsa.......malik ya fito afirgice yana kallonsa,baima lura da hannunsa dake zubar da jini,cikin b'acin ran da bai tab'a ganin malik aciki ba yace masa. "Abdoul wlh idan kasake wani abu yasamu yar mutane zaka sha mamakina,don wlh zan cire sanayya na yimaka rashin mutuncin da baka tab'a tunani........kai baka bin komi asannu,komi saika zafafashi idan ma karuwarce meya shafeka ne wajenka take zuwa.kai da kake zuwa club d'inka wani ya rik'eka kokuwa wani ya kiraka da d'an iska.......yarinya tana iyakar kokarinta duk don kai duk don kadawo cikin hayyacinka kagane daidai da ba daidai ba,amman naga alamar so kake ka nakasta yarinyar mutane." Kamar Abdoul yasamu tv haka yake kallon malik,cike da tsananin mamaki da rud'ani. Tunda Allah ya had'asu tsawon shekara tara kenan irin wannan tsawar da hargagin malik bai tab'a yiwa Alfah ba........kauda kai malik yayi ganin irin kallon da yake masa,cike da sassauta murya yace"inhar baka son musamu matsala karage wannan zafin ran,karage yiwa wannan yarinyar azaba kar tsotsai yasa ka nakasta ta." Har lokacin Alfah bai samu damar tankawa ba,binsa yake da kallo kurin kamar wani status. Har malik ya juya zai shige cikin gidan idonsa ya kai ga jinin da yake zuba ga hannunsa.......cikin tsananin tsoro da firgice ya dawo garesa yana niyyar rik'o hannunsa cikin wani irin sauri Abdoul ya kauce ya shige yabarsa nan,binsa yayi cike da tsoro yana kwala mashi kira amman bai juyo ba. Shigewa yayi bedroom dinsa ya banko k'ofa yama rasa mezaiyyi sai ya silale kasa yadafe kai,yanzu zafin ya zame masa uku gana ciwonsa gana maganganun yarinyar nan,ga kuma wad'anda malik ya gama jera masa duk akan wannan kidahumar yarinyar..........tashi yayi yajawo first aid box yazo ya fara bawa kanshi treatment,tunda bayan tsawon lokaci bai tabajin ciwo ya yi yunk'urin tai makon kansa ba sai yau,hasalima kullum kokarin neman abunda zai zubar masa da jini yake,amman yau saiya tsinci kansa da bawa kansa kulawa........amman har lokacin wannan xafin na cikin xuciyarsa bai barsa ba,yana gamawa ya nad'e da bandage ya canza kayansa dasuka b'aci da jinin,ya kalli agogo nan da minty arba,in jirginsa zai fashi yana gama shirywa ya dauko bakin glass da fesing cap ya saka,ya rufe fuskarsa wadda duk da rashin murmushin da baisa ba,hakan bai hana ruwan kyansa fitowa ba......muryar malik yaji cikin rauni da danasanin kalaman daya gaya masa yace. "Kayiwa girman Allah abdoul ka bud'e kofarnan wlh dressing kawai zan maka nasan maganganuna sun b'ata maka rai,kayi hkr ingama yimaka dressing din saimuyi magana............baigama rufe baki ba ya ji yabud'e k'ofar yafiro rataye da jikarsa,dayan hannun kima jaye da trolley sa bai kula sa ba yayi gaba sannan yace"inkana iya kaini airport bismillah inkuma baka iya wa naje na hau taxi." Yana gama fadar haka ya wucesa zuwa waje. Mamaki ya daskarar da malik,ganin sabon canjin Abdoul daya zo dashi yanzu.yajima kafin wani kayataccen murmushi ya kubce masa,yana daka tsalle yace "yesssss,wlh anfara nasara gaskiya ngd sofiyyah,wlh aikinki yana kyau." Ficewa yayi da sauri yaje ya samai amota. Har sukaje filin jirgi malik sai surutu yake masa cike da jin dadi,kuma yauce ranar da Alfah bai dakatar dashi daga surutun da yake masa ba,da dane cikin tawa zaice ko kamun shiru kona bar maka motar. Har jirginsu ya tashi Alfah bai takama malik ba,sai kalma guda daya ce masa da ta sake jefashi cikin farinciki. Cewar da yayi..... _TAKE CARE FOR UR SELF_ koda Alfah ya zauna babu abunda yake sai tunani,kalaman yarinyar suke ta mashi amsa kuwwa cikin kunne, duk sanda yajisu sai yaji wata suka cikin kirjinsa....... _macuci azzalumi mak'etaci baka san komi ba sari zallar cuta da shaye shaye,taya zakaji feeling din tausayi cikin ranka ai bana tantama inkace zakai kisan kai,don kuwa y'an shaye shaye kamarka babu abunda basa yi,wannan la,anannar giyar babu abunda bata sawa.wani ma saboda ita uwarsa yayi wa fyade._ Runtse idonsa yayi yana karairaya glass din dake hannunsa,jiyake kamar ya fashe.......... _wannan la,anannanr giyar babu abunda bata sawa. wani ma saboda ita uwarsa yayi wa fyade._ Ya sakejin kalaman suna sauka acikin kunnensa......duk'ewa yayi yana dafe kunnensa,wata dake bayansa ta lura da halin dayake ciki ta d'an tab'osa kad'an. Afirgice ya d'ago kamar wani tab'ab'b'e ya zuba mata dara daran idonsa,babu arxiki tayi saurin koma wa inda take. Durk'ushewar yasake yi yana jin kamar ya kurma ihu ko zaiji saukin masifar dake addabarsa cikin rai. *kuyi hkr yau ban yi posting kan lokaci ba wlh bamu samu wuta ba shiyasa,kuma kuyi maleji dashi wlh banda time ne.* Mrs bb ce Mom muhseen 09034722970. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........20 Malik ya kasa samun natsuwa saboda farincikin da yake ciki,so yake yasamu wani yayi sharing feelings dinsa dashi,fiyah ce ta fado masa ya lumshe ido yana murmushi mai kyau......zama yayi yana cigaba da murmushin,kafin tausayinta ya cika masa xuciya yasan tana can cikin halin ciwo wayarsa ya lalubo gaban aljihun rigarsa yana dailing no dinta,ta jima tana ringing ba adauka ba yabari bayan sallar isha,i ya sake kira. Tashi yayi ya nufi masallaci don baisan rasa jam,I yana son ya sake rok'on Allah daya cigaba da basu sa,a akan Abdoul.don wannan nasarar tayau tayi tsananin sakashi cikin nishad'i inama zaisamu damar yin waya da mami ya bata labarin halin da d'anta mafi soyuwa agareta yakeciki,amman yaji kashedin Abbi bazai so yayi silar barinta wannan gidan ba bayan duk wadannan k'alubalen dasuka faru. 💞💞💞💞💞 Yau suna cikin farin ciki don gaba ki dayansu suna kan tabarma tsakar gida suna hirar da suka jima basuyi na kwana biyi da babu baba. Kowa ka kalla zaka gansa cikin Annashuwa da farinciki,amman fuskar fiyah da saukin walwala,duk motsin da zatai bak'ak'en kalaman Abdoul suke dawo mata cikin kanta,saidai ta fakaici idonsu ta goge kwalla,har baban ya lura yace"halan sofiyyah rigimarce ta motsa,meke damunki naga kwata kwata hankalinki baya nan." Danne kwalarta tayi tace"aa baba ciwukan nne suke man zafi,inakuma son in kwanta." Cikin tausayawa yace"Ayya sannu to,anshi paracitomal kisha ga mamanki zaki samu sauki saikije ki kwanta tunda kinci abinci." Kamar jira take ta tashi ta shiga d'akin mamar ta dauko maganin tasha sannan tayi masu saida safe ta shige d'aki. Koda taga misscall din malik bata bisa ba,don shima haushin sa takeji inbacin shi aida haka bata sameta ba,baida abun sanar da ita yasata tazo wannan marar imanin yakusan kasheta.......hawaye ta share tana jin wata zuciyar tana bata shawara akan ta rabu da wannam wahalar,ina dalili kana niyyar taimakon mutum shikuma baida aiki saina kashe kashe da neman makasarka.,bayi ta wuce tayo Alwallah daker tayi shafa,i da wutri sannan tatashi karatun kur ani tayi kadan,sannan ta ajiye tana jin kewar isalamiya na damunta,don lectures dinsu yanzu duk na yamma ne su suka hanata zuwa. Kwanciyarta kenan malik ya sake kira dogon tsaki taja tana danne wayar da fillow,amman zuciyarta na son dauka don gani take tayi masa wulakanci........bayarda ta iya ta daga filon ta dauko wayar,daidai sanda ya sake kira.dagawa tayi tana kangawa ga kunne hawayenta kuma sunata zuba,cikin shashshekar kuka tace"nidai yaya malik wlh nagaji,nagaji hakanan da wannan masifar,Allah ya sani niba yar iska bace ban san ma me ake nufi da kalmar ba,amman zai ringa aibatani yana cewa inyi yawo tsirara." .......sai kuka ya kubce mata duk yabi ya d'imauce ya ma rasa mezaice mata cikin kermar murya yace"kinga fiyah kiyi hkr don Allah kiyi hkr wlh Abdoul bai kyauta ba,kuma nima saida nai mashi fad'a bazai sake kwatanta maki irin haka ba,amman ki cire batun cewa kin gaji Ai daman inhar kana aikin lada dole zakasha wuya,kiyi hkr ladarki tana wajen Allah amman karkice kingaji karma zuciyarki ta sama ki fasa niyyarki." Tana share kwalla tace cikin raunin murya"yaya malik baka ga fa yadda ya saka kafafuna su kai ba,kilama ban iya sake tafiya"ta sake rushewa da kuka......dafe kai yayi yana murmushi lallai akwai shagwab'a nan wajen,danne dariyarsa yayi yace cikin tausaya wa. "Ayya y'ar kanwar malik,ya zakice haka kinga kidaina insha Allah babu abunda zai samu kafarki,kindai sha magani ko." Cikin kuka k'asa-k'asa tace"uhm" Ajiyar xuciya ya sauke yace"duk kin rud'ani wlh,nakiraki ina murna da d'okin samar dake wani labari kuma sai najiki ahaka." Dandanan ta wartsake tana goge sauran kwallarta tace"gaya man menene." Cire wayar yayi daga kunnensa yayi dariyar san ronsa sannan ya mayar yace"akan mutumenki ne." "Mts!nikadai na ban son ma ni ko sunan sa inji." Dariya yayi yace"sorry mana ansafiyya na,kiyi hkr kiyafe mashi kinjiko watarana da kanshi zaibaki hkr." Zaro ido tayi kamar yana ganinta tace"wannan dan zafin kan lallai! kaima yaya malik ka fad'a don tsokana." Dariya yayi yace"am serious kiyi ta mashi Addua zakisha mamaki,yanzufa yau abunda yayi ya ban mamaki sosai." Yabata lbr abunda yafaru d'azun. Itama tasha mamaki hartake jin ai yanzu ma ta ska k'afa cikin rayuwarsa har sai inda karfinta yakare,saita ga abunda ya turewa buxu nad'insa cikin jin dadi tace "Ashe abunda nake har zai iya canza sa zuwa haka yaya malik." Cikin tabbatar wa yace"sosai ma kuwa yar kanwata,kisake dagewa inyadawo sai kidora daga inda kika tsaya,idan da halima kicanza salo." Dariya tayi tace"kai yaya malik wai incanza salo uhm,zanyi dai bakin kokarina amman katabbatar da bazai sake shak'eni na." Dariya yake sosai yace"bazai kara ba aiyau nai masa fad'a sosai wanda ban tab'a masa ba kuma baiyyi fushiba,don da yayi ba zai mun magama ba." Tace"insha Allah i will try my best." Sunjima yana janta da hira har saidantaji yasmin zata shigo ta latse wayar tayi adduo inta kamar kullum suka kwanta. 💞 *Australia*💞 jirginsu yana sauka mutanen sa suka zo suka d'auke shi zuwa hotel d'in da zai sauka,don saukar dare yayi zuwa safe aroud 9:00 zasu fara abunda ya kawosu. Bin garin yake da kallo kamar ya canza mashi,alhalin ko kadan ma bashi yake kallo ba,in zaka tirkeshi bazai iya cewa ga abu da yake kallo ba,tsabar tunanine kawai,zuwa lokacin ya sausauta fuskarsa kodan mutanen da zai hadu dasu amman ba dan yabar jin wanan ciwon cikin ran saba,babu wanda yayi magana dashi ko saud'aya saidai hannu dayake anfani dashi wajen maganar,ko kuma fuskarsa da zai canza ma salo alamun dai bayar da ansar maganar da ake mashi. KO kadan baison magana da kowa abunda yake damunsa kadai ya ishesa,koda suka isa hotel din mutanen suka kai mashi kayansa har room din da suka kama mashin,sannan suka tbayai yana bukatar wani abu yayi masu nuni da coffee kawai yake so.har wanda yaba umurnin coffen ya juya sai yadawo don yasan idan yazo irin wannan time d'in yana buk'atar mutuniyar tashi cikin ladabi yace"sir what of win?" Idanunsa daya kalla yasa yayi saurin kauda kai,shikuma cikin fushi yace"I said only coffee." Aguje yafita don sun san hali yanzu zai ci uban mutun babu wasa. Zubewa yayi kan gafo yana kallon sama ko combus dinsa bai samu damar cirewa ba,ya runtse ido yana juya kai don kan nashi har ciwo yake masa,cikin wata irin so cool vioce yace"banzar yarinya kawai,win din zan sha ke nayi maki fyaden bayan na gama bulbula maki ita cikin ciki,wawuya kawai........zuwaan kuma wani killer smile ya kubce masah ni kaina saida yaban mamaki,saboda yadda yayi masifar fiddo masa duk kanin madarar kyansa cikin wani sauti yake magana kamar mai rad'a. "Da Idonta kamar nawa,dakin sake kinsha ta sai uwarki ko ubanki ya yankaki,kafin kisanar dashi inda kika samota mts!yarinya yar mitsila ta samun rud'ani cikin kai." Maganganun malik ne suka fara masa jeran giya,akwai maganar daya fad'a data sashi cikin shakku. _Abdoul idan kasake wani abu yasamu yar mutane zaka sha mamaki na don wlh zan cire sanayya nayi maka rashin mutuncin da baka tab'a tunani ba_ "Me Malik yake nufi?meya had'asa da wannan yarinyar......" Runtse idon sa ya sake yi wata maganar tasake shigarsa kenan.........aka turo k'ofar dakin mutumen daya zo dazun tambayarsa abunda zaisha. Cikin ladabi yace"sir.......bai bari ya idasa ba yace"drop it inside" Yaje ya ajiye ya fita ya barsa. Mirginawa yayi ya yi rubda ciki yana sauke numfashi yana jiyo muryar Malik cikin kunnensa. _yarinya tana iyakar kokarinta duk don kai duk don kadawo cikin hayyacinka,kagane daidai da ba daidai ba.amman naga alamar so kake ka nakasta yarinyar mutane._ Tashi yayi zaune dafe da kanshi da yake tsananta ciwo. "Mekenan,ina bukatar nazari ina bukatar sanin komi kar tunani ya tarwatsamun k'walwa." Wata xuciyar tace kaida kullum kake neman abunda zai kawo maka mutuwa aida kacigaba da tunanin. Mik'ewa yayi yana jan tsaki kamar da wani yake magana cikin jin haushi yace"to ina ruwanki yanzu kuma na canza ra,ayi." (😂😂wlh Alfah ya zare) Wannan daren saida Alfah yayi da gaske kafin bacci ya iya surarsa,don yana da tarin tambayoyi bila adadin da yake bukatar amsar su.amakare ya tashi wajen six sannan yayi salla yana jin haushin rashin yinta akan lokaci ba. Bayan ya yi sallar wayarsa ya dauka ya soma kiran malik wanda jiya bai samu damar kiran sa ba ya gaya mashi ya iso lfy. Malik baccin sa ma yake don shi tun biyar daidai yayi sallar sa kuma cikin jam,i ya samu ladarsa full 27. Ihun wayar yakeji daker yabude ido ya lalubota don jiya bai samu kwamciya da wuri ba saboda aikin da yasha kan computer don yau karfe goma inya fita zuwa company shida dawowa gida kuma sai six. "Sai yanzu ka kirani yallabai" Cewar malik dake kwance cikin lumtsetsiyar katifarsa. Abdoul kamar baya so yake amsa shi "Ya kake?" Murmushi malik yayi yace "yarda kake to,ina tambayarka kana sharewa." Numfashi ya sauke yace"na sauka ban da caji,and kaina naciwo shiyasa na kwanta da wuri." Jinjina kai malik yake yana jin duk sauran baccin yana fita daga idonsa,wani dadi ya kama malik,indane Alfah bazai iya masa magana har haka ba zaidai kirashi cikin shan k'anshi kalma guda zai furta mashi ataikaice cewa"na iso ba saika korani ba." Amma yanzu har yana gaya mashi halin da yake ciki.cikin jin dadi yace "don Allah karka wuce kwanakin da kace don gidan yayi man girma." Maimakon yaji ya gwalesa ko yaja tsaki ya kashe wayar sai yaji sab'anin hakan........."bazan wuce ba kilan ma kwana uku ya wadatar ka kula da kanka zanje yanzu na idasa abunda zanyi nafita." Ya kashe wayar baijira me malik din zaice ba,shikanshi Alfah ya jimabyana kallon kansa ga mirrow,mamakinsa yake yadda ya canza daga jiya zuwa yau,shikansa baisan meyasa maganganun yarinyar sukai tasiri har haka cikin ransa ba,amman yazayyi ba umurnin kansa bane na zuciyar sa ne. Mrs bb ce Mom muhssen [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........21 Cikin kwana kin da yayi Australia jinshi yake daban,saboda yadda duk d'abi arsa suke son juyewa sukoma wasu kala dabam,tunda yazo sau d'aya yasha mutuniyarsa,itama kuma baita zauna ba saboda rashin bawa kansa hutu da ishashshem bacci yasa masassara ta kamashi,randa yashata kwana yayi yana amai jikinsa kamar an masa dukan bala,i........daga lokacin bai sake nemanta ba yana son yasha amman daya kai bakinsa kalaman yarinyar da ko sunanta bai sani ba suke dawo mashi ras,kamar lokacin take sanar dashi su. Fiyah kau saida tayi jinyar kwana uku bata je ko ina ba,da yake juma,a ne kurin ba taje makaranta ba sauran kwanakin anshiga weekend ne. Baba ya wartsake ya koma hidindumun sa na yauda kullum,ya fita batun Alh muazzam don yanzu zaman lafiya yafie mashi komi da kuma zama cikin iyalinsa,tunda yagane cewar inhar baka dashi to kau kaine wulakantacce,ko da kuwa kwana kake masallaci kana sallah.duniyarce ta lalace anzo wani zamani da saidai ace innalillahi wa inna ilaihir raju,un. Feea kuwa tana can tan fama da dakon soyayyar Abdoul,ga shirye shiryen bikin Abbanta babu abunda akafasa,don kamar baitab'a aure ba haka yakeji komi na gidansa an sakeshi......har lokacin kuma mominsu bata dawo ba. B'angaren fiyah da Malik kuwa suna waya sosai don duk rana zai kirata da safe suyi kusan minty talatin suna waya,sannan yakira da rana ya kuma kira da daddare,shakuwa ta shiga tsakanin su sosai fiyah ta sake dashi har idan bai nemeta ba tana kan gaba wajen nemansa.........ana gobe Abdoul zai dawo Anty jamila ta haihu ansamu baby girl. Fiyah ta shirya kayanta itace yar zaman bakwai,har rigima sukai da yesmin akan ita zata fiyah tace"keda kin cika lalacin tsiya me zaki tsinana mata dallah matsa mun." Mama tace"Ato nidai ai bazan tura ku kudu ka ba kamar wata wadda bata da hankali,kume ke safiyyah ai ga makaranta da hkr kikai tunda ita ta gama zaman banza take." Silalewa kasa tayi tana dirje dirjen kafafu don yau rigimar takeji bilhaki da gaskiya "wallahi mama dama nasan saikin kware mun baya,kullin saikin nuna ni baki goyon bayana tsakani da Allah nida nake babba ai ni zakice intai." Yesmin tace"kiyi hkr Adda wlh ni daman janki nake don inji me zakice." Ta fada tana dariya mama na taya ta kallonsu take tama kasa cewa komi mama tace"kinji kunya wlh safiyyah kullum ke bakida wani girma saina jiki." Ranar da daddare bayan sallar magruba ta shirya kayanta zata wuce,baba yace yaya jalal ya raka ta ta samu abun hawa."don kin matsa uwata ai da bari akai saida safe,wlh ni bana son fitar dare." Yaya jalal din yace "yo baba sai abuna take so don gidansu,ke maza maida wannan akwatin saida safe zakitai,don ubanki kamar wacce ake cizo cikin gidan ko ker mar ubanme take." B'are baki zatai ta wage da kuka yafaske bakin "kisake inji sautin numfashinki sa niyyar kuka kigani." Daki na koma nayi kuka na bakuma komi yasa nakeson fitar ba munyi sa malik zaiso bakin titi ya wuce dani baban najiyosa yana cewa"kayi hkr Abdoul jalal barta tai kila itama jamilar tana can jiranta take." Kwala man kira nai nafito hararata yayi yace"kina iya wucewa muje ai,fitinanar wofi ke ko kunya baki kiji ga yar kanwar ki nan bata addabi kowa ba saike katuwar wofi." Haka ya tusani har bakin titi sai sababi yake shida Anty jamila insuka fara fada kamar bazasu barka ba,koda ya tari taxi din cewa yake"wlh kika bari naji labarin kin kai saurayi gidan nan zaki gaya masu." Yabiya mai taxi din mukatai. Wayata keta haske alamun kira na Ake don silent take kar akirani gabansa inshiga uku. "Yaya malik yayane ta tarar mun taxi kaganni nan ma mun tafi kabarshi mun hadu gobe ai inada lectures." "Aa yar qanwata gani nan bayanku fa" Zaro ido tayi tana lekawa aikuwa shine saurin tsayar da mai taxi din tayi tace"daka ta malam saukeni anan yi tafiyarka." "Amman hajiya kinajin kashedin yayanki." Cikin masifa tace"dallah can niba kudin zan ansa ba mak'olo kuma ina ruwanka da shiga sabgar da babu kai." Hkr yabata sauka tai ta shige motar dariya yake mata yace"haka kike masifa qanwata." Murmushi tayi tana cewa"yaya malik naga zai kawo mun raini." "Toya kike kinsan kuwa nayi kewarki." Jin kalamar nayi kewarkin tayi bala,in sata shock har ta kasa kallonsa kauda kai tayi gefe,yana lura da ita yasake cewa. "Na saba kullum ina ganinki kwana hudun nan jinsu nake kamar na shekara,koke bakijin yadda nakeji." Shirun ta sake yi masa dariya yayi kasa kasa yace"tunda baki magana gaya man sunan unguwar." Daker ta lalubo abun fad'a tace"gwarunfa" Hira yake mata amman ta kasa cewa komi don yau da wani salo yaxo dashi wanda ya sata shiga shakku.........sakin maganar yayi ya kama wata "kinsan kuwa zakiya aure zatai in the next 4 weeks" Sai lokacin ta bashi duk kanin hankalinta tace"dagaske!kashhh banji dadi ba amman ya zamuyi yanzu." Karka ta wa yayi yasa hannu ga Aljihun wandonsa na baya,ya zaro wata pos mai shegen kyau ya mik'o mata. Ansa tayi tana binsa da kallon karin bayani. Hankalinsa na kan tuk'i yace"ta yarda ita ne bakin bank,ina gefen hanya nazo shigar da kudi,Allah yasa ni kadai na gani nai saurin dauketa,duba ciki kiga akwai information din duk da mukeso jikin wami card nan,phone number,address da sai sairansu to duk ciki dai ba kamar phone no din itace abu mai muhimmanci,gashinan na bar maki sauran aikin." Alamar jinjina tayi mashi tama smile dinta mai kyau da gigita wanda ake mawa. Ajiyar xuciya ya sauke yace"gobe 12:00 na rana zai sauka zakimun rakiya." Tana rik'e da card din data fiddo tana kallo tace masa"ni kau mezan yo." Murmushi yayi yace"kece da abunyi kau,zaki je tarbarsa ne harma da guzirin flower." Dariya tayi tana girgiza kai tace"kaima yaya malik da neman magana kake to miye na wani zuwa da wata flower saika ce wasu lovers." Rage gudun yayi yana kallonta asace wanda hankalinta yana kan card din dake hannunta,kauda kai yayi ya cigana da tukinsa. "Ba dole sai masoya ke haka ba,kawai zakiyi masa ne don muga action din dazai bada." Rausayar dakai tayi tana kallonsa kadan kafin ta kauda kai tace"oky let me see" Sun iso unguwar lafiya yayi parking bakin get din ya ja kofa taki budewa,juyowa tai ta zuba shi ido kamar yadda ya zuba mata nashi masha Allah..........kasa jura tayi ta janye idonta ta rasa wadannan sale salin da malik yake mata ko namiye......."kin ga" Daker ta oya sake juyowa don wlh yadda bai tunani bata son hada ido dashi,tana jin kunyar kallon da yake maka mata. Lumshe ido yayi ya jawo wani d'an gift daga bayan motar an nadesa da irin ledar nan da ake nade gift da ita. Kasa ansa tayi tana kallonsa tace"na miye yaya malik?" Ajiyar xuciya yaja yace"just for u,na gani ne yayi mun kyau nace zaifi dacewa da hannunki." Tunda suka fara muamala yaune ya taba bata abu,don haka bata jin zata bashi kunya cikin sanyi ta mik'a hannu ta ansa. "Thank u so much yaya malik." Hannunsa yasa gefen kansa yayi mata salute alamar sara wa. Murmushi tayi tana masa saida safe. "Karki manta fa zanzo nan natai dake kizama cikin shiri." Daga masa kai tayi tana shigewa cikin gidan. Dora kansa yayi saman sikiyarin motar yana magana can kasa,bazan iya juyo meyake fada ba,yajima wajen sannan yaja motar yabar unguwar. Da saukin mutane gidan don makociyarta ce kadai sai wasu mutun biyu dangin uncle yahya,ta gaidasu tana isa ga jaririyar ta dauketa cike da jin sonta. "Welcome to d world my princess Allah yayi maki albarka ya raya ki bisa sunna,amman don Allah karkiyo fadan Anty wlh bata wa zamuyi." Dariya duk suka saka masu itama fiyar tana dariyar,tace"Allah kuwa dagaske nake,dama dama ma inkika biyoni da naji dadi." Nan ma dariyar sukai Antyn dake shigowa dakin tace"kice dana shiga ukuna wlh,aiban mance masifar da kika gana ma mama ba,sannan kice ta biyoki aa ban lamunta ba." Hira suka ringa sha yaka junan su da kuma mutanen cikin dakin,saida dare yakara sannan duk sukatai,nan suka bude sabuwar hira saida uncle din ya dawo sannan tayi masu saida safe ta wuce dakin da zata sauka,komi akwai bata bukatar komai shirin bacci take tayo wanka hade da alwalla tayi ksha,i da shafa,i da wutri sannan ta saka kayan baccinta ta haye gado wannan gift din ta dauko tana warwarwa,wani box ne ya hadu sai daukar ido yake ya budesa ............wow wow masha Allah kawai take furtawa zobene yasha kyau,dan karami kuma sannan yazauna daidai kan yatsarta ta kusada ta tsakiya,dan danan ya haske mata hannun damabgata da dogayen yatsu da doguwar akaifa......bata fita cikin shaukin zoben ba kiransa ya shigo. "Fatan kin kwanta." Cikin annashuwa tace"ina zan iya bacci yaya malik." Cikin rashin gane kan maganarta yace"ban gane ba." Ajiyar xuciya ta sauke tace"shaukin zoben nan ya kawar da baccin,wlh yayi kyau sosai baka ga yadda yayi kyau ga hannuna na ba,kuma daman ni mutunce mai son ring." Wani dadi yaji jin abunda take cewa,murmushi mai sauti yayi yace"daman ina ganin sa nace bai dace da hannun kowa ba sai yatsar qanwata safiyyah." Kwanciya tayi tana kallon hannun bace komi ba,wannan damar ya samu ya sanyaya muryarsa yace"ya kikeji." Murmushi kan fuskarta tace"i'm feeling happy yaya malik har na mance rabona da zobe." "Karki damu indan wanan,fatan zaki kasance cikin farinciki har waye war gari,zanso inga yadda fuskarki take Annashuwa,kinsan duk sanda kike cikin farinc ciki duk kan wani kyau daAllah yayi maki safiyyah yana fitowa,kamar misali kinga inkikai dariya wushoryarki tana bayyana,yayinda take kara fiddo annurin face naki,and than kywawan hakoranki wadanda ake kira da hakoran kyau suna fitowa su haskeke fuskarki,bayan wannan ma kina da abu mafi soyuwa dayake kara mun ganin kyanko shine dumful dinki left and right,ta ko ina Allah ya baki ki gode masa." Tunda yafara magana tayi lub cikin bargo,idonta arufe yake ruf,kunnenta ne kawai yake sauraren kalaman malik,da take jinsu amar acikin bacci shin idan ta dorasu bisa ma,aunin tunninta anya atayi gaskiyaa abun da take zargi,meyasa haka to ko dai shi haka yake salonsa saika ce wamda yake cikin soyayya........wata zuciyar tace aa ba haka bane malik bazai soyayya dani ba,aini bana soyayya yanzu ban ma iyaba wata kuma tace mata"bakison sa kenan,meyarasa duk abunda kake bukata ga namiji ya mallaka.....runtse idonta tayi tana ciro wayar taga kodai shirmene na tunani ban gaskiya ba,amman still yana online. Muryarta kamar wacce aka shake tace"zan kwanta saida safe." Ta kashe wayar ba wai don wulakanci ba aa bata san dai abunda za tace masa ba,daker tayi addua ta kwanta amman baccin ya jima bai zo ba. Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........22 Tunda tayi asuba bata koma ba ta fito ta kama gyaran gidan,don tana da lectures around 8:00 yau suke covering lectures din don week mai zuwa exams ne zasu fara biyowa baya,dolene ta bama kanta hutu kodan exams din nata.kafin mai aikin tazo fiyah ta gama shara da goge goge duk wani lungu da sak'o ta share ta gyara,sannan ta gogeshi tas kamar kasunkiya ka lasa don tsananin yadda ta goge tayils din,dama gashi fari sai ya sake haskawa. Ta bud'e ko ina da turarukan wuta dakin Antyn ne kurin bata gyara ba. Saifa bangaren uncle yahya shikuma sai ya tashi kilama saita dawo ta gyara,duk da tasan Anty da kokarin tsafta take ba ma lallai yayi wata daud'aba. Falukan biyu da extra rooms din ta gama dasu da daining room. Kitchen ta wuce ta duba abun da suke dashi tahau hada kalaci,tana yi tana ankare da time. Kunun alkama tayi mai hade da markad'ad'dar gyada yasha madara sai daukar ido yake.sai ta dumama wani ferfesu data gani cikin frig,sannan ta fere doya ta tadafa ta sannan ta daketa tayi sakwara daman akwai kayan miya tayi greeting dinsu ta yi yar sos mai hade da kwai da vegetables........dan danan k'amshi ya karad'e gidan. Wainar fulawa ta hau soyawa bayan tasaka mata albasa mai lawashi da cabbage,sai kwai data xuba aciki da magi.......kafin takwas da rabi harta gama da wanna fannin ta wuce tashiga wanka. Duk abunda takeyi kalaman malik na jiya suna mata yawo cikin kai,ta rasa wani waje zata ajiyesu duk inda ta duba taga basu da waje amman kasancewar malik mutunne mai mutunci da dadin zama,saitaji bai dace da wofintar waba koba komi sun saba kuma aduk hasashen irinsa take yiwa kanta fata. Wanda ba dan kowa ba bai kuma da jijidakai irin na masu shi,wanda yasan girma da mutuncin iyaye wanda zai girmama mata nata,wanda bai dauki duniya da abunda ke cikin ta ba.wayayye mai fara,a da boye bacin ransa akowane hali. A iyakar zaman su ta karance shi duk haka yake,malik yana da kudi don kuwa zaman sa da Alfah ya samu kudi da shi kansa baisan yawan su ba,amman bai dauki kansa bakin komi ba bai kuma kalli kudin matsayin masu darajar da zai iya yin komi dasu ba. Yana yin komi yadda ya dace da ace wani ne yadda yake kokarin ganin ya faranta mata,to zaiyyi anfani da dukiyarsa don yana ganin ai kodan ita zata saka yasamu duk abunda yakeso. Sai akai sa,a shima malik din ya ganeta yaga kudi da wasu kyalekyale na duniya basu gabanta,iyayenta sunyi kokarin gina mata tarbiyya da duk wanda yazauna da ita ko ta zauna dashi zayyi sha,awart. Fitowa tayi tana tsane jikinta bakin gado taji budewar kofar juyawa tai taga Anty ce. Murmushi tayi tace"Anty maijego barka da tashi ga ruwa can baya an kwashe maki karya huce,ya kwanan princess." Cikin jin dadin kulawar yar uwar tata ta idasa shigowa tace"princess dinki bata da kirki jiya bata barni nayi bacci ba wlh sai biyu da rabi,nikau in tace ke zata biyo wlh na bani uku na safiyyah." Me fiya zatai ba dariya ba tana lakuto mai tana bin jikinta dashi tace"Allah yayi wa princess albarka ai kema mama tace kin mata kuka har taji da ana bayarwa data samu maiso ta bada saboda kukan ki." Murmushi tayi tace "aigashinan kau ana rama mata,ke wai kinji yadda take kuka saboda wulakanci wai kar a kashe wuta kuma karna zauna kiji min yarinya ita nan har tasan wani zama da wani haske ita da tazo shekaranjiya." Fiyah shafarta take tana dariya tace"Ato sai kushirya don aradu akwai aiki." "Uhm Bari kawai,fiyah duk ke kai ayyukan gidan nan,gaskiya kin kyauta Allah yabiya ki yabar ki da muhseen." Dam taji kirjinta yace ita wlh ta ma manta da babin wannan gayen,tunda ta anshi wayarsa bata taba yunkurin kiran sa ba. Tabdijam ashe anty nanan kan bakanta nashigesu yazan yi,don wlh ni ban ra,ayinsa ya cika yanga wlh. Yak'e take tace"uhm Anty kenan." "Kamar ya anty kenan badai baku waya ba,mekike nufi fiyah?" Bata bari sun hada ido ba tace"kai anty shidin ya ce maki bamu waya?" "Ban sani ba" Dariya take ciki ciki tace"sorry kwantar da hankalin ki muna waya amman ba kullin ba gaskiya." Sai lokacin ta washe baki "koke fa yar qanwata,wlh ina maki sha,awar muhseen yaron kirki ne baida wata matsala." Uhm kawai fiyah tace ta shiga saka kayanta juyo mata bata tayi "mak'ala mun Anty." Cikin haushi tace"tirr da ke shekara ashirin da biyu baki iya saka bra ba,ba doke yesmin take maki dariya ba." Ya mutsa fuska tayi "Anty hannuna ne fah bai kaiwa,nidai ki makalan mun sauri nake in da class." Makala matan tayi tana nufar kofar fita"ga kudinki can bisa frig kitchen,nasan sadda zaki fito ina wanka ga kaya can da za asaka mata idan za,ai mata wanka." To tace mata sanan ta fice ita kuma ta idasa saka kayan ta murza farar powder da libstick bata sa kwalli ba fiyah irin mutanan nan ne da zaka ga koba su saka kwalli ba sai kaga kamar sunsa,haka idonsu yake daga Allah ne. Hijab har kasa ta zuba bayan riga da siket din data saka don inhar ta sasu tofa bata saka karamar hijab,saboda duk shap dinta bayyana yake tubarkallah. Saida ta tabbatar ta yi abunda Anty tace sanna tayi break sama-sama ta dauki kudin har 1k ta jinjina kokari irin na uncle yahya. tasan shine zai dauki nauyin zuwa makarantar ta har ayi suna. Karo sukai da feea zata shiga itama shan mur fiyah tayi tana wuceta feea na gama parking har sauri take ta iske fiyah karta shige aji........"fiyah,fiyah magana nake fa don Allah kitsaya." Juyowa tayi tana kallonta "lafiya wannan kira haka kamar makauniya." Numfashi ta saue tace"hkr nake ta son inbaki akan abunda yafaru rannan,kar kiga laifi na wlh iya gaskiyata na fada maki akan Abdoul,amman tunda naji bayanin ki na dauki hkr na sama raina,damuwata guda zakiya da Abba zai aura wlh kau don Allah kiyi hkr mushirya bana jin dadin shariyar da kikemun." Tunda ta anbaci zakiya wani irin dum taji tana sake ware duk idonta akan feea kafin taja hannunta tace"feea kin tabbata ita zai aura." Jinjina kai tayi "wlh kau fiyah kinga ma invitetion nan." Ta zaro ta nuna mata gashinan zakoya muazzam and Alh jamilu badaru (kwangila) Cikin tsananin mamaki ta kalli feean tace"insha Allah baza ai auren nan ba,karki damu zan taimakeki ki kwantar da hankalinki" Zakiyya!zakiyya!! Abunda take nana tawa kenan tana da tarin tambayoyi sosai amman zakiyar kawai ce zata ansa mata su,kallon ajinsu tayi babu malami ta kalli feea sannan tace"kije class ga shi can inajin ma last test zakuyi,zamuyi magana kicire komi aranki." Haka suka rabu fiyah ta shiga class dinsu ta samu waje ta zauna tunani ta shiga yi. "Zakiyya na son auren ko aa,in har bata so wane dalili ne yasa zata aureshi wanda ya haifeta sau uku ko hudu.kai bama yarda zai zakiyya ta so auren sa,lokaci guda bai isa ta manta da nasser ba har tayi wani auren..........haka akai wannan lecture daker taba da constretion dinta ga abunda ake masu tana yi tana jotting,ganin abunuwan suna da amfani sosai kuma tasan shi tsaf zai iya makosu cikin questions din exams. Tayi mashi tambayoyi sosai tana yi tana rubuta duk abunda yake sake mata bayani.......sai sha daya suka fito waje ta samu ta zauna koda taga sakon malik share wa tayi.don ba shine gabanta ba bata ma duba shi ba, No din zakiyya da tayi save tun jiya ta shiga lalubowa ta kasa kunne taji kozata shiga,cikin sa,a ta shiga tana ta ringing saida ta kusan katsewa sannan ta dauka . "Hello,wake magana" Ajiyar xuciya ta sauke tace"Sunana safiyyah,don Allah ina magana ne da zakiyya muazzam." Cikin tabbatar wa tace"yes I'm zakiyya,who is safiyya mekikeso." Fiyah tace"no tukunna dai yanzu dai magana nake son nayi dake amman ba awaya ba,ki saman time sai nazo na kiyi mana wajen da xamu hadu,maganar is very important awajen ki.bayan haka pos dinki da kika yar a bakin bank tana wajena." Cikin dokantuwa tace"plss ina Central park kizo mu hadu yanzu don Allah saboda banda isasshen time ina hidimar bikine." Fiyah tace"no yanzu ina makaranta kuma kona tashi banda time akwai ayyuka da zanje nayi kisamu lokaci kedai,inkin yanke time kikirani sai anjima." Ta yanke wayar tana jin insha Allah komi zaizo da sauki,don naga alamar bata da zafin kai irin na yaran masu kudi. Sakon malik ta shiga dubawa tana jin kirjinta yana bugawa,bata son ganin kalaman nan nashi wlh tada mata hankali suke. Ilai kuwa sune _Kyakkyawa acikin kyakkyawai fatan kin tashi lfy,jiya kin gudu kin barni da jimami Allah yasa dai kalaman malik basu hanaki bacci ba_ Runtse ido tayi tana fita daga cikin text app din. Tana tsogumin wannan sabon salon na shi,wata qawarta ta iso tana cewa "Fiyah ana nemanki wani guy ne gashi can bakin department." Zaro ido tayi tana binta abaya aikuwa malik ne hararar sa tayi shikuma yana mata dariya, "Amman meyasa bak kirani ba zaka zo har nan baka san yanzu mutun ake kiwo ba ba dabba ba.idan wani yaje ya kai labari ga baba ko yaya jalal fah." Kama kunnesa yayi duka biyun zai durk'usa tai maza tatare shi har suna karo danjuna. "Meye haka yaya malik,don Allah ka daina muje idan magana ka keso dani amman ba nan cikin mutane ba wani dan sa idon yana can yana gulmata fiyah tsaye da namiji." Dariya yake yana shigewa gaba tana bin bayansa wai gowa yayi yace "wai tsoron aganmu tare kike?" Bata kalleshi ba tace "yaya malik kenan don baka san yan sa ido ba,to yanzu wani nacan yana cewa ashe dai safiyya el-ladan ashe daman musulmar karya ce kuganta can tare da saurayi bayan bata tsaya wa da kowa duk makarantar nan." Me malik zai banda dariya kallonta kurin yake yace"Ashe dai qanwata ba wasa har tsoron tun kararki ma ake,to miye idan anganni dake ba sai kice yayanki bane." Jinjina kai tayi tana rik'e haba tace"uhm yaya malik kenan wlh wata ko wani nacan suna mana kallon masoya raba kanka da mutane." Daidai isowarsu bakin motarsa ya juyo yana rungume da hannun sa ga kirji ya zuba mata mayatattun idanun sa. Shiru tayi tana neman hanyar buya daga idonsa dake mata wannan kallon da bata so,yasha gabanta yana murmushi mai sauti leko fuskar yayi yana son su hada ido dariya yayi ganin ta runtse idonta. Motar ya bude mata yana cewa"bismillah gimbiya safiyyah." Wannan suna ya shigeta har saida ta kallai cike da mamaki,shi kuma ya kanne mata ido guda tai saurin shigewa motar tana jan numfashi. Dariya yayi yazaga yashiga suka bar makarantar. Don ma kar yayi anfani da yin shirun ya sake yi mata abunda bata so yasa tace. "To da bangama lectures ba fa" Hankalin sa naga tukin uace"ai dayake ma nayi sa,ar kun gama." Rausayar dakai tayi tace"ina zamu yanzu to." Kwana yayi yana cewa"siyen flower,wace kala ce tafi yi maki kyau cikin flower." "Yanzu wannan flower da tsiya sai ansiyeta, don Allah nidai kabarta kasan halinsa yanzu haka muna isa karshe kila ma dani da ita zaiyi watsin ala tsine damu cikin mutame." Dariya yayi yace "karki damu Allah bazai maki ba." "Hum to idan yayi manin fah" "Saki rama kaina" Dariya tayi "da haka kace sai kiyi hkr,inbanda abunka ina ni ina iya bugunka ai saidai kabarni da ciwon hanu." Hirar su suke har suka isa wani waje da flowers din kawai ake siyarwa zalla,gasunan gwanin sha,awa sai wadda ka keso........tunda suka tsaya ta hango wata pitch color and dark pink color,dance danan taji ta burgeta inda take kalla yabi da ido yayi murmushi yafita yabarta. Inama ace mutumen kirkine zata ba kuma in ta bashi ya ansa cikin jin dadi da annashuwa,wanda tasan har abadan bazai yada ba saidai idan yabarta inda zata bushe,da tace ya dauko wadda ta gani don tayi bala,in burgeta Amman bazata so taba wanda baisan mutuncin mutame ba,banda yunkurin kisa bai iya komai ba saifa zafin ran banza. (Nikau nace uhmmm gaba dai gaba dai ansafiyyan malik😊) Dawowa yayi da ita rik'e ga hannu,an sakota cikin wata fation leda mai zanen flowers din. Banda kamshi babu abunda take duk ta cika motar da kamshi,mamaki da al,ajabi ya rufeta ganin wadda dai taketa santi itace ta siyo baki bude take kallonta Kasa cewa komi tayi murmushi yayi yace "baki ce tayi kyauba." Kauda kai tayi gefe"yaya malik ba kyau ake nema ba ai,fatan da ake abashi ya ansa cikin girmamawa shine kawai bawai kyau ba." Kunshe dariyar sa yayi yaja suka bar wajen. Tunda suka tunkari airport din kirjinta ke amsa wa,tunda take tunda tafara wannan aikin wahalar bata tabajin faduwar gaba irin ta yau ba,duk sai taji ta diririce tun ma kafin suyi ido hudu dashi...........kallon sa tayi cikin raurau da ido don har gobe bata mance wahalar da ya bata tace"yaya malik nidai bazan iya fita ba kaje kai dai wlh ni tsoro nake ji wlh." Ajiyar xuciya yaja yace"relax safiyya,karki saka tsoro nace maki bazai maki komi ba ai yadauki fada na" Ajiyar xuciya ta sauke tana sake jin gabanta yana faduwa. Fitowa sukai daidai sana akafara sanarwar saukar jirhin.duk atsorace take kamar ace kes ta ruga da gudu.........ahankali mutanen suka fara saukowa duk wanda yaga nashi sai ya je ya tare sa,har zuwa sanda idonta yakai ga wani balarabe yana saukowa yasha suit dinsa bakake,amman ya cire ta saman yana rake da ita ga hannu,sai side bag dinsa idonsa da bakin glass bayansa wasu mutane guda biyune suna dauke da akwatinsa biyu.......saukowa yake cikin jarumta da natsuwa iya haduwa nasser ya hade tau,sai yasake yin fresh gashin fuskarsa sai daukar ido yake,haskensa ya karu tunda ya sauko idonsa ya kai ga su malik,iska ya shaka yafesar yana sake dire idonsa akanta.......ayadda yake kallonta yagano tsoro da shakku atare da ita,baisan ma wani killer smile ya kubce masa ba.......yana ayyana wa aransa cewa"yarinya zaki gaya masu." Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........23 "Masha Allah laquwata illa billah,gaskiya Abdoul ya karo kyau zuwan sa Australia,baki gani ba fiyah?" Malik ya Sanar da ita yayinda ta tabbatar wannan balaraben da take ta faman yaba wa cikin ranta she Abdoul dinne,babu hassada kam yakaro kyau da haske wannan idan ya shiga cikin larabawan ma bazaka tantance sa ba idan ba hausa akaji daga bakin sa ba. Amman da yake bata haushin sa da tsanarsa yasa taja tsaki tace"idonka dai bai gani daidai ba yaya malik,ina abun yake wai maye yaci jariri." Dariya yayi yana mik'o mata flower yace"banda dai jealous ansafiyya kifadi gaskiyar abunda yake ranki." Gabanta ya fadi karfa ya gane ta yaba kyansa,sake shan mur tayi tace"mts Allah na tuba koni dai nafisa kyau." Ganin yana tunkaro su yasa baice mata komi ba,nan fa gabanta yaci gaba da lugude,ta rasa da fuskar da zata anshe sa. Rungume juna sukai shida malik,yayinda fuskarsa ta sake ba kamar yadda tayi zato ba,hannunta banda rawa babu abunda yake kallon flower take tana jin bakin cikin mik'a masa ya yi watsi da ita,runtse ido tayi tana karanta duk adduar data zo bakinta sannan ta bude,tana saka dauriya aranta ta fara takawa zuwa garesa,tayi jarumtar saka kyakkyawan smile mai kyau a fuskarta........jerowa sukai shida malik yana rike da side bag dinsa daya ansa,duk idonsu akanta yake amman haka ta maze tana sake sakin murmushi,hakoranta suna bayyana kallonsa ta soma yi aslowly tun daga kasa zuwa sama,tana yi tana juya idonta ta sigar kallon banza,sanna cikin siririyar muryarta data sake fidda sauti mai dadi tace. "Ur highly welcome drinker guy." Ta fada tare da saka duka hannayenta biyu tana tallabe da flower ta mika masa,tana sake nitsar da idonta cikin nashi.don yana isowa ya jare glass din. Wani dakikin murmushi ya sakar mata,yana tsareta da kyawawan idanunsa ya juya gefensa yayiwa yaronsa guda nuni da flower hannunta yace atakaice"take this john." Zuwa yayi zai ansa ta janye daga garesa tana dan matsawa daga garesa cikin kallon banza tace"ai bashi na kawo ma wa ba,bacin haka taya zan rike abu arene ya rik'e it's not possible." A bun mamaki da al,ajabi dariya suka gayi yana isa wajen john yana dafa kafadarsa cikin nishadi yace"kina kyamarsa ne?" Juyar da kai tayi gefe tace"fadi bacin baki." Jinjina kai yayi yana ciro hankcif daga aljihunsa ya nade hannun sannan ya isa gareta kamar zai koma cikin cikinta yana kallon cikin idonta yace"tunda kin matsa saina ansa ba laifi,asar yayi yana gogata ga fuskarta,muryarsa kamar yana rad'a yaci gaba da magana still yana gogamata flower ga fuskar,hakan yasa mata tilas runtse idonta don karya tsole mata shi. "toni nafi kowa kyamarki,dana ta6a abunda kika taba gara naci abinci da wancen da kike kyamar,kin ga kau su basa tsarki amman na gwammace hakan.saboda kinfisu datti." Wadannan kalaman na Abdoul sun rushe mata duk wani juriya da take ciki,sun narkar mata da zuciya ta yadda har takejin d'acin su akan halshenta,hawaye suka taro tab cikin kwarin idonta ta rasa yadda za tai ta mayar dasu.......saboda kalaman sa suyi nasarar jefa zuciyarta cikin kunci sai taji inama dukanta yayi basu ya gaya mata ba,ashe daman akwai kalaman da zakaji gara ayita dukan ka da agaya maka su..........murmushi ya saki ganin yayi nasarar cusa bakinciki cikin ranta,kila ta fita daga rayuwarsa yanzu ya samu weakness dinta,dungure mata kai yayi saboda yadda jikinta babu kwari saida tayi taga taga zata fadi,kafin taci nasarar tsayuwa daker........tunda suka iso wajenta malik yaja gefe wajen mota yana kallonsu,da farko yaga kamar za,a rabu lafiya har yana murna ........sai kuma yaga abun ya cakude. Har Alfah yakai jikin mota anbude mashi zai shiga yaji takunta bayansa,tsaya wa yayi bai juyo ba cikin raunin murya wadda da kaji kasan kuka kiris yake daya subuce mata tace "Duk mutumin dake fifita kafiri akan musulmi yayi asara ba yar karama ba,kuma wannan mutumen ya cancanta duk wanda yake tare dashi ya nisancesa,sai akai sa,a bayan fifita kafirin mutun da kayi akan musulma. ka kasance wanda Annabi ya tsinewa ya la,ancesu don duk mashayin mutun wanda keshan abunda zai gusar masa da hankali Allah yana fushi dashi.kuma Annabinsa ya tsine masu,kaga kuwa wannan ba baurgewa bane asarace ta sameka kuma ina maka fatan Allah ya shiryeka.don Annabinmu yayi mana hani da la,antar la,ananne saboda zai sake lalacewa don haka ina sake maka addua Allah ya shiryeka,ya maidoka hanya madaidaiciya in kuma baka shiryuba Allah yayi mana tsari da kai da masu take maka baya." Malik daskarewa yayi a inda yake tsaye,don ba ma Abdoul ba shi kanshi malik kalamanta sunyi bala,in daure masa kai ya kuma ji dadi data rama don aga yau zaisa cewa idan baki yasan me zai furta bisa me za,a maido masa ba. Idanun Abdoul sunyi jajawur har fuskar sa saida tayi jaa saboda yadda ransa ya b'aci.......tabbas ya san kalamanta gaskiyane akan sa,amman ba wai ya furta mata haka bane don hkan yana nufin har cikin ransa ba,aa don ya kuntata mata zuciya yadda take masa,amman sauran kalamanta dasuke nuni da cewa giyar da yake sha sunyi mashi tsayuwar giginya cikin ransa.....inama zai iya gaya mata cewar rabonsa da giya tun anan kasar,inama zai iya shaida mata yabar shanta amman yadda yakejin zafin kansa bazai iya sanar da ita ba,hakan yana nufin kamar yana tsoronta kamar ya ji zafin zagin da take masa ne ya daina,bacin tsoron Allah ne yayi masa kwaranya lokaci guda.duk da hada gudun mawar kalamanta ayadda yakeji yanzu bazai iya ce mata komi ba kuma bazai iya kai hannunsa jikinta da sunan duka ba,ya ma rasa ta kamaimai abunyi don kuwa yadda mutane ke kallonsu idan yace yadauki action to sunan sa sake baci zai,kuma ba hakan yaso. Lumshe idonsa yayi na seconds ya bude ya sake xuba mata su yayinda kwallarta ke mata zarya kan kuncinta........duk tsirarun mutane kallonsu ake sai yayi anfani da wannan damar ya isa gareta kamar zasu zama abu guda. Sunkuyowa yayi sosai daidai fuskarta abun mamaki da al,jabi da kuma rud'ani jitai halshensa yanabin kuncinta har zuwa saman idonta,dayan gefen shima yayi masa haka........cikin rudani da tsoro ta ja baya afirgice yayinda mutanen suka fara bajewa,daman haka ya keso kurin sai juyawa yayi yabarta nan tsaye kamar gunki.......daman malik na ganin haka ya shige mota maimakon naga canjin yanayi da nuna haushi akan fuskar mali,sai naga murmushi mai kyau akan fuskarsa.ya shiga yazauna ya kwantar da sit din gaban ya silale ya kwantar da bayansa da kansa,idonsa rufe ruf. Jin malik yatashi motar yasa shi magana batare daya iya bude idonsa ba . "Kasan nan zaka barta meyasa kazo da ita?" Daman haka yake jira ya bude motar yafota ya iso wajenta magana zai mata ta juya ta barsa wajen. Gudu gudu sauri sauri haka take hadawa don isa inda zata samu abun hawa...........jitai kamar tana bisa iska zuwa sadda zata dawo cikin hayyacinta saidai tajita anyi jifa da ita cikin mota.........sannan suka tafi. Wai ashe Alfah ne yabiyita yadaukota kamar yar tsana yasata motar,don yayi imanin kafin ma ta isa inda zata samu taxi sai kafarta ta kusan cirewa don ciwo........shiyasa kawai yaje yadaukota don idan suka tsaya janjani zata bata masu lokaci,shiyasa kawai yayi mata haka. Kuka ta fashe dashi don tama rasa me zatayi tama hana zuciyarta yin wani tunani ta kuntace ta waje guda,babu mai magana amotar don su ukune yaran sa sun wuce company da kayan d suka duko. Sutin kukan kurin kakeji mai cike da bakin ciki kafin ta gaza jure k'un cinta take cewa. "Allah ya isana ban yafe ba mug.........kasa idasa mugun tayi tana shashshekar kuka Alfah dake gaba kwance idonsa lumshe jinta kurin yake murmushi yayi mai sauti har saida malik ya juyo yana kallonsa, "Malam Kalli gaban ka karka zubar damu." Dole malik ya kauda kai don shi yau Alfahn duk ya zamema sa kamar wani sabon mutun. "Haka kawai ka samun wana kazamin bakin naka mai shan giya,gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh kaida Allah ban yafe ba." Sika sakejinta tana fadar haka. Bai motsa ba yace"naga dai alamar giyar nan sonta kike kina sha,awar d'an d'anawa karki damu zan baki kisha." Bata sake magana ba har suka isa gidan su Malik,don babu abunda taki jinin ji daga garesa irin yace zai bata giya,tasan kadan daga cikin aikinsa ne tsaf zai danneta ya dura mata ita.wai Allah da tashiga ukunta kau. Fitowa tayi tana sharben majina ta wuce titi bata saurari kowa ba ta tari taxi ta wucw gida.........koda taje anty tace ta huta tayi masu girkin dare cewa tai bata da lfiya,dole sai Mai aikinsu ce tayi masu. Mrs bbce Mom muhseen 09034722970. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.......... Wannan dare safiyya bata iya runtsawa ba ta tayi kiskuren runtse idonta sata ganshi yana lashe mata kumatu,dandanan zata ji tsikar jikinta tatashi tayi zunbur ta tashi zaune ta rabka tagumi..........ga baccin yana cinta amman bata son ganinsa cikin baccita,meyasa ya tsaya man garai ni fiyah?meyasa wulakancin sa bai tsaya man sosai irin yadda salonsa ya tsaya mata ba.hatta kayan jikinta yau ta gagara musanya su saboda kamshinsa dake jikinsu,dandanan Allah yasa mata kaunar turaren.daga ta mirgina can saita mirgina can har dai mulmulowa tayi kasa bata ma san tayi ba saida tajita tim kasa.........dafe kai tayi tana mamakin kanta wai meke damuna ne yau,akan wancan dan rainin hamatar na ke duk wannan,aa ba zai yuwuba shidin banza da wofi wlh saina yi baccina yau insha Allah. Koma wa tayi kan gadon tana sake wata adduar tana gama wa ta tofe ko ina ta shafe jikinta ta kwanta. Duk yadda take dambe da zuciyarta abun yaci tura,amman haka ta daure ta runtse idonta gam da tsiya sai baccin ya dauketa. Ganin babu sarki sai Allah yasa tatashi tayo Alwallah tazo ta fara sallah,saida tayi raka,a shidda sannan tadauko qur,anin ta tafara jero karatu cikin tsantsar tajwidi.........saida ta shafe akalla awa daya da rabi sanan ta ajiye ta koma ta kwanta.......dan danan baccin yazo ya sureta. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Tunda suka shigo ya wuce ya watsa ruwa sanan yyi sallar magrub a cikin dakinsa yunwa yakeji da gajiya baison yin magana kwata kwata yanzu,soyake ya kwanta yana bukatar tunani. Yasan malik inzai shigo zai taho masu da abinci tunda kukun nasu baya nan. Kasa ya kwanta yana filo da hannayensa idonsa rufe kafafunsa ya dora su bisa wani dan table,yayi crossing dinsu yana girgiza guda. _haka kawai kasa mun wannan qazamin bakin naka mai shan giya gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh.kaida Allah ban yafe ba_ Murmushi ya subuce masa mai shegen kyau,har fararen hakoransa kyawawa suka bayyana. Kafin Annurinsa ya fara b'acewa saboda kalamanta na farko. _ur highly welcome drinker guy_ Runtse idonsa yayi yana jin zafin kalamin cikin ransa,tabbas yasan ankirasa da wadanda sukafi wadanna ada bama da ba har yau akwai masu yi mashi wannan kallo,amman zuwa sadda ya rikice ya daina jin zafi da dacin kalaman shine lokacin da ya kulla damarar shanta.daga lokacin baya jin haushi baya jin radadi don ance masa mashayi.........ammman yanzu da yaji din rad'in kansa ya barta bari na har abada,sai yaji kalaman basu dace dashi ba,Allah shike ganin zukatan bayin sa amman yasan badan wannan yarinyar yabar giya ba,saidai yasan cewa kalamanta suntaka rawar gani wajen taimaka barinsa da ita,don tunda yaje Australia daya shata ma sai yayi amai kuma sai yayi masassara,lokacin ya dan gana da asibiti don radin kansa wanda shi knsa yayi mamakin ganinsa gaban likita wai ya kawo kansa,bacin kullum hanyar da zata lahanta rayuwar yake nema. Amman baisan meyasa yanzu yakejin yashirya yin rayuwa mai kyau koda shokadaine cikin duniya,yaji haushin kansa lokacin da dr yohana yake gaya masa cewar wine din takai limit din da bata kara iya daukar hunhunsa,saboda ta mashi rauni a wajen wanda muddin ya sake yasha ta ko yasha lemo mai gas yana iya rasa ransa,haka zalika ya hana shi shan abu mai zafi sosai da kuma mai sanyi sosai,don zasuyi mashi lahani........sannan abun daya sake bashi mamaki da haushin kansa wai arne da baisan kansa ba wanda bai yarda da Allah da manzon sa ba yake mashi nasihar zaman duniya,da kuma abunda zaiyyi maikyau da marar kyau. Ranar yayi kukan da tunda yabar gidan iyayensa baiyyishi ba,yayi nadama da dana sani yafi akirga,saida ya kwana biyu baifita ma aikin daya kawoshi ba. Mafarin ya fara ansar magani daga shi dr yohanan yace masa duk bayan wata uku yazo aduba shi don zai iya yuwiwa amai aiki,idan kuma yana warkewa to basai anyi aikin ba......duk sanda ya tuna wannan lamarin saiyaji kansa yana sarawa,hakika yayi sake yabari shaidan da sherin zuciya sunyi galaba akansa.meyasa abunda ake masa kallo dashi bayyi yunkurin kiyaye kanshi dashi ba,yanzu kenan da Allah bai sa ya bar sauran shaye shayen dayayi ba Allah kadai yasan abunda zai faru da rayuwarsa.da mezaice ma mahaliccinsa baida bakin da zai iya kare kansa. Hawaye suka silalo mashi yaji wata kaunar malik ta cika mashi zuciya,tabbas malik abokine na musanman duk wanda yasamu aboki amini irinsa yadace yayi dacen da har tutiya ma inyayi babu laifi. Don yasan irin wuyar dayasha kafin ya rabashi da sauran kayan mayen.sannan binciken dayasa akai mashi ya nuna mashi cewar shine ya kawo wannan yarinyar cikin rayuwarsa,don ta taimakeshi yadawo dashi daidai..........meyakai wannan arayuwa inda wanine fita sabgarsa zaiyi yaje koma me zayyi yayi aiba dan uwansa bane ko wami nashi.........wannan dalilin yasa yaji zuciyarsa tayi sanyi tayi cool dinda baisan rabonsa dajin haka ba,yaji natsuwarsa na dawowa yaji happenes dinsa cikin kaso dari kashi arba,in yana dawo wa jikinsa da ruhinsa.dalikin kenan yasa ya nuna masu canjin da suke ta fafatukar nema shida wannan yarinyar da baisan sunan taba har yau. Kuma yyi kudurin basu goyon baya har sadda zai idasa dawowa normal,insha Allah bazai sake daga hannu da sunan duka gareta ba,don tana yin komene don yaji haushi yabar abunda yake,kuma sunyi nasara kuma suna kan yin nasara. Amman alwashin sa guda daya dauka shine koda gaskiya ta bayyana tsakaninsa da iyauensa bazai sake komawa cikin zuriarsa ba,don kozai manta komi bazai iya manta wa da irin tozarcin da yafaru dashi ba shekara ta shidda kenan. Sun bata mashi suna ga duk mutanen dake masankallon nagari kuma natsatstse,tome ma zaije yayi masu baida zuciya kenan.........."Abdoul!!!" Muryar malik ce ta dawo dashi daga hayyacinsa,goge fuskarsa yayi dake ta hawaye,mamaki tsantsa ya kama malik tunda suka farazaman kansu cikin wannan gidan baitab'a ganin hawaye afuskar saba sai yau.kallonsa yake sosai yana idasa shigowa cikin dakin ya zauna yana ajiye takeaway din daya shigo dashi. Alfah tashi yayi zaune yana tankwashe kafafunsa irin zaman nan nacin tuwo,bai kalli malik ba ledar yajawo yana budewa don yunwa yakeji sosai. Bai kallesa ba yace"i need water pls." Tashi yayi yaje yadauko mashi cikin firg dinsa dake cikin dakin. "No pls bani marar sanyi in akwai." Kallonsa kawai yake yace"Kaoda baka shan ruwa marar sanyi." Hanunsa yasa yana shafa fuskarsa zuwa gashin sajensa konace kasumbarsa data kwanta tayi lub yace"yanzu kuma inso." Komawa malik yayi yadau ko mashi ya dawo ya tusa si yana son tamayarsa kukansa amman yasa ba zaishi ba shi ansa ba. Ruwa yasha kadan sanan yafara cin kazar dae ciki don bai iya cin shinkafar zata saka cikinsa nauyi,gashi yakwana wajen biyar bai motsa jikiba duk ba yajin dadin jikin. Saida ya cinye kazar an tas ya idasa shanye ruwan yana adduar gama cin abinci kasa kasa. *Alhamdulillahil lazi ad'a amana wasa qana waja alana muslimin.* Duk yada yayita ciki ciki hakan bai hanaa malik yaji ba. Shidai yau Alfah duk ya zamar mashi wani daban,Alfah da baison ma katusa shi gaba inzaici abinci,kuma bai magana ko kadan sannan bai tabajin koda wasa ya yi wata addua ba. Ko salla ya gama zai tashine kurin inya gama tazbihi,baya rokon komi. Amman yau shine da adduar gama cin abinci!lallai akwai wani abu,wannan aikin asu shida fiyah bai kai har hakaba, Yana gama wa tashi yayi ya hau wani abun exercises yana yi,don abunda yaci ya narke yaje ya kwanta. Gajiya yayi a kallon da alik yake mshi yace"man what's happen" Ajiyar zuciya yasauke yana sake kallonsa yau Alfah ke tambayarsa meke damunsa gaskiya lamarin azimunne. "Katai ka kwanta kagaji kila,ko kabar yi mun wannan kallon" Cewar Alfah Malik kamar jira yake yace"ba dole nake kallon ka ba." Bai jiyoba yace"dana yi me kenan?" "Uhmm kaima kasan abunda kakeyi wai shin wani abune yafaru can da bazaka iya gaya man ba saidai kazauna kayita rusa kuka" Saukowa daga kan machine din gudun yayi yana kyalkyala dariya malik hangame baki yayi yana kallonsa cike da rudani,after six years saiyau Alfah yake dariya. dariyar ma irin wadda tun taletale yakeyi. Saida ya gajiyace mashi"ni ake rusa kuka malik,na lura kafara koyon karya wajen wannan marar kunyar yarinyar,ols kace mata tadaina koya maka karya babu kyau." Toilet yashige donyin bush yabar malik da saki baki galala.......(nikau ace maza dao sauro ya atayaciki🤣🤣) gajiya yayi da zaman ya fita yabarsa shima ranar yajima bai bacci ba,yana mamakin lamarin Alfah kamar wani mai aljanu. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Wayarta dake ta ring ta tasheta daga baccin bayan sallar asubah data koma. Tana murtsike ido tatashi badan baccin ya isheta bata lalubo wauar bata ma tsaya kallon mai kiran ba ta dauka. "Assalamu alaikum" Cewar fiyah da muryarta cike da bacci. "Wa alaikumussalam,sorry na tasheki daga bacci" Ciro wayar fiyah tayi don ganinwsye sunan zakiyya data gani yasata idasa wartsakewa. "Aa ba komi wlh ai gara ma dakika kira intashi haka nan ashe ma har shadaya tayi inanan ina bacci." "Aikuwa dai tayi,dama.kira nai ince maki don Allah kozaki zo mu hadu tun jiya da muka rabu awaya kin barni cikin tunani wlh." Mik'a fiyah tayi tana salati tace"zuwa karfe nawa kenan?." Tace"arond 4:00" "Okay ba damuwa kimun text din wajen da zan sameki saina zo karki damu ba wata matsala babba bace,inhar kin bani hadin kai yadda ya kamata" "Kome kenan dai sister sai kinzo." Ta kashe wayar saukowa tayi ta shige kewaye . Wanka tayi tay brush ta dauro alwallah harta mance rabonta dayin walha. Shirya wa tayi tana tunanin yau wayayi masu karin safe don ita bata masan yadda ta kaya ba bayan sallar asuba data dora masu ruwan wanka,tasan dai ta dawo daki kila daga nan bacci ya saceta b'arawon banza shida bai kunyar satar kowa. Dariya tayima kanta ta shirya cikin doguwar riga mai kyau,dirarren jikinta ya bayyana yadda rigar take dashap sosai. Turare tafesa dandanan kamshinsa ya fado mata arai da dramer su ta jiya kamar wata zararra ta kama dariya kafin tace"mugunbanza saina rama wlh" Wayar ta ta saka caji tabarta tarufo kofar ta fito kasancewar jibi suna yasa gidan tun yanzu da yawaitar jama,a amman ba sosai ba. Dakin maijogon ta nufa tun kan ma ta karsa take jiyo kukan princess dinta. Da sallama ta shiga tana cewa. "Mun shigesu princess wannan kuka haka kamar ana zarar ranki,Anty mekika ma haka da zafi nasan dai princess dina bata kukan banza." Wata kanwar uncle dake gefe ita da wata mata inajin kawar Antn ce tace"aikuwa safiyyah wannan princess din taki bama kukan banza ba hardana wofi yi take,tunda ita bata son uwarta ta huta bata son goyo kuma bata son adauketa azauna kijimun wana mulkin mallakar." Dariya fiyah tame tace"Uhm Anty falmata kenan don bakusan yadda Anty jamila ta ba wa mama walaba ba da ba zakice haka ba." Harararta antyn tayi tana jijjiga babyn tana bata nono tace"aikau safiyya kin cuceni da kikai fatan ta biyoki,da yesmin ce nayi imanin har nagama goyonta bata mun wannan masifar,amman yarinya tun randa tazo duniya sai azabtardani take." Duk dariya suka saka mata nan kuma suka shiga hirar kuruciyar juna suna raha saida fiyah taji cikinta naniyar kullewa tatashi taje tayi break. DA yake babu aiki daya wa ta gama duk abunda zatayi har sanwar rana ta gama ta koma daki ta dauko handout dinta tafara karatu don tasan exams is around the corner. Ta jima tana karatun kuma cikin yardar Alkah da kuma jajircewa da takeyi duk abunda take karatun yana zama,wani kuma dan dubawa zatai tariga ta rike bayanin sa tun cikin class. Ana kiran la,asar ta ajiye tayi alwallah tayi sallar sanna tafoto ta tambayi antyn idan akwai abunda za,ai tace mata"babu komi gaskiya amman fa inason kidan hadama Muhseen don wani abu zuwa anjima zaizo ko bakuyi waya yace maki yazo ba." Wani irin faduwar gaba taji ta sameta rasss ita yau ita tashiga ukunta ,wai wanna kaddarerren mutumin bazai shafa mata lafiya ba,wlh ita fa bata son sa. Yak'e tayi tace" kai anty nafa sani Amman bai gaya mun time din da zai zoba gashi xanje yanzu makaramta xan anso hand out don exam tataho zuwa next week insha Allah." "Yace sai dare inhar bazaki dade ba ai har kinje kidawo" A haka suka rabu tafice don inba haka tayi mata ba balbalin masofarta ma sai ya hana fitar. Mrs bbce. Mom muhseen [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........25 Tana fitowa sukai cibis da yaya Jalal shida wani abokinsa sunxo ganin baby,wani duka kirjinta yayi don wlh yana iya hanata fitan ma gabaki daya. Kallonta yake Sama da kasa cike tuhuma,ita Kau banda yak'e babu abunda take,ta gaida abokin nashi ya na tambayarta baby tana ansa mashi cikin kulawa. "Yaya ashe zakazo nai zaton yar taka ma bazaka zo ganinta ba." "Ina zaki haka da yamma?" Bazata banbanta karyar da tayi ma Anty da wadda zatayi ma shi ba ana iya samun Matsala,."yaya na gaya ma Anty zanje makaranta kasan exams tataho shine Zan anso handout in fara karatu." "Salan kikai dare,naga take takenki kafafunki sunfara sanin gari kin iya yawo." "Bazan Kai dareba yaya Amman don Allah kakara man kudin taxi wlh basu isata wannan." Kafinma yafiddo abokin yaciro Dari biyar yabata,godiya tayi mashi sosai sannan suka shige. Wucewa tayi itama tana murmushi itadai ai hankalinta ya kwanta tunda tayi nasarar ficewa,text din data turo mata babujima ta shiga dubawa. _ina nan magic land,inkinzo ki kirani saina zo na shigo dake._ Dandanan ta tari taxi ta gaya ma shi inda zai Kai ta,jingina tayi da kujerar da take tana tunanin hikimar daxatayi Mata anfani da ita wajen shawokanta harta gaya mata abunda take bukata,Amman muddin taji gaskiyace zatafada bawai karyaba dole zata kunna recording,don shine abumafi sauki damutun zaiji yayarda dakai,Yakuma yi amanna da cewar wancen bashida laifin komi sharrine na mahassada. Duk da cewar abunda take shirin fadan tanajin faduwar gaba kuma tana tsoron faruwar wani abu,Amman dolene tayi hakan don shine hanya mafi sauki data dace tatunkari zakiyyar. Amman harga Allah tana tsoron wani abu guda dayake mata yawo cikin kai,wata xuciyarce takegaya Mata "inaruwanki safiyyah,kedai ba burinki gaskiya tafito ba to inaruwanki da duk abunda zaifaru tsakaninsu." Ajiyar xuciya tayi tana jin wani zuka cikin kirjinta,duk da haka dai batason hakan ta kasance. Har bakin Kofar shiga wajen ya sauketa ta salameshi ta fito, Kiranta tayi awaya saigata ta fito,wannan ne karon farko da tahadu da ita.....gabanta taji yafadi ganin zakiyyar kyakkyawar gaske duguwa Mai dirarren jiki,gaskiya dole Alfah take rikicewa akanta,aman tana tantamar idan gaskIya tafito tabbas wannan tsuhuwar soyayyar zata iya tashi. Wani lugude taji kirjinta yayi Mata saitaji haka kurin tana tausayin kanta,murmushi shimfide akan fuskar zakiya Wanda ya sake bayyana ainahin ruwan kyanta,Amman kuma azahiri safiyya tacewa zakiyya kauban wuri Amman saboda wani abudake ranta yasa ta kasa tantance itada zakiyyar waye yafi wani. "Assalamu alaikum." Zakiya tafada tana mikawa fiyah hannu. Cikin rashin kwarin jiki ta na mata yake ta mika mata nata hannun tace"Wa,alaiki salaam,zakiyya muazzam ko?" Cikin Fara,a tace"haka yake sunan,muje ciki to nima har kinsanar dani naki." Jerawa sukai suna tafiya hakanan zakiyya taji fiyah ta kwanta mata arai,Ku ma ta yardarma ranta bazata cucetaba. "Ai tun ranar dana kiraki nafada maki sunana kindai manta ne" Cewar fiyah dake kusada ita tana kallon wajen gwanin burgewa. "Ohhh anyi haka,Amman wlh na manta kasancewar abubuwa sunmun yawa." Fiyah tayi murmushi tace"haba aiba komi kasancewar ki amarya aianama amare uziri hidima ce tayi masu yawa." Dandanan fuskar zakiyya ta canza,yanayinta ya canza sosai harta kasa cewa fiyah komi akai. Tun anan fiyah taharbo jirgin,zarginta ya tabbata cewar zakiya bata son auren Alh kwangila,to meyasa zata auresa.? Wajene ta tanadar masu Mai tsananin kyau da burgewa,kuma wajen is save zasuyi maganarsu cikin sirri babu Wanda zaijisu ko yasa musu ido. Zama fiyah tayi tana ajiye jikkarta agefe,ta tsurama zakiyya ido tana kallo tana sake karantarta tsaf. Zakiyya zaman tayi itama Amman gabaki daya fuskarta ta canza babu wannan walwalar da tazo da ita afarko. Hannu tasa tana dafeda fuskarta natsayin wani lokaci kafin ta iya dagowa tana cewa cikin sanyin murya. "Bari akawo maki a bun ta'bawa ko." Cikin kulawa tace"Aa zakiyya,kibarshi har nakoma gida ban bukaci wani abunba,yanzu dai ga pos dinki duba kiga komi dakika San yana ciki yana nan yadda yake." Murmushin karfin hali tayi tana cewa"bama sai na duba ba nayarda dake gani nafarko dake,nasan bazaki cuceni ba." Murmushi fiyah tayi tace"karkiyi saurin yarda dani taya kikasan bazan cutar dake bah." Ajiyar xuciya zakiyya taja tace"nasan ki ai,sunanki ne kurin ban rikeba Amman yadda nasan gidan dakika fito ya tabbatar mun bazaki cuceni ba,duk da ganin danayi maki baiwuce uku ba." Cikin mamaki fiyah "inakika sanni." Dariya tayi tace"nikinga banzanyi mamaki ba da kika sanni,dafarko nayi lokacin dakika kirani,Amman ganina dake yasa mamakin yafita,don unguwa daya ba wasa bace gidanku yana opposite danamu kohar yanzun kina mamaki." Jinjina Kai tayi tace "nabar mamakin yanzu ai" Shiru sukai fiyah tana jinjina halin kirki da rashin wulakanta mutane irin na zakiyya,Sam batayi Kama da yangidan masu kudin dasuke wulakanta Wanda sukasan kasansu Yakeba. "Kince zamuyi magana dake,tundaga ranar hankalina baisake kwanciyaba har yanxu,sonake naji abunda kikeson muyi magana akai." Sadda Kai fiyah tayi tace"inhar kinyi amanna dani cewar bazan cucekiba, zakiyya kiyimun alkawarin cewar duk abunda nake da bukata zaki fadamun gaskiya." Kallonta take tana nazarinta kafin ta iyacewa"mezai hana,ai koda kingujeman gidanku bazai gujemun ba,balle nasan ba zaki yi abunda zasakani cikin damuwa bah." "Karkiyi saurin cawa haka zakiyya,don kuwa abunda nazo dashi zaijefaki cikin damuwar da wata kila kinyi bikin binneta cikin ranki,abunda nazo dashi zaifama maki wani ciwo da kikatabaji cikin ranki,Amman Ina maitabbatar maki yadda na fama makishi haka insha Allah zanwarkar maki dashi ki bani yardarki da kuma amanarki." Cikin dokantuwa dason jin abunda fiyah tazo dashi zakiyya tace"kin sakamun kwadayin jin wannan lamarin,koma miye nayi maki alkawarin baki yardata dakuma amanata,nabarmaki wuka da naman,don nayi imanin kinfini sanin yadda zakiyi dani." Gyara zama fiya tayi tace" I know kinsan *ABDOULNASSER MUAZZAM CANJI*" wata irin razana da gigita ce tashiga zakiyya,yayinda dandanan kwalwarta tashiga yomata tariyar duk abubuwan dasuka wuce abaya,tsawon shekara shidda kenan. Dandanan idonta yawanke fuskarta DA ruwan hawaye,zuba kawai sukeyi babu kakkautawa........har lokacin idonta yana kan fiyah hannunta tasaka tana rufe bakinta,Wanda kukan dake tahowa zai iyajawo hankalin mutanen wajen Kansu. Fiyah batayi yukurin dakatar da ita ba don so take ta yi kukan tagama sannan sucigaba da maganar. Kwantar da kanta tayi bisa table din wajen tana kuka sosai maitaba zuciya,magana take cikin kukan ta na cewa"Ina kikasansa?Ina kikasan indayake rayuwa don Allah,hakika yau kin tayarmun da mikin da kullum nake dannesa cikin raina,Abdoulnasser shine duk wani farincikina shine duk wani burina,Zan iyace maki magabaki daya shine jigon rayuwata............Amman rana guda lokaci guda komi yawargaje komi yalalace,yabarni nabarsa alokacin damuke tsakada tsananin dokin juna da bukatar juna. Abdoul shine haskena dake haskaka duniyata,shine Wanda idan inacikin duhu yake haskakamun gabana.Amman nawayi gari babushi banajin muryarsa,ba ganinsa wani abunma dazai tuna mun dashi Ana kokarin ganin annesantani dashi........kiyiwa Allah da manzonsa kigayaman wajen Da ABDOUL yake.inason sa hargobe bazan iya daina sonsa ba.koda naman jikina za,ayanka zuciyata bazata dakata daga tunaninsa ba,shiyasa sukayanke mun hukincin da ko inso kobana so dole zanbar Abdoul...........kuka yaci karfinta. gabaki daya jikin fiyah yayi Mata wani mugun sanyi,kwalla sukacika idonta natausayi. Zakiyya Ashe ba tamanta dashiba,hargobe tana nan tana dokon kaunarsa,tana renon soyayyarsa taya ni Safiyya Zan iyaceto da wadannan masoyan masu tsananin begen juna. Na tabbata yadda zakiyya take cikin wannan yanayin na shauki da begensa haka shima yanajin wannan feeling's din,saidai taurin xuciyarsa da kafewa bazai barshi asan DA haka ba. Kukan yayi kasa sosai tana shashshekar kukan kasa kasa, Wannan lokacinne fiyah ta Fara magana cikin natsuwa da furta kalma dalla dalla. "Sunana safiyyah kabir El-ladan wadda mutane sukafi kira da fiyah...........ta zayyane Mata tas tushiya mafarin dawa,daga lokacin da ta hadu dashi sanda akaban keshi tatasho makaramta,zuwa sanda sukai rigima da feea da mafarin shigarta rayuwarsa komi ta zayya nema zakiyya,wadda kukanta yadawo sabo jin halinda masoyinta abun kaunarta yake ciki. "Nasha wuya,konace inacikin shan wuyar akan lamarin Alfah.don yadda yake da xuciya tunkararsa wani tashin hanakine,badan Allah yakiyayeni ba zakiyya Abdul karya kafafuna zai tas.Amman nima inada tawa kafiyar idan nasa kaina Abu,shiyasa duk abunda yakemun nake shanyewa,tunda har malik yajure abunda yake yi nima naji Zan jure.saida nafetsare idona na fitsare kafafuna sannan lamarin Abdoul Allah da ikonsa yafara dawowa cikin natsuwarsa,Amman har yanzu da saura.zakiyya banda wani buri daya wuce na maido ma mami d'anta,na dawo maki da masoyinki na dawoma Da ABBI dansa.Wanda malik yaban labarin rayuwarku dana soyayyarku,amman haryau basu san farin wannan tashin hankali ba.......da nazauna nayi tunani nayi dogon nazari naga cewar,babu Wanda Zan iyatunkara da wannan maganar na tsira saike dubada tsarin soyayyarku da kuma yadda abun yazo kema bada son rankiba." Tana kuka tace"wlh fiyah bada son raina ba,Allah shike ganin xukatan bayin sa na tabbata yaga tawa xuciyar ban so ba.........." Katseta fiyah tayi tace"nayarda zakiyya bada son rankiba Amman da saninki,kinsan komai duk wata kullallaiya da kunshe kunshe kinsani kuma dake akai,anyi anfani da karfin iko an jaki ciki kuma kin aikatan." Tana kuka sosai tace"fiyah,wlh duk hasashenki haka yake ba aikin kowa bane sai na mahaifiyata umma da yaranta,saboda kiyayyar da sukewa Abdul da mahaifiyarsa............."ya isa naji wannan zakiyya,Amman yanzu matsayin ki na masoyiya wadda Abdoul yaso soyayya Mai inganci,wace irin gudunmawa zaki bashi kasancewarsa cikin wannan halin,sannan nasan kece wadda Abban su feea zai Aura watau Alh kwangila,kuma basai na tambaye ki ba nasan bakison wanan auren akwai dalilin kullashi ko nayi karya." Share kwallarta tayi tace"bakiyi ba fiyah,tabbas aurena da Alhaji kwangila duk shirinsune shida umma ta........muryarta tayi rauni sosai tace"wlh safiyyah Ina bakincikin halin da umma tajefa kanta kuma tajefa mu,Alh kwangila dadiron umma ne Abdoul ne ya tab'a ganinsu sau daya,mafarin suka Fara shirya masa tuggu.daman ga kiyayyar da suke mashi sai a bun ya zame ma shi biyu.Zan sanar dake komi Safiyya don kuwa nasan zaki taimaka mun,kuma bazaki Bari Abdoul ya wulakanta ba,Amman Zan so kiban lokaci zuwa jibi sai musake haduwa zanzo da abun recording kidauki duk hirarmu,koda bayan raina nasan Abdoul ya wanku mutanen dake masa kalon dan iska mashayi zasuzo suna dasun Sani." Cikin jin tausayinta tace"zakiyya mezai tsayar damu har jibin,karki manta aurenki fa sake matsowa yake." Tace"haka ne,inason binciko wasu abubuwane,domin ahalin yanzu umma a bun tsoroce safiyyah.akwai abunda suke shiryawa ita da yaranta zuwairat DA Ameenah DA haulat. Khadija ce kurin shiryayya,itama bayan barin abdoul Naringa janta da nasiha da kwatanci har nayi nasarar jawota jikina,yanzu so nake nasan mesuke shirya wa Wanda zan recording komi nabaki ajiye." Jinjina Kai safiyya tayi tace"wannan ma dubara ce,Amman inajin tsoron kar suganeki suyi maki wani abu." "Ai yanzu sun dauka na mance da komi,nashiga cikinsu,ganin na anshi auren hannu biyu ban nuna kiyayyata dashi ba,ina anso masu kudi wajen Alh sunayin yadda sukeso. Daman nashirya daukar recording komi naje naba mami mahaifiyar Abdoul.don nayi alkawarin Ana gobe daurin aure Zan gudu inshiga duniya." Sai gashi Allah ya turo Mani ke,naji dadin hakan kuma naimaki alkawarin baki hadin Kai dari bisa dari,koda Abdoul bai auran ba nayi abunda ya dace." Fiyah tace"balle ma insha Allah nadauki nauyin wanan cikar burin naki zakiyya." Kallon agogo fiyah tayi tace"inason naje na ga malik,inkoma gida da wuri kome kenan zakiyya zamuringa waya kafin jibin. Rungume juna sukai suka nufi motar zakiyar wata dankareriya tace"Alh kwangila yasiya mun,saboda farin cikin zan auresa mafarin fa yasaki matarsa uwarsu rafeea." Fiyah tace"ta gaya mun shiyasa ai na zage insha Allah aniyarsu zata koma masu." "Muje na kaiki gidan inma zansamu ganinsa." Murmushi fiyah tayi tace"zakigansa harma saikin ringa korarsa" Dariya tayi tana tukin ta na cewa"Allah ya nuna man wannan rana." Fiyah tace"Amen summa Amen tanajin wani abu yana yin raga ragada zuciyarta da ruhinta. *plssss sorry kwana biyu kunji shiru wlh banda lfy ga ciwon ido I need ur prys* Ina alfahari daku masoyan ABDOUL-NASSER ALFAH. MRS BB CE MOM MUHSEEN. 