🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Da Sunan Allah mai rahama maijin kai TSOKACI Ina rokon Allah yasa yanda nafara littafin nan nagama Lapia Allahumma Ameen.... Banyi littafin nan Dan cin zarafin wani ko wata Bah. Nayi neh Dan nishadi dakuma fadakarwa...ngd.. Page1⃣ *MASARAUTAR GOMBE* Motoci neh wajan guda biyar suka shigo cikin Airport din dai dai inda jirgin ya sauka sukai parking, fadawa neh suka dinga fitowa daga motocin, biyu daga cikinsu suka shimfida wani hadadden red carpet a daidai step din jirgin, niko ummy na gyara tsayuwa dan naga wanene zai sauko daga jirgin yanda naga fadawan sai Rawar jiki suke. Andau mintina kamar sha biyar Sannan wani hadadden saurayi fari tas ya leko tareda yatsine fuska, Ahankali ya soma saukowa daga step din jirgin, motar dake tsakiya wani bafade ya bude, wani dan dattijo ya fito cikin kayan sarauta, Tsantsar kamar da suke da saurayin neh yasa na tabbatar da mahaifinshi neh.. Dan Murmushi saurayin yayi daidai sanda ya iso inda mahaifinshi yake tsaye, dasauri ya qarasa tareda rungumeshi, cikeda kasaita mai martaba ya dan bubuga bayanshi tareda cewa "barka da dawowa my son", dan murmushi yayi sannan yace "Am vry happy to see uh dad" murmushi mai Martaba yayi aka bude musu kofar motan suka shiga.. Basu tsaya koina bah sai katafaren gidan sarauta, horn motar farko tai aka wangale gate din Gidan, dagudu motocin suka shiga cikin gidan zuwa inda yakamata su tsaya, tsakar gidan bayi neh burjik kowanne yana aikinda aka sashi, Sanin dawowan Yarima Fardeen dakuma halinsa yasa duk ma'aikatan suka aje aikinsu don zuwa kwasan gaisuwa, mai martaba da yarima na fitowa sukai cikin gidan, tareda rakiyan fadawan dake take musu baya, ganin haka yasa kowa yakoma bakin aikinshi.... Kishingide suka samu fulani a babban falonta wata baiwa tana mata tausa, da sallama mai martaba ya shigo hannunshi cikin na danshi, baiwar na ganin sun shigo ta rusuna ta gaidasu sannan tabar wajan dasauri, mikewa zaune fulani tai tana murmushi tana kallan dan nata, cikin sanyanyan murya tace "barka da zuwa dana" murmushi kwance akan fuskarshi yace "lapia lau mum nasameku lapia?" fulani daketa kallan dan nata cikeda farin ciki tace "lapia lau, ya Karatu ina fata ansamu abinda akaje nema" kai ya gyada, mikewa mai martaba yayi tareda cewa " umm ni kunga tafiyata tunda ni ba'a gani bah, mutane na jirana" dan dariya fardeen da fulani sukai ya fice daga falon yana cewa " nima lokacina na nan zuwa", mikewa fulani tai tace "zakaci abincine Yanzu ko sai kayi wanka??" Dan jim yayi sannan Yace "bari nai wankan tukun", side dinshi ya nufa, ko ina a gyare tsaf ya shiga bedroom ya chanza zuwa towel sannan ya fada toilet... *MASARAUTAR ZARIA* Zaune take kan wani hadaden carpet bayi zagaye da ita ko wacce qoqari take dan taga ta farantawa uwar gijiyarta rai, wata da kayan itatuwa a gabanta tana barewa, wata kuma farce take gyara mata, wata kuma gashin kanta take taje mata tareda sa sinadarai masu sa gashi laushi da kanshi akai, wacce take kusada ita koh labarai take bata na ban dariya ita kuwa sai dariya take gwanin ban sha'awa, suna cikin nishadinsu jakadiya ta iso wajan dasauri tareda rusunawa Sannan tace " Allah ya taimakeki, uwar gijiyata nasan ganinki" bata rai tai Sannan ta kalli jakadiyan cikin bacin Rai tace "jakadiya mai yasa koda yaushe kikesan batamin rai??" na fada miki ki daina durkusa min kinqi, banaso naga babba kamarki ko wanda bai kaiki tsufaba yana durkusa min, cikeda ladabi tace "Tuba nake ranki shi dade insha Allah daga yanzu na daina" Mikewa tai Altine baiwarta itama ta miqe, jakadiya na gaba tana biye da ita har side din mahaifiyar nata... A bakin kofa jakadiya ta tsaya ita da Altine suka karasa, da Sallama suka shiga dakin zaune suka sameta hannunta riqe ta Apple tanaci, dasauri Altine ta tsugunna tareda kwasan gaisuwa, Apple dinda ke hannunta ta aje sannan ta amsa gaisuwan tace "Altine dan bamu guri", dasauri tabar dakin, ta Kalli yar nata Tace " Parveen dama bah wani abu baneh, Aisha ce ta kirani ta roqi Alfarman Tanaso kije kiyi mata hutu koda na sati daya neh" shiru Parveen tai kanta na Qasa, Ummanta ta kalleta Sannan Tace " banji Amsarki bah??" dan dagowa tai Tace " umma ban ganeh wa kike nufi bah??" umma tadanyi Murmushi Tace "Aminiyata Aisha Matar sarkin Gombe" Damm! Gaban Parveen ya fadi idonta cikeda kwalla tace "Umma kinfa san halin Yarima nidai Banaso naje"... Haquri Umma ta soma bata dakyar ta shawo kanta ta amince badan Ranta yaso bah. Da daddare mai martaba Ya kirata dan Tambayanta Shawaranda ta yanke, Batareda bata lokaci bah Ta amsa mai, cikeda murna yace "ki shirya Gobe in Allah ya kaimu sai mu tafi nida kaina zan kaiki dan inaso dama nakai ziyara masarautar gombe".. Tho fah! Ya zaman Parveen zai kasance da Fardeen?? Sai kun biyoni dan jin yanda zata kaya.. Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 A WANI MASARAUTA 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol Page2⃣ Haka Parveen tabar dakin mahaifinta jiki bah kwari, koda ta isa dakinta hana kowacce baiwa ta shigo mata tai. Dakanta ta hada kayanta da duk wani abu datake buqata duk da tasan chan kamar a gida take, dakyar barci barawo ya kwasheta a daran.. Washe gari wuraren karfe Shadaya jirginsu ya tashi zuwa garin gombe, Koda suka isa sun samu mutanen mai martaba na jiransu, dan haka jirginsu na sauka suka shiga motoccinda aka tanadan musu tareda yan rakiyansu zuwa gidan Sarkin Gombe.. Fulani sai shige da fice take kamar bah matar sarki bah, cikin mintina kadan aka gyara mah Parveen dakinda zata zauna Tareda haka kalolin Abinci iri iri, yau Fulani cike take da Farinciki yarta zatazo, tana daki zaune Fardeen yayi Sallama ya shigo, amsawa tai tareda dagowa ta kalleshi, yadanyi murmushi Yace "Fulani wai sarki Salman na Qasar Saudi Arabia neh zaizo ko ko Obama??" naga Sai rawar Jiki Ma'aikatan gidan nan keyi, naga Mai Martaba Sai Fara'a yake, gashi kema nazo nasameki. Murmushi tai Sannan Tace "Yarima knan, Sarki Khaleed neh Tareda Yarshi ke Tafe inaga ma yanzu suna Cikin Garin nan Qarasowa kawai ya Rage, Yadan Yatsine Fuska Sannan Yace "badai Wannan Yarinyan Tashi bah Mara kunya n I hope Bah zama Tazoyi bah" Hade rai Fulani Tai zatai Magana sukaji Horn din motoci, Dasauri Ta mike Tafito daga dakin, Bayinta dake take mata baya suka rusuna suka gaisheta Sannan suka Soma binta a baya... Futowan Fulani daidai da Fitowan Parveen daga mota, dagudu ta Qarasa tareda Rungumeta, cikeda Farinciki Fulani Tace "Barka da zuwa Yata" Bayin dake Wajan suka zube dan diban Gaisuwa, Parveen ta Yatsine Fuska tace "Ni Fulani banaso bayi na duqamin pls kice su daina" Dan Dariya Fulanin Tai Sannan Tace "Har yanzu dai kina nan da Halinki, Wannan Shine Ikon ai" Hannunta ta Kama sukai side dinta Cikeda Farinciki.. Sarki Khaleed ya Shiga fada Cikeda Farinciki, dasauri Mai Martaba Ya mike sukai Musabaha tareda Rungume juna, Sarki Alameen Yayi Matukar Farinciki da Ganin Abokin nashi, sun Zauna a Fada, Dakatai, Masu Anguwanni, da Sauran Masu Muqamai na Sarauta nata Kawo Gaisuwa, Sai Bayan Sallan La'asar Sannan Suka Samu kebewa a Side din Mai Martaba. Suna Cikin Hiran Bayan Rabo Yarima Fardeen Yayi Sallama Ya Shigo tareda Rakiyan Abokinshi Adnan da fadawanshi, Zama Sukai Kan Carpet din Falon Sannan Suka Soma Gaida Sarki, Sarki Khaleed Ya kalli Yarima Cikeda Kulawa Yace "Yarima an Girma Ya Karatu??? Ka Kammala neh?" kai Ya gyada Sannan Yace "Angama Ranka ya Dade", Sarki Khaleed Yashafa Kanshi Yace "Allah yamaka Albarka" Yarima Ya amsa da Ameen Sannan Suka Mike Suka Bar Falon... Side din Yarima Suka nufa shida Abokinshi, har sunkai Bakin Kofan Ya Daga Hannu Batare daya Juyoba Fadawan dake Take musu baya suka Bar wajan Dasauri, Adnan Ya bude kofan Suka Shiga. Kan Three seater Ya Fada Tareda Sakin Wani dogon Tsaki, Adnan Yakalleshi Cikeda Mamaki Yace "Deen Yadai Whts Wrong?" tsakin Yakuma Ja Sannan Yace "Wallahi Mai Martaba neh Waishi dole sai nayi aiki a Nigeria nikuma Sam Banasan Zaman Kasan nan" adnan Yadan nisa Sannan Yace "Buh Yarima Yan Kasan nan nabuqatanka matuqa, Suna neman kwararun Likitoci Kamarka, Shiyasa Zakaga Mutane na fita Qasashen Qetare Ganin likita. Kuma Bawai dan Fararen sun Fimu baneh Aa! Zakaga Yawanci mah Baqaqen Fatan neh Anan tho.... Saurin Katseshi yayi ta hanyar dagamai Hannu, Dasauri Yayi Shiru, ya Mike Sannan Yace "pls katashi kaban waje I need privacy" Mikewa Adnan Yayi dasauri dan Yasan Halin Abokin nashi Yamai Sallama Ya bar Side din... A Dakin Fulani Suka Yada Zango itada Yar nata, Hadimai Sai Hidima suke da Parveen kamar zasu hadiyeta, Hira Suke Sosai Cikeda Farinciki, Sunci sunsha Sannan Jakadiya ta nunama Parveen Dakinta Sannan ta Nunama Altine Nata dakin..Kwanan Sarki Khaleed biyu Ya Koma.. *Bayan Kwana Biyu* Cikin Sauri Yarima Yafito fadawanshi na takemai baya, hannunshi Riqe da Agogo yana qoqarin Daurawa, Daidai Nan Parveen Tafito daga dakinta Cikeda Farinciki Tana Waya da Ummanta, Hankalinta Sam baikai kanshibah, Shima haka. Jitai Tayi karo da mutum Ta dago Zara xaran idanunta dasauri suka hada ido, Hade Rai Tai, Hadiye Yawu tai dakyar Da Qarfin hali Tace "Haba Mallan baka Gani neh" da Mamaki Yarima Ya Kalleta Yace.... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 A WANI MASARAUTA 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol Page3⃣ Jitai Tayi karo da mutun Ta dago Zara Zaran idanunta dasauri suka hada ido, Hade Rai Tai tah hadiye yawu dakyar. Da Qarfin Hali Tace "Haba Mallan baka gani neh??" da Mamaki Yarima ya Kalleta Yace "Keh Har kin Isah ki Hanani Yin Abinda nagadama a masarautar Ubana" Cikeda Tsoro Tace "Gani nai kana abu irin na Jahilai dabasuje Islamiya bah" Zaro ido Yayi karo na Farko A Rayuwanshi Ya daga Hannu Cikeda Fushi Zai saiga Fulani, dasauri Yabar wajan Yana Huci, fulani Ta qaraso inda Parveen ke Tsaye Tace "Lapia meh ya Faru?" dan Murmushi Tai Sannan Tace "Bkmai dama Tunda nazo bamu hadu baneh Sai Yanzu" Kallanta Fulani tai na Alamar Rashin Yarda Tace "Shknan kije ki Shirya nasa Sarkin mota yakaiki Yawo" Tsalle Tai Tareda Rungume Fulani tace "Shiyasa nake Qara sanki fulani" Dakinta tai dagudu tabar fulani nan Tsaye Tana Dan Murmushi... Dakatar da Bayinshi Yayi dae dae kofar Fadan ya shiga da sallama, Mutanen Yan fada dake Zazzaune suka amsa mai Ya nemi guri ya zauna cikeda ladabi Sannan Ya soma kwasan Gaisuwa. Dogarin Dake gefen Sarki Yace "An Gaisheka Yarima! Sarki ya amsa" Waziri dake Chan gefe Ya kalli Mai martaba Yace "Allah ya Taimakeka Yarima Ya iso" Mai Martaba Yamai nuni dan Haka Ya Cigaba da cewa "Dama Maqasudin Kiranka Fada Shine, Sarki Yace a Qara jadadama ba Komawa Qasar Farin fata dan Cigaba da Aiki, Yanzu haka Ya bada kwangilan Gina maka Asibiti naka na kanka a nan cikin Gari" shiru Fadan Yayi Alamar ana Jira Aji Mai Yarima Zaice, Murya chan Qasa Yace "Duk Yanda kace Haka za'ayi Mai Martaba Godiya nake" Dogarin Dake gefen Sarki Yace "Yarima ya gode" Waziri yace "Zaka iya tafiya". Mikewa Yayi jiki a Sabule Ya Fice daga Fadan, Bayinshi dake Waje suna jiranshi suka take mai baya har side dinshi, Daidai bakin kofa ya musu alama dasu tafi, cikin Rawar jiki suka bar Wajen Ya shige Falonshi... Maganar Parveen ke Yawomai cikin Qwaqwalwarshi, Kai Kawo Yasoma Yi Cikin Katafaren Falonshi lokaci lokaci Yakan furzar da iska Tareda naushin Tafin Hannunshi na hagu, A hankali Ya Furta "Harni Kamarni Yarinyan nan zata kira jahili?? Lallai batasan Yarima fardeen bah" Yana cikin Safa da marwanshi Abokinshi kuma Dan uwanshi Bilal (Yaran waziri) ya Shigo da sallama ya zube kan kujeran tareda Fadin Wash! Koh Kallo bai Ishi Yarima bah, Ganin safa da marwan da yake Yasa yace "Wai Yaneh Yarima meke Faruwa??" Tsaki Yarima yaja Baice Komai bah, Bilal Ya kyalkyale da Dariya Yace "Koh duk akan Maganan Rashin Komawa Egypt neh??, Mallan Kasha Zamanka A nigeria" Ya Qara Fashewa da Dariya Yace "nasan Matsalarka bah komawa balle a cigaba da Duniyancin da Aka Saba" Dariya ya cigaba dayi harda riqe Ciki. Yarima ya Kalleshi Cikeda Quluwa Yace "Bansan iskanci Bilal, Danma fah kaine da Yanzu Nasa an zanemin kai" Tsagaitawa da Dariyan Yayi Yace "Nayi shiru dan nasan Bah mutunci ka cikaba yanzu kasa a suburbudenin Anma a Waje dan A Cikin gidan nan kasan ban Tabuwa, Yanzu Dai Fadamin meke Faruwa??" Batareda Ya Kalleshi bah Yace "Bah Matsalarka bace" Bedroom ya shige Bilal ya kwanta kan 3seater Ya Soma barci... Yinin Ranan Yarima Bah abinda Yakeyi Sai Saqawa da kwancewa, lokaci zuwa lokaci yakan Maimaita Kalmar "Jahili" Sam Yama Manta da Maganan da Aka fadamai a fada akan qin amincewa daya koma Kasar Waje. Yanzu mah haka Yakai kusan Awa biyu a Zaune Yana neman Mafita, Chan Ya saki wani Lalausar Murmushi wanda ya Qarawa Fuskarshi Kyau Yace "hakan mah Za'ayi" Ya mike dsauri Ya Shiga Toilet dan Watsa Ruwa... Wuraren Qarfe Takwas na dare Parveen zaune itada Fulani Suna Hira, Hadimai Nata Hidima dasu Bangaren Kayan Marmari abinci kala kala, dadai Sauransu, Fulani Tana Kishingide Ana Tausa mata Qafa, Ta Kalli Parveen dake Tauna Apple a hankali tana latsa wayanta Tace "Parveen wai yaushe zamuzo musha biki?? Dan Murmushi Tai Tareda sunkuyar dakai. Fulani ta murmusa Tace "Allah ya kaimu lokacin, Dai Dai nan Yarima Ya shigo Tareda Sallama, a Tare suka amsa, ya zauna kusada qafan Fulani Yace "Yanzu Fulani Abinda akamin Ydace knan??, A hanani komawa. Nidai Gaskiya inaso na koma" qurrri Tamai Tana Kallanshi Harya gama ta hade rai Tace "Tashi Kaban guri" Da mamaki ya kalleta Yace "Haba Fulani keda nazo na fadamiki damuwata ko naji sanyi" kofa ta nunamai sannan Tace "Idan bazaka fita bah ni zan bar maka dakin" Mikewa Yayi Sah sah Yabar dakin, Duk abinda Yake Faruwa Parveen na Zaune tai Kamar batajishi bah tanata latsa wayanta har ya fita... Yau Parveen Ta tashi dasan zuwa yawo, dan haka tana wanka ta shirya cikin atamfa ja mai Ratsin baki, Dinkin Riga da Skirt kayan sun amsheta Sosai, Dakin Fulani ta nufa Altine na biye da ita riqe da Wayoyinta da Jaka, Da Sallama ta Shiga ta rusunna ta gaidata Sannan ta fada mata, Fatan Alheri Fulani tai mata Suka Fito, Drivern dazai Kaiso Ya qaraso Dae dae qofan dazasu fito Yayi Parking, Duk abinda akeyi Yarima Nachan cikin Runfar Shaqatawa Yana Kallansu, Cikin isah Parveen Ta fito Altine Tai saurin Bude mata qofan Ta shiga, Sannan Itama ta zagaya ta Shiga, Drivern Yaja motan suka bar Gidan, Dasauri Yarima Ya Tashi Ya nufi side dinshi ya dauko Makullin motanshi, Bayinshi Sukai Saurin rufamai baya Ya Tsayar dasu dasauri Sannan Ya shiga motar Ya fice daga gidan dasauri. A hankali yake binsu Har Yaga sun nufi wani Hadadden wajan shaqatawa, A Hankali Ya saki lallausan Murmushi har saida Fararen haqoranshi suka baiyana.... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 A WANI MASARAUTA 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol Page4⃣ A hankali yake binsu Har yaga sun nufu wani Hadadden Wajan shaqatawa, A Hankali ya saki Lallausan murmushi Har saida Fararen Haqoranshi suka baiyana, Parking sukai Drivern Ya fito dasauri ya zagaya ya budemata kofan, qafan damanta ta sako a qasa Sannan ta Sauko na Hagu ta fito a hankali tafara takunta Maijan Hankali Altine na take mata baya riqe da wayoyinta da jaka, wani dan Qaramin Canopy suka Samu, Parveen ta zauna Sannan Taima Altine alaman itama ta zauna. Samarine da Yanmata a wajan dukansu cikeda farinciki, kowanne canopy ka juya zakaga masoyane zaune suna Hira cikeda nishadi, Dan Murmushi Parveen ta saki daidai nan service din wajan ya iso, Cikeda ladai ya kalli Parveen Yace "Ranki ya dade meh kikeso??" Altine tai Saurin tareda da Fadin "Ruwa zaka kawo sai fayrouz da meat pie" Amsawa yayi harya juya parveen tace Cikin lallausan muryanta batareda ta kalleshi bah "Make it 3 pls" Amsawa yayi yabar wajan dasauri.. Daidai nan Fardeen ya qaraso wajan tareda neman kujera ya zauna, Altine ta mike dasauri, Murmushin mugunta Yayi yana Kallan Parveen data hade rai Yace "No! Bah sai kin tashi bah yanzu zan bar wajan" juyawa Yayi yaga mutane burjik a wajan kowa na Harkan gabanshi, Yawanji Masoyane. Ya kara Sakin Murmushi Sannan Yace Cikin Zazzakar muryanshi kamar namai jin barci "Paveen Or What ever uh r Cal, Har keh kin isah kizo gizanmu ki gayamin Magana??. Ni Nafi Qarin a Wulaqantani, indai Jahilci neh zan nuna miki koh Hali irin na jahilai" Tabe Baki Tai Tareda Kauda kai. Bata Ankara bah Taga ya Buga Tabur din tareda mikewa, Hakan yasa kowa dake Wajan Hankalinshi ya dawo kansu, cikin Kakausan Murya Ya nunata da dan yatsa Yace "Kinyi Kadan, Bakeba kaf danginku. Soyaiya ceh nace banyi dole neh?? Meh zanyi dake Har dazaki dinga bibiyata, Oh! Dan nace bana sanki Shine Zaki rinka bibiyana Akan na Kusanceki??, Mutanen dake wajan suka zazzaro ido suna kallan juna Yace "meh kike dashi??, inaso naja miki kunni kar ki qara kiran wayana ko kice zakizo nemana Akan daqiqin qudirinki na fada miki, Banza Mazinaciya", yana Gama fadi yabar wajan dasauri tareda jan tsaki, Har Yabar wajan Mamaki neh Qarara a fuskarta, Hawayen dake Maqale a idonta ya qarasa zubowa, Mutanen Dake Wajan sai Kallanta suke Tareda Allah wadai da Halinta.. Kallan Altine tai idanunta chabe Chabe da hawaye Tace "Altine mu tafi" Altine ta kwashi Wayoyinta da jakanta, kuka sosai Parveen take a mota har Suka iso gda, Dakinta ta nufa tama Altine alama na karta biyota, Ta fada kan Gado ta fashe dawani matsanancin kuka. Fulani taji Dawowansu tanata sa ido taga Parveen anma Shiru har wajan Minti talatin, dakanta ta nufi dakin Tareda Sallama, Parveen najinta ta mike daga kwancen datake ta gogoge Hawayen Fuskanta, Fulani ta qaraso dakin Tace "Lapia Parveen naji dawowanku inata sa ido naganki yau nayi kewanki baki nan balle muyi hira" qago Murmushi tai Tace "Lapia lau fulani, Nagaji neh shiyasa dama Yanzu nake shirin zu..." Saurin Katseta Fulani tai da Fadin "Ya naga idonki yayi ja?? Parveen fadamin Gskiya meke damunki??" duqar dakai tai tace "Bkmai Fulani wani abune Ya fadamin ido" Dan Murmushin rashin Yarda fulani tai ta riqe Hannunta ta miqar da ita tsaye Tace "Muje kiga Wani abu" Tare suka fito Haraban gidan, Kamar ance ta dago suka Hada ido da Fardeen Dake chan nesa dasu Cikin Yar runfa suna Hira Shida Abokinshi, Wani Malalacin Murmushi ya Sakar Mata ta kauda kai dasauri Fulani na rike da Hannunta, Garden din Gidan Suka nufa, Sakin Baki Parveen tai Tana Kallan Garden din, A hankali ta Saki Hannun Fulani ta Qarasa Cikin Garden din, Saita nemi Bakin Cikin dake damunta ta Rasa, Ado Akaima Garden din, Fulawas neh burjik gwanin ban sha'awa, Daga gefe Guda hotunanta neh kala kala, Sai dan wanni kyalle da Aka Rubuta "Welcome to Badras Kingdom Princess parveen" Dariya tai Ta juya tana Kallan Fulani, Dagudu ta Qarasa tareda Rungumeta tana Dariyan Farinciki, Cikeda jin dadin yabawan datai Fulani Tace "Mai Martabane Yasa Akai Wannan" Sakin Fulani tai Ta karasa kan Wani hadadden Carpet dah aka zube Gifts Kala Kala, Ta zauna Tana Budewa Cikeda Farinciki... Fardeen dake Zaune sanda su Fulani suka Wuce Hankalinshi Yaqi kwanciya Ya Kalli Mahdi Yace "Au b ryt back pls" bai jira mai zaice bah ya nufi Garden din, mutuwan Tsaye yayi yana Kallan Garden din, Ranshi neh Ya baci dan Yasan bah Wanda zaisa ai Wannan Sai mai martaba. Ranshi a bace Yabar Wajan a Ranshi Yana cewa "Banason Zuwan Yarinyan nan I hate her, duk sanda tazo banasamun kulawan Mai martaba balle Fulani" da Wannan Tunanin ya nufi side dinshi kota kan Mahdi bebi bah ya wuce... Tho Fah mudaije Zuwa... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 A WANI MASARAUTA 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol Page5⃣ Dare Ya tsalla, Duhu ya mamaye bah Abinda kake gani sai Hasken Fitulu ko ina. Masu iya magana kance Dare mahutar bawa. Duk mai Rai yana Barci a wannan lokacin, Parveen na hango tsaye a dakinta Sai safa da marwa take, A hankali na qarasa dakin don in tabbatar da abinda idona ke nunamin, hawaye ne chabe Chabe a idonta, lokaci bayan lokaci takan zauna tareda Fashewa da wani sabon kukan, Dakyar ta kwanta badan tasamu mafita bah, Saidai tuna idan tacigaba a haka batai barci bah zata cutu, dakyar bacci barawo ya saceta duk da bah baccin dadi bneh... Fardeen Kwance Kan makeken Gadonshi, daga gefenshi wani Kyakyawar Yarinya cikin bargo sai sheka Barcinta take, Dan Tsaki yayi lokacinda ya juya ya kalleta, Ya mike Ya shiga toilet, Wanka yayi ya fito ya zauna, Abinda yafaru dazu ya tuna, Ya saki Qayataccen Murmushi, lokaci guda ya hade rai tuna abinda yagani dazu, A hankali ya furta "I have to do something" tsaki yaja ya mike Yasa kayan barcinshi Ya koma Falo dan bazai iya kwantawa akan gadonba kuma... Dasassafe ya Shirya cikin Kayan motsa jiki, yana fitowa suka hade da bilal shima cikin shiri, Bilal yadanyi dariya Yace "dama nasani banzo bah najira kabiyomin" hararanshi yayi yace "kataba ganin nabiyama wani" wani dariyan ya saki yace "Aa ban taba gani bah, Anma ka kusa" Tsaki Yarima yaja Yace "Dallah mutafi dan indai kaine sai akai gobe kana zuba", Gum Bilal yayi suka nifi gym dinda keh gidan, Wai! Nayi Matukar mamaki yanda naga Yarima na daukan Qarfe, A raina nace Lallai dama haka yakeda Qarfi, labewa nai inata kallansu har suka gama. Wani bawa na riqe da towel dinshi yana tafiya cikin isa dan qarasawa side dinshi, Daidai nan Parveen ta fito Daga side dinta cikin Kaya na Alfarma Altine natake mata baya, Koh Kallanshi Bataita haka shima har suka qarasa side din Fulani. Da Sallama ta shiga dakin sannan tama Altine alaman ta tsaya, Fulani dake kishingide jakadiya na gefenta ta amsa Fuskarta dauke da murmushi, Wuri tasamu ta zauna Tareda Gaida Fulani cikeda ladabi, Fulani ta amsa Fuska a sake.. Jakadiya tai Saurin Gaidata Sannan ta mike Tabar dakin, Shiru neh ya ratsa dakin, Chan Tai Qarfin Halin Cewa "Fulani dama inaso nakoma Qasarmu neh" Mamakine Qarara a Fuskan Fulani, Ta mike Yazauna Tareda Kallanta Tace "Saboda meh Parveen?? Koh Wani ya bata miki Rai neh?? Dan Allah ki Fadamin, kwananki Fah uku knan shine Har zaki tafi" Shiru tai kanta na Qasa. Fulani Cikeda damuwa tace "koh Umman nakine Tace kidawo??" Girgiza kai tai Alamar Aa, Fulani tamike tadawo kusada ita ta zauna tace "Fadamin Parveen meh ya faru meh aka miki" bude baki tai zatai magana anma ta kasa saima fashewa da kuka datai, A hankali tace "Ina kewar Umma neh" Murmushi Fulani tai tace "Allah ya shiryeki Parveen" dakyar ta lallasheta tai Shiru suka cigaba da hira anma Har lokacin bata saki jiki bah... Mai martaba zaune shida mutanen Fada, Yarima neh Ya shigo da Sallama tareda Rakiyan Bilal, Guri suka samu suka xauna tareda gaida Sarki da mutan Fada, Sarki Ya Kalli Yarima Yace "Maganar Ginin Asibitin danama Alqawari Ya tabbata, Yanzu Haka an Fara Gini dan Haka saika zama Cikin Shiri Saboda kasan Bazai dau lokaci bah, Sannan Abu na biyu ina Fata mahaifiyarka tama bayani??" girgiza kai Yayi Alamar Aa! Cikin isa mai martaba Yace "Kaje Wajanta zataima bayani" Ya Mike sukai musu sallama Suka nufi side din fulani, Bilal sai tsokanarshi Yake yana Kiranshi "Dah Proffesional Doctor" Yarima koh Sai hade Rai yake. Fulani ita kadaice Zaune Sai Hadimanta daketa kaiwa da komawa, Bilal neh Yayi Sallama Ta amsa suka Shiga, Har Qasa Ya Tsugunna Ya gaida Fulani, Ta Amsa cikeda kulawa. Yarima koh kan 1seatern dake gefen fulanin Ya zauna yana Hade Rai, Bilal Yace "Dama Mai Martaba neh Yace muzo akai wani saqo daya bari" Fulani takalli Yarima daketa Hade Rai Tace "Bah komai baneh, Mai Martaba Yace Kai Qoqari ka Fitoda Mata kai Aure" Zaro ido yayi Yace "Aure Fulani??!" tace "Kwarai Aure" bata Fuska yayi Ranshi a bace Yace "Haba Fulani har nawa nake da Za'ace nai Aure am just 26 fah" Hararanshi tai Ta Kalli Bilal Tace "Kutashi Kuban Waje", Suna Qoqarin kiqewa Parveen tashigo dakin dagudu tareda Fa'dawa jikin Fulani tana dariya Tace "Fulani gst what??" fulani tana Murmushi Tace "Wht??" fara'a kwance kan fuskanta Ta kwalla ihu Tace "Umma na zuwa" itama dariyan tai Qasa Qasa Tace "Allah ya kawota Lapia" Sam Parveen bata lura dasu Yarima bah, Hankalinta ya tafi, Suko su Yarima Tv tazaman musu Sai Kallant suke, Muryan bilal datajine yana cewa mun tafi fulani Yasa ta juyo suka hada ido da Yarima, Hararanshi tai suka bar dakin... Zune Take Cikin Garden din Gidan Sanyanyan iskan dake Wajan sai bugunta yake cikeda nishadi, Zaman jiran qarasowan Ummanta kawai take, Jakadiya ce Tashigo Garden din Ta durqusa Har qasa Takwashi Gaisuwa Sannan Tace "Mai Martaba nasan Ganinki yanzu Yana haraban gida yana jiranki" Tho Tace tareda miqewa Altine na biye da ita, A Haraban Gidan suka iskoshi tareda fadawanshi, Ta Karasa dasauri tareda tsugunnawa, Saurin tareta yayi yana murmushi yace "Tashi Tashi" ta mike tana Murmushi, Ya kalli fadawanshi yace "ku tsaya anan" Sannan ya kalli Parveen yace "muje koh??" murmushi tamai suka Fara tafiya yana janta da hira... Bayan gidan suka nufa, sai bata labarai yake masu dadi daban dariya, Parveen koh dayake ansamu abinda akesi sai dariyan take, sunyi tafiya mai nisah har Suka Qarasa wani rafi dake bayan gidan, Carpet neh shimfide a wajan sai wasu bayi dake tsatsaye a wajan, nuna mata yayi ta zauna Shima ya zauna, aka Fara hidima dasu da kayan ciye ciye kala kala, Mai Martaba Ya Kalli Parveen Yace "Mahaifinki mutumin kirki neh, haka mahaifiyarki kiyi qoqari kibiyo hali irin nasu" murmushi Parveen tai kanta na Qasa. Yace "Parveen ina jinki kamar Yarima, Ki saki jikinki. Dake da Yarima duk daya kuke a wajena" Murmushi tai Batace komai bah. Shima murmushin Yayi Yace "Mahaifiyarki na hanya koh??" Kai ta gyada yace "Allah ya kawota Lapia" Ameen Tace suka cigaba da hiransu cikin nishadi. Sun dade suna hira Sannan Suka bar Wajan, Mintina kadan motoci suka Shigo gidan, Sam Parveen batasan Fulani ta fita bah saidai Ganinta tai an Bude mata qofan mota ta fito Sai Ga Umma itama ta fito, Ai a 360 ta tafi ta rungume Ummanta tana dariya harda hawaye, dakyar ta saki umman nata sukai Side din Fulani dukansu Cikeda Farinciki, Bama kaman Parveen... Muje zuwa...! Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 A WANI MASARAUTA 🏤🏤🏤 👑 By Ummy Abduol Page6⃣ Sam Parveen batasan Fulani ta fita bah saidai Ganinta Tai an Bude mata qofan mota ta fito saiga Umma itama ta Fito, Ai a 360 ta tafi ta rungume Ummanta tana dariya harda Hawaye, Dakyar ta Saki Umman nata sukai side din fulani Dukansu cikeda Farinciki, Bama kaman Parveen. Anci ansha Anata Hira, Saida ta huta Sannan Ta Qarasa ta kwashi Gaisuwa wajan mai martaba, Yayi farinciki Sosai da zuwanta... Suna Zaune Ya da uwa a side dinda Aka sauketa, Umma Ta kalli Parveen tace "My Baby yanaganki Wani iri? Tl mie whts wrong??" qirqiran murmushi tayi tace "Bkmai Umma" kallan Rashin Gamsuwa tai Tace "Bansanki da Qarya bah Parveen Tl mie??" Ta dago zatai magana Akai Sallama, Jakadiya ta shigo tareda Tsugunnawa, Umma Fuskanta dauke da Murmushi tace "Jakadiya ya akai" Cikeda Ladabi Tace "Yarima Yace aimai Iso" Umma Tace "Kice Ya Shigo" Ta mike Dasauri Ta fita. Turo Baki Parveen tai ta kauda Kai, Da Sallama Ya shigo Yana Murmushin shi Mai Daukar Hankali, Umma Cikeda Fara'a Tace "Nayi Fushi Yarima" Dariya Yayi Mara sauti Yace "Ummana Am Sorry Wallahi Abubuwane Suka Sha kaina, Buh kinga Yanzu ai nadawo" Itama Dariya Tai Tace "Tho Shiknan" ya Qara Kallanta Yace "Naji Dadin Zuwanki Fah Ummana pls ki taimakeni da Wani Abu dan Allah" Umma Tace "Haba Yarima Ai bah Saika Roqa bah Just tl mie" Yadan Kauda Kai Yace "No Bah Ynxu bah Inason dagani Sai keh neh mu Tatauna" Murmushin Manya tai Tace "Shiknan" Hira Sosai Umma da Yarima Keyi Parveen koh Ta hade Rai, Ganin Hiransu bana Qare bneh Ta Mike a Qule Tace "Umma Goodnight" Umma Tace "Tun Yanzu??" Kai Ta gyada Tabar Dakin Fuuu... Dan Murmushi Yarima Yayi Yace "Nima Umma Barinje Nabar Mutane" Umma Tace "Shiknan Saida Safe" ya Mike Tareda cewa "Allah ya tashemu Lapia". Parveen na Fita tasamu Sarkin Mota, Dakyar Ta Lallabashi Tareda Bashi Kudi Masu Tsokah ya bata keyn Mercedes Benz ta hau tabar Gidan Aguje, _ni kaima Ummy Abduol bansan inda zata bah_ Washe Gari dasafe Ta Tashi Cikeda da Farinciki, Side din Fulani ta nufa Cikeda nishadi, Sun Gaisa Fulani Ta kalleta Tace "Iyeh Parveen Umma Tazo koh?? Naga Yau Sai nishadi kike" dan Murmushi Tai Kawai Ta mike Tace "Bari Naje nagaida mai Martaba. A Side dinshi tasameshi Yana Break, Ta Tsugunna har Qasa ta gaidashi ya Amsa Fuska a sake, Yace "An Tashi lapia?? Ya Ummanki??" Ta Amsa da lapia lau, Tare sukai Break din Sannan Ta Qarasa Side din Ummanta, Sun dade suna Hira, Agogon Hannunta ta duba Taga goma na Safe, Ta mikr dasauri Tace "Umma Ina Zuwa" Umma ta gyada kai. Kitchen ta nufa inda Ma'aikata ke girki, Altine tasamu a Wajan Ta kirata Suka Qebe, Altine Tace "Ranki ya Dade komai yatafi Yanda Akeso, Wacchan ta nuna Wata baiwa Tace "Itace komai na Dangane da Girkin Yarima Yake Hannunta" Parveen ta tabe Baki Tace "Tho Yanzu ya Ake Ciki??" altine Ta Sadda kai Tace "Ranki ya Dade komai yatafi Yanda Akeso" dan Murmushi Parveen tai Tace "I hope komai Yatafi yanda akeso" Altine tai Murmushi Tace kwarai Kuwa Ranki Ya dade" kyada Kai Parveen tai Tana Murmushin Mugunta. _shin Fans meh Parveen ke qoqarin yi??_ Miqewa yayi zaune Tareda miqa, Yarinyan dake kusa dashi Ya Kalla tareda murmushi, Yau bah ta rannan bace, daga Gani bama musulma bace. Ya shiga Tashinta A hankali yace "wake up!" ta mike Tana Yamutse Fuska, Yadan Hade Rai Yace "You have to lyv now" ta marairaice Fuska tace "why pls, Am Stl sleepy n tired" tsawa ya daka mata ta mike dasauri ko wanka batai bah tasa kayanta, Bandir din Yan Dubu ya wurga mata Ta fita Tana Gungunnai, Tana Bude Qofan Falon Tai Kicibus da Bilal, Matsawa yayi dasauri Yabata wuri ta Wuce. Binta yayi da kallo tareda Girgiza Kai Sannan Ya shiga Falon, Kan kujera ya zauna ya kunna kallo, Saida Yarima Yayi wanka Sannan ya fito falon, Bilal yabishi da Kallo ya girgiza kai, yarima Ya dake Yace "meye kake wani kallona kana girgiza kai" Bilal Yace "Yarima Ina jiyema Ranan da Mai Martaba zai San kana kawo mata Gidan nan" tsuke Fuska Yayi yace "Tho idan ma yagane ai inace bah damuwanka bneh" Bilal Ya girgiza kai Yace "Kai Bakasan Abokin Barawo akance Barawo baneh" bata Fuska Yayi yace Kai Kajiyo... Cikinshi ya shafa yace "Am Hungry wai Har Yanzu Banzayan nan basu kawomin break bah" koh kallanshi bilak beyi bah yacigaba da kallanshi, Fridge ya bude Yaga bah komai, yaja tsaki Ya mike yadawo Falon. Sha daya Dai dai Ma'aikaciyarshi Ta Shigo dasallama ciqe da tray dauke da nauikan Abinci kala kala, Wata ma Ta shiga da Wasu, Saida Suka Kwashi gaisuwa koh kallansu beyi bah Sannan Suka Aje a dinning, Altine Ta Shigo da Sallama Dauke da Tray da Ruwa akai da chi- exotic akai, Sam Bai lura da ita bah har suka aje suka Fita... Bilal neh ya mike Yayi Serving dinsh ya koma ya zauna ya cigaba da kallanshi, Abincin Yaci sosai saboda Yunwan dayake ji, Sannan Yasha Exotic dinda Aka zubamai a cup, kurba daya yayi ya Aje Saboda Ji dayayi ya chanza Taste, Harya Mike Ya Qara daukan Cup din Ya kwankwade Saboda bai Sama Cin Abinci baisha bah, Ga mamakina Qara Zubawa Yayi ya shanye ya Aje cup din. Niko ummy Abduol nace Kodai Saboda Hadimar Parveen ce ta kawo??? Altine na fita ta nufi side din Parveen tana murmushi, Parveen cikeda zumudi Tace "Ya akai Altine" Altine Tace "An gama Ranki ya dade" Tsalle Parveen tai tace "Yauwa Haka nakeso" Sai kuma mu jira cika aiki kawai, Itama Altine Murnushin Tai... Tho Fah Fans meh Parveen ke qoqarin yi??? Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page7⃣ Tsalle Parveen tai Tace "Yauwa haka nakeso" Sai kuma mu jira Cika Aiki kawai, Itama Altine Murmushin tai, Parveen tace "Muje Wajan Umma" tana tafe Altine na take mata baya, Lokaci lokaci takan saki Murmushi har suka qarasa Side din, Sun baje Umma nata bata labarin yanda Tai kewanta Sanda Bata nan, Parveen koh saima Umma dariya take, lokaci lokaci Takan duba Agogo. Har Umma takaiga cewa "wai Parveen wannan duba Agogon Fah??" tai Murnushi Tace "Bkmai".. Bilal idonshi nakan kallan dayake Coz ana Favorite hindi film dinshi "Mujshe dosti karoge", Yarima koh tunda ya zauna yake jinshi wani iri ya mike yana dan tangaji Yace "Bilal idan kagama ka tasheni, Zamu fita da mai martaba anjima Around 12, am Slipy" kai kawai Bilal yadaga batareda Ya Kalleshi bah, Daki ya Shga dakyar Ya fada kan Gado, Barci neh mai nauyi ya daukeshi, Sam Bilal ya manta Yana Gama Kallanshi Yabar Side din. Shiru shiru Mai Martaba Baiga Yarima bah dan Haka Yasa amai kiran Jakadiya, Ta karasa Fadan dasauri, Umartanta yayi ta kiramai Yarima, Amsawa tai ta nufi side din Yarima, Kai Tsaye Ta shiga Side din, Bah kowa a falon don Haka Tai knocking a kofar bedroom din, Nanma Shiru, Rakai Minti goma Tana Knocking jin shirun yayi yawa Yasa Ta murda ta shiga da Sallama.. Kwance ta Sameshi shame shame kamar Matacce Yanata Barci, Mamakine Qarara a fuskan Jakadiya, Ta shiga Tashinshi a Hankali tana Kiran sunanshi Yarima! Yarima!! Shiru, Dakyar tasamu ya Bude ido dakyar, Tace "Mai Martaba Nasan Ganinka ranka Ya dade" cikin Muryan Maye Yace "dallah Mallama Getout, Kije Kice Baza'azo bah" da Mamaki Jakadiya Ta Kalleshi Tace "Ranka Ya Dade Lapia?? Ban saba ganinka Cikin Wannan Halin bah" Mikewa Yayi Zaune yana wani lullumshe ido Yace "I Said get out!" alajabi ya hana jakadiya koh motsi. Tunda Take Bata Taba ganin Yarima cikin maye bah Sai Yau, Mikewa Yayi yana tangani Yace "keh wacce irin Tabbace, Fitar min daga Daaaki dallah. Kinbi kin ishhheni da Warrri" ta fita Dasauri ta Nufi fada harda dan gudunta... Tsugunawa Tai Ta gaida mai Martaba Sannan Tace "Ranka Ya dade bansan Yanda Zaka dau Maganan nan bah Anma...waziri Yayi saurin Katseta da Cewa "Meya faru Jakadiya??" kuka ta Fashe dashi Tace "Yarima Ya jefa kanshi cikin hali irin na Yaran Zamani, Naje dubashi naganshi Cikin Maye yanata Sambatu" Mai martaba Yace "Jakadiya Kin Tabbatar da Abinda kike fada" ta Share kwallan idonta tace "kwarai Ranka Ya dade" Dogarawan Dake Wajan Mai Martaba Ya Kalla Yace "Kuje ku tahomin da Yarima" suka Amsa suka fita dasauri. Sunsha wuya kamin su daukoshi sai sambatu yake, Parveen ta Fito zata Shiga Garden taga an daukoshi Sai Sambatu da Buge buge Yake kamar Mahaukaci, Tai Murmushi Kawai suka hada ido da Altine. Garden din suka shiga Saida Tasamu wuri ta xauna sannan Ta fashe da dariya Harda Kwanciya, Saida Tai Mai Isarta sannan tajawo Wayanta ta Shiga Instagram Tanata Liking post din wayanda Take following cikeda nishadi... Jakadiya dasauri ta qarasa Sashen Fulani tasanar da ita abinda ke faruwa. Hankali Tashe Itada Umma Sukai Fada, Zaune suka Samu Yarima Sai Sambatu Yake, Takaici Ya hana mai Martaba magana, Fulani ta qarasa kusada Yarima ta tsugunna kusadashi tana Girgiza Shi Tace "Yarima meyasa zakai haka, meh Yasa ka jefa kanka cikin wannan Halin??" kuka take sosai dakyar Umma Tajata Suka bar Wajan... Mai Martaba Ranshi a bace Yacema dogarawa "ku kaishi ku dauremin shi" waziri yace "Ranka ya dade Aimai afuwa, Muna roqamai Sassauci" baice komai bah suka bar wajan riqe da Yarima, Parveen na xaune akazo aka wuce dashi, Dariya tasaki tareda yin kwafa... Yarima baisan inda Kanshi Yake bah Sai washe Gari dasafe, Bude ido Yayi ahankali, Ganin Dakin duhu Yasa ya daga kai dakyar, haske ya hango ta Window, Dasauri ya tashi zaune tareda bin dakin da kallo. Mamakine Qarara a fuskarshi, Mai Yakeyi anan dakin?? Kamarshi yarima Fardeen dan Sarki kabeer ya kwana a Magarqama, Dasauri ya miqe ya fara Ihun kiran bayin dake gadin wajan, daya daga Cikinsu Yazi dasauri tareda Rusunnawa, Ya kalleshi da jajayen idonshi "Meh nakeyi a nan?? Waya kawoni" Ranka ya dade tun jiya kake nan kuma mai martabane Yasa a kawoka. Mamaki qarara a fuskarshi, dafe kanshi Yayi dake saramai Sannan Ya dago ya kalli bawan "Jeka kiramin Bilal" Tho Ranka ya dade Ya tafi dasauri, Yana Fita daga wajan yayi kicibus da shi a hanya, Bilal ya Kalleshi "Yariman ya Farka kuwa" Kwarai ranka ya dade shine ma Yace nazo na kiramai kai. Ai bai gama Maganan bah ya Nufi Magarqaman Dasauri, Yarima na ganinshi ya qaraso wajan Qarfen daya musu iyaka Yana Kallan Bilal da damuwa "Bilal meke Faruwa?? What am I doing here" Ai kai zan tambaya Yarima, Why! Why yarima?? Meyasa zaka jefa kanka cikin Wannan Halin??.. Da Mamaki Yarima Ya kalleshi "Meh kake nufi" Yanzu Yarima Abin naka ya wuce neman mata Har Shaye Shaye ka fara Why?? Kakosan Yanda mai martaba Yayi Fushi dakai jiya?? Ranshi ya matuqar Baci musamman Sanda Aka kawoka Gabanshi kana maye Zaro ido Yarima yayi tareda Fadin WHAT?? "What are you trying to tel me Bilal kai kanka Kasan banashan Komai" Shiru Bilal Yayi Sannan Ya kalleshi Ina Zuwa insha Allahu Everything wil b olryt. Yabar wajan dasauri. Dukan Qarfen da aka rufeshi dashi Yayi tareda Fadin Daim It! Muje zuwa... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page8⃣ Bilal Side din Fulani ya nufa, Kuyanginta Yagani suna kaiwa da komawa, daya daga cikinsu yasa tamai iso, tadawo ta fadamai ance Ya shigo. Dakin Fulani ya Shga da Sallama, Zaune ya Sameta itada Umma sai Parveen dake gefe, Ya rusunna Ya gaidasu, Ummace Ta amsa tana yar Fara'a. Ya duqar dakai "Fulani dan Allah Alfarma nazo nema wajanki" Batareda ta Kalleshi bah "Alfarman meh fah?? Ina fata ba'akan Yarima baneh" Qara duqar dakai Yayi "Fulani dan Allah kiyi Hakuri ki tayamu bah mai Martaba Haquri, Nasan Yarima Yayi kuskure Anma Insha Allahu bazai sake bah." Fulani ta dago Tana Kallanshi "Dama Kasan Abinda Yake Bilal anma ka biyemishi baka Fadaba?? Ya dade Yana cikin Wannan halin knan sai Jiya Allah Yasa Muka sani koh" Saurin dagowa Yayi "Wallahi Fulani Bansan Yarima nashan wani abu bah, ni tunda nake dashi ban taba gani bah, kuma zan iya miki Rantsuwar Yarima baishan komai dah bansan Yanda akai ya fara bah" Ya Kalli Umma dake Kallansu "Dan Allah Ranki ya Dade ki Tayani bah Fulani haquri tasa baki aba mai Martaba Haquri" Numfasawa Umma tai ta kalli Fulani "Dan Allah yace sannan Ya bada Haquri, Inaso bayan An saki Yarima ki tambayeshi menene Matsalarshi, kila akwai dalilin dayasa Hakan ta kasance" Bah Tareda ta kalleshi bah Tace "Kaje Ka samu mai Martaban Tukun, sannan namai Magana daga baya" Godiya yayima Fulani da umma Yabar dakin dasauri Parveen dake gefe bah abinda take sai Qunshe dariya... Fada ya nufa kai Tsaye, Dakyar Mai Martaba Ya Yarda Ya Qarasa Fadan. Yayi Magiyan yayi kamar zaiyi kuka, Jama'ar dake wajan sukasa baki wajan tayashi bada haquri, Dakyar mai martaba ya bude baki Yace "Zanyi tunani akai" Godiya yayi sosai Yabar fadan zuwa inda Yarima ke Garqame... Yaje Ya Tarar an kawomai abinci anma Baici komai bah Saima hada kai da guiwa dayayi, Yana ganin Bilal ya mike dasauri ya qaraso wajan kofar "Bilal ya akai??" Har yanzu fah bah wani abinda akace, Mai Martaba Yayi Mummunan Fushi Wallahi. Yadaice Zaiyi tunani akai Shiru Yarima Yayi ya dago dakyar idanunshi Jawur "Bilal wah yamin Wannan Abin?? Menaima Wanda Yamin Haka??, banaso inji nabatama Mai Martaba Rai. Yanzu dawani ido Zan Kalleshi??. Ni nasan bah abinda nasha Shiru Bilal yayi kamar mai tunani Sannan Ya dago "Am suspecting ur Maid, mai kawoma Abinci, Dan ita kadaice Ta kawoma Abinci bayan kaci hakan ta faru" Yarima baice komai bah sai dafe kai dayayi "Karka damu Evrytyn wil be Fine, inasa Ran insha Allahu zuwa anjima komai ya wuce" Gyada kai kawai Yarima ya iyayi, Bilal Yamai Sallama Yabar Wajan.. Fulani, Umma da waziri suka hadu wajan bah Mai Martaba Haquri, Dakyar akasamu ya haqura anma Yana Fushi mai Tsanani da Yarima, Yarima baibar Magarqaman bah Sai Bayan Sallan Magrib, duk ya jeme kamar bashi bah. Da temakon Bilal yaje side dinshi, Ruwan wanka ya hadamai ya Shiga Shikuma Ya koma Falo.. Washe gari dasafe Umma zata Koma, Parveen Harda dan kukanta bataso Umma ta koma, har Airport suka rakata itada Fulani, Saida Sukaga Tashin Jirginsu Sannan Suka dawo, Parveen cikeda kewan Ummanta. Motoccinsu Suka Shigo Gidan Sukai Parking, Daidai nan Yarima Ya Fito shida Bilal da Mahadi dan Zuwa Fada Roqan Mai Martaba, Parveen na fitowa Suka hada ido da Yarima. Murmushin Mugunta ta saki, Ta nuna kanta sannan ta nunashi ta Girgiza Hannu (nida kaine!) dariya tasaki Suka Bar wajan Itada Altine da Fulani tareda kuyanginta. Mamaki Qarara a Fuskan Yarima kardai Yarinyan nan neh Tamai Wannan?? Lallai indai wannan Yarinyan neh ta gama dashi, Da Wannan Tunanin Suka Qarasa Fada, Bah Kowa dan Haka suka nufi side din mai martaba, Iso Aka musu dan Saqon Yadawo "Yace kar Wanda Ya shigo mai nan" Suka hada ido, Yarima ya kalleshi Rai Bace "Bakacemai Yarima baneh??" Yallabai na fadamai haka Yace nasanar daku Hannunshi Bilal ya kama "Muje pls Har Yanzu bai Sauko baneh" Haka suka jashi suka soma side dinshi... Safa da Marwa ya somayi a dakin, Bilal koh Sarkin Indian Film ya kunna ya soma Kallo mahdi na Tayashi, Rashin Samo Mafita Yasa Yaja Tsaki Tareda Daka musu Tsawa, Dallah ku Kashe mana Wannan Kallon, Mahdi dabe Tolerating nonsense Ya mike tareda jan tsaki Yabar Falon, Bilal mah miqewan Yayi zai fita, Yarima Ya dago ya Kalleshi "Kah kiramin Jakadiya" Bai Amsashi bah ya fita, shiru Shiru har yayi tunanin Bai kiratan bah zaije dakanshi sai gata... Da Sallama Ta shigo ta rusunna Ta kwashi gaisuwa, Bai Amsa bah "Kije ki kiramin Yarinyan dake kawomin Abinci" Tho tace ta fita dasauri, chan sai gata itada Baiwar. Ta rusunna ta gaidashi, Ya kalli jakadiya "Zaki iya tafiya" Ta mike tabar wajan dasauri. Kallan baiwan yayi dakyau "Shekaran jiya wah ya dafamin abinci??" Muryanta na rawa kanta a kasa "Nice Ranka ya dade" Tsawa ya daka mata "Ki fadamin Gaskiya" Walla...Wallahi Ran..Ranka ya dade nina dafa "Ok.naji. Nabar drinks dayawa a Fridge din Falon nan Anma na duba babu Ranan shi kuma mai zakice akai?? Keh kadai keh Gyara Side din nan Inda inda ta soma Tana Muzurai Tsawa ya daka mata, idan baki fadamin Gaskiya bah kisani yau a magarqama zaki kwana bayan bulala hamsin da za'a miki Kuka ta fara harda shesheqa, Sannan tace "Wallahi Ranka ya dade ba...Bah lefi nah baneh, Ni...nima sani Akai?? Ido Ya zaro Waya saki?? Tho fah! Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page9⃣ "Wallahi Ranka ya dade bah...bah lefina bneh. Ni...Nima sani akai Ido Ya zaro waya saki?? Dukar dakai tai sannan tace "Hadimar Gimbiya Parveen ce" Damamaki ya Kalleta "Wato za'a Iya hada baki dake a kasheni a cikin gidan nan koh" Girgiza kai take tana kuka sosai Ta window ya leka tareda kiran dogarawanshi dake qofar Falon Dsauri suka shigo ya umarcesu dasu dauki baiwar su kaita Magarqama.. Suka Amsa ciki na rawa suka dauketa suka fita. Kan kujera ya Fada Mamaki fal a ranshi, Lallai dan haqin daka raina shike tsole maka ido. Anma yarinyan nan Ta Cuceshi Wallahi Mikewa Yayi ya nufi side din fulani, Duk yanda yake tunani abin ya wuce haka. Dakyar ya Samu ya lallabata ta Haqura.. Washe Gari dasafe ya shirya Cikin Kaya na Alfarma ya nufi fada, Yayi Sa'a mai Martaba na nan, Ya shiga da Sallama Tareda Duqawa, Mutanen Gurin Ya gaida sannan Ya soma bah Mai Martaba Haquri, Bah Irin Magiyan da Yarima beyi bah anma sarki kememe Yaqi saima Cewa Yayi ya tashi yabashi waje. Jiki Sabule Ya mike Tabar Fadan. Yana Qoqarin Komawa Side dinsh Yayi kicibus da Parveen dake qoqarin Shiga mota, Mummunan Kallo ya bita dashi ta Dan Dara Sannan Ta shiga mota Drivern yabar Gidan a Guje... Bilal dayaga duk abinda ya Faru Ya Karaso inda Yarima ke Tsaye "Wai meye Tsakaninka da Yarinyan nan??, Naga Tana Kallanka tana Dariya" Wani qayatacen Murmushi Yarima Ya Saki Tareda Shafa Suman kamshi "Bah Komai" Cikin Isa Ya fara taku hannunshi daya cikin Aljihunshi Ya Qarasa Side dinshi. Bedroom dinshi ya nufa Ya chanza kayan jikinshi Ya Fito Yana Kallan bilal "Tashi Ka Rakani muje naga wajanda mai Martaba yace Ana Ginawa" Kallan Mamaki Bilal Yamai "Yau kuma??" Bansan iskanci idan Zaka Rakani kazo ka Rakani. Bah musu Ya mike Suka Bar Falon.. Yauma Kamar Rannan, Chan bayan Gidan Mai Martaba Sukaje Shida Parveen, Hira Suke Sosai Cikeda Nishadi. Labararaku kala kala Yake bata Tanata Dariya Harda Kyakyatawa. Mai Martaba najin dadin Zama Tareda Parveen Saboda yarinyace Mai Saurin Shiga Rai, Mai Hankali da natsuwa. Shigowan Yarima Knan daga Yawonshi, Fada Ya nufa koh Allah zaisa Yau Mai martaba ya haqura, Dogaran dake wajan suka sanar dashi yana chan bakin ruwa.. Chan ya nufa wit full confidence, tun daga nes ya hango waja zaune duk daukanshi Fulani ce, Ya qarasa wajan da Sallama, Mai Martaba ya daga kai ya kalleshi, Ganin Parveen a wajan Yasa ya tsuke fuska yaji dama baizo bah, gefen qafan mai martaba ya zauna ya gaidashi, Amsawa yayi a takaice, yarima yadan sunnan dakai Ya fara rokan mai martaba, Parveen koh wayanta ta zaro tahau chatn. Mai martaba rai bace Ya kalleshi "Tashi kabarmin nan" Magiya yahau yi, Dakamai tsawa yayi dole ya mike yabar wajan jiki a sabule Parveen neh ta kalli mai martaba cikeda ladabi "Dan Allah Ranka ya dade kamai Afuwa, Idan Har ya sake sai kadau hukuncin da duk ya dace" Dan Murmushi yayi "Shiknan Parveen" Dogarin dake gefensu mai martaba yasa ya kiramai Yarima wanda har yayi nisa ya kusa barin wajan Chan sai gashi ya dawo ya zauna, Mai martaba Ya kalleshi dakyau da kauda kai "Kaci darajan Parveen ta Roka na yafemaka anma idan bah haka bah, bah Yanda za'ai na sauko yanzu" Godiya yama mai martaban Ya mike Suka hada ido da Parveen, Harara ta sakar mishi Yaja guntun Tsaki mara sauti Yabar Wajan Fuuu.. Side din Fulani ya nufa, Baiko sa amai iso bah ya shiga kai Tsaye, Zaune take kan Darduma tana lazimi, ya Qarasa ciki tareda neman wajan zama. Saida ta Gama Sannan Ta kalleshi "lapia?? Meh kuma kakeso??" Furzar da iska yayi rai bace "Fulani I hate dat girl pls ta koma Garinsu, Banasanta! Banasanta!! I hate her!" Dam! Gaban fulani ya fadi, ta dake Tana kallanshi "Saboda meh??" Wai yanzu fisabilillahi fulani inata Rokan mai martaba akan yamin afuwa anma yaqi, wai saida wannan wawiyar Yarinyan tace Sannan" Dan Murmushi fulani tai tana Kallanshi "Duk Abinda ya faru ai kai Kaja, bakaji masu iya magana nacewa wani lokaci da dan uwa gwara bare bah. Ai duk abinda kagani yanxu kai ka saya da kudinka. Sannan kasha kurumin kah indai Parveen ceh nanda kwana biyu zata bar gidan, Zata Koma garinsu" Mikewa Yayi yace "Dayafi Mata" Barin dakin Yayi yadau waya ya kira Mahdi, Bugu daya ya dauka, Yarima yadanyi jim har saida Yace "Yarima kanajina" "Kazo gida inasan Ganinka Pls" Tho Mahdi Yace tareda kashe wajan. Ba'adau lokaci mai tsawo bah saiga shi. Direct Side din ya nufa, Falon ya shiga ya tarar da Yarima zaune yayi crossing leg sai jijiga nasaman yake. Mahdi ysamu guri ya zauna, Shiru ne ya ratsa Falon, Chan Yarima Ya dago Tana Kallanshi "I Hope kasan Wata yarinya yar Gidan Sarki Khaleed na Kasar Zaria koh" Shiru Mahdi yayi nadan sakanni Sannan Ya dago "Yes! Gimbiya Parveen koh??. Wata Kyakyawa, Kamar Rannan danazo gidan nan naganta. Kai Babyn ta hadu bah karya kaga m.... Saurin Katseshi Yarima yayi da Tsawa. "Shut Up dallah" Labarin Zuwanta yahau bah Mahdi har zuwa sanda Tamai Abin nan Mamaki qarara a fuskan Mahdi.. "Ka Tsaya Kana Kallona kaman tv, Mafita nake nema, jibi zata tafi, Inaso nai mata wani abu wanda harta mutu bazata mantani bah Dan dariya Mahdi yayi yace "Indai wannan neh tazo gidan sauqi" Muje zuwa.. Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣0⃣ Labarin Zuwanta Yahau bah mahdi har zuwa sanda Tamai Abin nan Mamaki Qarara a Fuskan Mahdi... "Ka Tsaya Kana Kallona Kaman Tv, Mafita nake nema. Jibi zata tafi, Inaso nai mata Wani Abu wanda Harta mutu bazata Mantani bah Dan Dariya Mahdi yayi yace "Indai wannan neh tazo gidan sauqi" Da Mamaki Yarima ya Kalleshi "Kamar Yha Meh kake nufi??" Dan murmusawa Mahdi yayi Sannan Ya kalleshi "Haba Yarima Sai kace baka waye bah??. Har kamar yarinyan nan zataima Wannan Rashin Mutumcin ka Kasa daukan mataki?" Tsaki Yarima Yaja "Kawai ka fadamin meh za'ayi Ynxu" Qara murmushi Yayi "A Nawa tunanin Kawai ka Aureta, Ka Maida Ita Sex Machine dnka Kawai Sannan a Gefe Kaita Gana mata Azaba. Kaga dai bah Halin... Saurin Katseshi Yarima Yayi ta hanyar Dagamai Hannu Kaifa Banza neh Mahdi, Kai Kanka Kasan Banida Ra'ayin Aure Ynzu. Idan ma Inadash bah Wannan Stupid Gurl din bah, Naushin Hannun kujeran dayake kai Yayi "I Hateeee Her Wallahi" Mahdi yadan dara Sannan Yace "A nawa Tunanin Wannan neh kawai mafita, Buh ka tsaya kai tunani Akai. Kaga Idan kai Kama daina Neman Matan nan dakake" Yarima baice komai bah, Yadan Zame daga Zaunen dayake Tareda Lumshe ido Mahdi Ya Mike tareda Farin " Ni Natafi, Inada Uzuri Yanzu" Kai Kawai Yarima Ya gyada mai Ya Fita... Yini Yayi yana Saqawa da kwancewa, Anya Zai iya Auren Parveen?? Lokaci Lokaci Yakanja Tsaki "Ni Ban Shirya Aure bah, Am just 26 fah" Idan kuma Ya tuna da Dalilin auren saiyaji Zuciyarsh Ta aminta da Hakan. Haka Ya Cinye kwanaki Biyun nan Cikin Tunanin Mafita.. Fulani da Mai Martaba Sun Wayi Gari Yau ransu bah Dadi, Kasancewar Parveen zata Koma, Ita Kanta Sai Taji Batasan komawan. Anma bah yanda Zatai saboda Makaranta. Altine che Ta shirya mata Kayanta Tareda Sawa amota, sun Fito don Tafiya, mai Martaba Harda Fulani suka Fito don rakasu, Kallan Fulani tai Wanda duk Ranta bah dadi, Ta juya Ta kalli Mai Martaba, Kawai Saita Fashe da Kuka... Fulani ta Qarasa ta Rungumeta Tana Lallashinta, Magana take Mata a kunni wanda ni kaina bansan meh take ceh mata bah, Saidai naga Ta daina kukan tana dan Murmushi, Fulani ta Share Mata Hawaye Sannan Suka Dunguma Zuwa Airport. Kyauta Sosai Mai Martaba Yama Parveen har Tana Mamaki Saboda Yawanshi, Sallama Tai Musu Suka Hau Jirgi tana dagama Mai Martaba da Fulani hannu, Suma Hannun Suke daga Mata. Hawayene ya Gangaro mata, Tasa Hannunta na Hagu ta share Ta Shige Cikin Jirgin don inta Tsaya Kallansu Zata iya Fashewa da Kuka... Cikin Awan da bai wuce daya bah suka iso masarautar zaria, Already dogarai tareda bayin umma suna jiransu, Jirginsu na sauka suka Fito tareda shiga motan da aka tanadar musu zuwa gida. Sai Taji dama bata dawoba, ranta bah dadi har suka Qarasa Gda.. Umma Daketa Hidima dan Jiran Yar nata taji Shigowan motoci, Mikewa Tai Dasauri Umma Ta nufi wajan cikeda Farinciki, Kuyanginta neh Suke Take mata baya, Har sun kai Bakin Qofan Fita side din Umma, Sukai Kicibus da Parveen dake Qoqarin Shigowa Side din. Parveenta qarasa dasauri ta rungume umman nata tana dan dariya, Umma Cikeda farinciki Tai mata Sannu Suka qarasa cikin side din. Sun baje Anata Hira, Sunci Sunsha, Parveen ta nunama Umma kyaututukan da Mai Martaba Yamata, Godiya sosai Umma tai Tareda Farinciki... Saida ta huta Sannan Ta nufi Side din Mai Martaba bayan tasa Jakadiya tai mata Iso. Mai Martaba na ganinta ya Mike Cireda Fara'a Tareda bude Hannu, Dasauri ta qarasa ta rungume mahaifinta, Kanta ya shafa Yana mata Sannu da Dawowa. Dan dagowa tai ta Kalleshi "I Missed uh dad" Murmushi Yayi Shima yana Kallanta "I Missed uh My Princess" Dariya tasaki Ta zame jikinta daga nashi ta nemi guri kan Carpet ta zauna Hira suke Sosai Ya Tambayeta Fulani da Mai Martaba, Kyautan da mai Martaba Ya mata Ta fadama Mhaifinta. Yayi Murmushi "Ai sarki Kabeer Akwai Mutumci da datako" Itama murmushin Tai tanata bah shi Labarin Yanda Mai Martaba da Fulani ke Santa, Batabar Side din mai martaba bah saida aka kira Sallan Magriba Sannan.. *Bayan Sati Biyu* An Kammala Ginin Asibitin Yarima Budewa kawai Ya Rage, Sam Ran Yarima Baiso Hakan Bah, Anma bah Yanda zeyi dole Yayima Mahaifinshi biyaiya...Harynzu ya kasa Haqura Akan Abinda parveen Tamai, Dole Yadau Mataki. Dole Ya Rama, Saiya nuna mata Shi yarima fardeen neh kuma ya haifu, Sun Zauna shida Mahdi Abokinshi, Qara nusar Dashi Lalillin Hakan Mahdi Yayi yar Ya Yarda. Sun Yanke Shawaran duk Yanda Za'ayi, Yarima Ya Saki Lallausan Murmushi Sannan ya Kalli Mahdi "Kwanyanka naja Frnd" Shima Mahdin Dariyan yayi... Hadadden Motarda Mai martaba Ya siyan mata Qirar Dodge Ta nufa Dasauri Hannunta rataye da jakan Laptop, Sai Keyn motanta, Motan Ta Shiga Ta Fita Daga Gidan Dasauri. Gudu Take dan Takusa Yin Latti, Ahmadu bello University naga ta nufa dasaurinta, Horn taketa ma Student din Demostration da Sukai Cincirindo a gate sun shiga. Tsaki taja ta Qara danna Horn, Agogon Hannunta ta duba taga 7:56am Gashi 8:00am Takeda Lectures kuma Tasan Lecturan baida mutumci. Dakyar tasamu Ta wuce ta nufi depertment dinsu, Cikin ikon Allah tasamu ta shiga hall din, tana shiga lecturan ya shigo. Saida Tagama Sannan ta fito Tai Kicibus da Aminiyanta... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣1⃣ Dedicated dis page to *Maradin Zazzau's Family..Alh Haruna Muh'd Jumare* Allah Yaja kwana Uncle👍🏻 Cikin Ikon Allah tasamu ta shiga Hall din, tana Shiga lecturan ya shigo. Saida Tagama Sannan Ta fito Tai Kicibus da Aminiyarta Hadeeza Yar Maradin Zazzau. Parveen ta Qarasa ta Rungume Deeza, Deeza ta hade rai ta Rungume Hannu "Lallai Parveen Kikai Tafiyanki, Saidai na kira naji kina Gombe" Dan Murmushi Tai Ta Marairaice Fuska "Am Sorry Bae! Wallahi Tafiyan neh Yazo min cikin Gagawa, Sai ana gobe Zan Tafi nasani. Buh ai nabaki Haquri" Tabe Baki Deeza tai Tareda Murmusawa "Na Haqurah Anma nima zan Rama" Parveen ta shafa Cikinta Tareda Yatsine Fuska "Muje Musamu Wani abu Yunwa nakeji" Ok muje. Motan Parveen suka Shiga Suka Fita daga cikin Schl din, Wani hadaden Eatry Suka nufa, Abinci mai Raida Lapia Parveen tai musu odering, Sunci Sunsha Deeza ta Kalli Agogon Hannunta "12 Dai Munada Lectures knsani" Itama Agogon Hannunta ta duba, Ai Yanzu 11:31am neh munada Sauran 30mint koh??" Kai Kawa Deeza ta daga Tana daddana Wayanta. Chan ta kalli Parveen "Ahan Bae Wai dan Allah dagaske kike abinda kika Fadamin Rannan??" Parveen ta dago Tana Kallanta "Nameh fah??" Maganarki da Yarima mana Tabe Baki Parveen Tai "Qwarai kuwa" Idonta ya Ciko da Kwalla ta Kalli Deeza "Tunda Nake a Duniyan nan Ba'a Taba Cimin Mutumci irin Ranan Bah, Yanzu dawani ido zan Kalli Mutanen Gombe??" Hawayen dake Maqale a idonta suka Gangaro "I Hate Him Deeza, I Hate Him! Tunda Nake Ban Taba Tsanan wani bah Kamar Yarima. Na Tsaneshi! Na Tsaneshi!!" Kukane Ya Kufce Mata, Deeza ta Dawo Kusada Ita ta zauna tana Lallashinta "Kiyi Haquri Pls, Ai kema kin Guma Masa. Nasan Wannan Abinda kikamai bazai Taba Mantawa dakebah Har Qarshen Rayuwarsa" Dagowa tai Idanunta Chabe Chabe da Hawaye tadan Mata Murmushi "Deeza Mazinaciya fah ya kirani" Ta Qara Rushewa da wani Sabon kukan Haba Bae! Kar wannan Ya daga miki Hankali, Ni Shaida ce akan Halinki. Karki Bari Maganganun Yarima Suyi Tasiri a zuciyarki Pls, Karki Damu Allah zai Saka miki kinji??" Kae Kawai Parveen ta gyada, Dakyar Deeza tasamu ta Lallasheta Sannan suka Bar Wajan Suka Koma Makaranta.. Yanma Lis Parveen ta Dawo Gida, Direct Side din Ummanta ta nufa, Dakinta tq shiga ta fada Jikinta Tana Yar Shagwaba. Umma Ta Kalleta baki Bude "Lallai Parveen sodai kike ki Qarasani ki Huta koh??" Turo Baki Tai Tana gungunai "Kinga Fah Fulani Tana Yarda Nahau Jikinta Har Barci nakeyi" "Iyeh! Tho ai Fulani kikace, Nikam bazan iya bah" Qara Turo baki tai Ta Mike "Ni Natafi tunda Bakyaso ina Hawa Jikinki, Kuma Ana qarayin Hutu zan koma Wajan Fulani nabarki" Bata jira mai Umman Zatace Bah tabar Dakin tana gungunai Murmushi Umman tai "Parveen! Parveen!! Allah ya Shirya" *Masarautar Gombe* Yau Mai martaba bai shiga Fadaba Yana Side dinshi Tareda Manyan baki da sukazo Ganinshi daga Kasa Kasa, Kowanne Yazo neh Dan Tallata hajarshi na Kayan Aiki na Asibiti, Wasu kuwa neman Aiki sukazo, Saida Ya Sallami Kowa Sannan Yasa Amai kiran Yarima. Ba'adau lokcibah sai Gashi, da Sallama ya shigo ya samu guri qasan carpet Ya zauna tareda Gaisuw, mai Martaba ya Amsa Fuska a Sake. Kallan Yariman Yayi "Ina Fata ka gama dukkan Wani Shirye Shiryenka dan sati mai zuwa insha Allah za'a bude Asibitin" Kanshi a duqe ya Girgiza kai "Na Gama ranka ya dade, Allah kuma Ya kaimu" Ameen Inji Mai Martaba Ya Qara kallanshi "Inaso na Hada Qayataccen Biki dan bude Wannan Asibiti, Kana iya Gaiyatan Abokanka na kusa dana qetare Duka dan Zuwa tayaka Murna" Qara dukar dakai Yarima Yayi Yanadan Murmushi "Godiya Nake Ranka ya Dade" Yarima Inaso Kazamo mai Gaskiya da Ruqon Amana Akan Aikinka, kazamo mai Juriya da Tawakalli. Karka zamo Cikin Ma'aikata Masu Wulakanci da Talakawa da Rashin Zuwa duba Marasa lapia dawuri. Dan Allah kai Qoqarin kiyayewa, Sannan Kazamo Maiba Na Qasa dakai Hakinsu daidai Kwargwado banda Cuta da muzgunawa." "Insha Allahu Mai Martaba Bazaka Sameni da Duk Wadannan bah, zanyi qoqarin kiyayewa." Murmushi Mai Martaba yayi "Allah ya maka Albarka" Ameen Ya Amsa Tashi Kaje Ya mike Yamai Sallama Yabar Side Din... Side din Fulani Ya nufa dan Fada Mata Qudurinshi, Kishingide ya sameta A Falo tana cin Yayan Itatuwa, Wata Kuyanga Tana Matsa Mata Qafa, Ya Zube Kan 2Seater Yana Kallan Fulanin, Fulani Ta Kalli Kuyangar, Tashi Kije. Ta Amsa Tareda Mikewa Dasauri ta Fita. Kallan dan nata tai "Yadai Lapia??" Yadan Dago "Bakomai Dama Akwai Maganan danakeso nafada miki neh" Ta Mike Ta Zauna Sannan tace "Ina Sauraranka" Dan Murmushi Yayi "Fulani na Dade inasan Parveen Anma narasa Ta Yanda zanyi na Fada miki, Pls ki Fadama mai Martaba Aje a Nema min Aurenta dan Allah" Da Mamaki Fulani keh Kallanshi "Yarima Kasan meh kake fada kuwa??" Kai ya gyada Yana Kallanta "Nasani Fulani, Idan ban Aureta bah..Ya taba Kirjinshi, Zan Shiga Cikin Wani hali pls ki Taimaka min" Kusan d'a da Mahaifi Tausayinshi Taji ya kamata Ta Kalleshi Cikeda Kulawa "Karka Damu Insha Allahu Parveen Matarka Ce, Kuma Nasan Bazata qika bah" Wani Qayataccen Murmushi Ya Saki "Thank Uh Fulani Shiyasa Nake Qara Sanki" Itama Murmushin Tai, Ya mike Yabar Falon Yana dariyar Mugunta... Tho Fah... _Shin Fans kun. Yarda yarima Ya auri Parveen??_ Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣2⃣ Wani Qayataccen Murmushi ya Saki "Thank uh Fulani Shiyasa Nake Qara Sanki" Itama Murmushin Tai, Ya mike Yabar Falon Yana Dariyar Mugunta... Hidimar Bude Asibiti ne Ya kankama, Gaiyata Sosai Mai martaba Yayi, daga Ciki akwai Gwamnoni, Sarakun, Yan Majilisu, Ya uwa da abokan Arziki, Haka Itama Fulani Tayi Gaiyata Sosai dan a Tayata Murnar Bude Asibitin Dan Nata... Umma nazaune Katin Gaiyata ta Sameta. Dukda Dama sunyi waya da fulani ta fada mata, Katin parveen Musamman Aka Kawo Mata daga Mai Martaba. Lokacinma Tana Schl, sai dt dawo tagani. Dan Tsaki Tai Ahankali Ta aje Katin Umma dake kallanta Sun Sanda Ta Dau katin Tace "Naga Kin Bata Fuska neh, jibi neh dai Kuma Tare zamu Tafi" Tsuke Fuska Tai Tana Kara Kallan Katin "Nifa Umma Inada Lectures Ranan" "Haba Parveen, Dan kinyi missing Lectures na kwana Biyu zuwa uku Shine meh?? Kinga Fah Wannan Gaiyatar daga Sarki Kabeer Take. Shi Yace Abaki, kinga bai kamata ki Watsa mai Qasa a ido bah" Gyada Kai Kawai Tai "Shiknan Allah Ya kaimu" Umma Tace "Ameen" Barin Wajan Tai Tana gungunai, Ita bawai Batasan Zuwa bneh, Kawai Saboda Maqiyinta neh Yasa batasn zuwan, Tsaki Taja Ta qarasa dakinta Tana nazarin Yanda zata Subulbule zuwan. Da Daddare Mai Martaba Yayi Kiranka, Ta Je Side dinshi Ta Gaidashi Tareda Neman Wajan Zama. "Gobe in Allah Ya nufemu da kaiwa zamu Tafi Masarautar Gombe dan Kinsan Akwai Taro na bude Asibitin Yarima Fardeen, Dan Haka Ki Zamana cikin Shiri" Bata Fuska Tai Tadan dago ta Kalli Mahaifin nata "Gobe fah inada Test harda Jibi, nima sai dazu ake Fadamin kuma idan banyi bah Zai Shafi result dina" Shiru Mai Martaba Yayi Nadan Seconds Sannan ya klleta "Shiknan Allah Ya bada Sa'a" Ameen Tace Tana Yar Murmushi Tashi Kije Abinki" Duqawa Tai Kanta Qasa "A Tashi Lapia" Sannan Ta mike Tabar Falon Cikeda Farinciki.. Haka kuwa akai Parveen batabi Su Umma bah, Umma Dai Sam Bata Yarda da test dinda parveen tace Suna dashi bah. Abin bah qaramin daure mata kai Yayi bah, tho mai yasa Parveen batasan Zuwa Gombe?? Da Wannan tunanin Suka Kai Masarautar Gombe. Gidan Cike Yake da Baki Yan nesa, an Karamasu Tareda Basu Masauki, Umma Kam tana Chan Wajan Aminiyarta Fulani. Washe Gari Aka Hau Biki A Chan Haraban Asibitin Mai Suna "Fardeen Specialist Hospital" Taro Yayi Taro, Kowa Daka gani Yana Cikin Farinciki, Bama Kaman Mai Martaba Da Bakinshi Yaqi Rufuwa... Yarima Nachan Zaune Cikin Abokanan Shi Sai Hira Suke, Wanda Yawanci Wayanda Sukai Karatu neh Tare, Anan Yake Fada Musu Ya kusa Aure. Niko Nace "Wah Yce Ya Bashi?? Yaushe Akai Maganan Balle" Yawancinsu Mamaki Suke Saboda Sunsan Yarima Baisan Kalmar Aure, Sanin halinshi Yasa kowa Yaja bakinshi Yayi Shiru, Saidai Fatan Alheri dasuka mai... Anci ansha, Sannan Aka Bude Asibiti, Mutane Suka Shishiga Aka Zagaya Ko Ina Na cikin Asibitin, Niko Ummy Abduol Sakin Baki nai Ina Kallan Asibitin, Kayan Aikin ban Taba Ganin Irinsu anan nigeria bah. Mutanen dake Wajan Sai Santin Asibitin suke Saboda Tsaruwanshi da kuma Kayan Aikin dake ciki. Addua Sosai Akai Sannan Kowa Ya Watse Cikeda Nishadi bayan An Raba Kyaututuka Kala kala. Su Mai martaba Gda Suka koma, Haka su Fulani da Ummah. Saida Aka Natsa Da Daddare Lokacin Duk baki Sun koma, Fulani da Umma Sai Sarki Kabeer da Sarki Khaleed Zaune a Side din Mai Martaba Sunata Hira, Kayan Itatuwane a Gabansu, Da Abinci kala kala. Fulani ce Ta Kallesu Tace "Damako Akwai Wani Abu danakesan Fadama Mai Martaba, Anma Tunda Ga sarki Khaleed Saina Fada Duka" Sarki Kabeer Ya Kalleta "Maganan Meh Fah?" Fulani Ta gyara Zama "Last Week ina Zaune Yarima Yazo ya Sameni akan Maganan Parveen, Yace Gaskiya Yana santa kuma Aurenta Yakeson Yi" Murmushi Sarki Khaleed Yayi Yace "Indai Wannan neh Bah Matsala ni nabashi" Itama Umma Murmushin Tai "Wannan Ai bah Abin Damuwa baneh. Allah Ya shige Mana Gaba Ya Sanya Alheri" Sarki Kabeer koh Tsuke Fuska Yayi "Niko Sam Ban Amince bah" Dukkansu Suka Juyo Suka Kalleshi da Mamaki Ya Gyada Kai Sannan Yace "Yarinya Mai Hankali kamar Parveen za'a dauka aba Fardeen??, Aa Bazai Yuwu bah. Salan Yaje Yayita Cutanta" Dan Murmushi Sarki Khaleed Yayi "Na Yarda da Tarbiyan Yarima, Nasan Bazaiyi Abinda Kake tunani bah" Girgiza Kai Kawai Sarki kabeer Yayi yana Murmushin Qarfin hali Umma Tace "Bah Damuwa Ranka Ya dade, Yarima Mutum neh Na Qwarai bashida Matsala" Shidai sarki Kabeer bai Qara cewa komai bah Akan magana, Haka suka Cigaba da Hiransu... _Shin Fans Kodai Sarki Kabeer naciki neh??_ Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣3⃣ Shidai Sarki Kabeer bai Qara cewa Komai bah Akan Maganan, haka suka Cigaba da hirarsu..Kwanansu uku Suka Koma, Ranan da Suka koma fulani ta iske Mai Martaba a side dinshi, Newspapern dake Hannunshi Ya Aje Yana Kallanta, Ta zauna Kan kujera tana Kallanshi, Dogaran dake gefenshi Yama nuni Suka Bar Falon Dasauri... Ya Kalleta Cikeda Tsokana "Uwargida Sarautar Mata, Yana Ganki neh Yau wani iri??" Fuskanta bah Fara'a Ta kalleshi "Ranka Ya Dade bai Kamata Kai Irin Furucin nan Akan danka bah" Ya Dago "Kamar Yha??" "Muna Magana Akan Yarima da Parveen kuma naji ka Sako wani Maganan" Murmusawa Yayi yana Kallanta "Rabiatu knan! Keh Kanki kinsan Hali irin na Yarima. Bah saina Fada Miki bah, Tho Fisabilillahi Jibi abinda Yayi Rannan Har Saida Ya Kwana Magarqama" Saurin Katseshi tai da Cewa "Wannan Ya wuce, Rayuwar dana nake Tunani, Yace bazai iya Rayuwa bah parveen bah. Ni kuma banason rasa shi" Dariya Mai Martaba Yayi qasa, Qasa yana Kallanta "Maida Wuqar Uwargida, Na gama Shirya Komai. Sati mai kamawa Insha Allahu za'aje nema mai Aurenta" Murmushi Fulani tai ta Harareshi da Sigar Wasa "Mai Makon ka fadamin tunda na Shigo ka barni inata Asarar kalamaina" Dariya Sosai Mai Martaba Yayi Suka Cigaba da Hirarshu Cikin Nishadi... Yau Monday Tushan Aiki, Tunda Asubah da Yarima Yayi Sallah bai Koma bah, abubuwan da Duk yake Buqata Yasa dogaranshi Suka Hada Mai a Wata Yar Jaka, Wanka Yayi Ya Shirya Cikin Yellow Suit da Black Shirt, Sai black tie. Qafafuwanshi Cikin Wata Hadadiyar Black cover. Ga Gashin.nan Yasha Gyara Kamar Na india. Kayan sun Matuqar Amsarshi, abinda da Farin Fata, Ni Kaina Ummy Abduol Saida Ya Burgeni. Yana Tafe Dogaranshi na Takemai baya Rike da Breifcase dinshi.da kuma Wata Yar Jaka, Dakin Fulani Ya Shiga Ya gaidata Ta Kalleshi Tana Yar Fara'a "Yau Za'a Fara zuwa asibiti??" Kai Kawai ya Gyada Yana Danna Wayarshi "Tho Allah ya Tsare Ya kiyaye Hanya, A Kula Dan Allah da Haqqin mutane. Sannan Ka Tuna Ran dan Adam Kake Aiki akai Banda Sakaci" Mikewa yayi Yana duba Agogon Hannunshi. "Insha Allah Fulani" Fatan Alheri tamai ya fito Ya nufi side din mai Martaba dan Safiya neh bai Isa ace Yaje Fada lokacin bah Zaune Ya Sameshi Yana Lazumi, Saida Ya Iddar Sannan Ya Amsa Yamai Addua Sosai Tareda fatan Alheri, Ya Fito Ya Shiga Motarda Aka Tanadar Mai Dan Zuwa Aiki, Dogaranshi Suka Shiga Dayan Sai "Fardeen Specialist Hospital" *********** Parveen Na Cigaba da Karatunta Cikin Kwanciyar Hankali da Annasuwa, Koda Su Umma Suka dawo basu Mata Magana Akan Yarima bah, Jira suke Sai Sanda Akazo neman Auren Sannan ta Sani, dukda ita Lokaci Zuwa Lokaci Takan Tuna Yarima Sannan Taji Gabanta Ya Fadi. Addua Take Sosai dan neman Tsari daga Sharrin Yarima. Tana Yawan Fadama Aminiyarta Deeza Halin datake ciki, Kwantar Mata da Hankali koda Yaushe takanyi Tareda Jadada mata Dagewa da Addua... Cikin Satin Nan Yarima Yaba Aikinshi Mahinmanci Sosai, Kuma Yana Matuqar jin Dadin Asibitin, Kasancewarshi Gynecologist (Likitan Mata) hakan Yasa yawan Harka da Mata, Wasu daga Cikin patient Masu zuwa Asibitin Suna Zuwa neh Kawai dan Ganinshi Saboda Yanda Sukejin Labarin Haduwarshi, Hakan Yasa Neman Mata wajan Yarima Ya Qaru "Allah Ya Kyauta"... Ranar Juma'a Da Safe Sarki Kabeer da Tawagarshi Suka nufi Kasar Gombe, Tun a Airport suka Hadu da Tawagar Sarki Khaleed da Sukazo tarbarsu. Suna Sauka Suka Shiga Mota Suka Nufi Gida, Saida Akai Sallan Juma'a Sannan Suka Samu Suka Qebe, Bayan sunci Sunsha, Umma Tazo Ta gaida Mai Martaba sun dan Taba Hira Sannan Tabar Falo, Sarki Kabeer sai Tambayan Parveen Yake, Mai Martaba Yace Tana Makaranta.. An Tsaida Maganan Aure, An Bada Sadaki Naira Dubu Dari. Sannan Ansa Ranar Biki Wata Daya, Sarki Kabeer bai Kwana bah Suka Juya Tareda Tawagarsa Cikeda Farin Ciki, Sun Koma Gida Lapia. Fulani Ta Iske Mai Martaba a Side dinshi, Bayani yamata duk Yanda Akai, Farin ciki Tai Sosai Ta mike Tana Cewa "Yau Yarima Zaisha Albishir" Dan Dariya Mai Martaba Yayi Tadan Rusuna "Ka Huta Lapia" Ta fita daga Dakin Fara'a Kwance Kan Fuskanta... Yarima na dawowa Fulani tasa A mata kiranshi, Ya qaraso Side din yana gungunai. Gefenta yasamu ya Zauna yana Turo baki. Ta kalleshi tana Murnushi "Kasan Dalilin Kiranka??" Kai Ya gyada Alamar Aa Qara Murmushi tai Tana Kallanshi "Mai Martaba Yaje Qasar gombe Yau Akan magananka da Parveen" Gyara Zama Yayi Yace "Tho ya Ake Ciki fulani??" Sumar kanshi ta Shafa "An Gama komai biki nanda Wata Daya" Dariya Ya saki Ya Rungume Fulani "Much Thanks Fulani, Shiyasa Nake Sanki" Ya Mike "Barinje Naima Mai Martaba Godiya" Bai Jira mai Fulani zatace bah Ya fita Yana Fara'a Kamar dagaske.. Parveen Bata dawo gidan bah Sai Yanma, Saida Taci Abinci ta huta Sannan Jakadiya Ta Shigo, Rusunawa tai ta kwashi Gaisuwa Sannan Tace "Ranki Ya dade Mai Martaba Nasan Ganinki" "Tho Tace" Jakadiya tabar dakin Ko Minti daya bata Qaraba Ta mike ta Nufi Side din Mai Martaba da Sallama.. Ya Amsa Ta nemi guri ta zauna.. Shiru ne ya Biyo baya. Chan Ya Dago Ya kalleta Yace "Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman da Zamu zaba Miki Miji wanda mukaga ya Dace da Tsarin Rayuwanki, Mai Hankali mai Tarbiya dan Gidan dattako. Gabanta neh ya fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣4⃣ Dedicated dis page to *My Facebook Fans* Allah Ya barmu Tare.. "Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman Da zamu Zaba Miki miji Wanda Mukaga Ya Dace da Tsarin Rayuwarki, Mai Hankali da Tarbiya dan Gidan Dattaku. Gabanta neh ya Fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi "Dan Haka A Matsayina na Mahaifinki na Zaba Miki Miji wanda Nasan Zakiyi Alfahari dashi ko bayan bah Raina" Kanta na Qasa Batace Komai Bah "Ina Fatan zayi Na'am da Wannan Auren, Anma Inaso ki Fadamin idan da Wanda Kikeso. Duk da Nasan Its Too late Saboda Har an Kawo Sadaki an kuma Sa Rana Nanda Wata Daya" Hawaye ne Ya fara Zarya a fuskanta, Qoqarin boyewa Tai Kar Ya gani.. Dan Murmushi Yayi yana Kallanta. Bakicemin Komai bah Parveen Kanta Na Qasa Muryanta na Rawa Tace "Ranka Ya Dade banida Tacewa. Na Amince, Zabinka shine nawa kuma ina godiya" Murmushi Mai Martaba Yayi "Allah ya Miki Albarka, Tashi kije" Ameen Tace Tareda Mikewa Tabar Falon.. Tana Fitowa Ta Fashe da wani Matsanancin kuka, Ita bah Kukan Auren da Mai Martaba Zeyi mata bneh Aa, kukan Karatunta Take. Haka Ta Qarasa Side din Umma Tana kuka Sosai, Jikinta ta xube Tace "Umma Meh Yasa mai Martaba bazai bari na Qarasa makarantana Bah Sannan Ya Auramin duk wanda nakeso??" Shafa Kanta Umma tai "Kiyi Haquri Parveen, Da nan da Gidan Aurenki duk daya neh. Kamar Yanda za'a kula dake anan Haka a Chan, karki damu kanki kinji??. Maganar Makaranta kuma Za'a miki Transfer Zuwa Chan Garin Sai ki Cigaba da Abinki" Batace Komai bah Ta mike Tana Kuka Sosai Tabar Dakin.. Kwana Tai Kuka, Kota Kan wanda Za'a Aura mata batabi Bah. Washe Gari da Safe Tanada Test Dakyar Ta Tashi ko breakfast batai bah tai Wanka Ta Tafi, Idanunta Luhu luhu. Saida Aka Gama Test din Sannan Suka Hadu da Deexa. Kallanta Tai Da Mamaki "Meya Sameki?? Daga Ganin idanunki kinyi kuka??" Kamar Jira Parveen take Ta Fashe Da Kuka Tana Kallan Deeza. Hannunta Ta Deeza ta kama suka Shiga Motanta, Kuka Parveen Take Sosai Dakyar Deeza Ta lallasheta Ta danyi Shiru "Pls Bae Banasan Ganinki cikin Wannan Halin Fadamin menene?? Ko Yariman neh kuma" Girgiza Kai Parveen tai Hawaye na Cigaba da Zuba "Mai Martaba neh Yakeso Yamin Aure" Dafe Kirji deexa Tai "Aure!? Y??" Girgiza Kai Tai "Nima bansani bah Deeza, Niba Auren da zaimin ke damuna bah, Karatuna. Ke kanki kinsan Yanda Naci buri akan Karatun nan, Inaso na Zama Gynecologist. Inaso na Taimaka ma Yan uwana Mata. Dafata Deeza tai "Wannan Bah Abin damuwa bneh Bae, Ko kina gidanki Zaki Iya Yin Karatunki indai Mijinki zai Yarda" "Ta Yaya Deeza??, Yanda Fa Umma Kemin Bayani Ba Inan Garin Zan Zauna Bah?? Tho ya makomar Karatuna??" Shiru Deeza Tai Tana Nazari "Karki Damu Pls, Allah Yana Tare Dake. Ki Cigaba da Addua Kinji??" Kae kawai Parveen ta Gyada batareda tace komae bah Haka Tai Yinin Ranar Hankalinta ba Akwance Yake bah.. Kwanaki Sun ja, Anata Shirye Shiryen Biki daga Duka bangaren Biyu. Har Yau Parveen batasan Wanda Zata Auraba kuma Bata Tambaya bah. Iyayen neh Kawai ke Shirye Shiryensu, Yarima ko da Parveen bah abinda Suke Shiryawa Bama Kaman Parveen da Tunda Akai mata Maganan Auren Batada Aiki sai kuka Sai tunani, Makarantan ma Ta daina Zuwa, Kullum idan Deeza ta tashi makaranta Sai Tazo ta Lallasheta... Sarki Kabeer Yasa Anata Gyaran Inda Yarima Zai Zauna da Amaryanshi, Cikin Gidan neh anma Da Tazara Sosai Tsakaninsu Da Fada Sides din fulani da Martaba. Shiko Yarima Sam Baisa Maganar auren Akaba Aikinshi Yake bah Ruwanshi. Bilal ne Kawai keta Fadi tashi akan Bikin, Duk Wanda Yakama Ya sanar Mawa duk Ya Sanar... Ana Saura Sati Biyu aka Kawo Lefe. Lefene Nagani na fada Ko lefe Zahra buhari albarka lol, Anata Yaba Kayan Lefen Itako Parveen na daki qudundune cikin Barko sai kuka take. Ganin Batada niyar Yin wani abu lokacin Bikin Yasa Umma ta nemi Deeza, Katin Gayyata Taba Deeza Tace Ta rabama Qawayenta, Tareda Ankon da umma Tasa Akai Oder dan Rabama Yan uwa da abokan Arziki, Deeza Ce Taita Zarya na Rabo Itako Gimbiyar Tana Gida Kullum Cikin Kuka... Fulani Tasa an Hada dinner Wanda Za'ai Washe Garin Biki Haka Umma Itama ta Shirya Events Kala Kala Tareda Taimakon Deexa. Ana Saura Sati Daya Hajiya Shuwa daga Maiduguri Tazo dan shirya Amarya, Ansha Daga da Parveen Saida Umma Tai mata Jan Ido Sannan Ta Yarda Aka Fara Gyarata Tana Kuka Sosai. Kullum Sai an Mata Gyara Cikin kwana Hutu Ta Qara Kyau kamar ba Itaba. Ana Jibi Daurin Aure aka Fara Events Wanda Aka Fara Da Arabian Night. Da Taimakon Hajiya Shuwa ta Shirya cikin Hadadden Arabian Gown Baki, Kwalliya Hajiya Shuwa tai mata Ta Fito Sak Kamar Balarabiya, deeza Ta Shigo dakin itama Cikin shiri, ta Rike mata Hannu Suka Fito Zuwa Hall din Cikin Gidan. Suna Shiga Wajan Yadau Tafi, Sai a Sannan Parveen ta Dago, Mamaki Ne Kwance kan Fuskanta Ganin Kawayenta na nesa dana Kusa, Wasu mah Tunda Suka gama Secondry schl bata Qara Ganinsu bah, A Hankali ta Rintse ido Tareda Duqar dakai Wasu zafafan Hawaye Suka gangaro mata... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣5⃣ A Hankali ta Rintse ido Tareda duqar dakai Wasu Zafafan Hawaye Suka Gangaro Mata. A Haka Suka Qarasa Inda Amarya Zata Zauna. Saida Ta Zauna Sannan aka Fara Chashewa, Ganin Kawayenta da Yanuwa Yasa Tadan Saki Jiki tana Murmushi... Haka Akaita Bukukuwa Har zuwa Ranar Daurin Aure. Parveen Ranar Daurin Aure Yini Tayi Kuka, Dakyar umma Ta Lallabata Ta Shirya Cikin Wani Hadadden Lace Light blue. Anmai Dinkin buba, Kayan sun Mata Kyau Sosai. Kana Kallan Idonta Kasan Tayi kuka, Hajiya Shuwa Ce Tai Mata Makeup ta Fito Princess Parveen dinta Sosai.. Karfe Daya da Rabi na Ranar Sati Aka Daura Auren Fardeen Kabeer da amaryarshi Parveen khaleed a Kofar Fadar Sarki Khaleed a Bisa Sadaki Dubu Dari. Daurin Auren daya Tara Manyan mutane Tun daga Kan Shugaban Qasa Har Zuwa Gwamnoni, ministers, Senators, Sarakuna. Babba da Yaro manya da Qanana. Ni Kaina Ummy Abduol Saida na kashe qwarqwatan ido na Baje kolin Hajata na Litttafai Inata Ciniki..lol chan na hango Umma Yahaya musa Da Ummiekhaleel Sunata Dambe akan takeaway..lol Cikin gida ma Y cika maqil, Matan Manya neh anata Hidima Cikeda Farinciki, misalin Karfe Hudu Aka Tafi da Amarya Gidanta. Parveen Tayi kuka Kamar ranta Zai fita, Dakyar Ta Yarda Ta Shiga mota bayan Mai martaba ya Gama Mata Nasiha. Koda Suka Shigo garin Gombe, Gidan mai martaba taga sun nufa. A Tunaninta Za'a Kaita neh Fulani Tai Mata Nasiha, Saida Aka kaita Side din Fulani Tai Mata Nasiha Sannan Aka wuce da Ita Bangarenta. Bata Qara Tsinkewa bah Saida Akace Mata Nan neh Gidanta... Deeza dake kusada Ita Ta Kalla Idonta cikeda Kwalla, Deeza Wanene Mijina?? Shiru Tai Nayan Seconds Sannan Tace "Nima Bansani bah Parveen" Qara Kallanta Parveen Tai Cikeda Mamaki "Nanfa Gidansu Yarima Fardeen neh, Meh Nakeyi a Nan??" Shiru ne Ya biyo baya. Ganin Deeza batada Niyan Magana Yasa Parveen ta Sulale ta Kwanta Kan Gado Tareda Lumshe Ido. Shin wa Zata Tambaya?? Yarima Fardeen koh Babban riga Yasa Fari Kar, Kayan Sun Amsheshi Sosai. A Wajan Daurin Aure sai Washe Baki Yake Yana Gaisawa da Mutane Kamar da Gaske. Shiko Bilal Har Ranar Mamaki Yake Wai dagaske Yarima Neh kuwa Yau Ya Yarda Zeyi aure?? Ana Gama Daurin Aure ko Walima Yarima bai Tsaya bah Ya juyo zuwa Gida. Yana Tsa Gida Ya Chanza Zuwa Black Trouser da White T Shirt ya Fito. Matan dake Haraban Gidan Sai mai Tsiya Suke, Murmusawa Kawai Yake Yahau motarshi yabar Gidan, wani hadadden Gida Ya nufa Wanda tun dawowanshi Ya Siya. Horn Yayi mai Gadi Ya bude Ya Shiga Yayi Parking ya fito. Cikin gidan ya Nufa Kai Tsaye, A Hankali ya bude kofan falon. Wata Kyakyawar Budurwa ce Daga Gani bah musulma bace Ta Taso ta rungumeshi Tana Mai murmushi, Shima Murmushin yake Mata Ya Dagata chak Sai Bedroom din dake Falon.. Fardeen bai dawo gidan bah sai washe Gari da Safe, Fulan ta tareshi rai bace. "Daga ina kake Yarima??" Sosa Keya yayi "Wallahi Na...Umm Naje wajan mahdi neh jiya da Daddare Sai Barci ya kwasheni a Chan" Kallanshi kawai Fulani tai tareda Girgiza kai "Shiknan jeka. Ka Shirya Anjima Akwai Dinner" Dan Tsuke Fuska Yayi baice Komai bah Yabar wajan Mamaki neh Sosai a fuskan Fulani. Binshi tai da Kallo tai Har yabar Wajan Sannan Ta Wuce... Amarya Nachan Side dinta ita da Qawayenta da Yan Uwanta. Fulani ce Tareda Kuyanginta Sukai Sallama, Duka mutanen Falon Suka Amsa, Gaidata Sukai Ta amsa Fuska A sake Sannan ta Nufi inda Amaryan Take. Kwance ta Sameta, Qawayenta Sun Zagayeta, Tanajin Muryan Fulani ta mike ta zauna. Saida Suka Gaida Fulani Sannan Suka bar dakin. Fulani Ta Matso kusada Ita Tana Murmushi "Amarya Kinsha Kamshi" Turo Baki Parveen Tai "Nifa Fulani Har Yanzu ban Gane bah" "Menene Baki ganebah??" Tsintan Kanta tai da Kasa fadama Fulani Rashin Sanin waye Mijinta Fulani ta kalleta "Ina jinki" Shiru Parveen tai ta Dukar dakai tana wasa da zoben zinarin dake Hannunta.. Cikin Tsa Fulani Ta soma kiran Kuyanganta "Ladi! Ladi!!" Ta amsa ta shigo dasauri dauke da Wani Hadadden Trolly. Ajiyewa tai ta Fita Fulani Ta kalli Parveen "Anjima Akwai Dinner, Wannan Kayan nakeso kisa Kinji my Daugther??" Kai Parveen ta Gyada Sannan Tace "Nagode Fulani" Shafa Kanta Tayi tana Murmushi "You dont hav To" Itama Murmushin Tai. Fulani ta mike ta mata Sallama Tabar Dakin... Karfe Bakwai da Rabi dai dai Aka Gama Shirya Parveen Cikin Hadadden Gown. Kwalliya Aka Mata Ta Fito tai Kyau Sosai, Deeza Dake gefenta Sai Kodata Take. Parveen Koh Sai Bata Fuska Take Kamar zatai Kuka... A Bangaren ango shima Shigan Hadadden Shadda Yellow Yayi, Sai Farin Hula Da Takalmi. Abinka da Farin Mutum, sai Yellow Shaddan Ya Haskashi Sosai. Mahdi dake Gefenshi ya kwashe da Dariya. "Menene na Dariya" Qara Tuntsirewa da Dariya Mahdi Yayi "Allah mutumina Kaji Tsoron Allah, Duk wanda Ya ganka Zai dauka Auren Soyaiya Kayi. Nanko Bah Haka Baneh" Baice Komai Bah Saima Qara Hade Rai da yayi "Nifah Wallahi Badan Fulani ta Matsa Bah dah Yanzu inachan Eneh na Jirana" Zaro ido Mahdi Yayi har ya bude baki zaiyi magana Bilal ya Shigo. "Ango Kaifa Ake jira Ka Fito" Tsaki Yarima Yayi ya kwashi wayoyinshi ya fita, bilal da Mhdi Suka bishi a Baya... Yana Fita Yaga Mota a Qofar Side dinshi, Baiyi wata Wataba Ya Shiga drivern Yaja Sukabar Wajan. Ganin Sun nufi Cikin Gidan Ya Kalli Drivern "Ina Zamu kuma??" Sarauniya Fulani ce Tace idan na daukeka Naje Na Dauki Amarya, Tace a Mota daya zamu. Dogon tsaki yarima Yaja Ya Juyar dakanshi yana kallan Window... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣6⃣ Sarauniya Fulani ce Tace Idan na Daujeka Naje na Dauki Amarya, Tace a Mota Daya za'a Kaiku.. Dogon Tsaki Yarima Yaja Ya Juyar dakanshi Yana Kallan Window.. Koda Sukaje Gidan Amarya Duk Qawayenta da Yan uwanta Sun Tafi daga Ita Sai Deeza.. Drivern neh Ya Fita Ya musu Magana, Parveen Ta Miqe Deeza Na Biye da Ita, Drivern Ya Bude mata Qofan motan Ta Shiga Ta zauna, Sam Bata Lura Da Yarima bah saida ta Zauna Sosai, Juyawa Tai Suka Hada Ido da Yarima, Dasauri Ta bude motan ta Fita Dagudu, Deeza Datake qoqarin Shiga Gaban Motan Taga parveen ta Fito a Guje. Binta tai tana kwala mata kira.. Shiko Yarima Kafada Ya Daga Ya Kira Drivern Yace Su wuce. Bah Musu drivern yaja Suka Bar Haraban Wajan, Taro Yayi Taro, Duk wanda Aka Gaiyata Ya Halarta Amarya da Ango kawai ake jiran Isowarsu. Dai dai Bakin kofan Wajan Drivern Yayi Parking, Mahdi da Sauran abokanan Ango tareda Qawayen Amarya Suka Qaraso wajan Dan Musu Rakiya Zuwa Ciki. Mahdi ne Ya bude Kofan Motan Ganin bah Amarya Yasa Ya Kalli Yarima "Were is our Bride??" Kafada Yarima Ya Daga Ya cigaba da Daddana Wayanshi Sassauta Murya Mahdi Yayi "Kaifa Dan Iska Neh Fardeen. Ina Amarya Pls?? Komai ya Tsaya a Wajan nan ku kawai ake jira" Tsaki Yarima Yaja "Pls Mallan Karka dameni" Wayanshi Ya Ciro Ya Kira Layin Bilal dan Yasan Bai riga Ya Iso bah, saida Yayi Ringing so biyu Sannan Ya daga "Pls Bilal kana Ina??" "Ina Gida Yanzu zan Fito" "Dan Allah idan Fulani basu Taho bah Ka Fada Mata Amarya Ake Jira" "Tho" kawai bilal Yace Tareda Kashe kiran.. A Falo Parveen ta Cire Takalman Qafanta ta wurgar Ta nufi bedroom dinta a Guje tana Kuka. Deeza na Shigowa Tayi tuntube da Takalmin Saura Kadan ta fadi, Dakin Ta nufa tana Cigaba da Kwallama Parveen kira. Kwance Ta Sameta Ruf da Ciki Ta kuka Da Qarfi. Dasauri Ta Qarasa Tareda Dagota Zaune "Why all dis Parveen?, Yanzu bah Lokacin kuka baneh" Dagowa Parveen tai Tana Kallanta Cikin Kuka "Deeza Uh Mean Ya..Yarima ne Mij..M..mijina??" Gyada Kai Deeza tai Tana Share Mata Hawaye "Ki Shafawa Zuciyarki Ruwan Sanyi Pls Parveen. Try to Fight Wannan Damuwan, Karki Sama Kanki Ciwo. Believe Me Evrything Wil Change Insha Allah" Kuka Parveen Ta Cigaba Tana Dukan Gadon da Hannunta "Why! Why!! Umma, Meyasa tuntuni Baki Fadamin Yarima neh mijina bah" Sanda Saqon Mahdi yakaima Fulani, Dasauri Itada Mutanenta Suka Nufi Side din Amarya, Har Yanzu tana nan kwance Tana Kuka. Fulani na shiga Bedroom din ta qarasa bakin gadon Dasauri Ta Riko Parveen Tana Kallan deeza Tace "Meya Sameta??" Bayanin duk yanda Ya faru Deeza Taima fulani.. Shiru Tai Tana Tunani, Dakyar ta Samu ta Lallasheta aka sake mata kwalliya motarsu daya da Fulani Suka Nufi wajan. Mutane Sun Gaji da jira, Mutane Har sun Fara Tafiya... Wuraren karfe Tara da Kwata motarsu fulani ta iso wajan, Har Yanzu ango na Cikin mota sai Waya yake da Yanmatanshi. Fulani ta fito tareda Kuyanginta, Deeza Ta riqe Hannun Parveen Suka Fito daga Motan, Mahdi Ya Qaraso wajan, Fulani Tace "Kacema Yarima Ya fito" Dasauri ya nufi motan da Yarima ke Ciki ya fadamai Saqon Fulani, Ya Fito Yana Taku irinna Qasaita. Daidai Inda Parveen ke Tsaye Suka Jera zuwa Cikin Hall din. Itadai Parveen kanta na Qasa bah Abinda Take Sai Zubda Hawaye... Suna Shiga wajan Ya gaure da tafi da Kidi har Suka Qarasa inda Aka tanada musu suka zauna. Raye Raye aka Fara Tareda abubuwan bada Dariya, anci Ansha Sannan Aka Umarci Amarya da Ango su Tashi dan Yanka cake. Gaban Parveen Ya Fadi anma Ta dake Ta mike suka qarasa inda Cake din yake, Shiya Fara Riqe wukan Sannan Itama Ta Riqe Chan Qarshe Suka Yanka. Tafi akai musu, Mc Ya Umarci Ango Yaba Amarya Cake a Baki. Dakewa Yarima Yayi ya Yanko Yakai Mata Baki, Kauda kai Tai Tareda Yamutse Fuska. Tuna Mutane na Kallansu Yasa Ta Maida Fuskanta Ta gutsura Kadan. Tafi aka qara Musu Sannan Mc ya Umarci amarya taba Ango a Baki.. Dakyar ta Yanka qato ta dan dago Suka hada ido, kuda kai tai dasauri, Yadan rankafo takai mai Baki. A Hankali ya bude Bakin, ganin baida niyan Budewa Yasa Ta Tura Mai a Baki duka. Dariya akai Tareda Tafi, Yawancin Mutanen abin ya burgesu, Itako amarya da Gaiya Tamai dan Kawai ta batamai rai. Dakyar ya iya Cinyewa Ysa Hankie Ya goge Bakinshi, Ga Mamakina Gani nai Ya Kama Mata Hannu suka nufi wajan Zamansu, Suna Qarasawa Ta Fizge Hannunta Tana Turo Baki. Murmushin Mugunta yayi ya kauda Kai... An Raba kyaututuka Iri Iri tun daga kan Joters, colenders, Takunkuna, Hankies, dinner sets, mugs, Ceramic plates dadai Sauransu, Haka Akai Dinner kowa Ya watse cikeda Farinciki. Kamar dazu Amarya mota Daya Suka koma gida da Fulani. Shiko Gogan Motarda Ta daukoshi Ita ta Maidashi Gida... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣7⃣ Kamar dazu amarya mota daya suka Koma Gida da fulani. Shiko Gogan Motrda Ta daukoshi ita ta Maidashi Gida... Washe Gari da Safe Mutanen Zaria Yan Rakiyan Amarya Suka Fara Shiri, Parveen na Ganin Deeza zata tafi ta Fara Wani Sabon Kukan. Bah Irin Lallashinda Ba'ai mata bah Anma ta Tubure, Hakanan duk mutanen Suka Tafi Suka Barta Ita Kadai Kwal a Cikin Gidan Kamar Mayya... Mai Martaba neh Zaune Da Fulani a Gefenshi Sai Yarima dake Kan Carpet kanshi a Kasa. Mai martaba ya Kalleshi Sannan Ya Fara Dacewa "Yarima Yanzu Ka Zama Babban Mutum, Duk darajan da Akeba Mutum baikai idan Yayi aureba. Ina Maka Nasiha Akan ka Kula da Matarda, Kamar Yanda Kasani Yanzu Ci da Sha, Tufatarwa Da Wajan Kwanciya da Sauransu duk Yana Wiyanka. Banaso Naji daidai da Rana daya ka sabama yarinyan nan, Ku Zauna lapia Allah ya muku Albarka" Yarima Da Fulani Suka Amsa da "Ameen" "Insha Allahu zanyi Kokarin Kiyayewa" Fulani Tai Murmushi "Ni Kuma Maganan dazanyi, Kaga Yanzu Kai Aure. Maganan Shashancinka daka Saba Babu Shi Yanzu, Banda Fita Yawon Dare Dan Allah Yarima. Kaga Dai Ita Kadaice A Gidan Kuma bah dadi mutum Ya zauna shi kadai a Gida" Hade Rai Yayi kanshi na Qasa "Tho Fulani Zan kiyaye" Ta Qara Murmushi Tace "Allah ya maka Albarka" Ameen Yace Ya mike Yabar Falon... Side Dinshi ya nufa, Direct Bedroom Ya Wuce, Dakin Yagani Wayam bah Kaya Sai Funitures din dakin kawai. Qarasawa Yayi ya bude walldrop Yaga Wayan, ranshi ne Ya baci Ya Nufi Side din mai martaba. A Hanya Yaci karo da Fulani tana qoqarin Zuwa nata bangaren, Ta kalleshi da Mamaki "Ina zuwa??" "Fulani ina aka kaimin Kayana?? Na Duba basa Side dina" Hararanshi Tai Cikin Sigan Wasa "Ina Kuwa Za'a Kai maka in bah Sabon Side Dinka Bah" Bata Rai Yayi Baice Komai Bah ya juya Zaibar Wajan, Fulani Ta kira Sunanshi. Juyawa Yayi ya Kalleta Tace "Ina Kuma Zaka??koh ka manta Amarya Nachan Tana jiranka neh" Ranshi Bace Ya Juya ya nufi Gidan Amarya... Parveen Taci Kuka Ta Qoshi, Ganin Kukan bazai Pisheta bah Yasa Ta mike Ta Shiga Toilet, Wanka Tai Ta Dauro Alwala ta Gabatar da Sallan Magriba da Isha Sannan Ta Sauya Kayanta Zuwa na Barci Ta Kwanta. Barci ne Yayi Qaura a idonta, Tunani ta Soma Yi Kala kala, Yanzu ya zamansu Zai Kasance Da Yarima?? Tsaki Taja A Fili Tace "Saidai Wallahi Mu Goga, Bazan Zauna Ka Raina min Hankali Bah" Murmushi Tai Ta Gyara Kwanciya A Hankali Barci mai nauyi ya dauketa Cikeda Mafarkai Kala Kala... Koda Yarima Ya Shigo Side din Parveen Ta Dade dayin Barci. Dakuna Yagani Guda Biyu, Shiru Yayi Yana Tunani, Chan Ya bude na Hannun Damanshi Ya Shiga, Hadadden dakine, Wanda Yafi Wanda ya Baro, komai Akwai a Dakin, A Hankali ya Qarasa Ciki, Turarukanshi Da Lotions dinshi Ya hango Kan Mirrow Din Dakin. Riqe Kugu Yayi "So Nan Fulani Tasa a Kawomin Kayana, Umm Not Bad!" Toilet Ya nufa Ya Watsa Ruwa Ya Fito Daure da Towel, Wayanshi Ya dauka Ya Soma neman Wani Layi, Yana Fara Ringing Aka dauka, Banji meh akace achan Bangaren bah. Dan Murmushi Yayi Yace "Am Waiting For You" Sannan Ya Kashe Kiran, Baifi Awa Daya da Wani abu bah Akai Knocking Kofa, Dsauri Yarima Ya mike Ya Fita Ya bude, wata Kyakyawar Yarinya Ce Fara Ta Shigo Ta Rungumeshi Tana Dariya. Shima Dariyan Yayi Tace "Ka Manta Dani Prince, Ai naji kayi Aure" Gefen Fuskanta Ya Shafa Yana Kallan Kwayan idonta "I Dnt Hv time For All dis Conversations, Am in need" Daukanta Yayi Chak Tana Dariya ya Nufi Dakinshi da Ita.. Kiran Sallah neh Ya Tashi Parveen, Addua tai Ta Mike Ta zauna Sannan Ta mike Ta Nufi Toilet, Wanka Tai Ta dauro Alwala Ta Dawo Dakin, Kayan Jikinta ta Sauya Tasa Hijabi Ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallah, Tana Idarwa Tai Adduointa. Shiru Ta zauna Jugum Tana Tunani. Chan Ta Mike Tuna Jiya Deeza Ta bude kit taga Qur'ani, Budewa Tai Ta dauko Qur'anin Ta dawo Kan Sallayan Ta Zauna, Suratul Maryam Ta bude Ta Shiga Karantawa a Hankali Cikin zazzaqan Muryanta, bata Tashi bah Saida Taga Garin yayi Haske a Hankali Tace "Sadaqallahul Azim" Ta Rufe Qur'anin Ta maida Cikin Kit din... Knocking Aka soma Yi a Qofan Falo, Ta Fita Ta Bude, Kuyangi neh dauke da Kulolin abinci kala kala, hanya ta basu suka wuce, kan dinning Suka Aje Sannan Suka Zube dan Kwasan Gaisuwa, amsawa tai suka fita. Shafa Cikinta Tai ta yamutse Fuska, Waige Waige Ta Soma Yi, wani qofa Ta Hango Ta qarasa ta bude a Hankali. Kitchen Ta gani, komai na Buqata Akwai a Ciki, Sosai Kitchen din ya burgeta. Dube dube ta Soma Yi, chan Ta Hango Wani set din plates, kwalin ta bude ta dauko daya ta Wanke, da Dauki chokali Shima Ta Wanke Ta Fito. Tana Zama Kan Dinning din Taji An Bude wani qofa daga Gefenta, Kai Ta daga Cikeda Tsoro... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣8⃣ Tana Zama kan Dinning din Taji An Bude Wani qofa Daga Gefenta, Kai Ta Daga Cikeda Tsoro dan A Tunaninta ita kadaice Ta kwana a gidan. Wata Kyakyawar Yarinya ta gani Ta Fito Sanye da Wani Matsatsen Wando da Riga, Kafanta Sanye da Dogon Takalmi, Kan nan Yasha Attachment. Ko inda Parveen Take Bata Kalla Bah Tai Hanyar Kofan Falon, Juyawa Parveen Tai Cikeda Mamaki, daidai Nan Yarima ya fito Sanye da Brown Jallabiya, Bai ko Kalli Parveen Bah Ya Riqema Yarinyan Hannu suka Fita Daga Falon.. Mamaki neh Kwance Kan Fuskan Parveen, Tunani ta Soma, dama Yarima Na neman mata meh?? Wata zuciyar Tace "Ina Ruwanki da neman Matanshi" Tsaki Taja Ta Soma Zuba abincinta, saida Taci Ta qoshi Sannan Tadauke Plate din Takai Kicin Ta koma Daki. Wanka Ta sake Ta Shirya Cikin Pink and Purple Atamfa, Simple Make up tayi tasa Mayafi Pink, Tadau Flat Shoe Shima Pink Tasa. Wayanta ta Dauka Ta Fito Falo, Tana Qofarin Bude qofan Falon Aka Bude. Yarima Neh, Yana Ganinta Ya Hade rai, Itama hade Ran Tai TaKauda kai, ta gefenta Yabi Ya Wuce ya Shige Dakinsa. Tsaki tai Ta Fita Ta nufi Side din Fulani.. Fulani na Ganinta ta Tareta da Murna, Har Kasa Ta Tsugunna Ta Gaida Fulani, Ta Amsa Fuska A Sake Tana Fara'a. Parveen Tsintan Kanta Tai da Jin Kunyan Fulani, Lura da Hakan Yasa Fulani Tace "Amarya kinsha Kanshi" Sadda kai Parveen tai tana dan Dariya "Bai Kamata Ki Fara Fita Tun Yanzu bah, ki Bari idan kikai Sati daya Saiki Fita. Sannan Maganan Makaranta Mun Gama Magana Da Mai Martaba nan da Sati Biyu saiki Fara" Dagowa Parveen Tai Fara'a Kwance Akan Fuskanta "Nagode Allah Ya Qara Girma" Fulani ta Amsa da Ameen Mikewa Parveen tai tace "Na Barki Lapia" Fulani Cikeda Sigan Wasa tace "A Gaidamin da Ango" Murmushi Parveen Tai Tabar Dakin.. Koda Ta koma Yanda Tabar Abincin Haka Tadawo tasameshi, Tsaki Tai ta Kwashe Kwanukan Takai Kicin. Daki ta Koma Tai Kwanciyarta Tareda Jawo Wayanta, Numbern Umma Ta kira, Yana Fara Ringing ta dauka. Ajiyan Zuciya Parveen Tai Sannan Tace "Barka da Safiya Umma" Umma Cikeda Murna Tace "Parveen kin Tashi Lapia? Ya Kwanan Ango?" Jim Parveen Tai Sannan Tace "Yana Lapia lau" Tho Madallah "Umma Ya Mai Martaba??" "Yana Lapia Lau, Dazu koh muka Gama Maganan ki" Murmushi Tai "Ina Gaidashi" Insha Allahu Zaiji..Kashe Wayan Umma Tai, Parveeb Tabi wayan da Kallo. Tayi Missing din Ummanta, Nan da Nan Hawaye Suka Fara zuba A Idonta... Kwanciya Tai Ta Lumshe Idonta, A Haka Barci Ya dauketa Cikeda Kewan Gida.. Haka Suka dau Tsawan Sati, Kullum Sai yarima Ya kawo Yanmatan shi. Sam Parveen Hakan Bai Damunta, Tunda Tazo gidan Magana bai Taba Hadasu dashi bah. Ita Hakan mah Yafi mata.. Ranar da Takai Sati Daya Fulani ta Umarceta data Fara Girki..Da Yanma Ta Daura Tuwon Shinkafa Miyan Ugu, Kasancewar Komai Na Dangane da Kayan Miya Akwai a Cikin Kicin din.. Nan da Nan gidan ya Gauraye da Kamshi, Saida Ta Gama Komai Ta zuba a flask Ta Kawo Dinning, Mai Martaba ta Zubamawa a Wasu Hadaddun Kuloli. Baiwar dake Taimaka Mata da Goge Goge Taba Takai Ita kuma Ta Koma Dakinta dan Watsa Ruwa... Watsa Ruwa Tai Ta Fito Daure da Towel a Kirjinta, Sai Qarami datake Tsane Ruwan Kanta, zama Tai kan Stool din Mirrow Tana Cigaba da tsane Kan nata. Saida Ta Gama ta dago ta Kalli kanta a Mirrown, Ganin Mutum kawai tai Kan gado Yana Kallanta, Dasauri ta mike Tareda Kwalla ihu. Saura Kadan Towel dinda ke Kirjinta ya Fadi, Sam batama Lura da Waye bah Tabar dakin a Guje. Baiwarta Atika Taci Karo da Ita, atika ta Kalleta Hankali Tashe "Lapia Ranki Ya dade Maiya Faru??" Dakinta Ta Fara nunama Atika a Rude Har atika ta Nufi dakin Taga Yarima Ya Fito Hannunshi daya Cikin Aljihunshi, Fuskan nan Daure Tamau. Barin wajan Atika tai Kanta a Qasa Kamar munafuka... Sai a Sannan Parveen Tasan Yarima Neh, Dogon Tsaki Taja Tareda Kauda kai Gefe. Dariya yarima Yaso yi anma Ya Dake, Shima Tsakin Yayi yabar Falon Zuwa Dakinshi "Anma Allah ya Isa, Mutum Yayita Abu kamar bah musulmi bah" Dakinta ta koma Ta Shirya Sannan Ta Fito. Kan Dinning Ta Sameshi Yana Daddana Wayanshi, Guntun Tsaki Taja Ta Qarasa Wajan Tahau Zubamai Abincin... Malmala Hudu tasamai Gasu Manya Sannan Ta Zuba mai Miya a Dayan Plate din, Kallanta kawai Yarima Yake Da Mamaki, Tana Gamawa Ta juya Zata Bar wajan, Tsawa Ya Daka Mata, "Ke Dabban inace da Bakisan Yanda Ake Serving Mutane Bah. Wannan Abincin Suwa kika zubama Wah?? Koh kin dauka ni kece da Baki Saba Cin Abinci bah". Saurin Katseshi Tai Rai Bace "Karka Qara Kirana Dabba, Tunda Baka Ganni da Jela Bah Balle Qaho, Kai Yakamata Ka Kira Kanka Dabba Kaida Bakasan Darajan dan Adam bah. Kai kanka Kasan Nafi Qarfin Abinci, Koh Ka manta daga Gidan da Nafito neh." Qarasa maganan Tai Rai Bace "Kai Qoqari ka Koma Islamiya dan Har Yanzu Jahilci na Dawainiya dakai!" Wani Kukan Kura Yarima Yayi Ya Mike ... Tho Fah??.. Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page1⃣9⃣ Qarasa Maganan Tai Rai Bace "Kai Qoqari ka Koma Islamiya Dan Har Yanzu jahilci na Dawainiya Dakai!" Wani Kukan Kura Yarima Yayi ya Mike Tsaye, Mari kyawawa Guda biyu Ya Saukewa Parveen Wanda Saida Taga Stars. Shaqeta Yayi Fuskan nan Nashi Na Chanza zuwa ja, inda Abinda Yarima Ya Tsana Bai wuce Parveen Ta kirashi jahili bah. Huci Yake Sosai, Hannunshi Na Kan wuyanta Daya Maqure, Parveen ko Sai Tari Take Dakyar Idanunta Sun Firfito, Ganin Bah sarki Sai Allah Gashi Bah Iya Magana Zatai bah Yasa Ta Rarumi Glass Cup dinda Ke kusa da Ita Ta Bugamai Akai. Sakinta Yayi dasauri ta Fadi Kasa Tana Rike Da Wuyanta, Wurin data Bugamai cup din Ya Dafe Ta mike Dakyar Ta nufi dakinta A Guje Tareda Sa Key.. Ranshi Bace Ya bita Da Kallo, Hannunshi dake kanshi Ya Sauke Yana Dubawa, Allah Yaso Cup din Bai jimai Ciwo bah. Wayanshi Ya dauka Yabar Falon a Zuciye. Parveen Kan Gadonta ta Fada Ta Saki kuka Mai Karfi, Anya Kuwa Zata Iya cigaba da Zama a Gidan nan Da Yarima?? Tsagaita Kukan tai Tana Tunani. Inko Har Zata Cigaba da Zama dashi to dole Tadau Damara Dan Ta Nunamai Itama Macece. Da Wannan Tunanin Ta Yini Yar Yanma.. Satin Parveen Biyu kullum Idan tai Girki Sai Tasama Mai Martaba Da Fulani, Shiko gogan Idan ya Dawo Atika take Sawa Tai Serving Dinshi. Ranar data Cika Sati biyu Kuma a Ranan Zata Fara zuwa Schl, Da Safe Ta shirya Cikin Hadadden Shaddanta Purple, Dinkin Riga da Skirt. Side din mai Martaba ta Fara nufa Don Kwasan Gaisuwa, Tana Shiga Ya tareta Da Fara'a, har qasa ta Tsuguna Ta Gaidashi. Ya Amsa Fuska a Sake, Godiya ya Mata Akan Abincinda Take aikomai, Dan murmushi kawai Tai Sannan Tace "Bakomai Ranka Ya Dade. Kaima Ai Mahaifina neh" Gyada Kai Mai Martaba Yayi "Hakaneh Parveen, Inajin Dadin Girkin da kike Min, Yanzu duk na aje Girkin Turawan nan" Dan Dariya tai Qasa Qasa, Ta Sadda Kai "Ranka Ya Dade Yau kace Zan Fara Zuwa Makaranta" Kai Mai Martaba Ya Gyada "Hakaneh yanzu idan kin Shirya sai Aima Sarkin Mota Magana Yakaiki, Kije ki Zabi duk motar da Kikeso a Kaiki a Ciki" Dan Murmushi Tai Tareda Godiya, ta mike Tabar Side din Cikeda Farinciki.. Side din fulani Taje Ta Gaidata Sannan Ta Mata Sallama. A Wani Hadadden Buggatti aka Dauketa Zuwa Makaranta. Ta samu An Gama Mata komai, Lectures Kawai Zata Fara Attending, Dadi Taji Sosai, A Ranan Tai Sabuwar Qawa mai Suna Yasmeen... A Gida Kuwa yarima Cikin Shiri Ya Fito dan Zuwa office, Dogarinshi na Binshi dauke da Jakan laptop dinshi. Wajan Motocin Gidan Suka Nufa, Ganin Bah Motan Da yayi niyan Fita Dashi Yasa Ya Hade Rai, juyawa Yayi Ya Kalli Dogarin. Jeka Kiramin Sallau, Tho Yace Ya Tafi dasauri. Chan Sai Gasu Tare, rai Bace Yarima Ya Kalleshi, Ina Motar danasaka Ka Wanke. Sosa Kai Sallau Ya Fara. Tsawa Yarima Ya dakamai "Kai make Saurare" "Ranka Ya Dade Gimbiyace Tace Abata Motan Dashi Za'a Kaita Makaranta" Wace Gimbiya??" "Amarya Ranka Ya Dade" Tsawa Yarima Ya Dakamai "Har Ni Inyi Magana Akan Inason Abu, Anma ka Dauka Kaba Wani Chan??" Dogarin Dake Gefe Ya Kira Tareda Bashi Umarnin A Tafi da Salihu amai Bulala Hamsin Sannan A koreshi. Dasauri Sallau Ya rusunna yana Bada Haquri "Dan Allah Ranka Ya Dade Kamin Rai, Da Wannan sana'an Nake Cida Iyayena da Iyalina. Na Yarda Amin Bulalan Anma Kar a Koreni" Tsaki Yarima Yayi, ya