09034722970 [9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* _WANNAN PAGE DIN KYAUTANE GAREKU ALFAH FANS,KUYI YADDA KUKESO DASHI MALLAKIN KUNE SABODA IRIN KAUNAR DA NAKE MAKU_😊💞💞💃 🅿️.........26 Zakiyya ta sauke fiyah tajuya badan ranta ya so zata tai ba,saidan batasan mezata yiba kuma tafi bukatar indan komi ya bayyana sai su hadu alokacin zata gane cewar idan yana kan turban soyayyarta kobaya bisa,Amman yanzu tabbas idonsa yasauka akanta tashiga ukunta yadda taji fiyah tana gaya Mata yadda Abdoul yakoma yanzu saurin fushi dazafin xuciya. Kwallarta tashare tafurta"kayi hkr masoyina bayadda na iya da mahaifiyata muddin nace zan Saba Mata ratuwata zata lalace,hakika nayi kuskure abaya da har bari akai anfani dani wajen lalata maka rayuwa Abdoul,Amman yanzu kam ko hakan zayyi sanadiyyar rayuwata wlh saina bayyana gaskiya domin maidomaka da hasken rsyuwarka daya disashe,Abbi yana cikin tashin hankalin rashinka Abdoul,bazai dai iya fitowa fili yanuna ba,don bala,in umma bazai barshiba.nayi imanin cewar duk randa kasan cewar abunda Abbi yayi maka bayacikin hayyacinsa zaka mashi uziri,zaka hucedaga kullatarsa dakai.insha Allah muddin Ina numfashi cikin ikon Allah komi zaizo ya warware." Hawaye takeyi natausayin kanta DA shi kanshi abdoul din. (Nikau nace bakisan YAN ALFAH FANS suna can suna kare maki tanadi😂😂) Malik yini yayi yana tunanin Anya ba fushi fiyah tayi ba,ganin tun safe yake nemanta baya samun ta. Soyake yabata hkr da abunda Alfah yayI mata airport,kartun yanzu tace tagama aikin bacin akwai saura,duk da ganin cewa canjin da Alfah yazo dashi maigirma ne bai dace tace zata barsa a haka ba,zaiso muhimmin al,amari maigirma yawanxu cikin xukatansu,abunda yaketa ma fafutuka kenan don ahalin yanzu baiga wadda tadace da Alfah ba bayan safiyyah.Amman yaga babu hakan tattare da ita to balle shi da Idan yabotsare babu mai iya daidaitashi bayan itan. Gajiya yayi da kwanciyar yatashi yayi wanka San an yawuce masallaci,don Alfah tun bakwai da rabi na safe yana company. Yana kan hanyar dawowa daga masallacin ya hango kamar tsayuwarta,wani dadi ya kama shi ganin dagaske itance tana kokarin kiransa,murmushi yyisaddakiran yashi go mashi dauka yayi yana cewa"nayi tunanin kinyi fushi qanwata" Sautin murmushinta yajiyo yana kallo fuskarta data Kara yin kyau sosai. Jiyai wani iri cikin ransa,inama baiyyi alkawarin hadasu da amininsa ba,da babu abunda zai hana yayiwa kanshi kamu,da ace sannan kwanakin dasuka wuce da tsotsai yasa salon da yake mata ya Kama ta tuntuni,to tabbas a bun nasu zaijuye yarikide ya koma zazzafar kauna,Amman saita kibashi hadin kai Wanda shi kanshi hakan ya burgesa ba macen da za,akamace da wuriba........."yaya malik inata magana ko baka nan,gashi nazo maka da labari mai shegen dadi." Ajiyar xuciya yasauke yana murmushi yace"oh qanwata a u serious." Tana dariya tace"yes yaya malik,I'm serious,kayi nisa ne." "Gani nan bayanki ai" Juyawa tayi tana rike da wayar ga kunnenta. Tana ganinsa ta ya mutsa fuska kamar karamar yarinya tace"kai yaya malik,shine zaka cinyemun dan katina." Dariya yayi yana nufar kofar shiga gidan karamar yana cewa"abu mai sauki ba samarinki na nan ba ai saisu sakamaki wani." Binsa tayi ciki tana cewa"uhm,kai kasan wasu samari yaya malik,Allah yasa wannan dan giyar baya nan kasan har yanzu tsoronsa nake karfin haline irin nawa." Dariya yake Mata yace"naga alama ai,Amman ai kina kokari ko ni bana mashi tsage tsage kamar yadda kike mashi,kinga kuma ai muna samun cigaba" Yau wani part din daban suka shiga shima yasha kayan more rayuwa,don yafi yi mata kyau sosai akan wancen data tab'a shiga. "Zauna qanwata mezan kawo maki tukun?" "Uhmmm,barshi yaya malik sauri nake ance Karna yo Dare kasan yau muka hadu da zakiyya." Dalalo idonsa yayi yana kallonta cike da mamaki"dagaske kanwata?Allah yasa komi ya tafi lafiya lau" Gyara zama yayi yana saurarenta.jikkarta ta zuge ta did do wayarta tana cewa"ai bakina ma bazai iya baka wanan labarin ba yaya malik gara in kunna maka kaji da kunnenka." Ta fada tana danna wayar don gano recording din datayi dasuna magana da zakiyya,har taci Sa,ar ganoshi takunna mashi ta kure ma shi volume.........muryoyinsu suka fito tar cikin speaker wayar,kanajin komi dalla dallah har kukan zakiyya data keyi gashinan Kamar gabansa take yinsa. Shiru yayi yakama habarsa ya rike cike da mamaki da al,jabin abunda yakeji bakin zakiyyar,har Zuma karshen tattaunawar da sukai ya gama ji yana kallon fiyah,shi tsabar iya Lauya maganarta da Ku ma kaifin tunaninta yake mamaki,yajin jina kokarin ta don kau ba kowane zai iya wannan dubarar ba balle yatsaro irin kalamanta,yasan tahada dawayau da dubara harta yarda da ita ta kuma bata amanarta.duba da yadda zakiyyar tayi saurin yarda da ita. "Gaskiya qanwata kinyi bala,in burgeni naji dadin wannan lamarin ba Kadan ba nake gaya maki Allah yayi maki Albarka yakuma baki miji nagari wanda zai kula dake har illa masha Allah." Sadda Kai tayi tana murmushi aranta tace Amen yaya malik,Amman afili kasa ansawa tayi. "Yanzu kenan in share waje na zauna najiraki, komi kenan zanji daga gareki" "Insha Allahu yaya malik,Aikomi yataho karewa kasan har na k'agu na kammala aikin nan." Murmushi yayi yace"nima zanso komi ya kammala Amman kuma banson rabuwarmu dake,mun saba sosai sai nakejin kamar yar gidan muce ke." Dariya tayi batace komi batana sadda kanta,hakika kamar yadda yace sun saba haka a bun yake itama cikin ranta sun saba sosai,duk randa suka rabu zasuyi kewar juna.......koba komi yaya malik ya iya zama da mutane,ga barkwamci da Fara,a. "Yaya malik Zan wuce gida kasan har yanzu inacan wajen Anty sai anyi suna zan koma gida,Wanda daker kuma in nakoma in ringa fita inba school zanjeba." "Ba damuwa ba,arasa yadda za,ai ba muje saina tarar maki taxi don nasan baza kiso inkai kiba." Fitowarsu kenan aka bude get din gidan motarsa zata shigo,wani lugude kirjinta yake mata. Bata shirya haduwa dashiba ahalin yanzu don Sauri take shidda tayi takoma gida hakan,gashi Anty ta tsirar mata hada wani abun banza saboda wani muhseen. Tsaye sukai itada malik,ita tana tararrabin yadda zasu rabu shikuma yana murnan zai samu damar hada su. Cikin rawar murya tace"yaya malik karka barshi ya tabani wlh sauri nake idan ban koma gida da wuri ba Anty fada zatayi mun." "Ki kwantar da hankalinki bazai maki komi ba,shizan saka ya mayar dake gida yanzu." Xaro kyawawan idanunta tayi tana kallon sa cike da tsoro tace"bana so wlh so kake mutai ahanya yaje yayi cinikina wani waje aa barni infita salin alin." Fitowa yayi daga cikin motar cikin kayansa kana na masu masifar kyau,fesincap ce Sam an kansa kalar rigarsa light blue da rubutun *ME&YOU* ajikin rigar fuskarsa da walwala ba kamar yadda tayi tunanin ganinsa ba,direct wajensu ya mufo idosa akan ta hannunsa guda rike da briefcase dinsa,ya ratayota ta kafadarsa said gudan Hannun kuma yana rike da wayarsa.shan mur fiyah tayi tana kauda Kai harga Allah yayata Kyau babu karya. "Malik tsayuwar me kuke,halan jirana kuke inzo inbata giyar tasha" Murmushi malik yayi yace"Aa ita ai batasha ko sOfiyyah." *"SOFIYYAH!!!"* Alfah ya maimaita sunan cikin ransa kasan ransa yana cewa"nice name" Hanyar fita tanufa tana dalla masa harara tace"angaya maka kowa ma irin kane,mtsss!" Kankace tak Alfah ya fincikota yadan sha mur yace"ke kullum bakinki da magana ko,da alama kinsha rishin kunya kin koshi inbakiyi wasa ba Allah kinji na rantse zan danneki saina baki kinsha." Yadda ya damke Mata hannun yasa idonta yakawo kwallah cikin rawar murya tace"dallah can sakemun hannu Kai inbanda mugunta babu abunda ka iya,kaima din da gani kashata ka koshi muguntar." Sake damkar hannun yayi yana mamakin taushin fatarta kamar ta jarirai, Kara ta saka tana kwalama malik kira wanda yaja gefe yana smile, "Abdoul karfa ka karya Mata hannu." "Babu ruwanka malik kabarni na koya mata hankali,tunda ita kullum.bakinta baya mutuwa." "Wlh aka mun fada acid allah ya isana ban yafe ba,Kuma saina Kai kararka wajen Allah." Yatsa yasaka ya d'alle Mata baki yana sassauta muryarsa da gajiya tasaka tayi laushi tubus kamar fulawa. "Nima saina Kai karar taki kina mun sharri da abunda banba." Kokowar kwatar kanta take idonta jagejage da hawaye"dallah malam ka kyaleni,aiba karya akai makaba inyanzu aka duba motarka sai ansamu kwalaben giya,waya sani ma ko harda wiwi.......sake d'alle Mata bakin yayi yana guma mata goshinsa ga Nata goshin. Kuka tasaka mashi tana kiran malik,shikau yau abun dadi yake mashi,ganin Alfah yamai da abun nishadinsa. "Harda koken ma duk za,a samu Amman in har ba samu kogudaba mezan maki." Cikin jin azaba tace"ban saniba mugu azzalumi baka iya komi ba sai mugunta............kafarta yatake da kafarsa dake sanye cikin wasu combus hadaddu white and light blue. "Wayyo kafata nabani na lalace wallhi ban yafeba Allah ya isana,yaya malik kana gani ko kana gani zai karyani kace masa ya kyaleni intai gida Anty fada zatayi min,na bani kafata Hannun zai ballemun.............hakanan haji bai kyauta ba sauke kafarsa yayi ya sassauta rikon hannunta daya malkashe shi tabaya,numfashi takeja tana zubar da kwallah. Samun kansa yyi da kalonta yana kallon fuskarta data baci da ruwan hawaye,hanky dinsa yafiddo cikin aljihun wandonsa yana tsane mata hawayen......juye juye take alamun bata so yadaina,Amman bai dainan ba saida ya goge su Tas sannan yace "daga yau kisake mun rashin kunya,hamisu budemun get din nan zanfita." Ya kwalama maigadin su kira. Bai saki hannunta ba har aka bude get din,maido kallonsa yayi gareta yana dage mata girarsa guda sama yace"muje badan halinki ba na saukeki gidan" Da harararsa zatai saita fasa takauda kai tana cewa"ban so." "Ashe kau zaki kwana nan gidan,,kuma duk dan iskan kwarton ki daya biyoki nan saina guntile kafarsa alqur an." Malik dariya ya zauna kasa yanayi don wlh yau abun yabashi nishadi sosai. "Karka sake cemun kwartayena niba yar iska bace" Fizgota yayi daga jikin bangon ya nufi motar sa yana cewa"anje ance maki kwartayenkin karya akai maki wace macen kirkice zata ringa yawo gidajen maza Inba kwartuwa ba." Kuka tafashe dashi cike da kunan xuciya,wannan kalmar takwartanci tana bakanta zuciyarta,sosai take kukan tana ma malik magana"Wallahi yaya malik inbaka mashi magana ba bazan idasa abunda kakeso ba, wannan ai cin fuskane gaban ka yake zagina yana aibata ni kanaji kakasa takawa." Sai lokacin malik yataso yana daidaita fuskarsa yana son yadaina dariyar wajensu ya isa yana cewa"Itafa ba yar iska bace Abdoul kadai na cemata kwartuwa Haba don Allah." Shikanshi dariyar yakeson yi amman ya danne yasha Mur yace"oh babu dadI Keenan nida take ma sharrin giya,bazan daina ba har sai Rana data daina gaya mun kalaman da banso." "Shikenan zata daina amman saketa tatai gida dare yayi fada za aimata" Wani kallo yayi Mata yace "tashiga nakaita kasan Dai ba abun hawa zata samu yanzuba saboda duhu yafara,inba dan arxikin kaba wlh bazata shigarmun mota ba kucaka kawai." Saboda takaicin sa kasa agana tayi don ganin ma maganar kular da ita take,gashi anata Kiran salla ga wayarta akahe tasan anty nacan nakiranta hankalinta yatashi,bata san ma karyar da zatayi mata ba inta je,tsoran ta guda karta kira mama ta tambayeta kona biya gidan hakan zaisaka mama tayi tunanin yawo natai hankulansu yatashi daganan kashinta yagama bushewa wlh. Malik ya kalleta yaga duk ta zama so coll banda kwallah babu abunda take cikin tausayawa yace "kiyi hkr ya kaiki kinga kinyi dare zakufi isa da wuri akan kice zaki hau taxi ya zu,kafinma kisameta kin kara bata wani lokacin." Ba tace mashi komi ba don shima ya gama kular da ita over,bude mata gaba yayi tashiga kamar ta babbake takeji don haushi. Saida tashiga San an Alfah ya tilla mashi key dinsa yace"ban ma kaiwa kaida takejin maganarka saika kaita ba shikenan ba ." Kifa kanta tayi tana kuka tana data sanin zuwanta gidan. Binsa malik yayi da sauri yarikoshi cikin yadan canza fuska yace"Wanda yace kace kaizaka kaita shizaisa ka kaitan yanzu wlh ban kaiwa saidai takwana bisa titi," ya aje mashi key din yashige yabarsa don yasan dole zaikaitan shi kawai so take su shirya kansu. Fiyah kau ta gudirci cewa ita da sake xuwa gidan har abadan abada,cin kashin ya isa haka sai idan yasake ganinta sannan zai mata duk wulakancin daya ga dama. Fuska babu walwala ya dauki key din yawucr ya shiga yatada motar sukabar gidan. Kukanta take sosai saboda tasan yau Anty saita mata rashin mutunci. Kasa jure sauraren kukan yayi yakalleta cikin sanyin murya yace"aini zanyi kuka bake ba,amman shine don ke raboce shine kike kuka don kijaman sharri,nida ban iya kukan ba Ko" Kamar daman jiransa take tahau faa sa masifa tana cewa"Don kana ganina gidanka shiyasa kake mun duk cin kashin da ranka yake so ko,tau daga yau har gaban abada bazaka sake ganina ba balle har kaci zalina,kuma idan nace ban yafe ba kiran da karuwa da kake sai Allah yasakaa man." Murmushi yayi yana kallon waje yana son kar murmushin ya bayyana yace"gaya man inda zan kaiki kokuma na kaiki kasuwar siyar da mutane." Kirjinta yasake dukan tara tara babu arxiki tai saurin gaya mashi,sannan yadauki hanyar unguwar. hankalinsa kwance yake tukin hannunsa gudane yake juya sikiyarin dayan kuma yana shafa kansa sannan ya jujjuyashi gefe da gefe alamun dai kilan ciwo yake mashi kokuma gajiya ce ke dawainiya dashi. Baisake mata magana ba haka itama bata sake mashi magana ba don cike take dashi,don ita tashin hankalin da zata. tadda agidan shine damuwarta. Juyowa yayi yana kallonta harararsa tayi ta gefe ya miko hannunsa kamar zai tsole mata ido Mata saurin janyewa tana turo baki tana magana kasa kasa Unguwar suka shigo tafara mashi kwatancen gidan har suka zo kofar get din. wanda mutane suka tarar cikinsu har uncke yahya da muhseen sai wasu abokansu,wani rugugin tashin hankaline ya taso mata kallonsa tai shima ita yake kallo hawaye suka wanke mata fuska tace"hankalinka ya kwanta yau za,ai ferfesuna gaidanmu burinka ya cika to bari kajii muddin labarin yaje ga babana har yayi silar dana bar makaranta ta kaida Allah,wlh baxan yafe maka bah" Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️..........27 Kuri yayi da idonsa akanta,yayinda kalamanta suke masa zafi cikin xuciya,yadda take furta mashi Allah ya isa take cemasa shida Allah.jinsu yake kamar ana zuba mashi dalma cikin ransa,dandanan zuciyarsa ta hau ransa ya b'aci baiso bayyana bacin ransa ba,yaso su rabu lafiya yadda bazata rikesa ba,shima kuma daya riketan zai yafe mata idan xuciyarsa ta huce,amman ta wargaza komi bazai iya jure zafafan kalamanta akanshi ba. "Kabar kallona haka kabude mun nafita inyaso kome zasuyi mun suyi mun din........hannusa ya cire ya dalla ma fuskarta mari,idonsa yana rikid'ewa cikin muryarsa data canza amo yace"karkiga nayi sanyi kidauka ko lusari nakoma,inanan ayadda kika sanni nabarki da wannan kilan yazama silar fitar cikin rayuwata,ficemun amota ballagaza ya sunkuyo ta wajenta yana bude mata kofar wanda har gashin kasunbarsa saida ta shafi hancinta da bakinta,,,,,wani irin tsammm taji tsikar jikinra tatashi yana gama budewa,duk idon mutanen akanta. Jitake inama ta tsaga kasa tashiga dawane idon zata kallesu ga hawaye share share sun bin ta,wane kallo zasuyi mata. Bata da wani zabi daya wuce tafito,haka ta fiton jikinta a mace kafarta daya take dazun take ciwo har yaja mata d'ingisawa. Mai mako taga yaja motar ya tafi saitaga ya fito yana nufo su uncle dke tsaye suna kallonta......"nashiga ukuna mezai gaya masu,karyaje yaja mun sharri zai iya yin komi don ya bata mun suna,suna ganina da mutunci suzo sudaina,kamar ta fizgoshi takeji amman ina yayiriga ya isa har suka gaisa dasu uncle ita dai tana tsaye kamar antsamota daga ruwan zafi,innalillahi kurin take kira don itace zata kawo mata dauki. Can tajiyo muryarsa yana cewa uncle"na dawo daga wajen aiki shine tsotsai ya gitta na banketa,so sai na kaita asibiti aka duba ta ko tayi rauni,to Allah dai ya kiyaye kafarce ta dan bugu babu mummunan ciwo......tanata kuka bazata biyoni ba naga yadace na daukota don kar asamu matsala,kuyi hkr don Allah." Uncle mamakine ya kamashi ganin Alfah don yasansa sosai,friend dinsa ne lokacin da sukai karatu Spain,amman ya lura baigane sa ba. "A haba ba komi wlh ai tsotsai baya wuce rana,mu munanan hankula sun tashi anata nemanta,ga wayarta kashe abunda duk ya sake tada mana hankali kenan,ai angode Allah tunda komi lafiya xoki shige gida sofiyyah,sannu kinjiko." Muhseen da ya kafeta da ido ya isa inda take yana ansar jikkarta yana mata sannu kamar zai dauketa,idon Abdoul yana kansu har suka zo suka rabasu zasu shige. Uncle yahya yace"bazaki masa godiya ba." Kallon cikin idonsa tayi kwalla tab ga idonta tace"thank you"ta wuce mujseen na biye da ita kamar jela. Maido hankalin sa yayi ga uncle yahya suka sake gaisawa har zai wuce yace masa"kamar Alfah ko." Jiyowa yayi da murmushin karfin hali yana kallon uncle din sosai. Kafin yace"yahaiya quru!!" Dariya sukai suduka suna sake sabunta gaisuwar cike da jin dadin ganin juna,nan fa suka hau hirar yaushe rabo kamar bazasu rabu ba karshe sukai exchange din contact yatafi. Bayan shigarta gida Anty na ganinta ta ajiye babyn tana nufota cikin masifa zata mareta muhseen yayi saurin tarewa, "Haba Anty bazaki ji komi ba saidai kihau dukanta,ai ko bakiji bayanin ta ba bakin daki babbar budurwa irin wannan ba,ta wuce bugu ai" Hararasa tayi tana cewa"tare mata zakai,kigaya man gidan ubanda kika tsaya daman kin tsaranine don kitai yawonki ko,to wlh baruwana dadai irin haka gara ki koma gida yafiye mun kwanciyar hankali." Uncle yahya yashigo yasamu tana ta balbalin masifa fiyah banda kuka babu abunda take,don bayan bakincikin Alfah ga wani nan tana kwankwada,meyasa anty bata da uxiri koda yaushe. "Dadina dake bakya da hkr,ko halin data shigo ai kinduba kitambayi lafiya,amman zaki tusata da masifa haba jamila yarinya namaki abun kirki kina neman kureta,safiyya faba yarinya bace tasan kata tanada hankali,bazatayi abunda tasan ranta danaku zaibaci ba.haba wlh banson wannan halin." Muhseen cikin jin haushin bata ma sahibarsa rai da akai yace"dafa marinta zatai da ban tare ba." "Mari!jamila saifiyyar zaki mara,lallai kin kyauta ai" Tashi fiyah tayi tabar wajen cike da bakin ciki tana jiyo muhseen yana mata bayanin abunda yafaru. Bata tsaya jin abunda antyn za tace ba ta shige ta kulle kofarta,ta kudurci da sassafe zata bar mata gidanta ai hakurinta ya kure,Anty jamila bata da uziri kokadan,indai kayi abu bata jiran bayani zata hau balbalin bala i.to tunkan ta koreni nizan kori kaina,ainaga mata moriya tunda gobe suna ko." Wannan dare safiyya bata runtsa shi yadda ya kamata ba,kamar yadda Abdoul ya kwana yana cikin wani yanayi na tunani,sunanta yazauna daram cikin ransa.amman zafin kalamanta sun hana sunan yin tasiri aransa,ko kallon malik bai sake ba tun daya dawo. Sai yakoma ainahin Alfah dinsa na kwanakin baya,wani bangare na zuciyarsa yana tuno masa da wani sashe daya riga ya binne tun shekara shidda baya,saiyakejin kamar feelings na kauna da shauki na soyayya atare dashi,bawai yana yiwa wataba aa yanajinsa atare dashi yana bukatar wadda zai sharing wannan feelings din da ita amman wacece?kenan har xuciyarsa tayi sanyin da zai iya kallon mace da sunan kauna?Aa impossible nayi bikin binne soyayya shekara shidda baya,yana ma mace kallon namiji rabonda dayaji yana son mace kusadashi ko yaji yana bukatar kasancewarta garesa tun wancen lokacin,wanda yakejin kansa koda yaushe cikin shauki da mararin zamanta cikin rayuwarsa. Yau lamarin ya canza masa,kasancewarta gefensa,kukanta sautin muryarta kalamanta sun ja hankalinsa ainun wajen juyoda lamarinsa baya,wani shauki daya danne tsawon lokaci yake niyyar tasowa,duk da yadda tariga ta bata ransa ta cusa haushinta hakan bai hana wannan abun tasiri akansa ba. Mirginawa yayi yana runtse idonsa yanajin wani yanayi kamar zaiyyi kuka,amman ba kukan bane yanajin kamar yayi dariya amma ba dariyar bace,yanajin dukan jikinsa yana macewa,sannan tsikar jikinsa tana tashi salon numfashinsa yana canzawa. Filo ya rarumo ya makalkaleshi yana jan numfashi,ya tattare jikinsa ya dunkulesa waje guda,jujjuya kansa yake yana jiyo wasu kalamai da suka shude suna mashi ansa kuwwa cikin kunne,baiyyi auneba yaji hawayensa suna silalowa suna bin kuncinsa idonsa arufe amman hawayen basu fasa fitanba. Bakinsa ne yake kerma kamar zaifurta wani abu,amman kirjinsa yayi masa nauyi rubdaciki ya koma yana murtsike murtsike kamar mai ciwon ciki,saida bakinsa ya furta wannan suna ya samu sukuni. *"ZAKIYYAH!!!"* wani gauron numfashi ya sauke yana tashi zaune kansa yasa cikin kafafunsa yana zubar da kwallah. Tun bayan barinsa gida yacireta aransa,daidai da rana guda baiyi tunaninta ba bai tuno komi nata ba,baya kallon mace balle ta tuna mashi da ita,shiyasa ya yiwa mata wata irin tsana.wadda har yau yakejin baidaina tsanar suba,don sune silar jefa rayuwarsa cikin garari da damuwa. Amman yau anwayi gari shine yake magana da wata,yake hada jikinsa da wata yake daukar wata cikin motarsa.tsawon zamansa hakan bata taba faruwaba,ko dacan zakiyya kurin yake dauka duk da tarin bataliyar matan dake binsa.kusancinsa da yarinyar nan yau yasaka yaji komi na zakiyya yana dawo mashi..........cikin muryar kuka yace"why zakiya,why why me???." Wannan dare dai Abdoul haka yagansa baisamu sukuni ba saida ya karanta qur ani,sannan yasamu salama har bacci ya daukeshi. Itako fiyah kiri da muzu baccin yace baisan haka ba,tasha kukanta ta gode waAllah.don gabaki daya tarasa inda natsuwarta ta nufa,duk irin Abunda Abdoul yayi mata yau maimakon taji haushinsa kamar yadda ta dawo da abun,amman abun sai yagagareta data hangoshi sanda yake sunkuyowa yana bude mata kofa zataji gabaki daya hankalinta ya tashi,har lokacin tanajin gashinsa ga fuskarta..........mulmula kurin take agefe guda ga hirarta da zakiyya da irin alkawarin data daukar mata cewar zata mallaka mata Abdoul dinta zata dawo mata da soyayyarta.to taya?ta tanbayi kanta wata xuciyar tace ta yadda kika ansa mata ta haka zaki yi kihadasu ki sasanta su. Ga haushin Anty ga na Alfah amman jitake na Alfah baikai na Anty girma ba,duk da kalamansa sun take na antyn girma da munu aman ta kasa ganin bakinsu ayanxu,sabanin lokacin dayake gaya mata su. Tun daren fiyah ta gama hada akwatinta,don data gama abunda xatai saidai ta nemeta ta rasa shikuma wancen muhseen din ya gaji yabarta,inma don yabata wayace aiba rokonsa tayi ba bakuma zata bayar ba,kwata kwata baya cikin shirginta. Zuciyarta tace mata"to saiwa yake cikin shirginki?badai Abdoul din dakika gama yiwa wata alkawarin hadasu ba?" "Mtss mezan da dangiya nikau safiyyah,ai inajin ko maza sukenan shida muhseen bana son su bana aurensu gara na mutu ahaka." Still xuciyarta tace"inkince Abdoul dan giya ne shikuma muhseen mezai hana kisoshi?" Dirkowa tai daga kan gadon tana cewa"ohh ina ruwanki ne kirabu dani don Allah." (🤣🤣🤣) Zaman dirshen tayi kasa tana tagumi. Tunani ta shiga yi daga sanda ya fito daga mota dawowar da yayi daga office,shigarsa tayi kyau rubutun rigarsa ya dauki hankalinta *ME&YOU* lumshe ido tayi tana silalewa kasa ta kwanta bia tayils din dakin. "Nida kai ko,uhmmm saidai idan kaida zakiyya" Idonta alumshe tana tuna sanda yake tsane mata hawayenta,kamshin turatensa mai shegen shiga kwalwa ya kasa barin hancinta.komi nashi mai tsadane. _kuma duk dan iskan kwartonki daya biyoki nan gidan saina guntile mashi kafa alqur,an_ Ta tuna maganarsa sanda tace bazata bisa amotar sa ba, "Wanan Kalmar ta kwartanci tana mata ciwo,wai shi baya ganewa ne meyasa zaimun wannan zargin,wlh Abdoul niba yar iska bace ban shigo rayuwarka don komiba saidon ina tausayinka,saidan na taimakeka ka koma cikin ahalinka,amman meyasa ka kasa fahimta. kenan da haka zaka saka mun.koda yake bana bukatar sakayyarka ladata tana wajen Allah,kuma duk abunda kayimun na yafe maka Allah yasani bana gaya maka wadansu maganganun don karan kaina kaine kakeja,kuma duk don in nuna maka cewar abunda kake babu kyau ba halin kirki bane shan kayan maye,addinin mu yayi hani,Haramunne akwai zunubi mai yawa ina maka fatan shiriya Allah yasa wahalata bata tashi abanza ba." Afili duk take fadar haka kwallah na mata zarya afuska,ta rasa dalilin zubarsu.abunda tasani kawai shine tana tausaya mashi hakan rashin uwa da rashin uba da yan uwa dayake ciki,kowa daya sansa baya mashi kallon mutumen kirki. Shafa kuncinta tayi inda ya mareta dazun cikin mota, Lumshe idonta tayi amman kwata kwata bataji zafin marin ba,cigaba tayi da shafa wajen tana jin haushinsa yana bajewa cikin xuciyarta tausayinsa yana maye gurbin haushin nasa.duk ta duka takare tunda nayi alkarin bazan sake xuwa gidanku ba zangani idan inda rana kokuma banda ita. Shin rashin ganina zai dameka ko bazai dameka ba tsaki taja jin wata xuciyar tana cewa "ke awa zai damu don bakizo bakenan kin saka wani abu aranki game dashi" "Ohhhh niban saka komi cikin raina ba Abdoul na zakiyya ne nace maki ko" (😄😄fiyah ta zare aradu) Haka wannan daren ya kasance wa safiyyah har asuba,kuma kokadan ta nemi baccin tarasa tashi tayi taje tayi sallah sannan ta dora ma maijegon sanwar ruwan wanka,sannan ta koma daki tana karatun kur ani. Sanda gari zaifara haske tashiga ta hada break miyar kwaice da kabeji tayi musu da ruwan tea mai na,a na,a da lemon grass sai citta da kanun fari kamshi kurin yake,ta soya dankalin turawa sannan ta hauda ferfesun naman kaza bata so aikin ya kaita ga takwas ba,shaf shaf ta yi nata break din tayi shara da mopping bata tsaya wanke wanke ba ta dauki akwatinta tayi get. Karo sukai da muhseen ya shigo gidan, Tsaki taja cikin ranta tana mitar "ko ubanme yazo yi tunda uwar safiya" "Ah fiyah ina zuwa haka tun da farar safiya." Yake tayi mashi tana gaidashi. "Gida zanje na kai kayana anjima kadan zan dawo." "Oky to muje na kaiki daman break nazo nayi wajenki tunda kuma baki nan shikenan" Don dole take murmushin tace"ah wlh kashiga kayi ainariga na gama hadawa,bazama zanyi ba gidan" Ansar akwatin yayi yana yin gaba yace"no muje kawai ai ganinki ma yasaka naji yunwar ta tafi idan na kaiki saina dawo nayi." Ya zatayi da shi da alama wanan naci garai kamar magan disu. Shiga tayi gaban motar tana yaba tsarinta da kyanta,gashi sai kamshi take. Zagayowa yayi yashiga yatada suka dauki hanya. Duk sai tajita atakure shikau jiyake yau kamar amashi bushara gashi ga safiyyan sa,cikin janta da fira yace"ko sannu da zuwa bakiyi mun ba safiyyah." Saitaji bata kyauta ba cikin kunya tace"sorry pls andawo lafiya" Murmushi yayi yace"no karki damu aike bakya laifi safiyyah,nayi hkrin kuma nadawo lafiya fatan kuma na sameki lafiya." Ya ta iya dashi dole ta sake tana ansa mashi hirar tashi."komi lafiya yaya muhseen" Cikin kwarewa yake jan motar yana sarrafa sikiyarin yace"Amman sanda na tafi Anty bata baki sakona ba" Wayar hannunta ta kalla tace"wannan?" Girgiza kai yayi yace"no ba wannan ba,i mean bata yi maki wata magana akaina ba" Sai yanzu ta gane inda ya nufa, Girgiza kai tayi tace"Aa gaskiya kilan ta manta" "Kokuma kece kika manta ba,don munyi magana da ita sosai har idan muyi waya wani lokaci tace ashe muna waya dake ban gaya mata ba,to kasancewar nasan kingaya mata ne don kitsira daga masifarta yasa nima nake kokarin kareki,sai kawai nace mata eh munayi sosai ma.Aman tambayata anan safiyya itace meyasa kika mata karya." Shiru tayi tana jin kunyarsa na kamata,hakika muhseen yana da kirki kuma duk wasu qualities da ake bukata ga namiji ya nadasu kawai dai kowa da nashi ra,ayin itadai bai mata ba batajin zatayi soyayya dashi balle aure. "Kayi hkr" Abunda tace dashi kenan. "Ba maganar nayi hr bane kinsan me?nifa In my life duk abunda zanyi direct nake yinsa,kuma duk abunda yake raina ina fadarsa don idan nafadan ina samun saukin xuciya,don haka babu boye boye tsakanina dake inasonki kema kuma kinsan ina sonki kawai dai kilan ban maki ba shiyasa kiketa yimun hanya hanya,kin ban wuya.watana uku abuja ina godalan inganki muhadu in sabunta soyayyata amman kikakiya safiyya,aman saboda ina kaunarki bazan iya fushi dake ba gani na sake dawowa,don haka bazan koma ba sai kin gaya mun abunda kike nufi dani." Gabanta yafadi gaskiya bazata iya kallon cikin idonsa tace masa bata sonsa ba,kuma bazata kwari kantaba tace tana sonsa bayan kuma ba haka abun yake ba. Na bani yazanyi da shi. "Karki damu kanki u have enough of time da zakiyi tunani don zan jima ban koma ba,amman kafin kigama nazarin nawa zan iya zuwa wajen baba don neman izinin zuwa zance?" Wayyo tashin hankali ba,asaka mashi rana,muddin maganar taje ga baba shikenan bata da miji saishi,don inbazata manta ba haka akai da uncle yahya da Anty. YAZANYI NI SAFIYYAH? (TO FOYAH NA NEMAN MAFITA ALFAH FANS KU WARWARE MATA YADDA ZATAI,KO YAN ZAUREN MRS BB) MRS BB CE MOM MUHSEEN. [9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........28 Tsare ta yayi da ido bayan da sukai parking kofar gidansu,sadda kai tayi tace"kaban lokaci zan yi tunani" Relax yayi jikin kujerar yana shafa kansa yace"yanzu neman izinin zancen ma fiyah saikice sai kinyi tunani,gaskiya zaki wahalar da zuciyata,kenan bazan zo zance ba bacin ko awaya bama gaisawa." "Aa yaya muhseen indan wannan zamu ringa waya amman kabar maganar zuwa wajen baba yanzu saina shirya don Allah." Ajiyar heart yayi yac"shikenan na hkr amman gaskiya idan naji bazan iya jurewa ba saidai kiji sallama nazo zance." Ansar no din ta yayi yana zuwa ya bude mata sannan yafiddo mata kayanta daga cikin but,godiya tayi masa ta wuce cikin gidan kadan yahana ta banki baba dake tahowa zai fita. "Ah baba yi hkr ina kwana" "Safiyya kece tunda uwar safiya haka,yo ya akai naganki da kaya kamar wacce tayo yaji." Sadda kai tayi tana jin kwallah na zubo mata,ansar mata akwatin yayi yana cewa sushiga gida tau. Shiga sukai mama dake shara cikin gidan kaji ta fito tana ajiye tsintsiyar,biyosu tayi cikin gidan yesmin na ganinta ta rogo ta rungumeta. "Nayi kewark Addata,ya su Antyn ya kuma babyn." Daker take ansawa yesmin ansoshinta baba yace"yanzu mukai karo zaure naganta da akwati natambaya kuma ta fara kuka,shine nace tashigo ciki tayi mana bayani." Mama ta iso tana zama gefen fiyah dake matsar kwalla,ita masifar da Anty tayi mata ce tasaka tayo yajin,don baiyyuwa tana mata bauta amman bata iya mata uziri. "Safiyya dake nake magana nace meya faru keda jamilar?" Kuka ta saka tana gaya mata abunda yafaru jiya"mama Anty kullum bata canzawa da yaya muhseen bai saurin tareta ba duka na zatai fa,yanzu mama ban wuce duka wajen anty ba ai nai zaton zata tambayeni dalilin dadewata." Baba ya shafa kanta yana lallashi yace"jamila bata kyauta ba kuma nima gara dakika dawo bazan yarda ana cutar mun da uwata ba,yesmin kaimun akwatinta daki ko sunan ba kizuwa." Mama tace"Ba ayin haka babansu,komi jamila tayi wa safiyya ai kanwarta ce kuma yanzu saita baro gidan sunan tataho nan sabida Allah,idan banda yaya balaraba da yaranta wagareni dazan tura ya kama mata inaba dan safiyyar,komi tayi maki aibakin baro ta kitaho nan ba,kayi hkr anjima inta huta saita koma,kuma zanyiwa jamilar fada ita daman matsalarta kenan shegiyar xuciya da rashin uziri,haka dai yahaya yake fama nasani." Kuka na saka ina murje murjen kafafu nace"nifa mama kiyi hkr,sokike inje tayita hantarata wlh Anty ta kara lalacewa da masifa duk hkr na yau ta kureni alqur an." Murmushi baba yayi shida yesmin mama tace"haba Ansafiyyan mama kiyi hkr yanzu ma zan kirata nayi mata fada,aibakin barota ba kiyi hkr anagama hidimar ni daso nai ma kizauna har tagama wanka." Kukana nake ina murzar ido yesmin sai dariya take mun. Kafinma mama ta dauko wayar kira yashigo tace"kingani ma itace take kira." "Wlh mama idan bata bani hkr ba bazan koma ba" Bata kulata ba ta dauki wayar baba yace"zata baki uwata kwantar da hankalinki." "Yanzu jamila sakayyar da zakiyi mun kenan?na turo diyata don ta ragemaki wahala shine kika saka hannunki mai albarka zaki mareta,bacin ba dagangan tayi ba" Cikin rudewa jamilar tace"don girman Allah mama kiyi hkr wlh banyi da niyarr zalintarta ba hankalina ne yatashi har bayan magruba babu fiyah,shiyasa amman kiyi hkr bazan sake ba na tashi banganta ba naje har dakinta inlallasheta don nasan fushi tayi na iske bata nan,sai muhseen yake gaya mun shine ya kawota gida,kiban ita inbata hkr mama" Dayake hands free wayar take kuma mama duk dan fiyah taji yasa tasaka, Murmushi tayi jin za,a bata hkr baba dai daroya yayi yana cewa"uwata ko yar rigima kin iya rikici wlh,nidai natafi Saina dawo sukai mashi Allah ya kiyaye mama ta mikama fiyah wayar. "Hello Safiyya,kina jina." Cikin sunburar baki tace"eh Inajin" "Haba yar kanwata kiyi hkr kinjiko,wlh rudewa ce ta sani haka tsoro naji kar wani abu yasameki,amman insha Allah bazan sake ba don Allah kidawo kingani ma ga inna balaraba nan duk sunzo suna tambayarki harda hasana da umaima" Murmushi tayi tace"to zan dawo ya sunan princess dina" Dariya jamilar tayi tace"uncle dinku yace bata cancanta da kowane suna ba sainaki safiyyah,don haka ina maki murna kinyi takwara." Wani ihu ta buga tama tashi tana taka rawa "yeeee wlh naji dadi ngd Anty ganin zuwa yanzu zandawo wlh na huce wanan albishir ya wanke xuciyata mama kinji princess taci sunana yesmin kinjiko." Kashe wayar jamila tayi tana dariya,rigimar safiyya sai ita. Nan suka shiga murnan sunan yesmin tace"nikuma next sai asaka namu nida mamana(kasancewar sunan su guda hurairah) Dariya mama keyi tana jin dadin yadda yaran nata suke son juna suke kuma yiwa junansu uxiri tare da fahimtar juna,Allah ne yabata don kam yaranta babu mai halin banza kullum takai goshinta addua take yasa ta aurar dasu fiyah lafiya. Yesmin tace "ga yaya dalha can zai fita bari yatai dani idan natsaya jiranki Adda zan bata lokaci zanje na gano sabuwar Addata." Dariya fiyah tayi tace"saina taho"tasige aki tana hayewa kan gdonu tayi missing din sa kwana biyu. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Tunda garin Allah yawaye bai iya fitowa daga dakin saba tunda yadawo sallar asuba,yau saboda farin cikin ganin Alfah masallaci malik har da kwallarsa,yana godewa ubangijinsa daya taimakesu har Alfah yafara daidaita,yasan ko ahaka sunci riba kuma suna godewa Allah yana kuma godewa fiyah. Abdoul nacan yana mulmula akan gado yarasa meke mashi dadi,furucinta yake tunowa najiya. _aidan kana ganina gidanka shiyasa kake cin zalina ko,to nida sake zuwa nan gidan har abadan abada_ Cusa hannunsa yayi cikin sumarsa yana ya mutsata huci ya furzar,baccinsa da yarasa jiya yakeson maidawa amman tazo tayi mashi tsaue bakin xuciya taki fita ita kuma taki shiga, "Meyasa zakibar xuwa kiyi hkr bazan sake cutar kiba kidawo ga wanda kike xuwa gidan donshi nasan shima bazaiji dadiba laifin zai dora bisa kaina" Saukowa yayi yana layi kamar yasha mutuniyar sa, ya shiga bayinsa ya sakarwa kanshi ruwa mai sanyi sosai. Saida yaji sanyin ruwan har cikin ransa sannan ya kashe shower ya hada ruwan dumi ya shiga,lum yayi yana lumshe idonsa sai yatuna da wani lokaci sanda yake tashen barje soyayyarsa shida zakoyya. _qalbina yanzun nafito wanka banga kiranka ba wlh sorry_ _murmushi yayi yace"karki damu nour dina,fatan dai kin wanku sosai"_ _dariya tayi tace"uhm qalbi mekake nufi?nifa tun ina yar shekara goma umma bata sake mun wankaba,kuma wlh ina fidda kaina sosai don baka ga yadda ruwa yake darewa ba shikanshi soap din saida yace kikyaleni haka zakiyya_ _dariya yayi sosai yace mata "gaskiyane nayarda ta tunda har soap dakanshi yayi magana,amman kinsan watarana dakaina an sabeki na nadoki cikin towel"_ _"qalbi kunya nakeji wlh kadaina_ Numfashi yasauke yana sake lumewa cikin ruwan,zafin zakiyya da yakeji bai hana jin wani tsohon mikin kaunarta ya taso mashiba. "Kin cutar da rayuwata kiyyah,kin jefa rayuwata cikin qangin da bazan iya taba mancewa ba,bantaba tunanin zan iya dawowa irin haka ba,amman rana guda lokaci guda tashigo rayuwata shin mekike tunani zakiyya?inajin zafinki fiye da yadda wuta zata gona hannuna,haka inajin tausayin wannan yarinyar fiye da yadda nake jin tausayin kaina,ina son yimata sakayya akan sadauar da rayuwarta da lokacinta da jikinta akaina,amman banson wane irin sakayya zan mata ba..........nocking din kofar sa da ake ya kaste masa zantukan dayake yi afili cikin sassanyar lafazi da kwantar da amon muryarsa,inkaji zakai tunanin cewa yanantare da wani ko wata. Wanke jikinsa yayi yafito yana daura towel ya fito. "Lafiyarka Abdoul najika shiru baka fito ba gashi ankirani kanada baki office"................... *fatan zakuyi mun uxiri,wlh saboda yadda naga kunayin book din nan yasa na takure kaina nayi maku wannan kuyi manage dashi zuwa gobe idan Allah yasa munkai da rai da lfy,ina alfahari daku 100% ngd da adduoin ku gareni* Mrs bb ce Mom muhseen [9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........29 Kallonsa yayi na yan seconds ya dauke kai ya cigaba da tsane gashin kanshi dana fuskarshi,gaban mirrow din dakin nasa yayi burki yana dauko hand drayer ya jona yana busar da gashinsa,kamar ba mutun adakin bai niyyar cewa komi ba saida ya gama,malik ya zuba mashi ido yana kallonsa kafin murmushi ya kubce mashi. "Yau kuma azumin magana aka tashi dashi?" Mai yake shafawa ya kallai sannan yace cikin lallausar muryar shi "saidai idan azumin dole kake niyar tirsasani,tunda ko ruwa baka ban ba da safen nan,sai yanxu kake shigomun kana mun wani zance dabam." Ajiyar xuciya malik yaja yana zama saman gadonsa yace"sorry sir,me kake bukata to" Uffan ba ce mashi ba yaciga ba da abunda yake,kamar maijin tsoron fatar tashi haka yake shafa man. Fita malik yayi yaje yadauko mashi break din daya ajiye masa a falo tun goma na safe. Table yaja ya ajiye masa yana mashi nuni da break din. "Gashinan ranka yadade" Dan murmushi yayi kadan yace "tare dakai" Kaya ya fiddo suit farar shet da farar coat sai black trozer wanke su yayi da turare sannan ya hau sakawa,yana satar kalon malik zuwa can yace masa. "Karkaga wanan yarinyar bata zoba ta riga tace ba zata sake dawowa ba" Cike da madaukakin mamaki malik yace"wani abun ka sake mata ahanya ko?" Kafadarsa yadaga yace"daman nayi zaton haka zakace,toni ban mata uwar komi ba sarkin zargi" Murmushi malik yayi yace"saika shirya anjima muje ban hkr" Zaro kyawawan idanunsa yayi yana kallon malik yace"bcos?" Murmushi malik yayi yace"bcos of u,u Abdul kaine kaja har tayi wannan furucin,safiyyah yarinyace mai hakuri da kauda kai,yadda kake tunaninta ba haka take ba,she is innocent girl kaine ka kure hkr rinta shiyasa tunjiyan zuwa yau banga kiranta ba,nasan arina don haka kashirya anjima tonight zamuje dakai har gidan antynta." Dariya yaji Alfah nayi yana shan black tea har dariyar taso tea din ya zubar mashi ga kaya,ajiyewa yayi yana kallonsa kafin ya girgiza kai yace"u mean zan raka ka zance kome kake nufi,ina ruwana da zuwa bata hkr ainine ma zata dawo ba hkr saboda nitayiwa rashin kunya,imagine ta kallan tana furta mun Allah ya isa and nida Allah for what reason,inba sokake kasaka na zane ta cikin gidansu ba ajiye wannan maganar,suwaye bakin dake jirana office" "Shikenan na ajiye maganar amman bada na barta ba,i don't know KO suwaye sai idan munje inson ma inje nagaida daddy kozaka" Hararasa yayi yana cigaba da break dinsa. Tare suka fita amman kowa cikin motarsa,malik ya wuce store don duba halin da yake ciki sanan suyi lisafi afidda albashin ma aikata na wannan watan. Alfah kuma ya wuce company don haduwa da bakin nasa. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Suna yayi kyau mutane da dama su xo cikinsu kau harda momin feea takanas tataso daga katsina tazo sunan,don suna yi sosai da mama cikin estate din duka mutum biyu sukaje ma mama suna gidan Jamila. Fiyah kau anacan ana hidima da baki bakinta har kunne tayi takwara,suna tare da hasana sa,ata ce baifi one year dake tsakaninta da fiyah ba,umaimaice suke d same years. Dakinta suka sauka sunata hirar yaushe gamo,sai idan baki sun zo sufita su zuba masu abinci don ma ga inna balaraba da wata abokiyar wasansu da ta iso daga can garin su baba dutsi.inda mamanshi mai sunan fiyah take xaune. Suna yayi kyau sosai anraba jakunkuna da hoton little safiyya,sunan da takwarar tata ta zaba mata kenan. Zuwa magaruba kowa ya wuce gida sai su inna dasu hasana daketa faman gyaram gida,duk yinin yau fiyah zuciyarta bata da sukuni jitake matakin data dauka na daina zuwa gidan kamar bazata iya aikatashi ba,daga jiya zuwa yau wani irin yanayi take tsintar xuciyarta aciki,amman tayi iyakar kokarinta wajen dannewa,don ma gwamace wajen boye damuwa. Wayarta duk yau nata kunna ta ba,balle ma malik ya kirata yayi mata dadin baki,saida gidan yazama need sanan su inna suka tafi,amman anbar hasana don washe gari su kama ayi soye. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Malik bayan yadawo daga wajen dady yayi mashi bayanin da zakiyya tayiwa fiyah,yace komi kenan in sungama tattaumawar idan da bukayar yashigo ciki sai yazo ya gaya mashi. Office ya wuce wajen Abdoul don ya yi alqawarin koyanaso kobaiso sai sunje bikon fiyah,don yakira wayarta yafi sau goma amman anar gudace wayar kashe take. Gaidashi ake tayi tunda yashiga company har ya samu isa office din Alfah,wanda saika rantse wata duniyace daban saboda yadda yatsaru iyakar tsaruwa. Aiki yake kan compute ga bako kuma suna magana dashi,ciki ya wuce can cikin kiryar office din don har wani madaidaicin gado ke akwai. Bayan ya sallame mutumen ya biyosa har cikin dakin ya samai yayi shame shame yana shan iskar AC. "Ince dai lfy?" Shan mur malik yayi ya cakude fuskarsa yace"zuwa nai na daukeka idan anyi sallar isha,i zamuje bikon safiyyah" Tsaki yaja ya na juyawa zaifice b'igit malik yayi ya sha gabansa babu walwala afuskarsa alamun babu wasa yace"Alfah kabar wannan abun,dagaske nake saimunje dakai aikaine musabbabin komi yarinya tana maka abun alkairi........shiru yayi baison tona abun dasukeyi. Kallonsa yayi yana shafa sumarsa zuwa kasumbarsa yace"metayi mani na alkairin?zagin nawa kokuwa rashin kunyar,aa kila kirana datake dangiya shine abun alkairin,kaga ABDOUL-MALIK karka janyo muyi rigimar da muka jima bamuyi ba nace bazanje ba final" Ganin shan mur dinsa baiyyi nasara ba yasa ya saki fuskarsa don yatabbata idan ya matsanta zai rikice mashi ne. "Kaga sorry Alfah,kayi hkr ka rakani to ba dole ma sai kunyi magana ba nizaka raka don Allah." Cure hannunsa yayi daga kafadarsa ya fice yana tattara abunda zai dauka malik yafito ya daukar mashi jikkar system dinsa,yana cewa"muje yallabai ai kai hukumane saida lallashi" Bashiri dariya ta kubce mashi ya jefesa da biron hannunsa,sukai dariya sannan suka fito sakatarensa ya rufe office din. A mota guda sukatai Abdoul ybar tashi nan company,malik babu abunda yake mashi dadi irin canzawar Alfah lokaci guda,duk da yasan bazai taba dawowa kamar wancen lokacin ba,amman kaso sittin daga cikin halayensa sundawo saidai saurin fushin da ya zame masa jiki yanzu wanda ya hade da zafin xuciyarsa,shima nan gaba idan komi ya daidaita yana saka ran fiyah zata gyarasa,inhar Allah yasa suka daidaita kansu. Shiyake ta mashi hidima tunda suka dawo tunda ga kan ruwan wanka tea dayake sha idan ya fito,kayan sakawa daddare jansa da hira yana sashi ariya baishirya ba. Wasu riga da wando ne ya fiddo masu masifar kyau,don tunda yadawo daga Australia bai saka suba kuma suna daga cikin sabbin kayan sa daya dawo dasu. Wandon ruwan kasa brown amman light,sai rigar coffee brown mai hannun links,ya feshesu da turare yana murmushi,tabbas yasan fiyah ta ganshi yau duk kauda kanta saita rude,don ba yabon kai ba abokinsa karshene wajen kyau da daukar wanka. "Wai saikace wanda zaije zance?" Dariya malik yayi yace aransa kacanko daidai amman afili sai yace"aa nidai zaka raka nayo bikon qanwata,nasan fushi tayi dani tunda har yanzu her phone is switch off." "U hmm" "Don Allah yallabai karkace bazaka rakani ba,nikadai ban iya zuwa,ban san gidan ba" "Uh zanyi maka kwatance zaka gane" "Ohhh rankayadade wlh nafison muje tare plsssss kaimun wannan alfarmar" Kafada yada ga yace "is okay zanje" Wata kara ya fasa yana daka tsalle murmushi Alfah yayi yana nunasa da hannu"u malik" Fita yayi shima ya je yashirya suka fita sallar isha,i zanso kuga yadda kayan nan suka hau Alfah,kamshi kurin yake bugawa kamar wani sabon ango. Bay a sunyi sallar isha,i masallaci sannan malik yafiddo wata jibgegiyar car,wadda sai Alfah yayi wata bai hauba,daman suna dawowa yasaka maigadi ya gogeta don ma rufe tae ba kura tayi sosai ba. Sanan suka dauki haya Alfah na son fesin cap ita yasaka bisa kansa,ya rufe idinsa da ita,imagining yake yadda haduwar tasu zata kasance,zaiso yaga wadannan idanuwan nata kamar anzuba oil aciki suna daukar ido yaga ya zasuyi,murmushi ya kubce mashi kodawace fuska zata anshesu,yasan shidai mai laifine bama lallai ta kallai ba,amman bazaije yadawo bai saka idonsa cikin nata ba. Malik kamar anzuba mashi kankara cikin rai ganin yadda aminin nasa yake cikin annashuwa,alamar dai fiyah ta samu wani waje ta zauna aransa. Munata fira bayan mungama ayyukan mu Anty na can itada umcle yahya suna kallo falo,nida hasana da princess dina muna dakina muna ta hira da daroya,amman har cikin kokon raina banjin dadi,wata irin kewa nakeji wadda banson menake ma kewar ba.saina dauko wayata da niyyar kunna wa saina fa saboda nasan yaya malik zai neman.ikuma so nake na nuna mashi nayi fushi suduka susan babu wani abu cikin raina balle in har nabar zuwa inda suke wani yazargi bzan iya hakanba.princess dake mamulan hannu na kalla hasana kuwa ansa waya take,saukowa nai na nufi falon don anata mama tasha. "Anty little yunwa takeji,tun dazu fa baki tua da ita ba" Ansarta tayitana cewa"keta gado shegen tsotso,don haka da wuri zan fara bata cerelac ko priso." Uncle yahya dake ansa waya ya harareta naji yace"ok Abdoul saika iso" Kashe wa yayi duk sai naji na zargu wane abdoul din kenan,koda yake ai basu san juna ba kuma bata zaton zai iya zuwa yadda yake jida kansa........"safiyya wanda ya bankeki shekaran jiyane zaizo dubaki jeki gyara falon saukar bakin don Allah." Wucewa nai jikina yana wana irin sanyi,xuciyata banda zillo babu abunda take,ni narasa wannan sabon yanayi nawa.Anty naji tana tambayarsa"waye kuma haka uncle,badai da biyu xaizo ba don ni nariga nayiwa kanwata miji" Dariya yayi yace"inma da uku yazo jamila miye naki,ita mace ai Allurace cikin ruwa mairabo yake dauka,kuma shi abokinane sosai rabuwarmu tun school yasa abotar ta rushe,banda wani good friend banda shi,kuma dashi da muhseen babu wanda nake ma bakin cikin samun safiyya,don kuwa duk wanda yasameta zanyi murna su duka duk nawane,kuma kowane babu na banza cikinsu abunda zakiyi mata kawai shine addua da fatan alkairi" "Uhm,shikenan amman ni gaskiya ina bayan muhseen kuma zan cigaba dayi mashi canpen" Wucewa nai inajin zuciyata tana karkarwa,wai waye yace dasu wannan arrogant din yana sonta,shi wannan wacece ma zata soshi inbanda zakiyyar,yadda yake dashegen miskilanci da fadin raiAllah yasawake mun auren dangiya. Mrs bb e Mom muhseen. [9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........30 Gyaran falon tayi cike da rashin kwarin jiki,bawai don gajiya ba,eh to akwai gajiyar ma amman kuma zuwan Abdoul wajenta shine dalilin dayasa jikinta duk ya mace murus. Turaren wuta ta saka ta kuma kunna tsintsiyar kamshi,saida hayajin ya gama bud'e dakin sannan ta dauko freshner ta sake sawa,ta gyra labulbulun falon yayi lum gwanin sha,awa ga hasken kwan nefa farin haske da blue sai red green dake haskawa.fitowa tayi ta iske su cikin falon uncle yana rike da little fiyah suna hira da Anty. "Kishiga ki tanadar masu abunda zasu ci ko hakanan xasu zo sutai." Ya mutsa fuska tayi tace"Anty ruwa ma kadai ya ishesu" Harararta tayi uncle yace"haba dai fiyah,bakonka annabin ka jeki falona akwai snacks din da muka rage dazun da friends dina suka zo,basu ci daya wa ba sai ahada masu da lemo ko" Ba yadda ta iya haka ta juya taje ta dauko taje kitchen ta zuba su cikin wasu bowls,Anty tace akwai ferfesun yan ciki data saka akai mata dazun,tace ta dibar masu . Kamar zatai kuka tace"wai Anty saikace wani shugaban kasa ne zai zo" Kallon banza tayi mata tace"dalla banson sakarci,mutun baitaba zuwa inda kake ba yau zaizo kuma sai bazaka tarbeshi da kayan motsa baki ba,ni indan tanine wlh bamson zuwansa,don inajin kamar da biyu zaizo yana iya amshe ma muhseen kunerarsa. "Anty wai ance maki muhseen dinma wani sonshi nake,nifa wlh kawai don ba yadda zanyi dashine,nifa ba yanzu zanyi aure ba" Dungure mata kai tayi tana wucewa tabara. Bayan ta gama shirya masu abun da zasu bukata ta koma daki,samun kanta tayi da yin wanka hasana tace"bako zakiyi ne fiyah" Shafa take yi cikin mutuwar jiki "Wanda ya kadeni rannan zaizo dubani" "Kice daya kadeki sai kuma yayi wuf da xuciyarki" Murmushi tayi tace"waye yace maki,shi baya soyayya ai" Dariya hasana tayi tace" naga waliyyi,karewar baya soyayya bari dai mugani ni nasan badubiya kawai zaizo ba harda banruwa zaiyiwa flower sa." Dariyar da bata shirya ba tayi tam cigaba da abu da take. Uncle ne yafita jin karar mota gaisawa sukai sosai da Alfah da malik,sun jima a harabar gidan kafin yyi masu iso.hira suke da malik kamar sun saba,indai malik ne badai iya hira ba koya kahadu dashi zakaga ya jaka ajiki dandanan zaku saba baida bakunta. Anty ta wuce can ciki. har cikin falon ya sauke su suka cigaba da hirar,sai daga baya ya fito don kiran safiyyan. Simple make up tayi powder da lipstick sai kwalli,tasaka rigarta coffee brown da zanen milk color ajikin rigar,sai tayi rolling da milk din gyale tana fesa turare. "Safiyya kifito haka nan sun iso,hasana ki rakota saiku gaisa ko" "To uncle insha Allah" Kasa motsawa tayi ita wai dawace fuskar zata tarbi wannan mutumen,kuma ma dame yazo ne wai. "Kika zauna kuma ko gabanki yake faduwa ne?" "Kice bashi kadai ya kamu ba ace kema yayi carab dake," Murmushi tayi tana mikewa tace "muje" Tana tafiyar gabanta yana faduwa har xuwa bakin kofar shiga,togewa tayi hasana ta jata suka shiga da sallama..............idon malik akan su yana cikin kujera,hasana cikin fata ta nemi waje ta zauna tafara gaisa malik. "Kece yar rakiya kenan,ya kike yagidan" "Lafiya lau wlh anzo lafiya" "Alhamdulillah ansha suna Allah yaraya me akasamu" Dariya tayi tace tana nuna fiyah"gata nan itace aka samu" Cikin murmushi d mamaki yake kallon fiyar yace"iyye qanwata ashe takwara akayi," Murmushi tayi mashi bata ce uffan ba,hasana ta juya ga Alfah tana gaidashi,banyi tunanin zai kar mata fuska su gaisa ba. "Lafiya lau ya kike kunsha suna Allah yaraya" Cike dajin dadi ta ansa tana tambayarsa aiki. Malik ya ce"qanwata baku gaisa da abokina ba" Kamar karta kallai suna ta hira da hasana cike da wayewa da sanin makamar zance,kallonsa tayi sosai taga irin yadda yayi mata masifar kyau,har ta shaga da kallonsa saboda yadda kayan suka ansheshi,ga hasken dakin dake haskawa sai hakan ya karawa fuskarsa kyau. "Kinga yar uwarki zata cinyeni da kallo bacin ko gaidani batai ba"Alfah ya cewa hasana. Dariya duk suka saka mata wadda jitai kamar ta nitse don kunya,wai garin yaya ma har ta shagala da kallonsa haka. Sadda kai tayi tana murzar yatsunta hasana tace"kinji to fiyah,baki gaida bakon naki ba." Kasa magana tayi wai meza tace mashine itafa bazata gaidashi ba,malik yace"qanwata harni ma din bazaki a magana ba" Bata kallai ba balle ta tanka,hasana tace"kila fa kunyata takeji,kinga bari nabaku waje sai anjimanku fa mun gode" Sallama tayi masu ta wuce,malik yace"tunda ko ruwa baza,abani ba nibari nayi karanbanin dauka insha." Sai lokacin tayi saurin tashi tana ajiye wayarta ta matso da tabke din gabansu tana bude kwanukan tare da zuba lemukan acikin cups sannan ta zuba ruwa shima,dauka tayi ta ba malik cikin sanyin murya tace"kayi hkr yaya malik ga ruwan,don Allah kudan taba wadannan don ku Anty tayi" Ansa yayi yana cewa"ainayi hkr qanwata kece za,aba hkr don nasan fushi kike damu,tun jiya wayarki akashe meyasa?" Satar kallon Alfah tayi taga idonsa akanta ya shige cikin kujera yasaka yatsa guda yana sosa girarsa. Dauke kai tayi tace"ba haka bane yaya malik kawai dai nayi hakane don a barku kuhuta don naga alamar xuwa wajenu danake ysa ake cin xalina ake yimun ugunta ana gaya man aganganu babu suger" Malik yakalli Alfah yaga har lokacin fiyah yake kallo kamar zai hadiyata.har cikin ransa tayi masifat yi mashi kyau,amman bakinsa yayi nauyin da bazai iya furtawa ba,bayajin ma koda wasa zaiya furta hakan amman yadda tayi mashi yasa yaji wani abu yatsaya mashi ga makoshi,babu sannu da zuwa babu ina wuni babu karramawa.malik ne yace "Kiyi hkr to insha Allah baza akara ba,,ga Abdoul nan ma yazo taya ni baki hkr ko Alfah" Yajuya yana kallon Alfahn. Tashi yayi zaune yace"hakurin me zan bata bacin nida ba,a dauka da mutunci ba ko ruwan ba,a bani ba bae nasaka ran zan samu sannu da zuwa kaga kuwa zuwana baida anfani,kaida keda mutuncin da har za,a kulaka kana iya zama zanjira fitowarka." Ya mik'e ransa ab'ace don har cikin karshen ransa fiyah ta kuntata mashi,badan yaso yataho ba amman shine zai samu wannan tarbar. Dandanan taji hankalinta yatashi,haushin kanta ya kama ta bazata so yatai da fushinta ba koba komi bakonta ne,tara sa gane kanta zuciyarta rawa take inhar tana sauraren muryarsa,idaniyarta bata hutawa inhar yana mata wannan kallon,takaza control din kanta akan wannan sabon yanayin data kejin kanta,cikin sanyin muryarta tace ma malik. "Yaya malik kace yayi hkr yadawo wlh niban wulakanta shiba" Murmushi malik yayi yace "aa aibani nayi mashi laifi ba qanwata kece don haka kibishi kibashi hkr kafin ma kidawo bari naci wannan yana jawo kwanon snacks." Jikinta amace zuciyarta ta cushe bata son yatai da fushinta harga Allah bata so ransa yabaci ba, Kallonta yayi yace"kije mana" Kamar Mai tausayin asa tatashi tafara nufar kofar fita,dariya yake son yayi amman baison tagani. Waigowa tayi kamar zatayi kuka tace"yaya malik karya dakeni,karya zuciya ya mun tsawa." Girgiza mata kai yayi yace"bazai maki haka ba kidai bashi hkr kisamu yadawo ya ci wannan garar don wlh yamun dadi sosai maza jeki" Haka ta bude kofa ta fita aikamar jira yake ta fitan ya dunga kwasar dariya,lallai tarkon nan yayi kamu sosai,insha Allah komi zaizo da sauki. Yana cikin mota ya kwantar da kujerar zaman banza ya kwanta ya rufe fuskarsa da fesin cap di sa. Jikinta wani irin sanyi yayi ahankali ta kwankwasa glass din window din,tunda ta tsaya kamshinta ya iskoshi jiyai xuciyarsa na mashi kai kawo,ahankali ya sauke glass din baiyi magana ba baikuma dago ba,lawallar kuda ta kamayi tarasa abun cewa bakinta rawa yake wana mutun yana ata kwrjini cikin kwana biyunnan. "Sauro yana shigo mun inbakida abun cewa plss zan rufe glass dina" Bakinta yana kerma muryarta kamar zatai kuka tace"pl....s kayi hkr.....karka tafi kadawo don Allah" Wani sanyi dabai san daga inda yake ba yaji yana sirarowa cikin ransa,amman sai yayi shiru yana adduar Allah yasa ta sake bashi hkr karta tafi. Bata san dalilin hawayenta ba muryar na rawa tasake cewa"plssss kaji,im sorry........"maganar ta katse sanda kukanta yake fitowa Wani suka yaji ga kirjinsa jin muryarta na fidda sautin kuka,ahankali ya tashi jiyake kamar anzare mashi duk wata lakka daga jikinsa muryarsa kamar tafito daga cikin frig yace"come in" Ahankali ta zagaya wajen zaman driver ta shiga kanta akasa hawaye na bin fuskarta,tunda yake rayuwarsa bai tabajin kwatan kwacin irin halin dayakeji yanzu ba.koma wa yayi ya kwanta yanajin wani irin yanayi na sake bin gabbansa. Ahankali take sharar kwallah,inza,a yankata bazata iya cewa ga dalili ba. Hanky taga ya miko mata babu musu ta ansa tana kaishi ga fuskarta,wani kamshi ne ta shaka daya saka taji duk wani kunci na xuciyarta yaya yaye,ahankali take share kwallar har ta samu kwallar ta tsaya. Sannan ta mika mashi bai ansa ba yace"nabar maki" Tanajin yadda xuciyarta take bugawa numfashinta kanshi ya canza salon fita, Kamar mai koyon agana tace"kazo muje kayi hkr ko lemun kasha don ku akai" "Danshi dai,ni awa za,ayi abu danni daman ban saka ran samun tarba daga gareki ba saboda baki daukan mutun ba" Juyowa tayi duk da ba ganin fuskarsa take a tace"amman ai nabaka hkr ko" Murmushi yayi yace"baimun ba kije kawai ngd kin baroshi shimadai bacin dnke yazo" Kamar zata rushe da kuka tace"plsss mana kayi hkr to" Malik ne yafito shida uncke suna hira cikin fara,a duk sai taji ta kunyata. Fitowa Alfah yayi itama ta fito tana jin kunyar uncle tasan dole zai dauki wani abun,tunda gasu acikin mota su biyu. "Tunda kunya ta hanaka cin kayan tarban bakon Abokina gashinan na saka an yimaka takeaway dashi,don Allah karkace bazaka ansa ba tasha wuya fa wajen hada maka" Duk uncle ne yake wannan maganar. Kanta akasa malik ya isa inda take cikin kasa da murya yace"qanwata kuka kikai mashi" Tabe fuska tayi kamar zatayi kuka tace"kai yaya malik shine fa........kasa magana tayi tana sadda kai" Dariya malik yayi yace"qanwata gaya mun meyayi maki yasaki kuka" Kasa ansa shi tayi don bata san ma me zata ce mashi ba. Hanyar shigewa tayi zata shige gida uncle yace ah safiyya bakiyi sallama da bakon naki ba,xokuyi sallama aimun gama maganar." Sake musabaha sukai dasu yakoma cikin gida yana cewa maigadi idan ta shigo arufe gidan. Malik tuni ya shige mota yana jiransu kasa motsawa tayi daga inda take saidai shine ya isa inda take,ta juya baya ya tsaya daga bayanta. Tsayuwarsa yasa taji kamar ta koma kankara saboda wata irin mutuwar jiki tasame ta. "Goodnight amman karki manta banyi hkr ba,zan tai da cewar nazo kin wulakanta ni saboda..........juyowa tayi kadan yahana ata fda kirjina ba tayi saurin dan ja baya, "Don Allah..........lumshe idonsa yayi yana girgiza kai wanda kadan yahana numfashinta bai kare ba. "Goodnight" Haka yabarta kamar anshuka ta har motar tabar kofar gidan sannan ta samu karfin guiwar daga kafarta tashige. Wannan dare xukatan mutane biyu basu huta ba. Mrs bb Mom muhseen. [9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........31 Washe gari da wuri suka gama soyen raguna uku,zuwa karfe biyu na rana sun gama dan ma Suna da dan yawa kuma kasko uku sukai,duk yadda fiya take kwari kwari saida Inna balaraba da Anty jamila sukai mata magana ko bata da lfiya,saboda yadda duk ta zama sukuku,bacin sun santa da kazar kazar da yawan magana wani bin. Tun safe take tsammanin wayar zakiyya amman shiru kuma ta kirata bata samu ba,duk saitaji gabanta yana faduwa Allah yasa ba wani abunne zai faruba,haka taita tsammanin kiranta har karfe uku na rana. Daker ma taci abincin rana kadan kadan ta duba wayarta taga ko zata ga misscall amman shiru. Saida akai sallar la,asar ta sallame kenan taji karar wayar zunbur tayi ta jawota Kosallama batakai dayi ba taji muryar zakiyya tana magana cikin tsananin tashin hankali, "Fiyah........kina ina fito yanzu fito don Allah ki saman hanyar shoprite.......babu lokaci kifito don Allah akwai babbar matsala" Jikinta ya dauki karkarwa tace"ganinan zakiyya kiyi kokarin boyewa biyoki akai ne" Muryarta da alamun kuka take tace"eh biyoni sukai gasu nan bayana ina cikin mota na samu waje na lab'e kiyi sauri bari na turo maki inda zaki saman." Kashewa tayi tatashi zunbur ta canza abayarta ta suri wayar tafito falon. Anty na kitchen ta sameta tace"Anty don Allah zan fita bazan jimaba,result dinmu na islamiya zan ansa feea tace yau ake rabawa kuma basu bada na wani,don zasu tantance wadanda zasuyi musabaqa" Kallonta take kamar zata karyata ta amman kuma bata hujja, "Shikenan,amman safiyya don girman Allah kiyi kokari kidawo da wuri,banson kiyo dare nafison kina kusadani" "Insha Allah bazan ba" Fita tayi cikin hanzari saita dawo ta duba jikkarta tadauki kudin taxi ta sake ficewa cike da fargaba. Duba kwatancen tayi tasanar da mai taxi din ya karya kwana ya nufi wajen,suna shiga wani lungu ta hangi mota tsayw wajen,tunaninta ta zakiyyarce don bata sanar da ita kalar motar da take ciki ba. Sauka tayi ta sallami mai taxin ta nufi motar,kwankwasa glass din tayi aka sauke shi idonta akan wani bakin mutun fuskarshi babu kyan gani,shikadai ne cikin motar ja baya tayi tana rawar murya tace"kayi hkr nai zaton yayana ne yace mun yana kusa da nan" Kallonta yake yana zaro ido yace"bar nan kafin ina farka cikinki" Babushiri na yanki hanya amman jikina yaban akwai wani abu,labewa nai wani sakon gida ina leken motar wani katon mutun yafito daga wani gida hannunsa da wata jikka ta mata,yana fitowa daga gidan na hangi faduwar mukulli baisan ya fadi bama shi,shiga motar yayi ya jima sannan sukaja suka bar wajen. Saida na tabbatar sunyi nisa sosai na dawo da sauri na dauki key din,nashiga kofar da zata sadani da gidan don kofar babu marfi. Mukullin nasakana shiga bude gidan jikina ko ina rawa yake,daker ya bude na shiga gidan da gani andade babu kowa cikinsa. Kiran wayar zakiyar nayi tana ringing bata dauka hankalina yasake tashi,sako da lungu na gidan nashiga kewaye wa Allah baisa naga kofa mai irin mukullin hannuna ba,fitowa nai nayo hanyar fita naji alamun tsayawar mota jinai fitsari zai kubcemin.........wata mota da take ajiye ta lalace na kurda kasanta na kwanta gabana banda faduwa babu abunda yake,zuciyata kamar zata fito waje haka nakeji. Motace aka shigo da ita daga baya naga an fizgo mutun abayan motar idona akan kafafun mace,hankalina yasake tashi don tabbas raina yaban zakiyya ce.yadda take nishi da gurnani daji bakinta suka dade..........rawa kurin jikina yake bakamar jin danai wani yace"da alamun fa wani yashigo mu jefa shegiya can dakin muduba mugani." Dayan yace"nifa wannan yarinyar ban yarda da ita ba duk zargina tare suke" "Aa ban tunanin haka kamota mugani,shegiya zaki yi magana ne inkikaji ukuba,saikin fadi inda kika ajiye memory din nan" Wani daki dake bayana suka bude suka sata suka jawo suka rufe da kwado. Dube duben gidan kawai suke Allah bai basu sa,ar ganina ba,sannan suka fita nabada tsawon lokaci sannan nafito ina rawar sanyi duk da ba sanyin nakeji ba. Leka wa waje nayi naga basunan na koma ina b'ab'are na samu katon dutsi naringa bugun wannan kwad'on yana waigen bayana karsu dawo su saman. Nasha wuya kafin na samu nasarar balle kwadon. Shiganai dasauri itace kau kwamce daker take numfashi,cikin sauri na cire plaster da aka rufe mata baki,ashe bayan ma plaster saida suka cusa mata soso cikin bakin. Tari takamayi tana rike da wuyanta, "Tashi maza zakiyya bamuda lokaci,koda ace munyi asarar memory yazama dai ke bamuyi asararki ba,"daker tatashi muka fito janta nake daker muka fito duk arude nake,karar motar da mukaji abayan mu bayan fitowar mu daga cikin yasa ina juyawa muka hada ido da daya daga cikinsu,zakiyya tace cikin nishi "muruga fiyah yaya mamman ne karmu tsaya,idan suka kamamu bazasu barmu da rai ba." Tunkafin na idasa jin mezatace na fizgeta muka fara falfala gudu,yayinda suka rufa mana baya don insukace su shiga mota zamu bace masu. Gudu muke wanda tunda nake bantaba irin saba,zakiyya tun bata iyawa har ta zage itama damun ga sun kusa cin mana saimu sake himma...........wani gida dake bude muka fada muka labe bayan kyauren kofar,muna lekensu suna dube duben wajen. Jinake fitsari zai kucce man zakiyya durkushewa tayi kasa tana rufe bakinta,don nishi take take sosai karsujimu. Sun jima sosai wannan wurin har muka sadakar da bazasu tai ba sannan suka tafi. A gajiye suka fito suka yanki titi kamar zasu fadi kowa cikin su ya gama galabaita,zubewa sukai bakin titin suna maida numfashi. Xakiyya numfashinta sama sama yake daker tae fizgoshi,riko hannun fiya tayi daker take iya magana tace"fiy....ah.......kikira wani yazo ya taimakemu ina......buk...atar asibiti ga wannan mcard din ta ciroshi cikin breziyarta,ki adanashi....ko..namut..u foyah ki idasa wannan aikin........sumewa tayi nan wajen. Saida fiyah ta saki kara tana girgiza zakiyyar amman bata motsi,agigice take sosai. tafara tarar mota neman taimako amman babu mai tsaywa duba da yadda taimako yanzu yayi wuya,durkushewa tayi gaban zakiyyar tana kuka,kamar anzungureta tatuna da malik ta rarumo wayarta hannunta yana karkarwa ta shiga kiransa. Harta tsinke baidauka ba ta sake kira karo na biyu,nan ma haka jitake kamar zata haukace"kadauki waya yaya malik ina bumatar taimakonka" Runtse ido tai tana sake kira cikin sadakarwa saikuma taji andaga,bata bari yayi magana ba tace cikin kuka"yaya malik don Allah kataimakeni kazo ka taimake mu........kuka yaci karfinta ta kasa cigaba da maganar. Jitai ance"kina iya" Bata cikin natsuwar da zata iya tantance muryar waye amman tasan bata malik bace. Fadar inda suke tayi cikin dimaucewa da gigita,saidai shican ya kashe wayar. Kuka ta tisa zakiyya gaba tanayi idan zakiyya ta muti ya zatayi da rayuwarta. Babu jimawa taga mota tsaye inda suke saidai wanda yafito daga motar ne yasa hankalinta dawo jikinta,bakinta ne taji yafurta. *yah Abdoulnasser* kallon zakiyya tayi dake kwance kamar gawa sannan ta dago ta kallai,shikanshi wadda ke kwance kasan kusada fiyah ganin ta ya gigitashi,idonsa dan danan yayi jajawur yasha mur matuka bai sake dago kai ya kalli fiyar ba yayi kwana zaibar wajen batare da yunkurin yin wani abuba. Aguje tatashi ta bishi tana hawaye ganin dagaske koma wa zaiyyi. idan yatai yabarsu anan komi zai iya faruwa dasu wata kila zakiyya tana iya rasa ranta. Jiyai kurin ta rike hannunsa cikin rawar murya tace"karkayi haka plsss narokeka karka tai karka tai kabrmu a,inhar katai zamu iya rasa ranta bata camcanci haka ba kome katuna akanta baidace kabarmu ahaka ba......narokeka plsss yah Abdoul plssss.........ingijeni yayi na fadi agefe cikin fushi da na jima banganshi cikin sa ba yace"ina ruwana da mutuwarta ko rayuwarta,baishafan ba data mutu kotai rai karkisake zuwa inda nake balle kimun mganar wanna abar." Ya wuce kamar kububuwa yabar ni awajen.....zaman dirshen nayi ina kuka nashiga ukuna ni safiyya yau naga bala,i dagaske Alfah tafiya yayi wace irin xuciyace dashi haka,ya zanyi da zakiyya ni kau yau.nafi karfin minty talatin wajen babu wanda ya kulani kowa yazo wucewar sa yake.........kamar wasa saiga motarsa tasake dawowa wajen,inda muke lokacin naci kuka nakoshi har muryata bata fita,koda naga kiran anty kasa dauka nai namata sakon cewa naje gida amman zan dawo yanzu. Ko kallonsa banba banza nai dashi yana zuwa ya sungumeta yaje yasata baya yarufe,yayi tsaye baimun magama ba alamun intaho mutai,yadda ya bata mun rai bana jin ko kallonsa zan sake yi ahalin yanzu,tashi nai daga durkushin danake na kakkabe jikona na share fuskata na nufi tiri kurin,inajin xuciyata na zafi kamar garwashi. Madam bata lokaci kafin taxi ta tsaya nashiga nabarsa nan shida zakiyyar nasan dole zaikula da ita ko dawowar dayayi nasan xuciyarsa ce taji bazata iya barinta ta rasa rayuwarta ba bayan yana da damar kaita asibiti,can kukarata kaida ita wani abu yazo mun wuya ya tomare kuka nakeson inyi inba haka ba azai wuce ba,kukan naitayi wanda har cikin raina nakejinsa har mai taxin yana ban hkr ,ban ma sauraresa ba saida nayi na koshi sannan ya mikomun ruwa na wanke fuskata dashi bayan nafito daga taxin.na sallamai na shiga gida. Anty na ganina tace"kina lafiya fiyah?kuka kikai me akai maki" Wani kukan ya haomun nace"Anty yanzu don Allah sun kyauta mun kenan,inazowa na biyu amman suka ban na biyar wannan karon,har hakan yaja baza asani cikin musabaqa ba,wlh Allah ya isana" Dariya Antyn tayi tace"lallai safiyya har yau dai da sauranki,to waye yace maki kullum ake kwana bisa gado" ganin haka karyata ta ansu yasa nashige daki naci gaba da kukana. Don't share it plssss and plss [9/17, 3:39 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........32 Tunda na shiga daki kuka naitayi ni bazan ce ga abunda nake ma kuka ba,kawai dai nabarwa raina cewar yadda ya banzatar dani awajen bacin yaga irin halin da muke ciki,shine dayaga cewar masoyiyarsa zata zata rasa rayuwarta yadawo............saida naji kaina yafara ciwo sannan na hakura,m.card din da zakiyya tabani na ciro daga cikin aljuhun doguwar rigata na kura mashi ido,zanso jin abunda yake ciki amman ba yanzu ba sai tare da yaya malik,cikin jikkata naje nayi mashi kyakkywar ajiya sanan ta nufi bayi,don jikinta duk tsami yake mata. Gyare jikinta tayi tsaf sai kamshi take fitowa tayi don cin Abinci yunwa takeji. Sallamar muhseen ce tasaka ta juya shikadai ne daga bayansa kuma saiga uncle ya shigo shima,hira suke ta kwallo sai muhawara suke shi uncle dan arsenal ne shikuma muhseen dan Manchester united ne,sai gardama suke. Anty ta fito tana cewa"aifa kun fara halinku ko,wai meyasa baku gama duk gardame gardamen ku acan waje sai dole kunshigo mun gida da hayaniya." Fiyah dai na kan dining tana tsakurar tuwon shinkafa da miyar agushi taji zallar naman kaza. Uncle bai kula Antyn ba sai muhseen ne yake bata ansa suna ta fadansu itada shi dasuka zaba, "Safiyya babu magana" Yake take tace"uncle naji aikuna ta magana ne sannuku." Muhseen najin ankira sunan ta yai saurin juyawa yana washe baki,cike da jin dadin ganinta barin Antyn yayi yana nufar wajen da fiyah take. "Aa ah ashe kina nan nazo da yamma bakinan" Ta na Kai cup din ruwa bakin ta tace cikin sanyin murya"ina wuni yaya muhseen" Murmushi yayi yana shafa kanshi yace"lafiya lau ya kike,nayi kewarki yau zuwana biyu bana samun ki" Idan dayasan yadda takeji yanzu dayake isarta da magana da ya kyaleta,amman bata son yaga tayi mashi wulakanci dole ta ke dannar xuciyarta take bashi ansa. Uncle yace ma Antyn"meyasamu safiyya ne?" Dariya Anty tayi har muhseen yana juyowa yace"kinga kina hana mu sakewa wallahi" Harararsa tayi tace"nan gida nane kabari sai kayi naka idan naje saika mun iko kajiko" Ta share sa tana bawa uncle ansa"waifa daga tayo na biyar isalamiyya shine take fushi,da kuka ma ta shigo gidan nan don ta sana yo na biyu ko na ukku anbata na biyar take ta fishu" Murmushi yayi yajiya ga fiyar daketa cin magani yace"safiyya haka abun hake ba kullum kake nasara ba,dole daman wata ran kaga juyin mulki badan hakan nanufin kasawa ko rashin maida hankali ba,aa hakan na nufin rabon wanine ba naki ba kiyi hkr next exams saiki dage ki dawo da position dinki" Murmushin dole tayi tace"nagode uncle insha Allah zan gyara" Muhseen yace"kice dai yar gidana akwai kokari ban result din in gani tawan" Batare dataji komi tace"yana gida na barsa wajen mama" Duk yadda yaso hirar tayi tsayi abun ya gagara don taki bashi hadin kai,tashi tayi ta yi masu saida safe ta wuce dakinta. Bata da natsuwar yin karatu amman ya ta iya dole zatayi saboda baifi saura kwana biyar sufara exams ba,haka ta runtse ido tanayi ba laifi kuma yana shiga don fiyah inhar tasa kanta abu ba kamar in kan karatu ne tofa ba dagaske yitake har saitaji ta gamsu da abunda ta karan ta. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Tunda ya kaita asibitin ya dawo resuption ya zauna ya dafe kanshi dake wata irin sarawa,wani irin juyawa kanshi hakeyi dashi zuciyarsa kaikomu kurin take,duk yabi ya gigice yarasa natsuwarsa. Malik ne yakira sa ya kasa daukar wayar saida yayi mashi kira uku sannan ya iya dauka. "Kana ina haka" Atakaice yace dashi"tarauni specialist hospital" Cikin tsoro malik yace"mekake yi awajen ne haka Alfah baka lafiya ne koko mekaje" "Kazo kasaman wajen" Yana gama fadar haka ya kashe wayar ya dafe kanshi dake cigaba da ciwo,baisan ma kalar tunanin dazai ba. Yanan zaune ya iso Allah yasa baisha wuyar ganin sa ba. "Lafiya Abdoul,bakada lafiya ne meke damunka." Idonsa jawur yace"zakiyya na kawo" Zaro idonsa malik yayi yana kallonsa cike da tsananin mamaki "zakiyya!!!,zakiyya fa kace kai ina ka gamu da zakiyyar kuma meyasameta" Cikin wani irin yanayi yayi mashi bayanin abunda yafaru atakaice............likitan dake dubata ne ya karo wajen yace"Alhamdulillah ansamu nasarar samunta,kozamuje office ne nayi maku bayani" Malik ake kallon sa yace "oky ba damuwa muje" Kamar bazai tashi ba haka ya tashi suka wuce office din likitan,rubutu yayi kafin yace"Am tayi sa,a sosai don an shak'a mata koken,Allah ne yasa abun yazo da sauki,don haka zata jima bata tashi ba zata iya kai gobe ma har yamma,mun mata allurai mun saka mata drip,zakuje wajen biya kubiya ga bill din ku" Ansa malik yayi yai mashi godiya suka fito. "Suwaye zasu yi mata haka?metayi masu ne" Abdoul ya daga kafada yace"karka tambayeni ban sani ba wata kila wannan yarinyar zata iya sani" Kallonsa Malik yayi yace"yarinya kuma,wai baka san sunan ta bane Abdoul?" Tsaki yaja yana zama saman wani benci malik ya isa wajen biyan kudin ya biya yadawo ya zauna kusa dashi yace"yanzu yazamuyi da ita" Kauda kai yayi Allah kadai yasan yadda xuciyarsa take ciwo,ba kuma dan karamin ciwo ba da wuya idan ba sai yasha magani ba. "Munyi mai wuyar don haka muwuce gida randa ta tashi saita kama gabanta ko" Kallonsa yake cike da nazarinsa "ba zai yuwu mubarta ita daya ba Abdoul,don haka ina ga zanje in samu likitan ya tura nurse guda ta zauna da ita,kafin zuwa goben" "Can matsalarka" Inji Alfah. Tashi Malik yayi ya nufi wajen likitan,yayi sa,a kuwa aka sanya nurse guda dazata kula da ita,sannan yadawo suka tafi. Tafiyar so silent babu Mai magana kowa da abunda yake sakawa cikin ransa,kallon Alfah malik yayi yace"fiyah fa fushi yake dakai,don ayadda ka gaya mun tabbas ka bata mata rai,kuma kowaye dole zaiji haushi ka kirata ka bata hkr" Jajayen idanunsa ya watsa ma malik yace cikin muryar sa da saika rantse dukan tsiya akai mashi"ta shekara dubu tanayi" Jinjina kai malik yayi yana murmushi yasan cikin bacin rai yake,amman tabbas yasan wannan ban hkr sai Alfah yayi shi,don daga jiya zuwa yau ya fahimci wasu abubuwa tsakaninsu. Koda sukaje gida shigewa yai yakulle kofarsa ya fada kan gado dafe da xuciyarsa,murgina kurin yake yana nishi shikadai yasan azabar dayakeji aciki,yau ciwonsa na shekara shidda ya dawo sabo,wani radadi yakeji cikin xuciyarsa.fadowa kasa yayi timm har malik dake falo saida yajiyo karar faduwarsa,gabansa ya fadi ya rugo ya banko kofar dayake ba sosai ya rufe ba saigata tabude..........asume ya yadda shi duk inda hankalin malik yake ya tashi ainun,ya rude sosai rabinda yaga Alfah cikin wannan halin bazai iya tuna wa ba..........yana kerma yana karkarwa ya dauko phone dinsa yashiga kiran dr Alfah din. Bakinsa yana rawa yake gaya mashi halin da ake ciki,yace gashinan zuwa insha Allah. Haka malik yaringa kwaraya ma Alfah ruwa Amman baifar fado ba saoda likitan yazo yashiga nemo numfashinsa yasha wuya ba karama ba, kafin Allah yasa numfashin dawowa,amman dole saidai karamin oxygen aka saka mashi yadda zai taimaka mashi wajen numfashin,dr yace"xuciyarsa ce ta halba dakarfi,wanda hakan yajawo sumar tashi da alama dai yana cikin damuwa da tsananin tashin hankali,meya faru ne?" Dafe kai malik yayi yana sauke ajiyar xuciya yace"yaga abunda ya tuna mashi rayuwar sa ta baya,bacin ransa na shekaru da yawa shine yadawo mashi sabo,ya kasa control din kansa har hakan tafaru." "Allah ya kyauta gaba,ka kula dashi gobe zan dawo na sake dubashi yanxu dai kabarshi yayita baccin har sanda zai tashi,na xuba allurai acikin ruwan drip din zaitaima ka mashi wajen samun arfin xuciyar" Rakashi yayi yadawo ya tusa Alfah gaba yana kallo kamar yasamu tv ,tausayinsa ne ya kamashi sosai dole zai shiga wannan haki don kuwa kana ganin rayuwa. Koma wa yayi daga can saman kujera ya kwanta yana kallonsa. Ya jima yana cikin tunani da sakawa da kwancewa,kafin ya dauki wayarsa yashiga kiran fiyah. Ta gama alwallar bacci kenan ta fito tajiyo rurin wayar,kallonta tayi taga sunan malik,da dai kamar ta share amman sai xuciyarta takasa yin hakan. Ahankali ta dauki wayar tana sawa ga kunnenta. "Qanwata ban sanki da haka ba,yaushe kika b'aci da fushi ban sani ba" Turo baki tayi kamar yana gabanta ta haye kan gado tana jingina bayanta ga allon gadon cikin sassanyar murya tace"yaya haka ma zakace bacin,bacin abunda akaimun har zaka ce kar nayi fushi" "Ni bance karkiyi fushi ba,amman saiki yi mashi uziri abunda ya sakashi yin hakan kinsani meyasa bazaki mashi uxiri ba," Sake sunburo bakin tayi kamar zata yi kuka tace"yaya malik Amman basai yazo ya ban hkr inshiga ba amman fa gabansa na tsayar da taxi natafi baiyyi yunkurin dakatar dani baya kyaleni natafi" "Sorry qanwata zaibaki hkr Amman saiya samu sauki" Gabanta yafadi rasss "yaya malik baya da lafiya ne" Iska yafesar yana gyara kwanciyarsa yace"fadowa yayi daga kan gado ya suma xuciyarsa ce ta halba numfashinsa ya tsaya,amman ya samu sauki don gashi can likita ya saka mashi oxygen.xuwa safe zai farka cikin koshin lfiya insha Allah" Kwalla suka zubo mata cikin kermar murya kiris yarage ta fashe da kuka tace"yaya malik ka tabbatar yana lafiya,ya samu sauki sosai yaya malik nice na bata mashi rai ko?wlh yaya malik ni banson hakan zai bata ransa ba kuma wlh ni kai nakoira bashi ba,amman sai kurin naganshi yazo.......kasa cigaba tayi da magana don kukanta ya kusa fitowa" Jinjina kai yake yajiyo sautin kukanta tabbas safiyya ta kamu da abunda yake zargin cewar shima Abdoul din ya kamu,duba da yadda duk yabi ta rude ta tashi hankalinta. "Kuka kike fiyah,miye na kukan to?bakison wani abu yasamai ne" Shashshekarta ce ta fito fili takasa ansashi murmushi yayi yace"ki kwantar da hankalinki babu abun da zai sameshi,kiyi mashi Addua daya farka da safe zan kiraki sai kimasa ya jiki ko" Shiru tayi tana jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta ganshi,amma bata son Yaya malik ya fahimci kotana jin wani new feelings akan Abokin nashi. "Kinyi shiru qanwata" "Saida safe yaya malik zan kwanta" Murmushi yayi yanajin ina mace shine yayi dacen samun wannan tsadaddar yarinyar mai kunya da tarbiyya. "Shikenan qanwata Mma i promise u immediately daya tashi zan kiraki kizo ki ganshi,sannan zakiyya na asibiti ta samu sauki itama da safe ko zuwa yamma zata iya farkawa ai zaki xo ganinta ko saimuyi magana daganan" Daker ta iya ce mashi "oky,goodnight" Ta sauke wayar tana silalewa saman gadon tana jawo filo tana kwakwumeshi ga kirjinta. Plssss kuyi hkr gobe ba zaku samu posting ba saboda muna aikin suna sorry plsssss nasan ba zakuji dadi ba,amman inhar nasamu lokaci zanyi maku Pls don't share it i beg [9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* FOR SALE 300 VIA KISIYA KISHA KARATUNKI CIKIN NATSUWA. GA MAI BUKATA TA TUNTUBI WANNAN LAYIN 09034722979 WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ALFAH FANS GROUP* 🅿️.........33 "Anty bazan iya zama har kigama wanka ba,kinga exams ke gareni ina bukatar inje na natsu gida nayi karatuna,kiyi hkr nidai kibarni natai tunda kinga wlh yya muhseen baxai barni nasake ba inhar yasan ina nan gidan gara dai na tai can gida." "Shikenan,Bari na dauko maki naman ku kowa na mashi kullinsa don haka babu wata rigima,halinki nasani kan nama idan na sake na hadaki dana yesmin wlh kwararta xakiyi,har gara inkeda mamane wanan tana iya ma raba nata biyu takara maki ita ko baba,don naga dagaske kin anshe ma yesmin fadarta" Dariya fiyah tayi tana yiwa little fiyah rawa tace"uhm shedar da zakiyi mun kenan Anty?kuma ai dama can fadata ce tana zuwa naga alamar da niyar juyin mulki tazo saina zage don kar na rasa matsayina,amman duk da haka Anty Ai yesmin tafini fada aji wajen mama,da dai babane wannan nasan bai bari abunda zai bata raina,don ta nama ma saiya hkr da nashi yabani incinye" Tafada tana dariya antyn dake cikin daki tace"wlh karma kifara,kowa anbashi nashi kiji tsoron Allah kibarshi yaci,haba safiyya wlh nasan zaki aikata don Allah karkiyi haka" Tana dariyar tace"to inbaki so inyi nawa yafi na kowa yawa aradu" Fitowa tai da babar lea viva ta ajiye gabanta,ta fido wata bakar leda cike tab daker aka kulleta tace"wannan na kine kici kiyi kashi don ubanki,wanna kuma na mama gashinan nayi alama,wannan kuma na baba shima ga shedar shinan,inna balaraba tunjiya suka wuce da nasu banda su anan ciki,ga na yesmin ga na yaya jalal asaka mashi akitse tunda ya tafi randa ya dawo sai yaci" "Kai Anty,saikace dole nidai gaskiya ki kyale yaya kiban shi in cinye in yadawo sai inbashi hkr" "Uban hkr zaki bashi wallahi karnaji wannan labarin kinji dai na gaya maki,kodayake ma bari kigani." Ya daukeshi daga cikin sauran tace"nizan ajiye mashi dakaina" Suna cikin haka uncle ya shigo yace"safiyya badai tafya ba?" "Wlh uncle tafiya zanyi,inje na natsu infara karatu lokaci yana kure mana" "To gama bari nazo na saukeki,muhseen baya nan da nasaka ya kaiki." Aranta tace"nagode Allah" Sunyi sallama da Anty jamilar tana tayi mata godiya akan hidimar da tai mata,kamar zatai kwallah haka taji don dan zaman da sukai saitaji inama taita zama da qanwar tata,koba komi sunyi wasa da dariya kuma ta rage mata ayyuka,amman tasan baba bazai yarda ba kuma itama fiyar tafison kusada mama da baban. Suna tafiya yana janta da hira tana biyesa,har yazo kan maganar abokinsa. "Nikau safiyya ina kika san Alfah,ayadda na fahimta ranan ba bankeki yayi ba,karki boyemun inason in sanine saboda wani dalili" Saitaji bazata iya boyewa uncle din nata ba ta sadda kai ta fara bashi labarin haduwarsu da kuma dalilin shigarta rayuwarsa,har kawo abunda ya tsayar da ita bata dawo gida da wuri ba,harda cigaban da ya samu tadalilinta. Shiru yayi yana jinjina kai kafin yace"niyyarki mai kyauce safiyyah,amman kinsan hakan akwai hadari ga rayuwarki,wannan aikin namiji ne ya dace dashi ba ke mace ba,saboda yadda amana tayi karanci cikin rayuwar nan,kuma nima nasan da wannan labarin,shiyasa na tambayeki tabbas nima raina ba yadda Alfah zai aikata haka ba,duk da kowane lokaci mutun zai ita canza wa,amman da kamar wuya gaskiya.don haka ki kula ki kiyaye ya dace tun farko ki sanar da mama koyaya dai in wani abu yabiyo baya duk da ba fata ake ba,atleast tasan mekike ciki" "Uncle wlh bazata barni na taimakesa ba saboda abunda ya faru tsakaninsu da mahaifinsa,gabace maitsawo tunma ba aifemu ba muduka,abun ya faru shiyasa duk unguwar babu mai kulamu bamu banda yan tsirarunsu,shiyasa na boye abun babu wanda yasani cikin gidan mu don kar ahanani kuma Alhamdulillah komi yana zuwa da sauki nanda dan lokaci komi ya kammala,nima inhuta in samu natsuwa." Murmushi yayi baice komi ba don yayi imanin shigarta rsyuwar Alfah baya nufin ta fita,don ga dukan alamu ita dashi kowa yana jin wani abu game da dan uwansa,shiyasa bai bada karfi wajen ganin muhseen din sa ya sameta ba,yana da burin ta dawo da abokin nashi cikin hayyacinsa,kuma zaiso ace sunyi aure sauran halayyarsa ta idasa daidaita shi,shiyasa ma zaifara nema wa muhseen din Auren yesmin,don bazai so ace ya rasa daya daga cikinsu ba,don yarane da suka samu kyakkyawar tarbiya yadda ya kamata. Sauketa yayi suka shiga ya gaida mama lokacin baba bai dawo gida ba,yaba fiya dubu goma ladar aikin data sha na zaman bakwai.taba kowa naman sa na ajiye nata gaba tanaci saida tayi rbin ledar sannan mama dataga bata da niyya saurara mashi ta anshe tana fada. Wajen karfe sha daya na safe tana dakin mama yesmin taje islamiyya,maman kuma tana kitchen. Ta dora sanwar rana. Karatu take sosai duk da xuciyarta bata gareta hankalinta ya kasu kashi daban badan,ga zakiyya tana son jin halin da take ga Abdoul tana son sanin koya tashi jikin yayi sauki bata sani ba,shikuma wanda xai kiratan ya gaya mata shiru bai kiraba...........tana cikin wanna halin wayarta tayi kara,saurin kallonta tayi yaga sunan sa tai saurin dauka tana kanga wa ga kunne. "Yaya malik ina kwana" "Lafiya lau qanwata ya kika tashi,fatan kinyi bacci daren jiya" Juya ido tayi alamun me yake nufi da tayi bacci jiya lobatai ba, "Na tashi lafiya yaya malik" Kallon Alfah yayi dake kurban tea mai dan gumi don ya gasa cikinsa,kamar baisan da wadda yake waya ba. "Kinjini shiru ban kira kiba,walh sai yanzun ya tashi babu jimawa inbashi ko"? Tana son ansa kodan taji muryarsa,don harga Allah Abunda take son jikenan,amman idan tayi hakan wane irin kallo zai mata,kenan ma fushin nata baije ko ina ba,tunda daga jin baida lafiya duk na rikice. "Kinyi shiru" "Kyalesa yaya malik,kadai gaidashi da jiki Allah ya sawake" "Aa karmuyi haka dake,sannu fa kurin zakiyi mashi" Rutse idonta tayi tanajin kamar tace eh yabashi amman ajinta zai zube, "Ka kyalesa yaya malik,aibadole saina yi magana dashiba daga nan ma idan na mashi Addua zatazo,rabu dashi yanzu ma karatu nake zan ajiye wayar,kila idan na samu time anjima da yamma infito inga jikkin zakiyyar" "Shikenan,amman banji dadi ba da kikace kar abashi,kingashi nan fa har ya miko hannu sa...........karka mun sharri ta dauka dagaske kake ban son wanna game din" Cewar Abdoul dake shan tea din sa. Ras taji abunda yace wani abu ya tsaya mata ga makoshi,watau shi ko ajikinsa bai damu ba.kwalla taji sun silalo mata ta kasa gogewa muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka tace"yaya malik sai anjima,kayo mun text din asinitin da aka kaita da no din dakin" Saiyaji ta bashi tausai,hands free ya saka wayar yadda Alfah zaiji muryarta wata kila shima yaji abunda tajin. "Shikenan qanwata zan turo maki,amman kizo nan basai muwuce tare ba" Kwamciya tayi ta dora kanta kan filon mama hakanan kuka yana son kubce mata tace"yaya malik aina ce maka bazan sake xuwa gidan nan ba,kayi hkr bazan iya zuwaba mu hadu dakai Asibitin akwai maganar da zamuyi" "Shikenan saikinzo din" Kashe wayar tayi tana kwantawa ta dunkule waje guda tana kuka kasa kasa,wanan abun ya cuceta wai meke faruwa da xuciyata ne haka,Allah kaga niyyata karka saman Abunda zai wahalar dani bacin taimakone nayi,.......ta jima tana kukanta kafin bacci ya sureta. Tunda suka gama wayar ya silale inda yake ya kwanta,idonsa alumshe sautin muryata yake jin yana amsa kuwwa cikin kunnensa,tabbas kuka take wannane karon na biyu dake iya gane kukanta ta sautin muryarta,yana jin bai khauta ba abunda yayi matan shekaran jiyan,ya zaiyyi ba laifinsa bane zuciyarsa ce ta buga da ganin zakiyya,wadda tsawon shekara shidda ko mai kama da ita bai gani ba,haka xalika baya iya cewa ga lokaci guda daya zauna yayi tunaninta,saboda ya dora ma kanshi wata irin tsanarta da kinta gani yake tunaninta ma inyayi yacuci zuciyarsa,wani iri yakeji wanda bazai iya tantance meyakejin ba,amman shima da yana iyawa to tabbas kukan zaiyyi,don abun yafi karfi sa. Inama Zai iya lallashinta yanzu inama zai iya ansar no dinta yayi kiranta,bazai iya ba mezai ce mata dawace kalmar zaifara. Saiya tuna ranar da yake gidan yayarta fushin da yayi biyonsa da tai tana kwalla don ta bashi hkr,kenan ita bata camcanta dayayi mata hakan ba,dafe kansa yayi tare da saitin xuciyarsa don ciwo suke mashi. Malik ne yafito yayi shirin zuwa company tunda yau shibazai iya fita ba,kallonsa yayi yaga yadda yake shafa kirjinsa da kanshi ya iso inda yake ya zauna yace"daka taimaka ma xuciyarka kabar tunanin tunda bata so,inkuma inbaka no dinta kakirata niba wahala bane wajena,inkai kana ganin hakan kamar da wuya,gata nan na saka maka ka kirata ko karka kirata ya rage naka.daka cire ma kanka wannan nauyin ka fuskanci reality da yafiye maka sauki Abdoul,amman nasan indan nafurta abun da yake damunka zaka karyani kuma zaka dauki zafi,don haka nidai karufa man asiri kacire damuwa,zanje company daga can zan biya store.likita zai dubaka anjima amman kafin nan zanje naga jikin zakiyya." Uffan bai cemashi ba idonsa a kulle bai bude ba,har malik din yafita kallon wayarsa yayi yaga digit din numbers din daya kera mashi,daukar wayar yayi yana kallonsu na dan lokaci kafin yasa hannu ya goge su tas. Ya maida ya ajiye. Kuyi hkr babu yawa wlh masassara nake. Daker idan zanyi sanyin idaniya plsss kumun uziri. It's for sale if u need it meet me 09934722970 Don't share it plsss I beg [9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* *ABDOUL-NASSER NA KUDINE,INKIKA KARANTA BAKI BIYA BA KEDA LILLAHI,GA MAI BUKATA ZAI IYA TUNTUBAR WANNAN NO DIN 09034722970. WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........34 Bata tashi daga baccin ba sai bayan azahar,tatashi tayi wanka ta dawo tayi sallar azahar tana bitar haddarta ta dade bata biya ba,yesmin ta shigo masu da abinci falon mama sun kallon wani film merlin,mama itama hada ita ake kallon. Suna ci suna hira hankalinsu akan film din yayinda fiyah hankalinta nacan wajen tunanin karyar da zatayi ta fita anjima. Mama tace"safiyya duk don na hanaki naman nan kike fushi" Shagwabe fuska tayi "mama bafa haka bane,kawai dai tunanin exam nake wlh banyi wani karatun kirkiba,gashi ko time table bana da ita" "Addana garin ya haka,to ya za,ai kisan lokacin da zaku fara,kinma tunamun jiya Anty rafeea tazo nemanki" Mama tace"kitambayeta kila ita bazata rasa ba" Murna ta kamata ganin ta samu hanyar da take so. "Aa itama inajin ita tazo nema wajena,amman bari inkira Amatullah nasan ta siya." Tana jawo wayarta kamr gaske. Dandanan tayi wayar karya ta ajiye"mama tace ta siya zanje in ansa sainayi photocopy" Mama tace"haka din za,ai maida hankali kigama kokinje kidawo kar babanku ya tadda bakinan" Kamar zatai kuka tace"mama yanzun fa rana tayi kibari ayi sallar la,asar basai inje ba bafa nisa keda akwai ba unguwar tasu." "Shikenan Allah ya kaimu anjiman bandai so kikai magaruba awaje shiyasa." "Insha Allah mamana bazan Kai ba" Haka suka cigaba da hirarsu suna kallansu har suka gama cin abincin. Mama tana mitar baba baidawo gida yaci abinci ba,fiyah nadariya tace"Kai mama Kika Sani ko aiki ya mashi yawa yau." Ana kiran sallar la,asar tatashi tayi salla tana gama wa tacanza kaya xuwa doguwar riga pink ta wani material da sukai ankodinsa su uku Anty da yesmin sai ita. Yar karamar jikkarta tadauka ta saka wannan m.card din ciki,sannan ta fesa turare tafito tana cewa mama "mama zan tafi saina dawo" "Baki tafiya da yesmin" Bata fuska tai"Kai mama kamar dai wata wace zata bace" "Aisaiki ta tafiyar tunda kinfison kiyi tafiya kedaya kamar mayya" Ficewa tayi tana saurin nufar get din estate din. Cikin Sa,a ta samu taxi bata tsaya ko inaba sai asibitin,ta biyashi ta fito tana kallon asibitin kamar wadda zataga zakiyya saman allon sunan asibitin. Gefe guda taja tana fiddo wayarta don Kiran yaya malik ta sanar dashi ta iso..........motar data tsayace ta dakatar da ita daga kiran nashi,kallon motar take harta tsaya cikin parkin space din asibitin,kofar farko da aka bude ta driver malik ne cikin manyan kaya saidai banda hula,bayan wani lokaci kuma dayar kofar maizaman banza aka budeta,kafafunsa kurin yafara zirowa amman ta ganesa,bakuma donta taba tsaya wa kallon kafafun nashi ba,aa kawai tasan shikadaine wanda tasan cewa yana mu,amala da combus different colors inyau kaganshi da blue and white to gobe zaganshi da red and onother color din,da alama yana son sakasu. Tsaye tayi bakin kofar shiga entrance din asibitin don tasan idan sunzo shiga zasu ganta,ba saita kira saba. Dauke kanta tayi gefe don karma su hada ido dashi. "Ah qanwata Ashe kinxo yanzu nakecewa bari na kiraki,karaso to saimu wuce cikin" Jerewa sukai suna cigaba da tafiya yana mata magana. "Yaya malik ina wuni" Murmushi yayi yace"lafiya lau qanwata yasu little safiyyah" "Wlh suna gidansu dazun da safe nabaro gidan,daga gidanmu ma nake" Tunda takuya baya yake kallon bayanta,tayi halin ko inkula dashi har yanzun dai fushin take kenan,jinjinakai kurin yayi yana take masu baya. Dakin da aka kwamtar da ita suka shiga,cikin ikon Allah da yardarsa tatashi nurse cema take bata tea abaki,kallonsu take daya bayan daya safiyya ta karasa kusada ita gefen gadon tana riko hannunta I donta yacika tab da kwallah. Ogan kuwa yana jikin kofa ya harde kafafunsa,ya na tafaman danna waya alamun ko ajikinsa. "Zakiyya ya jikin naki" Kanta ta sadda kasa tana jin hawayenfa suna sauka saman hannunta. Daker ta iya furta kalma guda biyu"dasauki,ya kikaje gida" Ajiyar xuciya tasauke tana kallon yaya malik matsowa yayikusada su yace"zakiyya yajikin naki fatan kinsami sauki?" Kwalla take fitarwa sosai muryarta tana rawa tace"nasami sauki yaya malik" Shiru sukai banda shashshekar kukanta bakajin komi,likitane yashigo yana cewa"alhamdulilla harkun Kara so kenan gata nan tawartsake insha Allah,Amman zata ringa shan wadannan magungunan na kwana uku don mayen daya kamata ya idasa sakinta Allah yasawake Zan salameta yanzun,saiku tafi." Yaya malik ne kurin ya iya bashi respond. Ya anshi takardar magungunan yafita yatai pharmacy,za man kurame mukaita yi,shi wancen banda faman dane danne awaya babu abunda yake,zakiyya kuma kukanta take bilhakki da gaskiya. Nai zuru Ina sakawa da kwancewa nikadai,har yaya malik yaje yadawo. "Muwuce ko"malik yafada yana kallonsu itada fiyah,kallonsa fiyah tayi tace"ina zaku kaita yanzu,ince dai ba gidansu ba" "Inbanda can Ina zamu kaita ne uwar tsarawa" Cewar Abdoul cikin wata irin murya Mai amon mazan taka,wani kallon banza ta wurga Mai tace"to uban shishshigi kaji nakasa dakai?sai kabari nasanyo ka cikin maganata Sanan saika nuna halin naka." Zaro idonsa yayi yana kallonta cike da bacin rai wanda yasan cewar ba itace takar xomon ba"karkisake kice zakimun rashin kunya,don Zan dagula ranki ne" Tsaki taja tana sake maka mashi harara tanajin wani abu yana tokare mata wuya,kwallarta nason fitowa. Kauda kai tayi tana ma malik magana"yaya malik,inaganin karka kaita gidansu,akwai matsala don Allah kakula da zakiyya ina neman Alfarmarka,domin tana bukatar taimakon wani,inda hali kar tasake fita ko ina" Jinjina Kai yayi yace"shikenan safiyya duk vansan dalilinki na casa haka ba,amman insha Allah za,ai yadda kikace. Kamota muje mota" Kamota fiya tayi suka nufi hanyar fita,dogon tsaki yaja yana wucewa yabarsu nan. Fiyah tace"aikin banza ta tsukeka can Mai xuciyar karfe dabatasan tausayi ba" Yana jinta baitsaya ba ya wuce motar dasukazo da ita,gaba ya bude yashiga,kamar zaifashe don haushi daidai da second guda ya bude idonsa yaga zakiyyar wata irin tsanarta yakeji,zaiga inda malik zaikaita don badai gidanshi ba,mezai zauna yayi gida daya da ita. Bude masu bayan motar malik yayi fiyah tashigar da ita ta rufe. Kallonta kurin yake ta glass banda yabonta babu abunda xuciyarsa keyi,amman bazaka taba ganin hakan akan fuskarsa ba,inbacin haushin dake kwance sama. "Kika rufe ke bazaki shigaba" Murmushi tayi tace"yaya malik aini nan gida Zan wuce,don bance xan dadeba gaskiya amman ina zaka kaita." Shafa kansa yayi yace"banda wajen ajiye zakiyya daya wice gidanmu" "Amman wancen zaibari kuwah" Dariya yayi yace"rigima ce kurin zuyi dashi karshe baida yadda zaiyyi dani" Numfashi ta sauke tace"shikenan,banda ishashshen lokaci yaya malik,zan wuce ga wannan m.card din ka ajiyesa wajenka ranar Monday muke fara exams,Zan samu time dazamuje ga daddy sai akunnashi ani meke ciki,nan da kwana biyu kenan,nasan xuwa lokacin zakiyya ta Samu sauki saitayi mana bayanin abunda yafaru da ita har aka biyota za,a kasheta." "Hakane Allah yabiyaki ladar abun da kike yi,Zan mashi ajiya Mai kyau amman Nan da kwana biyu abokifa zaiyyi kewarki" Shagwabe fuska tai kamar zata bare da kuka tace"yaya malik ban so plss kadaina" Dariya yayi yace" tuba nake qanwata...........dallah malam kaxo kaja mutai,kobaka ga hadari ba." Alfah ne ya leko ta window yana mashi magana, Tsaki naja Ina cewa"inkaji haushi kaja da kanka mana amman bazai zo ba sai mun gama maganar da zamuyi." Wani haushi ya kamashi daman ga kukan zakiyya daya isheshi ya cika mashi kunne,jiyake kamar ya maketa ko kukan uban me take mashi,fitowa yayi afusace yayo wajensu kamar jira ruwan yake Nan danan aka zuge da ruwa sama..........aguje Malik ya shige motar yabarsu tsaye kamar an shukasu,tsaye yayi gabanta yana jin ruwan yana sauka har cikin xuciyarsa,duk wannan zafin ran yaji yanemai ya rasa. Juyawa nai Zan tari a un hawa don gasunan suna wucewa wasu babu kowa ciki,kasancewar muna bakin titi. Jinai ya cabko min hannu gam,kin juyowar nayi Ina kokowar kwatar hannuna,fin cikoni yayi gabaki dayana wanda kiris ya rage ban afaka cikin kirjinsa ba, nai saurin turjewa. dagani harshI ruwan ya gamajike mana kaya abayata tabi jikina ta lafe kasancewarta roba iyakar guiwata. Duk wani shaf na jikina ya gama bayyana,ban iya hada ido dashi ba amman sai kokarin ganin na anshe hannuna dake wajensa nake. Kusancinmu yayi yawa kamar zai sakani cikin jikinsa..........."dalla sakemin hannu baka ga taxi na jira na ba," Sake kusantoni yayi na juya baya inajin Dukan kirjina yana sake yawa.......shangaba yayi yana kallon taxi din ya bude bayan motar yayi mun nuni da inshiga harararsa nai na shiga maimakon inga yarufo Kofar saikurin ya shigo shima. "Yallabai zan iya tafiya" Cewar Mai taxi din. "Aa"kurin yace mashi duk na takire waje guda yabi ya isan da kallo........"duk haushina da kikeji yasa yau rashin kunyar taki tayi yawa kome? Kina gaya mun magana son ranki,kodan ban baki hkr ba" Kauda kainai ina tuno ranar ina sake jin ciwo abun cikin raina. Glass nake kallo yadda ruwan yake ake yawa........."karike hakrinka bana so" Iska yafesar baison wanna shariyar "kinga" Waigowa tayi tana juya idonta Wanda ita kanta bata San ma tana yi ba. Kunshe ido yayi yanajin tsigar jikinsa tana tashi,sai yatuna da wata rana. _idan kina juya mun idon nan my nour bazan iya jurewa ba,pls kidaina zaki cutar daraina_ _sorry habibi nimafa banson inayi ba,kawai daikwayar idonce don tasan tana tareda muradinta shiyasa take haka amman zan mata kashedi_ Ajiyar xuciya ya sauke muryarsa tayi cool sosai ya kalli cikin idonta yace"I'm sorry for yesterday i don't mean 2hot u okay!" Sakale nai Ina kallonsa girarsa guda yadaga mun,kirjina yabuga lumshe idonsa yayi ya sake cewa "bazaki sake mun rashin kunyar ba KO?" Kamar wata sakarai nadaga Kai kurin,girgiza kanshi yayi yace"magana zakiyi" Kanta ta sadda kasa yasaka hannu sa ya dago habarta yace"look at me saiki min maganar" Kamar zata kurma ihu saboda abunda takeji cikin ranta. Daker ta lalubo maganar don muryarta ta dauke d'af kasa saka idonta tayi cikin Nashi din dan abun Yafi karfinta. "Bazan sake ba I'm sorry" "Kallona nace kiyi" Girgiza kai tayi tace can kasan murya"bazan iya ba" Koma wa yayi jikin kujerar motar yajingina yakasa tabuka komi gabaki daya jikinsa ya mace mat, "Inason wucewa gida kar amun fada" Ta fada kamar maikoyon magana. Bude motar yayi zuwa lokacin ruwan yayi sauki. "Babu bankwana" Har lokacin kanta akasa tace"sai anjima" Hannunta ya riko yana kallon xoben dake jikin yatsanta,idan bazai manta ba shiya siyesa kuma malik ya ba ajiyarsa tun wasu kaya da akakawo masu company yaganshi yayi bala,in burgesa yaji koba komi yana son sa duk randa Allah yasa yaji zai iya aure,saiyaba matar da Allah yacida ita har takawo matsayin matarsa. Wani irin kyau xoben yayiwa hannunta,inama zai iya sumbatar sa Amman ya akai yazo gareta,dole zaiwa malik wannan tambayar. Yagama kallon hannun nata yasaki fita daga motar yayi yarufe kofar. Silalewa tai ta kwanta tama rasa in da zata dora wanan abu cikin xuciyarta. Kuyi hkr wlh waya ta keban Matsala shiyasa najima bakujini ba,maganar yawan typing banyi maku alkawariba gaskiya,Amman Zan kokarta hidimarce dayawa wlh. Don't share it pls I beg Bcos its for sale,inkina ra,ayi Kituntubi wannan no din09034722970. [9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........35 Har karfe goma nadare babu baba babu labrinsa,tun abun bai damun mama har ta kasa tsaye ta kasa xaune. Yesmin ce kurin tayi baci amman fiyah da mama idonsu biyu fiyah nata karatu mama kuma tana jan carbi,amman zuciyarta rawa take tana jin tsoron ko wani abunne ya sake faruwa da baban. "Mama bakijin bacci ne" Yake tayiwa safiyyar tace"zan kwanta yanzu" Cigaba tayi da karatun tana satar kallon mamar ganin duk tafita hayyacinta,agogo ta kalla tace" mama har yanzu baba baidawo ba lafiya" "Wallahi safiyya ban sani ba duk dadewar sa baidawo ba bai wuce tara da rabi amman gashinan har shadaya saura baidawo ba,babu kati wayata kiraman shi da taki" Saurin dauko tata tayi itama tanajin tashin hankalin,laluben sunan baban take cikin jerin sunayen kiransa tashiga yi amman wayarsa akashe,gabanta yasake faduwa tana kallon mamar cikin rashin sa,a "mama kashe take gabaki daya ma" Xunbur mama tai tatashi tana nufar waje biyota fiyah tayi cikin tashin hankali. "Mama ina zaki dare yayi kiyi hkr insha allah baba yana lafiya." Kamar zata fashe da kuka tace"safiyyah zan je ga dalha idan yanada number wani daga cikin wajen aikinsa ya kira mana yaji lafiya,hankalina ya kasa kwamciya wlh" Tare suka fita suka bubbuga shagon da yake kwana don har ya kwanta. Bayan yabude ya fito cikin bacci-bacci yace"mama,safiyyah lafiya?" Fiyah idonan har yacika da kwallah tace"yaya dalha babane baidawo gida ba har yanxu inkana da wata number ta wani daga cikin abokan aikinsa don Allah kabani nakira muji ko lafiya" Dan danan damuwa ta wanxu kan fuskarsa yace"wlh mama,safiyyah banda wata number amman aiga mashin dina nan bari inhau inje inji ko lafiya hakanan ai baba baya kai goma balle har shadaya." Saurin rikeshi mamar tayi tace"aa dalha bazan barka kafita wannan unguwar ba cikin wannan daren,muyi hkr har xuwa sadda Allah zai dawo dashi,inkuma bai dawo ba da asuba saika fita kaje kajiyo mana lafiya" Ahaka suka dawo cikin gida karatun da fiya bata karasa ba kenan,wannan daren haka suka ganshi babu wanda ya rintsa cikin su. Asubar farko kau dalha ya fita yatai can wajen aikin su baban,ya tadda ogan wajen kurin ya zo wajen ma yake kokarin budewa. "Yallabai barka da safiya" Inji dalha. Juyowa yayi yana ansa gaisuwar da cewa"saurayi kana tambayane" "Eh yallabai malam kabir ladan nake tambaya jiya bai kwana gidaba shine nazo inji ko lafiya naga kuma wajen babu kowa" Ajiyar xuciya yaja yana zama saman wani benci yadafe kanshi cike da damuwa yace"zauna saurayi abun bai zaiyuwu daga tsaye ba" Jikin dalha yayi bala,in sanyi ya sauko daga kan mashin dinsa yana zama kusa da shi jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali. "Kanaji ko,wlh jiya wani bala,i ne yasamu wajen nan yan dabane suka suka biyo Alh muazzam canji lokacin daidai tashin mu nida malam kabir don daman mukadai ake bari saimun gama tattara kaya sannan mu samu mutai. Bansan abunda ya faru ba amman na shiga kai kayan katako cikin shago,najiyo wani uban burki antaka bakin titin nan da kake gani,kabir ladan ne kurin wajen sadda zan fito ban ganshi ba,amman ga mota nan an ajiye akunne bama daidai akai parking din ba,daga can kuma ya nuna mashi wajen wani kango yacigaba motocine sunkai uku aka ajiye na fito ina naman malam kabir,don ban kai ga sallamar sa ba na nemai sama ko kasa ban ganiba.haka naringa zagaye area wajen babu shi babu alamarsa,dawowa nai naxauna ina tunani har na hakura zan tai na rufe wajen na hau mashin dina naga motar asibiti ta wuce ambulance kenan.........hankalina yayi kanta natada babur din nabi bayanta...........tafiya mukai mai nesa kafin muka iso wani waje,binsu nai har inda nafara ganin jini hankalina yayi mummunan tashi,muka cigaba da bin jinin har muka kawo kan inda abun ya faru,malam kabir ne kwance baya numfashi,ga Alh muazzam ya tusasa yana kuka harbine a bindiga ga kafarsa shikuma Alh muazzam yankane akai mashi ga kirjinsa sai goshinsa daya fashe yana fitar da jini,dan danan aka kwashesu akai ciki dasu. Har asibitin na bisu na tabbatar saida naga ya farfado likitoci sunyi masa aiki ancire bulet din sannan na tafi gida,yanzu haka so nake nanrage ayyuka naje na dubashi asibitin. "Nagode sosai amman ya sunan asibitin don inje insamar da iyalansa suganosho hankalinsa ya kwanta." Gaya mashi sunan yayi sannan ya hau mashin din sa yabar wajen,yana mamakin meya kai baba da shiga huddar da batashi ba,har hakan ya haifar da tsautsayi akanshi. Koda yaje gida kasa masu bayani yayi yace sushirya zasuje asibiti,tunda yafadi haka yesmin da fiyah suke kuka mama kau karfin haline yasaka bata xube kasa ba,don rudewa da firgici. "Kai dalha me zamuyo asibiti,waye ba lafiya in wani abunne yake faruwa daure ka gaya mana ba komi duk abu da ya samu bawa da sanin ubanhiji sai munemi sassauci daga garesa" Tafada cikin karyewar murya kwalarta na ka boyuw sunlalowa. "Malam dinne ya mutu kokuma wani abunne ya samai" Tausayin su yaji ya kama shi dole ya zauna yana lallashin su fiyah, tare da yi masu bayanin da ogansu baban yayi mashi. Kukan su ya karu fiyah tatashi ta rarumo abaya tana yin waje duk suka fito aka rufe gidan suka wuce bakin hanya suka tari taxi,mama da fiyah suka shiga taxi dalha ya goya yesmin ga bayan mashin dinsa,sannan suka nufo asibitin kowa da abunda yake nazari daga abunda sukaji bakin dalha. Suduka tunanin fiyah yasha banban da nasu don mama tana tunanin Alh muazam ne yasaka aimashi haka itada yesmin tunaninsu guda,dalha kuma yana ayyana taimako baban yazo yi wannan abun yafatu. Fiyah kuma tana tunanin wani abun nadaban,tana tuno hirarsu da zakiyya ta farko da suka hadu. _"Kiban kwana biyu zan nemeki akwai wani abu danake son ganowa suna kitsawa Abbi wata makarkashiya ne"_ Tabbas aikinsune nafarko kila suna son kasheshi su kwashi dukiya,na biyu wannan yaron mamman da suka biyo zakiyya umma tana son ya maye gurbin Alfah koma ince ya mayen,suna ganin asirinsu nangab da tonuwa yasa suka yanke wannan hukuncin,tunda har suka iya farautar ran zakiyya ta silar haka to kau babu makawa shima farautar ran nashi aka biyo yi don su smu cimmabumtr su sugudu.lallai akwai marasa imani cikin mutane dayawa,har ki iya saka wa akashe yarki sannan kisa abi mijinki shima akashe saboda abun duniya,wannan rayuwa abun tsoroce yayinda rai ya zama ba abakin komai bamutame sun maida kudi sune rayiwar duniya,akansu babu abunda bazasu iya ba. Har suka isa asibitin tana wannan nazarin. Dakin da aka kwantar da baban suka tambaya,dalha yake masu jagora har xuwa dakin. Togewa mama tai tana hawaye bata san mezata tarar ba,tanajin tsoron ganin abunda zuciyarta bazata iya dauka ba.......riko hannunta fiyah tayi cikin lallashi tace"mama kiyi hkr ki natsu babu abunda yasamu baba mai girma insha Allah kisaka natsuwa cikin ranki kar kitada mashi hankali" Da haka ta kwantar mata da hankali suka tura kofar suka shiga, Kwance yake yana bacci har lokacin ga kafarsa nan andaure da bandage,alamun itace keda matsalar. Kallonsa suke cikeda tausayawa yesmin har lokacin kuman take likitanne yashigo. "Sannunku kunxo ganin mai jikiko" Dalha ne ya iya bashi ansa yace "eh dr,yajikin nashi" File dinsa ya shiga dubawa yana cewa"he is very lucky,bulet din bai shigeshi sosai ba don kadan ya hana bai bita cikin kashin kafarsa ba,wanda da hakan ta faru sai anyi mashi aiki sosai.amman anyi sa,a hakan bata faruba ku godema Allah don cikin sati guda zai iya warkewa insha Allah.inhar yana shan magunguna yadda ya kamata,gasunan ma har ansiya tun dazun.yanzu da ruwan nan ya kare zai iya tashia amman bazamu baku saama yanzu ba akallai zai kwana biyu anan din." Ajiyar xuciya mama ta sauke tanajin sanyi cikin ramta Allah abun godiya dayasa babu wata babbar matsala. "Dr waye yasiyo magungunan?" Inji safiyyah "Alh ne ya bayar da kudin komi harna tsawon lokacin da za sallamai,shima mun bashi gad don shi ciwon da sauki bai kai ma wannan bawan Allah ba" Mamaki ya kama su sudukan mama har bakinta saida ta hangame saboda tsananin mamaki,Alh muazzam din zai iya yiwa baba wannan abun,to dalili dame? Mehakan ke nufi mamadai ta shiga shakku tace"likita anya kasan mekace kuwa" Daroya yayi yace "hajiya kenan to menene,koba shiba kowaye zai iya yin fiye da hakan akan mutumen dayayi saving rayuwarsa,yaji dadine kuma na tabbata ba iyakar abunda zai yi ba kenan bari dai har ya warke,don bacin mijinki hajoya bana tunanin iyanzu Alh muazzam ba,ai janazar sa ba" Kallon karin bayani suke mashi amman sai ya nufi hanyar fita kafin ya juyo yace"kuna iya zuwa kudawo anjima sai kudawo yafarka zuwa karde biyu amman kina iya barin wannan saurayin" Kowa da kalar tunaninsa akan wannaa sabon al,amarin. "Dalha ka zauna da baban ku zamuje gida in aka gama hada kalacin sai akawo maka." "Aa mama ki zauna ke sautai tare da su safiyyah idan suka hada sai akwo maki nakin,idan nakwo maki saikitai ni inzauna" "Toshikenan kuje din" Tafiya sukai gidan akabar mama wajensa. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 "Bafa ka isa kace zaka ajiye mun wannan yarinyar ba,inbacin inda sauran xuciyar imani wallahi bazan kaita asibiti ba saidai ta mace acan bisa titin,sannan taci darajar wannan yarinyar wallahi da ko sake bi ta kanta bazan ba,don haka inhar kana son muzauna lafiya ka dauketa daga cikin gidanna,inba haka ba bollah azim nizan fita kuma bazan sake dawowa ba,au kinci nasara wancen lokacin bai isheki ba akaina har sai kin sake biyoni cikin duniyar dana sake kin chaza mun kwalwa ko,to baki isaba tunda naga take-taken ki bakison kiganni ina rayuwa adoron kasa,to karya kike kinci karya kin kwana da yunwa wallahi." Tunda yafata balbalin masifarsa tana durkushe kasa tana kuka bilhakki da gaskiya..........malik kallonsa yake cikin takaici amman har yau baiga laifinsa ba akan abunda yake ma zakiyyar,laifinsa anan dayake hakikancewa lallai lalai bazata zauna agidan ba. "Yanzu ina kake tunanin zan kaita,shin kana ringa lissafi mana Alfah,wannan xuciyar karinga sassautama kanka ita kanada ciwo tare dakai kasan da wannan,don haka mubar tada jijiyar wuya akan wannan,zakiyya tana nan gidan bazataje ko ina ba" Kukanta ya tsananta tana cikin bakin cikin Yadda Abdoul dinta ya koma,tsanarta tayi guri tatare cikin ransa taya zata iya fahimtar dashi cewar bata da saka hannu cikin lalacewar rayuwarsa. "Fine,nandai zata zauna dai ko shikenan" Hanyar barin falon yayi cikin zafin rai,dagaske tafiyar zai kuma yayi alkawarin bazai dawo ba...........kamar antsikareta tatashi aguje tabi bayansa tana shashshekar kuka,part dinsa ya nufa yabanka kofar cikin fushi,don da ace ba kofar kirki bace saita balle. Akwati ya jawo yana hada kayansa,ko likewa babu cusawa kurin yake idan ya cirosu daga hanger. Shigowa tai cikin dakin Kamar anjehota tana nishi,rike hannu sa tai muryarta na rawa tace"na rokeka yaya Abdoul karka tai,muddin kabar nan bazan iya yafewa kaina ba,bacin wancen mikin dana sawa xuciyarka bazan iya daukar wannan ba,yaya Abdoul na gwammace ni inbar maka gidan inhar hakan zai saka kaji salama cikin ranka,zantai zantafi inyaso kome suke so suyi da rayuwata suyi mun,na cancanta da hakan." Ta durkushe kasa gabansa tana rike da kafarsa guda sosai take kuka mai tsuma xuciya. Wani irin ciwo yakeji cikin ransa,bai zaton har akwai sauran feelings game da zakiyyar ba cikin xuciyarsa,wani tausayi-tausayi yakejin yana tao mashi,yanajin kukanta har cikin kokon ransa.mezaimata?mezaice mata?bazai iya hucewa da wuri haka ba xuciyarsa yaudararsa take akan hakan,amman zakiyya bata cancanci yafiya da wuri ba. Tuntse idonsa yayi yana jin wani radadi,kalamanta suna sake dawo mashi cikin kunne. _yaya Abdoul na gwammace inbar maka gidan,inhar hakan zai saka kaji salama cikin ranka,zantai zantafi komi zasuyiwa rayuwata suyi mun na cancanta da hakan_ Su waye?me zasuyi mata?metayi masu.tsoro ya kama shi akan hakan,karsu cutar da ita dandanan yaji bazai iyabarinta tabar gidan ba,shima kuma ya hkr da barin gidan zaijira har koma me suke kullawa malik da wannan yarinyar ya bayyana,kafin ya san mizanin da zai dora zakiyyar. Juyowa yayi yasaka hannu riko kafadunta yadago ta,biyosa tayi idonta yayi jaa saboda kuka hawaye share share,take kallonsa da mamaki ko kadan batai tunanin zai saurareta ba balle har ya iya tabata. Malik yana bakin kofa yana kallonsu,murmushi yayi yana jinjina kokarin fiyah,na sassauta zafin ransa da saukowa da wuri. Zaunar da ita yayi bakin gadonsa ya juya baya don baison kallon idonta,don zata raunana mashi xuciya har yayi abunda bai niyya ba. "Kina iya zaman nan din,har xuwa sadda komi zai lafah sannan karki daman da wani ban hkrinki,kirike abunki bana bukata." "Bazan zauna ba inhar kaima zaka bar gidan don bakaine zakabar gidan ba nice" "Babu inda zanje inkinga kina iya zaman ga fili nanda dakuna" Ficewa yai yabar malik tsaue yana binsu da kallo. Isowa yayi gabanta yana mika mata hanky yace"ki kyalesa zai sakko,inha Aah komi aksan uwa karshe." Girgza kai tayi tana tace"zasu kashe Abbi sutsara yadda zasu farmashi,ban sani ba ko harma sun aikata abunda suka shirya din,saboda jiya zuwa yau sukace zasu aiwatar.inajin tsoron abunda umma dasu zuwairat da yaya mamman zasu aikata,yaya malik duk yadda kake zaton rashin imanin umma ya wuce nan,inhar akan kudine zasu iya yin komi wlh.yanzun haka kusan shekara guda kenan umma tayi yadda tayi Abbi baya kula Ammi,ko inda part dinta yake baya zuwa,suna cikin wani hali itada ni,ima.hakan yasa naje na sanar da dady halkn da ake ciki mafarin kenan yake hidima dasu,duk abu da suke so yake yi masu." Hankalin malik yayi masifar tashi,dajin abunda zakiyyar take fada saurin rarumo wayarsa yayi yana no layin Daddy. "Assalamu alaikum,daddy kana gida inason ganinka emergancy ne" "Malik,akwai matsala yanzun haka ina nan asibiti Abbinku ne baida lafiya ankawo mashi harine,Allah yakawo mashi mai taimakonsa mahaifin safiyya shine ya taimakesa,ta dalilin haka mahaifin safiyyar suka halbesa ga kafa shima ayanzu gashi nan asibitin." Cikin tashin hankali yace"baban safiyya dadyy,innalillahi wa inna ilaihir ra,ju un" Silalewa malik yayi kasa yana jin xuciyarsa kamar zata fito waje "daddy wane asibitinne,fatan suna lafiya babu dai wanda yarasa ransa cikinsu ko." "Anci sa,a Allah baibasu nasara ba Amman baban safiyya yafi Abbinku jinjiki gaskiya" Kashe wayar yayi duk ya gigice. Haka zakiyya kukanta yadawo sabo fil,duk abunda sukeyi Abdoul yana bakin kofa bai bar wajen ba yana jinsu,wata xuface take wanke mashi fuska da jikinsa,mahaifinsa da mahaifin safiyyah. Soyake kar abun hadamai soyake ya yakice tashin hankalin dayake ciki,amman ina abun ya ci tura abun ya gagaresa. Idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,mezaiyyi meya kamata yayi? Aa babu abunda zan mashi ko addua bazan mashi ba,bai dace da samun addua ta ba koma mai zai fatu dashi yaje yayita faruwa bai damai ba. Fitowarsu kenan suka hanhi shigewarsa cikin part din malik, Ayadda ya fahimci tafoyarsa tabbas yaji komi bazai iya gane wane irin hali yake ciki ba. Shida zakiyya suka shiga mota suka bar gida xuwa asibitin. Badai editing kuyi hkr da typing error. Don't share it pls i beg. Bcos its for sale inkina bukata ki tuntubi wannan number. 09034722970. [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........37 "Mama kune,banji tsayiwarku ba" Kallonta mamar keyi cike da tuhuma yayinda fiyah cikinta ya duru ruwa,tashiga ukunta inhar mama taji abunda take gaya ma ni,imah. "Mike gaya mata har yasata kuka safiyya?ke rayuwarki yan shige shige ya maki yawa,da kinga mutun na cikin damuwa saiki shishshige mashi,ina ruwanki da ita dake nake kinmun xuru da ido,mekikai mata" Kamar zata fashe da kuka tace"nikuwa mama mezan mata,daga na mata yamaijiki mungode da abinci,shine ta fashe da kuka tana cewa da badan baba ba da shima Abbin nasu sun rasashi kamar yadda suka raya yayansu,shinefa nake lallashinta" Harararta mamar tai tana nuna hanya "wuce muje,banson wannan shishshigin na gaya maki,ga dalha can zai kwana dashi muje kidauki takadda kicigaba da karatu tunda kinsan gobe iwar haka kin dawo daga jarabawar" Tafiya sukai gida don basai ma sun kawo masu abinci ba wanda ni,ima ta kawo ya wadacesu. 💕💕💕💕💕💕💕💕💕 Suna dawowa daga asibitin falon sukai ma tsinke,wanda suna shiga sukai kicibis da Abdoul xube kasa ya sankare.......aguje suka isa gareshi suna jijjigashi,Amman baisan sunayi ba. Tuni zakiyya ta rushe da kuka jikin malik har rawa yake ya lalubo wayarsa yashiga kiran dr............"babu lokacin gaisuwa kazo gida babu lafiya Abdoul ya suma ban san ma tun lokacin da yake ahaka ba." Tusashi gaba sukai harda malik din suna kuka,ita harda kara shine dai yake kwallah.tausayin alfah ya kamashi tabbas bayan tafiyarsu yashiga tention ba karami ba,dama ba idasa warkewa yayi ba daga wancen kwanciyar da yayi. Cikin kankanen lokaci saiga dr yazo yashiga dubashi,yafi awa akansa amman babu numfashin Alfah babu labarinsa. Cire abun awon yayi yana dafe goshi yace ma malik. "Malik saimun dangana da asibiti,abun babbane amman insha Allah bazata gagaraba" Daukoshi sukai sukasa shi mota zakiyya kamar zata haukace don kuka. Malik yace ta zauna gida fitarta hadarine ga rayuwarta.dole fa dawo ta dasa sabon babin kukan,saida dr yayo gayyar wasu likitocin suka dafkaka kanshi suna dubashi,kafin Allah yasa su iya gane matsalar.numfashinsa ya fara daidaita amman ciwon dake cikin cikinsa shine yajawo hakan,hanyar da zasuyi mashi maganin ciwo suke nema,koya farka zai iya sake sumar don ciwon ne aka fama. Fitowa dr yayi yana share gumi hankalinsa atashe,meyaja har ciwon yayi girma haka zuwansu na farko yaga ciwon karamine,wanda har yace ma malik inhar yabar shan giyar zai warke tas,daker idan nan gaba Alfah ba ai mashi aiki ba don ciwon ya kusan zama wost koma yace yakai. "Dr lafiya ya jikin nashi,Allah yasa babu wata matsala." Malik ne hake fada cikin rudu da rikicewa. Dafa kadarsa yayi yana riko hannunsa yace "cool down malik,insha Allah babu abunda zai faru kawai dai tambaya zan maka,daman ya jima da wannan ciwon ne kuma wane irin magani yake sha,don da alamar yana shan magani sanan yasha abunda ya tada ciwon.don raunin baya son cool water or heat,cikin biyu akwai daya." Kan malik ya kulle wane ciwo yake magana akai,a iyakar saninsa alfah bashida wanj ciwo,to ya kai dr yake mashi maganr ciwo.? "Kaga dr,nifa bansan Alfah da wani ciwo ba bai gaya mun ba,bacin ciwon xuciyarsa basan komai ba,wane irin ciwone yasamai don girman Allah dr karka bari narasa shi,bazan iya wata rayuwa mai dadi babu shi ba,dr kuyi iyakar kokarinku don girman Allah wlh ko nawane za,a biya" Girgiza kai yayi yace mashi"malik kwantar da hankalinka Abdoul zaitashi da iznin Allah,amman dole sai munsan magnin dayake sha akan ciwon,ta iya yuwuwa kaine baigaya ma wa ba,dole sai munsan sa sannan musan abunyi,kaje gida dakinsa kayi bincike sosai ka natsu kaduba bazaka rasa maganin dayake sha ba,saika kawo mana shi.kuma kabar batun kudi Malik ni xan dauki nauyin hidimar rashin lafiyarsa,bazan mance da alkairin sa gareni ba koza,a shekara dubu don haka karka damu maza kaje kadawo." _anan ina son jawo hankalinmu,yan uwa mu zama masu hallaci shi Alkairi abune mai kyau,duk wanda ya maka shi muddin kai dan halak ne,kuma mai rike amana dole wannan abun zai tsaya ranka,har kaima kaiyi burin mayar da wani alkairin bisa ga wanda akai maka,muguji mayar da sharri kan Alkairi wani zaimaka abun alheri,kaikuma zuciyarka babu Allah Aciki saika kudiri mayar mashi da sharri,wannan ba daidai bane akwai abunda za,ai maka duk kudinka da wadatarka zakaji dadi,mu zama masu amana da rike alkawari,duk wanda ya maka alkairi kokarta kaima ka saka mashi da makamancinsa,Allah yasa mufi karfin xukatanmu Allah ya tsare xuciyoyimu da aikata badaidai ba_ Haka malik ya juya ya nufi gida babu natsuwa kokadan,shiyasa ma yahau taxi don bazai iya driving ba. Dakin alfah yayi ma tsinke duk wata drower dake dakin yaringa haukacesu yana dube dube,duk kankantar takarda saiya dubata duk ya gigice gani yake kafin yaje za,ace mashi Alfahn ya mutu.xufa yake hadawa yana hwaye,Allah yasani yana son abdoul bayason rasashi abdoul yasha wuyar rayuwa bai cancanci mutuwa yanxu ba. Yafi minty talatin yana dubawa bai samu komi ba,ya tashi ya bude wadrop dinsa nan ma yayi mashi watsa watsa da kaya,daker da jibin goshi yasamu wasu kwayoyi cikin wata leda.daukosu yayi yana kallo bazai iya tantance ko namiye ba,don haka aljihu yasasu ya fice kamar walkiya. Zakiyya ma bata san zuwansa da fitarsa ba tana can tana rokama Abdoul samun sauki,tayi salla takai raka,a goma data sallame zata tada wata saida taji kafarta tagaji ta zauna ta rarumo qurani tana karantawa,har bacci ya saceta. Yana xuwa ya ba dr maganin yazauna yana jiran karin bayani,sun dade ahaka dashi yana dube dube da yan rubuce rubucensu na likitoci. Sannan ya tashi zai fita malik yasha gabansa. "Ina zaka bakaimun bayanin komi ba,kagaya ma maganin miye." "Janje pharmacy ne" "Aa ba wani inda zaka,wai dr kodai Abdoul ya rasune kuke boyemun" Tausayin malik din ya kamashi yace"wallahi da ranshi inson saina gama bincikena sainaji ddin yimaka bayani yadda zaka gane" Sakinsa malik yayi yana koma wa ya zauna kiran dadyne yashigo wayarsa,dauka yayi jikinsa amace "malik lafiya dai nazo gidanku na samu zakiyya take gaya mun halin da ake ciki,kuna wane asibitine oh ya Allah kakawo ma wannan yaron dauki" Hawaye suka silalowa malik yace "A.J.S.K hospital dake round din Ni,imah hotel." "Oky ganinan zuwa karka damu Allah yana sane da halin dayake ciki." Dr yaje ya gama duk abunda zaiyyi sun tattauna da likitocin da suke duba Abdoul din tare,sun gano cewar giyar da Abdoul yasha ce baya tayi mashi wannan illar,kuma shi yasan haka shiyasa yake shan magani,da alama ma yagana da wani likita babba,don duk garin wannan maganin babushi irin na wajene da ake shigowa dasu. Amman akwai allura guda da za,a iya mashi ya samu releif sannan in ya tashi sai yaci abinci yasha magninsa,zai samu sauki.amman duk randa irin haka ta sake faruwa ba makawa sai anma Alfah opretion. Sunyi ma dady da Malik wannan bayanin saboda tashin hankali dadyn kanshi saida yayi hawaye. Anmashi allurar sun saka mashi drip ya samu karfin jiki,sannan suka mashi Allurar bacci. Mafarin kenan ma dady da malim suka samu natsuwa,har suka tattauna maganar dayake shirin idan dare yayi yaje ya sanar dashi cigaban da aka samu. Amman yanxu sun bari gobe idan fiyah tazo sai suyanke abunyi. Yesmin da fiyah suke cin tuwo suna fira,Amman hankalin fiyah baya kan firar ansata kurin take badan tana son firar ba,jitake gabaki daya bata jin dadin ranta.tarasa abunda yake damunta tunda suka dawo gida,gabanta kuma yake ta yawan faduwa ta rasa gane kanta. Gajiya tai ta jiya lomar hannunta tatashi taje ta wanke hannu. "Safiyyah mekikaci anan,banson wasa da yunwa zauna ku idasa cinyeshi." Inji mama. Hawaye suka balle mata tana cewa"wallahi mama na koshi,idan nacigaba da ci amai xan kikyaleni" Sototo mamar da yesmin suke kallonta,"to miye na kuka anan daga magana sai kuka,ban skn sakarci fa ke baki girma rayuwarki haba mana saikace yar shekara goma." Gefe jata ta zauna tana cigaba da kukanta ita harga Allah wani kunci take ciki,tarasa dalili batasan meke damun xuciyarta ba. "Tashi anan tunda ba zaki bar kukan ba" Sake barewa tai da wani kukan tama cewa"to wai mama banda lafiya fa,ni bansan meke damuna ba zuciyata ta cunkushe ko.........taduke tana kukan. Shiru mamar tai tana kallonta saita sassauta fadan tace"zo nan to,zo kigaya mun mekikeji" Matsawa tai kusada mamar ta dora kanta bisa cinyeta tana shashshekar kuka. "Gaya mun yadda zan fahimta." Cike da shagwaba tace"gabana yake faduwa sannan ban jin dadin jikina, yayi mun sanyi xuciyata ta cunkushe kwata kwata abincin baya wucewa wani abu ya tsaya mun ga makoshi,kuma ban san komiye ba mama" Yesmin me zatai banda dariya ita wlh bata iya wannan shagwabar da Addarta keyi,haba ai ta girma amman ita bata jin komi. Harararta mama tai ta ke cema safiyyah. "Safiyya kina boye mun abu cikin ranki,halan kin fara soyayya ne ban sani ba" Zunbur tatashi zaune tana murtsike ido tana kallon mamar. "Eh haka nake nufi,saboda wannan yanayin dakike lissafi yayi kama da haka wata kila wanda kikeson ne yake cikin wani yanayi shiyasa jikinki yake baki,don haka sanar dani wanenen" *ANZO WAJEN*🤭 Don't share it plssss i beg. [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........36 Duk suna zaune baban shima ya jingina da filo ya gama cin abinci,suna dan hira da juna har uncle yahya yazo da Anty jamila,basu jima da tafita ba ma. Bude kofar akai aka shigo duk suka juya don ganin ko su waye,zaro idonta Safiyya tayi tana zubasu akansu,meya kawo su nan na shiga ukuna ni safiyyah. Gaida su mama sukai sanan sukayi ma baba ya jiki da adduar fatan samun sauki,kallonsu nake ta gefen ido ban so wani cikinsu ya anbaci sunana. Mama "tace samari daga ina bamu ganeku ba" Malik yayi murmushi yana shafa kanshi yace"mama daga wajen duba Abbi muke shine yace mushigo nan ma muga baban su fiyah shima abun ya shafeshi,Allah ya kyauta gaba ya rufa asiri." Jinjina kai mama tai tace "Ameen mun gode sosai,Allah yasaka da alkairi" Yace "Ameen bari mutai Allah yakara afuwa." Yana kallon fiyah suka juya suka fita,zakiyya na bin bayan sa "Yaya malik injin tsoron yan gidanmu su ganni nan wajen komi zai iya faruwa wlh,zasu cigaba da bibiyata har sugane inda nake sukasheni,wanan abun daya samu Abbi wlh shine shirin da su umma suke shiryawa,kuma nadaukeshi cikin m.card dinan yanzu idan kace mashi umma ce tayi wannan abun wlh yaya malik bazai taba yarda ba,shiyasa nakeson kakunna ma Dadday yaji da kunnensa,sannan shiyasan yadda zaije yi da Abbin har yasan komi,don haka kamai dani gida akwai hadari zamana anan." Ajiyar xuciya ya sauke yace"hakane zakiyya,tunda kinga ma bai saurareni ba alamun dai har yau yana kan bakanshi." "Hakane yana kan bakanshi anma cikin xuciyarsa yana jin wani feeling din wani abu,nayi imanin Abbi yana kewar yaya Abdoul,yakasa yardar ma kanshi abunda yake tunani,saboda asirin dake cinsa umma bata bar Abbi haka ba,wlh wajen boka zata kai sunan sa aimata aiki kanshi.kasan yadda Abbi yake da zafin rai da bin kwakwakwafi wlh da tuni yagano ta,amman saboda abunda tayi mashi baya jin maganar kowa sai tata,baida wasu y'ay'a dasuka wuce su zuwairat,sune yake jidasu ya mance da mami ya manta da ni,ima to balle wani Abdoul." Numfashi ya fesar yana cewa"zanje na ga daddyn da daddare idan Allah ya kaimu,komi kenan zuwa gobe fiyah zata fito exams saimu hadu can gidan dadyn,yanzu mukoma gida" Fita sukai daga asibitin suna shiga mota motar yan gidan ta tsaya,umma ce da dasu haulat da Amina.sai zuwairat din da khadija suduka dai yan dakin,sai mamman shine ya kawosu.fuskarsu babu alamun jimami ko tashin hankali,illa khadija daketa kuka haik'an har suka shige suna binsu da kallo,sannan malik ya tada motar ya fita daga cikin asibitin. Tunda suka fita gidan hanklinsa baya kwance ya kasa zama koda na minty gudane,duk ya firgice ya fita natsuwarsa. Duk yadda yaso cire dauwar abun ya kasa,wani irin kewa da tausayin Abbin nasa yakeji,ga kuma tausayin fiyah da ya gama kewaye gabaki daya jikinsa da xuciyarsa,kota wane hali yanxu?koya jikin baban nata Allah yasa bai tsanata ba,Allah yasa bata kuka duk jikinsa ya rikice zaman dirshen yayi kasa falon yana dafe dakansa,da zai iya zuwa da yaje yagansu kozai samu sukuni,tunda ya baro gidansu yauce rana ta farko dayakeji. Tsananin son ganin mahaifiyarsa da mahaifinsa,Allah sarki mami koya takeJi koya takejin kewarshi,wane irin kunci take ciki.jiyai wasu zafafan kwalla sun xubo mashi,yayi alkawarin duk wanda yayi silar jefasu cikin wannan kuncin da bakin cikin na shekaru shidda,shikuma yayi mashi alakwarin kare rayuwarsa agidan kaso,batare da hutawa ba kota dakika guda. Tashi yayi kamar antsikare shizai dauki makullin mota yaje yanemi asibitin yaga wane hali suke,yadda yakejin zuciyarsa da kirjinsa bazai iya jure rashin sanin wane yanayi suke ba,safiyya ta tsaya mashi garai yanzu haka tana can tana kuka har kanta yayi ciwo,kanshi ya sara,wasu zan tika suna mashi yawo cikin kai,har yakejin kan nashi yana sarawa. _kadauka cewa banda wani da acikin gidan nan mai kama dakai,babuni babu kai,ko ahanya kar kasake inga bakar fuskarka,na fiddaka daga cikin xuriata namance da na haifi da namiji,dana san zan haifeka Abdoul da ban auri uwarka ba,Allah ya isa tsakanina dakai.............._ Xubewa yai kasa numfashinsa yana sama da kasa alamun dai zai dauke..........idanunsa sun kakkafe,dandanan ya rarumo jarkar ruwan sanyi dake saman wani table ya kafa ga bakinsa,yaringa kwankwada ya mance da dokar likitansa na hanashi shan ruwan sanyi.zafi da kirjinsa yake mashi yasa ya ma mance dawata doka,kamar jira ruwan yake ya shiga cikinsa wani murdedden ciwon ciki ya mashi wata irin damk'a babu jinkirtawa ya fadi kasa sumamme. "Mama kibar wani tantama babu yadda Allah baiyyi da bawansa,kilan lokacine Allah ya kawo da zasu shirya ko baba" Murmushi yayi yace"uwata waye yace maki daman waye yace dake muna fada" Dariya tayi tace"baba ai bama ni ba,duk wanda yasanmu cikin wannan unguwar yasan cewa basu sonmu,shine mutun nafarko daya fara kyamatarmu,nafa sani baba don haka kilan wannan abun da kai mashi shine silar daidaitawar ku,kuma nima zanji dadi don banson inga ana gaba wlh" Mama tace"dadin ubanwa,bacin duk cin kashin da yamana ai taimakon da yayi mashi badon ya samu hanyar shiga jikinsa bane,kokuma su sasanta don yaringa taimakonmu,Allah ne yasa ma babanku xuciyar tausayi,kuma yaga yana da halin taimakon nashi shiyasa yayi,don haka ni bazan lamunci wata hidimarsu ba,wannan ma da sukai mungode " Dalha da baba na darita yesmin na taya su. Fiyah tace"baba kaji abunda mama tace ko,to wlh karka biye ta tata inhar yazo ya nemi sasanci wlh karka wani dauki maganar mama ku shirya ai Allah yasani babu kyau riko" "Iyye!don gidan ku ninake rikon kenan,?zaki rufe mana baki anan ko saina makeki,marar zuciya to ni bazan lamunta ba,azauna hakan yafi da aga rana guda ya shishshige mana ace son abun duniya ne ya kaimu" Nan dai kowa yaita fadar ra,ayinsa akan lamarin baban najinsu baice masu komi ba banda dariya da murmushi da yake. Wajen karfe shidda da rabi mama ta cewa sutashi sutai gida ayo sanwa akawo masu,aka shigo masu da wasu manyan kuloli,wajen guda hudu.wadda ta shigo da kayan safiyya take ta kallonta,tabbas wannan koba afada ba tasan jinin Abdoul ce babu mamaki ma itace ni,imah don komi na fusmar ta irin tashice,saidai kace shi na mijine ita macece. Gaidasu tai tana durkusawa tana ma baba sannu da jiki. Tace"mamina tace akawo nan tana gaida maijikin xata shigo" Mama tace"mungode amman ki mayar kice angode muma muna da namu........babane ya katseta da cewa"Aa ajiye yarinya kinjiko kice mun gode kigaida baban naki da jiki" Tace to ta juya ta fita tsunbul fiyah tayi tabita abaya mama na kiranta bata saurareta ba, "Ni,imah" fiya ta kirata juyowa tai tana kallon fiyar harta karaso inda take kallon juna sukai ni,ima tana mata kallon sani itakuma tana mata kallon tausayawa. "Kamar na taba ganinki unguwarmu" Cewar ni,imah murmushi fiyah tayi itama sai yanxun ta tuna sun taba haduwa,har suka gaisa ni,imah ce ta fito daga gida zata fita,ta yarda wata takadda to daidai fitowar fiyah daga gida kenan ta ganta,taje ta dauketa,tana sauri harta isketa tabata suka gaisa tana mata godiya. "Daman baban kune ya ceci Abbi,Allah sarki Allah yasaka mashi da Alkairi mungode sosai." Ta fada idonta yana ciwowa da kwallah. Riko hannunta fiyah tai suka zauna saman wani dogon table tace"kuka kike ni,ima meyafaru?" Share kwalar tayi tace"bacin babanku shima Abbyn da kila mun rasashi,kamar yadda tsawon shekaru kuma rasa yaya.........kukanta yakara karfi dakaji kuka kasan maiyinsa yana cikin halin kunci da damuwa. Tausayin ta yasa fiyah jin kwalla sun cika mata ido,yanzu umma ina zata da wannan hakkin,lallai mutane suna kusanta kansu da jahannama,kadauki hakkin wani saboda son xuciya da son abun duniya,wai ko suna mancewa da cewar duniyar karewa zatai oho. "Kibar kuka kinjiko,insha Allah shima yaya Abdoul din zai dawo kinjiko,ina mamin take" Tana share hawayenta tace"tana can gida bata zo ba,tadaice inkawo maku abinci" Shiru fiyah tai tana bukatar ganin mamin donta kwantar mata da hankali,don tabbas yadda ni,ima take cikin kunci da damuwa tasan mamin ta fita sau dubu.sun bata tausayi ta dafa kadarta tace"Allah yana sane daku qanwata,insha Allah komi ya kusa daidaita kicigaba dayiwa Abbinki da yayanki Addua Allah ya karesu daga sharrin mahassada da makiya,insha Allah za kaiki wajen yayanki amman kiyimun alkawarin zaki daina kuka kuma zaki sanar da mami itama,amman daga ita bance kigaya ma kowa ba,ita don tasamu natsuwa ki kwantar mata da hankali kice yaya Abdoul dinta yana nan cikin koshin lafiya,shima kuma kullum yana cikin kewarku." Mamaki da al,ajabin abinda fiyah kefada yasa ni,imah sakin baki tana kallonta da mamaki. Cikin doki da murna ta rungume fiyah tana cewa"na gode Antyna ngd Allah ya biyaku don Allah inzo yanzu muje" Murmushi fiyah tai tace"Aa ba yauba kiban no dinki idan na shirya zan kiraki gobe sai kizo muje karfa kigaya ma kowa" "Bazan sanar da kowa ba sai mamina nhd Antyna,bari intai driver yana jirana" Tatashi tatafi daka kalli fuskarta kasan tana cikin farin ciki. Juyowar da zatai don komawa dakin da aka kwantar da baban taga mama da yesmin tsaye bayansu. Iayakar rudewa tarude har saida hakan yabayyana ga fuskarta. "Mama kune........ Kuyi maleji plssss [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........38 Dabaki daya kan fiyah ya kulle jin abunda mama take fada,yesmin kau tayi sukuti taji me Addar tata zata fada dagaske ta fara soyayyar. Idonta duk awaje tana kallon mamar tama kasa furta kalma guda,duk wata basirarta ta karya ta kare ta nemeta tarasa. "Kiketa kallona safiyyah kina mamakine dana gane?" Girgiza kai tayi cikin dawowa hayyacinta tace"mama mekike fada,soyayya?ni nake son wani mama to waye?ni bansan saba gaskiya" Murmushi mamar tayi tace"karki daukan sakarai mana,nifa na haifeki babu wani abu da zaki boyemun cikin ranki,don haka saiki san abunyi koma waye inhar ba neman iznin mahaifinki yazo yayi ba,na abashi damar neman ki to wlh yana aikin banza,kuma duk randa babanku yaji labarin anganki da wani ko jalal yasamu wannan labarin wallahi safiyya karki rokeni inxo cetonki,tunda har kinyi wayon boye saurayi kuna haduwa awaje ko,saboda ke bakida hankali duk tarbiyyar da akai maki tatashi abanza kenan." Kuka ta fashe dashi mai rikitarwa,ita wallahi ba son wani take ba towaye ma zata so amman mama ta kama mata masifa tana cewa bata da hankali. "Kukan me zakiyi,don ina maki nasiha ina nusar dake abunda yadace da wanda baidace ba." Cikin kukan tace"wallahi Allah shine shedata shaidata ni bana soyayya da kowa,idanma zargina kike mama wlh nidai kin shiga hakk.........dungure mata kai tayi cikin fada tace"don gidanku nizan zargekin,nizan shiga hakkin naki to kinyi daidai kije kiyi duk abunda kikaga yadace da rayuwarki" Tatashi zata shige daki don ranta yabaci da fiyah sosai. Rarumo kafafun mamar tai tana kuka"kiyi hkr mama wlhh kinji na ramtse maki babu wanda nakeso,kuma babu wanda nake tsayawa dashi atiti,kiyarda dani idan da akwai aibazan yarda kisan halin danake ciki ba,nidai kiyi hkr idama don makaranta ce kike ganin ina fakewa da ita ina haduwa sa wasu to bazan sake fitaba,shikenan sai hankalinki ya kwanta mama" Janye kafarta tayi ta shige daki tabarsu da yesmin,kukan ta cigaba dayi tana data sanin yanayin data shiga har haka ya jawo fitina itada mahaifiyarta,abunda suka jima basuyi ba irin wannan fadan ita mamar. Yesmin keta bata hkr tana cewa"kiyi hkr Adda mama ba tayi bane don bata sonki ba,ita don tarbiyyarki takeyi wani idan ya ganki xai maki wani kallo na daban,kiyi hkr karki kullaceta." Kallon yesmin din take tashare kwallarta tace"kintaba ganin da nagari ya rike uwarsa mahaifiya garai,duk girman laifinta kuwa,don haka kibar cemun haka." Tatashi tashige daki tana shirin kwanciya,amman kalaman mama na mata yawo akai,hakika mama iyakar gaskiyarta ta fada,kuma tana tsoron lalacewar tarbiyarta shiyasa. Wayarta tadauko tana ma malik text,sai taga gara takirashi tayi mashi bayani. Ta gama komi ta kwanta yesmin dakin mama zata kwana,shiyasa ta sake ta kirasa. Lokacin sun rabu da Dady shikuma yana zaune gefen Alfaj daketa bacci,kallon wayar yayi ya yi picking. "Yaya malik ina wuni" Shima muryarsa tadan disashe yace"lafiyalau qanwata ykk yagidan" "Yaya malik baka da lafiyane?" Ajiyar xuciya yasauke yana kallon Alfah yace"dasauki dai qanwta,Alfah ne ba lafiya yayi doguwar suma daker akasamo ransa,Qanwata ashe Abdoul yana da wani ciwo bamu sani ba,nan yayi mata bayani atakaice,kuka yaji tanayi kasa kasa.shiru yayi yana tunanin daman sai haka ta faru barinta yayi take kukan ta samu natsuwa. "Yaya malik don Allah idan Allah yasa ya farka kace ina mashi sannu,zanso nazo na ganshi amman yaya malik Im sorry to say bazan sake zuwa inda kuke ba,domin kare abunda zaizo yaje mamana ta fara harbo jirgina,har tayi dogon fushi dani.kasan kuma fushin iyaye akan y'ay'ansu masiface babba,don Allah yaya malik kuyi hkr da rashina nayi iyakar abunda Allah ya bani iko,sauran kuma na barshi gareka da Zakiyya,ku karasa ni banyi don wani cikinku yabiyani ba nayine domin Allah da kuma tausayin sa daya shigeni ganina dashi na farko.don haka kuyi hkr zaku daina ganina,amman kila mun ringa gaisawa don gujewa fushin mamana" Hakika baiji dadin wannan labarin ba,don ya sake dagula mashi lissafi baiso ba yaso ace komi anyishi da ita,amman kuma iyaye suna gaba dakomi,shima mai goyon bayanta ne akan hakan. Numfashi yaja yace"bakomi safiyya ai aiki kam yazo karshe insha Allah,kin riga kinyi komi da kikai alkawari insha Allah ladarki naga Allah,haka nima daga gareni zan baki tukuici badan biyanki zanba,saidan yabawa da kokarinki don kinyi abunda dayawa mazan ma bazasuyi ba,ki sadaukar da lafiyarki,lokacinki kudinki da jin dadinki duk aka Abdoul ya dawo cikin hayyacinsa,to Alhamdulillah mungode Allah ansamu nasara don haka karki saka wata damuwa,Abdoul yagama dawowa *ABDOULNASEER ALFAH* Dinsa kuma insha Allah da kafarsa zaizo maki godiya,don haka ayima mama biyayya sannan abata hkr har sai ta sauko,kinjiko kanwata." Hawaye take sharewa sai takejin sunayin bankwana ne,kamar bazasu sake haduwa ba har abada.ga wani nauyi da kirjinta ya mata Abdoul take hangowa ranar da suka hadu Asibiti an sallami zakiyya,shigarshi cikin taci dinta da abunda ya faru wajen sai kurin taji kuka ya kubce mata. Shiru yayi yana saurarenta tabbas safiyyah ta kamu da soyayyar Alfah,Amman ita kanta bata sani ba don wannan kukan yasan duk akan shi takeyi,saiyaji tausayinta ya kamashi. "Kuka kikeyi safiyyah,miye abun kuka." "Yaya malik ka kula dashi don Allah,karka bari wani abu ya samai kagani baya da kowa saikai,kaine yake gani yana jin dadi,kamun alkawarin kulawa da shi yadda ya kamata." Baisan murmushi ya kubce mashi ba yashafa kanshi yace"indan wannan ne qanwata namaki alkawari,kidauka ma anyi angama kuma ai zamu ringa gaisawa time to time ko" Muryarta kasa kasa tace"insha Allah" "Oky to share kwallar,ki maida komi ba komi ba ai daya tashi zuwa safe ma zan kiraki saikiyi mashi yjikin da kanki ko" Shiru tai tana ajiyar xuciya.share maganar tai tace"yaya malik zan rako ni,ima nan asibitin yau mun hadu taje kawowa baba abinci inji mami munyi magana da ita har nai mata alkawari. Kawota wajen yayanta don haka idan zanje exam zan taho da ita na ajiyeta natai,kai saika sata taxi ta koma gida.wane asibitine kuke" Jinjina kokarinya yake lallai masu xuciyar fiyah sai antona. Gaya mata sunan asibitin yayi sukai sallama tana cewa yaje ya kaima daddy m.card dinnan komi kenan shiyasan yazaiyyi. Haka suka rabu kamar tabiyosa taganshi. Malik ya ajiye wayar yana nazarin hirarsu,duk abunda suka tattauna akan kunnensa,tas yaji wani babine mai girma ya budewa yarinyar cikin birnin xuciyarsa,hakika ita din wata fitilace mai mugun haske ga rayuwarsa,shin dame ya dace yayiwa wannan yarinyar sakayya.ta kawo cigaba arayuwarsa tayi tsaye tsayin daka akan rayuwarsa ta baya,ta sadaukar da ranta da kominta akansa,duk don ya dawo da rayuwarsa kamar baya,tana son dawo mashi da kimarsa daya rasa. Bai nuna ma malik ya tashi ba,cigaba yayi da kwanciyarsa yana nazarin kalamanta da yanayinta. Har wani sabon baccin yasace shi. Washe gari da safe duk wasu ayyuka da tasan tanayi tatashi da wuri ta farasu,don karfe tara da rabi time din shigarsu yaje farawa.ko yesmin bata tada ba ita kadai keta shige da ficenta tsakar gidan,ta share tas ta dora kalaci ta hau wanke wanke ahaka har ta gama ta dama koko ta juye ga plax,sannan ta shiga tuyar fanke,daman kuma tunjiya da daddare tanajin sanda mamar ta fito ta yi kwab'in. Tana gama wa taje tashiga wanka sai lokacin su mamar sua fito,yesmin nata kallon gidan tana mik'a. "Mama mun makara yau,duba kiga Adda duk ta gama ayyukan" Mamar ta dauki buta ta nufi bayi tana cewa"ta kyauta Allah yayi mata Albarka." Inda kurin bata gyaraba wajen kiwon kajinsu da dabbobinsu shine yesmin taje ta gyara shi. Duk sungama komi har wanka kowa yayi dalha yashigo yana gaida mama ta bashi kalacin baba yayi gaba kafin su gama nasu su taho. Fiyah tayi sukuku tunda ta gaida maman ta ansa bata sake cewa komi ba,duk jikinta asanyaye take break din Allah sarki uwa da diya sai mama taji duk babu dadi,yadda safiyyar ta saba da karkaina taringa karadi sa surutu tana jansu da abun dariya,duk sai taji tabata tausayi. "Kike ma Kalacin wani irin ci,kina duba lokaci kuwa" Inji maman. Yesmin tace"Adda tara saura minty ashirin fa" Kamar mai ciwon baki tace"na sani ai sai tara da rabi muke shiga." Feea ce tayi sallama duk suka jiyo suna ansa mata,idon fiyah akanta fuskar rafeea cike da annashuwa,kallonta taitayi suna gaisawa da mama har ta jiyo kanta tana cewa. "Kefa nabiyo mawa amman baki gama ba,zafa mu anshi exam card kar aje rabawa bama nan" Kasa cewa komi tayi taringa tura fanken tana binsa da ruwan kokon har ta samu suka shige baki daya,tatashi ta dauko abayarta da jikkarta,onready wayarta na ciki da duk abunda zara bukata. "Ki cire duk wata damuwa aranki kiyi jarabawarki cikin kwamciyar hankali,Allah yabada sa,a yatsare hanya sai kundawo kilan sanda zaki dawo muna can asibitin" Tace"to mama" Bin ta da kallo mamar tai tana jin babu dadi canzawarta,fita sukai da rafeea yau taxi zasu shiga bata fito da mota ba. "Baki tambayeni ba fiyah bacin nasan kin gane ina cikin farin ciki." Fiyah nata kokarin yin kira awaya tace"kinsan ai dole ne zan tambayeki don haka kibar saurin tambayata akwai abunda ke damuna nima,aman kiyi hkr bazan sanar dake ba" Murmushi feea tayi tana cewa"kobakice ba na gani afuskarki kuma daman ba tambayarki damuwarki zan ba,nasan idan kinyi niyya zaki gaya mun." Motace ta tsaya gabansu ni,imah ce driver ya fito da ita babu bata lokaci fiyah tace "muje ga sauki ya samu" Bata tambayeta ba itama ta bude bayan tashiga suka cigaba da tafiya,ni,ima na gaba tace"Anty ina kwana" Cikin murmushi tace mata"lafiya lau qanwata ya mami ta kwana" Murmushi tayi da alamar dai yau tana cikin farinciki tace"tana gida itama yau tana cikin farinciki tace ma na gaidaki sosai da sosai,kuma ta gode kwarai Allah yayiwa rayuwari Albarka" Wani sanyin dadi ya kama fiyah tace"Naji dadin adduar nan qanwara kice ngd sosai Allah ya kuma wanke mata bakin cikinta na tsawon shekaru,kuma kice mata cikin kwanan nan zataga suprise." Haka suka ringa fira tsakaninsu,feea dai tayi shiru tana mamakin meya hada fiyah da diyar gidan Alh amman datai nazarin maganganunsu ta gane cewar ta dalilin Alfah yasa,kuma babu mamaki a ni,imar zata kai wajensa.Allah sarki fiyah nada wata irin xuciya da mutane kalilan suke da ita,hakika tayi namijin kokari kuma Allah ne zai mata sakayya.ita tunda tasan Alfah ya mata nisa tasawa ranta salama,akwai wani d'an d'an kanwar mominta yake masifar sonta tana gwalesa,yanzu ta sassauto sunma daidaita kansu,tana ma fiyah fatan ace Alfah ya aureta don aurenta dazai shine kurin abun da zaimata ya saka mata..............sunxo bakin asibitin da aka kwantar da Alfah,fiyah taji wani ciwo cikin ranta inama taje ta ganshi,Amman babu wannan damar tayiwa kanta alkawarin dakatarwa hakanan,Amman tasan tsawon muamalarsu zuciyarta tayi wani mummunan raunin da bazata taba warkewa ba,illa tayita fatan Allah ya sassauta mata halin da take ciki. "Anty bazaki shigo ba ke" Girgiza kai tayi tana jin kwalla na tarar mata tace"aa ni,imah makaranta zanje exam gareni lokaci ya kusan wucewa kigaida shi da jiki kinjiko,sannan karkiyi kuka ki daga mashi hankali room 136 male ward zakije saiki ringa duba dakuna zaki ga daki mai no. 136 Sai mun yi waya byyyy." Suka sauka suka hau taxi suka wuce makaranta,kuka ta kamayi cikin mota feea bata ce mata komi ba,don ga dukkan alamu fiyah na cikin halin kaunar *ABDOULNASSER ALFAH* batai mamaki ba don daman hakan zata iya kasancewa,amman tasan ita kanta fiyar ba ganewa tai ba. Duk dokin sanar da ita dawowr mominta da take saita hkr har saita dawo natsuwarta. *don't share it pls I beg u* [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........39 Exams tayi dadi sosai wajen fiyah,batai tunanin zata iya ansa duka question din ba,ganin yadda suke da yawa basu samu kansu ba sai bayan la,asar feea ta kira waya driver yazo yatai dasu. Acikin motar ne fiyah tace"baki gaya mun farin cikin dakike ciki ba feea" Murmushi tai tace"dazun naga baki cikin mood mai dadi shiyasa,daman ince maki momi ta dawo shekaran jiya,dady dakansa yaje ya dauko ta,kuma maganar aurensa babu ita don ta gudu yarinyar ance ba,asan ma inda take ba shikuma dady yace sadda akaganta ayi inkuma ba aganta ba shikenan,ya hkr.mafarin yaje yadawo da momi kenan,nhd fiyah duk nasan yana daga cikin komarinki Allah yabaki abunda kike nema,kema Allah yabiya maki bukatunki yaba baba lafiya." Murmushi fiyah tai tace"Alhamdulillah insha Allah dady bazai sake yunkurin wani auren ba,dagashi sai momi" Dariya sukai asibiti aka wuce da ita saida feea ta gano baban sannan tawuce gida. Tunda tashiga asibitin take ta duba no din dakin da fiyah tace mata,kafinma idonta yagano dakin tayi tozali da malik.rabonta dashi bazata iya tuna wa ba,kwalla suka silalo mata aguje ta isa inda yake ta rungumesa ta baya tafashe dakuka,baisan hawaba kurin yaji mutun juyowa yayi idonsa akanta,ajiyar xuciya yayi yana rikota sosai. "Ni'imah!A U OKY kinga daina kukan haka karki tara jama,a xomuje ai ba kuka zakiyi ba dariya da tsalle zakiyitayi yaugaki ga yaya Abdoul ga yaya malik dinki,oya zo muje daman nafito neman dr ya sake duba jikinsa,muje to" Riko hannunta yayi suka wuce cikin dakin. Jingine yake da filo yana shan tea marar zafi sosai ga plet agefensa yana cin dankali kamar baya so. Bude kofar da akai yasa idonsa ya sauka wajen,daman yaji ajikinsa zaro ido yayi kamar zai fixge drip din yazo ya rungumeta,malik yayi saurin dakatar dashi. Aguje ta karaso ta rungumeshi ta fashe da kuka. "Yaya.............."sai kuka Runtse ido yayi yanajin zafin kukan nata wata irin kewartace ta kamashi,tausayinsu ya lillibeshi dandanan yaji kwallah suna sauka shima ga fuskarsa,sunfi karfin minty talatin haka dr yazo ya samesu,yaja gefe yana kallonsu cike da tausayi. Dagota yayi yana kallon fuskarta yana share mata kwallar yace cikin muryar marasa lafiya. "Ina mamina,tasan zakizo nan waya gaya maki inanan karfa Abbi yaji kinzo kishiga matsala" Tana goge kwallarta tace"Dady ne ma yace intaho babu wanda zai san nazo,mami tace ingaidaka tana kewarka har bakinta bazai iya furtawa ba,yaya yaushe zaka dawo gida wlh muna bukatarka mami kullum bata lafiya saboda rashinka,gashi Abbi yadaina kulamu har mancewa muke dashi agidan,saidai dady ne yake hidima damu." Yana rike da hannu ta cike da damuwa yace"karki damu zanzo watarana kice ma mami nima ina kewarta sosai,tacigaba da hkr watarana sai labari kinjiko,yajikin Abbin yake kinje kinganoshi" "Eh naje jiya acan ma na hadu da wata fiyah,itace tace inshirya zata kawoni wajenka,tare muke dasu.............jekice tashigo ya zaki barsu waje. "Aa yaya tatafi tace jarabawa gareta,amman ince maka tana maka yajiki Allah yasawake" Dafe goshinsa yayi wani irin feelings din yarinyar yana taso mashi,ta ko ina tagama mashi komi arayuwa. "Yaya lafiya" Daker ya bude idonsa yace"kinsan inda take ne,imean gidansu" Daga kai tayi tace"eh yaya muna opposite dasu gidan malam kabir el-ladan fa take" Tsura mata ido yayi kamar zaiga wani abu akan fuskarta,malam kabir el-ladan safiyya diyarsa ce daman,innalillahi akwai damuwa ya tabbata yadda yasan tsohuwar gabar dake tsakanin sa da mahaifinsa bazata taba bari yasameta ba. "Ka riga ka ansheta matsayin abun kaunarka kuma wacce kazaba ta zamemaka matsayin matarka???"tambayar da xuciyarsa tayi masa kenan nan take. Shiru yayi ya kasa magana malik shima nazarin maganar ni,ima yake tabbas shima yasan abbi baya hudda da su,shi sai yanxu yake gane ma mahaifin fiyar. Dr yace"lokacin bacci yayi karka takura kanka a dogon tunani,munbada sallahun maganinka jiya dr hisham yatai malesia nasan zai samo,don wanan bai wuce yayi maka five days ba.kuma bama son ya katse maka akallah kasha na kwana talatin,kullin kasha muga Abunda Allah zaiyi." Cire mashi drip din yayi yana mashi Allurar bacci,idonsa akan ni,ima gani yake kamar daya rufe ido bazai sake ganin taba. Riko hannunta yayi yace"zakixo gobe ko?karki damu zan samu lafiya,kikoma gida banson wani abu ya sameki,ki anshi no din malik sai kikirashi inkinje wata kila asallameni zuwa gobe,sai kixo gidanmu ko" Daga kai tayi tana rike hannunsa ta sumbacesa tace"Allah ya sawake yaya bari natai" Malik ya bita wajen xuwa wajen mota ta anshi no dinsa sukai sallama. Malik shiryawa yayi don samun daddy ayi wacce za,ai don yau insha Allah sai sun saurari abunda kecikin m.card din Daddare ya shirya yace ma Alfah zaije wajen dady yadawo,da ido kurin yabishi don gabaki daya yarasa natsuwarsa,rashin yarinyar na kwana biyu duk ya rikita mashi tunani,matakin da ta dauka akan su baimashi dadi ba,jiyake kamar yatuge wannan shege drip din ya je gidansu,amman yasan bazai iya zuwa ko da kofar get din ba,balle har yashiga ya dauki alkawarin shida maitama har abadan abada. Malik har gida ya iske dady suka gaisa da matarsa mai tsananin kirki,itace ma tai mashi iso ga dadyn har babban falonsa,aka kawo mashi kayan sha da ci amman ba tasu yake ba,soyake akawo karshen komi dake faruwa cikin rayuwar Abdoul,abun ya isa haka yana cikin kewa da mararin ganawa da mahaifansa,amman wannan babban ginshikin yatare komi,ya hana komi tfiya yadda ya kamata. "Malik sannu da zuwa ya hanya" Ya na zaune kasa ya sadda kai yace "lafiya lau dadyy,ya nasameku" "Angode Allah,ya jikin Abdoul din fatan yana samun sauki sosai,naso nazo dazun nasake dubashi sao aka kirani office,amman dasafe zamuzo da yara harda mamansu mudubashi" "Allah ya Kai mu dady,dayake ma goben ake saka ran sallamarsa ai" "Masha Allah Alan ya sa iyakar wahakar kenan,da alama dai akwai magana ko,to inajinka" Muskutawa yai ya ciro wannan m.card din daga cikin aljihun rigarsa,ya nadesa cikin wata takadda ya warwaresa yana cewa"dady wannan shine kedauke da duk wasu abubuwa damuke son sani game da makarkashiyar da aka shirya ma Abdoul,kuma anan ne zamu san suwaye suka hada wannan abun,musan kuma dalilin dayasa sukai hakan idan kayarje man zan sashi ga system din danazo dashi mu saurara." Jin jin jinakai dady yayi yace"naji dadin wannan magana malik,kuma hakika kaida wannan yarinya safiyya Allah ne zai biyaku,domin kunyi abunda za,a yaba maku Allah yayi maku Albarka,amman ina kta safiyyar ba kace tare zaku zo ba" Cikin jimami yayiwa dadyn bayani ataikaice shima ya fahimceta yace "babu damuwa ai tariga ta gama komi sai fatan Allah ya biyata,yabata miji nagari wanda zai kula da ita har karshen rayuwarsu.ni da nai zaton ma kana sonta Abdoulmalik,har nafara murna ta samu miji na kwarai." Murmushi yayi yana sosa kai yace"ai dady da nasotan,kuma naita fatan daburin na zama mijin nata,saidai duba da wasu abubuwa danai naga bani ne nadace da ita ba, ABDOUL-NASSER yafini bukatar samun mata kamarta,domin shine koda yaushe rayuwarsa take cikin hadari,koda yaushe ake neman kassarashi,sainaga safiyya yarinyace mai hankali da natsuwa tanada wasu abubuwan da zaka nemesu ga mata dayawa baka samesu ba,ga ilimin addini tana da wayau da dubara komi zatai saita yi nazarinsa ta lakancesa kafin ta aiwatar,haka zalika tana da juriya sosai ga uwa uba hkrinta shiyasa naga gara na hkr wata kila silar sadaukarwar danai Allah yaban makamanciyarta.shiyasa nai iyakar kokarina wajen ganin nahada su da juna,har saida naga nayi nasara don ina kyautata zaton suduka suna son juna Allah ne bai basu ikon furtawa ba,yanzun haka yana can cikin damuwar rashin ta kwana nan." Jinjina kai dady yayi yace"kayi tunani maikyau malim,kuma insha Allah Allah bazai barka haka ba,hakika zai maka tanadi na musanman.naji dadin jin wannan labarin don haka kasaurari kyautata daga gareni insha Allah." Dariya yayi yace"to godiya nake dady,zamu iya kunna wa duba da lokaci" Dadyn yace "mezai hana bismilla nima na zaku danajin abunda kefaruwa don akwai wani zargi cikin raina" Malik yasaka wannan m.card ga system dinsa yashiga yana uploading dinsa har yahau yashiga cikinsa yana dubawa,recording ne kashi uku guda daya kuma vidion ne. Kuyi hkr jiya nayi alkawari na saba,wlh ban dawo da wuri ba shiyasa kuyi manage dashi plsss *don't share it plss I beg* [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........41 Sanda yaje har anrubuta sallamar dr yana sake nanata masu kiyaye dokokin dasuka gindaya ma Abdoul din,na daina shan abu mai zafi sosai ko mai sanyi sosai,daga yadda malik yake Abdoul yasan ba yacikin mood mai dadi.kallonsa yayi tayi suna tafiya zuwa gida,hardai ya kasa jurewa yace masa"malik kana lafiya kuwa?" Ba tare da ya kallai ba yace cikin sanyin murya"kaina keciwo shiyasa" Shiru Abdoul yayi amman badan yayarda da abunda yafada mashin ba,baisake tambayarsa ba don yasan ba fada mashin zai ba.lumshe idonsa yayi yana sauraren xuciyarsa dake ta dawo mashi da moments dinsu nabaya shida safiyyah,wani yayi murmushi wani ya jinjina kai yana nadamar wasu kalamansa na baya da yake jifarta dasu,harta hkr batai fushi ba tacigaba da taimakonsa.yayi bincike bai hango yarinya kamarta mai irin wannan hankalin da hkr da tarbiyya ba,ga natsuwa idan zai kwana yana lissafa halayyarta kilan bazai gama ba,don yalura kullum da wasu sabbin halayen zai sameta.ahankali yafurta "mijinki ya More" jiyai kirjinsa yayi masa nauyi saboda abunda ya furta,kenan wani duk zai samu wadannan abubuwan gareta,wata xuciyar take kitsa mashi inka yarda kana sonta maizai hana kafito kabayyana hakan,girgiza kai yayi shikadai malik na ganin yanayinsa baice mashi komi ba,don shima danashi kason tunanin kilaman saiyafi nashi rudani da rikitarwa.har sukaje gida babu mai magana suna yin parking zakiyya tafito aguje tana zare ido.idonta ga Abdoul tana kallonsa,malik yadaure yayi mata murmushi yace"kekadai gidan ko,gashi babu abun ci gidan Allah yasa ko tea kinsha" Kwalla cike da idonta tace"aa bazan iya saka komi acikina ba yaya malik,hankalina duk baya kaina yana wajen ku ina tunanin ko yajikin sa." Abdoul yazo yara b'ata yawuce baice mata cikanki ba,duk suka bisa dakallo. Malik yace"yaji sauki sosai,aikin gani ko." Sadda kaitai kasa yace"karki damu kanki akansa zai warware zaku daidaita,bari nayi waya akawo mana take away kije ki kwantar dahankalin ki karma kisama kanki damuwarsa zai waiwayeki ne" Juyawa sukai suka wuce cikin apartment din babban wanda keda different part's acikinsa. Zube yake kan kujera ya rufe ido still tunani yake. "Daka sassauta ma ranka don gudun abunda zai sameka,kasaurari xuciyarka abunda kaga ta yanke maka akai maikyau sai kayi anfani dashi,amman dogon nazarin bashida anfani amman idan kaji shawarata." Ya wuce dakinsa habarsa da zakiyya daketa hawaye ita kogajiya batayi,tsaye take gefensa takasa mashi magana gani take kamar zai mata tsawa. "Kin tsaya bisa kaina plss move" Silently yayi maganar matsawa tai ta dawo gabansa tana zama tare da tankwashe kafafunta tace"yaya Abdoul yajikin naka" Batare daya kalleta ba idonsa yana kallon rufin falon yace"da sauki" Shiru tai ta cigaba da alwallar kuda kamar taza rushe da kuka tace"yaya Abdoul na gaza samun hanyar dazan fuskance ka da batutuwan dake bakina,bansan dame zan fara ba saboda nasan nidin mai laifice wajen ka,amman yaya Abdoul ka fahimceni duk abunda nai nayisa ne bisa dalilai da yawa kaban dama na warware maka dukullin dake faruwa." Malik ne yafito yanajin abunda take cewa yace"kyaleshi zakiyya bayanzu ba,akwai lokaci yana xuwa tashi kije ki shirya ga abinci nan ankawo.tashi tai tatafi kamar wadda kwai ya fashewa acikinta. 💕💕💕💕💕💕💕💕💕 Jikin baba yayi sauki sosai yana samun kulawar likitocin yadda ya kamata,har ansallami Alh muazzam amman kullin sai yazo ya duba jikin baban,mama dai ba dadin hakan takeji ba amman baba ya hanata nunawa,anty jamila ma sun sake xuwa ita da uncle harda muhseen,wanda dandanan sabo yashiga tsakaninsa da baban saboda yadda yakeda faranfaran da barkwanci,bayada bakunta kokadan.koda fiyah ta isa ma bai jima da tafiya ba,ta samu sai labarin suke gabanta yafadi badai muhseen ta nan yabiyo ba? Har dare suna tare da baba saida tara tai sannan suka tafi cike da mashi Adduar warkewa da wuri yadawo gida don suna kewarsa,yaya jalal gobe yana bisa hanya sunyi waya da baba. Koda sukaje gida fiyah wanka tai ta saka kayan bacci daman sunci abinci dare can asibitin,wanda mami ta aiko driver dashi yayi dadi sosai ga nama zuku zuku aciki,da lemu. Yesmin yauma tana wajen mama goma nayi suka rufe gida daman dalha shagon kofar gida yake kwana. Karatun ta take na exam duka da daman tariga duk ta rage yawanshi sai wasu wurare da basuda yawa,gajiya tai don duk maimaice take yi tariga ta haddace su tas. Hamma takeyi ta ajiye hand out din gefe da asuba tasake bita,har yanxu xuciyarta bata jin dadinta,wata irin kewa takeji jitake kamar ita daya take yawo acikin sararin samaniya.kwanciyatai tana yin lamo badan bacci ba,kamar wasa tajiyo rurin wayarta xunbur tayi tatashi tana rarumota,sunan malik taga ana yawo akan wayar tatashi sosai tana daga wayar "Assalamu alaikum yaya malik ina wuni" Shiru taji anyi ta duba wayar taga har lokacin wayar tana tafiya,sake magana tai. "Yaya malik inata magana lafiya kuwa" Ahankali taji wani sauti daya jefa xuciyarta cikin wani mugun shauki,taji gabaki daya duk wani karfi najikinta yana macewa,wata kasala na zuwa tana lillibeta bata san sadda idonta suka lumshe ba,wani abu yana bin duk ilahirin jikinata. Jitai yasake cewa. *"safiyyah"* Kadan ya hana bata yi sumar wucin gadi ba. Sorry Muhadu gobe at this time.don sanyin idaniya kurin zanyi dasafe alfah sai kamar yanzu. Don't share it plz I beg u Bcos its for sale. 300 naira only [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........40 Nuna ma dadyn yayi yace"gasunan dady zamu fara da videon ne ko mu gama sauraren audion sannan" Bayan ya duba yace "kunna audion muji" Jikin malik na rawa ya ja aro din computer zuwa wajen audio ya yi double click dinsa,dan danan yafara loading zai bude.sudukan gabansu ke faduwa don basu san me zasu saurara ba,yadauki almost 3mint sannan ya bude muryace tafara magana,wadda nan take suka dago ko murya waye. Watau muryar umma tana cewa"kwangila ina cikin tashin hankali,bacin tsana da kiyyar danake yiwa Yaron nan Abdoul nasser ya sake jefa kanshi cikin wani bala,in domin kuwa ajiya ina mai tabbatar maka da cewar ya gannmu sadda muke aikata son ranmu,idona idonsa bakin window wlh har ihun da kake yi akan kunnensa har saida yatoshe kunnensa,yajinjina kai yayi kwana yabar wajen.duk da nasan bazai gaya makowa ba dole ne mudauki mataki akansa,don kuwa zai zamemana barazana ga zamanmu dagani har kai" Alh kwangila ya sauke numfashi yana share gumi yace"innalillahi nashiga uku wane irin bakin labari kike gaya mun,har kice bazai sanar dakowa ba taya kikasan haka,to gaskiya niba zan dauki lokaci waje ganin mun kubuta tunda bacin shi babu wanda yasan ina zuwa wajenki muna muamala dajuna,kuma bacin haka mariya banajin akwai wanda xai dakatar dani daga muamala dake,kin sani tun kuna farkon xuwa unguwar nan nazama mijinki na biyu,kina mun dadin da matana bata taimun,don haka dolene zai dauki mummuna mataki akansa,kinga hanyar dakike nema wajen ganin kin kawar dashi daga gidan,domin kisamu damar tattare komi kafin plan B ya fara aiki ko" Dariya suka kwashe suduka harda sautin kashewa dasukai dajuna,tace"in maka na turawa zat wai ai lobiyu"suka sake kwashe wa da dariya kamar mahaukata. Yace"yanzu kina da wata dubara kowata shawarar yadda zamufara bulloma lamarin ko kinbar komi hannuna." Jim tayi tana nazari tace"abunda nake so kwangila wani tuggu nakeson ahada mashi,wanda bama mutanen cikin gidanna kadai ba har jama,ar gari kowa yatsanesa incusa tsanarsa cikin ran mahaifinsa ta yadda zai mashi mummunan kalamin da koxuciyar kare garai bazai sake tako kafarsa hanyar unguwar nan ba,ta haka zan saka mamman ya maye gurbinsa mumallake abunda nake hari shekara talatin tun ranar da aka haifeshi shegen yaro yazo da arxikin da shikanshi uban baiyyi tunanin zai samesa ba.shegiyar uwarsa daman ni bana kallonta wata matsalata da zaran na kora dan nata itakuma nasan ta inda zan biyo mata." "Kinata surutu baki gaya mun yadda plan din zai kasan ce ba" Murmushi tayi tace mekake ci na baka na xuba,zakaji amman saina gama tsara komi kasan zakiyyata suke soyayya,da har nafara daukar mataki akai sai yanzu kuma wani tunani yazo mun,don haka dole da zakiyya zanyi anfani,katashi katai kafin yarana sudawo su sameka don kosu ban bari sunsan ina bin mazan waje ba" "Mariya kice bani kadai nake nitso cikin fadamarki ba,har wasu kike bi awaje" Tsaki taja tace"to meye kaidinma ai bani kadai kake ma aiki ba,ansha gaya mun kana xuwa hotal kana shanawarka da yan shilan yara,to donme zan zauna dakai kaidaya kamar rai,mijina ma ban zauna dashi shikadai ba saikai,nimubar wannan maganar katashi katai zan sake tunani kafin na nemeka,nasan ma kafin na nemonka kai kakawo kanka maye kawai,kai mace bata taba isarka." Dariya yayi yace"inma zaki karaman wlh so nake don waccen dusar yadda kikasan hanyar da babu titi haka take," "Nibanson wulakanci,matarka mace mai kirki da tsafta da kiyaye wa amman karinga cin amanarta wlh sai Allah yasaka mata,amman dai shikenan tashi kabi ta baya kafece kafin aganka" "Shikenan saina sake zuwa" Daidainan audio guda ya kare. Shiru sukai kowa yana saka wa yana warwarwwa cikin ransa,dady yajima yakasa magana don wallahi daman zargin dayake kenan,amman bai taba kawo cewar suna neman juna ba kawai dai yasan cewar umma da Alh kwangila akwai saka hannunsa cikin wannana lamarin. Malik daskarewa yai yaka sa motsawa,maganganun sunyi masifar daure mashi kai,har rashin imanin umma yakai haka. Wata xuciyar tace bakaji komi na sai ka gama saurarar sauran. Ajiyar xuciya yaja yana kallon agogonsa yadago daker yace"dady zanje na duba jikin Abdoul wata kila ansallamesa yanzu,zuwa gobe insha Allah sai mu idasa sauraren sauran,zanbar computer anan saboda tsaro." Dady bai iya magana ba saidaga kai dayai,malik yafice daga falon yanajin kafafunsa suna mashi nauyi. *kuyi hkr da wannan insha Allah zan baku na dare* Don't share it plss Bcos its for sale 300 naira ne gamai bukata.ya tuntubi wannan no din. 09034722970 [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........42 "Naam" Can kasan makoshi ta ansa kiran da yayi mata Shiru suka sakeyi sai musayar numfashi dasuke,dan maxewa tayi muryarta kamar daga frig aka fiddota tace"wake magana,nai tunanin yaya malik ne sai naji ba muryarsa bane,who is on d line" Idonsa dake lumshe ya budesu akan malik dake kallon news,sannan yabude baki daker yace"malik kai take nema" Gabanta yafadi badai ajiye wayar zai ba yabarta da wannan kullellen mikin dake cin ranta,malik yace "ba nema na take ba kaidain dai take nema kasake saurare kaji" Taji abunda malik din yafada ras tayi murmushi kasa kasa tasake kwanciya tace"oh sorry yaya Abdoul ne ashe ina wuni,ya karfin jiki Allah yasa kaffarane" Ajiyar xuciya yasauke yana cewa"nagode,yajikin baban?" Bata san sanda muryarta take komawa yar karama ba tace"yana samun sauki,may be gobe musamu asallamesa" "Okay" Jin muryarta yake kamar yau yafara jinta,tundaga yatsansa na kafa yajin wani yanayi har cikin kansa,shirun itama tayi tana kwance kamar zata tsaga katifar tashige cikinta. "Ina zakiyya?" Bude idonsa yayi yabin hanyar dakinta da kallo,sai yasamu kansa cewa"gata nan kusa dani" Wani kullutune yazo mata wuya ya tsaya,duk miyan da take hadiyewa yaki wucewa,shiru tayi shikuma yasake anfani da yin shirunta yace"yana mun firane inasamu bacci,taje ta hado mun tea insha idan ta dawo zan baki saiku gaisa" Runtse idonta tai tana damkar zanen gado tare da sauke wani wahalellen nishi,mai tafe da hawaye.saurin rufe bakinta tai don ba wuya kukan na iya tahowa. "Are u on the line" Shiru tayi tana sake rufe bakinta,tana kukanta ahankali can kasa sosai. Natsuwa yayi don fahimtar yanayin ta,ahankali yakejin numfashinta yana sauka da sauri,yanayin kukanta yana shiga kunnensa. Tsikar jikinsa ce tatashi don kukan ta yatada mashi hankali ainun. Kin nuna mata yayi badan hakan baya taba shi ba,aa yana tabashi har cikin ransa amman dole zai bita ahaka badan yaso ba. *"sofiyyerh"* Ahankali cikin voice dinta data sha kuka tace"naam" Runtse ido yayi yana damke hannunsa jiyake kamar tana tafiya da numfashinsa,muryarsa silently so sweet yace"kina kuka ne" Daker tace "uh uh" "To menene?bakison zakiyya na mun firane" Ajiyar xuciya ta sauke tace"ina ruwana da hirar da take maka,meye nawa idan nace kar ta maka fira,kunfi kusa ai karka sake sani cikin batunku pls" Murmushin da bai shirya ba yayi har tana jin sautinsa yace"oky don't worry baza asake ba,hope kinyi exams lafiya" Kin bashi ansa tai tace"zanyi bacci saida safe" Lauya muryar yayi yace"oh sorry to kiyi baccin ki mana,zan so haka ma" Tsaki taja kasa kasa tace"kashe wayarka" "Kekika kirani ashe?" "Ban Sani na malam karka mun gori ai ban roki kakira ni ba balle ka raina mun hankali," Dariya tafara cinsa wadda bazaice ga lokaci. Daya yita ba. "Masifatu kurin,karki sake ki mun rashin kuya wlh har nan kan gadon naki zanzo na baki punishment,wanda nasan zai ladaftar dake." Yafada da wata irin murya hade da salo wanda nan take ya idasa kashe bakin fiyar. Shirunta dayaji yasa yayi murmushi don yasan sakon yaje,dariya yayi ta burgewa yace"matsoraciya,har kin tsorata da wuri tun kafin ma inzo,uhmm kinsan hukuncin naki ashe shiyasa kikai shiru." Ahankali kamar mai koyon magana tace"angaya maka ni Allahn musuruce dallah can saida safe karka sake kirana" "Okay Zane ringa kiranki sau uku arana,yayi maki ko" Tsaki taja tace cikin masifa"dalla cewa nai karka sake kirana" "Oh yayi maki kadan sau ukun,kenan sau biyar zan kira din." Batasan dariya ta kubce mata ba,don yadda yake juya mata magana abun ma saiya bata dariya. Shima taya ta yayi da murmushi mai tsada wanda da agabanta yake saita kusan suma don yadda zai daukar mata hankali. "Angaya maka ina bukatar kiranka?to inkakira ni mezan maka kokuma meza kaimun" Kamar yana rada yace"wai in ringa ladabtar da bakin nan naki mai rashin kunya" Babu shiri tayanke wayar don yama shirin kaita inda bata da mai maidota. Wanna dare dai xukatan mutun uku basu huta ba,zakiyya sabon son Abdoul dinne yayi mata dirar mikiya,jitake kamar yanzu ne tafara sosan bata da wani fata da burin taga sun june har takaisu ga mallakar juna,amman tasan akwai kalubale sosai don Abdoul hankalinsa baya kanta ahalin yanxu,ya zatai ta dawo da soyayuarta sabuwa cikin ransa. *SOFIYYAH* wata xuciyar ta anbata mata tabbas zata iya daidaita su har ma kilan sudawo sufi da son juna,zata nemota itace kurin hope dinta. Abdul kuwa saida yayi dagaske sannan ya samu bacci don kwata kwata xuciyarsa babu komi ciki sai shaukin son kasamcewa da wannan yarinya mai daukar hankali,gabaki daya baisan yadda zai misalta yadda yakeji ba,shidai yasan yana shan wuyar kewarta na kwana biyunnan. Haka yake ga fiya murje murje taitayi agado xuciyarta tana saka mata tana kwance mata,amman kishin zakiyya yaddane duk wani feelings dinta akanshi,hakika yadda takeji ga xuciyarta bazata iya shiga tsakaninsa da zakiyya ba,don ita masaniya gareta akan soyayyarsu.koda xuciyarta tayi kokarin ganin ta kaita inda bata dace da wajen ba,ita zata janye kanta.don bata iya daukar rebel sai goshin asuba bacci ya dauketa. Washe gari da wuri tatai school don eight sukeda exams yau sai shidda zasu dawo gida,don ko break bata tsaya ba feea na xuwa suka wuce yau da mota tafito. Mama tace idan tataso tayo gida kurin don da rana zasu sallamesa suyo gida. Malik saida yaje store yaduba yadda abubuwan suke tafiya sannan yaje company shima yarage wasu ayyukan kafin yakira dady don yaji yaushe yake zaune su idasa sauraren wannan Audio din. "Malik kabari sai dare yanzu haka ma ban garin,amman immediately dana dawo zan kiraka" "To daddy Allah yadawo dakai lafiya,ni sonake ma muzo da Abdoul yaji komi" "Aa karka zodashi yanzu bayada lafiya,tattalinsa ake idan har yaji ayanzu komi zai iya faruwa,kabari ya kara samun lafiya inso samune lokacin sun daidaita da safiyya abun zaifi sauki,duk yadda yahau zata iya sassauto dashi kagane menake nufi ko" Malik yace"hakane kuma dady shikenan Allah ya dawo dakai lafiya" Sukai sallama ya cigaba da aikinsa yana ganawa da costomers daga kasashe daban badan,kullum kamfaninsu kara cigaba yake yanzu haka yaga wasu schedule da Abdoul din ya rubuta cewar zai bude reshen kasuwancinsa can Australia,sannan zai ake fadada store dinsa zai sake hude wani wanda yafishi kayan nagartattau kuma masu kyau.amman baikai ga sanar da malik din ba shine dai yaga takardar cikin drower dinsa na adana muhimman abubuwansa. An sallami baba jikinsa alhamdulillah,yana dan taka kafar amma ba sosai ba,sun bashi yar sandar dazai ringa dogarawa har xuwa sanda zai take dakansa. Muhseen ne yazo daidai sanda zasu tafi gida,mafarin kenan ya daukesu amotarshi suka taho gida,yesmin keta mashi surutu duk da kasancewarta ba mai magama ba sosai amman saita samu kanta da yiwa muhseen din labari,har saida mama ta kwatseta sannan ta bari. Dariya muhseen din yayi yace"mama kibarta inajin dadin hirar,munada irinta gida ai ba takura man tai ba," baba yace ta kyalesu. Dole mama ta samasu ido tsayawa yayi yayi musu siyayya mai sunan siyayya,ledoji uku manya babu wanda ya damu don basusan cewar nasu bane da tun wajen baba yayi fada. Muhseen kau ya kudiri yau bazai tai ba saiyayi ma baba maganar fiyah,don yagaji da dakon kaunarta bacin ita bata shi tae a,hakan dazai mata shine zaisa dole ta kulashi ahankali tasoshi ga baya. Cefane ne leda guda sai dankalin turawa tiya uku sai naman miya na dubu biyar,sai fruits cike da wata leda ayaba ce kankana ce gwandace da abarba harda apple. Saida sukaga yana shigo dasu yesmin nataya shi sannan suka san ashe su yasiya mawa nan fa aba yayita fada yana cewa ya dauke yakai can gidansu meyaa zaiyyi dawainiya dasu har haka. Mama dai shiru tayi don ranta yabata wani abu,amman babu kyau zargi tabari maganar tafasu sannan. Anan muhseen yadade har akai sallar la,asar bayan yadawone yashiga zaima baba sallama yadurkusa yana sosa kai yace"baba zan tai ubangiji ya sa kaffarane Allah kuma ya kiyaue gaba" Sosai baban yaji dadi yaringa saka mashi albarka tare da mashi addua mai kyau,kasa tashi yayi bakinsa kuma sai yayi nauyi, sai sosa kai yake yana yake. Baban ya lura kamar akwai magana bakinsa sis yace"muhseen kana da abun cewa ko?kaga karka damu kamar jalal kake wajena sanar dani damuwarka koda banda magani ainabaka shawarar data dace matsayina na wanda yaga jiya yaga yauko" Yana yake yajinjina kai yace "hakane baba,daman........dam.....daman wata magana ce nakeson yi dakai" Ya tsura mashi ido yace"inajinka cigaba" Sai soke kai yake kasa yace"akan safiyya ne baba" Murmushi yayi yace "laifi tayi maka halan,ainasanta dashegen rawar kai" Shima murmushin yayi yace"aa baba,daman sonake kaban ixinin xuwa wajenta zance Allah yasa mun kaunarta da jimawa" Yafada kamar zai shige cikin kasa don kunya. Murmushi baban ya cigaba dayi yana jin dadin maganar da yazo da ita,don zaiyyi farin ciki ace yarsa kamar fiyah ta dace da samun miji kamarsa. "Muhseen kenan katabbata abunda kafada haka yake,muddin dagaske kake kana sonta to insha Allah babu wata damuwa ai safiyya diyatace kuma na isa da ita,zata soka don haka nabaka izinin zuwa wajenta zanyi magana da yayanka yahaya tashi kaje Allah yasa muji alkairi" Haka muhseen yabar gidan cike da jin dadin daya jima baiji ba,yaushine ya samu damar barje gumin soyayyar sa ga diyar daya jima yana dakon sonta,har yaje gida yana cikin nishadi. Abdoul gajiya yai da zaman gidan gashi zakiyya ta isai da salo salon munafurci,daga tayi mashi wannan sai tayi mashi wannan,batasan kara hauda fushinta take aransa ba,waje yafito ya hau saman motarsa ya kwanta yana karewa unguwar kallo,amman gabaki daya tunaninsa yatafi wajen safiyyah. Wayarsa ya fiddo yana danna wa tsaki yaja daya tuna ashe baida no dinta kwata kwata. Lumshe ido yayi yana tuna ranar da malik ya rubuta mashi mo dinta ga waya ya goge su shikuma,xunbur yayi ya sake dauko wauar yana dana digit din number din,tabbas idan bai manta ba haka suke amman bari ya jaraba yagani. Kiran ta yashiga yi tanata ringing harta tsinke yaja tsaki baiyyi fushiba yasake jarabawa,yanzu kuma bata shiga ba.yi yake kamar zai haukace don haushi kamar yajefar da wayar yakeji. Cikin Sa,a aka dauka lokacin tana daidai bakin hanya don feea ta rigata tahowa gida,yau ana wuyar taxi kodan hadarin dayake ta haduwa kadan yarage azubar da ruwa garin don kiris yakejira wannan hadarin. Sallama tayi don bata da no din"na makara ban kira da safe ba, da rana kuma baccin rana ya daukeni shiyasa na manta sai yanzu nasamu damar kira ykk" Tanajin haka tagane shine murmushi tai badan ta shirya hakan ba tace"nikuma bana maraba dakai,bcos ina akan hanya bana waya ahanya" Shafa sumarsa yayi yace"whare are u now" "Oh nima i can't say" Cikin lallashi yace"pls I'm serious kina ina bakiga hadari ba ko sokike ruwa yabaki kashi" "Yes inaso" Dirowa yayi daga kan motar yace"pls tell me kina ina zan daukokine shiru tai tana kallon sama hadarin a gaske yake,kuma bata a aniyar samun taxi don haka dole ta gaya ma shi inda take. Motar yashiga wayar na kan kunnensa yace"karki kashe wayar kin mun kwatance ni bakone" Dariya tayi tana biye mashi suna hira yana bin hanyar datace mashin tananan. Yana cikin tsananin nishadi saurarenta dayake har take mashi dariyarta dake dimautashi yarasa gane kansa. Hangota yayi bakin titin tana waigennhanya murmushi yayi yana rage gudun motar,magana zai mata awayar yaga wata bakar mota ta zo daidai setinta tabude motar sun jata ciki da sauri bata masan haka ba saida tajita anjta da karfin tsiya. Wani irin bugawa kirjinsa yayi ganin motar data dauketan ,number motar yabi da kallo kafin ya taka wani uban speed yabisu yana opreting phone dinsa yana binsu da gudu..................... TAUFAH AKWAI MATSALA FAH. DON'T SHARE IT PLS I BEG U. BCOS ALFAH ITS FOR SALE 300 NAIRA ONLY GAMAI BUKATA YA TUNTUBI WANNAN NO DIN 09034722970 [9/17, 3:43 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *ALFAH* 300 naira only if u need Contact me 09034722970 WRITING BY MRS BB. MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY. 09034722970. 🅿️..........43 Hankalinsa yayi masifar yashi,suwaye su?metayi masu?mesuke nema wajenta,safiyyah bata da fitina bai tunanin zata dauko rigimar da har za,a saceta. It can't be possible bin diddigin layin fiyar,don motar tuni ta b'ace mashi waya yayi da police mataimakin dady ya kira yasanar dashi halin da akeciki,ya tura masu location din inda yake expecting zasu je,don ga location din nan ya nuna mashi tsauni. Duk da yadda jikinsa babu kuzari har wani jiriri yake gani,amman bazai iya barin rayuwarta tatai abanza ba,bacin yana da ikon taimakonta. Gudu yake sosai yana kallon wayarsa addua yake Allah yasa karsu ga wayar su anshe ko su fasata,don ko kasheta sukai zai samu damar gano inda suke. Ya na xuwa daidai tsaunin yatsaya yana kallon benen wajen,idan bazai manta ba wannan wajen shine wurin da abbi yacike mashi takaddunsa ya mallaka mashi wajen,tun kafin ya kammala digirinsa na uku.amman har Allah yasa mai aukuwa ta auku bai anshi takadun wajenba,ginine mai hawa hudu mai different part's,babban gidane wanda idan kana da mata hudu zasu iya zamanshi,babu wata takura ko kuntata.kowace zata samu isasshen apartment.........ajiyar xuciya yaja yana sake zeroying mind dinsa don sake nazarin wajen,tabbas wani daga cikin na jikin dadyne da wanan aikin to amman why?ya tambayi kanshi. Fitowa yayi daga cikin motar yana kallon tsaunin yana sake zurfafa xuciyarsa wajen tunanin wanda zai aikata wannan aikin. *UMMA* sunan yayiwa zuciyarsa dirar mikiya,saurin bude idonsa yayi dasuka canza kala saboda tension,tabbas itace. itace zata saka asace ta don tayi yukurin ceto rayuwar zakiyya,sunyi haka ne don susan inda zakiyya take,yes of course haka a bun yake. Waya yakira ya sanar da yan sanda cewa suyi parking motarsu nesa danan,sai su iso dakafa. Haka kuwa sukayi sanda suka iso saida suka zagaye gidan kaf,sannan ogansu da alfah sai wasu majiya karfi su uku suka nufi get din. Maigadine yazo yabude yana ganinsu zai ruga suka daureshi jikin wani karfe tare da dademashi baki da sletip. Abdoul yasan kan gida sako da lungu don awancen lokacin baya sti biyu baizo ba,don yana son ginin akwai ni ima sosai area. Sando sukeyi tare da bin bango,ahankali wasu sukai hawa na biyu wasu sukai hawa na uku,ogansu da Alfah sukai hawa na karshe kuma anan yakejin jikinsa yana bashi nan suka tsareta,fatansa da tsoronsa karsuyi mata komi. Kirjinsa banda duka babu abunda yakeyi,labewa sukeyi ahankali suna bin sako da lungu. Maganganu sukaji cikin wani daki dake kulle. "Yallabai inajin kwadayin yarinyar nan don Allah ka yarje mun nayi ko na minty talatin ne,kafin abunda muka shak'a mata ya dawo da ita cikin hayyacinta,tunda dai kaga duk azabar da ka gana mata bata gaya mana inda zamu samu ita zakiyyar ba..............duk yadda ogansu ya hana Alfah shiga kai tsaye kiyawa yayi,atsananin fusace da gigicewa ya banka kofar da iyakacin karfinsa...........su ukune dakin duk suka mik'e tsaye. Idan kaga Alfah alokacin saiya baka tsoro ainun,saboda yadda yabirkice gabaki daya,wata shak'a yakaiwa mai maganar ya dangana shi da bango yaringa kai mashi naushi ta ko ina,kuma iyakar karfinsa yake dukansa.tuni mamman yayi hanyar tserewa agan yayi nasarar kame mutun guda,sai wanda Alfa ke duka kamar bazai barshi ba shima aka dauresu tare da dayan,aguje Abdoul yabi mamman gudu suke sosai cikin unguwar nan,ganin jiri na kwasarsa kuma tabbas mamman zai iya tsere mashi,kawai ya zaro bindigar daya ansa hannun ogan ya saita kafar mamman wajen steaminer dinsa ya sakar mashi harbi.Abdoul bai taba harba bindigaba amman yau saigashi shine a harba wa,bacin ma basan madannin ba yadaiji hannunsa kurin ga danna kunamar bingidar. Dandanan mamman ya zube kasa yana shure shure,jini yana anbaliya daga jikin kafar tashi saiga sauran police din sun fito da abokan mamman din sun sasu cikin mota ansaka masu unka. Ogansu ne yafito da fiyah dauke ga hannunsa bata cikin hayyacinta,jikin alfah rawa yake ya isa wajensu yana rawar jiki ya ansheta yasaka cikin kirjinsa ya rungume hawaye suna anbaliya akan fuskarsa. Lallashinsa ogan yayi yace"don't mind yallabai,zata farfado kuje asibiti bari muji da su komi kenan daga baya saimuyi contacting juna" Kai Abdoul ya iya daga wa don baya iya magana,yanan durkushe da fiya ajikinsa yana kuka,tallabo fuskarta yayi yana kallon innocent face dinta yana tuno murmushin da take mashi awaya lafin ya karaso inda take,baisan sadda ya sunbaci forehead dinta ba..........jikkarta wani daga cikin police din ya dauko yace"yallabai ga jikkarta nan" Bai ansa shiba suka wuce da su harda mamman daketa ihu saboda wannan harbin. Wayarsa ya lalubo yana karma yashiga layin malik,kiransa yake amman baya picking yakirasa yakai biyar,sarewa yayi don awana halin bazai iya driving ba.........landline dinsu ta gida ya tuna yasan zakiyya nanan sai kurin ua shiga kiran wayar,kamar tana gabanta kiran yashiga saigashi ta dauka. "Assalamu alaikum...............baibata damar karasawa ba cikin tashin hankali yace"plsssss ki dauko key na mota bedroom dina cikin bedside drower dina na hannun gadu,kitaho yanxu inanan yayi mata kwatancen unguwar da yake......" Jikin zakiyya yadauki karkarwa badai wani abun ya sake samunsa ba,sai kuka share share taje ta dauko key din motar ta fito tatadata maigadi yabude mata tafigeta aguje kamar zata sama. Gudu take hawaye na xuba bazata taba yafewa umma ba arayuwarta,ta cutar da ita, ta cutar da abunda take so fiye da komi arayuwarta,bata tunanin tana son kanta fiye da son datake ma Abdoulnasser,muddin tarasa shi itama babu tantama za,a ita sarata don sonshi yariga yayi reshi acikin ranta yayi ganye harda fure yana fitar da y'ay'a,taya ma zata iya hkr dashi bacin da sonsa ta rayu. Haka zakiyya taringa sabbatu tana kuka kamar ranta zaifita Allah ne gakaita garki lafiya. Tasan ginin daya gaya mata don sun taba zuwa tare yana cewa hawa biyu zai cika mata da kayan more rayuwa hawa daya na yaransu ne dayan kuma zaizama nashine. Murmushi tai da ta tuna da lokacin da yake sanar da ita,hango shi tayi kamar rungume da wata ajikinsa kansa yana soke cikin fuskar matar,daga nesa bazata iya gane ko wacece ba,amman tabbas macece kuma da alama kuka yake........innalillahi wa inna ilaihir raju,un kirjinta yabuga da mugun karfi,yayinda take furta wannan salatin tana sake murza idonta taga kodai gizone a gaskiya ba, wacece wannan?metakeji jikin habibin ta?daman Abdoul yana da wata yarinyar bayan ita,daman ya maye gurbinta da wata tun bayanxu ba.hazbunallahu wani imal wakil........sai kuka kamar me jitake bazata karasa ba,bata son ganin koma wacece.wata zuciyar ta hanata tafiya ahaka ta karasa tayi parking. Fitowa tai idonta akansu hawaye kamar famfo muryarta har ta dishe tatsaya daga bayansu don kanshi ya rufe fuskarta bazata iya ganin ko wacece ba. Daker ta iya tab'ashi afirgice ya dago yana juyowa ba shi take kallo ba,fuskar wadda take kwance jikinsa take karewa kallo,miyan bakinta taji ya kafe wani dunkulellen abu ya tokare wuyanta..........hawayenta suka karu sosai bakinta rawa yake ta furta "safiyyah" Kallonta Abdoul keyi cikin yanayin da bazan iya gane wa ba,amman kamar harararta yake cikin jin haushi ya dauki fiya yaje yasata cikin motar ya rufe ya kallota tana nan tsaye kamar bishiya yace"let's go 2 d hospital she need emergency now" Wani mahaukacin kishi da bakin ciki suka ciwo zakiyya tana fashe wa da kuka tace"bazan je ba,babu inda zanje taje can ta mutu inhar nice zan kaitan,ashe daman yaudarata kake Abdoul ashe duk wannan shariyar daman akwai abunda kake boyewa,wlh bazai yuwu ba saidai kazaba ni ko ita,taya na rayu da sonka shekara da shekaru sannan yanzu kazo kajuya mana baya,nice nan wacce ta fiddo ka daga cikin duhun da kake ba fiyah ba,inhar adalci zakai mun nice nadace da rayuwarka ba itaba,yaushe kasanta yaushe har tayi irin wannan girman cikin xuciyarka,har itan wacece da zaka sota..............jiyai kuzarinsa yana dawo saboda maganganun zakiyya,tana bukatar ansoshi kala daban daban amman bazai bata su yanzu ba,saidai zai gaya mata guda wadda yasan yau duk kaurin sunan da bacci yaci na barawo bai isa yadauketa ba. Takawa yayi har gabanta idonsa yayi jaa sosai,har fuskar ma gaba daya kanshi har wata jiji tafito.tsaue yayi gabanta hannunsa cikin aljihu yace"zakiyya kike ko,kinga waccen" Ya nuna cikin motar yana kallon fuskar zakiyyar,wadda tabi hanyar dayake nuna mata da kallo hawaye share share. Cigaba yai da cewa"ta fiye mani ubana,ta fiye mani yan uwana ta fiye mani kowa aduniyarnan baci mahaifiyata,kinga acikin jerin wadanda na jero ke babu sunan ki,don haka karki sake kija da izzarta don ita din rayuwatace idan babu ita rayuwata takare,are u understand sauran maganar zan adana maki ba yanzu ba." Ya wuce yabarta tada motar yayi yajata aguje yabude ta da kura anan. Plssss kuyi hkr da rashin post ajiya I'm not feeling fine,ngd kuma da adduoin ku Allah yasaka da alkairi. Don't share it pls I beg u [9/17, 3:43 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *ALFAH* WRITING BY MRS BB. MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY. 09034722970. 🅿️..........44 Agaggauce aka ansheta sukai dakin taimakon gaggawa da ita,jiyake kamar yabisu ayi komi gabansa,rabon dayayi wannan rudewar bazai iya tunawa ba,tabbas yasa itadin wani sashece cikin rayuwarsa,a watannin baya baitaba kawo cewa cikin kankanen lokaci za,asamu mai iya dawo dashi cikin wannan yanayin ba,yariga ya sadudu da kyakkyawar rayuwa,ya dauka cewa ahaka mutuwarsa zata zo ta sameshi. Kwatsam saiga sofiyyah yarinya mai hankali,natsuwa,hakuri,kamala,juriya,kauda kai mai da daukar damuwar wani ta zama tata.abu mafi soyiwa cikin halayenta shine hkr,tabbas tana da hkr sosai tataka rawar gani cikin rayuwarsa,don haka bazai zama butulu irin zakiyya ba,shi yasan abunda yake yasan ciwon kanshi,kuma bai zama cikin mutanen dake mance alkairin su ba.don haka saiyaga abunda ya turewa buxu nadi inhar akanta ne. Bazaice baison zakiyya ba don akanta yasan me akekira da so.akanta ya rude kofar xuciyarsa atunaninsa daga kanta yariga ya rufe,baitaba kawo ko kadan cewar rayuwar zata canza ba,saigashi rana guda lokaci guda komi ya canza,zanen kaddararsa yagoge wani yafito. Taya zai iya yakice fiyah daga cikin rayuwarsa ai tashigo kenan saidai mutuwa ta rabasu,amman yazaiyyi da zakiyya bazai iya wofintar da ita ba bazai iya tsallaketa yabarta ba,kodan hallacinta abaya da kuma yanxu da take kokarin wanke kanta gareshi,yana da buktar shawara da dogon nazari. Zakiyya durkishewa tai awajen tana kuka mai cin rai,ashe daman fiyah yaudararta take soyayya suke da Abdoul amman ta rufeta baibai,Lallai ta yarda fiyah ta ci amanarta har tana tunanin zata iya barmata Abdoul,bata san cewa don ita aka hallicceshi ba itace first love dinsa kuma da ikon Allah itace takarshe muddin tana da rai bazata iya yarda wata tashigo rayuwar Abdoul ba. Haka ta ringa kuka tana tafiya duk wanda yaganta saiyayita kallonta kamar wata zararra,har ta je bakin titi ta zauna dirshen tana kuka,nadamar sanar da fiyah sirrin dake boye take wanda shine yasa har Abdoul yaji yana sonta don ta na niyyar cetoshi,mema yasa tai saurin yarda fiyah tasan lokacin son kara saka Abdoul din cikin kwayar idonta duk ya rudeta yasa dandanan ta fayyacema fiyah komi,yazatai tagyara wannan barakar tana tsananin kishin Abdoul ko wata bata son taga ya kalla inhar sunan ta mace,to balle fiyah yarinyar da kallo guda zaka mata katabbatar da tsananin kyawunta,bata kwalliya afuska amman hakan bai hana ruwan kyanta bayyana ba.kodan wannan Dole Abdoul zai haukace akanta wai har tsawon yaushe haka tafaru.rushewa tai da kuka tana cewa"Allah ya isa fiyah,bazan yafe maki ba kin sace mun zuciyar Abdoul,to yakike son ninayi bacin na gaya maki bana iya rayuwa mai dadi muddin babu shi cikin rayuwata.........kamar ta haukace haka taita kuka abakin titin,mutane na kallonta kamar daga sama saiga malik yazo wucewa kamar ance yakalli gefen hanya idonsa akan zakiyya,zaro ido yayi yai saurin parking gefen hanya yafito. "Zakiya!kina lafiya kuwa?mekike anan kekadai kuma kika zauna akasa bakin hanya kina kuka kanki guda kuwa?" Kukan take tace"yaya malik kabarni nayi kukana don shine kurin abunda zan yi nasamu sauki,wallahi bansan safiyya munafuka bace sai yau,ta yaudareni bazan yafe mata ba tana shirin rabani da numfashina,yaya malik Andoul shine numfashina meyasa kuka sanyota cikin rayuwarku gashinan tayi dalilin rabani da rayuwata.........." Kallonta yake cike da mamaki shi gabaki daya baima fahimci abunda take fada ba,jan hanunta yayi tana biyosa tana cigaba da kukanta,ya bude motar ya sata yarufe surutunta take tana kuka,bai sake mata magana ba don bama zata natsu tayi mashi bayanin abunda yake tambayarta ba,saida yaje gida ya sauketa yaga Abdoul baya nan,wayarsa ya lalubo sai lokacin yaga missed call dinsa har guda biyar,fitowa yayi yakirasa lokacin shi yana can har lokacin ba afito da fiyah ba daga dakin gaggawa. Duk ya yamutse ya tashi hankalinsa daker ya iya daukar kiran. "Malik ina kashiga na shiga halin taimako na kira baka dauka ba,ganinan *care life hospital* na kawo sofiyya." Cike da tashin hankali malik yace"safiyya kuma?meyafaru badai wata matsala ko ganinan xuwa innalillahi wainna ilaihir raju,un." Yakashe yashiga motar bai tsaya xuwa company ba duk da bakin dake jiransa kurin sai yanufi asibitin............duk ya rude wannan wace irin masiface daga wannan sai wannan,mekuma yafaru da ita Allah karka saka mummunan abu ya sameta. Yanata wannan surutun har yaje asibitin,daker ya gano Abdoul din. yadda yaganshi saida hankalinsa ya ninka tashi,duk ya rikice yariko hannun sa yace"Alfah meke faruwa?ina safiyyar me yasameta ka kwantar da hankalin ka babu abunda zai faru da ita." Malik bai sake rudewa ba saida yaga Alfah yana fitar da kwalla muryarsa na rawa yace"malik,inajin tsoro inajin tsoron faruwar wani abu akanta,ta dalilina da zakiyya ta saka rayuwarta cikin hadari,dazun na kirata............ya zayyane mashi duk abunda yafaru yana hawaye,yace "tsorona kar ace sun mata injection,saboda hada yukurin fyade suka so yi mata Allah bai basu dama,yanzu haka suna can station sonake sainaga farkawarta kozan je" Lallashinsa yake yana goge mashi kwalla lallai Alfah ya fara dawowa Alfah dinsa na ainahi,baya ma abu kuka duk tsananinsa tun bayan da bunda yafaru agidansu,amman yanxu akan mace duk ya gigice yafita daga natsuwarsa. Yanxu ne yafahimci maganar zakiyya,kallon Alfah yayi yace"can na gamu da zakiyya bakin titi tana kuka sai surutu take wai safiyya ta yaudareta Allah ya isa bata yafe ba,meyafaru ne " Dogon tsaki yaja yace"kyale wannan mahaukaciyar,wai da safiyya zatai kishi harta ikirarin inhar ita zata kaita asibiti wlh bata zuwa,Allah ya kyauta saidai ta mutu.ni bantaba ganin butulun mutun ba irinta,ubanwa yajefa safiyyar cikin wanna matsalar inba itaba,ba ta dalilin ceto zakiyyar suka ganta ba har haka ta kasance,to wallahi inbatai wasa ba zan bata mamaki,mahaukaciyar baza da batasan abun arxikiba"mtsss yaja tsaki malik yayi ajiyar xuciya yace "dole zanje na sanar agidansu,nasan suna can suna jajanta har magruba bata dawo ba,ko zaka zo muje" Girgiza kai yayi yana shafa kanshi har lokacin baya cikin natsuwarsa shi xuciyarsa ma ciwo take"bazan je maitama ba ahalin yanxu,kaidai kaje din" "Shikenan kakula da kanka,zan biya na sallami baki acan company" Cikin yanayi marar dadi yace"kayi waya kace asalallamesu sun dawo gobe baka da lokacin zuwa company yanzu malik," Murmushi yayi yace"ok sir"yadda yayi harda sarawa yasa murmushi ya kubcewa Abdoul badan yashirya ba,fice wa yayi yatai wajen mota yana tunanin shiga unguwar,shekara shidda rabon dayaje ko kan titin unguwar balle bakin get din estate din. Jan numfashi yayi ance ranar dole sai dole yaja motar yatai. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Baba ne ya gama sallar magriba yace"nikau maman su kin kira uwata kinji inda ta tsaya hankalina ya kasa kwanciya tun dazu," Fitowa mama tai daga daki itama cikin yanayi marar dadi ta zauna gefen baba saman tabarma tace"wallahi babansu tun karfe shidda nake kiranta wayarta arufe,na kira jamila tace gaskiya bataje ba na kira balaraba tace ita rabonta da safiyha tun sunan jamila,shirun danai na dauka kafin kayi magana ta dawo,addua kurin nake tunda nashiga daki nai salla." Juyowa baban yayi yana kallonta cike da damuwa yace"haba maman su,meyasa tun dazun baki fada ba da ban tura dalha yaje can akaramtar yaji abunda yafaru ba." Sadda kai tai tace"kayi hkr babansu,na tura yesmin gidan su rafeea tunda tare suka tai data dawo tace mun ai rafeea can tabaro safiyyah basu gama ba wajen hudu da rabi,shine saina tura dalha nace yaje yagano mana ko lafiya,na boyene gudun tashin hankalinka." Shiru yayi yana tunani sai kuma yaji ta bashi tausayi,mace mai kulawa da gidanta da iyalinta.duk abunda tasan zai daga mashi hankali kokari take ta kiyaye wannan dinma don yafi karfinta bata da wata mafita. "Shikenan Allah yadawo da dalhan lafiya yasa kuma babu wata matsala,tunda bata kai har kamar yanxu inhar ba gidan jamila tabiya ba" Shiru sukai yesmin sarkin kuka har tafara xubda hawaye mamace ke lallashi ta itama jitake kamar tayi kukan,gabanta ke faduwa bana jin safiyya ba lafiya ba. Tunda ya shigo unguwar abubuwa dayawa suka ringa dawo mashi,unguwar ta canza sosai fiye da dacan,gine gine da abubuwan cigaba duk sun samu kasancewar unguwace ta yan siyasa da masu hannu da shuni,tafiya yake yana kallon gidajen daya bayan daya har idonsa yakai ga gidan da bazai taba mancewa dashi ba,gidan da ya canza mashi rayuwa ya fiddoshi daga cikin kangin talauci da kakanikaye.kwalla yaji ta fito mashi xuciyarsa ta karye abubuwan da suka faru ranar da ya dawi daga tafiya,ina ma ya bude idonsa yaga komi mafarki ne ba haka yake ba.amman ina wannan rayuwar tafi gaban mafarki. Kallon gidan dake opposite da gidan su Alfah yayi yajima yana kallon gidan,kafin yayi parking kofar gidan unguwar babu kowa amman hansken fitilu ya haske ko ina kamar ba dare ba. Tsaye yayi jingine jikin motar yana kallon gidan,ashe nan ne gidan su qanwarsa fiyah ko yaya iyayenta zasuji wannan labarin abun bazai masu dadi ba duba da jiya aka sallamo baban su daga asibiti. Mashin yaji yatsaya bayansa ya waigo yaga wani matashin Saurayi ya sauko yana kallonsa,isowa yayi yaba malik hannu suka gaisa yace"kana neman wani agidan" Malik yace"inadai son ayimun iso ciki zanyi magana da mutanen gidan" Dalha yana kallonsa yace"bari nashiga to muje bismillah" Gaba dalha yayi malik yana binsa abaya dalha yayi salama cikin gidan,dandanan mama da yesmin suka mike suna hada baki wajen tambayarsa. "Ina take tare kuke?" Yesmin kwalla suka cika idonta tace"yaya dalha ina Addata" Sadda kai yayi yanajin banu dadi yace"wlh naje har makarantar,na duba nayi tambaya ansar dayace ko biyu wasu dasuka santa sukace ai tatafi gida,wasu suce su basu santa bama,bana nan naje duk inda nake tunani bansameta ba wayarta har yanzu kashe take" Durkushewa yesmin tai tana kuka sosai mama da baba suna sallallami,dalha yace "ga bako nan yana son magana daku wata kila yasan wani bayani akan rashin dawowarta" Yaje zaure ya shigo da malik yana sallama daker suke iya danne ransu suka ansa mashi saboda halin dasuke ciki. Babane yace "matso nan yaro zauna ga tabarma,karka tugunna" Baiyyi musuba ya zauna gefen baban yana gaidasu "lafiya ba lau ba yaro,Allah yasa lafiya daga wajenka" Malik cikin natsuwa yace"am baba daman zuwa nai nasanar daku safiyya tana asibiti,yan garkuwa da mutane suka saceta to Allah yasa gaban wani dan uwana sukai hakan shine yabisu ya kuma sanar da yan sanda hakin da ake ciki,da taimakon Allah dana Dan uwana shida yan sandan akai nasarar samunta ankuma kama mutanen,amman dai yanzu safiyya na asibiti ana duba lafiyarta amman jikin ba tsananta wa yayi ba,shine na samu bayanin gidansu nace bari nazo n sanar daku don kar hakalinku ya rau gida biyu" Mama hawaye suka.kece mata tana cewa"lahaula wala quwwata ialla billa ni y'arsu,Allah kadubemu saita duke tana hawaye" Malik yace"kiyi hkr mama ai abun yazo da sauki da yanzu bamu san inda take ba,ku kwantar da hankalinku tana cikin kulawar likitoci insha Allah tana lafiya" Baba yace "mungode ma Allah wadannan jarabawowi dayake mana ya kuma bamu ikon cinyewa,kaima yaro mun gode maka Allah yayi maka albarka kaida dan uwanka,tunda ni bazan iya zuwa ba kuje dasu don Allah suganta ko sun samu natsuwa,sai abar yesmin wajenta inhar sun riketa zuwa wani lokaci" "To aba baby damuwa su shirya muje kaima kanena afito sai muje" Yace ma dalha. *********** Fiya ce kwance kan gadon asibiti an saka mata oxygen,Abdoul ne gefemta hannunsa cikin nata idonsa ker akanta,kamar ance mashi zata ruga yana tuno abunda likitocin suka gaya mashi dazun bayan fitowarsu. "Yallabai mun samu daidaiton numfshinta,sannan sanadin Allurar da sukai mata tagusar da hankali hakan ya jawo zata kwana biyu bata farka ba daga baccin da take ba,idan kuma jininta mai karfine alluran da muka saka cikin drip din suna iya daidaita mata hankalin ta kilan ta farka xuwa gobe,karka damu yallabai aita auna arxiki don wasu ma daga nan sun haukace wasu ma mutuwa suke,she is very lucky Allah yabata lafiya,saita warke za,ai bill din kudin." Ajiyar xuciya yaja yana kallon hannunta da yatsunta dasuke mashi masifar kyau,zoben hannunta ya tsurawa ido kamar ya kai hannun ga bakina ya sunbata,amman yanajin tsoron kar xuciyarsa ta zurma dayawa karshe yazo yashiga tension,jin alamar za,a shigo yasa yatashi da sauri yana koma wa gefe yana zama saman plastic chair's................ Don't share it s i Beg Abdoulnasser its for sale if u need it contact me on 09034722970. [9/18, 8:46 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️..........45 Idonsa bisa kofar shigowa malik ne farko sai dalha da yesmin,mamace last duk suka shigo mikewa Abdoul yayi yana sassauta fuskar sa cikin yanayin tarbar baki yace"sannunku mama,ha waje ki zauna"ya bata kujerar da yatashi akai. Zama tai yana sake cewa "ina wuni mama" yana sunkuyar dakai cikin sakin fuska tace"lafiya lau ya muka sameku,ashe kuma haka abun ya kasance to mun gode yaro Allah yayi albarka,Allah ya saka maka da alkairinsa sannunku" "Babu komi mama duk abunda kaima wani kamar kayiwa kanka ne,kaima akwai lokacin da zaizo kana bukatar taimako Allah shi zai turo mai taimakonka,shine kawai insha Allah likitan yace xuwa gobe ko jibi zata farka,saboda sun mata allurar maye idan jinin ta yana da karfi zata iya tashi nan da 18hours,ku kwantar da hankalinku babu wata matsala insha Allah" Yesmin kwalla take sharewa ta isa ga fiyah tana rike hannunta "Addata sannu kinjiko,Allah zai baki lafiya baba ma yana maki sannu bai iya zuwa da yazo ai" Abdoul tausayi ta bashi don da alama akwai kauna mai yawa tsakaninsu,ga kuma kamar da suke sosai dakaga fiyah kaga qanwarta..........mama tace"dalha sai mu wuce ita yesmin saita zauna kusada ita ko." Malik yace"mama inhar ba dai yarda damune bakiyi ba ai babu bukatar haka,tai tafiyar ta gida gobe saita dawo insha Allah,karkiji komi munan ai" Ajiyar xuciya tai tana satar kallon Abdoul,tabbas tagane yaron don tun baikai haka ba yake mutunta ta,inhar zata fito yaganta zai duka har qasa yace"ina wuni"idan unguwa zata zaice adawo lafiya,kirkinsa ba kadan bane,don yasha biya mata kudin taxi idan ta dawo daga wani waje suka hadu. Kwatsam taji wannan mummunan labari yafaru dashi,ta dade abun bai bar kanta ba kuma har gobe ta kasa yarda wannan natsatstsen yaron kamili shine zai haka,akwai wata dai akasa. Mikewa tai tace"aa yarona ai karka damu wlh nayarda daku sosai,wanda yyi maka wannan ai yafi gaban kace baka yarda dashi ba,naga kar atakuraku ne shiyasa amman tunda kace tatai shikenan Allah dai yayi maku albarka." Fitowa sukai suduka malik zai mayar dasu Abdoul zaimasu rakiya,har mama ta bude kofa kenan ta kalli Abdoul ta danyi murmushi tace"Abdoul-nasser ko?" Shima ya saki fuska yana shafa kanshi yace"eh mama baki manta ni ba ashe" "Taya Zan mance da kai ai duk wanda ya mance alkairi to abin cikesa gaskiya,kaidai Allah ya warware maka damuwarka.ya kuma kareka daga sharrin masu sharri,Allah yayiwa rayuwa Albarka.karo na babu iyaka kasake taimakona ta hanyar ceton guda jinina" "Haba kibar godiyar haka,ai safiyya kamar n,imah take wajena kibar damuwa" Shiga sukai malik yaja suka bar asibitin,tunani mama take barkatai meyasa ta hana safiyya abunda tai niyya kwanakin baya na taimakon wannan yaron,tunda har ta nuna alamun tana son taimakonsa tabbas kilan tana da wasu dubaru,da haka ta faru zataji dadi don wanda ya maka kaima kayi kokarin yi mashi,haka dai taita tunani har suka zo gida. Abdoul ya kwana asibitin don cewa yayi babu wata nurse dazai barma safiyya,idan ta farka cikin dare kuma nurse din tatai gantalinta fa,wazai kula da ita.malik dai dariya yayi yace to yallabai mukwana lafiya ni nayi nan,ya wuce yatai gida babu maganar xuwa wajen dady don dare yayi sosai,kuma yace in yadawo zaikirasa amman bai nemai ba. Washe gari malik ya gama shirin xuwa office ya wuce dakin zakiyya yayi mata nocking kamar bazata bude ba saigashi ta bude tai tsaye tana kallonsa babu ko gaisuwa saida yace"zakiyya ba gaisuwa kuma" Kauda kai tai gefe tana cewa can kasa kasa "ina kwana"murmushi yayi yace"kinga banine na kar xomon ba ko rayata ma ban ansa ba,kibari idan yadawo saikijuye haushinsa amman not me.yanzu kije kishiga kitchen kihada break za akaiwa fiyah,duk da bana tunanin ta farka." Wani kallo take mashi mai cike da haushi tace"yaya malik,ni zan mata girki?lallai ta mutu bata ci ba wlh" Kallon ta yake cike da mamaki "zakiyya" Kallonsa tai sosai tace"yes abunda kaji yaya malik,wlh bana iya ciyar da reble dina kamar dai banda hankali" Ransa yafara baci yasake cewa"i said go and cook her something" Juya baya tai tana kunkuni "ni gaskiya yaya malik, bazan iya ba haba don Allah mijina fa takeso shine zan mata girki" Cikin tsananin tsawa yace"zakiyya nace kije ki dora mata breakfast now,wlh har nadawo bakiyi ba zakisha mamaki na." Ta tsorata da tsawar da ya mata tunda take dashi haka bata taba faruwa ba,hawaye suka xubo mata ta sadda kai kasa tace"kayi hkr zanyi zuciyata ce take cike da kunci shissa" Sai tausayinta ya kamashi ya sassauta murya yace"idan xuciyarki tana cike da kunci zakiyya bakisan me zaki yi ta warware ba,bafa halinki bane kar son rai yasa ki aikata abunda zaki dade kina nadama,safiyya wani bangarene na rayuwar Abdoul,baza ki iya rabasu ba bazan ce suna son juna ba haka bazan ce basa son juna ba,amman tabbas suna ji da juansu,Abdoul yada baki tunani haka yake ji da fiyah.kuma abunda kikai mashi har yau yana kule dake,da zakiji shawarata dakin kauda idonki akansu,da kin saka masu ido kinga abunda Allah zaiyyi.nasan kina son Abdoul ni shedane amman kaddarar rayiwa ta hadashi da fiyah,ke kuma ta jefo wani babban shamaki tsakaninku.kiyi addua komi ya daidaita karki bata rawarki da tsalle,bana tunanin Abdoul yabar sonki zakiyya zan dai iya cewa kaso sittin aciki ya bare.don haka kisan mekike ciki muddin zaki ringa aibata safiyya kina fadar maganganu marasa dadi akanta,to ba Abdoul kadai ba nima nan zan kullaceki haka zalika zan canza maki,ya rage naki ki gyara tun kina da sauran lokaci,zanje store indawo kilan kingama time din" Haka zakiyya tasha kukanta ta gode ma Allah ta lallashi kanta,hakika tana jin wani azabebben kishi akan Abdoul,amman ya zatai dole zata hkr zata koyi danne wa har Allah ya dorata kanshi,bata iyajin zata barshi muddin bashine yafurta dakansa cewa yabarta ba. Jiki amace take hada breakfast din,kaza ta gasa mata tayi laushi sosai ta zauna ta zare kasusuwan,sannan ta soya dankalin turawa tayi mashi vegetable sos sai kamshi miyar take,sannan ta dafa ruwan zafi mai kayan kamshi sai tayi mata wainar indomi mai hade da kwai taji tarugu da albasa..........tagama ta hada su cikin basket taje tayi wanka,sanda ya dawo harta shirya tace"zan bika yaya malik inganota" Murmushi yayi yace"kokuma ki ganoshi ba" Sadda kai tayi tace"aa wlh suduka zan gano" Dariya ta bashi yace ta samai mota,mayafinta ta yafa ta dauko basket din ta biyosa,babu laifi tayi kyau tunda ita ma daidai gwargwado kyakykyawace sosai. Tunda yayi salla ya dan sake koma wa sai da kiran malik ya shigo ya tadashi,yayi mashi bayanin abubuwan da babu acan shopping mall dinsa da kuma wasu abubuwan,sun jima suna mgna yace zaije ya taho masu da breakfast.Abdoul yace ya taho mashi sa brush da merclean. har sha daya tataho yinwa yakeji, wayarsa yake danna nawa yana duba wasu abubuwan,yaji kamar sautin numfashinta,kamar tayi motsi ko nishi. Tsayar da idona yayi tam akanta yana kallonta,tsawon minty uku yaga ta sake motsawa tashi yayi yaje gaban gadon ya dora hannunsa bisa kanta yana mata addua,jiyai bakinta yana magana can kasa sosai saika kanga kunne zakaji abunda tace. "Alhamdulillahil lazi ahyana ba,ada ma amataha wa ilaihir nushur,innalillahi kaina zai fashe mama kaina ciwo yake kinji mama" Zuwa yanzu maganar tana fitowa adduar yake tofa mata akan da kuma fuskarta,ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai,dishi dishi tafara gani hannunta mai kanula ta saka zata murza idon yayi saurin rikeshi. "Akwai Canuler karki saka" Kamar mafarki take taji sautin muryarsa,amman dakin juyawa yake da ita ta gaza yarda ma a ina take shin,hannunsa yasa yana murxa mata idon ahankali,kamar yasan haka take so dandanan ganinta yafara dawowa. Dakin take kallo kafin ta dire idonta akansa,zaro manyan idonta tubar kalla tayi akanshi,wani irin yammmm yaji ajikinsa har saida ya lumshe idonsa yasake budewa still kallonsa take. Kafin kwalwarta tafara mata tariya abunda yafaru da ita,. Cike da rudani ta tashi tana waige waige duk ta firgice,idonta duk kwalla. "Inane nan,mesu kamun?menai masu don Allah kai ina nike bangane ba,miye wannan nashiga ukuna" Wata kara tafasa tana kiran "mamaaaaaa" Hankalinsa yayi masifar tashi riketa hake tana fizgewa duk ta haukace mashi,jikin ai rawa yake daidai shigowar su zakiyya da malim,sai yasmin. [9/19, 11:52 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️.............46 Gaba ki daya hankalinsu ya tashi ganin yadda fiyah duk ta bi ta haukace,tana fixge fixge tana kiran mama.yesmin kuka take sosai don inkaganta zaka dauka sabuwar mahaukaciya ce. Ganin tana niyyar fixge canuler hannunta yasaka yahadeta dukanta yayi mata wani kyakykyawan ruko cikin jikinsa,yana hura mata iska cikin kunnenta idan kagansu zaka yi mamakin yadda suka hade waje guda,numfashi takeja tana kuka kasa kasa yana shafa kanta tare da yimata alamar lallashi kamar yana lalashin yaro. Zakiya wani kudulelen abune ya tokare mata wuya,duk yadda take kowa da xuciyarta da kwayar idonta akan kar tayi kuka abun ya ci tura,juya baya tai tana shere kwallarta. Malik yana lura da ita bai ce mata komi ba,yesmin dai sai sharar kwallarta take. "Malik ka kira dr pls" Jinjina kai yayi yana fita daga dakin,zakiyya ma ficewar tai yabita da kallo kasan ransa tausayinta yake,amman bazai iya yin halin ko inkula da safiyya ba bacin tana bukatar taimakonsa. Ajiyar xuciya yaji tanayi kuma rikon da tayi mashi tana sassautashi,jikinta yana saki ahankali. dago fuskarta yayi ahankali ta bude idonta ta zuba mashi su lumshe mata nashi yayi yana karkta kai tare da dage girarsa guda,yakai bkinsa kan kunnenta cikin sanyin murya yace"cute baby relax mana,bude idonki ahankali zaki gane inda kike,qanwarki yesmin ma kinganta anan,karki sake rikice man plsss nima zan iya birkicewar oy open ur eyes and relax" Kalamansa kamar saukar kankara fakejin su cikin xuciyarta,waye yake mata wannan kalaman da takejin suna saukar mata da wata natsuwa ta musanman,jikinta yana sakewa kwalwarta tana dawowa daidai tare da tariyo abubuwan dasuka faru,ahankali yake zare jikinsa daga nata wanda yakejin wata irin kasala tana mamayesa,har yana jin tsikar jikinsa tana tashi. Komawa tai jikin bango ta tattare kafafunta ta rungume tana kallon dakin har idonta ya sauka akan yesmin,wata nannanuyar ajiyar xuciya ta sauke ahankali bakinta yana rawa tace"yesmin" Rugowa tayi wajen Addar tata ta rugumeta tana kuka"Adda kin warke ko,kice mun baxaki sake irin abunda kikai ba,kin tayar mun da hankali........dr ne da malik suna shigo ahankali take kallon malik tana kallon Dr ta juya ga Abdoul dake gefe yana dafe da kansa idonsa arufe. "Sannu qanwata kin tashi ko Allah ya sawake" Daga kai tayi tana kallon yesmin. Dr ne ya dubata yace"jiki alhamdulillah xuwa anjima ma idan ruwan can ya kare, ana iya bata sallama,anyi ta barka wlh wasu har rasa hankalinsu suke ta silar wannan allurar,Allah ya kiyaye gaba" Abdoul ne yace "dr tana gama karya wa zaka sallameta zaman me kuma zata zauna tayi bayan komi success" "To yallabai yadda kace din amman inso samune anfison ruwan yakare tukun" "Anjima zan sake dawowa idan ruwan yakare saina bata sallamar", Ajiyar xuciya yaja yana dora idonsa akanta,akai sa,a itama shi din take kallo. Tama rasa wane tunani zatai,sadda kai tayi malik ne ya fita yashigo da zakiyya daka kalli idonta kasan tasha kuka ba kadan,tunda ya mata kallo daya ya kauda kai bai sake kallonta ba,don zata raunana mashi xuciya,bacin bacin ran data sakashi. Toilet yashiga yayi brush ya fito ya zuba breakfast dinsa ga plet yaja gefe yana ci kamar babu kowa dakin,malik yace zakiyya ki zuba ma fiyah ta karya amman kidan kamata ta wanke bakinta." Yesmin tace "bari na taimaka mata ita ta xuba abincin kafin ta fito,daker take tafiya don gabaki daya jiri takeji,ahaka fa wanke fuskarta da bakinta tayo Alwallah suka fito,capet din dake malale tsakiyar dakin ta zauna sama tana jingina bayanta da bango,idonta nason kallon Alfah Amman tanajin nauyi,tana bukatar nazari don kusan duk abunda ya faru kamar tana sani kamar tanajin wasu abubuwan,amman girman Allurar yahana ta gane meke faruwa amman idan bazata manta ba,wasu kalamai suna mata amsa kuwaa ciki kunnenta da kanta,zakiyya jiki asanyaye ta ajiye komi gaban fiyah bakinta kamar anmata dole tace"yajikin naki" Ko kusa bata dago ta kalleta ba,saidai ta ansa mata cikin voice dinta data dishe bata fita sosai. "I'm feeling better" Daga haka bata sake ce wa komi ba,yesmin ke tayata tana cin abicin,kamar bata so. "Zan wuce office Alfah tunda jikin yayi sauki,ko akwai abunda za,ai" Bakinsa yake gogewa da tishu yace"jirani mutai,ka saukeni gida nayi wanka,duk rintsi yau zanje station dinan" Mikewa yayi yana saka wayarsa gaban aljihu yace"zanje na dawo idan ma bandawo ba driver zai zo ya maidaku gida Allah ya sawake" Kanta akasa tace"nagode amman kabarshi zamu shiga taxi,ga yesmin nan ai" "Okay" Yawuce kurin,zakiyya tashi tai itama tana cewa"Allah ya sawake" Uffan fiyah batace ba saidai yesmin ta ansa mata,daga ita sai yesmin adakin sunyi shiru kowa da tunaninsa. "Adda su waye wadannan" Bata bata ansa ba tana tsakurar dankalin kamar bata so. Tace"nima ban sansu ba,karki isan da tambaya" Nurse ce tazo ta mayar da drip din daya rage ba,a idasa saka mata ba,fiyah tace ma yesmin ta zauna tayi break tasan bata yo ba. Ahankali suke firarsu har rafeea tazo suka cigaba da firar,tana cewa ta auna arxiki sunada interval kwana uku aida abun baiyi ba, feea tace ai tabaro mama na shirin tahowa ita dasu Anty jamila harda kanen mijinta. Wata faduwar gabace ga samu fiyah badai muhseen bane zai zo,innalillahi Allah yasa to Abdoul karya dawo. Malik ya sauke alfah ya wuce wajen aikin shikuma yashiga yayi wanka ya dauki kamshi,yayi masifar yin kyau kananan kayansa yasaka t-shet dark blue sai black trouser,combus dinsa blue and white color,yau babu fesin cap dinsa.zakiyya dake falon zaune tana kallo wanda gabaki daya hankalinta ba kan tv yake ba,ta luka duniyar tunani,taji kamshinsa ya mamaye falon Tsaye yake yana daura agogo ga waya kare ga kunnensa ya makale ta da kafadarsa yana magana,shagala tai dakallon sa wani mahaukacin sonsa yana sake cika ruhinta,dandanan kwallarta ta cika idonta yanzu ace duk yadda wannan guy din yake zai iya zama haramiyarta,wace irin kaddarace wannan data raba tsakaninta da masoyinta,ada Alfah bashida wani buri daya wuce kasancewa da zakiyyarsa,yasota wanda shi kanshi baisan adadi ba. Ita kanta alokacin har mamakin kaunar da suke ma juna take,ashe akwai lokacin dazai zo saidai ta ringa tunawa. Ganin zaifita yasa ta dawo natsuwarta tai saurin ringanshi isa wajen kofa tana tare hanyar,idonta da kwalla tace"Bazan bari kafita gidan nan ba yaya Abdoul sai kagaya mun matsayina,na gaji da hakin da kake nuna man acikin gidan nan.gabaki daya ka daina sona kadaina damuwa dani,ka dauki gurbina ka maye da wata watacan da batasan darajark............"inkika sake furta makamanciyar irin wannan kalmar akanta zan baki mamaki,matsa bani waje kafin tafin hannuna yasauka afuskarki,kije kiyo karatun tanatsu inkina son magana dani,stupid girl" Yasa hannu yajanye ta ya wuce yana jin haushinta har cikin ransa, Station din yaje ya samu dpo din wajen sukai magana,yake gaya mashi . "Ai yallabai wadannan yaran kangararrune,tunda aka kawosu ake gana masu azaba akan su fadi wanda ya sasu wannan aikin amman wancen shegen yana hanasu,wai muddin suka fada sai yayi ajalinsu." Iska Alfah yaja yana fesarwa ya kalli inda aka kulle su idonsa akan mamman,wanda ya canza kammani daga kamanninsa nada. Yadai samu darajar anmashi aikin kafarsa ancire bulet din,anyi dressing. Shafa kanshi yayi yana kallon dpo din yace"to waye yace kace saisun fadi wanda ya sasu,ai bama bukatar wanda ya sasu.tunda abun afili yake kucigaba da cin ubansu har sufita hankalinsu,har sanda zan sake dawowa." "Yallabai sau uku ana zuwa neman belin su muna hana wa,saboda girman laifinsu,aman idan aka sake dawowa zamu iya sakinsu gaskiya,duba da cewar mai zuwa belin babban mutunne" Kallon dpo din Alfah keyi ransa yana sake baci xuciyarsa ta fara hawa jiyake kamar ya shakesa yaringa naushin dan isaka. Cikin bala i da rabon dayayisa yajima yace"to kubada din,billahil azim saika rasa wannan yar jskar kujerar,koma ubanwa ye yazo kace ni nace ban lamunta ba,inbanda rashin hankali irin naku har ku bada belin yan iska irin wadannan bacin kuna da tabbacin sudin hadarine,to wlh ka maida hankali na dawo gobe babu su." Juya wa yayi har yakai kofa dpo din yace"yallabai mahaifinka ne fa" Cak ya tsaya bai jiyoba yana jin wani emotion yana zagaya wa dashi,wani rauni yana kama zuciyarsa har hakan ya shafi muryarsa yace"koma waye ban lamunta ba,inya sake xuwa just call me zanzo da kaina" "Okay yallabai" Ficewa yayi yana jin kamar ya fashe da kuka me hakan yake nufi,da saka hannunsa aka sace fiyah,kokuma yazo ne yayi belinsu don yana dan uwan matarsa,to koma ubanwaye din matarsa wallahi wannan karon saidai ayi uwar da za,ai bazai daga kafa ba.inma ace shine suka farauta zai hkr aman badai rayuwarsa ba safiyya kenan. Asibitin yayiwa tsinke don yasan drip din ya kare yana son sake ganin yadda jikin nata yake. Rafeea ta jima sosai saida su mama da anty jamila suka zo sannan tatafi,don ita tana da exam da yamma. Sosai jikin fiyah yayi sauki. Hira suke da su mama da anty jamila little fiyah tana wajenta tunda suka zo,sai wasa take mata suna dariya tare tana son babyn yadda take da fara,a kamar dai iyayenta. Muhseen ne yashigo shida uncle yahya,wata gaduwar gaba ce ta sake riskarta,kauda kai tai tana rokon Allah yasa kar Abdoul ya dawo.tarasa gane dalilin dayasa bata son yasan meke tsakaninta da shi. Gaida uncle tayi yana mata sannu. "Safiyya ashe kuma haka abun ya kasance,to Allah ya rufa asiri ya kyauta gaba kuma" "Amen uncle nagode sosai" Yace ma Anty jamila "kitashi muje rana tayi sosai,komun isa da wuri" Fiyah tace"Au Anty unguwa ma zaku ko" Tace"eh wai kaduna zamushiga zamuyo dubiya kanwar hajiyarsu bata da lafiya" "Allah ya bata lafiya man abarmun little anan nidai"dariya sukai muhseen idinsa kamar zaifado saboda wani salon kallo dayake ma fiyah,mama tace"bakida kangado,yarinyar nashan nono abarta wajenki sabkda daukar alhaki" Uncle yace yana murmushi"Aa mama ai tana da madara sai abarta kawai tunda ta rage kukan banza yanzu" Yesmin tace"eh wlh uncle to abarta" Hararar ta mama tai face"ankiya din kuda bakuda gaba,jamila anshi diyarki ku wuce kinji nima tashi zan naje na dora sanwa har daya saura." Goya little Antyn tayi sukai masu saisun dawk sukatai,muhseen ne yace "mama muje na kaiki ko" Tace"aa barshi muhseen naga ruwan ya kusan karewa saika taho dasu ko" Kokadan bata so haka ba wai meyasa sukeson hadasu,tsaki taja kadan tace"aa mama kije yakaiki nifa akwai ma wani ruwan da za,a sake sakawa,kuma yaya Abdoul da yaya malik sunce zasu dawo karsuxo bamunan" Kallonta mamar keyi na tsayin lokaci,ita kuma ta kawar da fuska don karta karanci wani anu cikin maganarta,. "Muje to muhseen inka kaini saika dawo naga ma ko gaisawa bakuyi ba." Yesmin tace"mama zan biyoku sai mudawo tare zan tahoma da Adda kaya zatayi wanka" Fiyah kallon qanwar tata take sosai,don taga wani abu tare da ita tunda muhseen din yazo,saitaita kallonsa tana murmushi anya ba akwai wani abuba,kuma tasan mama ada bata yin haka inda dane ma bazata yarda tabarta da wani namiji ba,amman meyasa yanxu. Fita sukai suka barta ita daya tana shiga kogin tunani,amman maimakon tunanin abunda kefaruwa da yan gidan nasu sai xuciyarta tatafi wajen wanda idan tana tunaninsa,takejin kamar tama yawo saman gajimare,wani bakon yanayi yake bakuntarta. Tajima idonta arufe tana cikin wannan yanayin,taji budewar kofa. Kamar ance bude idonki tana budewa idonsu ya sauka cikin najuna..............[9/20, 3:41 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️.............47 Tsura ma juna ido sukai yana tsaye bai shigo ba yajingina da bangon kofar,yayi crossing legs dinsa hannayensa cikin aljihu. Baisan meya shagaltar dashi kallonta ba,kawai dai yasan yanajin wata magana disu tana jawo xuciyarsa xuwa gareta,ganin kallon sa bazai kare mata ba kuma idan ta biyesa zatai abunda bata shirya ma haka ba,shissa saita juyar da fuskar ta gefe tana kokowa sa kwayar idon ta akan karta cigaba da kallonsa. Hakika bata ma taba ganin kyansa ba irin yau,har wani daukar mata ido yake.lumshe ido tayi kamshin sa daya cika dakin yana nausawa cikin hancinta. Takowa yayi xuwa cikin dakin yana kallon drip din wanda ke digowa kadan kadan,hannu yasa ya murza yar tayar da ruwan zai zubo dayawa yana cewa batare saya kalleta ba. "Ya akai har yanzu bai kare ba kusan awa guda darabi" Itama bata kallai ba tace"nurse din data Samunce ta dawo tarage gudunsa bansan dalili ba" "Gashinan ni na sakeshi yayi ya kare kokinje gida" Zaro ido tayi gabaki daya tana kallonsa yana danna wayarsa tace"karka jamun wata matsalar,kaifa ba likita bane ko nursing nidai gaskiya ka mayar dashi yadda yake" Dago ido yayi yana kallonta cikin sassanyar murya yace"bazanyi abunda zai cutar dake ba don't mind" Lumshe idonta tai bata sake magana ba,suduka sai sukai shiru kamar ruqa yacisu. Wayarsa yake dannawa yace"ya kikejin jikin naki yanzu" Idonta rufe saboda yadda yanayin ya canza baki daya kamar suna wani filin sahara ita dashi, "Inajin ma nawarke" Murmushi yayi yace"sure?" Shagwabe fuska tai tace"yes 100% sure ma ni kaje kace suxo sucire mun kurin..........shigowa akai dakin da sallama yesmin ce da muhseen.......runtse ido tai tana karanta innalillahi,meyasa zasu dawo yanxu nashigesu ni fiyah. Kallo daya Alfah yayi mashi yaganesa wanda yaketa nan nan da fiyah ranar daya kaita gida,babu mamaki yana neman gindin zama.hade rai yayi sosai yesmin tace"sannu da zuwa yaya kadawo kenan" Yake yayi mata kurin ya cigaba da danna wayarsa,muhseen yabashi hannu yana mashi sallama. Kamar bazai bayar ba saida ya mula sannan yabashi suka gaisa,direct wajen gadon fiyah muhseen ya tsaya daidai kanta yana murmushi. "Dear bamu gaisa ba dazun yajikin naki" Wayyo jitai kamar ya maka mata guduma a tsakar kai,kamar ta rushe da kuka takeji,fuskarta babu walwala tace"nasamu sauki,yanzu ma za,a sallamemu aida baku dawo ba" Murmushin ya sake yi yace"to dear waye zai kaiki gida idan ban dawo ba,bayaga gaka ma sauri nake nazo naji muryarki don nashiga dimu kwana biyu" Tsaki taja kadan tana kauda kai tace"ga wanda zai mayar dani nan bayanka,na huttasheka kilan ma kana da abun da zakai" Saurin girgiza kai yayi yace"wlh koda indashi baikai ki muhimmanci ba,zan ajiye koma miye din nabaki lokacina" Kuka ne kurin batai ba don wadannan kalaman jinsu take kamar anwatsa mata yaji,satar kallon Abdoul tayi still yana kan phone dinsa inba kasanshi ba bazaka tabagane yanayinsa ya canza ba,amman kallo daya tai mashi ta hango wata jijiya bisa goshinsa,fuskar nan fara tas ta koma jaa abunka da farin mutun. Runtse ido tai tace"yaya muhseen kaga akwai ma wani ruwan da za,asake sawa bn tunanin yanzu zan tai kadawo anjima saika tafi damu." "Indai ba zaman naune bakiso ba wlh zan ita jiranki har lokacin" Muryarta tafara canza wa kamar zatai kuka tace"plsss mana nidai katai bana son kazo ka tsareni kamar wata yarka" Numfashi yaja yace"sorry dear na bata maki rai,yesmin kikula da ita kinjiko idan anjima zan dawo din dear karfe nawa ne sallamar" Banza tai dashi don tuni kwallarta tafara fitowa hakanan xuciyarta bata son Alfah ya dora ma ransa wani abu,sannan yadda yabi ya canza abu. Ya tabata,duk ta rikice taya zata daidaita masho mode dinsa,wani haushin muhseen ya kamata.........gajiya yayida jiran ansarta yafita. Banta san yadda akai ba kukanta ya fito,amman ko kallonta Abdoul baiba saima tashi da yayi yafita. Yesmin tace"Adda menene kuma na kuka,ke kuka baya maki wuya Adda.wlh yaya muhseen yana sonki kidaina mashi haka babu kyau" Wata harara ta banka mata tace"rufe mun baki malama ni bana sonsa idan dole sai qanwar Anty zai so ke yasoki mana,ni bansonsa" Shiru sukai da sukaji sallamar dr tare suke da Abdoul din. Har lokacin fuskarsa babu walwala "yallabai yama kare ruwan bari acire kuna iya tafiya yanzu Allah ya kawo sauki" Uffan baice ba yesmin dai na gefe tana zare ido,fiyah kuwa har lokacin kwallarta bata tsaya ba. Sallamar yabasu ya fita Abdoul ya kalli yesmin yace"kufito ina waje" Yafita kallon fiyah yesmin tayi tace"saiki tashi ko Adda" Yunkura wa tai daker tatashi cikin kayan da yesmin ta taho mata dasu ta dauki abaya tasaka,ahankali take tafita har suka fita daga dakin. Tsaye yake jikin wata mota bazakace a nigeria akwaita ba,yana hangosu ya bude yashiga kurin,bai wani tsaya bude mata ba. Kamar zata kifa haka ta isa gaban motar tashiga yesmin ma tashiga,kamar motarce ta bata mashi rai daya figeta saida goshinta yabugi gaban motar. Dan juyowa yayi kadan yace"sorry" Ya cigaba da bata wuta ko kadan baiji wani dar na dosar unguwarsu ba,ko kadan jiyake xuciyarsa adake take koda suka isa bakin get din maigadi yana hada ido dashi,ya zaro manyan idanunsa yayi saurin budewa yana durkusawa yana kai gaisuwa.ko kallonsa baiba ya shige ciki. Kofar gidan su fiyah yayi parking ko inda gidansu yake bai kalla ba,amman kasan ransa yanajin wani irin yanayi. Har hakan ya nuna cikin idonsa,yesmin tafice tabarsu anan. Kauda kai yayi gefe kurin ita kuma ta tsura mashi idonta yana jin kallon nata har cikin yan cikinsa,amman ya share daya gaji uace"karki cinyeni" Bata san tayi murmushi ba taja ajiyar xuciya tace"nagode da ceton rayuwata karo na farko,ngd sosai Allah ya saka da alkairi.sannan ina rokon Allah ya daidaita maka lamurranka.wannan xuciyar taka ina rokon Allah ya nuna man randa zatayi sanyi,sannan kace da zakiyya ta maida wukarta acikin kubenta,ta kwantar da hankalinta Abdoul-nasser nata ne domin ta mallaketa aka halittaka,don haka kullatata datai bashida anfani don on ready anmun miji agida.koba haka ba ma ni kafi karfina,ni diyar malam ce jikar malam bankai matsayin da zan maye gurbin zakiyya ba acikin xuciyarka,baya ga haka ma ni banda ra,ayinka kaima baka da ra,ayina shaidanne ya xuga xuciyarta hartake ikirarin inhar itace zata kaini asibiti saidai na mutu.imagine zakiyya take fadan haka saboda soyayya,banga laifinta ba sannan ni abunda nai maka banyi don neman tukuici ba,nayine domin Allah shine nake bukatar tukuici awajensa.itama kuma na taimaketa ne saboda Allah don inagani bazan bari wani ya cutuba,koda hakan yana nufin nizan cutun. Akarshe ina rokon Alfarma wajenka inhar kadaukeni da daraja arayuwarka yaya Abdoul kamance da komi,kayafe komi aranka ka hakura da duk wasu kudiri daka dauka akan abunda yafaru da rayuwarka ka auri zakiyya,sannan ka yafewa mahaifinka don shima abunne yafi karfinsa,zakaji anan gaba zakace nafada maka.yaua Abdoul Allah ma muna masa laifi mummuna kuma mutuba munemesa afuwa ya kuma yafe mana,saimune tsakanin mu kuskure zai gifta ace bazamu iya yafewa junan mu ba,idan ba,a yafiya taya ubangiji kai zaiyafe maka. Nidai inhar inada kima inda muhimmanci arayuwarka inhar inada alfarma wajenka.........muryarta ta karye sosai rawa take domin abunda take furta wa yana cutar da ita cikin ranta,amman dole hakan zatai don zakiyya tafita bukatar Abdoul tunda har tana kirarin wani yamutu saboda kishinsa. Jiyowa yayi gabaki dayansa yana zuba mata rinannun idonsa,yayinda idanunsu suka nitsa cikin najuna,wasu abubuwa masu girma suna shigar kowane acikinsu..........kwallarta datake boyewa bata san sadda suke anbaliya ba,har lokacin tana kallonsa don gani take shine kallo na karshe da zatai mashi. Girgiza mata kai yake bakinsa yayi nauyi matuka,muryarta sosai take rawa tace. "Yaya Abdoul inhar kana son faranta mun ka.....aur......ka auri zakiy.....zakiyya" Kuka ya ci karfinta tasaka hijab dinta tana rera abunta,wanda jinsa yake har cikin karshen ransa kamar ya jawota ya matse yana lallashinta,riko hannunta yayi sosai yanajin yadda kirjinsa yake halbawa..........yace"safiyyah" Kasa ansawa tai tana son amshe hannunta "kasakan zan shiga gida kar aga na dade" "Zan sakeki amman why are you crying,kefa kika fada da bakinki cewar baki dace dani ba,itace tafi dacewa dani,har kina rokona akan in aureta,to kuma kuka namiye kike" Tarage sautin kuka tace"babu komi" "Akwai komi,meye cikin xuciyarki inaji ajikina kamar kin kwari kanki,kamar kin cutar da xuciyarki amman bazan iya gane haka ba sainaji daga gareki" "Aa babu komi sai anjima" Rike hannun yayi sosai yana sanyaya muryarsa yana rage mata sauti,cikin wata murya da tasaka ta lumewa cikin kujerar yace " *did u love Abdoul-naser*" Jitai har numfashinta yana niyyar barinta,maganar ta daketa sosai da sosai kawar dakai tayi tana aro jarumta tasaka ma ranta ahankali tace" sorry i don't lov.......love u" Lumshe idonsa yayi baice komi ba,ya dan kai hannun bakinsa ahankali kamar zai mashi kiss suka hada ido yasaki hannun yace"sai anjima" Fita tai yaja motar yabar wajen. Kafafunta kamar ba nata ba haka takejinsu kamar mai koyon tafiya ta nufi cikin gidan. [9/21, 3:59 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️..........48 "Yajikin naki uwata" Cewar baba kenan bayan shigowar fiya ta zame saman cinyar mama ta kwanta,tana jin kamar taita risgar kuka ko zataji saukin abunda yake damun xuciyarta da gangar jikinta. Idonta arufe tace"na samu sauki sosai baba,ya naka jikin kaima" Yace"yanzu muhseen yace zai koma ya taho daku ashe kuma kun taho" "Uhm" kurin tace don bata son ma ko maganarsa aimata. Mama tace"kasan yaron nan nagidan Alh muazzam ne ya taimaketa,akan idonsa aka saceta Allah yarufa asiri yabisu tare da yan sanda" "Wane yarone na gidan Alh muazzam?" "Malam har kamanta yaron nan Abdoul nasser" Canxa fuska yayi yace"madalla ya kyauta sosai,ana son irin haka" Daga haka sai mama tayi shiru don taga baison maganar. Tunda koma gida ya shige dakinsa bai ake fitowa ba,yarasa abunda yake mashi dadi magananunta kurin suka mashi yawo cikin kai,meyasa takeson cutar da xuciyarta saboda wata wadda bata san darajar mutun ba,bata san karamci da mutunci ba.har ta buda baki yace mashi ya auri zakiyya,tsaki yaja yana dukan bedside drower dinsa da hannunsa ko zafi bayaji. Nizata kalla tace bata sona,to daman waye yace yana son nata ita nan har zata ja ma mutane rai.idan tana ganin hakan daidaine shikenan bai shirya ansar zakiyya ba amman tunda ta nuna itace tadace da rayuwarsa fine. Wani zafi yakeji aransa to inba ta sonsa kukan ubanme yake mashi amota,mtsss yaja dogon tsaki kamar zai fito da halshensa don haushi. Knocking ake mashi yasake jan taki cikin tsawa yace"waye nan,banson takura" Yasan itace don malik baya nan. "Yaya kabude kofar nan pls muyi mgn" "Bana son maganar nikuma,pls out" Marairaice murya tai tace"yaya don Allah mana" Cike a haushi ya tashi yabude kofar kamar zai kifa mata mari yake kallonta. Tsaye yayi bai bata damar wuce wa ba yace"fadi inaji" Langabar da kai tayi cikin sigar da zata jawo hankalinsa tace"yaya magruba ta taho babu kyau bacin yamma" Wani jakin kallo yake mata yace"sai akace maki bacci nake ko,pls go i need to rest" Matsowa tayi sosai kusada shi kamar zata rungumeshi,wani takaici ya cikashi miye haka zakiyya keyi,ko dacan bata mashi wannan iskancin balle yanzu da baya jinta aransa. "Yaya Zan debe maka kewa nasan kana cikin damuwa." Wani kullutun haushi yazo mashi wuya,yadda take wani kusantoshi abun yake kona mashi rai. Fixgo hannunta yayi damugun karfi yayo wajeda ita bai ajeta ko ina ba sai waiting falo,yayi wurgi da ita saman kujera yace cikin fushi. "Stay away from me,inbacin iskanci nizaki ringa turowa kirji,angaya maki dan iska ne ni.kokuwa danake sonki sha,awarki nake,zakiyya!zakiyya!!zakiyya!!! Kinji uku ko kita idona wane irin haline kika aro kika yafama rayuwarki.shekarun baya ban sonki da wannan abun ba,ban sonki da sonkanki ba.ban sonki da wofintar da darajarki ba.ban sonki da rashin kunya ba,why yanxu kike yi just bcos of her Imagine!kinji kunya yarinya kankanuwa tafiki sanin meyadace da rayuwarta,tasan darajar kanta gata da kawaici da hkr da kauda kai.saike dakika kusan haihuwarta kike aikata abubuwan da basu dace dake ba.to last worning kitsaya iya matsayinki kafin na yanke mummunan hukunci akanki." Yajuya afusace yabar wajen. Kuka ta rushe dashi tana data sanin daukar shawarar da xuciyarta tabata,ita kanta yatoshe kaunar Abdoul ta rikitata hanyar dazata shawo kansa take nema,gashinan tasake bata rawar ta da tsalle. Malik bai dawo gida ba yana tashi daga wajen aiki ya wuce gidan dady sunyi waya akan su hadu gidansa,su gama sauraren wadanna recording din. Baima biyo ta gida ba don karya sake bata lokacin yau yake son duk dare sai sungama sauraren komi,kafin asan wadda ake ciki. Falon dady ya shiga da sallama tv ce keta surutu yasamu waje ya zauna yana turawa Alfah text din cewa karyaga bai dawo ba suna tare da ddy. Dadyn ne yafito suka gaisa suna dan tattauna abunda ya gabata sannan ya miko system din yace ya kunna. Shiga yayi inda suke ya lalubo gudan audion da basuji ba,ya kunna. Muryar ummu ce ta sake fitowa ras kamar lokacin take maganar. "Zakiyya muddin kika bata mun shiri Allah ya isa ban yafe ba,ke ba Allah ya isa kadai ba zan maki ba tsine maki zan kishiga duniya,inhar nice uwarki duk abunda na tsara maki shizaki yi saba mani kamar kin zabi tsinuwata ne,duk lalacewa ta dai uwarki ce ni dole kuma kiyi abunda nace" Shashshekar kuka zakiyya keyi tana cewa"umma kiban umurnin komi amman ban wannan,bazan iya yiwa Yaya Abdoul karya ba muddin wani abu yasamai ta silata Allah saiya saka mai,nikuma bazan yafe ma kaina ba.umma kiyi hkr ki ji tsoron Allah karki aikata abunda kike shirin yi" Ji kake tas tas tas,an wanke zakiyya da kyawawan maruka har uku cikin bala,i umma kecewa. "Harna haifi dan zai mun gardama,kedin wacece don ubanki kuma duk abunda nake ba donku nake ba,ko kunfi son ya hada komi ya handame shida uwarsa,to bazai yuwuba ko dayardar ki kobabu zan aikata kuma wallahi kika tona mun asiri bazanji komi ba don saka ancire wuyanki shegiya,kilan ma asibiti akaimun musayarki." Dariya zuwairat da haulat sukai ummar tana cewa"haulat dake zamuje,don haka figarmun yar iska kikaimun ita mota inbaki iyawa kiramun mamman" Shiru ne ya biyo baya saidai motse motsen abubuwa da akeji,an dauki tsawon awa guda babu wata magana,malik zai kashe dady ya daka tar dashi. Saida akaci awa daya da rabi sannan sukaji magana tana fitowa,amman basu san kota waye ba ce "hajiya ai aikin ki baida matsala kawai kudi zaki xube sai kuma aljani gudunbala dake son kebewa da wanan" Cikin kidima umma tace"ban gane kebewaba boka,budurwa ce fa ya zakace haka aa ban yarda da haka ba.har gara ya kebe dani gaskiya" Kuka kefitowa daga cikin system din na haulat tace"wlh bazan yarda ba saidai idan zakiyyar ce za,a yi da ita umma nidai aa" Tsawa bokan ya daka masu yace inhar bazasu yarda ba sutashi subashi waje shiba mutumen banza bane. Haulat na kuka haka umma ta tusata cikin wani shegen daki da warina saiya saka gudawa. Biyota bokan yayi yana washe baki,ya dauko wani hayaki yana mata har hankalinta yagushe sannan yayi abunda zai da ita,yagama yafito yana lashe baki. Yace"sauran kudin aiki don Aljani kungunbala ya yaba da wannan kebewa yace aiki kam babu kakkautawa," Umma tace"godiya nake boka,ita wannan so nake asakar mata jini sosai wanda zai dauki hankalin mutun,na kwana uku sai adauke shi don plan dinmu yayi nasara,shikuma uban gayyar maigidan kenan sonake asaka mashi tsanar dan nashi,kuma duk abunda mukaje mashi dashi zai yarda ya aikata,sannan uwar yaron itama asakama maigidan tsanarta da ita da diyarta,boka sonake komi ya dawo hannun na nida yarana,matsayinda dansa ya samu nawa dan ya maye gurbinsa.kuma arufe baki kowa kar wanda ya tanka" Wata mahaukaciyar dariya ce bokan yayi yace"shegiya la ananna,ke kinma fini shedancin shegiya kenan,Aljani kututu ya kara maki ni,ima Alh kwangila yadade yana kwasar ganima" Kallonta zakiyya keyi cikin mamaki da al,ajabi harara uwar ta mata tace mawa kake bukata yanxu." "Ki bada miliyan biyar ta ishemu xubdajini" Babu musu haka ta fiddo kudin ta bashi tana mashi godiya,yace aiba sai yanada wani magani ba.tunda har Aljani kundunbala yasha romon diyarki saidai kuga aiki da cika wa,bari atado maku ita baccin wuya take" Bokan daya fiddo haulat yace"hajiya makarin wannan sihirin shine yaje kunnen wani bayan ku,muddin wani yaji wannan sirrin to ina mai tabbatar maki kwabarki zatai ruwa rayuwarki tana cikin matsala,bayaga hukuncin da zaki fuskanta wajen mutanen dakike tare dasu,anan aljani kundunbala zai mutu inhar yamutu ta silar haka to yan uwansa zasu dauki mata ki akanki,don haka kija kunnen yaranki" Kasa kasa zakiyya ke kuka tana Allah wadai da mahaifiyarta,har cikin ranta jitake inama ba itace ta haifeta ba,yo yama za,ai tayarda batare da daukar wani mataki ba,gyara zaman wayarta tayi dake cikin riga tana daukar komi. Amman kasan ranta tanajin tsoron abunda zai faru da ummar,amman kuma tana ganin gaskiya bazata iya barinta ba,ko nanda shekara nawane zata bayyanashi,koma me zai faru yaje yayita faruwa ai ita taja ma kanta. haulat har sukaje gida yana bacci. Koda suka isa gida umma hanata xuwa ko ina tayi,gudun kartaje ta bude baki ta gaya ma wani. Kasancewarsu tare yasa ta cigaba da daukar duk wasu wayoyi da umma keyi da Alh kwangila. "Alh katuro yanzu da kwalaben giyar akalla katan guda ajera su acikin frig din sa,sannan maganin baccin shima karka manta dashi.insha Allah gobe komi zai kammala.dariya sukai ita dashi suka kashe waya." "Don ubanki kallon me kike mun,jinin ya fara xuwa ne" Kwallarta suka xubo ta girgiza kai kurin. "Mai bakin hali duk cikinsu kece kika fita zakka,ko ubanki marigayi baida wannan halin to,banson gidan ubanda kika aroshi ba don nima ba naubane" "Umma don Alla..........buge mata baki tai tace"zaki mun shiru kokuwa,banza kurin" Haka zakiyya taita kuka tana biye da umma duk inda zata. Kasancewar Abdoul sai dare yake dawowa kuma key dinsa wani yana wajen zakiyyar,don wani xubin ita da ni,ima suna mashi kwalema su gyaremashi dakin tas,har ya masu kyauta. Waya Alh kwangila yayiwa umma cewar ga giyar ya aiko tafito itada xakiyar suka ansa hannun wanda ya turo. Zakiyya kamar ranta zai fita haka take kuka,haka umma ta tusata gaba suka ni ta baya xuwa part din Abdoul din,ta bude masu suka shiga frig biyune daya falo daya uwar dakarsa. Haka suka cikasu da kwalaben giya,sannan suka fito. Akwai wani mujitafa dake hidima da Abdoul din duk sanda yadawo daga wajen aiki,shine ansar jikkarsa xuwa bedroom shine hada mashi ruwan wanka,shine hada mashi dinner da dai sauransu. Dashi umma tai anfani ta danka mashi dubu dari biyar tace rabine ma inhar ya gama abunda zai mata to zata cika mashi dubu dari biyar din......wannan kudin suka janye hankalin mujitafa,ya saka ma Abdoul maganin bacci cikin lemunsa. Hankalinsa yagushe ya daukai da kanshi yaje har kan gadon umma ya kwantar dashi,tare da cire mashi kaya dagashi sai gajeren wando. Ranar zakiyya har sikewa tai saboda bakin ciki da nadama da dana sani. Mafarin kenan washe gari umma ta tashi hankaulan gidan,taje takai Abbi har part din yaya Abdoul tananuna mashi giyar dayakesha,sannan tace yamun ciki ya kuma kaini anxubda shi gashinan jini ya balke mun,saboda alokacin jini nake fitarwa sosai har yana bin kafafuna.idan kaga yadda umma ke kuka zaka dauka duk duniya itace da gaskiya,wai Abdoul ya je mata kwartanci.............kukane sosai yake tashi don duk zakiyya ce take wannan bayanin,tana sake cewa "banbiye ma umma don ina tsoron tsinuwarta ba aa na biye mata ne don in dauki komi in ajiye wataran kowa yasan meyafaru,amman banyi don yaudararka ba yaya Abdoul" Daga nan audio ya kare saura video Xuface suduka sukeyi sun shiga wani irin yanayi na rudewa,wannan wace irin rayuwace saboda duniya ki wulakanta kanki,ki watsar da darajarki ki munana wani sabida son xuciyark........... Dady yace"kunna video muga meke faruwa shikuma" Sorry ford let update I love u more fans [9/22, 6:48 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........49 Danna video yayi yana ganin hoton mamman farko yafara yawo aciki,yana saka bindiga cikin wata jikka agefe saiga umma tana ta washe baki tace"karkuyi wasa kokadan mamman,wannan ce damarmu ta karshe da zamu cinma nasara.kaga dai duk wasu kadarori da muke son mallaka daga Alh yasaka mana hannu ciki,sing din lauyan sa kurin ya rage.shima dayaga saka hannun Alh bazaija da mu ba,karkuyi sakaki.ina mai tabbatar maku tunda har shikadai yafita yau zaku iya cinmasa ku gama mashi aiki." Rungume ummar tashi yayi yace"bakida wata damuwa umma ina mai tabbatar maki yau zakiji kyakkyawan labarin mutuwarsa,ai ko gawarsa bazamu barta ba saimun tabbatar ya babbake ko kamanin sa baxa iya gani ba" Dariya suka sake kwashewa daita har rana kissing kuncinsa,tace"Kwangila yace mun zai tura acire mashi birkin mota.......wayarta tai kara ta duba tace kaga dan halak shine ma ya turo mun sako,har angama aikin gaskiya shima yana da kaso mai tsoka,hanzarta kajiko........karar rufe kofa sukaji alamun kamar anajinsu. Zaro ido sukai ita da mamman din,umma tace"maza jeka ga waye,karka barkowaye mamman,kakira abokan aikinka kowaye bance ko ragar masa ba muddin asirin mu yatonu kaikanka bazan kyaleka ba." Dagudu ya fita daga dakin........daidai karewar video kenan. Malik kansa akasa yana jin kofafin kansa suna toshewa,wace irin macece ita metake nema ta rasa cikin wannan gidan,wace irin hatsabibiya ce ita harta ke iya aikata irin wadanan abubuwan..........tunawa yayi da irin bakar rayuwar da Alfah yayi,da irin yadda ta bata mashi suna,duk mutanen dake ganinsa da kima da mutunci sun daina,ana mashi kallon dan iska wanda yarasa wadda zai nema sai matar ubansa,yadda rayuwarsa tashiga hadari baisan sanda kuka ya kubce mashi ba mai sauti,wanda rabon dayayi wannan kukan tun sadda yarasa gatan iyaye da danginsa,tunda kuma Abdoul-nasser alfah yashigo rayuwarsa duk wani kuka da kunci yayaye mashi,haske da farin ciki ya maye gurbin bakin cikinsa,amman kwatsam rayuwa tazo ta juya masu baya wannan la,anannar mata tajefa mashi abokinsa amininsa dan uwansa wanda yakejin bayada kamarsa ahalin yanxu,idan baiyyi kuka ba mezaiyyi.........lallashinsa dady yake wanda shima yaji kwallar sa tana cika idonsa. "Karka sare dana,duk wani tsanani yanada sauki,kuma kadauka daman kaddararkuce tazo ta hannunta,hakika hajiya mariya babu shaidaniya irinta,kuma ta daukowa kanfa babban bala,i don nayi alkawari kozan karar dakomi nawa sainaga na sadata da gidanzaman ta na har abada." Haka malik yayita kuka dady yana lallashinsa,daker yayi shiru yace yaje gida zai san yadda yayi yanemi ganin Abbi. Haka malik yafito jikinsa amugun mace daker ma yake jan motar,gabaki daya tsoron duniya da rudin shaidan yashigeshi,mutane suna kai kansu halaka saboda son duniya da abun da ke cikinta. Har yaje gida bai iya dawo wa daidai ba,ayadda ya hango dakin Abdoul idonsa biyu,agogo ya kalla shabiyu da minty goma. Kome yake bai bacci ba da alama dai akwai damuwar data hanashi runtsewa,kallon bedroom din da zakiyya take kwana yayi shima akwai haske,itama batai bacci ba,to meke damun su suduka haka. Baida natsuwar dazai fuskanci koguda acikinsu shiyasa ya wuce shima yayi wanka da sallar isha,i yasha ruwan tea ya kwanta yana sakawa yana kwancewa. 💞💞💞💞💞 Fiyah ce zaune gaban baba tayi shirin fita exam don yau suna da peper. Tare ma suke karya wa mama dan wake tai masu sanan aka dama kunun gyada,suna ci suna hira gwanin sha,awa yesmin na gefe itama ida mama kwanon su guda. Ganin yadda fiyah ta sake take ta annashuwa hakan yayiwa baba dadi,yaga damace daya kamata yayi anfani da ita wajen yi mata zamcen yaron nan muhseen. Cikin jan hankali da natsuwa baban yace"uwata wannan jarabawar itace ta karshen gama aji daya ko?" Tana kurbar kunan gyadar tace"eh baba itace,amman sai munje hutu munkoma mun sake wani karatun munyi wata jarabawar sannan mushiga aji biyu" Jinjina kai yayi yace"masha Allah kinga daman burina biyune akanku kullum keda yesmin," Kallonsa tai tace"baba wane irin buri kake dashi akanmu" Murmushi yayi yace"inason inga kun fadada iliminku bayan na secondary,inga kuma daidai gwargwado ban tauyeku ba kuma kun samu ilimin da zai taimakeku agobenku,bayan nan uwata kullum fata nake da burin Allah ya fiddo maku da mazajenku nagari wadanda zasu rikemun ku cikin amana da mutunci kamar dai yadda uncle dinku hake rike da antynku cikin kwanciyar hankali babu maijin kansu" Gabanta yafadi sosai har ta kasa kai dan waken dake hannunta cikin bakinta tace"baba ai banfa gama karatunba,duk fa ko rabi banba akwai aiki gabanmu sosai" Murmushin yayi yace"ai uwata shi aure baya hana karatu,haka karatu baya hana aure aduk sanda kasamu damar yin guda inhar anyarje maka saikaga kayishi cikin kwanciyar hankali," Gabaki daya ta rude dajin kalaman baba meyake nufi da ita,innalillahi Allah kasa ba wannan shegen muhseen din yazo ma baba da wata magana ba,wlh van sonsa bana sonsa.....idonta yadan caza tace"baba ai babu wanda nake kulawa tunda karatu nake in wani yazo saina gabatar dashi wajenka" Mama kallonta tai ta fahimci wani abu game da diyar tata,idan batai kuskureba tasan maganar da baban ke shirin yi mata,wanda yasa take kakkaucewa. "Ai kwantar da hankalinki uwata,Allah yana sonki don ya kawo maki miji har gida kuma wanda nake maki fatansa da kwadayinsa,badan abun hannunsa ba ko don kudin magabatansa,aa nagartarsa naduba da hankalinsa da natsuwarsa yasa banyi shawara dake ba nai na,am da maganarsa don haka kowane lokaci zaki iya ganinsa yazo wajenki." Bata son fiddo kwallarta gabasan yasa ta sadda kai tana kokowa da kwallar cikin kermar murya tace"waye baba,ni banda wani wanda nakeso kuma ban turo kowa ba wlh" Duk yadda taso karya gane rudewarta saida ya gane yace"kwantar da hankalinki ki natsu uwata,muhseen ne kanen uncle dinku.kema kinsan bashida wata matsala karkiyo tunanin komi,cancanta ce yasa nabashi ke kuma inada yakinin zai kula dake yadda yakamata ahankali zaki fahimceshi kuma har kisoshi." Idan tace zatai magana kukanta bayyana zaiyyi shiru tai tana zare hannunta daga cikin kwanan dan waken,amman kafin ma tatashi yesmin ta rigata ta fice tana tari da alama kware tai. Ahankali kamar wadda kwai ya fashe wa aciki take fita daga dakin,kallon yesmin take durkushe gaban maguji tana kuskure bakinta,idan ba gizo idonta yake ba kwallace ke fita daga idonta,tana gogewa kasa kasa tsura mata ido tai harta wanke fuskarta ta shige dakinsu bata kula fiyah ba. Jinjina kai tayi tana godewa Allah data kawo mata wannan damar,don kuwa bazata iya musawa baba cewa bata son muhseen ba,amman idan ta fahimtar dasu cewar yar uwarta naso hakan zaija hankalinsu su duba maganar. Wajen dalha taje ta anshi kudin taxi tabar unguwar xuciyarta cike da abubuwa. 💞💞💞💞💞 Wayar da akaimashi can caji office yasa ya tashi don bai niyyar fita ko ina ba yau,shiryawa yayi yanayin sa kwata kwata yau ahargitse yake.neman wanda zai juyewa masifar shi yake. Har zaifita idonsa akan jikkar fiya. Dawowa yayi ya dauketa yafifa,ko kallon kitchen baiba inda yake jiyo mktsin mutun yasan zakiyya ce,don har yanzu akuke yake da ita. Driver sa dasuke fita office ne yazo yace"yallabai yau babu office ne" Cikin shan kanshi yace"eh" Juyawa yayi yabarsa don yaga kamar cikin fushi yake. Yadda ya figi motar kasan kiris yake jira,gudu yake don yaje da wuri dpo din yace mashi ga yallabai nan ya sake dawowa neman belin su. Shikuma duk bala,in da za ai da masifar da za,ai bazai bari su kubutaba yau zaifuskanceshi bayan tsawon shekaru,yadda yake nuna mashi shidin ba dansa bane shima zai rufe ido ya nuna baima taba sanin sa ba,idan ma kotu za,axaje akan maganar ashirye yake. Go slow ya tsayar dashi idonsa ya sauka kanta tana cikin taxi,kanta kasa kamar tana duba wani abu. Saurin dauko bag din yayi zaifita saikuma ya fasa,yana son ganinta akebance wannan damace da zaije gidansu anjima. Koma wa yayi yana cigaba da kallonta jiyayi duk wani kuncinsa ya na yayewa,xuciyarsa tana sauka sabanin yadda yakejin wata irin temper tana taso mashi. Kamar kar yatafi yakeji amman babu halin hakan yana gani suka wuce shi shima ya wuce inda zashi. Malik bai tashi da wuri ba sai kusan shadaya wanka yayi yafito yayi break zakiyya ta gaidashi ta shige daki,binta da kallo yayi yana mamakinta to aibashi ya kashe xomun ba. Waya sukai da dady yake tambayarsa Andoul na gida. "Wlh daddy baya nan,yafita tun safe amman bari akirasa aji," "Aa kyalesa nasan inda zaije yana station kan case din safiyyah yana can shida mahaifinsa inajin tsoron kar xuciyarsa tajashi wani abu yafaru awajen shiyasa amman bari naje kaima inkana da time mu hadu can." Ai malik najin haka ya kafa kai ya shanye sauran costand din ya zari wayarsa don bazai fita da mota ba,addua yaje Allah yasa kar yaje ya aikata abunda bashine ba. Taxi ya tara yagaya mashi inda zai kaishin. Station Yana isa yaga motoci har guda uku yasan Abbin ne ya iso,fitowa yayi ya sake hade fuskarshi murtik kamar an aikobmashi da sakon mutuwa. Wani dan sanda ne yake bakin kofar shigar yasaka kafa ya ingijeshi yashiga. Biyosa yayi a fusace yana finciko rigarsa ta baya "uban waye kai da har zaka ingijeni kai makahone ehy..............naushin da ya kai mashi shiya janyo duk hankulan mutanen dake cikin station din. Saida Abdoul yafasa mashi baki sannan ya wurgar dashi yana huci. Abbi dayayi ido hudu da yaron nashi,duk zafin daya debo don juyewa akanshi saiyaji xuciyarsa ta karye,bayan shekara shidda ashe zai sake yin ido hudu da dansa,gudan jininsa.jikinsa yaji har wata rawa yake saboda tsuma da son rungumeshi ajikinsa,saidai yasan hakan bazata yuwuba yadda yagansa cikin wanna zafin ba tantama idan ya tabosa abun bazayyi kyauba,daman ga yanjarida canawaje sunajiran kiri sushigo sudauki rahoto. Watairin kaunar dan nashi yaji ta kamashi idonsa kamar zayyi kuka yaje inda yan sanda suka kakkamashi yace"ku sakeshi karkuji mashi rauni mana,ai laifin sane baiga ayadda yashigo wajenba ne zaiyi jaking dinsa." Sakale sukai da bakisuna kallon sa don sun san ba haka ya shigo ba yana zage zage ya shigo yana cewa duk ubanda ya bada umurninkar abada belinsa akirasa yanajiransa.amman gashi yanzu kuma sunga ba haka ba,shiyasa wani daga cikinsu ya nemo yan jarida yasan zai samu wani abu idan suka amu wannan labarin. Idon Abdoul yayi jaa yana kallon Abbin nashi can kasan ransa yana jinwani irin feeling amman sabkda abubuwan dasuka ringa dawo mashi na can baya sai yadanne yafixge daga rikonsu yana zakuda kafadarsa cikin bala,I yace"ina ruwanka da koma me zasuyi man?nace meye ne yasha feka dani muazzam,kabari suyi mun koma miye mana meye hadin kifi da kaska." Abbi jiyayi zuciyarsa tana ragargajewa rauni yana sake kamata wata irin nadama da dana sani suna shigarsa,matsawa yake inda Abdoul din yake muryarsa tana rawa yanason rikosa "daina daga murya yarona,nine fa Abbinka Abbinka ne maionka........dalla malam dakata anan karka sake ka nufoni,don zan maka rashin mutunci nace karka matsoni ko wlh zan maka abunda baka taba tunani ba." Alfah ke fadara haka yana hawaye,yanajin kamar ya dunga buga kanshi da bango. Hankulan mutane yafara yowa nan wajen. Abbi tuni idonsa yafara zubar da kwallar yana cewa"nine babanka Abdoul karka manta dani kar xuciyar ka ta saka maka tsanata,zoga babanka kajiko matso." Ja baya Abdoul keyi yana sake cewa"wlh idan ka matso inda nake saina kashe kaina,yafige wata bindiga daga hannun wani dan sanda yana saita kanshi da ita,daidai isowar yan jarida kenan da kuma zuwan dady da malik. Cikin rudu da rikicewa Abbi ya rike hannun dady yana kuka kamar ba babba ba yace"kaimashi magana karya halbi kanshi,kaje ka anshe bindigar yana iya halbawa tsoro nakeji inhar kana sona karka barshi yayi abunda yake niyya........ina sonsa ina son dana kaceceshi." Riko duka hannayaen Abbi yayi dadyn yana cewa"kwantar da hankalinka bazai aikata ba,ka natsu don Allah kalla fa kaga mutane yadda suke kallonka haba yallabai." Malik ne yayi saurin rike hannun Abdoul dake saita kanshi da bindigar yana sakin iyakar karfin sa,yana koklwar ansarta. Bilhakki da gaskoya kuka yake yana cewa, "Wallahi muffin yah I nasarar ceton wadancen yan ta addan saina yi abunda zaisaka dagani harshi mukare rayuwarmu agidan yari.taya zaoyyi yukurin ceton mutanen dake da hadari cikin al,umma masu satar jama,a suna yimasu allurar maye........kasakeni kafin kaima nayi maka illah...........wani gigitaccen mari dady ya sakar mashi yana sake lafta mashi wani marin,don baida wata dubara da ta wuce haka,yayi gigiceqr da baya saurren kowa. Shirune ya raysa wajen ya juya ga yan jaridar yace ma yan sandan duk wanda kuka kama cikinsu ku garkame shi tunda neman labari suke sai subada nasu yan iska ,basu da aiki sai neman rahoto suje su yayata." Abdul silalewa kasa yayi yana wani irin numfashi kirjinsa yana dagawa kamar zakifita daga jikinsa,inbada rawa babu abun da jikinsa keyi dole malik ya cikashi suna xuba mashi ido. Don Allah kuyi hkr wlh yau nashiga busy ga bakuwa danai ga hidimar gida shiyasa kuka samu wannan kuyi hkr plss. [9/24, 5:37 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️........50 Dady ne yace"malik kamashi ku wuce gida,indan kan sune kake wannan haukan to ubanwa ya gaya maka zasu kubuta,bana son hauka da shirme comon get up" Mikewa yayi idonsa jajawur yana kallon Abbinsa,yana jin wata suya cikin kirjinsa bangare guda kuma yana jin wata irin kewa da soyayyarsa suna sake narkewa cikin ransa.nunasa yayi da hannu yajinjina kai har zai fita ya juyo yace"dady safiyya fa sukai kidnapped,suka mata allurar maye hankalinta ya gushe,kasan me likita yace akai?cewa fa yayi taci sa,a jininta yana da kyau in wasune har haukatar dasu take,wlh tallahi da wani abu ya sameta na rantse da Allah saina cirewa kowanensu yan yatsu,sannan na zuba dalma cikin kunnensu to kugode Allah babu abunda ya sameta. kaikuma yanuna Abbin sa,sai kuma ya girgiza kai yana ficewa daga wajen,malik yana bin bayansa. Ansar tukin yayi don yaga alamar zai iya saka su accident, Huci kurin yake yana dukan hannunsa da dayan hannun,ya kwantar da kansa jikin makarin kujerar yana jin xuciyarsa tana tafasa soyake ya samu wanda xaima dukan mutuwa,soyake ya huce hanshinsa ko akan waye soyake yaga yafitar ma dawani jini ga fuska ko ya samu sauki cikin ransa,malik ya juyo yana kallonsa yace"ka ringa sassauta ma ranka wannan xuciyar Abdoul wahala zaka ringa sha abanza awofi,karshe ciwon ka yatashi ka samu a uku" Harararsa yayi yana jan tsaki,malik dariya ya danyi yana cewa"ko akaina zaka huce ne" "Idan kacigaba da bata mun rai babu mamaki na huce akan ka tunda neman wanda xan hucen nake" "To bismillah sarkin karfi kai naga alamar ma kafi doki karfi" Yafada yana dariya cikin fada da masifa yace"ba doki na giwa ce ni,karka sake hauda fushin da bana ka ba bazakaji dadi na ba wlh" "Sorry sir" yafada yana sara mashi. Tsaki yaja yana rufe idonsa kurin,har sukaje gida bai sake magana ba malik ma bai tanka mashi ba. ********** Cikin kermar murya Abbi yake cewa dady. "Abdullahi wacece safiyya,ya take wajen Abdoul dina meyasa su mamman suka yi kidnapped dinta?" Bubbuga kafadarsa yake cikin nuna kwantar da hankali,yace wa dpo din "koda wasa bance a sakesu ba,inda hali acigaba a basu horo har sai sun fadi wanda ya sasu wannan aikin" "Yes sir" "Sannan ko kusa kar wanda yazo neman belin su abayar don sudin yan ta adda ne bama wannan kadaine laifisu ba,acigaa da asu horo mai kyau" "Okay sir" Riko hannun Abbi dady yayi suka fito. "Ina zaka dani baka gaya man abunda nake tambayarka ba" "Yi hkr yaya sonake muje inda zan baka ansar,don bama ita kadai kake bukata ba ansar akwai ansoshi da dama dakake bukatar saninsu." "Ina zamuje yanzu" "Gidana dake gwarumfa zamuje sonake yau kasan wata gaskiya da kadauki shekara da shekaru baka santa ba,kasan masoyanka kasan makiyanka.kasan makasanka dake bibiyar rayuwarka,wai da kai xuwa kai belin wadancen yan iskan dakau kayi nadama ba karama ba." "Wai Abdullahi duk wadanna maganganun na miye,nifa tambaya guda nai maka" "Shiga mota yaya,bari na sallami guards dinka da driver ka alabashshi idan mungama saika tai inda zaka amman yau bazan kyaleka cikin kokwanto ba" Yaje ya sallami driver da sauran security dinsa ya dawo yashiga motar sa suka bar station din. ************ Tunda fiyah tabar gida ko kadan kalaman baba basu bar kanta ba,yadda yayi saurin na,am da muhseen din ne yake bata mamaki,dabadan tasan halin ba baban ba da saitace saboda hidimar da yayi masu ce sanda yana asibiti yasa baiyyi shawara da ita ba yabadata. Haka tai wannan exam babu sukuni,amman tana kyautaya zaton ta rubuta abun kirki. Feea ta isheta da tambaya meke damunta taga yau bata da walwala ko kadan,tafe suke suna tracking don samun taxi feea bata zoda mota ba........."bazan ji dadi ba ina tare dake kuma ki kasa gaya mun damuwarki,bacin ni idan ina ciki kina kokarin ganin kin warware mun ita." "Ba haka bane feea kawai dai inaga bai dace na damu wani da damuwata ba" "Karkice haka koda banda abunda zan maki ai na maki addua ko" Shiru fiyah tai tana nazari,bazata sanar da feea abunda ke faruwa itada Abdoul ba,har gara ta gaya mata baba ya badata ba tare da sanin ta ba. "Feea baba ne ya bada aurena ga kanen uncle yahya,fea bana sonsa ban taba son sa ba ko sau daya,kwatsam yaje ma baba da batun son aurena shikuma ya amunce mashi kaitsaye." Zaro ido feea tai yana cewa"aure waye wannan mai sa,ar.........hararar da fiyah ta sakarwa feea tasa tayi shiru tana dariya. "Sorry gaskiya banji maki dadi ba,irin haka babu dadi su daman irin samarin nan idan sukaga sun kasa samo kanka da kansu kurin sai su kai maganar ga iyayenka,inda sun san wasu baza a ki ansar tayinsu na" "Bayaga haka kuma abunda na lura dashi feea yesmin tana son guy din,din sadda baba yake sanar damu maganar fita tai ta kware tana tari,dana bi bayanta kuka naga tanayi aboye,alamar meye haka feea idan ba sonshi take ba" Jinjina kai feea tai tace"tabbas haka ne ma fiyah,son shin take don haka inaga wannace damarki da zaki kubcewa aurensa tunda har kin tabbatar yesmin tana son sa." "Daman abunda na yanke kenan zanje ma mama da maganar muyita cikin fahimta nasan zata yi wani abu akai" Da haka suka tari taxi suka wuce gida,aranta tana kewar Abdoul gashi wayarta bata nan jikkar ma duka bai bata ba. "Assalamu alaikum" Fiyah tayi sallama cikin gidan lokacin karfe hudu daidai,mama na alwallar sallar laasar ta ansa mata tare da cewa"sannu da dawowa safiyya kinsha yunwa dai yau,tunda baki wani ci abincin kirki ba kuma baki anshi kudin abincin ba" Dakinsu ta nufa tana cewa"bana jin yunwa feea ta siya mana abinda mukaci" Tshige kurin don so take mamar ta fahimci tana cikin damuwa kozata fara tambayarta abunda gake damunta. Anan saita zayyane mata abunda ke ranta,yesmin ta gani tagama salla tana linke sallayar. "Adda sannu" Kallonta tai taga bata cikin yanayin jin dadi,ba haka ta saba ganin yesmin dinta ba,zata iya rantsuwa da bata taba ganin ta cikin irin wannan yanayin ba. "Yawwa sannunki kema yauba islamiyar yamma kenan" Abayar ta ajiye saman kofar dakin tana cewa"aa akwai nice dai bazanje ba yau ban yi hadda ba" Wannan yasake jaddada mata cewar yesmin na da damuwa sosai,don bata fashin islamiya kuma ba,a taba biyota hadda ba.duk sanda ta dawo zatai bitar haddar har saita iya sannan. "Amman jiya ba naji kina yi ba,kuma banji inda baki iya ba" Gajiya tai da tambayoyin addar tata ta haye doguwar kujerar dake dakin ta kwanta tana juya mata baya. "Yesmin ba dake nake ba" Cikin kosawa tace"yaya muhseen yazo dazun ya kawo maki wasu kaya suna wajen mama" Dogon tsaki taja tace"ba shi na tambayeki ba ai,ina ruwana da kayan daya kawo tambayarsa nai ina son wasu kaya?ko zindir yaga ina yawo,yama dawo ya anshi abunsa don bana so maye kurin ana turesa yana kawo kasan wlh zaigane wanda yayi ma shishshigi ni banson maita,nace banayi ko dolene" Jiyuwa yasmin tai fuskarta babu fara,a ko walwala kamar zatai kuka tace"Adda kibar zaginsa babu kyau kana aibata wanda yake sonka" Kallonta take tana mamakinta lallai yesmin tayi nisa sosai,don ta sake tunxurata tace"anje anzageshin idan yaji haushi yace yafasa,ina ruwanki ma da zagin sa danake da aibatashin banson shishshigi kinajina,angaya mashi zai siyeni da abun duniya ne wofi dashi kurin." Idonta cike da kwallah cikin sanyin murya tace"Adda tunda bakison sa kibarshi da haka amman kibar aibatashi banajin dadi wlh don Allah" Ta fada tana jiyawa tana goge kwallarta. Mamakinta kashe fiyah yayi tace"yesmin mekike cewa,sake maimaita wa don Allah in tabbatar ma raina." Kukanta ta jiyo kasa kasa tama rasa me zatai saidai murmushi ya kubce mata,Allah sarki yar salihar qanwarta ta shigo layin manya.indai sone abunda yafi kuka ma yi mashi zakiyi. Kaya ta cire ta shige wanka tana jin dadin yadda ta tabbatar da abunda take zargi kan yesmin din. Wanka tai da Alwallah tayi salla sannan tazo tahau shiryawa,riga da siket ne ta saka ta yi simple make up tasaka turare tafito tsakar gida. Mama ke shara ta ansa tana yi mata suna dan taba hira, "Babanku tunda kafa tafara takuwa yafice agidan nan,kinganshi har yanzu bai dawo ba" "Ai haka akeso mama inkinga mutun zaune kamar baba to ba lafiya ba,Allah ya kara mashi lafiya.wai mama yaya jalal lafiya baizo ba" "Yayanku wata yar matsala ce ta faru can wajen aikin,mataimakin principal yayiwa wata yarinya fyade,to matsalarce aketa fama da ita shiyasa yace said satin sama" "Innalillahi fyade vice principal da kanshi,Allah ya kyauta gaba to" Mama tace"ameen iyakarta kenan" Shiru fiyah tai tana nazarin maganar da zata yiwa maman. "Kamar kina da magana dani ko safiyya?" Murmushi tayi tace"mama ai yadda zaki fahimceni nake tunani" "Karki damu ni uwace koma menene zan fahimcenki zan kuma dauki hanyar da zata daidaita matsalar." "Na gode mama,dama akan muhseen ne" ******** "Innalillahi wa inna ilaihir raju,un innalillahi wa inna ilaihir raju,un hazbunallahu wani imal wakil!!! wayyo Allah na wayyo Allah na Abdullahi na cuci kaina,na zalinci kaina na cutar da Abdoul dina.na wulakanta mahaifiyarsa ina zanje da wannan alhakin mariya mariya mariya!!! Saina kasheki saina yi silar rayuwrki wallahi bazan kyaleki ba,,,,,.......kuka ya kubce mashi matananin rikitarwa da gigitarwa kama shi dady yayi ya rungume yana jijjigashi don tausayin dan uwansa ya saka shima kwallar yake,jibi yadda jikinsa yake rawa duba yadda bakinsa yake karkarwa..........."kayi hkr ka natsu karka jefa lafiyarka cikin matsala,ka cigaba da anbatar sunan Allah shine zai kawo maka sauki.kadaina kiran kabani ba laifin ka bane kowa da tashi jarabawar kowa da kalar kaddararsa kadauka cewa kaida Abdoul mariya itace jarabawarku itace kaddarar ku.don haka godiya zakayi ma Allah ka nuna mashi farin cikin ka daya nuna maka gaskiyar da tadauki shekara shidda tana binne,hakika Allah yana sonku tunda har turo maki yarinya mai hankali mai tarbiyya da sanin ya kamata tashiga cikin wanna hadarin domin taimakonku,gefe guda ka malik dan albarka yaron da bamu haifar ba,bamuyi masa komi ba yazo ya dauki hidimar dawainiya da gudan jininmu,alokacin da kai ka yanke alakarka dashi.haka zalika ga zakiyya itama ta taka rawar gani cikin wannan aikin,don haka wadanan mutanen biyu bamu da kamarsu yaya.ina rokonka kiyayyar da kakewa malam kabir el-ladan kajanye ka yafe mashi idan ma ya maka laifi,bacin ma nasan baimaka komi ba,kashige ma yaronka gaba wajen ganin ya samu wannan yarinya guda tsoka daya amiya,ita daya tamkar dubu don Alfah bashida yarinyar data dace dashi bayan ita.Amman saika kaskantar da kanka wajen mahaifinta saika nuna mashi nadamar ka sosai da danasanin abunda yafaru abaya.koda zaka shigar da wannan bukatar. Mariya da mamman wannan kabarni dasu karka dauki mataki karka shigar dasu kotu domin sunan familyn ka zai sake lalacewa,Alh kwangila kuma na kaina zan mikashiga hukuma shida sake aikata irin wanan ko acikin mafarki bazai ba,don haka muje na kaika gida karka nuna mata komi zandai kaika wajen mami kanemi afuwarta duk da bagangan haka ta kasance ba" Ajiyar xuciya yak sauke wa yana jinjina kai yace"Abdullahi bana in sunan familyna ya sake baci,don haka cikin sirri agabatar da su ga hukuma har xuwa ga alkali,bana son ayimusu hukunci mai sauki,mariya inda dahali walahi sonake ayimun gunduwa gunduwa da namanta Abdullahi.murmushi Dady yayi yace "karka damu koba ai hakanba zata dandana kudarta kuma Allah bazai barta haka ba." Anayin sallar magruba yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya,yauce ranar dana ga Alfah yasaka manyan kaya don yana jimawa ainun kafin ya sakasu. Shimanshi yayi murmushi ganin yadda suka anshi jikinsa,sai annuri yake fitarwa kamar wani ango. Riga da wandone na farar shadda gizner yar dubu hamsin malik yayi masu dinkin da wata babbar sallar,tunda yaje idi dasu bai sake sakasu ba. Hannun mai links ne rigar iyakar guiwarsa wani fitinennen kamshi yake xubawa,ya taje kanshi malik ne yashigo yana kallonsa cike da tambaya kallon mamaki da al,ajabi yake mashi. "Mutumena ko anyi sabon kamune irin wannan hadewa gaskiya ko wacece na jinjina matsayinta,ni rabon dana ga kayi kyau irin yau bazan iya tuna wa ba gaskiya nawan" Yafada yana dafa kafadarsa cike da zolaya yana mashi dariya,murmushi ya iya mashi yace"karka fassara kwalliyata nayine don inji dadi insha iska kuma,badan wata ba ni bana yin abu don wani yaji dadi" "Uhmmm naji wannan to ga hula in aramaka don nasan ko guda baka da saboda baka son sakawa." Agogo yake daurawa yace"bana so rike kayanka idan inson sawa zanje insiya ne basai na araba" Hayewa yayi gadonsa yana cewa "ina zuwa don Allah" Wani banzan kallo yahi mashi yace"bana zuwa da kowa" Wayarsa ya dauka yana sawa ga aljihun gaban rigar ya dauki key. "Saina dawo" Dariya yayi yana cemashi "ka gaidata sosai" Baiko jiyo ya kallai ba yafito zakiyya na zaune tana kallo ta tusa abinci gabanta tana kallonsa ta kasa ci,kwalla ce ke fita daga idonta tana diga ga hannunta,ko kadan xuciyarta acinkushe take abubuwa sun mata yawa.bata iya bacci ko kadan tunaninsa da begensa sun mata tsaye ga rai,amman idan tatuna da cewar ba ta cikin shirginsa bata sanin sadda kuka yake kunce mata.haka zata raba dare tana kuka har sai kanta yafara ciwo sannan ta hkr tayi alwallah tayi salla ta roki Allah idan sonsa babu alkairi ya rabata dashi,ya kuma rage mata zafin kishim sa da takeji. Kamshinsa ya ankarar da ita yana tsaye kanta saurin saka hannu tai ta share kwallarta bata dago ba ta dauki plet din abincin wanda ko kwatarsa bata ci ba kuma bawani mai yawa bane. Tanufi hanyar kitchen jitai yacabe hannunta da babu komi..........wani abu ya tsarga mata tundaga hannun har tsakar kanta,runtae ido tai tana son sadakarwa amman xuciyarta na gargadinta da cewar tausayinki yaji bawai sonki ne yakejiba karki bada kanki zakiyya kibari inhr yna sonki a kanhi zai nemoki. "Meke damunki." Uffan batace mashi ba ta kwace hannunta tashige kitchen tana kuka kasa kasa. Ajiyar xuciya yayi yanajin babu dadi yadda yaganta cikin damuwa,komi kenan zai samu lokaci ya tambayeta. Fita yayi yashiga motar yabar gidan wani irin yaayi yake jin kanshi aciki,dokin ganin ta yake fiye da tunanin mai tunani amman baisan dame zaine mata ba,yasan dai jikkarta da sabuwar wayar daya siya mata sune suka karfafa mashi guiwar xuwa,amman baida wasu kalamai na musanman dazai fada mata yaja hankalinta suyi fira,amman kila idan idonsa yasauka akanta yaji kalaman sun sauka suma. Murmushi yayi wa kanshi inama ya dauko malik da zai samu saukin abun cewa shiya shi da magana bata kare mashi. Ko inda gidansu yake bai kalla ba yasamu waje yayi parking yafito,shagon dalha ya kalla yaga yana ciki wajensa yaje suka gaisa yace"don Allah abokina kashiga ciki kayi mun sallama da safiyyah mana" Murmushi yayi yace"to yallabai yanxu kuwa" Ya Vito yashiga gidan da sallama lokacin baba ya dawo duk suna tsakar gidan banda yesmin dake can daki,duk yinin yau taki fitowa saboda taji maganar da fiyah take gaya ma Mama. "Baba ana sallama da fiyah" Wani irin duka kirjinta yayi mama ta kalleta shima baban kallonta yake cikin alamar tambaya yace mata"waye" Sorry for let update fat an kuna lfy ina gaida kowa da kowa.✍🏻 [9/25, 5:29 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........51 Fiyah kamar mai hadiyar kunama sai zare ido take gabanta yana faduwa.saida ya sake maimaita tambayarsa idonsa akanta yace"bada uwata nake magana ba?nace waye ne" Kyafkyafta ido take tace"baba......ban....ban san ko waye ba wlh" Jiyowa yayi ga dalha yace muje inga kowaye. Tashi yayi suka nufi wajen yana zaune saman bencin dake bakin shagob dalha yana sauraren radio din da dalha ya kunna,yana ganin baba yayi saurin tashi yana jin wata irin kunya da giltness yana kamashi,sadda kai yayi yana shafa sumar sa cikin ladabi yace"ina wuni baba" Baban kallonsa yake a natse yana ayyana yadda ya koma,don yasha ganinsa ahanya baya ma cikin hankalinsa yasha ganinsa zaune bakin titi ko kaganshi akwance cikin yanayi marar dadi,amman yanxu sai yaga natsuwa da kamala ta kamashi.ga wata yar kiba dayayi kuma cikin shiga ta mutunci ta hausawa. Daker baban yace"lafiya lau wa kake nema" Shiru yayi yana mulmula maganar tome zaice,yazo zance ko yaya zaice tunawa yayi da jikkar fiyah da wayarta yace kanshi kasa "daman jikkarta ce data fadi tun rannan da wayarta ne nataho mata dasu,sannan na dubata a jiki" Jinjina kai baban yayi yace"yayi katabbata sukadai suka kawo ka?" Inama zai iya furta abunda yake karkashin ransa ga baban,inama zai iya cewa baba kaban ita kaban iznin nemanta........amman ina maganar tafi karfinsa yana jin nauyinsa fiye da tunani. "Eh shikenan" "To yayi zata zo ta ansa amman daga yau karka sake xuwa don Allah,domin idan wanda naba aurenta yazo yaganku zaiji babu dadi" Wani abune yatsaya mashi ga wuya,dandanan yaji kanshi ya sara mode dinsa najin dadi dayazo dashi yana guduwa yana barinsa,daker ya hadiye wani miyau kanshi still yana soke akasa yace"insha Allah" "Allah yayi Albarka mungode da dawainiya" Kasa ansa adduar yayi yaji dadinta amman dacin dake bacinsa da ciwon dake ransa ya hana shi ansawa. Juyawa baban yayi yashige gida. Bayan fitar baba mama ta kalli fiyah tace"kigaya man gaskiyar abunda yaje tsakanin ki da yaron nan safiyya,karki kwari kanki" Kanta akasa taji duk ta takure ita batasan me xata ce da mama ba,Abdoul baice yana sonta ba itama kuma bataji tana son sa ba don haka kenan bata da wata alaka dashi. "Mama babu komi wlh,idan akwai zangaya maki.kuma badan saboda ina gudun muhseen yasa nasanar dake halin da yesmin take ciki ba,wlh saidon ganin abun nata mai girmane ki fahimtar da baba inda matsalar take,ni idan ta nice zan iya hkr na zauna dashi koda bana sonsa don nayiwa baba biyayya,amman kinji dalilina wlh mama" "Shikenan safiyya,zan mashi magana kuma zai fahimta insha Allah." Daidai baban yayi sallama ya shigo ya samu waje kan tabarmarsa ya zauna fuskarsa babu walwala ciki ciki yace ma fiyah. "Kije yana jiranki,ban kuma ce ki dade ba" Mama kallonsa take da mamaki tace"babansu waye kuma" Baya yajuya yana kara volume din radion sa yace"yaron gidan Alh muazzam ne" Jikinta amace tatashi ta shiga ta sanyo abayarta har kasa zata fita har takai kofa,taji baban yace"kisake jaddada mashi karya sake xuwa daga yau" Daker tace mashi "to baba" Yana zaune cikin motar ya kwantar da kujerar baya ya kwanta shima ya dora ga hannayensa duka biyun,idonsa arufe shikadai yasan irin yadda yakeji cikin ransa,sallama tai tana knocking glass din window din Mai za man banza. Wani waje ya latsa kurin kofar ta dan bude,bismilla tayi ta shiga ta zauna amman kofar abude take,kamshinsa ne yayi mata sallama ya baibaye gabaki daya hancinta,har numfashinta jitake da kamshin yake fita. Kallonsa take sosai ganin sa da kayan da bata taba ganinsa dasu ba,akwai hasken waje na gidajen dake kallonsu ya hasko motar sosai,hakan ya taimaka mata wajen kallonsa duk da yana kwance. Inama zai cigaba da sakasu sunfi mashi kyau sosai da sosai.ta fada cikin ranta,ganin bai motsa ba yasa ta sake magana. "Ina wuni" Hannu ya mika baya ya jawo ledar wayar daya siyo mata,da jikkarta yana tasowa ahankali ya mika mata. "Ga jikkarki nan,wannan wayace waccen bata aiki ta samu matsala." Kallonsa tai dandanan ta gano damuwa kwance afuskarsa har tana iya ganin idonsa dasuka dan canza. "Baka da lafiya ne yaya Abdoul" "Meyasa kika kasa gaya mana aure zakiyi,oh sorry wanan ba hurumin bane Allah yasa alkairi ya bada zaman lafiya" "Nagaidaka baka ansa mun ba,na tambayeka lafiyarka shima baka ansa mun ba,kana mun wata magana daban.baka ga yadda yanayin ka yacanza ba" Dafe gefen kanshi yayi dake ciwo bai iya bata ansa ba,ta sake cewa. "Karinga daukar komi da sauki,ba komi ake zafafawa irin haka ba kai koda yaushe in abu yana damunka bakasan kayi addua ba,bakasan ka roki ubangiji ya yaye maka ba,saidai zafin rai da zuciya.wannan ba shine zai saka abunda kake ji ya sauka ba saima sake tun xura ranka cikin bacin da hakan zaiyyi,idan zakaji shawarata aduk sanda wani bacin rai ya sameka karka manta anbaton sunan Allah,domin shine kwarin guiwarka shine zaisa kaji ranka yyi sanyi,shawara ce ba tilasci ba idan banyi shishshigi ba zan iya sanin abunda yake damunka koda inada abunyi akai" Kalamanta jinsu yake kamar saukar kankara cikin xuciyarsa,duk sanda take magana xafin dayake ji cikin ransa yana raguwa,shin taya zai mallaki wannan yarinya mai tarin abubuwa marasa karewa,tabbas samunta matsayin mata shine abu mafi sa,a da muhimmanci itace ake cewa hasken rayuwa,hakika rayuwarsa data yaransa zata zama abun koyi ga sauran mutane. Jingina bayansa yayi yana ajiyar xuciya sau biyu,ya juyo yana kallonta idonsa cikin nata muryarsa da rauni tayi laushi sosai kamar mai jin bacci yace. "Sofiyya" Wani jirrrrrr taji ga jikinta tana runtse ido tana anbaton sunan Allah,saboda abunda taji bata taba jinsa akanshi ba,daker tace mashi batare data kallai ba "naam" Numfashi yaja yana dan ja baya yadda zaiji dadin kallonta,satar kallonshi tai taga ya xuba mata idanunsa dake narkar da yar xuciyarta dabata da karfi akanshi yanxu. Kamata yayi tana kallonsa murmushi yayi yana cewa"baba yace mun karna sake xuwa kar wanda yaba aurenki yaganni yaji babu dadi" Dagowa tai taxuba mashi idanunta,lumshe nashi yayi yanajin kallon har tsakar kashi. "Karki cinyeni pls" Sai lokacin taji kunya ta kamata ta juyar dakai tana jiya abun da yace mata aranta,to menene abun damuwa don baba yace haka. "Kince nafada maki ko kinada abunda zaki iyayi akai" "Amman meyasa zaka damu akan haka?" Shiru yayina dan wani lokaci kafin yace"inason na ringa xuwa muna gaisawa,so nake mu kulla xumunci shiyasa duk na damu" "Uhmmm" Bata sake magana ba don in akan wannan ne bata da tacewa,tunda har baban ya furta to dagaske yake akan hakan. "Akwai Sabon layi aciki na maki register zaki cigaba da anfani dashi,idan ina bukatar magana dake na kiraki,zan wuce sofiyya nagode da gundunmawar da kika bayar cikin rayuwata Allah ya baki zaman lafiya da wanda zaki aura,naso ace nasamu wata dama da zan nuna maki godiyata da kuma ladar abunda kikaimun,hakika na yanke kauna da sake rayuwa irin wadda nayi abaya,na fidda tsammanin zan dawo Abdoul-nasser din da nake ada,saigashi cikin lokaci kalilan lokacin da banyi tunani ba kin kawar mun da wannan tunanin,tun ina kaucewa har hakan ta gagara.donAllah ki yafeni abisa maganganuna nabaya akanki,bisa kuskurene,kuma insha Allah bazan taba manta wa dake cikin raina ba aduk sanda na tuna dake zan maki fatan alkairi. har yau ban cire rai ba da samun irin damar danake kwadayi daga gareki,lokaci yana xuwa idan ina da rabo amma. kar aga kin jima kina iya shiga gida" Shiru tai shima yayi shirun yanajin halbawar xuciyarsa,yana jin kamar zairasa wani bangare daga cikin jikinsa,kana sarawa yake baison tatafi amman baya son abunda xai saka aimata fada. Can yajiyo muryarta kamar tana rawa cikin sanyinta wanda yasake haddasa masa wani irin cikin ransa,. "Yaya Abdul wace irin damace karasa" Ajiyar xuciya yayi yana saka key din motar jikin makunnin yace"ta riga ta wuce idan darabon kiji idan nasake samu may be zakisani" "Shikenan yaya Abdoul nagode nima,amman karka manta da maganganun mu na baya akan alfarmar danake so kaimun,don Allah ka auri zakiyya domin tana sonka........."kekuma fa bakisona?" Cigana tai batare data tanka ba. "nibazan iya fadar irin son da take maka ba,nasan dai tayi nisa acikin duniyar kaunarka,kuma ta cancanta da zama matarka.........."ke kuma fah" Runtse idonta tai tanajin kamar yana zaneta da dorina saboda yadda takejin kuna akan abunda yake fada,girman kai baxai barshi ya iya furta mata yana sonta ba,sai itace xata xubda kimarta da darajarta tace mashi tana sonsa,abunda batajin zata iya koda hakan nanufin kwanciyarta gadon asibiti. "Koda ba aimun miji ba bana jin hakan zata faru tsakanin mu" Cikin sauri yace mata"why" "Saboda ban tsara haka araina ba,hasalima ni ba irinka nake mafarkin aure ba,kayi hkr" Baitaba jin ta bata mashi rai irin hala ba,kasa magana yayi yatada motar yana jiran ta fita yafigeta yabar wajen ko zai samu saukin wannan ciwon da tasake jiwa xuciyarsa. Saida tayi maganar taji bata kyauta ba,taji gabaki daya hankalinta yatashi. Har hakan ya nuna ga fuskarta jiyowa tayi zatai magana. Ya daga mata hannu cikin wata murya mai nuna bacin ransa yace"plzzz out" Jikinta yayi masifar sanyi ta fice kuka nason kubce mata,kamar antada tiyagas haka Abdoul yatada kura wajen yatafi. Aguje tashiga gida ko kallonsu mama dake tsakar gida batai ba ta hige dakinsu,adakin ma toilet ta rufe da kuba ta zauna kasa tana kuka mai taba rai.............. *don Allah kuyi hkr wlh yau kwance na yini banda lfiy,wannan ma karfin haline plsss kuyi mun uxiri lafiya na gaba da komi 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️.............52 "Kayarda da maganata babansu,wlh nayi imanin safiyya bazata taba bujirewa bukatarka ba saboda radin kanta,ta hango abunda mu bamu hangaba,anacewa abunda babba yahango yaro ko yahau rimi bazai hango ba,amman wannan karin maganar tasha banban da abunda yafaru,babansu ka godewa Allah daya baka yarinya tamkar da dubu safiyya nada hankali,tana da biyayya tana hangen nesa uwa uba hakurinta da kawaicinta,ta gaya mun cewa wlh bacin yadda taga yasmin ta shiga wani hali saboda jin abunda kayanke tsakanin safiyya da muhseen,da bazata taba nuna ma kowa bata sonsa ba,zata auresa kodan tayi maka biyayya tasan kuma bazata tabeba don kau mahaifinta ta yiwa abunda yakeso,kaduba kaga wannan zamani yadda wasu yaran suke jefa rayuwarsu cikin halaka saboda iyayen suna matsawa suyiwa yaransu auren dole,kanaji diyar yadikko harira har yau ba aganta ba saboda auren dolen da suke shirin yimata bata so,mafarin ta gudu kenan yau wata uku.sannan danginku kasan anyi haka diyar kawu shazali data yi yunkurin kashe mijin itama ta kusan kashe kanta,gobara ta saka agidan Allah ne kadai ya fiddasu basu mutuba suduka,saboda bata sonsa kuma yaki rabuwa da ita tagwammace sumutu suduka data cigaba da zama dashi,kaduba maganata babansu kuma kayi shawara da wani wanda kasan zai gaya maka gaskiya,idan kana ganin ni tawa ba komi bace" Tatashi zata bar mashi wajen don iyakar kulewa takule,ganin yadda yake yunkurin aurar da diyarsa mafi soyuwa garesu ga wanda bata so,bacin ga wanda ke sonta kuma bazai amunce da hakan ba. "Dawo nan mamansu" Badan ta so ba tadawo don iyakad shekarun dasukai atare irin haka na jimawa bata faru tsakanin su ba. Babu ma,auratan da basa samun sabani saidai ace na wasu yafi nawasu. Dawowa tai ta zauna tana jiran abun da zaice. "Inbanda ke wagareni dazai bani shawara irin wannan dakika ban?" "Uhm babansu kenan na dauka kaima ai kayarda da maganar nan da akecewa mata tunaninsu kalilan ne,basu iya bada shawara ba" Murmushi yayi yace"to aa banyarda da haka ba,don tawa matar tawice anan indai fagen hangen nesa ne da kuma tanadin abunda zai daidaita zaman takewar iyalinta,nakuma ji dadin wannan shawara kuma hakika nayarda uwata wajenki duk ta dauko wadannan halayen" Sadda kai tai tana murmushi"uhm Babansu kadai fadane amman safiyya kam ai kaine gaba daya" "Insha Allah zansan abunyi hakika da munyi kuskure babba,Allah ya kara rufa mana asiri." Duk hirar da suke akan kunnen fiyah da yesmin wadanda basuyi bacci ba kowa da abunda yake damunsa,yesmin batasan Addarta batai bacci ba amman fiyah tasan yesmin idonta biyu. Tun bayan data gama kukanta a toilet ta fito ta kwanta tana dana tasanin abunda ta gaya ma Abdul dinta. Amman wani shashe na xuciyarta yana gaya mata gara ta ja ajinta gara ta nuna mashi ita din mai ajice hakan zaisake jansa ga kaunarta.don sun ganin su sunda abunda dole ma yarinya ta kware masu,wanda hakan yakeja wasu matan suna rasa darajarsu wajen maza saboda tun awaje kin xubar da kimarki........har ga Ko son Abdoul zai kashera baxata iya kallan idonsa tace tana sonsa ba,haba ina kunyarta take ai mama ma saita kusan dukanta saboda fada.haka taraba dare tana sakawa tana kwancewa,adduarta guda kada Allah yasa xuciyarsa tayi na,am da auren zakiyya domin tanajin tafafi zakiyya jin kishinsa axuciyarta,jitake muddin haka tafaru duk wani jindadinta yakau adoran duniya,kawai dai ita tana iya control din nata ne tana iya danneshi alokacin dayake sata abunda ba daidai ba......ta furta ya aureta ne don bata da wara mafita,don kuma zakiyyar ta dace dahaka tayi sadaukar da rayuwarta ne dominsa,bai dace ya wofintar da ita ba.ajiyar xuciya taja sosai har yesmin ta jiyo tace"Adda baki bacci ba kema" Tama manta da yesmin wlh "aa nafarka ne keme ya hanaki bacci" Kamar zatai kuka tace"Wlh Adda xuciyata wani iri take mun nakasa baccin tunani ya isan ni bansaba haka ba abun sai yake mun wahala" Tausayi tabata don tabbas fadawa kogin kauna wadda ba,asan kanayi ba wahalane da ita,ba kowane zai iya jurewa ba sai mai tsananin hakuri da kauda kai,abune da kecin xuciya da ruhi abune dake taba dukkanin lafiyar jiki data kwalwa da xuciya ajiyar xuciya tayi tace mata"kije kiyi alwallah kizo ko raka,a biyu kiyi kidan karanta qur,ani ko sura biyuce zaki samu bacci mai dadi" Babu musu tatashi ta shige toilet din,dafe goshi tai tana adduar Allah yasa kar so ya wahalar da yar qanwarta. Komawa tai ta kwanta tana dasa tunanin nata,tabbas ayadda abdoul yafusata bata jin zaisake dawowa haka zalika zai nemeta,kuma zuciyarta tana raya mata abunda bata son,wani zafi taji ga kirjinta ahankali ta furta "bazan iya sharing dinka da kowa ba Yaya *NASSER* duk yadda xuciya ta kwallafa rai dakai dole xata barka,kishinka araina mai girmane bazai barni nazauna lafiya ba" Saitaji kwallarta tana silalowa saitaji tana sakawa ranta hakuri dashi tun yanxu,tabbas tanajin ajikinta Abdoul zai dauki maganarta zaije ya daidaita da zakiyya,zai aikata abunda ta fada ba shakka hakan zata iya faruwa.......danasani ya shigeta yafi sau dubu na fadar abunda ta fada karshe dai wannan daren ya dade bai karema ta ba tana gani yesmin tayi baccinta hankali kwance itako saidai juyi,asubar fari baccin ya sureta tare da mafarkin *(ABIN CIKIN RUHINATA)* motar Abdoul na fita ta su dady ta shigo cikin unguwar bin sa da kallo Abbi yayi yana cewa"Abdullahi motar Alfah ce naga tafita wlh shine Allah yasa gida yaxo Allah na rokeka Allah yasa hakane" Murmushi dady yayi yace"Adduarka ba haka take ba,zance yaje. ga dukkan alamu kuma anbata ransa" Hankalin Abbi atashe kamar zai kuka. "Wlh tsakanina da mariya Allah ya isa Allah kadaukar mun mataki akan matarnan,ta cutar dani tana kan cutar da rayuwata data iyalina,mekake tunanin yafaru dashi Abdullahi" "Kodai baisamu abunda yaje nema ba,kokuma mahaifinta ya ganshi ya dakatar dashi cikin daya biyu kokima duka" Abbi muryarsa tana rawa yake cewa"duk duniya bayan iyayena damuka rasa banda abunso sama da Abdoulnasser,kuma saboda farin cikinsa babu abunda baxan iya ba,har kwamciya ina iyayi kasa malam kabir yabi ta kaina inhar zaibashi farin cikin dayake nema,inhar zai mallaka mashi yarinyar nanan,don naga kamar son ta yake kamar rayuwarsa" Dady yace"rayuwar tasama bai adauketa da muhimmanci ba kamar safiyyah,shi kanshi baisan soyayyarta taimashi mugun kamu ba sai nan gaba tukun." Har cikin compound din gidan yakai Abbi sojojin dake tsaron gidan wani yazo ya bude mashi kofa yana sara mashi,bama tashi yake ba. Koke koke keta fitowa daga bangaren umma,cikin kuluwa yake tambayar sojan dasuke kula da bamgaren magana. "Ubamme yafaru acan wajen suke wa mutane ihu" Cikeda mamaki sojan daya kame don yasan baida magana mai dadi saita su umma,kullum daya zo zaice suna lafiya babu wani abu dai ko,amman yau sai yaji sabanin hakan. Cikeda bala,i Abbi yace"dakai nake shege ka tsaya kana kallona" Jikinsa yana bari yace"yallabai madam ce........itace......daman......dama......"dakai nake kana mun ina ina zan ci ubanka wallahi" abbi ya daka mai uwar tsawa saida ya daskare,yana nuna part din yana cewa"itace ta......ta hauk.....ace......ta yayyaga kayanta tana iface iface,tayiwa haulat dukan tsiya har cikinta yaxube,yanzu haka zuwairat na wajenta ca asibitin,ta jiwa khadija rauni ga kai saida aka daureta aka rufeta adaki sannan,amman taki shiru itace keta wancen ihun,ankiraka yafi sau ba iyaka yallabai naka dauki waya ba kagafarcemu" Murmushi yaga Abbi yanayi cikeda jin dadi yace"daddaden labari kana da kyauta ta dubu dari,ka tuna man da safe ban kuma ce uban kowa yashiga ba kunajina ya fada yana nuna sauran security din dake wajen. Dady yace"karkayi haka yaya..........Abdoullahi idan baka son raina yabaci kaimun shiru kama hanya kuma ka nufi gidanka iyalin ka najiranka" Ya wuce part din su Mami yanajin wata matsananciyar kewarsu ita da ni,ima.har tun tube yakw ya shiga jikinsa har wata tsuma yake,falon shiru sai karar Ac kallon falon yayi furniture's duk sun lalace,gabaki daya ma part din ya Lalace babu kulawa bawai rashin tsafta ba,aa komi ya lalace yana bukatar canji,wasu kwalla suka xubo mashi. Sako da lungu na part din yake dubawa yana hawaye. Motsi yaji kitchen ya leka mami ce keta kokarin sarrafa yar cus cus din data rage masu rabin leda tayi ma dady waya basuda abinci yace sai xuwa gobe. Julluf tayi ta juye ga plet zata bar kitchen din don ni,ima ce keta amai bata lafiya dataci abu saita amayar dashi,mafarin ta yimata ita. Juyowar da zatai taganshi tsaye bayanta yana goge kwallarsa,saboda tsorata sakin plet din tai kasa tana ja baya,don bazata iya tuna rabon data ganshi ba.......tsora ya kamata tuni hawaye sun wanke idon ta. *_ABDOUL-NASSER_* Ya na isa gida dakin zakiyya yayiwa tsinke................ *naga adduoin ku ina godiya sosai Sannan ina rokon Alfamar ku cigaba da man uxiri saboda yanayin jikina,ngd da nuna kauna* [9/30, 3:43 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️..........53 Saida yashiga falon yaga baidace yashigo mata acikin yanayin dayake ciki ba,frig dinta ya bude ya dauko ruwa har zaikai bakinsa yatuna da dokarsa,saurin dakatawa maimakon yasha saiya fito waje da robar ya tuttulewa kanshi ruwan har xuwa ga fuskarsa,yana sauke ajiyar xuciya sanyin yana ratsa xuciyarsa yana sauke mashi duk wani zafi daya debo. Jingina bayansa yayi da bango yana yin relax,saida ya kwashe minty biyar ahaka sannan ya samu sauki ya najin duk wasu makamai dake cunkushe cikin ransa suna sauka,duk da ba duka ba. Har yanxu kunnensa yana sake jiyo mashi munanan kalamanta,wannan ya nuna cewar hasashensa akanta duk gaibune,yana tunanin yadda yakejin masifar kaunarta cikin ransa yazaji itama haka,koma fiye dahaka ashe haukan banza yake.yana bukatarta cikin rayuwarsa da zai dora agaba idan Allah yabashi iko,yana ma yaransa tanajin uwa da tagari da zata dorasi bisa daidai.yana mafarkin zamun hasken acikin rayuwarsa agaba,amman duk wani burinsa da fatansa ta rusa mashi su. Saiwani nanata mashi maganar auren zakiyya take,ina ruwanta da aurenta da rashin auren ta dazai,amman yanaga wannan ce kurin damar shi.yadda ta nuna bata yi dashi duk maitarshi shima ya kamata yadaga mata kafa hakanan,karon farko yaji xuciyarsa ta raya mashi daidaitonshi da xakiyya,har xuwa sanda zai yanke shawarar data dace dashi. Bedroom dinsa ya nufa kurin ya fada toilet ya saki ruwa ya jima yana sauka jikinsa yafito da Alwallah yayi sallar isha,i sannan ya canza kaya yaje ya hado tea marar zafi sosai,yana sha ya gama ya duba system dinsa sakonnin costomers masu son ganawa dashi,yayi accepting wasu wasu kuma yayi reject. Haka yayita aikin da zai dauke mashi hankali daga tunaninta da bacin ranta,har dare ya tsala ya ajiye ta kwanta daker da sidin goshi baccin yayi nasarar daukarshi. Muryarta cikin kuka kukanda duk wanda yaji saiyaji kamar ya tayata,tundaga kasan xuciyarta kukan yake tahowa,numfashinta har sama da kasa yake maganar ma bata fita sosai,don muryar ta dishe saboda kuka. Yana rungume da ita cikin kirjinsa yana tayata kwallar shima,don shima kukan kurin zaiyi yaji ya samu saukin xucoyarsa. "Na gode ma Allah da wannan jarabtar domin na yi imani dashi,hakan yana cikin kaddarar rayuwarmu nida yarana,kuma bazan butulce mashi ba zan gode mashi da har ya waiwayo maka da hankalinka akanmu.hakika wannan hukuncin sa ne ba na kowa ba.sai kuma sila da dalili,banda kamar wannan yarinya aduniyata hakika Allah zai mata kyakkyawan sakamako aduniya da kuma lahira,malam kabir daka tsana arayuwarka shine dalilin dayasa kake raye ahalin yanxu,haka diyarsa safiyya itace dalilin dayasa muka tsinci kanmu cikin wannan halin na farin cikin daidaituwar komi,idan baka nemi yafiyarsa ba Allah saiya tambayeka matayinsa na makocinka mai hakki akanka,amman kasa kowa ya tsanesa bada wata hujja ba Abbin ni,ima kadawo cikin hayyacinka idan baka gina lahirarka ayanxu ba yashe zaka ginata,kana da tabbacin kana da kwana ki dayawa arayuwarka..........rufe mata baki yayi yana kwalla harda shashsheka yace"insha Allah nai alkawarin gyara kura kuraina mamin ni,ima nai alkawarin dawowa mutumen da al,umma zasuyi alfahari dani kuma zan dage da neman tsari daga shaidan da makarrabansa,domin hada rashin kiyaye azkar yasa koma me mariya tayi mun ya sameni.amman na dauki hakan matsayin darasi da kuma hanyar gyarace Allah ya nuna man,hakika zan gyara alakata da malam kabir inhar yaban dama xuria zan hada dashi." Jawota yayi suka zauna kan kujera yana rike da hannunta,yasoma bata labarin duk abunda ya sani ayau dinnan,kuka ta kamayi tana fadawa jikinsa yana sake godema Allah daya kawo silar fitarsu cikin wannan kangin. Wannan dare haka Abbi ya rungume mami da ni ima ajikinsa har garin Allah ya waye. ********* Yau da shirin koma wa wajen aikinsa ya tashi,tun wajen bakwai ya gam shiryawa yafito bai saka ran samun abun kari ba,don yasan irin wannan lokacin daga ita har malik basu isa tashi ba. Amman sai yajiyo wani kamshi wanda ya ankarar dashi cewar tatashi,dandanan yaji yunwarsa ta ake yunkurowa. Agogonsa ya kalla yaga ya kusan makara kuma yanzu haka mutanen da ya ansa zama dasu suna can har sun iso tun da asuba jirginsu ya sauka. Hanyar kitchen din ya nufa yana dan daidaita fuskarsa. Ta juya baya tana soya kwai ga dankali nan ta kwashe cikin gwagwa,saman gas din kuma farfesun yan cikine take idasa dafawa.ga placx nan komenene ta hada ciki kilan tea ne,inji xuciyarsa, Rungume hannu yayi ga kirjinsa yana kallon bayanta,doguwar rigace ta bacci iyakar guiwarta amman mai kauri baka ganin jikinta,gyaran murya yayi wanda ya sata tsorata har tana yadda ludayin datake juya kwan dake cikin kasko.lumshe ido tayi tana ajiyar xuciya ta duka ta dauki spoon dinta tana juya tace"ina kwana" Murmushi yayi ya ida sa shigowa sosai yana cewa"uhmmm wannan kamshi dakika bude gidan dashi haka,mekike aikata mana ne" Banza tayi dashi amman kasan ranta murna ce fal kamar me. "Don Allah ataimaka mun ahada mun cikin basket sauri nake kuma bazan iya jira naci ba,Allah yasa andafa dani" Nanma taimashi banza ta gama soya kwan ta dauko kwandon da yaje xuwa office dashi da containers din da take xuba mashi,ta fara xubawa ko inda yake bata kalla ba. Jinjina shariyar da take dashi yayi amman sai yaji hakan kuma ya burgeshi,hakika ballagazar mace marar aji batai ba ace kina mace Mai daraja kina watsar da ajinki da kimarki. (Yan mata take not akula da kima da martaba,suna da matukar muhimmanci ga rayuwarki ko kau ga mijinki ne balle saurayi) "Wai har yanzun fushin ake dani zakiyya" Wani kallo ta jefa mashi ta dauke kai ta cigaba da aikinta kurin. Dariya ya danyi kadan harta kalleshi don shidin bai cika fiddo dariya ba sai ta kama,gira daya ya daga mata ta dalla mashi harara. Ta gama xubawar ta ajiye mashi gefensa tana tattara wanke wanken wanda zatayi yanzu. Matsowa yayi kusa da ita kamar zai rungumeta muryarsa kasa kasa yace"I'm very sorry kiyya,nasan laifina yasa har yau kike fushi ko?"daskarewa tai awajen don gabaki daya jikinta ya dau wani sanyi,don abun yazo mata abazata. "Idan nadawo zamuyi magana oky" Daga kai kurin tayi yadauko abincin yafice sai lokacin ta sauke wani gauron numfashi. ************ Bayan fiyah ta dawo daga jarabawa yau wajen karfe shidda harda wani abu ma,tana shigowa gida akafara kiran sallar magruba. Baba bai dawo ba saida aka gama sallar yesmin na kitchen yau ita ke shirya abincin dare,tuwon shinkafane miyar agushi baba ya siyo naman rago an xuba aciki (harnaji miyauna ya tsinke🤭) Tunda fiyah ta dawo tana daki bata jin dadi ko kadan,don har wata masassara takeji.tana cikin tsananin kewarsa tana kan nadamar abunda yafaru,jitake inama ta fada mashi cewar soyayyarsa itace weakness dinta,itace farin cikinta da bakin cikinta.rashinsa gareta wani babban bigirene da bazata iya misalta shi da komi ba. Mamace ta shigo dakin don yesmin tace mata tana daki kwance. "Safiyyah lafiya kike kuwa" "Bandai jin dadi ne mama kamar xanyi xaxxabi" "Subhanallahi,ainace ku daura net kun kiya badole sauro ya cije kuba,bari dalha taxo saiya siyo maki ACT,kifito kici abinci harda yunwa ma kilan" Babane yashigo yasa mama ta fita tana ansa sallamarsa. Take gaya mashi abunda ke damun safiyyar,yaje shima ya dubata yace ta fito yasa mata tabarma tasha iska,saitaci abincin tasha magani. Gaba daya suke cin abincin a tire guda,sun hirar su gwanin ba sha,awa,kallon safiyya baban yayi yace"bayan masassara akwai abunda yake damun ki uwata ko?" Yake tayi tace"aa baba babu komi bayan ita,hada gajiya kullum ina kan hanya babu hutu shiyasa ma kila ta saukomun" "Allah ya baki lafiya,muhseen ya kiraki kuwa" Kanta yana kasa tace"eh ya kirani ina cikin jarabawa saida nafito na yasake kiraa" Jinjina kai baban yayi yace"idan ya sake kira ka safe,kice ina son ganinsa idan ya samu lokaci" Da to kurin ta bishi,tana jin dadin abunda zaifarun don tasan maganar yesmin zai mashi. Dalha ya shigo da maganin nasha yafita,bai jimaba ya dawo yace ana sallama dani. "Waye" Inji baban. "Kanen uncle yahya ne yazo" "Kace ya shigo batajin dadi bazata iya fitowa ba" Dadi ya kamani don kona fitar bansan me xance mashi ba. Yesmin naga ta shige daki tana jin ance haka,murmushi nai nace araina makira tasan ta samu abunda takeso. Sallama yayi mama ta ansa mashi baba na nuna mashi tabarmar dayakai. "Bisnillah anan dana zauna" Ya na murmushinsa na gado ya zauna yana gaidasu cikin girmamawa,hakika muhseen mijin aurene kawai dai ni banda ra,ayinsa ne shie kawai. "Yaya muhseen ina wuni" "Lafiya lau safiyya ashe bakiji dadi ba sannu Allah ya sawake" Tace"ameen nagode" Baba ya kalleta yace jeki ciki zamuyi magana dashi,kekuma mamansu xubo mashi tuwo karkace ka koshi zan dauka baka daukemu iyayeba" "Zanci baba kayi hkr" Mama tatashi taje ta xubo mashi ta kawo ta ajiye tana samun waje daga gefe itama ta zauna,yana ci baban yana janshi da hira kadan kadan har yaci dayawa yana ajiye spoon din. "Na koshi mama ya isan haka nagode sosai kuma tuwo yayi dadi ba kamar tuwon jawaheer ba" (kanwarsu dake bi mashi agida) Dariya mama tai baban yana tayata tace"kadai raina nata ne amman ba dadine babu ba" "Wlh mama karma ki hada da wanan nakin,don ita tuwonta kamar talge haka yake,kanaci zai ka nemesa karasa" Dariya suke ita baba ta GB wuce ta kai kwanonin kitchen baban yace"wannan din kuma da kake yabawa qanwarka yesmin tayi ai" Zaro ido yayi"dagaske,gaskiya ta yi kokari sosai zan turo jawaheer ta ringa koya wajenta. Gyaran murya baba yayi yace "muhseen" Jin yadda baban ya kirashi yasan maganace mai matukar muhimmanci,yadago yace"na,am baba" "Magana zamuyi dakai mai muhimmanci,ina fatan zaka fahimce mu kuma xaka dauki abunda muke nufi da kai" Jinjinakai yayi yace"insha Allah baba xanyi duk yadda kace" Gyara zama baban yayi yace"ammm muhseen alokacin dana ansa maka kan maganar uwata ashe munyi kuskure kadan,wanda har hakan yake son kawo damuwa. Inason nabaka hkr abisa abunda xance maka,don Allah ka hkr da safiyya ka nemi qanwarta yesmin.wasu dalilai suka nace haka saboda ganin cewar uwata batayi na,am da maganar ka ba kuma bata fadi cewar bata so ba,sainaga wannan zai iya kawo cikas ga zaman takewar ku maimakon kuji dadin zama da juna ana iya zamun akasin haka,saboda kaunar danake maka yasa naga bazan iya kyaleka ban maka tayin auren yesmin ba,ko ita za a mu dace amman idan kanaso bazan ta kuraka ba don bazan so wani ya cutu ba ya kagani,inbaka lokaci kaje kayi shawara agida kokuwa." Ajiyar xuciya yasauke yana jin wani dan ciwo kasan ransa,hakika babu abunda yakai kaso akika amman kuma hakan yafiye mashi sauki daya aureta bata sonsa,bazaiji dadin zama da ita ba koda kau ta danne ta nuna bakomi,amma ita ai abun zai cutar da ita,sannan itama yesmin din baida tabbacin zata soshi balle har yayi saurin na am da maganar baban,hakika yana son safiyya so marar iyaka,amman hakan bazai sakashi yaso kanshi ba don haka ya hkr da ita maganar yesmin kuma itama dole yasan idan ita tanuna tana ra,ayinsa shikuma zayyi alkawarin kulawa da ita fiye da tunani kuma zai yi iyakar bakin kokarinsa wajen sakata cikin xuciyarsa,har Allah yasa mashi sonta. "Kayi shiru muhseen,idan kaga akwai takura wlh babu tilasci kafafi ra,ayinka naji" Ya sake sadda kanshi yace"baba hakika na fahimce ka kuma abunda ka fada gaskiyane,ban boye maka ba tun wancen lokacin inason safiyya,amman sonta bazai saka na cutar da ita ba,don haka na hakura da ita Allah ya bata wanda takeso nagari wanda yafini,sannan maganar yesmin. Baba karku tilasta mata bazamu san meke ranta ba,kar axo ayi abunda zai kawo damuwa inhat yesmin bata da ra,ayina baba don Allah ayi hkr da maganar nan Allah xai bani wata makamanciyar safiyya" Tausayinsa ya kama baba da mama,baban baiso fallasa yarsa ba baiso sanar dashi son da take mai ba,amman ya xama dole kodan ya samu kwarin guiwa,don harga Allag yana son yaron yanason sake hafa xuria da ahalinsu.suna da kirki da daddatako. "Muhseen karka damu inhar akan haka ne,yesmin ta nuna mana kai takeso mafarin kenan uwata tazowa mamansu da maganar daba don haka ba,har ayi bikinku bazamu san bata sonka ba,kuma kaima nai imanin baxata nuna maka ba.amman saboda ta gano yar uwarta tana cikin wani hali akanka yasa ta yanke shawarar sanar damu,kaji dalilin zamanmu dakai.don haka kaje kayi shawara da mamanka ko dan uwanka,duk abunda sukace saikayi aiki dashi." Murmushi muhseen yayi yana tuna wasu abubuwa dasuka faru ranar dayaje gano baba asibiti,da lokacin daya daukosu daga asibitin,sai randa ta biyosa ya kawo mama gida sanda fiyah bata lafiya,hakika tana da hankali da wayau tana sonsa bata bashi wata dama dazai gane ba,saidai zata ringa janshi da labari na ban sha,awa da dariya.bazaka taba ganewa ba,tabbas da matan wannan zamanin ne damarta tafarko data samu sanda ya daukota bayan sun ajiye mama alokacin zata barje kolinta ta gaya mashi,amman tana da kunya da kawaici ta danne saidai aka gane amman badai ita ta furta ba. Murmushin yakeyi yanajin kaso sittin na amuncewa da ita yana saukar mashi,cikin sanyin murya yace"baba na amunce nima ina sonta,duk da haka zan sanar da su halin da ake ciki nasan bazasu ce aa ba,suma ai suna sonada daya daga cikinsu,Allah yasa hakan shiyafi alkairi" Dandanan fuskar baba ta washe hakika yaron yana da hankali Albarka yayi ta samai shida mama,da zaitai ya ajiye masu dubu goma yafice,baba nacewa ya barshi amman bai dawo ba. Fiyah na jinsu duk abunda ya wakana saitaji yabata tausayi,kuma ya burgeta hakika tana taya yar uwarta murnan zamun namiji irin muhseen,Allah ya samashi soyayyarta fiye da wadda yesmin take mashi. Kallonta tai ta dunkule waje guda tana raba ido,dariya ta kwashe da ita tace"to mrs love tashi ankashe maki boss din saiki bani ladata" Boye fuskarta tai tana dariya tace"nidai Adda kibari don Allah bana so" Cikin tsokana tace"ehyy bakiso meye bakiso muhseen din kuma yanzu shine bakiso,innalillahi bari inje insanar da baba to ashe hasashena karyane........Wlh Adda ba haka nake nufi ba kiyi hkr" Rike bakitai tana dariya tana kallonta,saida fada kuma kunya ta kamata ta soke kai tana dariya "Adda don Allah kibari kunya kike bani" "To nabari yar qanwata Allah ya tabbatar da alkairi yakuma kara kauna" Kin ansawa tai da amin din. 💞💞💞💞💞 Umma dai direct gidan mahaukata aka kaita,saboda hauka take tuburan idan kasake kaje inda take saidai akwasheka ayi asibiti dakai,yaranta banda kuka babu abunda sukeyi Abbi kuma ya sakasu daki ya kulle yasa wani soja yayi masu dukan tsiya,har saida xuwairat da haulat suka suma.Amina ce kurin bata suma ba,khadija kuwa Allah yasota bata ciki ta ruga ma wajen mami abunta,xindir haka aka fitar da umma daga gidan don duk kayan da aka saka mata saita yagasu tayima su fatafata,gashi duk tajima jikinta ciwo ta yayyage fatarta,sai ihu take tana tona ma kanra asiri wani abunma babu wanda yasan tayi,sai lokacin akeji ashe tun sanda tasan mami na da cikin Alfah taso atura mata aljanu su sace cikin,kuma su hanata daukar wani amman dayake Allah yace sai Alfah da ni,ima sunzo duniya Allah baibata iko ba. Haka aka kwasheta mutane sai Allah wadarai suke da ita,anan wau sukasan sharri akaima Alfah bai akaita abunda mutane suke zargiba. Alhaji kwangila kuwa yana tsaka da hira cikin iyalinsa don duk yinin ranar kin fita yayi,tsoro yakeji kar shima asirinsa ya tonu akamashi don ya tabbata Alh muazzam bazai kyalesa ba,shiyasa duk atsorace yake dayaji karar get zai zabura yace waye.saiyaga ba yan sanda bane ko sojoji saiya natsu. Ya sadakar kila yatsira wajen karfe takwas na dare kurin saiga sojoji mutun hudu yansanda mutun hudu,babu ma wani dogon bayani sukai sama dashi suka sashi motarsu aka dankara mashi unka,kiraya ke kubarni nayi magana da lawyer na nifa karya akemun wlh sharrine" Tunda wani bajimin soja ya makamai bakin bindiga baisake magana ba,don hakorinsa uku saida suka fito. Ranar momi da su rafeea sunga tashin hankali,jin rade raden cewa ai matar Alh muazzam yake zuwa dadiro wajenta.saboda kidima da tashin hankali saida momin rafeea ta suma,daker ta farfado suka hau kuka kamar Alhajinne ya mutu. Abdoul bai tashi daga office ba sai bayan isha,i don yau yayi ayyuka sosai daya kwana biyu baiba. Sanda yake kokarin tafiya dady ya kirasa awaya,bazai iya tuna ranar da dady ya nemai ba,awaya dai kamar haka komi yake neman sani akanshi zai nemi malik,amman yau dady dakanshi anya ba akwai wani abuba. "Hello ina wuni" Abdoul yafada daga can daddy yace"gobe wajen karfe goma na safe kazo gidana na maitama ina son ganin ka" Wata irin faduwar gaba ce ta sameshi "gidanka na maitama?"ya maimaita dadyn cikin bada umurni yace"eh shi ake nufi hakan ka manta address din na turo maka,kokuma xuwane bazakai ba ka nuna man har yau ba,a isa dakai ba" "Aa daddy ba haka bane kayi hkr zanzo amman awannan time din inada aiki office kodai na sameka office dinka idan narage aiki" Yafada yanason xillewa daga xuwa maitamar don inyaje ciwon dake kirjinsa zai fama. "Karfe goma nace ina son ganinka a maitama idan kuma ya zarta haka nidakai ne" "Afuwa daddy zanzo kayi hrk" Yaja tsaki yakashe wayar sauke tashi yayi yana jan numfashi,mezayyo maitama shifa ko kallon get din ma ayanxu baiso,aduk unguwar bakda wani masoyi bayan mami da ni,ima suma wataran yasan zasu hadu amman ba cikin unguwarba,babansa bai sonsa yan uwansa basa sonsa,yarinyar daya kwallafa rai da samunta tace bata sonsa tome yarage mashi amaitama?jiyai ma zai hada ma kanshi tension yayi saurin kawar da tunaninta yana shiga motarsa yabar company. Wajen masu suyar balango da kaji ya tsaya idan bazai manta ba tana masifar son balango,da fruits sai fresh milk. Murmushi yayi yau inason shiryawa dake dole zan nemi abunda zan faranta maki dashi kiyya. Fitayai yasiyo balangon shikuma ya siyar masu gasassar kaza shida malik,yakara gaba yasai fruits ayaba apple abarba da inibi.yasai fresh milk din Katan guda mai sanyi sannan yadauki hanyar gida. [10/3, 9:09 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️.............54 Suna falo yau da malik suna kallo news,babu laifi yaga canji daga zakiyyar yau amman bai tambayeta dalili ba yasan can tsakaninsu ne. Sanda ya shigo duk suka xuba mashi ido har ya karaso cikin falon,yana xubewa cikin kushin. Ya na furta "washhhh" Malik yace"sannu yallabai,daman nasan za,ai haka katara ayyuka dayawa dole zaka ringa over stres din kanka" "Wlh kuwa,don jinake gobe kamar karnaje nasan kuma hakan kara tara wasu zanyi" Zakiyya na shan lemon fata bata tsoma masu baki ba,idonta nakan news din da,aketa nunawa da hoton Alh kwangila ajiki ankamashi da cin amanar Alh muazzam canji,wanda hakan ya jawo an dauresa gidan yari daurin rai da rai........wani dadi taji yadirar mata koba komi dai asirinsu ya tonu izuwa yanxu tasan Abbi yaji komi ya koma ga Mami,kuma ba jimawa xai nemo dansa tilo kamar rai yanemi afuwarsa,koda Abdoul bai aureta ba wannan nasarar tafi komi dadi wajenta. Daga shi har malik kallon tv suke shi malik daman yasan hakan xata faru,amman Abdoul mamaki ya kasheshi meya hadoshi da Abbi,to kodai ya gano cewar baida laifi abunda duk ya faru? Kallon fuskar malik yayi yaga babu wani mamaki ko wani al,ajabi haka zakiyya saima murmushi da take abunta. "Malik meyafaru acan,nasan kana da masaniya" Kafada yafaga yace"i don't know yadda ka gani nima haka" Murmushi yayi yana mikewa"hakan ma ya sake tabbatar mun kasa komi,uhmm rike saninka Abdoulmalik." Har ya juya yakai bakin hanyar dakinsa ya jiyo yana kalonta yace"kiyya" Kamar bata so haka ta jiyo tabisa da kallo,lumshe mata idonsa yayi da suke cike da gajiya yace"wadancan ledojin kije dasu kitchen,naman asake gasashi fruits asasu frig plss." Lauya kai kurin tayi batace komi ba,shikuma ya shige don watsa ruwa ya kuma sauke sallolin dake kanshi don baiyyi magruba ba. Damuwar duniya tataru xikin xuciyar fiyah,data dauko wayarta saitaga aibata da no dinsa,bala,in son jinsa take wata irin kewarsa take ji wadda bata taba jin irin haka ga wani da namiji ba,idan ta tuna abunda yasa yayi fushi har kwalla take.yesmin ta lura tana cikin damuwa ta tambayeta. "Nikau Adda kamar wani abu yana damunki,don Allah ki gaya mun idan yafi karfina saina yi maki addua,kwanaki na dauka aka yaya muhseen ne to kuma naga maganar ta wuce still bakibar damu ba,kodai na gaya ma mama" "Karkifara kuskuren gaya mata don bata wa zamuyi" Cikin damuwa tace"amman Adda ni kina kokarin fitar dani cikin tawa damuwar taya kikeson zan jure ganin ki ahaka,kigaya mun ko shawara saina baki" "Yesmin idan lokacin sanin yayi zan gaya maki amman kicigaba da man Addua Allah ya zabamun abunda yake alkairi ga rayuwata." "To Adda insha Allah,amman kema ki dage kiyi tayi sannan ki rage saka damuwa bakiga yadda kika rame ba" "Zan rage yesmin karki damu" Tafita don kiran da mama ke mata,kalon wayarta take kamar xata ganshi aciki,wata xuciyar ce ta raya mata kila bazai rasa wannan sabon layin nata ba,don shine yayi mata register kila yayi saving no din.wannan yasata jin wani sanyi har cikin ranta,ta rarumo wayar da sauri amman saita rasa wace no din zata kira,idan tayi nazari xata iya tuno no din daya kirata atsohuwar wayarta amman daker idan daidai zata rubuta,haka ta fara sakawa sa bismillah tana adduar Allah yasa itace. Hannunta har karkarwa yake idonta cike da kwalla,bata san girman soyayyarsa acikin ranta ba amman koma ya take tana masifar azabtar da xuciya da gangar jiki. Kamar wasa taji tana ringing,wata zazzafar ajiyat xuciya taja harda lumshe ido. Yana dakin dayake aikin sa wani dakine na musamman da yake zama yana rage ayukansa akan computer,yana rubuce rubucensa fa takaddu.suna tare da malik ma alokacin yana nashi aikin shima,yace"yallabai wayarka fa tana neman agaji" Girgiza kai yayi yana saka biro ga bakinsa idonsa ga computer yace"bana jin zan iya waya aikina nake" "Idan someone special ne fah" Murmushi yayi yana kallon kofar shigowa don ya saka zakiyya ta hado mashi naman,da madarar daya shigo dasu ta kawoma malik nashi taje ta dauko na Abdoul din.daidai shigowarta yace"gata nan ai kaga kuwa duk wanda zai kira na musanman bayanta yake" Mamaki ya kashe malik baidaice komi amman yasan tabbas akwai abunda ya faru tsakaninsa da safiyya,kuma zaiso yaji koma miye. Jawo table tayi tana dora komi asama fuskarta kadaran kadahan,yana dan murmushi yace"bakiji ba hajiyata" Jiyowa tai tana kallonsa yadaga girarsa yace"eh ban gama dake ba pls sit here" Yana jawo dayar kujerar dake gefensa ya nuna mata,kallon malik tayi asace yayi kamar bai gansu ba,tadan jima kafin ta zauna.malik hakanan yaji abun bai mashi ba,ransa baimai dadi ba amman zaisan mezai. Tashi yayi da tashi system din yana ficewa. Rubda ciki tayi tana kuka mai sosa rai,hakika so masifa ne idan bakai dace da wanda kake son ba,tabbas kalar tata soyayyar idan banda wahala da ciwon xuciya babu abunda take haifarwa............amman tana so tasan dalilin yin fushinsa don kurin tace tana bata sonsa,bata ra,ayin auren kalarsa.duk da kalamanta sunyi tsauri tayine don ta gano ko yanajin makamancin halin da takejin kanta akanshi,ashe kwaba tayi bata sani ba.........hakika dole xai fushi saboda kalamanta amman ai yayi mata uxiri,tana mace ba kimarta bace furta tana son sa,hakan bai dace da ita ba. "Bayan duk abunda yafaru zakiyya na dauki zafi dake sosai,kuma har yau ban daina ganin laifinki ba.may be idan naji hujjarki zuciyata zata iya sassautowa,amman aduk sanda zan kalleki wannan bakar ranar nake tunowa" Hawayenta ta share tana kallonsa kamar xara hadiyesa don tsananin kauna. "Yaya Abdoul ka fahimceni wlh Allah ne shedata banda zabi banda wata mafita daya wuce bin bayan umma da sunan amuncewa,saboda wannan hanyarce kurin zan iya taimaka maka.ta cigaba da bashi labarin duk abunda tai har kawo kan abunda yafaru da ita da zamansu da fiyah komi ta sanar dashi ataiaice,wani malolon tausayinsu ne su biyun wata kaunar yarinyar ta sake dabaibaye xuciyarsa,yasan tabbas kaurace matan dayai tana cikin wani hali,amman shima yana cikin halin da yadace amashi uxiri. "Shikenan kibar kukan komi ya wuce,koma miye nasan gobe zanji abakin dady,nagode maki kiyya kuma kiyi hkr abisa rashin fahimta danai maki,duk wanda ya ga abunda yafaru zaiyyi ma fiye sa abunda nai kiyya,don haka ina maki albishir Abdoul din dakika sani baya he will return okay" Yafada cikin tsokana ta sadda kai tana murmushi,ahakali yake janta da fira suna cin naman suna shan fresh milk din,zakiyya jitake kamar tanayawo agajimare,yau itace da abdoul dinta haka lallai komi yayi farko zaiyyi karshe,amman fargabanta guda har yau yana kan bakarsa ta bangaren fiyah ko aa,tanajin zafi da kunan kishin fiyah yana taso mata,tana zargin Abdoul bazai iya rabuwa da itaba. "Kije ki kwanta dare yayi munyi mgn da safe" Badan tasoba haka tatashi tana waigensa,murmushi yake binta dashi har tafice. Dafe kanshi yayi dake masifar sarawa............abubuwa suna dawo mashi tsanar umma da yaranta tana ninkuwa cikin ransa,inama zai iya daukar doka ga hannunsa,ya rantse da saiya kashe duk mai saka hannu cikin tashin hankalin daya shiga,amman ina bazai iya ba yasan ko yayi yunkurin hakan baza,abarsa ba amman zaiso yaje yaji matakin dasuka dauka muddin bai mashi ba dole xai dauki nashi dakanshi. Ajiye ayyukan yayi yana daukar wayarsa daya samu missed call uku kalon no din yake yana karanta su,yayi saving no din amman baisaka suna ba,bangare duga na xuciyarsa yana jansa ga wani waje,amman yanaga hakan ba mai yuwuwa bane. Fitowa yayi yana wuce bedroom dinsa,shirin kwanciya yayi amman xuciyarsa ta azalzalesa akan kiran no din kodan ya tabbatar ma kanshi da cewar itace ko ba itabace,saida yayi relax agado ya kure Ac sannan yayi dailing number yanaji tana ring amman babu ansa. Kasa hkr yayi ya sake kiran. Lokacin fiyah tasha kukanta ta godema Allah tana cin alwashin muddin bai biyota ba ta yafeshi har gaban abada,koda hakan na nufin sonsa zai kassarata,tana jin wayar na vibration saida ta gama ta duba taga shine,bata bisa ba saida ya sake kira.hannunta yana rawa ta dauka wasu hawayen tausayin kanta suna silalowa,sai kurin ta sa kuka........ Kuyi hkr da wannan ina cikin jimamine wlh nagode da adduoi ku [10/5, 7:03 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........55 Wani abune yakeji tundaga kafarsa har cikin kanshi,ya wuce xuwa xuciyarsa kafin ya watsu cikin gangar jikinsa.runtse idanuwan sa yayi yana jin zafin kukan da kunan sa cikin ransa...........yana daukar duk wani alhakin kukata akanshi,hakika bata cancanci irin wannan ba,don kuwa halaccinta yafi yayi mata abunda xai sakata kuka,kukan ma irin wannan mai ratattake xuciyar mai sauraro.ahankali ta koma yin kukan kasa kasa,lumshe ido yayi yanajin inama inama,inama ace gashi gata take rera mashi wanan kukan wanda lallashin sa ya dace ace ajikinsa zai lallasheta,yana yi yana shafa kanta yana hura mata isaka afuskarta da kunnenta,tabbas ba shiru ba har bacci ma zatai.amman inaaa bazai sameta ba koda yasamu sai idan tana matsayin mallakinsa ne zai iya hakan,huci ya furzar cikin wata kasalallar murya yafara magana,wadda saboda salon maganar da yadda yake furta kalaman dole tasa kukanta yasake yin kasa,don wasu abubuwane masu kama da kibiya suke sukarta babu kakkautawa. "Serfiyyah plzzz stop crying,I'm sorry I'm very sorry.I don't mean to hurt you plzzzzz I beg." Ahankali take shashshekar kukan tana ajiyat xuciya don wadannan kalaman sunyi matukar tasiri acikin xuciyarta,sun wanke kaso hamsin na damuwarta. "It's okay an safiyyah na sorry goge kwallarki ki gaya mun waye ya taba mun ke yanzu aga fushina." Shiru tayi tana yin lamo akan katifarsu mai shegen laushi,tana jan numfashi da ajiyar xuciya.wani irin yanayi ne yake dawainiya da ita,hakika masoya sun sha azabar soyayya haka take ashe. (Nikau nace aa fiyah,kune dai dakuka saka wani abu arai kowa ya kasa furtaw) Shiru tayi mashi bata ce komi ba. "Ohhhhh may god kimun magana mana,menene ya saka ki yimun asarar hawayena,inhar baki fada ba zance ban yafe ba xubar dasu dakikai ba kan ka ida ba." Still bata yi magana ba murmushi yayi yana shafa kanshi,wani dadi yana kamashi at least dai yasan yana da wani matsayi mai girma cikin ranta,kuma yana da tabbacin shine silar kukanta.ashe dai ni jarumine tunda yadda nakejin ta abun bazai kwatantu ba,kukama rahma ne inhar ya samu yayi. Can yajiyo yar muryarta data dishe don kuka wadda yajita har cikin yan cikinsa don masifar dadin da tai mashi,yana imaging yadda bakinta yake furtawar,dan mitsitsi dashi kadan ya hana bai dariya ba sai ya dake yana saurarenta. "Wlh Allah saiya saka mun.....baka da tausayi ko kadan kasan duk yadda xaka cutar dani,ba tun yanzu kake saka idaniyata fitar da kwalla ba,Allah yana kallonka kuma zai saka mun" Ta kare da shagwaba kamar zata sake yin wani kukan,Abdoul mirginawa yayi yana manne wayar ga kafadarsa yana ajiyar heart. "Menai maki kuma safiyyah?atunanina ban miki komi ba,idan abaya nai maki wannan kinyi mun uxiri kema kinsan cikin condition din danake,kuma har yau kin ki bani damar da zan baki hkr abisa abunda nai acan lokacin,sannan ai bana jin nai maki abunda zakiyi kuka safiyya!nine kikai ma abunda zan dade ina kokawa,meyasa ke baki ganin laifinki sai nawa?" Cikeda shagwaba wadda bata san tanayi ba,jitai kurin tanayi don azahirin gaskiya tana cikin wata kauna da ta kasa control din mind dinta. "To ni menai maka ehy,ka wai nidai nasan ban maka komi ba ko." Murmushi mai hade da dariya yayi yace"naji toni me nai maki zaki tusani gaba da kukan shagwaba,ina mijin naki I think naji baba yace kin tsayar da wanda zaki aura meyasa saini zaki ma kuka" Hararar wayar tai tace"ai bashi yayi mun ba kaine" Shiru yayi yana jinjina rigimarta,shida ta gasa ma maganganu masu zafi baice haka ba sai ita mai raki. "Shikenan naji na dauka ayi mun hkr to" "Uhn uhm ni banyi ba" "To mezanyi ki huce?" Numfashi taja tanajin inama zata ganshi,inama zaizo baba ya barta tafita tana dokin sauraren jin ta bakinsa,tana son jin dagaske abunda takeji akanshi shima haka,idan hakane meya zai hana su mallaki juna..........wata xuciya tace xakiyya!runtse ido tai tanajin zafin sunan da xuciyarta ta anbata mata,har saida ta furta innalillahi. "Menene kuma" Ya fada. Numfashi taja tace "ba komi" "Ko kina son ganina ne inzo" Kamar tace eh amman saita daure tace"baba ya hana" "Baba ya hana kokuma kema kin hana kanki ganina wanene yafi karfi" Tabbas kila yanzu baba ya barshi ya ringa ganinta,tunda babu maganar muhseen amman bata tunanin hakan,don tasan baba yana hangen wani abun na daban. "Aa ba haka bane,kawai dai tunda ya hana mu hkr mana" "Zaki iya hakura dani safiyyah?" Kirjinta saida ya ansa,tabbas bazata iya ba koda ta iya tokau ba cikin dadin rai da kwanciyar hankali ba,cikin kwana hudu ma ta jigata inaga rabuwa ta har abada,bazata iya cewa komi akan haka ba,karta sake kwafsawa irin rannan. "Nima ban Sani ba" "Kin sani baza dai kifada mun ba,acikin kwanakin da mukai bamu hadu ba bamuyi waya ba,wane irin abu kika yanke akan hakan,still kinajin zaki cigaba da kulani ko zaki yadda ni ki kama mijinki" "Ban gane ba?nifa banda miji wanda baban ma yace yabadani din yesmin na barma wa,shima baidace dani ba" "Okay sai waye yadace dake" "Oho" Murmushi yayi yace"ni mekika daukan" "Yaya Abdoul inada exam gobe banma yi karatun kirkiba zan kwanta saida safe" Da yaushe kike fitowa. "Around 4:30 mun fito wani abune?" "Aa daman don na daukoki" "Bana so fa,baba zai ganmu" "To menene badai kin barwa yesmin wancen guy din ba,nikuma ba saina na shigo ba" "Kashigo kuma?kayi me" Dariya yayi yace"ince ma baban ni abani inyi manage" "Kuttt dani din?nizakai manage dani,to banso nikuma aiba neman kai yake dani ba baban,akwai maza cike da gari zan samu wanda nake so" "Ni bakisona kenan" "Kamar yadda kaima ba sona kake ba,zaka auran don ka maidani kurin borar ka,kuma ma kanada zakiyya me zakai da local irina" Shi wlh sai yanzu ma ya tuna da wata zakiyya,gaskiya yana cikin case ina zaya da mata har biyu.baida wannan tsarin yana son only one wife da zata haifa mashi yaransa masu tarbiyya,ina zai iya tara mata biyu. "Ina ruwanki da zakiyya ne wai,ko kishinta kike" Tsaki taja cike da jin haushi tace"Menene kishi?Allah ya kyauta to kishi basai ana son mutun ba" "Ya tabbata ba kisona ngd safiyya,ba komi tunda zakiyya na sona kuma ashirye take data aureni kinga no need na bata ma kaina lokaci,shikenan saida safen." Dandanan tabi ta rikice "yaya Abdoul........shiru yayi ya kyaleta kuma bai kashe wayar ba. "Kaji wai fushi kayi,yaya Abdoul magana fa nake maka,kayi shiru." Muryarta harta fara rawa sarkin kuka kurin. Ya furta "Badai kin barwa zakiyya ni ba,baki sona saboda baki iya auren kalata,dan giya mai neman mata ko?haka kike kallona har yau shiyasa kike cemun bazaki iya auren irina ba. Baiyi mamaki dayaji muryarta dakuka ba tana cewa"ni wallahi ba haka ba,nibana maka wanan kallon wlh na manta ma kataba shan wata giya,miye haka wai sai ta sake rushewa da kukan. Dadi ya kamshi yace"it's oky,yi shiru na bari ba haka kike kallona ba to meyasa rannan kika gaya mun haka" Cikin kuka tace"to ai ba laifina bane,kaine kakesani abunda banyi niyya ba" "shikenan ya isa yanzu zan iya sake dawowa karo na biyu na nemi iznin baba ya bani ke" "Baba fa zaiyi mun fada" "Bazan Bari yayi maki fada ba,kinji an safiyya na" Lumshe ido tai tanajin wani irin farin ciki,amman har yanxu bataji abunda take son ji daga gare shi ba,shiyasa tace"uhn bacin ba sona kake ba taya xai baka yarsa kaje kayita dukanta" Xaro ido yayi kamar tana ganinsa yace"rufaman asiri na dakeki,wlh bazan iya kai hannuna da sunan duka ajikin ki ba kiyarda dani,dacan ma kuskurene amman zan gyara oky" Shiru tayi tana sauraren numfashinsa. "Safiyyah" Can kasan makoshi yankirata,saida duk wata kofar gashi ta jikinta tatashi,daker ta ansa. "Na,am" "Safiyyah" Lumshe ido ta sakeyi tace "na,am inata fa ansawa." Ajiyar xuciya yaja sosai ya sake sauke muryar kasa. yace" *Did you marrie me?*" Dammmm taji kirjinta ya buga gabanta ya cigaba da faduwa,wannan kalmace mai nauyi bazata iya ansa mashi ba bacin bata san matsayinta acikin ransa ba,baya ga haka ga zakiyya bazata iya zaman kishi da ita ba,duk da tsabar kaunarsa da take ji ta gama kewaye mata ko ina. Numfashi take ja ahankali tama rasa me zatace mashi. "Safiyyah are. you hair me" Daker tace"uhm inaji" "Bakice komi ba" "Yaya Abdoul ba fa ka sona,ina kataba ganin anyi aure babu so tsakanin ma,aurata" Numfashi yaja yanajin wani sabon yanayi akanta,wata irin kaunarta yakeji tana bin ko ina na jikinsa. "Wannan ne kurin damuwarki?" Can kasa tace"uhm" "Goben kijirayeni cikin school dinku,plss kiyi zamanki bakin department zanzo harnan nima alokacin sainaji result dina,hakan ya maki" Jikinta yayi sanyi sosai tabbas tana sonji daga gareshi,amman kuma tana jin bakuncin kalmar tun kafin tajita akunnuwanta. "Eh" "Okay good night and sleep well ban yarje maki tunanina ba har sai bacci ya daukeki" Shagwabewa tai. "Yaya Abdoul taya zan iya hana xuciyata tunani" Lumshe ido yayi muryarsa tai sanyi yace"shikenan kiyi ammab kadan kinjiko kiyi addua sosai da asuba saikiyi tilawar karatun saiya fi zama" "Okay by" Ta kashe wayar tana mulmulawa can karshe gadon tanajin duk wata damuwarta ta yaye,yanzu tsakaninta da babane kurin case dinta shin zai anshi abdoul ko zaice baimashi ba.wannan shine fargabanta sannan ya matsayin zakiyya yake ahalin yanxu wajen Abdoul,zata so ace tasan wane hukunci ya yanke tsakaninsu. ************ Karfe bakwai yabar gida ko malik ma bai gaya ma inda zashi ba,duk da yaga sai wani sha mashi mur yake baisan dalili ba. Office ya tsaya ya fara rage ma kanshi wasu abubuwan don idan ya tafi wasu bazai yisu yau ba. Ahaka har karfe goma ta buga ya tashi ya fito yabar sakon duk wanda yazo ace baya nan,ya kirasa awaya. Maitama yayi kwana da motarsa ya nufa maganganun zakiyya suna sake dawo mashi dalla dalla,yana jin zafi da kunan abun duk yadda yake son daukar hukunci da hannunsa yasan hanashi za,ai amman tabbas idan yaga umma babu abunda xai hana bai kwalwa mafa maruka guda biyu da zasu fiddata daga cikin hayyacinta. Sukuwa su zuwairat da Haulat da Ameena wata tsanarsu yakeji,jiyake inama zai ciresu daga jikinsu ace su ba yayan Abi bane,aman yasan kome sukai kome suka xama dole za,a kirasu da yaran Abbin. Ya na shigawo yaga baban fiyah zai fita yayi saurin tsayawa yafito yana durkusawa kadan yace"baba ina kwana" Baban bai nuna komi ba ya ansa cikin fara,a yace"anzo wajen Alh ko" "Yace aa dama dadyne yake nemana ba wajensa zanje ba" "Shidinma ya dace ka mance dakomi Nasser kaje kuyafi juna,komi yana da dalili haka kuma kaddarar mutum bai isa ya kauce mata ba,aduk sadda kaji ranka da xuciyarka suna raya maka wani abu marar kyau kayi saurin korar shaidan ka kuma yi auziyya kana hazbunallahu wani imal wakil,Allah ya daidaita lamauran kaje Allah ya maka Albarka" Cikeda jin dadi Abdoul yce"na gode baba insha Allah zanyi yadda kace nagode sosai Allah ya kara girma" Ya fiddo kudi aljihu baisan konawa bane yace"baba ka hau taxi don girman Allah karkace bazaka ansa ba,wlh badan komi nai ba alherine nayi maka badan baka dasu ba" Murmushi yayi baban yace"don nayi maka nasiha nasser saika biya ni,kaga bani hanya ina sauri" "Don girman Allah baba nima dankane inda hakkin baka abu ka ansa,don Allah baba ka ansa" "Shikenan nagode Allah yayi Albarka" Ahaka suka rabu ya wuce gidan dady yana satar kallon gidansu fiyah,har ya kasa hkr ya kirata lokacin ma tanata shirin fita don shadaya suke shiga. "Gani kofar gida nazo nakaiki makarantar" Xaro ido tai har yesmin na kallonta. "Innalillahi kayiwa girman lillahi katai babu ruwana wlh idan baba ya ganka" Dariya yayi yana bala,in son yaga ta tsorara kyautake. "Mataoraciya to ai har baban ma mun gaisa dashi yanzu" "Jana kake yanxun haka ma kana kan gado" Wata dariyar yayi yace"I'm serious ki leko inanan unguwar dady nazo wajensa yana nemana" Ajiyar xuciya taja tace"bakaji wlh har naji gabana ya fadi,ina shiryawa sai anjima" Ta latse wayar don idan ta biye mashi ba lallai ta gama kan lokaci ba. Abdoul gaban dady ga kuma Abbi shima ga mami ga matar dady Umma salamatu............... Kuyi hkr don Allah nasan kuna hkr dani,ku kara kan wanda kuke ina ganin comment dinku kowa da nashi ra,ayin saidai zan baku hkr bisa ga wani abu guda.akoda yaushe marubuciya duk sanda xata dora alkalaminta don isar da wasu sakonni ga mutane,on ready ta riga ta tsara ga yadda lamuran da zasu faru,komi da kuke gani ahaka yataho,kuyi hkr idan kunga sabanin ra,ayinku haka labarin ya ke. [10/9, 5:48 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️..........56 Tunda ya gama sauraren duk wadannan evidence din da zakiyya tayi sanarar dauka idonsa kamar anzuba attarugu aciki,jijiyar kansa ta fito sosai kallo daya zakai mashi kasan cewa xuciyar ta motsa. Mikewa yayi atsananin fusace zai fita dady yayi saurin rikosa yace. "Ina zaka?" Yana huci duk jikinsa rawa yake soyake kurin ya ganshi gaban umma da yaranta yayi masu dukan da zasu kasa sanin wace duniya suke. "Zanje gidan ne" Jawosa yayi ya zaunar kusa dashi yace"duk hukuncin da zaka dauka baikai wanda ubangiji ya daukar maka akanta ba,domin mariya yanzu haka tana gidan mahaukata na nan garin,hauka tuburan take wanda ko kayan jikinta bata barinsu saita fatattatakasu,tsirara take zama kaga kuwa kai bazaka iya yimata haka ba.yanzu haka ma ana shirin kaita gidan mahaukatan dake legos don tana niyar fin karfinsu anan.don haka ka godema Allah daya bayyana komi,sanan ka godema safiyya da yarinyar nan zakiyya.sun sadaukar da komin su dominka,wannan ya zama izna gareka da duk mai hankali.sannan ga mahaifinka nan kaje ka nemi yafiyarsa kuyafi juna komi ya wuce Allah ya kyauta gaba." Kuka Abdoul keyi kamar yaro karami kasa motsawa yayi saidai Abbin da kanshi yazo ya rungumeshi yana kukan shima,wata irin kewar juna ce da tsananin kaunar juna ta kamasu.........bayan tsawon shekaru sai yau Allah yayi zasu sake ganawa,sai yau Allah ya bayyana sirrin daya boye sunsha kuka sosai suna rungume dajuna ni,ima da mami ma hawayen suke. Daddy da umma salamatu banda hkr da nasiha babu abunda suke masu,hakika idan kagansu saika tausaya masu don kowa yayi kewar dan uwansa Abbi jiyake kamar ya bude kirjinsa ya saka Abdoul dinsa aciki. Kira yake"kayafe mun yarona yafemun kaddararmuce tazo ahaka,babu wani tsumi ko dubara dole hakan zata faru,nayi kewarka har bansan adadi ba,nayi kukan rashinka har idona ya kafe da hawaye.............idan kanajin kalaman Abbi kai kanka saika zubar da kwallah,Abdoul yana shashshekar kuka yace"Abbi nima ka yafemun,xuciyata awancen lokacin ta gaza yardarmun cewar kana kaunata,xuciyata ta gayaman dama neman hanyar rabuwa dani kake,tunda har alakafa mun mummunan sharri irin wannan ka yarda tabbas kadaina sona,na yi iya yadda zanyi na koyama kaina tsanarka don ko sunanka bana son malik ya anbata mun,nayi rayuwa irinta dabbobi nayi abubuwa da basu dace dani ba,naso mutuwa lokuta dadama.nida kaina nake neman ta ninake kai kaina inda za,a bankeni.idan nai makaina rauni bana yarda naje asibiti don su dubani,malik yasha wuyata nayi masa abunda idan da wani dan uwana ne bazai iya zaman da malik yayi dani ba,Abbi nayi rayuwa cike da wahala kullum cikin kunci da bakar xuciya nake.xuwan safiyya rayuwata shine ya fara canzani,tasha wuyata ba yar karama ba idan na kamata kamar kato haka zan daketa,bana jin ko digon tausayinta.saboda lokacin babu wadda na tsana alokacin irin mace,bana kaunar ganinta idan har ta kusanto inda nake jinake tsaf zan kasheta..........nasha giya har babu adadi,kayan maye babu kalar wadanda ban sha ba,kafin malik da safiyya suyi nasara akaina.Abbi yanzu haka ina da illar da giya taimun,tayimun illar da bana tunanin zan warke,tamun tabo acikina wanda bazan iya shan ruwan zafi ba,haka bazan iya shan na sanyi ba.inko har nasha to gani can raina ahannun Allah.........rufe mashi baki Abbi yayi yana kwalla "Ya isa haka ya isa Abdoul hakika na zama uba marar anfani,amman kayi hkr ba laifina bane mariya ta cuceni Allah ya isa tsakanina da ita ..........ka gaya mun duk abunda kake Abdoul komiye zan yimaka shi inhar bai take sharia ba,zan dawo maka uba fiye da wancen lokacin" Ajiyar xuciya Abdoul yake yana kallon mahaifin nashi yace"Abbi safiyya nakeso,inason kaida dady kuje ga babansu kurukarmun shi ya bani aurenta,inasonta inajinta kamar raina idan ban sameta ni kaina bansan halin da zan shiga ba." "Inhar don wannan ne insha Allah nida dadyn ka zamuyi iyakar kokarinmu muga mun samomaka ita,nima zanyi alfahari da ita matsayin sirikata.zan iya yinkomi don farin cikinka wanda bai take sharia ba,don haka Malam kabir ko cewa yayi na kwanta ya takani zanyi,don kuwa nasan nayi mashi abunda zai bukaci hakan" Daddy ne yace"bama zai ce ba saidai wani abun na daban,to ita zakiyya fa Abdoul,kasan da cewar har gobe kai take so" Sadda kai yayi yace"dady na sani amman tayi hkr bazan iya zabarta akan safiyya ba,zanmata addua Allah yabata wanda yafini".............ko bai bata wanda ya fika ba zaibata wani wanda xai jibanci lamurranta,wanda zai share mata kukanta wanda zai taushi xuciyarta akan rashinka datai,ni zan aureta inhar taba dama " Daga bayansu sukaji wannan maganar,baki dayan su suka juya suna bin kofar shigowa da kallo,malik ne tsaye da zakiyya wadda idonta tuni ya gama lalacewa da kuka,da alamu taji abunda Abdoul ya fada. Daddy ne yace"malik dagaske kake" Riko hannun zakiyya yayi yajawora har cikin falon ya zaunar da ita gaban mami yace"dagaske nake Dady domin zakiyya mutuniyar kirkice,kuma inhar na sameta nasan nayi mata,saidai idan itace tace batayi dani" Zakiyya jikin mami ta fada tana idasa kukanta Abbi yace"malik Allah yayi maka Albarka Allah yabaka abunda kake nema duniya da lahira,hakika kayi mana komi ka zama fitila agaremu Allah ya saka maka da mafifcin Alkairinsa." Yana murmushi yace "Ameen Abbi nagode,maganar zakiyya fa anbani?" Yafada yana sosa kai yana kallonta tana kuka jikin mami, Duk saida suka mashi dariya Abdoul dai mamakin malik din yake,daman yana sonta kokuwa yanzu dayaji cewar ya fasa zaimaye gurbinsa aranta. Mami tace"kubar mun diyata ta huce tukun,kubamu lokaci zakuji daga garemu kuma kai ta nuna Abdoul saika bayarda toshiyar baki,tunda kakimu don gidanki" Sadda kai yayi yana murmushi,kunyar zakiyyar ma yakeji sosai amman ya ya iya da azalzalar da soyayyar fiyah kemashi.zai samu time ya lallasheta yasan zata huce. Abbi ya shafa kanshi yace"yanzu ina zaka son" Cikin wata irin kauna Abbin ya fadi shima ya shagwabe yana kwantawa jikin Abbin yace"office zanje in idaza ayyuka" "Okay yaushe zaka dawo gida to" Kalon malik yayi yana mashi alamar tambaya yaushe zai dawo. Dari ya umma salamatu da dady sukai mashi shima malik din yana tayasu yace"ka tmbayeni yallabai" "Shikenan xuwa dare daka tashi nan nakeson na ganka gida kajiko,kafinma ka dawo ankwaso maku kayanku tass za,a ajiye maku ana.amman abubuwan anfani kurim za,a dauko.kayan cikin gidan da gidan kanshi zanyi kyauta dashi.oky" Jinjina kai Abdoul yayi yace"duk yadda kayi Abbi daidai ne," "Allah yayi maku albarka,kaje karka bata lokaci idan kadawo zamu sake tattaunawa." Kowa kallonsu yake cikin jin dadi don ba tun yanzu wannan kaunar take ba,Allah ne dai ya kaddara sai haka tafaru. Rungume Abbin yayi yana mashi kiss ga kunci yaje ya rungumi dady yana murmushi"nagode dady,thank you very much kayi kokari" Wajen mami yaje itama ya rungumesu tare da ni,ima yana jin kewarsu sosai kallon zakiyya yayi wadda ta kauda kai bata son ganinsa. Itama kissing goshinta yayi yace"thank you for everything kiyi hkr zamuyi magaa daga baya" Tunkudeshi tai malik yana cewa"malam ya haka zaka wani shigema matata agabana,dalla wuce" Tashi yayi guiwarsa tai sanyi yana masu saiya dawo. *********** Yesmin ce keta kokarin hada sanwar dare sun hira da mama tana aikinta. Shinkafa da miya zatai mamar ke yanka mata salad ita kuma tana soya miya don har ta kwashe shinkafar,dalhane yayi sallama. "Aaha dalha ka dawo kenan" Cewar mama "eh na dawi ko shagon ma ban budeba saiga muhsen yatsaya,yace in turo mashi yesmin." Rudewar datai jin ance muhseen yana kiranta yasa ta yadda ludayin juya miyar tana zare ido,nashiga ukuna dawane idon zan kallai.daman kullum xullumin haduwarsu take. "Yesmin miye haka?" Muryarta tana rawa tace"ba komi mama faduwa yayi" Murmushi dalha yayi yace"ya za,ace mashi mama" Itama murmushin tai tace"kace tana xuwa yanxu" Ya fita don sanar dashi Mamar tashiga kitchen din ta ganta durkushe ta buga tagumi. "Tashi like ki gyara jikinki ki fita yana jiranki" Idonta yayi kwal kwal zatai kuka. "Mama nidai don Allah" "Banson shirme cinyeki zai ne kokuwa bakonki ne yau kuma,tashi karki bata mun rai." Haka ta fito ta wuce daki kaya ta canza duk da basu jima jikinta ba,amma akwai kaurin girki. Hijab tasaka kalar kayan data saka,ta fesa turare ta kalli kanta ga mirrow murmushi tai tana jin kunyar haduwar su,bata san dawane idon zata kallai ba. Muryar mama tajiyo tana cewa"halan sai yayi tsiru a kofar gidan sannan zaki fita." Dariya tai jin abunda mamar tace saida ta ga komi lafiya lau sannan ta fita. Mama na mata dariya kunya kamar ta nitsar da yesmin. Yana cikin motar amman kofar gefensa abude take yasha gayunsa don daman muhseen badai iya gayu ba. Hangota yayi yadda take ta sunkuyar da kai,murmushi yayi lallai yana da aiki waccen kunyar kwarar sa zatai,yana son ta saki jiki yadda zasu saba shima har yafara jin kaunar tata. Bude kofar wajen mai zaman banza yayi yana cewa"bismillah princess" Kasa ansawa tai yabar kofar bude tadan zauna adosane. Cikin natsuwa tace"yaya muhseen ina wuni" Kallonta yake sai kauda kai take. "Bazan ansa ba gaskiya tunda ma ko kallona baza xa ai ba yafada cikin muryar shagwaba kamar yaro. Kasa kasa tai dariya kafin tace"kayi hkr yaya muhseen kunya nakeji" "Yau kuma akejin kunyar tawa,to menayi har akejin kunyata" Kasa ansawa tai tana wasa da yatsunta. "Shikenan tunda bazaki fada ba,ya kike to yasu mama da baba" Ahankali cikin natsuwa take anashi,har lokacin ta kasa kallonsa. "Yesmin" Yakirata cikin lumana don yana son ta bashi hankalinta. "Na,am" "Kallona nakeson kiyi" Ahankali ta kalleshi ta sunkuyar dakai murmushi yayi yace"nasan kinsan komi daya faruko?" Daga kai tayi"ba daga kai ba kimun magana nafison inajin muryarki" Ahankali tace"eh yaya muhseen nasani" "Yawwa fatan zaki ansheni hannu biyu kuma zaki bani dama na baje kolin tawa baiwar ta soyayya,bazan so kin dari dari dani ba, ban kuma ce kibar jin kunya ta ba aa kunya abune mai kyau ga diya mace,amman ki daukar kamar yaya jalal ki saki jiki kina mun fira kamar sanda muke abaya,zanso ace munyi rayuwa mai kyau da fahimtar juna.har mukai ga inda muke fata oky" "Insha Allah Zan kokarta" "Yawwa kokefa princess yau ranar gabatar da kai ce ba dogon surutu don haka anshi wannan" Ya miko mata wata keda fashion harda dai kwalin waya aciki. "Banson jin aa anshi kurin tunda dai na kusan zama miji ko ba haka ba" Murmushi tai ta ansa cikin ladabi. "Nagode yaya muhseen Allah ya kara budi" Yaji dadin adduarta yace"thank you so much princess,kije gida magaruba ta gabato kisata caji anjima zamufara zance" Dariya tai tana fitowa tace"ka gaida hajiya da jawaheer" "Aikuwa kamar kinfada akunen su" Sallama sukai ta shiga gida tana sauke ajiyar xuciya. *********** Fiya basu fito exam ba sai karfe hudu da rabi agajiye suke feea daman ga rashin dadynta daka ganta kasan tana cikin damuwa matsananciya.duk ta rame ta zama so silent. Fiyah ta lura da canjin yanayin kawar tata bayan sun fito suna zaune bakin block dinsu tace mata. "Nikau feea mekedamun ki kinga wai yadda kika rame kamar wada ake dibar naman jikinta ana miya" Yake tai idonta yana taruwa da kwalla tace"fiyah duk abun nan bakisan me yafaru damu ba" Kallon mamaki take mata "ban gane ba,har wani abune yafaru daku wanda ban sani ba" Kwallarta ta silalo tana gogewa tace"yau kwanan dady biyar kenan yana prison,fiyah dady baimana adalci ba dady ya cutar damu.ban tabaji tsanar ubana ba fiyah irin cikin yan kwanakin nan" Tausayinta ya kama fiyah cike da damuwa ta rungumota cikin lallashi tace"innalilahi wa inna ilaihir raju,un.feea banji maku dadi ba dole zaki rame dole xaki shiga cikin halin damuwa,amman kidaina tsanarsa koma me dady yayi dai har gobe yana matsayin mahaifinki,don haka addua ce zaku ringa binsa da ita,kuna mashi fatan alkairi.hakika abun bai dadi ba amman ance hannunka baya rubewa ka yanke kayar,don haka kidanne xuciyarki harma kiringa tausar momi kuna binsa da addua har Allah ya kawo maku mafita." Kuka take ajikin fiyah tace"fiyah hajiya mariya matar Alh muazzam fa...........karki fada kibar shi matsayin sirrinku feea,kuyi mashi addua kuma ku saka hkr da juriya Allah zai dafa maku." Lallashinta fiyah tatayi tana sake kwantar mata da hankali har tasamu ta natsu,drivern ta yazo tace"bazaki bini mutai gida ba" "Aa kije ina jiran wanine" Haka tatai xuciyarta babu dadi. Wayarta ta kalla taga tana haske dayake silent ta sata no dinsa ce,don ta riga tayi mata hadar da ko cikin bacci aka tambayeta zata karanto tsaf. Tambayarta inda department din nasu yake yayi ta gaya mai ta sauke wayar tana bin cikin makarantar da kallo,duk yawanci antafi sai wadanda ke hostel ne keta shige da ficensu. Mota ta hango wadda bata tabagani sa da ita ba,land rover ce fara fat,duk wadanda ke wajen tsura mata ido sukai,suna jiran wanda zai fito.kamar yasan haka yaki fitowa ya kirata. "Inafa kallonki hajiya kitaso" Hararar motar tai "kafi karfin kai kabiyoni ko,to bazan taso ba inbazaka fito ba wlh tafiyata zan" "Basai kin gama rantsewa ba aike gimbiyace duk abunda kikace yi ake" Yafada yana murmushi mai tsananin kyau. Budo motar yayi yafito...........huking fiyah tai daga inda take zaune wata dankareriyar shaddace jikinsa tana maiko da walkiya black ce anyi masa dinkin harf jamfa hannun mai links akai mashi,hukarsa black haka takalman shi.kunsan farin mutun bakaken kaya suna masifar ansarshi,duk matan dake wajen tsayawa sukai suna kallonshi sake dabaki daga inda yake zuwa inda take da nisa amman ba sosai ba,tuni kamshinsa mayatacce ya gama karade hancinta. Lumshe ido tai tana budewa wasu yan mata ne taga suna dosar inda yake. Dan danan hankalinta yayi masifar tashi nadamar cewa yafito ta sameta,mema yasa tace yafito. Hoto taga sunyi dashi sun wuce suna daga mashi hannu.........wani kududu yazo mata wuya kamar ta fasa ihu. Tashi tai tun kafin ya karaso ta nufi hanyar barin wajen,ganin zata wuceshi din yaga fuskar murtik yayi saurin riko hijab dinta. Yana murmushi"ya haka madam,nafito ban saba umurnin ki ba kuma zaki barni anan" Kamar zata rushe da kuka tace"to yanzu kuma nace ka koma motar" Kunshe dariyar sa kurin yake yace"angama gimbiya yar sarki" Harara ta danna mai "ni ba yar sarki bace yar malam kabir ce" Bude mata gaban yayi yace"yar sarkin kenan irinku ai sai mai sa,a" tashiga tana kubure kubure. "Zamu iya tafiya rankishidade" Tsaki taja tana jin bakin cikin hoton da suka dauka dashi wadannan yan matan. Cike da masifa tace"idan bazaka tada motar ba wlh zan fita,saikake ka dauki wadamcen shashashun marasa aji dake daukar hoto dakai" Baisan sadda dariyar tashi ta fito ba,babu shiri yayita kyalkyaka abunsa.sototo tai tana kallonsa bata taba ganinsa cikin irin wana farin cikin ba,duk dariyarsa iyakarta murmushi da sauti amman ba irin wannan ba mai kyalkyalawar haka. Sai ta koma tana kallonsa yayi mata kyau sosai,har sada ya bar dariyar yana murmushi ya tada motar yajata ahankali. "I'm sorry ina maki dariya,kedince kika tunxira dole nayi miye don sunyi hoto dani,kema inkinaso basai muyi ba" Banza taimashi har suka fita daga makarantar.ahankali kamshin motar daya hade da turarensa ya saka mata wata irin natsuwa,taji duk haushin da takeji ya fice sanyin Ac yana shigarta wani yanayi yana bakuntarta,kallota yayi cikin canza murya kamar bashi ba yace"ina zamu" Ta na jinsa ta rufe idonta ita batasan ma mezata ce ba.bata son wannan sabon yanayin ya gushe shiyasa ma batace komi ba. Kida ne yajefita amotar batare da waka ba,sautin kidan mai ratsa uciya da ruhi,dan danan fiyah ta gigice da wata irin soyayya wacce bata san tanajinta ba sai yau. Bai sake cemata komi ba yana kura da yanayinta wanda shima kanshi yana jin irin hakan,wani wajen shakawa ne ya kaisu wanda fiyah bata taba ganinsa ba,amman bata son fita amotar. Shima kuma hakan yakeji shiyasa saiyayi parking kurin yana jingina bayansa da makarin kujerar yana sauke ajiyar xuciya ahankali. Ba Wanda yace komi tsayin mintyna uku,har yagaji da shirun ya bude wata loka gabansa ya ciro wani hadedden xoben xinari,dan siririne mai design maikyau sai kyalli yake jirkitowa yayi yana fuskantar ta,ahankali ta bude idonta ta xuba cikin nashi wadanda suka canza kala suka dawo lovers color,kasa dauke idanunsu sukai su kansu basu san cewar suna ma junan su wani irin kallo ba,fiyah komawa tai kamar wata duluwa.ahankali ya jawo hannunta dake cikin hijab dinta yana kallonsa,kamar zai hadiyesa ya rike yatsarta guda ta wadda ake cema ring pinger na kusada na tsakiya,cikin salo da nuna kauna yake saka mata zobe cikin yatsarta,kallon yadda take saka xoben take tana bin yatsarta da kallo yadda tayi masifar yin kyau. Yana gama sawa ya dago suka hada ido bata sanma ta lumshe su ba,ahankali ya kai hannun bakinsa cikin shauki yayi kissing hannun wanda yasa babu shiri ta bude ido tana kallonsa,girarsa ya daga mata fuskarshi na fidda wani annuri yace cikin wata swet voice di sa data sake rikita fiyah. *"I LOVE U FIYHA,I REALLY LOVE U. I LOVE U FOR REVER AND EVER,PLSSS MY LOVE DID U MARRIED ME?"* ahankali take anshe hanunta tana dunkukewa waje guda ibanda wasu abubuwa dake narke mata ga jiki babu abunda takeji,numfashinta yana sizen tunda take jin son Abdul da kaunarsa bata taba zaton sunkai haka ba,yau abun datakeji na dabanne shin mezata iyayi ita safiyya,zata ansa mashi bayan bata san ra,ayin mahaifanta ba kokiwa zatai rejecting har sai sadda baba ya amunce dashi. *tau fiyah dai na neman shawara* Don Allah kuyi hkr dani i sha Allah munkusan gamawa.ina alfahari daku. Fatan na wanke xukantan ku yau ina jiran comments😂😂 [10/10, 5:56 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........57 Jikinta gaba daya jitake kamar acikin frig aka fuddota,ta kasa kallon idonsa ta kasa motsawa daga cikin kujerar da take,hakika ta jima tana tsumayin kalaman nan tayi mafarkinsu har babu adadi,tabbas taji farin ciki taji dadi marar misaltuwa,amman ya zatai anya ansar soyayyarsa lokaci guda yadace da ita,anya bazatai kuskuren sadaukarwa da wuri ba?idan baba yazo yace bai yarda ba fa,bacin ta xurfafa kaunarta akansa hakan zaiyyi matukar tabata,zai girgiza xuciyarta don hakika Abdoul shine farincikin ta shine burin xuciya da ruhinta,tunda ta fara tunanin kasancewa matsayin mata awajen wani namiji dashi take hango rayuwarta,bazata iya daukar kalmar rabuwa daga bakin mahaifinta ba,babu tantama xuciyarta zata iya bugawa don ita kanta tana shakkar wannan ranar..............."safiyyah" Taji muryarsa mai dauke da wasu alburusan shauki suna shigarta ta ko ina,daker ta iya dago kyawawan idanunta ta zubemasa su ga fuskarsa,lumshe mata ido yayi ya bude yana kallonta shima.cike da shauki da kauna daker ma kalaman suka fito. "I need to say something plz" Ajiye idonta tai tana sauke wata sassanyar ajiyar xuciya cikin muryarta silent ta fara magana wadda dan danan yaji ta hade mai tashoshi daker yake control din kansa yana saurarenta. "Yaya Abdoul na gode da kaunarka gareni,domin banyi tsammanin zaka iya sona ba.duba da cewar nidin ba yar kowa bace face yar talaka bawan Allah mai neman rufin asirinsa akoda yaushe,sai kazo kaban mamaki tabbas nayi farin ciki dajin kalamanka wanda da zan iya fiddo xuciyata ka gani da kasha mamaki,Amman inason ka fahimceni yaya Abdoul inajin tsoro inajin tsananin tsoron abunda zai biyo baya,babana kaifi daya ne idan yace aa to mawuyacin abune yadawo yace eh,hakika kanada wani matsayi mafi girma acikin xuciyata,kayi nasarar cinye duk wani fili dake cikinta.kuma nima zan so ace na kasance...........shiru tai saboda kunyar furta kalmar dake bakinta. Matsowa yayi sosai cike da kauna yana rage muryarsa kamar baison wani yaji yace"plzzzz ki fada inason naji,karki boye mun raina yabiya dasonjin me zaki fada plz love" Kallon kasan ido take mashi kafin ya ganta ya daga mata girarsa guda,make kafadarta tayi cikin shagwaba tace"uhm uhm ba yanxu ba" "Sai yaushe" "Sai naje gida idan munyi waya" "Shikenan nasan dai kinsan muhimmancin alkawari don haka basai na tuna maki ba,cigaba da maganarki ina saurarenki" Numfashi taja tace"yaya Abdoul babana daban ne,inajin tsoron idan kaje mashi da maganata yace maka bai yarda ba kayi hkr,wannan kalaman sune suke tsorata ni" Ta tsayar da idonta akanshi. Shima kallon nata yake cikin low voice dinsa yace"meyasa kikekin tsoro" Sadda kai tai cikin jin nauyin abunda zata fada. *"Yaya Nasser banson in rasaka shiyasa"* Cike da jin dadi yace"a u sure love?dagaske don Allah sake fada naji" Dariya ta boye tanayi shima yana tayata kafin ya lauya murya kamar da yaro yace"bacin ma banji kince mun u love me ba" Dariyar ta sake yi tace"ba yau ba sai naji daga bakin baba,kayi hkr ina hango mana abunda zai iya faruwa don haka idan kana iya wa kazo yau kawai kayi mashi maganar." "Dagaske kike inje kuma ince kekika turoni" Daga mashi kai tai cike da jin kunya murmushi yayi yace"yau din tazo mun cikin sa,a hakika ina fatan farincikin danake ciki ayau ya dawwama,ko kinsan bacin wannan dakika sani daman da kwarin guiwata nafito" "Meyafaru to" Ta tambayeshi lumshe ido yayi yana kanne mata ido guda yace"yau muka shirya da Abbina" Xaro idanunta tayi masha Allah tana bube baki cike da mamaki da dariya tace"wow wow Alhamdulillahi dagaske kake amman naji dadi wlh,kamar ma nafika jin dadin meyasa tun daxun baka sanar dani ba" Lakuce mata hanci yayi yace"haka kike kyau idan kina dariya,na gaza ganewa harara da kuka da dariya wanne yafi maki kyau duk wanda kikai sai naga yafimun kyau miye sirrin" Hararar tashi tai tana dauke kai dariya yayi"wow I love it wlh plz karamun daya" Dariya ta saka tana boyewa cikin hijab dinta,tana mamakin daman haka yake da barkwanci gaskiya ba karamin alhaki umma ta dauka ba. "Nidai ka kaini gida kaga anfara kiran salla wani wajen" "Idan da zamukai gobe anan love bazan gane ba don kuwa idan ina gabanki ba komine nake tunawa ba,kilaman idan kince mun whats ur name cewa zanyi safiyyah" Wata dariyar ya sake bata haka suka cigaba da fira yana sata dariya har saida tadage yakaita gida sannan yaja motar,yana kallon kiran malik awaya yayi buris don karya bata mashi mode dinsa. Motar muhseen na fita tasu tana shigowa,kallon motar tai tana murmushi da alama dai sun daidaita da yesmin. Kofar gidan ya tsaya yana kallonta cikin kauna kamar xai cinyeta, "Karkasa na kasa tafiya kallon yamun yawa fah" "Don Allah ki gaya mun wani abu mai dadi karki tai kibarni" Hararar so tayi mashi tace"take care of ur self" Shagwabe fuska yayi "yamin kadan nidai" Nidai budeni banson baba ya fito ya ganni cikin motar nan plzzz" "Okay say something plz" Kiss tayi ga hannunta ta hura mashi ta dauke kai tana kunshe dariyarta relax yayi cikin kujerar ya bude mata harta fita yakasa cewa komi,Allah kadai yasan yadda yakeji cikin jikinsa da xuciyarsa........saida tazo kofar shiga ta daga mai hannu by by. Daker yaja motar ya isa bakin get din gidansu,yana tuno moments da dama dasuka wuce yana tuna ranar daya bar gidan,har ya isa yayi parking motarsa. *********** "Safiyyah ya akai yau kikai dare" Inji baba dake alwallar magriba zaije masalaci. Sadda kai tayi don tana tunanin yaji saukar mota,amman bazata iya gane wa ba tace"baba jarabawar sai biyar muka fito sannan mundan tattauna da yan ajinmu kan exam din gobe,sannan na taho" Jinjina kai yayi yace"yayi wuce kije kiyi salla" Yafice masallacinsa. Jiki sanyaye ta wuce daki tana rage kayan jikinta tana adduar Allah yasa baban baiji sadda aka ajeta ba. "Adda sannu da dawowa" Murmushi tayi tace"yawwa yesmin ya gidan" "Gashinan ya exmas din,wai yaushe kuke gamawa" "Wlh exams kam sai godiyar Allah i think sai jibi zamu karkare insha Allah,ina yaya muhseen dinki" Murmushi tayi tana juya baya "daxun yazo bakinan har yaba waya da turaruka" "Uhmmm soyayya dadi Allah yasa alkairi kingode,adai kula sosai yesmin kinsan yadda xamanin yake Allah yabar kauna" Can kasa kasa taji tace"Amen Adda" Dunguremata kai tayi"makira anaso anakaiwa kasuwa" Shigewa toilet tai tabarta tana dariya. Bayan sunci abuncin dare ne baba ya kalli safiyya yace"waye ya saukeki dazun awaje" Kirjinta yabuga dan danan ta rude ta sadda kai tana murzar hannu Allah yasota ta cire xoben dazun. "Dake nake kina jina" Kwallata cika idonta tace"baba Abdoul ne" Basai yatambayi wane abdoul ba don yau iyayensa sunje har wajen aiki sun samai. "Bance maki karya sake xuwa nan ba,ina kuka hadu har daukoki kika biyosa" Jikinta yana rawa tace "anyi wuyar abun hawa yau najima bakin titi saigashi yace inshigo ganin zanyi dare shiyasa nashiga kayi hkr" Bata da zabin daya wuce haka tayi astagfirulla saboda tasan tayi karya kuma babu kyau. "Inhar ba sokike musaka kafar wando daya dake ba karna sakeji karna sake gani,nace maki haka ne don ba sa,an aurenki bane wannan shine magana,don iyayensa sunje har wajen aikina yau sun mun magiya nace aa don haka idan kina son fushina kicigaba da tsayawa dashi." Kwallarta ke xuba ga hannunta saukin ma babu nefa kuma babu haske sosai balle su gani,amman yesmin dake jikinta tana jin yadda jikinta yake rawa sai tausayin Addar tata ya kama ta har itama taji kwallartata tafito. Ahankali tatashi ta shige dakinsu kan kujera ta zauna tana kuka kasa kasa,har kirjinta dagawa yake daman wannan abun takeji shi take tsoro tasan daman baba bazai huce daga abunda Alh muazzam yayi mashi ba,don inba haka ba inhar kan kudine da bazai bayar da anty jamila ga uncle yahya ba,tunda shima kudin garesu sosai. Amman bazata iya ja da hukuncin mahaifinta ba,koda hakan na nufin dawwamar bakin cikinta. Yesmin ce ta shigo ta zauna kusa da itana rungumota jikinta tace"plzzz Adda kibar kuka insha Allah baba zai fahimce abunda ke ranki insha Allah zai amunce dashi.tunda abunda ake zarginsa dashi karyane sharrine naji anafada rannan.kiyi hkr kiyita addua idan darabon ku kasance tare baba zai sauko zai hkr yabaki shi.zantaya ki addua kibar kukan Adda nima zaki sani" Rungume juna sukai suna kukan tare,mama na tsaye bakin kofa tana jinsu,badai ta shigo ba tasan za,a rina tasan safiyyah tajima tana sin wani kuma tasan ba tun yanzu suka san juna ba. Juyawa tai ta koma daki don bata ga fuskar yiwa baban su maganar komi yanzu ba. *********** Mamaki yasha yadda aka canza komi na part din ya koma sabo,don yadda yaji bakin ni ima yau akai fenti aka saka sabbin komi na wajen rungumeta yayi yana jin dadin dawowa cikin family dinsa,gefe guda ga sahibarsa ta gama wanke duk wani datti dake xuciyarsa. Shida malik gaba yau falon Abbi akai zaman fira ga mami ga Abbi ga ni,ima sai malik din,zakiyya tana ganinsa tatashi tabar falon baice komi ba don daman yasan za,ai haka amman soon zata sauko idan yayi lallashi. Duk abunda suka faru aketa bita wasu ayi kuka wasu ayi dariya,anan duk sukai dinner basu tashi hirar ba sai shabiyun dare. Anan Abdoul yake tambayar ina su Amina Abbi ya bata rai yace "suna can shashensu yabasu sati biyu su fiddo mazaje duk ya aurar dasu idan ba hakaba wlh ya rantse saakarsu zai bayar. Baice komi ba o aure ne shine ya dace dasu. Mami da ni,ima sukai daki don bacci sukeji akabar malik da Abdoul da Abbi suna tattauna wa game da duk dukiyarsa da umma taso rabashi dasu,har wadanda yariga yasaka mata hannu amman baikai ga bata ba. Nan suka tsara yadda abunuwanshi duk zasu dawo yadda suke basu tashi ba sai biyun dare. Duk maitar shi akan jin muryarta hkr yayi don yasan tayi bacci. Baisan fiyah tana can tana kuka ba,idan ta gaji tayi tagumi tana tunanin yadda zata rabu da Abdoul. Yashiga jininta da bargonta tamkar fitar numfashinta takejin soyayyarsa,lokaci guda kuma baba zai mata haka. Kashe wayarta tai don bazata iya ganin kiransa ta ki daga wa ba. Washegari kamar marar lafiya ta yini don ma exam din sai yamma haka ta yini daki,saiga yaya jalal ya dawo Anty jamila kuma tazo. Ranar yini tai tana surfa ma fiyah bala,i don taki muhseen shima yaya jalal din yana tayata.kuka kau idonta har ya kumbura,bata kara takaici da bakinciki ba saida maganar Abdoul nasser ta fasu duk suka sani ai kamar zatai tsuntsuwa tabar gidan haka taji. Don yaya jalal yace wlh idan yasake ganinta dashi ko aka gaya mashi anganta dashi saiya balla mata kafafu. Mama dai najinsu saida taga abun naneman zama hauka tace duk wanda ya sake mata fada akan haka saota bata mashi rai.miye laifin yaron kawai don anbata sunan sa shine kurin zaku tasanmata,to karta sakejin bakin kowa akan maganar. Wanna ranar fiyah bata san ma meta rubuta ga exam din ba,tasandai ta yi tubutu amman bazata iya cewa daidai tayi ba ko akasin haka,har dare bata kunna wayarta ba Abdoul nacan duk ya rude ya fita natsuwarsa,saiyazo xaiyyi sallama gidan saiya fasa kasa zama office yayi don tashin hankali,maganarta tajiya yake tunawa kardai baban nasu ya dakatar da ita akanshi.inko hakane dole ne yau yaje ya fuskance shi............daga jiya zuwa yau fiyah ta fita natsuwarta bata iya cin wani abun kirki data fara zata ajiye ta shige daki......mama duk tashiga damuwa kuma har yanzu baban daure fuska yake don yasan zata ce mashi wani abu.............bayan salar isha,i yagama cin tuwon masara da miyar kubewa danya da mamar tayi,har lokacin fuaka abace duk gidan ya zama babu dadi saboda abunda yafaru. Dalha ya shigo bayan ya gaida baban yace"kayi bako awaje yana son ganinka" Kallon dalhan baban yayi yace"waye" "Dan gidan Alh........katseshi yayi yace"cedashi ya shigo" Fiyah na daki tana jin haka dandanan wata masassara tazo ta rufeta,kirjinta yana duka me baba zaice mashi innalillahi nashiga ukuna Sallama yayi yashigo cikin wani yadi marar nauyi yayi kyau sosai,ya gaida mama dake bakin famfo ta asa cikin kulawa. Kafin baba yayi mashi iznin zama ka tabarmar dayake bisa. Yaya jalal ne yashigo yana ganinsa ya hade fuska,Abdoul bai damuba ya mika mashi hannu,Daker ya amsa mashi gaisuwar dayake mashi. [10/11, 7:23 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 *kafin muci gaba zanyi wani bayani.akan masu ganin ban kyauta ba dan nasaka Alfah bai auri zakiyya ba,harda cewa ina nuna duk girman laifin mutun ana yafita yes duk girman laifinka idan katuba ga Allah yana yafe mana,haka zalika niban nuna cewar Alfah bai yafewa xakiyya abunda tai ba,tariga ta sanar dashi komi kuma yafahimceta yace ya hkr komi ya wuce,sannan badole sai Alfah ya auri zakiya ne hakan zai nuna ya yafe mata ba.abunda nakeson kugane nifa labarina gaba dayansa akan Abdoulnasser da safiyya natsara shi,duk wanda kukaji sunansa to daga jikin daya daga cikinsu ne,kuma nayi hakane don na nuna cewar ba komine kake nema ka samu ba.duk sonka da abu idan babu alkairi tsakaninku Allah zai iya hanaka,haka duk gujewarka da abu idan rabonka ne dole zai kasance.ita rayuwa haka take xuwa ku kalli yadda abubuwan suke faruwa ko a reality zakiga abunda kikeso bashine yake kasancewa ba,wanda bakinson shine alkairin ka akan kanki ma idan kika duba abubuwa dayawa dakikeso baki samesu ba kuma karshe wanda bakison shine alkairinki.don haka ina mai bawa masu challenging dina hkr akan cewar haka labarina yataho,haka zai cigana da tafiya idan anan anbata maka wani wajen ana faranta maka.haka rayuwar take idan nan kaji dadi ba dole can kaji ba,idan yau katashi da lafiya gobe ba lallai kajika normal ba.don haka kubarni na tafiyar da labarina ayadda yake,haka natsara haka zai tafi plzzzzz idan wata ta kullaceni har tana ganin ta yi asarar kudinta ina bata hkr,nidai don wata kodon wasu bazan fasaba bakuma zan canza idear ta ba ina godiya sosai da challenging wannan yanuna man cewar duk yadda kake faranta ma dan adam duk ranar daka kuskure mashi to hakan nanufin sauran daka faranta mashi zaimanta dasu ya gaya maka magana.ngd ngd sosai da hakan na sake samun experience ahakan,daman arayuwa bakowane zakaima daidai ba nabarku lfiy BISSALAM* 🅿️...........59 "Zauna sosai magana zamuyi dakai." Baba yacewa Abdoul dake yakejin dukan kirjinsa yana karuwa. "Meke tafe kai tukun karna katse maka hanzari" Sadda kai yayi yanajin kamar ya tashi ya ruga amman muhimmancin safiyya arayuwarsa yafi gaban nan,wannace damarsa idan yara sata baisan ya zaiba. Cike da ladabi yafara magana cikin natsuwa "baba nazo ne akan kaban iznin xuwa wajen safiyya,inasonta na yaba da halayenta nagari da hankalinta da natsuwarta don Allah baba karkace aa." Yafada muryarsa tayi rauni tausayinsa ya cika xuciyar mama,jalal kuwa sai wani harararsa yake yaja karamin tsaki yace"kayaba da tarbiyyarta kaikuma fa,taka tayi daidai da tata kaga akwai tazara tsakaninku" Dago jajayen idanunsa yayi ya xuba mashi su yaajin zafin xuciyarsa yana hauhawa,hakika da babu baba da ba agidan bane tabbas saiya xubar mashi da hkr,amman yaci albarkacin qanwarsa dayake so yaci albarkaci baban da kuma mama. Cikin fada baba yace mashi"jalal tashi ana wajen,ina ruwanka dakai yake magana zan saba maka awajen ana oya fice man da gani" Ya ta shi yafice kamar iska. Kunya ce ta kama baban saboda yasan maganganun sunyi mashi zafi sosai. "Kayi hkr bashida wayau ne,naji bayanin ka Abdoul-nasser kuma ada na riga na yanke hukuncin cewa alakarka da safiyya bazata yuwa ba saboda ganin nisan dake tsakaninku bayaga haka kuma ina duba wani abun bayan wannan,da zanyi anfani da matsayina na mahaifinta in dakatar dakai itama na hanata saurarenka Amman ya zu zan kirata idan har uwata tace mun ta amunce tana sonka zata aureka hakika bazan takura ku ba.don gudun shiga hakkinku" Dadi Abdoul yaji ya kamashi duk wani haushin jalal yaji yana bajewa,yasan fiyah bazata kishi ba zatace ta amunce. Kallon mama baban yayi yace"kiramun uwata" Tashi tai tatafi tana kalon wannan lamarin,tabbas tasan fiyah babanta baya son hadin duk abunda baya so ko tanaso zata hkr,tasan wannan hanyace dayakeson korar Abdoul din batare daya kullace shi ba. Jinjina kai take tanajin tausayin diyar tata. Shiru dakin ko haske babu yesmin na waya da muhseen,fiyah na dunkule cikin bargo tana kuka can kasa. "Safiyya kifito babanku yana son ganinki kisanyo abaya" Fita tai don bata son ganita cikin wani hali zata sake karya mata xuciya. Ahankali ta sauko daga ka gadon tana jawo abayarta ta saka tana goge fuskarta sannan ta fita, Bata yarda ta kallai ba daga can gefen baba ta zagaya ta zauna cikin ladabi tace"gani baba" Kanta kasa bata yarda ko kayan jikinsa ta saka ga idonta ba. "Bakiga bakoba bazaki gaidashi ba" Muryarta can kasa tace"ina wuni yaya Abdoul" Wani abu yaji ya dirar mashi,kamar zai fashe dakuka don dajin muryarta kuka tamaga yi Cikin kulawa yace"lafiya kau safiyyah" Sukai shiru baban kanshi yanajin kamar bai kyauta masu ba,amma yana hangen abunda mutane zasuce akanshi zasuga kamar ya bayar da yarsa don ganin yaron nada kudi haka ubansa........."uwata ga nasser nan yazo kan batun neman aurenki,kina sonsa kin amunce zaki auresa bazan tauye ki ba" Jitake har numfashinta yana sizing meyasa baba xaice haka,idan ya amunce ai ansamashi kawai zai basai ya sanyota ciki ba ita yanxu ya zatai zata ansa mashi ta bar abunda baban keso kokuwa yazatai. "Kinajina uwata" Muryarta tana shakewa tace"baba duk abunda ka yanke akai dashi zanyi anfani ka yanke hukunci kawai,duk abunda kace yayi" Tatashi ta koma daki toilet tashige tana rushewa dakuka mai cin xuciya.........shikenan bata da sauran wani farin ciki baba ya rabata da burinta da walwalarta,waye zai iya maye wannan gurbin babu shi har abada kowaye zaice ta aura bazata tana sonsa ba,zata yi biyayya ta aureshi amman ba zata iya sashi cikin ranta ba har gaban abada. Shiruce ta biyo baya sai yanzu baban yakejin bai kyauta ba,hakika safiyya yarinyace mai hkr dakawaici da kauda kai,yayi imanin duk abunda ya yanke akan alakarta da Abdoul haka xata karba tayi mashi biyayya,tausayinta ya cika shi har ya kasa cewa komi Abdoul din ya mike yana cewa"baba Allah ya bamu alkairi Allah yasa hakan shine Alkairinmu saida safe" Yafice yana ganin bibbiyu don har wata juwa take daukarsa,metake nufi kenan ta bada damar da za,a nisanta shi da ita safiyya daman bata son sa bai sani ba,meyasa zata karya mashi xucya har haka daker ya iya gano get din gidansu yana shiga kau kamar jira ya yanke jiki ya fadi.........akan idon zakiyya ta fito daga sashen su khadija ta kaimasu abinci.....aguje ra karasa tana fasa kara tana jijjigashi dan da nan aka taru kanshi,sojojin dake waje suka daukai suka sashi mota,shigowar malik kenan yaga wannan tashin hankalin,kwana yayi yarufa masu baya don yasan asibiti za,aje dashi duk inda hankalinsa yak yayi masifar tashi don har yamance rabon dayaga Alfah cikin wanan hali,tabas abunda Abbi ya gaya mashi dazun akan maganar safiyyah da Alfah shine zai cosing wannan matsalar,kodai yaje gidan baban ya korai kokuma ya gaya mashi kai tsaye bazai bashi yarsa ba. Mami da ni,ima kuka suka kamayi gashi Abi baikai ga dawowa daga wajen aiki ba,babu shiri mami ta kirasa ta gaya mashi ai yafi kowa rudewa da tashin hankali.............. Mama kanta tasha takaicin baba shiyasa ko saida safe batai mashi ba ta shige dakin ta kwanta,wane irin halin rikaune da babansu yana gani yaran nan suna son junan su amman saboda wani ra,ayi can nashi na daban zai cutar dasu da haushinsa ta kwana shikanshi yaga canji amman bai iyace mata komi ba. Fiyah saboda kuka cikin dare zazzabi ya rufeta har hakoranta suna haduwa saboda kerma,hankalin yesmin ya tashi taita shafa mata ruwa saboda yadda jikin ya kidime baki daya banda kuka babu abunda yesmin keyi,fiyah kau bama ta cikin hayyacinta ganin dare yasa yesmin bata tado mama ba amman asubar fari dataga fiyahr har suma take agigice tafito tana kwalama mama kira cike da tashin hankali. "Yesmin kanki daya baki iya salati ba kike ihu da kururuwa menene" Tana shashsheka tana nuna dakinsu daker maganar take fitowa "Adda.......Adda ce gata can......su.....suma take tun cikin dare bata lafiya mama karta mutu...." Tare suka karasa cikin dakin duk sun rude mama had jikinta rawa yake tana jijjiga fiyah amman bata numfashi..........rungumta tai tana kuka lokacin baba yaje masallaci dan danan mamar ta kira anty jamila don basu san wanda zasu nemi taimakonshi ba wajen mota idan ba su ba. "Jamila kiceda yahya don Allah yayi hanzari yazo yakai safiyyah asibiti gata nan suma take" Ai xunbur tai daga kan gado tana fitowa har bakin get tana jiran shigowarsa daga masallaci ta gaya mashi kayan baccine jikinta ta saka abaya suka taho agigice,tabar little fiyah ga mairenonta. Sorry for d let update [10/13, 12:32 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️............60 Ansamu nasarar daidaiton numfashinta amman bugu xuciyarta bai dawo daidai ba,saboda jininta daya dan hau shiyasa amman sunyi iyakar bakin kokarinsu akanta sunyiwa uncle yahya bayanin cewa zata tatashi insha Allah,damuwace zata haifar mata da masassarar kuma dama akwai maleria jikinta.amman yanzu da bukatar ta huta tasamu rest of mind da alama tana da matsala da bacci amman data farka tasha magunguna kuma ga ruwa yana shigarta komi normal insha Allah" Godiya uncle yayi mashi yana komawa wajen baba da mama dasukai xugum xugum kamar masu zaman gaisuwa. "Yaya dai yahya me likitan yace?Allah yasa ba wani mugun abubane ya faru da ita?"mamace cikin damuwa harda yan kwallarta take mashi magana. "Ki kwantar da hankalinki mama safiyya zata tashi cikin koshin lafiya,ba wata matsala yamun bayani gamsasshe maleria ce da damuwa don har BP dinta yadan hau kadan amman yace data sha magani insha Allah normal,yamata allurar bacci data maleria karku damu abarta ta huta din kamar yadda yace" Jinjina kai tayi tana zama kusada Anty jamila da tayi tagumi,inhar akan wannan mutumen fiyah take wannan ciwon gara abata shi hankalin kowa ya kwanta,yarinya da yan shekaru harta samu hawa jini. Mama Ko kallon baba batai ba don har lokacin kule take da shi,ko magana ma batai mashi ba. Baban da uncle suka ware gefe suna magana akan matsalar data faru uncle yana bada shawara da fadar yadda yadace.................haka aka bar mama wajenta yesmin zataje ta shigar mata exam don yau suke ta karshe tana adduar Allah yasa ta iya ansa mata question din daidai,don bata san me za,a tambaya ba.duk yadda baban yaso magana da mama kiyawa tai saidai ta kauda kai kurin dole suka wuce gida suka kyaleta.dalha ne zai kawo mata kalacinta,Anty jamila tace zataje tayo wanka sai tadawo tataya mamar zama. ************* Duk inda hankulan iyalan Alh muazzam yake yakai kololuwar tashi,don kuwa ga Abdoul nan kwance gamar gawa baya numfashi,likitoci ukune kanshi suna bakin kokarinsu amman Abbi gani yake basu yin komi zarya yake bakin kofar dakin yana leke ta glass din kofar,daga can kuma mami ce dasu ni,ima zakiyya da malik kuka kurin suke,malik ne keta kokarin nuna dauriya.........dadyne ya iso shima cikin damuwa yake tambayar abi abunda yake faruwa kasa mashi bayani yayi yana kwalla,malik ne tace "dady duk ta kare yaje gidan su safiyya ne babanta ya korai kokuma kai tsaye yayi mashi iyaka da ita,abunda zai ita jefashi cikin wannan halin kenan don Abdoul yana ma safiyya soyayya mai zafi,rasata kamar yana barazanar shina rasa tashi rayuwar don gaskita cikin kwanakin nan inaganin canji sosai tare dashi,alamun sunriga sun daidaita da ita yarinyar gaskiya abunda nake zaton zai jefa shi cikin wannan yanayin kena" Xunbur Abbi yatashi zaifice dady yarikoshi "ina zaka?badai koma wa zakai ba duk irin abunda ya gaya mana rannan" Kamar abbi zai kuka yace"Abdullahi ina son rayuwar dana shekara nawa bana tare dashi,sai lokacin da komi ya wuce kuma wata matsalar xata shigo,zanje karo na uku na sake rokonsa kome yake son nai mashi inhar zaibarsu su auri juna wlh zan mashi,koda cewa yayi inkwanta ya bita kaina" Ficewa yayi dadyn ya bi bayansa don yana iya cewa acikin wannan halin zaija mota. ************** ***************** Fiyah cikin kwana uku tatashi ta samu sauki,ta dauki hkr ta sama xuciyarta amman fa ta rage walwala sosai da sosai don saita yini cikin daki bata fito ba idan ba wani abun xatai ba,zaka samu kowa tsakar gida amman ita tana daki babu yadda mama batai ba,babu irin lallashin da batai ba amman fiyah ta kasa dawowa daidai,abunda ya taba yesmin da mamar kenan shi kanshi baban yanajin babu dadi,shiyasa yaketa kokarin jawota jikinsa ko zata sake saidai murmushi kurin duk maganar da zakai mata idan har ba yazame mata dole ba bazakaji muryarta ba.tun Anty jamila na fushi da ita harta sauko tana jan yar uwartata jiki,jalal kau ko kallon inda yake batai ko ya mata magana uffan bata ce mashi.ana cikin haka aka saka ranar yesmin da muhseen alokacinne baba ya kira fiyah dakinsa da safe bayan angama karyawa. "Uwata kinsan dai nine mahaifinki ko,kuma kinsan irin son danake maki bazan yi abunda zai cutar dake ba,duk abunda zanyi inayine don martabarki da kimarki yanzu ma wata alfarma nakeso daga gareki" Dagowa tai tana kallonsa da fararen idanunta fuskarta ta saki daka kalleta kasan tana cikin damuwa don har wata irin rama tai. "Baba ni banace kayimun ba daidai bane,kawai inakokarin ganin na manta da komi zan dawo daidai kuma komi kake son yankewa akaina baba basai ka nemi alfarmata ba kana da ikon yanke hukuncin duk da ka ga dama akan rayuwata" Wani tausayinta yaji ya dirar mashi har kwalla ta cika idonsa "shikenan uwata Allah yayi maki albarka Allah ya albarkaci rayuwarki,wanine keson aurenki harna bashi dama ya turo iyayensa don harna yanke hukuncin saka rana guda keda yar uwarki,nan da wata uku idan Allah ya kaimu" Wani irin bugawa kirjinta yayi dan danan kanta ya sara damn ciwo yake,daker take jawi numfashinta ta dake sosai tace"Allah ya sa haa shine mafi alkairi baba" Tatashi tafice tabarsa yana binta da kallo,mamace ta shigo cikin tashin hankali take kallon baban "mekake shirin yi babansu?waikai bakajin digon tausayin yarinyarnan shin wace irin xuciya ce dakai babansu,inajin yaron nan har yau yana asibiti karshe dole aka fitar dashi kasar waje,duk da haka bazaka tausaya masu ba.har gida iyayensa suka zo suna magiya da roko amman vanji kace masu komi ba,gaskiya idan ka aurar da safiyya ga wani ba wannan yaron ba ka cutar dasu,kadaina ganin bata maka gardama Allah kadai yasan kuncin da kasasu baka tunanin Allah ya tambayeka.................ya i sheki nace ya isheki hakanan,ke zaki gaya mun abunda zanyi inace nima yatace,gaya maki kai ba nasonta?kinfini sanin daidai da ba daidai ba?to kinga daman kyaleki nake akan wannan abun,tunda akafara maganar nan kiketa mun wasu halaye marasa dadi safiyya dai yata ce kuma nine nakeda alhakin zaba mata miji wanda yake daidai da rayuwarta,don haka wannan yazama na karshe inajin kinji me nace" Ya saka hularsa ya fice yabar gidan. Tunda mma tazo gidan nan matsayin matarsa magana kwatan kwacin irin wannan mai zafi da daga murya baitaba mata ba,duk sabaninsu zasuyi abu su surufe sushirya babu wanda ya sani,kuma kullum suna cikin fahimtar juna daba juna uxiri,amman saigashi yazu da girmansu suke irin abunda baidace ba,har yaransu sunaji. Kukan da mama ta manta batai ba shine take yi,suma can fiyah da yesmin kukan suke,don basu tabajin irin haka da iyayen nasu ba. Fiyah naji nagani aka shiga shirye shiryen bikinsu itada yesmin,tun tana kuka tana damuwa tana kuncin,har ta shanye tazo ta zama kamar abun baya damunta,gidan koda yaushe da mutane yanuwan mama dana baba ana hidimar hada gara su cincin da dublan da alkaki da sauransu,shiyasa ma bata zama gidan tana gidan inna balaraba wajen hasana,ko tatai wajen feea. Wannan kenan...... Tunda akaga ciwon Abdoul ya gagari likitocin na Abbi yayi visa suka tai suduka can Australia wajen dr Abdoul din da yataba dubashi,don sunce xuciyarsace ke ciwo duk sanda zata halba dole zai sume saboda bata da isassar lafiya. Kuka kau mami sun shashi har idonsu ya kekashe,zakiyya tuni ta nemi fushin da take dashi ta rasa kullum suna cikin yi masa addua Allah ya tashi kafadarsa,sai ya zamana malik ne dan lallashi da nasiha da ban baki acikin sati ukun da sukai Australia sabo da fahimta ya shiga tsakanin zakiyya da malik,saboda shi ya ansa zai auri zakiyyarne don ya saukakama Abdoul matsala don tabbas yasan zai sabi fiyah akan zakiyya,shiyasa shikuma yaga yadace asamu mai lallashinta mai tausaya mata,don zakiyya ta cancanci wadannan abubuwan tarasa mahaifiyarta ta rasa masoyinta da tayi shekaru aru aru tana dakon sosan,amman zamanta da malik akai akai yana yawan yi mata nasiha da jawo hankalinta yana nuna mata cewar komi na rayuwa dan hkr ne,kuma duk abunda karasa arayuwarka ka dauka hakan alkairine,Allah yafimu sanin daidai da ba daidai ba,yana duba mana abunda zai zama alkairi arayuwarmu bisa ga wanda muka kwallafa rai. Komi yafaru da bawa dama can rubutaccene kariga karubuto abunka tun cikin ciki,shiyasa kafi son duk abunda kagani to ka godema Allah kayarda da wannan kaddarar don yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau imanine...........da haka malik ya jawo hankalinta kanshi,duk da sudukan babu maijin son wani amman akwai kulawa da fahimta tsakaninsu,haka mami ma take yawan yiwa zakiyyar nasiha akan rayuwa da kuma alakarta da malik,don tagaya mata muddin ta rasa shi ba fata take mata ba samun irinsa zaiyyi wuya. Ansamu cigaba ta bangaren lafiyar abdoul don ciwonsa na cikin ciki ya warke tas cikin kwana ashirin da dayan da aketa mashi treatment,xuciyarma kuma alhamdulillah bugunta ya daidaita don har yana farkawa yaci dan wani abu yasha magani,amman baya tankawa kowa maganarsa bata wuce eh,aa,yawwa ko idan zai gaida mami dasu Abbi zaice ina kwana atambayesa ya jikin zaice da sauki shikenan. Malik ne kurin yake dan mashi hira yana tankawa shima idan yagaji yayi mashi banza. Wani sabon miskilancine ya tsiro dashi aduk sanda yake sauraren maganar ta jiyake xuciyarsa tana kuna,har wata sa,in jikin ya rikice sai anmashi allurar bacci..........saida mami ta tusashi gaba da kuka tana ya sassautawa kanshi yaji tausayin kanshi da nasu,komi zaifaru yariga yafaru idan anhanashi safiyya bayana nufin karshen rayuwarsa ne yazo ba,akwai mata da dama Allah zai cire maka ita inhar ita din babu alkairin tare da ita,fada take mashi sosai har tasamu ya xubda kwalla ranar yini yayi baice komi ba,bayan kwana biyu kafin asallamesu dady da Abbi suka tai Nigeria saboda wani aiki daya taso anbar malik da su mami da ni,ima da zakiyya dai bayan sati biyu idan an basu sallama zasu dawo tare alokacin ne kuma Abdoul ya fara saukowa yana sakin jiki da yan uwansa zasuyi fira harda dariya shidai iyakarsa murmushi,ahakan ma sunajin dadi son da ai bama aiyin firar dashi. Yau shi kadaine su mami basu kai ga zuwa ba don gidan Abbi dake nan kasar suke zaune malik ne yake kwana dashi,idan safiya tai yaje gida yayi wanka yayo break. Xakiyya ce ta shigo da kwandon kalacinsa fuskarta da fara,a ganinsa zaune yana kallon tv dake cikin dakin nashi. Murmushin shima yayi mata ta ajiye kwandon bisa wani table tana dauko brush din sa ta matsa mashi maclean tace"yaya ina kwana" Muryarsa ta canza sosai tayi sanyi dakaji zaka san cewar yasha jinya. "Lafiya lau kiyya,yau manta wa dani kukai har shadaya saura babu wanda yazo" Murmushi tayi tace"wlh makara mukai yau,nice ma wai nai saurin fitowa sabida break dinka kayi hkr" "Yazanyi daku"ya mika hannu ta bashi brush din yafara kokarin saukowa hannunta ta bashi ya kaa saan ya sauko yana cewa"thank you" Murmushi tai tana bude mashi kofar bayin yashiga ta shiga tattara dakin tana gyara mashi gadin,duk dadai tun safe masu gyaran dakunan marasa lafiya suke shigowa su share. Freshner ta fesa dakin ya kama kamshi komi yayi lafiya lau sannan ta zuba mashi break din ta ajiye kafin ya fito. Kallon dakin yayi yajin jina kai kullum ita ke gayara mashi dakin yayita kamshi alamar jinjina yayi mata yace"kina kokari gaskiya da alama gidanku bazai kasance a datti ba ina taya abokina murna" Hararar wasa tai mashi tana juyar dakai tana murmushi. "Nidai bana so wlh" Zaro ido yayi yana zama kasa inda ta shimfida mashi darduma yace"abokin naune bakiso kome?" Itama zaro idontai tana rufe baki "nabani ni wlh ban ce ba karka jamun" Dariyar da yajima baiba yau yayi yana kallonta ita kuma ta boye fuskarta tana juya baya. Aransa yaji dadi da hakan ta faru,tabbas yasan duk wadda tasamu malik matsayin miji ta gama morewa,don shima gwanine wajen jawo hankalin mace akanshi,ya tabbata kokarinsa ne tasa har zakiyya take saurarensa kuma da alama tayi na,am da malik din. Shine ya shi go da fara,a yana kallon Abdoul din "alhamdulillah jiki yayi kyau wlh daman nagaji da zaman kasarnan haka gara katashi komunje muji inda tamu maganar ta kwana ko yakikace"yafada yana kallon zakiyya jitake kamar zata nitse awajen tsananin kunyarsu takeji mikewa tai zata fice Ya tare kofar yana leken fuskarta Abdoul murmushi yake masu yana break dinsa. "Ina zaki daga nayi magana shikenan tunda kunya kikeji na daina zoki zauna abunki,inkikatai ina zan iya zaman gadin wannan miskilin mutumen" Dawowa tai ta zauna suka cigaba da hirar su gwanin sha,awa. Har sadda su mami suka karaso. ************** *nigeria* Biki ya kankama don komi anriga da angama yiwa amaren,tundaga kan wani gyara da tsumi iyayen nasu sunyi bakin kokarinsu wajen yin hakan,idan kagansu zaka dauka cikin inji aka sasu aka wanke tass........damuwar da fiyah ke ciki itace ta shafi yesmin,duk yadda take murnar zata kasance da burin ranta idan ta tuna da cewar Addarta bata sanma mijin ba,saidai yakan kirata awaya shima bata taba dauka ba.kuma baya fushi zai sake kira saidai yesmin din ta dauka matsayin fiyar suyi firar ta kashe,tunda ance baya kasar sai karshen shekara yake xuwa amman yanzu da an daura auren zatabi jirgi ta sameshi can. Kwance take tana ta kallon no dinsa duk wasu moments dinsu dashi wanda tundaga kan haduwarsu ta farko da karshen haduwarsu saita fashe da kuka,kukan da tunda akafara hidimar bikin batai ba,don xuciyarta ta dunkule ta dake wanda takejin bata jin akwai abunda zai sake sata kuka ashe fadane kurin tai,haka taita kukan har yesmin ta shigo. "Haba Addata kiyiwa girman Allah kiyi hkr baki isa ki canza kaddararki ba,abunda Allah ya hukunta dole zaki ansheshi hannu bibbiyu,tabbas akwai ciwo akwai tashin hankali amman bamusan dalikin dayasa haka ta faru ba,kidauka Allah sonki yake dahar ya maki musaya da wani kila shine mafi alkairinki........."rungumeta tai tana cewa"yesmin nasani nasan dahaka amman taya zan cire shi daga cikin raina,yesmin yya Abdoul yayi reshe acikin xuciyata har ya fitar da tsiro,duk iyakar kokarina abun ya faskareni,yazanyi haka zanje gidan wani ina fama da wani cikin raina,ina jintsoron Allah ya kamani da wannan laifin" Kukan suke tare mama na baking kofa tanajinsu bata san sadda hawaye suka silalo mata ba,hakika Safiyya na cikin halin damuwa,kuma bata da yadda zatai da damuwar tata zata dai roka mata Allah yasa mata hkr da dangana. Yesmin har anje anmata jerenta unguwarsu Anty jamila,fiyah kuma kudin kayan dakinta baba ya danka mata ga hannunta yace tunda baza,a iya daukar kaya har kasar waje ba yaga bari yabata kudin tayi sana,a idan har mijin yabari acan ma saita karasa karatunta. Rungume baban tai tana kuka yana lallashinta tare daa mata albarka,nasiha yayi masu sosai don yasan ba lallai ya samu amar yi masu ba na da kwaa uku da yarage daurin aure. Dole fihay ta saka danaa dataga dai dagaske auren nan yinsa za,ai taroki allah yasa hakan shine alkairinsu ita dashi,shima allah ya bashi lafiya yakuma samashi juriya da dangana. Ta saduda kodan nasihar da baba yayi mata da kuma wacce yan hwanta suke mata,mama kam kullun ne saita bata baki tana bata labarin irin wadanda akaima aure irin nata da irin nasarar dasuka samu. Baba da Abbin Abdoul sun sasanta don har gaisawa suke yake mashi allah yasa alkairi,ai baisan biki za,ai gidan ba tunda shima baya zaune nan dai har ybashi gudun mawa mai yawa gaske haka dady ma. Tun dawowarsu Abbi yasa aka shiga hidimar gyaran gidanshi ba kama hannun yaro,don rana guda zai aurar da yara uku Amina da zuwairat da haulat.khadija yabarta said ni,ima ta samu miji sai ahadasu. Komi da komi aka canza ma gidan idan ka shigo unguwar bazaka gane shine ba. Sati biyu kacal aka dauka ana gyaran don komi yayi lafiya lau bazata yakeson yiwa su mami idan suka dawo duk da babu ranar dawowar bikin ma duk baifi saura wata guda ba. *Rana bata karya aidai uwar diya taji kunya* 😭😭😭😭ina tay Abdoul kishi tsakani a Allah mom banji di ba. 😂😉 Muhadu next page da sorry typing error [10/13, 5:31 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........61 Kasancewar masallacin juma,a aka daura ba kofar gida ba bakowane yasan an daura ba,saida aka fara shigowa abokan baba sunayi ma mama Allah yasa alkairi,saitaji kwalla ta cika idonta haka take daurewa tana ansawa,su yesmin suna gidan Anty jamila labarin ya samesu saitaji duk dokinta na kasancewa da muhseen yakau,kewar mamanta da Addarta yasakata ta rushe da kuka,ga kawayensu nan wasu na lallashi wasu na mata dariya. Fiyah na fitowa daga wanka maiyi masu make up tazo ta fara gyareta tana mulketa da wasu arnayen turaruka da tunda akafara yimasu gyara dasu ake mulke masu jikinsu,shiyasa dasun gifta ka zakaji sun barka da tarin kamshin.komi suka rike saiya kamu da wannan kamshi,ana cikin kwallaiyar ne dayake tace kartayi mata heavy make up simple takeso,wata kawar yesmin ce ta shigo tace"Adda safiyyah ga yesmin can tana kuka dagajin an daura aure" Wani irin duka taji ga kirjinta,har saida taji sautin cikin kunnuwanta dan danan jikinta yadauki rawa dakarkarwa daker tace mata"don Allah salaha kilallasheta kafin inxo idan akwai masuyi mata dariya sudaina hakan zai tun xurata" Tace "to bari naje" Tana fita tacigaba dajin wanan dukan a kirjinta,tsawon lokaci tana haka kafin wasu zafafan hawaye su sulalo mata,cigaba da xuba sukai babu kakkautawa mai kwalliyar ta dakata tana kallonta cikin murmushi. "Kema kukan kike,to inkekinayi ya za,ai ita tadaina.kuyi hkr kowace mace da haka ta saba agidan mijinta,kuma kugodema Allah wasu nacan neman mazan dazasu auresu suke sun rasa,amman kuganku ku da kananun shekarunku kunyi aurenku kun huta,kuyi hkr daman dole wataran duk shakuwarku da yan gidanku dole zaka barsu,ni kinga burgeni kuke wlh shekarata goma da gama secondary har yau Allah bai ban mijin ba,ba kuma don banda masu sona ba aa lokacine Allah bai kawo ba." Goge kwallarta fiyah tai tana shanken majina tayi murmushi na karfin hali tace"na gode Anty,insha Allah zandaina kuka itama zan lallasheta,kuma insha Allah zaki samu miji wanda baki taba tsammani ba" Murmushi tai tana jin dadin Adduarta cigaba da kwalliyar sukai tana janta da fira,don ganin har lokacin tana cikin damuwa. Bakomi take tunawa ba illa Abdoul,yanzu shekanan ta zama ta wani,duk wahalar dasuka sha akan juna daman bazasu rayu tare ba,wannan abunne idan ta tuna yake sata jin kirjinta yana zafi fiye dakima. Haka aka gama ta tayata shiryawa cikin wasu dankareren less na cikin lefenta da aka kawo akwati shabiyu,harda gwal aciki da xinarai abunda yafi dakar ma masu kallon lefen hankali irin jewelrys din da aka saka tsalatsala da daukar ido,hakika anma fiyah lefe na nuna ma sa,a haka yesmin ma akwatunanta goma ras,masu shegen kyau. Sunsha saka albarka wajen dangi da abokan arxiki,qawayen fiyah uku kacal ta gaya mawa daga feea sai yan class dinsu su biyu zuhra da ziyada. Zanso kuga yadda fiyah ta dauki kyau,hotuna mai kwalliyar tayi mata da wayar fiyah tana janta wai ta nuna ma angonta idan ta isa kasar,don karfe takwas na dare jirginsu zai tashi.yan rakiyarta duk mutun ukune daga yakumbo hajara yayar baba sai inna balaraba da Anty jamila saifa hasana diyar inna balaraba.yesmin ana gama sallar la,asar za,a mikata. Shiyasa tunda suka kulle kansu daki ita da fiyah basu bar juna ba,kuka kurin suke ita fiyah abun ya hade mata goma da ashrin,ga rashin masoyi ga rashi iyaye ga na yar uwarta rabin jikinta,tunda suka xo duniya basayin nisa da juna irin haka saigashi yau aure zai rabasu don dole. Motace akazo da ita ta abokin yaya jalal zai dauki amaren akaisu gida aimasu fada za,akai yesmin nata gidan. Ai jisukai kamar ance za,akaisu makabarta kuka kamar zasu mutu,Inna balaraba ce da Anty jamila suka jasu suka sasu motar sanan suka tai,gidan acike da mutane mama kokadan batai tunanin yan unguwar zasu shigo mata ba,bacin momin su feea. Saigashi har mutanen da batai tunani ba sunxo kuma ta samu abun arxiki sosai,dakin baba aka ajesu fura mai kindurmo aka dama masu harda xuma akasaka,don cikinsu babu wace tasaka ko ruwa aciki ta tun safiyar yau. Baban da kanshi ya tsaresu saida sukasha furar sosai,sanan shida baffa ubaidullah kanensa da yayansa baffa kalil suka sasu gaba da nasiha sosai,har jikinsu yayi sanyi suka daina kukan. Sannan yan uwan mama ma suka zo suka dora nasu,yinayi bari nabari ta rabaki da kowa tsafta,biyayya,ladabi,girmamawa da girmama iyauensa yan uwansa da duk wanda ya kawo.sune ke saka kiga miji yana bin matarsa,yana mata duk abunda takeso shike sawa har ace masa mijintace,idan kin tsare wadannan kin zama sarauniya kuma gimbiya agidanki,babu boka babu malam zaki kame mijinki kihanashi kallon wasu sai ke,idan har kin dauki duk abunda ake gaya maku ina mai tabbatar maku zakusha mamaki." Cewar goggo ladidi diyar wansu mama. "Hakuri shine jigon zaman aure,kiji kikiji kigani kikigani,ki kawar da idonki akan komi kiringa wa mijinki uziri komi kike idan har yashigo gida ajiye ki kula dashi,wannan na daya daga cikin abunda yasa maza da dama basa son dawowa gidansu kan lokaci.inhar kikai hkr dashi ananma xakici riba ba yar karama ba,sannan ki rike mashi amana kirike sirrinki kedashi kunyi karatun addini kunsan hukuncin mai tona sirrin ta tsakaninta da mijinta,don haka kurike sirrinsa kowane irine,sannan ku kula da dukiyarsu kuzama masu taka tsantsan da duk abun daya mallaka,karki zama mai saka mashi ido kan lamarranshi." Haka sukaita basu shawarwari da nasihu da kalamai kala kala da zasu natsu su zauna gidajensu. Har abokan muhseen suka iso da motoci dan daukar amarya,mota ashirin ce cif kowa dakeson xuwa saida ya samu waje. Harda fiya aka tafi raka yesmin kafin lokacin tashin nasu jirgin yayi. Motarsu guda da yesmin suna makale da juna,sai inna balaraba jusa dasu sai Anty agaba,dayake uncle yahya ne kejan motar. Gaskiya gidan yesmin yayi babu karya,don gudane na kere sa,a giane dan gaske wanda tawon rayuwarta bata taba kawo cewar zatai aure aciki ba,tana ganinsu unguwanni masu hali amman bata taba saka hakan aranta cewar wataran zata mallakeshi ba. Kowa idan yashigo saiya yi magana ana ta saka mata albarka,da fatan dorewa acikinsa har iyakar rayuwarsu,bed room dinta uku amman guda biyu baba da mama sukai kokarin cika mata da kaya,sai falukanta biyu suma acike da kaya na zamani masu kyau. Kawayenta harda hotuna daya daga cikin dakunan aka sauketa ita da Addarta,can suka shige kowa ya buga tagumin sabuwar rayuwar dasuka shigo,wanda tazo masu abazata don kokusa fiya bata kawo aurenta nan da shekara mai xuwa ba na balle wata uku.sunsha addua ga Mutane kafin suka fara ragewa ahankali ahankali har ya rage daga su sai inna balaraba da hasana saint feea da ziyada sai Antyn. Hira akeyi yadda abubuwan suka kasance inna na sake jawo hankulansu tana kwantar masu dashi,har yesmin ta dan fara dayayewa. Amman fiyah sauraren bugun kirjinta kurin take,zata so tayi ido biyu da wannan mai karfin halin daya aureta,taya zata fara rayuwa da wani namiji bacin ba wanda taje tsara rayuwarta dashi bane........sai hawaye tayi kukanta mai isarta ta hkr. Anayin magruba kawayen duk suka watse sai kawayen yesmin su biyu da zasu jirayi anguna kafin sutai,don baza,a kwana ba gaskiya. Babane ya kira Anty yace tayi maza tazo ta hada kayan da za,a tafi dasu na safiyya suma su idasa hada nasu lokaci na tafiya. On ready daman tun daren biki babban aminin angon yazo ya tai da lefenta da sauran tarkacenta,yanzu kurin kayan sawarta ne datayi amfani dasu za,a hado kamar zatai kuka tace"Anty dagaske dai barinku zan,barin garin nan zanyi nidai wlh bana so har cikin raina banso". Tausayinta ya kamasu inna ta rungumota tace"kwantar da hankalinki diyata zaki samu rayuwa mai kyau,kuma zakiyi mamakin mijinki da ikon Allah,kicire damuwa karki tadama kanki ciwi kinga ba lafiya gareki isassaba" Kai ta iya dagawa kurin tana kwanciya kan cinyar innar,Anty jamila ta shafa kanta ta fice don ganin anata kiran sallar magruba kamata yayi ace tanzu suna airport............ ************** ****************** Fiyah da mama kamar bazasu bar juna ba saboda kuka da jin inama karsu rabu,shi kanshi baban karfin hali yake kurin shine ya janye mamar su yakumbo sukai ciki da ita,shikuma ya kama hannun fiyah ya sata cikin mota,shafa kanta cikin rauni yace"Allah yayi maki albarka safiyya,kamar yadda kikemun biyayya Allahu yabaku xuria mai irin halinki,Allah ya albarkaci zamanku ya baku zaman lafiya,idan naimaki abunda kikejin ban kyauta ba kiyafe mun kinji yar albarka........kuka ta fashe dashi tana riko rigarsa "baba wlh bakayimun komi ba,nice zance ka yafe mun zantai wata duniya inbarku badan raina yaso ba don Allah baba kakula da mama inasonku kuduka,ina alfahari daku zancigaba da yin biyayya gareku don kune jigon duk abunda nazama arayuwa........kuka yaci karfinta duk wanda yake wajen saida yayi hawaye dalha kanshi kukan yake,yaya jalal juyawa yayi yanajin wani iri cikin ransa,lallai wannan soyayya tasu ajinjina mata. "Allah ya maki albarka uwata Allah ya saukeku lafiya kibi mijinki kicigaba da hkr kamar yadda kowa yasanki.........juyawa yayi yakoma don ga kwallarsa nan afili,kuka ta cigaba dayi tana jin inama bata girma ba har ta isa wani aure dazai rabata da iyayenta masu sonta da kaunarta.duk nacikin motar kukan suke amman na hawaye ita kadai akejin shashshekarta. Karfe takwas daidai jirginsu ya tashi sai *Australia* Gobe bazan typing ba gaskiya kila sai dare tunda har kukaja nai maku update biyu at d same time. [10/15, 3:03 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️.............62 Kafin su isa jikin fiyah ya rikice da zazzabi,da ciwon kai sosai duk hankukansu ya tashi addua kurin suke su sauka lafiya,su duka babu wanda ta bata tunanin nan kusa zai hau jirgi saigashi silar safiyya sun hau lallai dole su shimata albarka,ajikin inna balaraba ta rungumeta tana shafa mata addua idan ta karanto mata,sune basu sauka ba sai wajen karfe shabiyun dare suka sauka,nan fa idanun su yahau kalle kalle,har saida Anty tayiwa hasana magana. "Don Allah ki adana kauyancin ki har muje masauki,karkija ayita kalonmu" Dariya sukai su duka fiyah bata san ma mesuke cewa ba,zafin zazzabinta ya saka duk bata ma gane komi. Zaman jiran zuwa daukar su sukai awajen na minty biyar saiga mota har biyu tazo,aka kwashi kayansu aka loda ga but din motar sannan inna da fiyah suka shiga baya,sai abokin angon dake jan motar. Ciki mutuntawa yake gaida inna yana masu sannu da xuwa,tace"mun sauka lafiya yaro amman kam amaryarku ba lfiya don tun ajirgi jikin ya rikice zazzabi sosai ne ajikinta." "Subhanallahi aikuwa to bari mu wuce asibiti ku adubata ko magani sai surubuta mata." "To hakan ma yayi" Waya yayi wa driver daya dauko su anty jamila da hasana yace ya wuce dasu gidan zaikai amaryar asibiti. Kamar cikin mfarki take jiyo muryar malik,amman saita dauka ko tsananin begen Abdoul ne yasa takejin haka,da kuma zafin ciwo da takeji ajikinta,bata dai dagoba tana kwance jikin inna. Suna isa inna ta kamota suna binsa abaya,yaje yayi duk abunda xa,ai taga likita ya dubata sosai yace wannan saitasha drip akwai stress jikinta,da damuwa sune suka sakarmara fever and jininta ya dan hau kadan shima zadai muriketa nakega gaskiya." Inji dr dame magana da turanci shikuma yake ma inna bayanin komi,hankalinta yadan tashi"yaro ya zaai kenan" "Karki damu inna bari muyi magana dashi za,asamu maslaha" Ya fice yabi bayan dr har xuwa offce dinsa. Fiyah dake kwance anmara allura dazata rage mata zafin zazzabin,idonta arufe amman har yanzu ta gaza yarda da abunda xuciyarta take gaya mata,cewar malik ne to idan shine meya hadata da malik ahalin yanzu?bacin ba abokinsa ta aura ba.wata xuciyar ce tace mata to koshine mijin? Xunbur tayi tatashi tana zare ido inna tayi saurin riketa. "Safiyya kina lafiya kuwa menene kika zabura haka" Idonta ta kwalla tana kermar baki tace"inna......wan....wannan dayake magan.....magana waye shi" "Bangane waye shi ba,wani abunne yafaru ko kinsan sane" "Inna waye nidai nake tambaya,? Jin za,a shi go yasa tayi saurin komawa ta kwanta tana rufe idonta,karma taganshi taga dagaske din shine mijinta din yauni nabani Safiyya,kai gaskiya ba gaskiya bane bashine ba mai kama da murya shi ne.........."ya kukai dashi yaro" Inji innar. "Yace zai bada nurse muje da ita tayi mata komi,ta dan zauna da ita har xuwa safe aga yadda jikin yayi sai ta dawo,yanzu tafiya zamuyi gidan." Fiyah nason bude idonta tanajin tsoron ganin abunda take sake tabbatarwa da xuciyarta. Nurse din ce ta shigo ita ta kama fiya suka wuce mota yaja suka tafi gidan,inna sai kallon gari take tana jinjina kai ko amafarki bata taba tunanin haka ba. Ai bata sake shiga wani mamakin ba saida taga gidan da motar su ke danna kai ciki,dogon tsaunine wanda saida ta daga kai tabisa da kallo har iyakar karsheshi........tana zare ido ita dai kome xa,ace wlh saita kalla aibata bata xuwa ba balle ace,haka inna tafito tabi bayansa nurse tana rungume da fiyah saboda bata da karfin jiki har lokacin idonta rufe inna sakin baki da hanci tai tana kallon inda zasu bi sushiga gidan,sai an danna wasu malatsai sanna ta bude babu abunda take sai jinjina kai kamar kadangaruwa. Su anty jamila dasuka riga isowa har sun kammala mata mominta acikin bedrooms dinta sun sake kwata gidan banda kamshi bakajin komi saifa sanyin Ac dake ratsa kiji,har cikin daya daga cikin dakunanta aka kaita sai lokacin fiyah ta iya bude idonta tana karewa dakin kallo,ta ko ina ya gama hadewa komi White and pink color ne na dakin,gwanin ban sha,awa fessss dakin sai rabar saniyi da kamshi yake har saida ta rufa da duvet din da aka shimfida daga bakin bed din nata,hakika itama ta yi kyauyancin don gadon kanshi binsa da kallo take,tunda take ma ita bata tabaganinsa ba. Dandanan nurse din tace asamo mata wani abu taci ta watsa ruwa sannan sai a saka drip din. Cikin kankanen lokaci yaje ya siyo musu abinci isassashe wanda zai wadace su suduka,amman na amarya daban yake saida tayi wankan Anty ta zabo mata kaya marasa nauyi ta canza suka tusata gaba da lallashi taci abincin,saigashi tadanci dayawa don daman tunda aka fara hidimar bikin bata cin komi sai abu mai ruwa shiyasa duk ta rame,drip din aka samata sannan nurse din tace suje falo abarta tayi bacci. Hasana akabari don ta dan jata da fira kafin baccin ya dauketa,don harda allurar bacci akai mata cikin ruwan drip din. "Fiyah kin dace gida anan aduniya dai,sai fatan nacan dinma kidace kamar haka,wlh gidanki yayi bala,in haduwa gaskiya ki yadda maka manki kiyi rayuwarki mai kyau,bafa kece akafara yin irin wannan auren akanki ba.kuma naga ma mijin naki kamar nasanshi wlh amman na manta inda nasanshi,ki godewa Allah kiyi miji inhar wanda Anty ta nuna man ne.mun samesu anan harda yan gidansu kinga wai yadda suka tarbemu" Idonta rufe tana sauraren maganganun hasana yayinda gabamta yake bugawa,tabbas ita kanta tasan gidan yakai makura wajen kyau,kuma yayi mata yaburgeta amman ita bata san awane matsayi take ba wai waye wanan da bai nuna mata kanshi ba. "Naji ki kyaleni da maganar nan haka" "Uhmm zan kyaleki idan kinyi bacci amman inhar idonki biyu wlh santin gidan nan zan kamayi maki,wlh ni banma taba ganin miji da matar dasuka dace irin ku ba uhmmm zanso ganin yaranku wlh" Dammm taji gabanta ya fadi data san abunda xa ai har asamu yaran,tabdijam aikwai aiki gabanta wanan abunne zai yi mata tsananin wahala ta dauki budurcinta taba wani,wanda bata taba tunanin yin raywa irin wannan dashi ba,saitaji tausayin kanta dole fa wataran zaici karfinta kuma koba wannan,hakkinsa ne Allah zai kamata da lafin hakan inko har hakane dole ta xubar da duk makamanta ta rungumi kaddararta. Haka hasana taita mata surutu har bacci ya dauketa hasanar ta fita tabarta. Zuwa safe jiki yayi sauki sosai ta nemi ciwon ta rasa saidai abuna ba,a rasa ba na gajiya da rashin kwarin jiki,nurse din ta rubuta magani tace asiyo ta ringasha saida aka siyo sannan tatafi,sai lokacin Anty da inna suka jata dole saita kewaye gidan ta gani,daker ta iya binsu sako da lungu data gaji ta dawo falo ta zauna tana kalonsa,hakika komi sai sambarka yanzu damuwarta tafiyarsu anty gashi sunce gobe zasu juya,ai tunda sun kawota sunga waje Allah yasaka albarka,sai sundawo suna wannan kalmar ta sai sundawo suna ita tasata kuka har kanta yayi ciwo. Dadaddare suna hira falon ga kallo sunayi wanan mai murya irinta malik yayi sallama ya shigo,bayansa wasune dauke da kwalaye da ledoji manya yaudai saitaga waye wannan mai muryar yaya malik........jiyowa tai ta sauke idonta akansa yana murmushi suna gaisawa dasu Anty............duk idanunta ta fiddo tana zuba mashi su cike da tsananin mamaki da alamomin tambaya,amman sai ya wayence yana gaidata. "Amarya barka da dare ya bakunta".sarawa kanta yayi mehakan ke nufi miyanta ya kafe daker tayi gyaran murya tana yake tace"ina wuni" Kin ansawa yayi yana dire kayan gabansu yana ware wasu yana bayani. "Inna ga wadannan kayayyakin zaku tai dasu gobe duk nakune,inji angon yace kuyi hjr da safe zai zo kuyi sallama wadannan kuma amarya bari ashigar maku dasu store" Ya fada yana duka wa yana daukar su ya nufi store din,da murmushi fuskarshi bin bayansa tai da kalo kamar wata sakara kafin ta sauke wata nannauyar ajiyar xuciya tana dafe goshinta,duk a rikice take wannan lamarin da daure kai yake. Fitowa yayi yana cewa"zan wuce Anty saida safen zamuzo tare yayi maku sallama" Godiya sukai sosai suna saka mashi albarka. "Gaskiya mutanen nan suna da kyauta Allah dai ya zaunar daku lafiya safiyya kiyi hkr kinjiko,aure babu inda baya kai mutun kuma ki saki jiki da yan uwan mijinki suna sonki suna ji dake,shima kiyo kokari ku gyara tsakaninku Allah yabarku tare" Inji inna hasana na mata gwalo da dariya. Cikin muryar kuka tace"inna kinganta ko,dariya take mun tana mun gwalo" Murmushi innar tai tana ma hasana fada tace"kema kwanan nan zamu tsayar da magana ai,nagaji da laben da jalal yake mana duk sadda yazo,ana fakewa da zumunci" Duk mamaki da al,ajabi ya kama mu nida anty,itakuma tana rugawa daki tana cewa inna tayi shiru. Anan innar kecewa ai sun kai shekara suna soyayya shirutai dai taga gudun ruwansu,ganin basu d niyyar baiyyana kansu yasa tace zata gaya ma su baba. Abun ya mana dadi sosai har hakan yasa nasaki jiki dasu muka sha hirarmu ta bankwana,jinake inama zasu zauna dani amman nasan hakan ba mai yuwuwa bane. Bamu kwanta ba sai karfe daya ranar banyi bacci ba tunanika suka cika xuciyata,ina cikin kokwanto komi ya cushe man.duk yadda naso baccin gagarata yayi nai salla raka,a biyu na roki ubangiji daya sakamun salama acikin xuciyata,ya sanyaya mun raina nayi zaman aurena kamar kowace mace,ya ban ikon yin biyayya wajen mijin da bansani ba yaba ikon danne duk wani miki na soyayyar danake ciki. Rashin baccin yasaka na kamara sadda na tashi na nemi su inna ban gansu ba,duk inda zan ga daya naduba babu su dakin da suke kwana arufe falo na dawo na zube gefen kujera ina kuka,meyasa xasu tai bamuyi sallama ba meyasa haka kuka nake sosai da sosai. Gashi ko karya wa ban ba kuma yunwar nakeji sosai,na kasa tashi naje dining naci abincin tunda gashi can ankawo. Ina nan zaune naji anshigo mata ne biyu suka shigo turawa ne suduka,gaidata sukai suna cewa sune masu aikin gidan dayar zata iso. Kallonsu tai cike da haushi tanuna masu hanyar cikin gidan,tana binsu da harara kamar sune sukai mata laifin. Saida taji yunwa na niyar kassarata taje tahau cin abincin,tana hawaye gashi bata taho da waya ba mama ta barwa wayarta. Haka ta wuni cikin kewa daga tai salla taci abinci saita kwanta,har gajiya tai da yin bacci ita bata saba zaman haka ba babu aikin fari balle na baki,ahaka dare ya cinmata duk atsorace take haka tayi wankan ta ta dawo falo tai sallar magriba,itama sallar badan alam dake bugawa ba duk time dinta bazata gane ba,don bataga agogoba,itafa atakure take bata saba da wadannan abubuwan ba tafisaba wa dana kasarta nigeria. Tana gama salla mai aikinta linder ta iso cikin girmamawa tamika mata waya. Ansa tayi tana binta da kallon tambaya,cikin harshen turanci tace mata"ogane yace abaki akwai sako aciki kiduba" Harara ta maka mata amman ba gane metake nufi da hakan tai ba,ta juya ta koma bangarensu. Duba wayar ta cigaba dayi tana shiga ko ina bata ga komi ba,tsaki taja ta ajiye tana rabka tagumi,bayan minty biyu taji sako yashigo har kerma hannunta yake ta dauka tana dubawa. _"KIYI WANKA KISHIRYA IN THE THIRTY MINUTES AND WAITING FOR ME"_ kallon wayar take kamar zata cinyeta don haushi,au bazai iya kiranta ba saboda girman kai,shin wai taya ma zata iya zama da wannan bahagon mutumen.kodan yana ganin yana da kudi zaimun wulakanci shiyasa ya kawoni kasar da babu uwa babu uba babu dangin iya balle na baba,hawaye suka silalo mata tana sharewa itafa tasan sun kulla amana da kuka yanxu.daman gata sa arhar kuka,kallon jikinta tai taga bata jima da wanka ba,kawai dai kayan baccine jikinta. Tatashi tanufi bedroom din cike a tsoro,bata saba zaman gidansu babu kowa ba balle wannan uban gida mai girma ga sako da lungu gani take kamar wani xaixo ta shaketa ya kasheta yajefar da gawarta..........wani marron less ne da zanen manyan flowers milk sai kyalkyali yake,baya da nauyi shiyasa ta daukoshi riga da siket ne siket din yayi bala,in fitar da shaf dinta don randa ta fara sasu ranar alhamis din auren mutane sai magana suke gaskiya amarya tasha kyau,masha Allah tubarkallah.karshe saboda haushi ciresu tai saboda bata son ma abunda zai sa ace tai kyau abikin da ba sonshi take ba. Ajiyar xuciya tai bayan ta sak kayan,rigar irin mai budaddar kafadar nan ce akai mata,an kawata gabanta da wani style mai kyai. Powder ta saka da marrom din janbaki wanda ya sake fiddo ruwan kyanta kunsan fararen mata idan suka saka jan janbaki ko marrom sosai yake masu kyau. Saida tasa taji kamar ta goge,amman ganin bata fuskarta zatai yasa tabarshi.gyalenta dan karami wanda iyakarshi rolling shita dauko ta nade kanta dashi bayan gashinta data gyara ta saki jelar baya,bata aka kallabin ba rolling din kurin tayi tana saka kwalli ta gyara girar idonta sannan ta saka turaruka dake jere akan mirrow dinta,kala waje biyar kowane da kalar kamshinsa. Yar pos dinta milk da high hills dinta suma milk,ta saka masha Allah saita fito sak amaryarta tayi kyau sosai don fiyah bata taba kyau irin na yau ba,don ita kullum cikin hijab shiyasa baka gane dirin da Allah ya mata. Ahankali take takawa tana barin dakin,ita kanta saitakejin ta wani iri jinta take kamar wata sabuwar halitta,tasha ganin mata abuja irin yadda tai wannan shigar,saitake ganin Allah ya sawake tayi wannan shigar tafita,saigashi yau tayi kuma tana ganin tayi kyau amman kunya takeji tafita haka kamar za,aita kallonta saboda bata sa abaya ba. Falon ta koma tadora kafarta daya kan daya,tana kallon wayar da linder ta kawo mata. Minty talatin yana cika aka danna dow bell cikin sassarfa wannan arniyar tazo ta bude tana risina wa. Kalon kofar fiyah keyi tana kallon mutumen dake bakin kofar,bakinta taji yace"yaya mali" Murmushi yayi mata yana sallamar linder dake sunkuye. Hanya ya nuna mata da hannunsa yana dan rissinawa irin girmamawar nan,kamar sakara take binsa da kallo.ta kasa shigewa gaban kasa shanye mamakinta tayi karo na biyu tace"yaya malik kaine" Murmushin yake yana shafa kanshi baice komi ba yace"plzzzz let's go" Idonta yayi kwalkwal zatai kuka yagirgiza kai. "Karki bata kwaliyarki mana muje" "Bazanje KO ina ba saika yimun bayanin me ake boyewa man,ni nagaza gane wa" "Sorry muje zaki fahimta yanzu lokaci yana kurewa" Dole ta hkr ta shige gaba ya rufe kofar yana binta abaya har waje,wajen mota ya bude mata baya ta shiga ya shiga gaba shida driver suka dauki hanya. Gaba daya tunaninta ya rabu kashi kashi,xuciyarta tayi rugurugu da tunani wai wata aura ne meyasa ma tun tuni bata damu da sanin waye ba,saiyanxu da take son sani ake ja mata rai. Tafiya sukai wadda bata wuce minty goma sha biyar ba,suka iso wani plat din gida mai kyau shima tundaga kofar gidan zaka san an shirya wani gagarumin abu,docration ne akayi ta ko ina ga fitilu sun haske wajen saikace safiya ce,wani kafet ne aka malala tundaga bakin motar da zata fito har xuwa inda zata zauna acikin gidan,tsaye tai tana kallon malik shikuma yana mata murmushi mai kyau,kamar dazun yanzu ma risinawa yayi yana bata hanya jikinta yayi sanyi kalau ta kalli hanyar sannan ta fara kokarin binta ahankali kamar mai tausayin kasa kamar jira ake tafara tafiyar..........wasu flowers masu kyau kala daban daban suke sauka bisan kanta,tare da wasu kyalkyali masu daukar ido suna ta zubowa daga ko ina,kuma bata ga wanda yake xubo dasu ba.abun idan kagani saiyayi bala,in burgeka saiya baka sha,awa malik ke binta abaya har cikin babban tangamemen falon da shima ya gaji da haduwa,anyi mashi kwalliya fiye da ta wajen ga high tabke can anjera lemuka sunkai kala takwas,ga cups biyu da katon cake dogo mai hawa hawa,anmashi kwalliya kalar kayanta. Wutar Wake ta dauke sai dumlight dake haskawa yana walwalin kaloli daban daban. Tsaye tayi tana kallon malik high table din ya nuna mata yana ta murmushi mai kyau,jiki asalube ta hafa hawan steps din har ta karasa wajen kujerun ta zauna tana zama ta nemi malik ta rasa awajen,hankalinta tashe kirjinta bugawa yake sosai cikin second dabaikai biyuba tag walau haske ya bayyana ta ko ina wannan kyelkyelin yana tashi kamshi ta ko ina kida mai sanyi da sanyaya xuciya yana tashi awajen,kafin waka mai dadi tafara fitowa da turanci tana jin wata kalma cewa *HAPPY MARRIAGE LIFE FOR UR'S* kafin taga mutane sunfara fitowa daga ko ina daga cikin wanna aba falo,suna bin wakar happy marriage life din dake tashi jitai anrufe idonta daga baya ta bi hannun tana tabawa bazata iya gane kowaye ba,amman kamar macece ahankali ake zare hannun tayi saurin jiyowa tana bin mai rufe mata idon ta kallo. Zaro idonta tai bakinta yana furta. *"ni,imah"* Dariya take kyalkyalwa tana riko hannunta tana ta dariyar,bata gama shan mamakinba taji runguma daga bayanta cikin sauri ta dago tana sake dararo idanunta tubarkallah. *"zakiyyah,mami"* Dariyar suke mata suma dandanan tafara fara,a kwallah na fitowa daga idonta,zakiyya ta share mata tace "surprise again" Cikin tsananin farin ciki tace"again zakiyya" Daga mata kai tayi tace rufe idonki kadan to babu musu ta bude jitai ta saka hannunta cikin wani tattausan hannu mai kama da auduga,sannan tana jin wani sassanyan kamshi mai narkar da xuciya numfashi taja tana neman susucewa,ahankali zakiyya take zare hannunta daga idonta tana dariya tace "see ur husband" Kamar mai ciwon wuya take jiyawa ahankali take kallon gefenta tanajin numfashinta yana neman guduwa saboda rikita. Idonta ya nitsa cikin nashi wanda daga ita harshi saida numfashin kowa ya nemi guduwa. Bakinta abude idonta da kwallar farinciki nunashi take, tana kallon su zakiyya daketa masu dariya ita dasu mami da ni,ima ga malik rike da hannun zakiyya suna ta sakin murmushi. mutane kuma sunata kallonsu gwanin ban sha,awa. Labbanta rawa suke suna kerma hakoranta suna bayyana tsantsar farincikinta tace. *"yaya Abdoul kaine,dagaske kaine"* Naga Adduoin ku ngd sosai insha Allah mun kusan kawo karshen wanan book kuyi man fatan kammalashi lafiya. [10/17, 10:42 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........63 Baice komi ba illa kyawawan idanunsa dasuke ta kallonta kamar yauce rana tafarko daya fara ganinta. Malik da zakiyya suka iso wajensu zakiyya tariko hannu fiyah shima malik ya riko na Abdoul suna kallon juna,photographer ya yi masu kyakkyawan hoto sannan kiyya ta jawo fiya malik ya jawo hannun Abdoul suka hade hannayensu waje guda,suduka bin hannuwan nasu sukai da kallo kafin su dago mai hoton ya daukesu,nan fa yacigaba da kashe masu kala,wani dayayi kyau sun kurawa juna ido su kansu basu san ma hakan tana faruwa ba,don baki daya abun yazo masu acikin bazata. Kafin akaimasu baki daya na family,dady da Abbi ne kurin babu sai gobe zasu iso. Kafin sujuya baki dayansu,wajen zamansu suka nufa suka zauna amman gabaki daya fiyah gani take kamar mafarki take,saita kallai ta sadda kai shima saiya kalleta ya dauke kai.fuskarsa bazaka ce yana murmushi ba haka bazakace yasha mur ba,kadaran kada han yake itace dai kallo daya zakai mata kasan cewa tana cikin farin ciki,kidan ya cigaba da tashi masu rawa nayi masu shan drinks nayi,fiyah kallon zakiyya take yadda duk inda malik yayi tana biye dashi,kuma hannunsu cikin najuna.kuma bata ga wani ya nuna hakan wani abu bane,mami ce ta iso wajenta ta dafa kanta. "Diyata mekikeson ci" Sadda kai tayi tana murmushi cike dajin kunya tace"aa mami ba yanzu ba" Kallon Abdoul tayi tace"son kaifa" Dage girarsa yayi yace"ba yanzu ba" Murmushi mamin tai tana cewa oky ..........bayan wani lokaci kuma akazo za,a yanka cake wukar tana hanunta saiya dora nashi hannun bisan nata suna yankawa tare,mai hoto yanata daukarsu. Cirowa tayi ta kai bakinsa ya tsura mata ido yanata kallonta,baidace komi ba yajima idonsa kamar zaifado saboda kallonta sannan ya bude bakin yagutsira,haka shima ya bata sannan sukabi kowa suna saka mashi ga baki.sune har karshe shabiyun dare anata abuguda,karshe har nafara hamma hakan da mami ta gani yasa tacema malik atashi hakanan kowa yaje ya kwanta,ai angode Allah ita dama bada son ranta aka hada partyn ba duk zakiyyace da ni,ima. Hanuna cikin na mami tajani har dakinta daya gaji da haduwa komi yayi gwanin sha,awa. Zaunar dani tai bakin bed dinta ta shiga toilet ruwan wanka tahada mun daga inda nake inajiyo kamshin turaren wankan da take xubawa,don inajin ma ba daya bane gaskiya. Fitowa tai da towel ga hannunta ta bani. "Shiga kiyi wanka kifito saina rakaki dakinki,abincin ki yana can yana jiranki" Cikin jin kunya tace ansa da to mami,sannan ta shiga toilet din tajima tsaye tana kare mashi kallo,kamar wani wajen shakatawa gaka bayin yake komi gwanin kyau da burgewa. Kayan ta cire ta shiga cikin komin tana lunshe ido,ruwa mai dumi mai gasa jiki ga kamshi na gaske dake tashi,tabbas wanan zai jima jikinta bai fita ba. Akallah ta dauki minty goma sha biyar kafin ta iya fitowa tana tsane jikinta sannan ta dauro towel din,ta fito. Wasu kayan bacci ta gani riga da wando dogon wandone har kasan guiwa,sai rigar mai gajeran hannu kayan masu tsananin kyau da taushi.lotion ta shafa sannan ta fesa turare tasaka farar powder kasan da lipstick,ta gyara gashinta ta daure da ribon ta saka hular kayan. Tayi kyau Sosai da sosai har saida tayi murmushi,wata natsuwa takejin tana shigarta ta daban,jitake yanzu bata da sauran damuwa baba ya riga ya gama mata komi illa ta dawwama tana mashi fatan Allah ya biyasa da aljanna. Mamince ta shigo ta bata hijib kamar tasan bazata iya fita ahaka ba murmushi tai tana sada kai ta ansa ta saka. "Kibar jin kunyata har haka safiyya kamar ni,ima nake kallonki don Allah karki doraman nauyinki nima nafison muna yin abu irin na diya da uwa,kinjiko ki saki jikinki nima kamar mamanki ce" Tana wasada yatsunta tace"insha Allah mami zanyi yadda kikeso" "Yawwa Allah yayi maki albarka muje na rakaki" Tafiya suke har xuwa wani part din na daban,shima ba baya ba wajen kyau komi ya hadu har bakin bed room ta rakani tace"akwai abinci nanan an ajiye maki kici kisha ki kwanta saida safe" "Nagode mami mu kwana lafiya" Ta ansa mata cikin kulawa sannan mamin ta juya tatafi,fitowarsa wanka kenan yana shiryawa cikin kayan baccinsa hankalinsa kwata kwata baya tare dashi,abubuwa sun cunkushe mashi kai!wai suna nufin anyi aurensu da safiyya how comes tayaya bacin tace bata yinsa kuma babanta yace bazai bashi ba,duk ciwon dayayi akanta hakan baisa ya ce ya amunce ba su dady da Abbi babu irin zaryar da basuyi wajensa ba ya rufe idonsa to shine kuma bayan ya warke anga bai mutu don itaba aka daura auren.uhmmmmm tabbas sun bashi surprise kuma yagode don baiji koda daidai da kwayar zarra na sonta ya ragu ba,amman saiya rama abunda tai mashi.ya ajiye duk girman kanshi da ajinsa ya furta mata yana sonta yaringa zarya gidansu,amman ita anbata zabi tarufe ido tace bata san haka ba.murmushi yayi bai taba zaton cewa zai sameta ba,ba kamar dayaji labarin aurenta wajen malik...........turare yake sawa yaji anbude kofa jiyowa yayi yana kallon kofar,don yasan kowa ya kwanta saboda gajiya tun kwana biyu basu zauna ba sai hidima suke yasan dai an daura auren malik da zakiyya,duk tunaninsa hidimarsu ce ba tashi ba. Tsura mata ido yayi kamar yadda ta tsura mashi nata.jikinsa mutuwa yayi irin mutuwar da baitaba ji ba har saida ya runtse ido sannan,ya ajiye kwalbar turaren tana rungume hannuwa sadda kai tai tana murzar yatsunta cikin abayar,bata dauka daki daya zasu kwana ba aida bata shigo ba. "Lafiya malama,ko kinyi batan hanya ne" Kallonsa tai da mamaki jin abunda yace girarsa ya daga yace"ehy,waye yace nan ne dakinki" Kamar mai koyon magana tace"mami ce ta rakoni niban sani ba ai,kayi hkr" Tana jiyawa tanufi fita. "Wait" Ta tsaya tana jin gabanta yana faduwa ga duk alamu Abdoul fushi yake dan ita,kuma tasan hakan zata faru don abunda tai ita kanta ya dameta amman bata da yadda xatai da baba alokacin. Bayanta ya tsaya yana rungume da hannayensa yace"ina kuma zaki,bakince mamice ta rakoki ba its oky shigo ki kwanta" Jiyowa tai tana narai narai da ido ta girgiza kai"kabarshi zanje falo kayi hkr pls" "Okay kijamun abun magana ko,to ban amunce ba nace ki wuce halan ma wancen abin ba nau bane shiyasa kiyya har take rawar jiki waje jerawa" Ya nuna wani table da aka jera kuloli masu kyau da lemuka. Jujjuya kai tayi cikin sanyin jiki tace"ban sani ba ance dai abincin yana nan" "Okay muje ki dan sanmun yunwa nakeji" Ya wuce wajen table din tana biye dashi baya,kallonsa take kamar ancanza shi yayi rama sosai kuma ya kara haske da kyau.gashi ya sake barin gashi afuska saiya kara mashi kyau,dakin sai kamshi yake. Kujera yaja guda biyu dake zagaye da table din ya zauna itama ta zauna kan guda,shiya bubbude kulolon ferfesun kifi sai faten Irish yasha ganyenyaki,kaza gasassa da lemuka masu sanyi. Kalonta yayi yaga duk ta takure ya dauke kai,ya zuba nashi ya hauci baibi ta kanta ba,yana gama wa yaje ya haye gadonsa ya juya mata baya. Duk abunda yake na karfin haline,ba har xuciyarsa ba yana son dai ta gane cewar shi Santa yake da xuciya guda ba wani abu yake nema ajikinta ba. Hawaye suka silalo mata tashare,tatashi ta kwanta kan kafet din dake malele adakin tana dunkulewa cikin hijab dunta,me hakan yake nufi me yakesin nuna mata,wanan daren daga shi har ita basu runtsa ba saida ya tabbatar tayi bacci ya daukota ya sata gabanshi,tusata yayi kamar tv yana kallo haka asubar fari taxo mashi Kuyi hkr zuwa anjima zan sake wani postinig din kkda read more biyune [10/17, 4:57 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️............64 Tsintar idonsa tai cikin nata daidai zata juya kenan taji kamar kiran salla,kuma acikin dakin take jiyosa Kamar alam ne akasaka mai kiran salla idan time yayi,dauke kai yayi daga kallonta yasha mur. "Meya kawoki kan gadona,harda wani shishshigeman cikin jiki keda bakisona miye na kwakwata kuma" Zaro duka idonta tayi tana kallonsa tana kwalkwal da ido cike da son yin kwallah cikin muryarta ta bacci tace"wlh nibana kwakwarka kuma bani na hau gadon ba,Allah ma ya sani ni akasa na kwanta saidai idan..........tsura mata ido yayi yana kallon lips dinta sun mashi kyau sosai ya karkace kai yace"saidai me?saidai idan ni nine na daukoki ko saboda ina kwakwarki zanbiki har kasan kafet na daukoki,to inmaki me?" Harara ta watsa mashi tana tashi zaune taja blanket din xuwa kirjinta saboda babu hijab ajikinta,hakan yasa ta tabbayar shine ya daukota zai rena mata wayau. "Nafa gajii da halin da kake nuna mun daga jiya zuwa safiyar yau,wai ce maka akai nima damuwa dakai nai don Allah ka sallamani inhar dole akai ma" Tatashi tana saka abayarta ta shife toilet tayi fitsari tayi alwalla tafito,tana shan mur. Danne murmushinsa yayi yace"ke nida dakina zaki yimun rashin kunya,Wlh zan turaki falo duk sanyin dake can yakare kanki daga an rufa maki asiri" Wata hararar ta danna mai tana neman abun salla,"kaga banda lokacinka" Ta nufi inda taga an killace shi donyin salla saidai kuma wandonta bai kai mata har idon sawuba,kuma abayar itama bata wuce guiwa ba. Kauda kai yayi yana dariya can kasan makoshi,yaga yadda xatai sallar ai dole dai yakawo wani taimakon.satar kallonsa tayi taga ya juya baya yana kashe alam din daketa ki faman kiran sallah. Ganin bata ita yake ba yasa