Shiga benz dinda Ke Kusa Dashi Drivern Ya Tada Sukabar haraban Gidan... Parveen bata dawo gidan bah Sai Bayan La'asar, Side dinta ta nufa Saboda ta Gaji, Wanka tai ta Sauya Kaya Zuwa 3quater da Yar Qaramar Pink Tshirt, Saboda Lokacin Xafi neh. Kicin Ta Shiga ta Fara Hada Abincin Dare, Qulunta na waina ta bude Ta duba taga ko ya tashi har Yafara zubewa, Nan da Nan ta Fara Hada Miyan Alehonta Dayasha Kayan Hadi. Tana Gamawa Tahau Suyan Wainan. Bata Gamaba Saida Aka Kira Sallan Magrib, Sallah taje Tai Sannan Tazo Ta bada namai Martaba.. Zama Tai Taci Nata Sannan Ta koma Falo Ta kunna Tv tana Kallo, Yarima Bai Shigo Gidan bah Sai Wuraren Karfe Shadaya. Har Barci Ya kwasheta Tana Zaune Taji Bude Qofan Falon, Juyawa Tayi Taga Mai Shigowan, Yarima neh Ya Shigo Hannunshi Cikin na Wata Budurwa wacce bata wuce Sa'ar Parveen bah, Sanye Cikin wani dan qaramin Skirt, da Riga Half vest. Tsaki Parveen tai ta Mike Tabar Falon Zuwa Dakinta.. Washe Gari da Safe Tana Idar da Sallah Tadau qur'aninta Tana Karantawa, Bude Qofan Dakin Akai Aka Shigo, ganin Yarima neh Yasa Tace "Sadaqallahul Azim" Ta Rufe Tareda Hade rai Tana Kallanshi Shima Fuskan Nashi a Hade Ya kalleta "Yau Zan Fita da Wuri, Ki Tashi ki Hadamin Breakfast, Sannan Babyna Plantain Takeso da Egg Yau. Idan Na Fita Kiyi Qoqari Ki Gyaramin Dakina Kafin nadawo" Bai Jira Cewarta Bah Ya Juya Zai Fita. Murmushin Takaici Parveen Tai Tace "Ai Baka Aje Yar Aiki bah a Gidan da Zata Maka Duk Wannan Aikin. Koh Ka Ajene ni Bansani Bah" Juyowa Yayi ya Kalleta Rai Bace "Ai Dake da Bayin Gidan nan Babu Maraba a Wajena, Duk daya Kuke. Dan Haka Ina Jiran Breakfast Nan da 1hour idan Bah Haka bah..kwafa Yayi Yabar dakin Tareda Bugo qofan Dakin" Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣0⃣ Ai Dake da Bayin Gidan nan Babu Maraba a Wajena, Duj Daya Kuke. Dan Haka Ina Jiran Breakfast Nan da 1hour idan bah Haka bah..kwafa Yayi Yabar Dakin Tareda Bugo qofan" Bin Kofan Parveen tai da Kallo, Murmushin Takaici Tayi Tareda Girgiza Kai. Saida Ta Gama Karatunta Sannan Ta Mike ta Nufi Kicin din. Cikin Mintinan da Basu Wuce Sha Biyar bah ta Fito dauke da Food Flask guda Biyu akan Tray. Kan Dinning ta Aje Ta koma Dakinta.. Wanka Tai Ta Shirya Ta dau Jakanta da Kyalle Ta Fito, Kicin ta Koma Ta Hado tea Ta dawo Palour Tasha Ta Maida Cup din Sannan Tadau Trayn ta dosh Hanyar Dakin Yarima. Knocking Tai Ta Shiga Da Sallama, Budurwar Ta Samu Zaune Tana Daddana Waya, Yarima Kuma Ya Fito knan Daga Toilet Daure da Towel daga Gani wanka Ya fito. Kallanshi Tai Tace "Ranka Ya Dade ga Breakfast din An Gama" Mamaki neh ya Kama Yarima Anma Ya basar, Kan Bedside Ya Nunama Alamar ta Aje, Bah Musu ta Qarasa Ta aje. Ta Kalleshi Tana wani washe baki kamar Doluwa "Ranka Ya dade Akwai kuma Abinda kake buqata??" Girgiza Mata kai Yayi. Ta Kalli Yarinyan dake Zaune Tace "A Fito Lapia Yan Mata" Dakin Tabari Dasauri Ta bar Side din Gaba Daya, Saida Taje ta Gaidasu Fulani da Mai Martaba Sannan Ta Shiga Mota Driver Yajata Zuwa School. A Hanya Neh Danladi Driver ke Fadamata Koranda Yarima Yama Sallau bayan Bulalan dayasa Amai. Bah Qaramin Baci Ran Parveen Yayi Bah, Tace "Dan Ladi Kasan Gidansh?" Kwarai Rank ya dade ai baida Nisa da Gidan Sarki" Nisawa Tai Cikeda Damuwa "Inaso idan Ka kaini Ka Wuce Gidan Kace Injini Nace Gobe Ya koma Aikinsa" Washe Baki Dan Ladi Yayi Dan Shi kanshi baiji Dadin Koranda Yarima Yama Abokin nashi bah. Godiya Ya soma Mata, Batace komai bah Har Suka Qaraso makarantan Ya ajeta Ya Wuce.. Saida yarima Ya Shirya Sannan Ya Xauna Bakin Gadon, Budurwar Ya Kalla Yana Murmushi. Serve Us please, Murmushi Tamai ta miqe Ta Dauko Trayn. Gabanshi Ta aje Ta dauki Plate Dake Cikin Trayn Ta Aje Sannan Ta Bude Food Flaske Din, Danyen Plantain suka gani a Ciki, An Yanyanka Ko Bare Bawon Ba'ai Bah, Dagowa Tai Ta Kalleshi suka Hada ido, Dayan Kulan ta Bude nan ma Danyan Kwai Suka Gani Guda Goma a Ciki... Ba Qaramin Baci Ran Yarima Yayi bah, Dashi Yayi Yana Huci Ya fita Zuwa Dakin Parveen, Banko Qafan Yayi ya Shiga, Bai Ganta Bah Yasa Ya Qarasa Toilet din, Nan ma Wayam, Duk inda Yake Tunanin Ganinta Ya Duba Batanan. Sai A Nan Ya tuna Jiya Sallau Yace Mai Tana Zuwa Makaranta. Bah Qaramin Kunya Yaji bah Wajan Budurwarshi, Hakanan Ya Bata Haquri Suka Fita Ya Saya Mata Breakfast Sannan Ya Ajeta Gida Ya Wuce Office.. Zama Yayi a Office Yana Tunanin Yanda Zai Bulloma Parveen, lallai Yarinyan Nan Ta Raina Min Wayo Zanko Yi Maganinta Kwanan nan. Mahdi neh Yayi knocking Ya Shigo Office din, Zama Yayi Yana Kallan Yarima "Yaya Akaine Yariman Duk duniya" Dan Yaqe Yarima Yayi "Lapia Anma Fah bah Lau bah" Tho Fah Lapia ? Meya Faru?? Furzar da Iska Yarima Yayi yana Kallan Mahdi "Am Sick and Tired of That Stupid Girl, Wallahi Wani Lokacin Har mamaki take bani Yarinyan nan. Duk hanyarda Zatai disgracing dina Yarinyan nan Tasani" Dan Murmushi Mahdi Yayi "Yariman Duk duniya. Har Yanzu kaqi bin shawaran dana Baka, Shawaran Dana Bakan neh Fah Dalilin Aurenta" Shiru Yarima yayi yana Kallan Mahdi, chan Ya nisa Yace "Kasan Banasan Raini, N Na Lura Yarinyan Tashen Rashin Kunya Take. Buh Are you Sure it wil work??" Gyada Kai Mahdi Yayi Yarima Ya daga Kafada "Shiknan Zan Gwada" Hira Suka Shiga Yi Har Lokacin Wardround Yayi Yarima Ya tashi suka Fita Daga Office din... Yau Da Wuri Parveen Ta Tashi, Waya Tama Danladi Driver Yazo Ya Dauketa. Tana Zuwa Gida Ta Fada Wanka, Ta Sauya Kaya xuwa Abaya Baki, Indomie ta dafa Taci Sannan Ta Wuce Side din Fulani. Hiransu Suketayi Kamar Yanda Suka Saba Har Wuraren La'asar. Parveen kwance Kan Cinyan Fulani Tana Shagwaba. Dariya Fulani Tai Tace "Niko Wannan shagwaba Naki Parveen naso inga Idan kinada Ciki Zaki Haihu" Hannu Parveen Tasa ta Rufe Fuska tana Dariya itama Fulanin Dariyan tai Parveen Ta turo baki Tace "Wallahi Fulani wani Gugun Lecture neh Ya bamu Assignment gashi da Wahala Wai Muyi Submitting Jibi, ni narasa Ta yanda Zanyi Assignment din" Fulani ta Shafa Kanta Har Ta bude baki zatai Magana Sukaji Sallaman Yarima, Fulani ce Ta Amsa ya samu Guri ya Zauna Fuskan nan a Murtuke.. Fulani Tace "Ai Shiknan mah Ga Yarima Kinsan shima Abinda Ya karanta knan" Nan da Nan Parveen Ta hade Rai, A Ranta Tace "Wallahi danasani daban Zami Wannan Course din bah." Mikewa Tai Tsaye Tace "Fulani Barinje Nai Girki" Fulani Tace "Shiknan Sai Anjima, Ki aikomin da Assignment din" Tho Parveen Tace Tabar Dakin... _kuyi manage da Wannan Bah Yawa_ Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣1⃣ "Shiknan Sai Anjima, Ki Aikomin da Assignment din" Tho Parveen Tace tabar dakin. Parveen na Fita Ya kalli fulani "Wai Fulani meh namiki neh?? Yanzu bakya Sona" Dan Murmushi Fulani Tai Tana Kallan Yarima "Meh ka gani Kace Haka??" Turo Baki Yayi baice Komai Bah Dan Dariya Fulanin Tai "Yau Yarima Shagwaban Neh Ya Motsa?? Kai Kayi Matarka Tayi" Hade Rai Yayi "Fulani Tunda Nai Aure kika Daina Sona meh nai miki??" Kan Fulanin Tai Magana Sukaji Sallaman Atika, Amsawa Tai Tareda Bata Umarnin Ta Shigo.. Rusunawa Tai Ta Kwashi Gaisuwa Sannan Ta mikama Fulanin Takardan da Parveen Ta Aiko Mata, Amsa tai Atikan Ta mike Tabar Dakin Dasauri. Yarima Fulani ta miqamawa Tana Kallanshi "Gashi Kaima Parveen Assignment din, Dan Naga Kaman Kunyan Baka Take" Hade Rai Yayi Ya Amsa Ya aje Gefenshi. Dan Allah Kai Qoqari ka Mata Wai Jibi Zasuyi Submitting" Tho Kawai Yace Ya miqe Ya dau Littafin Yamata Sallama Yabar Dakin... Shinkafa Da Miyan Kaji Parveen Tai, Sai Farfesun Kayan Ciki, Tana Gamawa ta Zuba Na Mai Martaba Taba Atika Takai. Daki Ta koma Tai Sallan Magriba Ta Fito, Abincin Ta zuba Taci Sannan Ta Kofa Falo Ta Zauna Tana Kallo. Yarima Bai Shigo Gidan bah Sai Bayan Isha, Kan Dinning Ya Zauna Yana Danna Wayanshi. Yi tai Kaman Bata Ganshi Bah Ta Miqe Ta Koma Dakinta. Saida Tai Karatu Sannan Ta Kwanta.. Yarima Koh Barci neh Ya Qauracema Idonshi, Safa Da Marwa Ya Dingayi a Falo, Tunanin Yanda Zai Bulloma Shawaranda Mahdi Ya Bashi Yake, Har wuraren Qarfe Biyu na Dare Yana Kishingide akan Kujera. Qishi neh Ya Tashi Parveen Ta Mike Zaune Tareda Hanma, Tsaki Tai Ta Sauka daga Kan Gadon Ta Fito, Wutan Falon a Kashe, Wutan Kicin ke Dan Hasko Falon, kicin din Ta nufa Tana Miqa Tareda Turo Baki, Fridge ta bude Ta dauko Goran Ruwa guda Daya ta Rufe Fridge din Ta Fito, Wutan kicin din Ta Kashe Ta Fito dan Komawa daki.. Jitai Tayi Karo da Abu, Shafawa Ta soma Yi taji Menene, Alamun Mutum Taji a Tsaye Kam, Aiko Ta koma da Baya dasauri Tareda Kwalla Ihu. Saurin Riqota Yarima Yayi ya Toshe Mata Baki, Bakinshi Yakai Saitin Kunenta "Keh Nine" Jin Muryan Yarima Yasa Ta Soma Kici Kicin Kwace Kanta, Qara Qanqameta Yayi a Jikinshi, Tureshi Ta Cigaba dayi da Iya Karfinta Anma Kaman Bata Tureshi. Lalubanta Ya somayi yana Qoqarin Daga Shimin Dake Jikinta. Wani Qarfi neh Yazo mata Ta Tureshi Da Qarfi Har Saida Yayi Qoqarin Faduwa ta Falla Dagudu Daki, Ita Kanta Batasan Wani Daki Ta Shiga Bah, Key Tasa Ta Koma Dabaya dasauri... Ganin bah Dakinta Baneh Yasa Taja Tsaki Tana Kallan Kofan "Allah Ya Isa, Mugu Kawai" Tsayuwa Tai a Bakin Kofan Na kusan Minti Goma, Barci neh Sosai a Idonta. Har takai bakin Gadon, Taja Tsaki Tana Yamutse Fuska "Allah Ya kiyaye Nahau Gadon da Aze Zina, Mtcw" Bakin Kofan Ta Koma tayi kwanciyanta Duk ta Takure Waje Daya.. Yarima Koh Tana Shiga Dakin, Ya Biyota Kamin Yakai har ta Kulle qofan, Naushin Tafin Hannunshi na Hagu Yayi "Damn It!" Falon Ya koma Yayi kwanciyarshi, Dakyar Barci Ya Daukeshi.. Kiran Sallah Ya Tayar da Parveen, Ta Mike Dakyar duk Jikinta Ciwo Yake, Rashin Saboda Kwanciyan Qasa. Har Takai Bakin Toilet din Ta Fasa Ta dawo ta Tsaya bakin Kofan, Jin Motsin Yarima Tai ya Bude qofan Falo Alaman Ya tafi Masallaci, Ta Bude Dakin Dasauri Ta fita ta koma Nata dakin ta rufe da Key. Toilet ta Shiga ta dauro Alwala Ta fito, Tana Idarwa Tahau Gado Dan Batasamu Barcin Kirki bah Da Daddare, BaTa Farka Bah Sai Karfe Tara, Dasauri Ta duro daga Kan Gadon Allah Yaso Karfe Goma Yau Takeda Lectures, Falo ta Fito Don Yin Breakfast, Har Tayi Hanyan Kicin Ta Hango Littafinta Databada Akaima Fulani Jiya... A hankali Ta Qarasa Tadau Littafin Ta bude, Wata Yar Paper Tagani a Ciki Da Rubutu Kai, Kujeran Dinning din Taja Ta Zauna Ta Dau Paper ta Fara Karantawa Kamar Haka: _Zama Gyne doctor Sai Mai Kwakwalwa Da Hazaqa, Mai Juriya Mara Tsoro. In Banda Rashin Azanci irin naki Ina Keh Ina Zama Gyne Doctor da Wannan Qwaqwalwan naki na Kifi. Kada Ki Taba Tunanin Zaki iya Kamoni Dan Nagaba Yayi Gaba Na Baya Sai Labari. Sannan Karki Taba Tunanin Abinda kikamin jiya da Safe Kinci Bulus, Ina nan Tafe da Nawa Sabon Rashin Mutumcin_ Chan Kasan Papern Aka Rubuta "Dr Fardeen Kabeer" Dan Murmushi Tai Ta koma Daki Tadauko Biro, Juya Papern Tayi Ta Fara Rubutu... Don Jin Meh Parveen Zata Rubuta Sai ku Kasance Dani Ummy Abduol Gobe da Safe Insha Allah.. Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤 👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣2⃣ Dedicated dis Page to *Umma Yahaya Musa (Sisin Mama)* Thnks For Ur lav n support.. Dan Murmushi Tai ta Koma Daki Tadauko Biro. Juya Papern Tayi ta Fara Rubutu kamar haka: _Bandamu da Ko nazama Gyne dr ko Karnazama Bah Yanzu, Saboda Jidani Abinda Ka Karanta Knan. Alhamdulillahi Tunda nasamu wanda Yafi Mahimmanci, Bandamu da saina Rami na nasara Bah. Kaga ko A Nan Nafika, tunda Ni Bah Wanda Ya Taba Ganina Da Wani namiji mun Riqe Hannu Ma Balle Har Yakaiga Abinda kai Kakeyi...Kae qoqari ka koma koda Islamiyan Zaure ne Kasan Banbancin Duhu da Haske Dan Har Yanzu a Cikin Duhu tsundum Kake_ Shiru Parveen Tai tana Nazarin Mai Zata Qaramai Wanda zai Kara Baqantamai Zuciya. Ganin Tana neman Yin Latti Yasa Daga Qasa Ta Rubuta "Princess Parveen Khaleed". Papern Ta ajiye a inda Ya aje Mata Littafin, Tai dan Murnushi Tabar Wajan. Tea Ta Hada Tasha a gurguje ta Fada Toilet Tai Wanka Ta Fito, tana Shiryawa Ta Fito ta nufi Wajan Motoci, A nan Taga Sallau, Sam Batama Ganeshi bah Saida Taji Yana Mata Godiya. Kallanshi Tai Cikeda Tausayawa "Karka damu Mallan, Yiwa Kaine" Hannu tasa Cikin jaka ta ciro bandir din Yan Naira Hamsin ta miqa Mai "Kayi Haquri da wannan Bah Yawa" Godiya ya Shiga mata, Tai saurin Dagamai Hannu ta Shiga motan suka bar gidan. Duk abinda ke Faruwa a wajan Fulani na daga Chan Wajan Side dinta tana Hangosu, Murmushi Tai Tareda Girgiza Kai.. Shiru Fulani Tai tana Tunani Watan Auren Yarima da Parveen Daya knan, Ta Qara Gane Halayan Parveen Nason Kyautatama na Qasa da Ita, Da Sauransu. Ta Lura Akwai Wanni qulaliya Tsakanin Yarima Da Parveen tun Bayan Auren da Kwana Biyu, Kallansu Kawai Take... Yauma Qarfe Biyu Suka Fito daga Lectures, Kiran Dan Ladi Driver tai Yazo Ya dauketa. Yasmeen Daketa Kallanta Tace "Parveen Tun Sanda Mukasan Juna Kullum Nake Ganinki da Damuwa, Gani nai Kamar ni Wacce Zaki Fadama Damuwanki neh dan Nabaki Shawara Nakuma Tayaki da Addua" Kallanta Parveen Take Tana Murmushi "Babu komai Yasmeen, Anma Idan ma Kika Tayani da Adduan Bakiyi Laifi bah" Shiru Yasmeen Tai Tana Nazari, Chan Saiga Drivern Gidansu Yasneem Ya Qaraso, Sukai Sallama Ta shiga Ta Tafi. Shiru Shiru dan Ladi Bai Zo Bah, Kiranshi Ta Qarayi Ya bata Haquri tareda Fada mata Motarce Ta Lalace Masa A Hanya.. Shiru Tai Tace "Shiknan Idan An Gyara ka Wuce gda Kawai ni narin nemi Taxi" Tho Yace Treda Kashe Wayan... Tunda Yarima Yaje Office Tunanin Yanda Zamansh da Parveen Yake A Cikin Gidan Kawai Yace, Yanzu Yarinyan nan Tafara Bashi Mamaki, Yanda Batada Tsoro Take Taranshi Ido da Ido Ta Zazzaga Mai Rashin Mutumci Tai Gaba. Tsaki Yayi tuna Akwai Ayuka Gabanshi, Files din Daka Gabanshi na Patients Ya Fara dubawa. Dafe Goshinshi Yayi da Hannu Daya "Oh Shit! Tunanin Stupid Girl din nan na Nema Ya Taba Aikina, yanzu gashi na Manta da Files din nan a gida" Mikewa Yayi Yadau Car key dinshi Yabar Office Din, Haraban Asibitin Yake ketawa Cikin Taku Na Qasaita, Hannun Daya Cikin Aljinunshi, Matan dake Wajan Sai binshi Suke da Kallo har ya Shiga Motarshi Ya Tada Yabar Asibitin. Yana Isa Gida Direct Side dinsu Ya nufa, Dakinshi ya Shiga Yadau Files din Ya Fito. Har Ya Wuce Dinning Din Ya dawo Yaga Ko Tadau Littafin, Ganin Papern Shi kadai Yasa Ya Qarasa Wayan Yadau Papern Yana Dubawa... Abinda Ta Rubuta Yaci Karo dashi, Gyara Tsayuwa Yayi ya Karance Shi Tsaf, Ransh ne Ya Baci. Lalai Yarinyan nan na Qorarin qureshi. Wurgi Yayi da Takardan Ya Bar Falon A Fusace... Bai Dawo Gidan Bah Sai Bayan Isha'ai, Yana Shigowa Gidan Yayi Parking Motarshi Ya Fito. Sallau ne Ya Tareshi Yana Mai Sannu da Zuwa, Da Mamaki Yarima Ya Kalleshi "Meh ka Qara dawowa yi gidan nan??" Nan da Nan Jikin Sallau yadau Rawa dan Yasan Halin Yarima, Daidai Nan Parveen Itada Atika Sunzo wucewa Zuwa Side Din Fulani, Dan An Aiko Mata Batajin Dadi. Jin Abinda Yariman Ke Cewa Yasa Ta Qarasa Wajan Dasauri "Ni Nasa Ya Dawo Saboda banga Dalilin Koransh Bah" Juyawa Yarima Yayi Yana Kallanta Ido Cikin Ido "Akan Wani Dalili?? Har ni na Kori Wani Banza Talaka Ki Dawo Dashi. Koh Nan Masarautar Ubanki neh" Ranta Neh Yayi Mugun Baci, Ta kalli sallau Tace "Jeka Abinka" Rusunawa Yayi Ya Mata Godiya Yabar Wajan Atika Na Ganin Yabar Wajan Itama Tai Saurin Barin Wajan.. Kallan Yarima Parveen Tai Ranta Bace, Nan Bah Masarautan Ubana Baneh kamar Yanda Ka Fada, Anma Ka Sani, A Namu Masarautar Ansan Mutumci da Darajan Dan Adam. Kuma Dawowa Ya Dawo Knan, Kai Baka Isa Ka Koreshi Bah. Nunashi Tai da Dan Yatsa, Zan Zauna a Masarautarku Nakuma Fika Iko da Masarautar. Hannu Ya daga Zai Kai Mata Mari Sukaji Muryan Fulani, Qarasowa Wajan Tai Dasauri Tana Kallan Yarima Rai Bace "Karka Kuskura Hannunka Yakai Kan Kuncinta, idan Kuwa Yakai Ni dakaina Zan Rama Mata. Dama Yarima Dalilin Auren Nata kenan Kaci Mata Mutumci?? Duk Abinda Ke Faruwa a Gidan nan Atika Na Kawomin Labari Sharewa Kawai Nake" Nagode Sosai Ka Kyauta. Hannun Parveen Taja Suka Bar Wajan. Mutuwan Tsaye Yayi Ya Bisu da Kallo Har Suka Bar Wajan. Dukan Motan Yayi Rai Bace Yabar Wajan, Suna Shiga Side din, Fulani Ta Kalleta "Ki Cigaba da Hakuri Parveen, Nidai Bazan Rabaku Bah. Nasan Watarana Sai Labari kinji" Dan Murmushi Parveen Tai Kanta Na Qasa "Bakomai Fulani, Dama Nazo neh Naga Jikinku. Dazu Atika Take Fadamin Bakida Lapia" "Naji Sauki, Dama Dan Ciwon Qafa neh Kuma Yayi Sauki" "Allah Ya Qara Sauki" Fulani ta Amsa da "Ameen" Shawarwari Fulani Ta Dinga Bah Parveen Akan Yanda Zatai Hakuri Ta Zauna Da Mijinta, Sun Dade Tana Mata Nasiha Sosai sannan Tai Mata Sallama Tabar Side Din itada Atika. A Falo Suka Tarar da Yarima Kan 1seater Fuskan nan Yayi Jawur, Yayi Crossing Kafa Yanata Kad'a Na Saman, Alamar Ita Yake Jira... *Kuyi Manage da Wannan Banida Chargi neh dts Y" Ummy Abduol✍🏻 Ϥ🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣3⃣ A falo suka tarar da yarima kan 1seater fuskan nan yayi jawur, yayi crossibg kafa yanata kad'a na saman Alamar ita yake jira. Atika ta kalla taimata nuni data tafi, bah musu tabar falon. Kauda kai Parveen tai ta nufi dakinta batareda ta kalleshi bah. Tsawa ya daka mata cikin daga murya "Baki kai bah kinyi kadan, kamar ni yarima fardeen kisa fulani ta kusa Marina. Tashi tsaye Yayi ya qaraso inda take yana kallanta, who du uh tynk uh are?? Answeer mie!" Kallanshi tai ba Alamr tsoro a idonta "Ni bah kowa bace, kamar yanda kake ba kowa bah. Ni almajira ce kamar yanda kake almajiri, Haka zalika ni Talakace kamar yanda..." Saurin katseta yayi cikin daga murya "Ashe ilimin addinin naki na banza neh tunda baki san Yanda zaki daraja mijinki bah, Duk da kince ni jahili neh a dan a Cikin jahilcin nawa nasan Aljannar nace na qarqashin kafar mijinta, sai ya daga zata shiga" Dariya Parveen tai sosai tana kallanshi "Dan Allah idan kaine kesawa a shiga Aljannan idan nazo ka rufe kace ban shiga" mugun Kallo Yarima yabita dashi "Banida ikon na hanaki shiga Aljanna idan har Allah ya rubuta hakan, Ya nunata da dan Yatsa. Anma kisani tun daga ranar da aka daura mana aure kike cikin tsinuwar mala'iku, Knan ilimin naki da kike tinqaho dashi na banza neh tunda baki aiki dashi" Dogon Tsaki Parveen taja ta harareshi tabar falon dsauri zuwa dakinta.. Kwafa Yarima yayi shima ya nufi dakinshi a Fusace. Kwana Parveen tai tana browsing assignment dinta, sai gab da asuba ta gama ta kwanta. Gogan ko Yana dakinshi, juyi yake tayi ya kasa barci, Gashi duk yayi fada da yanmatan nashi. Kuma shi a tsarinshi baya bah Mace haquri saidai ya nemi wata, dakyar Ya samu barci ya daukeshi cikeda Tunanin Rigimarsu da Parveen... Ana kiran sallah ta tashi ta fada toilet, dan yau karfe bakwai takeda lectures. Wanka tai tareda dauro Alwala ta fito, tana idarwa ko hijabin bata cireba ta fito ta shiga Kicin ta fara Kiciniyar daura Breakfast. Arish ta fere ta Soya, Sannan ta soya kwai. Tana gamawa ta daura ruwan Zafi ta Dama kunnun gyada dan Yau shi take Sha'awan Sha, Tana Gamawa ta jeresu kan dinning ta koma daki ta shirya ta fito. Zama tayi tai breakfast dinta ta gama Sannan tadau jakanta da litatafanta, Har Takai Kofan fita daga falon tajiyo muryan Yarima ta bayanta "Were du uh think ur Going" Ba tareda ta kalleshi bah "School" Dan murmushin Mugunta Yayi Ya jingina da Bango Yayi folding Hannuwanshi "Da Izinin Wah??" Ganin yana neman Bata Mata Lokaci Yasa Ya juyo tana kallanshi "Da Izinin Mai Martaba" Daga Gira Yayi Yana Kallanta "Oh Mai Martaba ke aurenki koh Ni" Agogon Hannunta ta duba, 6:45am. guntun Tsaki taja "Mallan ur Wasting my Time, Inada Lectures karfe bakwai" Dinning ya nufa ya nemi guri ya zauna "Stop wasting ur time, bah inda zaki Yau. Come and Serve me pls" Idonta neh Ya Ciko da Kwalla, ta Dake Ta qi koh Motsi. Wayan dake Hannunshi Ya soma Dannawa, Sundau Kusan Minti Biyar a Haka. Chan Ya nisa Yace "Idan kuma kisano kije ga Hanya nan, Sai kiyi anfani da Ilimin da kikace Kinadashi ki Gani menene hukuncin Macenda Ta fita bada Yardar mijinta bah". Tsaki Taja Ta nufi dakinta a Fusace Murmushin Mugunta Yarima Ya Saki Ya fara Serving kanshi... Kuka Parveen ta Fashe Dashi, Wai mai Yarima ke Qoqarin Maidata neh. Agogo Ta duba Taga karfe bakwai Daidai, Wayan Yasmeen Ta soma Kira Cikin Sa'a kuwa ta Dauka "Parveen ban Ganki bah, Yanzu na shiga class. Kin yanzu lecturan nan zai shigo" Jim parveen tai "Bazan samu zuwa bah yasmeen banda lapia." "Assignment din fah?? Ko shine kizo kiyi submitting inyaso sai ki koma" Ajiyan zuciya Parveen tai "Bazan samu zuwa bah yasmeen, zandai bah drivern dake kawoni sai ku hadu a nan inda yake daukana ki amsa ki tayani submitting pls" "Bah damuwa. kodai dan babane ke wahalar dake" Dogon tsaki Parveeb tai, "Allah ya shiryeki Yasmeen" Bata jira me zatace ba ta kashe kiran. Wayan danladi driver ta fara nema ta fadamai sakon anma tace ya bari sai kaman karfe takwas yazo. Amsawa yayi ya kashe kiran... Bakwai da rabi Yarima ya gama shirinshi ya fito dan Zuwa Asibiti. Dakin Parveen ya kalla ya saki Lallausan murmushi tareda Kwafa, Yadau Jakan Laptop dinshi Ya Fita. Dogarinshi Ya gani bakin kofa yana jiransh, dasauri ya rusunna yana kwassan kaisuwa. Kyada kai kawai yarima yayi, dogarin yayi saurin amsar jakanshi ya soma binshi a baya... Yini Yarima yayi Cikeda tunanin anya Abinda yama Parveen ya dace?? Guntun tsaki yaja a Fili yace "Wai meyasa nake Yawan tunanin Yarinyan nan??" Wata Zuciyar Tace "Santa ka Fara" Dogon Tsaki Yaja, Daqarfi Ya furta "God forbid Allah kiyaye. Nadaisan ina Sha'awarta" Iska ya furzar Tunanin yanda zai bulloma Parveen ya shiga yi, Yadau kusan minti sha biyar yana abu daya. A hankali ya sauke wani lallausan murmushi ya mike yadau Wasu Files ya fita... Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣4⃣ A Hankali ya sauke wani lallaudan murmushi ya mike yadau wasu files ya fita. Yarima na fita parveen taima danladi waya yazo ya amsa sakon ya yafi. Kwanciya tai barci ya dauketa dan dama da daddare batasamu barcin kirki bah. Bata tashi ba sai wuraren karfe daya da kusan rabi, Tashi tayi ta fada toilet tai alwala ta Fito. Tana idar da Sallah ta jiyo knocking a kofar Falo, Ta tashi ta fito ta bude. Ihu parveen ta saki Cikeda murna. dasauri Deeza ta qarso tareda rungume parveen "Deeza Wannan Suprise??" Dariya deeza tai Tana Kallan Parveen Hannunta ta kama suka shiga Ciki, Kan kujera suka baje Parveen na cigaba da mamakin Ziyaran bazatan da Deeza ta kawo mata.. "Bae na dauka zanzo na sameki Kina Amai ai" Dukan wasa Parveen ta kaimata "Allah ya kiyaye, keh kina tunanin zan haihu da Yarima neh??" Girgiza mata kai deeza tai "Bai kamata kina irin furucin nan ba bae, komin lalacewarshi mijinki neh. Yakamata ki rinka furuci masu kyau akanshi" Dogon tsaki Parveen tai ta yamutse fuska tareda kauda kai "Deexa knan, koh kinsan Yarima har neman mata ya..." Saurin rufe mata baki deeza tai tana Girgiza mata kai "Sirrinki neh parveen bai kamata kina gayama kowa bah. Nifa laifinki nake gani bae" Kallanta tai da mamaki "Kamar ya??" Gyada kai tayi tana cigaba da kallanta "Kwarai kuwa, haba bae sai kace ba mace bah. Keh zaki sa ya daina neman mata, look lemme tl uh zaki iya juyashi yanda kikeso kece dai in baki so bah" Murmushin takaici Parveen tai tadau jakan deeza tana cewa "I hope wata zakimin" Bude baki tai da mamaki "Wata?? Haba dai sai kace mara hankali. Jibi ran sunday insha Allah zan koma" Tsuke fuska parveen tai "Haba wasa kike yarinya. Tashi mu shiga Ciki" Sun dade suna hira har akai Sallan la'asar sannan suka shiga kicin dan daura girki. Suna girkin take bah deeza labarin hanata zuwa schl dinda yarima yayi... Dariya kawai deeza tai batace komai bah, har abin yaso bah Parveen haushi. Bayan magrib Yarima ya shigo gidan, Lokacin sun zaune kan dinning suna cin abinci, Jin hayaniya yasa ya qaraso wajan dinning din da sallam, Deeza ce ta amsa tareda gaidashi. Da fara'a ya amsa tareda tambayanta tazo lapia, Ta amsa da lapia lau. Dakinshi ya wuce kai Tsaye. Deeza ta kalleta "Ya dawo baki kai mai abinci bah" Tsaki parveen tai ta cigaba dacin Abincinta "Keh fa matsalata dake knan bae, Bai kamata bah abinda kikeyi. Kada ki biye halinshi ko kin manta maganan da mukai dazu" Mikewa deezan tai ta shiga kicin ta hado abinci a tray ta ajema parveen a gabanta "Pls tashi ki kai mai" Turo baki tayi "Nifa indai abinda ya kawoki knan gwara gobe da sassafe ki kom gida. Nifa da kika gani bana shiga dakinshi, yanzu idan nakaimai saiya raina ni" Kafadanta ta dafa "Bah wani raini bae, Kiyi qoqari ki gyarashi zaki samu lada, ina miki kwadayin ladan da zaki samu nan gaba neh".. Turo baki parveen tai ta mike tareda daukan Trayn har ta doshi dakin deeza tace "Ki Tambayeshi akan maganan zuwa gaida fulanin" Batace komai bah ta qarasa dakin, Bata tsaya knocking ba ta tura qofan ta shiga kai Tsaye. Har ya zame towel dinda ke Jikinshi yana qoqarin sa Kaya ta shigo, Ihu ta Saki Tareda rufe idonta, ta saki trayn ta fita dsauri. Dariya Sosai ta bashi, Kayan Ya qarasa sawa Ya zauna bakin Gadon Yana cigaba da dariya.. Qanqame Deeza tai idonta a rude tana ihu, rufe mata bakin tai Tana jijigata "What?? Menene??" Sakin ta tayi ta ruga daki dagudu. Girgiza kai Kawai tayi ta zauna tacigaba dacin abincinta. Gado parveen ta fada tana maida numfashi, Ganin Surar Yarima tayi cikin idonta. Dasauri ta qara rufe ido tana Turo baki. A Hankali ta furta "Allah ya isa ban yafe bah" Kwanciyanta tayi tana chating har deeza ta shigo. "Wai wane irin abu wannan parveen??" Tashi tayi ta zauna tareda hade rai "Allah ya isa deeza, kin cuceni Wallahi. Gashi kinsa naje..kasa qarasawa tai ta ja tsaki" "Nidai yanzu kin tambayeshi maganan Zuwa gaida Fulanin" "Nifah karki dameni deeza, bazan koma dakin nan bah" cewar Parveen Tsaki deeza taja ta mike "Natafi Kallan Players a bollywood" Wup Parveen ta tashi tana washe baki "dan Allah dagaske??" Batace mata komai bah ta bar dakin, itama binta tayi zuwa Falon. Zama sukai suka soma kallo bah wanda ya qara cewa kowa komai, chan sukaji bude kofar dakinshi, ya fito ya qaraso falon. Parveen ya kalla Fuskan nan a daure "Hu wil clean up dah mess" Tsaki taja ta mike dan tasan zai iya dizgata a gaban deeza. Dakin ta shiga ta soma tattara wajan, tana gamawa ta dawo ta tarar dashi zaune a falon sunata hira da deeza kamar dama sunsan juna. Guntun tsaki taja tana kallan deeza "Ni natafi na kwanta" juyowa tai tana kallanta "Bazaki tsaya ki qarasa kallan bah??" Girgiza kai tayi alamar Aa Harta juya taji muryan Yarima yana cewa "Tashi to kuzo muje ki gaida fulanin sai naraka ki koh" Parveen ta qarasa daki ta zauna bakin gado, deeza ta shigo tana kallanta "Tashi muje pls ya rakamu, kinga ma dare ya soma" Dakyar ta lallaba parveen ta mike tasa hijabi suka fito. A hanya Deeza da Yarima sai hiransu suke parveen ko ta hade rai tana bayansu suna gaba.. Tare suka shiga side din da yarima, deeza da parveen suka zauna kan Carpet tareda gaida Fulani, Parveen ke fadama Fulani wacece Deeza a wajanta. Ta Taresu dakyau sun dade suna yarima ya fito falo ya zauna yana kallan news, Sai wuraren sha daya suka baro Side din, Kamar dazu hiransu sukaitayi suka barta a baya, Haushi abin ya bata sosai. Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu.. Tho fah kodai Parveen kishi take🤔?? Ummy Abduol✍🏻 🏤🏤🏤👑 *A WANI MASARAUTA* 🏤🏤🏤👑 By *Ummy Abduol* Page2⃣5⃣ Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu.. Ganin ran parveen ya baci yasa tama Yarima sallama ta shigo dakin. Kayan barci tarar parveen nasawa, ta qarasa ta zauna bakin gadon tana kallanta. "Lapia?? Naga ranki ya baci" Aiko kamar jira take tako hayayaqo mata "Ina ruwanki dashi?? Menene hadinki dashi?? Kin wani barni ni kadai kinata wani washemai Baki waike kuna hira" Dariya sosai abin yaba deeza, ta dade tana dariya hakan yasa parveen ta qara quluwa. Saida Ta gama Sannan ta Kalleta "Parveen kishi??, Ana cewa ba'asan yarima anma gashi ana kishinshi" Tsaki parveen taja tana yamutse fuska "Allah ya kiyaye nai kishin yarima. I hate him!" Dan murmushi deeza tai "Umm zakizo kiban labari".. Pillow parveen ta wurga mata "Banasan iskanci deeza, Bakisan yanda na tsani guy din nan baneh" Shawarwari deeza ta dinga bah Parveen Har barci ya daukesu.. Da Safe suna Kicin yarima ya leqo, Murmushi deeza tamai Sannan tace "Morning" Morning shima Yace Yana Kallan Parveen, Fuskanshi bah yabo bah Fallasa Yace "Haba Amarya bah Gaisuwa" Dagowa tai ta kalleshi da mamaki Gira ya daga mata, tai saurin kauda kai tareda hade Rai "Good Morning" Kintashi Lapia??" chewar yarima Batareda ta kalleshi bah tace "Lapia" Deeza ya kalla Yana yar murmushi "Frnd idan kun Gama ki Shirya xan kaiki yawo tunda yau saturday" Murmushi tai tana Kallanshi "Thank you very much Frnd" Baice komai bah Yabar Kicin din. Tsalle Deeza tai Tana cewa "Woaw! Kamar yasan abinda nakeso knan, Allah yarima nada kirki. Kece dai baki gane hakan bah" Dogon tsaki Parveen taja tacigaba da abinda takeyi. Murmushi Deeza tai tareda girgixa kai.. Suna Gamawa Deeza ta shirya Ta Kalli Parveen, pls ki tashi muje. Mugun Kallo ta bita dashi tareda jan tsaki "Bah inda zani, keh dai da kike uwar yawo sai kin dawo" Bah Yanda Deeza bataiba Akan Parveen tabisu taqi, Hakana ta haqura suka Fita itada Yariman. Yawo yakaita Sosai, Sun jaje wurare dayawa, dan Zaman da Yayi da Deeza ya samu Labarin parveen sosai da Halayenta. Basu dawo gidan bah Sai Qarfe tara na dare, kwance suka samu parveen kan 3seater har ta soma barci. Dagudu deexa ta qarasa inda Parveen take tai tsalle ta fada kanta.. Ihu ta saki tareda tureta, Dariya Sosai Abin yaba yarima yabar Wajan zuwa daki yana cigaba da dariya "Yarinya sai Rashin kunya ga shegen Tsoro" Tsarabanta Deeza ta bata, taqi amsa, saida tace mata da kudinta ta siyan mata sannan ta amsa tana dubawa. Abinci ta hada takai mai daki, Wannan karan knocking tai, saida Ya bata izini Sannan ta shiga, Gabanshi ta ajiye Ta juya zata Fita. Muryanshi ta jiyo yana cewa "Were are you going bayan mijinki na buqatarki a kusa dashi" Qarasawa tai Zata bude kofan taji yace "Haba Mallama uwar Malamai, Koh kin manta Malaiku na Tsinewa Macen da ta qauracewa Shinfidar mijinta" Juyowa tai tana Kallanshi gabanta na dukan uku uku "Nibah Malama bace, Har yanzu ni daluba ce. Bana tutuiya da ilimin danake dshi, bah kamar kai da kake iqirarin wani bazai iya karatun dakayi bah." Murnushi Yayi yana Kallanta "Bah Wannan na tambayeki bah" Tsaki taja tana kallanshi ido cikin ido "Kada ka Taba Tunanin taraiya dani a rayuwarka, Allah ya kiyaye. Mutumin da yagama zina da matan arna yace yanzu kaizo gareni, Allah ya kiyaye" Bata jira mai zaice bah tabar dakin dasauri.. Murmushi kawai yayi tareda girgiza kai, Baisan meyasa bah yanzu sam Maganganun Yarinyan basa batamai rai, Saima burgeshi datake Yanda take tsayawa a gabanshi tana fadamai maganan da ranta yake so. Kofan ya kalla tareda yin kwafa ya koma ya zauna... Washe gari deeza zata koma, Sam Parveen bataso haka bah. Tun da safe take qunci, Taso ace ta Qara mata koda kwana biyu neh anma Taqi, Hakanan ta Haqura. Da zata tafi parveen harda dan kukanta, Side din fulani ta rakata tai mata Sallama suka fito. Taso raka Aminiyar nata anma jin Yarima neh zai kaita Airport yasa Ta Fasa sukai Sallama tashiga motan suka tafi.. Side dinsu ta koma Cikeda kewar aminiyar nata, Yarima na kaita tasha Ya juyo ya Wuce Gidansu Mahdi. Yakoci Sa'a Yana Gida, Hira sosai suka shiga yi har suka gangaro kan maganan Parveen "Yadai mutumina Ina fata komai ya wakana" Girgiza kai Yarima yayi "Bbu komai mutumina Wallahi, ni Har mamakin kaina nakeyi. Narasa yanda zan tari yarinyan nan, tanamin kwarjinin dayawa" Dariya Mahdi Yayi "Haba Yarima bansanka da Tsoro bah, yanzu kasan meh za'ayi??" Girgiza kai Yarima yayi kallanshi Tashi mahdi yayi ya qaraso inda yarima keh zaune, magana yamai a kunne wanda ni kaina bansan meh ya fadamai bah. Kallanshu Yarima yayi "Are you sure hakan zaiyi?" Gyada kai mahdi Yayi "Kwarai kuwa mai zai hana" Sun dan jima Suna hira Sannan yarima yamai Sallama yabar Gidan... Ummy Abduol✍🏻