ta dan waigo "don Allah........" Mikewa yayi ya nufota dan danan kuma gabanta ya fadi,runtse ido tai tana adduar karya iso inda take amman adduar bata ci ba daf da ita ya tsaya har yana goga goshinsa anata dan danan ta mamuke jikinta tana runtse ido. "Kaga fa salla zanyi lokaci yana tafiya kuma bacci nakeji" Kuncinsa ya dora bisa nata idonsa rufe kamshin dake jikinta yakeji yana sashi wani yanayi,don baisa ma meyake shirin yi ba. "Ban hanaki ba ai,kiyi sallar ki" Kamar zatai kuka tace"ai ka tareni ko" Murmushi yayi yana jaye abayarta ahankali ahankali har cinyoyinta suna bayyana ya dora hannunsa akai.........numfashinta taja tana rike hannunsa "ahaka zaki sallar xindir" Kasa ta silale tana soka kanta cikin cinya tana jin kunyar duniya tana rufeta,har yanzu jitake hannun nashi yana cinyarta. "Tashi na baki kayana kisa" Babu shiri ta dago tana kallonshi cike da zare ido. "Allah ya kyauta nasaka kayanka" Dariya yayi yana nufar wadrop din kayansa yana budewa. "Yanzu kuwa zaki ga ikon Allah" Kallonsa take ita duk gani take kamar bashi ba,duk ya canza gaba daya tashi tai tsaye tana raba ido ita kam yau taga haza harda haxihi. Jallabiya ce ya dauko fara kal sai kamshi take,kuma zata shigeta saidai tsawon ne zai mata yawa. Mika mata yayi daga ina take"zoki ansa kisaka kokuma yanzu kiga ikon Allah" Babu musu tataho tana rabewa gefe ita wlh duk ta takure ita yau wata irin kunyarsa takeji,kamar ta bace ko tashige cikin bango. Mika hannu tai zata ansa taji yajata dakarfi xuwa jikinsa ya matse...............abun yazo mata bazata gaba daya jikinta ya dau rawa,dan danan kuma taji ta nemi natsuwarta ta rasa mutsu mutsu kurun take tana son kwacewa amman yayi mata riko bana wasa ba. "Zaki saka ko ni nasa maki,gardamammiyar yarinya kawai daga yau idan nace ga abunda zakiyi banson musu just do it kawai." Daga kai take kamar kadangaruwa tana kermar baki"to kasakan wlh zansaka Allah zan saka" Murmushi yayi ya tallabo face dinta yana kallon yadda ta rufe dukan idanunta,saiyaji sha,awar ya sunbaci idon nata. Ahankali ya matso da bakinsa ya mata sunba kan kowane idon nata,sannan yace "oya open ur eyes" Girgirza kai tayi ahankali kuma saita fara budewa tana zube mashi idon nata akan fuskarshi,gira ya daga mata yace "are u oky" Daga kai tayi yace"oky bari muyi jam,i zakiyi dani ko" Nan ma daga kai tayi ya saketa yana nufar bayin shima. Wata nannauyar ajiyar xuciya ta saki tana nufar inda ake shiga asaka kaya taje ta cire na jikinta tana sauri karya zo ya sameta,fadin ya yi mata yawa amman daga kasanta hips dinta sun cika kasan,sai tsawon daya mata yawa shima. Kalon kanta tai ga mirrow din dake wajen taga kuma tai mata kyau,saidai saman ne ya mata yawa Allah yasota bata cire bra ba da kirjinta yawo zaitayi aciki. Jin anbude kofar toilet din yasa ta fito tana sanye da abayar,kallonta yayi yana murmushi ya je shima ya canza kaya xuwa jallabiya yajasu sallar,karatunsa gwanin dadi kamar ya daina ashe daman ya iya qira,a haka aikuwa nan gaba idan komi ya daidaita zairinga mata kari don ita inda yake jawowa ma bata kawo nan ba. Suna sallamewa kowa yaja gefe yana azkar dinsa,amman kadan kadan sun saci kallon juna. Idan ya kamata tana kallonsa sai yayi mata murmushi kawai,idan itace ta kamashi yana kallonta saita watsa mashi harara jinjina kai yake ya rabu da ita ahaka har suka gama,zaman cin tuwo yayi yana kallonta yace"good morning love" Sadda kai kasa tai tana jin yana kashe mata jiki,ashe dai darabon zasu sake ganawa ashe dai darabon su mallaki juna,aduk sanda ta tuna saitayi wa baba addua marar iyaka. Ahankali tana wasa da hannunsa da yasha kunshin biki tace"ina kwana" Jingina bayansa yayi da abun gado yana ajiyar xuciya yace"bani nafara gaidaki ba" Murmushi ya kubce mata ta sake boye fuskarta tace"ai babba baya gaida karami inko har karamin ya ansa to ya cika marar sanin girman na sama dashi" Dadi yaji ya kamashi yace"oky to as from 2 day damun gama salla inason gaisuwarki ta fara shiga kunnena,are u hear me" "Insha Allah" Shiru sukai kowa da tunanin dayake hannunta hake kallo kunshin yayi masifar daukar hankalinsa,kamar ya kamashi yayita lasa.kamar kurame haka suka zama,jawo system yayi yana dannawa bakuma don yasan me zai ba,kawai dai yana son ya dauke hankalinsa daga shagala da kallonta basu ankaraba Alam ya buga karfe takwas,xunbur tatashi taje ta cire jallabiyar ta ajiye mashi gefen gado ta nufi kofar fita. "Ina zaki" "Wai kitchen naga time yana wucewa koba ku break da wuri anan" Baisan meyasa gangar jikinsa takeson rusa mashi plans ba,runtse idonsa yayi sannan yace"xonan" Ahankali take dawowa ta rabe gefensa ya ajiye computer ya matso kusada ita,kamar zai rike hannunwan saiya fasa yace"keda kike amarya waye yasaki shiga kitchen?" Soke kai kasa tai batace komi ba. "Ko kin manta amaryace ke?" Girgirza kai tayi yace"halan kurma kika koma" Shagwabe fuska tai bata san ma tayi ba tace"to ni ai nasaba agidanmu ko" "Ai yanzu tattalinki ake idanma mami ta ganki kitchen nabani ai" Kallonsa take cike da tambaya "to miye" Zaro ido yayi yace"ai ita yanzu ma duk tunaninta kinan kwance babu lafiya me zai iya fiddoki" Har lokacin kwalwarta bata bata komi ba,kallonsa take yadda yake murmushi tace"nifa ban gane ba,mezai sameni to bacin na warke" Matsowa yayi yarage murya kamar wani yana jinsa yace"kin manta kenan,ina nufin ai kowa gani zai na angonce yau kinga ai zasuga kinan kwance ina..........bata san sadda ta tashi ta shige toilet ba ta rufe kofar. Me zai inba dariya ba rabonsa da dariya irin wanan bazaie ga lokacin ba. Knocking din kofar falon yaji anayi ya tashi ya fita yaje ya bude,ni,ima ce da kaya ga hannu tace"yaya ina kwana" "Lafiya lau wadannan kayan fa" "Anty safiyya mami tace akoma wa" Bata hanya yayi tashigo ta ajiye su bisan kujera tace"mami tace karfe tara kufito ayi break su Abbima har sun iso" Jinjina kai yayi yana daukar kayan yana wuce wa dasu ciki. Har lokacin tana toilet din ya ajiye ya isa bakin kofar yace"ki budemun na shigo wanka zayi idan ke bakiyi" "Don Allah yaya Abdoul katai falo idan na gama saika shigo nidai wlh kana sani jin kunya don Allah karka kara"tafada cikin muryar kuka har da kwallarta. Dariya yayi yace"oky kiyo wankan bazan sake ba natai falon ina jiranki" Ya haye gado yana dariya kasa kasa wankan ta tube ta shiga yi da ruwa mai dumi,tayi anfani da kayan wankanshi ta jima kafin ta fito daure da towel dinsa tunda yace mata yana falon,ko kadan batai tunanin yana nan ba,kanta tsaye ta fito bata kali gadon ba ta nufi kayanta tana dubawa ta dauki karamin towel taa tsane gashinta...........sakarai ya koma ya saki baki da hanci yana karewa halittarta kallo,bata ankara ba saida taji kamar motsin mutun sakin karamin towel din tai kasa tafasa kara don har ga Allah ta tsorata bata dauka da kowa ba aguje ya sauko ya riketa tamau yana rufe mata baki "Keee karkitara mana mutane" Shiru tai ajikinsa yarungumeta suna sauke ajiyar xuciya tare,shafa kanta yake ahankali yana bubbuga bayanta ahankali har yakaita bakin mirrow.ya zaunar da ita, Kwalla sharrrr suka xubo mata saboda tsabar kunyar da taji tama rasa mezatai. "Shiiiiitt kukan me kike" Fashewa dakukan tai "nace maka katai falo meyasa ka zauna ehy,nidai don Allah karabu dani inshirya da kaina katai kaban waje" Juyawa yayi kurin with out say anything,sai taji bata kyauta ba koba komi dai mijinta ne yanzu. Amman kuma idan ba haka taiba bazata shirya cikin kwanciyar hankali ba,shiryawa take cikin natsuwa tasan fushi yayi bazai dawo ba. Doguwar rigace irinta indiyawa tayi masifar hawan jikinta komi fito masha Allah,sai dan mayafin rigar pich color be da dark pink rigar sai style din ya sake fiddo kyan rigar da wadda ta saka ta. Simple make up tayi don kayanda ni ima ta kawo harda kayan shafa tasan dakin namijine ba lallai asamu irin kayan shafe shafen mata ba. Tasa turarensa kadan don karya ringa tashi dayawa, Tafita falo jiransa shima baijima ba ya fito cikin suit yaa rike da rigar saman baikai ga sawa ba,sai farar dake cikin kawai sai agogo da bakaken takalma yayi kyau amma ta kasa fada wuceta yayi tabishi baya suka isa cikin main falon gidan kowa ya hallara su daman akejira daga nesa take hango zakiyya tana mata dariya,duk saitaji kunyarsu ta kamata kowa zai mata kallon sunyi wani abu bacin ba suyi komiba [10/18, 5:00 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️............65 Bayan angama break dady yajawo hankalin kowa anan yafara nasiha da nuna karfin kaddara da kuma rabo,duk inda kake inhar abu rabonkane saiya tadda ka yabada misali da auren fiyah da Abdoul yake cewa. "Har Saura sati daurin aure bamusan da cewar babanki zai bamuke ba,mun riga mun hkr shima kuma ya hkr kwatsam saiga kira daga maigadin gidan yaya(watau baban Abdoul kenan)yace malan kabir yana neman mu agaggauce,cikin hanzari muka samu visa bamu sanar dasu ba nan mundai ce kirane daga wajen aikinmu. Alokacin yake gaya mana yana son mubada sadaki da komi sati mai xuwa za,a daura auren tare da kanwrki,amman yace muyi shiru soyake ya maku bazata abun yayi bala,in yi mana dadi Abbinku kamar zai mashi sujjada din jindadi,haka muka bayar da kudi da komi sanan nayowa maminku waya cewar zan turo salamatu ta tayata hada lefe kala biyu,don mun yanke hukuncin harda na malik za,ahada rana guda ayi. Kuma ranar na zagayowa aka daura danaku dana malik da zakiyya,malik din kadai na sanarma wa saboda hidimar zuwanki don haka kudauki wannan matsayin darasi,inhar rabonka ne abu to kocin rami saiya bika saidai idan rabon yana nesa zaijima baizo ba. Don haka ina mai jawo hankulanku daku zauna da juna lafiya,kuyi hakuri da juna duka rayuwar bakomi ke isarbawa ba sai hkr,zamane bana yau ba bana gobe ba anafatan mutuwace zata raba,don haka ku matan kuzama masu biyayya ga mazanku sannan kukuma kuxama masu adalci da kyautatawa garesu,don haka ina maku fatan alkairi garayuwar aurenku Allah yasa maku albarka yabaku xuria dayyiba,ga tawa kyautar ga amare." Ya ciro check guda biyu yace"gashina kowace tana da miliyan biyar biyar" Zaro idanu mukai nida zakiyya muna kallon juna ya mika ma Abdoul guda ya bawa malik guda "kubasu kyautace daga gareni" Harda kwallata nake mashi godiya cike dajin dadi naimashi addua sosai,zakiyya ma tayi godiya sosai. Abbi yace "duk abunda zan fada dadynku ya fadeshi,saidai nace maku Allah yayi maku albarka kudukanku Allah ya kawar da shedanin mutun dana aljan tsakaninku,kuyawaira yiwa juna uxiri rayuwa babu uxiri zaizama babu zaman lafiya Allah yayi maku albarka,nima ga tawa gudunmawar." Ya fiddo keys na motoci ya mikama zakiyya ya mikomun. "Motocine sabbin shigowa yanzu haka ana kan hadasu,zuwa sadda zaku gama yawon amarci suna zaune agida suna jiranku" Sunkuyar dakai nai inajin kunya kamar ta hallakani. "Mun yi maku visa daga nan zaku zaga kasa uku sanan ku tsaya saudiyya kuyi aikin hajji sannan ku jiyo gida." Saboda jin dadi kuka nasaka ina jingina kaina kan kafadar mami ta rungumeni tana lallashi,godiya nake masu maitarin yawa da addua mai kyau. Mami tace"nima ai ba abarni baya ba ga tawa kyautar ni ima miko mun box din dana baki ajiya" Ta dauko ta kawo mata ta bude shi sarkokine na xinari sai daukar ido suke masu masifar kyau,ta ciro guda ta zagaya ta bayana ta saka mun ta cire yankunnen dake kunnena ta samun na sarkar sannan ta samun zobenta. Haka zakiyya ma tasaka mata rungume mamin mukai nida zakiyya muna gode mata itama,sannan Abbi yace"kuzama cikin shiri karfe shidda na yamma zamu bi jirgin Nigeria zamu koma gida,don sati mai zuwa daurin auren su zuwairat." Sai naji baji dadin tafiyar tasu ba,kenan mu muna nan ni wlh duk atsorace nake da wannan miskilin mutumen. Abdoul ya mike zaifita mami ta nuna mun briefcase dinsa daya ajiye,kamar zan kuka na dauka na bisa da ita wajen mota aharabar gidan. Yana jingine da motar nafito tunda nafito ya kafeni da ido,har jinake zanyi tuntube saboda yadda ya tsareni dakallo. Mika mashi nai ina daga nesa kadan. Hadawa yayi da hannayena ya fincikoni nida rigar muna shigewa jikinsa, Ya dago habata yana kallon idanuna dana zaro cike da tsoro. "Nikike kora karna ga jikinki ko,to duk wayon amarya dai dole asha manta,kigama boye boyen dakanki zaki budemun ingani" Runtse ido tai tanajin nauyin kalamansa, "Meyasa bakajin nauyin furta abu idan yazo bakinka,Allah ma ya sawake hakan bazata taba faruwa ba" Murmushi yayi ya sunbaci kuncinta ya sake rike kugunta sosai yana kallon cikin idonta yae"are u sure?" Dauke kai tayi tace"100% sure ma kau,ni ka sakeni kagani ga yaya malik nan zaifito nabani karya ganni" Kallon Kofar fitowa yayi yace"kalla kigani dayake shi matarsa tana sonsa kalli abunda take mashi" Dasauri na juya garesu na gansu rike da hannun juna,ya sunbaci kanta itama tayi tuntudo ta yimashi,sannan ta rungumeshi tana mashi by by. Kauda kai nayi gabana yana faduwa nidai wlh bazan iya wannan rashin kunyarba,acikin gida nan ga mami dasu abbi kai ko babusu nidai kunya nakeji. "Kingani KO" "Zanmaka amman sakarni tukun" Sakinta yayi yana hadiye wani uban yawu da yaji motsin na shanunta sun sauka daga kirjinsa. Ganin rugawa xatai yayi saurin rikota, Yana rungumo bayanta sosai ya saka kanshi gefen wuyanta,cikin yan second taji hankalinta yana neman tashi.batai aune ba taji wani zazzafan kiss ga wuyanta wanda yasaka duk wata kafa ta gashinta tatashi,sakinta yayi ya shige motarsa yabarta nan kafafunta suna rawa. Tunda take rayuwarta hakan bata taba faruwa ba,wanan sabon abune gareta daker ta iya takawa tashige cikin gidan,duk suna dakin mami suna hada kayansu. Can ta nu fa tana kokarin daidaita kanta, "Gama ta nan mami saiki fada taji sosai" Jiyowa mamin tai tana murmushi tace"yawwa safiyya zauna muyi mgana yanzu nace cewa zakiyya saita ringa nuna maki kulawa da miji,shi namiji dakike gani yana son tarairaya wajen matarsa musamman ma irin mazajenku,naga abun naki yana neman wuce misali,saikace ba wayyaya ba kinsanshi ya sanki batun yau kuke tare ba,idan kikai sake yadda yakeda farinjini zakiji asalansa.inasonki sosai ina maki kallon danake wa su ni,ima da zakiyya.kiyi koyi dasu yadda suke yi dani kema kidaukan kamar mamanki zanfi jin dadi.nima abunda uwa zata fadama yarta dan gyara zamantakewarta zan gaya maki don inasonki da Abdoul,kuma ina ganin yadda yanmata suke kara kaina akanshi bazanso hankalin yayi wajen wata ba bacin ke gaki,kisaki jikinki kinuna mashi soyayyar dakike mai da yadda kike kewarshi hakan zai dauke hankalinsa da tunanin kinbar sonshi,don haka zanba zakiyya amanar kula mun da lamarinku in naji sabanin yadda nakeso zan bata dake" Sadda kai tayi tana murmushi tace"mami shine fa yake wani dixgani wai nace bana sonsa,kuma wlh niba haka bane" Me zakiyya xatai ba dariya ba ita da ni ima mami tayi masu dakuwa"kunga naku kason,zakuyi mun shiru koko" Rage dariyar sukai zakiyya na boyewa tana yin abunta.mami ta jiyo ga fiyah tace"dayace haka aiba biye mashi zakiyi ba,alokacin saiki nuna mashin kina sonsa din bawai kitayashi nuna hakin ko in kula ba,don haka zagewa zakiyi kizama jaruma yadda zaiyyi alfahari dake kibar wanan sanyi sanyin bana sonshi" Daga kai tayi tana murmushi. Xakiyya tace"zamushiga lesson time to time ko amaryar yaya Abdoul" Harararta nai ina dauke kai. Taya mamin shirya kayansu muka cigaba dayi tana janmu da fira don nasake dasu,kuma nai kokarin yin hakan ina biyesu muna hira da dariya,har time na dora sanwa yayi nida zakiyya muka shiga kitchen din bayadda mami batai ba akan mufito zatayi amman muka kiya. Abinci mai lafiya muka sarrafa dan danan sai kamshi,mami da ni,ima na cewa sun kagara suji sunfara xubashi cikin cikinsu,haka suka yini cikin farin ciki suna farantawa junansu,Abdoul baidawo da rana ba malik ne kawai sai su Abbi,don yana ta son maido kasuwancinsa london mami tace karya tattago wannan aikin yayi hkr ya bude sabon reshi anan,yake mata bayanin kudin dazayyi asara kafin yafara samun nasara,kuma ahalin yanxu idan yace zai kashe wadannan kudin karshe dole ya saida wancen company na nigeria. Wannan hirar tasu Abbi yaji saiya saka baki yace"yabarwa malik wancen kasuwancin yayi mashi alkawarin bashi duk kudin dayakeso ya bude wani anan london,don yace bazai cigaba da zaman Nigeria ba saidai yaringa xuwa yaa gaidasu,kuma basu takura mashi ba. Hakan yasa yanzu yaketa fafutukar ganin ya samun wurin dazai tsira sabon company,sannan har ya saje bude wani store din saboda anan baifi sati ba,amman kayan nan sunfi nacan kyau da quality dan danan kuma dayake hannunsa yana da sa,a saiga customers daga ko ina ana dibar kaya har daga Nigeria anke xuwa.shiyasa yafara zaman busy. Karfe shidda nayi ya dawo gida lokacin har su mami sun fito daga cikin gidan shikadai ake jira. "Mami har na yi wanka infito ko" Harararsa tai tace "lokacin jirginmu ya jima da tashi idan azaka samu rakamu ba kayi xamanka matarka ma saita tayaka zama" Kallona yayi ina makale da hannun mamin murmushi yayi yana shafa kai yace "aa meyayi zafi kushiga muje su Abbi nacan munyi waya dasu" Malik yaga fiyah na niyar shiga wajen da mami ta zauna yayi dariya yace"hajiya fito ga mijiki can kiketa likemata dake za,a koma ne" Dariya sukeyi shida zakiyya,ahankali ta fito tana cewa"mami kimasu magana" Itama murmushin tai tace"kyalesu zangyara masu zama" Kamar wadda kwai ya fashewa aciki haka ta isa wajen motar ta shiga,sannan suka dauki hanyar filin jirgi. "Sannu da dawowa" Ta furta mashi hankalinsa yana kan titi. "Na zaci ai bakiga shigowata ba,meyasa kikeson canza dabi,arki kokuma ince kikeson juya alakarmu,na dauka kina sona ina sonki akai mana aure amman yanzu kina nuna cewar kamar tilastaki akai bakiso,kina behaving like wata yar ruga kinsan muhimmancin aure kinsan girman miji kinsan hakkinsa kinsan komi akan dawainiyar gidan aure,ke dalubar ilimice kila ma zaki fini sani akan wannan fagen why kike haka" Duk saitaji ta muzanta tabbas abunda ya fada hakane,ni kaina ina mamakin yadda nake mashi bacin irin yadda nakejin sonsa cikin raina,amman sainake ganin ai shine ya fara nuna mun haka. "Kayi hkr ganinai daga gareka" "Shine saiki biyemun?SOFIYYA! idan kina ganin antakuraki aurena dake why bazaki sanar dani ba." Gabanta yafadi sosai muryarta kamar zatai kuka tace" meyakawo wannan maganar" "Taya bazan kawota ba bacin kina nuna man bakisona baki damu dani ba" Muryarta tayi rauni sosai tace"wlh ni ba haka bane idan da kasan halin dana shiga danake shirin rasaka bazakace mun bana sonka ba,plss kabar cewa haka." Yaji dadin maganarta sosai har hakan yakusa nuna ga fuskarshi,amman sai ya dake don tasan cewar ba wasa take ba kuma baya son yadda take tafiyar dashi. "Taya Zan sani tunda ba ganinki nake ba,kuma ai bazan tabbatar ba tun yanzu dakika samenin sai kike nuna mun halin ko inkula,idan hakan ta cigaba da faruwa zuciyata zata karkata xuwa wani wajen,tunda ke kin nuna bakisona" Baiyyi mamakin jin shashshekar kukanta ba don yasan zatayi sarkin kukace ai,muryar tana rawa tace"wlh ba haka nake nufi ba,don Allah kayi hkr wlh na damu dakai daidai da second baka taba barin xuciyata ba,ina son.............shiru tai ta duke tana kuka son ranta. Murmushi take yanajin wani irin dadi yana dawainiya dashi,abunda yadade yana jira wadannan kalaman daga bakinta,kullum sai jamashi rai take vata fada ba saida taji wuta uffan baice mata ba har suka isa filin jirgin,goge fuskarta tai sosai don kar agane duk da haka daka kalleta kasan tayi kuka. Bata jira ya bude mata ba ta fito ta wuce wajensu mami,bankwana suka shigayi dasu sunajin kamar karsu tai mami tace "diyata waye ya taba man ke" Rungume mamin tai tana fashewa dakuka don abun biyu ya hade mata bata son mamin ta tafi ga kuma kalaman sa daya gaya mata masu kona xuciya. "Mami bashi bane ya sani kuka" Gaba daya dariya suka saka masu harda su Abbi da dady,murmushi mamin tai tace"mekika mashi" Bazata iyacewa ba dole ta gilla karya. "Cewafa yayi inkikatai zairinga gasa man aya ga hannu" Dariya kurin suke masu shikanshi Abdul din dariyar yayi abun ma saiya bashi sha,awa takuma burgeshi yadda take kukan shagwabar. Kiransa mami tai tace"xonan son" Takowa yayi ya iso ta dagoni daga kafadarta ta kama hannuna ta saka cikin nashi ta dan sha mur. "Ko kwarzane nagani jikinta saika gaya masu,don haka ka kulamun da diyata." Rike hannun yayi gam yana jawoni gefen kafadarsa yace"insha Allah karkisha damuwa saikinyi mamakinta kince menake bata idan kika ganta." "Haka nakeson ji kaima malik ka kulaman da diyata banason inga ta rame ko kadan ta rike hannunsu ta saka masu albarka sannan suka sake bankwana,ni,ima tana cewa"Anty zakiyya Anty safiyyah kuyomun tsarabar babies kafin kudawo" Dungure mata kai mami tai suna dariya har suka shige jirgin,malik yace"kinjito abunda qanwarki tace" Gaba tai tabarshi tana cewa"abunda ma wanda zaibayar da babyn baishirya ba waya sani ko tsorona yake" Ta fada tana darita biyota yayi dagudu itama ta karasa cikin mota da sauri don tasan sauran idan ya kamata, Yace"insha Allah shigar farko zan xuba twins shiga ta biyu kuma triple shiga ta uku.........rufe mashi baki tai tana bashi hkr suna dariya sun riga su Abdoul tafiya. Tunda taji abunda ni ima tace ta daskare awajen, takasa juyawa tana jiyo su zakiya ita da yaya malik,ta jinjina rashin kunya irinta ta ita ina zata iya wannan tabarar,amman kuma inbata dage da wannan kunyarba za,ayi babu ita. Jinshitai abayanta saida ta dauke numfashinta na wucin gadi kafin ta jiyo tana fuskantarshi. [10/20, 9:41 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........66 "Let's go home,and kipt ur thinking side Indai Akan maganar sister ne saita rasa wane zata dauka cikin twins din da zamu haifo" Dora hannu tai afuska tanajin girman maganar kamar zata rushe da kuka ta jiyo,cikeda muryar kuka. "Plsssss don Allah kadaina wlh kana sani jin kinya donAllah" Murmushi yayi yana sake matsota sosai ya saka hannunsa duka cikin aljihu yana leko fuskarta,cike da shakiyanci yace"wanna kunyar dai yakamata mu fidda raini nida ita amman ba damuwa Allah ya kaimu,muje." Ya riko hannunta tarasa yadda zatai ta cire kunya ta nuna mashi irin tata kalar kulawar,amman ahankali kila zata rage. Ba gidan da suka fito suka koma ba wancen gidan da aka daukota jiya suka nufa. Kallonsa take tace"munbaro can kenan,amman ina da kaya acan fah" "Indan ta kayane bakida bukatar su a tafiyar da zamuyi zaki mallaki fite da kalarsu oky" Jinjina kai tayi tana tunanin yadda zatace ya bata waya takira su mama,ga yesmin itama tana ranta taji intana lafiya tasan yadda yesmin tafita tsoro Allah yasa first night dinta bata suma ba. Bata san sadda murmushi ya kubce mata ba har ya ganta tanayi. "A u happy?" "Niba wani happy da nake kawai ina tuna yesmin ne" Shima murmushin yayi yace"yadda ta kaya mata kike tunani harda murmushi kibar dariya wa wata kema ki iya dakanki" Kallonsa tai cike da tsoro aman ta dake tace"bangane ba?" Murmushin yake yace"ehy kema bakiga naki daren ba balle ki yiwa wata dariya" Zaro idonta tai tana mamakin yadda yasan abunda take ma murmushi kenan. "Yes I know abunda keranki kenan" Shiru tayi ta kasa cewa komi dariya yayi harda dukan sikiyari yace"matsoraciya,kwantar da hankalinki ni ba bakon tsanani bane" Dakewa tai tace"wai nufinka tsoranka nakeji,uhmm da banji tsoronka ba ma sadda kake bugebugen mutane da cire masu kafafun baya balle sai yanzu" Dariya ta bashi sosai ashe bata mance lokacin dayace zai cire mata kafar baya ba,kallonta yayi yaga tana dariyar kasa kasa itama saiyaga ta kara mashi wani irin kyau ya lumshe idonsa kurin yana cewa. "Wancen time din da wannan ba daya ba,karma kifara hadasu" "Uhmmm" kawai tace mashi tafiyar suke ya tsaya yaje ya siyo musu take away binsa tai da kallo hakika Abdoul dinta kyakkyawane,kuma at any moment mata na iya kaimashi cafka to ita miye anfaninta inhar hakane,tunda har ta samu yana sonta so ba dan karami ba,wanda yaki kula yan matan dasuka fita aji yace lallai ilaihin sai ita aikuwa ta ciri tuta,kuma ta maganar mami idan ta sake Abdoul zai subuce mata ajiyar xuciya ta sauke tana tunanin yadda zatai yaki da wannan kunyar,ta tuna yadda kiyya ke nuna ma malik kulawa duk da ba wata soyayya sukai ba,yanzu ne suke kokarin ginata.sai ita data shekare tana dakonta kuma lokacin da ya kamata ta ci anfaninta tana niyyar cutarshi itana ta cuci kanta. "Ohhh may Allah kaban ikon yin wannan aikin ladar,kabani dakiya na nuna ma mijina how I feel about his love" Gangoshi tai da leda ga hannunsa suna magana da wata tazo shiga,rigace yar kanti jikin ta iyakar guiwarta sai rolling da dangyale kuma wai musulma. Wani mulmulelen abune ya tokare mata wuya,har tanajin karar dukan kirjinta ba kamar yadda taga suna dariya,by by taimashi shima ya maida mata ya nufo motar shigowa yayi ta mika mata ledar hannunsa ta ansa tana dauke kai. Yaja suka cigaba da tafiya ganin shirun nata yayi yawa yasa yace"what's wrong with u my love" Harara ta maka mashi kamar zatai kuka tace"wacece wacen ko har kafara kokarin mayarda wata acikin gurbin danake?" Ta fada tana kauda kai don kwallarta tana fitowa. Murmushi mai sauti yayi yana kallonta lokacin sun iso gidan motar malik ya gani,yasan daman suma anan din zasu zauna shima zaifi son haka din. Kwallarta take sharewa yayi parking har lokacin murmushin yake jiyowa yayi yace "kibar gigewa kiyi kwallarki zan share maki kinjiko sorry kedince naga kina ta wasan gare gare dani shiyasa ma na anshi phone no dinta. Azabure ta jiyo tana kallonsa wasu kwallar tana xubowa tace"are u serious?" Dakewa yayi yace"im serious mana love" Jinjina kai tayi tanajin wani kakkauran abu yana sake toshe mata makogwaro,wani irin kishinsa takeji har cikin ranta. Budewa tai ta fito ya dauko ledar yana biye da ita,idonsa akan kugunta yadda take sarrafashi kamar da gayya,amman yasan bata cikin mode din ma har dazata iya mashi haka,kotana ciki ma kunyarta bata barinta. Main falon babu kowa direct dakinta ta nufa daman abude ta barshi,amman tana turawa taji arufe tai tsaye cike da bakin ciki ga layi layin hawaye dakera zarya ga kuncinta isowa yayi ya zaro key din kofar ya matsa jikinta ya hardo hannunsa ta kasan kugunta ya hade da jikinta ya bude kofar,fizgewa tai ta shige tana samun gefen bed dinta tana durkushewa tana kuka kasa kasa. "Idan har zaka hada soyayyata da wata wallahi gara kadaina sona bana son soyayyar inhar zaka hadani da wata can kazama marar sanin darajar kanta halan ma jikinta ne yadauki hankalinka karude haka to wlh ban iyawa dole kasan wadda zaka zaba cikin.........jitai anyi sama da ita bata iya tantance mekefaruwa ba saida tajita tinjum cikin komin wanka abayi. Dauke numfashi tai saboda tsananin firgita daker kafin ta maidoshi cikin shashsheka kamar mai asmah. Tallabo fuskarta yayi data jike da ruwa ya zuba mata idanunsa dasuke cike da tsananin kaunarta,runtse idonta tai hakan bai damai ba ya dora goshinsa bisan nata yana sauke numfashi a slow,yana goga hancinsa ga nata hancin cikin sassanyar muryarsa yake magana wadda tasata sake lumewa cikin ruwan..........."bazan iya hada sonki da na kowa ba my love,kedin kekadai nakewa so na soyayya so irin na ma,aurata dake kadai xuciyata take ita rayuwa,da ace zan iya hakan da ban juyawa zakiyya baya ba dana hadaku alokaci guda na aureku,saidai kedin kaunar danake maki ban hadata data kowa ba,kidauna cewa wannan xuciyar" ya dora hannunta kan kirjinsa da babu komi jikinsa sai gashinsa kwance awajen,saida taji tsikar jikinta tatashi tana kokarin janyewa ya sake rike hannun.ya cigaba da cewa. "Amman inhar muka cigaba da tafiya ahaka wataran tabbas xan iya kallon wata da sunan ta burgeni,inason kulawar matata inason matata ta nuna mun irin son da take ikirarin tana mun,inason inga irin yadda kikai kewata inason ganin iyakar girman danake dashi cikin taki xuciyar"ya dora hannunta kan kirjinta dake wani irin bugawa sake runtse idonta tai don saman na fulaninta ya aza hannunsa,wanda takejin yana kokarin yawo dashi zuwa cikin rigarta,yayin da take kokowa da numfashinta kuma ta kasa hanshi abunda yake kokarin yi don yin hakan zata bata mashi,itama kuma tai alkawarin bazata taba bata mashi rai da ganganba tai wannan alkawarin saidai bisa kuskure. Dora kanta yayi bisa kafadarda yana zaga hannunsa ta baya yana zuge zif din rigar don doguwace,daker take jan numfashi don abun da bata taba fuskanta ba,wannan feelings din yasha banban da sauran feelings da take ji akanshi,yau na dabanne wanda takejin tsaf xata iya sumewa don koda wane lokaci juriyarta na ita karewa. Duk abunda yake idonta arunte yake bazata iya kallonsa awanan yanayi ba,tsananin kunyarsa takeji wai yau Abdoul dinta ne yake kokarin rabata da kayan jikinta.........tunaninta tsayawa yayi sanda take gama zare mata ita tazo iyakar kugunta kuma azaune take,bra dinta pink color ce ta bayyana tsayawa yayi kurin yana tsurama wajen kallo,idonsa kamar xaifado kasa lumshe ido yayi hakika shidin mai sa,a ne duk wannan nashine idonshi akan kirjinta yadda suka cika bra din sosai sannan gasu farare tas harma sunfi fuskarta haske,kokarin kwatar hannunta take don karewa amman ta kasa ahankali yaja wata ajiyar xuciya yana kama kafadarta ya mikar da ita tsaye,shafeffen cikinta ya bayyana wanda keda kwantaccen gashi liya liya asama,baisan sadda a furta "wow masha Allah" Jikinta kerma take saboda ruwan akwai sanyi sadda ta sakata,kallon yadda take rawar sanyi yayi yaja rigar kasa ya zare mata ita pant dinta ya bayyana shima pink kalar bra dinta,dunkulewa tai waje guda tana saka kanta cikin cinyarta. Murmushi yayi yanajin yau wata kaunarta yakeji ta musanman,tareda tsananin sha,awarta baitabajin irin wannan abun ba irin yau shower ya kunna yaji ruwan nata da dumi sosai ya kashe ya iso wajenta ahankali yana dago kanta,idonsu ya hadu suduka wani jirrrr sukaji ta lankwashe kai tana marairaicewa kamar zatai kuka,shima saiyatinga kwaikwayonta dukewa tai tana darita ciki ciki. Tana magana da yar muryarta ta sake tunzarashi wajen daukota daga cikin komin. "Ya...ya don Al...lah" Bakinsa ga kunnenta yace cikin salo. "Safiyyah plzzzzz" Kankameshi tai tanajin kamar tana zarar wani abu daga jikinta. Dire ta yayi yana kunna shower din,bayanta ya dawo ahankali yana shigewa jikinta har saida ta dauke numfashi kadan kafin ta sake narkewa tana lankwasar da kanta gefe ya saka kanshi gefen wuyanta yana goga fuskarshi wajen,ajiyar xuciya kawai sukeja cikin wayau da dubara ya fara balle mata bra dinta cikin wani irin yanayi ta jawo maganarta daker. "Yaya........Kar........ka cir.....cire plxxxx" Aikamar tunzurashi tai ya cireta ya jefar can inda kayanta suke. Duk hannunsa ya dora saman kirjinta wani marayan numfashi taja mai kamar tana rera waka,kusan tare suke sakin nishin ahankali cikin shauki da sha,awa yake murxa nipple dinta yana lasar kunnenta banda maker keta da rawa rawa da jikinta keyi bata komi sai wannan uban nishin kamar ana yankar namanta. Saitazo magana taji maganar ta kifitowa daker take fizogo numfashinta tanajin wani irin abu da tunda tazo duniya bataji ba. Shikanshi bazaice yana cikin hankalinsa ba,don da hankalinshi baitaba yunkurin taba mace irin haka ba,baima san yana da desire har haka ba sai yanxu. Fiyah kafafunta kasa daukarta sukai neman xubewa take atsayen,daga kasanta tanajin wani abu yana jalalomata mai sata jin kamar zata sume kirjinta take turowa sama tana bankarewa kanta ta hangameshi kan kafadarsa tarasa inda zata tsoma ranta,wani dadine da batasan kalarsa ba saiyau hannunsa taji yana yin kasa wajen pant dinta bata san sadda ta fashe da kuka ba,don abun is too much for her rungumeta yayi sosai yana lashe hawayen da ruwa ya wanke su,yana mata irin abun nan da akewa yara idan suna kuka shiiiii ga kunne,baisan sake tunzura mata feeling yakeba soap ya dauko yashiga matsowa yana mulkemata jiki dashi,duk ta rikece mashi shima din duk arikice yake,don zai iya cewama yafita rikicewar duk ta babbankare tana lakwashewa sai kuka da zan shiiiiii take irin kaci yajin nan ga bakinka jikinsa na nata yahade da kunfa still pant dinta yana nan daya kai hannu wajen zaiji tafara kokarin sumewa,murmushi yake yana jin wani annurin dadi yadda yagano cewar itama tana bukata. Silalewa tai kasa ya bita kama wuyanshi tai ta makalkale bakinta yana rawa numfashinta yana fizga tace"y......aya" Cikin dimauta yakai bakinsa kan lips dinta da sukai masifar daukarmai hankali yafara kissing dinta cike da shauki da nuna zallar so da kauna duk sun cure jikin juna da wannan damar yayi anfani bata sani ba ya rabata da pant dinta ruwa yana xuba jikinsu ya jingina bayansa da bango yasata gavanshi,sai lankwashewa take tana jan numfashi ga duk alamu kam fiyah bata cikin hayyacinta (nikam nace ko ina kunyar taje oho kila daita dawo hayyacinta tukun🤭😉) Cikin wani irin yanayi yana jan numfashi yakai hannunsa kasanta wani silbi da wani ruwa ruwa yaji saida numfashinsa ya dauko dafffff yana niyar sumewar kafin fiyar ta rigashi...........iyakar rikicewa sun rikicewa juna ita dashi acikin bayin nan,kamar wata mota haka yake sarrafata fiyah kuka take sosai tana nishi kamar mai labour,shi kanshi kukan yake don su duka bakin junane ta wannan bangaren saida yaga tana niyyar sumewa sannan ya barta badan ya hkr ba don yau bayajin zai iya bacci bai kai inda yake buri ba,daura ye jikinsu yayi yasata tai alwallah,shina yayi ya nadeta ga towel ya saka boxer dinsa ya dauko ta kamar jinjira ya dorata kan gado,ajiyar xuciya kurin take tanajin mararta tayi mata wani irin nauyi,tana mata ciwo. Boye kanta tai cikin filo tanajin kamar ta shige cikin katifar ta boye,har jan ajiyar xuciya takai goma. Kwanciya yayi gefenta yana dora hannunsa kan tashi marar,don jinta yake tana mashi wani irin ciwo abunda yake wajen kurin yake son juyewa. Amman yunwa yakeji gashi ko sallar magruba basuyi ba,har ishai ta wuce yanajin knocking din malik dazun amman inaaaa bazai iya fitowa daga bayin nan ba kila abinci zasuci yasan har sun shige daki wayasani suma abunda sukeyi kenan. Dariya yayi kadan yana kallonta yadda duk ta dunkule tana numfashi daker,dariya yasake yi yace cikin slow voice dinsa. "Safiyyah nah" Can kasan makoshi ta ansa "uhm" Lumshe ido yayi yana jin wata fitinannan sha,awarta tana sake ninkuwa yace"tashi mushirya muyi salla yunwa nakeji,koke bakiji" Nan ma "uhm" din tace numfashi yaja yace"sorry kinga niba kallonki zan ba bari natashi nasaka kaya tashi kema inbaso kike na samaki ba. Xunbur tatashi amman ta kauda kanta gefe tana nufar inda taga anshigo mata da kayanta bata san wanda yayi aikin ba.wadrop dinta ta bude ta dauko rigar bacci doguwa iya guiwa saita dora after asama ta saka hijab again,ta jawo ayar ta rufe fuskarra donma karsu hada ido. Murmushi yayi ya riko hannunta yajata inda ya shimfida abun sallar yatada salla.yana jansu jam,i a karatunsa mai ratsa xuciya. *banyi alkawari ba amman idan inada time anjima xan maku wani* Kunyarku nakeji yau 🙈 Nayi rashin kunya wlh🤭 [10/21, 7:33 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........67 Suna gama magruba suka tada isha,i sannan sukai shaf,i da wutri suka roki Allah zaman lafiya da zuria dayyiba ya kuma kawar da shedan tsakani su. Yace mata''kiraba kanki da wadannan kayan kisha iska" Ya tsareta da ido banda soke kai da sadda kai tana wurga idanunta babu abunda take yi,murmushi yake ya tashi yaje ya dauko take away din daya shigo dashi dazun,sannan ya fita xuwa kitchen ya dauko mazubi. Tana ganin fitarshi tai xunbur tatashi taje ta cire kayan,sai rigar bacin iyakar guiwarta amman ba,a ganin komi nata ta sauke ajiyar xuciya tai tana koma wa gefe inda zasuci abinci ta takure kanta. Har sadda ya dawo da plet da cups ya ajiye yana zama irin zaman da yaga tayi,ta jingina da gado. "Menene my wife" Kasa kallonsa tai ta murtsika ido tace "kamar inajin bacci" Murmushi yayi yana fiddo kazar da aka gasa mashi yana dorata ga farentin yana zare mata gashi yana cewa"kama ne ai ko?ba baccin kikeji ba" Tasan abunda take nufi kuma itama tasan dawuya ya kyaleta acikin wannan daren,marairaicewa tai tace"ba kama bane dagaske inajin sa har idona yana rufewa" "Amman ai bazai hanaki cikin wani abuba,don Allah sainaga kina niyyar amai kozan kyaleki" Wata madarace irinta larabawa cikin jarka tasha sanyi yaxuba ga cups din yana kallonta,yadda take satar nashi kallon. "Kibar satar kallona malama ba mai hanaki jiyowa ki kalleni form head to toy." Turubaki tai tana harararsa "niban wani saci kallonka ba" "Shikenan matso kigani" yana dauko naman yana nufar bakinta dashi,batai musuba ta bude bakin ta ansa ganin bata yake shi baici ba yasa itam tafara bashi din,kannemata ido daya yai yace"thanks love" Ahankali sukai rabin naman sanan ya yabude cheeps din shina yana bata,tana bashi har saida yaga ta dafe ciki tana shagwabe fuska. "Cikina yaya Abdoul zai fashe na koshi wlh" Cikin kallon kauna yace"aidan kar cikin dare ki hanani bacci kina kukan yunwa" Cikin salon soyayya ta mashi wani kallo ita duk tama rasa ina kunyar tace"nidai bari naje na wanke baki bacci zanyi" Ta nufi toilet dinta yana bin kugunta da kallo,tana imagining yadda zai ratsata dafe goshi yayi,koya damben zai kasance aman zai yi kokarin ganin ya mata mai sauki Allah yasa ya ita control din kanshi.fitowarta ta katse mashi tunani taje gaban mirrow dinta tana shafa turarukanta tana fesa mouth fresh,ta gyara gashinta ta daureshi shina baya ta mulkeshi da manshi. Ganin yana bayi yasa ta ruga ta haye gadon can kuryar gadon gabanta yana faduwa,ita kam tana jin tsoro kuma idan har yanema bazata iya hanashi ba,aman Allah yasani atsorace take tasha jin labarin wadanda ke suma da wadanda har sai anmasu dinki ankaisu asibiti,bata fatan hakan zata dauki maganar Anty jamila ana gobe zasu tai tace mata. "Nasan abunda kikema tsoro safiyyah kuma haka kowace mace wadda bata sayar da kimarta ba takeji,don haka karki tashi hankalinki kinatsu kisaki jikinki inhar kika saki jikinki to ina tabbatar maki bazakiji ciwo sosai ba,kuma zaki gaya mun" Ajiyar xuciya naja ina jin kwarin guiwa badan gaban nau yabar faduwa ba,inajin fitowarsa nai lamo ina jiyosa yana feshin turare.gabana fat fat kawai yake har inajin dukan xuciyar tawa ga kunnena. Baya na bashi nai shiru alamar dai bacci nake amman idona biyu har wata xuma nake don tsoro,duk da na,urar sanyaya dakin dake akwai. Kashe fitilar dakin yayi yana isowa kan gadon ya kunna dumlight kallon bayanta yayi yanajin tausayinta,inama bai tabata ba da zai ita jurewa har sadda zata saki jiki dashi,amman yariga ya dandanoma kanshi bazai iya hakurewa ba. Ahankali yahau yana matsowa ta bayanta ya jawota cikin jikinsa,saida ta firgita tanarke mashi tana kermar jiki. "Yaya Abdul" Lumshe ido yayi lokacin da yake saka hannu cikin kashinta yana yamutsawa,daker ya iya ansawa don wani irin sulbi da kamshin gashin ke daukar mashi hankali. "Uhmm safiyyah na menene" Ajiyar xuciya take ja tana shigewa cikin jikinsa saboda jin yadda yake mata nishi ga kunne. "Yaya karkayi mun da zafi tsoro nakeji" Bakinta yalalubo cikin shauki don muryar tatama jefashi yanayi take. Saida ya tsotsa saudaya sanan ya shafa fuskar yana kallonta cikin dan hasken dake dakin,yaga yadda take narkewa yace"idan kika ban hadin kai love bazan cuceki ba,idan kika kiya bazan san sadda zan maki abunda kike tsoro ba,plzzz ki saki jikinki kinjiko inason najiyar dake xumar dake cikin kaunata kinaso kiji?" Jujjuya kai tayi tana jin hannunsa yana yawo saman cinyarta daker tajawo numfashi cikin wahala tace. "Y...aya" Jiyai kamar xai suma da wannan salon da take kiransa,baisan ma ya zare rigarta ya jefar ba ya kama kan nipple dinta yayi mashi wata irin tsotsa saida ta saki wani marayan numfashi. "Ya...y..a zan......zan....mut...mutu" Ga kunnenta ya ke rada mata cikin shauki da zallar sha,awa "no my love bazaki mutu ba kina sona" Daga mashi kai tayi cikin wahala da jin kamar zai kaita sama ta daya,don jinta take wani iri. "OK....y love saki jikinki kinaso aikikace ko,"daker ta jawo maganar tana huttai. "Ehhhhhh" Kamar ta xugashi don rikicemata yayi gaba daya ko nace suka rikicewa juna,saiga fiyah na wata mika kamar mai aljanu,tana rike da kanshi dake kasanta bankarewa kurin take tana wani irin nishi,saika rantse yanaka ta ake. Kafafunta rawa kurin suke da jikinta,kafin numfashinta ya nemi guduwa. Ganin haka yasa yafara kokarin ganin ya dauki hanya,don shima tuni ya mance sunansa idan zakace ya sunan sa bazaiji ma mekake fada ba. Suduka sun lalata jikinus sun koma one. Ahankali yayi anfani wannan damar yanemi inda zaije ya samu natsuwa,yafara adduar saduwa yadauki hanya alokacinne fiyah tace bata san wannan yaren ba,tafara kokarin rikicewa cikin wayau da dubara da salo salo na so da kulawa ya fara kokarin danna wa amman wajen yace baisan wannan ba,tun yana yi ahankula yana shafa kanta yana hawaye tare da kissing din ta yana lallashi,haba dayaji zai sume baisan sadda ya bankada kofar ba.wanda suka sauke wani uban kuka tare gaba daya Abdoul baya sanin ma meyake shida yajishi sama jannati,kukanta jinsa yake kamar tana mashi waka duk ya gigice itama ta fita hayyacinta saboda wata azaba dake shigarta jitake kamar rodine yake turamata,muryarta bata fita sosai amman ahakan take kiran sunayen duk da sukazo kanta,har yaya jalal dai yau yasha kira,tun tana kokowar tureshi har karfin ya kare tanaji tana gani yake nukurkusarta idonta duhu take gani,kafin numfashinta yafara kokowar bari ta.........sai lokacin taji ya saki wata karamar kara yana riketa gam jikinsa yana rawa yana kuka sosai yayi realizing,atare suke sauke ajiyar xuciya tana kuka ta janye jikinta ta koma can gefe tana cigaba da kuka,kamota xai tanemi rugawa jikinsa ya saki kamar lagwani daker ya rikota ya maidata jikinsa yana aikin hura mata kunne da shafa kanta,yadau lokaci kafin yace cikin dishewar murya. "I'm sorry love,I'm so sorry I don't mean to hurt you plzzzz stop cry,Allah yamaki albarka Allah yasakawa baba da Albarka Ubangiji ya biyasu shida mama Allah ya tsindumasu Aljanna,kinbiyani kinman komi love su baba dasu dady Abbi sun gama biyana,kedin dai kenikeso amman ina farincikin samun natsuwa dake,da samun abunda kowane namiji yake fatan samu daga wajen matarsa first night dinsu.Allah ya maki albarka." Banza nai dashi ina shashshekar kukana don jinake daker idan ba ya farfarkani ba. Tun ina kukan har bacci ya daukemu nidashi bamu sani ba. Haka ta kasance ga su malik,don shi abun ma rikice mashi yayi dimuwa yashiga yi yadda yaji lamarin yasa baima zakiyyar da sauki ba sumarta biyu cikin wanan daren,baisan tanayi ba saida ya gama ya lura da bannan dayayi don yaji mata ciwo duk ya rikice ya dimauce,ruwan xafi yaje ya hada yasata tafasa wata uwar kara wadda tafarkar dasu Abdoul daga baccin da ya daukesu. Fiyah kuwa zazzabine ya sauko mata murmushi Abdoul yayi yasan malik nacan na aiki Allah yasa karya yaga yarinyar mutane. Cikin daren wajen karfe hudu yagyara an safiyyan shi tana ta mashi kukan shagwaba tana cewa saita gaya ma Mami yaci zalinta,hakuri yaketa bayarwa yana magiya.yadda taga yana kula da ita sai taji dadi duk da kafafunta awawware take tafita tana fitowa alam ya buga asuba tayi tayi salarta bata jirashi ba,ta rarrafa tahau gado. Lokacin malik sukafita asibiti shida zakiyya don abun tsoro yake bashi,yadda yaga tayi duk ya rikice Abdoul yana gama sallar ya leka ta taga yaga fitarsu,dariya yayi kadan yace. "Yanzu ai kingane idan tsorinki yake ko akasin haka,gashinan kin gaya masu ai." Kallon fiyah yayi tada dunkule cikin bargo yaje bakin gadon ya shafa kanta,yanajin wutar kaunarta tana ruruwa cikin ransa. Bude ido tayi ta narke fuska cike da shagwaba "yaya masassara nake kuma yunwa nakeji" Zunbur ya tashi "sorry love bari na kawo maki sauran namanki sai kisha tea ga magani nan kisha Sannu kinji ko my love." Harararsa tai tana fiddo kwalla "bacin ma baka kaunata" Zama sosai yayi yana shafa kanta "haba karkice haka ai wannan shine kaunar,kiyi hkr da ankara sau daya zai bari" Zaro ido tai cikin kuka tace"wlh banso baza yarda ba mami zan gaya mawa nidai banso karkamun wlh nasha wuya" Ta fada tana kuka lashe hawayen yayi yana shafa fuskarta"shikenan bazan maki ba har sai ki naso bari na kawo maki tea din" Ya tashi ya fita falo xuwa kitchen numfashi taja taa tuna azabar jiya saida ya gama lasa mata dadin yazo ya lasa mata azaba,duk zatonta abun bazai kai haka ba.uhmmmm koya zakiyya takeji yanzu koya yesmin takeji gaskiya abun na dabanne. Cikin kulawa da kauna da soyaya ya zauna yana ciyar da ita ita kuma tana ta mashi kukan shagwaba da narkewa har yasamu tasha maganin ta kwantar da ita jikinsa har bacci ya dauketa sannan ya tashi ya shirya yabar gidan xuwa asibiti wajen su malik don ya mashi text cewa an kwantar da zakiyya. [10/23, 6:28 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........68 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Saida zakiyya ta kwana uku asibiti tana jinya,fiyah ta warke sumul itace take zama tare da ita ranar ta tazo saida taci dariya don bata dauka duk kaudin zakiyya hakan zata faru ba,yada taga taa shishshigewa malik din tana nanikemashi saigashi farat daya ya farkerta saida taga zakiyyar na kuka yasa ta daina tana lallashinta. "Wlh Safiyya ban taba dauka abun ya kai haka ba saigashi ya zarce tunanina,dafarko karfi nasaka inason tureshi shima ganin ina niyyar hanashi yasa ya sakarmun karfi,wlh yaya malik mugune........."kaikaikai plzzzz kibari wlh baisane baisan zai maki haka ba,kuma kinsha gyara wajen mami ba dole yaji abun daban ba koni nasha wahalar ba wai ban shaba,Allah ne ya taimakeni baimun irin naki ba kiyi mashi uxuri"ta fada tana boye dariyarta yadda zakiyyar duk ta fita hayyacinta cikin kwana ukun. Ansallamesu sukadawo gida bayan kwana guda suka fara hada hadar wucewa yawon cin amarcinsu. Xuwa lokacin kasuwancin Abdoul ya gama bunkasa a kasar Australia,customers dinsa duk sun biyosa saboda sanin yadda suke samun garabasa dashi,malik ma ya fara kokarin ganin ya gama daidaita nashi,har lokacin zakiyya ta gaza yarda dashi duk ta tsorata da lamarin,su fiyah kau ai har anzama yan hannu wata irin kauna suke xubawa juna su Abdoul har shagala yake da hidindumunsa idan yana tare da ita,ta koya mashi salo salo kamar yadda ya riga ya dorata bisa nashi salo har tazo tace mashi kau ban waje,fiyah irin matan nan ne da sukeda bukata sama da mijinsu,bawai irin bukatar nan ta fita hankali ba,aa yazama yakan iya sati bainemeta ba ita kuma bata iya jure har sati guda,yayi gudun duniya yakai kwana uku abun yana dan tabata amman tana kokarin boyewa. Ya siya mata waya suna waya dasu mama dasu Anty jamila har yesmin suna waya inhar tana da damuwa xatace Adda kinji kinji abunda ke damuna ita kuma zatai iyakar kokarinta ta bata mafita da shawara. Itace dai har yanxu tarasa da wanda zasu tattauna maganar,bata son tanuna ma zakiyya akwai matsala tsakaninta da Abdoul duk da ba wata matsala bace da tasasu fada ko gaba,amman abun yana tabata don idan yatai london yana sati biyu ko kwana sha biyar idan yadawo bai wuce ya nemeta sau biyu ba ya kyaleta,abun yana tabata duk sanda sukai waya da anty jamila xata tambayeta ko akwai wani abun saidai tace "Aa anty babu komi duk muna lafita" "Ba ina nufin baku lafiya zamantakewarku nake nufi in akwai matsala kigaya mun inji" Saitayi kamar zata fada saitaga kamar ta tona ma mijinta asiri ko ta bayyana sirrinta. Sunje aikin hajji sunyi shi cikin kwanciyar hankali sannan suka wuce syprus sunsha yawo sosai da siye siye kamar hauka haka Abdoul yake kwasar mata kaya da tsaraba kala kala,duk abunda ta nuna tanaso saiya siyoshi kamar hauka har saitace ya mata yawa.tayiwa su mama dasu baba tsaraba don daga nan insuka koma Australia kwana biyar zasuyi suwuce nigeria. Fiyah nata shirya kayansu wadanda suka siyo Abdoul ya fita yaje zasu zauna da wasu customer dinsa dasuka biyosa daga Nigeria. Zakiyyace ta shigo dayake gidan kowa daban amman basuyi nisa ba,ganinta tai kurin zaune falo ta buga tagumi ta ajiye kayan tana kallonta,tatashi taje ta kawo mata fruit da ruwa ta ajiye. "Kiyyah lafiya ko sallama ma ban jikinyi ba" KWallah suka xubo mata taa sharewa wasu a xubowa hankalina ya tashi na sauko daga kan kujerar danake na zauna gabanta ina riko hannunta. "Kiyya!" Kasa ansawa tai tana cigaba da kukanta kasa kasa. "Kirufa man asiri kigaya mun abunda yafatu xuciyata duk arude take,ban taba ganinki haka ba amman tabbas ina lura tun muna saudiyya bakida walwala na dauka ma wlh ko mun samu babyne" Shashsheka take tafara magaa cikin kuka. "Fiyah......yaya malik ne" Zaro ido fiyar tai tace"innalillahi meyafaru dashi naji yaya Abdoul yace yaje india ya dawo kafin muwuce ko" Daga kai tayi tace"eh haka ne,fiyah abunda ke faruwa shine wlh yaya malik duk ya canza man fushi yake dani sosai,ko magana fa nai mashi baya ansani,baya cin komi nawa nashiga damuwa ina cikin tashin hankali,kuma wlh akan gaskiyata nake" "Subhanallahi kiyya,fushi kuma!akan me akan wane dalili mekika mashi kin tabbata bakiyi mashi komi ba" Tana share kwallah tace "bafa wani abune yafaru ba kawai fa tun daga sanda yajimun ciwon nan bana sakewa dashi,zaizo yana nemana ina nuna mashi nidai tsoro nakeji har muka baro Australia bamu sake kwanciya ba,saida muka sauka Germany shima har muka barota sau daya nabarshi yayi,fiyah ni wlh atsorace nake ko yashiga ban bari ya shiga duka nake takurewa yayi realizing intureshi,hakan danake fa shine yake fushi dani saida ya bari nafara sonsa shine zai juya mun baya,kumafa na sauko nadawo nace yayi hkr yazo yaringayi yakiya." Jinjina kai kurin take tana kallon kiyya cike da wauta da ganin rashin wayonta,tasan zakiyya ta girmeta amman ko ita bazatai wannan rashin wayon ba. "Lallai kiyya,kinbani mamaki wlh da girmanki da iliminki da wayewarki kinsan komi amman kike abu irin na yan kauye,haba badole yayi fushi ba idan bai fushi ba gaya mun mezaiyi?gaskiya kinbata wayonki na tabbata kin warke tas wata uku fa da faruwar abun nan kigaya mun baki yarda da mijinki har yanzu,gaya mun gaskiya bakida sha,awarne kome" Girgiza kai tayi tace"inajin feelings sosai amman tsoro ke hanani wlh" Tsaki fiyah tai ganin wauta irin tata ita tana fama da miji wanda abunma kamar bai damai ba ita andamu da ita har haka tana wasa. "To bari kiji wlh inbaki gyara ba zakiji asalansa muna koma Nigeria zaifara neman budurwa,tunda ke baki iya mashi komi dole zai nemi aure idan yana tsoron Allah kenan,inkuwa baya tsoronsa wlh matan waje zairinga bi don haka ya rage naki kigyara ko karki gyara,ki kwantar da hankalinki babu abunda xai faru zanbaki magnin da zakiyi anfani dashi yana rage jin zafi nima yesmin ta turomin sunan sa.kiyi kokari kija hankalin mijinki kanki inba haka ba zakiyya......basaina idasa ba" Dandanan ta rude tana kuka "zan gyara insha Allah zan gyara kiman wata taimako kikirashi kamar gaske kina kukan karya kice banda lafiya,inba haka ba wlh bazai dawo ba har ranar da zamu koma Australia,inason kuma ganinsa kafin nan" Dariya fiya tai tace"kinason mijinki kin tsaya wasa,ato nadai gaya maki,za kirashi kina fita ma zan rabka mai kira kije ki shashshabe inya kira layinki kisake nerke murya ahaka zai dauka serious ne ya taho afujajan" Sai lokaci tayi dariya tana rungume fiyar tana mata godiya,sannan ta saki jiki suka cigaba da firarsu. Saida Abdoul ya shigo sannan tatafi agabanshi ya kira malik tana mashi kukan karya yazo maza maza zakiyya babu lafiya abun ya tsananta. Saida ta gama wayar ya tsareta da kallo cike da tuhuma dariya tayi zata tashi ya danneta ya sakarmata nauyinsa,dariya take tana dukan bayansa amman bai niyyar dagata ba saita yaji numfashinta na sama da kasa sannan ya dagata yace"oya tell me what happens" Tana nishi take dan gaya mashi in brif yace"kece uwar sasanci kenan,aini na tunxurashi nace yadan bata isaka kila hakan zaisa ta dawo hankalinta" Cike da mamaki tace"innalillahi habibi baka kyauta ba,maimakon kaba shi hkr shine xaka xugashi babu kyau fa aurene kake kokarin lalatawa ni ba ruwana wlh" Ta fada tana turo baki da juya mashi baya. Rungumo bayan yayi yana dora kanshi bisa kafadarta. "My love ba haka bane tun inabashi hkr har yakai ga dole nace mahi ya dan kauce mata,ba wata india da yatafi yana cikin garinan nasan yanzu haka yana hanyar isowa..........kingashi nan yana irana" Dariya tai tana dalewa kan cinyarsa ta sakalo hannunta ta wuyansa tana sauraren abunda yake cewa tana kallon bakinsa dake tsananin burgeta. "I'm serious kataho gida matarka na cikin halin ciwo inajin tsoron faruwar wani abu,tun kan indawo gida love taketa kirana kan matsalar oky saika iso" Dariya sukai tare yana shinshinata yadda yaji ko ina jikinta kamshi yake,cike da shaukin soyayya yace"love muje kitayani wanka." Itama biye mashi tai don daman akan gaba take ta shagwabe fuska har da kukan karya. "Habibi daman kafata ciwo take dazun fa na gurde kofar bayi,nidai saidai ka daukan" Murmushin kauna ya mata yace"dan ma dauka ai mai saukice ya cabeta yana nishi "wlh love kinyi nauyi sadda muna Australia kamar kwalin omo nake daukarki" Dariya tai tana makaleshi tace"bakaine kake ta nausamun abinci ba wai don inmunje gida su mama dasu mami suce ka iya kiwo,nima din ai na iya kalli yadda ka fara ajiye tunbi" Zaro ido yayi yana direta tsakiyar bayin yana shafa cikinsa da ya dan taso amman ba tunbin bane yace"Are u serious nayi tunbi" Dariya take mashi ta rungumeshi ta baya tace"sorry habibi im joking" Hararar wasa yayi mata ya matso cikin salon soyayya yana kama gaban rigarta doguwa dake jikinta akwai dan gajeren xip agaba dake bayyana Boob's dinta idan ka xuge ahankali yake janshi kasa ita kuma tana lumshe ido. "Habibi wanka fa kace zan taya ka " Cikin kunnenta ya rada mata" inason na danyi wasa dasu kadan kinaso?" Yafada daidai sadda yake gama zagewar yana cirosu daga cikin bra dinta. Gantsarewa tai cike da shauki tace cikin wata murya ta enjoy "i love it continue habibi I love u too much" Kamar tana xugashi haka yake tsotsar mata su yana lagudarsu ita kuma tana tayashi jin dadin,ganin hakan bai mashi ba yasa ya fincike rigar duka yana cire singilet dinsa yabar gajeran wandon. Idonta yayi kalar jaraba ya shagwabe fuska tace"kasandai banajurar wannan wasan ko"cike da muryar karya tafada. Hanunsa yasa yana murza kugunta yana lasar bayanta da kan kafadarta yace cikin shakewar murya. "Nasani kadan zan maki ai yau hutu muke ko?" Yatambayeta cike da haushi ta kwace jikinta yayi saurin jawota ya sata cikin jikinsa yana cigaba da shafata da taba duk inda yakeso. Tanajin dadin yana kaimata har inda takeso amman tasan bazai komi da ita ba abunda yake kuleta kenan ita kuma,jin hannunsa tai kasanta yana wasa da wajen wanda ya lalace da ruwa jagaf. Nishi ta saki tana sake danna hanunnsa wajen cikin jin dadi tace "habibi karka daina plzzzzz" Ai saiya sake dageww yana wasa da ita yana rikitata kamar zata sume haka takeji karshe da abun yafi karfinta saita sa mashi kuka. Ta makaleshi tana kuka cikin damuwa yace"bakiso ko,sorry na bari shiyasa ai zakiga ban cika nemanki ba,wannan kukan da kike shike sani hkr dake sainai kwana nawa ina bukatarki man danzo kuma saiki kama kuka nikuma nafison lokacin dakike so yafimun dadi,inajin kamar ba aduniya nake ba. Dagowa tai tana kalonsa kardai ace kukan da take mashi wajen saduwa yake zaton ko bata so ko idan yana wasa da ita abun ya mata yawa bata sanin taa kukan ma. Shiyasa yake ganin kamar abun bai dameta ba innalillahi aikuwa doleta mashi bayani. Narkewa tai cikin salon ta kama lios dinsa ta tsotsa tana shinshina fuskarshi cikin shagwaba tace"habibi nifa duk sanda kaji ina kuka bafa yana nufin bana so ba,ko nagaji ba ko something like that hakan na nuna ina enjoying dinka fa" Ta fada cikin kunya tana boye kanta cikin kirjinsa. Cikin jin dadi yace"dagaske love dina?amman meyasa baki gaya mun sai yau,inashan wahala idan najima banjini cikinki ba wahaka nakesha ashe kwararki nake sorry love ganinake kamar ina kwararki fa." Girgiza kai nayi ina kan kirjinsa dariya yayi yace "muje kan gado komuyi anan" Boyewa tai tana dariya t Ya San wanda tafiso ai murmushi yayi yace "oky muje kibiya bashin duk sauran lokutan da baki bani ba" Haka suka bi suka cika dakin da sautin nishi da kururwar dadi,saiga Abdoul hawaye jage jage baisan meyasa yake hawaye da kuka ba idan yana riding dinta,baitabajin ta isheshi ba kullum idan ya kusanceta jiyake sabuwa take komawa ga wani dadi dayakejin tana yi mashi,shiyasa komi take bukata yake mata linkin balinkin dinsa.saida yaga jikinta ya saki sannan ya kyaleta. Abunda sukai tayi kenan har gari ya wayeda sun huta sai su sake komawa har mamakin kanta take yadda daya tabata zatai wani irin jirrrrrr akasanta har saita saki kara. Itake kamar zata haukace ida yana shocking dinta jikinta kamar mazari haka yake komawa.tanajin dadin kuma yadda yake ba breast dinta muhimmanci yasan takansu yasan kuma salon dake hauka tata. *Agurguje* Saida suka sake sati guda sannan suka koma Australia,tsakanin malik da zakiyya kam yanzu kamar maganadisu haka suka koma,dokin juna kawai suke su yanzu suke xuba nasu amarcin fiyah me zatai ba dariya ba idan suna hira da kiyya tace"Amman da kiringa kwarar kanki ba gashi ba kundinke abunku,ai bakisani ba shifa namiji wannan abun shine weakness dinsa,kuma dashi kina iya mallake mijinki wlh batare da wani boka ko malam ba,keda ki iya allonki kikuma kame kanki daga nuna mashi son abunsa.kidage da ladabi kina shagwaba da biyayya da kwantar dakai wlh babu abunda bazaki samu ba." Zakiyya tace"bansan inada sha,awa ba fiyah sai ranar daya dawo daman ina barin gidanku naje na markada kankanata da ayaba a lafata madara ingaya maki,ga miskina nai masti daman intakaita maki sosai na gyara wajen na je nai wanka na saka wata rigar bacci da bantaba sawa ba,kullum yace insa sai ince saikace yar iska kumafa ina sane kawai dai nima kunyar nakeji,sai lokacin nake ganin ashe dai bakida laifi.nayi wankan turare daman gidan nai mashi turaren wuta. Bargo nashige ina rawar dari da makerketa. Ba kamar sadda najiyo shigowarsa oganka agigice ya yaye zanen nan najin haka nai wuf na fada jikinsa ina kuka bihakki da gaskiya,ina murza mashi kirjina ina nukurkusarsa sai kokarin cironi yake ina sake mannewa karshe na gigitashi over kafin nima ya gigitanin ke ranar naga abunda ya isheni nice na koma kamar wata mahaukaciya,dayayi niyyar barina zan rikice mashi ingaya maki ranar saida muka kai safe ammanfa jikina yagaya mun." Fiyah dariya kawai take tana karawa haka suka cigaba da hirarsu. Rayuwar tana xuwa masu yadda ya kamata kowane jiyake da matarsa kamar kwai,sannan kuma komi suke so har rawa jikinsu yake wajen kawowa. Sadda zasu koma Nigeria fiyah na manne da babyn Abdoul ga mararta,amman daga ita harshi babu wanda ya sani saida suka sauka gida ai ranar ta kowane bangare jidasu ake mama kasa hkr tayi fiya ta shigo wajenta ta aika masu da abinci na musanman. Mami da ni ima sunga tsaraba harta hauka sai dariya take yadda taga yaran nata duk masha Allah,kuma ta gano duk cikunna ne dasu basu sani ba abun yayimata dadi kamar ta sasu cikinta takeji yadda taga suna cikin farin ciki kuma mazajensu kowane kokari yake ya nuna kaunarsa ga matarsa. Sai washe gari fiyah ta shiga gidansu dafarko ma bata gane gidan ba,saida taga yaya dalha ya fito zai alwallar azahar ta hangame baki tana kallon tsaunin gininsu. Come da mamaki tace"yaya dalha" Shima cikin murna da nuna jin dadin ganinta yace "aaah safiyya saukar yaushe kece haka tubarkallah" Dariya tayi tace"karkaima kace na canza don Allah" Cikeda dariya yace"aibama canza wa ba yadda kikasan inji akasaki aka wankoki" Dariya tayi tana nuna gidan "yaya waye da wannan aikin" Murmushi yayi yace"shiga daga ciki mama nanan baba ma yana kan hanyar dawowa yesmin ma tazo tun safe zasu baki labari bari naje sallah" Kallon ginin taje tana mamakin har yashe akai wannan aikin bata da labari ko awaya basu gaya mata ba. Shigatai tama rasa inda zata bi taga wata doguwar hanya ta bi tanan saiata cikin baban gidansu komi sabo wamda tasan ada basu dashi. Wata kofa ta gani da zata sadata falon gidan tabita wajen tana tura kofar mama na zaune yesmin na mata kitso. Mama bata san sadda taji wata kara ba yesmin tatashi daga kanta tai wake kofa suna rungume junansu. Suna karadin ganin juna mama sakin baki tai tana kallonsu cike da ji dadi sai dariya suke suna makale da juna,suka idasa shigowa ciki fiyah ta saki yesmin ta nufi mama da gudu cike da kwaba mamar tace"bargudun nan karki isomun nan kina gudu baki gudun kije kija wata matsalar." Xubewatai jikin mamar harda kukanta "mama nai kewarki wlh ba saa haka ai kewarku a saida aganku idai gaskiya bazanbi yaya Abdoul ba inanan wajenku" Ta fada tana kuka. Dariya sukaata mamar tace"kinanan kina wannan kukan ko safiyya,bakisan kingirma ba " Share kwallar take tana kallon gidan cike da jin dadi yadda aka gyara ma iyayenta gidan yayi kyau yazama kamar ba nasu ba nada. "Ama waye yayi wannan aikin wlh gidan yayi kyau ya hafu kamar indawo inyita zama nidake" Yesmin na dariya ita da mamar tace"lallai Adda kice kema irin nawa zakiyi wlh nima ranar danazo haka nace" Mama tace kuda nan gidan kuwa insha Allah Ai saidai yini ya kawoku ko idan wata ta haihu cikinku tazo wanka gida."duk sai sukai shiru don kunyace ta rufesu baba ne ya shigo da sallama har fiya tatashi zata ruga sai kunya ta kamata ta koma ta zauna don jitake kamar ta fada jikinsa yadda tai kewarsa. Murmushi yake har ya iso ya zauna shima kowa ya gaidashi dayi mashi sannu da zuwa. Idona ya ciwo da kwalla na sauko kasa ina gaidashi sai kukaya kubcemun mama da yesmin na dariya baban kuma murmushi yake cike dajin dadin ganin uwar tashi cikin koshin lafiya dagani bata cikin wata damuwa. Cikin kulawa yace"xo yaki uwata kukan namiye bacin kin samemu cikin koshin lafiya kuma kema muna fatan haka" Matsawa tai kusa dashi tana ajiyar xuciya "baba nai kewarku a nidai kace mashi karya tai dani yabarni wajenku." Murmushi yayi yace"inbanda abunki ga inda mijinki ke aiki meye anfanin zamanki nan kuma uwata?" Cikin kuka tace "baba nidai bana sin nesa nan wlh ina kewarku koda yaushe" Dariya duk sukai mata yace"kiyi hkr uwata aure babu inda baya kai mutun,don haka kiyiwa mijinki biyayya inhar yace zaitai dake kibishi bazaiji dadi kice bazaki koma ba knjiko keda ma zaki koma makaranta" Cikeda mamaki da jin dafin maganar baban ta dago kanta "dagaske baba,yafada maka ne ni baimun maganar ba kuma tsoro nake nayi mashi yace bazan koma ba shiyasa" Murmushi yayi mta ganin ta daina kukan tana dariya yace"insha Allah munyi maganar dashi tunma kafin kudawo kedai kicigaba da mashi biyayya kina hkr nasan ki gwanar hkr ce kikara kinjiko" Ta sadda kai tana cewa cikin sanyin murya "insha Allah baba" Have"mijinki yana da halin kirki kiyimashi addua koda yaushe kikuma yi mashi godiya don shine da wannan aikin na gidan nan,ya kuma samar ma yayanku aiki mai tsoka yanzu haka yana legos,nima kaina babanshi ya budemun wajen furnitures na xuba ma ,aikata sosai kuma alhadulillah muna samu fiye da tunani gaskiya,haka mijin yesmin duk watan duniya shine siyen kayan abincin mu uncle dinkuma wannan kunsani tun kuna gida albashi yake ban na musanman duk watan duniya,ban haifesu ba amman kasancewarku suna jin dadin zama daku yasa suke mana wannan hidimar,ina sake jawo hankalinku daku dage wajen biyayya da nuna kulawa kuna hkr duk mai hkr zaici ribar zaman duniya Allah yayi maku albarka." Duk muka ansa da ameen. Ranar ina gidan har bayan salar isha,i nabasu tsarabarsu masu uban yawa mama harda fada wai duk ina zasu da wadannanen kayan. Na ware na anty jamila da takwarata don ita akwati nai mata na daban. Wajen ten da rabi saiga yaya Abdoul din dasu zakiyya da malik sun shigo gaida su baban. Aikuwa nan aka dasa wata sabuwar firar duk da kunyar baba da Mama da Abdoul keji. Sai wajen shadaya baba yace mutai hakanan dare yayi na fashe da kuka nace nidai saina kwana amma ya rufe idinsa yace inbi mijina. DA man yes min tun da aka gama salar isha,i yaya muhseen yazo har muka gaisa dashi yana jana wai na koma baturiya irin yan kasar Australia. Haka ina kuka nabisu ina cewa kuma gobe saina dawo na kwana. Dari ya suka ringa man zakiyya na cewa duk son jikin na habibi ashe za,a iya barinsa akwana wani waje." Hararar zakiyyar yayi yace"ba wani nan ko love dina aidai don kar ace bakice zaki kwana a yasa kikai kuka ko." Bata kulashi ba ta shige shashen mami tana turo baki. Zakiyya da malik suka kama mashi dariya Wahse gari taje gidan Anty jamila bata dawo ba Sai can dare sosai yaje ya daukota sunsha hirar yaushe gamo. agidanta ma tasan tana da ciki don har PT strip ta bata tace wlh tayi awo tana mata kallon mai ciki,saigashi kau ya nuna kasa boye murnarta tayi har saida yagane ya isheta da tambaya ta gaya mashi aikuwa asibiti suka wuce aka aunata saiga cikin wata uku cif jikinta mamaki ya kamata tana tunano urin abubuwan data ringayi ashe duk alamunsa ne taga murna wajen Abdoul har goyata yayi ya kawota har cikin mota don murna. Wanna cikin yazo mata da sauki don bata komi saidai kwakwar mijin ta datake duk dare bata yarda idan ba,ai ba. taga kulawa wajen mami da mama kowa dake sonta yana son cikinta yaya jalal yazo sai lokacin suka shirya sosai yana kuma nuna mata jin dadin samun aikin sa,feea tazo har gidan mami inda suka sauka sunsha fira da ita take cewa har yau ba,a fiddo dady ba amman Abbi ya sauko yace zaitaimaka insha Allah zai fito lokacin bikinta ya taho baifi saura sati uku ba. Shima yaya jalal ansaka ranarsa da hasana ta wajen inna balaraba anyi bikin feea da sati guda za,ai nashi. Zakiyya ma cikinta yafito amman fiyah saita rigata haihuwashoyasa mami tace Abdoul nan zaibar fiyah harta haihu shikuma yace bazai koma ba har saita haihu sukoma tare. Mami tace"kota haihun saita gama wanka inkana kama hanya katai katafi ajiko" Badan ya so ba fiyah harda kuka ranar daxai tai dama malik shi yana nan abunsa,bayan tafiyarsa da sati uku akai bikin yaya jalal ya dawo ya hakarci taron daurin aure ya kuma ba ango kudi masu dama sosai. Anan cikin estate din Abbi ya bashI gida akasa hasana aciki,lokacin cikina wata tara zakiyya kuma bakwai kuma kamar yadda Yaya Abdoul kefata twis ne mace da namiji kullum zullumin zuwan haihuwar nake karshe dai tazo da matsala dole akai cs akafiddosu yara masu ruwan kyau inji Anty da yesmin. Yesmin din itama lokacin danata rabon wata shidda ,wadannan jarirai sunga gata baga ubansu ba baga kakarsu mace ba ba kakansu maza ba kowa dokinsu yake naga gata nikaina ,babansu kamar zai cinyemu nidasu haka muka dawo gida nai jinyar ciwona komi mami da ni,ima keyi mun mama da nata gujiri take aikowa ana kawomun ranar suna yara sukaci mamana da Abbin yaya Abdoul. Munga hidima mai sunan hidima tunda babansu ya dawo yaki komawa har saida na gama wanka duk da na towel ne saida nacika arba,in cif Nasha gyara mami gwanace sosai ganin ina samun kulawa daga mami yasa mama ta kwantar da hankalinta duk da banma haihu da kaina ba saida ta gyarani sosai yadda bazan cutu ba har kunyarta nakeji amman ita babu ruwanta. Jaririyar ana ce mata afnan jaririn kuma Affan sun ganin kauna kowa sonsu yake yadda suke da shegen kyau kamar ba diyar africa ba. Dazamu wuce kuka riris nake yi daker na baro gidan mama itama mamin kamar zan ballata haka aka rabamu jirginmu yatashi sai zakiyya ta haihu kozan zo ni. Mami ta hadani da yar aikinta guda yar yarinya ce bata wuce shekara sha biyar ba uwarta ma tana tare da mami. Nakoji dadinta don tana kulawa dasu Affan. . Yaya Abdoul kuwa kamar zai maidani cikinsa haka yake likemun gani nake ma yanzu yafi nanikemun akan sadda ina ina amarya nima kuma ina enjoying sosai don kamar wani sabon amarci mukeci don yayi hkr sosai rabonshi dani yafi wata hudu tun cikina yana wata takwas naji kuma ban son abun. Har na haihu kuma nai wata wajen biyu sannan ai yayi kokari. Muncigaba da rayuwarmu cikin kwanciyar hankali ina kulawa da twis sosai Abdoul yana sonmu yana mana komi zakiyya ta haihu ta samu namiji sunan baban yaya malik akasaka suna kiransa da walid. Yesmin ma ta haihu itakuma mace ana ce mata salma haka rayuwar ta cigaba cike da jin dadi duk da baka rasa kalubale ba ni nawa yan matane suka addabi habibi kullum ina cikin kishi amman ganin shi bata su yake ba yasa na maida hankalina kan mijina ina kulawa dashi yadda ya kamata. Dadyn feea ya fito bacin bakar wahakar ya caza kamanni ba ma lallai ka ganeshi ba.su mamman har yau suna magarkama babu ma ranar fiddosu.umma kau saidai mukaji labarin mutuwarta gawar kuma gudaje suka hau kai sunaci abundai babu kyaun gani bayan shekara biyar na sake haihuwar mace sunana aka samata saboda Abdoul yana masifar sona muna kiranta mimi daga nan ban sake haihuwa ba muka cigaba da tarbiyartar da yaranmu na gama karatuna amman bana aiki saboda Yaya Abdoul ya gama mani komi kasuwanci nake kasa ruka zan iya cewa komi sai hamdala zakiyya yaranta biyar cif yesmin kuma uku kamar ni Anty biyar itama hasanar yaya jalal daya. Rayuwa tayi kyau komi Alhamdulillah munzama family na gaske nidasu Abdoul *ALHAMDULILLHAI TAMMAT ANAN NAKAWO KARSHEN ABDOUL-NASSER DARASIN DAKE CIKI ALLAH YASA YAJE GA MASU KARATU NGD DA SOYAYYARKU ALLAH YASADAU DA ALKAIRI IDAN NAIMA WANI BADAIDAI BA YAYI HKR HAKA TSARIN RUBUTUN YAZO,SAI MUN HADU CIKIN ABU KHALIPHA INA ALFAHRI DAKU* BISSALAM.